Bin wayar yai da kallo bayan ya kashe, mikewa yai ya hau kan gado ya dauko littafi daya daga cikin wanda ta bashi yake karantawa, daga nan bacci yai gaba dashi.
Yau kasancewar Asabar ne yana zaune a gun Abba bayan ya taimaka mai yayi wanka yasa kaya, yana zaune suna dan tattaunawa, Abba ke fadamai labaran dayaji a tashar radio na yanda rayuwar yara kanana ke halaka.
Shiru yai da farko ya fara fahimta sai kuma ya tafi tunani, har Umma ta ajiye abinci bai san ta zo ba.
Sai da Abba yace "Khalid?Khalid?"
Kallan Abba yai da sauri yace "Naam."
Umma ta zauna tace "lafiya?"
Kallan Umma yai sannan ya kalli Abba yai murmushi yace "bakomai, ina tunanin abinda ka fadane, sannan na gano kuskurena na kin daidaita mai laifi irin haka."
Abba yace "wacece?"
Kai Khalid ya dan juya kadan yace "watace."
Kauda zancen yai yace "Asiya su Amir sun fice?"
Tace "wlh dazu ina aiki suka gudu."
Suna gama cin abinci ya shiga wanka, yana zaune a daki yai shiru yana tunani, me Zainab zatace mai?
Mikewa yao ganin ba wannan bane yanxu a gabansa dole ya kawar da babban abinda ya kamata yai.
Kai tsaye yawa su Umma sallama ya wuce ya hau bus zuwa kano, a Naibawa ya sauka, gidansu Raziyya ya nema kai tsaye ya nufi gidan yana fatan dacewa da abida yake shirin yi.
A bakin kofar ya tadda dan dattijon dake ta alwala, tsugunawa yai sai daya idar da alwalarsa sannan ya gaisheshi.
Dattijon ya kalleshi tare da ajiye butar a gefe cikin sakin fuska ya amsa ya daura da cewa "Daga ina??"
Khalid yace "Raziyya nazo nema."
Kallansa yai yace "Raziyya? Ai tun sati uku da suka wuce bata dawo gida ba, kasan ba a garin nan take aiki ba."
Kallan tausayi yamai sannan ya jinjina kai alamar gasmuwa yace "in ba damuwa ina san ka dan bani number dazan sameta."
Kallansa yai cikin yabawa da nustuwarsa yace "to."
Wayarsa yasa hannu ya dauko aljuhunsa sannan ya dan kanne ido yana neman number, can ya mikamai wayar yana cewa "gatanan."
Khalid ya amsa da hannu biyu sannany dau number sannan ya mikamai.
Kallansa yai cikin tausayawa yace "ya mai jikin?"
Da sauki yanayin jikin nata ne sai dai hamdalla, da alama kasan Raziyya sosai, yauce rana ta farko da wani ya tambayi abin cikin gida.
Khalid yai kasa dakai kafin ya dago cikin wani yanayi, kallansa yai yace "da wani abin ne?"
Khalid yace "Ina tunanin in ba damuwa ka kira Raziyya ta dawo gida."
Kallansa yai cikin mamaki yace "ta dawo gida kamar ya?"
Shiru Khalid yai kafin yace "an samu matsala a gun aikinta, sai dai rashin san saku a damuwa yasa ta kasa fada, sai dai ina ganin hakan ba karamin matsala bane ga 'ya mace."
Shiru Dattijon yai duk da yaji rashin dadi sosai dayai na rashin aikin daywace sai dai Khalid gani yai wata yar kwalla ta gangaromai, kallansa yai jiki a sanyaye.
Dattijon yai murmushi yana share kwallarsa yace "nagode dan nan, nagode sosai."
Khalid yai shiru, cigaba yai "yauce rana ta farko kuma da wani yaxo yamin nuni cikin hikima akan abinda ke faruwa, maganar gaskiya na dade nima ina zargin aikinta saboda gulma da zaginmu da ake a unguwa, sai dai ganin ita Raziyya ta nuna min ba hakan bane yasa nake kokarin sawa zuciyata ba hakan bane, yau zan kirata ta dawo insha Allah."
Yadanyi shiru kafin yace "Nagode d'an nan Allah ubangiji yasa ka gama da duniya lafiya, ya daukaka ka ya baka zuri'a ta gari."
Khalid jiyai idanunsa sun ciko a hankali yace "Ameen Baba nagode."
Dattijon ya sake kallansa cikin jin dadi, Khalid yamai sallama ya taso gaba daya jikinsa a sanyaye.
Wayarsa ya kalla, yana tunanin kalaman Zainab, wani dan karamin murmushi ne ya bayyana a fuskarsa, ya daga waya ya kira Salmanu.
Suna gama waya ya kashe, ya hau mota ya koma danbatta.
********
Yau tun safe take duba wayarta sai dai haryanzu bataga sako daga Khalid ba, bata minti biyar sai ta taba wayarta, kara volume na ringing din wayar tai wai incase ko sako ko kora zai shiga bata ji ba.
Ganin har dare yayi ba sako ba waya yasa ranta ya baci, ajiye wayar tai ta kwanta cikin rashin jin dadi.
Bayan tayi sallar asuba tana kokarin kwanciya ta dau wayarta.
Sakon data gani ne yasa murmushi bayyana a fuskarsa.
"Send me the address, zanzo Wednesday."
Nima sai anjima zanyi reply, ta fada tare da kwanciya.
A daren ranar ta nufi falan Dady, yana zaune yana waya ta shiga, Basma na zaune daga gefe tanata kara yanka mai cucumber din da yake ci.
Mika mata tai, Zainab tace "Alhamdulila."
Dady ne ya gama waya sannan ya kalleta, Zainab yanxu nake san kiranki ma ashe kinji dawowata."
Tace "an dawo lafiya?"
Yace Lafiya kalau, ya kalli Basma yace "ya isheni haka Hajiya."
Murmushi tai tace "shi yasa nake yankawa a lokacin yanda in yayi sai a ajiye."
Ruwa yasha yana kallan Zainab yace "tunani nake ke ko yar fita bazaki dinga yi ba haka zakiyi ta zama a gida? Ai ko bin Basma kyayi zuwa siyayya haka."
To kawai tace, kallanta yai yace "ya akai?"
Kallansa tai sannan tace "Dama bako zanyi ranar laraba."
Da sauri ya kalleta tare da gyara zama yace "bako?"
Basma cikin jin dadi tace "masha Allah."
Kallanta Dady yai yace "wanene? Ya akai kika hadu dashi ke da kike gida a kunshe?"
Murmushi tai tace "in yazo zaka ganshi, kaima ka sanshi."
Ni?
Ta daga kai alamar eh, gani Dady ya shiga tunanin waye yasa ta mike ta bar falan, tana hawa sama tai shiru a ranta tace "Sorry Dady wannan ita kadai ce hanyar data rage min."
***********
Mabalan botiran rigarsa ya shiga maidawa, agoggo ya kalla karfe 7 na safe, dole ya fita da wuri.
Fitowa yai, ya nufi hanyar Abuja.
Dady kam yana gun aiki yana kiran Basma akan yazo? Tace "a'a"
Itama tana kitchen ana shirya abinci kala kala dan sai da Dady ya sake sanarwa ayi abinci sosai.
Itakam Zainab batama san hidima suke tayi ba daga cewa zatai bako, tana daki tana tunanin yanda haduwarsu da maganar da zasuyi da Khalid, dan zaman datai dashi ta san halinsa sai dai tana ganin shi kadai ne zai taimaketa a wannan lokacin.
Karfe 2 daidai ya sauka garin Abuja, bai kirata ba duk da tace mai in ya iso zata turo a daukeshi, shi kuma gani yake a wani dalilin akuma wani matsayin za’a zo har a daukeshi?
Baisha wahalar ganewa ba saboda gidan mahaifinta sanane ne a unguwar.
A bakin wani tafkeken gida ya tsaya yana kallan gidan kafin ya nufi gate, knocking yai daga ciki mai gadin ya bude kofar.
Gaisawa sukai da Khalid, ya kalleshi yace “Ammm gun Zainab.....”
Jin abin yai banbarakwai hakan yasa yai shiru, da sauri yace “oh ko kaine bakon da za’ai?”
Kai ya daga, budemai kofa yai ya shigo harabar gidan sannan yace “bari na shiga na tabbatar kaine.”
Khalid yace “bari na kirata.”
Cikin jin dadi yace “yauwa to hakan yayi.”
Kiranta Khalid yai, kallan wayar tai, tunda take zata iya cewa gabanta bai taba faduwa dajin ringing ba sai yau, dauka tai cikin dauriya.
“Ina waje.”
“Okay bari na sauko.”
Jiki a sanyaye ya kashe wayar yana kara kallan gidan, tabbas wutsiyar rakumi tayi nesa da kasa.
Bata wani dade sosai ba sai gata ta bude kofar waje.
Daga nesa ta kalleshi, haka kawai ta samu kanta da zuba mai ido tana tunanin yaushe rabo?
Dayake dama can ita macece da batada lokacin wahalar dakai da bata lokaci gun kwalliya.
Tadai sa tsadaden lace dinta ta yafa mayafi light purple kalar lace din ta yafa.
Shikam shadda ce a jikinsa kalar madara an mata aiki da kalar ruwan kasa mai turuwa.
A hankali ya fara takawa, zuwa inda take har ya karaso bakin kofar, nan ta koma ciki ya bi bayanta suka shiga ciki.
Bangaren hagu tai dashi inda falan baki yake, shiga yai ya zauna.
Daga dan nesa dashi ta zauna, kallan juna sukai kawai a tare sukai murmushi.
Kallansa tai tace “murmushin na meye?”
Yace “yanda naga kina yi ne yasani.”
Tace “ban taba kawo wani gidan mu bane bawai namiji ko mace ba wannan ne karo na farko shiyasa nakejin abin daban.”
Kallanta yai yana san cewa Adam fa?
Kamar tasan me yake cewa tace “Adam?Dady ne ya kirashi a waya yazo, so karka min dariya.”
Shiru yai bai ce komai ba.
Bari na kira matar gidan ku gaisa.
Ta mike tai ciki, a kitchen ta taddata sun hama hade kayan abincin da Zainab yasata kallanta cikin mamaki, tace “duk wannan na meye?”
Basma tai dariya tace “Na bakon ne, naso tambayarki ko da abinda yake so Dadynki ya hana yace in kika sani cewa zaki sunyi yawa.”
Baki ta bude tana kara kallan jerin abinci da snacks su fruit da juices.
Basma tai dan dariya tace “inje mu gaisa, dadynki yace a kirashi kafin ya tafi shima.”
Sam mamaki ya hanata magana sai gani tai tasa mai aikinsu ta shiga da dishes din.
Kainta girgiza sannan tai ajiyar zuciya ta juya.
Basma ce ta fito cikin fara’a ta kalla Zainab tana dariya.
Ta sani yanzu zata ta kira Dady ta fesa mai, wucewa ciki tai, Khalid na zaune yana kallan ikon Allah ganin sai shigo da abubuwa ake ana jera wa.
Kunya duk ta kama Zainab, har aka gama, kallansa tai shima kallanta yai, idanunta tadan dauke hakan yasashi dauke nashi shima.
Sun danyi shiru kafin ta kalleshi tace “Yanzu ya zakai dasu Umma?”
Tafin hanayensa ya dan hade akan cinyarsa yace “ina tunanin sanar musu amma sai na samu wani aiki, dan na sake applying a gurare dayawa.”
Kallansa tai tace “I doubt it won’t be easy.”
Kallanta yai yace “it wasn’t easy dama.”
Kai ta dan jinjina alamar eh, shiru suka dan sakeyi kafin ya kalleta yace “Yarinyar nan”
“Wacce?”
Ta tambaya kafin ta hade rai tace “meya faru?”
Shiru ydan yi na yan dakiku kafin yace “tayi abinda tai ne saboda daukar fansar abinda Adam yama yayarta, ya rabu da ita saboda ke, in da hali ki yafe mata yarinyar has a difficult life.”
Shiru tai tana kallansa maimakon ta bashi amsar tambayar dayai mata sai jiyai tace “Ya zakai dasu Kabir?”
Kallanta yai yace “ya zanyi?”
Tace “eh I don’t plan to forgive them, sannan in har bai nemi yafiyar abinda ya mana ba banaji hankalina zai kwanta.”
Taya zaki dau matakin?
Shiru tai tana kokarin tattaro dauriyar ta, kallansa tai cikin dakewa kamar wanda gabanta ba faduwa yake ba tace “Dady zai bude min Tv station, sai dai bazai budemin ba sai nayi aure, anda ni yanzu banida plan na auran wani duba da yanayin yanda rayuwata take, bazan iya cigaba da ganin mutum azzalumi kamarsa yana cigaba da yin abinda yaga dama ba.”
So? Ya fada yana kallanta.
Kallansa ta sakeyi tace “i need your help.”
Ni?
Tace “eh me kake gani idan ka aureni?”
Dan yawon bakinta ta hadiya tace “ka aureni muyi aiki a tare a tv station din da Dady zai bude.”
Gaba daya maganar tazo mai sama ta ka dan har yama kasa cewa komai sai kallanta kawai da yake.
Ganin yanda yake kallanta yasa tace “ nasan yanda zakaji abin, amma na duba naga hakan ne kadai mafita daga ni har kai.”
Har ni?
Tace “eh, da farko bakada aiki kabar su Umma da tunanin kanada shi, sannan bakada tabbas din samun aiki nan da shekara uku ma nan gaba, haka zaka cigaba da yi musu karyar kana aiki? Haka zaka cigaba da rayuwarka?”
Samun kansa yai da wani murmushi sannan ya juyo sosai yana kallanta yace “sai na aureki a matsayin jari na?”
Shiru tai kafin tace “jari?”
Yace “Ba hakan bane? In aureki a matsayin me? Wanda kikeso? Wanda kike bukata? Ko wanda kike neman cika burinki dashi?”
Tace “koma menene zaka iya yin tunanin dakaga yama, amma kasan bada wata manufa na fadi hakan ba.”
Yce “okay mu barshi da zuciya daya kika fada, why me?”
Shiru tai kafin tace “kai kadai na yadda dashi.”
Wani murmushi ya sakeyi yace “kinsan halinane? Ta ina zaki yadda dani?”
Kallansa tai batai magana ba sai dai ta fara karzar farcenta.
Kallan hannunta yai sannan yace “kinasan muyi auren karya kenan ko me?”
Kallansa tai cikin dakewa itama tace “in ka fassarashi da karyar kenan.”
“In ban fassara ba fa?”
Ya fada yana kallanta sannan yace “in kuma naji inada wacce nakesan aura fa?”
“Sai ka aureta”
Haka kawai ya samu kansa dajin haushin wannan amsar.
Maimaitata yai yace “sai na aureta?”
Tace “eh, ra’ayinka ne, sannan kai mijin mace hudu ne, ban nemi komai daga gareka ba, let’s work as a partners, sannan nasan kafi kowa kishin kanka bazaka yadda da kudin da wani zai baka ba halak dinka ba, bazan shiga hakkinka ba balle na takura ma ba.”
Wani wahalalen murmushi yai yace “in kuma ban yadda fa?”
Yanayin fuskarta ne ya canza ta kalleshi.
Kallanta yai yace “meyasa kikesan yanke hukunci akan rayuwar wani?”
Rayuwar wani?
Yace “eh, aji ace na yadda munyi aure, in dawo gidanki in zauna in je gun aikin da yake mallakinki, me ya rage min keman?”
Kallansa tai tace “gun aiki daukanka nai kamar yanda nake da damar daukan duk wanda naga dama.”
Yace “Uhm hm”
Tace “wai kai bazaka taba bari ai nasara akan ka ba?”
Dan lebansa na kasa ya lasa kadan yace “bakya tunanin rayuwar da kike neman jefa kanki?”
Tace “ wace rayuwa?”
Taya zaki dauki daukan fansa a maimakon farincikin rayuwarki? Baki taba tunanin yin aure dan farin cikinki ba?”
“Bansan wannan ba, ban kuma nemi abinda ba zan samu ba, na sani ba wanda zai soni a yanda nake, tun daga kan hallayena har zuwa yanda tsarina yake, duk wanda zai aureni da wata manufar zai aureni, that’s why i choose you, ko zaka cuceni kamar yanda kace zakai a kalla nine na zabi ka cucenin sannan a kalla nasan tarbiyyar daka samu bazaka kawo mace cikin gida da sunan kanwarka ba.”
Wasu zaffafan hawaye ne suka zubo mata wanda yasa zuciyarsa yin rauni, wace irin rayuwa ta daura wa kanta?
Sharewa tai tace “kaci abinci Dady da matar gidan sunyi hidima gun shiryashi.”
Shiru yai haryanzu yana kallanta.........
******
Ayusher🏌🏻♀
🍀A GIDANA🍀
.........................
*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*Wattpad :-AyusherMohd*
Wattpad link👉🏻 https://my.w.tt/FKRWfhajS1
*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻♀*
#OneLove❣
Gaisuwa Batuul Maman🥰 Wish you Allah's Khair and Noor
{49}
Idanu kawai ya zuba mata, ganin yanda yake kallanta yasa tace "menene?"
Wani murmushin takaici yai yace "haka kika dau rayuwar?"
Cikin dakewa tace "eh, ba hakan take ba?”
Kai ya jinjina sannan ya mike tsaye yace "am sorry amma bazan iya yin abinda kikeso ba."
Kallansa tai ta kafeshi da ido cikin wani yanayi na jin haushine karara cikin idanunta, idanta ya ciciko yana neman kawo kwalla.
Yana kallanta da idanunsa da sukai dan jaa yace “did i hurt your pride?”
Batace komai ba sai dai haryanzu idanunta da kallan da take mai yana bata janyesu ba, yace “nima you hurt my pride.”
Kansa ya dauke saboda rauni da zuciyarsa ta fara yi taya zata zata ce ya aureta da kanta sannan bawai a dalilin komai ba sai akan aikinta? Taya zata.....kanta ta kawar gefe tasa hannu ta tadan maida kwallarta, tace "kaci abincin, a kalla baka wulakantasu ba su."
Juyowa yai ya kalleta, kanta na gefe ya koma ya zaune tare dayin shiru.
Sun danyi shiru na yan dakiku kafin yace "me ya kaiki yin wannan hukuncin mara ma'ana? Taya zaki nemi ruguza rayuwarki saboda daukan fansa?”
Kanta na gefe itama tace "ya bazanyi ba? bayan mutanen can basuda hankali? In ba hauka na kansu ba meye na sako rayuwar aurena a cikin haukarsu? Meye damuwarsu da rayuwata? Aiki nake nayi iya yina ta ya zan yafe musu na hauka da jahilcin da suka nuna karara?”
Bata jira amsarsa ba tace "sannan duba wani hauka na san akoreka da sukai? Taya zasuce ka sanar da wani sirrin cikin gida?"
Kallanta yai yace "akanshi ne kawai?"
Juyowa tai itama tace "kasan wahalar danasha kafin gun ya koma haka?
Idanunsa na kanta yace "I thought ke kika sa kanki?"
Wani takaicine ya kamata ta dau pillow din dake gefenta, kallanta yai yace "ba dai makamin za'ai ba?"
Harararsa tai ta ajiye pillow din a kasa tare da cewa "kaci abinci naga alama in na kara minti biyar anan zuciyata ce zata buga saboda jin bakaken maganganu."
"Ni da kika yaba min bakaken maganganun fa? ince me?"
Kallansa ta sake tace "yaushe? Me nace?"
Kansa ya dauke, mikewa tai ta fita.
Da kallo ya bita cikin tausayawa rayuwarta.
Daga kofa yaji tace “Dady?”
Dady ne ya kalleta yana dariya yace “Zainab? Yana ciki?”
Cikin mamaki tace “naga lokacin tashi baiyi ba.”
Yana dariya yace “sai lokaci yayi? Ai yai dole na fito nazo mu gaisa da sirikina.”
Siriki?
Ta maimaita cikin mamaki, da sauri tace “Dady muje falanka inada magana.”
Kallanta yai yace “mayi daga baya, dan inada meeting, saboda mu gaisa na zo, yanzu zan koma.” Ai kafin ma ta sake magana ya tura kofar glass din.
Khalid ne ya mike tsaye da sauri, Dady ne ya karasa yana kallan Khalid cikin tsananin jin dadi, yace “tunda tacemin nasan bakon jikina ke bani kaine saboda ba kowa dana sani ta bangarenta inba kaiba, ganin kai din ne da gaske ya sani kara jin dadi.” Ya karaso inda Khalid yake cikin tsananin jin dadi.
Khalid ne ya tsuguna a kasa yana gaisheshi.
Dady ya zauna a kasa kusa dashi yana amsawa cikin tsananin farin cikin dani kaina na da dade banganshi a fuskarsa ba.
Khalid ya kalla yace “Zauna sosai.”
Khalid ya zauna samun kansa yai da kunyarsa, Dady ya jawo plate ya mika mai shima ya dau daya, kallan Khalid yai yace “dan zuba mana abinci”
Khalid ya shiga bubudewa yana cikin wani yanayi da bai taba fuskantar kansa ba ko a lokacin yin interview ne kuwa.
Dady kam dadi duk ya hanashi sukuni, Khalid ya kalla yace “shinkafar ta isa haka nan zubamin ganyen dayawa.”
Nan ya ajiye mai, Dady nata matsa kafarsa, Khalid ne ya kalleshi yace “ciwo take?”
Murmushi yai tare da daukan spoon, suka fara cin abinci, shikam dai Khalid ci kawai yake duk jinshi yake daban.
Ganin yanda kafar Dady din ta tashi yasa Khalid yai shiru.
Dady ya sha kunun aya mai sanyi sannan ya kalleshi yana murmushi yace “ba wani abin bane, ciwon sugar ne kasan in muka zauna sosai ko mukai tafiya dayawa sai tadan hau.
Sugar?
Khalid ya maimaita jiki a sanyaye dan yasan yanda ciwon ke da ila, kallansa yai yace “amma ba hawan jini ko?”
Dady yai murmushi, wanda yake nuna akwai.
Cup dinsa ya ajiye gaba daya jikinsa yai sanyi, Dady yana murmushi yace “ Khalid nagode sosai sosai, magana ta gaskiya tun farkon ganinka nai sha’awar dakewarka, jajircewarka da kuma nutsuwarka.
Nagode sosai da ajiyeta agidanku da kai kafin nazo, zannan nagode sosai dan ta dalilinka ne muka shirya ni da ita.
A koda yaushe ina ma Addu’ar dace wa a rayuwarka, sai kayi hakuri da ita batasan yanda zata nuna jin dadi ko fadar magana yanda ya dace ba, duk laifi nane.
Ita ta raini kanta, har takai wannan matakin shiyasa a koda yaushe bata tunanin halin da dan uwanta zai shiga nata kawai ta sani, nasan zaka gyara mata halayenta, a matsayina na mahaifinta na gaza.”
Hawayensa ya share wanda suka dan gangaro ta kwarmin idansa.
Khalid kansa na kasa baice komai ba sai dai gaba daya jikinsa yayi sanyi, zuciyarsa duk ta karaya.
Dady ne ya cigaba “daga haduwarku da Zainab zuwa yanzu ta canza halaye da dama, duk da kai bazaka gani ba amma mu munsan ta canza wanda ita kanta batasan ta canza ba, shiyasa ina jin tace na san bakon na shiga fatan Allah yasa kaine.”
Yad’anyi ajiyar zuciya yace “nagode sosai da sosai Khalid, ina ji a jikina rayuwar da zatai yanzu bayan ta aureka rayuwace mai tattare da farin ciki da jin dadi, yau tun safe in na tuna hakan sai naji farin ciki.”
Aure? Abinda ya fada a ransa kenan da sauri ya kalli Dady.
Dady ne yai murmushi yace “Nagode sosai Khalid, ina tunanin yaushe kake ganin ya dace muga juna da iyayenka?”
Iyayena? Abinda ya fada kenan? Dady yce “eh, ko yayi wuri?”
Gaba daya Khalid ya rasa me zaice, Dady ne yace “ka duba ka gani, dan matsalar muna bacci muna tashi ne bamu san sanda rayuwarmu zata kare ba, sannan kullum lokacin mu kara tafiya yakeyi, muna rayuwa ne bama duba hakan, duk sanda mukai bacci muka tashi to fa kwana daya daga cikin rayuwarmu ta ragu ne, ya kamata a koda yaushe mu dinga tuna lokacinmu tafiya yake, bansan dogon buri amma ina fatan ganin jikana kafin tawa rayuwar ta kare.”
(Allah yasa mu cika da imani Ameen)
Jikin Khalid ne yai sanyi sosai, me zaice? Ta ina zai iya cewa wani abu a wannan yanayin?
Dady ne ya kalleshi tare da mai murmushi yace “ me kake gani in ka kwana anan? Akwai BQ a ta baya, gobe sai ka koma?”
Khalid yace “ a’a bakomai zan wuce dan anjima.”
Dady yace “to ko musai flight ticket? Dan tafiyar akwai nisa.”
Khalid yai murmushi yace “bakomai zan koma a mota.”
Dady bai musa ba ya jinjina kai yace “ba laifi hakan.” Agoggo ya kalla, yace “dole zan koma office inada meeting nan da 10min, bani number dinka, sannan in ka isa ka sanar damu ka isa lafiya, sanda kuka gaya dace na haduwar sai ku fadamana.”
Amsar wayar yai ya samai sannan ya kira wayarsa ya mika mai.
Dady ya amsa cikin jin dadi ya mike yana cewa “kaci snacks din.”
Khalid ya mike shima yana mai sallama, hannunsa Dady ya kamo wanda hakan yasa Khalid kallansa, Dady cikin jin dadi yace “nagode.”
Juyawa yai ya fita Khalid ya zauna akan kujera tare da sa hannu ya rufe fuskarsa yana tunani abinda ke faruwa.
********
Zainab najin alamar fitowar Dady daga falo ta gangaro da gudu dan dama sallah kawai tai a daki ta fito tana jiransa, sai dai kafin ta sauko ya fice.
Mikewa khalid yai ya dan shiga toilet din dake falan ya kuskure bakinsa sannan ya tada sallah.
Zainab tana ganin ya tafi tai falo da sauri inda Basma take, kallanta tai tace “Hmm Dady yace miki wani abu?”
Tace “a’a wani abin ya faru ne?”
Tace “a’a”
Juyawa tai gaba daya tana san fahimtar meke faruwa ita dai batace ma Dady siriki ba bako tace, yaushe sunan bako ya koma miji? Da wani ido kuma zata sake kallansa? Salan ya kara maka mata wata bakar maganar?
Hannuta tasa tadan dafa goshinta sannan ta nufi falan.
Jin tayi sallama shiru yasa tadan turo kofar, ruku’u yake lokacin, ido ta zubamai haka kawai ta samu kanta da kallansa, a hankali ta dan lumshe idanunta sannan ta tsaya a jikin kofar.
Bayan ya idar ne ya kalli inda take, shi kansa ido ya zuba mata kawai ya samu kansa da mata addu’a samun farin ciki a rayuwarta.
Idanunta ta bude kamar wanda akace ta juyo suka hada ido, da sauri ya janye nasa idan itama ta dauke nata tare da shigowa ciki.
Daga can kujerar farko ta zauna a saman hannun kujerar kallansa tai da idanunta yan madaidaita, ta bude bakinta wanda yake dan karami cikin yanayin burin kunya tace “me Dady ya ce ma?”
Mikewa yai yana nike sallayar yace “abinda kika cemai?”
Juyowa tai tace “abinda nacemai?”
Dan kansa ya karkatar yace “badai cemin zakiyi bakice komai ba?”
Hade fuska tai tace “kaji na musa?”
Kallanta ya sakeyi yana tuno kalaman mahaifinta yace “Hakan kikeso?”
Mefa?
Ki aureni saboda aikinki?
Dakewa tai tace “eh.”
Kai ya jinjina yace “okay, let’s get married.”
Kallansa tai da sauri, wani murmushin takaici ya saki yace “amma karkiyi tunanin na amince saboda wani tunani naki na can daban, sannan na amince saboda mahaifinki ba ke ba, sannan na amince ne saboda ni karan kaina.”
Idanu gaba daya ta zuba mai, yace “aiki? Kiyi aiki har ila masha Allah, sai dai zan sanar dake abu biyu, abu na farko bazanyi aiki a tv station dinki ba in ma harta kama zanyi sai dai nabi sawon masu jarabawa nayi in naci na fara, sannan abu na biyu, gidanki bazan zauna a ciki ba in har kuma na zauna a ciki to zan tambayi nawa ne kudin hayar gidanki, in har naga zan iya shima kenan in ba haka ba sai dai ki hakura da gidan, sannan abu na karshe....”
Shiru yai yana kallanta, wacce itama kallansa take, yace “wannan sai bayan auran zan fada miki.”
Yana kaiwa nan ya dau wayarsa tare da nufota hanyar waje.
Sai daya zo daf da ita tace “Bazaka tabi bari koda wasa ai nasara akanka ba?”
Tsayawa yai ya kallo gefen da take zuciyarshi na kara takaici auren da take neman yi da shi saboda aikinta.
Kallanta yai yace “meyasa kika auri Adam?”
Shiru tai shima bai nemi amsar ta ba yace “ meyasa kika dau aure abin wasan yara?”
Yaushe nace ma haka?
Dan kansa ya juyar kadan tare da dawo dashi inda take yai yace “ inba wasan yara ba kin auri Adam saboda kina san samun mijin da zaki juya wanda bazai nemi hanaki aikinki ba wanda zai zama karkashinki bazai taba yi miki magana akan yawan aikin da kike ba, ba haka bane?”
Bata rai tai matuka bakinta ya shiga rawa, ta kafeshi da ido, yace “ni kuma yanzu kina neman yi dani saboda ba wani wanda kike gani a kusa? Ba haka bane?”
Mikewa tai a zuciye tace “haka nacema?”
Juyowa yai gaba daya yace “ba hakan bane? Ke da kanki kikace saboda aikinki, sannan kika bani damar yin aure sanda naso ba haka bane?”
Zuciyarta ce ta shiga tafasa tana sauketa, tace “ko hakan ne sai ka fadamin ta wannan muryar?”
Murmushi yai yace “oh na manta ashe ke order kika saba badawa bakya san a baki, amma ya zamuyi? Dan nima ba abinda na tsana irin a dinga bani order balle akan rayuwata.”
Cikin kufula tace “In bakayi kace bakayi sai ka fadamin kalamai marasa dadi?”
Ido ya zuba mata, yace “me kike tunani?”
Haushi ne ya kara cikata ji take kamar tai ihu saboda yanda zuciyarta ke tafasa.
Kasa cigaba tai saboda yanayin rauni da zuciyarta tai, kallanta yai shima tashi zuciyar na rauni yace “am sorry in kinji zafi, but ko zan sake maimaitawa abinda zan fada kenan, nagode da karba kirki kimin godiya, zan wuce.”
Tana tsaye har ya fita daga falan, shiru yai bayan ya rufe kofar, na mata tsauri? Abinda ya tambayi kansa kenan, yawon bakinsa ya hadiya sannan ya fita, yaso yace tawa matar babansu magana suyi sallama amma baisan ya sake shiga dan kila sai sun sake wani fadan.
Fita yai kawai ya bar gidan ya nufi tasha.
******
Zainab kam ko kafa daya ta kasa dagawa tana maimaita kalaman Khalid, cikin kufula ta fito tai sama da sauri tana shiga daki ta rufo kofar da key ta kwanta akan gado.
Tunda take a rayuwarta an taba fada mata bakaken kalamai irin na yau?
Meyasa ta cigaba da tsayawa tanajin kalamansa masu kona mata rai? Ai da sai tabar gun.
Idanunta ne suka ciciko kawai ta samu kanta da zubar da kwalla.
(Khalid gaskiya ka kama kanka🙄)
**********
Haka ya shiga mota yana tafe gaba daya zuciyarsa ba dadi, taya zata tunkareshi da aure saboda aikinta? Kenan haka sukai da Adam?
Meyasa take sa aiki a saman aurenta?
Idanunsa ya rufe zuciyarsa duk a dagule.
**********
Wanke kwanuka take a bakin rijiyar amma hankalinta nakan su Asabe dake cin dan wake, cikinta ne yai wani kara, takaici ya kamata wannan tsinaniyar Safiyan ta basu dubu goma tace zata kara musu amma gashi har yau sati daya kenan basuda ko sisi a gidan.
Kallansu Asabe tai wanda suka dauke kai gefe suma suna jin haushin ta, dan sanda sunada kudi haka zasu jiyo kamshin abinci amma ko yar mitsilar roba bata taba san musu ba dan haka itama lokacin ramawarta ne.
Cikin daki ta shiga Adam ta gani a zaune akan katifarsa, rike da waya haushi ya kamata ta kasa kusa dashi ta talle keyarsa.
Dagowa yai da sauri yace “Goggo lafiyarki? Wai ni ya na zama saurayi amma baki da aiki sai makeni?”
Wani banzan kallo tamai tace “saurayi agidan uban wa? Ka tashi ka nemo mana abinci ko sai na saka a gaba nata maka?”
Ina zan nemo?
Tace “nikam mun shiga uku bama zancen abinci ya kamata muyi ba zancen kudin haya ya kamata muyi, jibi kace ko?”
Yace “eh yazakiyi yanzu?”
“Ya zanyi? Da yake ni kadai nake zama ba dole ka fadamin zancen banza ba.”
Kallanta yai yace “to ai ni kinsan bani da hanyar damun kudi.”
Kallansa tai tace “Adam me kake gani in kace wannan Safiya ko Afaro take ta nemoma aiki?”
Kallanta yai, yace “ko?”
Tace “eh mana ba kace Driver din nan take so ba zata iya komai akansa? Ka hada yar dabara kace zaka hadasu a zance kadan cafki rabanka.”
Kai ya jinjina yace “aikam to amma wani irin aiki? Nifa kinsan bansan aikin wahala nafisan na ganni a zaune a gikin makeken office dina ina juyi akan kujera, ga sanyi AC na kadani, in na taso daga mota na wuce gun Matata Zainab na dauko nasara a mora mu dawo......”
Kansa ta sake tallewa tace “kai dai bakada hankali wlh, naga randa hankali zai shiga jikinka.”
Kwanciya yai rigingine yace “Goggo?”
Meye?
Dan Allah Zainab bata hadu ba? Duk da ba fara bace sosai amma ba baka bace can, sannan tanada dan kumarinta dai dai, ga dan tsayinta daidai, ga idanunta yar caras........”
Kamin shiru ko sai na sa muciya nai ta makama? Dan ubanka kasan da hakan kaje kai lalata da wata can kedara? Banda haske me tafi Zainab? Sannan yanzu kazo ka sani a gaba kana min tatsuniya?
Ajiyar zuciya yai, tace “maganar nan dana ma wlh ta tafi da komai na cikina, Adam taimaka ka samo mana ko bread ne mu cucusa, yasin yunwa zatamin illa.”
Kawo lace dinki.
Shiru tai tace “in zani wani gurin in sa me?”
Yace “kisa atamfa dolene sai kinsa wannan?”
Cikin takaici tace “Allah sarki Zainab sai dai kawai naga kudi ko kaya, wannan wannan ni dai ka cuceni wlh.”
Adam yace “kawo lace nidai dan nima yunwa ta gama tattare ni.”
Haka Goggo ta dauko lace din, tana ja Adam na ja haka ya fizge yai waje dashi.
Zama tai cikin takaici da jin haushin rayuwarsu.
******
Ayusher🏌🏻♀
*******
🍀A GIDANA🍀
.........................
*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*Wattpad :-AyusherMohd*
Wattpad link👉🏻 https://my.w.tt/FKRWfhajS1
*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻♀*
#OneLove❣
Gaisuwa da Godiya gareki Maman Haneef 🥰ZeeKhalid na gaisuwa🤝
Ina kike Twins din Zainab😉? Tana godiya da zazzafan kaunarki gareta, jiya har rasa bakin magana tai da ina zanzaro mata tsananin kaunar da kike mata🤪Aka Biebie
{50}
Duk yanda yaso yau bacci ya daukeshi ya kasayi sai juyi yake akan dan karamin gadansa, ganin bacci yaki daukansa kawai ya mike ya fara karatun Qur’ani, cikin falalar karatun yaji bacci ya daukeshi.
Yana sallar asuba ya wuce daga can zuwa gun aikin da zasuyi, ya riga kowa zuwa haka ya fara aikin kafin su karaso har sai karfe 1, ya wuce cafe ya dukufa neman aiki, yana gamawa ya wuce shagon dayake zama sai magrib lis ya dawo.
A tsakargida ya tadda su Umma, sunyi dan malele ana zaune ana ci da yaji da manja suna hirarsu.
Yana shiga suka kalleshi cikin kulawa, karasowa yai ya xauna a gefen tabarma yana dariya yace “Umma yau kuma dan malele ake ci?”
“Kai dama ba kwanan ka anan, ga dai shinkafarkacan da wake aci lafiya.” Umma ta fada tana kallan Abba tacigaba “ku dai maza wlh sai a hankali, ni banga me dan malele yai ba.”
Abba ne ya kalli Khalid yana dariya tare da rage sautin radio dinsa yace “ku dai tunda kunaso kuci ni kam da inci abin nan gwara a bani kwadan kanzo.”
Khalid ya dauko kwanan sa da spoon ya zauna yana kallan su Amir da ko magana basayi sai cin abinsu, Asiya ya kalla wacce ta buda yaji dayawa a nata dai shishitun yaji take yace “sannu wannan uban yaji haka?”
Ruwa tasha tace “Yaya yaji.”
Zama yai tare da ajiye ledar bread din daya siyo, ya sa spoon yai shiru tunda yakai loma daya bai sake sa wani ba da alama ya tafi wani tunanin daban.
Umma ce ta kalli Abba, shima ya kalleta sannan suka maida kallansu kan Khalid.
Umma tace “Khalid lafiya?”
Kallansu yai yas murmushi sannan ya dau spoon din ya cigaba da ci.
Sai daya gama yasha ruwa ya shiga dakinsa yai sallah sannan ya dawo, lokacin daga Umma sai Abba a wajen, su Amir anyi bacci da alama Asiya tana daki.
Zama yai sannan ya kalli Abba sannan ya kalli Umma yace “Abba akwai abinda nake san fada muku.”
Hankulansu suka maida kanshi gaba dayansu, shiru yadanyi kafin ya dago yace “Umma me kuke gani in na kawo muku sirika nan kusa?”
Kallan Abba tai tace “sirika?” Da sauri ta sake cewa “aure?”
Dan kansa ya sosa tare da dan kallan Abba.
Dariya Umma tasa cikin jin dadi tace masha Allah, burin mu ya kusa ciki, masha Allah.
Abba cikin jin dadi yace “kayi tunani kyau, a ina take?”
Dan kallansa yai yace “kun santa.”
Mun santa? Suka fada a tare, yace “Zainab.”
Yanayin fuskar Umma ce ta canza tace “Zainab?”
Yace “Umm!”
Abba ne ya kalleta sannan ya kalli Khalid yace “tashi kaje.”
Mikewa Khalid yai cikin rashin fahimtar me Umma take nufi.
Kallanta Abba yai bayan yaga tafiyar Khalid yace “meke faruwa?”
Kallansa tai tace “ina san Zainab har raina kaima ka sani amma Khalid fa bai taba aure ba?”
Ajiyar zuciya Abba yai yace “ku mata kuna da taku matsalar, sai kuso mutum kamar me amma daga ta hadoku da ‘ya’ya sai ku fara canzawa, sam akan ‘ya’yan cikin ku sai ku nemi rufe ido, dan bazawara ce sai akai me? Ko kin manta Annabi da ita ya fara?”
Shiru tai kafin tace “nayi kuskure, nagode daka ganar dani”
Murmushi yai yace “nasan yanda kike san Zainab nasan kuma san da kike ma Khalid ne yasaki tunanin haka amma tunda shi yasan haka yake san auranta sai mumai fatan alkairi.”
Kai ta daga cikin gamsuwa da jin dadi, mikewa tai ta nufi dakin Khalid din.
Yana zauna yana duba wasu takardu dayai printing na wani aiki da zai cike.
Umma ce ta sallama sai daya amsa sannan ta bude labulen, mikewa yai yace “Umma inzo ne?”
Shigowa tai ta zauna a bakin gado tace “Abuja kaje jiyan?”
Kai ya daga mata alamar eh
Kalansa tai cikin jin dadi tace “dazu na katseka akwai abinda kake san sanar damu ko?”
Kallanta yai yana daga xaune a kasa yace “Eh bayan ma dawo ne nama Dady text akan ma dawo shine ya kirani bayan mun gaisa yake cewa na tambayeku lokacin da za’aje gaisuwa, sannan wai in ba damuwa da sa rana ayi a lokaci daya saboda yanayin nisan garin.”
Cikin gamsuwa ta jinjina kai tace “zamuyi magana da Abbanka, amma ya zakayi da abin lefe? Tunda yanaso a sa rana?”
Bakomai insha Allah.
Kai ta jinjina cikin gamsuwa tace “bari naje gun Abban naka.”
Mikewa tai ta fita, shiru yai kafin ya cigaba da abinda yakeyi, yau ma aga gun sallah ya wuce.
********
Dady ne ya kalli Basma yace “Zainab fa?”
Tana daki, bansan meke faruwa ba ko saukowa bata sanyi, sai dai ko abinci tana dauka take komawa, nadai je saman tace ba abinda ke damunta.
Kallan kofa yai sannan ya dau wayarsa ya kirata, tana kwance cikin bargo ta daga, dady yace “Zainab sauko kasa.”
To kawai tace ya kashe.
Mikewa tai kamar mara lafiya ta sa mayafinta akanta, ta sauka kasa.
Dady na zaune shi kadai a falan ta shiga.
Durkusawa tai kusa da inda yake, kallanta yai yace “meye hakan? Ji fuskarki? Ko bakida lafiya ne?”
Kallan Dady tai tana kokarin yin magana dai dai takaici ya hanata.
Kallanta yai yace “ke da Khalid ne? Dan ban taba ganin Zainab ta rasa abin cewa ba.”
Shiru tai kafin ta kalleshi cikin takaici tace “Wai bazai zauna a gidana ba sai dai ya biyani haya, sannan wai aiki ma sai yayi jarabawa ko me?”
Ta fada cikin kuluwa, dan wannan kalmar ko tunota tai sai taji komai nata ya tsaya guri daya.
Kallanta Dady yai kawai bai san sanda ya fashe da dariya ba yana kallanta.
Tace “Dady?”
Dariya yake ya tsagaita yana tunanin yaushe dayai dariya irin haka, yace “ke da cemai kikai ya zauna a gidanki? Sannan yai aiki a kasanki?”
Tace “ba hakan bane ya dace?”
Kallanta yai yace “da me kikaso ya ce miki? To Hajiya naji na gode ko me?”
Shiru tai kafin tace “nasan bazai ce haka ba amma amsarsa ce ban taba zata ba.”
Kallanta yai yace “Jin wannan abu yasa na kara yadda da Khalid, ba shakka shi kike nema a rayuwarki.”
Dady?
Kallanta yai yace “Tashi kije ki ci abinci”
Shiru tai kafin ta mike dan ta kula so yake ta tafi, tana fita ya daga wayarsa ya kira Khalid.
Khalid nahanyar komawa gida wayarsa tai ringing dauka yai ya gaishe da Dady.
Dady ya amsa cikin jin dadi yace “ko kana hanya ne? Naji kamar karar mota?”
Khalid yace “eh amma yanzu zan sauka.”
Dady yace “daga gun aiki?”
Yace “eh.”
“Wani aiki kake yi yanzu?”
“Ina zuwa garage, ina tare shago sannan ina aikin gini.”
Yanda yai maganar da Confidence dinsa yasa Dady jin dadi yace “masha Allah ba laifi, kunyi maganar?”
Yace “eh zan kiraka yanzu in naje gida kuyi magana.”
Cikin gamsuwa yace “Math kai ko?”
Eh
Dady yace “Akwai wani abokina dake aiki a bank, bansan ko da yanda za’ai ba nasan yanada mutane dayawa a banks na nan kano, zan tambayeshi in har ba damuwa daga gunka.”
Shiru Khalid yai dan baisan me zaice ba, Dady yai dariya yace “karka damu ka cancanta ne bawai dan na sanka ba, dan yanada tsauri bazai bari abaka aikiba ba tare da kanada jarabawa mai kyau ba, sannan kasan harkar kasar tamu duk yanda kai in har ba hanya a banza zai tashi, ba tabbatar wahalar dakasha gun karatu bazaka so ta tafi a banza ba.”
Bai jira yace wani abu ba yace “sannan sirri ne tsakanin mu dakai.”
Khalid yace “nagode Dady.”
Murmushi Dady yai yace “sannan na fahimceka taya zakai aiki a kasan matarka? Bayan ita tayi zurfi a aikin? Sannan kai ba abinda ka karanta ba kenan, ta fika sanin komai a fanni, duk wanda yazo kallan wanda ke kasan matarsa zai maka.”
Khalid yai murmushi yace “nagode da fahimta.”
Dady ne yace “maganar lefe dan Allah karkayi”
Khalid yace “dady ayi hakuri abarni nayi, ni nake san yi.”
Shiru dady yai yana kara san yaran a ransa, yace “shikenan tunda kai kake san hakan, in yaso in ta tare sai ka bata, angode sosai.”
Khalid yace “nine da godiya nagode sosai.”
“Ka turo min takardun ka ta email zan turo ma yanzu, inkaje gidan mayi waya da mahaifin naka.”
Khalid yace to angode cikin girmamawa.
Dady yace “sai na jika, in ba damuwa ka kirata.”
Nan sukai sallama, kallan wayar yai maimakon ya kirata kawai sai yai text yace “na dade da isowa lafiya.”
Tana zaune tana cin abinci tai karo da sakon, cikin takaici tace “banaji na tambaya.”
“Au tunda baki tambaya ba na goge maganar.”
Takaici ne ya kara makureta ta kira wayarsa, yana kokarin sauka daga mota ya daga.
Yana dagawa tace “na cikin wayata fa?”
“Sai ki danna delete”
“Cikin takaici tace “banda hannu.”
“Wanda kika kira dashi fa?”
Haushi ne ya tiketa ta kashe wayar, cila ta tai kan gado ta cije lebanta cikin takaici.
Zuciyarta ce tace “kinsan halinsa ai meyasa zuciyarki ta zabe shi?”
Shiru tai tana tunani kafin tace “saboda ni dashi akama laifi? Saboda shikadai nasan bazai cuceni ba? Ya akai nasan hakan?”
Ganin ta rasa amsa kawai ta jigina kanta da gado cikin takaici abubuwan da take kunsa na Khalid.
******
Tundaga wannan rana basu sake ko waya ba itakam fa dukufa sosai gun shirya abubuwan aikin da zata fara, shi kuma yana ta famar neman kudi, har Kawo Idris da yan uwan Abba suka zo garin Abuja, Abba kam ba halin zuwa, duk da yaso zuwa sai dai Dady ne ya hanashi saboda kafarsa.
Su Kawo Idris kam an koma da gulma a baki ganin zabgegen gida da irin uban hidimar da aka shirya musu, Matansu kam sunsha xance kai kace mata ne.
Wani kanin kawo ma cewa yai auren Jari su Khalid kesan yi.
Ansa rana wata biyu saboda Dady yace jan abin bashi da wani amfani tunda dai sun aminta da juna to ai abinda za’ai.
Khalid kam yai kokari dan Dady har fada sai dayamai na bada kudin gaisuwa dubu dari dayai.
Wanda a zahiri yasha wahala matuka kafin ya hada wannan kudi, tun asuba in ya fita aiki sai dare yake dawowa, sannan da weekend ma daina zama yai aiki yake fita, wani sa’in har sai goma yake dawowa gida.
Zainab kam takaici ya gama isarta na ko sako balle waya ba abinda yake shiga tsakaninsu ga gidansu sai wani shirin biki ake tun balle Dady, sai dai in ta tuna aikinta sai taji komai ya mata daidai dan dama saboda shi take san aure, tunda ta samu ba abinda take nema.
Dady ya sanarwa Abokinsa anyi dace dan takardunsa ya birge Mutumin, cikin jin dadi ya kira abokinsa a Zenith bank ya sanar mai, sannan ya fadawa Dady sai dai ya faro daga kasa dan baisan harkar zallunci.
Dady ya nuna shima hakan yake so.
**********
Kayansu yake cillowa waje, Goggo sai hakuri take bashi, Malam Salau kam ya rufe ido yace “wlh yau sai kum bar gidan nan ko za’a mutu ko kanin ubana bazan barshi har yai wata kusa biyu bai bani ficika ba.”
Goggo tace “kayi hakuri munyi magana da wata tace “zata samomai aiki.”
Wannan damuwarku ce ba tawa ba ni tawa daya ce ku hada kwamutsenku ku barmin gida, banda tsiya ma me kuke dashi daga katifa sai tv, na rasa uban me ake da tv gida ba komai, koma tv din yanzu zan tafi da ita ma rage zafin kudina.”
Adam ne yace “Malam ka shiga hankalinka da ci mana zarafi bafa matsiyata ka samu ba.”
“Yo ai ku da matsiyatan fakirai bakuda maraba.”
Yaja kofar dakin ya garkame da kwado ya fida daga gidan.
Kallan juna sukai tace “Adam ya zamuyi? Haryanzu bata kiraka ba?”
Bata nan ne sunyi tafiya da mahaifinta suna Ko Paris?
“Faras? Ni meya damen da wani Faras? Tazo ta taimakemu mudai dan Allah.
Nikam yau munshiga uku ina zamu nufa.”
Adam yai ajiyar zuciya na takaici.
*******
Dady ne ya kalli Zainab ya mika mata kudin, kallansa tai tace “ duk na meye?”
Gashi nan dai ya kawo, nima sai dana mai fada yayi yawa.
Kallan kudin tai, jikinta ne duk yai sanyi ta amsa.
Dady yace “kinga ana gobe biki su Nabila da Nusaiba zasu dawo.”
Kai kawai ta daga ta mike ta dawo daki.
A hankali ta bude ledar da aka nade kudin dashi, kallan yan dubu daidai din tai mai dasu tai ta rufe ta bude drawer ta ajiye sannan tai shiru, kafin ta jawo laptop dinta ya cigaba da shirye shiryen aikinta da take tayi a kwanakin nan..........
Eheeeeeem🤸🏻♂🤸🏻♂🤸🏻♂
An fa.................
*******
Ayusher🏌🏻♀
🍀A GIDANA🍀
.........................
*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*Wattpad :-AyusherMohd*
Wattpad link👉🏻 https://my.w.tt/FKRWfhajS1
*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻♀*
#OneLove❣
........Ahhh na fara lissafoku naga ina neman shanye rabin shafin😆😆
Thanks for the Love🤝
*THE QUEEN BEE (My 🥰🥰🥰)
*ZAUREN BIEBIE (Your Second page💋)*
*HUGUMA CONSERVATION ROOM*
*MASARAUTAR BILLYNABDUL*
*KUNDIN HASKE*
Much Love🤝 Khaleed da Zee na gaisuwa🤸🏻♂Goggo kam ta dau list din masu ce ma danta mau kwakwalar 🐟
{51}
Yana zaune a kasa a dakinsa daga shi sai wango dogo, hannunsa rike da rub na aboniki yana shafawa saboda uban aiki dayai kwanakin nan, kullum da ciwon jiki yake kwana.
Sallama yaji a bakin kofa hakan yasa ya amsa tare da sa farar vest din dake gefe yana cewa "Salmanu shigo."
Shigowa Salmanu yai ya kalli hannunsa yana dariya yace "in jikinka baiyi ciwo ba na waye zaiyi?" Yai maganar yana amsar man zafin aboniki da ke hannunsa.
Khaleed ya kalleshi yace "goben zamu shiga kanon?"
"Eh, kama mutumin magana?"
"Eh tun jiya.”
"amma kanada key din ne?"
"Ta waje zai duba ai."
Salmanu ne ya kalleshi yana dariya yace "tab to daki nawa ne a gidan?"
"Ina na sani kona taba shiga ne?"
Shiru Salmanu yai ya kafe Khalid da ido, Khalid yace "menene kuma?"
Salmanu cikin zargi yace "anya soyayya kuke da ita?"
Cikin waskewa da neman kare kai yace "ji wani zancen banza, kuma nake shirin aurenta?"
Salmanu yace "to abin ne da mamaki, ni ko waya ban taba gani kunayi ba, sannan gashi ka kasa tambayarta daki nawa ne a gidanta?"
Shiru Khalid yai kafin ya kalleshi yace "Nifa so nake gobe mu duba wasu gidajen ba wai waccen ba, dan bazan iya biya ba nama sani sannan ba san zama nake a ciki ba."
Salmanu yace "kai dai ka fiya tsauri wlh meye a ciki dan ka yi a gidan matarka?"
Khalid yai shiru bai ce komai ba, Salmanu ya sake cewa "daga kunyi aure kai da ita ai kun zama daya."
A hankali yace "hmm aikinta ta zama daya dashi dai."
Salmanu yace "mekace?”
Khalid ya dauke kai, su Umma sunyi maganar kudin sunyi yawa ko?"
"A'a dan tasan saboda ba halin yin lefe a yanzu ne yasa na dage sai dana hadasu, so nake yanzu na fara tara kudin gida, inyaso in anyi auren na hada lefen."
Salmanu yai ajiyar zuciya yace "Aiki na gabanka, da alama kafin ka gama komai wannan bayan naka sai ya kusa b'allewa."
Haka suka cigaba da tattauna har ya tafi bayan dare yadanyi.....
Da rana suka shiga cikin kano, mutumin da Dady ya hadasu suka fara nufa gidan Zainab, tundaga wajen gidan yace "gaskiya wannan sai yakai kusan dubu dari biyu duk shekara, nan Khalid yace "akwai wasu mu duba?"
Nan suka shiga motarsa, tafiya kadan sukai suka dan ko minti biyar basuyi ba ya tsaya a wani gida, kallan Khalid yai yace "bansan ko wannan zai ma ba."
Saukowa sukai dukansu suka shiga gidan, saban gida ne dan kana ganinshi zakasan ba wanda ya taba zama a cikinsa, dan karami ne madaidaici.
Kana shiga gate din farfajijiyar gidan ce inda za'a iya ajiye mota biyu amma a matse, mota daya a wadace, sai cikin flat din gidan, babban falo ne a gun marasa hali, sai toilet a cikin falan.
Akwai kofofin guda biyu daga jikin falan, daya daki ne madaidaici dauke da toilet dinsa, inka fito kuma dayar kofar dan corridor ne, daga cikin corridor din kofar store da kitchen ne a hade, in ka fito kuma a kwai wata kofa ta daya dakin.
Khalid kam gidan ya dauki hankalinsa dan karami ne mai kyau da tsari matuka, kallan mutumin yai yace "shi kuma nawa?”
Kallansa yai yace “kaganshi dai sabone, shi dubu dari ne duk shekara.”
Shiru Khalid yai, Salmanu yace “ka dan tambayi me gidan ya dan rage mana”
Waya ya dauka ya dan kira kafin ya kallesu, yace “dubu casa’in da biyar yace in ba haka ba ku barshi.”
Shiru Khalid yai yana lissafi akansa, ya nuna musu wasu gidajen a karshe dai wannan din Khalid ya amince da wannan saban.
A hanya Salmanu yace “ka kaita gida gunsu Umma mana kafin ka tsaya da kafarka.”
Khalid yai shiru aransa yace ta ina zan kaita a yanzu da aikinta kadai ta sani? Ya tabbatar duk yanda su Umma ke santa in sukaga bata damu dashi ba sai aikinta a hankali zuciyarsu zata fara canzawa dan wannan hali ne na dan Adam.
Ya dau hotunan gidan ya tura mata ta waya, yana gani sun tafi ya kashe wayarsa gaba daya ya wuce gun aiki.
*******
A zabure ta mike zaune tna kara zooming din hoton, nan ta shiga danna mai waya amma wayar a
kashe, da sauri ta sauko kasa ta nufi bangaren Dady, yana zaune dan yau asabar yana waya da alama da dan uwansa yake yana sanar dasu biki da kuma rashin taro da Zainab keso.
Yana gamawa ya kalleta yace “Zainab? Lafiya.”
Kallansa tai kamar zatai magana sai samun kanta tai da cewa “bakomai dama maganar rashin taron nazo tunama.”
Nan ta juya daki, zama tai a bakin gado tana kara kallan hotunan, nikam ko na janye ne? Bafa a dole, akan me zan zauna yana juyani yanda yaso? In nan yake san zama sai ya kirani ya fadamin, amma baya turon sako ya kashe wayarsa ba.
Zuciyarta ce tace “wayar da ba amiki bace ta baki haushi ko gidan?”
Cikin takaici ta kifa wayar tare da dafa kai.
******
Wasa wasa abu yazo, gidan Ango ne ake ta hidimar karbar baki, shikam Ango yana can hidimar kwadago.
Yau saura kwana biyu daurin aure suna ta shirin zuwa garin Abuja, dan saboda nisa Dady yace suzo a mota daya ya isa, tunda a massalaci za’a daura auren, anayi da rana yazo ya dau matarsa a motarta su tafi.
Yau Khalid ya samu kira daga bank na Zenith dake kan titin Naibawa, cikin addu’oi yaje interview, bayan sun gama sukace yaje zasu kirashi, haka ya taho cikin tsananin farin ciki da fatan dacewa, yau kuma ha sanar da Abba halin da ake ciki, Abba kam ya tausayamai ganin yanda ya dinga kula dasu sun buda baki sun dauka yana aiki, wanda hakan ne yasa ko maganar kudi sunyi yawa basu mai ba dan sun dauka na aikinsa ne.
Sai dai jin yaje interview yasa ya shiga addu’a yace zai sanar da Umma in dare yayi saboda yawan mutane da suka hallara.
Bangaren Amarya kam har fada sukai da Basma dan kunya tasa tana ta neman jan Zainab a jiki, sai hade hade take kawo mata wanda gaba daya yasa Zainab kuluwa, tun tana amsa ba musu har abin ya fara bata haushi.
Su Nabile da Nusaiba kam murna kamar zai kashesu, dan ma haushinsu ba taro, sunso an sha dinner su cashe, yau tunda suka dawo suka sa Zainab a gaba da tambaya.
Aunty ina kuka hadu?
Aunty a ina yake aiki?
Aunty yaushe kuka fara soyayya?
Zainab kam ko kala batace musu ba, kallan Nabila tai tace “Yaran nan Allah baku da kunya wato yaushe muka fara soyayya?”
Nusaiba tace “Ni wlh ba aurenki yanzu ba takaicina baza’a barmu muje gidanki ba wannan zuwan ni kuma Allah Uncle nake san gani.”
Gaban Zainab ne ya fadi, dan sam ta manta da wannan shiriritar ta Nusaiba, kallanta tai da sauri tace “Da gaske kike wai sanshi kike?”
Nusaiba ta kalleta tare da rufe fuska, Nabila tasa dariya tace “Hauka maganinta Allah”
A zuciye ta dadama Nabila dundu, sannan ta ruga a guje.
Zata bita Zainab ta kamo hannunta, kallanta tai tace “Dagaske take wai?”
Nabila tace “kinga haukar da take a school? Duk littafanta sunanshi ne a jiki.”
Idanu Zainab ta fito dashi, Nabila tace “menene? Kinsan dai shirmene da yarinta, sanda taji sunansu daya da wanda zaki aura bakiga murna ba.0
Zainab ta girgiza kai a hankali tace “bashi ke damuna ba....Nabila....Khalid din da take so ne..”
Tai shiru tana kallan Nabila wacce tace “mene?”
Shiru Zainab tai cikin wani yanayi.
Nabila tace “Khalid da take so?”
Kai ta daga mata shiru Nabila tai kafin tace “yarintace ita ke damunta ai baiko san tanayi ba.”
“Ita nake ji? Tunani za’ai da sanina nai hakan.”
Dariya tai tace “Mamanta?”
Shiru Zainab tai, Nabila tace “shareta jibi in zaizo daukanki zan janyeta daga gidan, in tazo hutu ne dai bansan yanda za’a kare ba.”
“Gwara ki barta ta ganshi yafi sauki akan taje gidan ta ganshi.”
*******
Da yake Dady kudi ya turama Aunth daga kano taje ta mata jere hakan yasa komai yazo da sauki, sai dai Aunty kam ko ita tayi gulmar karamin gidan ganin yanda take da gida da kuma yanda suke da kudi.
Sai dai Dady ne data kira tanawa maganar yace “ba ruwanshi itama kuma ba ruwanta da shiga abin su.”
******
Yau tun duku duku suka shirya tsaf suka dau hanyar Abuja, a gida kuwa ta hada kayanta tsaf, tana murnar barin xaman daki ta koma tai aiki balle yanzu da takejin wani nishadi da ba a kasan wasu zata kasance ba.
Sun iso garin Abuja wajen karfe 11 na safe, sauka ta girma da daraja suka samu a bangaren su Dady, dan ya gayyaci yan uwansa dake nan gari da abokansa.
Haka sukai karin kumallo anan, bayan sun gama cin abinci ne aka kawo motoci sua tafi masallaci da za’a daura auren.
Tana zaune a daki, tana jiyo yan uwan Basma dana Dady suna ta hayaniya a kasa, duk da ance ba taro amma na kusa sun samu sun hallara, itakam tundaga gaisuwa ta dawo dakinta.
Tana zaune cikin material mai yanayin lace, fuskarta dauke da wani hadi na kwai da wata matar kanin Dady tazo ta lafta mata, haushi duk ya bi ya isheta ta mike tana kokarin shiga toilet ta wanke taji an turo kofa bako sallama.
Ta juyo da san yin fada taga Nusaiba da gudu tana hakki, kallanta tai tace “lafiya?”
Nusaiba tana dariya tace “an daura, yanzu Dady ya kira.”
Haushi ne ya kamata ta kalli wayarta, dauka to ta bude bako missed call bare text.
Kallan Nusaiba tai kawai ta wuce toilet ta hau wanke fuska cikin zafin rai take gurza fuskarta, sai dataji zafi ya fara kamata sannan ta cire kaya ta sake wanka.
Tana kokarin sa Atamfa kawai sai ga matar data yabba mata hadin nan, kallanta tai tace “Maman Kulthum kimin hakuri yanzu nai wanka.”
Dariya tai tace “ba na dazu bane, wannan turaruka na kawo miki.”
Amsa tai da sauri dan itakam tana san harkar kamshi, lumshe ido tai tace “kai kamshin dadi.”
Mika mata dayan tai tace “ki shafa na jiki ne.”
Nagode, ta fada tana kara shinshinawa, juyawa tai ta fita tana dan tabe baki (Allah ya shirya mutanen mu a fuska faran faran a zuciya sai hassada da kyashi🤦🏻♀)
***********
Tawagar daurin aure sun dawo suka zauna a falan Dady suna hira, Basma ce ta kalli Nabila tace “Nabila ke da Nusaiba kuzo ku kai snacks din nan.”
Nabila ce ta kalli Nusaiba tace “bashi kawai zan kai.”
Tab ai ni ba kaiwar bane damuwata burina naga ango.
Nabila kamar zata sake magana sai ta fasa, shiru tai suka dau tire din sukai cike.
Sanye suke da kaya irin daya abin sha’awa.
Haka suka shiga suka ajiye, Khalid dake zaune kusa da Dady daga dan gefe ga Salmanu a kusa dashi ta kalla dan yanayin shigarsa kadai zai sa kasan shine Angon.
Sakar tire din kasa tai, da sauri Dady yace “Nusaiba lafiya?”
Jikinta ne ya shiga rawa tana kallan Khalid wanda ya sakar mata murmushi, ya maida kansa kan Nabila yana ganin tsantsar kamarsu da Zainab.
Nabila ta ja hannunta suka fita, suna fita falo ta fizge hannunta ta hau sama da gudu.
Dakin Zainab ta shiga wacce ta gama sa kaya tai sallah tana zaune rike da waya ranta a matukar bace, ai ko mage ka aura ka sanar da ita an daura? Abinda ta fada a ranta kenan cikin takaici.
Nusaiba ta gani ta banko kofa, ta kalleta tace “naga randa za’a dinga sallama in xa’a shigo.”
Nusaiba ta tsaya a kanta tace “Aunty mutumin daya sa babbar riga fara da hula baka shine mijinki?”
“Ina na ganshi dazan san meya....”
Shiru tai data tuna, Nusaiba tace “Khalid din da kika aura Uncle dina ne?”
Zainab tasa hannu ta jawota ta zaunar da ita kusa da ita, Nusaiba hawaye ne ya zubo mata.
Zainab tace “da gaske kike san Khalid?”
Kallanta tai tace “da gaske nake Aunty.”
Zainab tai murmushi tace “shekararki nawa shima Shekararsa nawa? Sannan ra’ayinki ne ke kadai Nusaiba, Allah yayi mijin yayarki ne, bazaki hakura dashi ba?Aunty tayi laifi bata sanar dake tun farko ba, Zaki yafemin?”
Hawaye ne ya shiga zubo mata tace “amma kinsan ina sanshi ai.”
Murmushi tai tace “na sani amma ina zan bari ki hada harkar rayuwarki da mai hali irin nashi?”
Kallanta tai tacigaba “kiyi hakuri har Ki girma Allah ya fito miki da mijinki kinji?”
Baki ya bude kawai ta fashe da kuka.
Nabila dake tsaye a jikin kofa ta kallesu, kai ta girgiza tace “Nusaiba kina fama da hau......”
Harararta Zainab tai, Nusaiba kam kuka kawai takeyi, haka ta bar gun Zainab ta wuce dakin Basma ta kwanta tana ta kuka.
Su kawu Idris wajen karfe d’aya suka taho, Khalid sai da aka watse ya sanar da Dady yanda sukai a gun interview, Dady cikin jin dadi yace “masha Allah, insha Allah za’a dace, nima nan da wata daya nake san zuwa ka rakani na gaida mahaifinka, sannan ina san zuwa muje a duba inda ya dace a bude broadcasting station din.”
Khalid yace “Allah ya kaimu, ya jikin?”
Dady yai murmushi yace “jiki yayi sauki Alhamdulila, ina godiya da gudunmawar samun sauki.”
Khalid yai kasa dakai yana murmushi, yushe zaku wuce?
Tambayar da Dady yamai ne yasa yace “sanda ta gama shiryawa.”
Dady yace “ka kirata kaji sanda ta gama, kar itama ya zama jiranku take.”
Mikewa yai ba musu ya dan fita waje.
“yaushe zaki gama?”
Ha ha ha.... abinda tai kenan tana gama karantawa.
“Ba lokaci.” Ta maidamai murtani ta ajiye wayar tare da zubawa wayar ido cikin takaici.
Ganin ba reply yasa tace “kaji inda dadi.”
Khalid kam dawowa yai ciki ya kalli Dady yai dan kasa dakai yace “minti 30.”
Dady ya kalli Agoggo yace “gwara ku tafi da wuri kam, dan da naso ku tafi a jirgi to amma motar dole sai am kaita daga baya, ga Mamman ya fara girma abubuwan na mai yawa.”
Khalid yace “bakomai wlh.”
Haka Dady yadan basu guri ya nufi dakinsa.
Waya ya daga ya kira Zainab yace tasameshi a daki.
Mikewa tai ta nufi dakin yana zaune akan kujera ta shiga.
Cikin jin dadi yake kallanta har ta durkusa gefensa.
Murmushi yai yace “nanda minti 30 kika ce zaku wuce ko?”
Kallansa tai dan batasan sanda akai hakan ba, jitai Dady yace “nasan saboda kinasan muyi magana kikace hakan.”
Murmushi tai batace komai ba, a ranta tace tanan ka bulo?
Dady ya kalleta yace “Zainab dan Allah ki dubi maraicin ki ki kula da auranki da mutuncin ki? Karki bari aiki da san kanki yafi komai tasiri a rayuwarki, na san Khalid zai kula dake matuka, dan haka kema ki bashi kulawar daya dace, kina gani bai taba aureba amma ya zabeki. Dan haka kiyi kokarin kyautatamai, kinsan bashi dashi amma zuciyrshi a wadace take, dan haka karki zama mai nuna mai rashinsa, kinji?”
To kawai tace dan batasan ma mezatace ba, haka ta taso tai daki tana shiga Nabila na shigowa tace “za’a saukar mata da kaya.”
Haka aka sauka da kaya sannan ta kara gyarawa ta yafa mayafi ta fito, Maman Kulthum ta gyara mata mayafi tadan rufe mata fuska.
Kallan Basma tai tace “Nusaiba fa?”
Tana daki bansan meya faru ba take ta kuka, Nabila tace kila rashin Aunty takeyi.
Dariya sukai aka fita da ita.
Khalid na jikin motar suka fito, bude musu kofa yai aka shiga da ita, Salmanu ya shiga mazaunin driver, shi kuma ya zagaya ya zauna kusa da ita aka rufe motar suka wuce.
Tunda suka dau hanya ba wanda yace ma wani kalla, Salmanu kam mamakin wannan Amarya da Ango din duk ya hanshi sukuni, text tamai ta cikin mayafinta “Zaman nan ya ishen i need my Ipad.”
Yana kallan text din ya dan matso saitin kunnenta cikin rad’a yace “batirin agoggon ya mutu, sai ki kira mu samu shago mu sai wani mu sa mai Hajiya Amarya.”
Ya daga tare da kwantar da kansa jikin kujera ya rufe ido, cikin kuluwa ta rasa abinda zata ce gashi ya matsa, waya ta dauka tace “nice agoggon?”
Kallan text din yai sannan ya maida mata “akwai wani agoggn bayan kene?”
Cikin kuluwa ta kalleshi ta mayafi, kafada ya daga mata sannan ya maida idanunsa ya kulle.
Hannayenta ta damke cikin takaici.....
Nace yanzu aka fara🤪
********
Yanzu Hindu ni kike fadawa haka?
“An fada miki din, in Kinyi zuciya ki kwashi kafarki ki bar mana gida, ni wannan abu ya isheni nan kika wulakantamu saboda ‘yancinki da sirikarki yanzu kuma kinzo kin takura mana.”
Naji kuyi hakuri ku barni na zauna
Shiru tai tana tuno kwanan waje da sukai cikin uban sauro da sanyi, uban wahalar data sha a kano har ta samu yar dari biyu ta karaso kura, gani take ko me za’a mata ai bazata tafi ba, zata jira har yar banzar yarinyar dake Farans ta dawo ta ba Adam aiki duk ta fanshe wulakancin da ake musu.
Adam kam a kano ya zauna yana zaune a soron Kamalu suna lalabawa, yace in Afreey ta dawo zai biyashi kudinshi, dan shikam jira yake ta dawo tamai dabarun da zai maida Zainab (Hauka maganinta Allah)
*********
Wata irin mika tai tare da ajiyar zuciya, sun glass din dake kan fuskarta ta zare ta na janye da akwatinta, murmushi ta saki ta kalli Abbi tare da cewa “Abbi ji nake kamar inyi ihu dan murna.”
Murmushi yai yace “meyasa kika damu da dawowa? Kida naso kiyi wata uku zuwa hudu? In aikinki ne kinsan a ajiye kike.”
Murmushi tai tace “ba aiki bane mijina zan dauka.”
Dariya yai yace “Allah yasa da gaske”
Miji😟? Jama’a ina yake?😳
******
Ayusher🏌🏻♀
*******
Tunda nake typing ban taba mai yawan wannan ba, saura kuce nayi kadan🥺su O’O☹
🍀A GIDANA🍀
.........................
*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*Wattpad :-AyusherMohd*
Wattpad link👉🏻 https://my.w.tt/FKRWfhajS1
*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻♀*
#OneLove❣
*Hauwa Saleh Allah ya kawo lafiya yasa kaffara ne🤢*
{52}
Idanunsa na rufe baisan sanda bacci yai gaba dashi ba, kwanakin nan kam yana bukatar hutu.
Zainab kam a zaune take kawai sai daddana waya take, har ta gaji tai shiru tanajin wakar Nura M.Inuwa dake tashi a cikin motar.
*****
Dady dake waya ne yace “ka tabbatar bai gane ba?”
“Ina zan bari ya gane? Sannan da alama baisan kan abubuwan ba, shiyasa bai kawo komai ba.”
Murmushi Dady yai yace “nagode sosai.”
Bakomai Alhaji mune da godiya, gashi ka sai gidan marayun nan.”
Nan sukai sallama ya kashe wayar yana murmushi, shiyasa baibi tagun Khalid ba gun hadashi da mai gidajen yabi ta hanyar Abbansa cikin dabara wanda shima ya tabbatar bai kawo komai a ransa ba, tunda basu san kudinsa ba bakuma suzo ba, duk labari kuwa yana zama shirme ne wani sa’in, yasan Khalid a yanzu bazai iya biyan gidan Zainab ba, sanan baisan ya sa jikinsa yin sanyi in har yaji asalin kudin gidanta, shiyasa yai wannan dabarar, ya rage wannan ya rage saban gida ta yanda bazaiyi tunanin komai ba.
*********
Karfe 8 na dare suka iso gidan..
Suna shiga gidan Salmanu ya ajiyesu sannan ya gangara unguwar ya nemi gun mai nama ya siyo kaza da yoghurt, dawowa yai ya dau waya ya kira Khalid.
Acan kuwa cikin daki suka shiga Zainab ta zauna a bakin gado, sannan ta sa hannu tana kokarin zare mayafinta, jin hannun Khalid tai akan hannunta.
Gabanta ne ya fadi, hannunta ya sauke mata sannan ya daga mata mayafin, sannan ya matsa kadan, a hankali ta dago idanunta ta kalleshi, gani tai kansa na kan waya da alama sako yake yi.
A hankali ta shiga yima dakin kallo, Khalid kam ya gama yima Dady da Abba text akan sun iso amma idansa na kan wayar har lokacin, ta gefe yake kallanta yana san sanin yanayin da Zainab zata dau gidan.
“Ina ne toilet?” Tambayar datai kenan, nuna mata yai da kai hakan yasa ta mike ta nufi toilet din.
Alwala tai bayan ta gama kawai ta samu kanta da tsayawa a bandakin, jin yanayin take daban, da gaske fa yanzu shi mijinta ne ko? Anya bata dauko ruwan dafa kanta ba?
Khalid ne ya amsa wayarsa dake kara, nan ya fita, tana ji an rufe kofa alamar fita ta fito daga toilet din, shiru tai tana kallan dakin sosai Aunth tayi kokarin gun shirya dakin, farin gado ne sai dai labulayen jikin dakin kalar sarararin samaniya ne,dan karamin dakin yayi kyau, dan karamin carpet din dakun ma kalar labulen ne, yayi kyau kwarai da gaske, kawai dai dakin ne karami a gun masu hali irin su Zainab kenan.
Jin knocking tai sannan ya bude, kallanta yai sannan ya ajiye ledar a drawer din gefen gadon, kallanta yai, ita ma daidai nan ta dago, suna kallan juna ta zare idanta da sauri, tana san cewa abin sallah da hijab amma sam ta kasa, meke damuna? Tambayar da ta shiga yima kanta kenan.
Khalid ne ya wuce toilet din, yana shiga ya saki wani lalausan murmushi, sannan ya dauro alwala ya fito.
Tana nan inda ya barta, ganin yafito ta daure tace “abin sallah.”
Kallan dakin yai yace “bansan inda suka ajiye ba sai dai mu duba.”
Nan ya mike yana dubawa, kallanta yai tana zaune, kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa yana bude wardrobe ya ganta a ciki.
Ajiye wa yai, akwatinta ta zuge ta ciro hijab sannan ta shimfida sallayar ta daga hannu zata tada sallah.
Jin hannunsa tai a kugunta saura kiris numfashinta ya dauke dan tafiya yai na wucin gadi, janta baya yai sannan ya dawo ya tsaya a gabanta ya fara tada harama.
Da kyar ta daidaita numfashinta tabi bayansa, sai da suka idar sukai addu’oi sannan ta mike kallanta yai yace “ga abinci can Salmanu ya kawo miko mana.”
Kallansa tai sannan ta kalli ledar, alama ya mata da ta miko da kai, fuska a hade ta nufi gun ledar ta jawota da karfi, kallanta yai yace “ajiye ki zauna.”
Tace “a ina?”
Kallan daya mata ne yasa ta ajiye ta zauna fuska a hade, bude ledar naman yai sannan ya jawo hannunta yasa a ciki, kallansa ta sakeyi cikin wani yanayin da ita kadai ta sani.
Daukan cinya tai tana mamakin ko kunya baya yi ya sakata gaba yana cin abinci.
Itakam da kyar ta ci cinya daya, kallanta yai yace “kunya kike?”
Kunyar wa?
Kallan dakin yai yace “shi nake san ji ganin ba kowa a ciki.”
Shiru tai ta dau wani ta karaci, yana kokarin mikewa aka dauke wutar nepa.
Da sauri tace “mekenan?”
Kallanta yai bai tanka ba ya kunna filitar wayarsa tare da cewa “namanta bansai fitila ba, ko na nemo kendir?”
Tace “dan tada mana generator dan inada aikin yi ma tun jiya naso yi bansamu nustuwa ba.”
Ransa ya sosu ya kalleta yace “banda Generator dan haka sai ki jira aikinki sai sanda suka dawo da wuta, in kin matso ko cikin dare sai ki yanka ki tashi kiyi.”
Hankali a tashe ta kalleshi tace “haka zamu zauna?”
Yace “sosai.”
Da sauri ta mike tace “ina key?”
“Ina zaki?”
“Inje gidana na dauko namu generator din sai na taho da solar in yaso gobe a kira mai hadawa ya sa mana.”
Kallansa tai wanda haryanzu kallanta yake, tace “ina key din?”
Hannu yasa ya zaro mata a aljihunsa, amsa tai ta nufi kofa, komawa yai ya zauna akan gado, yana kallanta sai dataje bakin kofa yace “in kika kuskura kika fita daga kofar dakin nan..” sai kuma yai shiru, juyowa tai ta kalleshi kamar zatai magana taga yanda ya zuba mata ido fuskarsa a murtuke.
Ji tai ta kasa daga kafa, haushin kanta ya kamata tace “to ka taso muje.”
“Naki.”
“To haka zamu zauna?”
Wani kallo ya mata ya dauke kai, takaici ne ya kara rufeta ta tsaya a gun batada alamar dawowa.
Sun fi minti goma a wannan yanayi, kawai ya kalli wayarsa ganin karfe 9 har da rabi, gashi yana da aiki da safe kawai ya mike, kusa da ita yazo batai auni ba taji ya sungumeta.
Shure shure ta fara tana cewa “Khalid meye hakan?”
Kan gado yasauketa, kallansa tai tace “mene...........”
Gani tai ya zagaye ta da jikinsa, numfashinta ne ya shiga fita da sauri da sauri, ta kame kam kamar mara rai, hannunsa yasa ta zagayenta ya zare pillow bai dago ba yace “pillow zan dauka.” Yai maganar cikin rad’a.
Gaba daya ta kasa maida mai martani saboda yanayin data samu kanta.
Mikewa yai tare da daukan pillow din, falo yakai sannan ya dawo yai toilet da alama wanka yai, dan taji karar ruwa.
Gani tai ya fito daure da towel a kasansa, ido ta zaro da sauri ta juya baya tare da rufe kanta.
Da sauri ta kwanta ta juya baya, jallabiya yasa sannan ya kalleta yace “asuba fa gari.”
Kallansa tai tace “ina zaka?”
“In kin gama aikin naki kyayi bacci bana iya bacci ana dane dane.”
A zuciye tace “ta ina zan......”
Gani tai ya rufe kofa, haushi ya kamata ta cilo pillow din dake kusa da ita jikin kofar, gani tai an bude kofa, kallan pillow din dake bakin kofa yai, sannan ya mata alama da wayarsa.
Kallanta yai yaga tana wani cika ita a dole an bata mata rai, wayarsa ya dauka, har ya juya daga yanda ya ke ba tare da ya juyo inda take ba ya dau pillow din ya cilla ta baya sannan ya rufe kofar.
Hakoranta ta datse tana ji kamar ta saki ihu.
Wayarta ta dako ta kuna fitila, sannan ta jawo akwatin ta zaro laptop dinta tana fatan da charge, ganin charge full yasata jin wani sanyi, nan ta bude ta sa wifi na wayarta ta fara aikinta, tana yi tana hararar kofa kar kace wanda ake hararar yasan anayi.
Jin yunwa yasa ta jawo ragowar naman nan ta ci stsha yoghurt din, kallan time tai taga sha biyu saura, hamma tai sannan ta mike ta dau wayarta ta nufi falo.
Yana kwance akan kujera ya dugunkune da alama sanyi yakeji.
Harararsa tai sannan ta haske fuskarsa da fitilar a ranta tace “A haka kamar ba shi ba.” ganin yana dan motsi da idanunsa ne yasa tai saurin janye wayar.
Kallansa ta sake, sannan ta juya ciki, harta zauna sai kuma ta kalli bargon dake nade akan gadan.
“Badan halinka ba zan sa ma.” Ta fada tare da daukanshi ta nufi falan.
Yana kwance yana bacci, dan kwanakin nan wani irin baccin gajiya yake da har wani sa’in in ya farka sai yaji yana neman kasa tashi.
Sa mai bargon tai ta juya zata tafi, jitai a hankali ance “Thanks.”
Juyowa tai tace “idanka biyu?”
“No”
“Farkawa kai?”
“Maybe”
Baki sai iya fadan magana, ta fada a hankali, ji tai yace “kin gama na shiga dakin?”
Da sauri tace “a’a”
Tai saurin shiga ciki ta maida kofar ta rufe tana cewa “kaji mun mutum.”
Kaya ta cire sannan ta kwanta, haushi ne ya isheta tace “naga sanda zasu dawo da wutar nan.” Ta karasa da jan tsaki sannan ta kwanta ta dau wani bargon ta luluba.
*********
Wani irin gundun bala yasa tare da saurin daga wayar tsabar ya rikice sai cewa yai “Hajiya Ta Khaleed.”
Murmushi tai tace “Adam ina khaleed yake?”
Dariya yasa yce “bansani ba amma in kin bada umarni a nemo cikin minti ashirin za’a nemoshi.”
Cikin takaici tace “baka sa ido ba kenan? Ka manta nace ka kula da shi da Zainab kafin ma dawo?”
Dariya yasa yace “in banda abinki tana Abuja yana danbatta ina xan iya sa musu ido? Sannan nifa nasan Zainab Allah bazata iya hada harka da Khalid ba.”
Tsaki tai tace “naka shirmen kenan.”
Yace “Allah da gaske nake.”
Tace “ta hada harka dakai Balle Khalid mai cikar zati da haiba? Kana gani yanda na kasa ganin wani namiji a idona bayan shi.”
Haushi ne ya kamashi ya kalli dan jikinsa dayake dogo ne shi jiki ba kiba, yace “ai ba fadin kirji da kyau nake nufi ba hali nake nufi.”
Tsaki tai tace “yo kai halinka har akwai na birgewa?”
Takaici ya kara kamashi yai dariya yace “a nemoshi ne?”
Tace “eh ina san sanin inda yake yanzu.”
To maganar aikin kuma fa?
Tace “yanzu ba wani aiki a kusa dai dai in kura xata maida aniyarta.”
Name??
“Yanda kasa Khalid dina yin driver kaima kazo kamin.”
Mene?
In bakaso sai ka cigaba da yawon da takardun naka muga mai zaka samu.
Yace “Safiyah!”
Tace “me? Yanzu masu first class da second class uppper ma ya suka kare a neman aiki bare kuma su”
Bata jira yace wani abu ba tace “ka nemo min inda yake zuwa dare.”
Ta kashe wayarta.
Cikin takaici da bakin ciki yabi wayar da kallo.
*********
Sai karfe 11 ta farka daga bacci, wani dadi taji gajin fanka na kadawa, mikewa tai ta fito falan, ganin ba kowa a falan yasa ta shiga kallan gidan, kitchen ta nufa, tana cewa “ina yaje shi kuma?”
Ganin a kayan gara da Aunty ta siyo aka ajiye akwai kayan tea kawai ta dau cup tana kokarin kunna gas, sai dai me? Ganin wayar gas din tai a gefe alamar ba cylinder.
Wani hucin takaici ta saki kawai ta dau dibilan ta fito.
Wanka tai sannan ta sa Atamfa riga da skirt ta zauna a jikinta dam, ta zauna a kasa tana ci dibilan din tana duba aikinta na jiya.
Karfe daya ya gama aiki kudin account dinsa ya duba gaba daya dubu takwas ne ya rage mai, shiru yai sannan ya nufi gun masu generator jin tsada yasa ya sai fitila guda uku sannan ya siyo kayan miya da nama ya ya taho gida.
Har ya shigo batama sani ba ta dukufa tana ta aiki, wannan abu ya dan sosa ransa, kallanta yai tana ta aiki, yace “Dan taso.”
Juyowa tai tace “oh ka dawo?”
“Ummm taso.”
“Ahhh aiki........”
Ganin yanda ya maida kofar ya rufe yasa ta harari kofar tace “mutum sai tsinanan isa.”
Fitowa tai ta tsaya a jikin kofar tace “ya akai?”
“Muje.”
Ina?
Gani tai yayi gaba tai ajiyar zuciya tabi bayansa, kitchen ya shiga sannan ya ajiye ledojin hannunsa yace “kinci abinci ne?”
“No dibilan naci”
“Okay yunwa nake ji ki mana abinci.”
Yanzu? Bari na gama abinda nake zuwa d’an anji........
Idanu ya kafeta dashi, tace “zanyi wannan tsari gidan na meye?”
Shiru yai baice komai ba, yasan komai sai a hankali baisan hada abubuwa dayawa.
Kallansa tai tace “dame zanyi girkin? Ba cylinder”
Ga karamin gas mai cylinder nan na siyo.
Kallansa tak tace “bansan ya ake amfani dashi ba.”
“Then sai ki sani daga yanzu.”
Kallansa tai tace “aikuwa indomie zan dafa.”
“Ayya sorry bana cin indomie ko taliya.”
Ido ta zaro tace “mene?”
Kafada ya daga mata yace “Haka.”
Cikin jin haushi tace “me kake so nayi yanzu?”
Karasowa kusa da ita yai, hannu yasa ya dau lighter, daf da ita ya nufa, zuciyarta ta shiga harbawa da sauri, daf suke da juna har suna iya juyo numfashin juna hannunta dake sauke ya bude yasa lighter din sannan a hankali yace “shinkafa da miya? Tuwo da miya?”
Yai dan murmushi yana kallan yanda ta karkato fuska cikin bacin rai tana kallan sa yace “na sani inada sauki gashi na baki zabi sai ki zaba san ranki, na yafe ba sai kin min godiya ba.”
Ya juya, wani irin azababan takaici ne ya kamata, tana kallo ya bar kitchen din.
Lighter din hannunta ta kalla cikin takaici ta cilar da ita kasa sannan tabi bayansa.
Tana zuwa ta ganshi a falo yana dan mikar gajiya, tace “Khalid me kake nufi dani?”
Kallo me alamar tambaya ya mata, tace “munyi aure ne akan aikina akan me zaka sani girki me wahala bayan kasan abu nake?”
Kwanciya yai akan doguwar kujerar ya sa hannu saman goshinsa ya rufe ido, haushi ya turnuketa ji take kamar ta wuce daki.
Sai dai batasan ya akai ba taga ta juya kitchen.
Haka ta shiga aiki ranta a matukar bace.
Nace daga baya kenan🤪
******
Ayusher🏌🏻♀
*****
🍀A GIDANA🍀
.........................
*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*Wattpad :-AyusherMohd*
Wattpad link👉🏻 https://my.w.tt/FKRWfhajS1
*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻♀*
#OneLove❣
{53}
Takaici ne ya kara kamata data kalli dan mitsilin gas din, ita ko ganin irinshi ma bata taba yi ba, haka ta hau kokarin kunawa sannanta fara yin shinkafa da miya, tanayi tana kwafa kai kace in ta gama dukan wanda ya sata zatai.
Haka ta share kusan awa biyu a kitchen saboda haushin fitowa takeyi, ga bakin cikin gas dan mitsili guda daya, tana gamawa ta jujuye a flask sannan ta fito daga kitchen din fuskarta a murtuke tam.
Yana jin motsinta bai bude idanunsa ba yace "ina Abincin?"
A kufule tace "yana kitchen."
Jeki kawo min.
Da sauri ta kalleshi tace "mene?"
Bude idanunsa yai ya juye saitin da take tsaye yace "wuce."
Tace "tab amma Allah kafi kowa iya wulakanci, in dafa ma abincin sannan kawo maka ma sai nayi? Bakada hannu ne?"
"Ina da shi yi ne bazan ba."
"Me kace?"
Neman wucewa daki tai ganin bashida niyar tankawa, yace "bakiji me nace ba?"
Juyowa tai ta kalleshi zuciyarta na wani irin tafasa na bakin ciki, tunda take ta taba kawo wa wani abinci?
Juyawa tai ta dauko tazota dire a gaban shi, yace "plate da spoon sannan ki taho da ruwa."
"Mai aikin ka ce ni?"
Wani kallo ya watsa mata wanda yasata mikewa tana cika tana batsewa taje ta dauko ta ajiye, tana neman juyawa yasa hannu ya rikota, kallansa tai tace "meye kuma?"
Kallan abincin yai ya kalleta, tace "meye?"
Kara kallan abincin yai ya kalleta, tace "badai kokarin cewa kake na zubama ba ko?"
"Haka!"
What?
Serving spoon ya mika mata, ta kafeshi da ido tana huce tace "Hannunka aiki me yake?"
Yace "bani da ra'ayin yi ne."
Ajiye wa tai tace "sai dai karkaci abinci."
Tana kokarin tafiya ya zauna cikin hanzari ya kamo hannunta ya jawota baya ta zauna akan cinyarsa, gabanta ne ya shiga harbawa da sauri da sauri, hannu yasa ya rikota ta gefen cikinta, tana kokarin kwace jikinta dankwalinta ya cire, saitin kunnenta yasa kansa yace "In sake magana?"
Dan juyowa tai gabanta na wani irin harbawa, yanda ta kalli idanunsa ne yasa ta kasa magana, a hankali tace "Amma abincin ma sai na sama?"
Yace "eh, haka nake so kuma dole kiyi."
Dole?
Ya daga kai alamar eh, kokarin kwace kanta ta shigayi, hannu yasa ya juyata tana kallan gefe sannan ya kalli fuskarta yace "in sake magana?"
Harara ta sakar mai cikin takaici idanunta suka ciciko tace "zan sama sakeni."
Saketa yai ta mike kamar zatai kuka haka ta zuba abincin nan, idanu ya zuba mata wani abu na taso mai, ji yake kamar ya kamota ya rungumeta ya lalasheta.
Tana gama zubawa ta kara harararsa tace "Banaji ko sarki yafika mulki."
Ta fada tare da juyawa, ta wuce daki ta banko kofa da karfi."
Murmushi ya saki sannan ya dau abinci yaci, sosai abincin yamai dadi, ga shi dama yunwa yakeji ya cinye wanda ta samai, ya sha ruwa, mikewa yai harzai kirata ta kwashe sai yaga bari yadan bata haka har zai kwashe kwanukan kawai ya barsu a gun.
Fitowa yai ya kalli kofar dakin kawai ya wuce ya fita.
Itakam da tunda ta dawo kwanciya tai a daki cikin takaici, tana jin ya fita ta sake yin kwafa ta mike ta fito.
Kallan kayan abincin tai a falo, mamaki ne ya kamata ta tsaya tana kallan kwanukan kafin tace "Amma mutumin nan ya rainamin wayau wlh."
Haka ta kwasa takai kitchen sannan ta zuba nata, tana kokarin shiga daki kawai taga an dauke wuta.
Wani kululun takaici ne ya kamata, inaaa bazata iya wannan zaman ba, kwana d'aya amma gaba daya tanajinsa kamar wata d'aya.
Waya ta dauka ta kalli number Dady ji take kamar ta kira, amma me? Me zatace? Itafa ta kawo Khalid da kanta, haushi ne ya isheta, ta kalli number Umma, me zatace mata? D'anta yaki bin umarninta? Haushi ne ya kamata kawai ta cila wayar kan gado ta zauna, tana cin abinci tana mita, ya fita bako irin na fita din nan.
Haka ta gamaci tai sallar la'asar ta dan jawo laptop dinta tana duduba plans din da take ta had'awa, awa d'aya da rabi laptop din ta mutu.
Ranta a matukar bace ta rufeta sannan ta zauna a kan gado, ganin ba wani abin birgewa bare nayi yasa ta fito falo ta zauna tai tagumi, nan ma taji zaman ba dadi ta mike ta bude kofar dake cikin falan, toilet ne? Ta fada tare da jawo kofar, kitchen tai tana kara kallan kitchen din, tana ditowa taga wata kofa a ta gefen kitchen, hannu tasa zata bude taji ta a kulle.
Dan kafa tasa tadan buge kofar, zafin dataji ne yasa tad'anyi kara, sannan ta rike kafar ta dawo falo, waya ta dauka ta rasa abinyi kawai ta hau nemo game, abin ma dariya ya bata dan bata taba tsintar kanta cikin irin wannan yanayin ba.
Hart fara game din taji bazata iya ba ta kira Khalid.
Yana gun garage, ya gama aikin wata mota kenan wayarsa tai kara, ya dade yana kallan sunan dake kiransa kafin ya daga.
Baice komai ba itama haushin baice komai ba yasa taki magana.
Sunkai minti daya a haka kafin yace "bye."
A kufule tace "bye?"
Yace "in ke bakida aikinyi ni ina da shi."
"In ni banda aikinyi? Waye ya maidani mara aikin yi in ba kaiba?"
"In mita kika kira zakiyi am sorry am not in the mood"
You are what?
Haka kawai jikinta yabata kashewa zaiyi da sauri tace "sun dauke wuta."
Baisan sanda yai murmushi ba wanda har ita ta jiyo sautin, tace "dariya kamin?"
Maybe?
A hasale tace "ina key dina? Na duba ban gani ba, yana nan a daki sai dai karki manta nike auranki kuma nace kar matata ta kuskura ta fita, kinfi kowa sanin abinda zan aikata." Bai jira tace komai ba ya kashe.
"Me za........."
Jin alamar an kashe wayar yasa tabi wayar da kallo, nashiga uku ni Zainab, me na auro wa kaina a kwana daya ana neman kasheni da raina?
Ajiye wayar tai, kamar zatai kuka ta fita waje tana ganin tsakar gidan, zuciyarta duk ba dadi.
**********
"Sir Am really sorry amma dan Allah karkace bazaka sake renewing din contract din nan ba, ka taimaka mana."
"Kabir kasan takaicin daka bani a watanni hudu da suka wuce? Fad'amin me na samu a watan nin nan?"
Director kabir yace "kayi hakuri zamu gyara matsalar yanzu duk yawanci programs din ne sun rage yin suna ba kamar da ba amma ina da plans sosai."
"In sun dameni kenan, meye amfanin plans ba kwararun masu kula dasu? Kafi kowa sanin sabida Zainab na amince na fara aiki daku, yanzu kuwa banaji zan cigaba."
Zai sake magana ya katseshi yace "ka nemi wani mungode."
Ya kashe wayarsa.
Director kabir ya mike tsaye cikin tashin hankalu dan babban inda suke samun kudi ne in har ya janye to lalai suna cikin tashin hankali.
Dole ya tambayi Afreey ko babanta zaisa baki.
**********
A hankali ta dau takalmanta tana neman fita kofar gida.
Raziyya!
Cak ta tsaya, sannan ta juyo ta kalli Babanta tace "Baba kati zan siyo."
Dawo, ya fada yana kallanta.
Cikin shagwaba tace "Baba dan Allah ka barni na fita Allah yanzu zam dawo."
Dawo nace ko?
Komawa tai kamar zatai kuka, tai hanyar daki gun mamanta, ta turo baki gaba.
Mahaifinta ya bita da kallo yana mata fatan shiriya tare da godiya ga Allah dayasa ya dau mataki tun da ransa.
********
Tana zaune a tsakar gida ta baza uban tagumi tana kallan yanda Hanne ke ta faman tuka musu tuwon dawa, ga gefe Sadiya yarta ce ke ta wanke kayanta.
Ajiyar zuciya ta saki cikin mugun takaicin wannan rayuwa "Goggo Akuyoyi zasu cinye miki shanyar ki taliyar ki"
Da gudu ta tashi ta bisu, suna tafiya ta zauna agun kamar zatai kuka, yar taliyar mirjin da aka sanmata shine suke so su cinye mata.
Wayarta ta dako a lalitarta, ga bata da kudi ga Adam haryanzu bai ko kirata ya fada mata halin da ake ciki ba, itakam inta kara sati a kauyen nan to lalai ne za'ai asibiti da ita.
********
Gyangyadi ne ya fara daukanta tsabar ta rasa abinyi, tana zaune a falo bayan tayi sallar magrib, tun tana gyangyadi har bacci ya dauketa.
Wajen karfe 8 ya bude kofar ya shiga bakinsa dauke da sallama.
Fitilar wayarta ce a kunne a falan, a hankali ya tako zuwa inda take, kallan kyakyawar fuskarta dake bacci yai, a hankali wani sanyanyan murmushi ya bayyana a fuskarsa.
Ya zubawa fuskarta ido kawai yaga ta bude idanunta a hankali, a kanshi idanunta suka sauka.
Bata tashi daga yanda take dan kishinged'e a hannun kujerar ba tace "ka dawo?"
Sannu da zuwa ake cewa.
Dan baki ta motsa yace "ban taba tunanin kina baccin wuri haka ba."
Dan harararsa tai tace "laifin waye? Ko ni ban taba tunanin ina yi ba"
Kallansa tai tace "Kh......." sai kuma ta kasa karasa fadan sunan haka kawai taji sunan ya mata nauyi, yace "me?"
Tace "bazan iya rayuwa haka ba, Allah."
Kallanta yai yace "kinyi abincin dare?"
Da sauri ta mike zaune tace "me?"
Yace "ba dai mijinki zaki ba abincin rana a matsayin dare ba?"ya fada yana zama a kujerar da take.
Juyowa tai gaba daya tana kallansa tace "kana san cemin bayan abincin rana danama na dare ma daban zan ma?"
Hmm ba haka kikaga anayi ba?
Su da basu da abinyi kenan.
Ohhh ke me abinyi kinfi karfi kenan?ko naki auren da nasu ba d'aya bane?
Kallansa tai tace "Wai dan Allah meke damunka?"
Wani kallo ya mata tace "nama wani abin ne? I feel like kamar da saninka kake sani abu."
Yanzun ma baice komai ba, tace "kafi kowa sanin dalilin auran nan meyasa kakemin haka?"
Wani abu ya had'iya na takaici sannan ya kalleta, mikewa yai ya sa hannu ya fizgota.
Kalansa tai tace "menene kuma?"
Janta yai har daki ya zaunar da ita kan gado sannan ya zauna ya jawo hannunta ya matso da ita daf dashi, har numfashin juna suna ji, idanu ta d'ago wad'anda suka fara yin jaaa tace "me kake shirin yi?"
Idanunsa ya kalleta da su wanda suka nuna bacin rai sosai, hannu yasa a kafadar ta yai baya dasu suka kwanta a gadon zuciyarta na wani irin bugawa da karfi, yanda taga idanunsa ne tsoro ya kamata, ta kanta ya rukufo yace "in nuna miki dalilinki na aurena bashida tasiri a kaina?"
Cikin tsoro tace "daga ni."
In naki fa?
Idanunta ne suka ciciko tace "fadamin me na ma?"
Mikewa yai tare da kallanta, kawai ya juya zai fita.
Da sauri tasa hannu ta kamo rigarsa tace "na gaji bazan iya girki yanzu ba."
Juyowa yai ya kalleta yace "Nikuma nace abincin dare nake so."
Ba akwai shinkafa ba?
Bana san ci.
Ko baka so ka cusa haka ai wani sa'in abinci badan aji dadi ake ci ba, sannan ni na gaji Allah bazan iya rayuwar nan ba, ta ina zan zauna ba wuta ba aiki ni kenan a zaune a gida kamar kayan wanki?kwana dayan nan jinta nake kamar na shekara.
Baisan sanda yai wani murmushi ba yace "in kingaji me zakiyi?"
Kallansa tai kawai taji ta kasa magana, yace "yunwa nake ji."
Ya juya ya fita.
Wani kululun takaici ne ya kamata haka ta fito kamar zatai kuka ta shiga kitchen, ai yasin sai dai kaci macaroni ai bakacd baka cinsa ba, nan ta hau yi randa duk a bace.
Da gudu ya ganta ta fito daga kitchen mamaki ya kamashi, tai daki a guje ta jona charge sannan tasa dariya ita kadai tace "ku taimaken ku bar wutar nan ta kwana dan Allah."
Fitowa tai Khalid ya kalleta yanzu kam ya gane me ta ruga yi, guntse dariyarsa yai balle da yaga ta fito ta make irin ba abinda tai din nan ta wuce, tana gama abincin har zata fito tace "yanzu fa zaice in kaimai?"
Ranta a bace ta dako abincin ta ajiye mai tai daki da sauri.
Da kallo ya bita, sannan ya sake yin murmushi.
Dan bayansa ya mike tare da d'an bunugawa dan ba karamin ciwo yake mai ba, mikewa yai ya bude kofar tana xaune a kasa tana duba abu a laptop dinta gefe ga takardu nan ta baxa da alama aiki take sosai.
Har ya shiga toilet din dakin ya fito bata ko dago ba, kallanta yai yace "kinyi isha'i ne?"
Ba tare da ta dago ba tace "zan yi anjima, ai isha'i ce tana da tsawo."
Kamar zaiyi magana kawai ya juya ya fita, a falo yai sallah sannan yaci abincin.
Shiru yai yad'an kunna tv yana kallan labarai a ransa yace "banaji akwai Amarya da Ango irin mu" sannan yai wani murmushin da shi kadai yasan me yake nufi.
Har karfe tara da rabi yana nan a zaune.
Kafin ya kashe tv din.....
Har ya kwanta yaji sai juye yake ya kasa bacci, gaba d'aya bayansa ciwo yake ga kwanciyar kujerar wahala take mai.
Mikewa yai kawai ya nufi d'aki.
Tana zaune tana rubutu a takard'a, bai ko kulata ba ya hau kan gado ya ja bargo ya luluba ya rufe idanunsa.
D'an dagowa tai jin batajin motsinsa bayan kuma tasan ya shigo.
Ganinsa a kwance yasa tace "anan zaka kwana?"
Eh
Da sauri tace "nifa?"
Ina na sani?
Kallansa tai tace "sorry amma gaskiya bazai yiwu ba."
Bai bude ido ba yace "sorry amma gaskiya bazai yiwu ba."
Baki ta bude tace "waccen kofar dake rufe ta meye?"
D'akina ni na rufe shi.
D'aki?
Shine kake kwance anan?
Bansan hayaniya in zanyi bacci, sannan karki manta bansan karan dane danen keyboards.
Tace "ni kake nufi ma tafi falo kenan?"
Wannan ra'ayinki ne ba nawa ba.
Tace "dan Allah tashi, ko kuma kaban key din dakin."
Baiko kulata ba ya juya baya ya rufe idanunsa.
Wata harara ta nakamai, ji take kamar ta samu bayansa tai ta makamai duka.
Hannu tasa zata rubuta abu a laptop haka kawai ta samu kanta da kasa danna komai, bansan karar keyboards.
Haushin kanta ne ya kamata kawai ta mike ta fito falo, harta zauna kuma ta mike taje kofar dakin ta kalla sannan ta dawo.
Ganin ta ita kadai a falo, yasa taji bazata iya zama ba bawai dan tana tsoro ba dan dai batasaba da gidan ba tukun, dakin ta koma ta dau pillow ta rasa ina zata kwanta, takaicinta daya inta juya ta kalleshi taga yana bacci zuciyarsa d'aya.
Ji take kamar tasa kafa ta tureshi daga kan gadan, wata kwafa tai, har ta kwanta a kasa ta mike ta hau gadan tace "in na barma gadan ma kaci galaba akaina."
Nace na nawa kuma🤪
*********
Ayusher🏌🏻♀
*********
🍀A GIDANA🍀
.........................
*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*Wattpad :-AyusherMohd*
Wattpad link👉🏻 https://my.w.tt/FKRWfhajS1
*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻♀*
#OneLove❣
{54}
Wajen karfe biyar ya bude idanunsa jintayai, a hankali ya sa hannu ya dau wayarsa ya dan kuna fitila, tana kwance tana bacci, kallansa yai sannan ya kalleta, dukansu sun bai gefen gadan sun dawo tsakiya, ajiyar zuciya yad'anyi sannan ya mike ya shiga toilet, wanka yai sannan ya dauro alwala ya fito.
Jin motsin watsa ruwa yasa ta farka, wanka da asuba? Badai mafarki yai ba? Abinda yazo mata kenan, can kuma tace "mafarkin wa?"
Tana kwance harya fito, ganin hasken fitilar wayarsa yasa ta rufe ido tare da dan kallansa ta gefen ido.
Ganin saman jikinsa a bayyane yasa tai rufe idanunta cikin faduwar gaba, mai ya shafa sannan yasa kaya, wayarsa ya dauka yace "in kin gama leken kya tashi kiyi sallah."
Ido ta bude daga kwance tace "wai kasan na tashi?"
Bai juyoba yana sa turare yace "zan wuce gun aiki daga can."
Ido ta zaro tace "aiki daga sallar asuba?"
"Eh, kinada sako?"
Cikin mamaki tace "wani irin aiki ne wannan?"
Juyowa yai yace "zan dawo cin abincin rana da na dare, akwai komai?"
Mikrwa tai ta zauna akan gadan tace "ina tambayarka bakace komai ba."
"Dan kin tambayen sai ya zama dole na baki amsa? Ko ni dana tambayeki amsar kika ban kai tsaye?"
Ya karasa maganar yana daukan agogon sa yana sawa.
Shiru tai kafin tace "wani irin aiki kake haka?"
Kallanta yai yace "gini? Zaman shago? Kanikanci?"
Gini? Irin wannan? Ta tambaya tana nuna bangon dake jikin gadan.
Bai tanka taba ya karasa daura agogonsa.
Kallansa tai tace "akan me zakai irin wannan aikin?"
Yanzun ma bai tanka taba ya juya zai fita, da sauri ta sauko tace "meyasa kake irin wannan aikin?"
Juyowa yai ya kalleta, kallansa tai tace "kanikanci? Gini? Taya zakai irin wad'an nan aiyukan kamar wanda bakada yanda zakai?"
Kinasan sani?
Ido ta zubamai tana kallansa, alama ya mata da hannu akan ta matso, kallansa tai kawai ba tare da musu ba ta matsa taje dan so take taji me yake sashi yi.
Dan tsayawa tai kusa dashi hannu yasa ya jawota, kallansa tai ya jawota sosai jikinsu na hade da juna, yana kallanta tana kallansa, tace "Sakeni."
Yace "amsa zan baki."
Tace "sai ka rikeni sannan?"
"Naga aikinki ne kadai a ranki, komai baya zama inba shi ba shiyasa zan sanar dake yanda bazaki manta ba." Cikin magana mai kamar rad'a yai maganar.
Dan yawon bakinta ta had'iya tana kallansa.
Yace "ke meyasa kike aikinki?"
Kallansa tai tace "dan ina so."
Hmmm ya fad'a tare da dan jinjina kai yace "ni kuma dan ya dace."
"Ya dace? Kai aikin gini? Nace muyi aiki tare kaki ka tsaya......."
Kallan daya mata ne yasa tai shiru, saketa yai yace "na wuce."
Kallansa tai har ya bude kofa, tace "ka dau motata mana."
"Motarki kika ce ba tawa ba."
Ya wuce.
Da kallo ta bishi tace "wannan wani irin mutum ne? Ganin duhu ya mamaye ta yasa ta lalubo wayarta ta kunna sannan ta kunna fitilar daya siyo.
Zama tai a bakin gado tana kallan ginin gidan, irin wannan yake?
Jitai gaba daya ranta ya baci, da sauri ta jawo wayarta ya fara checkin din yanda masu gini ke aiki, wani kululun takaici ne ya rufeta ta mike ta shiga toilet, alwala tai sannan tai sallah.
Duk yanda taso bacci ya dauketa ta kasa, inta tuna gini da wani kanikanchi sai taji wani takaici ya rufeta, tsaki kuwa taja shi yafi cikin bucket, ganin ma ta kasa baccin yasa ta mike kawai ta dau wayarta ta kira dady.
Yana shiga office kenan lokacin data kira, gaisawa sukai cikin jin dadi yace "Zainabu."
Tace "Dady dan Allah kama Khalid magana."
Name kenan?
Gini fa yakeyi.
To sai akai me?kece kike yi ko shi?
Shiru tai tambayar kanta tai meye nawa a ciki? Muryar Dady ne ya katseta yace "sana'arsa ce ki daraja masa ita kamar yanda yake daraja abar shi."
Shiru tai kafin tace "Yasu Nabila?"
Yace "tana nan lfy, Nusaiba ce dai ba lafiya, tanata zazzabi tun daren da kika taho."
Shiru tai dan tasan dalilin zazzabin, Dady ne yace "badai wata matsalar ko? Dan ke nakeji."
Tace "nice uwar laifi ba? Wlh Dady dakaga abinda yake min......."
Sai kuma tai shiru, murmushi yai yace "xaman aure kike ai ba wasa ba, dan haka ayi biyayya."
Bafa Gen a gidan, ga wuta sai sunga dama, sannan....." zatai maganar gas taji ta kasa.
Idan Allah ya bashi hali zai saimuku gen din.
Shiru tai dan taga ba amfanin cigaba dan Dady baxai bata gaskiya ba taga alama.
Sun dan sake hira kafin suyi sallama, shiru tai ta fito falo toilet din falan ta kalla kenan jiya anan yai wanka ya wuce?
Kitchen ta shiga ta kalli gas din cikin jin haushi haka ta kunna shi ta hada tea ta fito, shiru tai tana kallan tea din, haka zaiyi aikin bai sha ko tea ba? Oho ai ba yaro bane shi inyaji yunwa ya nema.
********
Aiki tadan fara laptop din ta mutu, wanka tai ta sa riga da skirt na atamfa, harta kwanta zatai dan bacci ta tuna zancen abincin rana.
Tsaki tai sannan ta mike rai a bace ta shiga kitchen, sink ta kala taga ta hada wanke wanke nan ta hau yi da karfi rai a bace, tana gamawa ta kalli kiyar jiya, wata dariya ta saki cikin jin dadi ta daura tukunya, wake ta dafa da shinkafa tace kaci da miya.
Tana fitowa taga azahar tayi.
Kwan wuta ta kalla haryanzu ba wuta? Sallah tai ta zauna ta baza tagumi tana kallan falan, wayarta ta dauko tana dane dane kawai.
********
Khalid ne ya dan mike bayansa sannan yace "kudin yau lokaci na yayi."
Shugaban cikin jin dadi ya mikamai kudinshi yace "gaskiya Khalid kana birgeni da kokarin yin aikinka."
Kallansa Khalid yai yace "akwai inda ake saida gen tsoho?"
Yace "eh kaje kasuwar bata."
Okay nagode, juyawa yai ya wuce bata, yaji dadin ganin ya samu karamin gen a kudi kadan, haka ya siya ya hau adaidaita ya dawo gida.
Bai sanar da ita ya siyo ba kawai ya ajiye shi a waje ya shiga ciki.
Tanata game sanda ya shigo, kallanshi tai tace “ka......”
Wani kallo ya mata, ta hade fuska tace “Sannu da....”
Jin abin tai banbarakwai, bai tanka ta ba ya zauna a kan kujera.
Itama shiru tai sai dai ta ajiye wayar hannunta.
Sunfi minti biyar ba wanda yai ma wani magana, shi kuma ya sa aranshi harsai ta san abinda ya dace, ita kuma haushin yaki amsa mata yasa tai shiru.
Ganin sun kara kwashe wata minti biyar din yasa ta kalleshi, idanunshi baya kanta sai dai hankalinshi na kanta ya kuma san ta kalleshi.
A kufule tace “ai ka amsa min dai.”
Kallanta yai yace “in mijinki ya dawo a zaune kina abinda kike zakice sannu da?”
Ido ta zaro tace “me kake so nama? In tashi in rungumeka ince sannu da?”
“Wannan ma ba laifi bane, sai dai at least ki bada hankali akan dawowar.”
Kauda kai tai tare da hade fuska, bai ko kalleta ba shima yace “bani abinci naci zan koma.”
Kallansa ta sakeyi tace “wai kullum sai na kawoma?”
Magana kikeso na sake?
Fuska ta hade ta mike tsaye ranta a bace tai kitchen, dako abincin tai ta kawo ta ajiye mai, zata mike yace “kin manta?”
Kallansa tai tare da komawa ta dau serving spoon ta zuba kamar zatai kuka take ji, tana gamawa ta mike a kufule tai daki.
Baiko bi ta kanta ba ya fara cin abincin, yana gamawa ya d’au wayarsa ya kira Abba, sun yi hira kafin Abba yaba Umma.
Umma cikin jin dadi tace “ina Zainab? Inata san kira nace bari na d’an sarara.”
Dariya yai yace “tana nan lfy, bakizo kinga gida ba ke da Asiya.”
Zamuzo amma sai wani satin, murmushi yai sannan yace “ina yan ball?”
“Suna nan rashinka yasa sunkara kaimi gun fita.”
Dariya yad’anyi, daidai nan ta fito zata dau wayarta data bari a falo, kallansa tai yana dariya, a ranta tace “kamar gaske.”
Jitai yace “gata ma tana san ku gaisa.”
Kallansa tai tamai alama da hannunta wa?
Mika mata wayar yai, ta karaso ta amsa, ganin Ummata a jiki yasa tai saurin amsa cikin jin dadi tace “Umma!”
Daga can Umma ta saki fuska sosai tace “sirikata”
Zainab samun kanta tai da d’an jin kunya, gaida Umma tai, nan Umma ta shiga tambayanta gida.
Umma can tace “Zan zo ganin gida da sirikata amma yanzu banadan jin dadi sai wani satin.”
Da sauri tace “meya sameki Umma?”
Dariya Umma tai tace “gajiyar biki ce kawai, nake san hutawa.”
Murmushi tai tace “bakomai ki huta, muna nan muna jiranki.”
Nan suka kara hira cikin jin dadi kafin suyi sallama.
Kallanshi tai taga ya daure fuska kamar ba shi ba, wayarsa ta mikamai, amsa yai ba tare da yace mata komai ba ya mike yace “bani ruwa.”
Kallan ruwan tai dake kasanshi, tace “ka dauka mana gashi a gabanka.”
Mikon.
Baki ta saki tana kallanshi, tace da haka kace na baka kasha mana.
Kallanta yai yace “bani nasha.”
Ido ta zaro tace “wai dan Allah haka kake ko yanzu ne kake neman zama haka.”
“Bani”
Mikamai tai kallanta yai kawai taga ya bud’e baki, wai bakan kake nufi nai?
Eh.
Da sauri ta mikamai tace “nan gaba sha ma zakace nai naga alama.”
Ta juya, harzata shiga daki yace “sun kawo wuta?”
Kallansa ta juyo tai ta harareshi, ruwan yasha sannan yace “zan wuce.”
Cikin mamaki tace “daga dawowa?”
Eh na tsaya wani gurine nayi late.”
Shiru tadanyi kafin tace “ina san abu a can gidan.”
Menene?
“A kayanane.”
“In na dawo maje.”
Ya juya.
Da kallo ta bishi tace “kaine agoggon ai ba ni ba.”
Kallan kwanukan tai tace “meye banbancina da mai aiki?”
Haushi ya isheta ta wuce ciki ba tare da ta kwashe ba.
Yana fita ya samu kansa da murmushin yana tuno sanda tace kace na baka mana.
*******
Da sauri ta dau wayar ganin sunan Adam, kafin ta dauka ta katse, hakan yasa tasan flashing ne.
kiransa tai tace “ka nemo inda yake?”
Afreey banda katin da zan kirashi.
Haushi ya kamata ta kashe wayar katin 1k ta tura mai Adam murna harda tsale, nan ya kira Khalid kai tsaye.
Khalid na kokarin shiga shagon wayar Adam ta shigo, dagawa yai dan dama yana nemanshi shima.
Adam yace “Khalid? Ina ka shiga ne? Inata nemanka?”
“Yaushe kake da lokaci akwai inda ya kamata kaje.”
Khalid ya fada ki tsaye, Adam yai dariya yace “Kwaro kai matsala ta dakai kenan komai naka serious, kana ina ne yanzu? Danbatta?”
“No ina kano nayi aure kwana biyu baya.”
Aure?
Adam yai tambayar cikin tsananin tashin hankali, shikenan Afreey ba shi ba samu daga gareta, hankali a tashe yace “kai uban me ya kaika aure bayan kasan da wacce ke jiranka.”
Baiyi mamaki ba dan ya saba da shirman Adam yace “Sorry Abba.”
Adam ya gane magana ya makamai yace “Khalid Afreey kila sai ta kasheni intaji.”
“Yaushe kake da time?”
Ina zamu? Gun Amarya?
A’a ka je Naibawa ka nemi yafiyarsu.
Yanayinsa ne ya canza yace “ina ka tare? Ina san zuwa ziyara.”
Ka tabbatar?
“Menene? Bakasan nunata?”
“Akan me zanyi hakan? Indai kai ka shirya ganinta to.”
Adam yace “Ai dole na nemi ganin matar kwaro.”
Khalid yace “ka samu kaje in har kanasan kwanciyar hankalinka da cigaban rayuwarka.”
“Naji zan duba.”
“Bye inada abinyi.”
Ya fada tare da kashe wayar.
Shiru Adam yai yana tunanin yanda zasu kare in Afreey taji lalai akwai tashin hankali, in kuma bai fada mataba ba shi ba neman d’an abu daga gareta.
*****
Sai magrib ya dawo, yana dawowa ya ga ba kowa a falan, kitchen ya wuce ya ajiye ledar kayan miya da nama da kuma lemon fata daya siyod’aki ya tura, tana zaune tana rubutu a takarda, tana ganin an bude kofar ta kalleshi, ganin yanda ya hade fuska yasa ta mike tace “Sannu da zuwa.” Yanda tai maganar kamar an sa mata goruba a baki ne ya dan bashi dariya sai dai baiyi ta ba yace “yauwa”
Kinyi abincin dare?
“Na tsaya abune in mun dawo nayi.”
Kin tsaya abu?
Eh, kaga, ta matso tana nunamai, dazu wata idea tazomin, me kake tunanin idan na ajiye wacce.”
Ta fada tana nunamai yanda ta tsatsada abin, kallan takardar yai sannan ya jinjina kai yace “kinfini sanin abin indai har kikaga hakan yafi to kiyi amfani dashi.”
Muje?
Ina?
Kace inka dawo zamu.
Alokacin dana dauka zakiyi abincin dare kenan.
Kallan mamaki tamai tace “yanzun ma in mun dawo zanyi ai.”
Wannan ra’ayinki ne, in kin gama tuwon kafin 8 maje.
Ido ta zaro tace “tuwo a daren nan?”
Kallanta yai ya tsare gida, kallansa tai tace “sai kai magana ka hade rai, taya zanyi tuwo a daren nan?”
“Wannan matsalarki ce ba tawa ba.”
Ya fada yana neman wuceta ya shiga ciki, da sauri tasha gabanshi tace “muje in mun dawo musai abu a hanya.”
“Banida ra’ayin yin hakan.”
Ido ta kafeshi dashi ranta a matukar bace, kalanta yai yace “matsa.”
Kin matsawa tai ta kara tare kofar da hannunta, kallanta yai yace “kinasan in nuna miki karfi?”
Taya zakace nai tuwo a daren nan? Bayan kai kace zamu gidana in ka dawo?
Kalanta yai bai ce komai ba, tace “meyasa kake min haka? Menama?” Tai maganar idanunta na cikowa.
Kallanta yai yace “kinsan yanda mace take a gidan mijinta? Kinsan abubuwan da wata macen take a gidan mijinta?”
Su kenan? Ni kasan me yasani...........
Bakinsa yasa kan lebanta ya ciza, itakam gaba daya numfashin ta ya dauke dif?
Kallanta yai yace “kada ki kuskura ki kara fadamin wannan kalmar, in kika sake kuma bansan me zai biyo baya ba”
Yana kaiwa ya matsar da ita ya wuce, har yayi gaba yace “ki wuce kiyi abinci, na ajiye nama da kayan miya a kitchen.”
Toilet ya shiga yana shiga ya furzar da wata iska.
Zainab kam da kyar ta daidaita kanta, shekarata hudu da Adam, ya akai ban taba samun kaina cikin wannan yanayin ba? Shi da yake saurayi? Nida nasan komai?
Samun kanta tai da wucewa kitchen ta daura ruwan tuwo.
Wayyo ni Zee na tuwo🥺