Zaman su lafiya cikin girmama juna. A yanzu fatansu bai wuce ganin Sumayya ta sauka lafiya ba.Tana kwance a doguwar kujera da yammacin tana ta nazarce-nazarcenta,tsohon cikin bai hana ta yin wasu abubuwan ba,taji muryar Mamanta.Wayyo!zama dak'yar ta shi da dabara kafin ma tayi yunk'urin ta shi ita ta shigo.
"Oyoyo Mama sannu da zuwa...
Da har na cire rai da zuwan ki. Taje ta d'auko ruwa da kanta tasha"Haba Kasham ya za ayi in k'i zuwa, bayan ni nace miki zan zo,kin san yanayin taran na mune yanzu haka ma sun tafi, ni a motar haya zan koma gida.Tabita da kallan tausayi"Sannu Kasham ALLAH yasauke ki lafiya, kwanaki ina ta mafarki wai kin haifi 'yan biyu. Tad'anyi murmushi kawai suka cigaba da hira.
Wannan karan bazan bar Kaduna ba har sai kin kaini gidan Shedrak.Tagyad'a kai"to Mama"takira Salim a waya dan baya gari.
"An ya Sumayya zan barki kifita kuwa? Ba likita ta ce banda yawan zirga-zirga ba?"Na sani kuma ban manta ba,dama Yaya Miqdad zan kira a waya yazo yad'auke mu.To idan baya kusa ko yana wani uzirin na shi baza ki takura mishi ba?"karka damu ai ta mu dashi bata 6aci,zan nemi alfarma na kuma san za a min.To shikenan ALLAH yatsare,kiyi zaman ki acan,nima Insha-ALLAH zuwa bayan Isha'i zan shigo sai inzo in d'auke ki.To nagode"ALLAH yak'ara tsare hanya yadawo mana da kai lafiya.Amin Sumayya nima nagode.
Makonni biyu da tafiyar Maman ta haifi kyakkyawar 'yar ta sunyi murna sosai dan ba a samu tangard'an kome ba,ranar suna yarinya taci sunan mahaifiyar Salim d'in da tadad'e da rasuwa Ruqayya suna kiranta da Ummi.Gidan Alhaji Hafiz takoma Maman Hasan tana kula dasu yadda yakama ta,jegon ya kar6esu dan sunyi shar dasu saboda cimar abincin me amfani me gina jiki da k'ara kuzari ai shine jego "Abincin ka lafiyar ka...
Cikin wani dare tana tsaka da bacci kiran Mama yashigo tad'aga cikin fargaban abinda kunnuwan ta za suji dan ta san tabbass ba lafiya ba.Kasham Judith ta mutu tafad'a tana kuka "lallai soyayyar d'a da mahaifa sai ALLAH"kalli irin wahalar data basu amma Maman take wannan kukan?Itama mutuwar tadake ta,duk da sun san k'arshen alewa k'asa.To amma ai ba yadda za suyi dan mutuwa dole ce ko mutum ya yadda ko bai yadda ba idan ajali yazo to fa silke baya tarewa, Kukan mutuwa kuma ba ya dawo da matacce.
Babu addu'a tsakanin musulmi da kafiri dan haka sai tashiga rarrashinta da kalamai masu dad'i har tasa mu tayi shiru"nagode, ALLAH yamiki albarka bawanda yakwantar min da hankali sai ke"To za kuzo funeral service d'in ne?A ah Mama ba wanda zai zo kuyi abinku,amma Insha-ALLAH idan mukayi arba'in za muzo ai.Shikenan sai da safe takatse wayar.Tun daga nan har garin ALLAH j'arasa wayewa Sumayya bata kuma rintsawa ba,sai juye-juye take tayi da tunani barkatai daya cika k'wak'walwarta.
Suna hirar su da Hafsa a D'akin-shak'atawa sukaji sallama tare da k'wank'wasa k'ofa.Hafsa tabud'e k'ofar tana amsa sallamar. Yana tsaye tad'anyi murmushi"au kaine tabashi hanya bismillah shigo "cikin ladabi yadurk'usa har k'asa yana gaishe da Sumayya.Tagirgiza kai" tana nuna mishi kujera"ta shi ka zauna meye na durk'usan? Bai zauna a kujeran ba sai yayi zaman shi a carpet d'in yana d'an murmushi"ai nan d'in ma yayi.Mamana bata nan ne?Hafsa tayi yar dariya "Aikuwa dai Maman Hasan yau tayi nisan kiwo tana can wajan tsoho me ran k'arfe Malam Muhammad Aminu.
Alhassan d'aya daga cikin yaran da suke zama ma Salim a kasuwa ne, yaro ne me hankali da sanin ya kamata,tunda yaji sunan Maman Hassan shikenan yake ce mata Mamanshi, shi kuma Usainar shi ta rasu tun suna k'anana. Itama Maman Hassan tana yi dashi sosai indai yazo tana gida to sai ta san abinda tabashi kome k'ank'antar shi, tun yana jin nauyi baya kar6a har ya saba dan takance"Kai Alhassan anya wannan Mamana da kake kirana ba a fatar baki kawai ya tsaya ba? Uwa ta ta6a ba d'anta abu yaki kar6a? Tun daga nan yaba ta hak'uri idan tabashi sai yasa hannu biyu yakar6a yayi godiya.
Ya ajiye ledar hannun shi a gaban Sumayya"Alhaji ne yace in kawo.Wai ya kira layinki ya k'i shiga,sai bayan la'asar zai shigo.Bakome Alhassan,nima ina ta kiran shi bata shiga akwai matsalar sadarwa yau"kace ina gaisuwa sai ya zo d'in"Yamik'"Zai ji"yad'an kalli Hafsa "idan Mamana ta dawo nima amik'a min sak'on gaisuwa zan dawo ranar Juma'a musamman dan in gaishe ta.Tagyad'a kai" tam za taji"sukayi sallama.
Tana gama wanka suka tafi Zonkwa ita da Hafsa sun sauka lafiya kowa yayi murnan ganin su.Kwanan su biyar da tafiya da yammacin ranar sai kawai ganin Salim suka yi.Takalleshi cikin kulawa da mamaki"ba ranar Alhamis mukayi da kai za kazo ba?Yamayar da kanshi jikin kujerar"ranar alhamis ne amma na ka sa daurewa ne,amma yanzu ai hankali na ya d'an kwanta danazo na ganku"gobe kenan za ka koma? Yabud'e idanun shi daya fara rufewa yakalle ta da sauri"wai kina nufin tafiya zanyi in barku? Tagyad'a kai"haka nake nufi ga waya muna magana da juna.Yad'an harareta"kina wasa ne ko?Wani irin wasa kuma?Ai naga kwana goma kaba mu to yau munyi biyar ba saura biyar ba?
"Sumayya...
Yakirata...suka zubama juna idanu na wucewar wasu dak'ik'u yasauke numfashi yasa hannu yana yata6a kirjinshi dai-dai saitin zuciya "kina so na kuwa? Takalleshi baki a bud'e saboda mamakin furucin shi"haba Baban Ummi me yasa za kamin irin wannan tambayar?Yad'ora hannayan shi a saman tebur "saboda kince gobe zan tafi ma'ana ni kad'ai? Sumayya akwai ayyuka masu yawa agabana amma naturesu gefe duk da mahimman cinsu naza6i zuwa wajanki,sai dai kash...hak'ata baza ta tadda ruwa ba, dan na ga kina so ki watsamin k'asa a cikin idanu.
Tad'an 6ata fuska ni dai gaskiya... Yatari numfashin ta"haba Sumayya ta tawa ni kad'ai yad'an d'age gira"bazan iya hakurin jure rashin ki bane,magana awaya kad'ai ni dai bata gamshe ni ba shi yasama kika ganni ganin idanunki yamata wani kallo"mhm me kika ce ne?
Tasunkwui da kai"haba Sumayya yi magana mana,Salim mijiki ke kad'ai ne fa.Tad'an harareshi bayan kace ba alk'awari kad'auka ba,dan dai dole sai ka k'ara auren nan.Yagyad'a kai"gaskiya banyi wannan alk'awarin ba,kar baki yaci idanu su zo suna jin kunya.Tace"Uhhh madallah to yanzu kake so mutafi?A ah ai yamma ta yi kuma kinga Mama bata dawo daga kasuwa ba dole ai sai mun mata sallama, gobe da sassafe sai muwuce.
Sumayya takoma makaranta dan hutun da aka basu ya k'are,karatu sosai sukeyi ba kama hannun yaro saboda wannan shekarar za su gama.Sumayya ba ta da wata gagarumar matsala a bangaran karatu duk abinda bata gane ba, to tana dawowa gida Salim zai warware mata shi,bata ta6a sanin me tarin ilmi bane sai bayan auransu data shiga wani d'an d'aki dayake yin nazari da bincike wallahi tasha mamakin irin tarin littafan addinin data gani.bai ta6a nuna mata ya san wani abu ba sai da zama yahad'asu. Salim jarumine me damuwa da damuwar iyalinshi.
Suna hirarsu a D'akin-shak'atawa cikin nishad'i yajuyo kukan Ummi daga d'akin baccinsu ta tashi daga bacci kenan, yaje yad'auko ta,yabata ruwan zamzam d'in da suke bata tasha ya mik'a mata ita" ga ta ki bata abincin ta yunwa take ji.Tamarairaice Sumayya a wajan shayarwa ba ta da jarumta"kai ma ka san daga ta shinta a bacci baza tasha ba.Yagalla mata harara"ba yunwa take ji ba amma take ta k'ok'arin kai hannuna bakinta? Kar6eta mana.Tamika hannu ta kar6eta Tad'an 6ata fuska"ai ban san kana harara ba sai na ga idanun a k'asa.Yayi yar dariya"Hunn Sumayya ta ke dai bata abincin ta kawai ba na san neman magana.
Sun gama karatu lafiya kuma sakomako yayi kyau Malam Muhammad Aminu shi yasamo mata gurbin karatu a Jami'ar Madina dan babban d'anshi a can yake da zama shi da iyalinshi Salim shi yanemi wannan alfarmar kuma aka mishi amma ba da san zuciya ba, a ah adadin makin da suke nema to na Sumayya ya kai...anata mata shirin tafiya inda zataje ta yi Masters a kan dai Islamic Studies.Kamar wasa tafara rashin lafiya yau ciwo gobe sauk'i,suka tafi asibiti aka mata gwaje-gwaje har aka gano abinda yake damunta ciwon siga(diabetes) amma sun d'ora ta akan magani da wasu sharud'd'ai da dole sai ta kiyayesu in dai tana san zaman lafiya,kuma sun bata kwanakin da zata sake komawa asibiti dan su tabbatar magungunan suna aikin da ake so ? Idan basa yi sai a canja wasu.
Abokan karatunta kullum suna tafe, basa gajiya da zuwa gaisheta saboda halinta na karamci "masoya da mak'iya ba a guzurin su duk inda kaje halin ka zai ba kasu"abun hannu ta bai ta6a rufe mata idanu ba.Ranan Salim yakalleta "yaushe na baki kud'in da har za kice sun k'are Sumayya?Tad'an marairaice"Baban Ummi ni dai dan ALLAH kataimake ni kawai,akwai wacce mukama alk'awarin ba ta tallafi a k'ungiyarmu ni wallahi na manta,anjima za tazo k'ar6a ai da bazan kashe wadan can ba aciki zan bata" haba nijina duk abinda kaba wani shine na ka,wanda kaci kashi yake zama,wanda kake ajiyewa ba lallai kai d'in ne za kayi amfani dashi ba, wata kila sai dai magada su gada.Alheri dank'one da baya fad'uwa k'asa banza.
Yak'irgo adadin data fad'a yabata"ina sanki Sumayya ta tawa ni kad'ai"Tasa hannu biyu takar6a nima haka mungode madallah Ubangiji yak'aro bud'i. Yad'an d'age gira yana mata wani kallo. Tagyad'a kai"Eh mana you're a good samaritan"Yad'an bata marin soyayya suka kyalkyale da dariya.
Abu kamar wasa k'aramar magana ta zama babba,ciwo ya tasa Sumayya a gaba, kullum magani akeyi ciwo yana dad'a k'aruwa, watan ta d'aya cur tana kwance a gadan asibiti sannan tad'an dawo hayyacin ta,ita tamatsa aka sallame ta tare da k'arin wasu sharud'd'ai da zata kuma kiyayewa dan ta zauna lafiya.
Yazuba mata idanu bacci take yi, tayi bak'i ta fita hayyacin ta,shima wallahi jinshi yake kamar mara lafiya.Yadad'a rungume Ummi da take bacci bayan ta gama rigimar a bata abincin ta kuma an yaye ta,ya had'a mata shayi amma tak'i sha,dak'yar dai ya rarrashe ta takoma bacci sai ajiyar zuciya take yi.Ya sauke gwauran numfashi "ALLAH yabaki lafiya Sumayya,ALLAH yasa kaffara ce".
A hankali tabud'e idanun ta takai hannu tana d'an shafa kan Ummi sannan ta kalleshi "sannu Baban Ummi wai har yanzu baka fita ba?Yakad'a kai"Kayyah... Sumayya duk inda naje tunanin halin da na barki bazai barni inyi wani sukuni ba. Amma ai yau naga jikin na ki da sauk'i ko?To me za ta ce? Ita kad'ai tasan azabar ciwon da take ji,ba tasan yawan k'orafi tunda yana matuk'ar k'ok'ari da jikinshi,aljihunshi,kalamanshi da kuma lokacin shi, duk tsadar magana bai ta6a nuna gazawarshi wajan siyo mata shi ba, haka irin kalar abincin da akace shi zata dinga ci dayawa yasiyo mata ya ajiye. Tad'an yi yak'e dayafi kuka ciwo"Alhamdulillahi ala kulli halin".
Ummi tasa hannu a baki tana tsotsa cikin dabara yazare hannu sannan ya kwantar da ita yana tambayar Sumayya abinda za taci da rana duk da a yanzu cin abincin na ta,ba wani na azo a gani bane,wasu lokutan ma sai yanuna 6acin rai sannan take d'an tsakura.
Salim...tabishi da kallo yazauna a gefen gadan yana kallanta shima ya d'anji mamakin kiran sunan shi da tayi yanzu kai tsaye.Yarik'o hannayan ta yana kallan yadda tafin ciki ya d'ashe kamar mara jini amma ko d'azu da safe Doctor Zainab ta tabbatar mishi tana da jini dai-dai yadda ake so baiyi kad'an ba"Uhun me kike so kifad'a min ne?Sharrr...sharrr...wasu hawaye masu d'umi suke zubo mata"muryar ta tafara rawa"ni dai nagode ma Ubangijin mu daya min gata da samun ka a matsayin miji. Ina san ka Baban Ummi...tamishi wani irin kallo da yasa zuciyar shi bugawa da k'arfin gaske.Yakauda kai "Sumayya me za kici?Yasake tambayar ta.Kar ka damu zan sha shayi.Yasa hannu yana share mata hawayen"ki daina kuka ALLAH zai ba ki lafiya mukoma cin had'ad'd'an abincin ki me rai da motsi.Tabishi da kallo cikin kissima wani irin yanayi a zuciyarta.Hawayen suka sake zubo mata sharrr...idan tafad'a mishi yadda take ji a cikin jikinta tayar me da hankali za tayi zai rasa sukuni dan haka taja bakinta tayi shiru.
Ranar da taje gidan Alhaji Hafiz suka wuni suna hira sai bayan isha'i yazo ya d'auke su.Sun kwanta lafiya lau cikin farin ciki sun dad'e suna hirar su kafin bacci yayi awan gaba dasu, amma cikin dare nishinta metsananin k'arfine yafarkar dashi daga bacci, yakunna wutar d'akin tana kwance cikin mawuyacin hali. Sumayya...!ko kallanshi ba tayiba, dan ba ta cikin hayyacin ta ne, idanunta sai rufewa da bud'ewa suke yi kamar wacce tasha kayan maye ta bugu sosai,bakin ta a bud'e ya bushe k'amas,ta rasa inda za ta tsoma ranta taji dad'i sai tafara wata irin shak'uwa,a gigice ya d'auko ruwa yana bata amma bata iya had'iya ba haka yake biyo gefen bakinta yana zubewa tana wata irin jijjiga... Sumayya...! Yafara girgiza ta Sumayya kalleni...!Ina hankalin ta baya jikinta tana gargara..."Laahaula wala quuwata illa billah "kome na ta ya saki a hankali tafara jan numfashi me tsawo sai ta sauke shi a hankali,sai takuma janshi sai yayi kamar ya tafi bazai dawo ba zuwa can sai ta sauke shi a hankali, haka tadingayi,yakwantar da ita yafara neman makullin motarshi amma tsabar rud'ewa wallahi sai yarasa a inda ya ajiyeshi,a fizge tafara kalmar shahada abinda yadad'a gigitashi kenan...zuwa can kuma kamar anyi ruwa an d'auke sai yaji d'ifff...
Sumayya...!yakira sunanta da k'arfi yata6a kirjinta difff...Numfashi baya shiga da fita...Sumayya! Yad'aga hannun ta na dama yarafff...yafad'i a kan katifa.Abubuwa da yawa suka yamutsa k'wak'walwar shi bangaran tunani sai yaji ruguzowar wani abu a k'ahon zuciyar shi da k'arfin gaske Dammm...!!!
Ta mutu...!Sumayya ta mutu...?!!!
Sai yafara k'arya ta zuciyar shi dan idanun sun fara mishi gizo sun nuna mishi ga tanan tana numfashin ta"Sumayya au dama baki mutu ba? Yasake kallanta idanun ta a k'ak'k'afe ruwan ciki yak'ame k'amas suna kallan sama tayi tsawo da wani irin kyau na ban mamaki shi bai ta6a ganin wannan kyan ba ko lokacin da take ganiyar lafiyar ta take kwalliya da gayu...bai san awani yanayi yake ba har sai da aka kirashi a waya.
Miqdad ne yake tambayar shi lafiya kuwa ban ganka a masallaci sallar asubahi ba,ko jikin Sumayyan ne?Asanyaye yace"Sumayya ta mutu.Cikin k'araji Miqdad ya sake tambayar shi"ta mutu? Yaushe?Wasu irin hawaye masu d'umi suka zubo mishi sharrr...sai kawai ya katse wayar yakifa kanshi a kusa da fuskar ta, ya rasa abinda yake mishi dad'i sai yafara Istirja'i...Miqdad shi yaje gida yad'auko su Alhaji Hafiz suka d'unguma gaba d'ayansu zuwa gidan hankali a tashe.Amma Salim yayi dauriya dan shi yamata wanka yashirya ta tsab aka mata sallah aka d'auketa a makara sai makwancinta na gaskiya kabari d'aki a cikin kasa"Uh uhun duniya rumfar kara...Wata rana zai fad'i.ALLAH yajikanki Sumayya yasa k'arshen wahalar kenan!
Lokaci d'aya Salim yayi wata rin rama kamar wanda ya shekara yana jinya.A ranar Iyayanta suka zo.Maman tana kuka ta rungume Ummi tana sambatu "Holy Jesus why? Why? Me yasa Kasham za ta mutu yanzu? Me yasa za ka bari a kashe min yarinya...To wallahi bazan ta6a yafewa ba...me Kasham ta tare muku ne?
Alhaji Hafiz ya k'araso wajan da sauri "haba Dinatu ya kike irin wannna kalaman ne? Mutane fa za suyi zatan kasheta akayi.To dama ba kasheta akayi ba? Kaima ai ka sani ko har ka manta tunda ba 'yar ka bace? Yakad'a kai cikin damuwa"ko na sani a yanzu dai na manta,mudai a addininmu na musulunci duk wanda yamutu to tabbaci hak'ik'a kwananshine kawai yak'are, amma ba mayune suka kashe shiba "ai sara da sassak'a basa hana gamji toho...a ah Shedrak wallahi Kasham dai kashe min ita akayi, ba ta zo sun ganta cikin rufin asiri ba?Takuma yin kururuwa cikin tafasar zuciya"Wai...Wayyoh...ALLAH!!! Kasham ta mutu...Judith ta mutu...oh Jesus Christ of Nazareth!
Shedrak!
Tazuba mishi jajayan idanun ta da suka rine da 6acin rai tadad'a rungume Ummi"bazan yafe ba. Yagyad'a kai"to naji amma dan ALLAH kiyi hak'uri da kukan nan muje ga abincin ku can kije ki k'arya.Bana ci, tasa gefen zaninta tana share hawaye da majina an kashe min Kasham an bar min grandchild cikin maraici... for God sake Shedrak Ummi guda nawa take da zata iya d'aukar wannan tashin hankalin?
Yakalli Ummin"tabbass Ummi ba ta san kome ba,bata ma san me ake kira da mutuwa ba bare har yatashi hankalin ta,guda nawa take?Ko shekara uku batayi ba to amma ya za suyi da hukuncin ALLAH?Yadda duk yaso haka yake zartar da hukuncin shi"idan yaso yafitar da rayayye daga jikin matacce,idan yaso yafitar da matacce daga cikin rayayye"Qaadiran alaa manyasha'u.Dak'yar yasamu ta yi shiru da wannan sambatun da take tayi cikin kuka da d'aga murya.
Makon su d'aya sukayi shirin komawa k'auyansu Madauci,Maman ta so k'warai abata Ummi ta tafi da ita amma Salim da Alhaji Hafiz suka bata hak'uri akan hakan bazai yiwuba kasancewar addini ba d'aya ba.Salim ma yasake ba ta hak'uri tare da alk'awarin kawo musu Ummi lokaci zuwa lokaci suna ganin juna.
"Mutuwa ba ta zama masifa ga mumini,mutuwa hutuce ga wanda yadace da kyakkyawar makoma...ALLAH ba yana nufin 6atama bawa bane dan ya d'auki wani bangare najin dad'in shi Iyaye, mata, miji,Ya'ya da yan'uwa.. Alhaji Hafiz yadafa kafad'arshi "Salim...na san kai namiji jarumi ne,to na rok'eka da girman ALLAH kayi hak'uri kaga yadda kazama kuwa a yan kwana kin nan? Sumayya ta riga ta tafi rayuwarta ta doron duniya ta riga ta k'are,ba abinda take buk'ata awajan mu yanzu sama da addu'a...Addu'a itace abincin mumini...to mu yawaita aika mata dashi.Kaima ka natsuwa kacigaba da zuwa kasuwa ALLAH yabaka macen albarka.Yahad'iye wani abu me d'aci dak'yar yayi furucin" nagode Alhaji ALLAH yak'ara girma...
Ummi tana gidan Alhaji Hafiz dan shi yanemi wannan alfarmar,amma Salim ya dai basu ita dan kawai sun cika mishi idanu ne,saboda yadda yake sintiri ba dare ba rana.Suna hira a D'akin-shak'atawa zuwan shi gidan a aranar karo na uku kenan.Alhaji Hafiz yakalleshi cikin natsuwa "Salim kayi aure mana.Yad'an yi murmushi kawai. Kayi shiru bakace kome ba?Alhaji ba auran ne bana so ba, tunani nakeyi anya zan samu mace kamar Sumayya?Wani irin zama mukayi me cike da amana, me cike da girmama juna,zan samu macen daza ta rik'e min Ummi da amana? Yagyad'a kai"me zai hana Salim?Kai da can abaya ka san za kuyi irin wannan zaman da Sumayya?To karka cire tsammani daga al'amarin Ubangiji mana.jikinshi yayi sanyi wannan gaskiya"nagode Alhaji ALLAH yak'ara girma.
Ummi ta shigo da gudunta dan taji muryarshi"Abba na baka tafi ba?Uh ban tafi ba.Tayi dariya"to muje ka kaini Galaxy...in kira Yaya Zuhair mutafi tare?Yakalleta da kulawa "Ummi baza muje Galaxy ba, lokacin makaranta ya kusa,baza mu sake zuwaba sai an bada hutu kinji ko?Ta6ata fuska sai kawai tajuya tayi tafiyar ta, kwallah sun cika idanun ta.Suka bita da kallo har tafice.
Me yasa kayi haka Salim?Dama taku da Ummi zata 6aci?Lallai yau na ganku a rana.Yad'an yi murmushi"ai ba duk abinda take so nake biye mata ba,wani lokacin ko akwai abin ina hanata saboda ta taso cikin sanin ba ko me da mutum yake so a rayuwa yake samu ba, ko da kuwa yana ganin abin baifi karfin shiba, kauna da soyayyar dana ke ma Ummi ba makauniya bace...
Lokaci k'ank'ani Salim suka dai-daita da 'yar limamin unguwarsu aka daura musu aure,shima sai ya samu sauk'in zirga-zirga tsakanin gidanshi dana Alhaji Hafiz saboda Ummi.Mariya tana kula mishi da Ummi gwargwadan ikon ta, shima ya yaba da hakan sai suka samu kwanciyar hankali dan kowa yana yaba k'ok'arin dan'uwanshi,sai tak'ara bada himma tana mata rik'on tsakani da ALLAH kamar yadda zata rik'e Ya'yan cikinta"yaba kyauta tukwuici.
Yana sanye da wandon chinos ruwan zinare sai riga me dogon hannu da ratsin ruwan zinari da bak'i,kwantaccen bak'in gashin kanshi yanata k'yallin hair fruits,k'amshin Arabian perfume d'inshi ya cika d'akin. Alk'asim da suke abokan wasa tawajan uba yashigo yana kallanshi "Lallai mutumin nan kana jin dad'in ka, kaga yadda kazama wani d'an matashin bak'in bature kuwa? Yabashi hannu suka yi musafaha.To ya karatun? Alhamdulillahi ai ya zo k'arshe tunda na gama rubuta Project d'ina.Ah lallai sai shirin tafiya bautar k'asa to Ubangiji yasa aje a sa a.Amin nagode. Yad'auki remote yana canja tasha baya san labaran CNN d'in nan,yan kanzagin Amurka (America)kanwa uwar gami ce,da yad'a propagandar k'arya akan addinin musulunci da musulmai.Yacire wayar shi da yasa a caji ta cika,suka fita zuwa gidan Hajiya sai dai gidan na ta da kwado sai sukayi zamansu a dakalin k'ofar gidan suna hira.
Aminu yak'araso yana kallan Julaibib cikin raha yace"hey dude what's up?Yagalla mishi harara "Amincin ALAH zaka rok'amana ba wannan ba..yatare shi cikin dariya"kar ka wani harareni kai kayi shiga irin ta su ai dole in maka irin al'adarsu,shima yazauna sannan yamik'a musu hannu sukayi musafaha.
Suna ta hira amma ya dai na jin abinda suka fad'a tunda ya hangota"indai yana gari to ranakun k'arshen mako irin haka yana ganinta.A natse take tafiya irin ta 'ya macen data san abinda take yi wato gefen hanya, yanata kallanta har tasha kwana.Wani murmushi yasu6uce mishi"Yarinyar can ya yaba da hankali da natsuwar ta.Aminu yayi yar dariya"Dan Sarai kenan biri yayi kama da mutum fa...na rantse maka ALLAH da zafi-zafi ake dukan k'arfe idan katsaya kallan ruwa...irin na Aisha to ko ba abinda zai hana kwad'o yamaka k'afa. Yajijjiga kai "tabbass zancen ka dutse...
Washe gari lahadi yakafa ya tsare sha d'aya da rabi yabar Musaddiq a shago yaje dakalin wajan yazauna yana fatan ganinta,dai-dai lokacin aka ta shi daga Islamiyar su,wucewar wasu yan dak'ik'u sai ko gata ta zo zata wuce,yabita da kallo tana sanye da dogon hijab me hannu ruwan sararin samaniya kafad'arta rataye da bak'ar jaka.
"Assalamu alaikum...
Karo na biyu kenan yamata sallamar.Dafarko tayi tsammanin ba da ita yake yiba shi yasa tayi shiru, sai da yasake maimaitawa,a hankali tad'an juyo ta kalleshi sannan ta amsa.Da sauri yamik'e daga dakalin ganin ta juya taciga da tafiyarta... "am... Dan ALLAH...Jimana.Tatsaya ba tare data juyo ba tana jiran abinda zai fad'a.Yayi k'asa da murya "kinga yanzu sauran d'aliban za su firfito kuma kamar zamu takura musu idan muka tsaya anan, ko zamu d'an matsa daga can bakin Library? Batace kome ba suka k'arasa wajan yad'an jingina da k'arfen allan bayani(signboard)d'in yana kallanta ta sunkwui da kai.
Ya Ilahi...sai yarasa abinda zai fad'a ta mishi arwa.Wucewar wasu dakk'ik'u tad'ago kai ta kalleshi cikin natsuwa dan shirun yayi yawa "Malam lafiya?Yad'an sosa kunne"Kiyi hak'uri da na san gidan da kike bazan tsaida ke a hanya ba,can d'in zan biyo ki dan kambamawar data dace dake kenan"Dan ALLAH ina ne gidan ku?Tagirgiza kai"ni ba yar garin nan bace karatu nake yi a Nursing School a cikin makaranta nake zama.
Ayyah...to ya muka ji da shan geron Sunday?(garin kwaki/rogo)yadda yayi furucin cikin jimami yasa tad'anyi murmushi"har da kai? Yagyad'a kai"eh ai duk kanwar ja ce,nima d'alibi ne gobe war haka ai na tsufa a makaranta.Atakaice yamata bayanin kanshi itama haka da garin data fito.
Adai-dai lokacin suka shawo kwana dawowar su daga makarantar allo kenan.Juyowar dazaiyi dan sunyi sallama da Bilkisu caraf idanun su yahad'u dana Sudaida"wani irin yanayi mara dad'i yatsirga ilahirin gangar jiki da zuciyar ta, tagalla mishi harara sannna takauda kai,cikin fushi tayi gaba su Khausar suka tsaya gaisawa suna d'an tsokanar shi"a k'ofar gidansu Nasmat tatsaya dan allanta yana hannun Nasmat d'inne kuma rubutu za tayi da wallahi bata tsaya ba"Khausar takalleta "to ke wai saurin meye haka kike yi?Sauri kuma ba wajan zuwa ba tunda gashi dole ta tsaya jiranmu.Tamusu wani malalacin kallo"shiru ma amsace.Nasmat tacigaba"anya waccan ba budurwar D'ansarai bace?Cikin tafasar zuciya ta fizge allanta"kya tambayi kaza hanyar rafi...?Fuuu tayi gaba tana k'unk'uni.Suka bita da kallan mamaki cikin tunanin abinda ya caza mata k'wak'walwa haka.Nasmat tad'an motsa kafad'a "wallahi can da yawarki yarinya.
Tun daga ranar D'ansarai bai kuma yadda sun had'u da Bilkisu a kwanakin k'arshen mako ba. Ranar wata Juma'a yayi shigarshi ta fararan kaya yad'auki motarshi sai Matsirga anan yayi sallar Juma'a.Yana fitowa daga masallaci yadinga bin kwatancen Bilkisu kasancewar shi ba bak'o bane a garin sai ko gashi a k'ofar gidan.Wani dogon dattijo kyakkyawan farin Bafulani yahango, shi da wani da bai k'arasa shi a tsufa ba suna magana, sun dad'e suna maganganunsu sannan sukayi sallama.
Julaibib yatare shi cikin sallama...
Malam Lamid'o ya amsa sallamar yana mik'a ma Julaibib hannu dan suyi musafaha amma ya nok'e a haka ya gaishe shi cikin girmamawa.Malam Lamid'o sai ya yaba da natsuwarshi yayi murmushi"samari daga ina? Cikin ladabi ya amsa"Baba ni bak'on kune. Yagyad'a kai yana kara nazarinshi"af to,to madallah sannu da zuwa to bismillah shigo ciki,yabud'e mishi d'akin zauran suka shiga yanuna mishi wajan zama"zauna ina zuwa"yajuya zuwa cikin gidan sai gashi ya dawo da damammiyar fura da nono tasha zuma da ruwan sha "bismillah samari"to Baba nagode"yajuya yasake fita dan yabashi waje. wucewar dak'ik'u talatin yasake shigowa lokacin Julaibib yad'an sha fura dan baya wani jin yunwa.
"Samari daga ina kake?
Julaibib Abdullahi D'ansarai...
Shine cikakken sunana daga Zonkwa nake.
Yabashi labarin kome game da had'uwarsu da Bilkisu...Ita kanta ba ta san zanzo nan ba.Ni nazo wajan kane Baba indai bakama Bilkisu miji ba to idan ka amince zan turo maka manyana.Yamishi kallan nazari" yanzu misali idan na amince ita kuma Bilkisu bata amince dakai amatsayin miji ba fa?Yad'anyi jimmm...sannan yad'ago cikin natsuwa yakalleshi "bazanji dad'i ba amma bazan ji haushi ba ,dan na san kome na rayuwar bawa yana rubuce ne,yana kuma tafiya daki-dakine kamar yadda numfashi yake shiga da fita ajikin d'an Adam,zan mana addu'a ni da ita Ubangiji yahad'amu da abokan zama na arzik'i.
Malam Lamid'o yabishi da kallo cikin zancen zuci"wannan d'an matashin tun yanzu yana da halin dattako to inaga ya dad'a girma,ilmi yadad'a cika k'wak'walwarshi? Julaibib idan har Bilkisu ta amince da kai to nima na amince dakai dan ni bazan ma Bilkisu auran dole ba sai wanda ta yadda tana so dan haka,kaje na yadda ka nemi soyayyar ta. Irinka nake ma Bilkisu sha'awa kasancewar ta me d'an ilmi duk da bai taka kara ya karya ba,to amma na san idan tazama matarka za ka ciyar da ita gaba,ta inda taka sa zaka taimaka mata har itama ta tsaya da kafafunta wata rana.
Nayi karatun addini dana zamani dai-dai gwargwado,shi yasa na hana Jauro auran ta saboda ba abinda ya iya ba abinda yasani sai kiwon shanu,ni na san illar zama da jahili dan bazai amfanar da ita da kome ba,d'an abinda tasani d'in ma idan ba tsananin raboba a haka zai k'are.Katuro min manyanka za muyi magana gemu da gemu.Ubangiji yasa Bilkisu rabonka ce.Yasunkwui da kai yana murmushi labarin zuciya a tambayi fuska.
Tana goge kayan sawanta abokiyar karatunta tazo mata da sak'on daya bata mamaki"Julaibib kikace yana nema na?Eh ai kibar wani mamaki dan ga kai ga k'afa ai ba tambayar me aka yanka, jeki wajan da ake ajiye abubuwan hawa za ki ganshi ganin idanunki.
Dogon hijab me hannu ruwan k'asa tasa, yana hangota yafito daga cikin motar.
"Bilkisu me gadon zinare...
Tagaishe shi cikin natsuwa.Ya amsa yana murmushi"Yau dai gani ALLAH ya nufeni da zuwa a wannan yammacin,da zan bari sai gobe to amma dana tuna yaufa Juma'atu babbar rana ce sai kawai nace barin dai k'araso in k'ar6i goron juma'a ta kawai.Tad'anyi murmushi "goron juma'a kake so? Ai ko ka tara ka samu sai ta mik'a mishi lemon Schweppes d'in hannun ta.Yasa hannu biyu yakar6a "wannan kyautar goron juma'ar ta faranta min rai naji dad'i na kuma gode dashi zanci tuwon dawar Inna miyar kuka.
"Bello yace a gaisheki"
Takalleshi tabbass ya je Matsirga tunda basuyi maganar yan'uwan taba, Bello kuma shine autansu. Yaushe kaje?Duk suna nan lafiya? A lafiyarsu kalau,suma suna gaishe ki dakyau. Yad'auko bak'ar leda yaba ta "Malam ne yace in kawo miki.Tarungume ledar cikin farin ciki "nagode.Yad'an kalleta sannan yasanar da ita abinda yake tafe dashi.Tasunkwui da kai"bazance kome ba sai abinda Malam yace"fad'uwa ta zo dai-dai da zama kenan"Malam ai ya amince dani Bilkisu.A kunyace tace to ai shikenan.Sukayi sallama dan rana ta tafi za ta fad'i magriba na shirin kunno kai.
Ana bikin duniya ake na k'iyama.
Akwai lauje cikin nad'i...
20 Jumaada Awwal 1441
15 January 2020
We Ibrahim's Daughters👇
Asdilat KD...2geda with Ra'ibs.
DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION
{Da Inganci Mukayi Fintinkau}
Bismillahi wabihi nasta'in
...GWAJIN DAFI💔
Almost true story
Daga alk'alamin🖊
Ya'yan Ibrahim
Saudat A.Baba (Asdilat KD)
Da
Bara'atu Ibrahim (Ra'ibs)
Masu k'orafin dan me Sumayya bata auri D'ansarai ba,da masu zaginmu wai labari ya d'auko dad'i sai kuma kawai a kashe Sumayya to duk mun ya fe muku bak'ak'en maganganunku, ALLAH ya yafe mana gaba d'aya.Sai dai ku sani shi Ubangijinmu baya ta6a barin wani dan wani, madamar wa'adin barin duniyar ka ya cika to fa ba tsimi ba dabara dole sai ka barta.Kuma ya kamata kufahimci wani abu,shi fa labarin nan idan kuna duba duk shafukan da suka gaba ta,ai muna rubuta"ALMOST TRUE STORY"ba k'irk'irar shi muka yiba,kaso casa'in na cikin shi ya farune,to sai ku gane ba dukkan abinda kake so ne kake samun shi a rayuwa ba,kuma dole ka kar6i rayuwar a yadda tazo maka,canja wani bangare na labarin to yana nufin canja labarin gaba d'ayan shine.
...GWAJIN DAFi💔Labarine me jigo kusan biyar d'unkule cikin d'aya,dan auna fahimtar makaranta.
Your comments is beyond our expectation...
Ibrahim's Daughters really appreciate.
1.Zainab Tijjani Ahmad (Ummu Bilqis)
2.Abdullahi Lawal Abdullahi (D'an Sarai).
3.Me Sunan Manya Khadija Kafanchan.
Ya'yan Ibrahim suna godiya,dan kulawa yabawace.
1.Ummu Ammar.
2.Salima Uba D'an Zainab.
3.Maimunatu Ibrahim.
4.Bilkisu Muhammad (Darling)
5.Zaynerb bello 36
6.عيناء ابرهيم عبد المؤمن
7.Ummul Ameen.
8.Shamsiyya Sani 661
9.Ummee Umar Musa.
10.Samira Garba.
11.A'isha Rabi'u.
12.Zainab A.Sulaiman.
13.Hafsa A.Sulaiman.
14.Khadija Bashir(Ummu Hanan)
15.Ummu aimanal habashiyya(Maman Kinanata)
16.My Sau'ash( Asdilat💋 for real)
17.Nasiba Namadi 'Yar Zonkwa😀
18.Khadija A.Muh'd (Ummu A'isha)
19.+234 813 109 04..I don't really no your name,but you care.
20.A'isha Nura Sani (Dr.Maidiyam)
21.Saudat Ibrahim Yahya.Takwarata wannan sunayen na kifa sune rayuwata💋😀ni Asdilat KD...ina yinki fiye da shurin masaki.
Shafi nagoma sha biyar.
Soyayyarsu ta bazu a dangi,wasu sun yaba sunyi sam barka,yayin dawasu suka koma gefe suna k'unk'uni an rasa gane manufarsu. Suna hirarsu da Hajiya yake fad'a mata"Megado tace a gaishe ki,wannan k'arshen makon baza tazo Islamiyya ba suna jarabawa.Dan haka sai kisa ta a addu'a.Tagyad'a kai"Ubangiji yasa a fara a sa a, yasa asamu kuma abinda ake nema.Amin Hajiya.
Sudaida tana share tsakar gidan tad'an ta6e baki"ni ana fad'in ban iya girki ba sai na iyayi,to su kuma Fulani kona iyayin ma ai basu iyaba,to su da abinda suka iyane banda tatsan nono da tallanshi gidaje da kasuwanni ne?Kai ALLAH yasauwake.Taja dogon tsakin dayasa Julaibib da Hajiya juyawa suna kallanta"lafiyar ki k'alau kuwa Sudaida?
Ta'ajiye tsintsiyar bayan ta kwashe sharan ta zubar.Takauda kai daga kallan da suke mata"kalau d'ina Hajiya gida zan tafi... fuuu tawuce cikin fushi ko sallama bata musu ba.Hajiya tabita da kallo cikin nazari...sai kuma tayi yar dariya"dawalakin goro amiya.
Julaibib yasauke numfashi "Hajiya kwana biyu yarinyar nan sai ta dinga cimin mad'aci,wallahi jiya data shigo wajan Inna tana kallona amma tad'auke kai ba ko gaisuwa kamar bata ganniba.Hajiya tace"yan wasan ne bata jin yi dakai,kaima ba sai ka share ta kaji da hayagagar...su Nasmat ba?Yayi d'an murmushi "Hajiyar mu ALLAH yaja nisan kwana me amfani. Amin Julaibibi amin.
Malam Lamid'o dattijon arzikine yayi karatun addini dana zamani me zurfi a yanzu hakama likitan dabbobine(Veterinary Surgeon) abinda yatarfama garinsu nono kenan Ya'yanshi suke yin karatun boko me zurfi.Bilkisu itace 'yarshi ta biyar,ya barta ta cigaba da karatune kasancewar ta me san karatun,kuma tun data gama Secondary ba wani tsayayye sai Jauro shi kuma yace bazai ba Jauro auran taba,data ce ga abinda takeso ta karanta aikin jinya da unguwar zoma,yaji dad'i ya k'arfafeta dan karatun da za tayi zai amfani mata yan uwanta.Shi da matarshi sunyi tufka me kyau da k'wari wajan tarbiyyar Ya'yansu, sai Ubangiji yadubi niyyarsu sai suka ta so cikin tsoron ALLAH da ganin girmanshi ga kunya da sanin mutuncin mutane.
Nurse Bilkisu Muhammad Lamid'o...
Farace Kyakkyawar matashiyar budurwa,kyau irin na tsurar fulani da bashi da gauraye da kowace kabila dan gaba da bayanta, uwa da uba typical Fulani ne, kome na ta irin na mahaifin tane sai dai bambanci na ita macece shi kuma namiji ne,yanayin maganarta da muryar ta shine kawai irin na mahaifiyar ta.
Bilkisu Megadon zinare...idan tayi murmushi ko dariya kai ko magana tayi sai kaga kamar da san a sanine...takeyi dan kawai tanuna yar lotsar(dimple)dake gefe da gefen fuskar ta da kuma yar siririyar wushiryar ta, abinda yak'ara mata kyau na musamman bak'in gashin kanta me yawa da tsantsi irin na asalin tsurar fulani,sai tattausan jajayan la66anta kamar ta turasu da jan jambaki... Bilkisu me kyauce ga sauk'in hali dan bata rud'u da kyawun halittar da Ubangiji yamata ko ilminta ba,kome na ta a natse take yinshi cikin mutunci da sanin kimar kai(a very meek damsel)Tun tana k'aramar Secondary ta sauke Alqur'ani me girma,har yanzu kuma tana karatun littafan addini.
Sauri take yi tana kuma addu'a ALLAH yasa tasamu abin hawa dan gaba d'aya d'alibai sun gama watsewa a hanyar,Khausar ma ai ta tsufa a gida taimakon ta d'aya da Khausar ta tafi mata da jaka, da harda jakar da littafan ciki da ita kanta ruwan saman da yake shirin sauka zai k'are akansu.
Takad'a kai cikin damuwa"gaskiya wanda duk baiji bari ba zaiji hoho,dama su Nasmat sun fad'a mata kar tasha maganin mura da tsakar ranan nan bacci zai sata,tamusu kunnan uwar shegu tawuce dispensary na makaranta takar6i maganin tasha aiko tun a masallaci suna sallar azahar bacci yafara kawo ma idanun ta ziyara,duk k'ok'arinta na korar baccin abin ya ci tura,ganin haka yasa tama Metron magana dan tasu da Sudaida ta zo d'aya sai ta bud'e mata Hostel"Clerkin's House"har kwanar Kakus d'inta, yar ajin suce amma sunan su d'aya da Hajiya dan haka suke kiranta da Kakus ta haye gadonta ta kwanta aiko bacci yayi awan gaba da ita har aka tashi bata sani ba,bata farka ba sai biyar saura na yammacin amma taji ta garau zazza6in da yake shirin rufe ta ya sauka,sallar la'asar tayi ta d'auki takalmanta tana sawa,lokacin Kakus ta takawo mata jik'ak'k'en k'anzon alkama da madara(corn flakes).
Na ga kina sa takalmi badai tafiya za kiyi ba? Tagyad'a kai tana murmushi"yanzu kuwa"tazauna agefen ta"to amma ai kya tsaya kici abinci na san baza ki iya cin garau-garau d'in dining ba shi yasa na had'a miki wannan me d'an ruwa-ruwa tunda kina fama da mura,tamik'a mata kofin.
Kakus...tasake dubu agogon dake d'aure a hannunta na dama.Uhun Jikalle me kike so kifad'a baza ki sha ba ko me?Tad'an marairaice"ALLAH Kakus...Sai kuma tayi shiru, tasa hannu biyu takar6a,cokali hud'u tasha ta'ajiye "nagode"taharareta"wannan dai dan kar ince baki sha bane kawai.Tadaki kafad'arta'ke yar rainin hankali, to ko akan me zan cika cikina da wanna bayan na san abinci na me rai da motsi yana jirana a gida.Ta tafa hannu cikin salati"Oh ni zamani! yanzu Jikalle ni kike dukar ma kafad'a saboda wuyanki ya isa yanka.Yadda tayi furucin kamar irin Kakar nan ta gaske yasa Sudaida ta kyalkyale da dariya,sai kuma tad'an marairaice itama"come on Kakus don't be upset"kema kin san bana miki haka,to yau d'aya dai ya kamata ki kar6i uzurina, Yaya Khausar ta dad'e da tafiya gida,kuma kinga hadari yana ta had'uwa sai cida akeyi bana so ruwa yatareni.Tadafa kafad'arta"na fahimce ki. Suka mik'e...muje in rakaki.Har gate d'in k'arshe nafita daga makarantar tarakata,dan ALLAH ni dai karki manta gobe ki taho min da soyayyiyar gyad'a,tad'an harareta"to anawa?A neman albarka tad'an zaro mata idanu ko bakya san albarkan manya?Sukayi dariya"so kai"sukayi sallama, sannan suka d'aga hannu suna ma juna adabo.
Iska me k'arfi tafara ta sowa garin yahad'e yayi bak'i sai cida akeyi ba k'ak'k'autawa, abubuwan hawa suka dinga k'ara guda dan tsira daga dukan ruwan watan bakwai,tak'ara sauri akwai gidan yar ajinsu Zamburan agaba sai ta samu tafake,amma ina hak'anta bata tadda ruwa ba,kad'an-kad'an yayyafi yafara sauka tanad'e hannayanta a cikin hijab,sanyi yafara ratsata tarintse idanu"wayyo ALLAH na! Shikenan sabuwar mura zata dawo!
Dagudu motar tazo tawuce ta,wacce yahango tacikin madubi yasa yayi ribas har yak'araso inda take,Caraf idanun su yahad'u yana bud'e motar,wani sanyin dad'i ya mamayeta. Yabud'e mata"to shigo mutafi mana kina ganin ruwan yana k'aruwa...tad'an harareshi sannan tashiga kamar wacce zata zauna a garwashin wuta.
Yaja motar"me kika zauna yi a makaranta? Kamar ba da ita yake magana b.Ba tambayar nake yi ba? Dak'yar kamar me ciwon baki dan haushin shi takeji tace"baccine yad'aukeni a dormitry"bai sake magana ba yacigaba da tuk'inshi cikin natsuwa,sai dai ruwan daya cigaba da zuba kamar da bak'in k'warya yasa shi gangarawa gefen titi yatsaya har sai yad'an tsagaita.
Yaya D'ansarai...
Yad'an kalleta"na'am.Taturo baki gaba"nifa gaskiya in dai ba so kakeyi in k'arasa mutuwa ba to kashe wannan mukayyib d'in(Air Condition) ...kafin tagama rufe baki tafara atishawa,sai da tayi biyar ajere"Yar hamukallah "yace mata bayan ta godema ALLAH."Yahdi kumullahu wayuslih baalakum"tasa hannu tana jan hancin ta daya fara toshewa,k'wallah yacika idanun ta dan wallahi sanyi takeji bana wasa ba gashi kayan jikinta ajik'e suke.Sai da yamaida ita heater sannan tafara dawowa hayyacinta motar ta d'auki d'umi,ruwan yad'an tsaigaita motocin dasuka tsaya kowa yaja yacigaba da tafiya.
Suna shiga gida Mama tace"Masha-ALLAH dama yanzu nake dad'a yima Adnan magana yad'auki mashin yabita makaranta yad'aukota"Yayi d'an murmushi"a hanya muka had'u dawowa ta daga Kaduna kenan.Adnan yafito daga d'akinshi yana mita"Mama banda kece da kanki kin cika min idanu kin shak'emin wuya da wallahi ba inda zani ruwa bai gama d'aukewa ba. Tagyad'a kai"to kayi zaman ka mana.Yak'arasa kulle k'ofar tashi"a haba dai Mama ai wata fuskar tafi gaban mari har abadan duniya.Yana shiga D'akin-shak'atawar yagansu...yauwa yayi yar dariya"kai madallah da autan Inna.Yamik'a mishi hannu sukayi musafaha,yajefama Sudaida mukullin"kai min d'aki".
Khausar tashigo da lemu ta'ajiye agaban shi bismillah fa.Yagirgiza kai"bazan shaba,kirasa abinda za ki kawomin sai lemu me sanyi bayan yanzu aka gama tsuuga ruwan sama har da k'ank'ara?Yamik'e dai-dai da shigowar Mama."Mama na wuce.A ah ka tsaya yanzu nasa Sudaida takawo maka kayan bud'a baki.Yad'an shafa kai"Nagode Mama amma kiyi hak'uri sauri nake yi dan gidan Hajiya zani kafin in wuce gida" To ai ba kome musha ruwa lafiya.Amin Mama.
Hey autan Inna...
Zai shiga mota yaji kiranta yajuya yana kallanta ta canja kayan jikinta da riga da wando kirar Pakistan ruwan k'asa da yarfin k'anana filawoyi ruwan hoda me haske,tad'ora farar rigar sanyi tasak'a da farar hula me harafin M.Gashi inji Mama.Bai kar6i ledar ba yace me wannan harafin M d'in yake nufi?Takai hannu tashafa harafin"Masoyi na Sinan ko da wani masoyi ne bayan shi?Yamata wannan rikitaccen kallan nashi takauda kai "gashi ni sauri nake yi. Yashige mota ya zauna"ki kaimin gida yayi tafiyar shi.Tabi danjojin motar da kallo har ta 6ace ma ganin ta.Takalli ledar taja dogon tsaki"kawai dan kabani wahala,shi dai wannan halin na shi ALLAH yasauwak'e mishi...tashige gida tana k'unk'uni.
A safiyar asabar suna hirarsu da Inna yana shan shayin na'a-na'a da ya'yan algarib tashigo da sallama, tagaishe da Inna sannan tazauna a kusa da ita tana fad'a mata sak'on Hajiya.
Yamaida hankalin shi ga sauraran wak'ar wani balarabe yana wake Habibti d'in shi da irin soyayyar daya ke mata wai"ya kamu da yunwar son ta,kuma ita kad'ai take da irin nau'in abincin da za ta bashi idan yaci sai yadawo hayyacin shi,dan yanzu shi ya zama kamar gawane da rai"yad'auki remote yad'an rage k'ara yana cigaba da sauraran tsadaddun kalmomin da yaketa bayyana irin k'aunar shi gareta me sanya zuciya bugawa a cikin shauk'in so,har baitin k'arshe sannan ya canja tasha.
Kiran daya shigo wayar shi yasa yamik'e yafita,Sudaida tabishi da kallo sai kuma tamik'e itama dan makarantar allo za ta wuce.
Yana tsaye a k'ofar gida yana wayar cikin sakin fuska,yayi k'asa da murya yana gyad'a kai"na sani Megado amma na manta ne,ALLAH yamiki albarka da wannan tunatarwan.Yayi jimmm...yana sauraro"to shikenan karki damu kinji ko?...yauwa to nagode sai na shigo.
Tawuce kamar bata ganshi ba.
"Am Sudaida...
Takalleshi fuska a had'e.Yayi yar dariyar data bata mamaki dan ba kasafai yake hakan ba.Yauma kin shigo gidan nan kin kuma ganni ganin idanun ki amma baki gaisheni ba,wai in tambayeki mana? Kallanshi tayi batace kome ba "Sudaida... wannan cin mad'acin da kike min bana jin dad'in shi kona miki wani laifi ne?Tad'an turo baki gaba sannan ta kauda kai"ni ba kome.Anya zan yadda dake kuwa?Takalli siririn agogon dake d'aure a hannunta sai kawai tajuya "gwamma da kai auran ka da gata kar inje insha dukan makara.Ki tsaya muyi sallama dan baza ki dawo makaranta ki same niba.Jikinta yayi sanyi amma bata tsaya ba tacigaba da tafiya"To ALLAH yakiyaye hanya ai zamuyi waya.Ki tsaya ki kar6i"tasa gudu nifa bana so.Yabita da kallo yana wata kissima a zuci.
Jikokin Hajiya sun cika mata gida sunata sha'anin gabansu.Sudaida takallesu"kun san ALLAH cikin makaranta zan koma(hostel)na gaji da trekking sai randa aka ga dama za a zo a d'aukemu.Nasmat takama ha6a"to makarantar allon kiyi yaya da ita? Idan an ba da hutu na dawo gida sai in d'ora daga in da natsaya.Hajiya tasa musu baki"yanzu ke saboda makarantar boko za ki bar makarantar Mahammadiyya? Bayan shine a hakku akanki?Taturo baki"ai ba cewa nayi na daina ba,kuma ai nafad'a ma Baba ya kuma amince.Hajiya tamata dakuwa"to ni ban amince ba zai kuma zo yasameni bokon banza bokon wofi, bokoko a wuta. Nasmat ta kyalkyake da dariya"Ke Hajiya bokon kike ma wannan zagin kamar bakiyi ba?eh na zaga,dan kayi karatun boko indai ba karatun Muhammadiyy ai shirme kayi...ko ba ga sunan ba marasa addinin k'wararrune a fagage mabambanta na cigaban rayuwa amma sai kika mutum wai yasa abinda zai bautama sai saniya ko rana ko kwad'o...wannan ba 6atan basira bace da rashin sanin tauhidi?Ai ba abinda zai baku rayuwa me inganci sama da Alqur'ani da hadisan Manzon ALLAH dan ya tattara kome shak'undum kenan.
Washe gari kuwa data je gaishe da Baba yake fad'a mata komawarta cikin makaranta an soke shi, Hajiya tazo da magana abar dubawa,yamik'a mata babban envelop foam ne guda biyar a ciki,ki kaima Nasmat na ta gida ko wacce tacike ranar Juma'a zaku fara zuwa makaranta,tasa hannu biyu takar6a"to Baba ta tashi tafita.
"HAYATUDDEEN ISLAMIYYA SAMARUN-KATAF"
yanzu har Samaru zamu dinga zuwa?Wallahi duk Hajiya ce da wannan aikin saboda kawai nace zan koma cikin makaranta shine har ranakun k'arshen makon ma bazata barmu mud'an sarara ba?Taja tsaki tana k'unk'uni,tad'auki biro tana ciccike inda ake so aciken.
Maganar Julaibib da Bilkisu ta kan-kama sun kai kome da a ke kaiwa an kuma tsayar da lokacin biki watanni uku masu zuwa dai-dai da gama karatun ta. Julaibib ya tafi bautar k'asa,jahar Bauchi aka turashi angama basu horan sati biyu a sansaninsu(camp)yakoma inda zaiyi service d'inshi a k'aramar hukumar Azare.
Sai da yayi wata d'aya sannan ya dira a Zonkwa dawani yammacin laraba rana ta tafi zata fad'i magriba na shirin kunno kai,yatsaya yayi sallar magriba sannan yatafi gida.Inna tayi murnar ganinshi dan bazata ya mata bai fad'a mata ko awaya ba.Baije ko ina ba sunata hirarasu ta yaushe gamo yana cin abinci ita kuma tanata kalan hotunan dasuka d'auka lokacin da a ke basu horo(training)tad'aga wani hoto tana murmushi ashe kunsha wahala?Yagyada kai"Eh Inna akwai wahala dan sojojine suka bamu horon cikin dare zasu kafa su tsare kowa sai yafito su fara bamu horo tayi yar dariya"lallai kun zama k'ananan sojoji.Amma ni ban wani sha wahala ba. Tagyada kai"ai baza kashaba tunda ka saba motsa jiki da manyan k'arafa yanzu har mata sai sunyi wannan?Eh har su sai sunyi masu tsohon ciki ne kawai naga an d'aga musu k'afa.Taja tsaki wannan tsarinne kawai bai min ba.Yad'anyi murmushi"To ya zamuyi Inna tsarin ne yazo da haka amma Insha-ALLAH bama cire rai da wata rana za a samu manya a harkar masu addini da zasu zamantar da abin dai-dai da shari'ar musulunci a raba mata musulmai da irin wannan shigar a bainan-nasi.Inna tad'aga hannu "Allahumma amin Julaibib.
K'arfe shida na safiya sukayi kaci6is akwanar gidansu,dawowar shi kenan daga masallaci sallar asubahi,k'afafunta sanye cikin takalmi sneaker fari igiyoyin d'aurewa ruwan bula,wando ruwan bulu,farar riga sai hijab iya gwiwa ruwan bula sun sha guga tana goye da bakar jaka da Maths-set a hannunta.Tad'an bud'e idanu cikin mamakin ganin shi"Kai Yaya D'ansarai saukar yaushe? Yabita da kallo duk da garin bai gama wayewa ko ina yayi haske ba amma dai tayi kyau"Jiya gab da magriba.Excursion za kuje? Tasake kallan farin agogon dake d'aure a hannunta na dama"ba wani excursion Mr Goje malamin turanci(English)ne yabamu jinga (Assignment) kuma to be submitted before seven O'clock"to shine kike wannan saurin kamar za ki tashi sama?Tagyad'a kai"eh mana wallahi ji nake kamar inyi tsuntsuwa,wai dan ma ba acikin makaranta muke ba shine yad'aga mana k'afa,su yan cikin hostel ai k'arfe shida yabasu,duk wacce tawuce shida koda da dak'ik'a d'aya ne bazai k'ar6a ba,shikenan kuma fa a matsayn C.A test d'in mune,kuma nayita rok'on Yaya Adnan yakaini yace ba abinda zai fitar dashi awannan sanyin,ai dai ALLAH yajik'an Yaya Aminu ba dan yamutu ba dayana gida na san zai kai ni.Tayi gaba da sauri.
A bayan ta taji horn yabud'e mata kofa"ke Sudaida zo ki shiga mutafi.Yad'an kalleta bayan sun hau titi"lallai baku raina Mr Goje ba.Yaya Julaibib wargi waje yake samu,shi wannnan Malamin mugune na gasken-gaske gashi kuma yanzu shine Labour Master,ya yanka ma mutum k'atan fili iya ganinka yace sai ka nome shi wallahi k'aramin abu ne a wajan shi.
Hankalin Sudaida bai kwanta ba har sai da taganta a Staff-Room agaban tebur d'inshi ta'ajiye littafin ta kuma sa hannu,tafito tana sauke numfaahi"wai ALLAH na! nayadda k'wallan mangwaro na huta da kud'a.Takoma wajan Julaibib yanata kallanta ta gilashin motar yana kissima wani abu a zuci,tad'auki jakarta. Yad'ora hannun damar shi a saman sitiyarin motar"kin ko karya?A ah.Yakalli agogon motar ai da sauran lokaci kafin kuyi assebmbly ko muje Staff-Quater gidan abokina Aminu Idris ki karya a can?Tagoya jakar"barshi kawai Yaya Julaibib,ai Yaya Khausar zata kawomin.Sukayi sallama,yad'an lek'o da kai "kuyi hak'uri yau akwai inda zani dana dawo na d'auke ku"tad'aga hannu tana mishi adabo ba matsala nagode,tabi motar da kallo har yafita daga gate d'in farko sannan tajuya zuwa ajinsu tana murmushi.
Kwanci ta tashi asarar me rai,biki saura wata d'aya,awannan lokacin Julaibib baya samun zama saboda zirga-zirga tsakanin Azare da Zonkwa,Yadad'a gyara bangaranshi dan anan zasu zauna tunda bai gama ginin shiba.Dasafe yaje gaishe da Kawunshi sunata hira musamman abinda yashafi kasuwancinsu,sai da zai tafi yamik'a mishi wasu mukallai na gidan kane,na baka d'aya daga cikin gidaje na na Unguwar-Rama daura da masallacin Yarbawa hakak malak. Julaibib yad'ago kai bayan ya duba takardar shaidar mallakar gidan sunan shinei ajiki"Kawu nagode ALLAH yasa da mafificin sakamakon shi, ALLAH yak'ara girma.Amin.wannan ai ba kome bane.
Yad'auki Musaddiq sukaje suka ga gida,sabone dal sai k'ura dayayi tunda bakowa yasa yara suka wanke lungu da sak'o na gidan.Kafin yakoma Azare sun sa kome da ake buk'ata suka kulle sau ranar daza a kawo amarya.
Yajingina da bishiyar mangwaran k'ofar gidan yana kur6an madarar shanun tatsar lokacin,hirarsu sukeyi cikin nishad'i irin ta masoyan juna.Bilkisu har naji kin fara k'amshin amarci fa.Tad'anyi murmushi.Yayi tsai da idanun shi yana kallanta"Megado baki ce kome ba? Takauda kai"Kazo ka tafi bana so kayi dare a hanya daga nan zuwa Azare tafiyace me tsayin gaske"Megadon bana san tafiya yau "Takalleshi cikin kulawa"saboda me?Yanunata da yatsa.
Tad'anyi luuu da idanunta kamar zata rufesu sai kuma ta sunkwui da kai"Julaibib ai kai nawane,ni d'in nan ta kace Insha-ALLAH,amma bazan so ace nice silar ta6ar6arewar al'amuranka masu mahimmanci ba,bautama k'asa a matsayin ka na d'an bautar k'asar dole ne,kome kuma za kayi to kayishi yadda ake buk'ata,kazama me amana; tafiyarka ai ba itace rabuwar muba,koda munyi nesa da juna to amma ai zukatanmu suna tare,kuma ga waya muna gaisawa,muna chatting, har video call duk munayi,tad'ago cikin natsuwa da kulawa tad'an kalleshi"duk basu wadatar ba D'ansarai?
Yanad'e hannayan shi a k'irji yana murmushi "sun wadatar Megado,ke macen alheri ce da bata taya 6era 6ari.Yamik'a mata kofin madarar yashiga mota yazauna yana d'aura belt "ALLAH yamiki albarka Bilkisu "tarufe mishi murfin"Amin D'ansarai nagode,sukayi sallama. Tabi bayan motar da kallo a hankali yake tuk'in har ya6acema ganinta.Tajuya zuwa cikin gida tana mishi addu'ar sauka lafiya.
Inna tabita da kallo"har ya tafi?Sai lokacin tasan Inna tana tsakar gida,ta zauna a gefan tabarmar tana d'an murmushi,kumatun ta suka lotsa ciki"a kunyace tace ya tafi Inna"sai kuma tamik'e da sauri ta shige d'aki.
Tana shan rake tana 'yan wak'ok'inta cikin nishad'i,Khausar kuma tana karanta wani littafi"The secret of occultics powers"su Nasmat suka shigo suna hayaniyarsu,A'isha tace ya naganku haka?Khausar takalle su "to da ya kike so ki ganmu? Tazauna a gefan gadon"banga kun shirya ba,za muje ganin d'akin amaryane. Khausar ta ajiye littafin"har kin tunamin ance da mahaukaci baya duka.Tabud'e wadrobe tad'auko hijab sannan takalli Sudaida"to mayyar rake badai za kice jiranki za muyi har sai kin gama shaba?
Tamusu kallan uku ahu"kuyi tafiyarku dan ni bana zuwa gayyar sod'i.Suka bita da kallo cikin mad'aukakin mamaki"gayyar sod'i fa kikace? Zuwa gidan Yaya Julaibib d'in?Tayi kamar bataji suba...zuwa can bayan ta shaki iska ta baki ta hanci tafesar tana wani tsuke baki"Eh shi d'in fa wani abu ne?Ni dai wallahi banga abinda zanje gani wanda ban san shiba,ban ta6a ganin shi ba, taja dogon tsaki"gado ne fa da sauran tarkace, tad'ora hannun damar ta a katakon gadan su, wannan ai gadone ko?To gashi na gani akaima nake bacci,sauran tarkacenma muna dasu a D'akin-shak'atawa da D'akin-girki,kuma bama amaryace za tazo da suba,ta kuma jan dogon tsaki cikin tafasar zuciya"kai ALLAH yasauwak'e ma Fulani,wai ace kome mijine zaiyi,ga uban sadaki da suka yanke mai,dubu hamsin sai kace siyar da ita za suyi"ai dai k'arancin sadaki yawan albarkar aure wallahi.
Khausar ta tareta da sauri"ke dakata haka malama ai a addinance dama mijine yakeyin kome na d'aki yakuma biya sadaki,dan hakkin akanshi yake ba akan iyayan taba,mu hausawa mune muka fifita al'ada sama da addini a wannan bangaran,kema ai kin sani sarai ban san abinda yasaki wannan furucin ba.
A'isha ma takalleta"lallai ma yarinyar nan yanzu idan ma siyar da itan za suyi sai su siyar da ita a kud'i me mugun rangwame haka? Dan ALLAH nawa ne 50K? Kai Sudaida me yake damun kine naga alama bakya san
Nurse Bilkisu Muhammad Lamid'o...
Ni kuma wallahi tana burgeni saboda sauk'in halinta,wallahi sam bata d'auki duniya kayan gabas me k'amshin turaran d'an goma ba, haka fa ranan nan da muka had'u da ita a hanyar Islamiyyar su itafa tafara gaishemu amma kikayi banza da ita,bakyau irin wannan halin ko Yaya D'ansarai da baya san kula mutane amma idan kika mishi magana zai kulaki ko sama-sama ne.
Nasmat tana ta nazarin kalaman Sudaida tayi yar dariya tana tafi tasake kallan Sudaida"kina kishi ne?Takusa k'warewa da raken da take sha Dammm... zuciyar ta tabuga tamata wani kallo"kishi kamar yaya,me zai sani yin haka?So...Nasmat ta bata amsa.Duk sai suka zubama Sudaida idanu"biri fa yaso yayi kama da mutum. Numfashinta yad'auke na wucin gadi... tamik'e cikin fushi tana kallan Nasmat "so fa kika ce?Tagyada kai"eh kwarai kuwa so.Sai tafara hayagaga..."eh so ne sai me?Suka kyalkyale da dariya ganin yadda take masifa"eh ina san nashi amma ba irin soyayyar da kike tunani bane, soyayyace irin ta yan uwan taka, karki manta ina da masoyi na da makaranta yake jira in gama sai in koma k'ark'ashin shi ta inuwar aure.
Nasmat ta daki kafad'arta tana dariya "ahaf ba mage ba miyauuu...Takalli su A'isha"kuzo mutafi kunji tunda baza tajeba.Tabisu da kallo har suka gama fita a d'akin.Tad'auki hijab tasa gwamma kawai tabisu,sai wani irin abu mara dad'i ya tsirga ilahirin jiki da zuciyar ta,kawai sai ta koma ta kwanta,tad'ora tafin hannun damar ta a saman goshin ta dayake barazanar yin ciwo, ta yamutsa fuska tana hura iskar bakinta tana jin wani d'aci kamar tasha mad'aci.
Mama uwargidan Alhaji Ibrahim macen albarka,macen k'warai dattijuwa me yakana da karamci, uwargidan cinta na dalci da amana takeyi,abinda yahaifar da kwanciyar hankali kenan,yasa zuri'ar gidan suka dunk'ule suka zama tsintsiya mad'aurinki d'aya.Duka Ya'yan gidan ta d'aukesu abu d'aya kamar ita ta haifesu.A d'aki tasamu Sudaida a kwance idanun ta a rufe,amma ba bacci takeyi ba.Ta zauna a gefan gadan,Sudaida tabud'e idanun ta da suka d'an canja kala.Mama takalleta da kulawa"wai mantawa kikayi da Sinan a waje?Tadad'a kwantar da kanta a saman matashi "Mama kaina ne yake min ciwo"sanin hali yafi sanin kama"sai tayi murmushi kawai"To ai ya kamata kije kifad'a mishi kar yayi jiran gawon shanu ko?A ciki ta amsa kamar ranta bai mata dad'i ba"to Mama na ji.
Tana fitowa yatareta"Sudaida Sarauniyar Sinan"taturo baki gaba tana d'an harararshi"kai baka san kaina ne ya dameni da ciwo kuma Mama ta matsamin dole nafito"yayi murmushi wani lokaci haka take abu kamar wata 'yar k'aramar yarinya wai an matsamata dole tafito.Sai ya marairaice"Oh ALLAH! Wayyo! Sannu Sarauniyar Sinan taso muje ki kar6o magani? Tagirgiza kai'ai ma navfara jin sauk'i.Yasauke numfashi"kai nagode ma ALLAH,dama ni ne maganin ko?Sukayi dariya.
Tana d'ago kai za tayi magana caraf idanun su yahad'u dana Julaibib,yana sanye da shadda ruwan k'asa yayi shar...shar dashi,magana yakeyi a waya yaja yatsaya nesa dasu.Tad'an ta6e baki"wayar tak'ici tak'i cinyewa,ba mamaki shi da wannna Bafulatanar ce.Yagama wayar sannan yamata wannan rikitaccen kallan da tadad'e bataga ya mataba,dama baya kulasu in dai yatarar suna hira ko magana tamishi sai yayi kamar ba dashi take yi ba"kunnan uwar shegu"tabishi da kallo har yashige cikin gidan.Takalli Sinan ni zan wuce"Shikenan anjima zan bada masoyin Sarauniyar Sinan akawo miki (rake) tayi d'an murmushi "nagode.
Ranar Juma'a suna gidan Yaya Karima sunje mata ziyara sai gashi yashigo da sallama.Yazauna suna gaisawa da Yaya Karima tana tsokanar shi"Kai autan Inna har wani haske naga ka fara ko kaima kana gyaran angwancinne dasu halawa da dilka?Yakai hannu yana sosa k'asumbarshi yana yar dariya"Kai Yaya Karima duk sukayi dariya;banda Sudaida da ta tayi kamar bataji me aka fad'a ba,tacigaba da cin sinasir d'inta,Nasmat tace"wai ina masar Bauchin dana ce ka kawomin tsaraba?Haba ke kuwa Nasmat ai k'aton aiki za ki bani ace tun daga Bauchi har Zonkwa in rik'o masa?Gaskiya bazan iyaba,indai za kici kantu(rid'i)to kije wajan Inna ki kar6a.
Ni masa nake so tunda baka kawo min ba ai shikenan nagode ALLAH kuma yabamu lafiya, amma da Bilkisu ce tace tana san masar ai baza ka d'auki hakan a matsayin k'aton aiki ba ko? To dake da Bilkisu Megadon Zinare...d'aya ne? Sudaida tamik'e"uh wannan Bilkisun dai ko gadon Mahogany ba ta dashi"tajuya za ta bar d'akin. Yarik'o gefen hijab d'inta..kafin yayi magana tajuyo cikin fushi"Yaya D'ansarai sake min hijab ka san dai bana wasa da maza.Su Nasmat suka kyalkyale da dariya kaji wata magana kuma? Yakalketa cikin natsuwa"idan kuma ban sake ba fa?Tayaye hijab d'in gaba d'aya daga jikinta tajefa mishi a fuska "kaje ka kai mata"fuuu...tafita mayafin Yaya Karima tajawo a igiya tayafa.Duk suka bita da kallo.Yaya Karima takama ha6a"to ana wata ga wata aure ya mutu ga gara.Takalli Julaibib ya sunkwui da kai"ranshi a 6ace yake,amma ta san bazai yi magana ba tunda yayi haka,wannan halin shine tun yana yaro indai ya sunkwui da kai.
Yamik'e da hijab d'in a hannun shi "Yaya Karima ni zan wuce idan Baban Abdul yadawo kya mik'a min sak'on gaisuwa.To auta mungode kwarai kagaishe dasu Inna sai na shigo.
Har yakoma Azare Sudaida bata yadda sun kuma had'uwa ba ko gidan Inna bata sake zuwa ba dan kar ma su had'u sai bayan data tabbatar ya tafi sannan taje.Yakirata sau d'aya a waya tak'i daga wa shima bai sake kira ba.
Tana zaune a dakalin k'ofar gida da tunanin inasu Mama suka suka tafi haka harda kulle gidan gaba d'aya bayan sun san za su dawo daga makaranta?Sagir yazo da gudunshi zai kwashi kayan wasa a inda ya6oye can wani sak'o, tarik'o hannu"su Mama ina suka tafi?Matsirga su da Yaya Musaddiq da akwatuna,tasake shi yatafi. Lefe sukaje kaiwa kenan? Tad'an ta6e baki.
Gidan Yaya Musaddiq tawuce. Safiyya tace"wata sabon gani.Tazauna a kujera tana yar dariya"ALLAH Yaya Safiyya ba lokacine kullum muna hanyar makaranta.Tagyad'a kai"na yadda,to shiga D'akin-girki kizubo abinci danna san kin kwaso yunwa,tak'arasa kwanciya a kujerar "ai azumi ma nake yi,ke me yahanaki zuwa garin Fulani kai lefen?Uhun ke dai bari har na shirya sai ga baki na yi ba zato ba tsammani basu dad'e da tafiya ba.Takuma ta6e baki tamaida idanun ta tarufe kamar tana bacci amma ranta in yayi dubu ya 6aci,taja tsaki tanata juye-juye,data gaji sai tamik'e tafito da littafin lissafinta tana nazarin Quadratic Equation.
Julaibib da Bilkisu suna tsaye a wajan da ake ajiye motoci na cikin makarantarsu, tana tambayar shi "ya me jiki? Yagirgiza kai"ni fa ki daina tambaya ta ya me jiki, idan kina san sanin ya take ai zuwa za kiyi ki gaishe ta ko? Haba Megado wallahi kin bani kunya ace Yaya Asma'u takwanta a asibiti kwanaki goma kenan amma ki kasa zuwa gaisheta,aiko ba soyayya a tsakanin mu to akwai hakkin musulmi akan musulmi koda ba dangin Iya ba na Baba,gaishe da mutum idan ba shi da lafiya yana daya daga cikin hakkoki biyar akan musulmi da musulmi.
Tasunkwui da kai"kayi hak'uri D'an Sarai Insha-ALLAH zan je.Yagyad'a kai"to muje in rakaki. Nagode zan je ni kad'ai suka d'an ta6a hira kad'an suka yi sallama. Abakin a sibitin ta tsaya ta sai kayan marmari sannan tashiga.
Sudaida ce tabud'e k'ofar,suka kalli juna Bilkisu ba girman kai sai ta gaisheta,tatsuke baki cikin yamutsa fuska ta amsa mata dak'yar sannan tabata hanya.Tashiga da sallama ta durk'usa ckin natsuwa me had'e da kunya tagaishe da Hajiya tana tambayar ya me jiki?Dan ALLAH amin uzuri da banzo da wuri ba yanayin karatun mune sai a hankali,Tamatsa jikin gadan tana gaishe da Yaya Asma'u da tambayarta karfin jiki.Tayi murmushi"jiki Alhamdulillahi tunda gobe ma za a sallame ni.
Hajiya ta kalli Sudaida"kawo mata ruwa mana.Tajuya tama Bilkisun wani kallo"Hajiya ita tace miki tana jin k'ishi?Mutanan d'akin suka bita da kallo in ka d'auke Bilkisu da Hajiya.Bilkisu ta sunkwui da kanta,Hajiya kuma tana nazarin Sudaida a karo na barkatai kenan tana nuna halin-ko-inkula da duk wani abu daya shafi Julaibibi tun lokacin da maganarsu da Bilkisu ta kan-kama, takad'a kai"lallai da magana karuwa ta ziyarci tuzuru.
Yanzu sai ta ce tana jin k'ishi za a bata ruwa Sudaida?Bak'on ka annabin ka.Tamik'e tana k'unk'uni tad'auko ruwan ta dangwarar a gabanta.Hajiya tadafa kafad'ar Bilkisu da sigar rarrashi dan abinda Sudaida tayi bai kyautu ba sam"kiyi hakuri Bilkisu"Tad'anyi murmushi me had'e da kunya"ba kome Hajiya,dan kar suce taji haushin furucin Sudaida ne da baza ta shaba tunda ba ta jin k'ishi,kad'an ta tsiyaya a kofi tana kur6.
Sudaida ta galla musu harara, tabud'e jakar ta tad'auko earphone tamak'ala a wayarta sannan ta toshe kunnuwan ta dashi, tashiga bin wak'ar, zaman d'akin ya gundireta sai tafita tabasu waje ganin hadari yana had'uwa yasa tawuce gida
Feshin ruwan yafarkar da Khausar daga baccin data fara,ga littafan data barbaza a saman tebur har sun fara jik'ewa,tarufe taga tasuke labulan sannan takalli Sudaida "saboda ALLAH kina ganin ruwa zai jik'a min littafai amma kika ki rufe taga?Tayi kamar ba da ita take magana ba,sai ta fizge wayar"bakya jine ina miki magana?Tabita da kallo"ke wai kwana biyun nan lafiya kuwa?Eh ita takawo haka,tamik'a mata hannu bani waya ta.Tabata wayar tana gyad'a kai"lallai kam nima naga alama lafiyar ce takawo haka,tayi d'as da yan yatsunta"to amma fa karki manta duk kanwar ja ce,baki fini tsummaba bazan zauna kina 6ar6ad'eni da k'wark'wataba, wallahi ban kar zomo;tanunata da yatsa ke baki isa ki kisa ni d'aukar rataya ba.Sudaida tabita da wani malalacin kallo"ALLAH sarki.
Suna tsaye kusa da rafin Matsirga D'ansarai yad'aga kai yana kallan Qudirar Ubangiji duk da ba ranar yafara gani ba,Tsawon tudun yayi gidan sama hawa uku tanan ruwan yake fitowa yana gangarawa wani rami a can k'asa me tsananin zurfi kuma a saman turawa sukayi titin jirgi k'asa kuma har yanzu tanan d'in yake wucewa,sa dai gaskiya duk wanda yafad'a ramin nan to ya gama numfashi a doron duniya wallahi.
Bello yarik'o hannun Bilkisu "Adda zo mu tafi gida kinga hadari yafara had'uwa kar ruwa ya 6alle.Julaibib ya kalleshi"to mutafi suna tafiya suna d'an ta6a hira har suka zo k'ofar gidan.Julaibib yabud'e mota yad'auko wasu wara-warai (Awarwaro)masu kyan gaske a d'an gidan su"wannan kyautar soyayyace ta musamman ga wacce tayi nasarar mallake zuciyar Julaibib... Bilkisu Megadon Zinare...Bilkisu Zinariya kike kinfi azurfa.Yamik'a mata tasa hannu biyu ta kar6a "nagode k'warai Julaibib D'ansarai".
Ke kad'ai nake so Megado...
Tasunkwui da kai tana d'an murmushi cikin jin kunya kumatunta suka lotsa.Yad'an d'age gira"au baza kice kome bane?Tad'an d'ago takalli Bello ya ko zuba musu idanu kuriii yana kallansu. Yayi murmushi"Oh na fahimta,a dinga sara ana duba bakin gatari ko?Tagyad'a kai.Sukayi sallama a gaggauce dan an fara yayyafi.
A sanda hantsi yadubi ludayi amma har lokacin garin da sanyi saboda ruwan saman da aka dinga tsuugawa kamar da bakin k'warya tun dare har wayewar gari sai wajan k'arfe bakwai da rabi ruwan yad'auke,Iska tana ta k'adawa. Tibishi yakalleshi amma jiya ka burgeni.Yakai mishi duka"wani burgewa ka sa inata tari kamar zan shid'e,sukayi dariya suka tafa"ai da haka za ka zama k'wararre.Tibishi yad'an ta6a shi"kai ga mutuniyar ta ka can,yajuyo da sauri "haba dai? Bai gan taba dan ta riga ta sha kwana" amma dai bata ganni bako? Yagalla mishi harara "kaji d'an iska to idan ma ta ganka sai me? Yamik'e"a ah wallahi da matsala,katafi kawai anjima anjima zan nemeka a waya.
Tabishi yarik'o rigarshi ta baya "dakata malam ai ba haka mukayi dakai ba,sai ka bani kud'i indai kana so katafi,baiyi magana ba yaciro d'ari biyar yabashi yajuya da sauri dan kar tayi nisa.Tabishi yabishi da kallo yana kyalkyala dariya"Sinan shegen duniya,kura da fatar akuya yad'an yi tsaiii...nawucewar wasu dak'ik'u yana kissima wani abu a zuci sai kuma yad'an motsa kafad'a"any way akwai dai ranar k'in dillanci ranar da hajar me gari zai 6ata.
Gudu-gudu sauri-sauri har ya cimmata yasha gabanta"haba Sudaida Sarauniyar Sinan ai ya dace ki tsaya ki saurareni ko?Tagirgiza kai"bai dace ba" Sinan katafi kabani waje karka 6ata min lokaci a banza a wofi.Yakwantar da murya yadinga mata kalaman rarrashi da bambaki har sai da yaga tana murmush"amma ai kai kafad'a min da bakin ka ka daina kulasu Tibishi amma ayyukanka suna k'aryata furrucin ka,jiya da yamma gab da za a fara ruwa tare naganku ka goyo shi a mashin kunyi hanyar D'One takalleshi cikin natsuwa wajan shan giyar koko ka kaishi da kanka Sinan?Yanzu kuma na sake ganinku tare kuna hirarku kuna ta dariya har da tafa hannaye; Sinan wai mantawa kake yi da d'abi'a tana na so? Zama da mad'aukin kanwa yana kawo farin kai fa. Haba Sinan me...
Yatari numfashinta"Kiyi hak'uri Sudaida amma wallahi Tibishi shi ke bibiyata,ni kuma abinda yasa nakasa korarshi muyi baran-baran ina mishi kwad'ayin musulunci,wata kila ta dalilin Sinan masoyinki sai kiga ya samu dacewa zuwa addinin gaskiya kina wannan ai babban jihadi nevko?Tajijjiga kai"mutum d'aya yashiryu ta dalilin ka yafi abaka jajayan rak'uma guda dubu "Yad'an shafa k'irjinshi bangaren zuciya"Oh ALLAH nagode maka"sukayi dariya yad'an taka mata sannan sukayi sallama tawuce gidan Hajiya.
Shi kuma yakoma wajan Tibishi yana fada mishi"abinda nake so dakai mudaina had'iwa a cikkn gari,ni idan inada buk'atar ganinka zan biyo ka har D'One.Yamishi wani malalacin kallo cikin fesar da hayak'in maro (wiwi) tabaki ta hanci "saboda wata Sudaida?To in tamabaye ka mana "haka zaka aure ta bata san kome a tare da kai ba sai halin waliyai?Ranar da duk tagano kana kanaga zata zauna dakai cikin aminci da amana? Yatareshi cikin hayaniya"kar kamin sanadin 6acin rai da sanyin safiyar nan dan zan gwada maka rashin mutum ci dan abu kazan uban ka,kafin Sudaida tasan kome ai na daina.Tibishi yagyad'a kai "wannan shine tazo muji ta tawuce ta bayan kunne.Yanuna shi da yatsa"indai muna tare da Sudaida to karka kuskura ka doshi wajan.Angama ranka yadad'e yajuya yayi tafiyar shi yana ma Sinan dariyar rainin wayo.
Kafin tayi wani yunk'urin tashi dan ta jiyo muryar shi,har sun shigo D'akin-shak'awar. Musaddiq yakalle ta"d'auko kayan da Baba yabaki kiba Julaibib tamik'e "to. Musaddiq yamik'a mishi hannu sukayi musafaha"to ALLAH yatsare hanya shi Musaddiq a Kaduna yake bautar k'asa yanzu zai koma.Yazauna zaman jiran ta sama da dak'ik'u talatin bata kawo mishi ba ya kira wayar ta ta k'i d'agawa,sai yamik'e zuwa tsakar gidan ana yasame ta sunata hirar su dasu A'isha.
Ke ina kayan ne? Tayi kamar bata ji ba. Khausar tabita da kallo tabbass wani abu ya samu k'wak'walwar Sudaida a yan kwanakin nan, d'azu ma haka sukayi da Yaya Aminu yace ta dama mishi custard;ta tafi d'aki tayi kwanciyar ta shima dagaji da jira yabiyo ta yana tambaya sai tace"Oh Yaya Aminu yi hak'uri na d'an mantane, barin je in dama maka.Yakalli agogo yagirgiza kai"idan natsaya gaskiya zan makara.Yad'aga mata hannu sai na dawo ko? Wallahi da sarki zalimu Yaya Adnan tama haka aida ta kwashi kashin ta a hannu.
Ke Sudaida!
Tamishi wani kallo bata amsa ba "d'auko min kayan mana sauri nake yi"Oh ga su can a kusa da d'akin Yaya Adnan.Yagyad'a kai "Khausar kawo min mota yajuya yana amsa kiran waya...tabi bayan shi da kallo tana wata kissima a zuci tad'anja tsaki tashige d'akinsu,tad'aga labulan taga yana jingine da motar shi har lokacin wayar yake yi,tad'an cije lebanta na k'asa sannan tasaki labulan takwanta a gado...
Ruwa da dorina da kada shigar shi sai dai Kwarawan asali.
24 Jumaada Awwal 1441
19 January 2020
We Ibrahim's Daughters👇
Asdilat KD...2geda with Ra'ibs.
DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION
{Da Inganci Mukayi Fintinkau}
Bismillahi wabihi nasta'in.
...GWAJIN DAFI💔
Almost true story
Daga alk'alamin🖊
Ya'yan Ibrahim
Saudat A.Baba (Asdilat KD)
Da
Bara'atu Ibrahim (Ra'ibs)
Shafi nagoma sha shida.
Yafito daga mota yana kallan ta, tana sanye da shadda me maik'o ruwan makuba tayi kyau sosai a cikin yammacin"Bilkisu Megadon zinare...zinariya kike kinfi azurfa,na rasa yadda zanyi in fasalta miki irin kyan da kike k'arayi amaryar D'ansarai.Tasunkwui da kai ganin wani irin kallo dayake mata,abinda yake so tattausan jajayan labbanta kamar ta turasu da jan jambaki "wai yau saura kwana nawa yarage muzama abu d'aya?Tagirgiza kai"nima ban sani ba,dan bana lissafi.Sai yakama kai"Innalillahi Megado bakya lissafi?Lallai baki damu dani kamar yadda nadamu dake ba.Tayi murmushi me sauti, kumatunta suka lotsa"ai ba anan take ba Julaibib, abari agani mana an ba bature 'yar bak'ar fata. Yagyad'a kai"kema kince wani abu,ALLAH yabamu rai da lafiya yanuna mana lokacin.
Sudaida takalleshi"Sinan jiya inata d'aga maka hannu.Fargaba taka ma shi, da d'an rawar murya yace"jiya da yaushe?Tayi shiru cikin nazarin shi kamar ya shiga rud'u"jiya da yamma, lafiya kuwa?Yasa hannu yashare zufan daya tsatstsafo mishi a goshi"jiya ya yi kato6ara amma da rana abin yafaru.Yad'anyi murmushi"a ah ba kome, kiyi hak'uri ban ganki bane. Nima ai na san da ka ganni baza ka shareni ba.
Tibishi aka sauke akan mashin yak'araso wajan cikin tam6ele da sambatun da kamru uwar laifi take haifarwa,yamik'ama Sinan hannu"sai ka bani kud'in da zan sallami me mashin ko?Dasauri yaciro yabashi; yajuya cikin irin tafiyar bugaggun mashaya"ka rufa ma kanka asiri da wallahi yau allura sai ta tono garma,banza kawai,wawa.Suka bishi da kallo Sudaida toshe da hanci saboda wari da hamamin daya cika wajan,ta tsirtar da miyau"kai ALLAH ya sauwak'e...ya amsa da amin.Ya bud'e baki zai mata magana sai ga Tibishi yasake dunfaro su"kai d'an iska kura da fatar akuya.Sinan yamik'e da sauri"Sudaida shiga gida kawai anjima zan dawo,tajuya da sauri dan cikinta ya fara hautsinewa saboda warin Tibishi. Yaja shi suka bar k'ofar gidan.
Danbarwa sosai sukayi da Tibishi bayan mayen uwar laifin ta sakeshi"Yahankad'e shi yafad'i tabaya,Sinan yafara nuna shi da yatsa"kar ka sake biyoni wajan Sudaida.Yamishi wani kallo"ALLAH ko?Na Sudaida ba da kanka asare idan kaje gida kace ya fad'i,haka kirarin na ku na hausawa yake ko?Eh hakane saura na Katafawa,yayi dariyar tura haushi"ai sama-sama kake jin yaran Kataf dan haka kona maka ba zaka fahimta ba,yamik'e yana kakka6e bayan wandan shi"ajuri zuwa rafi...wannan ma karin maganar ku ta hausawa ce ko?Sinan yakai mishi naushi cikin tafasar zuciya,shima da zafin nama yakauce yana fad'in"yau dai baka san gani na,to gwamma cikin girma da arziki in san inda dare yamin,yad'aga hannu yana mishi adabo sai mun had'u a D'One.
Aminu yana aikin sticker na wani biki da aka bashi kwangila,Sudaida tashiga da sallama, yace yauwa dama ina neman d'an tayan aiki na leka d'akin ku banga kowa ba,tazauna tana tayashi suna hira har suka gama,sannan ta tambaye shi abinda take so ta tambayar shi "Yaya Aminu Sinan baya shaye-shaye kuwa? Yamata kallan nazari"me yasa kikayi wannan tambayar Sudaida?Saboda duk abokan dayake mu'amala dasu yan maro ne (wiwi)Tibishi kuma bayan maro har uwar laifi yana korawa,idan hali bai zo d'aya ba anya za'ayi abota?Ni kwanaki ya min bayani amma danayi d'an nazari sai nake ganin kamar akwai lauje cikin nad'i.
Gaskiya a iya sani na dashi baya shan kome,to amma kinzo da magana abar dubawa,kibar kome a hannuna,zan bincika koma menene zamu gano Insha-ALLAH,yad'an d'age mata gira"kinga ne ko?Tayi yar dariya na gane, ALLAH yabarka da Siddika.Tazama sarauniyar Aminu kamar yadda kika zama sarauniyar Sinan ko?Sukayi dariya.Tana jin k'aunar Aminu fiye da duk sauran Yayyin su saboda sauk'in kan shi,yana jan su ajiki kamar ba babba ba,wasu lukutan har wajan budurwar shi Siddika tana raka shi hira,ko kuma yaba ta abu takai mata,shi Yaya Adnan shine me irin halin Umma baya san raini ko kad'an,da shine babban gidan nan ai da sun gama kad'ewa har ganyan su dan har yafi Yaya Musaddiq za fi.
'Yan lek'en asiri yasa amma basu gano mishi kome game da abotar Tibishi da Sinan ba.Yakalleta da kulawa,sun dai tabbar suna tare kuma sauran suna shaye-shayensu amma ko karan taba su dai da idanun su basu ga Sinan dashi ba,dan haka shawarar da zan ba ki tunda kin yadda dashi a matsayin mijin da za ki aura to karki tsananta binciken shi, babu wanda za'a tsananta ma bincike face sai an kama shi da laifi,su Baba sun amince dashi,kuma basuyi hakan ba sai da sukayi bincike,na kuma tabbatar da yana da babbar illar da zata shafi zaman takewar auran ku to baza su yadda dashi amatsayin surikiba,kiyita addu'a kina kuma nusarshe shi illar zama da irin wad'annan mutanan.To Yaya Aminu nagode. ALLAH yaba ka Siddika.Yayi murmushi.
Tana gidan Hajiya taji sallamar Julaibib.Yanad'e hannayen shi ak'irji yana kallan ta"kina kwance anan gashi can anata karatu a makaranta.Tad'an harare shi"uh na gajine yau da gobe ai sai ALLAH,dan dai rana d'aya mutum ya huta sai afara binshi da k'orafi? Yatsuguna yana duba wasu tsofaffin littafai adirowan Hajiya"hutun jaki da kaya aka ba.Tad'auki man zafi asaman kujerar"kai baka san k'afafuna ciwo suke yiba "me zai hana su ciwo tunda jiya kinsha rawar samba" daga baya suka jiyo muryar shi, Musaddiq ne.
Yagalla mata harara,sai ta sunkwui da kai"tashi ki wuce makaranta, tamarairaice"dan ALLAH Yaya Musaddiq...yatari numfashin ta shhh...yad'ora yatsan shi abaki,in dai ba so kike yi ki kwashi kashin ki a hannu ba to tashi kawai "tafara matso kwalla aranta tana addu'ar ALLAH yakawo Hajiya ita kad'aice zata ta ka mishi burki,itama d'in idan ta ga dama.Julaibib yasa musu baki"amata hak'uri mana tunda tana da lalura"wa zan ma hak'urin?Wannan yarinyar? Yanuna ta da yatsa"ai da lalurar arzikice da har pain-relief zan k'arama ta dashi,ai ka san jiya anyi Inter-School a Saint-Francis College to nan suka tafi tun safe har biyar da rabi ba makarantar da suka je ta allo data Islamiyya,ashe yauma basuje ba da safe suka kwanta bacci wai sun gaji,to d'azu ina gidan Umma takorasu kasan sun maida Mama kamar sa'ar wasan su koda tayi magana basu jiba,to su sauran sunji maganar Umma sun tafi ta yamma sai ita shafaffiya da mai tazo nan tayi kwanciyarta?Tafara kuka"ni dai ALLAH yanaji yana kuma gani banyi rawar samba ba.Yakalleta cikin fushi" karya zan miki ko?Me zai za k'afufunki suyi ciwo bayan wasan discuss kike yi indai ba rawan kika yiba?
Hajiya tashigo"yayane Sudaida kike kuka kuma?Musaddiq yayi kwafa"kyale ni da ita kawai Hajiya samun waje ne kuturu da gad'a a rama.Julaibib yadafa kafad'arshi"ka kyaleta mana wata kila bayan ciwon k'afafun akwai hujjar datasa tak'i zuwa,ka san hali da dabi'ar mata Iyayanmu, yan'uwanmu,k'anninmu sai hak'uri, sai ana kawar dakai awasu lokutan idan ba haka ba,sai su maida kai wani iri,yazame hannun Julaibib daga kafad'ar shi, yajuya yayi tafiyar shi;tasauke numfashi sai a lokacin tashak'i iskar yanci"kai Yaya Musaadiq barkono ne,yanzu haka yakema Safiyya wannan halin?Hajiya tace"barin kira miki shi yaba ki amsa dan wak'a abakin me ita ta fi dad'i.Takama ha6a"wuuu...Tabbb Hajiya rufa min asiri kar k'ilu taja bauuu...
Ya tashi sahur azumin nafila na ranar alhamis yana juya zuman dayasa a shayin na'a na'a da 'ya'yan algarib yayi tsai...cikin tunano mafarkin dayayi da daddare...
"Kasham yake gani da kayan fulani tayi kyau k'irar kalangunta ya fito rad'am,amma idan tayi magana muryar Sudaida yake ji.
Shekarun baya yayi wannan mafarkin to yanzu ma mafarkin ya dawo shi ya rasa gane kan wannan mafarkin.Yayi bismillah yafara kur6a amma ko kwata bai sha ba kome ya gundire shi,shayin yamishi wani irin d'and'ano mara dad'i,ya ajiye kofin a saman tebur.Yad'auki farar hular zita yasa yad'auki Alqur'ani me girma yana karantawa har aka kira assalatu daga mabambantan masallatai na unguwar,yayi raka'atal fajri sannan yafito suka tafi masallaci shi da Baba.
Tana fitowa daga asibiti motar shi tana tsayawa,yabita da kallo tayi kyau a cikin fararan kayan riga da wando da d'an madaidaicin farin hijab,suka kalli juna sai yamik'a mata hannu ta san me yake so dan haka tamik'a mishi ragowan Schweppes d'in da yake hannun ta"ya ajiye a mota dashi zan yi bud'a baki "Megado kinga kyan da kike k'arawa kuwa tun bamu fara cin Shahrul-Asal (Honey Moon) ba?Ya d'aga kai sama alamar tunani"Bilkisu k'wak'walwata 6angaren nazari da tunani ta gaza gano yadda zan fasalta irin kyan da kike tayi,wai meye sirrin ne?Yazubama tattausan jajayan la66anta idanu;tayi dariyar da tun had'uwar su bata ta6a irinta agabanshi ba, kumatunta suka lotsa ciki sosai yar siririyar wushiryar ta,ta dad'a k'awata fuskar ta,Ya ilahi... shi da kanshi ya kauda kai yana jin wani irin yanayi a ilahirin gangar jiki da sararin zuciyar shi game da ita.
Wai kai kwana biyun nan me yake damun kane sai kadinga wasu maganganu kamar lokacin kafara gani na?Yamata wani kallo"yunwar so ke damun zuciya ta. Matsirga zan tafi,takawar da wannan maganar.Yakalleta cikin makaki"wani irin Matsirga kuma da safen nan?Haba kibari kid'an samu bacci koda awa uku ne,kinga aikin dare kika yi na san baki yi bacci ba,idan kika d'an huta bayan azahar ba sai ki tafi ba?"ni dai dan ALLAH yanzu nake san tafiya kar inyi hutun jaki da kaya aka,agida sai in huta gaba d'aya.A ah Megado ban yadda ba,ba ranar lahadi da yamma kika dawo daga Matsirgan ba?Tagyad'a kai"Inna nake san gani, tayi yar dariya"wallahi gobe da safe zan dawo Insha-ALLAH.Ba ga waya ba kikara ta mana.Tad'an marairaice"ni dai nafi so inganta ganin idanu na.Yad'an harareta"shikenan tunda kin na ce sai kin tafi to muje in kaiki,idan muka kwana sai mubugo sammako da sassafe dan nima Zari'a zani a goben.
Tad'an bud'e idanu dan mamaki"ka kwana a ina?Bai bata amsa ba yashiga mota yazauna sannan yakalle ta"shigo mutafi mun... kiran wayar Baba takatse shi yad'aga da sallama "kazo yanzu na yi baki suna jiran ka a shago.Ya amsa cikin ladabi"to Baba gani nan zuwa.Yad'anyi jimmm...D'ansarai lafiya kuwa?Kiyi hak'uri Megado na so kwarai mutafi tare to sai dai hak'ata bata tadda ruwa ba,akwai bak'in da suke jirana a shago.A ah ba kome" tashiga ta zauna yaja motar.
Tasha yakaita yasata a motar haya, gidan gaba yabiya kud'in mutum biyun dan ta zauna ba takura,suna ta hirarsu yana fad'a mata wasu kalamai masu nauyi,tad'an harareshi sannan ta sunkwui da kai "ka san ALLAH idan baka daina fad'a min wad'annan kalaman ba zan daina sauraranka,kuma ko waya ka kira bazan d'aga ba, yayi yar dariya"ni kuma ban san inda kike bako? kaji yar rainin hankali kamar wata k'aramar yarinya, ba aikin asibiti kikeyi ba? Wancan makon ba d'akin yan hatsari kuma maza aka kaiku ku musu dressing ba?Wani dare ne jemage bai gani ba?
Tasa hannun damar ta tashafa dogon karan hancin ta,tayi kamar bata gane me yake nufi ba.Akwai dararan da jemage bai gani ba fa.To wani dare ne kuwa?Shima yatambaye ta. Tamishi wani kallo daya sa zuciyar shi bugawa Dammm...bai kuma san dalili ba.Daren da aka haife shi da daran mutuwar shi ko ya gani? Yagirgiza kai.Kiran Adnan yashigo wayar shi, yad'aga da sallama.Adnan ya amsa sannan ya tambaye shi"kana ina ne D'ansaarai?Ina tashar mota.Tashar mota kuma?Me kakeyi a tasha? Bilkisu zan sa a motar Matsirga.Tam dama Hajiya zan kai unguwa Yaya Aminu yafita da motar gida. Shikenan zo ka kar6i mukullin.Suka cigaba da hirar su har Adnan d'in yak'araso suka gaisa da Bilkisu a mutunce yakar6i mukullin motar yatafi.
Shafff...ya manta da kiran Baba sai da kiran shi yasake shigowa sannan ya tuna"Baba ayi hak'uri gani nan zuwa"yamayar da wayar aljihu "Bilkisu barin je in dawo.Takalleshi cikin natsuwa "bak'i fa kukayi kafin kugama abinda za kuyi ka dawo ai na tsufa a gida,sai dai munyi waya. Yagyad'a kai"shike nan nagode ALLAH yamiki albarka.Amin.
"Sai munyi waya...suka fad'a atare.
Sannan suka kalli juna sukayi murmushi yad'aga hannu yana mata adabo yajuya da d'an sauri dan kar Baba yasake kiran shi,tabi bayan shi da kallo har ya tsallaka titi ya6ace ma ganinta,tamaida kanta jikin kujera tana sake kiran lambar Inna dan ta kira sau shurin masak'i amma bata shigaba,saboda matsalar na'urar sadarwa. Motar su ta cika suna shirin tashi ta tura ma Julaibib sak'on murya(voice note).
"Julaibib yanzu motar mu ta tashi... Ina sauka kai zan fara kira,ta mishi sautin sumba muahhh... 💋"
Abinda yaketa rok'on ta ayan kwanakin nan tamishi kenan,amma k'ememe tace wai ita bata iya ba,rannan data bashi haushi yace"kar ALLAH yasa ki iya d'in za ki zo hannu duk sai kin biyani bashi dalla-dalla.
Yadawo daga sallar azahar zai shiga d'aki kiran Bilkisu yashigo,yayi murmushi "haba Nurse Megado ko dak'ik'u talatin bakuyi da tashi bare kice har kin sauka, yad'aga da sallama "hayaniya da kururuwane ya cika kunnuwan shi "Bilkisu lafiya kuwa?Wata murya ta amsa"ba Bilkisu bace kazo Wadom yanzu-yanzu sunyi hatsari ne"Innalillahi Wa'inna'ilahi raji'un" Istirja'in shi Inna taji fito daga D'akin-girki da sauri. Yajingina kanshi da bango jikin shi a sanyaye "lafiya kuwa D'ansarai? Sai ga Musaddiq ya shigo duk suka zuba mishi idanu su. Musaddiq yace"me yafarune?Inna tawatsa hannu"abinda nake tambayar shi kenan kashigo.Yadafa kafad'arshi"yi magana mana Julaibaib..."Megado ce sukayi hatsari.Inna da Musaddiq suka yi Istirja'i suma, yaja hannunshi"to tsayuwar me muke yi?Inna sai mun dawo.Tabisu har zaure bakin ta d'auke da addu'ar Ubangiji yatsare musu hanya.
Gudu sosai Musaddiq yayi.Wajan ya cika dank'am da mutane da jerin motoci,wani hukuncin Ubangiji kuma daga Bikkisu sai wani dake gidan baya sune sukaji mummunan ciwuka, sauran dai k'uk'k'urjewa kawai sukayi, shi dama d'an Wadom d'in ne yan'uwan shi sun zo sun d'auke shi zuwa asibiti.
Ruguzowar wani abu yaji a k'ahon zuciyar shi lokacin daya ga Bilkisu a kwance sambal cikin jini fuj'atan, zuciyar shi tafara wata irin bugawa da k'arfin gaske kanshi yasara, yahad'iye wani abu me zafi,yasa hannayenshi biyu ya cicci6eta zai sa a mota sai kawai wajan ya kaure da salati, masu ihu na yi,masu fad'in Jesus Christ,Holy Mary nayi,masu d'ora hannaye aka suna sambatu da yarukan su na yi, bai fahimci kome ba sai da yaga Musaddiq ya d'auki farin hijab d'inta da yarine da jini ya koma ja,yad'aure mata kai,ashe kan tsagewa yayi ana hango ciki, yashimfid'eta a bayan mota.
Jama'ar wajan na musu fatan su sauka lafiya, ita kuma ALLAH yata shi kafad'a yasa kaffarace.Shi kanshi Musaddiq ta maza yayi yake tuk'in saboda ya shiga rud'u da damuwa,a haka har suka koma Zonkwa.
"Saint Louis Hospital 6angaren hatsari da taimakon agaji na gaggawa(Accident and Emergency) aka wuce da ita,Julaibib ya kasa zaune ya kasa tsaye sai kai-kawo yake yi a barandar wajan.Musaddiq yarik'o hannun shi suka zauna"kayi hak'uri Julaibib na kira Malam Lamid'o a waya yanzu haka suna hanya.
Suna zaune jingum-jingum har su Baba da Malam Lamid'o da Yayyin Bilkisu Maude da Tukur sukazo, zaman awanni biyu sannan zugan likitocin da ma'aikatan jinya suka fito daga d'akin.Gaba d'aya suma suka mik'e kowanne hankali a tashe,Babban likitan yace ku biyoni office.
Cikin natsuwa yad'ago yana kallansu bayan ya gama yan rubuce-rubucen shi a wani fallan takadda me sunan asibitin"kuyi hak'uri Insha-ALLAH kome zai zo da sauk'i,yanzu dai mun bata taimakon gaggawa wanda za mu iya amma gaskiya abin ya fi k'arfin mu dan ya shafi k'wak'walwarta sai dai kuwuce da ita Shika, Ahmadu Bello Teaching Hospital Ubangiji yaba ta lafiya,yanad'e takaddan yamik'a ma Malam Lamid'o"Idan kunje ku ne mi...
"Doctor Garga Ibrahim Manogi...
Maude yagyad'a kai"Alhamdulilahi Doctor Manogi k'wararren ne akan abinda yashafi k'wak'walwa (Neurology) kuma k'anwar Innar su yake aure, dan haka fad'uwa ce tazo dai-dai da zama.Suka koma d'akin da Bilkisi take kwance, jikinsu yayi mugun sanyi,wallahi mutum ba a bakin kome yake ba, Ubangiji kamana kyakkyawan k'arshe👏Tukur yace muna 6ata lokaci ai gwamma muyi harama.
Malam Lamid'o da Tukur agaban motar sai Julaibib da Bilkisu a baya,su Baba dasu Musaddiq suka lek'o to Ubangiji yakaiku lafiya. Maude yace gobe sammako za muyi da Inna, Malam Lamid'o yagyad'a ka.Tukur yaja motar, suka bisu da kallo har suka fita daga asibitin suka hau kwalta.
Julaibib yazuba mata idanu zuciyar shi na bugawa da k'arfin gaske d'ik d'ik d'ikkk...wuyan ta ya karye an sa mata stiffness collar,kanta yana cinyar shi har lokacin jini bai daina zuba ba,bandejin da aka nannad'e kanta dashi saura kad'an yajik'e,hannunta nadama akwai karaya guda biyu,idonta na dama ya zurma ciki sosai alamar ya fashe ruwan ciki ya gama tsiyayewa,idonta na hagu kuma ya kumbura suntum har wani kyalli yakeyi,gaba d'aya kamanninta ya canja saboda kumburin da fuskarta tayi. Idanun shi sun kad'a jawur kanshi yana wani irin sara mishi,yakad'a kai cikin maimaita Istirja'i yana tallafe da kanta... motar tsittt kowa da yadda abin yadake shi,wucewar wasu dak'ik'u hannun hagunta da yarik'e yaji ya saki tayi wata ajiyar zuciya Dammm...zuciyar shi tabuga!Yasake zuba mata idanu yana ta6a wuyan ta,harbawan da yake yi ya tsaya cakkk...Tukur yana kalkanshi ta madubi a hankali yagangara gefen titi yatsaya.Malam Lamid'o tun shigar shi motar kanshi ak'asa yad'ago"Tukur lafiya?duk suka juya baya,Tukur yabud'e motar yakoma baya yana tatta6a ta,da rawar murya yace"Malam kamar fa bata numfashi.Sukayi shiru nawasu yan dak'ik'u.Malam Lamid'o ya tabbatar Bilkisu ta mutu!
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un!...KULLU NAFSIN ZAA'IK'ATIL MAUT!kowace rai sai ta d'and'ani mutuwa😭Ubangiji mun tuba,dama kowane d'an Adam me kuskure ne,sai dai mafi kyawun masu kuskure sune masu tuba.Ubangijin mu kamana gam da katar da kyakkyawan k'arshe,mu mutu cikin da'a da dokokin ka😭👏...
"Julaibib yace Malam Bilkisu fa bata mutu ba,dogon suma tayi.Tukur ma yagyad'a kai"nima haka nake tunani yakoma gidan gaba yazauna yana k'ok'arin tayar da motar"Malam inaga jinin da take ta zubarwa ne yahaifar da haka.Juya da motar nan mukoma gida a mata wanka akaita d'akin ta na gaskiya Ubangiji yasa k'arshen wahalar kenan Bilkisu,kwallah suka cika idanun shi,yasa gefen babbar rigar shi yagoge. Julaibib da Tukur sukace "a ah Malam Bikkisu bata mutu ba,Insha-ALLAH kuma za ta warke. Malam Lamid'o yadafa kafad'ar Julaibib"kar muyi haka daku mana, ni tunda naga Bilkisu dama na san indai ba wani hukunci na Ubangiji ba to baza ta rayu ba,idan ma ta rayu to za ta samu tasgaro me yawa arayuwar ta,kuyi hak'uri Bikkisu ta riga ta tafi ni naga mutuwa ba d'aya ba ba biyu ba.
A asibiti ma likita yabasu tabbacin ta rasu,dukkansu hawayene yake zubo musu sharrr... sharrr... Wayyo ALLAH!Duniya gidan ci rani,duniya gidan azo a wuce! kowa sai ya koma gidan shi na asali (Lahira)
Gidansu Julaibib suka wuce da gawar Bilkisu dan Malam Lamid'o ya ce ba sai sun tafi Matsirga ba,duk inda musulmi yamutu ai za a iya yi mishi wanka a mishi sallah akwaishi makwancin shi.
Inna da Musaddiq da Hajiya suna zaune cikin jimami sai ga Julaibib yashigo cikin tashin hankali "Lafiya kuwa Hajiya ta tare shi,me yadawo da kai? Ya zauna a kujera idanun shi sun kad'a jawur,wata jijiya ta fito rad'am a gefen goshin shi kamar shatin bulala, yabisu da kallo sai kuma yamik'e, jikinsu ya basu dan haka cikin zafin nama Musaddiq yarik'o shi"Hajiya tace kayi hak'uri... mutuwa ba ta jira ALLAH baya barin wani dan wani, ALLAH shi yayi Bilkisu, dama aran ta aka ba mu,to lokacin tafiyarta ta yi dan haka bamu isa mu hana ba,suka cigaba da rarrashin shi da kalamai masu taushi,Musaddiq yafita wajan su Malam Lamid'o dan har an shiga da ita D'akin-shak'atawar Inna.
Maude ne yazo da Inna,tana ganin ta a kwance sambal fararan kayan aikinta sun rine da jini sun koma kalar ja,tayi fari fattt...ta d'ashe alamar babu sauran jini ajikinta.Inna ta zuba mata idanu cikin hawaye"Bilkisu ke ce kika zama haka? takad'a kai cikin sarewa da al'amarin rayuwa, kamanninta sun canja ta zama wata irin halitta,a fuskarta ba irin halittar d'an Adam ba amma wai hukuncin Ubangiji sauran gangar jikin ta lafiya lau ko k'warzone ba bu na ciwo,in banda hannun damar ta "Bilkisu kece mace d'aya acikin 'ya'yana na so ganin auran ki sai dai kash... Kana na ka ALLAH na na shi kuma na ALLAH shine dai-dai,ALLAH yamiki rahama yasa k'arshen wahalar kenan,Bilkisu kin dace Insha-ALLAH dan kin mutu a d'aya daga cikin ranakun da babu tambayar kabari akan mamaci,kin mutu ranar alhamis, tasa hannu tashare hawaya ta fuskanci su Innan Julaibib "mu mata abinda aka fiso ama mamaci da gaggawa,su uku suka mata wanka suka samata likkafani suka sata a makara Innan tad'auko fallan zani aka lullu6eta,Maude da Julaibib suka fita da ita aka mata sallah sai makabarta! Sun dad'e suna ne ma mata gafara musamman mahaifinta da masoyin ta Julaibib da Yayyinta su Maude da sauran yan'uwa da abokan arziki.
"YA ALLAH!KA GAFARTA MATA!YA ALLAH KABA TA TABBATA!
Suka juya zuwa cikin gari jikinsu a sanyaye,zuciyoyin su cike da alhini da d'acin mutuwa.
Malama Lamid'o da iyalinshi suka fito za su tafi.Julaibib yana tsugune a gabansu ya sunkwui da kai,kukan shar6e yake yi hawayen suna ambaliya a fuskar shi, ganin haka yasa Tukur yarik'o hannun Inna da take matsar kwallah zuwa mota"Inna zauna.Cikin dauriya Malam Lamid'o shima yatsuguna yadafa kafad'arshi"kayi hak'uri Julaibib hak'ik'a wannan mutuwar babu wanda ta dake su kamarmu iyayanta da kai,to duk mu d'auki hak'uri kowa zaman jiranta yake yi,tabbasss da ina da wata 'yar bayan Bilkisu to dana ba ka, amma zan cigaba da maka addu'a"ALLAH yaba ka wacce tafi Bilkisu,yayita rarrashin shi sannan sukayi sallama dasu Baba.Tukur yaja mota suka tafi. Julaibib yabi bayan motar da kallo har tasha kwana ta6ace ma ganin shi sharrr...sharrr...wasu zafafan hawaye suka zubo mishi. Yakad'a kai cikin maimaita Istirja'i.
Bayan sallar magriba Inna ta kawo mishi kunun tsamiya da kosai.Julaibib daga dawowa daga masallaci sai kuma ka kwanta? Tashi kayi bud'a baki mana.Yamik'e zaune dak'yar dan kanshi na wani sarawa "Inna bana jin yunwa cikina ya cunkushe kamar na ci abinci"Tajijjiga kai"na sani D'ansarai to amma dai ai ka san an umarce mu da gaggauta bud'a baki,azumi fa kayi daure kaci dabino kaji... yakar6i guda d'aya haka dai yaci amma wallahi baiji d'and'anon shi ba dakyar ya had'iye.
Malam Abdullahi yashigo shima yazauna yadafa kafad'ar shi"Malam D'ansarai ai wannan lokacin yana d'aya daga cikin lokutan amsa addu'a,to ba sai kayi amfani da wannan damar wajan rok'ama Magado gafara dama kai kanka ba?Duk da yana cikin damuwa amma sai da yad'anyi yake ganin yadda suke ta rarrashin shi Inna wai ita sai ta bashi kunnun ma abaki wallahi kuma yau a d'akin baccin ta za su kwana tare "Karki damu Inna zan sha amma sai zuwa anjima kin san ba sosai nake cin abinci daga shan ruwa ba.Eh haka ne ,tamik'e ta barshi da Baba.
Washe gari su Julaibib da iyayan su motoci guda uku sukayi dan zuwa Matsirga ta'aziyya sun tafi da manyan kololin shake tam da abinci ,kullum sai sunje har sai da akayi addu'ar uku.
Yana rik'e da agogon da aka cire a hannun Bilkisu lokacin da za'a mata wanka sai jujjuya shi yakeyi,tunaninta da irin hirarra kinsu ya cika k'wak'walwar shi"Bilkisu a very meek damsel ta tafi ta barshi,burin su na zama ma'aurata bai cika ba.
"Sai na kira...
kalmar da suka fad'a ma juna ta k'arshe shi da ita kenan,sai sak'on muryar data turo mishi,yasake kunna sak'on muryar yana sauraro a karo na barkatai sau shurin masaki,ya kad'a kai"uh uhun mutuwa rigar kowa...
Sudaida tashigo tana kallanshi cikin zancen zuci"shi ko wani irin so yakema wannan Bilkisun?Kullum taganshi sai taga ya dad'a ramewa,tausayinshi yamamayeta dan ba ta jin dadin ganin shi a haka,itama tayi nadamar abinda tadinga ma Bilkisu wanda ita Bilkisun ko a fuska bata ta6a nuna ta ji haushi ba"Yaya Julaibib dan Allah kayi hak'uri,kaga yadda kake ta ramewa? Yad'an kalleta"to nagode.Ta ajiye rediyon tafita. Inna tafio daga D'akin-girki tana kallanta tana sa takalmi"ba dai tafiya za kiyi ba?Tafiya zan yi Inna dan zanyi rubutun allo yau akwai darasu,amma idan nagama zan dawo in sha fate na.To shikenan, ALLAH yamuku albarka"Amin Innarmu.
Malam Lamid'o yana zaune a d'akin zaure yajiyo sallamar Julaibib.Yafito da sauri kaine haka?To maraba yashiga suka gaisa.Malam Lamid'o yace ikon ALLAH dama Tukur nake jira yadawo anjima za muzo wajan na ku.Ya amsa cikin girmamawa"Malam shi yasa ma nazo dan Baba yafad'a min yadda kukayi ta waya"Indai za kuzo ne dan kawo wani abu game da kayan auran Megado to kubari.
Malam Lamid'o yagirgiza kai"sam-sam baza ayi haka ba.Ya amsa cikin ladabi"wallahi Malam kome da aka kawo saboda Bilkisu na bar muku har abadan duniya arabama yan'uwa da abokan arziki bazan kar6a ba.Malam Lamid'o yayi shiru cikin jinjina wannan al'amari,sai kawai yad'auki wayar shi yakira Alhaji Abdullahi yafad'a mishi abinda Julaibib yace"Baba yayi murmushi "haba Malam dan D'ansarai ya ce haka har sai ka kira?Tunda yace ya bari to ya bari d'in ne,kutaya mu addu'a kawai Allah yabashi macen alheri.Ya ajiye wayar cikin sanyin jiki.Karka damu Malam Julaibib yafad'a."Julaibib ALLAH yamaka albarka,ALLAH yasa kagama da duniya lafiya, ALLAH yaba ka wacce tafi Bilkisu.
Yamishi jagora zuwa cikin gidan. Innan Bilkisu tana ganin shi tafara kuka,ya sunkwui da kai cikin wani irin yanayi,ga tausayin ganin yadda Innar Bilkisu ta zabge,tayi bak'i, idanun ta sun k'ank'ance saboda yawan kuka"Inna kiyi hak'uri Bikkisu ba kuka take buk'ata a wajan muba,addu'a tafi buk'ata.Inna takad'a kai cikin hawaye "kaiya d'an nan ba kukan rabuwa da Bilkisu nake yi har yanzu ba,ina kuka ne saboda wata rana za a manta da Bilkisu wajan yi mata addu'a kaasatan(a ke6e) saboda bata bar baya ba,dama Ya'ya sune duk rintsi baza su gaji dama mahaifa addu'a ba,har sai ranar da suma suka koma ga Ubangiji.Yajijjiga kai haka ne,to amma Inna ya zamuyi da hukuncin Ubanguji?ALLAH bai k'addari za tayi aure ba, bare har ta haifi Ya'ya,Inna duk hukuncin Ubangiji akan bawan shi adalcine,duk da bata haihu ba to ai akwai sadakatul-jariya,sadaka me gudana kamar mutum yana raye adoron duniya ni zan je cikin k'auye inda duke wuyar ruwa zan gina mata rijiya...Malam Lamid'o yatari numfashin shi"a ah basai ka sake kashe kud'in kaba kabari kawai tunda kabar mana kome to zan gina mata da kud'in sadakinta...Inna tafashe da kuka ALLAH yabaka wacce tafi Bilkisu d'an nan, hakika kai masoyin Bilkisu na gaskene dan ka nuna mana haka duk da bata cikin doron duniya.
Idanun shi suka kad'a jawur"ni gobe zan koma wajan bautar k'asa dama sallama nazo muyi sai an kwana biyu,suna sallama Bello yashigo da gudu yana haki yana dariya"Yaya D'ansarai ina dabinon ajwa na da inibi na?Suka zuba mishi idanu ba abinda yadame shi sai tsallan shi yakeyi"k'uruci dangin hauka.Yamik'a mishi ledar daya shigo da ita a hannunshi.Yakar6a cikin tsallan murna"Yaya D'ansarai nagode ya k'ank'ame ledar akirjin shi"to yaushe zaka dawo? Yakalleshi da kulawa"zan dad'e ban dawo ba. Bello yad'an zaro idanu"kaiii kaima irin tafiyar da Adda tayi za kayi?Inna fa tafad'a min wai ita baza ta sake dawo wa ba sai dai muje mu same ta,ni fa shi yasa baza ni ba,kai ai za ka dawo ko?Insha-ALLAH Bello... Idanun Julaibib suka sake kad'awa jawur ya tuno da Bilkisu da take cewa gobe fa zan dawo Insh-ALLAH... Cikin wani irin yanayi suka yi sallama yaja motar shi yatafi,ya dad'e a Water-fall d'in Matsirga yana kallan ruwan yadda yake gudu cikin Qudirar Ubangiji ba dare ba rana shekara aru-aru.
Sagir yafito da gudu yana kiran shi" Yaya Julaibib wai katsaya.Inji wa?Yana hakin gudun da yayi yace"inji Yaya Sudaida.To ya shiga mota ya zauna yad'aura belt,k'afarshi d'aya tana waje.Tak'arsso wajan yana waya,wucewar wasu dak'ik'u sannan yagama wayar ya ajiye a gafenshi sannan yad'an kalleta kince in tsaya me zaki bani? Tabud'e gidan baya ta ajiye mishi wata madaidaiciyar leda ruwan hoda"Donut na maka, tarufe murfin tadawo wajanshi,wallahi tausayi yake ba ta duk yayi sanyi dama shi bame san hayani bane"sai yaushe zaka dawo?Ba rana sai dai kun ganni.Idanun ta suka cika da kwallah"dan ALLAH Yaya D'ansarai ka dinga cin abinci kaga yadda kazama kuwa?Ina cin abinci mana Sudaida ai d'an Adam bazai rayu ba abinci ba.Tad'an marariraice"to amma dai d'an tsakura ka keyi, kadinga ci dayawa,yamaida k'afarshi cikin motar tarufe murfin.Nagode Sudaida.kadinga cin abinci kaji?Tasake fad'a.To ya fad'a a tak'aice. Tasunkuyo"Allah ya kaika lafiya.amin Sudaida yaja motar tabi bayan motar da kallo har yayi nisa ya6ace ma ganinta,wani abu na mata kai-kawo a zuci,tasauke numfashi tabaki ta hanci sannan tajiya zuwa cikin gida ran ta ba dad'i.
A sanda hantsi yadubi ludayi na safiyar alhamis suna cikin hutun makarantar boko na ranar yara(Children's day)kuma yau ba makarantar allo ba Islamiyya kowa yana abinda yake so ne, dan duk sun gama ayyukan gida.Tana kwance ranta ba dad'i tunda Julaibib yatafi sau uku kawai sukayi waya yauma takira shi sama-sama suka gaisa yakatse,tasake kira yad'aga da sallama"Yaya Julaibib na maka laifine? A ah baki min kome ba.To me yasa kike min wani iri? Yad'anyi murmushi"Sudaida kenan ni ban miki wani iri ba fa zan shiga aji ya katse wayar...Tayi lamooo a gadan,tunani barkatai ya cika k'wak'walwarta ta rasa na za6a tayi.
Nasmat suka shigo suna hayaniyarsu kamar yadda suka sa ba,suka kalleta suka kwashe da dariya"Sudaida uwar tafakkuri (tunani)me kuma yafaru?Khausar ta ta6e baki tabud'e wadrobe ta d'auki kayan da zata goge a D'akin-shak'atawa tafita...Bata basu amsar tambayar su ba,takalli Zainab"ya maganar bikin saukar mu?Ta zauna a gefan gadan"ai Malam yayi tafiya sai ranar asabar zai dawo.A'isha tamik'e "barinje muk'arasa kallan mu dan yau bazan dad'e ba,angona Hashim anjima yana hanya.Nasmat tad'an daki kafad'arta"to gaggawa hannu hagu a romo mutumin da ko tasowa bai yiba.suka mik'e ita da Zainab.Nasmat tabi da Sudaida da kallo "dan ALLAH me yake damun kine?Tamaida kanta saman matashi"na fad'a miki ba abinda yake damuna to ki rabu dani mana.Sudaida na damu dake shi yasa nadamu da halin dakike ciki. Tamaida idanun ta tarufe...Nasmat ki kyaleni bana san hayaniya fa.Tamik'e ALLAH yabaki hak'uri, amma ina zargin wani abu koda yake...sai tad'an motsa kafad'a shikenan can da yawarki yarinya.
Sai da aka cinye zangon karatu d'aya sannan Julaibib yazo gida.Yau alhamis ranar da ake bikin saukar Alqur'ani me girma nasu Sudaida,kome an shirya shi cikin mutunci, bangaran maza daban na mata daban Liman yabud'e taran da addu'a yama daliban addu'a Allah yasa suyi amfani da abinda aka koya musu a kowani irin hali da yanayi suka shiga na rayuwa...aka biyama d'aliban allunan su sannan aka cigaba da wa'azi da fad'akarwa akan neman ilmi dan shine yake sanya rayuwa tayi kyau tayi albarka.
Bayan angama kome sannan aka shiga yin hotuna da rabama d'alibai kyaututtuka aka rufe taro da addu'a,Sudaida tasunkwui da kai abinda yaba mak'alallun k'wallan cikin idanun ta damar zubowa k'asa sharrr... wannan taran me tarin albarka mutane da yawa sun halacceshi amma banda Sinan,to me ya hanashi zuwa tunda ya sani?Tayi kwafa wallahi za mu had'u ne.
Tana d'ago kai,caraf idanun su yahad'u, wani sanyi dad'i taji a ilahirin gangar jiki da sararin zuciyar ta. Alk'asim yak'araso wajan "gaskiya yan matan nan kun had'u,zai mik'a ma Sudaida rufaffen envelop A'isha takai hannu za ta kar6e,yajanye hannunshi da sauri"a ah ya haka? Tagyad'a kai"eh haka nake nufi,kai kaga hakan zata sa6u bindiga acikin ruwa? Wasa tare ci bamban?Khausar tace ko muma abamu ko itama tarasa. Yayi yar dariya "mata problem kunga fa ba wani abu bane a ciki,rubutune kawai akayi da biro bulu.Eh koma dai menene to abamu na mu. Nasmat ta katseshi"to wai ma yahaka?Ana zatan wuta a mak'era sai ga ta kuma a masak'a?Wallahi wanda nayi hasashen zai bata kyautar kaasatan bai yiba sai kai?Yamaida envelop d'in aljihu "shikenan karku samu damuwa za kuji a salansa, Sudaida sun hana in baki hannu da hannu zan aiko miki dashi gida,yajuya yayi tafiyarshi bai saurari hayagagar da suke mishi ba.Suka jera suna tafiya zuwa gidan Hajiya"Aisha tace wai me yahana Sinan zuwa wajan saukar mu,naga har Hashim daba d'an gari ba ya zo?Tawatsa hannu"nima ban sani ba amma ina ga kamar ba k'alau ba.
Dayammacin ranar sai ga shi da kaya nik'i-nik'i lemukan gwangawani dana kwali, yana zaune a dakalin k'ofar gidan tafito cikin fushi Sagir na biye da ita da kayan,takar6a ta ajiye mishi "Sinan ba wad'annan nafi buk'ata ba,zuwanka wajan ya fi duk abinda za ka bani. Tajuya...Yasha gabanta da sauri yahad'a tafukan hannayen shi da sigar rarrashi"Sarauniyar Sinan kiyi hak'uri "Tagirgiza kai"ban hak'ura ba sai ka fad'a min abinda yahana ka zuwa.Yad'anyi jimmm... na wucewar wasu dak'ik'u"za ki yadda dani?Tayi shiru sai yacigaba"to ni dai na san na miki laifin da ban ta6a miki irin shi ba,Sudaida baccine yayi awan gaba dani,to ya zanyi?To wayar ka amfanin me takeyi na kira ka sau shurin masak'i baka d'aga ba,sai kace me baccin mutuwa? Yakad'a kai cikin damuwa"lallai na cancanci abani horo,itama fa wayar a yanayin shiru nasa ta,kiyi hak'uri Sudaida "ALLAH yana san masu hak'uri,masu had'iye fushi, suna da dama su rama abinda aka musu amma sai suke hak'ura su yafe,su maida kome ba kome ba saboda ganin girman ALLAH...yacika da dad'ad'an kalamai har sai da yashawo kanta. ALLAH da gaske ke nake so Sudaida alk'awari ba karyawa ni da ke sai mun zama abin kwatance mutu ka raba takalmin kaza. Da haka yaba Sagir kayan yamayar dasu cikin gida..
Kwana biyu da fara azumin watan ramadan yashirya shi da Musaddiq sai Matsirga. Inna tana zaune a d'aki taga ana shigo da kayayyaki tasa hijab tafito tsakar gida tana tambayarsu daga ina wad'annnan kayan? Sai ga Bello yashigo da murnar shi yana fad'a mata su Yaya Julaibib ne.Jikinta yayi sanyi tabi kayayyakin da kallo cikin zancen zuci"wato k'auna ta gaskiya tana d'orewa koda ba wanda ake k'aunar a doron duniya. Bello yarik'o hannunta "Inna na shigo dasu. Tayi murmushi"lale maraba,sannunku da zuwa bismillah tajuya zuwa cikin d'aki suka bita,cikin girmamawa suka gaisheta"Iyayan na ku k'alau ko? A lafiya k'alau Inna suna gaishe ku.To madalla ALLAH yamuku albarka,ku bakwa gajiya da hadima?Musaddiq yace"haba Inna ai bakome... yiwa kaine.To Ubangiji yasa ka muku da mafificin sakamakon shi;ALLAH yasa hakan amizaninku na kyawawan aiyuka. Amin,amin Inna.
Inna su Malam basa nan ne?Eh d'azu shi da Maude suka tafi Zango wajan k'annin mahaifanshi,Tukur kuma jiya yakoma makaranta. Suka d'an ta6a hira sannan suka mata sallama taciko musu jarkoki da kindirmo da manshanu, Bello yasa kuka shi dole sai sun tafi dashi Inna tayi-tayi ya zauna amma ya kafe ya nata ihu shi dai zai bi su,duk yamak'alk'ale Julaibib ya 6ata mishi farar shaddar da yasa da majina da ruwan hawaye,yarik'o hannun shi.
Inna bari muje waje muyi magana tabisu da kallo,a mota suka dinga rarrashin shi "kaga idan muka tafi dakai Malam bai sani ba idan ya dawo zaima Inna fad'a muma zai mana fad'a, yamak'ale kafad'a"uh uh ai idan tace kaine bazai yi fad'an ba,kuma kana da waya kafad'a mishi na san zai yadda,ni dai kawai ALLAH mutafi"to naji na kuma maka alk'awari idan aka samu hutu Insha-ALLAH zan zo in tafi dakai Zonkwa.Yad'ibo dabinon ajwa da yawa a aljihunshi idan ka yadda sai in bar maka wannan dabinon,yakalleshi sannan yakalli dabinon" to duka zaka barmin?Yayi murmushi"eh mana sa hannunka ka kwashe ma, yana ta d'auka da d'ai-d'ai da d'ai-d'ai yana sawa a aljihunshi har ya kwashe duka sannan yayi dariya aina kwashe, to sai ka zo d'in barinje in nuna ma Inna,yauwa Bello mutumin kirki barin rakaka,har ciki ya kaishi ya kuma fad'a mata yadda sukayi tayi murmushi kawai sannan suka sake yin sallama sunama juna asha ruwa lafiya.
Rana ta tafi zata fad'i magriba na shirin kunno kai,an kusa shan ruwa takashe rediyon da take sauraran tafsirin Alqur'ani me girma a gidan rediyon jahar Kaduna(FRCN)farin gida kafin Sardauna.Tayi doguwar hamma tasa tafin hannun dama tarufe bakin ta, tana Isti'aza yau ba laifi tana jin azumin nan ajika dan ma yau Khausar ce da aiki da wallahi bata san yadda za tayi ba kanta har barazanar ciwo yake yi,daga can D'akin-girki tajiyo kiran Umma tamik'e da sauri tafita.
Umma gani.Umma tamata wani kallo "ba tun d'azu nace ki d'auki dabgen Hajiya ki kai mata ba?Baki ji bane ko zuwan ne baza kiyi ba? Tad'an sosa kai Umma fa boss ce,bata d'aukar raini ko na sisin kwabo"Yi hak'uri Umma barin d'auko hijab,tasa hijab ta d'auki kwanan samiran sannan tad'an kalketa cikin shakka"Umma dan ALLAH daga nan zan biya gidan Inna.Tayi shiru kamar bata jiba sai da tagama zuba wani dabgen a wani samiran ta rufe sannan takalleta"adawo lafiya suma ki tafi musu da wannan.Wani murmushi yasu6uce mata dan ba k'aramin aikin Umma bane tahana"nagode Umma tarik'o hannun Hanifa'yar Musaddiq ta fari suka tafi.
Tana shiga sai ga Nasmat itama takawo ma Inna hadaddan kunun aya kafin a kira sallar magriba sunyi alwala,ana kiran sallah sukaci dabino da lemun 6awo da ruwa me rangwamen sanyi sannan suka tada kabbarar sallah.
Julaibib da Baba suka shigo da sallama sukama juna barka da shan ruwa sannan ya ajiye ledan hannunshi a gaban Inna.Nasmat tajawo ledan gabanta tafara shan abarban da yake ciki da kankana yankakku tana fadin"kyan rawa da makar6i.Sudaida ma tasa hannu ta d'auki kankana tana cema Hanifa sa hannu ki d'auka...Baba yayi murmushi ganin irin kallan da yake musu,yayi k'wafa yajuya zuwa d'akin shi Inna tana mishi dariya itama.Sudaida ta ka sa cigaba da sha, ranta ba dad'i har yanzu bai dawo yadda tasan shiba, ba wani kyan gani da yayi,yabar k'asumba ba wani gyara,kana mishi magana zai bika da wannan rikitaccen kallan,ya ya6a maka bak'ar maganar da ko barinje (mahauci) iya karta kenan.
A sanda hantsi yadubi ludayi na safiyar laraba yana nazarin wani littafin tafsirin Alqur'ani me girma Hajiya tashigo da sallama,yamik'e da sauri yataro ta"maraba da zuwa Hajiyar mu,ta ture shi"kai tafi can matsa kabani waje,ta zauna a kujera tana murza k'afafunta,ya d'auko man zafi zai shafa mata tajanye k'afafunta da sauri"bana so.Yayi murmushi"haba Hajjaju makkatu wal madinatu gwiwata a k'asa,kaina bisa wuyana.Oho ashe kaima ka san kayi laifi,saboda ALLAH Julaibibi tunda kazo garin nan sau d'aya rakkin rak kazo gidana,ba fad'a to me yakawo wannan gabar? Kiyi hak'uri Hajiya bana jin dad'i ne.Tajijjiga kai tana mishi kallan nazari"kai Julaibibi tunanin Bilkisun ce yake susuta ka haka?Yagirgiza kai "haba dai Hajiya ba wannan bane.
Yamik'e da sauri ya d'auko madara da maltina da kofi.Hajiya tabishi da kallo cikin mad'aukakin mamaki"ciwon har yakai ba ka iya yin azumi ne Julaibibi?Yadafe kai "Innalillahi.Ina yi, wai dama ke zan kawo ma na man tane.Tamik'e wa?Ni kaga tafiya ta.Yarufo gidan"barin taka miki suna tafiya suna hira"anjima da daddare zan zo miki hira sai ki tanadar min garwashi zan zo da d'anyan masara in gasa mana"To ALLAH ya kaimu har gidan Kawun shi yakaita.
A D'akin-shak'atawa Sudaida ce kawai tana kwance a doguwar kujera tana waya,tamik'e zaune saboda shigowar su,kusan dak'ik'u goma sannan tagama wayar,tad'ago tana kallan Julaibib bayan ta d'ora ha6arta a kafad'ar Hajiya"Hajiyarmu you're welcome.Kin san abinda bature me jan kunne yake nufi da haka?Tajijjaga kai"tun kafin in haifi uban ki ya haifeki kuwa.Tad'an turo baki, Julaibib yayi murmushi yana shafa k'wantaccen bak'in gashin kanshi"Yo kya 6ata fuska ba tambaya kikayi nabaki amsa ba?
Mu turancin mu ma gangariya masu abu da abun su kura da kallabin kitse, turanwan ne fa suka koya mana baki da baki,To me yasa bakya yi?Tad'an kalleta kaji wata magana to yaran turanci yarena ne?Ni yarene hausa idan takama ayi turan cin inayi mana"do you get me? Sudaida takyalkyale da dariya saboda yadda Hajiya tayi furucin tagyad'a kai"yes grandam.Su Mama suka shigo suna gaishe da surukar ta su cikin girma da mutuntawa.
Da daddare yana gidan Hajiya suna hirarsu takalleshi"tunda katafi Azare kayi zaman ka shiru ba amo ba labari ko wata bafulatanarce takuma rik'e mana kai?Ya jujjjuya masarar sannan yad'ago yakalleta"ko d'aya Hajiya.To in dai haka ne ya kamata ka nemi wata,ga yan mata nan burjik a cikin dangi sai ka za6a ka darje,kana gani ganin idanun ka Musaddiq Ya'yan shi biyu ga cikin na uku nan.Cikin wasa yace"Hajiya banga wacce nake so ba ko za ki tayani nema?Tagyada kai"anyi an gama maye ya auri makauniya.Bai wani dad'e ba yamata sai da safe, saboda akwai tashi cikin dare domin yin munajaati ga ALLAH buwayi gagara koyo ga kuma tashi yin sahur.
K'arfe-k'arfene sai dai a cikin k'arafan akwai zinare da azurfa.
Idan baka san gari ba...saurari daka.
Abdullahi Lawal Abdullahi (D'ansarai)
Saudat Ibrahim Yahya (Takwara ta)
Mungode da tunatarwan ku bisa wani kuskure da mukayi a shafi na goma sha biyar..
Falmata Maiduguri mungode da kulawa.
28 Jumaada Awwal 1441
23 January 2020