"Hannun Shattima yaji bisa kafad'unsa, da sauri ya juya yana dubansa, dubansa Shattima ma yayi har lokacin hannunsa naga kafad'ar Jalal,.
"Murya cike da Al'ajabi Shattima yace " Ina ka sami wann mark d'in..
"D'an murmushi Jalal yayi kafin yace " I was born with it...
"Shiru Shattima yayi sai k'ura masa idanu da yayi, don kuwa ya tuna akwai lokacin da coincidence yaga irin wann tabo exactly a kafad'ar mai Marta wani rana yana sanye da 'yar shara suna hira da Shattima irin na d'a da mahaifi dukda bashi ya haifesa ba, ya tuna Mai Martaba ya basa labarin wann tabo da ya gani a gefen kafad'arsa cewa, babu wani sarki a masarautarsu Face yanada wann shaida, ..... Sosai ya k'ura ido yana k'are wa shaidar kallo batada maraba dana Mai Martaba.... Muryar Jalal ne ya dawo dashi daga duniyar tunanin da ya tafi...
"D'an dafa kafad'ar Shattima Jalal yayi kafin yace " Don't get wrong idea nasan zakayi tunanin k'ila tatu ne nayi ko, to ba haka bane, I'm a good Muslim nasan babu kyau yin tattoo, Believe me I was born with it, yanda ka gansan nan..
"D'an murmushi k'arfin hali Shattima yayi kafin yace " Kayi alwalan ka I'll make some coffee, it will help you...
"Gyad'a kansa kawai Jalal yayi kafin ya shige bathroom...
"Gaba d'aya jikin Shattima yayi sanyi, kai wani babban Al'amari na shirin faruwa dashi,...
*************
"Washe gari tun ida sallahan asuba suka nufo suleja, to their greatest surprise Dr Khaleesat is there too, tana ganin Jalal ta sakar masa murmushi tace " You can go through this, don't worry kaji, we would find her...
"Murmushin k'arfin hali kurum ya sakar mata ba tare da yace komai ba..
"Annah ta rungumesa tana maida hawayen da ya kufce mata, Murya na rawa Jalal ke fad'in" Annah I couldn't find her, what if something bad happens to her, I'll never forgive my self...... Shigowan Hamma Habibu da Hadiza ne ya katse su don dama sunji tsayuwar mota...
"Kai tsaye hannun Jalal ya k'arasa ya rik'e yana fad'in" Jalal ka samo mun k'anwata, ka samota koh, nasan kai kad'aine zaka iya kular min da ita, ka fad'a min ka samota tana cikin k'oshin lafiya, idan wani abu ya sameta Inna da Baffah zasu gani daga makwancin su koh, zasu ce ban kula da ita ba ko,........
"Tausayi ya cika illahirin zukatan mutanen dake wajen.
"Hannayensa Jalal ya rik'e gamida zaunar dashi saman dakalin dake a veranda d'in kafin yace " Ka kwantar da hankalinka Hamma, I promise I'll find Zubaidah where ever she's, nayi alk'awarin zan samota duk yanda take da izinin Allah koda hakan zai zama sanadin rasa rayuwata, ka kwantar da hankalinka Zubaidah bazata so ganin hankalinka a tashe ba, kayi mata addu'a kaji...
"Haka Hamma ya ringa gyad'a kansa yana goge hawayensa da riga tamkar k'aramin yaro.....
"Kaman daga sama sukaji wayar Annah na ringing, Hadiza tayi saurin shigewa d'aukar wayan don Annah kam bataci ta kula waya ba.
"Jin muryar Zubaidah cikin wayar yasata fitowa da sauri tana fad'in itace Zubaidah ce.....
"Daga d'aya b'angaren kuwa Zubaidah cewa take " Ki bani Annah da Hamma na,..... Daidai sanda Annah ta fizgi wayar, Jalal kam mutuwar tsaye yayi yana binsu da Kallo.
"Daughter where have you been, we were all worried about you, Annah tace cike da nuna damuwa...
"D'an jim Zubaidah tayi duk sai taji babu Dad'i, Annah bazataji dad'in abunda tayi ba, despite all her efforts on her. A hankali take fad'in" Annah ina nan lafiya shiyasa ma na kira na sanar daku don kar ku damu, I just want some space ne, I'll come back to you soon, ina Hamma na.... Ta k'arashe a hankali.
"Annah bata iya furta komai bar, sai manna wayar a kunnen Hamma Habibu da tayi....
"Shida baya tareda su ya tafi duniyar kuka jin muryar Zubaidah a waya yasa sa mik'ewa zunbur yana murmushi,
"Zubaidah, Zubaidah na, Zubaidahn Baffa da Inna, ina kikaje.... "Jalal ya damu dake..... Gaba d'aya suka dubesa jin statement d'insa...
"Hamma yaci gaba da fad'in" Nima na damu dake, Don Allah ki dawo garemu kinji k'anwata, duka muna sonki, muna sonki....
"Share hawayen da ya zubo mata tayi kafin tace " Nima ina sonku Hamma, zan dawo kwanan nan kaji, kar ka d'aga hankalinka idan ba haka ba kuma bazan dawo ba, ka kwantar da hankalinka kaji.....
"Muryar Jalal taji cikin wayar yana fad'in" pls come back, if you want I'll leave the house, but pls don't put your self in danger, Hamma is worried so much about you, ki dawo don Allah ko kuma ki fad'a mun yanda kike, I'll get you right a way....
"Cike da masifa take fad'in" I won't listen to your lies again, I hate you even more, snn kar kayi tunanin zan dawo nan kusa, and lastly don't you dare involved police idan ba haka ba, wllhi kaji na rantse I'll leave you all for good, snn bazan dawo ba...
"Yanajin sanda tayi tsuka ta kashe wayar.....
"A hankali yana mai lumshe ido ya k'arashe da " I love you.... Be safe dear.......
"Gaba d'aya suka k'ura masa idanu cike da tausayawa.
"Dr Khaeelsat tace yi mun dialing number d'in, babu musu ya sake dialing amma sai jinta yayi a kashe, a sanyaye yace " is switch off..!!
"Gyada kanta tayi kafin tace let's talk private, babu musu yabi bayanta...
*************
"Mik'a ma Zulaihat wayar tayi tana mai zama bisa sofa ta shiga share hawaye, Zulaihat ta dafa ta kafin tace " Meyasa bazaki koma ba, suna sonki, you're so lucky da kika sami family haka masu sonki da yawa ta k'arashe zancen sanda take cire sim d'in da zubaidah tayi amfani dashi don dama extra sim d'inta ne wanda take solo ma Alhazawanta dashi, ..
"Girgiza kai Zubaidah tayi kana tace " No bazan koma ba, snn ko zan koma sabida mutane biyu ne, Annah da Hamma na, su kad'aine basa min k'arya...
"Zulaihat ta sauk'e ajiyan zuciya kafin ta mik'e tana gyara mayafinta tace " Okay ni zan fita breakfast na kitchen, ki shiga kici duk abinda kike so, zaki iya kulle gidan gaba d'aya.
"Gyad'a Kai Zubaidah tayi kafin ta dubi Zulaihat tace " Na gode, thank you for your kindness.
"Gajeren murmushi kawai Zulaihat tayi kafin ta suri jakarta tace " See you soon.
"Window Zubaidah ta k'araso tana lek'en Zulaihat da Imam, Imam harda mata murmushi da waving, bata kulasa ba sai sauk'e labulen da tayi ta k'arasa ta rufe k'ofar parlorn....
*************
"Annah dasu Jalal harma da Dr Khaleesat suka ja gefe suna tattauna lamarin bayan Dr sun gama ganawarsu da Jalal, ,
"Shattima yace " Nifa ina ganin we should report that to the polic, the earlier the better...
"Girgiza kai Jalal yayi kafin yace " Tace muddin mukayi reporting bazata dawo ba,.
"Are you sure babu wanda ta sani ko a cikin Abuja ne, Dr Khaleesat ta tambaya.
"Da sauri Annah ta kuma d'ago kai ta dubi Shattima, ta tuna kwanaki ya kawo masu budurwarsa, cikin sauri ta k'arasa gabansa tace " Kai kuwa ina yarinyar da kazo da ita kwanaki gidan nan, matar da zaka aura don ban mace ba haka ta fad'i mana, ita kad'ai Zubaidah ta sani me yuwa gidansu taje...
"Jalal yayi saurin mik'ewa yana recalling tabbas anyi haka...
"D'an jim Shattima yayi harga Allah Ya mance tare suka zo da Zulaihat amma ta ya ta zama matar da zai Aura, rabonsu da waya ma yana ganin tun wancan lokacin ne, k'ila ita tace masu haka knn...
"Da sauri ya furta "Zulaihat, Annah ta gyada kai tace k'warai...
"Kan kace Me Jalal ya fuzgo hannun Shattima yana fad'in" Muje pls take me to their house....
"Wait Jalal wllhi bansan gidansu Zulaihat ba, ban tab'a zuwa ba...
"Wani mugun kallo Jalal ya watsa masa kafin yace " Matar da zaka aura d'in ne baka san gidansu ba,
"Matar da zan Aura..? Shattima ya maimaita.
"Annah ta gyad'a kai tace "K'warai haka tace mana,.
"D'an girgiza kai kawai Shattima yayi kafin yace " Wllhi ko gidansu ni bansani ba........ Baikai aya ba Jalal ya shak'ure masa wuya yana fad'in" K'arya kake, then why did you bring her here, meyasa ka kawota nan.... Usman yayi tsalle yana k'ok'arin ceton Shattima...... Annah ta tafi da sauri tana Janye Jalal....
"Da k'yar aka k'waci Shattima daga mak'uran da Jalal ya masa....
"Janye hannun Jalal Annah tayi suka wuce d'aki rai b'ace...
"Ni bansan yanda zaka kai wann zuciyar taka ba, haba haba Jalal, idan kayi haka me kake tunanin Habibu zaiyi, You always let your temper get the best of you, kamata yayi ka nustu musan abin yi, idan neman Zulaihat d'in za'ayi sai ayi, and wnn yaro da ka masa haka bai deserving haka ba, he's here to help he cares about you, me kake tunanin Usman zaiji .
"D'an shiru yayi amma har lokacin huci yake a hankali ya furta " I'm sorry Annah....
"D'an dafa kafad'arsa tayi ta sassauta murya kafin tace " Son I know this is difficult for you, it hurts me ganinka a wann condition d'in, but we all need to remain steady, akwai mutanen da suka fimu rauni cikinmu, think about her brother abin yayi affecting d'insa sosai, pls kayi composing kanka kaji Son, and Dr Khaleesat bazataji dad'i ba regarding what you did earlier, tashi muje and apologize to them...
"Gyad'a kansa yayi kafin ya mik'e jiki a sanyaye..
"Gaba d'aya basuji zafin abinda yayi ba, saima tausaya masa da suka yi, Shattima ya dafa sa kafin yace " I know exactly how you feeling, and I'm willing to help Jalal, na kira wayan Zulaihat munyi magana tace " Zubaidah bata wajenta, but she sounds very wired like something is wrong with her, batayi rawan kan nata data saba ba, she was quite strange , the best abu shine mu fita mu nemi resident d'inta...
"Gaba d'aya sunji Dad'in shawarin Shattima, Jalal ya d'an dafa kafad'arsa yace " I'm sorry again Shattima, murmushi kawai yayi yace " That's what bothers are for, let's get going the earlier the better...
"Gaba d'aya suka gyad'a kai, Dr Khaleesat ma Office tace zata wuce ganin k'arfe takwas tayi snn tace " suyi keeping nata update duk abinda ake ciki, a tare suka fice, Dr Khaleesat ta nufi motar ta yayinda Su Jalal suka wuce Ride d'in Shattima...
***********
*Sheraton Hotel, Abuja*
"Kallon d'akin da yake kwance a ciki yayi, ya dubi suturun dake jikinsa masu d'an karen tsada, his life is different now, komai ya canza, he's rich handsome and educated, abu guda da ya rasa shine ZUBAIDAH She suppose to be here with him enjoying the luxury, this is the life he's been dreaming of, finally ya samu, what next now???? Ya tambayi kansa. Zuciyarsa ne ta basa amsa kai tsaye
"GET HER BACK, Get your girl back, she's yours, she's meant to be with you no one else, get back what's rightfully yours...
"Mik'ewa yayi ya soma shiryawa, cikin drawer ya hangi tsohuwar phone d'insa wanda tunda yayi kud'i ya jefarta ya sai iPhone8, sauk'e ajiyan zuciya yayi sanda ya tuna irin baran baran d'in da sukayi da iyayensa sanda ya koma masu yayi kud'i dare d'aya, gaba d'aya basu yarda da arzikin nasa ba, d'an tab'e baki yayi kafin ya d'au wayan halama sun kirasa, duba wayar ya soma yi yaga sakk'wanni da kira masu yawa, yyawanci na abokinsa Balele ne da Zulaihat, na Zulaihat ya soma dubawa, ya shiga kiran wayarta yaji a kashe, ita kuwa masu amsan kud'in gidan haya ne da Shattima suka sakata kashe wayarta, ya kira ya kira a kashe, karanta sak'on data tura masa yayi,
"D'an jimm yayi kafin ya furta " I shouldn't have abandoned you anyway, you help me sanda na zo, fita yayi ya wuce Mall ya soma mata shopping, kaya sosai ya saya mata kafin ya nufi gidanta......
Sameena ce
[1/23, 22:21] +234 803 619 0581: 🌘🌘🌘🌘 *ZUBAIDAH*
47
*©Sameena Aleeyou...✍🏾*
_Queen Samy Novels Forum...📖📚_
*Dedicated To All Victims Of Rape...*
*"Salam. Ina rok'on Allah yayi maki albarka fiye da k'ok'arinki, Ya shirya maki iyalanki fiye da tarbiyarki, Yayi maki Rahama fiye da tubanki, Yaji k'anki fiye da tunaninki, Ya k'ara azurtaki fiye da nemanki, Ya karb'i ibadunki fiye da k'wazonki.... Allah yayi ma Mahaifanki gafara ba tareda binciken ayyukansu ba, Allah Ya rufa maki asiri duniya da lahira.... Ina maki barka da Jumma'ah*
*"Sak'onki a gareni 💅🏼Maman Sadiq💅🏼......👆🏽*
*Na gode na gode k'warai da gaske da kyawawan addu'o'inki da nuna k'aunarki a gareni, Ubangiji ya saka maki da khairan, Sameena na k'aunarki, Alkhairin Allah Ya kai maki duk yanda kike... 🤝🤝the whole chapter is yours dear😍😘*
"Imam don Allah ka bar duk abinda kake kazo muje, wann mutumin ba mutunci ne dashi ba, wai Ya kira Tariq ma bai d'aga wayarsa, he's talking nonsense, wai saidai ya kwana dani tukunna zai d'aga min k'afa, kasanni bakina baya shiru nan na gaggaya masa magana son raina, probably nasan yana hanyan zuwa gidan ya min watsi da kaya ga Zubaidah tana can pls kayi sauri.... Ta k'arashe maganar tana yarfe hannu...
"Daga d'aya b'angaren Imam yace " Gani nan zuwa, just send me your location, cikin sauri ta amsa gamida tura masa....
*******
"Tana zaune gaban kayan kallo tana kan duba plates d'in da suke jere a cikin drawer d'in dake mak'ale jikin TV stand, yawanci Americans films ne saiko Nigerian films, bangon d'aya kaset d'in ne yayi mugun d'aga mata hankali don kuwa abin babu kyaun gani basai ance maka bluefilm bane, k'irjinta ya shiga bugawa da sauri da sauri, tayi saurin jifa da kaset d'in ta shiga k'ank'ame jikinta ita kad'ai tana matsawa jikin garu.... Hakan yayi daidai da soma knocking, Zubaidah ta kuma firgita, toshe bakinta tayi da iyaka k'arfinta da duka hannayenta biyu, tsoro da firgici ya mamaye ta baki d'aya.... Da alama mai knocking gajjiya yayi kokuwa ya tafi.
"Cikin sand'a ta isa jikin labulen window tana lek'awa, kasa gasgata abinda idanunta suka gane mata tayi, is that really him, ba don ta masa faran sani ba tabbas zata ce bashibane k'ila an canza sa, this one's different from the Umar she knows, sanye yake cikin kaya na alfarma hannunsa rik'e da d'an makullin mota, fuskarsa sunkuye yana rubutu jikin takarda, gama rubutun da zaiyi ya k'arasa jikin wata da ba sai ance maka taji kud'i ba, Zubaidah tana gani ya shiga lodo kaya yana ajiyesu bakin k'ofar had'i da d'aura note d'in saman shopping bags d'in....
"Sulalewa tayi a wajen k'irjinta na barazanar tarwatsewa, ta nemi kukan da take ta rasa, tana jin tafiyar motar tayi saurin fitowa ta d"auki note d'in.... Abinda ta gani a ciki yafi komai girgizata.
_Hello, I've been calling your number wasn't going, I wanted to thank you for your kindness and for accommodating me, snn to be honest with you, akanki na soma sanin Wata mace so bazan mance ki a rayuwata ba, when ever you've time pls phone up me.. ... UMAR_
"Durk'ushewa tayi a wajen kaman zararriya ta soma fad'in" No bashi bane, it wasn't him, Umar bazai tab'a yin haka ba,....... Kuka mai k'arfi ya kufce mata, tana tsaka da kukan taji an daki windown dake gefenta da sauri ta mik'e tsaye tana tattare hijabinta.
"Wani murtuk'ek'en mutum bak'ik'irin ta gani idanunsa tamkar garwashi sai muzurai yake, tsawa ya daka mata tuni ta yarda takardan dake hannunta, ta shiga ja da baya.
"Da kakkausar murya mutumin ya soma fad"in" Ina zaki gudu munafukai kawai, tsayawa zakiyi ki fad'a mun yanda shegiyar k'awar taki ta tafi, don nasan plan kuka had'a tunda na gaya mata zanzo amsar kud'ina tunda daduro ba k'anwar uwarta bane balle na ubanta, shegu kawai kunsan bazaku iya biyan kud'in haya ba kuka baro gidajen iyayenku kuka fito daduro, toh wllhi akanki zan amshe kud'ina, munafuka harda wani hijabin munafunci saikace sallahn kuke, .......
"Jiki na kararwa Zubaidah ke ja da baya tana fad'in "Wllhi bansan kom...... Bata kai aya ba ya kai mata sura tayi wani tsalle had'i da ihu, daidai nan Zulaihat da Imam suka shigo,....
"Zulaihat baki na rawa take fad'in" Duguja wani irin bura'uba ne wann yaya zaka tsorata min k'awa.... Wawan naushi ya kai mata a baki saida jini ya fettsesu... Zubaidah ta kuma sakin wani k'ara cike da firgici, Imam kuwa kukan kura yayi ya cakume Duguja da duka, Ai Zubaidah na ganin haka, ta zura hannu bakin k'ofa ta suri jakarta ta soma gudu tamkar zararriya... Zulaihat dake kwance shame shame a k'asa da k'yar take iya k'walla kira wa Zubaidah amma inaa, ko juyowa batayi ba, tamkar mahaukaciya haka take gudu bisa layin, mutane 'yan layin kuwa wanda akasarinsu karuwai ne suka fito bama ido abinci sai shewa ake memakon ayi yunk'urin rabasu, babu tarbiya sam... Allah ka tsare Al'umman musulmi ameen...
"Da k'yar da mak'ek'yata suka sami wanda yasan gidan Zulaihat, har layin aka kaisu, tundaga nesa gabansu ke fad'uwa ganin yanayin mutanen dake wajen da yanayin layin mmusamman sabida fad'an da akayi.. tabbas wann waje babu danshin tarbiya.
"Murya na rawa Jalal ke fad'in" I can't believe my wife is here, Shattima this is a Barracks bana tunanin matar aure me mutunci could leave in this place, Shattima ya paka motar kafin yace " Nima dai abinda zance knn, but she says she's leaving with her Aunt muje dai muga... Usman cewa yayi I'm speechless, that bitch lied to you...
"Tunda suka soma tafiya matayen wajen ke admiring d'insu, duk macen da suka wuce saita Bank'are masu k'irji ko kuma tayi wani salon wasu harda fad'in" Wow cuties.... gaba d'aya suka sha jinin jikinsu..
"Suna isa suka tarar k"ofa a Bud'e har lokacin bala'i ake Duguja yana fad'in sai ya amshi kud'in hayarsa a jikin Zulaihat Imam ya kasa ya tsare yace bai isa ba.....
"Da mugun mamaki suke kallon wann sure d'in, Ganinsu yasa Duguja guduwa don ya d'auka kiransu sukayi su kamasa. Yana gudu yana juyowa yana fad'in" Shegiya kariya nasan kiransu kikayi ban gama dake ba ina nan dawowa wllhi sai na amshi kud'ina, idan suna sonki su biya maki ko ki biya da jikinki agwagwa kawai...
"Kallonta kawai Shattima keyi cike da k'yama yana girgiza kai, unbelievably. Jalal kam tuni ya shige cikin gidan sai bankad'e banked'e yake yana neman Zubaidah.
"Imam ne yabi bayan Jalal yana fad'in malam lafiya, yaya zaku shigo gidan mutum ku hau masa bincike...
"Wani mugun kallo kawai Jalal ya watsa masa jijiyoyin jikinsa sunyi rud'u rud'u yake fad'in" Where... Is..... She.... Word by word yayi maganar,
"Imam kuwa Ba tareda ya fahimci me Jalal ke nufi ba yake dubansa , wani uban tsawa Jalal ya kuma daka masa " Where's My wiiifeee! I know she's here, just tell me ina takeee,.. Ya k'arashe maganar yana mank'uran Imam, da sauri cikin kakari Imam yake masa nuni da waje kafin yace " She left, she left...... Sake sa yayi ya fito waje a guje yanda su Shattima suke. Gaban Zulaihat ya k'arasa yana bata wani irin look wanda da an maka sunanka sorry kawai, ...
"Ina take??? Ya tambaya yana daka tsawa, baki na rawa Zulaihat take fad'in" Wllhi ta... ta tafi tun sanda aka soma fad'an nan...
"Idanunsa sun kad'a sunyi jazir, kana iya jin hucin da yake kaman kububuwar maciji, shak'eta yayi da iyaka k'arfinsa ya had'a da jikin garu yana fad'in" I'll kill you Garbage, .... "Da k'yar su Shattima suka k'waceta ganin zaiyi kisa...
"Sumkuyawa tayi tana tari tana sosa wuyarta ga jinin da ya kuma b'allewa a bakinta ciwon da Duguja yaji mata,..
"Yana fiffizgewa yake fad'in" If something bad happens to her I swear you'll kill you, tell me are you working for them, you're working for them right, you are working for the Dasukis, admit, just admit you bitch...
"Da k'yar ta d'agi kai tana fad'in" I've no idea what you talking about, Zubaidah ita ta kawo kanta nan, I didn't drag her here,.....
"A zuciye Shattima yace " Then why did you lie to Us, meyasa kika min k'arya, why did you even show up in my life, idan ba kinada wani bad intentions dinki akan Zubaidah ba, . First you lied to me cewa da Aunt d'inki kike zaune, while ba haka bane you're just a prostitute, second kinma Zubaidah k'arya cewa ke fiancee d'ina ne, tell us what do you have in mind, what ate your intentions...
"A zuciye ta mik'e cike da jin zafin maganganun Shattima kafin taci gaba da fad'in" Yes I lied to you I admit, I was only using you to get close to Zubaidah sabida na gane mutumin do nake so gangar jikinsa da ruhinsa na gareta, mutumin nan ba kowa bane illa Umar her Xfiancee, he loves her very much wanda har takai bazai iya kallon wata mace ba face ita, wann shine dalilina, snn zaman da Zubaidah tayi a wajena ban cutar da ita ba Allah shine shaida na.... Ta k'arashe maganar tana hawaye .....
"FFuskar nan tasa tayi jajazur gashin jikinsa sun mimmik'e haka idanunsa sunyi jazur, kaman mutun mutumi haka ya tsaya a wajen, sai dunk'ule duka hannayensa biyu da yayi...
"Shattima ma ya zama shocked sosai, a hankali ya soma jan hannun Jalal yana fad'in" Let's get out of here, babu musu ya soma binsa tamkar rak'umi da akala, har sun isa jikin mota Shattima ya juyo ya dubeta kafin yace " I'll never forgive you.. Daga haka ya soma k'ok'arin bud'e mota, Usman ne ya karb'i keys d'in yana fad'in" Let me drive, babu musu Shattima ya mik'a masa ya koma seat d'in baya .....
"Kifa kansa yayi gaban mota sanda yaji wani irin hawaye mai k'una ya ciko idanunsa. Why all this, why why, why life has to like this,... Jin zuciyarsa na neman kaucewa rahamar ubangiji yasa soma karanto innalillahi wa Inna ilahirraji'un, Allahuma ajirni fi musibati wa aklifli khairan minha....
Sameena ce
[1/23, 22:22] +234 803 619 0581: 🌘🌘🌘🌘 *ZUBAIDAH*
48
*©Sameena Aleeyou...✍🏾*
_Queen Samy Novels Forum...📖📚_
*Dedicated To All Victims Of Rape...*
"Tafi minti biyar tana durk'ushe a wajen tana kuka, for the first time data soma jin takaicin irin rayuwar data jefa kanta ciki, rarrsshin duniya Imam yayi tak'i kulasa, sai snn ya kula da shopping bags d'in da akayi patali dasu a gefe, k'arasawa yayi ya tattaro su, komai na cikin jakar are sealed, daga can gefe ya hangi 'yar k'aramar takarda, d'aukowa yayi ya ajiye gabanta kafin yace " Kiyi hak'uri ga sak'o nan I'm sure is yours..
"D'ago rinanun idanunta tayi tana bin kayan da kallo wanda ita kanta batasan dasu ba sai yanzu, goge hawayen idanunta tayi ta amshi takardar ta soma dubawa, tana gama karancewa ta kuma fashewa da wani matsanancin kuka.... Tunowa da tayi tabbas Zibaidah ta karance takardan nan koma tayi arba da Umar yasata sakin wani murmushi, ko babu komai yanzu Zubaidah zata fahimci Umar ya barta for good snn da har yanzu yana sonta da bai tafi ya k'yaleta ba, da ya tafi da ita...
"Wani murmushi Zulaihat ta kuma Saki kafin ta shiga bubbud'e kayan, kaya ne masu d'an karen tsada haka ta ringa fitfito dasu Imam na tayata, fad'i yake, ai gwara ki kira mutumin da ya kawo kayan nan ya biya maki kud'in hayar ki, don daga gani he's loaded, ..
"Zulaihat dai bata kulasa ba sai firfito da kaya take, wayarta ta d'auka ta shiga dialing lambar Umar sand take umurtan Imam ya shigar da kayan ciki....
"Bugu biyu ya d'aga wayan, ba tare da ta iya furta komai ba sai kukan data fashe dashi.... "Cike da damuwa yake tambayarta lafiya..
"Cikin salo Zulaihat ke shesshek'an kuka tana fad'in " Pls come to my place, dan Allah kazo yanzu, come before he kill me... Daga haka ta katse wayar...
"Hankali Tashe ya bar breakfast d'in da yake ya fito ya nufo gidanta...
"Mintoci kad'an ya kawosa apartment d'in Zulaihat, tana ganinsa ta fad'a jikinsa tana shesshek'ar kuka, sosai ya razana da ganin yanayinta, fuska a daddauje gashi Tana kuka,..
"Rungumeta yayi cike da tausayawa, murya cike da mamaki yake fad'in" What happened to you, who did this to you...
"Cikin kuka Zulaihat ta labarta masa komai na maganan gidan haya,...
"Rai b'ace yake fad'in" If I see that jerk I'll make him pay, ta yaya zai bugeki, you should have called me right away,....
"Goge hawayen tayi ta kuma matsewa cikin jikinsa kafin tace " Banyi tunanin haka ba, I thought you will never come back to me, ...
"D'ago ido tayi tana dubansa sanda ya k'ura mata idanu, hannayensa ta rik'e kafin tace " Me ka fad'a wa Zubaidah, I thought idan ka ganta you won't let her go, now I believed you feel something for me, ka zab'eni ko..?? Ta k'arashe maganar tana sakar masa murmushi....
"Jin maganganun nata yayi kaman almara,..
"Wait you mean to say Zubaidah's here with you..? Ya tambaya yana zaro bold eyes d'insa...
"D'an jim tayi tana tunanin toh kodai basu had'u bane kafin ta d'an girgiza kai tace " but not anymore, she left awhile ago...
"Mik'ewa yayi yana fad'in" Ina kike tunanin ta tafi, ina zan sameta, ... Wait how did you know her...???
"Ganin gaba d'aya ya rikice yasa jikin Zulaihat yin sanyi...
"Mik'ewa tayi ta shiga tattaro kayayyakin da ya saya mata ta shiga jibgawa a gabansa tana fad'in" You'll never stop loving her, will you,... Just get out of here, I don't wanna see you ever again..... Turasa ta shiga yi da iya k'arfinta tana dukan k'irjinsa har suka isa k'ofa kafin ta rufe k'ofar ta durk'ushe wajen tana kuka...
"Hannu yasa ya shafi askinsa wanda yake low-cut kafin fuzar da iska, cikin ransa yake fad'in" No Zulaihat I can't leave you, zaki min amfani wajen cimma burina, I need to work with you, I must know ta yaya kika san Zubaidah har tazo gidanki while halayyan ku ya banbanta.. you must be an important person to her....
"Jingunuwa yayi jikin k'ofar gamida k'ank'an da murya kafin ya soma fad'in" Pls Zulaihat let's talk, don't shut me out pls, I'm sorry I mean it....
"Cikin kuka take fad'in" Ka tafi don Allah bana son ganinka and don't show up ever again...
"Bai tafi ba sai ma magiya da ya ringa mata,... A haka Imam ya iso ya iske a bakin k'ofa ga sautin kukan Zulaihat da yake jiyowa,.. A sittin Imam yayi kansa ya cakume masa wuya yana fad'in" What's it again, who are you.. Me ka mata...
"Jin Imam ya kaure Umar da fad'a yasata saurin bud'e k'ofar tsakaninsu ta shiga ta rabasu gamida daka wa Imam tsawa tana fad'in" Just go Imam I can handle this,.. Cikin tsawa shima yake fad'in"No I won't let any jerk lay a finger on you again..
"Then nace ka tafi ka tafi pls, is not what you thinking.... Mugun kallo ya watsa wa Umar kafin ya k'araso gareta ya rik'e kafad'unta yace " Always remember that you can count on me, I'll be here when ever you needs me, kin wuce k'anwa a wajena...
"Murmushi ta sakar masa gamida gyad'a masa kai, daga haka Imam ya fice yayi tafiyarsa.
"K'arasow Umar yayi gamida bata light hug cikin k'ank'an da murya yace " I'm sorry, gaba d'aya sai ya tafi da Zulaihat, tuni ta mak'ale cikin jikinsa tana sauk'e ajiyan zuciya..
"A hankali ya soma fad'in" I didn't mean to hurt you Zulaihat, ki min uziri, what I went through babu sauki, I was to marry her, dakawai baikona a kanta kafin wann Jerk d'in Jalal ya aureta, Zubaidah betrays me, my whole life nayisa ne bisa sohayayyarta but still she chooses to be with that imbecile, ba komai yasa nake son sanin yanda take ba a yanzu illa to take my revenge on her and her so called husband, I want to make them pay I wanna see them suffering,... Ya d'an Dad'a matseta cikin jikinsa kafin yace " Believe me I'll never leave you again, you have me completely.... Da sauri ta d'ago idanu tana dubansa gyad'a mata kai yayi kafin yace " Yeah I promise, all I want from you is to tell me everything every single thing you know about Zubaidah kinji my luv...
"My luv ta maimaita a hankali batasan sanda murmushi ya kufce mata ba... Da sauri ta kuma rungumarsa very tied....
"Murmushi shima yayi gamida k'urama waje guda ido, cikin zuciyarsa yake fad'in" You'll help take Zubaidah back, she's mine.....
**************
"Neman duniyar nan basu sameta ba, ga dare ya soma yi, ga ruwan da ake kan zabgawa kaman da bakin k'warya, gaba d'aya ya fita hayyacinsa, duk tausayinsa ya rufe su,..
"Usman ya dafa sa yace " Bro mu mik'a cigiya kafafen watsa labarai ko Allah zaisa a sameta, kaga dare yayi ga ruwan da ake kan zabgawa, kaga yanda ruwa ke d'iga a jikinka zakayi ciwo.....
"Kallon Usman yayi da rinannun idanunsa kafin ya soma fad'in" I don't care Usman ban damu nayi ciwo ba, All I want is to see her again, what if she couldn't take care of her self, what if something bad happens to her, me kake tunani.... Yasa hannunsa gamida kwantar da sumansa da ruwa ya jik'a had'i da fuzar da iskan bakinsa, ga wani sanyi da ya soma kad'asa...
"Juyawa yayi ya kalli Shattima wanda har yanzu cikin damuwar abinda Zulaihat tayi yake kafin ya k'arasa k'asar bishiyan da yake.... Bud'e bakin da zaiyi da niyyan magana wa Shattuma ya hangi mutum kwance bayan katakon shagon dake k'ark'ashin bishiyar, hijabin makarantar ta ne a jikinta, kwance take tamkar maras numfashi da alama ruwan ya jima yana bugunta..... bai iya ce masu komai ba sai k'arasawa wajen da yayi, cikin sauri suma suka k'araso wajen gaba d'aya....
Sameena ce 👌🏾
[1/23, 22:22] +234 803 619 0581: 🌘🌘🌘🌘 *ZUBAIDAH*
49
*©Sameena Aleeyou...✍🏾*
_Queen Samy Novels Forum...📖📚_
*Dedicated To All Victims Of Rape...*
"D'agota yayi ya rungume cikin jikinsa hannayensa na rawan sanyi, murya na rawa yake fad'in" I'm sorry, you'll be I got you.... Zafin jikinta da nasa suka gauraya waje guda yana jin fitar turirin numfashinta a hankali , haka ya ringa sumbatu still tana rungume cikin jikinsa, Shattima ne ya dubi Usman kana yace " Get the car buddy,
"Yeah sure, Usman ya fad'i ya nufi yanda suka faka motar ya k'araso da ita yanda suke, ...
"Dafe shoulder d'in Jalal Shattima yayi kafin yace " Muje Jalal... Babu musu ya mik'e gamida d'aukanta a hannu tamkar baby... Shattima ya bud'e masa back seat suka shige yayi saurin wucewa mazaunin Me zaman banza....
"Dr Khaleesat ta d'an ja medicated glass d'inta k'asa kad'an ta duba agogon dake d'aure a hannunta na hagu ya nuna k'arfe 10 da wasu dak'ik'ai sauk'e light breath tayi kafin ta dubi Annah data rapka uban tagumi tace " Ki kwantar da hankalinki Insha Allah everything will be alright, is getting late ni zan wuce gida idan yaso gobe sai muyi reporting to the police snn mu kai cigiya kafafen yad'a labarai...
"Gyad'a mata kai kawai Annah tayi ba tare da ta iya cewa komai ba..... Kaman daga sama suka jiyo muryar Hamma Habibu yana fad'in
"Annah Annah sun sameta, sun samo k'anwata, Jalal ya samo mun ita....
"A tare Annah da Dr Khaleesat suka mik'e, Hadiza ce mai d'aga labule Hamma na gyara mata, Tana nan rik'e a hannunsa ya shigo bai tsaya ko ina ba sai bedroom d'in Annah cikin sauri suka d'unguma suka bi bayansa, ajiyeta yayi saman bed ya shiga rarumo bargo yana rufa mata, sai gaishesa suke faman yi amma bai sami zarafin amsa su ba, she dai kawai yaga Zubaidah ta zama safe, ... "Jin jikinta ya kuma yin zafi yasa sa d'ago kai yana duban Dr kafin yace " Her temperature is burning ko asibiti za'a kaita..
"Let me see, cewar Dr Khaleesat , da sauri Jalal ya matsa gefe ya bata waje sunkuyawa tayi tana tattab'a jikin Zubaidah jafin ta girgiza kai tace " No babu komai tsananin fever ne kawai kuma ruwan da ya jima yana sauk'a jikinta ya saka mata give her paracetamol idan ta tashi and I'll prescribe her medication as soon as I get home idan yaso sai na maka texting, ta d'anyi murmushi tana duban Jalal kafin tace " Mr Jay baka lura kayan jikin matar taka a jik'e suke ba ka ajiyeta haka and still ka rufa mata bargo, take off the clothes ka saka mata wasu snn a matsa mata jikinta da warm water with a towel sabida zafin jikin ya sauk'a.....
"Kaman jira Hadiza take nan tayi karaf tace " Ni Dije zanga yanda za'a canza wann kaya mutanen da ko kwana d'akj guda basu tab'a yi ba shine za'a ce ya sake mata ka...... "Aya ta saka ma zancen nata ganin wani irin muguwar kallon da Jalal ya watsa mata.... "Babu wanda yace k'ala sai Dr Khaleesat data kuma duban Jalal tace " you should change your clothes too before you fall sick, kai nasan kaima baka da lafiya, zan maka prescribing magani kaima, don I'm pretty sure ciwon soyayya kuke.... Gaba d'aya suka murmusa harda Hamma wanda ke durk'ushe yana rik'e da hannun k'anwarsa.
"Toh ni zan wuce and pls a guje duk wani abinda zai b'ata mata rai for now.... Dr Khaleesat bata Kai aya ba Hamma ya dubi Hadiza yace " Kinji koh Hadiza likita tace kar a b'ata mata rai dan Allah kar ki mata masifa kinji.....
"Kallon fuskokin mutanen wajen Hadiza tayi kafin ta kafesa da wani mugun harara tace " Da shike nice uwar 'yan bala"i koh, dan na nuna damuwata akanta ashe nayi laifi.... Banji ba ban gani ba balle kuce nace.... Ta buga wani uban tsaki gamida ficewa fuuuu....
"Gaba d'aya suka bita da kallo, Hamma ya mik'e yana dariya wanda shi a tunaninsa murmushi yake ya dubi Dr yace " Kar ki damu haka take, haka take... Zan je na mata magana, ya k'arashe maganar yana nuni da k'ofa, ...
"D'an murmushi kawai Dr tayi gamida gyad'a kanta... Annah kuwa kaman ta nitse sabida takaicin Hadiza, sallama suka kuma yi da Jalal kafin Annah tayi ma Dr rakiya....
"Tsura mata dogayen idanunsa wanda basu faye girma ba yayi yana tunanin ta yanda zai soma canza mata kaya, .
"Mik'ewa yayi jiki babu laka ya nufi drawer d'in da yake tunani nata ne kafin ya bud'e, kayanta ya gani a shirye tsaf a ciki.... D'an fuzar da iska yayi kafin ya ciro wasu kayan. Ya dawo yanda take...
"Ya jima yana durk'ushe gaban gadon yana dubanta, fuzar da iska ya kumayi kafin yasa hannu ya yaye bargon,... K'irjinsa ya shiga bugawa da sauri da sauri sanda yake k'ok'arin rabata da rigar jikinta.... Abubuwan da suka faru a wancan daren suka shiga dawo masa, fuskokinsu yake hangowa sanda suke keta mata rigarta.... "Da k'arfin gaske ya runtse duka idanunsa biyu... Kasa cire mata rigar yayi sai mik'ewa tsaye da yayi cikin sauri ya nufo parlor, a k"ofa suka had'u da Annah sai rawan sanyi yake.... Kan ta sami zarafin magana yayi saurin mik'a mata kayan Zubaidah dake hannunsa yace "Barin duba su Shattima..... Ya k'areshe maganar cikin rawar murya irin ta maras lafiya....
"Kallonsa Annah tayi kafin tace " Ah sun tafi ai, sunce zakuyi waya.... "Baka da lafiya ne, she added..
"D'an jim yayi kafin yace" I'll be fine Annah just take care of her, I'll be in my room idan kina nema na..
"D'an gyad'a kai kawai tayi ta bisa da kallo cike da tausayawa har ya fice..
"Layin Shattima ya soma kira yajita a kashe, nan ya kira na Usman, .
"Usman ya sanar dashi Shattima ke da journey gobe da sassafe, zaije sa Kaduna and daga chan maybe ya wuce Gombe...
"Jalal ya kuma tak'urewa cikin bargo kafin yace " I feel bad you know, I couldn't have chance to thank you... Zan sake kiransa gobe da safe insha Allah... Na gode na gode sosai Usman " You guys are incredible Allah Ya bar zumunci...
"Haba Jalal ka daina fad'im haka pls, that's what brothers are for.. I'll see you tomorrow Allah k'ara rufa asiri...
"Ameen Jalal ya amsa dashi sukayi sallama kafin yayi hanging up...
"Washe gari tunda ya tashi tun safe bai fita ko k'ofa ba dukda jikin nasa ya masa dama dama breakfast ma har d'aki Annah ta kai masa, lokaci zuwa lokaci yake tambayar ko Zubaidah ta tashi..
"
"Wajajen k'arfe sha biyu da rabi goshin azahar ya fito ya nufi d'akin Annah...
**************
*Dasuki Holding*
"Zaune yake yana juyi saman kujeran nasa waya mak'ale a kunnensa ba sai ance maka da sahibarsa yake wayan ba, banda uwar harara babu abunda Labib ke watsa masa....
"Salim yaci gaba da fad'in" are you serious sweetheart, wait how comes bansan kina shirin had'a mana spectacular dinner ba.
"Murmushi yayi sanda ta basa answer kafin yace " Okay kice k'aramar biki zaki kuma had'a mana, okay zan fad'a wasu Daddy right away tunda duka suna nan har Pappy... Ohh my Baby can't wait to see you, kar dai kiyi aiki sosai ki gaji kinji Baby na... Ya kuma yin want murmushi mai sauti yana juyi bisa kujeran kafin yace " Okay my darling kisses to you.....
"Har ya k'arashe wayar Labib bai daina danna masa harara ba...
"Mik'ewa Salim yayi yana gyara suit d'insa ba tareda ya dubi Labib ba yake fad'in" Kausar is inviting us all for dinner tonight zanje na fad'awa su Daddy right away su Mummy ma will be there,... Bai damu da rashin ansa sa da Labib beyiba idan da sabo ya saba da halin d'an uwan nasa...
"Har ya kai k'ofa ya juyo yace " Pls ka kira Tariq ka fad'a masa though his family is invited too, amma dai pls ka fad'a masa idan yaso sai ya zama kaman farewell party d'insa...
"Bai amsa sa ba sai faman kad'a biro da yake, yana ficewa yaja tsuka gamida furta " Useless..
Sameena ce 👌🏾
[1/23, 22:22] +234 803 619 0581: 🌘🌘🌘🌘 *ZUBAIDAH*
50
*©Sameena Aleeyou...✍🏾*
_Queen Samy Novels Forum...📖📚_
*Dedicated To All Victims Of Rape...*
*I've received your messages masoyan k'warai wllhi lisaffo sunayenku ma aiki ne sabida yawanku.. Nonetheless ina sonku irin totally d'inan Alkhairin Allah Ya kaimaku duk yanda kuke...😍😘❤*
"Ya jima yana tsaye bakin k'ofa hannunsa a Hard'e kan k'irjinsa, kallon siraran hawayen da suke bin k'uncinta yake...
"Jikinta ne ya bata da kwai mutum a wajen snn wann k'amshin nasa bai barin hancinta da sauri ta d'ago kai tana dubansa,... Fuskan nan nasa a mirtuk'e babu alamun Fari'a, yana sanye cikin inner red Mai V-neck had'i da lallausar wando Wanda da kad'an ya wuce gwiwarsa....
"Cikin sauri ta kauda kai gefe don bata juran kallonsa...
"Taku kad'an yayi ya k'araso cikin parlorn.... Cak ya tsaya a gabanta cikin dakakkiyar murya ya soma fad'in"
"Why... Me yasaki yin haka, .... "K'ara sautin muryar yayi cikin tsananin fad'a yake fad'in" Tell me why, what... What if I couldn't find you, what if I couldn't protect you.... Do you even realize the kind of trouble you almost got your self into huhhh..?? Do you think you the only suffering..?
"D'agota yayi sanda kukanta ya k'aru ya rik'e arms d'inta da k'arfin gaske suna fuskanta juna yaci gaba da fad'in" Look into my eyes and tell me what the heck did I do to you this time around...
"Bud'e jik'akk'un idanunta da suke sharkaf da hawaye tayi ta sauk'esu kan farin fuskarsa da ya turning red, siriryar jijiyar goshinsa ta fito sosai, siraran dogayen idanunsa sun firfito waje, sirirn hancinsa wanda bai faye tsawo ba k'ofofin sun bubbud'e, his cute pink lips keeps blowing kaman ya shafa lipstick....
"Ta tuna yanayin data gansu da Tariq zuciyarta ya shiga mata zogi da rad'ad'i..
"Da k'arfin gaske cikin tsananin kuka take fad'in" Eh gwara na tafi ko ina ne, 'cause you all the same, you... Are... Just... Like... Them... You all raped me... Snn I saw you with him hugging each other probably planning something again ...
"Are you going to deny it, huhh.. Ka fad'a mun Me kuke shiryawa akaina, ka fad'a mun kuna shirya yanda zaku...... ENOUGH.!!!!!! YA daka mata wata tsawan da saida hawaye ya fita daga idanunsa.... Annah dake kitchen saida ta yarda ludayi....
"Ita kanta Zubaidah shaking ta soma tana kallonsa bata tab'a ganinsa cikin irin wann yanayi ba....
"Ido cikin ido yake dubanta in a furious tune yaci gaba da fad'in" I love you.... I love you ultimately more than you might think. And you know I'm not asking you to love me back.. All I want is protect you and to keep you safe koda hakan zai zama ajalina.... I don't care anymore if you don't believe me..... Daga haka ya juya ya fice daga parlorn cikin sauri.......
"A bakin k'ofa suka had'u da Annah, bata sami zarafin masa magana ba ganin yanyain nasa, ta jima bataga irin wnn yanayi a tattare da d'an nata ba, ... "Cikin sauri ya nufi d'akinsa. Kallo Annah ta bisa dashi har ya shige. Sauk'e nannauyan ajiyan zuciya tayi ta shiga parlon tana addu'an Allah Ya kawo k'arshen wann Al'amari.....
"Har lokacin kuka Zubaidah take, lallashi ya zame ma Annah jiki...
"Yana shiga d'akinsa wandosa ya canza zuwa ta jeans kafin ya fice.
"Suna jin ficewarsa ko sallama bai masu ba.
"Zubaidah ta kuma shigewa jikin Annah hawaye na fita idanunta, tausayin kanta ya kuma kamata, for the first time dataji babu Dad'i abinda tayiwa Jalal, Kalman *I love you and I'm not asking you to love me back* ta ringa nanatawa cikin zuciyarta, wani hawayen na kwarara mata musamman idan ta tuno abunda Umar da Zulaihat suka mata....
*******************
*Police Department Headquarter Wuse2 Abuja*
"D'aga idanunsa yayi ya kuma karantawa, zuciyarsa tana Dad'a basa k'arfin gwiwa akan abinda yayi niyya, kai tsaye ya kutsa kai ciki, tuni ya nemi ganin IG, ba'a basa daman ganin sa ba, ya jima yana jiran neman ganinsa bai samu ba har saida IG ya fito daga meeting, haka kurum yaji yana son ganin Jalal, nan aka masa izini.....
"Kai tsaye bayan sun gama gaisawa IG ya tambayesa "How may I help you young man.
"Without any hesitation Jalal yace " Sir I came to confess...
"Kalllonsa yayi da kyau kafin ya kuma tambayarsa, kai tsaye Jalal ya kuma nanata masa... In details Ya fad'i komai bai b'oye ba mai d'aukan rahoto bisa computer Ya rubuce komai.
"Inspector yasha mamakin abun sosai, don kuwa babban mutum a k'asa irin Kasim Dasuki bai zaci zai yi haka ba, koda yake mutane for their children babu abunda bazasuyi ba...
"Kallon Jalal yayi da kyau kafin yace " Mr Jalal I've heard your confession and zamu rik'e Ka a nan, but before muyi arresting sauran sai ita victim d'in tayi magana you understand what I mean say tayi filing complaint..
"Intercom ya danna kafin wani Sargent ya shigo ya fita da Jalal...
"Annah tasan halin d'an nata idan yayi fushi tasan kalan zuciyan Jalal, sai iya shafe sati ba tareda sun gansa ba, lambarsa ta shiga nema,
"Sargent d'in da ya d'auka ne ya sanar da ita Jalal na police station. Ai tuni Annah ta mik'e tsaye tana tambayarsa me ya kai d'anta police station, Kai tsaye Sargent d'in ya mik'a ma Jalal wayan...
"Cikeda tashin hankali ta soma magana, Jalal, me kayi aka kama ka, me ya faru......
"A hankali yace " Annah ki kwantar da hankalinki ni na kai kaina, I confessed everything,
"Annah ta nanata a fili daidai sanda ta juya taga Zubaidah ta mata k'uri alamun tana saurarenta... Da sauri ta k'araso tana fad"im Annah Dan Allah barin masa magana, tana maganan cikin rawan murya zuciyarta cike da takaicin kanta don kuwa ita tayi provoking d'insa.....
"Pls come back home, dan Allah ka dawo I promise bazan sake ba, kaji but pls don't leave me all alone by my self..... Abunda yaji knn cikin kunnuwarsa wanda ya kasa gasgatawa.
"Damk'e wayar yayi sosai kafin ya soma fad'in" I'm doing this for us to live in peace, all I want from you is to talk, don't remain silent, File a complaint against your enemies, don't let them get away with it, kiyi magana kiyi magana, talk kinji babu rufarufa from this very moment, let the whole world know the truth, let us get what we deserve, kinji... Pls talk.
"Kaman na ganinta haka take nodding kanta tana hawaye take fad'in" I'll talk Right away, I'll speak up, kaji, you'll be safe and you'll be free..... Kuka ya kuma kufce mata, Annah ce ta karb'i wayan ta tambayesa station d'in da yake......
****************
"A hankali ta turo k'ofar d'akin har lokacin zuba kaya yake cikin luggage d'insa, dafasa mum tayi kafin tace " Tariq da gaske tafiya zakayi ka barmu, Tariq you are our only son bazan iya jure rashinka ba.....
"D'an jefar da rigar hannunsa yayi ya d'ago yana dubanta kafin yace " Oh com'on Mum do we have to talk about it again, bazan iya ci gaba da rayuwa a nan bar, I need a change of environment Mum, I need to forget everything that happened here, I need to start a fresh....
"D'an goge hawayen idanunta tayi kafin tace " Zan ringa visiting d'in ko yaushe, ..
"Murmushi yayi gamida hugging d'inta da hannu d'aya cikin arms d'insa kafin yace " Bazaki iya visiting d'ina ko yaushe ba, munyi nisa, Moscow da nan akwai nisa sosai Mum, all I can say you'll always remain here.... Ya k'arashe yana nuni da k'irjinsa ma'ana heart d"insa... Murmushi ta sakar masa itama ta rungume sa sosai... Sa hannu yayi ya share mata hawayen idanunta...
"Tayasa arranging kayan taci gaba dayi, sunayi suna hiran sanyin da zai tarar a Moscow, nan ta tambayesa ko zaije dinner d'in da Kausar ta had'a anjima..
"D'an jimm yayi kafin yace " I'm not so sure coz flight d'ina da safe ne so banson nazo ban tashi da wuri ba...
"Shafa kansa tayi tana fad'in" No excuse you are going, at least kayi sallama da kowa.... Zaiyi magana ta d'aura hannu bisa lips d"insa tace" Final you are going na gama magana....
"Murmushi yayi kana yace " Alright Mum just because you insist, that's my boy ta fad'i sanda take zipping jakar....
"Around 7:00pm ya nufo stirs d'in Mum don jin kota shirya su tafi tare, wayan da yake jiyowa daga d'akinta yasa gabansa ya yanke ya fad'i.
"Mum taci gaba da fad'in" Haba Barr Munir na fad'a maka zanzo zanzo , idan Tariq ya tafi ma mun huta had'uwa a hotel coz gobe zai tafi, tayi wani dariya kafin taci gaba da fad'in" Haba kar ka damu alak'armu bazata Tab'a yankewa ba don bazan tab'a bari Alh Maina ya sani ba.....
"Bibbiyu Tariq ya soma gani, ya kasa gasgata abubuwan da ya gama ji, cikin sauri ya juya ya sauk'a k'asa, kai tsaye motar sa ya nufa ya fice a guje, fuskar Barr Munir kawai yake hangowa, shi kad'ai yake huci yake fad'in" I'll kill that Bastard with my very own hands.........
*At the company*
" Salim Ya kuma duban Labib kafin yace " Hey stop being so stubborn, dalla ka tashi mu tafi, kaifa mugun D'angelo iska ne, you wai uwar Me zaka tsaya yi ko anan zaka kwana ne.
"Da wutsiyar Ido Labib ya kallesa kafin yace " Do I always have to explain my self, nace maka bazanje ba fine, ka tafi mana abunka...
"Rufe laptop d'in gaban Labib Salim yayi yana wata murmushi yake fad'in" Hey your crush is gonna be there too, Asmah I'm pretty sure tana chanma probably helping Kausar, com'on don't be stubborn tashi muje.....
"Hararansa kawai Labib yayi kafin ya mik'e yana zungurin k'eyarsa yace " You such a jerk you know....
'Dariya Salim yayi yana fad'in whatever.... Dariya kawai Labib d'inma yayi kafin suka nufi lift suka sauk'o k'asa.
"Dukansu motar Salim suka shige, Labin yayabawa wani security car keys d'insa yace ya kaimasa gida....
"Suna fitowa k"ofar company d'in motocin police , cike da tashin hankali suke bin polisawan da kallo, guda d'aya ne ya fito ya nufi motarsu... Tuni suka bud'e motar..
"Cike da gadara Labib yake fad'in" Lafiyanku wa kuke nema snn bakusan nan company bane, and idan wani kuke nema working hours zakuzo ba yanzu ba... Police biyu Suka fito,
"I'm Detective Amir you need to come with us to the station..
"Sai snn Salim ya fincike marfin mota ya fito yana fad'in" Officer what the heck are you talking about, you can't arrest us just like that, besides meyasa zamu biku station...
"Idan munje chan kwaji bayani ya fad'i sanda ya kalli Sargent biyu yace ARREST THEM , No... No you can't do this to Us, kunsan su waye mu, kunsan mu 'ya'yan waye.. You will all regret this, you doing this to loose your job.... Salim ya fad'i sanda yake kallon securities d'in company d'insu yace" Call my Dad right away.....
"Haka sunaji suna gani aka tasa k'eyarsu.....
*At Salem's House*
"Su Daddy da Pappy suna parlour suna hira, akasarin hiran kan business ne da kuma forthcoming election, Alh Kasim yana bawa Alh Tahir shawarwaei kan garuruwan da ya kamata suje convention su kuma gudanar da Rally....
"Mummy da Mumsy suna k'aramin parlon Kausar suna nasu hiran, yayinda Kausar da Asmah da ma'aikatan ta guda biyu suke zarya daga kitchen zuwa makeken dining area d'inta wanda table d'in ke d'auke da kujeru goma sha bbiyu...
"Barr na waje yana amsa kiran da aka masa cewa anyi arresting su Salim, kaman daga sama yaji sauk'ar naushi a kumatunsa sa saida wayar ta tarwatse a k'asa, cakumosa Tariq ya kumayi yana fad'in" I'll kill you, you Bastard....
Sameena ce 👌🏾
[1/23, 22:22] +234 803 619 0581: 🌘🌘🌘🌘 *ZUBAIDAH*
51
*©Sameena Aleeyou...✍🏾*
_Queen Samy Novels Forum...📖📚_
*Dedicated To All Victims Of Rape...*
"Kaman Allah ne ya aikosa haka yake dukan Barr Munir da iya k'arfinsa.... "Hankulan securities masu tsaron Gate ya tashi cikin sauri suka nufi cikin gidan suka sanar dasu don sun kasa dakatar da Tariq da irin dukan da yake ma Barrister..
"A sittin suka fito gaba d'ayansu hakan yayi daidai da isowan su Mum d'in Tariq da Dad d'in sa...
"Su Mumsy su Mummy Kausar da Asmah gaba d'aya suka daskare suna kallon wann ikon Allah...
"Alh Tahir da Alh Kasim suka yi kansu suna rirrik'e Tariq..
"Fuzgewa yake yi yana fad'in "Let go of me, let me go.... Let me kill this Animal.... Alh Kasim ya janye Barr yayinda Alh Tahir ke rik'e da Tariq...
"A tamanin Su Mum d'in Tariq suka fito daga mota suka nufo su....
"Da gudu tayi kansa tana fad'in" Tariq my Baby Me ya faru....
"Idonsa na zubda hawaye yake nunata da yatsa yaci gaba da fad'in" Don't you dare come near me, you have no idea how shameful it is being your son.... You are disgusting, I can't believe you're his mistress. Na tsaneki na tsaneki snn ke ba mahaifiyata bace.
"Juyawa yayi ya kalli Barr dake zaune shame shame a k'asa fuska duk jini yace" I'm not done with you, you miserable coward, sai na kashe ka har lahira Worthless imbecile... Mark my word.... Cikin sauri ya nufi motar sa yana haki....
"Kallon k'yama da mamaki Alh Maina ke watsa wa Mum d'in Tariq dake tsaye tana zuban hawaye.... Jin yanda Tariq ya kwashi motar yasan komai ka iya faruwa yasa sa saurin shigewa motarsa yabi bayan d'ansa....
"Gaba d'aya jikkunansu sunyi sanyi babu kaman familyn Kausar, this is a disgrace, ace uncle d'in Inlaw d'insu ne wann, Mum d'in Tariq jiki a sanyaye ta fice daga gidan cike da kunya da nadama...
"Mummy da Daddy suka ja Barr suka nufi guestroom dashi, yanda take shiga bata nan take fita ba, yanda kasan ba yayanta ba haka take tsefe sa,
"Ka rasa wa zaka nema sai k'awata kuma matar aure, matar abokin mijina uwar abokin d'ana haba haba gaskiya nidai baka kyauta min ba ...
"Daddy ne ya shiga lallab'anta yana nuna mata kuskurene da sharrin shed'an Amma he can fix this taje taji da bak'i...
"Mummy ta kuma narka masa harara kan nan nasa a k'asa kaman munafukin k'adangare, bai iya furta komai... Tsaki tayi ta fice fuuu tana tunanin da wani ido zata kalli Haj Raliya Mum d"in Kausar....
"Mummy tana fita Alh Kasim ya matso kusa dashi kafin yace " Kayi kuskure yaya zaka nemi wacce you are somehow closed to her family, ai idan zakayi bariki waje zaka fita ka nema, kaga yanzu ga abinda ya haifar, me kake tunanin Alh Tahir zai d'auke mu, Irresponsible mutane ko me??? ....
"Dafe kansa yayi gamida buga uban tsaki yana goge jinin bakinsa kafin yace " Ai wann Me sauk'i ne kan abinda zan fad'a maka...
"Police arrested Salim and Labib, wayan da aka mun kenn ana gaya mun kafin d'an iskan yaron nan ya iso, nasan shima the cops are after him Allah sa su capke shege.....
"Wait. Wait.. Wait..... Daddy ya dakatar dashi da fad'in haka, kafin yaci gaba da fad'in" Kana nufin kace " An kama only son d'ina....
"Galala Barr ya kallesa kafin yace " Me yasa basu iso ba har yanzu, for your information your precious little boy is spending the night in a jell....
"Mik'ewa Daddy yayi yana girgiza kai yake fad'in" k'arya ne wann, babu wanda ya isa ya kulle mun d'ana, tashi maza ka tafi, you are their lawyer, kar ka bar wani shege ya tab'a mun lafiyan yaro..
"Mik'ewa Barr yayi yana goge hancinsa mai zuban jini yake fad'in" Yarinyar nan ta b'allo ma kanta aikin da bazata iya ba.... Turasa k'ofa Daddy yayi yana fad'in" Just go I'll take care of the situation here....
"Duk sunyi jigum jigum a parlor suna jimamin abinda ya faru, kowa da kalan tagumin da ya rapka, suna hango Daddy Kausar ta mik'e tana fad'in" Daddy ina Salim he should be here by now, me ya hanasu isowa har yanzu.....
"Jim Daddy yayi yana duvansu kafin yace " ..... The girl..... Shiru yayi sakamakon k'irjinsa dake bugawa,... Dakewa yayi yaci gaba da fad'in" The... Girl Filed a charges against them. An tafi dasu police station...... Ai bai gama rufe baki ba Kausar ta Saki wani irin k'ara gamida zubewa k'asa, cikin sauri Mumsy da Asmah suka rik'eta....
"Kuka take tana fad"in" Na sani na san ba k'arya take mun ba, kune mak'aryata macuta mayaudara azzalumai kuka bari na auri criminal son d'inku...... Pappy ne ya dubi Mumsy da Asmah yace su haura da ita sama...
"Fuzgewa Kausar ta kumayi ta k'araso gaban Mummy tana watsa mata mugun kallo take fad'in" Aren't you going to say something Haj Farha, kiyi magana mana Ashe kinsan d'an iskan d'anki rapist n....... Bata kai aya ba Pappy ya d'auketa da wani wawan mari..... D'agowa Kausar tayi tana dubansa cike da mamaki tun tasowarta ko zunguri bai tab'a had'ata da mahaifinta ba sai gashi yau ya mareta... Cikin kuka dafe da k'uncinta take fad'in" Pappy you shaped me because of these worthless people.... Da k'arfin gaske ya kuma fad"in " Raliya I said take her up stirs...
"Mumsy da k'walla ya ciko idanunta da sauri ta shiga jan Kausar Asmah na tayata suka haye sama d'akin Kausar.
"Mummy jiki a mace take kuka ta nufi balcony...
"Wani mugun kallo Alh Tahir ke watsa ma abokin nasa kurum...
"Daddy ya d'an fuzar da iska kafin yace " I guess we need to talk, babu musu Alh Tahir yabi bayansa suka koma cikin parlorn suka zauna....
"Bud'e baki Daddy yayi zaiyi magana Alh Tahir ya dakatar dashi ta hanyar d'aga masa hannu kafin ya soma fad'in" No more lies Alh Kasim, just go straight to the point and tell me the exact truth.... In a furious tune yayi maganar....
"Sauk'e ajiyan zuciya Daddy yayi kafin ya soma 'yan kame kame....
"Ai Mr President kasan halin yaran yau, kwata kwata basa jin magana, duk iya k"ok'arinka na ganin ka wadata su sai Sun sab'a kasan yar..... Da wutsiyar ido kawai Alh Tahir ke kallon Alh Kasim kafin ya d"aga masa hannu alamun dakatarwa yace " Mr President go straight to the point, Did they commit the crime or not..???
"Tura hulansa baya yayi kafin yace " Yes the Did, but...but....
"Period abinda nake son ji kenan, cewar Alh Tahir Marafa kafin yaci gaba da fad'in" Ban tab'a zaton amincin dake tsakaninmu zaisa ka rufa wann babban laifi da d'anka ya aikata ba ka bari na aura masa tilon 'yata, ka bani kunya Alh Kasim.
"Cikin sauri Daddy ya soma fad'in" Yaran nan yara ne, kuma ita yarinyar mun wadatasu da kud'i rashin godiyar Allah ne yasata maka k'ara....
"Jinjina kai Alh Tahir yayi kafin yace " Yanzu na gane cewa kai wani irin mutum ne, na d"auko dukiyata na zubata a company d'inka snn na d'auki only daughter d'ina na Aura ma d'anka.... For your information I'm taking all my money I mean all my shears out of the company, I don't want you to drag me and my family into this mess of yours.....
"K'ok'arin mik'ewa ya soma Alh Kasim ya k'arasa ya dafe kafad'arsa kana yace " You already in the mess kar ka mance d'ana na auren 'yarka snn if you are thinking sabida siyasarka zaka yanke alak'a damu then you are mistaken sabida you can't go anywhere without us, Alh Tahir you perfectly well know Me, kasan kalananyan mutanen da nake dasu a k'asar nan, kasan I can ruin you, your carrier in politics and last your Reputation, so ina mai baka shawara just back down, muci gaba tunda kaima ka shigo cikin mess d'in....
"Buge hannunsa Alh Tahir yayi kafin yaci gaba da fad'in" Your criminal son must divorce my daughter don ban haifa mata ma criminal irinsa ba, snn da kake maganan you can ruin me, fine go ahead, abu guda ne nasan bazan bari ka lalata mun ba shine Reputation d'ina, you can go ahead and ruin my carrier in politics but I'll not allow you to ruin my reputation a idanun duniya kaman yanda naka sunan yake gab da b'aci..... Daga haka ya fice cikin sauri yana sab'a babbar riga, gaba d'aya ma ya mance dasu Kausar.....
"Kallo Daddy yabisa dashi har ya fice, da k'arfi ya daki garun parlorn da yasha ado da golden wallpaper yana fad'in" Damn it dammit...... I'll not allow you to bring me down you filthy mere girl....
"Mumsy wllhi sai na bar gidan nan, ko kwana bazan kumayi ciki ba, snn wllhi dole Salim Ya biyo ni da takarda na ko na maka sa a kotu, ..... Ta k'arashe tana jefa kaya cikin trolley d'inta, Asmah dai tama rasa wanne zatayi, haka suka had'u ita da Mumsy suketa faman lallashin Kausar..... Ana haka Mummy ta turo k'ofa tana k'ok'arin shigowa jiki a sanyaye uwa munafuka..... Harara kawai Kausar ke b'alla mata sabida duk sun san gaskiya suka take....
"Mik'ewa tayi tana fad'in" What are you doing here, kin karb'o mun takardan Saki na ne ko me..??
"Cike da b'acin rai Mumsy ta daka mata tsawa gamida zaunar da ita, bana son rashin hankali Kausar, kina shaye shaye ne kike fad'a wa manyan mutane maganganu irin haka, especially uwar mijinki.....
"Cikin kuka Kausar take fad'in" Mumsy wllhi ni ba uwar mijina bane, wllhi sai ya sakeni....
"Kallon Asmah Mumsy tayi tace " Rik'eta ku sauk'a k'asa ina zuwa,.. Gyad'a kai kawai Asmah tayi kana ta rungumo Kausar suka nufi downstairs....
"Mummy ta Kalli Mumsy jiki a mace, da k'yar ta iya bud'e baki da niyyan magana, Mumsy ta dakatar da ita...
. "Haj Farha I know you must be having a hard time, but inaso ki sani dukanmu muna cikin tashin hankali a yanzu, ban zaci zaki iya manipulating d'ina haka ba, claiming to be my friend, ta yaya zaki bari Yata ta auri criminal bayan kinsan mafarkin ko wata uwa 'yarta ta kasance cikin auren soyayya da kwamciyar hankali, my daughter is suffering, tunda muke da Kausar bata tab'a zama maras kunya ba sai yau, ko da yaushe cikin obeying d'inmu take, kema shaida ce, dole ma abin yayi affecting d'inta, ta yaya zakiji ace ga mijinki ana shari'a dashi ya aikata babban laifi irin fyad'e, ko ke da kike mahaifiyarsa abun bazaiyi affecting d'inki kaman matarsa ba, abu guda da zai dameki shine rashinsa da zakiyi muddin aka jefasa gidan yari, So pls kar ki soma tunanin zan lalashi Kausar tayi zaman gaibu da d'anku, snn kema mace ne, ko baki haifi d'iya mace ba, kiyi tunanin irin k'uncin rayuwar da yaranku suka jefa wancan yarinyar a ciki, iyayenta wani hali suke ciki, ni Mace ce kuma mother of Mace, Ni dai abunda zan iya cewa Allah shi karb'a wa mai gaskiya hakkinsa.. Snn maganar auren Salim da Kausar dole a datsesa.. Daga haka Mumsy taja akwatin Kausar ta nufi k'asa rai b'ace...
"Mummy kam kifa kanta tayi bisa gado ta shiga rusa kukan abubuwan takaicin da suka sameta a yau...
"Cikin tsananin tashin hankali Dad d'in Tariq yaci gaba da suka gewaye motan yana fad'in call an ambulance.... Cikin mintoci kankani ambulance ta iso aka saka Tariq da ya kwankwatse a mota aka wuce dashi emergency
***************
*Gombe, Palace*
"Kai tsaye parlorn mai Martaba Babban gwani ya nufa, he's looking tired and exhausted, bisa ga alamu bai jima da shigowa garin ba...
"Tundaga waje fadawa ke masa kirari,
"An gaisheka Shattima, Sallama ya gaisheka, Madawaki ma gaisuwa yake, An gaisheka D'an Wazari badad'in Mai Martaba, ...... Gyad'a masu kai kawai yake yana mai ci gaba da tafiyar sa, yana isowa k'ofa Shamak'i ya basa hanya yana gaishesa yana fad'in" Shiga cikin aminci baka da Shamak'i....
"Zaune ya taddasa da shalelensa Zahidah... Da sallama kai a k"asa cike da ladabi irinta babban gida Shattima ya shiga wargajejen parlorn.... Rusunawa yayi yana mai mik'a gaisuwarsa ga mai Martaba, Ta k'asa k'asa Zahida ke kallonsa tana tunanin yaje yaga sahibarsa Zulaihat... D'an satan kallonta shima yayi sanda ta mik'e tana gyara alkyabbanta ta rusuna tace " Abba na barka lafiya. Murmushi yayi kana yace " Allah Ya sada mu da Alkhairi mamata... Ficewa tayi Shattima ya d'an biebayanta da kallo don baiso Mai Martaba ya Kula kallon Zahida yake, juyowan da zaiyi ya sauk'e idonsa kan makeken hoton babyn nan, gabansa ya yanke ya fad'i sakamakon hango fuskar Jalal da yayi cikin hoton.....
Sameena ce 👌🏾
[1/23, 22:23] +234 803 619 0581: 🌘🌘🌘🌘 *ZUBAIDAH*
52
*©Sameena Aleeyou...✍🏾*
_Queen Samy Novels Forum...📖📚_
*Dedicated To All Victims Of Rape...*
"Har lokacin ta kasa saka komai a cikinta, hawaye na kan zuba a idanunta, Allah sarki Jalal koda ace yayi raping d'inta Ya cancanci yafiyarta balle ma ta yarda dashi tasan iyakar gaskiyarsa knn beyi ba, sa bayan hannunta tayi ta goge hawayen, Kamal ne ya matso kusa da ita kana yace " Didi wai inji Mama na uncle Jay bazai tab'a dawowa ba wai kullesa za'ayi...
"Wani hawayen ta kuma gogewa kafin tace " Zai dawo zai dawo garemu, idan kayi sallah ka ringa masa addu'a kaji.. Gyad'a kansa yaron yayi fuska fal damuwa kafin yace " Ina sonshi bana so ya tafi ya barmu... Kema kina sonshi ko Didi... Wani sabon kukan ya kufce mata, batasan sanda ta shiga nodding kanta da sauri ba gamida jawo Kamal ta rungumesa...
"Annah dake hangosu daga veranda ta goge k'wallan da suka cika idanunta....
"Cell d'in gefe da Jalal aka jefasu, ... Salim fad'i yake Officer you can't arrest us just like that, you've no clue who you really messing with...
"Labib kuwa hango Jalal yayi, fincikian k'arfen ya shigayi yana fad'in" This is all your fault you Trader, I swear I'm gonna make you pay for this,.... " Da k'arfi Jalal ya mik'e yana fad'in" Shut your Trap you criminal....
"Labib ya kuma watsa masa harara kafin yace " You're nothing but a Trader, how dare you betrayed us, bari kaga na fito daga wajen nan sai na sata ta k'aryata abinda ta fad'i......
"Naushin da Jalal ya kai masa ta cikin k'arafunan Ya hanasa k"arasa maganar,
"You Imbecile ka gama maganganunka akaina but the moment ka sake wani magana akan matata sai na kashe ka. Bas... tard..... Ya fad'i sanda yake komawa wajen zamansa...
"Janyo Labib Salim yayi kafin yace " K'yalesa kasan tsiyan talaka abinda ya gada knn, 'cause bai gaji arziki ba, we are getting out of here soon, and we will take our revenge.
"Zama kawai Labib yayi bisa benchin yana goge jinin bakinsa yana watsa mugun kallo wa Jalal...
***************
"A ranar da suka cika kwana biyu aka fito dasu za'a canza masu cell, gaba d'aya families d'in sun had'u a station harda Mamin Labib data riski labarin gangaratsau....
"Babu yanda Barr beyi ba akan abada belin su IG ya hana yace sai an shiga kotu sati mai zuwa duk abinda alk'ali ya yanke fine.. Coz bashida say a yanzu tunda ta shigar da k'ara..
"Hannayensu cikin handcuffs aka fito dasu, su mummy da Mami Me zasuyi banda kuka,..... Salim girman carpet da Ac jikinsa har wani daddaujewa yayi, jajazur kaman me borin jini a d'an kwana biyun da yayi cikin cell....
"Mummy Daddy pls take me out of this place, I can't stand it, pld Dad do something, don't let them take me away.... Haka Salim ya ringa fad'i polisawa na turasa suna fad'in move..
"Labib kuwa da taurin zuciya sai k'arfafa gwiwa wa Maminsa yake..
"Barr ne ya fito yana fad'in" Kar ku damu zanyi komai wajen tsaya maku... Uncle pls do something.. Salim Ya kuma fad'i...
"Kausar bata bari Asmah ta gama parking ba ta bud'e motar ta isa gaban Salim tana fad'in" You liar this is where you belong, make sure ka rubuta min takardan sakina....
"Kausar my love pls don't believe her, she's just lying... Bai kai aya ba Kausar ta kuma fad'in" Just shut up you imbecile, I'll give her my unconditional support, until I see you locked up in jell... Asmah ta shiga jan Kausar baya ganin Journalist sun cike wajen sai d'aukan rahoto suke, sai faman d'aukan fuskar Kausar suke yanda take zuba masifa ma Salim...
"A kunnenta Asmah take rad'a mata Kausar let's get out of here, kinsan su Pappy basu san mun fito ba, zasu k'ara fushi sosai tunda an hanaki fita... Kan su ankara sai ganin abokan aikinta Journalist wa'enda basa good terms suna d'aukanta suna fad'in" Mrs Salim Dasuki da alama kema baki bayan mijin naki knn da gaske ne kema kin yarda ya aikata laifin da ake zarginsa ko kuma dama wann hali d'abi'Anas....... Jawo mayafinta Kausar tayi ta shiga rufe fuskarta tana tutture Jama'a tana neman hanyan fita daga wajen....
"Daidai sanda aka bud'e masu motar masu laifi adaidaitan su Zubaidah ya paka a wajen itada Annah...
"A guje ta fito gamida k'walla masa kira da k'arfin gaske " JALAAAL, a hankali ya furta Zubaidah, saurin juyowa yayi sukayi ido hud'u gaba d"aya mutanen dake wajen kallo ya koma kanta.... Gefe da ita ya hangi Umar ya paka motarsa ya fito....
"Fincika yayi da k'arfin gaske yana fad'in" Don't come near my wife, don't you dare come near her, I swear I'll kill you.... Gaba d'aya kallo ya kuma komawa kan Umar....
"Gaban Zubaidah yayi wani irin yankewa Annah ta rik'eta sosai tana fad'in" Kar ka damu Jalal, I'll look after her for you, I'll take care of her...
"Just take care of yourself son...
"pls Annah do that for me, ki kular min da ita....
"Cikin kuka Zubaidah take fad'in " Don't worry I'll be safe, promise me you'll come back to me....
"Siriryar hawaye ta fito daga idanunsa sanda ya furta I love you.... Kafin ya shige bayan motar....
"Hanki d'in hannunsa kawai take hangowa har motar ta wuce....
"Annah tayi saurin rik'ota suka nufi adaidaitansu sanda Journalist sukayi chaaa akanta suna jefo mata tambayoyi.....
"Alh Kasim ya kafe Umar da ido kafin ya sunkuya saitin kunnen Barr yace " I thought we made it clear to that idiot that he should get lost, what heck is he doing here??
"Barr kuwa wata murmushi ya Saki kafin yace " Zai mana amfani, bai jira cewar Alh Tahir ba ya saci idon Jam'ma'a ya nufi motar Umar, zama yayi a Front seat yana fad'in " Keep driving...
"Galala Umar ke kallonsa kafin yace " Ban gane ba ina zan kaika,...
"Gajeren tsaki Barr yayi gamida fuzar da iska kafin ya kuma fad'in" Don't be such an idiot just keep moving.
"Karya staring mota yayi kafin suka mik'a titi.....
***************
"Tunda suka soma tafiya hankalin Annah ya karkata kan tunani guda, ina zasu samu lawyer wani lawyer ne zai tsaya masu, kai komai na duniyar yanzu ma saida kud'i yaya zatayi....
"Hannun Zubaidah taji cikin nata, tayi saurin d'agowa tana kallonta,.
"Murya na rawa take fad'in" I'm sorry Annah, believe me nima bana son ganinsa cikin wann halin, da nasan zai tafi police station da banyi provoking d'insa ba.....
"Damk'e hannunta sosai Annah tayi tana girgiza kai kafin tace " None of this is your fault Zubaidah, abinda Jalal yayi yayi daidai, let them all be punished, sun zalunceki, they shouldn't get away with it, Allah yana nan baya bacci da sannu zaibi kadin mai gaskiya...
"Babban abinda ke gabanmu a yanzu shine samun lawyer.... D'an jimm Zubaidah tayi kafin ta d'ago da sauri tana fad'in " Dr Khaleesat,.... We should talk to her right away maybe she can help....
"Shiru Annah tayi tana dubanta tana nazarin maganan nata kafin tace " Dr Khaleesat tana mana k'ok"ari I don't want us to be a burden to her...
"Damuwa ya kuma nunawa a fuskar Zubaidah, shiru tayi ta shiga wani tunanin daidai lokacin da mai tasi ya ajiyesu....
"Da mugun mamaki suke kallon motar dake pake k'ofar gidansu, k'irjinsu ya yanke ya fad'i lab'ewa bayan Annah Zubaidah ta soma tana fad'in" Annah bazasu tab'a k'yalemu ba na sani....
"Annah ta rik'e hannunta sosai cikin nata tana fad'in" Kar ki damu babu abunda suka isa su mana, muje...
"Kausar tana hangosu tayi saurin fitowa a motar, ganin Kausar ya basu mamaki, take Zubaidah ta had'e rai tana fad'in" Me kike nema a nan, me ya kawo ki nan, kinzo ne ki kuma k'aryatani kaman yanda mak'aryacin azzalumin mijinki yayi, idanma kinzo sayan mu da kud'ine kaman yanda kuka saba toh ki sani bakuda arzikin da zaku sayemu... We won't back down. Justice must be served.....
"Annah ta dubi Kausar kafin tace " Kinji da kunnuwanki toh tun wuri ki tafi kafin muyi filing retraining order against you....
"Rik'ota Asmah ta soma tana fad'in" Mu tafi Kausar....
"Kausar ta soma girgiza kai cike da tausayi kafin tace " Kar kuyi tunanin ina tareda su, wllhi bana tareda su, nima babban burina shine na gansu behind bars, hawaye ya soma zuba a idanunta sanda taci gaba da fad'in" Auren Salim shine babban kuskuren da na tapka, ta rik'o hannayen Zubaidah duka biyu taci gaba da fad'in" I'm here for you, I want to help I want them to be punished, pls don't push me away, let's do this together.....
"Girgiza kai Zubaidah ta soma kafin tace " Pls leave we don't want more trouble, idan suka san we are seeing each other, things might get more complicated.
"Annah ta gyad'a kanta tacee" Haka ne Kausar, kinga family d'inku are related Don Allah ku tafi kafin ku b'allo mana wani abun...
"Goge hawayen idanunta tayi kafin tace " They will never find out,... Kun sami lawyer ne..?? Ta tambaya tana dubansu..
"Shiru kaman babu me cewa komai cikinsu Annah tayi murmushi tace " Kar ku damu zamuyi komai cikin talaucinmu Ko bamuda kud'i do mulki munada Allah, da sannu zai kawo mana mafita, snn abu na k'arshe dan Allah kuyi nesa da gidan... Mun gode k'warai da kulawarku.. Daga haka taja hannun Zubaidah suka shige gida...
"Asmah taja hannun Kausar suka shige mota..
"Suna tafe Asmah ta d'an juyo ta dubeta sanda take karya Stairing mota kafin tace " Kausar I think they are right, we shouldn't be creating more problems, the Dasukis have eyes everywhere, they might be watching all our movement especially now that we are against them....
"Harara Kausar ta galla mata da rinanaun idanunta masu zuban ruwa kafin tace " I don't care, they can do their worse but I swear I won't back down har sai na gansu cikin k'unci da damuwa like the way they caused me , I want to see them suffering, I want to see them going down.... Ta k'arashe maganar tana huci ita kad'ai.....
"D'an sauk'e ajiyan zuciya kawai Asmah tayi gamida maida hankalinta ga driving....
"Suna gama parking a haraban gidan suka hango Pappy daga saman balcony hannayensa hard'e a k'irji ya kafesu da ido fuskan nan tamau.. K'irjinsu ya soma dukan uku uku......
Sameena ce 👌🏾
[1/23, 22:23] +234 803 619 0581: 🌘🌘🌘🌘 *ZUBAIDAH*
53
*©Sameena Aleeyou...✍🏾*
_Queen Samy Novels Forum...📖📚_
*Dedicated To All Victims Of Rape...*
*Where are you Bintu Abiha and Habiba love... This one's for you guys, I read your chats jiya and nasha dariya sosai sosai oo 😂😂... 😍😘*
"Sosai Pappy Ya masu fad'a Mumsy ma fad'an tayi masu sosai, Harta car keys d'insu saida ya karb'e yace " No should drive again har sai komai ya lafa....
"Kafin dare an soma yad'a abinda Kausar tayiwa Salim a social media 'yan adawan siyayasan Pappy abu ya masu Dad'i..
"Shiru yayi gamida k'ura ma Video d'in ido, yasan wann kad'an ne da aikin Alh Kasim, he promised to ruin him completely, kan kace me party chairman d'insu ya kira urgent meeting akansa, a halin yanzu ana gab da amshe ticket d'insa na presidential election....
"Zama yayi yana nazarin kalaman Barr.
_We want you to testify against Zubaidah in court_
"Zulaihat ne ta zauna gefe dashi gamida rungumo kansa cikin k'irjinta tana wani mayaudarin murmushi. Gani tayi gaba d'aya hankalinsa baya tare da ita, d'an rik'o kumatunsa tayi kafin tace " Hey what's the matter, meke damunka....
"Sauk'e ajiyan zuciya yayi kafin yace " Zubaidah Filed a complaint...
"Zama da kyau Zulaihat tayi kafin tace " So, meye naka na damuwa ka kyalesu suci kansu...
"Shafa fuskarta yayi kafin yace " Kin tuna nace maki you'll help me to get my revenge on them ita da mijinta....
"D'an jim Zulaihat tayi kafin tace " We are living a happy life nida kai bana so muyi engaging kanmu cikin wani matsala...
"Mayaudarin murmushi yayi kafin yace " No matter what I'll never leave you alone, just help me do this kinji baby na.
"Ganin tayi jim tana dubansa yasa kamo kugunta sosai snn yaci gaba da fad'in" Pls Baby do this for me ko baki son ganin farin ciki na ne,
"D'an tab'e fuska tayi kafin tace " Toh me zaisa ka damu dasu bayan yanzu haka ma cikin tashin hankali suke...
"Wata murmushi ya kumayi kafin yace " Idan naga ta rabu da Jalal har abada zaifi komai yi mun Dad'i, snn na maki alk"awari bazan koma mata ba, kinsan ina sonki, as they say, if they love you they will come back to you, kinga da na tafi ai na dawo gareki meaning I can't do without you, so iyaka abinda zaki iya mun shine ki taimaka min na d'au fansan abinda aka mun...
"Murmushi Zulaihat tayi kafin tace " Toh how may I help you,
"Shafa low cut askinsa yayi kafin yace " Zubaidah spent a night here with you, meaning ta gudo daga Chan gidansu, I want you to give your testimony in court...
"Da mamaki Zulaihat ke kallonsa kafin tayi magana yace " this is all I'm asking of you my love, I'll explain everything to you later. Yanzu barin mana placing order ina zuwa, daga haka ya mik'e ya fice yana neman layin Barr Munir...
*************
"Tun daga k'ofar abisitin tasha jinin jikinta, kamar wacce k'wai ya fashe ma a ciki haka take tafiya..... Ai tun daga k'ofar ward d'in da ya hangota ya mik'e yana fad"in " Kar ki k'araso nan, kar ki kuskura kiyi gigin zuwa kusa da d'ana kije wajen d'an iskan sairayin naki tunda mun baku space sosai yanzu a gidan, but don't you dare think of coming closer to my son...
"Mum rakub'ewa tayi jikin garu tana kuka.... Daidai nan cops suka iso, Alh Maina ya mik'e da sauri yana fad'in " Lafiya officer..
"Guda d'aya daga cikinsu yace " Lafiya Sir, muna nan ne don tsaron d'akin da d'anka yake
...
"No.. No Officer you can't do this, my son isn't out of comer yet, idan ya ganku hankalinsa zai kuma tashi...
"We are sorry but we are only doing our job..You there you over there.... Haka ogan nasu ya jejjefasu kowa da wajen da ya tsaya.....
***************
"Yau ya rage saura kwana uku a shiga kotu gashi basu sami lawyer ba, gashi Dr Khaleesat bata nan ta tafi wani seminar a Lagos, gaba d'aya abu ya rincab'e masu, Gashi tun baya kama su Jalal Usman bai lek'o ba, Annah har garejinsu taje bata sami Usman ba, abokan aikinta na makaranta ma ta baza cikiya neman good lawyer, amma kunsan mutum a yau komai saida abin duniya... Zubaidah kullum cikin kuka take, Ga Hadiza ta sakata gaba da tsangwama tana cewa laifinta ne, datayi hak'uri da Jalal bai kai kansa ma polisawa ba, kuma wllhi ta zama bazaura bazata zauna da ita ba, tayi d'awaiyinyarta tun k'uruciya bazatayi har zauwarci ba....
"K'unci ya taru ya mata yawa, kullum cikin addu'a da neman taimakon Allah suke.....
***************
"Asmah pls, wllhi nasan basu sami lawyer ba, you know how people are nowadays,.....
"Ajiye littafin hannunta Asmah tayi kafin tace " For crying out loud Kausar me kuma kike so nayi, kina ganin irin fad'an da aka mana da irin dokar da aka sa mana a gidan nan, me kike so nayi, na gaji da taro mana damuwa da kike yi....
"Tasowa tayi daga saman gadon kafin tace " Kina zuwa school kina samun Chance na fita, that's why I'm asking you to do this, don Allah ki samar masu lawyer I'll take are no fun his bills all I want is for justice to be served, Asmah kema fa mace ce, kuma kar ki manta ciwon d'iya mace na d'iya mace ne, it could happen to us, zamu iya zama Victims muma, pls Sis let's do this.....
"Shiru Asmah tayi kafin tace " You are absolutely right, but abun da muke niyyan yi yanada matuk'ar had'ari ba garemu kawai ba harda family d'inmu, idan suka sani zasu sa wa pappy harma damu takunkumi, kiga videos d'in da suka watsa suka sa aka dakatar da pappy a jamk'iyarsu, what if they find out we are helping her, things might get worse...
"Kausar ta goge hawayen idanunta kafin tace " Na sani, kar ki damu akwai Allah bazai barsu suyita zalunci ba, let's do it...
"Asmah ta rik'e hannunta sosai kafin tace " Zanyi zanyi Kausar sabida ina son ganin murmushinki randa aka jefa Salim a prison. Rungume juna sukayi suna hawaye....
*************
"Tsaye suke a bargan dawakin Mai Martaba suna zab'an dokin da zasu hau su fita kilisa,
"Khalifa ya dubi Shattima da gaba d'aya 'yan kwanakin nan ya canza, dafasa yayi kafin yace " Wai meke damunka ne, kwana biyun nan kana looking dull,
"Murmushi Shattima yayi Wanda iyakacinsa fatar baki kafin yace " Babu komai kwai banjin Dad'i ne kwana biyun nan...
"Khalifa yayi wata k'asaiteccen murmushi kafin yace " Ko kuma kana tunanin Gimbiya Zahidar ka ta kusa zama Mallaki na a ranar da za'a nad'ani sarautar Yariman masarautar nan...
"Galala Shattima ke kallonsa kana yayi murmushi yace " Zahida ta fah kace.
"KKhalifa ya gyad'a kai yace " K'warai kuwa kowa yasan irin shak'iwar dake tsakaninku tamkar yaya da k'anwa, a ranar data zama matata zan saka maka katangar k'arfe tsakaninku tunda de kai ba muharraminta bane..
"Murmushi kawai Shattima yayi sanda yake d'ale doki had'i da yin gajeren tsaki kafin yace muje da Allah, dan wllhi muka k'ara minti biyu bamu fita ba zan fasa fita kilisan nan....
"D'ale doki Khalifa yayi yana mai ci gaba da fad'in jikina na bani nine sarki mai jiran gado.
"Shattima baice komai ba sai tunanin da yake yawan yi a 'yan kwanakin wanda ya rasa ma waye zai soma fad'i gashi abun ya damesa sosai...
*Manage this 'yan uwa zaku jini later insha Allah... 😘😍*
[1/23, 22:23] +234 803 619 0581: 🌘🌘🌘🌘 *ZIBAIDAH*
54
*©Sameena Aleeyou...✍🏾*
_Queen Samy Novels Forum...📖📚_
*Dedicated To All Victims Of Rape...*
"Kai tsaye gida ya wuce bayan sun sauk'a daga dawakin.
"Parlron Ummansa ya shige ya tarar babu kowa sai TV dake faman aiki.
"Zama yayi gijif cikin sofa gamida turo hulansa gaban goshi ya lumshe idanunsa,
"Umma ce ta fito tana k'wala kira wa Ameera k'anwar Shattima.... A'ah Shattima yaushe ka shigo, Umma tace sanda take zama cikin d'aya Daga cikin kujerun.
"D'an mik'ewa yayi ya zauna sosai kafin yace " Ummah barka da gida.
"Tsaresa tayi da idanu don ta lura da canzawansa kwana biyu.
"Bud'e murya Umma tayi kafin tace " Kai wai lafiyanka kwana biyu kake neman zama lusari, gaba d'aya ka canza kaman bakai ba, idan akan auren yarinyar nan Zahidah da Khalifa ne, na fad'a maka ka cire ta a ranka, Zahidah ba matarka bace sanin kanka Baba Ciroma ba barin wani zaiyi ya auri Zahidah ba tunda ya k'wallafa ma wann d'an nasa mai wuya kaman marken lema....
"Tunda ta soma magana Shattima ke kallonta, Umma dai bazata Tab'a canzawa ba, wnn masifa nata ya rasa taxation da ita...
"D'an jim yayi kafin yace " Umma am I that obvious??
"Wani uwar harara ta kuma watsa Masa kafin tace " Bana son iskanci Karma ka soma min turancin rashin kunya ka bud'e baki ka fad'a min abunda ke damunka baka da wacce ta wuce ni mahaifiyarka...
"Shattima ya kuma sauk'e ajiyan zuciya kafin yace " Ummah ba tunanin Zahidah nake ba, besides na cire Zahidah a raina tuntuni tunda yau wata uku cif ya rage aurenta da Khalifa childhood friend d'ina, abinda ke damuna wani abu ne daban snn tun da akayi maganar aurenta take avoiding d'ina, Umma bazan iya jure rashin maganarta a gareni ba..
"Shek'ek"e ta kallesa kafin tace " Au ka yarda ka bari wani ya aureta, ka yarda ka badakai a aura mata wanda bata so...
"Kllonta kawai Shattima keyi cike da mamakin halin Umma saikace ba itace yanzu take masa fad'an ya cire Zahidah a ransa ba..
"D'an fitowa yayi daga cikin kujeran ya turo gaba kafin yace " Umma ba wann ba, wani tambaya nake so na maki..
"Ina jinka menene?? Ta fad'i tana karyan goro.
"Tab'e fuska yayi yana dubanta kafin yace " Umma wai Don Allah ke ba tsohuwa ba sai cin goro, bakisan illansa ba koh..
"Tab'e baki tayi gamida ci gaba da taunar goronta tana fad'in" Idan ka gama iyayinka da felek'en sai ka sanar dani Likita bokan turai, kai wannan da likitanci ka karanta da kad"ifirin naka da yauk'in yafi haka..
"Shafa kansa yayi gamida bata hak'uri.
"Saida ya cire hular kansa ya ajiye saman hannun kujera kafin yace " Umma kince mun matar Mai Martaba ta fari d'iyar sarkin Zazzau k'awarki ce kafin Allah Ya mata rasuwa...
"Cak ta tsaya da taunar goron da take tana dubansa, k'walla ya ciko idanunta,...
"Shattima yaci gaba da fad'in" Umma wai meye asalin labarin mutuwarsu itada jaririnta Modibbo,..
"Umma ta goge hawayen idanunta kafin ta soma fad'in" Dadda (sunan da ake kiran marigayiya matar mai martaba a masarautar)d'iya ce ga sarkin Zazzau wanda yake sonta sama da sauran 'ya'yansa, zata girme mun a shekare sabida lokacin da aka auro ta masarautan nan ba'a ma soma maganar aurena ba, auren soyayya na saurayi da budurwa sukayi da Mai Martaba, a lokacin da akai masa wankan nad'in sarauta a lokacin aka Aura masa ita..
"Sun d'au lokaci sosai Allah bai basu haihuwa ba, don har akayi aurena da mahaifinka shiru babu labari, Nida Matar Ciroma k'anin Mai Martaba a jere muka haifeku kaida Khalifa amma har lokacin shiru matar Mai Martaba bata haihu ba, kasan babban gida da k'anan maganganu musamman ganin K'aninsa ya haihu shi bai haihu ba, ..
"Mahaifiyar Modibbo da kanta ta rok'i Mai Martaba ya k'ara aure, snn ita da kanta ta zab'awa Mai Martaba yarinyar da zai Aura, ko ya sani a masarautar nan baya son auren amma sabida Mahaifiyar Modibbo da kuma Mahaifiyarsa shi kansa Mai Martaban suna so yasa sa amincewa, nan aka auro mahaifiyar Zahida a lokacin bata fi shekaru goma Sha biyar ba zuwa sha shida, ashe tun lokacin da akayi auren Mai Martaba da Ummin Zahida Dadda nada juna biyu babu wanda ya sani.... Bayan biki da kad'an cikinta ya bayyana, nan fah kulawa ya tattara ya koma kanta gaba d'aya, Mai Martaba har mancewa yayi yayi amarya, Madaki mahaifiyar Mai Martaba nan itama kulawarta ya k'arau sosai akan Dadda, wann dalili ya sanya Ummin Zahida cikin tsananin bak'in ciki ga k'uruciya da yarinta, a lokacin har saida suka sami sab'ani sosai da Mai Martaba, Dadda matar arziki 'yar Babban gida ita ta gyara komai, suka ci gaba da zamansu lafiya, taci gaba da rainon cikinta, wata tara cif ta haihu, haihuwar da ba'a tab'a irinsa ba a masarautar nan, anyi biki na haihuwarsa wanda ba'a tab'a irinsa ba yanda yaro yaci sunan Modibbo Lamid'o....... Kukan Umma ya tsananta.. Shattima ya tashi daga kujeran da yake ya dawo gefenta ya zauna gamida rik'o kafad'unta...
"Goge hawayen tayi kafin taci gaba da fad'in Daren da akayi suna da kwana bakwai daren data zama bak'in dare a wann masarauta daren da ya sauya farin cikin wann masarauta zuwa bak'in ciki, daren da har yau ya kafa tarihi a masarautar nan, daren da aka masa lakabi da BAK'IN DARE, a wann dare aka wayi gari aka tarar da gawan Dadda snn aka nemi Yarima Modibbo aka rasa......
"Kuka sosai Umma keyi har saida Shattima yaji dama bai d'ago maganar ba, da k'yar ya samu ya lallashi Umma tayi shiru. Mik'ewa yayi ya fice ya nufi d'akin sa yana tunanin al"amarin " What if Modibbo is still alive, what if..... K'irjinsa ta shiga bugawa da sauri da sauri, What if Jalal is Yarima Modibbo, But.... How's this be possible....? No way Jalal has his own family , mahaifiyarsa tana nan da rai, ta yaya ma zai soma fad'in wann abu, da Mai Martaba zai soma ko kuwa da Jalal zai soma.... Toh wai ma how did he come up with all this, dafe kansa yayi gamida zama bisa sofa, yana addu'an Allah Ya bayyana Modibbo a duk yanda yake matuk'ar yana raye...
*****************
"Hamma ne ya fita ya amsa sallamar da ake, ganin mutum cikin bak'ak'en kaya black suit yasa sa komawa cikin gida da gudo yana neman abun d'auka, can ya hangi muciya wajen wanke wanke ai nan ya rarumo muciyar nan ya nufo waje a guje...... Zubaidah dake kwasan shanya a sittin ta biyo bayansa tana tambayarsa lafiya...., Annah ma fitowarta kenn daga bayi ta ajiye butar hannunta tabi bayansu cikin sauri.
"Hamma kam fad'i yake " Turoka sukayi koh, wai zaka gane kuranka..... Da iya k'arfinsa ya nufi bawan Allahn nan, Zubaidah tayi ta maza ta k'wace muciyar hannun Hamma tana fad'in" A'a a'a Hamma....
"Barr Ansar Kumo dafe kansa yayi yana jiran ta Allah ta samesa...
"Zubaidah ta shiga jan Hamma yana fizgewa yana fad'in" Ki barni na gama dasu ki barni dasu Zubaidah, sunga babu Jalal suna tunanin zamu bari su ci zarafinki...
"Gida ta shige dashi yayinda Annah ta k'arasa ga Barr Kumo tana fad'in" Lafiya bawan Alla, idan Dasuki ne suka turo ka tun wuri gwara ka tafi kafin mu kira maka 'yansanda...
"Kallonta Barr Kumo yayi kafin ya sauk'e nannauyiyan ajiyan zuciya yace " Sannu Hajiya.... Em by the way sunana Barr Ansar Kumo, ni lauya ne daga k'ungiyar kare rajin hakkin bil adama musamman Mata da k'anan Yara....
"Cike da rashin hamsuwa Annah ke kallonsa don tasan Dasuki's zasu iya turo sa,... Zubaidah ce ta fito Hadiza na biye da ita....
"Barr Kumo ya dubi Zubaidah data masa k'uri yace " Kar ku damu banazo nan bane don cutar daku sai don taimaka maku ......
Katsesa Hadiza tayi da fad'in" Malam ka dubeka kasha bak'in kaya uwa d'an fashi kai ai da ganinka ma babu alheri a tare da kai, .. Hararan da Annah ta narka mata yasata yin shiru....
. "Girgiza kai Zubaidah ta soma kafin tace " Malam ka fad'a mana gaskiyan wanda ya turo ka wajenmu nasan sai ankai k"orafi kungiyarku snn kuke ba wa mutum d'auki, mu kuwa bamu kai ba don bamu da hanya, nasan su suka turo ka don fad'ar damu a kotu, Kayi wa Allah ka tafi ka k'yalemu, ka tuna idan hakan ya faru akan d'yarka yaya zakaji. Don Allah kar ka taimaka masu su ci gaba da zalunci...
"Tausayinta ya cika zuciyar Barr Ansar, sauk'e ajiyan zuciya yayi kafin yace " Kinyi gaskiya Zubaidah snn labarinki ya zama media circus, yasa hannu ya ciro jarida cikin 'yar jakan dake hannunsa ya nuna mata kafin yace " Kin gani, a halin yanzu labarin ki is everywhere a cikin k'asar nan, people are curious to know more about you, Zubaidah ni na kawo kaina nan da ra'ayina ba tareda taimakon wata k'ungiya ba....... Idonsa ya kad'a yayi ja sosai sanda yaci gaba da fad'in" Those Despicable are hiding behind their shadows, they must pay for each and single crimes they had committed....
"Gaba d'aya suka bisa da kallon mamaki sanda yasa bayan hannunsa ya goge hawayen da suka zubo masa.
"Annah jiki a sanyaye tace mu shiga daga ciki.....
"Daga yanda Faisal ya paka motarsa ya danna wayarsa, bugu biyu Alh Kasim ya d'aga " Ina saurarenka Faisal..
"Sir no doubt they've got an attorney.......
"Mik'ewa tsaye yayi yana fad"in what.!!!!!
"No way they can't find a lawyer, abinda nake so da kai follow him and see who's helping them, Faisal bana so a sami failure make sure kayi clean aiki... Yeah I trust you..... Daga haka ya katse wayar yana safa da marwa shi kad'ansa a parlour....
"Yanda Alh Kasim ya umurcesa haka yayi..... Har suka shigo cikin Abuja Barr Kumo baisan ana biye dashi ba. A k'ofar gidansa dake unguwar APO yayi parking ganin Asmah cikin tasi tana jiran isowarsa....
"Fitowa tayi daga tasi d'in sanda shima ya fito daga motarsa suka sakar ma juna murmushi. A hankali tace " My chewing gum how does go.
"Murmushi Barr Ansar yayi kafin yace " My silly girlfriend na fad'a maki ni nafi k'arfin your chewing gum saidai your super glue. D'an hararansa Asmah tayi kafin tace " I'm not your girlfriend you know....
"Murmushi yayi kafin ya kuma cewa we can't talk here mu d'an shiga daga ciki, hararansa ta d'anyi kafin tace " I hope su mommin ka na ciki...
"K'walla ya kuma ciko idanunsa sanda ya soma tafiya ba tare da yace mata komai ba, d'an girgiza kai kawai tayi tabi bayansa tana fad'in" Ansar bazaka daina wann hali naka ba, a da nayi zaton ko wani abu ke damunka amma yanzu kam na gane tsaf halinka ne....
"Gida ne apartment me kyaun gaske, saidai tun daga waje Asmah ta gane kaman shi kad'ai yake rayuwa a gidan, parlorn sa tsaf yasha furnished sai picture wanda ba sai ance maka na family d'insa bane, saidai duk hotunan yana yaro ne Wanda bai wuce shekaru sha biyu ba, harda 'yan k'annensa mace da namiji guda biyu....
"Drinks ya kawo ya ajiye mata ta dubesa da kyau kana tace " Attorney kasan dai bazan sha komai a nan ba tunda da alama 'yan gidanku basa nan.....
"Mik'ewa tsaye yayi in a furious tune yake fad'in " Yeah basa nan kuma bazasu tab'a dawowa ba, I'm all alone, I've no family, ya k'arasa ya d'auko hoto guda d'aya yana nuna mata yake fad'in" Kinsan dalilin da yasa farko nak'i amince wa buk'atarki, kinsan dalilin da yasa nace maki " I didn't want to have anything to do with that Despicable Kasim Dasuki...????
"Zaro ido kawai Asmah take tana girgiza kai, Ansar yaci gaba da fad'in" That Bastard is the reason why I'm all alone now, that imbecile destroyed my Family,
"My Father was an international Business Man, Kasim Dasuki ya yaudaresa ya saka kud'ad'ensa gaba d'aya a company d'insu, back then bana zama a k'asar nan, ina can Qatar da Grandmother d'ina, My Dad my Mum and my two siblings were living here in Nigeria, rana d'aya heart attack ya kama mahaifina sabida karyasa da Kasim Dasuki yayi, Dad d'ina ya shigar da k'ara baiyi nasara ba, sabida Kasim Dasuki is very powerful Man, Mum d'ina tayi jinyarsa ya soma, babu yanda banso naga Mahaifina ba amma babu kud'in da zanzo Nigeria, Grandma d'ina da take jinya itama a can Qatar depression na ciwon mahaifina ya mata yawa, kwana kad'an Allah yayi mata cikawa, ni kad'aina no family no relatives ga k'arancin shekaru haka da taimakon bayin Allah na k'warai aka kai grandma makwancinta, Dad d'ina yana riskan labarin shima Allah Ya masa cikawa, .... Kukansa ya k'aru sanda yaci gaba da fad'in" I couldn't have chance to say goodbye to my Dad, Mum d'ina ta d'aukaka k'ara dare d'aya gidansu tayi gobara k'urumus, da Mamata da k'anne na guda biyu all died a gobaran. Ban tashi sani ba sai lokacin da na saka k"afata a k'asar nan, bayan shekaru masu yawa, bayan all the hardships I gone through ni kad'aina a k'asar Qatar, aikatau babu kalan wanda banyi ba, har na sami kud'in jirgi na dawo, na tarar da wann bak'ar labari wanda nasan ba aikin kowa bane illa aikinsa sabida Mum d'ina ta d'aukaka k'ara shiyasa ya halak'asu. Wann shine dalilina na zama lawyer to bring Justice to the society,...... Zama yayi bisa sofa hawaye na bin k'uncinsa,
"Tausayinsa ya cika zuciyar Asmah batasan sanda hawaye ya shiga gangara mata ba. Hanki ta ciro cikin jakarta ta mik'a masa, ya karb'a ya goge hawayen kana yace " Thank you....
"Har Asmah ta isa layinsu jikinta a mace yake da jin labarin Barr Ansar, ta k'ofar baya ta shige hide....
"Faisal da sai lokacin ya karya kan motarsa ya danna wayar uban gidansa kana yace " Sir the Marafa's are the ones helping them....
"Murmushi Alh Kasim yayi kafin yace " Alh Tahir Marafa dabinmu da kai bata k'are ba, I'll prove to that no one messes with the Dasuki's.......
"Wayan Barr Munir ya kira kafin yace " Ka bincika wanene wann lawyer d'in nasu his profession at work and his family.... Sai naji feeback, do that fast attorney we don't have much time, kwana d'aya jal ya rage mana a shiga kotu....
"K'asar akwatin ta ta bud'e ta ciro zoben tana murmushi, tasan wann ba k'aramin amfani zai masu ba tunda za'a shiga kotu, tasan Alh Kasim Dasuki zai biyata mak'udan kud'i ta gudu ita da d'anta taje ta sami miji mai hankalk tsaranta ba wann susu shashan ba..... Wata dariya Hadiza ta kuma fashewa dashi kafin ta sunce bakin zaninta ta d'aure zoben, mayafin ta ta shiga yafawa.....