"Jalal Ansar ku zauna a gida kawai ku kula da gida ni zan fice neman ta, zan wuce police stations na sanar da 'yan sanda ko Allah zai sa a dace, don kunsan tunda ba'a kama Umar har yanzu ba komai ka iya faruwa...
"Shattima ya gyad'a kai kafin yace " Haka ne, I'll go with you..
"Jalal da Ansar suka rako su har parking space, suna addu'an Allah yasa a dace.
"Cikin gida kuwa Annah da Zubaidah sai faman lallashin Hamma da Kamal suke...
"Motar Shattima sukayi anfani da suka fice. Bayan fitar su Ansar ya juya ya nufi d'aki dun gaba d'aya baya jin dad'i. Jalal ya take masa baya yana d'an d'ingisawa sabida ciwon sa...
"K'ofar d'akin Ansar ya tura ya shiga da Sallama...
"Zaune ya hange sa yana kallon hoton Asmah a cikin wayar sa, d'aya hannun sa rik'e da hoton family dinsa...
"Da sallama Jalal Ya shiga gamida zama gefen Ansar , har lokacin Ansar bai d'ago kai ba ga dukkan alamu hawaye ke zuba a idanunsa...
"Jalal ya d'anyi still kafin ya dafa Ansar da hannun sa maras ciwo, kasa ce masa komai yayi sabida tausayin sa dake ratsa zuciyar sa....
"Da k'yar ya iya furta " Friend kayi hak'uri......
"Cikin muryar kuka Ansar yake fad'in" No matter how hard I tried bro, but I just couldnt help.... Duk sun tafi sun barni Jalal, meyasa mutanen da nake so the most suke tafiya su barni, why why Jalal.... Ya k'arashe yana mai kifa kansa da gwiwoyin sa.....
"Jalal ya kuma dafa sa kafin yace " Kalan taka k'addaran da jarabawan knn friend, Allah Ya bamu ikon cin jarabawar mu baki d'aya... " Ka sani Ansar, we are all here for you, together we would overcome this horrible tragedy, snn insha Allah Umar bazai tsere ma jami'an tsaro ba, duk iya gudun sa akwai ranar da Allah zai kama sa, and he'll pay for all the crimes he's committed...
"Ansar ya d'ago Face d'insa da jajayen idanun sa had'i da d'aura hab'ar sa saman hannayen sa da ya dunk'ule waje guda...
"Cikin wani irin siga yake fad'in" Ba zallan aikin Umar bane, I'm quite sure the Dasuki's are behind this, na sani wnn aikin Alh Kasim ne, shi kad'ai ne yake farautar rayuwa ta, That imbecile took everything away from Me.... I swear, na ranste I won't rest until he's locked up in jell.... Da shi da 'ya'yan sa duk sai sun tafi prison snn a lokacin zai d'and'ani zafin rashi.... Ya k'arashe siriryar hawaye na gangaro masa....
""Jalal ya d'an basa light hug cike da tausayawa
***********
"Da k'yar ya samu jinin ya tsagaita, sai ciccija leb'e yake, a haka ya hangi wata motar kaya ta yo jidon doya zata shigar k'asashen north east, wato Arewa maso gabashin k'asar nan, yankin da Jihar Gombe take...
"Da dabara ya samu ya d'ale cikin doyan nan ya kwanta abinsa ba tareda kowa ya gansa ba...
"Mai trailer kuwa yana zuwa yaja motar sa ya d'au hanya....
"Da k'yar Faisal ya samu ya fice daga warehouse d'in da ya b'oye, da cizge baki da dabaran gujewa jami'an tsaro ya samu ya iso Dasuki Holding....
"Daga gate d'in baya ya kira wayar Barr ya sanar dashi halin da yake ciki yana buk'atan treatments amma yasan muddin ya tafi asibiti police will arrest him...
"Barr yayi wata murmushi yana kallon Alh Kasim kafin ya katse wayar yace " Ta zo gidan sauk'i abin farautar mu ya kawo kansa gida, ..
"A tamanin Alh Kasim ya mik'e yana fad'in" He shouldn't be here, idon 'yan sanda na kanmu... Babu shiri suka nufo waje suna neman sa ba tare da sanin kowa ba..
"Faisal kuwa daga yanda yake rakub'e ya hange su, ya fito cikin sauri ya nufesu yana jan k'afar da k'yar...
"Yana isowa yanda suke Alh Kasim ya d'auke sa da wani wawan mari... Kafin yace " This is exactly the reward of a Jerk like you.... Daga haka ya zaro k'aramar bindiga a gefen business suit d'insa yayi pointing Faisal dashi...
"Faisal yana girgiza kai cikin rashin yarda da abinda yake gani yake fad'in" Boss no.... No Boss kar ka min haka, ni ne Faisal babban yaron ka...
"Alh Kasim ya tintsire da dariya kafin yace " And also babban idiot, A jerk like you bai kamata yaci gaba da rayuwa ba, rayuwar ka na nufin mutuwa na, kaga idan ka mutu banida sauran damuwa zanci gaba da b'uya a inuwar Umar, baka raye balle idan yabada statement d'insa ayi tunanin zak'ulo ka ni kuma ka zak'ulo ni, snn kayi failing aikin ka tunda har yau Barr Kumo na numfashi.. So I'm sorry but you've to go..... Daga haka ya d'auke kan Faisal da harsashi...
"Shida Barr suka fashe da wata dariya, Barr yana nunsa yana dariya yake fad'in baka da kyau, kayi amfani da mutum ka yar dashi... Alh Kasim ya kuma murmusawa kafin ya hura bakin bindigar yayi ido masu James kafin suka k'araso, ya Kalli James yace " Get rid of this mess... Daga haka suka nufi motocin su shida Barr....
***************
"Saida suka zaga station uku kafin suka ci karo da case d'in Hadiza, 'yan sanda suka fad'a masu yanda abin yake, tun daga zuwan ta banki da kuma dalilin kawota cell...
"Ba Hafiz kawai ba harta Shattima saida yayi mamaki, toh me zai had'ata da Dasuki's... Suka kasa nemo amsar gaba d'ayan su ...
"Babu yanda basuyi ba a basu belin hadiza 'yan sanda sun k'i yarda, suka ce case d'in ba nasu bane, Alh Kasim tuni yayi pressing charges...
"Hafiz yayi shiru yana nazari kafin Shattima yace " Ai sai mu k'arasa can gidan muji ko akwai wani abinda suka sani gameda batun....
********
"Gaba d'aya mamaki ne ya ishe su, Hadiza da Alh Kasim toh ma ina zataga check, kai kurum Zubaidah ta shiga girgizawa tana fad'in" Bazata daina hali ba, ni na tabbata wani abin take k'ullawa tareda su a bayan idanun mu reshe ya juye da mujiya.
"Jalal ya sauk'e ajiyan zuciya yana tunanin toh me matar nan zata k'ulla da Dasuki's..
"Annah kuwa girgiza kai kurum tayi kafin tace " Yanzu abinda ke gaban mu shine muyi k'ok'arin sanin me take k'ullawa dasu ko ta samu ta kub'uta daga hannun 'yan sanda..
"Hafiz ya fuzar da iska kafin yace " Nifa abin ma wllhi ya dame ni ko kad'an na kasa gano me zai had'ata da wad'an nan mutane...
"Zubaidah ta d'an girgiza kai kafin tace " Idan dai Yaya Hadiza ce kunga kad'an, halin ta ne bazata canza ba, ni na tabbata wani abin take k'ulla min tare dasu, ina tausayin Hamma na, da Kamal,.... Ta k'arashe tana goge hawayen idanun ta... "Jalal ya d'an yi amfani da hannun sa guda ya d'aura saman yatsun hannun ba tareda kowa ya lura ba yana mai mata alama da idanu kan she should be strong...
"Annah ta bud'e murya tace " Aiko ko kusa kar ayi Hamma yaji wann zancen.... Kaman daga sama suka jiyo muryar sa yana fad'in"
"Na sani nasan bazata daina tsanar k'anwata ba, na sani wani abin take k'ulla mata tareda wad'ancan azzaluman mutanen. Kuyiww Allah kar ku karb'o ta, ku dubi girman Allah ku k'yaleta a can ta koyi darasin ta... Ta sha fad'i min inada nakasu a hallita na.. Amma ko kad'an ban d'auki hakan nak'asu ba don ban zamto tamkar ko wani namiji ba..
" Allah Ya gani a iya zaman mu ban tab'a tauye mata komai na rayuwa ba, ta zalunci Zubaidah tun tasowar ta, Na sani Allah bazai barta haka kurum ba taita aikata zalunci a bayan k'asa ba.. "Ya k'araso gaban su sosai yake kuka duk ya jik'a hannun rigar sa sabida goge hawaye kafin yaci gaba da fad'in" Zubaidah kin ga yanda Allah ke canza Al'amran sa koh,.... Duk hassadar da take maki kullun ci gaba kike, ki yafe ni k'anwata babu yanda na iya ne tuntuni...... "Bai kai aya ba Zubaidah ta k'arasa ta rungume sa tana fad'in " Hammaaa.... Kuka ya kufce mata, sosai shima yake kuka..
"Gaba d'aya suka tausaya masu...
"Bayan wasu mintoci Shattima ya masu sallama kan cewa da safe jet d'insu zata d'aga zuwa Gombe..
"Har bakin parking space Jalal ya rako sa suna ci gaba da wata 'yar tattaunawar su..
"Shattima ya dubesa yana murmushi kafin yace " Prince you and I need to have a serious talk...
"Ya kamata a koya maka d'abi'un Babban gida da madafan iko, ..
"Jalal ya d'an Harare sa kafin ya Tab'e baki yace " Kaima kasan nazan iya wann abubuwan hidiman sarauta sarautan nan ba, it sucks, besides I'm only ordinary, I'm not used to all those kind of things...
"Shattima ya murmusa kafin yace " Then you must adopt... Kai fah dole ne ka zama committed don lokacin hutu na nima yazo, zan maka handling abubuwa da dama...
"Jalal bai saurare sa ba ya k'arasa ya bud'e masa marfin mota yace " Oya zo ka wuce you talk too much...
"Shattima ya murmusa ya shige kafin suka kuma yin sallama...
"Tsaye yayi yana kallon su daga bakin k'ofa itada Kamal tana kwance gefen sa tana karanta masa tarihin Annabi Yusuf yanda 'yan uwansa suka masa duka suka jefar dashi but at the end ya taimake su...
"Jalal sai murmushi yake yana hangosu itada ya ransa watarana hakan ne zata kasance da izinin Allah....
"D'an gyaran murya yayi had'i da sallama kafin ya shigo d'akin...
"Zubaidah ta mik'e tana rufe sharab'arta da suka bud'e.. Kamal kuwa da gudu ya tafi wajen Jalal yana fad'in " Uncle Jay kaima ka d'aura irin abinda John Cena ya d'aura a hannun sa ne...
"Jalal yayi murmushi ya durk'usa yana shafa kan yaron kafin yace " Yes Champ amma kasan reason d'ina na sakawa..
"Kamal ya girgiza kai alamun a'a..
"Jalal ya murmusa sai satan kallon Zubaidah yake kafin yace " Ciwo naji amma soon zan cire kaji na ci gaba da d'aga ka sama harma da Didi ..... Ya k'arashe yana kallon ta...
"Kamal tsalle yayi yana murna Jalal ya d'an dunk'ule hannu yana fad'in" Give me punch... Kamal ma yayi yanda Jalal yayi suka d'an buga hannayen su a tare lightly.... Gaba d'aya sukayi dariya kafin Kamal ya fice yana fad'in" Zaije duba Umman sa ko ta dawo.... Cike da tausayi suka bi yaron da kallo....
"Ya rage daga Zubaidah sai Jalal a cikin d'akin. Babu wanda yace ma kowa k'ala sai yunk'urin mik'ewa da take daga saman gadon..
"Kafin ta tashi saiji tayi ya mata runfa... Suka shiga kallon juna cikin ido.... Ga k'irjinta dake faman lugude...
"Gaba d'aya ya sauk'e nauyin sa saman k'irjinta kasancewar bai iya amfani da d'aya hannun sa...
"Yana jin yanda jikinta ya soma shaking.... " Cikin kunnenta yake rad'a mata, Why..? Are you still not ready... Ya k'arashe cikin kashe murya yanai mata wasu salo masu rikita ta...
"Kwiwkicewa tayi kafin ta soma fad'in" Ya Jay this is not the right time neither the right place , kaga Kamal zai iya shigowa any moment.. And.... And... Kuma Baka da lafia....
"Dad'a tura kansa cikin wuyar ta yayi yana rad'a mata " Bakiji addu'an da Abbah da Annah suka mana bane, suna son ganin grandchildren d'insu, basu san ke ce kika hana a samo grandchildren d'in ba...... "Zubaidah dai gaba d'aya ko sauraren sa bata yi, burin ta kawai ya tashi daga kanta.... Shi kuwa Jalal yayi nisa wata duniya....
"Har saida ya zame ya d'an fad'i kan hannun sa mai ciwo..
"D'an k'ara kad'an yayi sabida zogi da ya ji wajen na masa...
"Zubaidah ta tashi a firgice, hankali tashe take rik'e hannun sa tanai masa sannu idanunta duk sun firfito waje sabida tashin hankali..
"Da zafi ko, ka fama ciwon ka koh, oh my Allah barin karb'o first aid a wajen Annah ta K'arashe maganar tana k'ok'arin kintsa kanta zata sauk'a daga gadon ya rik'ota ya rungume cikin jikin sa had'i da lumshe dogayen idanun sa... " A hankali ya furta "I love you Zubaidah...
"Tayi lamo cikin jikin sa tana shak'an k'anshin body spray na AXE ba tareda ta iya furta koda kalma guda ba...
"Sun d'an jima a haka kafin suka jiyo muryar Annah daga downstairs tana kiran Jalal sun san bazai wuce shan maganin dare ba...
"K'ofa ya bud'e ya d'an dafa staircase kafin yace " I'm coming Annah..
"Annah tace ka kira Zubaidah ma itama tasha nata maganin...
"Jalal ya amsa da toh Annah, yana mai kallon Zubaidah yana d'aga mata gira had'i da murmushi irin itama lambar ta Ya fito d'in nan....
"Zaune suka same su gaba d'aya a parlor Ansar yana daga balcony yana amsa wayar inspector akan maganar Case d'in Hadiza...
"K'arasowa parlorn yayi ya same su bayan ya gama wayar kafin yace " That was inspector Bilal, ...Suka kad'a kai gaba d'aya suna kallon sa kafin yaci gaba da fad'in" Har yanzu no news on Umar, snn ita kuma Hadiza tak'i magana, tak'i fad'in dalilin da yasa checks d'in Alh Kasim ya isa hannun ta... Shi kuma Kasim Dasuki yayi blaming namu da cewa muna turota ta masa sata ne don ya sami kariyar arziki, ita kuma tak'i magana kwata kwata balle a k'aryata sa, that Jerk can do anything to frame us, don kawai yayi dividing attention d'inmu for the forthcoming trial, shari'ar da yasan dole ya tafi Jell da izinin Allah...
"Jalal ya d'anyi shiru yana nazari kafin yace " I've feelings that she's hiding something from us, what if she's working with them, the Dasukis..
"Annah ta katse sa da girgiza kai kafin tace " Don't jump to conclusions mu jira har lokacin da zata sadududa ta fad'i gaskiya tunda wajen ba dad'in zama ne dashi ba....
"Gaba d'aya sukayi na'am da batun Annah, k'ok'ari suke suga suna d'an kawar ma Hamma tunanin abin, shi kuwa Kamal ce masa sukayi maman sa ta tafi Dukku ne ba jimawa zatayi ba...
**********
"Washe gari Shattima yayi rakiya wa Mai Martaba zuwa k'asar ta Gwambawa d'iban fari...
"Ba tareda saninsu ba Mai Martaba yayi hiring private investigator wanda aikin sa kawai shine ya nemo likitan da yayi aiki ma Zubaidah lokacin da tsautsayin ya faru..
"Yayinda Shattima keta shirin business da Dasuki's wanda ko Mai Martaba ma baida masaniya akai, iyakaci dai yasan Shattima zai dawo Abuja sabida su Jalal da kuma wani business matter da zaiyi dealing....
**********
"Allah Ya taimake sa motar doyar K'asae Taraba ta nufa, ana wuce Gombe kad'an ya samu ya dire daga motar ya kutsa daji.....
"Da wuya da babu dad'i ya samu ya isa garin Dukku, kai tsaye gidan su abokin sa Balele ya nufa, Balele yayi mmakin ganin Umar cikin wann yanayi na tsananin ciwo, tun kan ya soma jero masa tambayoyi yace " Ka tabbata babu wanda zai ganni, ka taimaka min da d'akin ka da abinci har na gama jinya ta....
"Balele ya kallesa cike da tausayawa gamida girgiza kai, Allah sarki raguwar su a da can yake tunowa kafin Umar Ya dawo something else..
"Babu yanda Balele baiyi ba ya fad'a masa a ina yaji ciwo fir yak'i fad'i, k'arshe ma sai ce masa yayi idan bazai taimaka masa ba zaiyi tafiyar sa.. Balele bai kuma tuntub'ar sa ba sai mik'a masa kwanon tuwon sa da yayi...
"Koda Umar Ya bud'e kwanon ya jima yana kallon abun, rabon sa dashi har ya mance, babu yanda ya iya haka Ya nad'e hannu ya dinga gabzan loma....
******************
"Sauri sauri ta fito daga gidan bayan ta d'an tattaro duk wani savings d'inta, ta dnna security lock d'in motar Umar Ya bud'e, tana k'ok'arin zura key ma k'ofa taji bakin bindiga a k'eyar ta... Cike da firgici ta saki hand bag d'inta a k'asa, jikinta na rawa take karanto innalillahi...
"Danny ya daka mata tsawa da fad'in" Shut up, ina d'an iskan mijin naki, he think he can outsmart us ko, kuna planning barin gari ba tareda ya biya mu kud'in aikin mu ba....
"Zulaihat baki na rawa take fad'in " Wllhi I've no idea.... Ban.. Ban San yanda yake ba, pls don't hurt me I'm innocent....
"Danny ya fizgi car keys d'in dake hannun ta kafin yace " Mun tafi da wann, God save you ba don muna sauri ba da mun had'a ke.....
"Tana jin yanda suka fincike motar suka fice daga layin da gudun gaske...
"Durk'ushewa Zulaihat tayi a wajen had'i da toshe kunnuwan ta tana kuka, gaba d'aya 'yan kud'ad'en nata ma sun kwashe... Tana a haka Imam ya k'araso. Ganin yanyinta yasa sa cakka burki a sittin ya fito yayi kanta yana tambayar ta lafia, cikin kuka ta labarta masa abinda ya faru...
"Taci gaba da fad'in" Imam ta yaya zan had'u dashi ya bani takardan saki na, I can't take this anymore..... Ta k'arshe cikin kuka...
"Cike da tausayawa Imam ke kallon ta Ya shiga lallashin ta da tausasan kalamai... Saida yayi calming nata kafin suka nufi asibiti..
"To her surprise Imam shi yayi settling hospital bills d'in Innah gaba d'aya..
"Wani sabon girman Imam ta shiga gani a idanun ta, lallai kuwa masu iya magana sunyi gaskiya da suke cewa wani babban girma ne kurum ya tara babu hankali yayin da wani yaron ya ninninka wani babban a sani ya kamata, tabbas yau bata ma Imam kallon yaro a idanunta kaman yanda ta saba... Tausayin sa ya cika zuciyar ta, wani babban Al'amari take ji a tareda shi... Ashe kuwa tabbas ba kyaun halitta bane kurum yake sa a so mutum, tabbas kyaun hali na taka babban role a soyayyar d'an Adam....
"Innah ta kalle su su duka biyu bayan ta d'an farfad'o, cikin maganar ta D bai fita sosai ta ringa saka masu albarka, ta tuna yanda tak'i jinin Zulaihat daga farko, Allah sarki ashe duk munin halin mutum yana good side, snn shi mutum magani ne, sai ka haifi d'a baka moresa ba ka mori na wani..
"Haka Inna tayita saka masu albarka da muryar ta da bai fita sosai..... Idan ta tuno Baba Wuro kuwa sai kaga ta soma wani nishi tana shid'ewa...
************
"Kwanci tashi babu wuya wajen mai sama, Jalal ya sami sauk'i sosai har an warware bandage d'in.. Sosai Zubaidah ke kula dashi kai harma da Annah, Ansar ma ya d'an soma dawowa normal, haka Kausar da Mumsy ma...
"Hamma yaje yaga Hadiza yanda halittar ta Ya sauya lokaci guda. Idan ka ganta baka shaida ta ba, fuskar ta duk ya tuttuje ya dauje, matan cikin cell kullin sai sun zaune ta sun lakkad'a mata duka, musammman da sukaji tsugugun yawan kud'in da tayi niyyan sata.
"Babu yanda Hamma Habibu baiyi da Hadiza ta fad'a masa yaya akayi hakan ta kasance ba, fir tak'i, saidai kurum tace duk cikin sharrin su Alh Kasim ne, Alhali cikin zuciyar ta kuwa tsoron fad'in" gaskiya take, tasan zasu tsaneta harta Hamman... Daga bisani ya fad'a mata zasu tafi Gwambe kwanan nan, ya bata labarin duk yanda Al'amran Ubangiji suka kasance...
"Hadiza ta d'aura hannu aka ta kurma ihu tana fad'in" Na shiga uku na lalace ni Hadiza, yanzu Zubaidah ce ta zama matar d'an sarki, lallai hausawa sunyi gaskiya da suka ce hassada GA Mai rabo taki, zakaran da Allah Ya nufa da cara, ko ana muzuru ko ana shaho sai yayi, duk iya hassadan ta datayi ma Zubaidah ganin ta dak'ushe rayuwar ta tun tana yarinya hakan bata kasance ba....
"Tana komawa cikin cell taci gaba da yima oganniya matsa k'afafu, idan batayi daidai ba saidai taji sauk'an mari a kumatun ta, fuskar duk shatin yatsu Ya cika......
****************
*Dasuki Holding*
"Bakin Alh Kasim ya gaza rufuwa sabida farin ciki, finally yau President na Modibbo Cooperation zaizo su sami ganawar su, yau dai zai yarda k'wallan mangoro ya huta da k'uda, wato Hon Gali, gaba d'aya Company har wani sanitation na musamman yasa ayi..
"Daga can kuwa Shattima cewa yayi ya tabbata Companyn sa akwai wadaceccen tsaro sabida Mr President ba ko wani irin waje yake zuwa ba, kasancewar ya yarda da Dasuki Holding ne shiyasa zaizo..
"Alh Kasim baki har kunne, this is a huge honor, musamman da yanzu yasan Modibbo Cooperation MALLAKIN WAYE,.. An gyara hall anyi komai, su Salim da Labib sai kai komo suke, don suma gwara su tsaya ayi introducing nasu ma owner of the great company mai tashen suna da kud'i a yanzu. Tabbas sun san zasu iya samun contracts, tunda yanzu Dasuki Holding nafsy nafsy ake....
"Tafe suke cikin luxurious cars d'insu, in convoy, ko wani plate number na motocin sunan Company d'insu ne akai, ....
"Suna isowa Dasuki Holding kaga yanda ake hangame masu Gate, haba tuni su Barr Munir an rud'e an shiga kai komo ganin komai ya tafi normal.
"Motocin suka pappaka a haraban Companyn, Sai diri kawai suke AC na aikin sa...
"Escort guda ne ya fito Ya bud'e wa Shattima k'ofa suka nufi building d'in, zo kaga yanda ake basa tsaro, su Alh Kasim duk a zaton su Mr President ne da kansa....
"Kai tsaye akayi directing nasa to Hall d'in, su Alh Kasim sai rawan jiki ake, su Labib kuwa mamaki ne ya cikasu ganin President na babban company kamar Modibbo cooperation k'aramin yaro ne bazai wuce tsaran su, ba, su kuwa su Alh Kasim tunani suka soma yi k'ila d'ansa ne ke tsaya masa a hidimar kasuwamcin sa tunda shi bashi da wann lokacin...
"Bayan Sun gaggaisa har an bawa Shattima wajen zama sann ne yake fad'a masu, shi PA ne na Mr President, shigowa yayi ya tabbatar da tsaron wajen kafin Boss d'insa ya shigo, idan sun tabbatar da tsaron dake cikin company d'insu Boss d'insa zai sami damar shigowa...
"Su Alh Kasim baki har na rawa suke jaddada wa Shattima tsaron dake cikin company d'insu.
"Suna gani ya ciro Intercom suit pocket d'insa ya shiga kiran Orderly na Mr President ya sanar dashi everything cleaned zasu iya shigowa...
"Gaba d'aya baza baki da hanci sukayi suka k'ura ma k'ofa idanu suna jiran suga wann bawan Allah da zai shigo....
************
"Ansar ya ajiye documents d'in gaban Mumsy kafin yace " Mumsy komai ya zama intact, I've already talked with one of the best architectures company in Turkey, So probably they are working on the Design now...
"Mumsy ta kad'a kai tana jinjina masa, caraf suka jiyo muryar Kausar tana fad'in" May I interrupt....
"Ansar ya juyo ya dube ta yana murmushi kafin yace " Sure... Kausar ta k'araso tana murmushi.
"Mumsy dae kallon su kawai tayi tana murmushi.
"Kausar ta zauna gefen Mumsy kafin tace " Gina sabon Company yanzu ba namu bane, abinda ya kamata muyi shine mu saya Company..
"Mumsy ta juyo ta dubeta da alaman tambaya.
"Kausar ta gyad'a mata kai tana d'aga gira kafin tace " Mumsy nasan zamu samu.
"Murmushi kawai Ansar yayi don for sure ya gane plan d'in Kausar. Gyad'a kai shima yayi kafin yace " Yes Mumsy I go with her, sayan ginanne bazai kai wanda za'a gina ba, snn already zamu samu employees, saidai kawai mu k'aro k'wararrun Engrs da Architectures kawai tunda Construction Company ne...
"Mumsy ta d'ago tana duban su kafin tayi murmushi tace " Okay my children yanda kuka yi deciding...
"Kausar da Ansar suka kalli juna had'i da sakar ma juna murmushi....
*************
"Mamaki ya hanasu motsawa daga yanda suke gaba d'aya.
"Salim da Labib a tare suka mik'e suna kallon ikon Allah... No is this for real, kai kodai kamanni ne, no this can't be... It can't be him..
"Yayi tsananin kyau cikin business suite d'in sa, guards biyu ne a gefensa all in black sun toshe idanun su da shades...
"Shattima kuwa kallon sa kawai yake yana murmushi kafin ya juyo yana kallon su Alh Kasim wanda suka koma tamkar gumaka...
"Shattima ya soma introducing nasu ma Jalal yana gaisawa dasu, daga bisani aka basa seat dake a center ya zauna...
"Har lokacin su Alh Kasim basu dawo daidai ba..
"Su Salim kuwa sai shafe kai kurum suke suna kallon sa...
"Shattima ya d'an ware hannayen sa kafin yace " Gentle Men let's proceed.... Ya k'arashe yana mik'a wasu takardu gaban Jalal..
"Kallon petition d'in Jalal yayi kafin ya zaro pen a gefen suit d'insa kaman zai yi rubutu sai kuma ya fasa... " Barr sai fad'a masa abubuwan da sukayi ordering yake, kalan kayayyakin da zasu shigo dasu da kuma ingancin su.. Kana jin maganganun nasa kasan da k'yar yake yana yi yana kurb'an ruwa.
"Jalal ya kafesa da idanu kawai yana murmushi kafin yace " Hold on Attorney, you don't have to explain everything, I perfectly well know you... All of you...
"Alh Kasim ya shiga muzurai yana share zufan dake keto masa duk sanyin dake cikin wajen..
"Jalal ya mik'e ya isa gaban Alh Kasim kafin yace " Alh Kasim Dasuki kaji mamaki ne, well wann ba abin mamaki bane a wajen wanda yasan Allah, yasan zai iya juya al'amran sa duk lokacin da yaso...
"Your Company is going bankrupt, and you expecting me to negotiate with you.... Ya d'an murmusa kafin yaci gaba da fad'in" Saving your company is your top priority now, but too bad I don't deal with a scumbags like you...
"Koda yake ni ba mugu irin ka bane, zan maka donating huge amount of Money, nasan it will help... Ya k'arashe yana kallon guard d'insa guda d'aya... Da sauri ya ciro wani kud'i cikin envelope, ya mik'a ma Jalal..
"Jalal ya amsa yana murmushi kafin ya tako har gaban Alh Kasim, ya ajiye envelope d'in yace " Take a look of it Alh Kasim da fatan ba'a canza komai ba. D'auka ka duba ka tabbatar kud'inka na nan intact...
"Gaba d'aya suka bi envelope d'in da kallo, tabbas kud'ad'en da suka basa ne lokacin da suka tursasa masu auren juna shida Zubaidah, don asirin 'ya'yansu ya rufu....
"Wann rashin mutunci har ina, shine Jalal zai zo har companyn mahaifin sa ya ci masa mutunci.. Da sauri Salim Ya k'arasa zai kai cakuma ma Jalal yake fad'in" How dare you, you Trader....
"Guard d'aya ne ya finciko Salim da hannu guda zai kai masa duka, Jalal ya dakatar dashi ta hanyar d'aga masa hannu kafin ya matso fuskar Salim yace " Salim Dasuki kai naka ba'a nan bane sai mun had'u a kotu.... Ya k'arashe yana murmushi kafin ya juyo ya dubesu gaba d'aya yace " Gentle Men if you excuse me, zan wuce coz I have alot of commitments to take care... Daga haka ya sakar masu murmushi yace " See you in Court.... Guards dinsa suka rufa masa baya Shattima kuwa sai mirmusawa yake abin ya masa dad'i bai zaci zai sami had'in kan Jalal haka ba, Jalal ya burgesa, don farko da yazo masa da batun k'i yayi daga baya kuma da kansa ya shirya komai....
"Gaba d'aya suka wuce guards d'insu suka rufa masu baya...
"Salim sai wani fincika yake yana fad'in" You scumbag you won't get away with this... Labib ya jawo sa yana karkad'a masa kai alamun a'a...
"Alh Kasim tuni ya rik'e k'irjinsa dake masa zafi Ya fara durk'usawa jikin table yana k'ak'ari... Kan kace me ya zube a k'asa, nan hankulan su Salim da Barr ya dawo Kansa...
"Salim yayi kansa a tamanin yana jijjiga sa yake fad'in" Daddy daddy... No no daddy... Call an ambulance.... Ya fad'i cikin tsananin d'aga murya yana rungume da Alh Kasim..
"Ko gizau Labib beyi ba, sai Barr da ya fice a tamanin
Sameena ce
🌘🌘🌘🌘 *ZUBAIDAH*
90
*©Sameena Aleeyou...✍🏾*
_🌈KWA_
*Zauren Karatu na Biebee Isa kuna raina, Na gode k'warai da irin k'aunar da kuke nuna min da rubutu na, Allah Ya bar k'auna.. Love you all so much... This Chapter is yours guys kuyi yanda kuke so dashi... 😘😍❤*
"Ruwa ruwa aka kwashi Alh Kasim aka wuce dashi asibiti.
"Hankalin su Mummy da Mamy sosai ya tashi musamman Mummy kuka kawai take Mamy da Salim sai lallashin ta suke suna nuna mata Daddy zai sami lafiya da izinin Allah.
"Barr Munir na daga can gefe sai sak'e sak'e yake yana zaga reception d'in, things turned out yanda basuyi zato ba balle tsammani.
"Labib kuwa ko a jikin sa, zaune yayi can gefe yana karantar su da idanu... Tunanin canzawan Jalal dare d'aya kurum yake, lallai hakan na nufin rugujewar Dasukis ne yazo, gwara tun kafin 'yan sanda su ankare ya cika ma rigar sa iska, don shakka babu wann shari'an kam basu da alamun nasara, .
"Dafe kansa yayi thought d'in ya hanasa sukuni...
"Dr ne ya fito gaba d'aya suka nufesa suna tambayar sa..
"Dr ya d'an fuzar da iska kafin ya soma fad'in" Calm down ku kwantar da hankulan ku da sauk'i sosai, abinda yake buk'ata shine ya rage yawan shiga damuwa, don yanzu haka ya sami Facial Stroke, amma idan yana kula da magani da kuma dokokin likita toh zai koma normal, and pls a daina stressing nasa out, I repeat...
"Barr ya shiga gyad'a kai yana fad'in" Za'a kiyaye Dr, Mummy kuwa kwantar da kanta tayi jikin Mamy dake faman lallashin ta, hawaye na bin k'uncin ta.
"Salim hankali tashe yake duban Dr kafin yace " Dr can we see him...
"Dr ya gyad'a kai kafin yace "Sure zaku iya shiga, amma dae kar a damesa da magana, regarding his condition...
"Kwance suka hangi Alh Kasim saman gado bakin sa ta soma karkacewa gefe, suna shiga abinda ya fara fad'i masu cikin muryar sa da bai fita sosai shine. " Where is that Jerk, k'arya yake ba kampanin sa bane, b'arawo ne, ni na tabbata b'arawo ne, D'an matsiyata ne Sarkin Gombe bai da d'a na miji..... "Salim Ya k'arasa yana girgiza masa kai yake fad'in" Daddy com'on ka daina maganar nan ka daiji abinda Dr yace..
"Alh Kasim ya kalli Salim kafin yace " Son I can lose my company, we have to do something right away... Tamkar zararre haka yake maganar gashi muryar ta koma tamkar ta me koyon magana...
"Mummy ta k'araso ta rik'e hannunsa tana fad'in" It doesn't matter anymore, what matters shine ka sami lafiya.... " Ai bata kai aya ba, Alh Kasim ya soma girgiza kai yana fad'in" No no Farha, we.. We need to do something right away... We need to get to the bottom of this issue.... That company is my life, rasa sa na nufin rasa rayuwata...
"Munir ya k'araso ya dafa sa kafin yace " Alh Kasim you better take things easy idan kanaso ka sami lafiya... "Baza ka rasa company d'inka ba, we are all here for you, we would do anything possible to save the company, but for now lafian ka shine mai muhimmanci...
"Labib dake gefe tab'e baki yayi ba tareda ya furta komai ba..
****************
"Tana zaune saman stool gaban dressing mirror tana saka 'yan kunne ya d'anyi knocking had'i da turo k'ofar bakin sa d'auke da sallama, kallonta ya tsaya yi tayi kyau sosai cikin atampa Sea green mai touches d'in peach, d'inki riga da raper skirt ya zauna sosai yayi kyau a jikinta, dukda kayan bai matseta sosai ba amma tayi kyau.... Shap ya shafa'a da kallon ta, ta masa kyau har ta gaji...
"Ta cikin mirror take kallon sa yanda ya kafe ta da idanu hannunsa rik'e da handle na k'ofa, ya mata kyau har ya gaji.
"Sanye yake cikin Jampa Sky blue ya buga hula zanna bukar Dark blue, sosai yayi kyau, da yasan yanda jampa ke masa kyau da bai lak'anci saka kayan turawa ba inji Zubaidah.....
"Ganin tayi sakare tana kallon sa yasa k'arasowa cikin d'akin ya tsaya a bayanta suna kallon juna ta mirror, wow perfect match inji Sameena..
"K'ok'arin saka sark'a take sai jin tattausan hannunsa tayi saman nata, a hankali ta sake masa sark'an yaci gaba da saka mata.
"A hankali ya sunkuyo da kansa yayi kissing wuyar ta ta baya... Mik'ar da ita tsaye yayi gamida juyo da ita suna facing juna ya sakale hannayen sa a waist d'inta..
"A hankali ya furta "Baby kinyi kyau, har naji banaso a gane min ke a fadah, kinsan waje ne mai Jama'a da yawa, I'm jealous of you Zubaidah...
"Murmushi take tana kallon sa yanda komai nasa abin burgewa ne, kasa jure ma kallon nasa tayi ta kuma kasa ce masa komai sai sadda idanun ta k'asa da tayi...
"Rungumeta cikin k'irjinsa yayi kafin ya soma fad'in" Thank you, thank you Zubaidah for coming into my life, and also for opening your heart for me, I know it's hard for you to accept someone like me, despite everything that happened, Kin yafe min kika accepting d'ina, kika trusting d'ina completely,....Ya d'an ja fasali.. Kafin yaci gaba da fad'in" And.... for that I'll love you not only for the rest of my life, but for the rest of your life.... Koda ace bana nan koda ace mutuwa nayi kisa a ranki zan mutu da soyayyar ki cikin raina..... It's a promise.
"Ya d'an sassauta rik'on da ya mata hannayen su rik'e cikin na juna ya soma fad'in" Daga rana mai kaman ta yau, zamu fuskanci wata rayuwa, wanda bamu saba da yanayin ta ba, da mutanen wajen da d'abi'u da Al'adun su, But I assure you idan bakya so, we won't live there, zamu gaishe su snn mu dawo mu nemi gidan kanmu mu ci gaba da ordinary simple life d'inmu...
"Gani yayi hawayen ta ya d'igo saman hannayen su,.
"Da sauri ya soma k'ok'arin d'ago face d'inta yana fad'in" I'm sorry Zubaidah, na fad'i abinda ya b'ata maki rai koh... Kiyi hak'uri I didn't mean to..
"Girgiza masa kai tayi tana k'ok'arin share hawayen ta kafin ta soma fad'in" Ko kad'an baka fad'i abinda ya b'ata min rai ba... Hawaye nake sabida ban tab'a tunanin zan samu wanda zai soni tsakani da Allah ba, bayan yana sane da tsautayin da ya same ni, a da na d'auka shiknn rayuwa ta tsaya min, na d'auka na gama farin ciki, ashe ba haka bane... Ya Jay kayi hak'uri dani a lokacin da nafi kowa tsanar ka, kayi hak'uri dani a lokacin da nake wulak'antaka son raina, duk don na rama abinda baka da laifi akai, Na yarda Allah da zuciya yake aiki, bayan abinda ya sameni ko a mafarki ban tab'a tunanin samun miji kamar kai ba, ... I hope those who are suffering from what I suffered will remain hopefully, kar suyi fushi da Al'amarin ubangiji domin kuwa wani hani GA Allah baiwa ne, snn wani tsautsayin zai kaika ga Alkhairi...... Ina sonka, ina sonka Ya Jay, ina sonka for who you are, ko a wani irin rayuwa ka tsinci kan ka, I'll be with you and I'll still love you till the end..... "Rungumota cikin jikinsa yayi siriryar hawaye ta sauk'a masa, tsantsan soyayyar ta da k'aunar ta ne ke Bin jini da b'argon sa, a b'angaren Zubaidah ma hakan ne ta kasance..
"A haka Annah ta turo k'ofa hankali, ta hange su, yanda suka k'ank'ame juna... Tausayin su ya cika mata zuciya had'i da soyayyar su...
"D'an knckng tayi jikin k'ofa, Sukayi saurin sakin junan su, Cike da kunya Zubaidah ta matsa baya tana mai sadda kai k'asa had'i da k'ok'arin kintsa kanta...
"Jalal ya sakar ma Annah murmushi yana d'an shafa k'eyar sa yake fad'in" Annah nah kin shirya zuwa Fadan dai koh, kar a harba bindiga su tsorata min keh...
"Murmushi Annah ta kuma sakar masa kafin tace " Kasan dai flight d'in k'arfe 10:am ne gashi yanzu already past 9 idan ba so kuke mu kuma booking wani flight d'in ba...
"Jalal ya d'an murmusa kafin yace " Tab aiko Shattima zai kashe ni da waya, wai ce min yake tuntuni aka jera dawakai a k'ofar fadan, Annah I'm feeling a bit nervous,.....
"Annah ta k'araso cikin d'akin tana murmushi ta d'an dafe Face d'insa kafin tace " This is natural dear, amma kwanan nan zaka ga ka saba da komai, we are all here for you kaji, ...
"Ya d'an murmusa kafin yace " I love you Annah.
"Murmushi itama tayi kafin tace " And I love you too Son.
"Zubaidah ce ta fito daga closet sanye da yalwataceccen mayafi wanda ya dace da shigar ta, Annah ta sakar mata murmushi kafin tace " Daughter an shirya,.
"Zubaidah ta murmusa ta gyad'a mata kai alamun eh..
"Jalal ya d'an saci kallon Annah, ya kalli Zubaidah ya kashe mata ido had'i da d'aga mata babban d'an yatsan hannun sa ya furta " Superb" a hankali... Hararan wasa kawai Zubaidah ta d'an aika masa gamida gyara mayafin ya rufu kif a kanta, sai ta k'ara girma..
"Annah ta soma ficewa tana fad'in " Toh maza ku fito da Allah, Ansar da Hafiz suna jiran mu...
"Luggage d'insu aka ringa jerawa a bayan trunk kafin suka shige motocin Hafiz da Ansar suka d'auki hanyar Nnamdi Azikiwe International Airport Abuja.
"Hafiz da Ansar kuwa basu bar Airport d'in ba har saida suka ga tashin su tareda masu fatan sauk'a lafiya.....
"Jirgin su tana landing a Gombe suka tarar Shattima tuni ya iso Airport, kai tsaye yayi directing nasu yanda aka paka wasu arnan Lexus ko wanne lambar jiki kuwa Emirate Council ne, harda k'aramar tuta a gaban motar.
"Hawaye ya cika idanun Annah ganin wann d'aukaka yau da Allah Ya basu, tabbas kar kayi mamaki da Al'amarin uban giji...
"Hamma kuwa hawaye ya shiga sharewa yana fad'in" Wai yau shine ya sami wann d'aukakar ta hanyar Zubaidah... Allahu akbar inama Innah da Baffah suna nan su sha kallo, yau ga Zubaidar su, ma'abociya kiwon dabbobi da tallan nono Allah Ya d'aukaka ta, wanda har d'aukakan ta shafe su.....
"Zubaidah ta lura da yanayin sa, ta d'an k'arasa ta rik'e hannun sa suka sakar ma juna murmushi zai saka hannun rigar sa ya share hawayen sa tayi saurin ciro hanki a jakar ta ta goge masa hawayen, Murmushi ya sakar mata kafin yace Allah Ya maki albarka Zubaidan Baffah..
"Ba tareda b'ata lokaci ba suka shige motocin aka d'auki hanyar Fadah babban gida, motar securities na gaba ana zuba hidiman iko...
"A can gidah fadah kuwa duk a zaton su sabida dawowar Baba Ciroma ake wann hidimar, kasancewar shima yau ne ranar sallamar sa daga babban asibitin Bauchi....
**************
"Wata uwar harara Labib ya watsa masa kafin yace " Will you stop pestering me Salim ... Waima.... Just wait a second, are you questioning my decision..?
"Idan bazaka bini mu tafi ba fine, you can stay here and go to prison, kadai ga irin rayuwar da mukayi a d'an wattani biyu da mukayi cikin prison, toh yaya kake tunani idan aka ce an yanke mana wasu shekaru masu yawa, tun Companin nan tana nan a sunanta Dasuki Holding mu kama kanmu mu tafi wani wajen, koda as illegal emigrants ne, kasan dai an amshe passports d'inmu balle muyi tunanin barin k'asar by flight, barin k'asar ta jirgin ruwa zai fi mana sauk'i, tun akwai d'an sauran savings d'inmu kazo mu tafi Lag muga abinda Allah zaiyi....
"Salim yayi shiru yana kallon Labib kafin yace " What about my Dad, Labib a condition d'insan nan bai kamata na tafi na barsa ba, and my Mum needs me now more than ever.
"Labib yayi wata shu'umar dariya kafin yace " Wai tausayin Kasim Dasuki kake ne, kar ka mance kalan zaluncin da yayi a doron k'asa, wllhi nasan zunibin sa ya ninninka nawa, bazan tsaya azaban sa ya shafe ni ba, domin kuwa shakka babu Allah ne ya fara kama sa, idan kaga kana iya tsayawa fine, idan zaka bini mu tafi fine, nima ai akwai mamy na bata da kowa sai ni, amma da taga ina tafiya jell for many years ai gwara na gudu wani wajen at least nasan wata rana za a gaji a bar nema na, idan nayi kud'i a yanda zan soma fresh life, kaga sai na dawo na d'auke ta, na kuma soma tunanin ajiye family, kai if possible har identity na zan canza domin kuwa Dasukis sun tashi a aiki...
"Ya k'arashe yana zura kayan sa cikin jaka...
"Salim dai shiru kurum yayi yana kallon sa ba tareda ya iya furta koda kalma ba..
***************
*Fadah*
"Yau ta kasance babban rana ga d'aukacin wann masarauta, rana ce wacce ta shafe bak'in tarihin da ya auku shekaru 26 da suka wuce, rana ce wacce ta kafa d'inbin tarihi..
"Sanda Jalal ya saka k'afar sa ta dama da niyyan shiga gidan, hawaye ne ya shiga gangaro masa, bai tab'a tunanin rana irin wann zata zo ba...
"Tun daga waje ake zube masu ana mik'a gaisuwa, ga fadawan da suka soma hangosa daga waje, zubewa kawai suke cike da mamaki sunai masa fadanci, wann fuska tasa ko ba'a fad'a ba Ahali Lamid'o ne, d'aya ne daga cikin iyalan Sarki Lamido na uku mai rasuwa..
"Gaba d'aya Jalal ji yayi zai iya zubewa a k'asa sabida yanda yake ji a jikinsa, yau gashi nan, a gidan su kuma mahaifar sa... Shattima ya lura da hakan yayi saurin rik'e sa, duk bafajen da ya gaishe su, Shattima ne ke k'ok'arin amsa su...
"Sanda suka saka k'afar su a babban gwani, wato babban parlorn Mai Marataba Sarki Aliyu Mu'allayid'i Lamid'o na goma sha uku.... Allahu akbar gaba d'aya mik'ewa fadah tayi, su Waziri, su Hakimi, su Ajiya, kai gaba d'aya king makers manya manyan sarakunan gargajiya mik'ewa sukayi, tabbas wann Lamid'o ne ya bayyana, hawaye ya shiga bin fuskar Baba Waziri sanda ya hangi Shattima da Jalal suna takowa...
"Mai Martaba ya kasa daina murmushi jin dad'i da yake, yau ga Modibbo ya dawo mahaifar sa, yau Allah Ya cika masa burin sa.
"A yayinda hankulan mutane yayi kan Su Jalal a lokacin Mai Martaba ya zame ya kalli alk'ibla ya gabatar da sujudusshukri ga Rabbil Izza Sarkin da babu kamar sa Mai Mulkin sama da k'asa...
"Baba Waziri yana ganin Mai Martaba yayi haka, ya tabbata wann shakka babu Lamid'o ne, kk'arasawa yayi yana hawaye kafin ya rungume Jalal yana fad'in" Allahu Akbar Lamid'o ka dawo gidan ku...
"Wann furuci na Baba Waziri ya kuma karkata hankulan jama'an fadah dake cikin parlorn, nan kaji Fadah ta amsa lokaci guda, kan kace Me, Sank'ira ya soma shlela a cikin fadah cewa Lamid'o Modibbo ya dawo gida...
🌘🌘🌘🌘 *ZUBAIDAH*
91
*©Sameena Aleeyou...✍🏾*
_🌈KWA_
*Dedicated To All Victims Of Rape...*
"Cikin Ummi gaba d'aya ya d'uri ruwa, k'irjinta sai dukan tara tara yake. Lamid'o a gidan nan... Kai kodai ba daidai taji ba..
"Jakadiya ta kuma rusunawa murya na rawa ta maimaita mata sak'on Mai Martaba.
"Zufa ya shiga keto ma Ummi ta ko ina, wayyo Allahn ta bata tab'a nadaman abubuwan da tayi a rayuwar ta kamar yau ba.. Ina ma bata bari ya kashe Suhaima ba, ina ma bata jefar da Lamid'o ba, kaicon ta, ina zata kai wann tarin danasanin... "Tsawa ta daka wa Jakadiya ta shiga zagaye katafaren d'akin nata tana mai Zullumin fita, don kuwa k'iris ya rage k'irjinta bai tarwatse ba..
"Hannun Madaki Zahida ta rik'e tana goge mata hawayen ta tana murmushi kafin taci gaba da fad'in" Ya dawo, ya dawo Madaki, Modibbo ya dawo gare mu..
"Tsohuwa Madaki kallon Zahida kawai take ba tareda ta fahimci komai ba, k'arasawa tayi ta d'au hoton sa dake ajiye saman Chase of drawers ta shiga shafawa tana fad'in" Shekaru ashirin da shida kenan rabon mu dashi, shekaru ashirin da shida kenn da b'acewar sa, anya kuwa Fatima kinji da kyau....
"Zahidah ta kuma rik'o hannun ta hawaye na Bin idanun ta amma murmushi take kafin tace " Mai Babban d'aki naji da kyau, shiyasa ma Abbah ya turo a tafi da ke cikin fadah ki gansa.... Zaki sake ganin jikan ki da a kullum kike kwana kike tashi dashi....
"Shattima ya k'araso yana murmushi yake kallon Zahidah kafin ya rik'o hannun Madaki guda yace " Muje Mai Babban d'aki, muje kiga Modibbon ki...
"Madaki ta d'ago ta kalle su su duka biyu hawaye na neman b'alle mata suka soma tafiya a tare, Shattima na rik'e da hannun ta na dama yayinda Zahidah ke rik'e da hannun ta na hagu...
"A haka Khalifa ya hange su, zuciyar sa ta shiga masa zogi, tausayin kansa ya cika masa zuciya, wann wani irin al'amari ne, Modibbo ya dawo masarautar nan wanda hakan na nufin babu shi babu sarauta, snn Zahida bazata tab'a son sa ba, tuni tayi nisa da soyayyar wanin sa, mahaifin sa ya dawo daga jinya babu baki babu k'afafu, meyasa rayuwa ta kasance haka.... Kasa komawa cikin Fadah yayi ya nufi hanyar fita...
"Shafa fuskan sa take hawaye na gangaro mata, yayinda shima hawayen ne ke bin k'uncin sa, Kuka sosai ya b'arke ma Dattijiuwa Madaki, rungume ta Jalal yayi ba tareda ya iya furta koda kalma ba...
"Zahida ta kuma damk'e hannun Zubaidah tana jin har ranta take k'aunar ta...
"Madaki ta soma maganganu cikin harshen fillanci tana godiya ma Allah.
"Allah sarki hak'ik'a yau rana ce wacce bazata tab'a shafewa ba a tarihin masarautar...
"Ba zallan Fadah kawai ba harta garin gaba d'aya labari ya d'auka, long lost son d'in Mai Martaba ya dawo..
"Wann labari ya haifar da farin ciki ma d'aukacin mutanen garin..
"Gaba d'aya Dattijuwa Madaki ta kasa sakin jikan nata, haka ta rik'e hannayen su k'amk'am shida Zubaidah,.
"Baba Ciroma zaune saman wheelchair d'insa, ya sami kariya sosai a k'ashin bayar sa, snn sun masa lahani wajen sauraren magana da maidawa, a tak'aice dai likita yace zai d'au lokaci watak'ila mai tsawo kafin ya warke watak'ila kuma Ya iya warkewa a 'yan kwanakin nan, abin dai na Allah ne sai yanda ya gudanar da Al'amran sa..
"A b'angaren Ummi kuwa hakan ba k'aramin dad'i ya mata ba, Kai Allah ma yasa ya tabbata a haka, tunda hakan na nufin rufuwar asirin ta.
"Ummi harda hawayen ta sanda ta k'arasa ta rungumi Jalal, wanda mutane sun zata na farin ciki ne, amma kuwa ita kanta batasan hawayen Me take ba, walau na bak'in ciki ne ko kuwa na tsoro da fargaban abinda ka iya zuwa yazo....
"Harta Zubaidah saida Ummi ta rungume ta tana mai nuna farin ciki..
"Baba Ciroma kuwa kallon ta kurum yake babu halin magana.
"Sai kalaman yabo da godiya Ummi ke jero ma Annah, haka kurum Annah taji matar bata kwanta mata ba, kaman tana da b'oyauyyen Al'amari k'ulle cikin zuciyar ta...
"Masauk'i me kyau Mai Martaba yasa aka bawa su Annah, gefen Jalal da Zubaidah daban wani ratsentttsen sashe, basu shige ciki ba a cewar Mai Martaba sai zuwa gobe idan anyi bikin basa sarautar Yarima had'i da gabatar dasu a fadah a matsayin mata da miji kafin su shige sashen su cikin salama...
"Sanda Jalal da Shattima suka fito ya salam zo kaga yanda fadawa da masu sarautar ke kwasan gaisuwa had'i da fadanci..
"Gaba d'aya sai jin kansa yake uncomfortable.
*************
"Har Labib ya fito Salim Ya k'walla masa kira, tsayuwa yayi yana kallon sa kafin yace " What, ka gama shawarin ne, you lucky ban tafi ba, now d'auko mana car keys d'inka ka gani..
"Salim Ya kalle sa kafin yace " Ban gane na d'auko car keys d'ina ba, me kake nufi...
"Labib yayi gajeren tsaki kafin yace " Garage d'in Emeka zamuje mu saida ta mu k'ara kud'in guziri....
"Zaro ido waje Salim yayi kafin yace " You're crazy, this is ridiculous, man ka min maganar da hankali zai kama, motar tawa, Benz d'in nawa kake magana a saida a garejin Emeka wanda baifi ya taya mana dubu d'ari ba, kai ya gama k'ok'ari ya taya 200k... Motar over 7mlln.
"Tsaki Labib yayi kafin yace " You know what Salim you really wasting my Time, idan bazakayi tafiyar nan ba fine, da kake maganar Benz dinka miliyan bakwai ni nawa ride d'in miliyan nawa ne, ina ce na sayar sann da kud'in nasa a mana booking Ship, idan ma ka bar motar ka a nan ne toh wllhi k'arshe Alh Kasim ne zai biya bashin mutane da ita ko kuma Kawun ka Munir ya d'auka yayi gaba dashi don na tabbata eventually he's gonna betray Kasim Dasuki....
"So Dude if you ready for the escape ka d'auko car keys d'inka idan kuma ba haka ba, ka nemo 1mlln wanda za'a saya Captains dasu.....
"Idanun Salim suka ciko da k'walla, cikin sauri ya koma cikin gida ya bud'e bedroom d'insa, ya d'au keys d'in dake ajiye saman side drawer.
"Kallo ya tsaya yake bin d'akin dashi sanda ya tsaya a k'ofa hannun sa rik'e da handle, ya tuna duk wann luxury life d'in da yake ciki bashida wani option bayan ya fice ya rabu da ita, he never experienced financial hardships before, what ever he wants he got it...... But now, things are gonna change, ...... Muryar Labib yaji yana k'walla masa kira, cikin sauri ya soma sauk'owa daga stirs d'in gudu gudu....
"Yana fitowa ya danna security luck 4matic E350 d'insa ta bud'u, Labib ya murmusa kafin ya bud'e backseat ya jefa luggage d'insu, ya zagayo frontseat ya bud'e ya shige....
***************
"Washe gari ta kama Juma'a rana ce wacce aka gabatar da Yarima Modibbo da iyalan sa a matsayin ahalin gidan sarki. Hawan dubur sosai aka gabatar, tun safe ake gudanar da Dabur, lokacin sallan Juma'a tanayi suka sauk'a daga dawakan suka nufi babban masallaci don gabatar da nasu sallan.
"Abbah yana lura da yanyin Jalal, k'arshe dai kafin su fice ya tsida Shattima yace " Abdullah a koya wa Modibbo Al'adu da d'abi'un cikin gida..
"Cike da rusunawa Shattima ya amsawa Mai Martaba..
"Yau rana ce ta bikin murna, tambura sun bugu a wann rana, algaita sun kad'u,.
"Da yamma kuwa Mai Martaba yayi kiran iyalan sa gaba d'aya cikin fadah, wasu kujeru na alfarma masu kyaun gaske jera ma Jalal da Zubaidah, Ummi da Annah su suka rufa masu alkyabba, na Jalal fari k'al harda rawanin sa yayinda na Zubaidah ya kasance golden colour, Masha Allah kurum mutane ke fad'i..... Take kaji algaitu sun ci gaba da tashi..
"Marok'a nayi fadawa nayi, Allah Ya baka gidan ku, AAllah ya ja zamanin Yarima. D'an sarki jikan Sarki, D'an na gada kafi d'an na koya, gaban salamun baya salamun.... Baiwar Allah Allah Ya baki, Allah yaja zamanin matar d'an sarki, kin shigo ahalin alkhairi.. Allah Ya azurta ku da zuri'an alkhairi....
"Ire iren Kirari da aketa yi knn a cikin fadah.
"Dukda Jalal bai saba da hidimar sarauta ba, but for sure he feels something yaji wani abu a jikin sa. Tabbas ya yarda jinin sarautar na yawo a cikin jikin sa...
"Bayan an tashi daga wajen sahsen Ummi aka wuce da Zubaidah, wani abin mamaki har gyaran amarya su wasu dangin turarruka da kayan ci masu gyara Mace Ummi ta bawa Zubaidah, idanun Annah dai na kansu, sai ta yarda da ingancin abin kafin ta bari Zubaidah taci ko tayi amfani dashi, sosai Zahidah taji dad'in yanda Ummi ke nan nan da Zubaidah, kai kowa ma abin ya birge sa ga wad'an da suka santa shekarun baya sun sha mamakin canzawar ta, koda shike ba abin mamaki bane tunda a da can baya akwai k'uruciya a tattare da ita, ba kaman yanzu da girma yazo mata ba ta kuma samun hankali...
"Umman Shattima dai karyar goronta kawai take tana tab'e baki don kuwa sam bata yarda da kirkin da Fulani Kilishi ke yi ba....
"Da misalin k'arfe 8:30 na dare aka shigar dasu parlorn Mai Martaba na cikin gida Don lokacin ya tashi daga fadar sa, wato babban gwani...
"Ummi sai nan nan dasu take wanda hakan ya faranta ran Mai Martaba sosai, wasu alkyabban aka kuma rufa masu Ummi ta feshe su da turare kafin Abbah yayi masu nasiha mai ratsa zuciyar Mai saurare. Had'i da sanya masu albarka, daga nan sashen Madaki aka wuce dasu itama ta sanya masu albarka...
"Annah, Umman Shattima , Ummi da kuma Maman Kahifah matar Baba Ciroma sune sukayi rakiya ma Zubaidah zuwa sashen ta, tun daga waje bayi ne sukayi layi suna jiran isowar uwar gijiyan tasu...
"Wow Masha Allah, wann gida ya amsa sunan sa, komai yaji yayi kyau sai Allah son barka..
"Bayan kowa ya watse Annah ta kuma yima Zubaidah nasiha sosai kafin ta mata sallama ta shige sashen ta itama...
"Tana zaune saman katafaren Royal bed d'in wanda ya dace da hamshak'in d'akin, kanta har lokacin yana rufe cikin Alkyabba, a hankali ta yaye alkyabban ta shiga bin d'akin da kallo. K'walla suka ciko idanun ta, a hankali ta saki wani sassanyar murmushi zuciyar ta cike da gode ma ubangijin ta,...
"Tun daga k'ofan sashen nasu ya hangi bayi sai kai komo suke, masu saka turaren wuta na yi masu shigar da warmers na abinci na yi, " D'an juyowa yayi ya kalli Shattima kafin yace " What's all this for...??
"Shattima ya murmusa kafin yace " What do you expect,...
"Jalal ya d'an girgiza kai kafin yace " I had to put up with hargajiya things amma wad'an nan kuyangin sunyi yawa a nan, gaskiya ni bana son tak'ura...
"Shattima dariya ya soma har yana rik'e ciki kafin yace " Zan so naga zamanin naka sarautar inaga fadar kawai ta 'yan boko zata koma, za'ayi watsi da d'abi'u da Al'adun mu na gargajiya...
"Jalal ya d'an tab'e baki kafin yace " You're not helping you know...
"Kaga kasan yanda za'ayi a rage wad'an nan matan a nan, don ni gaskiya tak'urani zasuyi..
"Shattima ya k'unshe dariyar sa kafin yace " Wai kai meye naka na damuwa, naga dai ba akan ka zasu zauna ba snn kaga can... Yayi masa nuni da gefe wasu d'akuna kana yaci gaba da fad'in" Can shine d'akunan su, ba cikin gidan ka zasu kwana ba balle su tsare maka wani abu... Idan ka gansu gari ya waye ne, idan gimbiya tace bata buk'atan su bazasu shigo ba har sai gimbiya ta aiki yardajejjiyan tayi kiran su, idan buk'atan hakan ta taso, ka fahimta...
"Tab'e baki Jalal yayi daidai sanda suke shiga cikin kataparen parlorn wanda ya sha ado da kayan kwalliya na alfarma.
"Kuyangin nan suna ganin su suka zube k'asa suna kwasan gaisuwa, daga nan ficewa sukayi baki d'ayan su...
"Shattima ya d'an kalli Jalal yace " See.
"Bai wani zauna ba shima ya fice yayi tafiyar sa, waya mak'ale a kunnen sa da alama da sahibar tasa Zahida yake wayar.....
"Ya d'an jima a parlor yana bincike site d'in company d'in su don yanzu gaba d'aya zama busy Man ya kama sa, don ma Allah Ya taimake sa akwai Shattima, lallai yaga k'ok'arin Shattima da yake running company d'in...
"Daga bisani mik'ewa yayi ya haura sama.....
"D'akin dake a center ya soma shiga, shakka babu wann shine d'akin sa, bathroom ya fad'a ya sakar ma kansa shower had'i da d'auro alwala kafin ya fito ya shirya tsaf cikin silk jallabiya, fara k'al, sai k'amshi ne kurum ke tashi a jikin sa... Daga nan fitowa yayi ya nufi d'akin Zubaidah.
"Tana nan zaune wajen ta jiyo mostin tab'a handle da sauri ta kuma rufe fuskar ta heart d'in ta na beating fast sai kace ba Ya Jay d'inta data saba dashi ba haka taji...
"Da sallama saman bakin sa cikin tattausar muryar sa ya turo k'ofar ya shigo..
"Murmushi kawai yake yana kallon ta yanda tayi zaune tsakiyar gadon irin dai yanda amare ke yi...
"K'arasowa yayi ya zauna gefen ta, kafin Ya tambaye ta taci abinci, gyad'a masa kai tayi alamun eh...
"Jalal ya murmusa kafin yace " Baby mu biyu ne fah, only the two of us, ki bud'e bakin ki ki min magana, Ya Jay d'ink ne fah...
"Shiru bata kulasa ba, murmusawa Ya kuma yi gamida kai hannun sa saman nata hannun dake ajiye bisa gado...
"A hankali ta soma janye hannun.
"Tsam ya rik'e hannun ya hanata k'arasa janyewa, yayi amfani da hannun sa guda ya bud'e alkyabban da aka rufa mata.
"kyakkyawan fuskar ta ya bayyana.
"Sadda kai k'asa tayi ba tareda ta kalle sa ba, fuskar ta d'auke da sihirtaceccen murmushi...
"Jalal ya kuma matse 'yan yastunta kafin yace cikin sigan shagwab'a " Wifey can't I have a glance.... Ko baki son gani na ne yanzu nayi flying na wuce Abuja..
"Tayi saurin zaro idanu tana dubansa... Ya wani kapse harda d'aga mata gira sama... " Murmushi kurum tayi tana mai kauda kai gefe, still murmuahin ne saman Face d'inta...
"Baby nifa duk wann shiru shirun naki ban gane ba, you'll explain it to me later, yanzu dai tashi kije kiyi alwala kizo muyi sallah..
"Satan kallon sa tayi taga hankalin sa ya tafi kan wayar salulan sa, cikin dabara ta kwab'e alkyabban ta shige bathroom d'in ta d'auro alwala...
"Ga mamakin ta, tana turo k'ofar bathroom d'in ta hangi Jalal tsaye gaban Sip yana ciro mata wasu arnan night wears, tayi saurin kauda kanta gefe ganin ya juyo da duban sa gareta...
"Baibi ta kanta ba yaci gaba da a binda yake, saida ya gama d'aukan abinda zai d'auka kafin ya dubeta yanda tayi zaune gefen gad kana yace " Shall we..
"Ta d'anyi Far da idanu kafin tace " Where,..
"Ya d'an murmusa cikin ransa yace " Yarinya zancen kike nema, bata ankara ba saiji tayi ya sureta, basu zarce ko ina ba sai huge bedroom d'insa, wayyo Allahn ta what's Ya Jay doing..
"Ya shimfid'a masu abin sallah, kafin ya mik'a mata hijab d'inta.... Sallah raka'a biyu suka habatar kafin daga bisani ya juyo yana fuskantar ta, d'an tambayoyi game da addini ya mata duk da yasan ta sani amma dae yin hakan yanada mahimmanci, daga haka goshinta ya kama ya karanto mata addu'o'i...
"Sun d'an jima suna zaune suna chats har ta soma sakewa kafin ya mik'a mata kayan baccin ta yace wear this kafin na dawo...
"Tabi kayan da kallo tana kuma kallon sa k'asa k'asa...
"Bai saurari abinda zata ce ba, ya nufi downstairs... Jim kad'an ya shigo hannun sa rik'e da glass cups na madara har guda biyu..
"Ganin bata canza kayan ba bai mata maganar ba sai ajiye cups d'in da yayi saman rug, ya tako a hankali ta baya ya rungume ta....
"Lumshe idanun sa yayi yana shak'an daddad'an k'amshin ta....
"A hankali ya masu masauk'i saman rug d'in, bisa laps d'insa ya d'aura ta kafin ya d'au fresh milk d'in ya shiga bata a baki, saida tace masa ta k'oshi kafin ya k'yaleta, shi d'in ma ya d'an tab'a kafin daga bisani yayi hugging nata tsam cikin jikin sa yana fad'in" Yaya baki canza kayan ba, oya barin canza maki.
"Ya shiga zuge zip d'in rigar ta... Tsam ta rik'e hannun sa wanda hakan ya hanasa k'arasawa.
"Cikin wani irin yanayi take fad'in" Ya Jay zan iya canzawa da kaina..
"Murmushi Jalal yayi still tana matse cikin jikinsa kafin yace " But I insist, just let me help you pls, besides wann aiki na ne not yours...
"Kasa musu ta masa haka ta runtse idanun ta sanda taji Jalal ya rabata da rigar jikinta..
"A hankali cikin soyayya da shauk'i yake gudanar da komai..
"Har saida ya masu masauk'i saman tampatsetsen gadon sa..
"Abubuwa da dama suka shiga ziyartan zukatan su....
"Jikinta ya soma shaking tana mai yunk'urin hanasa..
"Manne ta yayi sosai cikin jikin sa , cikin wata irin kasaltecciyar murya yake fad'in" Baby pls don't deny me my right... I love you Zubaidah, I wanna be with you, I wanna smell you, I wanna feel you, I wanna show you how much I love you, ina so na mantar dake wancan daren 🌘... Pls don't say no kinji....
"Hawaye na bin idanun ta, ta k'ank'ame sa, azaban da ta sha a wancan daren kurum take tunowa...
"Cike da so da k'auna Jalal yake sarrafa ta, bai k'yaleta ba har saida ya mantar da ita wancan DAREN 🌘.
*Daren Alkhairi 🌘* Daren da ya goge bak'in cikin wancan daren, daren da ya kasance zai dawwama cikin tarihin rayuwar su...
"Sosai ya k'ank'ame ta hawaye na bin idanun sa....
Yanzu haka su Salim suka d'and'ana masa Zubaidar sa, Kai amma Allah Ya isan sa, bai jin zai tab'a yafe masu..
"A wann dare Zubaidah ta yarda cewa Jalal masoyin ta ne, duk wani hidiman da ake ma Budurwa a first night d'inta Jalal bai fasa yi ma Zubaidah ba, he's just treating her like a Queen, haka ya ringa ririta ta, har saida taji wani iri, hawaye ya shiga gangara mata sanda ta tuna itafa ba cikakkiyar budurwa bace.
"Kaman ya gane tunanin da take, ya shiga goge mata hawayen yana girgiza mata kai alamun " bai son ganin hawayen ta..
"Rungumota cikin jikinsa yayi kafin yace " I don't care, nasan dalilin da yasa kika kasance hakan, what matters is that I love you, ni ke d'in nake so Zubaidah, kinfi min ko wacece za'a kawo min.. Thank you, thank you for tonight, Allah Ya maki albarka ya azirta mu da zuri'a d'ayyiba...
"Ta kwantar da kanta cikin k'irjinsa had'i da rufe fuskar ta da tafukan hannu kafin ta furta " Ameen My Hubby....
***********
"Washe gari da sassafe tun kan Zubaidah ta tashi, ya tashi yayi wanka ya fice zuwa kabarin Mahaifiyar sa, yanda ake bisne matan sarakuna, Addu'a yake kan jero mata kaman daga sama yaji muryar Abba a gefen sa yana amsa masa da Ameen..
"Sun d'an jima kafin suka fito a tare suna zaga fadah cikin tafiya ta sarauta,
"Jalal sosai kayan Kufta ta masa kyau, tun daga riga da wando har takalmi kai har d'an hulan dake a saman kansa na kufta ne. Kowa ya gansu yanda suka jera sai yaji sha'awar su.
"Bayan ya raka Abbah har cikin fadah fitowa yayi Ya nufi sashen Madaki ya gaishe ta, nan ta rik'e sa dole tayita tura masa karin kumallo, sosai soyayyar tsohuwar ya shiga ran Jalal, daga nan sashen Annah ya nufa suka gaisa, ya tarar Kamal nata sharan Baccin sa a kan gadon Annah,
"Kana ganin Jalal yau kaga sabon ango, Annah saida taso fahimtar hakan, zuciyarta ta cika da farin ciki, fatan ta Allah Ya azirta su da zuri'a d'ayyiba.
"Daga sashen Annah ya nufi na Ummi, wai zo kaga yanda ake nan nan da Jalal tamkar a goya sa, ko da ya tambayi Ummi Zahidah fah sai ce masa tayi ai ta fice gaida kakar ku, k'ila kunyi sab'ani.
"Jalal ya d'an jinjina kai kurum kafin ya mik'e da niyyan tafiya.
"Su Jakadiya kaman a kifa k'asa sabida fadanci. Ga uban gizo da Charisma da Jalal ke masu..
"Sosai Zahidah da Zubaidah suka sake, gaba d'aya Zubaidah bata saba da abubuwan mulki da sarauta ba.
"Aike kuwa ta ko wani k'ofa shigo ma Zubaidah ake dasu, kama daga k'ofar Madaki yayi su k'ofar Ummi..
***************
*Abuja*
"Kasancewar ya sami partial stroke yasa yake dogarawa da wata 'yar sanda, tafiyar tamkar a karb'a a masa, yanayi yana hutawa.
"Mummy ce mai taimaka masa, ta rik'e sa ta side guda...
"Barr bai fad'a masu tafiyar su Salim ba saida ya tabbata sun isa gida kafin ya masu breaking news d'in don shi Salim Ya kira ya sanar, Alh Kasim hakan yama fi masa sauk'i zai samu yaji da Bankruptcy d'in da suke fama dashi a company d'insu,.
"Mummy da Mamy kam sosai fuskokin su ya nuna damuwa. Gashi babu hali su kira yaran nasu don tuni sun cire simcards d'insu sun jefar kafin ayi tracking nasu...
**************
"Wayan Balele ya karb'a ya shiga neman layin Zulaihat.
"Tana zaune gefen Innah taji wayar ta na ringing, ganin bak'uwar lamba yasata d'agawa cike da fad'uwan gaba.
"Daga d'aya b'angaren Umar yace " Ya kuke, ya Innah, ina take, da fatan bata d'aga hankalin ta ba???...
"Bata sami zarafin amsa masa tambayar sa ko guda d'aya ba sai zuciyar ta dake faman tafasa, cikin sauri ta mik'e ta fice daga d'akin kafin ta soma amsa sa cikin muryar kuka da tsananin b'acin rai..
"You got some nerve to even call.... Ka cuce ni, ka yaudare ni Umar, why, meyasa zaka min haka,... I hate you, I hate my self for loving you.... Daga can ya daka mata tsawa da k'arfin gaske,.
"Just shut up,!!
"Da k'arfi itama tace " Don't you dare scold me,... Kana so kaji halin da muke ciki ne, kana so kasan halin da ka barmu a ciki ne, Fine..
"Ka bar mu cikin damuwa, you are a criminal, I was wrong about you, da nayi zaton ka canza, ..... Kuka ya kufce mata sanda taci gaba da fad'in" Bak'in cikin Ka ya jefa mahaifiyar ka cikin tsananin ciwo, kullum da bak'in cikin ka take kwana ta tashi, she's very ill, I'm afraid she's dying...... Ta k'arashe tana kuka sosai...
"Jikin sa yayi sanyi sosai, duk shak'iyancin sa yana son mahaifiyar sa sosai,.
"Cikin wani irin murya mai cike da damuwa ya soma lallashin Zulaihat yana fad'in" I'm sorry, I'm Zulaihat, zanzo zanzo kinji, pls ki turo min address na hospital d'in, zan canza kamanni coz I know police are after me. Pls kar ki bari wani yasan zan zo kinji.... I love you Zulaihat, I know you still love me,.
"Zan d"auke ku keda Innah mu gudu gaba d'aya...
"Zulaihat ta murmusa kawai kafin tace a ranta.. " It's over between us, You are going to Jell this time around ...
"Daga haka kashe wayar tayi ta shiga neman layin Imam....
🌘🌘🌘🌘 *ZUBAIDAH*
92
*©Sameena Aleeyou...✍🏾*
_🌈KWA_
*Dedicated To All Victims Of Rape...*
_For those who read Mijin Haneefah and Mallakin Waye 😍_
*Lagos, Apapa*
"Kallon yanyin d'akin hotel d'in kawai Salim yake shaye da mamaki, gaba d'aya irin local hotel d'in nan ne, Kai bai jin zai iya bacci a nan balle cin abinci.
"Tsaye yayi ma Labib dake zaune saman 'yar gadon yana latsa wayar sa.
"Labib ya d'ago ya kalle sa kafin yace " Miye ka wani tsayan aka ko ce maka nayi ina buk'atar guard.
"Salim Ya fuzar da iska kafin yace " For heaven's sake meyasa zaka kama mana wann hotel d'in, ta yaya zamu soma rayuwa a nan, ba sati d'aya ba har sati biyu, gaskiya I can't, kasan inada allergy, something small can irritate me.
"Tsegege Labib ke kallon sa kafin yace " Wllhi bansan yaushe zakayi wayo ba kaikam, ina kake so muje, expensive hotel, wajen da we can easily get caught ko me, wai meyasa IQ d'inka bata aiki ne.. Okay na gane ba laifin ka bane, you're well brooded Ajeboter ko, iyayen ka sun gama sangar ta ka, that's why you're a coward, kai da Mace babu maraba...
"A hankali Salim yace " Enough of this Labib, don't insult me.
"Or what, me zaka min. Ba gaskiya nake fad'i ba.... Kai idan kaga bazaka iya zama dani ba kana iya tafiya it's not a big deal...
"Salim bai kuma cewa komai ba sai ajiye luggage d'insa da yayi a gefe ya zauna gamida rapka uban tagumi....
"Labib ya rakasa da harara, cikin zuciyar sa kuwa burinsa kawai shine ya provoking Salim yayi tafiyar sa su raba hangar....
*************
"Ba tareda sanin kowa ba Jami'an tsaro Suka sa duk wani kafofin sadarwa suke d'aukar maganar da Dasuk'is suke a waya sabida hakan zai taimaka wajen fito da gaskiya. Musamman yanzu da su Salim suka b'ace. Don zai taimaka masu wajen sanin ina su Salim suka dosa tunda iyayen sunyi biris sunce basu sani ba, amma ko tabbas sunsan zasu ke magana da iyayen su.
"Bayan kwana biyu Alh Kasim ya soma warewarewa har Office yau kam yaje shi.
"Tun daga waje suka hangi cincirindon employees a reception kowa yana nasa k'orafin, sun gaji da zama babu salary.
"Hankalin Alh Kasim ya tashi, cikin zuciyar sa banda tsine ma Jalal babu abinda yake, duk shine ya jawo har aka kawo wann peak d'in, da yanzu yayi Business partnership da Modibbo cooperation da ba haka ba. Kai dole yasan yanda zai yi yayi defeating shegen yaron nan a kotu... Barr Munir sai shafa kansa yake yana neman mafita,..
"K'arshe dai Barr ya fito ya same su ya soma calming nasu sai bore suke ko kulasa basa yi, su dai kawai Mr President ya fito ya sanar dasu matsayin da suke ciki. Daga can conference hall kuwa shear holders ne suke ta fafatwa, kowa na yunk'urin cire dukiyar sa a Dasuki Holding sai dai babu abinda za'a biya su dashi. Don kuwa sosai wann company ta shiga matsin tattalin arziki.
"Barr ya dubesu gaba d'aya kana ya bud'e murya ya soma fad'in" All of you should calm down.... Za'a yi komai yanda ya dace, I assure you this company would do everything possible to answer to each and everyone of you, ku k'ara mana hak'uri, haba I suppose mu daku mun zama d'aya, a irin wann situation d'in bai kamata kuke mana haka ba idan baku taru mun rufa wa juna asiri ba,....
"So pls ku k'ara hak'uri meeting d'in da muke a yanzu haka ma sabida ku ne, please kowa yayi hak'uri ya koma bakin aikin sa, komai zai zama daidai da yardar Allah..
"Daga me tab'e baki sai mai gunaguni sai mai k'anan mita haka suka nufi ofishoshin su,..
"A can conference meeting kuwa abu ya kwab'e, baran baran aka tashi da shear holders daga masu cewa zasu suing Alh Kasim sai masu cewa ya fito masu da kud'in su don basu yarda da ysautsayin sa ba,..
"Hankalin Alh Kasim idan yayi dubu ya rabbi, ga likita ya hanasa shiga damuwa amma babu yanda ya iya, dole ne ma ya shiga damuwa...
"Kaman daga sama Barr yaji wayar sa tana ruri, ya d'an matsa gefe ya soma amsa wayar...
"Cike da mamaki da jin dad'i Barr ke amsa wayar jin wani k'aramin company ne suke son sayan hannun jari..
"Alh Kasim dae shiru ya d'anyi kafin yace " Kasan fah nifa bana huld'a da k'anan mutane, basu haifar da komai sai tab'arb'arewar kasuwanci.
"Barr ya murmusa kafin yace " A halin da muke ciki ai bamuda wani zab'i ya wuce muyita amsar su, daga baya idan mun gama settling muyi watsi dasu, tunda kaga abubuwa ne da dama a gaban mu..
"Alh Kasim ya gyad'a kai yace haka ne.
"Wasa wasa mutane da dama daban daban sukayita sayan hannayen jari a Dasuki Holding har aka samu aka biya ma'aikata,.
"A k'alla saida kusan mutane 10 suka saya hannun jari a Dasuki Holding, daga mai sayan 15% ,10% , har dai masu 5%.... Alh Kasim sai murna yake, at least he'll still remain the president, tunda babu mai shears d'in da yafi nasa, .... Zai bunk'asa hark'ar kasuwancin sa sosai yasan kafin nan da wani wata mai kamawa yayi watsi da Hon Gali, da sauran masu damun sa kan kud'ad'en su...
************
*Gombe Fadah*
"Zaune yake saman tampatseten Carpet d'in Turkey da ya kusa mamaye parlorn, MacBook d'insa ne a gaban sa yana aiki bisa, har wani fresh ya k'ara, kana ganin sa kasan kwanciyar hankali ta samu,.
"Zubaidah ce ta fito daga wani k'ofar wanda nake zaton kitchen ne, hannunta rik'e da k'aramin paranti, saman parantin glass cup ne na fresh pineapple juice,cikin tsanaki da yanga take tafiyar nata.
"Tun daga nesa ya kafe ta da idanuwa yana sakar mata sassanyar murmushi,.
"Itama murmushin take har ta k'araso gare sa tana mai masa sannu da aiki take k'ok'arin ajiye plate d'in saman center table....
"Hannu ya mik'a ya d'auki cup d'in zuciyar sa fari k'al yake murmusawa yana duban ta, saida ya kurb'i drink d'in kafin ya jawo ta cikin jikin sa yace " Sannu Baby Wifey, na gode koh Allah Ya maki albarka...
"Zubaidah har ranta take jin dad'i idan yace " Allah Ya mata albarka....
"Hannunta ya rik'e cikin nasa yana kan murza su a hankali idanun sa k'yam akanta yanda ta k'ara fresh da wani muslumin kyau kafin yace " Baby wai ni me Ummi da Annah suke baki ne kike wani fresh da kyau haka, naga kullum da safe sai anyi aiken Zahidah ta kawo maki abu kuna k'usk'us baku so naji.......
"Sosai ya bawa Zubaidah dariya yanda yayi maganar...
"Ta ware daradaran idanunta kafin tace " Wato dama sa ido kake mana kullum koh, aiko zamu canza takun...
"Murmushi shima yayi yana warware d'aurin kanta yake fad'in" Ince dai ba maganin mallaka ake kawo min ba... Ya k'arashe teasingly...
"Sosai take dariya tana fad'in" Haba kaima dai kasan wuce nan ai.. " Rungume ta yayi ya matse cikin jikin sa kafin yace " Ai nikam ma kin gama mallaka ta, da kai da k'afan duk Kin same su, I'm all yours... Ya k'arashe yana mai kai mata sunbata... Sukayi nisa cikin wata duniya har saida wayan Jalal yayi interrupting nasu...
"Ganin Ansar ne me kira yasa sa saurin d'agawa yana Fad'in " Attorney mtanen Chamber ka b'uya fah, still tana nan zaune saman cinyar sa yana wasa da abubuwan da suke MALLAKIN SA ne,.
"Daga d'aya b'angaren Ansar yace " Daga jin muryar kan nan kana gane ma garin Gombe, a tare suka dara kafin Jalal yace " Kaji alama kenan.
"Ansar ya murmusa kafin yace " Kafin ka b'aro min wata zance yaya su Annah su Zubaidah.!?
"Jalal ya amsa da duk suna nan lafiya suna gaida ka,... Ina Hafiz two days kenan ina kiran wayar sa bana samu...
"Ansar yace " Wllhi ya d'an tafi can Ghana duba family kasan iyayen sa can suke...
"Jalal yace " Au shine babu ko sallama..
"Kai tafi can waye zai tsaya kiran ka, ba kashe layin ka kayi ba don kar talakawa su dame ka da kira, ga sarauta ga angwanci...
"Sosai Jalal yake dariya kafin yace " Kazo a baka sarauta amma sai ka kawo mata...
"Ansar ya murmusa ba tareda yace komai ba don kuwa tabbas ya tuno masa da masoyiyar sa Asmah..
"Jalal d'inma kuma sai yaji wani iri da ya fad'a masa hakan...
"Ansar ya kawar da zancen da maganar gudun su Salim wanda dama shine mak'asudin kiran...
"D'aga Zubaidah yayi daga cinyar sa kafin ya mik'e ya nufi wani parlorn don baiso taji snn yaci gaba da amsa kiran. Nan suka soma tattauna lamarin.
*******************
"B'adda kamanni yayi ta yanda baza'a gane sa ba, yana sanye da bak'ar jacket da kuma facing cap, idan ba ka masa farar sani ba bazaka tab'a ganesa ba.
"A haka ya lallab'a ya shige ward d'in da ta masa kwatance.
"Tana zaune gefen Innah tana bata tea a baki suka ji an murd'a k'ofa a hankali, ba'a shigo ba sai lek'e lek'e da ake....
"Zulaihat tayi saurin mik'ewa a d'an tsorace tana tambayar waye... Kan ta kai aya sai ganin sa tayi ya bayyan a gaban ta...
"Jikinta ya shiga rawa kamar mazari don harga Allah tsoro yake bata yanzu...
"Sun jima suna kallon juna shida Zulaihat kafin suka jiyo muryar Innah wanda bai fita sosai tana tambayar Zulaihat wanene ya shigo ko likita ne...
"Zulaihat bata iya amsa mata ba sai hawaye dake k'ok'arin bin k'uncin ta..
'Cikin sauri ya wuce Zulaihat ya k'arasa ga Innah dake kwance saman gado ya rik'o hannayen ta yana fad'in" Innah.. Innah nine, Baba wuron ki ne, ......
"Jin haka yasa Innah bark'ewa da kuka dukda sautin kukan nata bai fita, take ta kasa magana sai shafa fuskar sa da take yi, tana son yin maganar saidai kaji alamun hakan amma muryar bai fita..
"Kwantar da kansa yayi saman kafad'ar ta Ya shiga zuban hawaye yana fad'in" Ki yafeni Innah, ki yafe ni, nasan na sab'e ki na sab'i Ubangiji na, na zalunci mutane, amma su suka fara zalunta ta, suka rabani da abinda nafi so, suka nesanta ni da ita, suka saka mana sha mak'i.. Innah ba laifi na bane....
"Zulaihat kam bata iya jure jin kalaman Umar ba sai ficewa da tayi zuwa corridor, tana kuka da duka zuciyar ta... Wann wani irin rayuwa ce, a duk lokacin da ta ga Umar sai taji soyayyar sa cikin zuciyar ta koda tana yak'i da jin hakan, tana dakwan soyayyar sa yana dakwan soyayyar wata.... Tabbas soyayyar ya zautar da Umar ya kurmantar dashi ya makantar dashi.... Tausayin kanta da rayuwar data tsinci kanta a ciki ya cika mata zuciya.
"Share hawayen ta shiga yi kafin ta shiga scrolling number a wayar ta zuciyar ta na mata wani irin bugu... Bata da zab'i face ta aiwatar da abinda tayi niyya. Wann shine iyakacin soyayyar da zata nuna masa snn yin hakan shine zai kawo peace ma kowa da kowa...
"Hello Inspector..!!!!!
"Ta fad'i cike da dakewa....
*********
"Jim kad'an bayan ta gama wayar da Inspector ta komo cikin d'akin har lokacin yana nan kwance gefen Innah yana kuka sosai...
"Zaman Zulaihta da kad'an aka soma knocking a k'ofa.... "K'irjinta ya yanke ya fad'i.... Har saida aka buga k'ofar a karo na uku kafin ta sami k'warin gwiwar mik'ewa....
"A lokacin shima ya mik'e yana jiran yaga mai shigowa, dukda ya razana amma yasan bazai wuce likita bane...
"Imam ne ya shigo hannun sa rik'e da leda yana mai bin Zulaihat da kallo ganin hawaye kwance saman fuskar ta..... Mamaki ya hanasa furta komai sanda ya hangi Umar tsaye yana watsa masa wani mugun kallo..... Daidai lokacin da Cops suka shigo cikin d'akin...
"A firgice yayi niyyan haurawa window sukayi pointing nasa da bindiga suna fad'in" Don't move.... " You're under arrest for the murder of DT Kaita and Barr Asma'u Marafa and also for the Kidnapping of Mrs Jalal Lamid'o..... You've the right to remain silent, duk abinda ka fad'a zai zama hujja akan ka a gaban Alk'ali.....
"Huci yake yana kallon Imam kafin ya soma fad'in" You imbecile kaine ka kirasu... Wllhi sai na kashe ka...
"Imam dai kallon ikon Allah kawai ya tsaya yi.... "Zulaihat na kuka ta k'araso gaban sa sanda ake d'aura masa handcuffs kafin ta soma fad'in" Ko d'aya babu laifin Imam saidai ma taimaka mana da yake yi, Ni ce nan na kira cops, tasa hannu tana goge hawayen ta kafin taci gaba da fad'in" Alhamdulillah, kowa zai zauna cikin kwanciyar hankali yanzu, kasani Umar wann shine k'arshen soyayyar da zan nuna maka...... Kuka ya hanata k'arasa maganar...
"Girgiza kai kawai Umar yake yana kallon ta kafin ya iya furta " Kinci amana ta Zulaihat, kin ci amanar soyayya, I'll never forgive you for this..... "Daidai lokacin da 'yan sanda suka tasa k'eyar sa.... Tarjewa yake yana kiran Innar sa da tuni numfashin ta ya soma fita sama sama.... Mik'a hannu Inna ma takeyi tana son rik'o hannun d'anta yayinds shima Umar d'in tarjewa yake yana son kamo hannun Innar sa..... Ina Cops sun fice dashi a d'aure...
"Zulaihat ta fashe da wani irin kuka tana mai durk'usa gwiwoyin ta k'asa yayinda hankalin Imam gaba d'aya ya kasu ga Innah dake faman shid'ewa rai a hannun Allah.... A saba'in ya fice yana k'walla ma nurses kira ya nufi ofishin Dr....
"Zulaihat ta yunk'ura tayi kanta tana jijjiga ta....
"Allahu Akbar, saidai kafin Dr ya iso rai tayi halin ta.... Haka yayita basu hak'uri aka shiga warware na'urori...
"Tausayin Zulaihat ya cika zuciyar Imam, inama yanada damar rungumar ta, tabbas da yayi hakan ko ta sami sauk'i cikin zuciyar ta....
"Kuka Zulaihat keyi tana mai d'ora ma kanta alhakin mutuwar Innah tunda itace ta kira 'yan sanda suka tafi da Umar..... " Imam sai faman lallashin ta yake yana nuna mata ko ta kira 'yan sanda ko bata kira ba wa'adin Innah yayi sann dole ta amsa kiran mahaliccin ta, Abinda ya rage su bita dashi shine add'u'a, Allah ya mata rahama yasa k'arshen wahalan ta knn, snn kiran 'yan sanda da tayi shine daidai domin kuwa barin Umar na yawo a tsakanin Al'umma babban had'ari ne.. Allah Ya ga nufinta yaga irin soyayya data nuna ma Umar, Allah yaga rufa masa asiri da ta ringa yi... Amma dashike shi d'in ba mai karb'an k'addara bane ga irin rayuwar da ya jefa kansa..... " Allah ka mana tsari da bak'ar zuciya Ameen, Allah ka shirya mana Al'umma baki d'aya Ameen....
"Gidan Goggo aka wuce da Innah aka mata sutura da komai da komai, Imam ya amshi layin Balele wajen Zulaihat Ya kira ya sanar dasu halin da ake ciki snn yace dashi sai ya sanar da 'yan uwa da abokan arziki....
******************
"A zuciye Salim ya mik'e yana watsa wa Labib mugun kallo kafin yace " Don't take me for a fool, akan bansan me kake shiryawa bane ko me... Bari kaji na fad'a maka I over heard you kana magana da wani on phone kana ce masa zakayi fitowar dare ku had'u a tashan jirgin ruwa na Tinkan Island, ko ba haka akayi ba...
"Labib baice komai ba sai mugun kallon da yake watsa wa Salim.
"Salim Ya kad'a kai kafin yace " Ni zaka cuta Labib, of all ppeople ka rasa wa zaka cuta sai ni, ka bani kunya kuma ka bani mamaki.....
"A zuciye Labib ya mik'e yana huci yake watsa masa mugun kallo kafin yace " Don't you dare raise your voice on me, who the heck you think you are..?
"Da kake maganar cutar ka zanyi kai ba wata ka cuta zaka gudu ba kar a kama ka, snn idan nayi cuta da zalunci ai gado ba karambani bane tunda a bayyane take worthless Uncle d'ina Kasim Dasuki na gada.... Ai bai kai aya ba Salim da zuciyar sa ke faman tafar fasa yayi tsalle ya kai mai naushi a hanci.... Haba nan suka kauri da kokawa, dukan juna suke ko wanne da ci da zuci yake dukan d'an uwan sa.... K'arahe k'ofar d'akin suka fincika suka fito har stirs suna dukan juna....
"Da shike hotel d'in irin wanda marassa kamun kai suka fi zama ne nan akayi chaa ana kallon su....
"Manager kuwa daga zuwa ya patattake su kafin suja wo masa hankalin Police ya rasa customers..
"Haka manager yayi masu watsi da kayyayakin su, aka raba tafiya, k'asar gada Salim Ya samu ya pake gashi duk kud'in hannun sa Labib ya amshe ya kaisu ma Captains drobobin jirgin ruwan a cewar sa...
"Labib yanaji shine mai kud'i a hannu kai tsaye wani club ya wuce zuciyar sa na tafarfasa don ba haka yaso abin ta kasance ba, yafi so sai ya tafi Salim Ya laluma yaji wayam...
"Double whiskey yace a had'a masa, nan ya dinga kwankwad'ar giya yana k'arawa...
"Wasu area boys dake zaune can gefe sai karantar sa suke, kai daga ganin sa ma kasan d'an masu kud'i ne tun daga siturun dake jikin sa da kalan whiskey d'in da yake kan faman kwankwad'a ba tareda tsoron bill ba..
"D'aya ya tab'a d'aya ya masa nuni da Labib...
"Murmushi yayi sukayi magana da juna k'asa k'asa kafin sukayi wata murmushi suka k'arasa gaban bar d'in yanda Labib ke zaune saman wata doguwar kujera....
"D'aya ya d'auki whiskey d'in Labib ya shiga sha ba tareda ya tambaye sa ba...
"Labib yazo wuya, dama already cike yake da haushi, bai kulasu ba ya mik'e zai tafi d'aya ya sha gaban sa.....
"Labib ya d'an fuzar da iska kafin yace " What do you want from me..????
" Murmushi suke masa su duka biyu d'ayan na neman kai hannu aljihun sa... Labib yayi wata tsalle ya kai mai naushi....
_Get to f*ck_Kan bala'in can, ashe gang d'insu guda ne a wajen nan sukayi kan Labib gaba d'aya club ta tarwatse.... Kan kace me fad'a ya kaure, suka sutale sa tsaf suka masa jina jina... Police suna zuwa suka gudu suka bar Labib.... Haka police sukayi arresting Labib aka wuce dashi station..
"Salim daga nesa ya hangosa kasancewar k'asar gadan da yake da club d'in babu nisa,, jin hayaniya Ya kaure shi ya ja hankalin Salim wajen... Girgiza kai kurum yake lokaci guda ya juya a guje ya koma yanda ya fito yayinda Labib ya d'ago idanu kurum ya kalle sa gamida sunkuyar da kai...
"Washe gari aka tafi da Labib Abuja, yanda ake tsare dashi a police station, babu yanda basuyi ba Labib ya fad'i dalilin gudun su, fir yak'i yarda, k'arshe ma ce masu yayi bazai yi magana ba sai Lauyan sa yazo..
"Alh Kasim ba k'aramin dad'i yaji ba sanda ya riski labarin Labib kawai aka capke, Barr Munir ma kin zuwa wajen Labib yayi, dole aka ci gaba da tsare Labib,..
"Sosai Mamy da Mummy suka sha kuka sanda suka je cell suka duba sa, ga bakinsa da hancin sa duk alamun ciwo yanda aka lakkad'e sa.
"Shi kuwa Labib tunda yaga haka, Alh Kasim da Barr Munir sunyi watsi dashi ya k'udura a ransa bazai tab'a bada statement d'insa ba har sai ranar da aka capko Salim...
"A b'angaren su Alh Kasim kuwa hankalin su yayi nisa kan business d'insu komai ya soma tafiya normal yanda suke so, ko kad'an bata Labib suke ba..
"Yau ta kama rana ce wanda zasuyi conference meeting da gaba d'aya shear holders d'insu, musamman domin sababbin masu hannun jari...
"Gaba d'aya hall d'in ta cika fam, an zauna ana gudanar da meeting sanda Alh Kasim yake introducing sababbin shear Holders na company d'in...
"Wani abin mamaki shine a lokaci guda wayoyin su suka soma ringing.
"Gaba d'aya suka mik'e kowa yana fad'in " Boss d'insa ya iso..
"Speechless Alh Kasim da Barr suke binsu da kallo don basuyi zaton hannun jarin ba nasu bane, basu tsammaci hakan ba sam...
"Barr ya washe baki yana fad'in toh ai sai su shigo a ci gaba....
"Innalillahi mutuwar tsaye Alh Kasim yayi sanda ya hangi masu shigowa...
"Ba kowa bane illa Hajiya Raliya matar marigayi Tahir Marafah, gefe da ita d'iyarta Kausar ce yayin da Ansar ke d'aya gefen,.. Guards ne suke take masu baya, gaba d'aya sun sha ado cikin tufafi na alfarma...
"Alh Kasim bai gama mamaki ba saida yaga gaba d'aya Shear Holders d'in nan sun mik'e suna rusunawa suna fad'in" WELCOME MADAM.
*Sameena Aleeyou Mrs*
🌘🌘🌘🌘 *ZUBAIDAH*
93
*©Sameena Aleeyou...✍🏾*
*Dedicated To All Victims Of Rape...*
"Cikin sakon guda bugun zuciyar Alh Kasim yakan harba sau babu adadi.. " Kai tabbas abinda yake ganin na shirin faruwa ba gaskiya bane, kai shakka babu imagination d'insa ne... Hakan bazata tab'a kasancewa ba... Muryar Barr Munir ne ya katse sa sanda yake fad'i cikin in.. Ina da cijewar murya..
"Me...nene... Hakan, su waye ku, lafia, me kuka zo yi a nan..??? Ya k'arashe yana k'ok'arin k'arasawa gare su...
"Cikin sauri guard guda d'aya ya taresa da hannu guda yana girgiza masa kai, alamun he should respect him self....
" Murmushi kawai Hajiya Raliya keyi yayinda Shear Holders d'in suka soma nuna mata wajen zama suna fad'in" You arrived on time Ma'am, the meeting is just about to start....
"Kausar ta murmusa kafin tace " Ai ma dole a jira isowar ta kafin a soma, snn koda an fara dole a koma baya a matsayin ta na me majority Shears of the Company...
"Ba Alh Kasim kurum ba harta Barr saida yayi kusan sakin fitsari mai d'umin gaske a wandon sa.... "Muryar Ansar ya dawo dasu daga duniyar tunanin da suka lula sanda yake fad'in"
"You are absolutely right lil Sis , She's the owner of the Company sai yanda taso za'ayi snn sai wanda taga dama ta bari a company d'inta, and I'm pretty sure bazata had'a kasuwancin ta da gurb'atattun mutane ba. A yau mutum zai gane cewa Allah Ya wuce gaban wasa, snn duk nisan jifa k'asa zata fad'o, k'arshen alewa k'asa ne inji masu iya magana...
"Ya k'arashe yana mai gyara wa Mumsy kujeran dake a center har yana bangaje Alh Kasim kafin yace" Bismillah Mumsy, you are the President Of the Company, at the center ya kamata ki zauna....
"Mumsy ta murmusa kafin tace " Thank you My boy... But I really need to clear things up kafin na zauna.... Ta k'arashe maganar daidai sanda ta iso gaban Alh Kasim wanda ya kasa d'ago idanu ya kalle ta sai juwan dake neman d'iban sa, ga uban zogi da k'irjin sa ke masa...
"Mumsy ta bud'e murya kana tace " Kasim Dasuki, ka sani ba'a son raina bane zan k'ige ka from your position of being the president of the company, no saidai bazan iya barin dukiyan mutane a hannun ka kana running ba, snn abu na gaba don't think negatively ba k'wace maka company nayi ba.
"On the contrary I'm only saving the company from going bankrupt.. Ko ba haka bane..??? Ta k'arashe da alamar tambaya. Bai ce komai ba sai kallon k'asa da yake yi ya kosa motsa koda yatsar k'afar sa..
"Mumsy ta murmusa kafin taci gaba da fad'in" Na tabbata kud'ad'en da nayi amfani dasu wajen sayan hannun jari a company d'inka really helped, tunda an biya ma'aikatan da suke barazanar ajjiye ayyukan su snn ya taimaka wajen farfad'o da compnayn daga matsin tattalin arziki da kariyan arzikin data fad'a.. Kasan da shike ance D'an halak bai mance Alkhairi, ni ban mance kai d'in tsohon aminin mijina bane kaman yanda kai ka mance Shi marigayi tsohon aminin ka ne, nasan kasan irin mutuwar da mijina yayi wanda shakka babu abu ne wanda aka aiwatar sa da shiri, ma'ana da nufi ne koma wanene yayi wancan aikin.
"Alh Kasim mijina ya mutu an k'ona sa da dukiyar sa baka ce komai ba a matsayin ka na aminin sa dukda cewa nasan sab'ani ya shiga tsakanin ku kafin ya bar duniya..
"Amma tabbas nasan da ace kaine hakan ta faru akan ka, duk kalan sab'anin da kuka samu sai yanda k'arfin sa ya k'are wajen zak'ulo wanda yayi wann aika aikan... Baka yi ba sai wani babban abin mamaki da muka gano kwanan nan, duk abokan kasuwancin sa da suka azzala mana biyan su hakkokin su da suka k'one, kaine ka dinga binsu d'aya bayan d'aya kana tsara masu hakan, kana jawo su jikin ka... Idan baka sani ba ka sani, Hon Gali is one of them, yana d'aya daga cikin abokan kasuwancin mijina da ka ringa bi mail d'insu kana tura sak'wanni na k'arya, just to make my life and my daughter's life so miserable,... Ta d'an ja fasali hawaye na ciko idanun ta kafin taci gaba da fad'in" Me muka maka da tsanani Alh Kasim... Don mun k'i amincewa ma criminal Son d'inka auren d'iyar mu, wann har ya isa ka jefa rayuwar mu cikin garari.... Ko kuwa don mijina ya zame dukiyar sa daga cikin naka wann har ya kai ka mance duk alkhairan da suka faru a baya...??....
"Hall fah tayi tsit muyar Mumsy kawai kake ji, tausayi ya cika zuciyoyin jama'an dake wajen yayinda Barr da Alh Kasim suka kifa kawunan su a k'asa cike da rashin gaskiya...
"Mumsy ta murmusa ta goge hawayen da suka Zubo mata kafin taci gaba da fad'in" Ka sani I won't kick you out of the company but zanyi k'uri'a da gaba d'aya shear holders, idan majority sunce a barka a company d'in a matsayin employee fine za'a barka, don bincike na ya nuna min single scent baka da saura cikin company d'in, da bazar mutane kake rawa, banda tsugugun bashin da na clearing a different Banks without your knowledge... Ta murmusa sanda ya d'ago rinanun idanunsa yana duban ta kafin tace " Nasan baka san da wann ba, abu guda da ya rage kaje ka wanye dasu sune masu binka bashi irin su Hon. Gali wanda nima bana buk'atar su a company d'ina..... Idan hakan ya maka kana iya zama a ci gaba da tattaunawar.....
"Kaga yanda annuri ya cika fuskokin shear holders, tuni sun soma jefo k'orafe k'orafen su, takardu sun cika gaban Mumsy kaji ana ambatan ta da MADAM PRESIDENT, President Dasuki Holding...
"Murmushi kawai Mumsy tayi kafin tace " Akwai changes da dama zamu aiwatar a company d'in, ciki harda canza sunan Company d'in daga DASUKI HOLDING zuwa MARAFAH CONSTRUCTION COMPANY, kar ku damu da jin construction company, not only Engineers and Architectures, everyone is welcome to invest his money here matuk'ar dukiyar sa babu gauraye da haramun...
"Barr ya soma k'ak'aro murmushi yana k'ok'arin had'a kalamai saman harshen sa yake fad'in" Ai... Ai... Hajiya I mean Madam President, ai ya kamata ni zanyi accrediting gaba d'aya changes d'in a matsayi na na Attorney of the company...
"Tsegege kawai Kausar ke kallon sa kafin tace " And who told you muna buk'atan people like you a nan??, We've nothing to do with an incompetent Attorney like you.... Park your wahala and get lost...
"Ansar ya murmusa kafin ya k'arasa gaban Barr Munir yace " Attorney ko kad'an banyi niyyan taking position d'inka ba, amma babu yanda na iya don bazan iya barinka ka rab'i new family d'ina ba ku rabani dasu kaman yanda kuka rabani da wad'ancan... Right Alh Kasim... Ya k'arashe yana mai kai duban sa ga Alh Kasim wanda bai gane meke faruwa.. Shidai kawai yana jin sautin mutane ne sama sama....
"K'arasowa har gaban sa Ansar yayi kafin yace " Nasan ban tuno maka kowa ba face marigayi Alh Ma'aruf Kumo wanda kayi destroying nasa da family d'insa with your selfishness, amma kar ka damu I'll add more charges against you, bayan shari'ar ku da Zubaidah you'll answer to me, you'll pay for each and single crimes you had committed...... Ya k'arashe in a furious tune idanunsa suna masu ciko da hawaye masu zafi....
"Shin wai da gaske hakan ce take faruwa ko kuwa dai tunanin sa ne ke basa haka, kai yafi aminta da mafarki ne, Ma'aruf da Tahir mutanen da ya cuta a duniya yau shine iyalan su ke rama masu, kai da gaske Dasuki Holding is not longer his, Kai a'a haba dae, babu wanda ya isa ya mallaki Dasuki Holding face shi....
"A zabure ya nufi waje yana kwab'e takalman Sara hannu yana rik'ewa yake fad'in" No.... No this can't be, I'm Kasim Dasuki the owner of Dasuki Holding, this company is mine,..... Karya kuke karyar ku tasha k'arya..... " Mutane sai kallon sa suke....
"Barr yayi kansa ya rik'esa yana fad'in" Alh Kasim hauka ne kayi,..?? Are you gone insane..??
"Fincika yayi yana watsa masa mugun kallo yake fad'in" Sune mahaukata da suke tunanin zasu iya k'wace company na daga hannu na, nothing is wrong with my sanity.... Kai ko Jamilu ma ban bar masa compnayn nan ba balle ku..
"Kausar ta mik'e tana kiran guards kana tace " Pls take this man out of here.... Bubbuge su Alh Kasim yake yana fad'in" Raliya kinsha k'arya ki k'wace min company na... Ya zabura yayi kan shear holders d'in da Mumsy tayi amfani dasu yana fad'in" 'yan k'wal uba munafukai, duk sai na kashe ku, dama had'a baki akayi daku... Duk sai kun mutu.... har aka iso floor d'in Office d'insa fincika yake yanda ya hangi sai parking stuffs d'insa ake cikin Cottons ana sealing nasu sann ana zuba sabbin Furniture na Hajiya Raliya....
"Fincika yake yana ihu yana fad'in" Shine Alh Kasim, shine mamallakin Dasuki Holding... Ina ko sauraren sa guards basuyi ba suka watso sa waje... Barr na biye dashi rik'e da takalman Alh Kasim da hular sa...
"Basu gama rikicewa ba saida suka ga ana d'aye babban singbord na company d'in, GB sunata faman aikin su suna b'anb'arota tun daga k'asa suna saka sabon sunan company d'in wato MARAFAH CONSTRUCTION...
"Alh Kasim shi kad'ai yake zabura yana ya nufi kwalta, saida Barr da su James suka agaza aka jefa sa cikin mota kafin suka nufi gida dashi....
****************
"Zaune suke wajen ganawa da prisoners... Sunfi minti goma suna jiran ya fito amma shiru bai fito ba..
"Zulaihat ta d'an dubi Imam kafin tace " Kodai muje ne kawai nasan bazai fito ba..
"Imam ya d'an sakar mata murmushi don ya k'arfafa mata gwiwa kafin yace " Zai fito yanzu insha Allah mu d'an k'ar hak'uri...
"Murmushin itama tayi kafin ta jinjina masa kai alamun toh..
"Minti biyar zuwa bakwai suka k'ara kafin suka hange sa ganduro ba ya fito dashi yana sanye cikin uniform na prisoners...
"Tana hangosa taji ta kasa tsaida hawayen da suka ciko idanun ta, tausayin sa da soyayyar sa na ratsa zuciyarta lokaci guda ta tafi ta rungume sa tana wani irin kuka yayinda Umar ko gizau baiyi ba balle yayi tunanin zai mayar mata da martanin rungumar ta...
"Imam kuwa har cikin ransa yaji wani irin k'una, mik'ewa yayi ya fice daga wajen cikin sauri yana mai tausaya ma kansa...
"Da k'arfin gaske Umar Ya b'anb'are ta daga jikin sa yana watsa mata kallon tsana yake fad'in" Uban me ya kawo ki wajena, ba kinyi abinda kike ganin shine daidai ba, kin sa an kama ni which means bazan kuma ganin farin cikin rayuwa ta Zubaidah ba, toh waima kukan me kike ne?? Ai na d'auka idan mutum yaci riba ba kuka zaiyi ba murna zaiyi.. Kin wani kwaso k'afa sabida tsaban munafun ci dake da d'an iskan saurayin ki wanda kuke cin amanata tare kinzo koh??? Toh ki min me..???
"Hannu tasa ta shiga share hawayen ta kafin ta soma girgiza masa kai ba tareda ta furta koda kalma ba..
"Fizgo hannun ta yayi da k'arfin gaske suka nufi kan wata benci ya zaunar da ita da iya k'arfin sa wanda saida ta buge k'afar ta jikin table d'in dake tsakiya..
"Hararan ta kawai yake har lokacin hawaye take muryan kukan nata ma baya fita...
"Umar yaci gaba da fad'in" You shouldn't have bothered, zuwan ki nan da rashin sa all the same, don tuni ni Umar na janye igiyar aurena akanki, ma'ana na sake ki...... Abu guda zaki min ki burge ni shine ki kawo mun sanyin idaniya na na kuma sakata a k'wayan idanu na, ke kanki kin sani sabida na mallake ta na aure ki bacin haka babu abinda zanyi dake karuwar banza....... "Tafasa kawai zuciyar ta keyi bata san sanda ta kwashe sa da mari me kyau ba tana faman huci..
"Shaye da mamaki yake bin ta da kallo, yau shine Zulaihat ta mara,.... Baiyi yunk'urin ramawa ba sabida gandurobobi da suke daga can gefe. Dafe da k'uncin sa yake kallonta yanda take magana cikin karaji...
"Kar ka kuskura ka kuma kirata karuwa, idan sanin da ka mun a da ne, toh Allah Ya shirye ni, snn duk girman laifina bai kai na kashe wani ba snn baikai girman mutum ya nemi matar wani ba... Idan wann soyayya ce tir da irin soyayyar ka, snn ka sani da ni da kai duka Makahuwan soyayya muke, tabbas na yarda soyayya ya hanani ganin laifin ka, snn bakin iyaye shi yayi tasiri a aure na da Kai, ka sani ni Zulaihat Allah Ya jarabce ni da soyayyar ka, kayita aikata kurakurai a baya bana gani sabida soyayyar ka ta rufe min idanu..... Umar wllhi na hak'ura da kai duniya da lahira, snn bazan gushe ba ina maka addu'an Allah Ya sassauta maka ya shirya ka hanya madaidaiciya snn shikan da ka min yafi komai faranta mun rai at least nasan na rabu da kai har abada....
"Abu na k'arshe shine ka sani Innah ta tafi, ta tafi gidan ta na gaskiya, a ranar da aka kama ka a ranar Allah Ya d'auki abinsa,.... Kuka ya kufce mata sanda taci gaba da fad'in" Ta tafi da bak'in cikin ka...... Ta k'arashe maganar tana mai toshe baki had'i da kuka lokaci guda zuciyar ta Ya shiga tashi... Cikin sauri ta mike ta bar wajen, ta barsa tamkar an dasa dutse...
"Innah... Innar sa.... Wani irin k'ara ya Saki yana kama kansa da dukka hannayen sa biyu yana wani irin kuka had'i da durk'ushewa k'asa, zuciyar sa cike da kaico da tarin nadamar da bata da amfani..
"Tana fitowa ta ringa k'waza amai kaman zata amayar harda kayan cikin ta, a tamanin Imam yayo kanta yana mata sannu hankali tashe.....
*************
"Suna isowa gida suka tarar da wani sabon tashin hankali, Hon. Gali ya turo sai fatalin da kayan gidan ake su Mummy da Mamy na tsaye a gefe suna sharb'an kuka....
"Alh Kasim na fitowa ya cire babban rigar sa yayi jifa da shi yayi kan masu firfito da kayyayakin yana fad'in" K'arya kuke, wllhi wllhi bazai yuwu ba... Juyawan da zaiyi ya hangi parking lots d'insa babu ko mota k'wara sunce d'auke ni....
"Dafe k'irjinsa dake masa zogi yayi yana layi shi kad'ai yana fad'in" Babu.. Babu.... Haj Farha ta k'araso a guje ta rik'e sa tana fad'in" Daddy meke faruwa, waye babu, wani abin ne ya sami Salim, ina Salim d'ina, kunyi waya ya sanar da kai yanda yake..... "Bata kai aya ba Alh Kasim ya shak'e mata wuya yana fad'in" Babu abinda ya sami precious little boy d'inki but it happens to me.... I'm completely ruined... Hajiya Farha sai k'ak'ari take saida Barr ya b'anb'are Alh Kasim Mamy ta taimaka ta janye Mummy..
"Kuka shar shar Alh Kasim yake da idanun sa yana fad'in" Duk 'ya'yan ku ne suka jawo min, shegu tsinannun yara, basu anfane ni da komai ba sai tsiya... Ya k'arashe yana dafe da k'irjinsa kan kace Me ya zube a k'asa hannayen sa biyu dafe da k'irjin sa...
*Toh fah readers the Dasuki's are going down... Ku agaza ma Alh Kasim da addu'a kar ya margaya.... 😨 lol.....*