BABI NA SITTIN DA DAYA.
Numfashi taja mai zurfi kafun ta tura laɓɓanta cikin baki tana cizawa idanuwanta har zuwa wannan lokaci suna kan Baseera zuciyarta sai kara harɓawa take yi da sauri-sauri fargabarta da tsoronta suna kara daɗuwa sosai take hango rashin yarda da amincewa gami da rigima cikin idanun Baseera wacce tayi mata fakare tana yi mata kallon tuhuma.
'Ya za ta dauki lamarin in na sanar da ita anya kuwa zata yarda har ta aminci da bukatata?'.
Mariya ta fadi haka a ranta tana kara matse hannun Baseera a cikin nata.
"wai me ke faruwa ne?".
Baseera ta fada gabanta ita ma na cigaba da faduwa.
"Baseera ki Auri Dr.Aqeel".
Ta fadi tana runtse idanunta sosai a cikin jikinta take jin wani iri zuciyarta na matsewa da wani irin yanayi da yake mikata wani mataki mai girman gaske.
Dariya Baseera tayi cikin rashin baiwa batun muhimmanci sosai tana kallon Mariya da idanunwanta ke a rufe.
"Ban gane ba Mariya me kike nufi kin san kuwa abin da kike cewa?".
Buɗe idanunta tayi sosai wanda suka kaɗa sukayi jajir ganin hakan yasanya Baseera nutsuwa tana kallon ta lokaci guda zuciyarta ta buga da wani irin tsoro da ya mamaye duk ilahirin jikinta.
Gyaɗa kai Mariya ta shiga yi kafun ta motsa laɓɓanta.
"Ki taimaka ki auri Dr.Aqeel Baseera".
Ta sake fadi tana kara kusanto Baseera fizge hannunta tayi gami da mikewa kallon Mariya take yi da wani irin yanayi kafun ta ja da baya sosai tana sake yi mata wani kallo mai kama da na tsoro ita kanta Mariya ta tsoro ta da irin kallon da take yi mata mikewa tayi tana takowa in da take ta sake riko hannunta tana sarkewa da nata.
"Ki taimaka Baseera ki aure shi wannan hanyar ce kawai nake hango mana mafita a gareni da kowa ma".
Kallonta take yi sake da baki kwanyarta take ji tana mikata wani mataki mai kokarin kona mata kwanya zuciyarta take ji tana harbawa da sauri-sauri.
"Ki taimaka ki aure shi na san za ku dace kuma za ku so juna".
"Ba zan iya ba Mariya ba za ayi wannan cin amanar dani ba".
Ta fadi tana fizge hannayenta tana kokarin ficewa daga cikin dakin da sauri Mariya ta riko ta sosai ta juyo da ita idanuwanta suka kawo kwalla sosai cikin rawar murya Mariya ta fara magana.
"Karki kawo cin amana a wannan lamarin Baseera ni nace na amince miki kuma na san ba haramun bane don haka don Allah ki anshi bukatata hakan ne zai tabbatar da amincin ƙawancenmu".
"Ki yi hakuri ba zan iya ba Mariya".
"Ki taimaka ki auri Dr.Aqeel Baseera ba za kiyi da na sani ba ni za ki taimakawa".
"Mariya....!".
Da sauri Mariya ta kai hannunta ta rufe mata baki tana girgiza kai hawaye na sauko mata saman fuska.
"ko MATAR MIJINA kika zama Baseera ba zan taba da na sani ba domin na san halin ki kuma na san ba zaki taba abin da zai cutar dani ba Baseera matsayin yar'uwa kike a wajena kina da matsayi mai girma a gareni ki anshi bukatata ki daure karki ce dani a,a".
Runtse idanu Baseera tayi tana jin zuciyarta na mikata wani mataki mai girman gaske gabadaya komai ya cunkushe mata ta rasa wani tunani ma zatayi ba ta taba zato ko tsammanin Mariya wannan bukatar zata nema a gareta ba in da ta san haka ce zata faru ba abin da zai kawo ta wannan gidan amma ina ALKALAMIN KADDARA ya zano mata rubutun da sai ta zo ta karance shi.
'Anya ba cin amana in ta yarda da batun Mariya anya hakan ya dace bata jin son Dr.Aqeel a ranta ba ta jin sun dace a tsakanin ita dashi to in ita ta yarda shi fa a yarda ta ga yana mayan son Mariya an ya kuwa zai dube ta da idanun kirki har ya anshe ta a matsayin matar aure gareshi ina! ba zata yarda taje in da ba a son ta ba ba za ta je in da ba za a ganta da mutunci da kima ba ba zata yarda ta shiga in da za a din ga yi mata kallon kamar dole akayi masa ba'.
Nazarin da ta shiga yi da zuciyarta kenan cikin wani irin yanayi tsoro da fargaba na kara bayyana a gareta.
'Mariya ta cancanci komai fiye da haka za ta so ace sanadin ta ta samu farin ciki za ta so ace ta sanadin ta rayuwarta ta sauya ta dawo mai armashi amma ta ya ya hakan zata kasance bata tunanin auren Dr.Aqeel shine mafita'.
Kamar Mariya ta san nazarin da take yi da zuciyarta dubanta tayi cikin kara narkar da murya da son biyan bukatar ta duk da tana jin wani iri a zuciyarta ta.
"Ki daina shakka ko fargaba akan Dr.Aqeel Baseera zai so ki ba zai taba wufutar dake ba so zai yi miki mai an suna so zallar sa karki sake ki saka wa zuciyarki fargaba ko tsoro".
Hannu ta saka tana dauke hawanyen fuskarta tana mai kokarin zaunar da Baseera amma ta kiya ta kwace kanta.
"Gida zan tafi Mariya kaina ciwo yake yi don Allah rabu dani zan yi tunani".
"Ban yarda ba Baseera ba zan yarda ki fice daga cikin gidan nan ba har sai kin ansa mani bukatata in kuwa har baki an sa ba to na tabbata amincin dake tsakaninmu ba kai ya kawo ba wallahi tallahi Baseera ko mijin da nake aure ki ka zo ki ka nuna kina so wallahi zan yarje miki ki zama MATAR MIJINA".
Da mamaki Baseera ke dubanta fuskarta na sakin wani murmushi wanda yafi kuka ciwo sosai ta kamo hannun Mariya ta saka a nata.
"ki daina kiran amincin dake tsakani na dake kina danganta shi da wannan lamarin ni nace miki ki bari nayi tunani ba yarda za ayi na ansa wannan batun lokaci daya Mariya ba sauki fa lamarin nan gareshi ba duba zakiyi da shi Dr.Aqeel ba shi yace yana so na ba ke yake so kina tunanin in ya ji batun nan zai yarda har ya dube ni da kima da mutunci ya anshe ni amatsayin da kike kokarin daura ni?".
Murmushi ita ma tayi zuciyarta na kara matsewa.
"Alkawari nayi miki zai so ki so da bai taba yi wa wata 'ya mace...".
"Ya isa haka Mariya maganar ta isa haka ki daina danganta KALMAR SO a wannan bahagon tunanin naki mara tushe kece mace ta farko kuma ta karshe da Dr.Aqeel yayi wa son da ba zai sake yi ma wata mace ba a duniyar...".
"Na karya taki Baseera a wannan matakin ni nace miki in har kika aminci da Dr.Aqeel sai yayi miki so fiye da wanda yayi mani a filin duniyar nan ki rubuta wannan ki ajje ni dai BURINA ki amince".
Kanta ta dafe da take jin yana sara mata maganganun Mariya suna kokarin saka mata ciwon kai bata san yarda za tayi da ita ba amma Allah na gani zuciyarta na fargaba kan lamarin nan.
"ki je ki samu yardarsa in har ya amince nima na amince".
Tana gama fadin haka da sauri ta kwace kanta ta fice daga cikin dakin zuciyarta da kwanyarta sai hayaki suke yi kamar za su kama da wuta duniyar take ji tana juya mata kafafuwanta take ji suna kokarin zubda ita ga wani zafi da take ji tun daga kasan ruhinta har zuciyarta komai kallon sa take yi kamar a mafarki ba gaske ba laɓɓanta take turawa cikin baki tana cizawa gami da runtse idanuwa.
Dafe kanta Mariya tayi gami da jan kafafuwanta da take jin su ita ma suna kokarin zubda ita kasa ga wani hayaniya da take ji a kwanyarta zuciyarta take ji tana harbawa da sauri-sauri idanuwanta a runtse ta isa bakin gadon ta zauna tana faman fadin.
"Yaa Hayyu Yaa Kayyum".
Numfashi take fiddawa a hankali zuciyarta na kara mikata wani mataki abin da tayi ne a yanzu take jin wani banbarakwai ji take yi kamar ba gaske ba ji take yi kamar cikin barcinta ne komai ke faruwa girgiza kai ta shiga yi kafun ta buɗe idanuwanta wanda suka gajiya da kaɗawa sosai zuwa ja murmushi ta saki gami da rufe fuskarta da tafukan hannayenta ta fada kan gadon ta baya.
Tunanin ta yarda zata fuskanci Dr.Aqeel take yi ba ta san ta yarda zai dauki maganar ba in ta je masa da ita bata san duban da zai yi mata ba akan wannan maganar anya ba zai ce ta yaudare shi ba anya ba zai ce ta ci amanarsa ba anya ba zai ce tayi masa BUTULCI ba?
Tunanin da take ta faman yi kenan zuciyarta kuma ta kasu kashi biyu bangare daya na bata kwarin gwuiwar tunkararsa dayan barin kuma yana tsoratar da ita yanayin da za su kwashe da Dr.Aqeel sosai ta ji ko ina na jikinta yana sanya kwanyarta na kara rikicewa da rigimar da zuciyarta ke hango mata za su kwasa da Dr.Aqeel a maganar nan ya kamata tayi wani tunani dole ne ta nemo hanyar da da zata samawar kanta mafita sannan ta samu cikar fatanta da burinta.
*******
Kai kawo kawai take yi tsakiyar dakin gabadaya ta hargitse yarda ka san wacce ta kwato kanta daga gidan mahaukata hannayenta saman kai sai yamutsa sumar kan ta take yi lokaci-lokaci take tsayawa tana jan numfashi tun da ta dawo gida ta rasa gane kanta maganganun Mariya ne kawai ke yi mata safa da marwa gabadaya take jin kwanyarta na kamawa da wuta ga zuciyarta na ta faman kokarin fallewa da gudu daga kirjinta tashin hankalinta na daɗuwa ji take yi gabadaya duniyar na sauya mata ji take yi kamar ba ita ba.
Saitin katon Mirrow da ke dakin ta isa ta tsaya tana kallon kanta ta cikinsa l fuskarta take shafawa tana runtse idanu gani take yi kamar ba ita ba gani take yi kamar wata Baseerar aka ajje aka dauke ta ainihin.
'Ta ya ya za ta so Dr.Aqeel bayan sun taba soyayya da ƙawarta aminiyarta ta kut-da-kut anya kuwa zata iya zuciyarta take ji kamar ba zata amince ba ji take yi kamar zaman kishi za su yi da Mariya ji take yi kamar in ta amince Mariya zata dauke a maciyar amana a gareta'.
Zuciyarta ce take ta faman dauko mata wannan maganganun suna kara rikita mata lissafi kofar dakin da taji an taba ne ya sanyata saurin juyawa Yah Tareeq ne ya shigo ganin yanayin da take ya sanya shi saurin isowa gareta yana yi mata kallon tuhuma.
"Me ke damun ki Sister?".
Ya fadi yana kokarin riko hannunta da sauri ta ja da baya dafe da kai ta zauna bakin gado tana mai da numfashi harɗe hannaye yayi a kirjinsa yana dubanta cikin wani irin yanayi kafun ya isa kusa da ita ya zauna kan loka din kusa da gadon.
"Tambayarki nake me ke damun ki kin yi mani shiru".
"Yah Tareeq bana jin dadi ne don Allah ka yi shiru bana son surutu".
Da mamaki ya dube ta ganin yanayin da take ciki ya tabbatar masa da gaskiyar abin da tace mikewa yayi yana kokarin fita har ya kai bakin kofa sai kuma ya tsaya gami da juyowa ya dube ta ita ma shi take duba dawowa yayi da baya hakan ya sanyata runtse idanu so take yi ya fita so take yi ta zauna ita kadai zaman kadaici take so kwanyarta take so ta sauke daga hayakin da take yi tana bukatar zaman ita kadai domin samun mafita akan wannan Bahagon lamarin da yake kokarin rikita mata lissafin rayuwa.
Kusa da ita ya zo ya zauna bata ce dashi komai ba har zuwa lokacin idanuwanta a rufe suke tana faman jan numfashi da sauri-sauri.
"Sister wai shin ya maganar nan ta mu ne har yanzu ba ki ce dani komai ba lokaci tafiya yake yi?".
Duban sa tayi ta gefe idanuwanta a zazzare ji take yi kamar ta kwala ihu don haushin abin da yake cewa da ita so yake yi ya sake rikita mata lissafi bayan tashin hankalin da take ciki laɓɓanta ta tura cikin baki ta ciza da karfi har sai da ta dan saki kara ta dube shi sosai sai fama gyaɗa kai take yi.
"Yah Tareeq ka san me nake so da kai?".
Girgiza yayi cikin mutuwa jiki ganin yarda tayi masa maganar.
"Ka taimawa kan ka ka taimaka min ka bar maganar nan don ba zata taba yuwu ba ne Yah Tareeq kayi hakuri ka je ka nemi wata matar amma ba Mariya ba don a halin da ake yanzu bana tunanin za ta iya dubanka har ta anshi tayin ka in har ba so kake yi abubuwa su lalace ba".
Zaro idanu yayi waje sosai gami da mikewa cikin hanzari ya shiga kokarin magana amma Baseera ta dakatar dashi bayan ta mike idanuwanta sun kara kaɗawa sun yi jajir.
"Don Allah na roke ka Yah Tareeq wallahi tallahi abi nan ba zai taba yuwuwa ba kawai bata lokacin mu za muyi sannan kuma kayi dakon son da ba zai yi maka amfani ba sai ma matsala da zai ja maka kawai kayi hakuri ka nemi wata ZABIN ALLAH shine kawai mafita".
Tana gama fadin haka ta koma ragwaf! ta zauna dafe kansa yayi da yaji yana juya masa kamar zai zubda shi ya shiga ambaton Allah a hankali ya fara jin saukin zafin zuciyarsa kallon Baseera yayi yanayin da yake ganinta a ciki ya tabbatar masa da abin da take gaya masa da sauri yaja jiki yana hada hanya ya fice daga cikin dakin dagowa tayi ta dube shi bayan taji alamun ficewarsa ta girgiza kai ta koma ta kwanta....
*KAMALA MINNA*😘😘😘😘
[10/22, 5:24 PM] DEENY MINNA🙋♂: UKU BALA'I
NA.
KAMALA MINNA.
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร.
BABI NA SITTIN DA BIYU
Gabanta take ji yana faduwa sosai da sosai ga wani irin yanayi da take jin gangar jikinta na shiga runtse idanu tayi a daidai lokacin da Umma ta shigo cikin dakin dauke da bokitin Cake da ta gama yi can gefe ta ajje shi sannan ta juyo ta dubi Mariya da tayi shiru kamar wacce ake yiwa wasiyya girgiza kai tayi kafun ta motsa laɓɓanta.
"Kin ga Cake din nan na yau ya bani mamaki kamar ba yarda ake yi ba wallahi yayi albarka sosai".
Ta fadi tana mai zaunawa gefe gudu har zuwa lokacin idanuwan Mariya na buɗe sai faman ajiyar numfashi take yi hannu ta kai saman kirjinta ta dafa gami da buɗe idanuwan nata tana duban Umma.
Murmushin yak'e ta sakar mata kafun ta mike ta iso gareta jikinta a sanyaye.
"Umma jikina nake ji wani iri wallahi ga kirjina sai bugawa yake yi kamar wani abu zai faru dani tun safe nake jin haka".
Dubanta Umma tayi idanuwanta na yawatawa akanta so take yi ta hango wani abu da zai bata ko tabbacin abin da yake damun Mariyar.
"Addu'a kawai zaki tayi Mariya irin haka in yana samun bawa musamman faduwa gaba Innalillahi wa inna ilaihir raji'un ake so ya ta maimaitawa".
Gyaɗa kai tayi tana juyar da ganinta zuwa ga bokitin Cake din sannan ta juyo ta dubi Umma.
"Yayi auki fa a hakan ma na gani...ko da yake Birin gidanmu ba ya nan shiyasa Cake din bai shiga uku ba".
Mariya ta fadi tana murmushi ita ma Umma murmushi tayi don ta gano da Mu'azzam take....
Da gudu ya fado cikin dakin yana hak'i ya fada jikin Umma dukkan su suka dube shi da mamaki dago fuskarsa yayi ya dubi Umma sannan ya dubi Mariya.
"Ga wasu mutane nan a kofar gida su hudu har da masu kayan fulani".
Gaban Mariya ne ya yanke ya fadi kamar yarda yake yi mata tun dazu da sauri ta dubi Umma dafe da kirji yanayin ta ya sauya lokaci guda.
Ita kanta Umma ta ji faduwar gaban sosai don sai da taji cikinta yayi kara zuciyarta na tsalle kamar zata fito waje.
"Wai cewa yayi na zo na sanar daku nan gidan su ka zo daya daga cikin mutanan yace mani haka kuma yana kama da Yah Mariy....".
Wata irin zabura Mariya tayi ta mike kan kafafuwanta idanuwanta a warwaje bugun zuciyarta take ji yana sauyawa sosai haka kawai take ji a jikinta akwai abin da ke faruwa.
Umma kuwa rintse idanu tayi tana ambaton sunayen Allah da dukkan wata addu'a da ta zo mata baki haka kawai ta ji a jikinta akwai kamshin wani abu muhimmi a batun Mu'azzam.
"Yace fa ku zo yanzu Umma".
Ya fadi ya na mai jan hannun Mariya bayan ya tashi daga jikin Umma a hankali Mariya ta shiga bin sa kamar rakumi da ak'ala tana kallon Umma ita kanta Umma rasa abin yi tayi domin gabadaya take jin wata gajiya da kasala ta dirar mata a jiki lokaci guda ga wani bugu da zuciyarta take ta faman yi ba ƙanƙautawa laɓɓanta tashiga motsawa ta na son yi wa Mariya magana amma kamar an dora mata katon dutse a harshe hannunta tayi mata nuni dashi ta dauki mayafi .
Duban jikinta tayi ita sam ta manta ma da kayan dake jikinta a hankali ta kwace kanta daga hannun Mu'azzam ta ja kafafuwanta da take jin su kamar za su zubda ita kasa ta janyo hijabin Umma ta zira ajikinta fita tayi cikin kokarin saita kanta Mu'azzam na gaba tana biye dashi har suka isa soron gidan nan ta ci burki ta tsaya jin yarda zuciyarta take dokawa da sauri-sauri jingina tayi da bango tana mai da numfashi Mu'azzam shi kam idanu ya zuba mata har ta gama shan sharafinta ta taka a hankali suka cigaba da tafiya har suka isa kofar gida sai dai me.
Abin da Mariya ta gani ne ya kusan kashe ta da ranta runtse idanuwanta tayi sosai tana mai daura hannu aka ta kurma ihu gabadaya ta sulale zuwa kasa da sauri suka yo kanta ba wanda ya tabata ganin Babbar mace ce duban Mu'azzam sukayi gabadayan su kafun Baffa yace
"Me ya same ta?".
"Mu'azzam da yayi firi-firi da idanu cikin yanayi na tsorata.
"Yah Mariya".
Ya fadi ai Bello na jin haka ya sake dubanta sosai zuciyarsa da kwamyarsa suka mika shi wani mataki mai tsayin gaske da ya gama shuɗewa sosai yaji wani irin abu ya dokar masa zuciya mai girman gaske.
'Mariya'.
Ya furta hakan a ransa yana sake muntsuka idanunsa yana saukewa akanta juyawa yayi da sauri ya fizgo gorar ruwan dake rataye a jikin Ja'e ya balle kanta ya shiga kwarara mata kamar yarda hawaye lokaci guda suka shiga zubo masa a fuska wani dogon numfashi ta ja gami da buɗe idanunta ganin mutanan dake kanta ya sanyata saurin runtse ido tana furta.
"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un".
Da karfi komai ganin sa take yi kamar ba gaske ba sosai zuciyarta ta tsorata ta sosai take jin jikinta wani iri gani take yi kamar a mafarki ba gaske ba laɓɓanta ta tura cikin bakinta tana cizawa zafin da yake ratsa ta ne ya tabbatar mata da GASKIYAR LAMARI da sauri ta sake ware idanunta.
Fuskar dake saitin ta take kallo fuskar da take hango hawaye suna zuba a samanta fuskar da ta jima tana cigiya fuskar da ta bace mata a rayuwa tsayin shekaru wai ita ce yau take gani kunnuwanta ta rufe da tafukan hanayenta gami da sake runtse idanu zuciyarta na harbawa da wani irin yanayi wanda ba za ta ce ga matsayin da zata ajje shi ba.
"Mariya".
Muryar da ta shuɗe sama da shekaru bakwai ita ce yau take jinta a saitin ta tana ambatar sunanta muryar da tayi kewarta muryar da kullum take yabonta da shi mata albarka yau ita ce ta dawo gareta bayan shuɗewar lokaci.
Wani irin kuka ne taji ya zo mata da saurin ta rufe bakinta amma ina sai da sautin sa ya fita da sauri ta shiga kokarin mikewa amma ina ta kasa gaɓɓanta take ji kamar an doke mata su kamar daga sama taji hannaye da tajima da saninsu sun riko mata kafaɗu cikin wani irin yanayi suna mikar da ita kan kafafuwanta wani numfashi take ja mai tafe da kuka buɗe idanuwanta tayi sa'ilin da taji ana dauke mata hawayen fuska sosai take kallon sa da wani irin yanayi na mamaki da tu'ajibi gani take yi kamar bashi ba gani take yi kamar gizo yake yi mata hannayenta ta shiga dagawa tana kokarin kai fuskarsa amma ta kasa da sauri ta shiga ja da baya tana duban sauran fuskokin wanda bata shaida su ba amma a jikinta take jin wani irin yanayi game da su.
Da gudu tayi cikin gida kamar wacce za a sace a soro suka ci karo da Umma da Mu'azzam a hargitse domin tun lokacin da ya ga ta fadi din nan ya kwasa yayi cikin gida yana kiran Umma.
Kallon ta Umma take yi da wani irin yanayi gabanta take ji yana yankewa yana faduwa hawayen da ta gani a fuskar Mariya ya kara rikita mata lissafi da sauri ta riko hannunta jikinta sai faman ɓari yake yi bakinta na karkarwa.
"Su waye Mariya...tambayarki nake yi su waye?".
Yanayin da take maganar kawai ya isa ya tabbatar maka da cewa sosai take cikin firgici Mariya da ta ga yanayin da Umma ke ciki ya sanyata sake rushewa da kuka kafun ta tsagaita da cewa.
"Umma Allah yasa ba mafarki nake yi ba gaskiya ne Abbana ne...".
Da sauri ta sake ta tana ja da baya gabanta na kara tsananta bugawa kafafuwanta take ji suna lauyewa idanuwanta suna lullubewa lokaci guda taji duniyar na juya mata kwanyarta na ansa kuwwa sosai jingina tayi da bango tana maida numfashi kafun ta zabura kamar wacce aka tsikara tayi hanyan waje da sauri a daidai lokacin shikuma ya sanyo kai cikin gida cikin rashin tsammani suka bangaji juna taga-taga Umma tayi zata fadi dama ba wani karfin jiki take dashi ba da sauri ya rikota gabadaya jikinsu ya dauki wani irin yanayi runtse idanu Umma tayi sosai tana jin yarda jikinta ke ansawa da wasu bakin lamari masu girman gaske gareta.
A hankali ta shiga kokarin buɗe idanuwanta tana saukewa gareshi bakinta dauke da addu'a don gani take yi kamar a mafarki ba gaske ba jikinta na rawa ta dago hannunta tana shafe fuskarsa lokaci guda wasu hawaye suka shiga kwaranyo mata a fuska zuciyarta na kara matsewa kwanyarta take ji kamar za ta kama da wuta a hankali ta zare jikinta daga na shi tana ja da baya kallonsa take yi a yanzu cikin tuhuma shi kansa ya hango hakan da sauri ya dube ta amma ita juyawa tayi tana kokarin komawa cikin gida.
"Tare da su Baffa nake".
Da saurin Maganganun nasa suka bugar mata zuciya da kwanya lokaci guda jinin jikinta da numfashinta sukayi tsayawar wucin gadi ji tayi kamar ba a duniya take ba kunnuwanta sai faman maimaita maganar da Bello yayi suke wani GWAURON NUMFASHI taja da take jin kamar zai fasa mata kirji tsoro ne sosai ya bayyana a gareta maganar take ji kamar ba gaske ba so take yi ta gasgata zuciyarta take jin tana ansawa tana amanna da batun juyawa tayi cikin wani irin yanayi mai wuyar fassaruwa ta dube shi wani kuka mai girma taji yana zuwa mata zuciyarta na buɗe wani wawaken ciwo da ta jima tana jinyarsa.
A hankali ya isa gareta yana riko hannayenta gami da girgiza kai idanuwanta sai faman bin shi da kallo suke komai take ji kamar almara gani take yi ko a cikin barcinta hakan ba zai faru ba amma zuciyarta sai kara karfafa mata guiwa take yi a kan ta yarda.
Mariya da Mu'azzam suka iso garesu kallon kallo suka shiga yi a tsakaninsu Bello na duban su Mariya da Mu'azzam yana kuma duban Umma wacce ta zama wata butun butumi a tsaye zuciyarta take ji tana mikata wani mataki mai girma dauke da tashin hankali da ciwon rai ciwo ne mai girma zuciyarta ta fama mata shi wanda take ta jinyarsa ya kasa warkewa.
Duban Mariya yayi yana son yin magana amma ya kasa wani irin yanayi yake jin kansa a ciki ji yake yi kamar ba shi ba.
Sallamar da su Baffa sukayi ne ya sanya Umma mutuwar tsaye zuciyarta tayi wani bugun da sai da kirjinta ya daga da saurin ta runtse idanun tare da yin cikin gida da sauri sai faman hada hanye take yi.
A daidai lokacin da suka shigo ta karasa shigewa cikin gidan don haka Bello yayi musu jagora suka karasa shiga sai bin gidan suke yi da kallo Baffa na faman gyaɗa kai zuciyarsa na matsewa da ciwon da yake ji yana motsa masa tsayin lokaci wai shine yau a garin Gwada garin da yayi wa kansa alkawarin ba zai taba WAIWAYE izuwa gareshi ba yau shine a ciki a kuma gidan da 'yarsa take aure wacce ita ce silar barin sa garin hawaye idanuwansa suka kawo da sauri ya shafe su ciki da nadamar abin da ya aikata wanda yake jin ya cuci kansa sannan ya cuci 'yarsa.
Har cikin dakin su ka shiga zaune take ta hada kai da kafafuwanta zuciyarta na ta faman harbawa da wani tashin hankali mai girman gaske sallamar da taji Muryar Baffa na yi ne ya kara jefata tashin hankali runtse idanuwanta tayi gami da sake kankame kanta da sauri Mariya ta isa gareta ta zauna gefenta ganin halin da mahaifiyar tata take ciki ya sanya ta duban su Baffa da sukayi carko-carko a tsakar dakin lokaci guda kirjinta taji ya buga kallon Baffa ta shiga yi zuciyarta na dauko mata wani lamari da tunanin mai girma da take son ta tabbatar da gaskiya a kansa can kasar zuciyarta take furta 'Baffa' da sauri ta sake duban Umma sannan ta dubi Baffa zaro idanu tayi waje ta shiga nuna shi da yatsa laɓɓanta sai motsawa suke yi.
"Umma dago kanki wannan kamar Baffanki?".
Mariya ta fadi Muryarta na rawa sosai Baffa da ke tsaye a hankali ya tako ya iso garesu hannun Umma ya riko wanda taji rikon a bazata sosai ta firgita tare da kau da kanta domin bata son kallonsa ta san ita mai laifi ne laifin ta mai girma ne a gareshi.
"HABEEBA!".
Ta ji ya ambaci sunanta da muryar mai laushi wacce rabon da taji ta har ta manta dago kanta tayi wanda sukayi face-gace da hawaye ta sauke a fuskarsa murmushi ta ga yanayi mata hakan ba karamin mamaki ya bata ba bakin ta na rawa.
"Baffa na san ni mai laifi ce ban cancanta ka dube ni ba ban cancan ci ka zo gareni ba Baffa na tuba na san na kuntata maka na san na dasa maka ciwo a zuciya shiyasa tun da na rabu da kai har yau ban samu natsuwa da kwanciyar hankali ba...".
"Habeeba".
Ya sake fadi da muryarsa mai taushi gami da nuna mata alamun tayi shiru hakan yayi matukar bata mamaki wai Baffanta ne haka yau shine yake yi mata magana a cikin salama ba zata taba manta ranar da ya rabu da ita ba ya mikata a hannun Bello yace ya yafeta amma yaushi ne a gareta abun yayi matukar daure mata kai sake runtse idanu tayi don ita har yanzu ba ta yarda wai Baffa da Bello bane a gabanta.
"Habeeba ki daina fadin haka ni Mahaifinki ne nasan na dauki hakkinki na sanya ki cikin damuwa da rashin kwanciyar hankali a dalilin son zuciya irin tawa ina neman afuwanki ki yafe mani nima na yafe miki duk wani laifi da ki kayi mani ga mijin ki nan ya fada min komai".
Wani kuka ne ya sake sarke ta shiga yin sa ba kankautawa ba wanda bai tausaya mata ba cikin dakin Ja'e da Iro su kan su sai da suka ji tausayin yayar ta su gwuiwowinta a kasa take neman afuwan Baffa Mariya da Mu'azzam suma haka suke yi suna taya ta rokon Baffa kamar yarda suka ga tana yi sai da suka shafe tsayin lokaci a haka kafun suka yi shiru nan dakin ya dau shiru.
Baffa ya shiga karanta mata komai da ya faru da Bello don sam! Umma kamar ba tayi maraba dashi ba sosai yayi mata bayani sannan ta yarda shima ya kora mata da irin matsalolin da ya fuskata da irin SIRAƊIN RAYUWA da ya fada sosai Umma tayi kuka jin irin bala'in da mijinta ya fada ciki musamman da taji yace bai san lokacin da ya tafi ya bar su ba shi dai kawai ya tsincin kansa a wani waje ne.
"Wai hayaniyar me nake ji ne cikin dakin nan tun dazu kamar gidan yan barik...".
Guntse sauran maganar ta tayi daidai lokacin da ta daga labule idanuwanta suka sauka kan na Bello da ya kafe ta da idanu hannunsa rungume da Mu'azzam mutuwar tsaye tayi kafun ta dawo hayyacinta tana duban mutannan cikin dakin daya bayan daya idanuwa a warwaje kamar wacce tayi wa sarki karya bakinta ya fara motsi jikinta yana rawa ta shiga fadin.
"Bello dama kana duniyar nan".
Da sauri ya ansata da murmushi a fuskarsa.
"Ga zahiri kin gani Goggo Marka".
Da sauri ta juya tayi waje har tana tuntube dukansu suƙa hada idanusu kowa da abinda ke ransa...
*KAMALA MINNA*😘😘😘😘😘
UKU BALA'I
NA.
KAMALA MINNA
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร.
BABI NA SITTIN DA UKU.
Hajiya Layla ce ta dubeshi a karo na ba adadi zuciyarta na mikata wani mataki na tausayi amma so take yi ta kwace kanta domin sam Dr.Erena ba abin tausayi bane ba abin ma a tsaya ana sauraron batutuwan da yake yi bane na rashin hanyyaci.
sosai zuciyarta take kuna gami da suya kwanyarta take ji tana kokarin kamawa da wuta laɓɓanta ta shiga motsawa tana kokarin yin magana amma ta kasa sai ma wani tari da ya zo mata da sauri ta koma gefe nesa da inda Dr.Erena yake a kwance saman gadon asibiti yana ta faman numfarfashi gabadaya ya sauya daga kamanininsa yayi wani irin baki ga idanuwansa da sukayi jajir sunyo waje sosai bakinsa ya karkace ya koma ɓarin dama fuskarsa gabadaya duk ta mokaɗe.
Tari take yi sosai wanda har sai da ya kaita zaunawa tana dafe da kirjinta hannu daya kuma ta rufe bakinta dashi sosai tarin take jinsa yana mata ciwo daga cikinta har zuwa kirjinta da take ji kamar zai fashe.
Areefa dake zaune can gefe daya takure gabadaya ita kanta tayi zuru-zuru kamar wacce ta tashi daga amai da gudawa mikewa tayi da sauri gami da daukar gorar ruwa ta nufi wajanta gami da riko mata hannu sai dai me? Abin da ta gani ya sanyata saurin ja da baya tana duban hannun Hajiya Layla da ta cire daga bakinta
sosai idanuwanta sukayo waje wani bakin abu ne mai kauri gami da yauk'i yake zubowa daga bakinta runtse idanu Areefa tayi sannan ta buɗe mikar da Hajiya Layla tayi ta kai ta Toilet ta wanke mata baki sannan suka fito.
Gefe guda ta zauna tana ta faman mai da numfashi kamar wacce tayi gudun ceton rai.
Sosai zuciyar Areefa ta karye sosai take jin wani irin abu nayi mata ciwo a zuciyarta tsoro na kara bayyana yanayin da take ganin Hajiya Layla a ciki ba karamin tashin hankali yake saka bata ba tun yau ba ta lura da ita tana cikin matsala amma take boye mata ko tayi mata magana su je asibiti a dubata cewa take yi a,a ta barshi akwai maganin da take sha a da can baya tana dadewa bata yi ba amma yanzu a wuni sai tayi tari yafi a lissafa.
Motsin buɗe kofa ne ya katse mata tunanin zucin da take yi da sauri ta dubi kofar Alhaji Abdulwahaab ne ya shigo fuskarsa a tanke kamar ba a taba halittar fara'a fuskar ta shi ba duban su yayi su duka ganin yanayin da Hajiya Layla ke ciki ya sanya shi tsaida kallonsa a kanta.
"Hajiya Layla ya ya dai na ganki cikin wannan yanayin?".
Girgiza kai tayi ba tare da tace dashi komai ba can gefe yayi ya dauko Remote dake kan loka din gadon asibitin ya shiga Control din Tv bango da yake a kusurwar dakin na dama a can sama a hankali ya shiga canza tasha har ya zo kan tashar NSTV MINNA sannan ya tsaya yana mai maida hannayensa duka baya ya juyo ya dubesu suma shi suke duba bai ce musu komai ba har illa nuni da yayi musu su mai da hankalin su kan labaran da ake yi cikin harshen turanci.
A hankali ka shiga labarai hankalin su na kai har aka zo in da ya kusan kashe su a zaune Areefa ce ta mike da sauri tana nuna Tv da dan yatsarta dake ta faman rawa Company din Dr.Erena na ne aka nuna yan kwana kwana na ta aikin kokarin kashe wutar da take ta faman ci akan sa kamar WUTAR DAJI sosai mutane suka cika wajan sai faman kallo ake yi yan kwanakwana na ta aikin su amma ina kamar kara rura wutar ake yi.
Dr.Erena da yake cikin halin rashin hayyaci da yake Tv din na saitin sa idanuwansa na kan Tv din ganin abin da ake haskowa ya kara rikita masa jiki da sauri ya shiga mutsu-mutsu yana faman kakari yana kokarin daga yatsarsa amma ya kasa dukkan su duban sa suka shiga yi ba wanda ya motsa suka cigaba da kallon su ihun da yake kurmawa ne da wani irin kuka kamar na kare ya kara rikita dakin da sauri Alhaji Abdulwahaab ya kashe TV din tare da komawa gefe ya harɗe hannayensa yana duban su Areefa da hankalin su ya gama tashi.
"Ajiya cikin dare Company ya kama da wuta ba tare da kowa ya sani ba tun misalin karfe biyu na dare a halin da ake yanzu duk masu gadin Company din sun mutu wajajen Asuba ne aka ankara da wutar nan aka sanar da yan kwana-kwana suka iso to dai har zuwa wannan lokacin ba suyi nasarar kashe wutar ba kuma sai kara ci take yi yanzu haka fitar da nayi can na nufa manaja din ne ya kira ni yake sanar dani abin da ke faruwa".
Ya karashe cikin nuna halin-ko-in-kula yana duban Dr.Erena da ya gama ficewa daga hayyacinsa gabadaya ya muttsuke jikinsa yana ta faman kartar fuskarsa.
Jinin da yake zuba a bakinsa ne bakinkirin ga hannayensa da ya saka ya shake wuyansa a hankali ya dinga ihu mai tsananin kara lokaci guda ya tiko kasa yana numfashi kirjinsa na faman dagawa lokaci guda kuma ya tsagaita ya daina motsi gabadaya.
"Kun ga ku tashi mu bar asibitin nan tun kafin wahalar mutumin nan ta kashe mu ai mun yi masa na Allah tunda har muka kawo shi asibiti mukayi jinyarsa ta kwanaki".
Ya fadi yana duban su kafin ya shiga toshe hancinsa wani irin warine yaji ya karaɗe dakin gabadaya da sauri ya juya ya fice ji yayi kan sa na juyawa Hajiya Layla ce ta dubi Areefa da tayi tsaye cikin tsananin tashin hankali ganin yarda Dr.Erena ya koma kamar bashi ba wani irin tsoro da fargaba suka shige ta ta daga hannu tana kokarin nuna shi da sauri Hajiya Layla ta riko mata hannu suka fice daga cikin dakin.
Alhaji Abdulwahaab suka hango tafe da wani likita cikin hanzari ya iso garesu gami da duban su kafin yasaka kai cikin dakin runtse idanu yayi ganin yarda Dr.Erena suffar ta juye ta koma kamar ta kare a hankali ya taka hannunsa toshe da hancinsa jin warin da yake yi dubansa ya shiga yi kafun ya tabo wuyansa sannan ya shiga auna shi sosai ya tsorata ganin baya numfashi sake auna shi yayi domin tabbatar da abin da yake zargi mikewa yayi kan kafafuwansa.
Yana kokarin fita ya ji wani kuka mai kama dana kare ya karaɗe dakin shi kansa sai da ya tsora ta da sauri ya juya ya dube shi gani yayi ya dawo hayyacinsa yana numfashi kusa dashi likitan ya karasa bakinsa ya gani yana motsi magana yake yi amma bata fita sai da yayi tari gami da watso wani bakin jini sannan sunan Areefa ya fito daga bakinsa yana faman nuna kofar waje jikinsa sai karkarwa yake yi juyawa likita yayi ya dubi kofar gami da mikewa ya fita can ya hango su har sun kusan barin bangaren kwala musu kira yayi gabadayan su suka juyo yayi musu nuni da hannu da su dawo.
Ko kallon arzuki ba suyi masa ba sai da yayi musu magiya sannan Areefa da Hajiya Layla suka dawo jan su yayi cikin daki suna shiga suka tadda Dr.Erena magashiyan likita ne ya isa gareshi gami da dago hannunsa ya saki ya fadi ragwaf da dauri ya sake duba sa saidai ina tuni lokaci yayi.
Numfashi ya ja mai karfi gami da mikewa kan kafafuwansa yana duban su gyaɗa kai ya shiga yi.
"Allah yayi masa cikawa".
Zaro idanu sukayi waje gabadayan su kafun Hajiya Layla ta dubi Dr.Erena wani irin yanayi ta ji ta a ciki zuciyarta na kara tsorata wata irin nadama da kaicon wannan rayuwar tayi sosai take jin zuciyarta na mikata wani mataki na tsoro wai yau Dr.Erena ne haka cikin wulakantaccen yanayi cikin yanayin da ko kallonsa ba za ayi ba batare da an kau da kai ba wai yau Dr.Erena na ne haka duniya kenan mai yayi duniya kenan wacce ba ma tabbata ba kuma ba aljanna ba.
Da sauri ta dubi Areefa wacce jikinta ya gama yin sanyi sosai idanuwanta du cika da kwalla hannunta ta kama tana kokarin fidda su daga cikin dakin likitan ne ya tsaida su yana mai fadin.
"Sai ku zo ku dauki gawar ko domin yi mata suttura".
Ko ta kan sa ba su bi ma shima bai damu ba duk a nasa tunanin mutuwarce duk ta ruɗa su haka shimfiɗar gadon ya janyo ya lullube gawar gami da ficewa daga cikin dakin yana jan kofar.
******
Kwance take tayi ruf! da ciki tunanin duniya duk yabi ya dame ta gaɓadaya duniyar take ji ta tsana komai na cikinta ya daina burgeta zuciyarta sosai ta tsorata ba abin da take tunawa sai yarda ta ga Dr.Erena ya koma kamar bashi ba halittarsa gabadaya ta sauya kamar ba ta DAN'ADAM ba Company din sa take tunawa yarda taga yana ci da wuta tunda take a rayuwarta bata taba ganin harshen wuta na tashi kamar igiya ba sai ranar wuta har kore-kore take yi yarda taga ana watsa ruwa amma kamar ana kara rura wutar hakan yayi matukar daure mata kai.
Dafa kafadar da ta ji anyi ne ya sanya ta saurin jan numfashi gami da dawowa hayyacinta mikewa tayi ta zauna tana duban fuskar Hajiya Layla da murmushin yak'e zama tayi bakin gadon itama tana dubanta cikin wani irin yanayi kafun ta ja numfashi ita ma.
"KHAIRIYYA!".
Ta fadi da wata kwantacciyar murya da sauri Areefa ta dubeta jin ta kira sunanta na asali.
"Ya kamata ace kin ajje komai a gefe na sani batun Dr.Erena na ne ke damun ki ba wani abu ba kuma ya kamata ki ajje batun sa agefe shi ai duniyarsa ta kare".
Gyaɗa kai Areefa tayi gami da goge kwallar da ta zubo masa.
"Maama zuciyata nake jin wani iri wallahi babu dadi tsoro nake ji yanayin da na ganshi a ciki".
"Khairiyya kenan ai duk wanda yace zai kauce hanyar Allah yana aikata abin da ransa ke so aiko ba zai taba ganin daidai a rayuwarsa ba kin ga dai Dr.Erena kin ga yarda rayuwarsa ta kare a duniyar nan baki daya kamar ba a taba yin mai sunansa ba kina dai ganin dukiyar da ya tara da kadarori amma ba su yi masa amfani ba kin ga kenan duniyar ma bakidayanta ba komai bane wajan Allah balle kuma bawa da yake a cikinta yake abin da ransa ke so".
Gyaɗa kai Kawai take yi tana jin wani tsoro na kara ratsa mata zuciya da duk wani sashi na jikinta sosai ta firgita da yanayin wannan rayuwa a wannan duniyar.
"in har son zuciya zai zama ado ga dan'adam to tabbas yana cikin gagarin rayuwa in har dan'adam zai daura wa kansa buri na son abun duniya to yana tare da tashin hankali".
ta sake fadi tana riko hannayen Khairiyya idanuwanta na kawo kwalla.
"Khairiyya ki yafe mani na san nayi miki laifi mai girman gaske a filin duniyarki ina da hannu dumu-dumu wajan fadawarki wannan bala'in da kika fuskarta ina mai rokon afuwarki a karo na ba a dadi Khairiyya nayi dana sanin mu'amala da Dr.Erena nayi nadama nayi kaico in da nasan wannan rayuwar zan zaba miki wallahi ba zan taba amincewa da bukatarsa ba...".
Da sauri Khairiyya ta kai hannunta saitin bakinta tana rufewa.
"A,a Maama ki daina fadin haka dama can tun fil'azal ALKALAMIN ƘADDARA ya rubuto min hakan sai ya faru a gareni ba laifin ki a ciki".
Wani kuka ne ya kwacewa Hajiya Layla sake damke hannun Khairiyya tayi tana jin wani irin kauna da sonta na kara ratsa mata zuciya da dukkan gangar jikinta sosai take jin Khairiyya kamar ita ta haife ta.
"Ban san iyaye na ba san nan na rayuwa cikin kazamar rayuwa gashi ni ba aure nayi ba bare na samu wata zuri'a da za su jibance ni ina cikin UKU BALA'I a rayuwa ta Khairiyya...".
Da sauri ta sake rufe mata baki hawaye na wanke mata fuska itama.
"Ki daina fadin haka Maama kina da dangi kina da zuri'a ni duk zan zame miki duk wadannan abubuwan da kika rasa a rayuwa ki dauke ni a matsayin 'Ya Maama ki rikeni har karshen rayuwa mu rayu tare cikin MARAICI da ALKALAMIN ƘADDARA ya zano mana a rayuwar nan tamu".
Sosai ta rungumeta ta matse ta a jikinta wani kuka ne sukeyi gabadayan su mai taba zuciya da ruhi kuka suke yi gabadaya sun fice daga hayyacin su an rasa mai rarrashin dan'uwansa a tsakaninsu sai da sukayi mai isar su sannan Khairiyya ta kokarta tayi shiru tana rarrashin Hajiya Layla wacce kukan nata ya kasa tsagaitawa sai yinsa take yi mai hade da tari kamar ranta zai fita...
*KAMALA MINNA*😘😘😘
[10/24, 9:23 AM] DEENY MINNA🙋♂: UKU BALA'I
NA.
KAMALA MINNA.
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร.
BABI NA SITTIN DA HUDU.
Duban idanuwanta yake yi dauke da wani irin yanayi mai taba zuciyar masoya wanda suka tsumu cikin kugin soyayya da kaunar juna fuskarsa sai kara yalwatuwa take yi da murmushi mai girman gaske janye idanuwansa yayi lokaci guda yana mai da numfashi kafun ya motsa laɓɓansa.
"Mariya kin yi shiru baki ce komai".
Murmushi ita ma tayi gami da tura dan yatsanta guda cikin baki kafun ta shiga kokarin magana.
"Duniyarnan a yanzu jin ta nake kamar ba wanda ya kai ni farinciki a cikinta".
Cikin mamaki da tuhuma yake dubanta jin abin da tace dashi sosai yake ji a zuciyarsa wani iri yanayi musamman yarda ya ga ta saki jiki dashi yau rana daya tana dariya gami da murmushin da yake kokarin hallaka masa zuciya.
"me ke faruwa ne Preety? da alamun zuciyoyi sun kusan barin kunci zuwa farinciki".
Runtse idanu tayi gami da buɗe su sosai akan sa kafun ta juya ta kalli kofar gidansu.
"Mahaifina ya dawo".
Zare idanu yayi cikin mamaki da kuma al'ajabi bakin sa yake motsawa yana son yin magana amma ya kasa wani farinciki ya ke jin kansa a ciki a daidai wannan lokaci da bai taba tsammani ba lokaci guda yaji kamar an watsa shi cikin aljanna don farin cikin da sauri ya kara takowa zuwa gareta kamar zai hade jikinsa da nata da sauri ta ja baya da murmushi afuskarta.
"Are you Seriuos?".
Ya fadi yana mai tallaɓe haɓarsa sai faman zabga murmushi yake yi gyaɗa masa kai tayi da sauri ya juya yana kokarin tunkarar kofar gidan da sauri ta daga masa hannu tana mai sanya idanuwanta cikin nasa.
"Me kenan kake kokarin yi?".
"Oh God! don Allah ki bar ni naje na gan shi kin ji kuwa yarda zuciyata take farin ciki kin ji irin dadin da nake ji a wannan ranar sosai nake jina a wani mataki mai girma wanda na jima ban shige shi ba ZUCIYARMU DAYA ne ni dake abu daya muka zama dole na tayaki farinciki dole na nuna kauna ga yanayin da kike ciki ayanzu".
Yana gama fadin haka ya riko hannayenta ya fara kokarin janta da sauri ta fizge tana dubansa lokaci guda ta daure fuska tamau kamar ba ita bace mai dariya da farinciki yanzu idanuwanta take amfani da su tana tura masa hukuncin kuskuren da yayi a yanzu abin da ta tsana abin da bata so shine yau yayi mata tana soron irin wannan yanayin sam bata so ko numfashi suna hadawa da ɗa namiji domin kuwa sosai ta tsorata dashi musamman ganin halin da Hafsat ta shiga A DALILIN ƊA NAMIJI duk da dai ita har da yardarta da amincewarta domin ba yarda za ayi namiji ya saka mace yin abu dole ba tare da amincewarta.
Sosai ya gane yayi kuskure sosai yake jin kallon da take masa yana bula masa jiki yana yanke masa hukunci mai girma runtse idanu yayi ganin yarda fuskar tata ta sauya a lokaci guda.
"Kiyi hakuri Mariya hakan ba halina bane ban yi da wata manufa ba dokin farincikin ki ne shi ya je fani a wannan matakin da na so aikata kuskure mafi girma a gareki".
Kau da kanta tayi batare da ta ce dashi kala ba ta fara tafiya domin komawa cikin gida shi kansa ya tsorota sosai ganin yanayin da take ciki a hankali ya fara bin ta a baya tana jin ta kunsa amma tayi banza dashi domin kuwa sai ta nuna masa kuskurensa ko da kuwa ba da gangan yayi ba.
Ko da suka isa cikin soro juyowa kawai tayi ta dubeshi ta dauke kanta hakan ya sanya shi saurin tsayawa sai faman ware idanu yake yi yana jin yarda zuciyarsa ke wani irin abu kamar zata faso kirji ta fito waje.
Bai san gangancin da ya kai shi aikata haka ba bai san tsautsayi da ruɗun da ya shige shi ba har ya aikata haka ba yake kokarin yiwa kasan salalar tsiya ya manta rabon da ya ga bacin ran Mariya amma yau daya abi sa kuskuren sa yana kokarin yi wa kansa SAGEGEDUWA...
Motsin da yaji ne ya sanya shi saurin dawowa hayyacinsa daga duniyar tunani Mu'azzam ya gani tsaye hannunsa dauke da babbar sallaya da sauri ya isa gareshi yana kamo hannusa gami da durkusawa gabansa yana kallon sa cikin idanuwansa da wani irin yanayi riko sosai yayi wa Mu'azzam har sai da ya fara mutsu-mutsun kwace kansa.
"Dagaske Abba ya dawo?".
Ya tambayeshi don ya rasa ma abin da zai ce dashi fuskarsa yake kallo kamar ta Mariya sak! Runtse idanu yayi kafun yaja wani dogon numfashi ganin yarda Mu'azzam ke kallon sa kamar a tsora ce.
Sakin sa yayi gami da mikewa ya anshi Sallayar ya shimfida Mu'azzam ya juya yana kokarin komawa ciki ya riko shi gami da jan sa a jikinsa suka zauna kan sallayar.
Sun dauki lokaci a haka Dr.Karami sai faman tambayarsa yake tun yana ɗari-ɗari dashi har ya saki jiki dashi yana bashi labarin abin da ya sani suna cikin haka sai ga Abban ya fito da sauri Dr.Karami ya shiga kokarin mikewa yana sauka daga kan Sallayar yana zubewa cikin girmamawa da ladabi da sauri Abba ya riko shi fuskarsa da murmushi a cikinta.
"Haba Hisham meye kuma haka kake yi sai kace wani karamin yaro tashi ka koma ka zauna".
Ya fadi yana mika masa hannu suyi musabaha amma Dr.Karami sai wani nokewa yake yi yana mai jawo Mu'azzam yana zaunar dashi kan cinyarsa.
Soron ne ya dau shiru na yan dakikai kafun Dr.Karami ya kara kasa da kai cikin murya kasa-kasa ya shiga yi masa jaje akan abin da ya faru.
"Bakomai Hisham komai da ka ga ya faru a duniyar nan to dama tun fil'azal Allah ya rubuto shi a KUNDIN ƘADDARARMU".
Ya nisa gami da sake duban Dr.Karami sosai, da kansa ke kasa wata kunya ce yaji ta lullube shi tun da yake bai taba yin haka ba yau ce rana ta farko duk sai ya jishi wani banbarakwai.
"Ban san da bakin da zance da kai komai ba, ban san da wasu irin kalamai zan yi maka godiya ba, Hisham kayi mani komai a rayuwa kayi mani abin da ko dangina da yan'uwana bana tunanin akwai wanda zai iya hakan. Sosai naji dadi sosai naji farin ciki zuciyata ta jima tana kuna da takaici acan cikin wahalar da na tsinci kai na ban damu da tawa rayuwar ba sai ta IYALINA sosai nayi kuka nayi bakin ciki akan rashin basu kariya a ga rayuwarsu musamman a yarda na bar su na shiga tashin hankali tashin hankali mai girman gaske na tsani kai na tsani rayuwar da nayi dalilin ban san halin da IYALINA suke ciki ba...".
"Abba da ka daina TUNA BAYA abin da ya wuce ya rigaya ya wuce kuma komai ya faru damu a duniyar nan ALKALAMIN ƘADDARA ne sila ba a son ranka komai ya faru ba ba wai kayi haka bane da wata manufa Allah ya ƙaddara sai ka je wani wajan ka rayu akwai abin da Allah ya gani ya sanya ya turaka wata duniyar kayi rayuwa".
Dr.Karami ya fadi muryarsa can kasa sai faman wasa yake yi da yatsun hannun Mu'azzam.
Hawaye Abba ya goge wanda bai san sun zubo masa ba sai da ya ji dumin su a hankali ya shiga baiwa Dr.Karami labarin rayuwar da ya tsinci kan sa har izuwa haduwarsu da Baffa...
Sosai ya ji zuciyarsa wani iri sosai yaji tausayin su Mariya ya kamashi dago kai yayi ya dubi Abba da idanuwansa ke ta faman ZUBAR KWALLA zuciyarsa yaji tana kara matsewa da kaunar ahalin nan masu ciki da SADAUKARWA da kaunar juna su musamman yarda yaji AKAN SO suka fada wannan rayuwar su dukan su ashe haka akewa SO BIYAYYA ashe haka ake sadauƙar da komai da kowa a rungumi masoyi ashe shi bai ma yi so ba.
Numfashi yaja mai karfi yana sake duban Abba wanda ya shafe fuskarsa kamar bai yi kukan ba sosai yake duban Dr.Karami yana jin wata kaunarsa na ratsa masa zuciya sosai yake jin zai iya yarda ya zama mijin 'yarsa domin ya yi amanna dashi da kuma irin nagartarsa ya tabbata 'yarsa ba zata koka ba a gidan sa so yake yi yayi masa magana amma ya kasa so yake yi yaji daga bakin sa in har ya furta KALMAR SO ga Mariya shi kuwa zai masa tukuici da ita.
A hankali Dr.Karami ya shiga kokarin tashi alamun tafiya sallama sukayi ya mike har zuwa lokacin Mu'azzam na like dashi hannu ya saka ya zaro kudi masu dan dama ya ajje kan sallayar ya juya yana kokarin tafiya.
"HISHAM!".
Yaji Abba da wata irin muryar mai girma da zurfi a jikinsa yake ji kamar akwai abin da yayi ba daidai ba da sauri ya juyo ya dubi Abba kallon da ya ga yanayi masa yayi matukar bugar masa da zuciya sai dai murmushin da ya gani kuma ya bashi mamaki.
"Zo ka dauki kudin ka don Allah".
Ya fadi shima yana mikewa yana kara faɗaɗa murmushin sa, kuri yayi masa da idanu wani irin kwarjini ya ga yanayi masa magana yake so yayi amma ya kasa a hankali ya ja kafafuwansa ya iso gami da sanya hannu ya dauki kuɗaɗen.
"Abba kayi Hakuri...".
"Bakomai Hisham hidimar za tayi yawa ka gaishe da Hajiyar taka".
Ya fadi yana mai juyawa ya koma cikin gida cike da farin ciki da kwanciyar hankali yarda yaga halayen Dr.Karami dama tuni Umma duk ta karance masa komai da komai da yake faruwa.
Dr.Karami hannusa rike da na Mu'azzam suka isa bakin motarsa ya buɗe wata katuwar leda ya dauko ya mika masa kafun ya sake dauko wata ya bashi.
"Wannan taka ce kai kadai ko Yah Mariya karka baiwa wannan kuma Umma za ka kaiwa".
Dariya yayi gami da fadin 'Nagode' sannan ya juya ya fara tafiya yana daga masa hannu shima hannu yake daga masa yana jin kaunar wannan Iyalin na kara ratsa masa zuciya da ruhinsa..
*****
Da mamaki yake dubanta zuciyarsa na yayyagewa da tashin hankali bai taba zaton abin da zata fada masa ba kenan bai taba zaton in ya zo abin da zai tadda ba kenan in da yasan wannan bakar maganar zai tadda da bai zo ba zuciyarsa kara matsewa take yi da tashin hankali idanuwansa sun kaɗa sun yi ja duk wani farinciki da ya jima yana yi tun da yaji ta sanar dashi dawowar mahaifinta har rawar jiki yake yi wajan zuwa taya ta murna sai dai ashe ba nan gizo ke sakar ba.
numfashi yake ja wanda yake jin sa kamar zai tafi masa da ransa duban ta yasake yi karo ba adadi kanta akasa yake yana hango yarda hawaye ke zubowa saman kuncin ta wani irim rauni ya sake jin zuciyarsa tana kara mikashi a ciki, hannayensa duk biyu ya dafe kansa dashi da yake jin yana faman kumbura kamar zai tarwatse laɓɓasa ya tura cikin bakin sa yana cizawa.
"Mariya dama bakya so na dama duk BIYAYYAR SO da nake yi akan ki ta banza ce ashe akwai ranar da zaki nuna min iyakata haba! Mariya don Allah karki ce dani wannan maganar gaskiya ce don Allah ki ce wasa kike yi".
Ya fadi yana jin duniyar na kara yamutse masa da wani irin tashin hankali mai girman gaske dago idanuwanta tayi wanda suka kaɗa sukayi jajir bakin ta sai rawa yake yi hannayenta dafe da kirjnta da take ji kamar zai tarwatse ita kanta ta san tayi ganganci ba ta san abin da yasa ta aikata hakan ba abin da take gudu kenan nayin BUTULCI ga Dr.Aqeel ta san batayi masa adalci ba batayi wa ita kanta adalci ba numfashi ta ja kafun ta sake dubansa sosai.
"Kayi hakuri Dr.Aqeel ban yi haka don na tsane ka ba hasali ma ni ce mai son ka da kaunar k...".
"Ya isa haka ki daina yiwa so karya akai na kawai ki fito fili kice bani kike so ba wani na kike so".
Runtse idanu tayi tana jin sautin muryarsa mai sauti tana dukan zuciyarta da kwanyarta wani kuka ne ya kwace mata da sauri ta rufe bakinta jikinta ya shiga rawa numfashinta ya shiga tsittsinkewa hakan da Dr.Aqeel ya gani ya kara rikita shi da sauri ya iso gareta ji yake yi kamar ya rikota ya hadata da jikinsa ya rarrashe ta.
"Kayi hakuri na san ban kyauta maka ba na san naci amanar soyayyarmu amma ina so ka dube ni da idon basira sannan ka fahimce ni ban yi haka don in tozarta ka ba ban yi haka don ba na son ka ba in da bana son ka ba yarda za ayi har nake tsayuwa da kai in da bana son ka ba yarda za ayi na bar zuciyata ta kauna ce ka ka sani ni da Baseera abu daya ne duk wani abu da kake tsammanin zaka samu gareni na kulawa da biyayya a soyayarka zaka samu a gareta fiye ma da haka hasali ma Baseera tafi ni komai da komai na rayuwa ina rokonka don Allah don Annabi ka dauki Baseera kamar yarda kake dauka ta ka sannan ina so kayi mata so kamar yarda kake yi mani koma fiye da hakan don Allah na roke ka in har son da kake yi mani kana so na kara gasgata shi to ina so ka komar dashi kanta".
Ta fadi cikin rawar murya a hankali ta shiga ja da baya idanuwanta na kara ballewa da hawaye hannu ta daga masa kafun ta juya cikin sauri ta fada cikin gida.
Runtse idanu yayi maganganunta yake ji suna yi masa yawo akai zuciyarsa yake ji tana kara matsewa da kalamanta da sauri ya ja jiki kafafuwansa yake ji suna harɗewa kamar za su zubda shi kasa ya fada cikin motarsa tare da yi mata key ya fizgeta ya fice daga cikin unguwar zuciyarsa na wani irin mataki wanda ba zai ce gashi ba...
*Kamala Minna*😘😘😘
[10/25, 9:41 AM] DEENY MINNA🙋♂: UKU BALA'I
NA.
KAMALA MINNA.
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร.
BABI NA SITTIN DA BIYAR
Sosai ya kasa gane kansa komai yake jinsa yana sauya masa lokaci guda zuciyarsa yake ji tana harbawa da wani irin yanayi mai raɗaɗi a zuciya bai san yarda zai yi ba bai san abin da ya kamata yayi ba zuciyarsa ta cushe kwanyarsa sai hayaki take yi kamar zata kama da wuta duniyar gabadaya yake ji tana kai komo dashi jin sa yake kamar bashi ba kamar wani daban aka dauko aka ajje.
Numfashi yasake ja karo na ba a dadi yau kusan kwana uku kenan yana jinyar kansa kokari yake yi ya saita kansa amma hakan ya gagara zuciyarsa taki amanna akan abin da ake so yayi sosai yake jin GURBIN SO mai girma wanda ya baiwa Mariya ba zai iya barinsa ya so wata daban ba baya tunanin hakan zai iya kasantuwa son Mariya ta zama komai nashi ita ce rayuwarsa dama numfashin sa baya tunanin rayuwarsa zata yi karko in har ba soyayyar Mariya bace tadawo gareshi sosai yake kallon kansa a matsayin GAWA DA RAI.
Hannayensa duka biyu ya dafe kansa da su yana faman jan numfashi mikewa yayi kan gadon yayi zaman dirshan gami da zabga tagumi yawatawa ya shiga yi da idanuwansa komai gani yake yi yana sauya masa komai yake ganin baya burgesa a filin duniyar nan komai yake ji kamar ciwo ne a gareshi zuciyarsa yake ji tana matsewa da wani irin tashin hankali mai girman gaske ji yake yi ko wani sashi da lungu na zuciyarsa na kara yayyagewa da son Mariya kokari yake yi ko zai iya abun da ta bukata amma ji yake yi kamar kara rura wutar sonta ake yi a zuciyarsa.
A hankali ya zuro kafafuwansa zuwa kasa ya mike akan su jikinsa sanye da kayan barci farare masu dingo blue maballin gaban rigar ya gyara da ya fice ya zura silifas din dake yashe a kasa toilet ya nufa cikin rashin kwarin jiki da na zuciya.
Yana shiga ya sakarwa kansa shawa mai ruwan dumi sosai yake jin ruwan na ratse shi ta ko ina zuciyarsa dake zafi yake jin tana sauka kadan-kadan runtse idanuwansa yayi yana furta.
"Yaa Hayyu Yaa Kayyum".
Kusan minti ashirin ya shafe a toilet din kafun ya wanke bakinsa gami da dauro tawul a kugunsa da wani kuma a hannunsa yana tsane kansa da sajen fuskarsa da yake karawa fuskart asa kyau da kwarjini fitowa yayi ya tsaya gaban Mirrow yana kallon kansa sosai yake hango ramar da yayi shi kadai ya san wahalar da yake sha shi kadai ya san azabar da zuciyarsa take kawo masa gabadaya ya daina jin dadin komai WALWALAR ZUCIYA gabadaya yanzu bai samunta har ya manta yaushe rabonsa ya jidadi da nishadi a duniyarsa.
Numfashi ya ja gami da juyawa ya nufi sif din dake manne da bangon dakin buɗewa yayi yana kallon ko wani sashi na cikin sa kaya ne makil a cikinsa a shirye hannu ya sa ya shiga dagawa yana kallo so yake yi ya zabi wanda zai saka amma gabadaya kayan ma jin su yake yi wani iri ya jima a tsaye yana zarowa yana mai dawa ya rasa wanda zai dauko lokaci kankani duk ya yamotse sif din kafin ya zaro wani lallausar yaɗi light-blue mai dikon dark anyi masa dinkin zamani wanda ya fita sosai.
Bakin gado ya ajje su sannan ya juya ya koma wajan Mirrow din fuskarsa ya dan gyara sannan ya koma ya zura kayan a jikinsa wanda sukayi matukar hawan sa sosai suka kara fidda masa da kyansa gami da kwarji agogon Rolex ya daura a hannunsa gami da kafa hularsa wacce ta hau kayan sosai takalmin kafarsa sau ciki baki sai daukar idanu yake yi glass ya saka a idanuwansa wanda ya kara sirrinta yanayin da yake ciki.
Key din motarsa ya dauka gami da wayoyin sa bayan ya feshe jikinsa da daɗaɗar turarurruka masu sanyin kamshi a hankali ya shiga taka kafafuwanta yanayin sa kadai zai nuna maka ba ya cikin nishadin zuciya saidai cikar halintarsa da mazatakarsa da ka kalla zaka gane namiji hadadde mai ansa sunan sa na mijin.
Kokari yake yi ya aikata abin da zuciyarsa take hana shi so yake yi ya koyi wannan rayuwar da aka zaɓar masa bashi ya zaɓa ba so yake yi ya koyi rayuwar da ake cewa ba zai yi nadama akan ta ba so yake yi ya matse zuciyarsa ta koyi abin da ake so ta koya so yake yi a wannan ranar komai ya canza so yake yi zuciyarsa da koyi kaunar wacce ake so ya mikawa soyayayarsa ya sani SO ƘADDARAR ZUCIYA ne so ne kadai ke wahalar da ita ya sata cikin duk wani kunci da gangar jiki zai wahala shi ma.
Da wannan tunanin ya isa gaban sabuwar motarsa kirar Benz mai kalar baki sai faman daukar idanu take yi sai da ya kare mata kallo yau ne rana ta biyu da zai hau ta tun da yayo odarta haka kawai yaji yana bukatar ya fita da ita daga can nesa ya hango mai gadin sa hannu ya daga masa da gudu ya iso gareshi yana mai kwasar gaisuwa kafun ya mike ya nufi wajan Get ya hangame shi a daidai lokacin shi kuma Dr.Aqeel ya shige motar har yayi mata key ya doshi Get din a hankali har ya fice mai gadi nayi masa a dawo lafiya sannan ya mai da Get din ya rufe.
****
Gabanta ne ya yanke ya fadi sallamar da tayi ba ta karasa ta ba taja burki ta tsaya sai faman rarraba idanu take yi shi kuwa ya kafe ta da idanu kamar zai haɗiyeta hakan ya kara rikita mata lissafi ji tayi kamar ta juya ta falle da gudu amma jin muryar Hajiya ya sanyataa motsa kafafuwanta da take jin su kamar za su zubda ita kasa a hankali ta shiga takawa tana karasa cikin falon ko ina na jikinta rawa kawai yake yi ga wani dokawa da gabanta ke yi musamman irin kallon da ta ga Tareeq na yi mata kau da kai tayi shiyasa sam bata son zuwa gidan nan ko don saboda shi ba ta son irin abin da yake yi mata.
"Ina yini Mami".
Mariya ta fadi bayan ta isa gareta ta zauna.
"Lafiya lau Mariya ya gida ya su Umman taki da Abban naki?".
Gyaɗa kai tayi kafun ta ansa da cewa.
"Lafiya lau duk suna gaishe ku".
Daga nan bata sake tsinkawa ba sai Mami ce ta sake cewa.
"Shekaran jiya ai mun je kina Islamiyya ba mu tadda ki ba".
Murmushi tayi gami da kokarin mikewa.
"Umma ta gaya min Mami Allah ya saka da alheri ya kara buɗe gami da rufin asiri...".
"Mariya kar ki sake kin ji ko ai mun zama daya komai aka yi muku a gidan nan ai ba faduwa bane kun zama yan uwanmu mu ma haka duk an zama abu daya...mutuniyar taki tana ciki kisan dai san halinta kullum tana kunshe a daki kamar mai zaman takaba".
Dariya ta sake yi sannan cikin hanzari ta nufi sama sashin Baseera zaune ta same ta hannunta rike da littafi da sauri ta karasa kusa da ita ta zauna sam hankalinta ba ya jikinta domin tunani take yi ba wai karatun littafin ba da sauri Mariya ta zungurar mata kafaɗa a firgice ta dube ta ganin Mariya ya sanyata zaro idanu waje tana mai da numfashi ta shiga motsa laɓɓanta tana son yin magana amma ta kasa.
"Kin kyauta Baseera wato shi ne kika dauke mani kafa ko kirana ma da kike yi a wayar Umma kin daina sabida na yi miki laifi mai girma ko har da ya kai kiyi mani hukunci irin haka....Hmm Hakuri na zo na baki akan abin da nayi miki ba daidai...".
Da sauri Baseera ta rufe mata baki wasu kwalla na taruwa a idanunta ta shiga girgiza kai .
"Ba haka bane wallahi ba na jindadi ne...".
Turo kofar da akayi ne ya sanya Baseera saurin yin shiru tana goge fuskarta Mami ce ta shigo duban su tayi ganin yanayin da suke ciki batare da tace komai ba sosai suka gane kallon zargin wani abu take yi musu.
"Baseera kin yi bako".
Abin da ta fadi kenan ta fice daga cikin dakin gaban Baseera ya buga gami da duban Mariya da ita ma idanuwanta suke kanta kallan kallo suke yi wa juna kafun Mariya tayi murmushi tana mai dafa kafaɗarta.
"Kin yi bako aka ce".
Runtse idanu Baseera tayi tana jin yarda gabanta ke yankewa ya na faduwa.
"Ban san waye ba Mariya ba muyi da wani zai zo waje na...".
Daga mata hannu tayi tare da mikewa tana kamo kafarta doguwar riga ce a jikinta don haka ta janyo mata gyalan rigar ta yafa mata fuskarta ba wata baci tayi ba don haka ta ja hannunta suka fice.
A harabar gidan suka hango mota girke da sauri suka dubi juna gaban Mariya ne ya fadi tana tunano inda ta san motar nan sosai ta ke ji a ranta ta taba ganinta amma ta rasa waye mai ita...
Bata gama tunanin tuno mai motar ba ta ga an buɗe kofar ana kokarin fitowa da sauri ta runtse idanu jin yarda kirjinta ya doka rikon da taji Baseera tayi mata ne jikinta na karkarwa tana jin yarda take kokarin yi mata magana amma ta kasa hakan ya tabbatar mata da zarginta da sauri ta zare hannunta daga na Baseera tana kokarin juyawa ta koma ciki amma jin amon muryar sa ya sanyata tsayawa cak! tana mai da numfashi takun takalminsa da yake tunkaro su hakan ya kara rikita mata lissafi ta kara danke idanuwanta kamshin turarensa take ji ya dokar mata hanci zuciyarta take ji tana matsewa da wani irin yanayi tana mikata wani mataki bata san ya za tayi ba bata san da wani idanu zata kalle shi ba sosai take jin rashin adalcin da tayi masa a ranta haka kawai take jin wata kunyarsa ta ratsa ta.
"Gani na zo domin yiwa so biyayya Mariya abin da kika bukata shi na zo yi domin tabbatar da abin da kike tsammanin ba haka bane".
Wata irin bugawa taji zuciyarta tayi da sauri ta juyo gami da buɗe idanuwanta da suka kaɗa sosai ta dubi Baseera da tayi fakare da idanu tana dubansu daya bayan daya zuciyarta na bugawa da tashin hankali ashe da gaske Mariya take ashe abinda take faɗi mata zatayi ashe zata yi din da gaske.
girgiza kai ta shiga yi tana saka idanuwanta cikin na Mariya da ta gama shiga wani yanayi mai wuyar fassaruwa.
"Ban gane ba Mariya mai hakan ke nufi?".
"Soyayyarta ta sadaukar gareki".
Zare idanu Baseera fuskarta da wani irin yanayi mai girma a zuciyarta sosai take jin zuciyarta na matsewa da tashin hankali maganganun Dr.Aqeel take jin su wani iri a gareta sosai take jin suna hawa mata kai hannunta taji Mariya ta kama ta damke sosai da sauri ta dago ta dube ta idanuwanta ta gani cike da hawaye suna kokarim zuba.
"Kin yi mani alkawari in har ya amince ke ma zaki amince don Allah karki watsa min kasa a idanu Baseera ki dubi Dr.Aqeel a matsayin masoyi mai kaunarki tsakani da Allah kiyi mani wannan sadaukarwar don Allah ban taba neman alfarma gareki ba sai yau don Allah ki anshe ta".
Fizge hannunta Baseera tayi tana mai da numfashi zuciyarta take ji tana bugawa da wani irin yanayi.
"A,a Mariya ba na tunanin hakan za ta faru karki takurawa zuciyoyin da ba sa kaunar junansu karki yi kokarin hada abin da kika san ba zai taba faruwa ba karki hada abin da kika san zuciyoyi ba za su samu farin ciki ba".
Ta fadi muryarta na rawa wasu hawaye na zubo mata a hankali ta shiga ja da baya tana girgiza kai.
A daidai lokacin shi kuma Dr.Aqeel ya kara takowa kusa da su sosai zuciyarsa yake ji tana matsewa da kuna gami da radadi runtse idanu yayi kafun ya buɗe su akan Mariya wacce gabadaya ta gama shiga wani yanayi idanu suka hada tayi saurin dauke nata zuciyarta na harbawa da sauri-sauri.
"BASEERA!".
muryar Dr.Aqeel ta doki kunnuwanta sautin na ansawa a kwanyar zuciyarta na buɗewa sosai tsayawa tayi cak! tana mai da numfashi kafun ta dube shi kallonta yake yi da wani irin yanayi wanda ba zata ce ga matsayin da zata ajje shi ba.
"Na anshi soyayarki in har zaki iya bani nima zan baki zuciyata gabadayanta".
Ya fadi yana mai runtse idanuwansa zuciyarsa yake ji tana matsewa da wani irin yanayi mai kokarin haifar da bugun zuciyar sosai yake jin idanuwansa na zafi da raɗaɗi ko ina na jikinsa yake jin lokaci guda ya tsaya jinin jikinsa yake ji ya shiga gudu da sauri-sauri kwanyarsa yake ji tana hayaki kamar zata kama da wuta.
Mariya kuwa mutuwar tsaye tayi ba abin da take fadi sai 'Innalillahi wa inna ilaihir raji'un' wata katangar tashin hankali ne taji ta rikito mata hannayensa duk biyun ta saka ta dafe kirjinta da take jin yana barazanar tarwatsewa kanta taji ya shiga dokawa kamar zai rabe biyu muryar Dr.Aqeel da taji yana furta kalaman so jin saukar su take kamar garwashi wuta runtse idanu tayi gami da kokarin saita kanta kafun ta taka kafafuwanta da take jin su kamar za su watsar da ita kasa hannayenta ta kamo ta sarke a cikin nata.
Idanuwansu suka sarke da juna murmushi Mariya tayi mai tafe da hawaye.
"Ki amince ke ma Baseera zuciyoyinku su kasance waje daya su rayu tare su zama abu daya har gaban abada".
Girgiza kai Baseera ta shiga yi idanuwanta na kara ballewa da hawaye a hankali ta zare hannayenta gami da duban inda Dr.Aqeel yake wani kallo tayi masa kafun ta juya cikin hanzari tayi cikin gida.
Mai da numfashi Mariya tayi tare da duban Dr.Aqeel shima ita yake kallo kafun ya girgiza kai yana cizon laɓɓa wani murmushi yayi tare da juyawa ya nufi motarsa...
*Kamala Minna*💞💞💞💞
[10/25, 5:38 PM] DEENY MINNA🙋♂: UKU BALA'I
NA.
KAMALA MINNA.
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร.
BABI NA NA SITTIN DA SHIDA
A hankali take tafiya kanta akasa ga wani zundumemen Hijabi da ta saka a jikinta har yana sharar kasa hannayenta cikin hijabin sai wasa da su take yi.
Kallo daya zaka yi mata ka gano yanayin rashin kwanciyar hankali a tattare da ita fuskarta tayi fari sosai ga wata rama da ta zabga kamar wacce tayi ciwon shekara guda.
Ratso layin take yi tana bin gefe mutane sai binta da kallo suke yi kamar sun ga watan ramadana sosai take jin zuciyarta na zafi da raɗaɗin wannan fitowar da tayi bata taba zaton zata tsani kanta ba sai a cikin wannan kwanakin da fita ma gagararta take yi in kuwa ta fito an dinga zundenta kenan ana nuna ta da baki wasu har tararta suke suna gaya mata magana son ransu sai dai ba yarda zatayi ita ta jawo wa kanta.
Cikin wannan yanayin ba zato ba tsammani taji an janyo mata hijabi ta baya wata irin dokawa taji gabanta yayi zuciyarta harba da sauri ta dago kanta cikin wani irin yanayi na tsoro da firgici dubansa take yi tun daga kasa har sama bata san shi ba bata san daga ina yake ba.
"Ke ba kya ganin mutane ana yi maki magana kin yi banza da mutane iye wacece ke dan kan...".
Ya lailayo ashar ya dire gami da daga hannunsa daya yana kokari kife ta da mari mai ya gani kuma sai ya sauke yana mai da numfashi.
Sosai tsoro ya bayyana a fuskarta a hankali ta shiga ja da baya tana raɓashi zata wuce don ta lura dan iskan gari ne dan kwaya in ba don haka ba ai bai isa yayi mata wannan cin mutuncin ba ta kyaleshi da sai ta keta masa rashin mutunci amma halin da take yanzu ba zata iya ba duk da zafi da raɗaɗin da zuciyarta ke yi akan zagin kare dangin da yayi mata.
Sake fizgo mata hijabin yayi ganin tana kokarin raɓashi ta wuce ya tsaya dab da ita har suna shakar numfashin juna ba abin da ke tashi a jikinsa sai warin solisho da sukuɗaye kau da kai tayi da sauri gami da toshe hanci wani yinkuri taji zuciyarta ta nayi tana kokarin yin amai.
Ganin abin da take yi masa yasanya shi duban fuskarta da take yatsine masa tana toshe hanci wata irin ashariya ya danna mata gami da cafko hijabin jikinta ya cikuikuye.
"Ke dan kan uban ki ni kike toshewa hanci to ubanki ne ke wari ba ni ba matsiyaciya karuwan banza da wofi".
Yana fadin haka ya fizge hibajin gabadaya daga jikinta daga ita sai zani da ves ga katon cikinta da ya fito sosai wanda haihuwarsa nan kurkusa runtse idanu tayi gami da toshe kunnuwanta wani kuka ne ya zo mata da sauri ta durkushe tana mai sakin sa shi kuwa sai faman danna mata ashar yake yi.
Lokaci kankani mutanan layin duk suka taru aka rasa wanda zai zo ya kwace ta domin kuwa suna tsoron TANGA ba wanda bai sanshi ba a fadin garin nan tattarin dan jagaliya ne kashe mutum a wajansa ba komai bane yayi zaman gidan kaso yafi a lissafa a fitowa dashi.
"In kana yiwa Allah da Annabi ka bani hijabi na".
Ta fadi cikin muryar kuka jikinta sai rawa yake yi wani takaici take ji a zuciya ji take kamar ta hadiye zuciyar ta mace.
Cilli yayi da hijabin da sauri ta rarrafa za ta dauka ya danne mata yatsun hannu ta kurma uban ihu a daidai lokacin motar Dr.Karami ta sanyo kai ganin abin dake faruwa a layin ya sanya shi taka burki ya fito da sauri yana duban mutanan da sukayi cirko-cirko suna kallon rigimar Hafsat da Tanga da sauri ya isa wajan sam bai san wacece ba amma ganin irin cin zarafin da ake yi mata ya sanya shi zuwa ya hankaɗe tanga a daidai lokacin ita kuma Hafsat ta dago kai.
'Innalillahi' abin da Dr.Karami ya furta kenan yana ja da baya duban ta yayi kafin cikin hanzari ya isa ya dauko mata hijabin nata ya yafa mata a jikinta cikin sauri duban mamaki yake mata da al'ajabai ganin yarda ta koma kamar ba ita ba.
"Hafsat me ya hadaki da wannan mutumin har yayi miki wannan cin zarafin?".
Girgiza kai kawai take yi zuciyarta na suya hawaye sai ambaliya suke yi mata a fuska numfashi taja mai cike da takaici ta mike kan kafafuwanta ta dubi Tanga sannan ta dubi Dr.Karami a hankali ta raɓashi zata wuce gabanta ya sha yana mai sake tambayarta amma ta kasa bashi ansa kuka kawai take yi abin duniya ya yi mata yawa abin da bata so a gane yau gashi a bainar jama'a kowa ya gani kuma ya san halin da take ciki dama an dade ana zarginta yau dai gashi zargin ya tabbata kowa zai tsine mata da kazamar rayuwar da ta zaɓawa kanta wanda take ciwa mutunci take yi wa kallon banza ta sani yau sai sun zuba ruwa aka sun sha.
Ihun da taji ne ya katse mata dogon tunanin da take yi cikin razana ta juya Dr.Karami ta hanga ya cakumi Tanga sai jibgarsa yake yi gabadaya ya kumbura masa fuska bakinsa har ya fashe yana zubda jini ware idanu tayi mamaki ya sake cikata da sauri ta ja jiki ganin hankalin mutane ya bar kanta ya koma wajan su Dr.Karami.
Tafiya take yi cikin sauri-sauri kamar zata kifa hijabin sai harɗe ta yake yi tattareshi tayi sosai ta rike a hannu ta shiga jefa kafarta a duk in da taji ta dira idanuwanta sun kara kaɗawa sun yi jajir tana kokarin karya kwanar da zata shigar da ita gida suka yi arba da Abulle kallo ta bita dashi daga sama har kasa kafun ta dauke kanta cike da takaici da bakin cikin wannan rayuwar da 'yarta ta tsinci kanta a ciki Allah na gani tayi bakin ciki tayi takaici tayi kuka sosai a kan wannan lamarin zuciyarta ji take yi kamar za ta soye don raɗaɗin da take ji tun da abin nan ya faru ta kasa kwanciyar hankali kullum cikin fargaba take akan abin da zai je ya dawo.
"Daga ina kike?".
Ta fadi fuskarta a daure tamau kamar bata taba yin dariya ba ba alamun tausayi amma in da zaka fasa zuciyarta tausayin 'yar ta ta ne makil a cikinta.
Girgiza kai Hafsat tayi hawaye na sake balle mata sautin kukan da take boyewa ya bayyana sosai hakan ya kara tayar da hankalin Abulle da sauri ta riko mata hannu tana mai tambayar ta cikin yanayi na firgici amma ta kasa magana sai girgiza mata kai take yi tana kai hannayenta saman bakinta tana toshewa.
Riko ta tayi sosai ta sanyata gaba suka nufi gida tafiya suke yi gabadayan su zuciyoyinsu na suya musamman Hafsat in ta tuna cin zarafin da akayi mata a bainar jama'a sai ta sake rushewa da kuka kamar numfashinta zai dauke a soro suka ya da zango Abulle sai mai da numfashi take yi ita kuwa Hafsat zubewa kan gwuiwowinta tayi ta rufe fuskarta da tafukan hannayenta tana hadiyar zuciya sai shassheka take yi idanuwan nan nata sunyi luhu-luhu jikinta na faman kyarma.
"Ya isa haka Hafsat dai na kukan fada min abin dake faruwa?".
Dago jajayen idanuwanta tayi ta sauke su kan Abulle cikin wani irin yanayi muryarta na rawa ta shiga bata labarin abin da ya faru da ita a yanzu...
Wani kuka ne ya sake kufce mata ta rarrafo ta riko mata kafa.
"Don Allah Umma ki yafe mani na tuba wallahi ba zan sake ba ina cikin bala'in rayuwa ita cikin kazamar rayuwa wacce ni ne na zama silar faɗawa cikin ta don Allah ku yafe mani abin da nayi muku na san ban kyauta muku ba a matsayin ku na iyaye na...".
Da sauri Abulle ta toshe mata baki tana mai duba kofar gidan da soron gidan ganin ba kowa ya sanyata duban Hafsat wacce gabadaya ta fice daga hayyacinta.
"Hafsat kukan ya isa haka nan kiyi shiru karki haifarwa kanki da wata matsalar ciki ne a jikinki wannan kukan kuma da kike yi kina ta da hankalin ki sai ki fuskanci matsala...".
"Nafi kaunar in shiga matsalar da zan mutu akan wannan rayuwar da nake yi na tsani wannan rayuwa na tsani wannan duniyar na tsani kaina...".
Da sauri ta rufe mata baki ita kanta 'yarta ta tausayi take bata kwalla ne suk cika mata idanu da sauri ta kau da kai ta dauke su ta janyo Hafsat jikinta.
"Ya isa haka ki daina fadin haka komai da kika ga yana samun bawa a duniyar nan ƙaddararsa ce haka...".
"A,a Umma wallahi ba ruwan kaddara ni ne sila komai da yake faruwa dani ni ce sila kiyi hakuri Umma ku yafe mani na gaji da rayuwar nan nafi kaunar mutuwa da wannan rayuwar na san ko a wajan Allah ni mai laifi ce nayi abun da yake fushi dani nayi abin da ya kauce hanyar addini na kaico! Umma nasan na aikata kuskure Umma duk abin da kika ga yana faruwa Goggo ce sila ita take sanya ni".
Da sauri ta sake rufe bakinta tana mai girgiza mata kai.
"Nace kiyi shiru ko bana son jin komai daga gareki...".
"Umma ki bari na fadi domin ni dai na san rayuwata ta kare gwanda na fadi komai domin ki rokar min afuwa wajan mahaifina da wanda ya zama ina da hannu cikin faɗawarsu hukubar rayuwa".
Nisawa tayi tana mai da numfashi kafin ta gyara zaman da tayi dirshan akasa ɗan cikinta take ji yana ta faman juyawa yana tokare mata kirji laɓɓanta ta ciza gami da runtse idanu hakan da Abulle ta gani ya sanyata ware idanu tana tambayarta ko lafiya amma ta kasa bata ansa sai da ta dauki lokaci a haka kafun ta nisa wasu zafafan hawaye suka zubo mata.
"Duk halin da su Mariya suka shiga da Ummanta Goggo ce sila haka bacewar Abban su Mariya Goggo ce sila ita taja ni muka je wajan wani mutumi a dajin kauyen Sulalla akayi masa kurciya...".
"Innalillahi wa inna ilair raji'un".
Abin da Abulle ke maimaitawa kenan tana dafe kanta da take jin yana kokarin rabewa biyu lokaci guda idanuwanta suka kaɗa sukayi jajir wata irin tsanar kanta take ji tana tsanar zaman ta a duniyar nan a daidai wannan lokacin wani takaici ne da bakin ciki ya turnuke ta bata san tsanar da Goggo tayi ma su Bello har ta kai haka ba ta san kiyayyar da take masu takai haka ba.
Mikewa tayi kan kafafuwanta tana duban Hafsat kafin ta fidda hannu cikin zafin nama ta dauketa da Mariya hagu da dama har sai da ta tuntsira ta bugu da bango hancinta da bakinta duk sun fashe suka dinga zubda jini da sauri ta ja jiki zuciyarta na suya ta fice daga cikin soron zuciyarta take ji tana kara ya mutsewa gabadaya taji ta tsani zaman ta a duniyar ina ma numfashinta zai dauke ta rabu da wannan takaicin da bakinciki da uwarta da 'yarta suka cusa mata a zuciya.
Hafsat ganin yarda Abulle tayi mata ta sake rushewa da kuka tana hada kanta da bango kamar ba a jikinta yake ba sai da tayi kuka ma ishinta sannan ta mike tana faman hade hanya ta nufi cikin gidan.
********
Fizgo shi yayi suka isa kofar gidan sai faman cin magani yake yi Alhaji Abdurrazaq ya kwala sallama hannunsa rike da Huzaif da gabadaya ya gama kumbura ji yake yi kamar ya fashe don takaici da bakin ciki wai mahaifinsa ya yi masa irin wannan cin zarafin akan wata banza wacce bai ganin ta da wata kima ko daraja.
Abban su Mariya ne ya fito yana duban su daya bayan daya don bai san su ba Alhaji Abdurrazaq ne yayi masa sallama ya ansa shi cikin yanayi na son karin bayani.
"Kai ne mahaifin Hafsat?".
Bello ya gyaɗa kai yana duban Huzaif ganin yarda aka riƙe shi kamar wanda yayi sata shi abin har dariya ya so ya bashi.
"Sunana Alhaji Abdurrazaq ni ne mahaifin Huzaif wanda ya ci zafin 'yarku ya keta mata haddi".
Zaro idanu yayi sosai yana duban su zuciyarsa yake ji tana bugawa da sauri-sauri wani takaici ya kume shi da sauri ya juya cikin gidan dakin Goggo Marka ya nufa ba ko sallama ya shiga tadda ita zaune yayi ta hada tagumi can gefe kuma Hafsat ce ta dukunkune sai faman numfashi take ja tana saukewa.
"Kunyi baki ku taho suna jiranku"..
Yana fadin haka ya fita daga cikin dakin zuciyarsa na raɗaɗi gami da zafi ya jima yana takaicin wannan lamarin tun lokacin da ya gane wa idanuwansa ya tambaya amma Goggo Marka ta so ci masa mutunci tun daga wannan lokacin bai sake magana ba sai dai yaje har gidan Abulle ya hadu da mahaifin Hafsat suka zauna sukayi magana a nan ya san komai yayi bakin ciki sosai yayi takaici.
Tabarma ya dauka yanufi soro da ita ya shimfiɗa sannan yayi musu iso har lokacin Huzaif na hannun mahaifinsa ya ki sakin sa zama sukayi amma shi Huzaif ya tsaya kerere a tsaye a daidai lokacin suka iso su kuma Hafsat tun da ta hango huzaif ta ji gabanta ya yanke ya fadi wani kallo ta ga ya watsa mata ita ma kallon ta watsa masa daga nan ta kau da kai.
Alhaji Abdurrazaq ne ya muskuta ya dubi Goggo Marka da tayi wiri-wiri da idanu sai hada gumi take yi abi duniya duk yabi ya addabeta.
"Maganar da mukayi kwana ki dake na cewa zan aurawa ɗana jikarki domin kuwa cin zarafin da yayi mata ba zan yarda dashi ba domin ba zan yarda ko 'yata ayi wa haka ba don haka shine nake so ku bashi aurenta domin ba wanda zai aureta bayan shi in kuma ba ku yarda ba ni zan shigar da wannan maganar kotu kuma zan tsayawa Hafsat kai da fata har in ga an kwatar mata hakkinta".
Bello ne ya dube shi sosai yanayin sa ya burgesa yarda ya nuna ba yarda ba akan cin zarafin da ɗansa yayi wa Hafsat ba ya ji dadin haka sosai ko ba komai ya nuna shi mutum ne mai mutunci da sanin ya kamata duban Goggo Marka yayi kafun ya kau da kai.
"Ba sai maganar taje kotu ba ni ina bayanka nima a matsayin uba nake ga Hafsat in dai ta haihu ni na aminci ya aureta sai dai kuma magana daya akwai sharaɗi na lura kamar dole kayi wa ɗan naka don haka zan masa gargaɗi in har ya aureta ya ci zarafinta ko ya kuntata mata wallahi tallahi ni da kaina zan shigar da maganar nan kotu sannan a sake tada tsohon duk wani cin zarafi da yayi mata".
Wani kuka ne ya zo wa Hafsat mikewa tayi ta dubi Huzaif da yayi tsiru-tsiru da idanu sosai take jin har yanzu tana son sa bata jin zata iya rabuwa dashi duk da abin da yayi mata son sa ya zama jinin jikinta wanda hakan har yanzu ya kasa sanyata ganin laifinsa duban su tayi dukkan su kafin ta ja kafafuwanta da sukayi mata nauyi ta shige cikin gida....
*Kamala Minna*💞💞😘😘
[10/26, 9:20 AM] DEENY MINNA🙋♂: UKU BALA'I
NA.
KAMALA MINNA.
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร.
BABI NA SITTIN DA BAKWAI.
Gumi ne kawai ke ta faman keto mata kamar wacce aka juyewa diron ruwa sai faman yamutse fuska take yi tana cizon laɓɓa gabadaya ta gama galabaita ta fice daga hayyacinta lokaci-lokaci take ajiyar zuciya ita kadai tasan bala'i da masifan da take ciki yau kusan kwana uku kenan tana jin ciwon a tsaitsaye amma na yau ya shafe na kwanakin da tayi.
Jikinta har karkarwa yake yi buɗe idanuwanta tayi da suke runtse sun kaɗa sunyi jajir jijiyoyin goshinta sun fito sosai kamar shirya su akayi kan fatar goshinta hawaye ne suka kwaranyo mata karo na ba a dadi duban dakin tayi gani take yi yana juya mata sama na dawo kasa kasa na dawo sama sake runtse idanun tayi gami da yin wani yinkuri da ya sanyata sakin wata kara mai razanarwa kafun lokaci guda tayi luf! kamar ba ita bace tayi ihun ba.
Goggo Marka ce ta fado dakin cikin hanzari tana dubanta ganin yanayin da take ciki ya sanyata saurin isa gareta rikota tayi tana faman duddubata kafun lokaci guda ta gano abin da ke wakana da sauri ta gyara mata zaman dirshan da tayi tana mai rike mata kafadu da sauri ta fizge kanta daga hannun Goggo Marka tana faman sakin wani wahalallan numfashi hawaye sai ambaliya suke mata a fuska.
Sake kai hannu tayi zata rikota a daidai lokacin cikin nata ya sake juyawa wata irin zabura tayi gami da wancakalar da ita gefe guda kan ta ya hadu da gadon karfen dake gefen su da sauri ta ja da baya tana riko goshinta don sosai ta bugu lokaci guda wajan ya kumbure sosai duban Hafsat ta shiga yi idanuwanta suna kawo kwalla gabadaya ta gama rikicewa kanta gabadaya ya gama shiga duhu tunda Hafsat ta fara nakudar nan a tsaitsaye hankalinta ya kai kololuwa ba ta san lamarin zai kai ga haka ba wai yau Hafsat ce za ta haife musu abin kunya ɗan shege na gaba da fatiha ba ta taba dana sanin wannan lamarin da kaico ba kamar yau zuciyarta gabadaya ta gama karyewa da tashin hankali bata san yarda za tayi ba bata san wa za ta kai wa kukan ta a daidai wannan lokacin ba kowa ya juya musu baya musamman Abulle da gabadaya ta dauke musu kafa ta daina bi ma ta kansu ga gidan yanzu ita kanta kunyarsu take yi ta rasa dalili ko da yake ita kadai ta san abin da ta aikata a garesu sosai take jin zuciyarta na kara karye da komai na duniyar ma.
Ihun da Hafsat ta kuma yi ne ya sanyata dawowa hayyacinta dubanta ta shiga yi a tsaye take sai faman ya kice kayan jikinta take yi tana jifa dasu laɓɓanta cikin baki sai faman cijesu take yi kamar ba a jikinta ba idanuwanta a rufe da sauri Goggo Marka ta ja gefe ganin al'amarin ya girmama waje tayi da hanzari tana faman hada hanya Umma ce ta fito ta dubeta ganin yanayin da take ciki ya tabbatar mata ba lafiya isa tayi gareta tana riko hannayenta ba abin da jikinta ke yi sai karkarwa.
"Habeeba Ban san abin da ke faruwa da Hafsat ba ga ta can cikin dakin sai fizge-fizge take yi".
Zaro idanu tayi tana ambaton innalillahi wa inna ilaihir raji'un da sauri ta saki Goggo ta nufi daki durkushe ta same ta sai faman nishi take yi ga wani mahaukacin gumi da ta hada gabadaya tayi jagaf! duban kasan ta tayi ganin ruwa na kwarara ya tabbatar mata haihuwa ce da sauri ta fice ba tare da ta taba ta ba can ta hango Goggo sai safa da marwa take yi hannu aka hakan yayi matukar bata mamaki yau kuma girgiza kai tayi gami da komawa daki mayafinta ta dauko ta yi hanyar waje.
Tana sanya kai kofar gida ta hango su da sauri ta yo baya tana mai da numfashi ita gabadaya ta manta ma Mariya na waje lekawa tayi a daidai lokacin ita kuma Mariya idanuwanta na kallon kofar gidan don ta ga lokacin da Umma ta fito ta koma da sauri ya fito ta tayi da hannu sannan ta koma cikin soron sai faman kai kawo take yi don yanayin da ta ga Hafsat a ciki yayi matukar tsorata ta ba abin da ta tuna sai lokacin haihuwar Mu'azzam sosai zuciyarta ta karye lokaci guda hawaye su ka zubo mata a daidai lokacin Mariya ta iso ganin Umma da hawaye a fuska ya tsoratar da ita da sauri ta iso gareta tana tambayarta lafiya numfashi ta ja kafun ta runtse idanu jin yarda zuciyarta ke mikata wani yanayi.
"Mariya Hafsat na cikin wani yanayi matuka haihuwar ce na ke zaton lokaci yayi amma yanayin da take ciki yana bani tsoro".
Gaban Mariya ya yanke ya fadi idanuwa a waje.
"Haihuwa!?".
Ta fadi tana dafe kirjinta Umma ta gyaɗa mata kai da sauri ta juya tayi kofar gida wajan Dr.Karami ta koma kallo daya yayi mata ya gano tashin hankalin da take ciki da sauri ya iso daf! da ita kamar zai koma jikinta bakinsa har rawa yake yi wajan tambayarta lafiya runtse idanu tayi kafun ta buɗe su da kwalla hakan ba karamin kara tayar masa da hankali yayi ba.
"Hafsat ce take wani mataki na haihuwa amma lamarin sai a hankal...".
Tun kafin ta rufe baki yace da ita.
"Muje!".
Da sauri ta juya yana biye da ita suna shiga cikin soro suka tadda Umma wata irin kunya ce ta lullubeta shima Dr.Karami sadda kai yayi kasa don ba su yi tsammanin tadda da juna ba da sauri Umma tayi cikin gida shikuwa sai kokarin buɗe baki yake yi don gaishe Mariya ce tayi masa jagora zuwa cikin gidan dakin Goggo suka nufa wacce take bakin kofa lokaci-lokaci take daga labule tana duban Hafsat sai hawaye su zubo mata shar-shar.
Daga labulan yayi ya shiga da sauri ya isa gareta ya dago kanta da ke sunkuye yana kiran sunanta amma ina ta kasa ansawa da sauri ya kalli inda take durkushe shiru yayi na dan lokaci kafun ya mike ya leka waje Mariya ya yafito dake tsaye ita ma cikin yanayin fargaba da hanzari ta iso gareshe.
"Ku kamo ta kawai mu wuce asibiti ina ganin hakan zai fi dace wa don kin ga dai yanzu ko nace zan yi wani abu ba komai na aiki a wajena da zan taimaka mata domin ba a san yarda haihuwa zata kaya ba duk da dai gaf! take da yinta...".
Wani ihu ne ya cika musu kunnuwa da sauri Dr.Karami da Mariya suka faɗa dakin a daidai lokacin kan jaririn ya sanyo kai ware idanu yayi kafun yayi waje da sauri cikin sakanni ya dawo hannayensa da safa a ciki duban Mariya yayi wacce ta runtse idanu har da rufe fuska da mayafin jikinta girgiza kai yayi kafun ya isa wajan Hafsat wacce sai faman nishi take yi na wahala da taimakon Dr.Karami cikin ikon Allah Hafsat ta haihu bayan ta gama kururuwa jaririn na fadowa ta ta baje a kasa numfashinta na fita kadan-kadan.
"Mariya anso mani reza wajan Umma".
Da sauri tayi waje ta isa inda Umma ke tsaye sai faman Addu'a take yi idanuwanta sun kaɗa Mariya na isa ta dubeta jiki a sanyaye.
"Umma reza ake bukata".
Da sauri ta faɗa daki ta binciko sabuwar reza ko buɗeta ba ayi ba ta mikata mata zuciyarta na rage fargaba tunda ta ga an anshi reza da alamun an haihu da sauri Mariya ta juya ta koma dakin tana mika masa ya buɗeta ya yanke cibi a daidai lokacin kuma mahaifa ta fado dauke jaririn yayi wanda ya kasance namiji kyankyawa dashi dube-dube ya shiga yi.
Mariya ta lura dashi kuma ta gane abinda yake nima don haka da sauri ta kara so ciki dakin can gefe ta nufa inda wata akwaku take budewa tayi ta zaro wani sabon zani da alamun ko daura shi ba a taba yi ba ta mika masa goge jaririn ya shiga yi dashi sai da yayi masa tsaf! Sannan ta sake dauko wani ta mika masa ya nannaɗe shi a ciki ya mika mata komawa yayi wajan Hafsat ya dubata ganin yanayin da take ciki ya sanya shi yin waje da sauri Goggo Marka ya duba da ta gama firgicewa can gefe Umma ce ganinsa ya sanya ta yin kasa da kai.
"Alhamdulillah ta sauka".
Yana fadin haka yayi waje da sauri su kuwa har rige-rige sukeyi wajan fadawa dakin duban juna suka shiga yi kafun Umma ta shiga tsaftace dakin ta gyarawa Hafsat jikinta sosai ta tsorata ganin yarda ta karu a kasan ta hakan ya fadar mata da gaba duban Mariya tayi wacce itama idanuwanta na kanta gyaɗa mata kai tayi ba tare da tace komai ba a daidai lokaci Dr.Karami ya yi sallama suka ansa shi shigowa yayi hannunsa dauke da dan karamin kwanati (First Aid Box) cikin taimakon Allah yayi mata dinkin inda ta karu gami da allurai duban Umma yayi bayan ya ajje kunyar gefe.
"Jininta ya hau sosai kar ku saka mata ruwan zafi yanzu a dai samu mai dumi ta wanke jikinta dashi sannan ga wannan magangunan...".
Ya mikawa Mariya ledar yana mai cigaba da fadin.
"In ta ci abinci sai ku bata ta sha tsarin na nan a ciki Mariya sai ki duba ki gani Allah ya raya ya ɗayyaba".
Yana gama fadin haka ya mike yana duban Hafsat wacce ta dawo hayyacinta idanuwanta sai zubda hawaye suke yi ta kasa kallon kowa ma a cikin dakin yana kokarin fita yaji muryar Umma nayi masa godiya gami da Addu'a murmushi yayi gami da cewa 'Ameen' azuciyarsa sosai yaji dadin addu'ar a ransa.
*****
A wulakance ya anshi jaririn da ta mika masa sai faman cin magani yake yi yana hararar Hafsat da kanta ke kasa ita kadai ta san yanayin da take ciki tunda ta haihu yau kwana uku kenan gabadaya taji komai ya canza mata bata jin dadin komai rayuwar ta take ji gabadaya ta gaji da ita zuciyarsa sai zafi take yi ruhinta kamar zai kama da wuta.
"Meye haka Huzaif ya naga kana riƙe shi a wulakance ne kamar ba jininka ba ban son rashin hankali fa".
Mahaifiyarsa dake zaune ta fadi dama tunda da ta mika masa jaririn ta ga rikon da yayi masa ranta ya ɓaci sosai ji take yi kamar ta mike ta kwada masa mari don sosai take jin haushin sa tun a gida don da kyar da dole sannan ya zo wajan ganin jaririn da Hafsat ta haifa masa.
Sake turbuɗe fuska yayi yana dubanshi ya wullawa Hafsat wani mugun kallo cikin tsana da takaici abin da ke kara bata masa rai yarda jaririn yayi kama da shi sak! kamar kak'i yayi ya ajje hakan na kara kona masa zuciya domin kuwa bashi da wata mafita ko yace ba shi yayi ba ina ma zai ce bashi yayi ba ba yarda za ayi ba yarda ya ga kowa na gidan su ya dau zafi dashi akan Hafsat har sun fi kaunar ta dashi a yanzu.
"Ka tafi ka kaiwa mahaifin naka shi ya ga jikansa".
Ta sake fadi cikin ba da Umarni gabanshi yaji ya yanke ya fadi tunawa yayi da mutannan da suke soro a zaune ga Abban su Mariya ga nasa ga kuma mahaifin Hafsat wani irin ihu yaji kwanyarsa tayi saura kadan jaririn ya suɓuce a hannunsa da sauri ta kai hannunta ta na cilla masa mugun kallo.
"Wai mai yasa Huzaif kake son bata min rai ne kai yanzus aboda rashin imani ɗan naka zaka yasar saboda wata banzar akiɗa taka da bata da madafa ko mafaka kasan Allah zan bata maka rai in baka yi wasa ba kuma ka rike shi ka mika musu shi tun kafin na bata maka rai".
Da sauri ya juya ya fita ta bishi da mugun kallo kafun ta juya da idanuwanta ta dubi Hafsat dake ta faman zubda hawaye.
"Kin ga irinta ko Hafsat duk macen da bata kama kanta ba har namiji yayi galaba akanta tana cikin masifa duk son da namiji zai nuna miki duk kaunar da namiji zai ce zai miki karki sake ki saki jiki dashi har wani abu ya shiga tsakanin ku domin duk namijin da ya kasance da mace ba tare da aure ba har ta yarda to wallahi ya daina ganinta da daraja da kima kenan yanzu dai kin ganewa idanunki wani uba ne zai dinga wulakatar da ɗansa har haka in da kunyi hakuri kunyi aure ba ku keta hakkin Allah ba duk haka ba zata faru gareku ba kuna da son zuciyarku so na rufe muku ido har kuyi sake Shaidan yayi tasiri akan ku kina dai kallon yarda Huzaif yake yi miki a yanzu wanda ni sam bana jindadin haka don ba zan goyi bayan sa ba ina so ki kwantar da hankali ki ajje komai a gefe ki fuskanci rayuwa ki raini ɗanki sannan ki dauki komai a matsayin ƙaddara a rayuwarki ta duniya kuma nayi miki alkawari in har auren nan naku ya tabbata ni zan tsaya miki ba zan taba yarda Huzaif ya cutar dake ba ko yaci zarafin ki".
Dago idanuwanta tayi ta dubi Mahaifiyar Huzaif idanuwanta na kara rikicewa da zubda kwalla zuciyarta take ji tana kara yamutsewa wai ita ce yau namiji ke wulakanta wa bayan shine ya yi mata cin zarafin da ya zama bala'in rayuwa a gareta gaban kowa yake yi mata kallon tsana da k'yara ɗan cikinta da ya kasance jininsa shima bai tsira ba kaicon wannan rayuwa duban tsakar dakin tayi niki-nikin kayan da su kawo mata take bi da kallo kafun ta kau da kai ta cikin yanayi na zafin rai da kaicon wannan yanayi da ta tsinci kanta a ciki.
Huzaif sai da ya gama safa da marwa a tsakar gida domin kuwa kunya ce gabadaya ta gama baibaye shi ya kasa zuwa ya kai musu jaririn duk abin da yake yi Mariya na laɓe a labulan dakin su tana kallon shi ji take yi kamar ta fita ta rufe shi da duka don takaici yarda taga yana duban jaririn yana harararsa ya bata haushi da sauri ta dage labulan ta fito wani firgita yayi don ya dauka mahaifiyarsa ce ta fito har zai kwasa da gudu jin gyarar muryar da Mariya tayi ya sanya shi tsayawa yana dubanta kallon sa ta shiga yi zuciyarta na zafi da raɗaɗi kafun ta dauke kanta ta koma cikin dakin fakare yayi da idanu yana kallonta kamar ya ga sabuwar halitta zuciyarsa yaji ta buga da wani irin yanayi kwanyarsa na ansawa runtse idanu yayi sannan ya buɗe a hankali ya taka kafafuwansa ya shiga cikin soron gabansa na yankewa yana faduwa yana shiga gabadaya suka zubo masa idanu ji yayi kamar ya nutse cikin kasa don kunya kafafuwansa sai harɗewa suke yi ji yake yi in ya kara taku daya zai baje a kasa mahaifinsa ne ya dubeshu da mugun kallo kafun ya ce dashi cikin daga murya mai cike bacin rai.
"meye haka zaka zo ka tsayawa mutane a kai in ba zaka iso ba ka fita mana".
Da hanzari ya iso gareshi gami da mika masa jaririn ansa yayi ya shiga dubansa kafun ya dago kai ya dubi Huzaif sak! kamar su ta bayyana a ransa ya dinga ina ma ina ma ace da aure ka samar masa wannan jikan da sai yafi kowa farinciki da jindadi a rayuwarsa amma ƙaddara ta rigayi fata.
"Ƙayi masa huɗuba ne?".
Ya fadi yana kallon Huzaif da yayi kasa da kai abin duniya duk yabi ya dame shi dago idanuwansa yayi ya sauke a na mahaifinsa yana girgiza kai.
"Wa kake so to yayi maka wa ka mai da dan aikin ki haka za ka haifi 'ya'yan baka yi musu huduba don baka san darajar su ba?".
"Ayi hakuri Alhaji miko min shi nayi masa ni zan wakilce shi".
Abban Mariya ya fadi da murmushi a fuskarsa.
"Da kan sa zai yi masa ko nan gaba ya koya".
"Ba za ayi haka ba".
Ya sake tarar sa, shi dai Mahaifin Hafsat abin duniya ne duk ya addabe shi ya kasa cewa kala sai bin su yake yi da kallo yana wurgawa Huzaif mugun kallo ji yake yi kamar ya mike ya rufe shi da bugu.
"Wani suna za a saka masa?".
"Tambayi shi rasa kunya din".
"Hakuri za kayi".
"Saka masa Muhammad Huzaifa".
Dukkansu suka dube shi cike da mamaki Huzaif kuwa daskare wa yayi a kasa yanayin da suka ga Fuskar Alhaji Abdurrazaq ba wasa ba wanda ya tanka shi Abban Mariya yayi masa huduba sannan ya mika wa Mahaifin Hafsat amma sai ya kau da kai ya ki ansa ba yarda ya iya dashi ya mikawa Huzaif shi.
"In tayi arba'in za a daura musu aure in Allah ya kaimu".
Alhaji Abdurrazaq ya fadi ya harara Huzaif da ya mike jiki a sanyaye ya koma cikin gidan.....
*Kamala Minna.*💞💞💞😘😘😘
[10/27, 11:01 AM] DEENY MINNA🙋♂: UKU BALA'I
NA.
KAMALA MINNA.
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร.
BABI NA SITTIN DA TAKWAS
*BAYAN SATI UKU*
Kai kawo kawai take yi tsakar dakin gabadaya ta gama firgicewa yau sati guda kenan ta rasa gane kanta tunda Dr.Karami ya sanar da ita zai turo iyayensa ta dauka abun wasa ne sai taga ya tabbata hakan ba karamin kara rikita mata lissafi yayi ba musamman da Abba ya turke ta akan tsakaninta da Dr.Karami duk da ya san komai amma sai ya matse ta sosai domin ta tabbatar masa da cewa Dr.karamin ne zabin ta ita dai Umma yar kallo ce har sukayi kidin su sukayi rawar su fata alheri kawai take yi don ta fi kowa farinciki da jindadin wannan lamari.
"Wai ke lafiyarki kalau kuwa cikin kwanakin nan gabadaya na rasa gane kan ki?".
Umma ta fadi tana duban Mariya numfashi ta ja kafun ta daga laɓɓanta tana koƙarin yin magana wayar Umma dake yashe ta dau kara tsuke bakinta tayi tana duban wayar ganin su Baseera ya sanyata saurin daukar wayar jiki a sanyaye.
"Mariya kina ina ne?".
Muryar Baseera ta karaɗe mata kunne ba tare da tayi sallama ba yanayin muryarta da ta yi maganar da alamun tsoro da fargaba numfashi Mariya ta ja kafun ta nisa.
"Ina gida ya akayi ne?".
"Wai kin ji yau za a kawo lefe inji Dr.Aqeel jiya yake sanar dani da daddare kin san shekarar jiya iyayensa sun zo tambaya".
'Innalillahi wa inna ilahir raji'un'.
Mariya ta fadi a zuciyarta tana mai runtse idanuwanta kanta taji yayi mata wani gingirin gim! kamar an daura mata dutsen dala da goron dutse zuciyarta taji ta matse da wani irin yanayi komai take jin sa yana sauya mata ji take yi kamar ba ita ba komai take ji tamkar a mafarki yake faru.
"Meye kuma haka ya za ayi kiyi shiru kuma kina jin ana zuke mata kudaɗen wayar ta ta".
Umma ta fadi ganin yarda Mariya tayi mutuwar tsaye wayar a hannunta amma ta kasa furta komai kwanyarta take ji tana hautsewa da tashin hankali lamarin ne take ganinsa kamar ba gaske ba kalmar 'lefe' ce kawai ke mata hayaniya aka.
"Nima haka take Baseera yanzu haka shirye shiryen da nake gidanku zan taho don bana son...".
Shiru tayi tana duban Umma da ta kafe da idanu cike da zargi kau da kai tayi ta fara jan kafafu za ta fice daga cikin dakin Umma ita dai ido take watsa mata tun da aka fara maganar bikin nan na ta ta rasa gane kan 'yar ta ta komai nata ya sauya ga wani sanyin jiki da yake damunta ita dai ba ta ga abin damuwa a wannan lamarin ba abin farin ciki ya same ka amma gabadaya kuma sai ka sauya kamar mara lafiya.
"...Uhmm fa kin san mi nima fa yau za su kawo anya Dr.Karami ba hada baki sukayi da Dr.Aqeel ace daga fara magana sai su zage suna kokarin rusa mana rashin mutunci nifa Allah na gani ban shirya ba...".
Fizge wayar taji anyi da sauri ta juya Umma ce a tsaye fuskarta a hade kamar bakin hadarin dake kokarin zubda ruwa kasa tayi da kanta ganin irin kallo da Umma take yi mata nuna ta tayi da dan yatsan hannunta tana kokarin yin magana Bello ya shigo bin su yayi da kallo kafun ya dubi Mariya da kanta ke kasa.
"Me kuma ke faruwa naga kun yi cirko-cirko da ku haka kamar zakaru?".
Ba wacce tayi magana a cikin su Umma ta juya da sauri ta koma cikin dakinta duban Mariya yayi.
"Ke me kika yi mata na ga ranta a ɓace?".
Girgiza kanta tayi idanuwanta na kawo kwalla.
"Ni ba kuka nace kiyi mani ba kin san natsani wannan hawayen naki ko don haka ki shafe su ki fada min abin da ke faruwa".
"Ni ban yi mata komai ba Abba kawai dai...".
Shiru tayi tana susar gefen kuncinta kafun ta dago kai ta dube shi shima ita yake duba kafun ya juya yayi cikin dakin Umma ya hango zaune ta zabga tagumi da sauri ya isa gareta zauna gefen ta gami da cire mata tagumi.
"Me kuma ya hadaki da 'yar taki yau abin da ban taba gani ba?".
Kallonsa tayi kafun ta dauke kai tana ajiyar numfashi.
"Mariya har yanzu hankalin ta bai gama zama daidai akanta ba in ban da rashin hankali da wauta bayan an gama magana meye kuma na son mai da hannu agogo baya wai maganar nan fa ta kawo lefen take tayi wa kunci alamun bata son wai yayi wuri kaji fa shiririta".
Murmushi yayi kafun ya shafi haɓarsa.
"Da sauki in ba auren ne tace bata so ba duk labarin kanzon kurege take son biya miki ba wani abu ba".
Ya fadi yana mikewa kan kafafuwansa dubansa tayi da mamaki.
"Au haka ma zaka ce Abban Mu'azzam kasan dai halin yaran nan abin da kake ganin ba komai ba sai ka ga su sun girmama shi".
Tsayawa yayi da tafiyar da yake yi ya juyo ya dube ta yana gyaɗa kai.
"Bana so kina saka kokwanto a ranki don Allah ki daina in Allah ya yarda ba abin da zai faru sai alheri".
Gyaɗa kai tayi gami da daga kafada tana mai da kallon kan Mu'azzam dake ta faman sheka barcin sa hankali kwance tashi tayi ta shiga kokarin gyara dakin domin ta san yau dai gidan sai abin da hali yayi ta san yanzu haka iyalan su Baffa da wasu tsirarun dangin Abban su Mariya na hanya domin su ne za su zo har da su za a anshi lefen.
Fita tayi can ta hango Mariya tana cigaba da gyaran gidan ba ta yi mata magana ba ta bi sahunta lokaci kankani duk suka kammala komai nan suka hau girke-girken tarar baƙi.
Sosai Mariya ta gaji domin ba su gama aikin ba sai wajan daya kuma karfe biyu yan kawo lefen za su zo so take yi ta bar gidan amma Umma ta kasa ta tsare ta hana ta sak! ji take yi kamar ta daura hannu aka ta kurma ihu musamman yarda ta ga Umma ta tsare mata gida ko magana kuma ba tayi mata tun da safen.
Zaune take ta zabga tagumi sai faman tunanin yarda zata bar gidan take yi gidan su Baseera ta so zuwa to ita ma gashi an yi mata bazata an kwakuya mata rashin mutunci tana tunanin hadin bakin su ne Dr.Aqeel da mutumin nata.
*******
Horn taji anayi mata sam! bata dauka da ita ake ba sai da taji abin yaki ci yaki cinyewa sannan ta tsaya gami da waigowa motar da ta gani ne hakan ya sanyata tsuke fuska tana kokarin cigaba da tafiyarta.
Da sauri ya kashe motar ya fito da hanzari har da gudu gudu ya isa gareta gabanta ya sha yana kure ta da idanu ita mata kallonsa take yi kafun ta kau da kai tana jin yarda zuciyarta ke bugawa da sauri-sauri.
"Ina zaki je bayan kin san dai yau rana ce ta musamman".
harararsa tayi kafun ta dauke kanta hakan da ya gani ya so bashi dariya don ya san laifin sa yayi mata abun da ba ta san dashi ba shi kasan kasa rike kan sa yayi tun da aka yarje masa an bashi ita gabadaya ya ji kamar nan da wani lokaci wani zai kwace masa ita musamman in ya tuna irin TAQADDAMA da aka kwasa.
"Ba laifi na bane laifin mutumin ƙawarki ne".
Da sauri ta dube shi kafun ta motsa laɓɓanta kamar mai son yin magana amma ta fasa.
Gyaɗa kai yayi fuskarsa da murmushi.
"Har kun gama rigimar taku ne?".
Ta tambaye shi idanuwanta cikin nashi dariya ya tuntsure da ita kafun ya sake dago kansa ya dube ta.
"Rigima ai dama kece sanadi tun da kuwa kika yi masa tukuici ƙawarki komai ya koma normal tun ranar da abin ya faru ya sanar dani komai kuma mun yafi juna SHARRIN SO ne kawai dama ba wani abu ba".
Da mamaki take dubansa kafun ta saki murmushi tana mai rufe fuskarta da hannayenta.
"kin rufe fuska mana tunda kin hada zuciyoyi masu cike da ingantacciyar ABOTA suna rigima kamar mu abokai tun na makaranta amma ace a SANADIN 'YA MACE mun samu matsala abinda ya bani mamaki sannan na kara yarda SO ba abin da bai zai haifarwa zuciya ta aikata ba".
ya fadi yana juya idanunsa da suke kara rikita mata lissafi.
"Ina kika nufa naga kin fito a daidai wannan lokacin?".
Juyawa tayi ta dubi Kofar gidan sannan ta dube shi tana yatsine fuska.
"Ba zan iya zama bane su Baffa sun iso fa kuma hayaniya yayi yawa ni kuma bana so bayan haka kuma nasan yanzu...".
Sai kuma tayi shiru ta kasa karasa abin da tayi niyyar fadi tana mai sunne kai kasa murmushi yayi don ya gano in da zancen nata ya dosa.
"Zo muje ki raka ni tunda zaman gidan ne bakya so".
Da sauri ta dube shi idanuwanta da wani irin yanayi kafun ta shiga girgiza kai alamun a,a shima mamaki ne ya cika shi ganin abin da take yi masa.
"Saboda me ba zaki ba, ba fa nisa za muyi ba?".
"Ka bar shi kawai ai ba dadewa za suyi ba nima makota zan shi akwai abin da zan yi ne".
Ta fadi tana mai kokarin wuce shi ta tafi shan gabanta ya sake yi yana dubanta cikin idanunsa da suke kokarin sanya mata gajiya a jiki.
"Baki yarda dani bane ko meye nufin ki?...ko da yake zo mu je to na kai ki gidan mutuniyar taki na san zaki fi sake wa a can din".
Yana son takura mata ba ta son abin da zai dami zuciyarta so take yi ta tafi ta huta ko ta samu hutun kwakwalwarta don ta san tabbas in tabi Dr.karami surutunsa ya isa ya hanata sukuni ko kuma yayi ta yawo da ita ba su can shagon ba su can wajan shan Icea Cream ita kuma bata son yawa ce ya wacen nan.
"Ina yini Dr.Karami".
Kamar daga sama suka juyo muryar daga bayan su da sauri suka ji ya macece sanye da nikaf a fuskarta bayan ta da goye kallo daya Mariya tayi mata ta gane wacece kau da kai tayi a daidai lokacin ita kuma ta dage nikaf din Hafsat ce gabadaya ta rame tayi zuru-zuru da ita ga wani baki da ta kara yi kamar wacce ta jima tana jinya duban ta sosai yayi kafun ya gane ta murmushin yake ya saki yana ansawa.
"A,a Hafsat daga ina haka da ranar nan".
Murmushi tayi itama na yake duk ta sha jinin jikinta domin kuwa gabadaya kunyar Dr.Karami take a yanzu.
"Wallahi Huzaif na kai asibiti ba shi da lafiya ".
'Huzaif' Ya fadi a ransa sunan nayi masa yawo kwanya kafun ya dawo tunaninsa ya sake yi mata magana har tayi gaba duban Mariya yayi wacce takure shi da mayun idanuwanta ta na jefa masa kallon mai dauke da yanayin bacin rai kau da kai yayi shima a zuciyarsa dariya yake yiwa Mariya ganin yanayin da ta nuna masa yaji dadin haka sosai ko ba komai ya hango kauna gami da kishinsa a tsakar idanuwanta.
"Kallon na meye haka?".
Ya fadi yana murmushi hakan ya kara tura mata haushi sake tsuke fuska tayi tana kokarin wuce shi da sauri ya kai hannu zai riko mata hijab mai ya gani kuma yayi saurin janye hannunsa zuciyarsa na bugawa ba zai taba manta yarda suka kwashe da ita ba lokacin da ya rike ta bisa kuskure in kuwa ya sake maimaitawa a yau ya san zata dauka a gaske yayi Allah kadai ya san hukuncin da za tayi masa numfashi yaja daidai lokacin da yaji tsayuwar motoci ita kanta Mariya tsayawa tayi da tafiyar da take yi ta juyo ganin motocin sunyi parking kure su tayi da idanu gabanta taji ya yanke ya fadi ta tabbata yan gidan su Dr.Karami ne masu kawo lefe don haka da sauri ta juya ta dube shi ganin yana yi mata dariya har da gwalo ya sanyata turo baki gaba tana harararsa kafun ta juya da sauri ta fada gidan makotansu.
Shi abin ma dariya ya bashi bai san wacce irin kunya bace Mariya gareta ko da yake jinin fulani in yayi duba da Umma sak! ita ma haka take da sauri ya shiga motarsa ya ja ya isa inda motocin suke mazaje ne ziryan ba Mace ko daya a cikin su sune yan kawo lefen.
Gaida su yayi bayan ya fito daga cikin mota wani kanin Hajiyarsa ce ya kalle shi cikin harara.
"Au wai ke dama kana nan unguwar ko biye damu kake?".
So sa kai yayi kafun ya dubi sauran yan uwan mahaifin nasa da sukayi masa kuri da idanu suna dariya.
"Kawu Sako fa na kawo mata shi...".
"Sako eh tabbas na ga sako ai sai ka zo muje Lefen ma mu kai da kai tare ko".
Gabadayan su suka kwashe da dariya a hankali ya ja da baya kansa akasa ya fada cikin motarsa ya yi mata Key sannan ya leko da kai waje.
"Kawu sai kun dawo a dai yi duk abin da ya kamata surukar taka ta musamman ce".
Ya fizgi motar da gudu yana faman sheka dariya suma dariyar suke yi kafun su bude kofofin wata mota kirar Benz sabuwar dalla sai daukar idanu take yi suka shiga sauke tika-tikan akwatina masu kyau da tsari har set biyu kallo daya za ka yi musu ka kasa dauke idanuwanka domin sun hadu iya haduwa tsayawa masalta su wani cin lokaci ne da nuna kauyanci...
*Ina Yan Team din Dr.Karami da Mariya lokaci fa ya zo ku zo ku fara shirye shiryen biki ku fidda mana da Anko domin biki mai ansa sunansa biki za ayi*
*Haka ma Yan Team din Dr.Aqeel da Baseera Ku shirya shagalin ku*😀😀
A gefe guda ga bikin su *Hafsat mai jego da angon karni Huzaif...lol*😀😀
*Kamala Minna.*💞💞😘😘😘
[10/28, 8:42 AM] DEENY MINNA🙋♂: UKU BALA'I
NA.
KAMALA MINNA.
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร.
BABI NA SITTIN DA TARA.
Dubansa take yi zuciyarta na kara mikata wani mataki na son sa duk cin mutunci da wulakanci da yake yi mata sam bai damunta kamar yarda yake bayyana kiyayyarsa gareta sosai take jin zuciyarta na suya ruhinta da kwanyarta ja take kamar za su kama da wuta numfashi take ja a hankali idanuwanta sai zubda hawaye suke masu zafi ta duɓe shi a karo na ba a dadi hannunta rike da Huzaif.
"Huzaif yau ni ce kake wulakanta wa Huzaif yau ni ce kake ciwa mutunci bayan kai ne silar faruwar komai gareni...".
Wani banzan kallo yayi mata kafun ya mika mata Huzaif dake hannunsa dama duk ya gaji da rikonsa ji yake yi kamar an daura masa ƙaya a hannu in ba don Hajiyarsa tayi masa umarni da cewa ya dinga zuwa ba in ba haka ba zata bata masa ba abin da zai kawo shi wajan banzar yarinyar nan da bai san ma ya akayi ya fara kulata ba a yarda yake na matashi mai jini a jika amma ace shine yake tsayawa da wannan kazamar har za ta zama matar auren sa nan da sati guda.
Wani kunci ne ya mamaye zuciyarsa ji yake yi kamar ya sheka ta ta mutu kowa ma ya huta.
"Karki sake daura min laifi don bani na kawo ki ba ke kika kawo kan ki gareni sannan ban yi miki dole ba balle kiyi tunanin ko na KETA HADDI a gareki".
Runtse idanu tayi tana jin yarda maganganunsa ke ratsa zuciyarta da kwanyarta suna haifar mata da wani yanayi mai kokarin kona mata duk wani sassa na jikinta girgiza kai ta shiga yi numfashinta sai kai kawo yake yi kamar zai dauke.
"Ki rubuta ki ajje ko da kin aure ni wallahi ba zan taba son ki ba bana kaunar ki daidai da kwayar zarra a zuciyata domin ni ba zan auri jahila...".
"Ya isa haka Huzaif ya isa nace maka!".
Hafsat ta fadi cikin karaji tana toshe kunnuwanta da take jin maganganun kamar za su fasa mata su kuka ne ya sake kwace mata duban sa tayi.
"Ba sai ka gaya min baka kauna ta ba sannan ba sai ka gaya min ka tsane ni ba amma ka ajje wani abu a ranka wallahi tallahi Huzaif sai na aure ka kuma wallahi sai ka so ni a yarda nake don ba wanda ya bata min rayuwa sai kai ba wanda ya jefani cikin bala'i sai kai don haka wallahi tun da muka dama tare da kai sai mun shanye sai dai in an kai ni gidanka ka dinga yagar nama kana watsarwa".
Ta fadi tana hadiye kukan Huzaif ta saba abaya ta goyashi sannan ta sanya hannu ta shafe fuskarta da hawaye suka ki tsayawa da zuba wani abu ta hadiye mai tauri kafun ta dubi Huzaif da yayi fakare yana kallonta wani kunci da takaicinta na kara turawa zuciyarsa bakin ciki murmushi ne mai ciwo ya wanzu a fuskarta.
"Kasan Allah Huzaif sai na aure ka a baya ina jin takaicin cin mutuncin da kayi mani bayan ka keta mani haddi amma tun da abin naka haka ne MU ZUBA MU GANI shege ka fasa".
Da sauri ta juya zata tafi sai kuma ta tsaya zuciyarta na bijiro mata da wani tunanin juyowa tayi ta dube shi da mugun kallo a fuskarta goyon ta kwance sannan ta iso in da yake tsaye mamaki duk ya gama cika shi ganin yarda lokaci guda Hafsat ta juye kamar ba ita ba gaban motarsa ta isa ta ajje jaririn kafun ta dube shi hawaye na kara balle mata.
"lokacin da muka hadu da kai ni kadai ka gani ba tare da wannan jaririn ba".
Ta nuna Huzaif da yake ta faman wutsul-wutsul da kafa kafun lokaci guda ya balle da kuka.
"ka dauke shi don bani ni ne ya kamata na rike shi ba a halin yanzu ka je kai ma ka ɗanɗana abin da ake ji".
Tana gama fadin haka ta juya da sauri ta shige cikin gida kunnuwanta sai faman ansa sautin kukan ɗanta suke yi wani irin yanayi take jin kanta a ciki gabadaya duniyar take ji ta sure mata ina ma ace za ta mutu da sai tafi kowa farin ciki.
Kwalla mata kira yake yi amma ina ko ta kan sa ba ta bi ba juyawa yayi ya dubi Huzaif ganin yarda yake rusar kuka gabadaya yaji ya firgice da sauri ya isa gareshi ya dauke shi yana jinjigashi amma ina kamar ana kara rura wutar kukan nashi waige-waige ya shiga yi amma ba kowa a layin da sauri ya isa kofar gidan ya tsaya idanuwansa sunyi tsuru-tsuru gabadaya kwanyarsa yake ta rikice kafun ya ankara yaji saukar fitsari a jikinsa wani ihu ya saki yana daga shi daga jikinsa fitsari sai tsartuwa yake yi hakan ya kara bata masa rai ya shiga yatsine fuska ji yake yi kamar yayi cilli da jaririn amma ya kasa ya leka soron yana zundumawa Hafsat kira amma ina kamar yana kiran dutse tana jin sa amma tayi banza dashi zuciyarta kuwa sai zafi take yi in ta jiyo kukan ɗan nata ji take yi kamar ta tashi ta anso shi amma in ta tuna abin da Huzaif yayi mata sai ta komata zauna tana rusar kuka.
Mota ce kirar Benz tayi Parking a daidai kofar gidan su Mariya da Baseera suka fito daga can gefen direba kuma Dr.Karami ya fito fuskarsa da yalwataccen yanayin farin ciki duban su yake yi su duka kafun ya sauke akan Mariya da tayi kasa da kai Baseera kuwa sai zabga dariya take yi tana duban Dr.Karami da yake harararta.
"Malama ba ma son ranin sense ga ya za ayi za ki dinga mana dariya".
Ya karashe shima dariya na kokarin kwace masa a daidai lokacin Mariya ta dago kai ta dube shi tana watsa masa harara.
"Malama zo mu wuce ciki in kun gama dariyar".
Mariya ta fadi tana duban Baseera Dr.Karami ne ya miko musu jaka mai dauke da IV Baseera ta ansa tana dubawa kafun ta mikawa Mariya.
"Naki yafi nawa kyau gaskiya".
"Ai sai ki sauya".
Ta fadi tana harararta sake tuntsirewa da dariya Baseera tayi kafun ta ja hannun Mariya su fara tafiya.
"Au ko sallama babu da yake nayi muku abin da kuke so ko, ai ko ni direbarku ne sai haka inda na san haka Allah sai dai naki Dr. ya zo yayi wannan yawon dake amma saboda son kai ya tashi ya gudu ya barni da iyayinki".
Dariya ta sake yi kafun ta dubi Mariya da gabadaya ta ki sakin jikinta sai faman hade fuska take yi.
"Kai ka san in da ba abin da ya sanya shi gaba ba abin da ba zai mani ba kuma ko da ka tafi dani ai na taimaka maka ita mutuniyar taka mai tayi bayan zaman shiru komai ni nake yi".
Tana gama fadin haka ta ja Mariya sukayi gaba bin su yayi da kallo zuciyarsa na mika shi wata duniya ta musamman sosai yake jin zuciyarsa na kara narkewa da wani irin yanayi game da Mariya ji yake yi kamar ya sake janyo lokacin bikin ya dawo nan da kwana biyu ba sati guda ba.
Sai da ya ga shigewarsu sun sha kwana sannan ya shige motarsa cike da farin ciki ya ja ya tafi.
Turus suka tsaya a kofar gidan ganin abin da ke faruwa Baseera ce ta dubi Mariya baki na rawa.
"Mugun abu Mariya me nake shirin gani?".
Wani yaƙe Mariya ta saki kafun ta dubi Huzaif da yayi wujiga-wujiga dashi gabadaya jikinsa ya gama bacewa da fitsari da kashin ɗan nasa fuskarsa kawai zaka kalla ya baka tausayi don gabadaya yayi laushi ji yake yi kamar ya kurma ihu don takaici sam bai lura da su Mariya ba sai da suka iso kofar gidan za su shiga ya gansu ji yayi kamar ya nutse a kasa don kunya duk sai yayi wani wiƙi-wiƙi dashi kamar wanda yayi wa sarki karya Baseera kuwa abin dariya ya bata amma sai ta kanne dama ta dade tana jin haushin Huzaif tun lokacin da ta samu labarin abin da ya faru tana kokarin yin magana taji Mariya ta fizgi hannunta sun faɗa soro da sauri ya bi bayan su yana kwalawa Mariya kira cikin wani irin yanayi na rawar murya tsayawa tayi cak! batare da ta juyo ta dube shi ba.
"Don Allah taimaka ki mikawa Hafsat ɗan nan tun dazu yake ihu na kirata amma ta ki zuwa ban san mai take nufi ba".
Baseera ce ta juyo ta dube shi a wulakance.
"Meye nata ita da kake cewa ta anshe shi ta kai shi ai na dauka gidan ba bakon ka bane ko ai sai ka shiga ka kai shi ba ma wannan ba ai na dauka ɗan ka ne ka ga ai kaima zaka iya zama ka rarrashe shi ba dole sai uwarsa ba".
Runtse idanu yayi domin sosai yaji maganganun Baseera sun taba masa zuciya amma sai yaki nuna haka a fili sai ma murmushi yaƙe da yake ta faman yi yana sanɗa kai domin ba abin da yafi bukata a yanzu illa a raba shi da yaron nan don ya gama firgitashi gabadaya musamman in ya dubi jikinsa yarda ya baci duk abin duniya ya bi ya dame shi.
"Don Allah na roke ki".
Ya fadi da muryar tausayi ganin Baseera ta ja hannunta za su shige juyowa tayi ta dube shi.
"ka bari za a turo maka ita sai ta anshe shi da kanta ban san abin da ya hada ku ba har ta bar ɗan nata a nan ba zan asa taje taga baƙina ba".
Tana fadin haka ta juya suka shige shi kuwa ji yayi kamar ya kurma ihu don takaici sai ya tafi kamar zai shiga cikin gidan sai kuma ya dawo da baya.
Suna isa cikin gidan suka hangota can kofar daki ta hada kai da gwuiwa sai shsashekar kuka take yi Baseera ta dube ta ta taɓe baki kafun ta saki hannun Mariya ta fada dakin Umma.
" Bai kamata ace kin zo nan kin zauna kin barshi rike da ɗanki ba ya kamata kisan darajar ɗa kuka yake yi fa amma kin zo nan kin zauna ai ko mai yayi miki shi Huzaif din bai kamata ki haɗa hukucin da zakiyi masa har da ɗan naki ba domin shi bai san komai ba bai ma san abin da kuke yi ba don haka ki je ki anso shi don ya ɓata masa jiki sosai".
Tana gama fadin haka ta juya ta shigewarta dakin Umma zuciyarta na kara tausayawa yanayin da Hafsat take ciki gabadaya ta sauya kamar ba ita ba Mikewa tayi tana faman tankaɗi kamar wacce ta kwana ta wuni bata sakawa cikinta komai ba a hankali take tafiya har ta isa soron yanayin da ta ga Huzaif din a ciki sai da zuciyarta ta harba da sauri ta isa gareshi ta anshe shi tana wurga masa wani kallo kafun ta juya ta koma cikin gida ranta ba dadi gabadaya.
Umma ce ta dube su su duka kafun ta dubi ledar da Baseera ta ajje gefe guda.
"Wannan kuma na meye...ba ma wannan ba ina kuka tsaya tun dazu ku da kuka ce mani ba daɗewa za kuyi ba".
Ta karashe tana duban Mariya da ta koma gefe ta takure kamar wacce bata da lafiya.
"Wallahi abin da muka je ansowa ne muka samu ba a karasa ba".
Baseera ta fadi tana zaro Iv din tana mikawa Umma ansa tayi tana dubawa kafun ta dubi Baseera.
"Amma fa sunyi kyau sosai".
Murmushi Baseera tayi kafun ta dubi Mariya wacce itama izuwa lokacin ta dago kai.
"AMAREN BANA".
Baseera ta fadi cikin zolaya hararar ta Mariya tayi kafun ta dubi Umma.
"Ya kamata Umma ki yiwa Mariya magana gabadaya taki sakin jikinta shi kansa Dr. sai da ya tambaye ni ko akwai abin da ke damunta ne nace masa a,a gaskiya yanayin da take nunawa kamar akwai abin dake damunta".
Numfashi Umma ta ajje kafun ta dubi Baseera.
"Ni ban san ta ina zan fara miki ba nima yanayin da Mariya take nunawa ya fara isa ta wani in ya ga haka sai ya dauka kamar auren dole za ayi mata..."
Bata karasa maganar ba wayar Baseera ta dau kara da sauri ta zarota daga jaka ganin sunan Mami ya sanyata saurin mikewa.
"Umma bari na tafi kin ga har Mami ta kira ni nasan tana can tana jira na itama daɗewar da mukayi yayi yawa".
Tana fadin haka ta dauki jakarta da ledar IV dinta ta fice bayan ta yiwa Umma Sallama Mariya ta mike jiki a sanyaye tayi mata rakiya....
*Kamala Minna*💞💞💞😘😘
[10/29, 9:38 AM] DEENY MINNA🙋♂: UKU BALA'I
NA
KAMALA MINNA.
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร.
BABI NA SABA'IN
Runtse idanunta take yi zuciyarta na zafi ji take yi kamar ta haɗiyi zuciyarta ta mutu don bakin ciki kukan da take yi tana samun sauki a yanzu ya zama wahala a gareta HAWAYEN ZUCIYA da take jin zubar su suma tana samun sauki kadan suma sun dai na zuba idanuwanta gabadayan sun kekeshe ba alamun za su zubda hawaye zafin zuciya ne da na ruhi kawai take jin su kamar a wuta aka jefa ta.
Dago kanta tayi ta dubi jikinta wani kunci ne ya sake mamaye zuciyarta in ta tuna yarda ta ga Mariya a wannan rana cikin yanayi na alfarma da shiga ta burgewa a matsayinta ta amaryar gobe har da ita amma ita ko wacce ta fi kowa rashin gata a duniyar nan sai ta fita jindadin irin wannan ranar wai ita ce yau kayan ma da zata saka ta fito a matsayinta na wacce za a daurawa aure amma sun gagareta kaicon wannan rana.
Sautin guɗar da taji ta karaɗe gidan ne ta daki kunnuwanta ya sanyata sake runtse idanunta gami da toshe kunnuwanta ji sautin take kamar ana zirara mata ruwan dalma cikin kunnuwanta mikewa tayi kan kafafuwanta tana faman haɗe hanya fuskarta kadai zaka kalla ka gane kuncin da take ciki duban Huzaif tayi dake kwance a yan kwane kamar wanda ya fado daga sama ba uwa ba uba kau da kai tayi tana taka kafafuwanta tana kokarin fita a daidai lokacin Goggo Marka ta sanyo kanta cikin daki cikin yanayi na razana saura kadan su yi gware idanuwansu suka sarke da juna idanun Goggo Marka lokaci guda suka kawo hawaye da sauri ta kau da kai tana karasawa cikin dakin tayi zaman yan bori gami da dafe kanta wani irin kunci da takaici suke nukurkusar zuciyarta ga wani raɗaɗi da zafi da take jin ruhinta na yi mata kwanyarta take ji na ta faman ihu da hayaniyar abin da ya jefata cikin wannan halin bata taba zaton rayuwa zata juya mata haka ba bata taba zaton duniya zata yi mata gwatson mage ba sai yau.
Dago jajayen idanuwanta tayi ta sauke a fuskar Hafsat wani irin tausayinta take ji na kara narkar mata da zuciyarta tana kaico da wannan rayuwa da suke ciki wacce ita ce ta zamo sanadi garesu baki daya ita ce silar faruwar duk wani bala'i da masifa da suka tsinci kan su.
"Kiyi Hakuri Hafsat ki yafe mani NA YI NADAMA...".
Wani banzan kallo ta wurgama mata dama cike take da ita tun jiya da ake ta shagalin baki tana kallonta ta kwashi jiki ta shiga tana farin ciki ita kuma ta barta da kayan takaici makale cikin daki sai dai in mutuwa za tayi tayi kenan haka a shekaran jiya Huzaif ya zo suka kai ruwa rana akan bikin nan nasu akan haka yayi fushi uban komai bai bata ba kuma duk Goggo Marka ce sanadi dan kayan ma da ake yi cewa yayi ba zai yi ba ita kuma bata so ta hadashi da iyayensa saboda yanayin da suka nuna mata ba ta so ta nuna masu yanayin da suke ciki da ɗansu domin ɗa da iyaye Allah ne kawai ya san tsakanin su tana tsoron su canza mata da ga kulawar da suke bata.
"Me zaki fada min Goggo ai kin rigaya kin gama cuta ta ba abin da zan ce da ke sai Allah yayi mani sakayya ba wanda ya jefani cikin bala'in rayuwa sai ke ba wanda ya zaɓa min wannan kazamar rayuwar sai ke bani ga karatu gani da dan shege ga shi mijin aure ma wulakantani yake yi tun kafin naje gidan sa wannan UKU BALA'In da mai yayi kama ni dai na san na gama ASARAR RAYUWA a filin duniyar nan".
Wani kuka ne ya kwace mata da sauri ta zame bayanta na kartar bango ta zube kan kafafuwanta wani kuka ne mai cin rai take yin sa amma idanuwanta kemadagas ba alamun hawaye runtse idanuwanta take yi tana buɗe su so take yi kawai ta buɗe su ta ganta a wata duniyar ba wannan ba...
Sallamar da ake kwaɗawa tsakar gidan ya sanya su duban junansu jin ana ambatar Hafsat da sauri ta fice ta leka ganin tsirarun mutane yan biki suna ta kai kawo sai wasu mata biyu da suke tsaye wanda kallo daya zaka yi musu ka gane cikakkun masu ji da kan sune gaɓadayan su sai wani yatsine fuska suke yi suna taunar cingam gaban Hafsat ne ya yanke ya fadi kafun ta juyo ta dubi Goggo da tayi fakare da idanu.
Da sauri ta fice daga cikin dakin gabanta na cigaba da buguwa ta isa garesu dubanta sukayi tun daga kasa har sama kafun su watsar dayan ta ja tsaki gami da tsartar da yawu hakan ya jawo hankalin yan bikin da suka fara taru har da na dakin Umma duk sun fito.
"Kece Hafsat?".
Babbar ciki ta tambayeta tana nunata da hannun hagu daga kai Hafsat tayi gabanta na kara tsinkewa ganin irin kallo da suke watsa mata a sa'ilin da ta tabbatar musu ita ce Hafsat din.
"Da farko dai ni sunana Assama'u yayar Huzaif wanda kike fata ya zama mijin ki ta ko wani irin hali sannan ina so in sanar sake cewa ki shirya zaman kunci da takaici a gidan sa sannan ki sani mu zuri'armu ba 'yar iska sannan babu wacce tayi yawon ta zubar har ta samu kyautar tukuicin ɗan shege na gaba da fatiha wanda kika likawa kanina kika ce shine sanadin sa".
Gabadaya mutanan gidan idanuwansu yayo waje don wasun su da yawa ba su san abin da ke faruwa ba abin ka da mata nan aka fara kuskus ana duban Hafsat wacce ta gama sankarewa a tsaye gabadaya ta ji duniyar na juya mata kafafuwanta take ji suna lauye suna kokarin zubda ita kasa numfashi taja mai tafe da zafin zuciya duban su ta shiga yi daya bayan daya kallon da suke mata mai cike da tsana da kiyayya ya kara tsinka mata zuciya.
"Na san ba komai ba ne ya sanyaki makale masa har kika kunsa masa wannan sharrin saboda an ga gidan dala an ga gidan da jar miya ke kai kawo ba a saba lasa ba mai dattin hula ba ya kawo shine za a makalewa ɗan mutane to ki rubuta ki ajje bar ganin hajiya da Alhaji na goya miki baya to kisa ni ba da su za ki zauna ba da ɗan su za ki zauna har ɓarin jiki kike karen ki ya kamo zomo to wallahi zaki ya kawo miki wanda zai zaɓa miki UƘUBAR RAYUWA a gareki".
Dayar ta fadi tana watsowa mata ledar dake hannunta gabadaya kayan suka zube a jikinta daidai nan wasu hawaye na takaici suka surnano mata a saman kunci gabadaya ta kasa motsi jin komai take kamar a mafarki ba gaske ba dafa kafaɗar ta taji anyi a hankali ta juyo Goggo Marka ce tsaye ita ma idanuwanta na zubda hawaye duban matan tayi cikin jin haushi kafun ta hadiye wani abu da ya tokare mata zuciya.
"Rashin arzukin har ya kai haka ai ba karya akayi ba shi Huzaif din ai ya san shi ya lalata mata rayuwa don haka ya kamata ku gyara kalamanku sannan ku sani ba a 'yar iska daya dole sai an samu dan iska...".
"Tsohuwar alagidigo tsohuwar banza gayyar kwadayayyu kisan dai ba yarda za ayi namiji ya tursasa mace akan wani ra'ayi ko dole sai ta aminta abu ke tabbata don haka karki sake karki sake dorawa Huzaif kalmar dan iska domin wannan karuwar 'yar taki ita ce silar komai".
Gabadaya gidan ya dau salallami Umma dake tsaye bakin kofa idanuwanta sun kawo hawaye da sauri ta iso garesu ta shiga ba su hakuri da su tafi amma ina kamar kara ingiza su ake yi nan suƙa shiga hayaniya suna tsinewa Hafsat da Goggo Marka a cikin wannan yanayin Abulle tayi sallama ta shigo hankalinta yayi matuka wajan tashi ganin abin da ke faruwa da sauri ta isa ga Goggo Marka dake ta faman rusar kuka kamar ranta zai fi janye ta tayi ta kai ta daki kafun ta fito idanuwanta itama sun kaɗa sun yi jajir ta dubi Hafsat ta watsar domin kuncin da take ji a ranta akan Hafsat ji take yi kamar ta hauta da bugu domin komai ya faru duk ita ta jawo musu.
Rigima ce ta balle sosai gidan biki ya hautsi ne sai da akayi da gaske bayan Umma ta kira Abban su Mariya ganin abin ya ki ci yaki cinyewa sannan komai ya lafa yan uwan su Huzaif suka fice Hafsat ta koma daki cike da takaicin wannan rayuwa da ta faɗa nan gidan biki lamari ya sauya nan da nan batun Hafsat ya zagaye ba abin da ake tattaunarwa akai sai maganar cikin shege da tayi Abulle ganin abin ya girmama kasa zama tayi ba tare da kowa ya sani ba ta fice daga cikin gidan cike da ɗacin rai.
****
Sosai wajan ya tsaru tun da ga Get din in ka kalla zaka gane ba karamin waje bane aka kama domin shagalin bikin kamu na yau da za ayi tsaruwar ciki kuwa ba a magana ko ta ina haske kwayaye ne ke walwali kamar a kasar turai ga wani daddaɗar kamshi mai sanyaya zuciya kawai ke tashi ga wani CoolMusic dake ta faman tashi yana kara jefa al'ummar dake wajan kara faɗawa kogin nishadi sosai wajan ya ƙawatu da kayan alatu na more rayuwa ga wasu lafiyayyun kujeru za gaye da wani hadadden Table mai shimfiɗe da wani kayataccen yadi mai kalar Pink sai a tsakiyarsa an ajje wata fulawa mai kyalli da daukar idanu.
A daidai lokacin da jama'a suka gama hallara ana jiran amare su ido Mc sai faman zubda zance take yi da yake mace ce KHADEEJA S MUHAMMAD yarda ka kusan taci bakin aku kawai nishaɗantar da mutane take yi ana ta dariya a wannan lokacin aka fara sanar da cewa amare sun iso a hankali Mc ta sanya Dj ya canza kiɗa wani lafiyayya sauti ya shiga tashi ga duka na faman ratsa jikin yan biki nan suka shiga gyaɗa kai suna rausayawa hankalin su gabadaya ya koma kan kofar Hall din wani turirin kamshi ya shiga fesowa kawayen amarya guda biyu daga gaba suƙa shigo hannayensu dauke da kaskon turaren wuta suka shiga zagaye wajan da shi kafun cikin sakanni AMAREN BANA Mariya da Baseera suka sanyo kai cikin Hall din da yake hada bikin akayi waje daya.
Sanye suke cikin wani tsarren material Mariya ta saka Yellow colour ita kuma Baseera ta saka Light-Blue fuskokin su kawai zaka kalla ka gane suna cikin farin ciki da nishaɗi ratsantsiyar kwalliyar da akayi musu ta kara bayyanar da kyan su.
Nan da nan waje ya hargitse shewa kawai ake yi sauti na cigaba da tashi a cikin wannam yanayi har suka iso mazaunin su suka zauna sannan Mc ta bada umarni a tsayar da kiɗa nan ta shiga jawabin da abin da ya tara su a wajan kafun ta nemi daya daga cikin yan biki ta zo ta buɗe taro da Addu'a Anty Yusra ce ta fito yayar Baseera tayi addu'o'i na neman yin taro lafiya a tashi lafiya sannan ta goɗewa duƙ wanda ya samu damar zuwa wannan bikin daga nan kuma lamari ya sauya a ka shiga biki gadan-gadan
Malam Sanah S Matazu aka gayyata ta gwangwaje amare da wa'azi da duk wasu karin haske na zaman gidan miji da nuna masu hanyoyin na salo salo na kula da miji da yi masa biyayya sannan da hakuri da juriya da boye sirrin miji sannan da girmama iyayen miji da yan uwansa da duk wani majibancin sa wa'azi sosai tayi musu mai ratsa zuciya da jiki tsayi lokacin mai nisa kafun daga bisa lamari ya sauya sosai da sosai kamu ya ƙawatu sai son barka nan ka shiga ciye ciye da shaye shaye kafun wani lokaci kuma komai ya zama daidai misalin karfe shida da rabi a ka tashi na yamma domin mazajen sun ce ba su yarda su kai dare a wajan ba ita kanta Mariya bata so yin taron ba bayar da za tayi ne Baseera son bidi'a gareta sannan ta samu goyan bayan su Dr.Karami.
Haka ko waccen su ta koma gida a gajiya Mariya gabadaya ta gama yin la'asar musamman in ta tuna gobe kamar yanzu ta jima da zama matar wani abin sosai take jin sa wani iri banbarakwai a cikin wannan daren sai da Umma ta kara kwantar mata da hankali sannan ta kara nuna mata darajar aure da martabobinsa ga 'ya mace sanna ta tunatar da ita fa'idar hakuri da juriya a gidan aure da duk wasu tsarurruka da yakamata ta bi domin dacewa da gidan aurenta sosai ta tsoratar da ita akan raina miji da dangin sa sosai ta nuna mata illar kin biyayya ga miji da duk wasu abubuwa da za su bata mata gidan aure ta.
Gyaɗa kai kawai Mariya take yi tana jin yarda zuciyarta ke kara tsinkewa da lamarin a wannan daren barci sai dai barawo ne ya yi yawon gaba da ita...
*Kamala Minna*😘😘😘😘
[11/2, 8:27 AM] DEENY MINNA🙋♂: UKU BALA'I
NA.
KAMALA MINNA.
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร.
BABI NA SABA'IN DA DAYA.
Zazzaɓi ne mai zafi rufe ta, bata tare da kowa ya sanin ba, sai karkarwa take yi numfashinta na kai wa da kamo wa, sautin haduwar hakoranta sai bada sauti yake yi gabadaya ta jigata, cikin wani irin yanayin tun a daren jiya. sosai take jin jikinta ba dadi, sosai take jin kamar akwai abin da ke shirin faruwa da ita, motsin da taji na shigowa ne ya sanyata kara kankame jikinta, zama taji anyi kusa da ita gami da yaye bargon da ta lulluba dashi, kara runtse idanuwanta tayi.
"Mariya".
Taji sautin muryar Umma ta sauka a saitin kunnuwanta, numfashi taja kafun ta buɗe idanuwan nata a hankali, ta sauke su a saitin Umma.
"Me ke damun ki haka Mariya, sosai naji zazzaɓi a jikinki, me yasa haka mai yasa kike son cutar da kan ki ne, bayan kuma kin san wannan abin ba abin cutar bane gareki, mu ma iyayenki mun sani ba za mu so abin da zai cutar dake a duniyar nan ba".
Ta karashe cikin sanyin muryar tana riko kafadunta, ta tayar da ita zaune, tana dubanta.
"Ban son haka Mariya, ya kamata ki ajje komai na fargaba da ke a zuciyarki duk wani bahagon zance da zaki ji zuciyarki da kwanyarki na kawo miki ki ajje su gefe, shaiɗan ne kawai ke miki kuwwa yaka so ya bata miki lamarin ki na alheri, ki kokarta ki mike lokaci tafiya yake yi nan da wasu awanni MATAR WANI zaki zama, karkashin wani zaki koma komai naki zai koma garesa, rayuwar taki ma kacokan zata bar hannunmu, mu iyayenki zata koma karkashin sa. kin ga kuwa bai kamata ki saka wa zuciyarki wata damuwa ba zama ne muke fatan har gaban abada ayi shi, zama ne mai daraja da martaba da kuma hanyar tsira gareki da mu kanmu iyayenki, Mariya ina horar dake ki rike darajarki da ta mijinki ki anshe shi a matsayin miji na tabbara Hisham ba zai taba cutar dake ba, duk da dai ansan DAN ADAM ajizi ne amma bana SHAKKA akan sa, ke ma na san ba za a taba samun matsala ta fannin ki ba".
Hayaniyar da ta kaure ne a tsakar gidan ya sanya Umma saurin mikewa ta fice, yan biki ne suka cika tsakar gidan, ga wasu tika-tikan tukwane da aka daura an banka masu wuta ko wani bangare ka duba na cikin gidan, zaka gane eh biki ne na musamman za ayi sa na masu rangwamin rufin asiri.
Haka abubuwa su kai ta tafiya, har misalin sha biyu da rabi, da yake daurin auren karfe daya ne nan da nan maza masu zuwa daurin aure suka fara shiri, amarya kuwa na can kudundune acikin daki, gabanta sai dukan uku-uku yake yi.
Zaune take tana faman rarraba idanu tana duban jikinta yarda ya canza lokaci guda yayi haske gami da laushi, ga wani kamshi da yake ta fesowa daga jikin nata lokaci-lokaci take dago hannayenta tana kallo zane suke da lafiyayyan lalle baki da ja hakan ya kara ƙawata hannun nata sosai da sosai...
Wayar Umma ce ta dau kara, da sauri ta dube gefenta in da take ajje, sunan da ta gani a jikin wayar ne ya tsinkar mata da gaba, runtse idanu tayi zuciyarta na mikata wani mataki mai girman gaske tana jin yarda zuciyarta ke kara buɗewa da wani al'amari mai girma a gareta, sosai take jin wani shauƙi da begen Dr.Karami na kara bula mata jikinta ta ko ina, burinta da fatan ta za su cika muraɗin zuciyarta yau zai kasance tabbatacce.
A hankali ta kai hannunta ta dauki wayar gami da kaiwa kunnanta bayan ta latsa madannin ansa kira.
Wani numfashi mai sauti ta ji ya ajje, kafun ya saki wani murmushi da taji shi har kunnuwanta runtse idanu tayi, tana buɗe su sosai.
"Me yasa haka Mariya. kin san dai a irin wadannan lokutan sosai nake bukatar ki kusa dani ko na ji muryarki, amma tun jiya nake kiran wayar nan kin ki dagawa kin san kuwa yarda nake ji a raina, kin san kuwa irin damuwar da na shiga jiya zuwa wannan lokaci, ji nake yi kamar bani ba, zuciyata nake ji kamar ba ta kirjina kwata-kwata...".
Da sauri ta zare wayar daga kunnuwanta tana duban fuskar wayar, don tabbatar da wanda take waya dashi. jin abin take yi kamar a mafarki, gani take yi kamar ba Dr.Karamin da ta sani ba, sautin kalaman take ji suna ansawa a cikin kunnuwanta da zuciyarta suna haifar mata da kasala.
"kice wani abu mana Mariya Please, kin ganni nan yanzu haka na kasa shiryawa saboda rashin jin ki ko barci banyi ba jiya, sosai nake ji a jikina kamar akwai abin dake faruwa dake".
Numfashi ta ja lokacin da ta mai da wayar kunnuwanta, tana jin yarda yake furucin nasa mai kokarin rikita mata lissafi, muryar take ji kamar batasa ba, muryar take ji ta sauya mata...
"Please ki ce wani abu da zai karamin karfin guiwa mana, na kasa shiryawa, kin ga Dr.Aqeel har ya gama shiryawa tun dazu yake kirana a waya, suna hanya amma ni nakasa aikata komai Mariya sosai nake jin wani iri a jikina, sosai nake jin kamar akwai abin da zai faru..."
Runtse idanu tayi gabanta yayi wani irin dokawa, mikewa tayi kan kafafuwanta kafunta ja numfashi mai tsayi.
"Nima haka nake ji a jikina, ban san dalili ba".
Ta fadi da wata irin murya mai taushi, wacce bata san tana da irinta ba.
"Yaa Rabbi!!".
Ya furta da sauti, kafun ya saki muryarsa sosai.
"Dafatan dai ba wani abu bane yake damun ki ba, Mariya Please fada min abin da ke damun ki...ko da yake bari na zo yanzu kin ji...".
"A,a ba sai kazo ba, ba komai Allah..".
Ina! tun kafin ta ida zancenta har ya kashe wayar, sosai taji jikinta yayi sanyi komawa tayi ta zauna ragwaf! tana mai da numfashi bata san abin da ke damunta ba, gabadaya take jin wani iri a jikinta, kamar bata da lafiya.
Sallamar da akayi ne ya katse mata hanzari, wasu mataye guda biyu suka shigo fuskarsu kunshe da murmushi suka isa gareta kallo daya tayi musu ta gane su waye, itama murmushin yaƙe tayi musu kafun ta hadiye abin da take ji ya tsaya mata a makoshi.
"Ya kamata ki tashi ki yi wanka fa, lokaci tafiya yake yi kin ga har su Baffa sun wuce wajan daurin auren".
Wani irin bugu taji gabanta yayi runtse idanu tayi, kafun ta buɗe su a saitin su, tana duban su daya bayan daya, wannan rana sosai take jin ta tana haifar mata da wani yanayi a zuciyarta, da ma jiki baki daya. komai take jin yana sauya mata komai na duniyar take ji yana canzawa.
"Yaa Mariya..Yaa Mariya".
Mu'azzam ne ya shigo da gudu har yana kokarin faduwa, Mariya ta kai hannu ta riko shi tana dubansa.
"Kizo wai inji...".
Da sauri ta rufe masa baki, tana ajje numfashi. a zuciyarta ta shiga mamaki da tu'ajibi akan zuwan Dr.Karami, don ta tabbata shi ne ba wani ba. tana mamakin sa cikin yan kwanakinnan musamman irin kulawa da yake bata, numfashi ta ja kafun ta dubi su Asiya da suka zuba mata idanu, kau da kai tayi yarda zata fita ne take tunani ta tabbata ba za a bar ta ba, amma zuciyarta sai tunzurata take yi akan ta fita taje domin kuwa ita akaran kanta tana son ganin sa.
Mikewa tayi ta ja hannu Mu'azzam sukayi tsakar gida, su dai su Asiya ba su ce mata komai ba, sai bin ta suke da kallo, ba su gano abin dake faruwa ba.
A hankali suka karasa tsakiyar tsakar gidan hankalin yan biki duk yana wajan aikin da suke, kara sauko da gyalen jikinta tayi, ya rufe mata fuska sosai, sai da ta tabbatar ba Umma a wajan da sauri ta fada soro sannan suka tsaya ta dubi Mu'azzam.
"Dr.Karami ne?".
Gyaɗa kai yayi. Batare da ta sake cewa dashi komai ba, suka nufi waje can ta hango shi jikin motarsa, jikinsa sanye da riga da wando kananu wani haske taga ya kara yi mata gami da kwarjini kau da kan ta tayi, zuciyarta na mikata matakin son Dr.karami da take jin yana kara narkar da zuciyarta.
Sam bai lura da su ba sai da ya dago kansa daga wayar da ake ta faman kiransa ya kasa dagawa, da sauri ya shiga takowa garesu ji yake yi kamar fizgarsa ake yi idanuwansa gabadaya suna kan Mariya ya kasa dauke su, har ya iso inda take tsaye bai sani ba numfashi ya ja lokacin da yaji wani kamshi mai ratsa zuciya na dukan hancin sa, idanu sosai ya zuba mata kafun ya shafi fuskarsa.
"Me ke faruwa ne?".
"Ba komai".
Ta bashi ansa a daidai lokacin wayarsa ta sake daukar burari da sauri suka dubeta su duka, sunan kawunsa ya gani da sauri ya daga, ba tare da yace komai ba na yan sakanni ya numfasa.
"Ga ni nan zuwa Kawu, ina kan hanya yanzu haka kayi hakuri".
Ya fadi yana sauke wayar, idanu ta kura masa kafun ta ce.
"Sai da nace karka zo, don Allah ka tafi na san suna can suna jiranka".
Tana gama fadin haka ta juya cikin gida da sauri, tana jin yana kiranta amma ko ta kan sa ba ta bi ba, saboda yanayin da take jin dukan zuciyarta.
*****
Misalin karfe daya da mintina ashirin aka shaida daurin auren DR.HISHAM MUKHTAR KARAMI da MARIYA BELLO GWADA sannan na DR.AQEEL MUNKA'IL da BASEERA HARUNA SA'AD daga karshe aka daura na HAFSAT DANLITI da HUZAIF ABDURRAZAQ sosai babbar masallacin juma'an garin Gwada ya cika, sai kace ranar idi gabadaya ma garin in ka shiga zaka gane ana gagarumin biki, Angwaye biyu bakin su a buɗe cike da farin ciki da muraɗan jindadi, haka yan uwa da abokanan arzuki, sai dai Ango daya in ka kalle shi kamar bakin kumurci haka ya koma, domin ana gama daurin auren ya bar wajan zuciyarsa yake ji tana zafi da raɗaɗi bai so zuwa ba kawai don ba yarda ya iya ne huzaif wannan ranar ta kasance masa ta bakin cikida takaici a filin duniyarsa, bai taba zaton abin zai tabbata ba sai yau, sosai yayi kudiri a zuciyarsa sai ya baiwa Hafsat mamaki sai ta gwammace zaman gidan yari da gidansa, sai ya gana mata azabar da sai tafi kaunar mutuwar da ita.
Misalin karfe biyar na yamma aka shirya hadaddiyar Dinner a Hdyro hotel dake cikin Birnin Minna, sosai liyafan ta hadu waje ya cika makil amare da angwaye sun sha kyau na musamman kowa ka gani fuskarsa kunshe da farin ciki da jin dadi.
Misalin karfe tara aka tashi ko wacce amarya da ta wagarta suka nufi gidan su, zuwa lokacin Mariya ta gama sadakarwar komai ya tabbata, ta zama matar Dr.karami sosai take jin zuciyarta na buɗewa tana kara haifar mata da son sa, komai take ji nata na duniya ta mika masa.
Lokaci lokaci take dauke hawayen da suke kwaranyo mata musamman in ta tuna rayuwarta a can baya, yarda ta kasance wai yau ita ce a wannan mataki ikon Allah kenan.
Ko da suka koma gida nasiha sosai akayi musu mai ratsa jiki da zuciyar duk wani wanda yake zaune a wajan, Mariya kuka take yi mara sauti tana jin yarda a yau za ta rabu da Ummanta, zata rabu da Abban ta da Mu'azzam din ta, lokaci guda ta tuna lokacin da Dr.Karami yake cewa da ita anya zata iya rabu da Mu'azzam yarda take nuna masa so da kulawa?.
Tabbas yau ga ranar ta zo ranar da zata koma wani gida na daban, gidan da Umma tayi mata fatan zama na har abada.
A banagaren Hafsat kuwa rigima ce ta kaure sosai domin suna zuwa gidan amarya suka tadda su Assama'u sun kasa sun tsare tun daga lokacin da Hafsat ta sako kafar cikin gidan bayan an gama artabu wajan daukota don sai da akayi dak'yar sannan aka aiko da mota daya abin ya kara tayar mata da hankali ganin irin luntsuma luntsumar motocin da aka zo daukar Mariya da su sun yi jejir gwano a kofar gida hakan ya kara tabbatar mata da cewa Huzaif da gaske bai kaunarta.
Numfashi ta ja wasu hawaye su zubo mata a kunci zuciyarta take ji tana sanar da ita irin kalubalan da zata fuskatan tun a yanzu a daren farkonta an fara yi mata rashin mutunci da wulakanta wanda suka kawo ta ina ga kuma an barta ita kadai ta san Huzaif da su Assama'u romanta ne kawai kila ba za su sha ba...
*Kamala Minna*💞💞😘😘😘
[11/2, 8:27 AM] DEENY MINNA🙋♂: UKU BALA'I
NA.
KAMALA MINNA.
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร.
BABI NA SABA'IN DA BIYU.
*BAYAN WANI LOKACI...*
Sosai take kuka ta mike kan kafafuwanta gabadaya take jin jikinta wani iri, ga wani zafi da radadi dake jinsa a duk wata gaɓa ta jikinta nayi mata, bata taba zaton muguntar Huzaif ta kai haka ba, bata taba zaton rashin imanin nasa ya kai haka ba, ta yi zaton zaman na nasu zai sauya tayi zaton zasu fahimci juna, ashe ba haka bane duk inda take zaton Huzaif ya shalle tunaninta da nazarinta.
A hankali ta shiga dafa bango tana jan kafafuwanta har ta isa kofar toilet ta buɗe ta shiga, zuciyarta take ji tana kuna da suya ji take yi kamar zuciyar zata faso son sa na nan har yanzu ba abin da ya ragu, sai ma kara buɗewa da zuciyarta take yi da son sa.
Ruwa mai dumi ta cika kwarmin wanka da shi sannan ta shiga sosai zafin ke ratsata ta ko ina, sosai take jin zafin na kaiwa duk wani sashi da gurbi da take jin yana ansawa.
Runtse idanu tayi lokaci guda ta buɗe, sosai take jin rashin nadama akan son Huzaif alkawari tayi ko da yana yankar naman jikinta zata zauna dashi har karshen numfashinta, ta gwamma ce ta ji azabar gidan miji da dai ta koma waccan bakin gidan na Goggo Marka, ta koyi rayuwa tun daga irin cin zarafi da cin mutunci da gori da ta ake mata a wannan gidan ta tabbata in ba tayi wasa ba su Assama'u so suke su fidda ita, amma zata jajirce zata nemi gafarar Allah ya yafe mata laifukanta ta sani abubuwan da ta aikata ne yake bibiyarta ba komai ba a duniyar rayuwarta.
Ta jima kafun ta tsane jikinta ta fito sam ba ta lura da mutum dake tsaye bakin kofa ba yana ta faman sakar mata wani irin kallo, sai da ta zauna bakin gadonta sannan ta lura dashi gabanta taji ya yanke ya fadi runtse idanu tayi tana tuna artabun da suka kwasa a jiya zuwa yau, goshin sa ta kalla kinkimeman bandeji ta gani runtse idanu tayi tana tuna fadawa da Huzaif yayi jikin Mirrow ya fasa masa goshi, sosai ya yanke shi don jiya ta ga ta shin hankali bata taba zaton Huzaif zai rayuwa ba, musamman irin jinin da ta ga ya zubar da irin sambatun da yake yi.
A hankali ya shiga takowa ya iso gareta gefenta ya zauna fuskarta da wani irin yanayi mai cike da alamun nadama idanuwansa sun kada sunyi jajir gabanta ne ya yanke ya fadi sosai take kokwanto akan abin take hangowa cikin idanuwansa tausayi abin ya bata mamaki.
*****
Hajiya Layla ce ta dubi Khairiyya dake zaune ta zabga tagumi LAMARIN DUNIYA gabadaya ya kara hargitsa mata lissafi, komai na duniyar take jin sa wani iri babu dadi, duk da a yanzu bata da wata matsala a rayuwarta wacce zata addabeta amma in ta tuna wacece ita sai taji zuciyarta na kuna gami da suya, hawaye suka zirnano mata a hankali ta dauke su tana ajiyar zuciya.
"Khairiyya!".
Hajiya Layla ta fadi da sauti a muryarta mai cike da rarrashi da karfafa mata gwiwa akan lamarin rayuwar da suke ciki a yanzu, kusa da ita ta karasa tana toshe bakinta jin tari na kokarin sarke ta, a hankali ta zauna tana mai yatsine fuska alamun akwai abin da ke damunta na rashin jindadi.
"Haba mana Khairiyya. bana so nake ganin ki cikin wannan yanayin gabadaya sai naji babu dadi, na rokeki ki mai da komai ba komai ba duba za kiyi da baya da irin rayuwar da mu kasance da kuma yanzu, ai abubuwa sun yi sauki kuma kisan ita rayuwa ba ko yaushe take zama daidai ba, kuma ba wani bawa a doron duniyar nan da zai ce miki ya dawwama a farinciki da kwanciyar hankali a rayuwa kowa da yarda Allah ya ke kunsa masa matsalarsa, sai dai ace ta wani bawan tafi ta wani".
Ta karashe tarin na kara sarke ta, da sauri Khairiyya ta dube ta cikin yanayi na tausayawa.
"Maama kin sha maganinki kuwa?".
Gyaɗa mata kai tayi gami da sakin murmushi kafun ta dafa kafaɗarta.
"Khairiyya Ina son mu sake zama na biyu dake, kuma ina so wannan zaman ya zama na karshe tsakanina dake, sannan ki sani ba zan tursasaki ba sannan ba zan yi miki dole b,a ni dai fata na kawai ki samu kwanciyar hankali ako ina kike shine BURINA sannan shi abin da na fi bukata a duniyar nan, Khairiyya so nake yi na zama sanadi na wanzuwar farin cikin ki har kashen numfashinmu a doron duniyar nan...".
"Maamaa".
Khairiyya ta fadi da alamun rigima a muryarta, kafun ta juyo sosai ta fuskance ta tana bayyana wani kunshin murmushi, wanda ta san zai kara kwantarwa Hajiya Layla da hankali.
"Ina jin ki faɗa mani menene zan anshe shi a duk yarda ya zo mani, zan yi AMANNA dashi BURINA a duniyar nan shine na faranta miki, kullum na ganki cikin farin ciki Maama kece farincikina kece komai a rayuwata kece kika zama tsanin ganin rayuwata ta gyaru...".
Hawaye ne suka kwanranyo mata da sauri ta kau da kanta, tana jin yarda zuciyarta ke kara buɗewa farinciki na kara samun gurbi a cikinta.
"Maganar Alhaji Abdulwahaab Khairiyya ina muka kwana?".
Ta fadi tana saka idanuwanta cikin na Khairiyya, so take yi ta hango gaskiya, so take yi ta gano in da Khairiyyar ta dosa da batun, so take yi ta ga yanayin ta ko na sauyi a yarda ta dauki maganar a yanzu.
Numfashi taja gami da fesarwa kafun ta mike kan kafafuwanta, zuciyarta take ji tana kara buɗewa kaunar da Hajiya Layla take nuna mata bata san da mai zata saka mata ba, ta nuna mata so ta nuna mata kauna tayi tattalinta ta bata duk wani lokacinta, sannan ta bata farincikin daidai iyawarta ya kamata ita ma ta nuna mata godiyarta sannan ta anshi duk wani abu da ta zo dashi, hakan zai kara tabbatar wa Hajiya Layla da cewa sun zama UWA DA 'YA.
"Maama na lura dai so kike yi ki samu suruki".
Ta fadi fuskarta da murmushi ita ma Hajiya Layla murmushi take yi kafun ta mike tana faɗar.
"Ba suruki kadai ba har da jikokina nake so na gani, kafun lokacina yayi so nake yi ni dake ki saman mana DANGI da zuri'a, zan yi alfahari da hakan sannan ko na mutu zan san nima ina da dangi".
Ta karashe da kwalla a idanuwanta.
"ki anshe shi a matsayin miji na san Alhaji Abdulwahaab zai rike ki a yarda kike zai kula min dake, zai tattale ki zai zama MIJIN MARAINIYA a gareki, na san ba zaki taba kokawa ba duk da dai an san DAN ADAM ajizi ne, amma a zuciyata fata nake ke da Alhaji Abdulwahaab ku zamo abu daya har a gidan aljanna".
"Shikenan Maama nifa wannan kukan naki ne bana so, Allah ki dai batun Alhaji Abdulwahaab kuma ai tuni labari ya sauya kawai fadi miki ne ban yi ba".
Zaro idanu Hajiya Layla tayi cikin alamun mamaki, kafun ta kai wa Khairiyya dukan wasa ta goce.
"Ja'ira dama kallona kawai kike yi, ina kidina ina rawa ta ko? Allah ya shirya min ke ni nan na saki baki ina cewa sai na hada miki da tsayuwar dare ayi auren nan, ashe tuni kin mai dani wata kakarki to ai shikenan Allah yasa hakan shine yafi zama alheri a garemu ga baki daya, Allah yasa fatan da muke ya tabbata Allah ya kau da duk wata fitina da abin ki Allah ya kare miki rayuwa 'yata Allah ya kawo zuri'a tagari kiyi ta haifar mani tagwaye".
Ta karashe tana goge hawayen da suke zubo mata ta jawo Khairiyya jikinta ta rungumeta sosai suke jin wata natsuwa da kwanciyar hankali na wanzuwa garesu.
"Ameen Yaa Rabbi Maama na".
Khairiyya ta ansa muryarta na rawa.
******
Da Sallama ya shigo cikin gidan, yana bin duk wata kusurwa da kallo yarda gidan ya dawo tsaf! komai ya zama sabo zuciyarsa yake ji tana kara buɗewa da farinciki gami da kwanciyar hankali, ba abin da zai ce sai godiya ga Allah da kuma Dr.Karami da ya zama sanadin samun waraka a rayuwarsu duban jikinsa yayi kafun ya sake duban gidan kwalla suka tarun masa kafun ya dauke su, a hankali ya shiga takawa yana isa dakin Umma, daga labulan yayi bakin sa da Sallama.
Zaune take gabanta da katuwar roba mai cike da CAKE tana lissafawa jin sallamar maigidan ne ya sanyata tsagaitawa, ta ansa sallama tana kokarin mikewa ta anso kayan hannunsa ya iso da sauri yana fadin.
"Matar nan kin zama Hajiya fa Kasuwancin nan ya anshe ki sosai kin yiwa 'yata wayo ita da koya ke da karbe sana'ar".
Murmushi tayi kafun tace.
"Yo da zaman banza ai gwanda aiki kishiya kuma ai bani nace ta bar mani ba kuma ko ma kace na anshe mata ai ba gida daya muke ba ita za ta iyayin nata a gidan auren ta kowa ya ci da rabon sa".
Zama yayi yana mai fadin.
"To Allah ya dafa mana kin ga na shagon ma da kika kai shekaran jiya kusan karewa na lura Cake din nan yana karbuwa sosai wajan jama'a da mutum yaji cikin sa yana masa yaƙi sai ya zo ya hada da lemo sai ki ga ya dawo hayyacinsa".
Murmushi tayi batare da ta kara cewa komai ba, amma zuciyarta tana goɗewa Allah tana shiwa Dr.Karami Albarka yarda ya fiddo dasu daga cikin kangin rayuwa ya baiwa mijinta jali ya buɗe shagon kayan bukata na rayuwa gashi ita ma sanadin karatun 'yarta ta samu sana'ar yi ba abin da zata cewa Allah sai godiya da fatan karin kwanciyar hankali daga gareshi.
"Wai ina karya jali yake ne?".
Ya tambaya yana murmushi, dubansa tayi.
"Au kai ma Mariya ta bar maka sara ko ɗan nawa ne karya jali ai yanzu na uwarsa ne ko ya karya ba damuwa wata rana shi zai daura...yana can ya tafi Islamiyya".
Dakin ne ya dau shiru na dan lokaci, kafun Bello ya ja dogon numfashi ya dubi Umma.
"kisan mi ina labarin yan matan nan da nace miki mun hadu da su wajan mutanan nan da suke garkuwa da mutane?".
Umma ta gyaɗa kai tana gyara zamanta ya cigaba da fadin.
"Yanzu a shagon Alhaji Adamu mai bulawus na gan su an nuna a talabjin ashe lokacin da na bar su tana da juna biyu shugaban tawagar na su shi yayi mata a cikin sauran yan matan ma akwai masu juna biyu duk sun haihuwa yau na ga shari'ar da aka yi musu yau aka yanke musu zaman gidan kaso na rai da rai duk kan su su kuma yan matan gwamnati ta dauki nauyin rayuwarsu saboda kin san garin na su an kone duka sannan duk an kashe iyayen su ba su da kowa ba su da komai yanzu naji tausayin su sosai".
Umma ta dauke hawayen da suka zubo mata domin ta jima tana tuna wannan labarin na mutanan da suka kama mata miji sannan da yan matan da ya bata labari akan su.
"Allah ya sa iyakar wahalar rayuwarsu kenan Allah ya jibanci lamarin su su kuma wadannan mutane Allah yayi mana tsari da irin su ya kare mana rayuwa da ta yan uwanmu daga fadawa hannun su".
"Ameen Ya Rabbi".
Ya ansa jiki a sanyaye yana mikewa.
"Ka duba Jin Goggo fa don Allah Malam bai kamata ace kana mata haka ba, ita ma uwa ce a gareka duk wani abu da tayi maka na cutarwa ina rokon Alfarma ka yafe mata, rayuwar duniyar nan ba komai bane...".
"Naji kuma ai ni tuni na yafe mata, kowa dai yayi na gari dan kan sa".
"Malam don Allah ka manta komai a rayuwarka da tayi maka, ita ma ai tayi nadama ko halin da take a ciki yanzu yaci ace ka tausaya mata".
Bai sake fadin komai ba ya fice daga cikin dakin, tsayawa yayi yana kallon dakin Goggo Marka kamar ba zai je ba, sai kuma ya taka a hankali ya isa kofar dakin daga labule yayi can karshen gado ya hangota gabadaya ta gama yankwanewa idanuwanta a buɗe tarwai sai dai ba su da amfanin komai kusan watanni hudu kenan cutar MAKANTA ta lokaci guda ta kama ta tun da akayi wata iska kura ta shigar mata idanu shikenan ta makance kuma dama gashi tana faman da cutar hawan jini da tayi mata mugun kamu har ta kashe mata ɓarin jiki tashima bata iyayi daga kwanciya sai kwanciya...
*Kamala Minna*😘😘😘
[11/2, 11:56 AM] DEENY MINNA🙋♂: UKU BALA'I
NA.
KAMALA MINNA.
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร.
BABI NA SABA'IN DA UKU
*MARUFI...*
"Mai Ciki".
Kamar daga sama taji sautin muryar Bassera na fadin haka, cikin dariya a hankali ta mike tana gyara doguwar rigar dake jikinta, ta taka hankali ta nufi kofar fuskar da murmushi, Handle din ta rike gami da buɗewa.
Baseera ce tsaye, hannunta sarke da na Dr.Aqeel hankalinsa gabadaya na wajan wayar da yake yi sai ɗan ta TAUFEEQ dake sagale a kafaɗar Dr.Aqeel din.
Numfashi Mariya ta ja kafun ta zaro idanu waje, da sauri ta koma ciki tana mai kwalawa Dr.karami kira, da yake kicin. Wai yana yi mata wainar fulawa tunda ta tashi take kwadayinta shi kuwa ya zage sai yayi bayan kuma tace zata aikawa Umma tayi mata, yace bai amince ba shi ma ya iya.
Da sauri ya fito idanuwansa sun yi jajir, hannunsa rike da cokali fuskar gefe guda duk Manja, bata san lokacin da ta kwashe da dariya ba ta shiga nuna masa kofar shigowa falon tana yi masa alama da baki amma ya kasa gane wa, sai ma harara da wurga mata yana fadin.
"Ni ko ai ko ba za ki ci wainar nan ba tun da abin ya zama haka...".
Bai karasa ba Baseera ta bayyana cikin falon, duban su tayi kafun ta sauke idanuwanta a saitin Dr.Ƙarami da yayi wiki-wiki dashi.
"Iyee ba shakka, likita kai ne haka".
Ta fadi tana kwashewa da dariya, a sa'ilin da Dr.Aqeel ya sanyo kai shima yana kokarin sauke TAUFEEQ a kafaɗarsa, ganin abin da ke faruwa ya sanya shi isa cikin falon da sauri ya kwantar da Taufeeq da ya yi barci ya zauna gami da zabga tagumi yana kallon Dr.Karami, kafun lokaci guda ya kwashe da dariya.
"Aboki ashe kai ma kuku ka zama tabbas arzuki yaci uban na da, an sai da gida an sai yashi".
Gabadayan su suka kwashe da dariya, kafun Dr.Karami ya juya da sauri ya fada kicin, yana tuntsirar dariya shima.
"Billahillazi baki da M matar nan yanzu Doctor guda ya zama kukun ki".
Baseera ta fadi tana duban Mariya, taɓe baki tayi tana mai cewa.
"Dadin abin ai ba ni kadai ake yi wa wannan gatan ba na ga wata mike kafa take yi ta tura mijin nata kicin ya yi ta fama da cokali a hannunsa".
"Rabu da ita Maman Jawwad yanzu haka kafun mu fito, nifa nayi girkin wai bata da lafiya ba yarda na iya haka na shiga na zabga girkin kuma saboda rashin tsoron Allah ta miki kafa ta buɗe ciki ta ci".
Dr.Aqeel ya fadi yana marere cewa alamun ya ji jiki wani kallo Baseera tayi masa kafun ta ce dashi.
"Au haka ma zaka ce? to shi kenan tun da kace haka da ga yau raba girki za mu din ga yi da kai, kowa ya din ga yin kwana bibbiyu".
Zaro idanu yayi gami da daura hannu aka, kamar wanda ya ga wani mugun abu ya shiga marmaɗi da idanu kamar wanda yayi wa sarki karya.
Baki Mariya ta saki ganin yarda yayi a daidai lokacin shi kuma Dr.Karami ya fito, hannunsa dauke da faranti shake da wainar fulawa taji manja ya iso gaban Mariya ya kalle ta sama da kasa kamshin wainar ta doki hancinta lokaci guda taji miyau dinta ya tsinke, da sauri ta kai hannu zata dauka ya kau ce yana yi mata gwalo gaban Dr.Aqeel ya isa ya zauna ya dube shi.
"Wannan aikin maza, ne don haka zo mu ci a tsakaninmu, in sun yi zuciya suyi na su mugani".
Ya fadi yana daukar waina daya ya kai bakin sa kafun ya mike ya nufi firji ya buɗe ya dauko musu gorar ruwa da ta lemo masu rangwamin sanyi.
Baseera baki ta saki kafun ta dubi Mariya dake tsaye tana ta faman hadiye yawu, fuskarta duk tayi wani iri kamar zata fashe da kuka a hankali Baseera ta mike ta dube su.
"Dadin abin mu ba kutare bane, sannan kuma muna da hannun da za muyi bari ma ku gani".
Tana fadin haka ta mike ta nufi in da Mariya take sai faman hadiyar yawu take ta rike hannunta suka nufi Kicin.
Da gudu Dr.Karami ya mike hannunsa da waina daya gaban su ya sha ya riko hannun Mariya gami da bude mata baki, ya tura mata wainar aiko kamar jira take ta shiga taunawa har tana kokarin kwarewa.
Baya Baseera tayi tana kallon ikon Allah kafun ta juya ta dubi nata Mijin da ya dauke kai yana ta faman kai loma bakinsa.
"IKON ALLAH"
Abin da ta fadi kenan tana rike haɓa.
*****
Karar faduwar abu ne ya sanyata fitowa daga kicin cikin sauri, sai faman jan kafa take yi da turtsetsen cikin ta tana cizon laɓɓanta daidai benen da zai kai ta sashinta kafarta ta turguɗe ta yo baya runtse idanu tayi don ta sadakar taje kasa har ta hango irin zabar da wahalar da zata sha jinta tayi jikin mutumin da bata taba zato ba, wani numfashi ta ajje a daidai lokacin da ya riko mata kugunta ya haɗe da jikinta sosai kamshin turaren sa Dark-wood wanda ya rigaya ya zama jikinsa ya daki hancinta hakan ya kara sanyata lafewa a jikinsa.
Sun dau lokaci a haka kafun ya ja numfashi bayan ya gama shinshinar kamshin da ke fita daga cikin sumar kanta da ta sha gyara ta tufketa da rumbos.
"Kashe ni zaki yi ko Preety?".
Ya fadi yana mai dago haɓarta da hannu daya, idanuwanta a runtse suke har zuwa wannan lokacin taki buɗe su ita kadai ta san yanayin da take ciki a wannan mataki, zuciyarta take ji tana mikata wata duniya ta daban mai cike da farin ciki na tsanani kaunar da take ji zuciyarta na kara narkewa ta mijin nata abin alfaharinta.
Iska ya shiga hura mata a idanu ta shiga motsa manyan kwayan idanuwanta ba tare da ta buɗe ba, wani murmushi na kara bayyana a saman ƙyankyawar fuskarta wacce tayi fayau ba digon ko tabo a jikinta laɓɓanta masu taushi da kalar ja sai faman motsa su take yi a hankali ta shiga buɗe idanuwanta daya bayan daya ta sauke su a saitin fuskarsa.
"Jawwad!".
Ta fadi da wani irin sauti a muryarta kafun ta shiga kokarin mikewa daga lallausar jikin nasa da bata gajiya da kwanciya a kanshi kirjinsa da ya zame mata abin kwanciya a kullum in ba a nan ta kwanta ba ta taba jin dadi sannan ba ta iya barci.
"Me ya yi kuma?".
Ba tace komai ba ta mike daga jikin nasa gabadaya ta kwace kanta daga rikon da yayi wa kugunta a hankali ta shiga takawa tana kokarin hawa sama amma jin yarda kugunta ya ansa ya sanyata tsayawa cak! tana mai cizon laɓɓanta.
"wash!!!".
Da hanzari ya riko ta, yana mai duban inda ta rike.
"Ya dai me ke damun ki haka?".
Turo bakin tayi gaba gami da taba kugun nata da take jin sa kamar zai karye.
"Shiyasa nace maki ki dawo dakin kasa da zama amma kin ki wannan benen so yake yi ya karya min bayan mata wallahi".
Kafin ta ce wani abu caraf! ya sungume ta kamar wata Baby ya hadata da jikinsa sosai ita kuwa ta shiga kiciniyar kwace kanta amma ina rikon da yayi mata ba na wasa bane hakan yasanyata yin lamo a bayansa tana cizan masa kunne har suka isa dakinta da sauri tace dashi.
"Don Allah sauke ni Jawwad yana ciki fa!".
"Ai baki isa ba wallahi sai na kai ki har ciki sannan na rama cizo na da kikayi mani".
Jin abin ya yace ya sanyata marere cewa tana shagwaɓe baki alamun son yi kuka hakan da yaji da sauri ya sauke ta yana riko hannunta.
"Ai wallahi sai na rama haka kawai so kike yi ki rage mani farashi budurwa tace bata so na ko".
Zaro idanu tayi waje tana dubansa gabanta taji ya yanke ya fadi kafun ta tako kusa dashi tana zira idanuwanta cikin nasa.
"Me kake cewa wacece gangancin da neman ciwon zuciya take so ta zama MATAR MIJINA a garin nan?".
Yanayin da ta nuna yayi matukar bashi mamaki bai hango wani razana ko tsoro a idanuwanta ba amma ya hango tsantsar so da kuma kishi na asali a cikin idanuwan nata.
"Abin da kika ji shi na fadi".
Ya karashe yana rike Handle din kofar ya tura yana kokarin shiga ciki da sauri ta sha gabansa tana sake saka idanuwanta cikin nasa.
"Ban hango akasin gaskiya a idanuwanka ba bai kamata kake barin harshen ka na kokarin fadin abin da ba daidai ba".
"Injiwa ya fada miki ba gaskiya nake fadi ba ai kina sauke mani TAGWAYE na zan dakaro miki sabuwar amarya fil a leda".
Zaro idanu tayi kafun ta mai da kallonta zuwa cikinta ta shiga shafawa.
"Tagwaye fa kace ni gaskiya a,a cikina guda daya ne kacal zan haifa ba wani tagwaye".
"Au! Wasa kika dauka to ai shikenan Allah ya kamu lokacin zaki ce na fada miki".
Ya karashe da dariya sosai a fuskarsa ya fada cikin dakin, sake da baki ya barta tana bin sa da kallo, sannan ta bin cikin nata da yayi katoto ba kamar cikin Jawwad ba gyaɗa kai ta shiga yi, a zuciyarta tana jin kamar maganar Dr.Karami gaskiya gabanta taji ya yanke ya fadi ba abin da ta tuna sai lokacin haihuwar Jawwad yarda aka sha artabu.
Wata dariya ce ta zo mata lokaci guda ta saketa da gudu ta fada cikin dakin duban Dr.Karami tayi da ya baje a gadonta can gefe kuma Jawwad ne da kwalbar Humra din ta da ya tarwatsa ta da sauri ta isa gareshi yana ganinta ya mike yana shirin gudu ta riko shi sannan ta dubi Humra din da ta kwarare a tsakar dakin sannan ta dubi Dr.Karami kara ta saki a razane ya tashi yana dubanta wani kallo ta watsa masa kafun ta turo baki gaba tana nuna masa Humra din ta dariya yayi kafun ya dubi Jawwad da yayi tsuru-tsuru.
"Ni fa ba ruwana ke da ɗanki ne jiya nan yayi mani barna zan dake shi kika hanani don haka sai ke kiji in dadi".
Jin abin da yace yana kunshewa dariya hakan ya sanyata duban Jawwad ta talla ke masa keya ta shiga dire-dire da kafafu tana shagwaɓe fuska alamun son yin kuka.
Da sauri ya taso ya iso gareta ya kamota ya hadata da jikinsa sosai ya sanya bakinsa saitin kunnanta yana yi mata raɗa fizge kanta tayi ta tureshi bai ankara ba yaji ya faɗa kan gadon bin shi tayi tana kokarin turmushe shi yayi sauri matsawa gabadaya ta fada kan gadon binta yayi ya danne yana mai yi mata cakulkuli dariya ta shiga yi sai da yayi mata lilis da jiki sannan ya daga ta idanuwanta a rufe sai mai da numfashi take yi kiss ya manna mata a kumatu kafun ya riko hannunta ya shiga kallonta zuciyarsa na kara buɗewa sosai a son ta GURBIN SO da ya bata a duk wani fanni na zuciyarsa yake ji yana kara buɗewa da kaunarta kaunar da har abada ba ya tunanin zai iya yiwa wata ƴa mace a filin duniyar nan.
"INA KAUNAR KI".
Ya furta da wata irin murya da ta galabaitar da zuciyar Mariya a lokaci guda ji take yi zuciyarta na mikata wani waje na musamman mai tatttare da so da kauna zalla ta Dr Karamin ta sosai take jin zuciyar na kara buɗewa da kaunarsa sosai take jin duk bugun numfashinta na kara haifar da sabuwar kaunarsa a zuciyarta.
"INA KAUNAR KA".
Ita ma ta fadi da wata murya da ta daki kunnuwansa runtse idanu yayi yana jin yarda bugun zuciyarsa ke karuwa saitinta yaje ya kwanta yana jawota cikinta sosai ya matse ta har sai da ta saki ƴar kara ta buɗe idanuwanta.
"Dady kai ko".
Kamar daga sama suka jiyo muryar Jawwad na fadin haka da sauri suka dube shi don sun manta ma dashi a wajan gwalo Dr.karami yayi masa kafun ya mika masa hannu alamun ya taho da sauri yaje maimakon yaje wajan sa sai ya nufi wajan Mariya da sauri yana faɗawa jikinta.
Dukkansu ya hada ya matse a jikinsa yana furtawa Mariya kalamai zafafa da suka kara tabbatar mata da Dr.karami na tane ita kadai har gaban abada.
KARSHE!!!.
ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH!! ALHAMDULILLAH!!!
Godiya ga Allah da ya bani ikon kammala labarin na ina godiya sosai ga maso wannan labarin da su ta jimirin bibiyata har zuwa wannan lokaci ina godiya
Ina neman afuwanku ga dukkan wani makaranci da na batawa rai da wanda na sani da wanda ban sani ba ku sani dan adam ajizi ne.
Ku masoya ne ba na tunanin zan yi abu da gangan don na bata muku ku ajje haka a ranku
Yau dai mun sauke labarin Uku bala'i
Shin wani darasi kuka dauka a labarin nan?
Mai ya bata muku rai a cikinsa?
Me yafi faranta muku cikinsa?
Wani jarumai ne suka fi burge ku sannan wanne su ka bata muku rai?
Tsakanin jaruman nan me za ku iya cewa a ko wani dayan su
Kalma akan Mariya
Kalma akan Baseera
Kalma akan Dr.Ƙarami
Kalma akan Dr.Aqeel
Kalma akan Hafsat
Kalma akan Goggo Marka
Kalma akan Areefa
Kalma akan Hajiya Layla
Kalma akan Dr.Erena
Dss
Shawara ko gyara
Kofa abuɗe take
Whatsapp 08076708191
Call 07039355645
Gmail.Kamalminna217@gmail.com
Fatan alheri ga kowa da kowa ina son ku masoya sai mun hadu a sabon aiki a sabuwar shekara mai taken.....😁Sai kun ji...lolz