"Gudu gudu sauri sauri Ummi ta nufi sashenta, Uwar d'aki ta shige ta zube saman gado tana maida numfashi da k'yar.. Abubuwan da suka faru shekaru ishirin da d'oriya baya suka shiga dawo mata.... Lamid'o Modibbo, Lamid'o na raye..... Girgiza kai ta soma ita kad'ai ta soma sunbatu... " Kai dukda nasan nice na hana a k'ashesa amma an tabbatar min Lamid'o bazai tab'a dawowa ba, in fact yayi nisa da masarautar nan..... " A haka Jakadiya ta iso cikin sauri ta tadda Ummi....
"Cike da rusunawa Jakadiya take fad'in" Allah Ya taimake ki da fatan lafiya na tadda ki..
"Ummi jiki na rawa take girgiza kai tana furta " Jakadiya ina so na had'u da yaya Ciroma duk yanda za'ayi....
"Jakadiya ta zaro ido waje don kuwa ba komai ne ya fad'o mata ba illa bak'in aikin da suka aikata shekarun baya......"Ummi ta katse mata tunanin cikin daka tsawa.... "
"Da sauri Jakadiya ta saita kanta kafin tayi saurin rusunawa tana fad'in" Tuba nake Allah Ya taimake ki, zan tafi yanzun nan babu b'ata lokaci..... Daga haka ta nufi k'ofa har tana tuntub'e.... Doka mata kira Ummi ta kuma yi wanda yasata dawowa babu shiri ta zube saman tiles...
"Zagaya d'akin Ummi take tana huci, komai na shirin rincab'e mata a lokacin da take cikin tsananin farin ciki na aurar da d'iyarta... Kai dole tasan yanda zatayi ta hana Lamid'o dawowa rayuwarta, dole Ciroma yasan yanda zaiyi su b'atar da wann zance idan ba haka ba kuwa wllhi wllhi Zahida bazata auri Khalifa ba......
"Sunkuyo da kai tayi tana duban jakadiya kafin tace " Jakadiya kin tabbata kin jefar da Lamid'o yanda babu wani d'an wann masarauta da zai tsince sa....
"Cikin Jakadiya yabada wani irin k'ugi.... Tambayarki nake " Ummi ta kuma daka mata wata tsawan...
"Jakadiya ta shiga gyad'a Kai tana fad'in" Allah Ya taimakeki na rantse da girman zati nayi yanda kika umarce ni, da hannaye na jefar da Lamid'o gaba jeji baya jeji, dajin da idan kuraye da zakanya basu cinyesa ba toh kuwa tabbas saidai fulanin daji masu kiwo su tsince sa.....
"Ummi ta goge gumin da ya keto mata kafin tace " Jakadiya Lamid'o yana gap da dawowa wann masarauta, Jakadiya bansan yaya zanyi ba muddin asiri na ya tonu..... " Jakadiya ta mik'e da sauri ta tallafi uwar gijiyan nata ta zaunar ta saman gado tana mata kalamai masu taushi duka tashin hankalin data tsinta kanta ciki, don kuwa tasan tabbas k'wai ta fashe za"a yanke mata hukunci mafi tsauri ita kuwa Fulani Kilishi iyakaci a maidata masarautar su da takardan saki.....
"Takarda da alk'alami Ummi ta d'auka tayi rubutu kafin ta aiki Jakadiya ta isar da sak'on zuwa hannun Baba Ciroma tunda shine silan komai.....
**************
"Dr Madi ya girgiza da ganin yanayin Mai Martaba... "K'irjinsa ya rik'e ba tareda ya iya furta komai ba.... " Sai yanzu yake ganin kuskurensa na sanar da Mai Martaba wann batu despite his health condition, ba son ransa bane he just couldn't help it ne shi kansa..... " Zubewa a k'asa Mai Martaba yayi yana rik'e da k'irjinsa....
"Cikin tsananin tashin hankali Dr Madi ya shiga k'ok'arin ceto rayuwar Mai Martaba in any way possible..... Waya yayi asibiti ba tareda b'ata lokaci ba, ....." Yana cikin danna k'irjinsa Baba Ciroma da Kahlifah suka shigo.... "Cakumo Dr Madi Baba Ciroma yayi yana fad'in" Me ka masa me kayima d'an uwana, if anything bad happens to him I'll have you arrested..... "Jakadiya dake daga waje ta jiyo maganganun Baba Ciroma a tamanin ta nufi sashen Ummi ta sanar da ita, babu shiri Ummi ta fito cikin tsananin tashin hankali.....
**************
"Tunda suka shiga motar ya kunna Ac d'in motar take numfashin Jalal yaji yana tafiya shi kuwa Umar already hancinsa da bakinsa a rufe suke... Jim kad'an Jalal ya rasa a yanda yake.... " Gudu kawai Umar ke faman falfalwa bisa kwalta.....
"A hankali ya soma tari yana yunk'urin bud'e idanunsa.... " Zabura yayi zai mik'e yajisa a d'aure gamgam jikin kujera, tundaga hannayen sa har zuwa k'afafunsa a d'aure suke, snn anyi sealing bakinsa da k'atuwar sellotape....
"Kallo ya shiga k'are ma wajen da idanunsa, kangon waje ne snn da alama cikin daji ne, don baka jiyo komai sai sautin kukan tsuntsaye..... Ya jima a haka kafin Ogan ya shigo cikin tafiya ta k'asaita, hannunsa rik'e da kwalban wine sai tangad'i yake tamkar zai kifa k'asa..... " Banda wani irin mugun kallo da Jalal ke watsa masa baya komai, baki a rufe babu halin magana. ...
"K'arasowa Umar yayi gaban Jalal yana k'are masa kallo kafin ya fashe da wata irin dariya yana nuna sa da kwalban wine d'in yake dariya kaman tababb'e.... Lokaci guda ya daina dariya fuskar sa ta koma tamau babu d'igon annuri balle imani..
"Hannu yasa ya dafi kafad'un Jalal cikin muryar maye ya soma fad'in" Jalal the Hero... Let's see if you can protect your wife again..... Opss na mance " She's never yours and she's never going to be yours.... Zaka rabu da ita a yau d'in nan like it or not Buddy...... "
"Zabura Jalal yayi yana yunk'urin yin magana, babu hali, gaba d'aya jijiyo jikinsa sun tattashi... Huci kawai yake yana watsa wa Umar kallon tsana......
"Dariya Umar Ya kuma fashewa dashi kafin ya ciro wayarsa ya shiga video d'in Jalal yana fad'in" You know you look good here, this is exactly where you belongs...... Oya d'ago kanka da kyau so that na nuna ma matarka kafin na kashe ka..... "Ya kuma fashewa da dariya kafin ya shiga juye ma Jalal wine d'in a jikinsa yana fad'in" Nasan kayi missing d'insa coz yanzu ka daina sha, kar ka damu I've alot here, I'll bury you with 10 bottles kaje can kayita sha..... Ya k'arashe yana wata muguwar dariya.....
"Saida ya gama yima Jalal wulak'anci iri da kala kafin ya jawo kujera ya zauna gaban Jalal suna facing juna "
"Bayan wucewar wasu dak'ik'ai Umar Ya soma fad'in" It will be very simple if you cooperate, abu d'aya zakayi and you'll be set free.... So your time starts now.... Ya k'arashe yana duba agogon hannunsa kafin yasa hannu ya d'aye selotape d'in dake manne a bakin Jalal....
**************
"Alluran bacci Dr Madi dole yayi ma Mai Martaba kafin ya shiga basu hak'uri yana fad'in" Su kwantar da hankalin su idan Allah yaso babu abunda zai faru, da zaran ya sami bacci ya farka shiknn...... Yana cikin bayani wayar Shattima ya shigo masa...
"Gani sukayi ya mik'e cikin tsananin tashin hankali sanda yake amsa wayar, a daburce ya furta " Jalal ya b'ace, innalillahi wa Inna'ilahirraji'un... Ganin nan zuwa, I'll be there right away..... Katse wayan yayi ya shiga bama su Ummi hak'uri yana fad'in" Suyi hak'uri but he really needs to go, don an nemi patient d'insa an rasa.... Daga Ummi har Baba Ciroma hakan ba k'aramin dad'i yayi masu ba, don kuwa yanzu zasu san makomar data dace da Mai Martaba.....
"Cikin tsananin tashin hankali Dr Madi ya iso asibitin, dole ma ya shiga damuwa don kuwa shine za'a tuhuma muddin aka rasa Jalal...
"Tun daga k'ofar ward d'in ya hangi cuncirindon securities, hankali tashe ya paka motar sa ya fito... Shattima kuwa yana ganinsa ya mik'e ya nufi Dr Madi yana fad'in" Dr I couldn't reach his phone.. Lambar sa baya zuwa... Hannun Shattima Dr Madi ya rik'e suka nufi cikin Ward d'in.......
************
"Huci kawai Jalal keyi yana watsa wa Umar mugun kallo kafin yace " You're insane, a delusional..... "Naushin bakinsa Umar yayi saida tayi jini kafin ya soma fad'in" On the contrary idiot..... " Bari kaji na fad'a maka " Zubaidah is mine, mine alone, dole ka rabu da ita for good coz she still loves me snn duk duniyar nan babu wanda ya dace da ita saini....... "Shut up Animal.... Jalal ya daka masa tsawa kafin yaci gaba da fad'in" Kar ka sake kiran mata ta da wann bakin naka.....
"Dariya Umar Ya fashe dashi kafin yace" Kaman yanda na fad'a maka Hero cikin uku za'ayi d'aya... " Is either ka saki Zubaidah for good, I mean Saki uku na har abada, ko kuma na kashe ka na d'auketa mu gudu na kasance tare da ita for the rest of our life ko kuma na kasheta da ni da kai duka mu rasa, nasan sai yafi maka k'unci ganin gawarta fiye da komai........ Wani kukan kura Jalal keyi yana jijjiga d'aurin da aka masa yake fad'in" I'll kill you... You imbecile.......
"Dariya Umar Ya fashe dashi kafin yace " Sati guda cif kake dashi, idan ka saki Zubaidah before then zaka tafi a raye, idan baka saketa ba zan kasheta ranar da za'a shiga kotu....Huci kawai Jalal keyi ba tareda ya iya furta komai ba.. .
**********
"CCTV Cameras suka soma kallo daki daki na cikin asibitin.... Tun daga shigowar Umar har ficewar da sukayi shida Jalal, tabbas ba forcin d'insa yayi ba, da kansa ya shige mota suka fice... Shattima ya sauk'ar da nannauyan ajiyan zuciya kafin ya shiga neman layin Jalal.....
"D'aukar wayar Umar yayi yana k'are ma screen d'in kallo kafin ya d'ago ya kalli Jalal bindiga Ya ciro cikin aljihunsa ya manna wayar a kunnen Jalal gefe d'aya kuma ya danna masa bakin bindiga akai yace " Oya do as I say if not I'll kill you.....
"Zuciyar sa ta shiga masa zafi, he has no choice, dole yayi abinda Umar Ya umarce sa coz Zubaidah still needs him.......
**************
"Pir pir Ummi tak'i aminta da shawarin Baba Ciroma cewa lallai saidai a danne kan Mai Martaba da pillow a k'arasa sa... Suna a cikin haka Zahidah ta shigo cikin kuka ta fad'a kan Mahaifinta..... "Har wuya takaici ya cika Baba Ciroma.....
*************
"Yau kusan kwana uku knn take tashi da matsanancin zazzab'i da ciwon kai had'i da jin nausea, gaba d'aya bata a hayyacin ta, ga takunkumi da shear holders na Marafah Construction suka saka masu ita da Mumsy d'inta, duk wasu savings d'insu dasuke bankuna sun k'ararsa wajen biyan shear holders d'in da suka k'i aminta, wasu kuwa cewa suke a raba asara, basuda komai bayan gidan su da suka mallaka...
"Mumsy da Asmah jigum sukayi suna kallonta har ta gama aman da take... " A hankali Mumsy ta k'arasa ta rik'eta kafin ta fito da ita daga bathroom d'in, mazauni ta mata saman gado tana k'are mata kallo, Asmah ta mik'o mata glass of water tanai mata sannu.....
"Tabbas ko ba'a fad'a ba Kausar juna biyu ke gareta... Innalillahi wa inna ilahirraji'un Mumsy take karantowa lokaci guda hawaye ya wanke mata fuska...
"Tsuru sukayi suna kallonta daga Kausar d'in har Asmah....
Sameena ce 👌🏾
[1/23, 22:27] +234 803 619 0581: 🌘🌘🌘🌘 *ZUBAIDAH*
71
*©Sameena Aleeyou...✍🏾*
_🌈KAINUWA WRITERS ASSO🤝_
*Dedicated To All Victims Of Rape...*
*For Those Who Criticize 😻*
"Da gudu Kausar ta kuma komawa bathroom ta shiga k'waza wani aman...
"Asmah zama tayi gefen Mumsy ta rik'o hannayen ta kafin ta soma magana cikin sigan lallashi..
"Mumsy pls why those tears, Mumsy idan kina kuka mu kuma me zamuyi, pls Mumsy you need to remain steady for us nida Kausar, especially Kausar now that she's sick... I know you going trough a difficult time and it breaks our heart seeing you suffering ... But Allah bai mance damu ba , I believed everything is happening for a reason, Allah bawai yak'i mu bane yake jarabtar mu haka... I'm quite sure idan mukayi hak'uri muka rungumi k'addara zamu ga alfanunsa a gaba domin Allah yana son masu hak'uri snn yana tareda su.....
"Hannun Asmah ta kama suka fice daga d'akin zuwa wani d'akin....
"D'agowa Mumsy tayi tana kallon Asmah kafin ta share hawayen ta tace " Asma'u bansan kukan me nake d'aya ba, na farin ciki ne ko kuwa na bak'in ciki ne.. For all our lives we've been dreaming to have a grandchild, nida Pappy, ... How I wish he's still here... I wish zaiga wann rana his little Angel is carrying a baby in her womb...." Asmah dai kallon Mumsy kawai take ba tareda ta fahimci zancen nata ba...
"Mumsy ta d'an murmusa kafin tace " Bansan makoman farin ciki na ba Asmah, bansan yaya Kausar zata karb'i abinda ke cikinta ba, I don't know how she would react when she finds out that she's pregnant..... " And I worried so much about my unborn grandchild, ina addu'a Allah yasa lokacin da zaizo duniya thinks will change to better...
"Sai yanzu ta gane me Mumsy take nufi.. Tabbas Kausar nada juna biyu, hawaye Asmah ma ta soma yi don kuwa tabbas akwai babban k'alubale a gabansu muddin Kausar ta fahimci hakan....
**************
"Ida wayarsu da Shattima keda wuya wayar Annah ya shigo... "Umar Ya kuma kallan screen d'in kafin ya dubi Jalal dake faman huci kurum yana watsa masa mugun kallo....
"Manna bakin bindiga Ya kuma yi a saitin goshin Jalal kafin yace " Repeat what you just said to that idiot friend of yours.... Yana gama fad'in haka yayi picking call d'in gamida sakawa a speaker...
"Idanun Jalal sunyi jazir tamkar garwashin wuta so as his flesh... Hararan Umar kurum yake yanaji kaman yayi tsalle Ya shak'e sa.
"Assalamu alaikum....Hello, hello... Jalal can you hear me.... Annah tace.
"A hankali Jalal ya amsa ta, sauk'e ajiyan zuciya tayi kafin ta soma fad'in" Son are you sure you're fine, Shattima ya kiramu a while ago yana fad'a mana you disappeared from the hospital, meke faruwa..???
"Saida Ya watsa wa Umar wata muguwar kallo kafin yace " Annah just don't worry about me okay, kici gaba da kula min da Zubaidah.... Na tafi neman wancan Dr d'in ne sabida ranar Trial d'in dad'a matsowa yake, tell Ansar he shouldn't worry either... Ku kwantar da hankalinku I'm perfectly fine. ...
"Sauk'e ajiyan zuciya tayi ta Kalli Zubaidah da tayi jigum tana kallonta a hankali tace " But why did leave ba tareda Dr ya sallame ka ba, you know that was wrong, zaka saka sa cikin damuwa koma ya rasa aikinsa..
"A hankalki yace " We've already talked about that with Shattima... " Annah I'm sorry but I don't wanna let Zubaidah down in the forthcoming trial... Ki fad'a mata ina mata murnan k'are jarabawa lafiya...
"Muryar Zubaidah suka ji na fitowa daga speaker d'in " Hello Ya Jay.... Ta fad'i cikin sassayan murya, Daga Jalal d'in har Umar saida suka sami fad'uwar gaba..
"Zubaidah taci gaba da fad'in" Pls come home kaji, don't get your self into trouble, bakada k'oshin lafia, pls ka dawo gida Ya Ansar is doing all his best yaga munyi nasara, you don't need to worry, all I want is for you to come home.... Ta d'an sassauta voice d'in nata kafin taci gaba da fad'in" I.... I missed you. We all missed you, Dan Allah ka dawo kaji Ya Jay.. .
"K'iris ne ya rage zuciyar Umar bata tarwatse ba sabida wani irin zogi da bugu da take yi....."Muryar Jalal ya sinkayo yana fad'in"
"Ki kwantar da hankalin ki baby I'll soon comeback kinji, bazan barki ke kad'ai on your own ba that very day (the trial day) I'll insha Allah make it.... Just take care of yourself and my Annah... A hankali cikin wani irin siga ya furta " I love you Zubaidah...... "D'ifffff Umar Ya katse wayar yana wani irin huci.... Wata wawan naushi yakai ma Jalal a hanci kafin ya kamo k'asar hab'ansa yana fad'in" You miserable jerk k'arya kake baka sonta, da kana sonta you shouldn't have let those idiots friends of yours raped her.... You were there and couldn't stop them because you are nothing but a coward..... " Muryarsa ya soma rawa hawaye suka ciko idanunsa yaci gaba da fad'in" Everything was perfect, our lives was amazing even though we were poor... Why why ..... Why did you have to show up in our livesssssss.. Whyyyyy...!!! Ya k'arashe yana matse k'asan bakin Jalal da iyaka k'arfinsa.....
"Da k'arfin gaske Jalal ya fincike fuskar sa yana wani irin turiri da huci yake fad'in" Yessss I admit I was a coward back then, I couldn't protect her..... And until now I still can't forgive my self.....
"What about you, what did you do to save her back then.... Me kayi tell me.. You judged her by people's scandals... You didn't give her chance to explain... Do you have any idea how she overcome this horrible experience...??? Huh fad'a mun.... Baka sani ba, all you know shine "Cin amana, yaudara, k'arya da son abun duniya.... You never loved her, She doesn't deserve you.... She deserves someone with dignity ba irinka ba karen farautar Kasim Dasuki.....
." How dare you...... "Umar Ya katse zancen ta hanyar kai naushi ma Jalal a bakinsa.... Jini ya soma zuba..... "Dukan cikin Jalal ya shiga yi da iyaka k'arfinsa hawayen taurin zuciya da k'unci na zuba a idanunsa....
*****************
"Shattima ya dubi Dr Madi da yayi d'an jim kafin yaci gaba da fad'in" Dr bansan wani irin farin ciki nake ciki ba, my whole life fatana shine Abba ya sami long lost Son d'insa..... I'm I'm just extremely happy Doc... " You know I always have that feeling, ever since I saw that Mark a jikin Jalal, but banida k'wakk'waran dalilin da zaisa nace Jalal shine Lamid'o coz yanada nasa family d'in, if to say a street ko a gidan marayu nasan sa toh shakka babu zance shine Modibbo, amma yanzu da ka tabbatar mana haka tabbas na yarda, snn duk yanda akayi akwai babban al'amari a tattare da b'acewar sa....
"Dr Madi ya jinjina kai yana murmushi kafin yace " Wann haka ne Shattima, mu k'arasa don nasan by this time ko Mai Martaba bai farka ba yayi kusan farkawa....
"Motar Dr Madi suka nufa Shattima na fad'in" Jalal is desperate to catch that incompetent Dr.... Yana son Matar sa with all of his heart.... He's so dedicated, Abbah zaiji dad'in samun d'a kaman Jalal....
"Dr Madi ya murmusa sanda ya karya kan mota suka fice daga asibitin kafin yace " Haka ne Shattima, duk burin uba ya sami d'a na gari.....
"Shattima ya kuma murmusawa kafin yace " Jalal couldn't give me a chance to break this news.....
"D'an kallonsa Dr Madi yayi kafin yayi murmushi yace " Fad'a masa wann labari could be heart broken, tunda bamusan wani labari uwar goyon nasa ta basa ba game da kansa.... Snn wann magana ne dake buk'atar nutsuwa kuma ba a waya ba, in person ya kamata...
"Shattima ya d'anyi jim gamida jinjina kansa kafin wasu tunani suka shiga ziyartan kwanyar sa, " Could Annah be a kidnapper..?? Kai she's just an amazing and an incredible mother to Jalal.... Kai there must be something behind this...... Da wann tunane tunane suka isa Castle d'in Mai Martaba.....
"Ummi na zaune daga chan gefe sai k'ullawa take tana warwarewa, Baba Ciroma ma gefe guda yake sai gumi dake karyo masa, tabbas shigowar Zahidah tai masa cikas da yanzu ya aika da k'aninsa lahira ya gaji abinda ya jima yana Mafarkin samu sarautar Mahaifin sa.... Can gefe ma Khalifa ne ya k'urawa Zahida idanu kaman ya had'iye ta, zancen ya kuma fad'o masa wai an sami Modibbo Lamid'o shiknn mafarkinsa na zama Yarima zai tashi a aiki, shiknn komai ka iya faruwa... Toh shin dama Modibbo ba mutuwa bane yayi tareda uwar sa.... " Sauk'e nannauyan ajiyan zuciya yayi don kuwa babu mai amsa masa wad'an nan tambayoyi nasa...
"Ciroma ya kuma kallan Zahida yana so ya kawar da ita daga parlorn ya cimma burinsa amma da alama Zahida bazata iya fita ta bar mahaifinta a halin da yake ciki a yanzu ba.... Dabara ta fad'o wa Baba Ciroma, k'arsawa yayi ya dafah kafad'an Zahidah yana lallashinta da kalamai masu taushi ya buk'aci ta koma cikin gida komai zai zama normal da izinin Allah, Mai Martaba zai sami lafiya....
"Bata iya furta komai ba sai faman share hawayenta da take yi.... Baba Ciroma ya dubi Khalifa yace " Baffah tashi ka rakata koh, maza ka kula da ita, snn kar ku bari Madaki ta sami wann labari....
"Jiki a sanyaye ta mik'e saiji tayi Mai Martaba ya rik'o hannunta..... Gaban Ummi yayi wani irin mugun fad'uwa... Baba ciroma kam k'iris ya rage bai Saki fitsari ba..... Hakan yayi daidai da shigowar Shattima da Dr Madi....
Sameena ce 👌🏾
[1/23, 22:27] +234 803 619 0581: 🌘🌘🌘🌘 *ZUBAIDAH*
72
*©Sameena Aleeyou...✍🏾*
_🌈KAINUWA WRITERS ASSO🤝_
*Dedicated To All Victims Of Rape...*
"Zahidah ta koma ta durk'usa jikin tumtum d'in da mahaifin ta ke kai.... Tana murmushi tana hawaye take fad'in " Abbah ka tashi, Alhamdulillah.... " Ta k'arashe tana rungume mahaifinta...
"Hannunta ya kama kafin yace " Fatimah Allah Ya tayar dani don na sake ganin d'an uwan ki... D'an uwanki yana raye snn yana kusa damu...
"Zahidah dai sam jin kalaman mai martaba tayi wani iri, ko kusa bata fahimci ina ya dosa ba, tabbas tasan maganganun nasa yana da alak'a da Hamman ta Lamid'o ... "Girgjza kai ta soma tana tunanin shiknn kwanyar mahaifinta ya tab'u....
"Idon Mai Martaba ya sauk'a kan Shattima da Dr Madi da suka rusunar da kawunan su baki d'aya.... Mik'ewa yayi sosai ya zauna kafin ya soma fad'in" Abdullah kun taho min da Modibbo ko, ina yake, ku nuna min shi..... "Hawayen da Shattima yake rik'ewa ya kasa resisting d'insu.... Kuka ya fashe dashi lokaci guda ya tafi ya rungume Mai Martaba yana fad'in" Abba da gaske ne, da gaske ne, Jalal shine Lamid'o Abba your long lost son is alive.... I'm sorry for not telling you tuntuni.... Ka yafe min Abbah but bansan yaya abun zata kasance ba, bansan gaskiyar Al'amarin ba, bansan komai akai ba Abba... Jalal da Annahn sa su kad'ai zasu iya fayyace mana komai.....
"Duk k'arfin hali irin na Mai Martaba saida jikinsa ya karaya, babu abinda yake so tamkar ya saka d'ansa a idanunsa...
"Zahidah da mamaki da tsoro ya cika ta kasa furta komai tayi sai kallon datake kan faman bin mahaifinta da Shattima dashi...
"Khalifa kuwa ji yake tamkar ya shak'e Shattima sabida wani bala'in haushin Shattima dake cinsa....
"Ummi kuwa gaba d'aya neman hanya ficewa take daga parlorn don gaba d'aya batama gane meke faruwa..
"Zururu Baba Ciroma yayi da idanu ba tareda ya iya furta komai ba....
"Mai Martaba ya rik'e hannayen Shattima yana murmushi Mai cike da Charisma da tarin farin ciki kafin yace " Ubangiji yayi maka albarka Abdullah, koda ace bani na haifeka ba Kai d'a mafi soyuwa ne a gareni..
"Ka sadaukar da lokutan ka masu amfani don duk wani hidimar da na umarce ka, snn a dalilin ka Modibbo ya dawo garemu, Nan duniya banida abinda zan iya biyanka... Na ajiye maganar sarauta a gefe, ina maka magana ne a siga ta D'AN ADAM na gode na gode Abdullah....
"Cikin sauri Shattima ya katse sa ta hanyar girgiza kai yana fad'in" Abbah don Allah kayi shiru, zan jima ina jin zafin godiyar da kake min, don Allah Abbah ka daina.....
"Murmushi take tana hawaye kafin tace " Ya Shattima da gaske zan ga Hamma na, finally our family will be reunited again... Ina yake, ka kaini wajen sa pls dan Allah ka kaini.. I can't to meet him.... "Kallon soyayya kurum suke aika ma juna daga Shattiman har Zahidar....
"Cikin ransa ya furta " Damn it, I can't take, I just can't... You really crossing the line Shattima.... "Ba tareda fahimtar kowa ba ya mik'e ya fice daga tampatsetsen parlon... "Mahaifinsa ne kurum ya lura da hakan, baibi ta kansa ba donmin kuwa shima tasa yake nema ta ficcesa a wann situation d'in....
"Ummi dai yak'e ta soma tana karanto godiya ga ubangiji, sai ka rantse har cikin ranta farin ciki take....
"Daga ita Ummin har Baba Ciroma farin cikin su suka shiga nunawa tsantsa...
"Mai Martaba ya dubi Dr Madi kafin yace " Likita ai sai a sallamo min d'ana na gansa ko kuma ni naje da kaina na gansa....
"Daga Shattima har Dr Madi saida cikinsu yabada wani sauti, don basu san me zasu cewa Mai Martaba ba tunda bashida masaniya akan komai, rayuwar Jalal is different, he's dealing with alot....
"Murya na d'an rawa Dr Madi ya kuma rusunawa kafin yace " Allah Ya taimake ka.... Dama shirin sallaman nasa ake.... Toh saidai.... Saidai.... Gaba d'aya suka kafe Dr Madi da idanu.. Ummi da Baba Ciroma kuwa addu'a kurum suke cikin ransu Allah yasa ma mutuwa yayi kowa ya huta, basu gansa ba balle hankulan su ya tashi....
"Take annurin fuskar Mai Martaba ya d'auke cak, ya koma asalin sarkin sa Mai cike da madafen iko.... Jira kurum yake yaji me Dr Madi zai fad'i...
"Zahida kuwa mik'ewa tayi cikeda d'oki take fad'in" Nice zan fara sanar da Madaki wann babban Albishir, cikin sauri ta fice tana tattare alkyabban ta....
"Ganin haka yasa Shattima d'anyin gyaran Murya kafin yace " Abbah dama akwai d'an abinda ya kamata ka sani gameda Jalal...
"Mai Martaba ya jinjina kai yana duban Shattima kafin yace " Abdullah fad'i ko menene, ko menene Modibbo yake so ayi za'ayi sa da izinin Allah.. Idan gadon mulkin yake so, yanzun nan zan sauk'a na damk'a masa wann masarauta, Amma kar yace bazai dawo garemu ba....
"Shattima ya d'anyi murmushi k'arfin hali kafin yace " Allah Ya tainakeka Abbah, ko kusa ba haka bane, Jalal ba irin wad'an nan mutanen bane.... Jin Shattima ya d'anyi shiru yasa Dr Madi rusunawa kafin yace " Allah Ya baka nasara zan koma bakin aiki idan ka min izini.....
"Mai Martaba ya jinjina kai, cikin sauri Baba Ciroma yace " Ba a maka izinin tafiya ba likita bokan turai, dole ka fayyace mana ina d'anmu yake..???
"Kallon Ciroma Mai Martaba yayi kafin yace " Yaya mun masa izini....
"Har wuya Ciroma ya kawo don jira yake yaji Dr Madi yace " Lamid'o ya cika ne... "Godiya Dr Madi ya shiga yi cike da rusunawa har ya fice...
"Gaba d'aya sunyi nisa duniyar tunanin da suka tafi sai jiyo muryar Shattima sukayi sanda ya soma bawa Mai Martaba labarin tun farkon had'uwar sa da Jalal, da irin k'alubalen da shida family d'insa suke fuskanta a rayuwa.....
****************
"Annah why am I having this feeling... I don't know but Im so anxious.... Kaman wani abu zai same sa, what if he's hiding something from us, jiya jiya yace mana zai dawo gida right away da zaran an sallame sa, buuuttt.. Why the sudden change of mind..
"Annah ta d'an rik'o hannayen ta tace " Ki daina tunani haka daughter, besides kinsan halin Jalal da kafiya ma abu, he might be planning for this for a long time, nasan bazai k'yale maganar neman Dr d'in nan ba har sai ya cimma burinsa, he can do anything for you dear...
"A hankali Zubaidah ta gyad'a kanta kafin tace " I hope he'll be safe... I hope wata rana komai zai wuce ya zama tarihi....
"Rungumeta Annah tayi tana murmushi kafin tace " Soon darling, insha Allah komai yazo k'arshe....
"Hadiza dake mak'ale saman staircase tayi wani murmushi mugunta kafin tace a zuciyarta
_"Wahala bazai tab'a k'yaleki ba Zubaidah domin kuwa a cikinta aka haife ki, snn a cikinta kike rayuwa, zaki dawwama a cikin ta.... Ayi shari'ar mu gani...._ Daga haka ta kuma yin wata murmushi ta kuma yi ta juya ta nufi d'aki.....
*************
"Tofar da jinin dake bakinsa yayi kafin ya d'ago yana huci yake fad'in" No no ka gama duk abun da zakayi akaina you imbecile, but don't you dare go near my wife.... I swear if you dare hurt her I'll kill you.... Katakon hannunsa ya kuma buga wa Jalal a k'afafun sa kafin ya kuma ajjiye masa pen da paper saman cinyar sa dake d'aure gamgam da jikin kujera yace " Oya write, go ahead and sign the divorce...
"Kallon sa kawai Jalal keyi yana wani irin huci.....
"Ya kalli agogon hannunsa kafin ya sauk'a k'asan kangon yana amsa kira da wayar sa..... Bayan kaman wucewar wasu awanni ya dawo hannunsa d'auke da takarda nannad'e da snacks..
"Kujera ya janyo ya zauna gaban Jalal suna watsa ma juna mugun kallo kafin yace " Are you hungry Hero....??? Ya fad'i yana wata murmushi.... Tuntsurewa da dariya yayi kafin yace " Yeah why should I even asked, you must be starving... Ya shiga d'aura snacks d'in saman 'yar karyayyiyar kujerar data raba tsakanin su, ya warware takardan tsaf kafin ya soma ci yana fad'in" Let's eat Dude, go on have some.... Yana gyad'a kai yake fad'i..... "Dariya ya kuma fashewa dashi gamida sassauta murya yana fad'in" Oh I'm so sorry na mance ashe bazaka iya ba... Kana so na kira sweetheart d'inka so that she should feed you.... Opss this place is quite far for her..... Poor you..... " Okay okay fine if you want ni zan baka... Ya shiga tura masa cake a baki yana fad'in" Oya take it, open your mouth and eat...... Da k'arfin gaske yake danna cake d'in a bakin Jalal.....
"Fuzarwa Jalal yayi yana wani irin huci yake fad'in" You imbecile you'll pay dearly...... Tuntsirewa da dariya Umar yayi kafin ya sauk'a downstairs a tare suka hauro da wasu k'artai guda biyu.... Dubansu da kyau yayi kafin yace " Danny take care of this brat.... Make sure he's safe here, idan yunwa taci uwar sa Ya buk'aci abinci ku basa,...
"Danny ya gyad'a kai kafin yace "Yess Boss...
"Umar Ya sunkuyo daidai fuskar Jalal kafin ya soma fad'in" I brought you company Mr Hero, look ka gansu, zasu kula da kai sosai, saidai fah bazaka tab'a barin kujeran nan ba until you sign these papers... Ya d'ago takardan yana karkad'asu a fuskar Jalal... Dariya ya kuma fashewa dashi kafin yace " Enjoy your stay..... Daga haka ya nufi downstairs yana wata irin dariya.....
****************
*Prison*
" A zabure ya tashi daga mummunar mafarkin da yayi yana k'ara wanda yasa gaba d'aya sauran 'yan d'akin suka tashi...
"Labib ya k'arasa da sauri yana rik'e Tariq yana k'ok'arin calming nasa, kan su ankara sai ganin fitsari sukayi na tsoyayowa daga gadon Tariq.....
"'Yan d'akin kuwa me zasuyi banda dariya da shewa har saida ganduroba d'aya ya shigo ya daka masu tsawa....
"Labib ya jawo Tariq suka dawo gadon sa dukda fiffizgewa da Tariq d'in keyi.... Salim kuwa dafe kansa kurum yayi cikin wani irin yanayi.. Ya k'agu kwanaki hud'un nan su cika a gudanar da shari'a su fice daga wann kurkukun.....
Sameena ce 👌🏾
[1/23, 22:28] +234 803 619 0581: 🌘🌘🌘🌘 *ZUBAIDAH*
73
*©Sameena Aleeyou...✍🏾*
_🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝_
*Dedicated To All Victims Of Rape...*
*Where is she👀👀👀 My Fadindin Aka Fadila Talba 💋.... This one's hers.... Allah k'aro baseera darling aci gaba da suburbud'o mana RAYUWA TA 😻😍*
"Shiru Mai Martaba yayi yana jinjina labarin da Shattima ya basu... Tausayi da soyayyar d'ansa ya cika zuciyar sa..
"Ummi kanta saida ta tausaya ma Jalal, Baba Ciroma kuwa bai furta komai ba sai tunane tunanen da ya soma, neman hanyar da zai salwantar da Lamid'o ya shiga yi tunkan ya iso wann masarauta...
"Shattima yaci gaba da fad'in" Abba a gani na tunda shari'ar kwanaki ne ya rage ayisa, ina ganin idan mun bari an gama komai zaifi zuwa cikin sauk'i don na tabbata bazamu sami kan Jalal a yanzu ba, snn abubuwa zasu masa yawa... Abbah kuma idan son samu ne a b'oye samun Lamid'o har sai lokacin da zaizo masarautar nan sabida na tabbata wa'enda sukayi sanadiyar b'acewar sa muddin suka ji labarin an same sa zasu iya yin wani abin to stop him from coming back...
"Cikin Ummi ya d'uri ruwa ji take tamkar Shattima ya gane she's behind everything, gumi ya shiga keto mata dukda manya manya Air conditioner dasuke hurawa cikin parlorn...
"Baba Ciroma kuwa cikin ransa yayi murmushi yace " Kaman ka sani yaro.. A fili kuwa cewa yayi.. " Wann shawari taka tayi Shattima, haka kurum za'ayi don guje ma sharrin abokan gaba...
"Mai Martaba ya jinjina kai kafin yace " Haka ne....
"Shattima yayi godiya kafin ya rusunar da kai yana fad'in" Abbah idan anmin izini zan dakatar da Zahidah daga sanar da Madaki sabida idan ta sani yanzu zatayi ta saka damuwan son ganin sa a ranta...
"Jinjina Kai Mai Martaba yayi kafin yace " Kayi gaskiya Abdullah mun maka izini... Allah Ya albarkaci rayuwar ka.... Ya kuma rusunawa yana godiya kafin ya fice...
"Bayan Shattima ya fice "Mai Martaba ya dubi Ummi da Baba Ciroma kana yayi gyaran murya ya soma fad'in" Alhamdulillah dukan ku biyu kuna nan, zanyi amfani da wann damar na sanar daku mun d'aga bikin yaran nan Khalifa da Zahida har sai Al'amra sun daidai ta, Yaya sai a sanar dasu Waziri maganar d'aga auren....
"Baba Ciroma ya jinjina kai kafin yace " Hakan yayi...
"Ummi kuwa kasa cewa komai tayi don kuwa she's not there gaba d'aya...
"Kusan karo suka kusan Yi da juna.. Zata fad'i yayi saurin tallafo ta.... Sun jima suna kallon juna kafin Zahida tayi k'arfin halin k'wacan kanta.... "Da sauri Shattima ya saketa kafin yace " Oh I'm I'm sorry, I didn't know you were coming.....
"D'an gyara alkyabban ta tayi kafin tace " No no its okay.... Ta d'an sa kai zata wuce Shattima ya kuma shan gabanta...
"D'ago ido tayi tana dubansa, gani tayi he's looking so pale.... Da sauri ta d'auke idanunta had'i da kauda kai gefe....
"Murya can k'asan mak'oshi yace " Muna fad'a da juna har haka ne...?? Lately you were nice to me sabida an samu Hamman ki, and now ko gaisuwa bazan samu ba.?? Remember you still my little sis no matter what happens..
"Ya Shattim pls stop making this difficult, bana so azo pick d'in da I can't take it.... Pls kaji...
"Murmushi Shattima yayi kafin yace " It won't come to that pick... But you need to keep this in mind.... Seeing you happy makes me feel happy..... Snn ganin ki cikin akasin haka yana jefa ni cikin akasin farin ciki... Yanzu da nasan ganin Hamman ki zai saka ki cikin farin ciki I won't rest until I brought him here for you and your family.... Ya k'arashe yana murmushi mai bayyan hak'wara... "Murmushi Zahida ma tayi ba tareda ta furta komai ba, cikin zuciyarta kuwa tsantsan soyayyar sa ne.....
"Shattima ya katse shirun da fad'in" Da fatan baki sanar da Madaki batun ba..
"Girgiza masa kai tayi alamun a'a kafin tace " No na samu tana bacci...
"Shattima ya jinjina kai kana yace " Good, nan ya sanar da Zahida uzirin su na rashin sanar da Madaki yanzu, itama taji dad'in haka, daga nan tambayoyi ta shiga jero ma Shattima gameda yayan ta....
"Shattima ya murmusa kafin yace " I can see someone's curious.... Ya k'arashe teasingly...
"She chuckled sann ta d'an rufe fuskar ta da tafukan hannu kana tace " I just can't wait to meet him, kana da pics d'insa pls show me, I knw he's handsome.....
"Murmushi kawai Shattima yayi kafin yace " Kar ki damu soon zaki gansa.... "Ta murmusa tace I hope so...
"Har Zahida ta shige sashen su farin ciki take ji maras misaltuwa.....
"Daga yanda Khalifa ke tsaye ya hangi Shattima yanda ya raka Zahidah da kallon soyayya, fasa shigowa yayi ya juya, a fili yake furta " That idiot is really getting on my Freaking nerves.... I've do something tun wuri... Putting him in his place... Fadawa na gaishesa na masa gadabout kota kansu baibi ba yayi ficewar sa.
*****************
"What you're very stupid, what rubbish are you talking about.... " Jirgina yayi sinking.... No no this is ridiculous, ka fad'a min abinda hankali zai kama.......
"Dafe kansa yayi gamida zama gijif cikin kujera yana sunbatu shi kad'ai.....
"Barr Munir ne ya shigo da files a hannunsa yana tafe yana magana yana duba takardun... "Turus ya tsaya ganin Alh Kasim zube cikin kujera yana maganganu shi kad'ai...
"Barr ya dafa sa yace " Mr President lafiya... Are you okay, is everything alright..???
"Da k'arfin gaske Alh Kasim yace " No no... Nothing is alright,... Jirgina jirgina ta shak'o kayan over 1million Dollars wai Captain Bala yana ce min tayi sinking...... Can you just imagine.. " No no this is not going to happen,...... "Kamasa Barr Munir yayi ya zaunar sa yana k'ok'arin calming d'insa dukda shima ya jijjiga da jin batun....
"A zabure Alh Kasim ya mik'e ya nufo waje ba tareda sanin ina ya dosa ba, Barr ya take masa baya...
"A reception suka ga ana kallon News sai nuno labarin ake da sunan Company d'insu Dasuki Holding... Fuzar da iska kurum yayi ya karkata babban riga kafin ya fice...
***************
Yau ta kama sauran kwana guda tak a koma kotu, gaba d'aya hankalin Zubaidah ya gama tashi, hankakin ta sam bai kwanta ba da rashin dawowar Jalal, kowa ya ganta zai gane hakan, idan ta kira wayar sa baya shiga, saidai text da yake turo mata cewa yana lafiya ta kwantar da hankalin ta, abin har ya soma k'ona mata rai, itafah a halin yanzu ganinsa ya fiye mata shari'an dake gaban ta, meyasa Ya Jay yak'i fahimtar hakan.... Jin muryar Ansar da Annnah a downstairs yasata saurin zura hijabi ta sauk'a....
"Ya Ansar did he call you, Ya gaya maka ina yake ne...
"Daga Ansar d'in har Annah saida ta basu tausayi, Annah ta k'arasa ta rik'ota suka zauna saman sofa.
"Ansar ya d'an girgiza kai kafin yace " Bamuyi magana ba, but he texted me, I'm quite sure he won't stop har sai ya sami Dr d'in.... Ya jaddada min he'll make it to the trial... I knw Jalal he's gonna keep his word... Ki kwantar da hankalin ki Zubaidah... Jalal is doing all this for you...
"Yanzu ko Tariq baiyi confessing ba at least munada option b... Balle ma Tariq ya tabbatar min he'll confess everything, Zai fad'i iyakacin gaskiyar sa a gaban Alk'ali, da wad'an nan hujjoji masu k'arfi muke saka ran Allah zai bamu nasara ...
"Zaro ido Annah da Zubaidah sukayi cike da farin ciki suke hamdala, Annah ta rungume Zubaidah tana fad'in" This a great news.... Alhamdulillah.... Ansar Allah ne kurum zai biyaka ladan aikin ka..
"Zaro ido waje Hadiza tayi daga yanda take lab'e kafin tace "Aiko banci ta zama ba.... Ba tareda kowa ya lura da ita ba ta samu ta sulale ta fice daga gidan.....
***********
"Just how flipping damn stupid are you..?!!! Don't you gerrit, wuya tsanani matsi tak'ura bazasu tab'a sa na rabu da Zubaidah ba... You can keep me here for good, but I swear.... Na rantse da wanda ya halicce ni bazan saki Zubaidah ba, she's mine, tawa ce.... And the moment I step out of this damn chair..... Your hell will start right here on earth .... "
"Da k'arfin gaske Umar Ya matse bakinsa yana huci yake fad'in" Shut the fuck up you idiot.. You took away what is rightfully mine .... "If you fricking think you leaving this place alive kayi kuskure.... Coz this place is your hell..... Ya mik'e yana yarfe hannunsa kafin yace " Apparently the heroin is tomorrow right... Yayi wata murmushi kafin yace " I'll be there snn zan kawo maka ita nan na kashe ka in front of her..... And finally zamu kasance tare in our new world..... Ya k'arashe cikin tuntsurewa da dariya...
"Huci kawai Jalal keyi yana jijjiga kujeran yake fad'in" You're despicable, I swear to you I'll kill whoever messes with my Wife.....
"Kira Umar Ya shiga doka ma Danny.... Da sauri Danny ya hauro sama yana amsa kiran uban gidan san...
"Bindiga Umar Ya mik'a masa kafin yace " Make sure he didn't escape, if he tries to do anything stupid shoot him without thinking twice..... Daga haka ficewa yayi ko sauraren Danny bai tsaya yi ba....
"Sunajin yanda ya kwashi motar sa da bala'in gudu... Ni kuwa Samee nace _fast and furious, maza Allah hadaka da Paul Walker 😂_
***************
"Tunda ya fice su Danny suka sami sarari sukayita d'irkan giyan su kota kan Jalal basu bi ba...
"Shi kuwa Jalal d'an fashashen kwalban da ya samu yake kan faman yanka d'aurin da aka masa yake ta baya ba tareda sanin su ba... Gaba d'aya ya yayyanke hannunsa, dukda zogi da azaba da yake ji bai fasa ba, he really need to get out of this place before that idiot does something drastic to his wife.....
**************
"Kausar ta tsare Asmah da idanu har saida Asmah ta soma zargin anya wann kallo na lafiya..?
"Dafe kafad'un Kausar tayi kafin tace " Sistu jikin ne? Ko akwai abinda kike so ne...?
"Shiru Kausar ta mata ba tareda ta furta komai ba..
"Sauk'e ajiyan zuciya Asmah tayi kafin ta kwashi books d'inta ta nufi k'ofa tana fad'in "I'll be downstairs if you need anything... "Ji tayi Kausar ta rik'e hannunta guda. A hankali Asmah ta jiyo tana duban ta kafin tace " Sistu idan kina son wani ne pls tell me, ko wani abin ci kike kwadayi I'll prepare it for you right away....
"Murmushi Kausar tayi kafin tace "Really.... Okay fine na gode, amma ni yanzu tambayar ki zanyi.. Why are you hiding things from me now....
"Galala Asmah ta d'an kalleta kafin tace " Hiding things, com'on Kausar me zan b'oye maki.... I'm only worried about you ne.
"Of course you hiding something, keda Mumsy, you don't want me to find out.... "D'an girgiza kai Asmah tayi kafin tace " For crying out loud stop being so paranoid Kausar.... Kinga bakida k'oshin lafia ki kwanta, I'll prepare something delicious for you..
"I perfectly well know you Asmah, idan kina b'oye min wani abu na sani, idan akwai wanda yasanki better than I do toh Ansar ne... Amma tunda kince ba haka bane bara na fad'a maki abinda kuke b'oye min.. Baku so nasan I'm crying Salim's child ko ba haka bane....
"Gaban Asmah ya fad'i, ta d'ago tana duban Kausar... "Murmushi Kausar ta sakar mata kafin tace " Nasan I'm pregnant tun sanda na soma ciwon nan, and this is exactly 2mnths without me having my days... "So tell me what were you afraid of, huh..? Tsoro kuke kar na zubar da cikin ko me..??
"Asmah ta d'anyi shiru kafin tace " Kausar nasan halinki snn nasan right now you are so devastated ko baki nuna mana ba, we all knw how much you hate Salim and his family muddin kika san kinada ciki you might freak-out and komai ka iya faruwa... Amma na sha mamakin ganin kin sani bakiyi komai akai ba....
"Murmushi Kausar tayi kafin tace " No one can escape his destiny sistu.... Mu kuma kalan namu jarabawan knn, Salim ruins my life but that doesn't mean zan kashe abinda ke ciki na ko na k'yamci abinda ke ciki na bisa laifin mahaifin sa,, Zan so d'ana with all my heart, tasa bayan hannu tana share hawayen ta had'i da murmushi k'arfin hali kafin tace " Children are great treasure, they are blessing ... Muryar ta Ya soma rawa sanda taci gaba da fad'in" I'll give my child a different story, he must not know about his Dad, bazai san mahaifinsa na gidan yari ba da wann bak'in laifi da ya aikata.... Hawaye ya kufce mata sanda taci gaba da fad'in" Tell me Asmah am I making the right decision ... Ki fad'a mun 'yar uwa... "Rungumeta Asmah tayi kuka ya kufce mata ba tareda ta iya furta komai ba...
"Mumsy dake tsaye bakin k'ofa k'arasowa tayi ta had'asu duka biyu ta rungume tana fad'in" Alhamdulillah, Allah na gode maka daka blessing d'ina da 'ya'ayan albarka.... Allah Ya maku albarka sweethearts, always remember that I'm here for you kunji Angels...
"Suka d'ago suna kallon Mumsy had'i da share mata hawayen ta.. "Mumsy ta rik'e hannun Asmah tace " Koda bani na haifeki ba ina jinki tamkar 'yar dana haifa a ciki na, you've always been there for my family, I owed you alot my niece.... " Da sauri Asmah tasa hannu ta toshe bakin Mumsy tana girgiza kai take fad'in" Mumsy don't say those things pls kinji, haihuwata ne kurum bakiyi ba but you've done more than enough for me... Murmushi sukayi gaba d'aya kafin Mumsy ta kuma bud'e masu hannu tace oya family hug.... Gaba d'aya suka rungume juna fuskokin su d'auke da annuri...
************
"Alh Kasim ya bigi kujeran dake gaban sa da k'arfin gaske kafin ya dubi Barr yace get me Faisal.... Cikin sauri Barr ya matsa gefe ya shiga dialing lambar Faisal....
"Check d'in bogi ya kuma rubutawa ya mik'a ma Hadiza, ta washe baki tana murna... Daga nan ta mik'e ta fice cikin sauri gudu gudu, sai waige waige take kar a ganta...
"Alh Kasim ya kuma watsa wa Alh Maina wata uwar harara kafin yace " You better stop your Son, don wllhi kaji na rantse idan yayi confessing I'll ruin you just like I did to Tahir Marafa, shida yake da arziki balle kai...
"Alh Maina ya shiga girgiza kai yana tattare naman goshin sa yake fad'in" No no I can't lose my only son.... I need to stop him right away..
"Alh Kasim ya tab'e baki kafin yace " Da yafi maka, don wllhi d'ana Salim Ya tafi jell for years akan shi I'll make your life a living hell, .... Daga haka mik'ewa yayi ya fice suka had'u da Faisal a wani waiting....
"Kallon Faisal ido cikin ido yayi kafin yace " Gobe ne or never, idan ba'a gama shari'ar nan a gobe ba na baka go ahead ka kashe Attorney Kumo... Ka kashe sa har lahira...
"Ficewa yayi sabida wayan da aka masa yanada clients da zasu soma maganar sayan hannun jari don kuwa kampanin sa is going bankrupt.....
***********
"Cikin sa'a Allah Ya basa dama ya yanke igiyan dake d'aure da hannayen sa da k'yar... Cige baki yayi sabida zogi da hannayen sa ke masa, a hankali ya soma warware na k'afafun sa, har ya kwance su tsaf..... Sad'af sad'af ya mik'e yana d'ingisawa da k'yar....
Sameena ce 👌🏾
[1/23, 22:28] +234 803 619 0581: 🌘🌘🌘🌘 *ZUBAIDAH*
74
*©Sameena Aleeyou...✍🏾*
_🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝_
*Dedicated To All Victims Of Rape...*
"A hankali yake takawa lokaci guda yana d'an cije leb'e sabida zogi da rad'ad'i da wounds d'insa ke masa..
"Can ya hangi su Danny sai sharan bacci suke ga kwalaben barasa har kusan guda uku a gaban su.. "Jalal yaci gaba da sauk'owa daga benen cikin dabara . Danny ne ya d'anyi juyi yana sunbatu yana gyara zaman bindigar a saman k'irjinsa.
"Jalal yayi saurin durk'usawa ya b'oye jikin rub'ebb'iyar katon staircase d'in.. "Jin Danny yayi shiru yaci gaba da baccin sa yasa sa mik'ewa yaci gaba da sauk'owa cikin dabara..
"Ga sanyi da ya gauraye gari ga duhun dare ga rigar sa gaba d'aya jini ya b'ata, uwa uba bai san ina ne wajen ba.... "Cikin dabara ya k'arasa ya d'auki jacket d'in dake lank'aye jikin wata katako ya soma k'ok'arin barin wajen ganin d'aya gardin na mutsu mutsu alamun zai tashi...
"Da dabara da taimakon Allah Jalal ya samu ya fice daga wann kango na gini... Tafiya yake yana jan k'afarsa da k'yar ba tareda sanin ina ya dosa ba, don kuwa ga dukkan alamu wann gini a k'ungurumin daji yake, ko alamun kwalta bai hanga ba balle yayi tunanin ganin ginannakin mutane.
"Saida yayi tafiya mai nisa kafin ya zauna k'asar wata bishiya ya shiga treating wounds d'insa. Yage gefen hannun rigar sa yayi ya shiga d'aure yanda jini ke zuba. Ya d'ago jacket d'in da yana dubawa ko Allah zaisa ya sami waya a cikin ta...
"Fuzar da iska yayi gamida dafe kansa ganin babu waya a ciki saiko wata garin hoda.. Sosai yaji takaicin hakan, saidai ganin damuwa bazata ficce sa ba yasa sa mik'ewa ya gabatar da taimama kafin ya soma sallah....
*************
"Firgit ta farka daga mummunar mafarkin da tayi tana mai ambaton Allah.
"Ta jawo igiyan wutan side lamp ta kunna kafin ta jawo wayar ta dake gefe da lamp d'in ta danna don duba lokaci.
"K'arfe 2 da wasu mintoci agogon wayar nata ya nuna..... "Sauk'e nannauyan ajiyan zuciya tayi kafin ta karanto addu'a ta shafa... Ta jima tana zaune saman gadon tayi jigum zuciyar ta naci gaba da yankewa.... "Da sauri ta soma girgiza kai tana fad'in" It's only a dream, My Ya Jay na lafiya, babu abinda zai samesa da izinin Allah.. Domin kawar ma kanta tunanin mik'ewa tayi ta nufi bathroom ta d'auro alwala ta tada sallah... Haka ta ringa nafilfili tana kai kukan ta wajen Rabbil Izza...
"Ba ita ta koma bacci ba sai wajajen uku da rabi na talatainin dare... Da asubahi kuwa har kusan makara tayi don saida Annah ta lek'o ta tasheta don gaba d'aya ba wani samun nitsettsen bacci tayi ba...
"Gaba d'aya jikinta ya gama sanewa tun kan su tafi kotun. Bata da burin da ya wuce tayi tozali da Jalal...
**************
*National High Court Abuja*
"Tun daga waje zai tabbatar maka babban shari'a za'a gudanar.
"Motar prison ta paka nan aka soma fito dasu hannayen su rufe cikin handcuffs.. Su Mummy Mamy da kuma Mum d'in Tariq gaba d'aya suka nufi 'ya'yan nasu suna masu fashewa da kuka ganin yanda suka canza lokaci guda tamkar ba su ba, 'Ya'yan hutu masu ji da gata.... So suke sukai hannu su tab'asu amma inaa Cops sun hana, sai faman kakkare su suke suna fad'in" No touching..
"Journalist kuwa tamkar anyi ruwan su haka sukayi chaaa suna wurgo ma duk wanda suka gane nada alak'a da Shari'ar..
"Gaba d'aya su Mummy dasu Alh Kasim suka d'unguma suka bi bayan su Salim wanda keta faman juyowa yana fad'in" Daddy pls... Uncle Mummy pls ku fitar dani a wajen nan.... I can't go back to jell....
"Mata matasa kuwa harma da manyan mata sune suka cika bakin kotun kowa da k'atoton takarda a hannunta an rubuta *JUSTICE FOR ZUBAIDAH* da manyan harrufa, sun d'add'aga sama suna fad'i tamkar masu biya karatu....
"Zubaidah dake zaune a reception k'irjinta yaci gaba da fad'uwa... Gefe da ita Annah ne, sai Hamman ta Habibu daga b'angaren dama, daga can wani kujeran kuwa Ansar ne da Hafiz sai faman tattaunawa suke k'asa k'asa. Hadiza bata zo ba tana can gida tareda Kamal...
"Fuskokin su ta hango ana shigowa dasu, tun daga nesa suma suka hangesu, banda mugun kallo babu abinda suke watsa masu, musamman Labib wanda yake a tsakiya.... Kafe su da idanu Zubaidah ma tayi, ihun su da shewan su ya shiga yawo a kunnuwan ta da kwanyar ta, dariyar su take ji sosai cikin kunnuwan ta, fuskokinsu take hangowa sanda Tariq da Salim suka Bank'are ta Labib ya keta mata riga daga sama har k'asa...... "Wani irin k'ara ta Saki lokaci guda gamida toshe kunnuwan ta had'i da runtse idanu da k'arfi..
"Annah tayi saurin rik'eta sosai tana mai karanto mata addu 'o'i.... "Ansar da Hafiz suka k'araso cikin sauri suna fad'i wa Annah kodai Zubaidah ta zauna da Hamman ta a can waiting d'in ne, tunda ganin su Labib na jefata cikin tashin hankali....
"Annah da Hamma duk sukayi na'am da hakan.. "D'ago kai Zubaidah tayi tana girgizawa kafin tace " No no Annah Ina so najisu suna confessing inaso ihun su da shewan su ya b'ace min ta hanyar jiyo muryoyin su suna confessing, I wanna see them been sentenced to jell... All of them. I want it to come to an end.... Ta k'arashe tana goge hawayen idanun ta....
"D'ago ido da zatayi sukayi ido hud'u da Labib idanun sa cikin burin d'aukan fansa... Da sauri ta dubi Annah tace "Annah mu koma ta can pls kinji.... Babu musu Annah ta rik'o hannun ta suka nufi tacan gefen...
"Labib ya bud'e murya yace " You miserable liar.... Tell them you're lying ... I swear you won't get away with this.... I'll make you pay.. All of you will pay...... "A zuciye Ansar ya k'arasa yana fad'in" Shut your trap you criminal.... Barr Munir yayi saurin tasowa Ya sha gaban Ansar yana fad'in" Don't talk to my client you good for nothing.. "Hafiz ne ya rik'o Ansar yana janye sa..
***********
"Alk'ali yana isowa aka bud'e d'akin shari'a.....
"Kowa ya nemi waje ya zauna, sanda Alk'ali ya shigo gaba d'aya aka mik'e don girmamawa, saida ya zauna bisa kujeran sa kafin kowa ya koma ya zauna...
"Ba tareda b'ata lokaci ba aka soma gudanar da shari'a..
"Gaba d'aya hankalinta baya wajen, idanun ta naga k'ofa, gani take tamkar zai bud'e ya shigo... Why isn't he here yet, what took him so long... Why did he leave me all alone by my self .. He should be here by now. He promised to be with me in this very day. "Cikin zuciyarta taci gaba da fad'in" I need you, I'm so restless, I can do it without you , I'm so scared, zasu k'aryata ni kaman yanda suka saba... You're my strength pls don't let me down..... Pleaseee...... Ta k'arashe zancen zucin nata tana mai runtse idanu...
*************
"Fadan k'arshe mai motar ya sauk'e sa kafin yace " Bawan Allah na maka iyaka k'ok'arina tunda na d'aukoka tun daga Toro har fadan k'arshe babu sisin kwabo...
"Jalal ya jinjina kai kafin yace " Ka taimake ni bawan Allah. Nasan kamin kayi iyaka k'ok'arin ka amma don Allah ka cikita ladan ka ka shigar dani Abuja, insha Allah zan biyaka kud'ad'en ka..
"Mai vectra ya jinjina kai kafin yace "Shiknn muje tunda kace zaka biyani kud'ina... "Ci gaba yayi da tuk'i yana satan kallon Jalal cikin rashin yarda dashi, sabida yanayi da yake ciki, ga dukkan alamu idan ba d'an fashi bane, toh kuwa d'an dambe ne... Da wann tunani ya ringa palpala gudu don gujema binciken jami'an tsaro...
**************
"Gaba d'aya kotu tayi tsit tana saurarn amsar da Tariq zai bada..
"Alk'ali ya kuma gyaran murya yace " Malam Tariq shin ka yarda ka amince ka amsa laifin da Malama Zubaidah take tuhumar ka dashi... "Did you commit the Crime..
"D'agowa Tariq yayi sukayi ido hud'u da Alh Kasim .... "Wani kallo Alh Kasim ya jefa masa gamida sakin murmushi.... Tariq ya kuma duban mahaifin sa da cike da tausayawa... Suka kuma yin ido hud'u da Ansar..... Ya kuma juyawa ya kalli Zubaidah.......
" Girgiza Kai Tariq yayi idanunsa tabb k'walla kafin yace " I deny it your Honor I'm not guilty.....
"Runtse idanunta tayi hawaye masu zafi suka sauk'o mata.... Da sauri Annah ta rungume ta ba tareda ta iya furta komai ba jiki a mace...
"Alh Kasim dasu Salim kuwa hak'waran su kasa rufuwa yayi sabida farin ciki..
"Hankali tashe Ansar ya k'arasa gaban Tariq yana fad'in" Kar kayi haka Tariq, kar kaji tsoron su, kar ka fasa fad'in gaskiyan da kayi niyya, kar ka bari su razana ka donmin bazasu iya maka komai ba face abunda Allah Ya k'addara.... Tariq you promised you'll tell the Jude the truth.... "Finciko sa Barr Munir yayi yana fad'in" How dare you, why just can't you leave my client alone..... " Cike da b'acin rai Ansar ya juyo gamida dunk'ule hannu yakai ma Barr Munir naushi a baki...
"Ran Alk'ali idan yayi dubu ya b'aci... "Cike da b'acin rai yake buga table yana fad'in " Silence..!!! Silence..!!!!! Attorneys respect your selves, you are not in your chambers.. "Get out of here all of you get out..... Alk'ali ya fad'i cike da b'acin rai...
"Ansar ya dafe kansa kafin ya k'arasa gaban Alk'ali yana me neman afuwa...
"Saida Alk'ali ya nuna b'acin ransa sosai kafin shari'a taci gaba...
"Bisa ga rashin k'wakk'aran hujjoji da lauyan wanda take k'ara ya kasa gabatar wa gaban Alk'ali, da kuma rashin samin takamemmen hujja da zai tabbatar da cewa wa'enda ake k'ara sun aikata lafin.. Kotu ta d'aga wann shari'a zuwa ranar ashirin da bakwai ga watan January sabuwar shekara mai kamawa.. Snn wann zama ta shari'a da za'a gudanar shine zai kasance shari'a ta k'arshe, idan babu wann k'wakk'waran hujja da zai tabbatar wa'enda ake k'ara Sun aikata laifin, kotu zatayi fatali da shari'ar... Snn kotu ta bada belin Salim Tariq da kuma Labib, baza 'a ci gaba da tsare su a gidan kasu ba..... "Daga haka alk'ali ya mik'e...
"Wai zo kaga murna a fuskokin su Salim da iyayen su.... "Rungume juna kawai suke suna masu bayyana farin cikin su...
"Ansar kuwa zubewa yayi a wajen saman gwiwoyinsa had'i da zame hular sa ta lauyoyi a hankali... Wani irin k'una da zogi zuciyar sa ke masa... "Hafiz ya shiga basa baki yana nuna masa wann ba shine k'arshe ba, yayi hak'uri ya fawalla ma Allah komai, snn ya sani iyawan sa da k'warewar sa bashine zai basu nasara ba, a'a komai sai Allah yayi... Tabbas bazasu tabbata a doron k'asa suna zalunci ba....
"Kuka shar shar da hawayen sa Ansar yake kafin ya soma fad'in" Hafiz am I that incompetent...? I failed Hafiz, I failed them all.. "Rungume sa Hafiz yayi yana calming d'insa had'i da k'arfafa masa gwiwa..
"Ansar ya d'ago yana duban Hafiz kafin ya dafa kafad'arsa yace " Bro take Zubaidah and Annah home pls.. I..... I just can't face them right now, nasan Zubaidah is completely heart broken, we let her down... Both ni da Jalal.... Pls take them home, will you??
"Gyad'a kai Hafiz yayi kafin yace " Of course I will bro... Just take care of yourself okay..... And pls don't do anything violence, just try to remain calm kaji.... Kaga what you did earlier was very wrong.... Remember kai Attorney ne, you shouldn't have let your temper get the best of you.....
"Ansar ya gyad'a kai kafin ya dafe kafad'an Hafiz yace " Haka ne friend, it won't happen again insha Allah... I just can't stand that worthless damn man ne.... But insha Allah hakan bazata sake faruwa.... Thank you for everything...
"D'an dafe kafad'arsa Hafiz yayi kafin yace " I'll go ahead, see soon... Ansar ya gyad'a masa kai kurum suka fito a tare...
"Cincirindon mutane sun hanasu wucewa especially journalist, kowa yanason jin ta bakin su, kowa yana son jin a ina aka kwana a shari'a... "Zubaidah tana sako k'afafunta akai mata chaaa, journalist sai faman d'aukan hoto suke suna mik'a abin magana suna jefo mata tambayoyi.... "Annah kuwa sai kakkare ta take har suka wuce 'yan matakalan da basu wuce biyar ba wanda ake bi takansu a shiga cikin kotun...
"Hafiz yayi saurin k'arasawa motar sa ya bud'e masu yana fad'in" Su k'araso nan..
"Suna hango Ansar sukayi masa chaaa, kowa naso Ansar ya amsa tambayar sa...
"Ansar yayi gyaran murya ya soma magana cikin dakewar zuciya sai faman d'aukar sa ake da cameras " This is not yet over.. We will insha Allah prove to the whole world the kind of people they are.. Most especially Kasim Dasuki.. Da yardan Allah wann shine shari'a ta k'arshe da za'a danne mana gaskiyar mu.. We will patiently wait for the next trial to come.... Sannu sannu bata hana zuwa, rana dubu na b'arawo snn rana guda ta mai kaya... Daga haka yasa kai ya wuce, suna kuma binsa suna jefa masa tambayoyi...
"Barr Munir suka hango dasu Alh Kasim tuni sukayi wajen su suna son jin ta bakin su... Su Labib kuwa tuni an bud'e masu Luxurious Cars d'insu sun wuce ciki... Tariq ma motar mahaifin sa ya wuce.....
"Tun daga nesa jikinsa ya gama yin sanyi, mutane sun soma watsewa a bakin kotun, daga can ya hangi Ansar dafe jikin mota, ya kifa kansa... Yanayin da yaga Ansar ya tabbatar masa akwai matsala.. A hanakali ya k'arasa har k'asar bishiyar da Ansar ke tsaye...
"Kaman daga sama Ansar yaji hannun mutum saman kafad'arsa...
"Da mugun mamaki ya d'ago yana kallon Jalal,... Tsaki yayi gamida fincikan marfin mota zai shige... "Jalal yayi saurin rik'o hannun sa kafin yace " Wait Ansar, tell me how did it go, where is Zubaidah, how's she, ka fad'a mun tayi nasara, tell me su Labib are already sentenced to jell...
"Huci kawai Ansar yake yana watsa ma Jalal mugun kallo kafin yace " Let go of me Jalal, and old don't ask me that again..
"Jalal ya girgiza kai kafin yace " No Ansar, you need to tell me everything, kar ka mance na bar amanar family na a hannun ka.
"Ansar yayi wata murmushin takaici kafin yace " Where is the Doctor, ina yake..???
"Jalal ya d'an shafi kansa kafin yace " Ansar it's a long story, yanzu haka my life is in danger, but I managed to escape just to protect Zubaidah... Pls tell me how did the Heroin go..???
"Ansar ya sauk'e deep breath kafin yayi briefing Jalal duk yanda ta kasance...
"Huci kawai Jalal yake yi yana tuno irin Pain d'in da Zubaidah take ciki a yanzu haka.... Fizge keys d'in Ansar yayi kafin ya shige motar yayi mata key sai huci yake tamkar zaki....
"Ansar ya bisa da kallo ba tareda ya iya furta komai ba...
"Jalal ya kwasa a guje tamkar mai barin k'asa... Ansar yabi bayan motar da kallo still speechless...
"Umar dake chan gefen kwalta da motar sa, yana ganin fitowar Jalal cikin mota a guje ya furta, "You imbecile you can't runaway from me.. "Bastard".... A guje yabi bayan Jalal don kar ya b'ace masa...
"Faisal ma dake chan gefen titi yana jiran fitowar Attorney Kumo ya cika umarnin uban gidan sa, nan yaga ba Ansar bane a cikin motar... Tsaki ya buga gamida buga kan motar a lokaci guda, cikin sauri Ya tada motar sa da niyyan barin wajen kafin a soma zargin sa....
"Gudu yake kan falfalwa saman kwalta tamkar mai shirin tashi sama, bai tsaya ko ina ba sai k'ofar gidan su Tariq,.
"Isowar su Tariq gida knn Dad d'insa Ya sauk'a yana zuge gate yayinda Tariq ke zaune cikin motar tamkar mutum mutumi...
"Yana gama parking Ya isa jikin motar ya fincike marfin da k'arfin gaske ya fizgo Tariq waje.... Jansa yake a k'asa har Ya isa jikin motar ya bud'e marfin motar ya jefa sa ciki yana huci.....
"Dad da fitowar sa knn daga gidan zai zauna a mazaunin driver Ya shigar da motar sai ganin k'ofar motar yayi a bud'e snn babu Tariq, .... Hankali tashe ya hangi mota wacce basai ance wa'enda ke ciki ne suka masa kidnapping d'a ba, cikin sauri ya shiga jiran security number yana sanar dasu lambar motar.....
"Suna fitowa daga Layin su Tariq Umar Ya shiga bin bayan su..
"Zulaihat wacce tun daga kotu take biye da Umar tace da mai mashin d'in yabi bayan wancan motar...
"Tariq ya d'ago yana duban Jalal kafin yace " Jalal what this is all about??
"Bai tankasa ba sai gudun da yake faman falfalawa idanunsa sunyi jazir haka fatar jikin sa, kana iya hango jijiyoyin jikinsa yanda duk suka tattashi sukayi kore shar... "Shiru Tariq yayi bai kuma cewa komai ba...
"Saida ya kusan barin gari kafin ya shige wani bend ya paka motar... Daga can ta waje Umar Ya paka tasa ride d'in ya nufi cikin kwanar da sand'a.... Zulaihat ma ta sauk'a daga babur d'in ta gyara lik'abin dake fuskar ta, tabi bayansa cikin sand'a da dabara........
"Bud'e marfin motar yayi yasa duka hannayen sa biyu ya finciko Tariq waje had'i da kai mai naushi a ciki.... "Tariq ya kama cikin sa yana fad'in" Jalal friend why all this...
"Kamo hab'arsa Jalal yayi ya damk'e da k'arfin gaske yana fad'in" Don't don't you dare call me friend, you nothing but a disgusting being, now tell me why didn't you tell the truth to the judge why.. Why Tariq.... I thought you not like them, I thought kayi nadama kaman yanda kace, I thought bazaka k'aryata Zubaidah a kotu kaman yanda sukayi ba... But I was wrong, you're just like them, you're even worse than them..... Fincikewa Tariq yayi yana hawaye yake fad'in" Yeah I'm worse than them, I was a coward and so selfish.... But I did it to save my family, I have no choice than to lie.... If I confess Kasim Dasuki will destroy my father... Jalal believe me I did that to protect my father... Kana tunanin abun baya cina a rai ne, kana tunanin inada wata rayuwa da zanji dad'inta a nan gaba, .... " Dukansu biyu hawaye suke daga Tariq d'in har Jalal d'in... Tariq yaci gaba da fad'in" Babu ita Jalal, babu sauran rayuwa mai dad'i a gareni, I'm life is a complete nightmare, it started from that Night, daren da Ya kasance mafi muni a rayuwata, Jalal I regretted every single thing that I did, I wish I wasn't born, I lost you my best friend, I lost my mother, and my Dad bansan makomar rayuwar da zai shiga ba randa ya wayi gari babu ni, don nasan nawa tazo k'arshe, Jalal bazan iya ci gaba da rayuwa ba.... Dan Allah ka kashe ni na huta..... Ya k'arashe yana zuba gwiwoyin sa a k'asa yana jijjiga Jalal....
"Jalal na k'ok'arin maida hawayen sa yake fincikewa daga rik'on da Tariq ya masa, a hankali ya furta, you can't manipulate me again, I've had enough already, ... Friend or should I call you foe alike kaida saura abokan naka, I hate you all, I despised you all..... And I won't rest till I see you all behind bars.... Daga haka ya janye k'afarsa ya shige mota ya bar Tariq a nan yana k'walla masa kira da iya k'arfinsa, Jalal d'inma d'ingisawa yake don ba wai Ya gama warkewa bane, da mugun gudu Ya kwashi motar ya bar wajen.....
"Daga yanda yake lab'e ya fito ya cakume Tariq ya shiga kai mai naushi ta ko ina yana fad'in" You Criminal, I'll kill you, ... Tariq k'ok'arin k'watan kansa ya shiga amma ina baza a had'a mai lafiya da wanda bai jima da tashi daga jinya ba ...... Tun Tariq na motsawa har takai ga ya kasa motsa koda d'an yatsan sa ne... Dukan sa kawai Umar yake yana fad'in " Kun shiga tsakani na da ita, you'll all get what you deserve...... Ya kuma d'ago Tariq ya buga sa da jikin wani dutse take jini ya b'alle ya soma kwarara.... "Ganin haka yasa Umar soma jada baya....
Sameena ce
[1/23, 22:28] +234 803 619 0581: 🌘🌘🌘🌘 *ZUBAIDAH*
75
*©Sameena Aleeyou...✍🏾*
_KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝_
*Dedicated To All Victims Of Rape...*
*MU SHAA KARATU 📚* *Novel group this spectacular chapter is yours guys 😍😘 .... I laughed so hard jiya 😂🤣😂😂😂 kai bansan Alh Kasim nada tarin mak'iya ba snn Jalal da Zubaidah nada tarin masoya har haka ba.... Nonetheless habibtys Sameena hearts each and single soul that belongs to that forum ❤🌹😍😘*
"Da baya da baya Umar Ya ringa ja ganin Tariq baya alaman numfashi...
"Zulaihat kuwa tsoro da firgici ne ya cika ta, k'unshe bakinta tayi da k'arfin gaske tana girgiza kai hawaye na fita daga idanun ta.
"A guje suka hangi motar ta fice daga kwanar.... "Kallo 'yan sandan suka bi motar dashi tabbas itace motar da mahaifin Tariq yayi reporting. Detective Amir ya d'anyi Jim kafin yace a zuciyar sa " That car is Barr. kumo's... Mi yayi a nan, knn shi ya kidnapping Tariq.... "Da sauri Ya shiga girgiza kai cikin rashin yarda da abinda zuciyar sa ke gaya masa...."Da sauri yace da driver d'in ya shiga bend d'in...
"Basu tarar da kowa a wajen ba, can gefen d'an wani dutse suka hangi Tariq, cikin sauri suka k'arasa yanda yake..... Da sauri suka nemi taimakon Ambulance... Suna masu ci gaba da gwaje gwaje...
**************
"Tana zaune a farfajiyan gidan gefen furannin da suka k'awata d'an madaidaicin gidan... Ko sauraren mota batayi ba don gaba d'aya tayi nisa duniyar tunani, daga ciki ma fitowa waje tayi to be alone....
"Ya jima yana kallon ta daga yanda yake tsaye bak'in cikin dake zuciyar sa ta yaye lokaci guda.... A hankali ya soma takawa har ya iso yanda take...
"Jikinta ya bata na wajen, yanayin da take tsintar kanta a duk lokacin da suka keb'e shi take ji..... " Juyowa tayi a d'an zabure.... Cak ta tsaya tana dubansa sanda sukayi ido hud'u.... "Sun jima suna kallon juna a haka kafin Zubaidah tayi saurin juyawa tana maida k'wallan da ya ciko mata idanu,... "Da sauri Jalal ya rungume ta ta baya... Ya d'ora hab'arsa saman kafad'ar ta had'i da lumshe idanu...
"Kasa katab'us tayi sai lumshe idanun ta da tayi siraran hawaye suka sauk'o..... "Cikin wani irin murya mai cike da rauni tace " Ya Jay pls let go...... "Dad'a matse ta yayi sosai hannayensa saman marar ta kafin ya soma fad'in" Baby I missed you, so very much.... I'm so sorry, I knw it hurts.... But believe me sweetheart it was never my intention to let you down.....
"Kukan da take matsewa ya kufce mata.... K'ok'arin b'anb'are hannayen sa take a jikinta amma ta kasa...
"K'aran motar police ya gauraye street d'in..... Gaba d'aya daga Jalal d'in har Zubaidah basu ji ba, don kuwa juyar da ita yayi kana yayi hugging nata sosai cikin jikin sa, duk jinin ciwon dake hannayen sa sun b'ata mata jiki.... "Har su Annah su Ansar Hafiz Hamma da kuma Hadiza suka fito daga cikin gidan Jalal da Zubaidah na rungume da juna...
"Detective Amir ne da wani Sargent suka shigo cikin gidan.... Ansar yayi saurin k'arasawa yana mik'a hannu ma Detective yake fad'in" DT how may I help you...... Sai sann Zubaidah da Jalal suka Saki juna...
"Kallo suka soma binsu dashi Jalal Ya k'arasa da sauri yayi hugging Annah had'i da mik'a ma Hamma hannu sukayi masabaha.... Daga nan ya k'araso wajen su Detective dasu Ansar...
"Shiru sukayi sanda Jalal ya k'araso.... Kallo kurum suke binsa dashi ganin rigar sa duk bushesshen jini ya b'ata... Jalal d'in ma kallo yake binsu dashi kafin yace " Detective Attorneys lafiya..? What is going on here..???
"Daga Ansar har Hafiz kasa cewa komai sukayi.
"Det Amir ya d'an zura hannayen sa a aljihu kafin yace " Jalal I'm sorry but you need to come with us to the station.... Earlier Alh Maina reported that his son was abducted.... Ya bada lambar motar Barr Kumo a matsayin suspect,........ "Tun kan yayi shiru Jalal ya soma girgiza kai yana fad'in" No no..... He was asking to kill him, he was even begging, ..... But I swear I didn't, I did not kill him..... Gaba d'aya ido suka zuba masa.... Su Zubaidah kuwa tuni suka k'araso fuskokin su fal tsoro..
"DT ya d'an girgiza kai kafin yace " I'm sorry Jalal but you really need to come with us..... Juyowa Jalal yayi yana kallon Zubaidah wacce bata fahimci me ake ciki ba...
"DT pls is there something we can do, pls Amir.... Cewar Ansar cikin tsananin tashin hankali..
"Girgiza kai Amir yayi kafin yace " Attorney I'm sorry but there's not.... All I can say shine get him a lawyer.... Hafiz yayi saurin matsowa kafin yace " I am, I'm his lawyer... Ya dafa kafad'un Jalal yace " I know you are innocent, I know you didn't kill him, zan tsaya har sai gaskiya Ya fito.....
"Kasa furta komai Jalal yayi sai ambaton Allah da yake yi cikin zuciyar sa...
"Amir ya d'an dubi Sargent yace " Cuff him.... Kamo hannun Jalal Sargent yayi ya zura su cikin handcuffs.....
"Daga Annah har Zubaidah mutuwar tsaye sukayi tamkar gumaka... Hamma kuwa tuhumar 'yan sanda ya soma yi yayinda zuciyar Hadiza ta cika pam da farin ciki..
"Kallon Detective Amir yayi kafin yace " Just a minute pls... Detective ya gyad'a masa kai kafin ya k'arasa gaban Zubaidah da Annah wanda dukan su biyu hawaye ne kurum ke fita a idanun su...
"Jalal yakai hannayen sa da suke d'aure cikin cuffs ya rik'o hannayen Zubaidah da Annah kafin ya soma fad'in" I didn't...... Muryar sa ta soma sark'ewa a hankali yaci gaba da fad'in" it shall all pass kunji wata rana sai labari..... "Annah kasa resisting hawayen ta tayi ba ta iya furta koda kalma guda ba...
"Zubaidah kuwa girgiza kai take tana kuka sosai.... Cikin tsananin kuka take fad'in" Pls don't leave me ya Jay dan Allah kar ka tafi ka barni, nasan wann duk a cikin sharrin su ne....Hannu ya d'ago ya share mata hawayen ta kafin yace " Take care kinji.... Ki kula min da kanki da Annah na, I love all so much..... Daidai nan Sargent ya jawo hannun sa suka soma tafiya...
"Binsu ta shiga yi tana fad'in" Ina zaku kai min miji, ku dawo min da mijina, he's not a criminal, he's innocent.... Dan Allah ku dawo mun dashi... Ta k'arasa gaban Ansar tana kuka sosai take fad'in" Ya Ansar zasu tafi dashi, sun tafi dashi.. Ta dawo gaban Hafiz tana fad'in" Barr pls do something, don't let them take my husband zan iya rantsewa bashida laifi.... Ganin babu mai iya tankata cikin su yasata dawowa wajen Annah tana fad'in" Annah pls kice su dawo dashi, I can't lose him..... Pls..... Hamman ta ne ya k'araso Ya rungume ta shima kukan yake harda majina...
"Hadiza ta tab'e baki tace " Haba haba abu yak'i ci yak'i cinyewa, gaba d'aya kowa sai shan wahala yake akan ki ke rai guda, ina ke ina shari'a da wad'an nan mutane, tun farko da baki fara magana ba da baki shigar da k'ara ba da abun bai kawo har nan ba, sai kace akan ki aka soma fyad'e wa 'yammata... Toh ai yanzu ga nan irinta kina gani, Ba budurci kurum ba harta Jalal d'in sai kin rasa sa..... "
"Ansar da Hafiz mota suka shige suka bi bayan su Jalal... Annah kuwa girgiza kai kurum tayi hawaye na ci gaba da zuba mata ta nufi cikin gida don bata iya fahimtar komai..
"A zuciye Zubaidah ta k'arasa gamida d'aga hannu zata kwad'a ma Hadiza mari.... Ganin Hamma datayi a gefenta yasata sauk'e hannun idanun ta na ci gaba da ambaliyan hawaye.. ..
"Ayyiriri hiyye lallai Zubaidah wuyarki tayi k'wari, yau har nice kike d'aga min hannu zaki mara lallai kuwa zaki iya marin wann lusarin yayan naki.... Ki musa mana idan k'arya nake, muna zaman zaman mu a garin mu muka baro a dalilin ki.. Kowa na shan wahala a dalilin ki, ko ina mukaje muna kaffakaffa da rayuwar mu duk a sabida ke, ke ko tsoron hakkin mutane bakiji,... Toh wllhi bari na fad'a maki, duk abinda ya sameni ko ya sami d'ana a sabida ke bazan tab'a yafe maki ba, ... Ta bita da uwar harara kafin ta kuma jan tsaki tace " Annoba kawai... Daga haka Hadiza tasa kai ta wuce cikin gida....
"Durk'usawa Zubaidah tayi a wajen saman gwiwoyin ta, tabbas duk abinda Hadiza ta fad'i haka ne, everyone has to suffer because of her selfishness, why is all this happening, why why.... If only batayi pressing charges ba, da duk ba'a kawo wann peak d'in ba.... She can't take it anymore, she just can't.... Ta k'arashe zancen zucin nata tana girgiza kai cikin tsananin kuka m...
"Hamma ne ya durk'usa ya shiga share mata hawayen yana lallashin ta, yana fad'a mata ko d'aya ba laifin ta bane, duk abunda ke faruwa muk'addari ne daga Allah.... Rungume Hamman ta tayi tana ci gaba da kuka mai tsuma zuciya.....
***************
"Allah ya taimake ka Abbah mun shirya zamu wuce.
"Mai Martaba ya jinjina kai cike da jin dad'i irin wanda bai tab'a ji ba kafin yace " Ubangiji ya kaiku lafiya ya baku nasara Abdullah.. Baban ka Ciroma yana waje zaku tafi tare, ku biyu tak na amince na d'aura ku bisa wann Al'amri, duniyar nan banida wanda na aminta dashi tamkar kai Abdullah... Yaya Ciroma kuwa yaya nane mahaifin mu d'aya nasan zaku rik'e min amana, ku taho min da d'ana lafiya...
"Shattima ya kuma rusunar da kai kafin yace " Abbah insha Allah zaka same mu muna masu rik'e amanar ka tsakani da Allah.
"Mai Martaba ya jinjina kai kafin yace "Tashi kaje Allah yayi maka albarka...
"Shattima ya amsa da ameen kafin yayi godiya ya fice Mai Martaba na masu fatan sauk'a lafiya....
"Babu yanda Shattima baiyi ba akan suyi amfani da private jet d'in companyn Mai Martaba *Modibbo Cooperation Company* amma fir Baba Ciroma yak'i yace da mota zasu tafi kuma Shattima zaiyi driving, ko kad'an Shattima baison musu wa babban mutum kuma mahaifin abokin sa kaman Baba Ciroma, d'an girgiza kai kurum yayi kafin yace " Shiknn Baba tunda ka zab'i hakan, amma magana ta gaskiya isan dare zamuyi sosai, tunda Gombe da Abuja ba Gombe da Bauchi bane....
"Baba Ciroma ya gyad'a Kai kana yace " K'warai kuwa Abdullahi. Kai bakasan tafiyar mu a mota zaifi sirri ba koh, .. Ai idan munje ba kai tsaye zamu nuna kanmu ba, sabida guje ma abokan gaba da mahassada, kasan duniyar nan ta cika famm da azzalumai....
"Jinjina kai Shattima yayi kafin yace shiknn Baba Allah Ya kaimu lafiya....
"Baba ciroma na murmushi ya amsa da ameen Audullahi.....
*******************
"What..!!! No no uncle don't even start, ta yaya zaka ce za'a sayar da gidan Dad d'ina bayan kasan wann gidan ne kurum ya mutu ya bar mana... Labib yace cikeda d'aga murya...
"Alh Kasim ya d'ago ido tsegege yana kallon sa kafin yace " Labib kasan dai bazan lamunci duk wani iskanci da iya shege da ka min a baya ba, masu waye nake yin wann, duk ba akanku bane, su waye suka fara jawo min experiencing wani abu mai kama da kariyar arziki, duk ba ku bane, idan baka sani ba ka sani gidan mahaifin ka is never yours don kuwa har rana mai kaman ta yau ba'a gama biyan bashisshikan sa na banki ba.... Snn waye za'ace ya biya ba ni bane, recently na rasa jirgina da ta shak'o kayan masarufi, nasan kasan wann zancen don babu yanda labarin bai isa ba a nahiyar Africa... Dole a sayar da gidan Jamil ku dawo nan gidan kaida mahaifiyar ka, tunda it can contain us all, our company is going bankrupt sabida d'unbin asaran da mukayi, da kuma cire shears d'insa da Alh Tahir yayi.... Labib ya d'ago yana duban Alh Kasim kafin yace " Uncle don't tell me the Marafa'a and the Dasuki's are not more business partners, me ya faru....
"Daidai nan Salim Ya turo k'ofar parlorn ya shigo, .. Alh Kasim ya dubesu dukan su biyu, sai yanzu ya tuna ashe lokacin da Alh Tahir ya mutu suna prison... D'an gyaran murya yayi kafin ya basu labarin k'onewar company d'insa da kuma mutuwar da yayi a cikin wutar...
"Girgiza kai kurum Labib yake yana fad'in" You are a monster Uncle, you're not human, I'm pretty sure is all your doing....
"Salim kuwa tsalle yayi ya cakumo wuyar mahaifin sa yana fad'in" You killed her father.... Why why Dad, Kausar is the love of my life and and ka jefa rayuwar ta cikin garari..... I'll never forgive you for this Daddy....
"Enough...?!!! Alh Kasim ya daka masa tsawa kafin yaci gaba da fad'in" You are all stupids, you ungrateful children, I did it all for you, to save you from going to jell..... I'm suffering because of you, I almost lost my company because of you.... If only you didn't rape that girl.. Things will be different... Ku ne, kune silan komai.....
"But we are not heartless like you.... Labib ya fad'i cikin d'aga murya.... Daidai nan Barr Munir ya shigo cikin tashin hankali yake sanar dasu abinda ya samu Tariq....
"Gaba d'aya suka fice cikin tsananin tashin hankali....
Sameena ce 👌🏾
[1/23, 22:28] +234 803 619 0581: 🌘🌘🌘🌘 *ZUBAIDAH*
76
*©Sameena Aleeyou...✍🏾*
_🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝_
*Dedicated To All Victims Of Rape...*
*For All Cat Lovers 😻*
"Tunda ya dawo gida hankalin sa ya gaza kwanciya gaba d'aya Innah ta kasa gane kansa, d'aki ya shige k'arshe ya b'alle buttons d'in wuyar rigar sa ya nufi d'an k'aramin fridge d'in dake a cikin d'akin ya d'au kwalban whisky ya shiga kwankwad'a zuciyar sa naci gaba da tafarfasa...
"A hankali yake furta " I've already started and I'll accomplish it, all of you must get what you deserves... Yayi wata murmushi kafin yace " Now Jalal dole kowa ya yarda kai Ka kashe Tariq... I got rid of you two... And the remaining two. The Dasuki's Salim and Labib.... I'll come for you too... Ya d'aga kwalban whisky shi kad'ai snn yace da kansa cheers Umar to the beginning of your success..... Ya k'arashe yana fashewa da muguwar dariya....
**************
"A tare su Alh Kasim suka shigo asibitin gaba d'ayan su... Mum d'in Tariq sai sharb'an kuka take kaman ranta zai fita, Alh Maina kuwa zama kurum yayi gamida dafe fuskar sa da duka hannaye biyu...
"Duk wani basu baki dasu Alh Kasim suke ba fahimta suke ba, a haka Dr ya fito daga theater room d'in yana zame gloves d'in hannayen sa, a tare suka mik'e gaba d'aya suka nufi Dr...
"Dr how's my son... Tell me he can go through this, tell me pls.... Cewar Alh Maina cikin rawar murya... Mum kam tuni ta wuce ta nufi d'akin saida Salim yayi saurin k'arasawa ya rik'o ta.. " Fad'i take" Let me see my son.. Just let me see him, he needs me right now.... Haka Salim Ya ringa k'ok'arin rik'eta dukda fuzfuzgewar da take....
"Dr ya d'an shafi goshin sa kafin ya dubi Alh Maina yace " Follow me to my office... Babu musu ya shiga binsa tamkar rak'umi da akala.. Alh Kasim na biye dasu...
"Dr ya d'ago yana dubansu kafin yace " I'm sorry Alh Maina.... "Jin wann kalma yasa Alh Maina soma girgiza kai yana fad'in" No no I can't lose him, he's my only son.... "Alh Kasim ya dafa kafad'ar Alh Maina kafin yace " Ka kwantar da hankali friend everything will be alright,....
"Doc ya d'an fuzar da iska kafin yace " Alh Maina your son isn't die yet, but... But... I'm sorry to say ya sami internal injury in his brain.. The same wajen da ya samu a kwanaki, a wancan karan munyi k'ok'ari mun cire jinin coz bai tab'a k'wak'walwar sa ba.... Buy this time aroundwe just couldn't, already ta shiga cikin kansa sosai, magana ta gaskiya d'anka rayuwar sa tana cikin tsananin had'ari.... Dukda rayuwa da mutuwa na Allah ne, amma ko yayi rai memory d'insa zaiyi matuk'ar wuya ya dawo..... Snn ya sami problem a medulla spinalis d'insa, ko zaiyi rai he won't be able to walk again...... Dr ya d'anyi shiru yayinda Alh Maina ya soma girgiza kai kurum... Alh Kasim kuwa cewa yake who ever did this to him must pay....
"Dr ya d'ago hannu kafin yace " Try to calm down Alh and pls if possible kar a bari mahaifiyar sa taji wann, shiyasa na keb'e daku.... "Alh Kasim ya jinjina kai kafin yace " Haka ne Dr mun gode sosai..
Kamo kafad'un Alh Maina yayi suka nufo reception yanda su Labib suke... Har lokacin Salim na zaune gefen Mum dake cizgan kuka...
"Basu sami ganin Tariq ba don kuwa yana intensive care unit, banda sautin na'uran bature baka iya jin komai a wajen....
"Salim Ya dubi Labib kafin yace " I can't believe Jalal is capable of murder...
"Labib Ya d'an fuzar da iska kafin yace " Me either.... Ko Jalal zai kashe wani bazai kashe Tariq ba, among all of us yafi shiri da Tariq..
"Salim Ya d'an tab'e baki kafin yace " That girl changed him completely, we don't know him anymore.... Idan kuwa ya kashe Tariq toh kuwa duk muna cikin list d'insa, he'll surely come for us... I'm just terrified....
"Tsaki Labib yayi kafin ya fashe da dariya yace " Coward police already got him arrested, ka daina jin tsoro he won't come for you.... Mama boi... I thought prison did change you ashe babu abinda ya ragu.. You still Salim Dasuki.... Labib ya kuma fashewa da dariya..
"Gajeren tsaki Salim yayi kafin yace " Stop joking around already, this is a serious matter you know...
"Dariya Labib ya kuma yi daidai nan Barr Munir da Alh Kasim suka k'araso yanda suke..
"Alh Kasim ya dubesu kafin ya soma murmushi yace " You boys are lucky ku gode ma Allah...
"Kallonsa sukayi da alaman tambaya d'auke a Face d'insu...
"Alh Kasim yayi murmushi yace "Nasan baku gane me nake nufi ba, amma yanzu zan fayyace maku nufi na, abinda muka hanga maku nida Barrister..
"Saida ya karkata babbar rigar sa kafin ya soma fad'in" Is something very easy, Nasan dukan ku kunsan Jalal bazai iya kashe Tariq ba... Suka gyad'a kai a tare
"Alh Kasim ya kuma gyara tsayuwa kafin yaci gaba da fad'in" According to Jalal's statement Tariq kafin ya mutu yayita rok'onsa Ya kashe sa, amma bai kashe sa ba, snn kunsan tun ba yau ba, Tariq Was planning to commit suicide, yanzu abu ne mai sauk'i zamu fad'a wa Zubaidah... If she dropped the charges, we will set her husband free. Nasan she will definitely do it right away... Kunga idan tayi haka muka sai muce zamu bada testimony d'in mu in court cewa Jalal bai kashe Tariq ba, hasali ma Tariq ne me yunk'urin kashe kansa ku da kuka rayu dashi a prison zaku bada wann shaidan.... Kunga daga nan no more worries, an rufe babin Zubaidah har abada....
"Dariya suka tunsture dashi su duka biyu, Salim harda hugging Dad d'insa yana fad'in" Nice suggestion ever Dad, ...
"Labib kuwa cewa yayi " Uncle baka tab'a burgeni irin ta yau ba....
"Alh Kasim ya murmusa kafin yace " Ai nasha fad'a maku all this fad'i tashi da nake yi I'm doing it for your future ne.. So yanzu abinda nike so daku, keep this between us, no one should know, not even your Mums kun gane...
"Gyad'a kai sukayi cike da jin dad'i kafin suka fice daga asibitin....
*****************
"Tafiya suke kan shara bisa kwalta duk wani lungu da sak'on hanyar Gombe to Abuja tsaf Shattima ya haddace su akan sa...
"Baba Ciroma sai goga ashwakin munafunci yake yana zazzare idanu....
"Banda sautin k'ira'ar Shuraim cikin suratu Yusuf babu abinda ke tashi a motar...
"Sun d'an wuce Bauchi kad'an har sun wuce wani k'awye dake d'an gaba da Narabi kad'an Baba Ciroma ya dubi Shattima yace " Audullahi niko inaso na tsaya a nan na d'an kama ruwa...
"Shattima ya d'anyi slow ya kalli agogon jikin motar ta nuna k'arfe shida da wasu 'yan dak'ik'ai, cike da gurmamawa Shattima yace " Baba ai da ka bari mun shiga Tilden Fulani tunda mun kusa shiga amma nan wajen is very risk ba'a faye tsayawa ba, iyanin sai muyi sallahn mangaribar mu....
"Baba Ciroma ya cika yayi fam, take ya soma bore yana fad'in" Aikin banza aikin wofi, nine Aliyu (Mai Martaba) zai had'ani da yaro a tafiya kuma na fad'i abu ace baza'a yisa ba, sarauta ce Allah ne me badata, kuma da Allah yaso da yanzu nine a kujeran nan ba Aliyu ba, ina binsa da umarnin sa sauda k'afa dukda k'anina ne amma bazan lamunci wulak'anci da raini daga yara 'ya'ayan ciki na ba.....
"Cak Shattima yaja yayi burki cike da mamaki, me Ya kawo wadann maganganun....
"Baba Ciroma yaci gaba da fad'in bud'e min na fita d'an k'wal uba.....
"Murya har na rawa Shattima ya shiga basa hak'uri had'i da bud'e lock.... Aiko Baba Ciroma na fita wasu mutane da sanduna da gorori suka nufo su suka shiga dukar motar da iyaka k'arfin su....
"Dukda fasa masa glass d'in mota da sukayi bai hanasa danna giya da k'arfin gaske ba yayi rivers lokaci guda..... Bada son ransa bane ya bar Baba Ciroma dole ya tafi ya nemo masu d'auki kafin ayi kan me uwa dawabi ba wan ba k'anin karatun arne... Tunda baya dasu kad'an sun wuce checkpoint na Sojoji.
"Dukan Baba Ciroma suke da iyaka k'arfin su yana fad'in" Ba shi bane ba ku saurara ba shi bane ba, wllhi shine wanda ya gudu, na rantse maku ni na biya kud'in" Kar ku kashe ni kuyi min rai....
"K'auyawan nan kuwa sai raptama masa sanda suke suna fad'in" Aradun Allah k'arya kake, yace mana zai ajjiye ka a nan wajen mu gama da kai, ku buge shi.... Rititim suka ci gaba da aza masa sanda .... Banda k'alu innalillahi da Baba Ciroma ke iya fad'i baya komai.... Tun yana iya motsi har ya bar motsawa... Daidai nan su Shattima da sojojin checkpoint suka k'araso... Aiko nan suka gudu suka shige daji.... Ruwa ruwa aka kwashi Baba Ciroma aka shige dashi mota suka nufo dashi Babban asibitin Bauchi Abubakar Tafawa Balewa University Teaching Hospital Bauchi.... Cikin sauri aka karb'i Baba Ciroma a emergency rai a hannun Allah.....
*****************
"Tunda ta dawo gida tayi jigum ko abinci ta kasa ci, wunin ranar guda haka tayisa babu cin abinci... Goggo ta lura da hakan, don kuwa duk barkwancin Zulaihat yau kam shiru ta b'ace....
"Imam ne ya shigo gidan dawowar sa knn daga makaranta don yau ya jima yana lectures bai sami zarafin yin tasi ba, sabida tutorials da ya gudanar ma 'yan ajin su....
"Ya sha mamaki ganin yau basa zaune saman tabarman da ya saba dawowa yana iske su... Kai tsaye d'aki ya wuce ya ajiye littafan sa kafin ya canza kaya ya nufo d'akin Goggo.
"Zulaihat bata a parlor sai Goggo dake faman saita radio...
"A'a Imamu an dawo Goggo ta tambaya tana murmushi...
"Imam ya k'arasa yana fad'in" Eh 'yar tsohuwa Allah yayi sun sake ni na dawo... Goggo ta murmusa tace toh bismillah maza kazo kaci abinci yau mutumin ka akayi d'an Wake... Imam dai murmusawa kurum yayi amma hankalinsa yafi karkata ta ina zai hango Zulaihat...
"Goggo ta katse sa da fad'in" Lafiya dai koh... D'an jim yayi kafin yace " Goggo Zulaihat fah..
"Goggo ta d'an rage murya kafin tace " Tana ciki yau haka nan ta wuni, k'ila bata jin dad'i ne, maza ka shiga ka tambaye ta nasan zata fad'a maka...
"Bata jin dad'i ya fad'i fuskar sa fal damuwa... Mik'ewa yayi ya nufi uwar d'akin goggo yana fad'in barin duba ta kana yayi knocking a k'ofa....
"Da sauri ta shiga goge hawayen idanunta kafin ta d'auko mayafi ta rufa snn ta basa izinin shigowa...
"Tun daga ganin yanayin ta yasan babu lafiya... K'arfin hali ta shiga yi tana k'ok'arin d'aura murmushi saman fuskar ta tace " Student yau baka dawo da wuri ba, you got us worried ...
"Tsareta da idanu yayi kafin yace " Meke damun ki, ..."Far da idanu tayi tana masa hararan wasa kafin tace " Ban gane ba, I'm fine..
"Imam ya sauk'e ajiyan zuciya kafin yace " you look so weird, snn goggo tace min yau haka kika wuni, ... By now kinsan na sanki sosai... So just tell me what's up with you...
"Zulaihat ta share hawayen da taji sun ciko mata idanu.. " Cikin zuciyar ta take fad'in" I can't share it with you Imam, I can't tell anyone, I'm so scared.....
"Imam yayi shiru yana karantar ta, a hankali yace " Ko ana maki wani abinda baki so ne...
"Girgiza kai tayi kafin tace " Never, kawai.... Kawai... I'm just missing home ne, even though my momma died I still want to see my father again, dukda watsar da rayuwata da yayi, I wanna see him again and ask for his forgiveness, nasan ba laifin sa bane, laifin evil step-mom d'ina ne.....
"Tausayin ta Ya cika zuciyar Imam, cikin sanyin murya ya shiga lallashin ta yana nuna mata insha Allah zai kaita har Adamawa wajen mahaifin ta...
"Murmushin yak'e kurum tayi cikin zuciyarta kuwa baubuwa ne da dama suka mata cunk'us... Don kuwa babban abin takaicin ta shine ta kasa yakishe soyayyar Umar cikin zuciyar ta....
************
"Ya jima yana tsaye a waje babu Kausar babu alamun ta... Sai faman d'aga kai yake yana hangen benen gidan...
"Asmah ta kuma suban ta a karo na biyu tace don girman Allah Kausar kije ki sallame sa wllhi ba tafiya zaiyi ba idan bakije bar, kinga babu yanda Mal Liti baiyi dashi ba, yak'i tafiya...
"Mik'ewa Kausar tayi a fusace kafin tace " This is the worse mistake of his life... Wllhi sai yayi nadamar tako k'afarsa gidan nan..... Da k'arfin gaske ta fizgi k'ofa ta fice...