Dasafe yayi wanka yana sanye da yadi ruwan madara mara nauyi,yayi lamooo a cikin kujera.Tashigo da sallama tabi kayan abincin da kallo yana nan yadda ta ajiye"Yaya Julaibib har yanzu baka karya ba? Yagyara zama"na d'an sha kunun gyad'an, ina jin bakina ba d'and'ano ne.Tad'ago tana mishi kallan tuhuma bayan ta bud'e kofin"na ce bakaji sauk'iba ka ce ba haka ba,yanzu wannan kunnun an sha shi kenan?Kur6a d'aya kayi ko? Yad'anyi murmushi"afwan Zaujatiii...zan sha anjima.A hankali yamik'e"barin je gidan Inna ko za kimin rakiya?Uh uh adawo lafiya.ALLAH yasa.Ta amsa da amin tabi bayanshi da kallo wata irin k'auna da tausayin shi suka tsirga ilahirin gangar jiki da zuciyarta,bata ta6a ganinshi a irin wannan yanayin na daren jiya ba.Tasauke gwauran numfashi"Ubangiji yasa kaffarace Yaya D'ansarai nah... Takoma D'akin-girki tak'arasa ayyukanta sannan taje tayi wanka ta shirya cikin shigar mutunci da sanin kimar kai kamar ko yaushe tatafi makaranta.
Bayan sallar Isha'i yashigo yana kallanta, itama ta idar da sallah tana azkar,tagama ta mishi sannu da zuwa zata cire hijab yarik'o ta"bar hijab d'in ki muje kimin rakiya gidan Hajiya d'azu ban samu na shiga ba, muna ta hidimar jama'a a shago.Tad'an turo baki gaba"a hakan da ba ka da lafiya me makon kadawo gida kayi kwanciyar ka,kaima kahuta ma ranka?Ai naji sauk'i. Tazuba mishi idanu nawasu yan dak'ik'u sannan tace"tun safe har zuwa yanzu me kaci?Na sha shayi a gidan Inna. Tad'an harareshi"shayi dai shayi dai ai sai kaje kayi ta sha, toh yanzu ga abincin dare na jiranka muje kaci sai mutafi gidan Hajiyan.Yagirgiza kai"bari mu dawo sai in ci yanzu banajin yunwa.
Hajiya tana shan dabgen bindin sa suka shigo da sallama.Sudaida tasa hannu wai wai wai gaskiya matar nan kina sha'aninki wallahi,tagalla mata harara"kema wa yahanaki na ki sha'anin? Sakarya kanki kawai kika sani,toh maza d'auki faranti ki zubama mijin naki mana.Yad'aga hannu"a ah barshi kawai Sudaida bazan iya ciba.Suka zuba mishi idanu"har yanzu jikin ne Julaibibi? Hajiya ta tambaye shi.A ah naji sauk'i Alhamdulillahi.
Ganin ya sake anata hira yasa suka saki ransu.Hajiya ta ajiye tsinken data gama sakacen naman daya mak'ale mata a hak'ori"to ko wannan zirga-zirga da kukeyi ai dole yakarar daku daga kai har matar taka,duk da yanzu na ga tafara sabawa, tana maida jikinta a hankali.Yad'anyi murmushi yana kallan Sudaida"ai Insha-ALLAH zirga-zirgan zai ragu dan an d'aukeni koyarwa a Gidan-Waya, farkon wata me kamawa zan fara zuwa.Hajiya tafad'ad'a murmushinta zuwa dariya"kai Masha-ALLAH...Wow Congratulations.
Suka kyalkyale da dariya"Hajjaju makkatan ashe dai baki manta karatun ba?Inji Sudaida.Tamata dakuwa"ungo nan,mu turancin muma gangariya turawa yan misionaries su suka koya mana baki da baki.Toh Hajiya kingama aji bakwai d'in danaji ance anayi a zamanin da amma bakiyi aikin gwamnati ba?Oh oh k'arya ciwo aji hud'u nayi Baba ALLAH yajik'anshi da rahama yamin aure.Sudaida takalleta cikin natsuwa"toh kema nan kunyi soyayya ke da mijin naki?Hajiya tafara tafa hannaye cikin salati da sallallami.
Sudaida tad'an yamutsa fuska "daga tambaya sai ki fara salati.Hajiya tajawo carbi zata shaud'a mata tamik'e dasauri tafita da kwanan da tagama cin dabgen tawanko hannunta sannan tadawo tana kallan Julaibib daya tsaida gwiwoyinshi yasa duka hannayen shi ya rungumesu,tazauna kusa dashi tad'an marairaice" Yaya D'ansarai anya kaji dad'in zaman nan?Yakalleta me kika gani?Kamar kana jin sanyi...Tabbasss sanyin ne yafara ratsashi amma bai nuna ba,sai yamik'ar da k'afafun na shi yasa hannu yana shafa kwantaccen bakin gashin kanshi "ba kome fa.Tagyad'a kai.Hajiya kuma tagalla mata harara "to iyayin yace me?Julaibib yakalli Hajiya "Sudaida fa amaryace kin kuma san amarya bata laifi,idan kina matsa mata to abu me sauk'i ne tayi yajin zuwa gidan nan.
Takad'a kai tana yar dariya ALLAH sarki wacece amaryar? A in da ba amarya dai a kira ta da hakan,to dan ta daina zuwa gidan nan sai me? Sudaida takalle shi"lallai naji da kunnene dan haka Yaya Julaibib tashi mu kama gabanmu wannan farin watan sai yamana illah gwamma dake Hajiya auren ki da gata.Hajiya tagyad'a kai"ba shakka ai wuyanki ya isa yanka.Suka mata sallama tarako su har zaure "ALLAH yamuku albarka nagode,nagode Ubangiji yabamu alheri, yatashe mu lafiya.Amin Hajiya.
Suka jera suna tafiyarsu a hankali suna hira har suka zo gida.Takawo mishi abinci yabud'e yana gani tuwon alkama miyar ku6ewa d'anya,yad'an kalleta a marairaice"Zaujatiii...dare yayi fa...itama ta kalleshi"uhun me yafaru?Yamayar da murfin miyar ya rufe"bai kamata in ci abinci me nauyi da yawa ba tunda kwanciya zan yi.Tayi shiru kamar bataji abinda yafad'a ba.Zaujatiii...ba ki jine?Na ji...amma da kasan baza kaci ba tun farko ai da mun tafima da almajirai suma suci da d'uminshi,takalleshi cikin kulawa"toh yanzu me za kaci?Yasake wani marairaicewa yanata kallanta yak'i magana,ta kyalkyale da dariya dan abin dariya yabata"Yaya D'ansarai wai meye haka kake ta wani kallo na kamar wata bak'uwarka? Me za kacine?Za ki bani abinda nake so?Tana yar dariya tagayd'a kai"ALLAH zan ba ka.To ni dai shayi zaki had'a min kuma dan ALLAH kar kimin mugunta kisa min siga,dan haka take mishi wani lokacin idan ba taso yasha shayin shi kuma ya nace sai yasha.
Angama autan Inna"ke zo nan dawa kikeyi ne? Tashige D'akin-girki da wanda ya tsargu nake yi.Taje tahad'o kofi biyu tamik'a mishi d'aya ta rik'e d'aya yabita da kallan k'arin bayani,tagyad'a kai "tayaka shan abinda kake so zanyi ko ban kyauta bane?Yayi murmushi"kin kyauta mana,tad'ibo donut tabashi amma baici ba haka yasha na shi,itace dai taci guda d'aya suka gama takai kayan D'akin-girki sukaje suka wanke baki sannan sukayi shirin bacci.
Cikin sulusin daren yaketa juyi dan ya kasa bacci,yatashi yazauna,yakoma yakwanta yayi hakan kusan sau biyar,har bacci yafara d'aukeshi yasake tashi zaune yakama kanshi da duka tafukan hannayenshi abin ba sauk'i wai ciwon arna,wani zazzafan zazza6i yarufeshi sai kuma sanyi yafara ratsashi"Sudaida...a hankali yafara kiranta ita kuma baccinta yayi nisa,yakai hannu yana d'an bubbuga k'afarta Sudaida...kamar a mafarki taji kiran tayi juyi sai tasake jin kiran tabud'e idanun ta taganshi jingine da gadon yana cigaba da kiranta,dasauri tamik'e zaune kamar zata hantsila zuciyarta na bugawa da k'arfin gaske tayi Istirja'i"Yaya Julaibib wai meke faruwane?
Wani irin ciwone haka sai cikin dare? Yadamke hannunta gangam Sudaida sanyi nake ji rufeni.Tagyad'a kai" tabbasss garin akwai sanyi ga sanyin farin wata daya haske doron duniya kaafatan, dole mara lafiya yaji sanyi,to amma jikinshi yayi mugun zafi kuma yana jin sanyi to bai kamata kuma a rufe shi da abu me nauyi ba dan ba a so zafin yakoma jikinshi.Yana karkarwa yace"Sudaida rufeni sanyi nake ji,dakyar yayi furucin,tamik'e ta d'auko zanin a tamfa ta rufeshi. Yagirgiza kai"ban daina jin sanyin ba d'auko bargon mana,ta lalla6ashi yakwanta"yanzu zan d'auko kaji?Tarik'o hannunshi"kayi hak'uri Yaya D'ansarai tajik'a k'aramin tawul a ruwa tana fara goge mishi jiki yarik'e tawul d'in tamauuu"kyaleni bana so,kwanta kiyi baccin ki.Takwanta tanata kallanshi har wani baccin wahala yad'aukeshi dan daga ganin yanayin fitar numfashin ka san baya jin dad'i.
Yashigo da sallama yazauna a kujera yana kallanta har ta idar da sallar,ta sunkuyo tana mishi sannu da jiki tana ta6a jikinshi har yanzu da zafi, a ranta tana yaba k'ok'arinshi dakyar yayi alwala saboda ciwon kan bai sake shiba,amma a haka yagangand'a yatafi masallaci dan samun jam'in sallar asubahi"ALLAH gari na dad'a wayewa asibiti zamu tafi,ni ciwo cikin dare tsoro yake bani.Yayi yar dariya"tsoro kikeji kar in mace miki? Sudaida ai ko da rana idan lokaci yayi tafiya zan yi. Tamishi wani kallo dayaji tasirin shi har a zuciya"ni bana san irin wannnan kalaman fa gaskiya,cuta ai ba mutuwa bace, wata kilama ni zan rigaka macewa,ba dai wanda yasan gawar fari"ALLAH dai yasa mucika da kyau da imani.Amin Zaujatiii...yazame yakwanta yanata kallanta tana shige da ficenta har wani bacci yasake awon gaba dashi.
Sai da tagama shiryawa sannan ta tasheshi yaje yayi wanka su tafi asibiti.Yamaida kanshi saman kujera yana kallanta cikin shigar doguwar rigar atamfa da dogon hijab me hannu"ba makaranta za ki tafi bane?Can ne amma sai mun gama da asibiti zan wuce.Yamik'a hannu yakar6i jakarta yasa mata kud'i a ciki yamik'a mata,tasa hannu biyu takar6a tana godiya "ALLAH yak'aro bud'i Yaya Julaibib.Yayi murmushi kawai sannan yamik'e muje in taka miki.Takalleshi kayi wanka dai mutafi ko? A ah naji sauk'i fa ni anjima kad'an ma Kafanchan zan tafi.Takalleshi wani iri kamar za tayi magana sai kuma tayi shiru.
Yau da wuri tadawo sai kawai tawuce gidan Inna suka sha hirar su Inna tamusu faten tsaki sai bayan la'asar tamata sallama takoma gida,tana ganin kiran Julaibib tad'aga a kame sallama kawai tamishi tayi shiru"Zautajiii...kin dawo daga makaranta ko kina can in biya in d'auko ki.A takaice ta amsa"nadawo.Lafiya kuwa?Tasake amsawa da"Uh batare data bud'e baki ba.Baki da lafiya ne najiki wata iri"k'alau nake.Yasauke numfashi"toh shikenan ganinan zuwa.Ta amsa da uhun.
Taje tayi wanka tana zaune a gaban madubi tana kwalliya ya shigo da sallama ta amsa sallamar tare da mishi sannu da zuwa tacigaba da abinda takeyi bata wani damu da ganin shiba,yanad'e hannayen shi a k'irji yana k'are mata kallo,yau ta mishi kyau fiye da kullum,yak'arasa wajen ta da karsashi "Zaujatiii...kinyi kyau fa.Ganin ya d'okantu da ita yasa tad'an tsuke baki kamar me shirin yin fito,kamar bataji abinda yafad'a ba tacigaba da shafama la66anta jambaki ruwan hoda.
Sai yad'ora mata ledar raken a jikinta"ga mutumin ki.Tad'anyi tsaki. Yabita da kallon nazari"tun a waya nakiji wata iri yanzu kuma tsakin me kikeyi Sudaida?ALLAH dai yasa banine na 6ata miki rai ba.Tad'an harareshi tana k'unk'uni.Ke karki sani a uku fa kin san ina k'aunarki.Ganin ta mik'e zata bar d'akin yasa yarik'ota da sauri sannan yakalleta cikin natsuwa"fad'a min laifina zan baki hak'uri,durk'usama wada ba gajiyawa bane.
Haushin shi yakamata"na rantse maka da girman ALLAH idan bakazo munje asibiti ba to ko ciwon ka yatashi cikin dare ni karka tasheni ina tsaka dajin dad'in bacci na eheee,yasan za a rina...wannan fushin,haba-haba dai ke kuwa ya zaki fad'i haka? Yanzu lalurata ba taki bace?Takwace hannayenta tana turo baki gaba"eh batawa bace,ta kace kai kad'ai dan haka kaje kaji da ita kai kad'ai tunda na baka shawara baka jiba...Yayi yar dariya"kinga to kisha kuruminki Sudaidan D'ansarai yajata suka zauna a kujera sannan yaciro ledar magani da d'an k'aramin katin shi na ganin likita"duba kigani"daga asibiti nake abinda yasa ban dawo da wuri ba kenan,likita yamin test,wai typhoid ke damuna ga magungunan daya bani da allurai"anjima bayan sallar Isha'i za ki rakani allurar,kin san bana son allura idan nak'i tsayawa sai ki d'an bud'e idanun ki nan da nan sai kiga na tsaya amin ba tare da ankai ruwa ranaba ko kuwa?Tayi dariya"lallai kuwa wannan shine ta6ara megida da kukan yunwa.
Tad'auki rakenta tafara sha da bismillah"da fa yau har yajin shan raken nan zanyi da bakaje asibitin ba.Ke d'in kuwa?Ke mayyar rake ce kuma ban ta6a k'in siyo miki ba,amma ni idan nace ki had'a min shayi sai kawai ki kama fushi wai bazan sha bak'in ruwa ba to haka a ke rayuwa?Kowa ba da abinda yafi so ai ko kuwa? Tajijjiga kai"ka fini gaskiya, toh kayi hak'uri na dai fushi da shan bak'in ruwa... tawani shagwa6e"nima ai gashinan a hankali na fara koyan sha,shekaran jiya ba tare muka shaba? Yagyad'a kai"Yau me kike dafa mana be?Tad'an kalleshi"ni fa da bazanyi wani girki ba,idan zamuje allura muje gidan Inna kaci tuwo ni zan sha Yoghort dan bana jin yunwa.Yamik'e"to shikenan,yatafi d'auro alwala dan anfara kiraye-kirayen sallar magriba daga mabambantan masallatan unguwa.
A hankali cigaban rayuwa take zuwa daki-daki har zuwa sanda bawa zai had'u da aljalinshi,alokacin numfashi da duk wani abinda ALLAH yarubuta zai samu ko zaiyi a doron duniya ya gamayin shi.Julaibib Abdullahi D'ansarai a yanzu yasake samun cigaba daga matakin lecturer zuwa senior lecturer.
Yana zaune a D'akin-shak'atawa yana yan rubuce-rubucen shi a na'ura me kwakwalwa,yayi k'iba yak'ara kyau da wayewa,bak'ar fatarshi tanata shek'i dan ta jik'e da hutu da kwanciyar hankali,shigarshi kamar kullum ta fararen kaya,hularshi dara daratsin fari da ruwan k'asa, agefe kuma Ya'yanshine Ya'yan abokinshi amininshi,kuma d'an'uwan shi Musaddiq suna zaune tankwashe da k'afafunsu cikin ladabi suna cin abincin rana. Asma'u tayi sallama tashigo. Julaibib yad'ago yana amsa sallamar yana mata sannu da zuwa,tazauna suka gaisa sannan tabi d'akin da kallo"ina madugar baza ta fito mu gaisa bane? Yagirgiza kai"Sudaida baza tak'i fitowa ku gaisa ba matuk'ar tana cikin gidan nan ko da kuwa bata jin dad'ine.Tata6e baki"haka fa, toh madallah.
Suka cigaba da hirarsu ta zumunci,a hankali har tasako mishi zancen k'arin aure"Lillahi warasulihi ka dinga zama kenan da mace juya? D'ansarai ai kowa yana son ganin d'a na kanshi. Yad'anyi murmushi"haihuwa ai d'an lokacine Yaya Asma'u.Tawatsa hannu" kai tafi can,tunda an maida kai hannun zani dole za ka fad'i haka mana,ka barta tana ta karatu to yaushe kuwa zata yadda da haihuwa, haihuwa yaja mata koma baya a wajen karatunta,na sha fad'a maka yarinyar nan tsarin Iyali takeyi,idan ba haka ba me zaisa har yanzu bata haihuba? Su sauran da akayi bikinsu rana d'aya ba ga shinan daga me haihuwa biyu sai me uku ba?
Jiya kuma nake jin wani k'arin abin haushin,abin duka ba sanda wai Gidan-Waya sun fara degree program dan haka ka barta tacigaba,haba dan ALLAH D'ansarai ina hankalinka da tunaninka suke ne?Ganin yayi shiru yasa tacigaba da zugashi da k'ara tabbatar mishi lallai tabbasss Sudaida ita take hana kwanshi zuwa duniya.
Zuciyarshi tafara mishi tubka da warwara game da kalaman Asma'u.Tasake kallanshi "D'ansarai wai kai har yanzu baka ga biri yaso yayi kama da mutum bane?Yazuba mata idanu yana zancen zuci"anya Sudaida za ta mishi haka?Yana lura da ita,ita kanta fa tana san Ya'ya dan duk lokacin da za suje siyayya a kasuwa taga unisex riga indai ya mata kyau to sai ta siya,ran nan yashiga d'akin baccin su yatarar da ita tana jera kayan a babban a kwati trolley;yazauna yana kallanta
"Zaujatiii...wai wa kike sai ma wad'annan kayan ne?Tad'anyi murmushi idanun ta sun ciko da kwallah alamar zuciyarta tayi rauni "takauda kai sha'awa suke bani Yaya D'ansarai musamman wad'annan biri da wandon(over roll) duk lokacin da ALLAH ya bamu d'a toh na shine ko na tane...kawai sai ta fashe da kuka"d'azu A'isha takirani wai ta kuma haihuwa d'a na uku kenan ta haifa... Maryam ta kusa haihuwan na ukun...kowacce tana da Ya'ya mu kad'ai ne bamu dasu...yafara rarrashi"kiyi hak'uri Zaujatiii... ALLAH yana sane damu bai manta damu ba,kome d'an lokaci ne,wata rana sai labari yayi ta rarrashinta har yasamu tayi shiru sannan yakalleta cikin natsuwa "Zaujatiii... ki daina wahalar da kanki a kan tara kayan yara na sha'awa duk wannan me sauk'i ne in dai ALLAH ya azurtamu da samun d'an, dan kyale-kyalen kullum sabunta su akeyi"budurwar bana tafi ta bara...
Bayan haka kuma kullum gidan nasu cike yake da Ya'yan yan'uwa in dai tana gida,kai ko bata gidan in dai shi yana nan kuma ba makaranta za suje ba toh zama sukeyi su jirata,saboda san su da takeyi da kuma irin garar da take had'a musu,duk abinda yaro yake so in dai tana dashi to anyi angama maye ya auri makauniya"in dai abin ta6akalashe ne. Toh Lillahi warasulihi me irin wannan halin ce,za a ce baza ta bar nata Ya'yan suzo duniya ba saboda karatu?Anya kuwa?Yariga yasan Yaya Asma'u kowa ma za ta iya kushewa tazaga in dai taku batazo d'aya ba.Yakad'a kai cikin sauke numfashi"ALLAH yakyauta. Tabishi da kallan mamaki"ALLAH yakyauta fa kace? Eh Yaya Asma'u to me zance daya wuce haka?
Tadad'a gyara zama"kai ko kake da abin cewa,cene da ita aure za kayi...kayi auren ka amarya tazo taita haifa maka Ya'ya,toh idan taga Ya'yan kake so taga amaryar taka tafara cika maka gidan da sanyin idanu to ai zata daina abinda takeyi na tsarin iyali ko kuwa?Toh zanyi tunani.Tamik'e"ya dai kamata,ni me zan samune a gidan? Tana fad'in haka ta nufi d'akin da suke ajiye kayayyaki tagama dube-dubenta tafito"kome ma ya k'are.Yauwa gwamma da kika gani ganin idanunki,dana fad'a miki ba kome ba yadda za kiyiba,kin san ni d'an albashine ga shi kuma wata yakai tsakiya,abubuwan sai dai godiyar Ubangijinmu a kowani hali da yanayi.
Taja dogon tsaki tana mishi kallon uku ahu"amma a hakan kake k'ok'arin biya mata wasu mak'udan kud'ad'e dan tacigaba da karatu, tamik'a mishi hannu"ni bani abinda kayi niyyar bani kawai in tafi.Zan ai ko miki dashi har gida,Yaya Asma'u kidinga tausaya min mana.Tanunashi da yatsa"kai d'in?Na rantse da girman ALLAH ba ka da matausaya.Yakalleta da mad'aukakin mamaki yana nuna kanshi"ni d'in ne bani da matausaya Yaya Asma'u?Ko shakka babu dan ni banga matausayan ba,ba d'a ba jika to ko hidimar me kakeyi da har za a tausaya maka saboda yawan buk'atu?Daga kai sai matarka kuke cin karanku ba babbaka,takalleshi"za ka bani ne ko sai madugar ta dawo in zo in kar6a? Baice kome ba yasa hannu a aljihun gabar rigarshi yaciro kud'ad'en ciki yana nuna mata"kingani yan canjine wallahi bani da kud'i.Tasa hannu takar6a"eh kawo da hanau gwamma mannau ni na wuce.Yabita da kallo har tafita a D'akin-shak'atawar, yagirgiza kai "Yaya Asma'u matsala,ALLAH yashirye ta da masu hali irin na ta.
Sun dawo sallar la'asar da yammacin,shi da Musaddiq suka tsaya a k'ofar gidan suna tattauna al'amuran daya shafi kasuwancinsu ta dawo daga makaranta,ta tsaya suka gaisa da Musaddiq sannan tawuce ciki da mamakin kallan k'urillan da Julaibib yake binta dashi wanda ba halinshi bane yawan kallan da har sai kaga munin mutum.Tana kwance a tsakar d'akin yashigo,tamik'e zaune suna kallan-kallo na wucewar wasu dak'ik'u "Yaya D'ansarai lafiya kuwa? Me yafaru ne? Yasunkwui da kai,sai gwiwoyinta suka sage dan ta san wannan halin na shi tuntuni in dai yasunkwui da kai to bazaiyi magana ba ko da menene,tajingina bayanta da kujera tare da lumshe idanun ta,tunani barkatai ya cika k'wak'walwarta"ita dai tasan lafiyar ALLAH suka rabu har tana tsokanarshi
"Zaujiii...kafin in dawo kamana faten tsaki mana.Yagalla mata harara"na rantse da ALLAH tun kafin wankin bargo yakaiki ga dare ki tsaya kiyi abinki, danni ba bawa bane.Takyalkyle da dariya wato ya rama abinda ta ta6a fad'a mishi shekarun baya,farkon auren su kenan.Tawani marairaice"haba mijin Sudaida tamu dakai fa ba ta 6aci,kar fa faten tsaki yasa a ganmu a rana,tarik'o hannayenshi"dan darajar k'auna da soyayyata da take dank'are anan tad'an daki k'irjinshi dai-dai saitin da zuciya take, kamana faten tsaki,sukayi dariya,yagyad'a kai"eh zanyi amma ba fate ba tunda nima a wancan lokacin ba a hanani ba sai dai an jamin zarene.
Yamik'e,tabishi da kallo"Yaya D'ansarai... takira sunanshi.Yakalleta kawai"dan ALLAH kayi hak'uri idan na maka wani abu ne.Yayi kamar baiji abinda tafad'a ba,zuwa can kuma yasake kallanta sai yad'anyi murmushi yad'auki mukullin mota a saman tebur yafita.Ta lumshe idanun ta tanata ayyane-ayyabe a zuci.
A sanda hantsi yadubi ludayi rana ta haske ko'ina na safiyar talata,tana zaune a in da ta idar da sallar walha Hauwa'u tashigo tana fad'in"ina wannnan mijin naki me bak'in idanu da ba ya san zuwa gaisheni? Abokan wasa suke da Julaibib Ya'ya maza amma tasu da Sudaida ta zo d'aya,suna mutunta juna.Sudaida takama ha6a"yanzu mijin nawane me bak'in idanu Hauwa'u? Tajijjiga kai 'tabbasss,to ni duk zuri'ar D'ansarai da wanda yafishi bak'i ne?Sudaida tad'an harareta"lallai daga yau na san in da zan ajiyeki tunda kike cima rabin raina fuska a gaban idanuna,to amma kuma kyau tsagwaron shi da wanda yakama k'afar Yaya D'ansarai nahhh a duk zuri'ar Doctor Julaibb D'ansarai? Bata bata masa ba taje tad'auko lemun peach.
Sudaida tawatsa hannaye"ahab ni dama na san irin abin nan ne na na makaho da yace ido da wari.Hauwa'u tayi murmushi"mu ai gaba d'aya a zuri'ar Doctor Julaibib Abdullahi D'ansarai kyawawane.Sudaida tagyad'a kai"muma ai hakan take a zuri'ar Ibrahim Me-Lambu.Sukayi dariya sannan suka gaisa suna hirarsu ta yaushe gamo dan sun d'an kwana biyu basu ga juna ba saboda yanayin karatun Sudaida da baya barinta zama a gida musamma tada fara karatun degree.
Hauwa'u tafara ba Sudaida shawara"ku k'ara komawa asibiti mana ko wannan karan ALLAH zai sa a dace.Takalleta cikin natsuwa"Hauwa'u a asibiti ake ba da haihuwa?Tagirgiza kai"ba a asibiti bane,amma idan kunje d'in ai zasu k'ara dubaku,idan har yanzu ba me matsala a cikin ku za su iya canja muku magunguna da k'arin yan shawarwari ko kuwa? Tagirgiza kai"uh uh ni dai bazan koma ba,sauran magungunan ma na daina sha shekaran jiya na zubar dasu nagaji da shan k'waya kullum kwanan duniya bayan an tabbatar mana lafiyar mu k'alau, na fauwalama ALLAH duk yadda yayi dai-dai ne.
Duk san mu da haihuwa idan ALLAH bai k'addaro mana ita a rayuwarmu ta doron duniya ba, toh fa bawani magani da dabaru da likita zai bamu da za suyi amfani,tad'an yi murmushi"ki cigaba da tayamu da addu'a itace babbar makamin mu.Hauwa'u tarik'o hannayen Sudaida cikin k'auna da tausayi "wannan halin na ki na maida al'amura wajen ALLAH me kowa da kome yasa nake dad'a k'aunarki,addu'a ina tayaku da ita kuma zan k'ara,Ubangiji yamana jagora ya iya mana kar yabarmu da iyawarmu dai-dai da k'iftawar idanu.Amin Hauwa'u.
Asma'u tashigo da sallama tana musu wani malalacin kallo ganin hannayen su a had'e"to fa wani sabon salo ne wannna zuwa karuwanci da uwa? Hauwa'u ta amsa"eh mana to ya san ranki Ma'u?Kafin tayi magana Habiba Yayar Hauwa'u tashigo,tafad'a kujera tana wata yatsina wai ta gaji daga shagon d'inki take.Asma'u takar6i ledar ta zazzage kayan"toh bari muga style,material ne da da leshi kuma d'inkunan sunyi kyau sosai,wai ankon sunan da za ayine idan ta haihu.Hauwa'u ta d'auki material d'in tana dad'a gani dan shine ya burgeta "gaskiya da ina da kud'i da sai na yi shi.
Asma'u tace"tunda baki da kud'in wannan ai akwai atamfa ta yaku bayi,dama ai dai-dai ruwa dai-dai k'urji.Habiba ta cafe"ah to shi mutum ba zai tashi ya nemi na kai ba,kome an dogara da miji har abinda ba wajibinshi ba a gida yakamata Iyayenshi su mishi amma basuyi hakan ba,kai ni wannan rashin tausayi dame zan kwatantashine?Kome dai miji?Taja dogon tsaki,toh gwamma dai mutum yasani shi mijin nan ba dan mace d'aya aka halicceshiba,ko bajima ko ba dad'e dole wasu mata ukun da izinin ALLAH sai sun shigo an dama dasu suma.
Sudaida tayi tsaiii...cikin nazarin kalaman Habiba,babu kome a cikin su daya wuce shagu6e. Hauwa'u da bata gano dawar garin ba tace kai"sharri dai ba kyau wallahi,kuma kun sani ai ina sana'a sai dai banyi k'arfi bane,yaro kuma ai da rarrafe yafara,ni kuma dan san a sani yaji da kwarin miji da banten suriki da d'an masu gida bazan kwashe jarin nawa dan yin ankon suna na rana d'aya in dawo in tsuguna ba,kuma da kuke maganar kome miji toh dan girman ALLAH wace macece a doron duniya da baza taso ace kome mijin na tane yake mata harma da wanda iyayen nata suka kasa mata ba?Kudinga adalci a kalamanku fa...Asma'u da Habiba suka kalli juna suka kyalkyale da dariya Asma'u tace"ballagaza bankaura, sakarai ba ta da wayau...inji Sa'adatu(Barmani Choge)
Sun so wacce sukai hakan dan ita ta tanka amma sai batace kome ba tashige d'akin baccinsu tad'auko material da leshi launinsu d'aya dana Habiba sai dai zanen jiki ya bambanta,tana fitowa ta d'orama Hauwa'u a cinya"gashinan ki d'auki d'aya,wannan karan dai na ceceki,dan haka daga yau ki tashi haik'an da niman kud'i dan ki huce takaicin zamani,duk da dai na ga zafin nema ba shi yake kawo samu ba,haka kuma dare d'aya ALLAH kanyi bature, indai kina da wadatar zuci to abun kowa bazai tsone miki idanu ba.Hauwa'u Tajijjiga kai "tabbasss zancen ki dutse.
Tabi kayan da kallo"kai ko wanne fa ya d'auku,sai dai kawai in rintse idanu in d'auki d'ayan. Sudaida ta koma ta zauna"toh barinyi maganin ruwan idanunki kawai,kirik'e su duka na bar miki.Hauwa'u tad'an zaro idanu cikin mamaki"duka na wa?Kin barmin? Sai tafad'ad'a murmushinta zuwa dariya"kai masha-ALLAH jazakillah khaira-khaira jaza'ih...ALLAH yabarki da Alhaji D'ansarai me bak'in idanu har gaban abada.Takallesu ku tayani godiya mana.
Zuciyar Asma'u ta gama tafarfasa har ta k'one,ankon fa takema D'ansarai magiya yamata yace shi bashi da kud'i shine yanzu matarshi har take kyauta da kala biyu,itafa d'aya ma tace mishi tana so..Lallai wanna akwai shegiyar yarinya wato kome na shi ya tattara mata kenan?Taja tsaki"itama Inna tana da matsala(🤔kunji fa)wai idan an fad'a mata sai tace wannan dai sa'idanune a abinda bai shafe kaba, ita ba matar shi bace?Ai ko ba aure a tsakaninsu yan'uwan junane,kuma duk Ya'yantane,tanuna Asma'u da yatsa"wallahi kina tare da wahala idan baki bar wannan banzan halin na kiba,ke wayasan damfarar da kike ma mijin ki da wannna shegen wayan na ki?Tasake jan tsaki Inna bazaki gane irin bautar da yakema wannan yarinyar ba wallahi dan ba kyau zuwa gidan nan kina gani ganin idanunki ne.
Habiba ce taja dogon tsaki"kina ta wani zuba godiya kamar wacce a kamata gafara,ba fa sai kin gode ba tunda kowa ya san ai k'oshin wake na ruwa ne,da kud'in d'an uwanki D'ansarai aka siyesu, kuma ko ke zai iya sai miki wanda suka fisu ma... Hauwa'u ta tari numfashinta"a ah wallahi k'arya da ciwo gyambo da wari.
Sudaida tayi dariyar tura haushi"ah toh gwamma dai da kika tuna mata,takalli Habiba tana murmushi"wad'annan da kike ganinsu tanuna kayan data ba Hauwa'u ni na siyesu da kud'i na,ai idan zan siya da kud'in Yaya D'ansarai toh bazan sai wad'annan masu rangwamen farashin irin ta gama-gari yakubayi ba,tunda kud'in ni nake zamansu.
kufa yan uwane ba dole ne ya mukuba,sai dai yayi dan kara yasamu ladan zumunci, idan kuma yak'iyin haka ba wanda zaice dan me?kuma ko a wajen ALLAH bashi da laifi ko na sisin kwabo tunda ku ba a hakk'unshi bane,ni ce nan tanuna k'irjinta da kwibinta ni ce k'ashin hak'ark'arinshi,kinga ni ce nazama dolenshi, wallahi idan ana san zaman lafiya dani toh fa sai na fad'i irin wanda nake so,idan an kawo naga kalar bai min ba dole yakoma yaza6o wani, ko kuma in ce yad'ibo su da yawa in za6i wanda suka kwanta min a rai...Habiba ta tari numfashinta"tabbb ai ko baki isa ba,tamata wani kallan uku ahu kai... ALLAH ko ya isa da wannan iko sai kace ke kika kawo shi duniya.
Sudaida ta kalleta cikin kukawa"Habiba kenan kisa ranki a inuwa dan ko ba iko dama ALLAH ai ya isa da kome,shine dama me kowa da kome na doron duniyar nan. Asma'u tamik'e"ke fa yarinyar nan wato salan mulkin ki kenan ki hana mutum rawar gaban hantsi ko? Batayi niyyar maida martani ba to amma Yaya Asma'u ta dad'e tana shiga mata hanci da k'udundune ya kamata ta fyaceta,kuma kunyar mara kunya ai asarace,idan babba ya yadda girman shi to ai ba laifi bane dan an taka.
Sai tagyad'a kai"ai kuwa dai Yaya Asma'u na zama kuturwar uwa zama dani dole,kuma duk wanda zai zauna dani d'in to d'aurin gwarmai nake mishi.Habiba da take ji kamar ta shak'e Sudaida dan haushi tace"to ai barewa baza tayi gudu yar ta tayi rarrafeba.Sudaida ta kyalkyale da dariya"ai dama kyan rawa da makar6i,kyan d'an yagaji ubanshi. Asma'u tafara tafiya "to Sudaida na yi gida amma dai kiyi a hankali dan ni bazan mulku ba, idan kuma kika matsa da yawa to abu ne me sauk'in gaske cire wando taka inyi waje dake.tak'arasa fita ba dan bata da sauran abin fad'a ba,a ah sai dan kar k'ilu taja bauuu...ga Hauwa'u nan itama munafuka ce idan anzo maida magana Sudaida za ta goya ma baya sai a d'ora mata sata da maitar,amma lallai sai tasa Dannarai ya k'ara aure, itama Sudaida ta so data tsaya ta ba ta amsa dan haka duk sunji ciwon kalaman juna.
Tacire hannun Hauwa'u da tayi tagumi dashi tana kallan su kawai,ta kashe ta da lallausan murmushi tunda ance iya ruwa fidda kai."kiyi hak'uri ba kud'i a hannuna amma idan bafade na autan Inna yadawo ranar jumma'a to zan turo miki shi wallahi har gida yazo yabaki kud'in d'inki dana takalmi da hijab,dan kin san ni a gidan nan k'arfine dani na gaban shari'a kum...Hauwa'u tasa tafin hannun ta rufe mata baki"dan girman ALLAH ya isa haka Sudaida.
D'akin-shak'atawar ya d'auki shiru na wucewar wasu yan dak'ik'u.Habiba tayunk'ura tamik'e cikin fushi bata musu magana ba tayi hanyar fita.Sudaida tad'an d'aga murya"toh uwar biyu sauka lafiya sai kin kiramu,ALLAH yaraba lafiya.A ciki ta amsa da"uhun.Tana fita Hauwa'u ta kyalkyale da dariya"matar D'an Sarai yau kin burgeni.Takad'a kai"ni har ga ALLAH banyi niyyar kula suba to amma naga abun na su yana neman wuce gona da iri ne,shiru-shiru kuma ai ba tsoro bane gudun magana ne"dodo d'aya akema tsafi,ba su suke aure na ba Yaya D'ansarai ne dan'uwan ku,duk fad'in mutanan doron duniya idan za suce yarabu dani idan yana so na,yana san zama dani to ba wanda ya isa ya rabamu,tunda ba wanda yake mishi auran nan,shi d'in da kanshi yake abinshi,haka kuma idan yace ba yayi ba wanda zai tilasta mishi zama dani.Hauwa'u tajijjiga kai "tabbsss zancen ki dutse"ALLAH yashirye su da sauran dangin miji masu mugun hali na mugunta "abun wani banza na su dukiya.
Tana kallan shirin Akhbar-Al'an tana cin awarar madarar shanu Khadija yar Khausar tashigo da gudunta cikin d'oki tafad'a jikinta"Inna Mamace tace in zo in tambayeki wai anjima za tayi tuwon shinkafa miyar shuwaka,shine tace wai a k'aton kwano guda nawa za a zuba miki? Sudaida tayi murmushi ta san wayau aka mata, kafin tayi magana kiran Khausar yashigo"Nana Khadija ta k'araso kuwa?Eh gatanan ta kuma fad'a min sak'on,ina za ki?Asibiti zan kai Misbahu ta kuma na ce dole sai munje da ita.Wayyo! har yanzu jikin ne?Shine Sudaida daren jiya kusan kwana mukayi bamuyi bacci ba saboda kukan shi. Toh ALLAH yasauwake zan shigo anjima idan kun dawo. Sukayi sallama.
Inna me zan fad'a mata?Takalleta da kulawa"bari sai anjima idan nayi wanka sai muje can muci ko?Toh Inna amma kamar kinyi wanka ga shi kina ta k'amshin irin turaren Baba D'an Sarai,ina son k'amshin. ALLAH Khadija?Khadija tayi d'an tsallan murna kamar yadda yara keyi"ALLAH Inna,to maza shiga d'aki ki d'auko kema in fesa miki,da gudunta ta d'auko Sudaida tafesa mata.Nagode Inna.Tad'an kama ha6arta"yauwa Khadija ga yoghort can kije ki d'auka,tad'an mak'ale kafad'a"Inna ni dai nafi son Caprisonne.Tamik'e shikenan muje in baki.
Sudaida tazuba mata idanu cikin tasbihi ga Ubangiji,k'udurar ALLAH dayawa take,wai yaushe-yaushe akayi auren su amma gashi har an haifi yar da za a aikota daga wani gida zuwa wani gida da k'afafunta da bakinta"oh ALLAH kaine ALLAH.Sharrr...sharrr...hawaye masu d'umi suka zubo mata"anya za taga gudan jininta a doron duniya kuwa?Ta rungumeshi a k'irjinta yaji d'uminta na uwa itama taji d'uminshi na d'a?Ta tuno da bak'ar magana habaici da dangin Julaibib suke mata,wanda in dai da mutum shi yake da ikon ba kanshi haihuwa to kuwa da tayi zuciya ta haifo musu yan hud'u a haihuwar farko,to ina ALLAH ne,ba kuma a mishi dole...tasake tuno kalaman Inna,Mama,kai rannan har Umma sai da tadinga kwantar mata da hankali akan dai tayi hak'uri tayi hak'uri,kullum haka suke fad'a mata musamman idan sun ganta cikin damuwa ko da ba wannnan ne abinda yake damunta ba "kiyi hak'uri Sudaida hak'uri kan tadda rabo,wata rana sai labari..
Khadija tamatsa wajenta"kukan me kikeyi Inna?Waya dake ki?Tarungumeta kawai tacigaba da kuka Khadija na tayata,sai da sukaci suka k'oshi dan kansu sannan sukayi shiru a hankali kuma bacci yayi awon gaba dasu.
Kiran wayar Julaibib yatashe ta daga bacci"wash ALLAH Zaujiii...yatare ta da sauri"me yafaru ne Sudaida?Tayo k'asa da murya"ba kai bane ina cikin baccina me dad'i ka tashe niba.Yayi murmushi"to fa tawa tasameni kenan malami da tallan jigida,kiyi hak'uri ki koma baccin anjima mayi magana.Uh uh ai kuma ko na koma baccin ba lallaine yazo ba sai dai in ta juyi"goben zaka dawo?Na so haka to amma bazai yiwuba dan gobe muna da serminar a jahar Katsina idan na dawo kuma akwai jarabawar da zan ma d'alibai,nima na so zuwa dan zan ba Inna wasu kud'i,amma barin miki transfer idan kika ciro sai ki kai mata,yanzu zan kira ta in mata bayani.Ranta bai mata dad'i ba amma ta daure ta amsa da to tare da addu'ar ALLAH yakiyaye hanya,sukayi hirarsu ta kewar juna sukayi sallama.
A sanda hantsi yadubi ludayi na safiyar laraba tabawa ranar sa a,Nasmat tazo gidan,suka rungume juna"oyoyo Nasmat...Sudaida ta d'auki Ahmad tana mishi wasa shi kuma ya bud'e wawulan bakinshi yana kyalkyala dariya.Nasmat taje tad'auko lemun sprite tabud'e tana mita "Sudaida kin zama abinda kika zama wallahi,abinda yasa meki ALLAH yasa kar yasamu sauran dangi.Tamata kallan k'arin bayani...Nasmat tagyad'a kai"in dai na zo gidan nan ni zan ba kaina ruwa ko abinci?Haka ake ma bak'o?Taja tsaki"na d'auka wani laifin nayi to kar kisha ruwan mana cikin wa zai shiga?
Takama ha6a"kar dai zama da mad'aukin kanwa Yaya Asma'u ya sa kema kin zama abinda kika zama? Haushi yasa Sudaida tak'i magana tanama Ahmad wasa yana cigaba da dariya.Itama tamik'e zuwa wajan taga tana amsa waya,tagama wayar tad'an kalli dai-dai kun mutanen da suke kai-kawo a safiyar sannan tacema Sudaida"na biyo miki ne muje duba yar gidan Yaya Asma'u da jiki.Hu'un tafad'a ba tare tadata bud'e bakintaba.Menene kuma hu'un?Nasmat ta tambayeta.Tamik'e zaune daga kwanciyar da tayi tad'ora Ahmad a cinya"ke ni fa bazani in da raina zai dinga 6aci a banza ba,dan na riga na k'una bana tsoron wuta.A ah Sudaida kiyi hak'uri kawai idan an miki kan kara karkice za kiyi na itace.Tayi wani huci cikin kad'ai"ai na rantse da girman ALLAH ni yanzu har na gungume zan iyayi yadda zai shekara yanaci,kawai sai tarufe idanu tana zazzaga fad'a,Nasmat bata kar zomo ba amma an bata rataya.
Tazuba mata idanu har tayi tagaji dan kanta tayi shiru,sai kuma tayi kwafa"banda ina duba darajar yan'uwantaka da dangantaka kinaga zan bar Yaya Asma'u tacigaba da cin dunduniyata tana min hawan k'awara yadda taga dama?Nasmat tagirgiza kai sannan ta amsa cikin natsuwa"a ah baza kiyiba, to amma karki manta hak'uri kan tadda rabo...idan ka gaida wada da tsawonka zaka mik'e...Sudaida ALLAH yana son masu hak'uri masu had'iye fushi,da dama su rama abinda aka musu amma sai suyi hak'uri ba saboda kowa da kome ba sai saboda zatin ALLAH... tacigaba da rarrashinta har fushin daya mamaye zuciyarta yalafa,ta kuma yi nasarar janta suka tafi dubiyan...
Da kunu da miya har abadan duniya ba za su had'uba sai dai a cikin ciki.
27 Jumaada Thani 1441
21 February 2020
We Ibrahim's Daughters👇
Asdilat KD...2geda with Ra'ibs.
DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION
{Da Inganci Mukayi Fintinkau}
Bismillahi wabihi nasta'in
...GWAJIN DAFI💔
Almost true story
Daga alk'alamin🖊
Ya'yan Ibrahim
Saudat A.Baba (Asdilat KD)
Da
Bara'atu Ibrahim (Ra'ibs)
Shafi na ashirin da biyu.
A wulak'ance da halin-ko-inkula kamar yadda tasaba haka yauma ta amsa gaisuwar Sudaida, amma tanata jan Nasmat da hira suna shirin tafiya sai ga Hauwa'u itama ta zo dubiya,suka tsaya ana gaisawa, Hauwa'u tamatsa kusa da Sudaida "yar'uwa yayane jikin ne ko garin ne,ko wannnan bak'in mijin na kine dayaje yashare waje a Gidan-Waya?Takai mata duka a kafad'a,tagoce da sauri yabi iska.Kin sama mijina rabin raina idanu fa,meye darin gamarki dashine wai?Asma'u da wata k'awarta yar duniya me irin halinta sukayi dariya suka tafa"haka fa kullum ana nuna ana k'aunar miji amma an k'i nuna mishi k'aunar a zahirance,ta hanyar barin Ya'yanshi suzo su shak'i iskar duniya,takad'a kai cikin ta6e baki"kullum ana ba mutum amma har yanzu ya kasa yin zuciya yak'ar6a ko da sau d'aya ne,sai dai ayi ta asara,a wanke abun yabi rariya.
Hauwa'u takalleta"ke wai Asma'u kullum ba ki da abinyi sai gori?Sannan ma dake ake magana me ko ko ita tace miki ba tajin dad'i?!Nasmat ma ranta ba dad'i tace"haba Yaya Asma'u wannan ba girmanki bane wallahi,kin san duk me gori matuk'ar bai tuba ba to yana haramtama kanshi rabon alheri ne a lahira, sannan wannnan gorin ma d'an Adam d'in doron duniya ba shi da iko akanshi,wannan ba huruminki bane Yaya As...kafin tak'arasa sai ga Hajiya tashigo d'akin tana d'agama Nasmat hannu "dakata Nasmat in dai gori ne ta tara ta samu, Hajiya tanuna kanta"ni d'in nan yau har goruba zan mata, zanyi maganin iya shegen nan k'auri da kare.
Tayi d'as d'as d'as da yan yatsunta"ki bud'e kunnuwanki da kyau ki saurareni,na rantse miki da girman ALLAH in har Sudaida bata haihuba to ba itace ba ta haihuwaba,k'aninkine Julaibibi,matan kakanku ai su biyune uwargidan shice mahaifiyar ubanki,su uku tahaifa,amma amaryar shi sai da ta haifa mishi Ya'ya goma shabiyu, ubanki gashinan shima Ya'ya uku yahaifa,d'aya kanin na shi yahaifi Ya'ya biyu, d'ayan kuma ai har yakoma ga ALLAH bai haihuba,matar shi data gama takaba tayi wani auren bagata can da Ya'ya bakwai ba?
Karima Yayarki Ya'yanta biyu,ke kuma yarki d'aya jallin-jal kamar rai,sai 6ari da kika ta6a yi sau d'aya duk shekarun da kukayi a gidan miji,mata nawane ta dangin kakar ta ku ga sunan a gidajen miji ba haihuwa sai dai suci su k'oshi suje masai su juye kayansu?Ai suna da yawa saboda ku ba irin haihuwa bane,toh Sudaida fa?Su goma sha takwas ne a gidansu,kuma duk cikin Ya'yana ba uwarki ce kawai me Ya'ya uku ba?Tanuna ta da yatsa"to dan haka ahir d'inki hawainiyarki takiyayi ramar Sudaida, kuma ko yanzu da k'anin na ki zai rabu da ita,toh idan ma na rantse ba kaffara a kaina bazata rufe shekara a wani gidan auren dazata yiba za ta haifo gudan jininta takuma sa zani tagoye abunta,ai ga sa'o'in auren na ta nan kina ganinsu ganin idanunki kowaccensu ta fara kafa na ta Iyalin...
Tambayar me jikin da batayiba kenan ta ajiye ledar ayaba da lemun tajuya cikin fushi"jahilar addini kawai wacce bata yadda kome muk'addari ne tun daga lauhul-mahfus ba,na rasa a ina kika d'auko wannan bak'in halin na ki,banda ma ke shimmeruwa uku ce(sha-sha-sha)Sudaida ba yar'uwarki bace da zaki iya tare mata fad'a a inda kikaga za a wukak'anta taba?Toh karki daina abinda kikeyi ai hassada ga me rabo ta kice...Nasmat da Hauwa'u sukayi lallausan murmushi suna shima Hajiya albarka"ALLAH yak'ara girma me amfani Hajjaju makkatan...kaza dai garin tuno-tone take tono wuk'ar yanka kanta...baki shi ke yanka wuya.Sai da Hajiya tabar gidan sannan Asma'u tafara nad'e tabarmar kunyarta da hauka.
Da wannnan 6acin ran Sudaida tawuce ATM taciro kud'in da za ta kaima Inna,sukayi kaci6is da Aminu shima ya zo ciren kud'i yabud'e mata murfin motar"shigo ki jirani tunda yau na ga ba layi.Dak'ik'u basu wuce goma ba yadawo.Yaya Aminu gida za ka koma? Yana tayar da mortar yake amsawa "Jos zani,amma ke zan mayar gida wani abune?Tasa hannu ta share hawayen da suka zubo mata sharrr... "mutafi kawai sai ka saukeni a Gidan-Waya.
Sun d'auki hanya sosai sannan yajuyo cikin kulawa yakalleta"wai yau waya ta6a kanwata rabin raina ne?Tad'anyi murmushi"share kawai Yaya Aminu ni da Yaya Asma'u ce.Yakama ha6a wuuu... Asma'u ciwon idanu sai hak'uri,ai ko jiya danaje dubiya nima sai da muka hau sama muka fad'o,wai nayi kud'i bana son zuwa gaisheta,kinji sai kace wata Yayata.
Sudaida takawar da zancen ta hanyar tambayar Siddiqa nan da nan ko yayi lallausan murmushi suka shiga hirar arziki har suka iso Gidan-Waya,har k'ofar gidan da Julaibib yake yakaita anan rukunin gidajen malamai,yasake kallanta cikin kulawa"Sudaida kiyi hak'uri na san kinayi amma ki k'ara wata rana sai labari,ai duk abinda yayi farko to tabbasss yana da k'arshe,wallah-azim da ana siyan haihuwa da kud'i toh dana sai miki kome tsadarshi,toh ina abin na ALLAH ne "ance da kare me sunan maza.Tajijjiga kai"na sani Yaya Aminu na kuma gode, duk cikin Yayyina kaine taurarona"Ina sonka sosai.Sukayi murmishi"nima nagode kanwata rabin raina data za6eni sama da kowa a matsayin tauraronta,toh me kike so in siyo miki a matsayin tsaraban mutan Jasawa?Tagirgiza kai"bani da za6i kasiyo min ko menene nagode.
Yayi yar dariya"tunda kin bani wuk'a da nama Insha-ALLAH za6in nawa zai burgeki,idan nadawo zan shigo in baki tsaraban,sai in kar6i kud'in da kikace zan kaima Inna,kiyi hak'uri ko?Nagode Yaya Aminu tabud'e motar tafito,tarufe mishi"adawo lafiya ALLAH yatsare,suka d'aga hannu suna ma juna adabo.Tabi danjojin motar da kallo har ya6ace ma ganinta.Tarik'e k'ugu tana fesar da iska ta baki ta hanci sannan tasa hannu a jaka ta d'auko mukullin gidan tabud'e tashiga.
Wani k'amshin turaren d'aki da sassanyar iskar da take shigowa ta tagogin da suke bud'e yamamaye ilahirin gangar jiki da zuciyarta,sai taji ta samu natsuwa ta lumshe idanunta tana jan numfashi"Yaya D'ansarai wallahi me tsabtane,ji yadda yazauna yagyara gidan kamar mace. Tashige d'akin bacci,tazauna a gefen gadon tad'auki wani d'an k'aramin hotonta da ya ajiye a dirowar gefen gadon,ta d'auki hotonne a wani excursion da sukaje a Wadom akan harkar gona tun tana aji biyu a k'aramar secondary,tak'arema hoton kallo tana tuno irin kyan da Julaibib d'in yace wai tayi...Wanda ita dan haushin irin munin da tayi ta turo baki gaba zata yaga sai gashi ya shigo gidan shine yakar6a,tamaida hoton ta ajiye tana murmushi ita tama manta ta ta6ayin hoton.
Taje tayi wanka tabud'e wardrobe tad'auko riga da zani na shadda ruwan makuba dan dama akwai kayanta a gidan,wasu lokutan idan tazo makaranta ba ta komawa Zonkwa sai tayi zamanta koda ba Julaibib a garin tunda baya samun zama yau yana Zari'a gobe yana Katsina, jibi yana Kaduna,haka dai haka dai ake ta gwagwarmaya da zirga-zirga a cikin rayuwar.
Tana azkar d'in yammaci bayan ta idar da sallar la'asar Aminu yashigo ya ajiye mata injin d'in matse ruwan rake tagama azkar d'in sannan takalleshi cikin murna da shakka tanuna injin d'in tana kallanshi"Yaya Aminu da gaske?Yajijjaga kai "Sudaida ko da nake da raha ai na san irin rahan da nake yi da kowa,bazanji dad'i ni akaran kaina amin irin wannan kyautar bayan na sa hannu na k'ar6a,sai kuma a kar6e wai wasa akeyi,dan haka bazan ma wani ba, bare ke kanwata da nake ji da ita a cikin k'annina,yad'an kalleta a kwai rake a gidan nan? Tamik'e ai ba a rasa nono a riga sai dai idan rigar ba ta tsurar fulanin asali bane,a na'urar sanyaya abubuwa(fridge)tad'ibo ferarrun rake guda biyar takawo mishi,yauwa d'auko wuka kigani.
Yakar6i wuk'ar yak'ara yankasu k'anana sannan yasa a ciki,yan dak'ik'u kad'an yad'auki Kofi yajuye mata tataccen tsurar ruwan rake, yamik'a mata tasa hannu biyu takar6a takai tsakanin la66anta da bismilla takur6a,sai kawai tacigaba da sha har sai da tashanye duka.Suka kalli juna,yad'an dage gira"toh ya?Takyalkyale da dariya tana jijjiga kai "Alqur'an yayi ba k'arya,nagode Yaya Aminu ALLAH yasaka maka da mafificin sakamakon shi.Amin Sudaida"ke ma muk'amuk'inki sa huta da tauna,to kai baka shaba?Yagirgiza kai"sanda za a nuna min sahihancin injin d'in an matsa min na sha. Yamik'e yana gyara zaman hular shi"to barin kama hanya,taje ta d'auko mishi kud'in da zai kaima Inna sukayi sallama.
Tana wanke d'anyen na'ana'a yashigo D'akin-girkin a d'okance"Zaujatiii...saboda ALLAH dama kinzo garin amma baki fad'a min ba?Yazuba mata idanu"to yanzu dana wuce Zonkwa ne fa? Tad'an motsa kafad'a"duk d'aya 6arin manshanu a miya.Yarik'ota cikin kewa sai kuma yasake ta barinje in sallami d'aliban da suke jira a waje yawuce D'akin-shak'atawa yad'ibo wasu takaddu yafita.
Sai da yayi sallar Isha'i sannan yashigo yazauna a kusa da ita yana ganin rubutun da takeyi a na'ura me kwakwalwa"barka da shigowa Yaya D'ansarai.Yagyad'a kai"barkanmu kema kinzo lafiya?Tayi shiru kamar bataji shiba,wucewar wasu dak'ik'u kuma tad'an kalleshi"yayi murmushi kina k'ok'ari fa ALLAH yak'ara basira.A tak'aice ta amsa da "amin.Sai kuma tarufe Laptop d'in tamayar ma'ajiyarta.
Ta dawo tazauna a d'aya kujerar suna fuskantar juna,zama nesa dashi da tayi yabashi tabbacin akwai maganar da zata fad'a mishi me mahimmaci dan haka take yi,dan haka shima yadad'a gyara zama dan yaji yau kuma dame tazo?
"Yaya D'ansarai kana k'aunata kuwa? Baiyi tunanin abinda za ta fad'a kenan ba,amma sai ya 6oye mamakinshi ya amsa mata kai tsaye"eh Sudaida ina k'aunarki.To na rok'eka da girman ALLAH karabani da damuwa,kome yanada iyaka to tsakani da ALLAH abinda zuciyata za ta iya d'auka kenan,idan ba haka ba to ba abinda zai hanata kumbura ta fashe k'arshen rayuwata a doron duniya ya zo kenan,tanuna kanta da yatsa,ni na san ba autar mata bace dan haka zan tayaka addu'a ALLAH yabaka wacce tafini, wacce zata haifa maka sanyin idanu tunda ni na kasa, nima ALLAH yabani dai-dai ni.
Yakalleta cikin natsuwa"me aka miki da kike zancen rabuwa?Da mamaki takalleshi"au yanzu baka gani ba?Saboda bakai ake ma ba?Tayi wani huci cikin kad'a kai"toh madalla,amma Yaya Julaibib gaskiya ni dai bazan iya wannan zaman ba,duk lokacin daka shirya nima a shirye nake zan ba ka sarari.Tamik'e.Jinan Sudaida koma ki zauna. Bata zauna ba sai kawai ta durk'usa a gabanshi tafara kuka
"Yaya D'ansarai kaji tausayina mana bazan iya jure wani wulak'anci da bak'ak'en maganganu ba dan kawai ban haihuba,bana so zumunci ya6aci ne amma na rantse maka da girman ALLAH da da kaina zan d'auki mataki.Tasake fashewa da matsanancin kuka,kukan abu biyu take yi,gana rashin haihuwar akaran kanshi,gana wulak'anci da tozarcin da ake mata akan dai rashin haihuwar me makon ma abarta taji da abinda yake damunta.Haka ta dinga fad'ar duk maganar data fito daga bakinta ba tare data tauna ba.
Yad'ago ta fuskarta sharkaf da hawaye da majina yazuba mata idanu na wucewar wasu dak'ik'u saboda ya rasa abinda zai fad'a mata,sunyi waya da Hajiya kuma tafed'e mishi bire har bindi "tabbasss an dad'e ana mata wannan cin k'ashin, amma shi da ita bata ta6a fad'a mishi ba,ko ya ganta cikin damuwa idan ya tambaya za ta girgiza kai"tace ba kome ko tace wani abu kazane ba gorin rashin haihuwaba,yayi tsaiii...har yasamo bakin zaren,sai yayi murmushi"kinga Sudaida share hawayenki tabbasss ni D'ansarai ina k'aunarki dan haka zan rabaki da bak'in ciki da damuwa.Takalleshi kallan k'arin bayani"Yajijjiga kai"kiyi hak'uri kibani lokaci zanyi tunanin yadda al'amuran za su kasance ba tare da an 6ata zumunci kamar yadda kika hango haka ko?
"Zaujatiii...ina so kimin alk'awari zaki bani lokacin ba tare da kin sake tambaya taba har sai na zo miki da zancen,lokacin na samu mafita...za tayi magana yatari numfashinta"dan ALLAH kar kice kome,ai kin san ba zanyi abinda zai cutar dake ba. Tayi shiru kawai tana share hawaye tamik'e zuwa d'akin bacci takwanta tare da d'ora kanta a saman matashi.
Kad'an yaci abincin daren sannan yaje yayi wanka yasa kaya marasa nauyi na shan iska,yazauna a doguwar kujera ya barbaza wasu takaddu yana aikin cikesu d'aya bayan d'aya sai dai ya kasa jure rashin Sudaida,kewarta ta dame shi dan haka yamik'e zuwa d'akin.Suka kalli juna tana kwance da wani littafin lissafi tana nazarin shi,tamaida kanta cikin littafin amma ta gagara cigaba da nazarin,yazauna a gefen gadan sannan yasa hannu yakar6i littafin.
Tawani 6ata fuska"Yaya D'ansarai gobe fa muna da jarabawa shi yasa nake nazarin nan.Yamata wannan kallan da yake ba ta haushi yagyad'a kai"uh na sani...ni ma gobe zan tafi Katsina yaya kenan? Tad'an turo baki gaba tana dad'a gyara bargon data rufa"toh kowa sai yakwanta yayi ishashshen baccin da ake so mutum yayi duk dare,gobe kowa sai ya tashi a watstsake katafi Katsina,ni kuma in shiga makaranta ba shikenan ba?
Takauda kai daga kallan dayake mata, tafara jero azkar d'in kwanciya.Ai ko ba shikenan ba,ki sallameni.Tagyad'a kai"toh jeka na sallame ka, ALLAH ya lullu6eka da rahamarshi da albarkarshi, asubah tagari.Yayi murmushi sannan yasa hannu yana mata wani salo...salon data kasa daurewa tamik'e zauna tana dariya"Yaya D'ansar...sauran kalaman suka mak'ale sakamakon wani sak'o d'aya bata me girman ban mamaki me sa a fita a hayyaci.
Da safe yagama shirin shi tsab natafiya cikin shigar farar shadda yana zaune a D'akin-shak'atawa, yayi shiru cikin nazarin kalaman Sudaida dan ko da asubahi sai da tadad'a tabbatar mishi tana nan akan bakanta,ta kuma bashi sarari tana zaman jiran shi.Yadda yake juya zuman da yasa a shayi haka yake juya kalaman;tafito daga d'akin baccin su cikin shigar mutunci da mutunta kai kamar ko yaushe za ta shiga makaranta.Tazauna a hannun kujerar "Yaya D'ansarai wai har yanzu shayin ne baka shaba?Tun kafin in shiga wanka fa nakawo maka.Yasunkwui da kai.Sai kawai tamik'e tad'an kalleshi nawucewar wasu dak'ik'u
"Yaya D'ansarai ALLAH yakiyaye hanya...
Tad'an sunkuya tabashi sumba sannan tayi furucin da wani salon shagwa6a"sai munyi waya ko?...tajuya tayi tafiyarta dan tasan ba magana zaiyi ba in dai yayi wannan sunkuyar da kan"sanin hali ai yafi sanin kama.
Yabita da kallo yana lallausan murmushi yayi d'as da yan yatsunshi"hak'ata zata tadda ruwa Insha-ALLAH ai ni dake mutu karaba yarinya.Yakalli agogon dake d'aure a hannunshi na dama,lokaci yaja a gurguje yagama karyawa,yad'auki jakar shi ta matafiya ya rataya a kafad'a da mukullin mota yakulle gidan yana addu'ar fita daga gida"bismillah tawakkaltu alallahi walahaula walaquuwata illah billah.Yashiga mota ya zauna yana d'aura belt yana kuma amsa wayar wani abokinshi na koyarwa da za suyi tafiyar tare.Tun daga ranar Julaibib yacanja taku tunda abin iya ruwa ne...
A sanda hantsi yadubi ludayi na safiyar litini (Monday)ranar aiki ko nasara na tsoron ki tana kwance cikin bargo tana baccinta na tofan gira dan yau sai yammaci zata shiga makaranta kiran wayar Inna yashigo tad'aga da fara'a"Innarmu Sudaida takirata tana yar dariya"na'am yar gidan Inna,suka gaisa Inna tace"na ji autana shiru ni da Alhaji har mun gaji min kira layinshi sau shurin masak'i,da tana shiga baya d'agawa amma daga baya kuma ta daina shiga kwata-kwata.
Dasauri cikin d'an bud'e idanu dan mamaki tace"shi Yaya D'ansarai d'in Inna?Eh shi d'in,ko baya jin dad'i ne kuke 6oyewa?Fargaba takamata dan kwana biyun nan itama fa bata gane mishi wallahi"a ah Inna lafiyar shi k'alau,yanzu ma yana cikin makaranta bari ya shigo inji abinda yafaru.Toh ALLAH yadawo dashi lafiya,ALLAH ya jishshemu alheri sukayi sallama Sudaida tana amsa addu'ar Inna da amin,amin Inna.
Tafito D'akin-shak'atawa kawai taganshi kwance a doguwar kujera.Yaya Julaibib takira sunan shi. A hankali yabud'e idanun shi yana kallanta"har ka dawo ne amma baka nemi ni ba? Ni banji shigowar kaba.Yauwa sai tajuya ta d'auko wayarta"munyi waya da Inna d'azu barin kirata,yafizge wayar ta bishi da kallo yakasheta gaba d'aya sannan yatura a aljihun gefen rigarshi ta dama"rabu da ita Sudaida.Tazauna a k'asa gefen k'afafunshi tana bud'e idanu da mad'aukakin mamakin furucinshi"Innarce za a rabu da ita? Bai bata amsa ba yamaida idanun shi yarufe.
Tasake bin shi da kallo cikin tsoro da shakka"to ko dai Yayi Julaibib ya fara k'arama sama hazo ne?data isheshi da tambaya sai kawai yamik'e yashige d'akin baccin su har yanasa mukulli,bai fito ba sai da za shi masallaci sallar azahar.Tamik'e ta tare k'ofar.Yad'an yamutsa fuska "ke bani hanya yanzu za tada sallah.Tagyad'a kai"ba in da za ka har sai ka fad'amin abinda yake damunka da har za kace a rabu da Inna..
"Adai-daita sahu a had'a kafad'a...
Suka fara jiyowa daga masallaci yad'an kalleta cikin natsuwa"barin dawo daga sallah sai muyi maganar ko?
Daga masallaci makaranta yawuce bai koma gidan ba,tagaji da jiranshi,itama tatashi tabishi,yana jin an kwankwasa k'ofar ya amsa daga ciki"na'am bismillah shigo,bai zaci itace ba.Takulle k'ofar tazare mukullin"Yaya D'ansarai ni fa ka sani a rud'ani wallahi, wai me yake damunka ne Inna za tayi magana dakai kace wai a rabu da ita sannan ka k'wace waya ta ka kashe,ta kama ka kashe me yafarune?Ni ma kwana biyun nan kwata-kwata bana gane maka.Yamaida kanshi jikin kujerar"to Inna me za tamin?Inna bata da maganin damuwata fa.
Da rawar murya tafara nuna shi da yatsa"Kai Yaya D'ansarai Innarce..ba..ta da maganin... damuwarka?To duk fad'in duniyar nan ma kana da kamar tane?Takalleshi cikin takaici"to wa yake da maganin damuwarka?!
Yajanye kanshi daga jikin kujerar yad'ora duka hannayenshi a saman tebur d'in sannan yakalleta cikin natsuwa"Zaujatiii...ke ce maganin damuwata,ina k'aunar ki, ina jin takaicin ace wai ni Julaibib yanuna kanshi da yatsanshi wai ni zan rabu dake dan kawai ba kya haihuwa, ni ina son ki a kowani irin hali da yanayi na rayuwa,Sudaida ko baki haifa min Ya'ya ba ba na nadamar aurenki.
Ni yanzu abinda yake damuna yahanani rawar gaban hantsi shine na kasa samo mana mafita ta yadda zamu rabu salin-alin ba tare da Inna ko Kawu ran wani daga cikin su ya sosuba, kema kuma na san kin k'osa amma kina min biyayyane kawai saboda na rok'i alfarma kar kice kome...Dammm... Zuciyarya tabuga...tanajin wani irin yanayi mara dad'i yana bin ilahirin gangar jiki da zuciyarta,gaskiya idan tarabu da Yaya Julaibib...kai anya? Sai tabar wannan ayyane-ayyanen na zuci.
Yawani marairaice"ALLAH yamiki albarka Zaujatiii...yarik'ota da wani salo"ko ke zan d'aurama wannan aikin na lalubo mana mafita danni dai har yanzu na ka sa, amma ko bama tare Zaujatiii...ki rik'e wannan a zuciyarki "ke ce mace ta farko dana fara k'auna,k'auna irin wannan ta aure zan kuma cigaba da k'aunarki ko da bama taren.Jikinta yadad'a yin sanyi da jin kalmar nan ta rabuwa...ganin hakan da tayi sai yacigaba da zugata ta hanyar kambama halayenta na kwarai,da kuma mamakin da yakeyi wai ita da kanta take ikirarin saki bayan ta san hadisin Manzon ALLAH da yace duk macen data nemi mijinta yasake ta batare da wata hujja ta shari'aba toh k'amshin aljannah ma bazata shak'aba,kuma shi k'amshin aljannah ana fara shak'arshine tun daga tafiyar shekara d'ari biyar,haba Zaujatiii...da ilminki da wayonki da kome na ki,tayaya wasu dangin miji can za su rabamu,bayan basu suka had'amu ba,ni fa nake auren nan ba wani ne yakemin ba,ai nine zan miki gorin haihuwa kece kin d'anji haushi ko?Karki kuma d'aga hankalinki a kan duk maganar masu magana,sau nawa muna zuwa ganin likita akan rashin haihuwa ana kuma bamu tabbacin dukkanmu lafiyar mu k'alau lokacine kawai baiyi ba,ba da bakinki kikace ke kin daina shan wata k'waya dan neman haihuwa kin barma ALLAH ba?Me Yaya Asma'u za tayi ta6ata miki rai?Yau kika san halinta?Ai tun kafin mu zama ma'aurata kin sani dan ko gidanku taje sai tanuna wannan halin na ta,kin gani ganin idanunki ke ganauce kuma jiyau..
Rashin haihuwa ba k'ask'anci bane wallahi,Idan kika duba gidan Manzon ALLAH a duk matanshi ba wacce ya keso sama da Nana A'isha kuma har ta koma ga ALLAH bata haihu ba,bayan ita a kwai wash matayen na shi da basu haihu ba,to me garage darajarsu?Annabawan ALLAH nawane da basu haihuba?
Ganin damar ALLAH me idan yaga dama yabaka Ya'ya maza zallah,ko yabaka mata zallah,ko yahad'a maka maza da mata,haka kuma ganin damarshice yabarka bakarare(Mara haihuwa) kinga da...
Bai k'arasa furucin shiba ta k'ank'ameshi tana kuka,yayi lallausan murmushi dan hak'anshi ta tadda ruwa,yacigaba da rarrashinta"Zaujatiii...ni D'ansarai ni ne me auren nan kuma na ce mutu ka raba,ko kin haifa min Ya'ya ko baki haifa min Ya'ya ba,kuma na miki alk'awari zan yima tufkar hanci,ba me kuma samun ke a damuwa a dangina,su suje su rungumi mazajensu cikin annashuwa ni kuma su dagulama Zaujatiii...nah lissafi?Toh karki damu kinji ko?Tad'ago takalleshi"Ya'ya D'ansarai nagode maka da wannan tunatarwar ta ka"idan rai ya 6aci to bai kamata hankali ya gushe ba...kai mijin alheri ne;tasauke gwauran numfashi
"Rayuwata idan babu kai a cikinta za a samu tasgaro me tarin yawa,tadad'a k'ank'ameshi tana shak'ar k'amshin deodorant da arabi'an perfume d'inshi,yad'ago fuskarta suka kalli juna yad'an dage kira yana mata wani kallan k'auna yana murmushi "mun zama k'arfe da mayen k'arfe ko? Tajijjaga kai"eh wallahi autan Inna,D'ansaran Baba,Zaujiii... Ustazun Sudaida yar Ibrahim,jikar Ibrahim Me-Lambu.Suka sumbanci juna yace kuma"mayyar rake abin ma yasamu shiga wai d'an wake a hotel har da injin d'in matse ruwan ko da ta zama tsohuwa ba hak'ora ko?
Tad'an daki k'irjinshi,shi kuma yabata marin soyayya suna dariya.Tad'auki wayarta a saman tebur d'in ta kunna"toh kira Inna gaskiya dan ta damu da rashin jinka tunda har takirani.Yagirgiza kai "gwamma mutafi Zonkwa ayi kome idanu na ganin idanu"zan fad'a mata kece kika hanani.Tad'auki jakarshi taraya a kafad'a suka fito daga office d'in, suka jera suna tafiya zuwa inda ake ajiye motoci da mashinan malamai tana fad'a mishi"Inna baza ta ta6a yadda ni na hanaka kiran taba,tunda ni kullum sai mun gaisa ko ta kirani ko in kirata.
Watannin Sudaida bakwai kenan da tafiyarta Gidan-Waya,duk wannan watannin zuwanta Zonkwa sau hud'u,yanzuma tanata mishi magiya yabarta taje tunda sun samu hutu amma ya hana,wai tayi zamanta a in da mijinta yake ai shine zai fi mata kwanciyar hankali,tagyad'a kai"ni ma na sani ai bawani dad'e wa zanyi ba mak'o d'aya dan ALLAH, amma ya hana,haka dole ta hak'ura,dangin Julaibib kuma sun barta tana rawar gaban hantsi bata san me yafaru ba,amma tabbasss...ta dad'a yadda da kalaman shi kamar yadda yace ba me sa mishi mata a cikin damuwa.
Da safe tana kwance tak'i tashi tahad'a mishi shayin shi ko ruwan wanka,shi yamusu kome,yagama shiryawa sannan ya zauna a gefen gado"Sudaida yakira sunanta.Tad'ago tana kallanshi yana sanye da babbar riga yar ciki da wando na farin yadi yana karya hular zita"har yanzu baza ki tashi daga kwanciyar k'asan nan ba?Tasauke idanunta k'asa"ni dai nafi jin dad'in nan.Yagyad'a kai"sauri nake yi damunje asibiti.Tamik'e zaune dakyar"ba sai munje asibiti ba,naji sauk'i Yaya D'ansaarai.Yagirgiza kai"za dai kiji sauk'i,tun yaushe nakai miki ruwan wanka amma har yanzu baki tashi kinje kin yiba?Yamik'a mata hannayen shi"ta so muje in cud'a ki.Tayi yar dariya"bayan ka shirya?Ai zaka 6ata adon ka,yi tafiyarka yanzu zan yi.Yad'an motsa kafad'a"uh to menene a ciki,ba sai in canja wasu kayan ba? Tamik'e tana mishi rakiya,kad'an ta taka mishi ta dawo tayi kwanciyar ta dan dama bata so tayi wankan,idan tafad'a mishi to sai ya tilasta ta yin wankan ko ta so ko tak'i.
Har yadawo tana kwance yayi tsaiii...yana kallanta yana bin d'akin da kallo,ba abinda tayi yakad'a kai cikin damuwa"wannan ba halin Zaujatiii...bane tabbasss bata da lafiya.Dakyar yatashe ta sai wani narkewa takeyi, amma tanayin wanka sai tajita garau...yana kallon tashar larabawa suna nuna yanayin al'adunsu yana cin gasashshiyar kaza me kayan lambu tashigo yabita da kallo tana sanye da material bak'i me yarfin filawoyi ruwan k'asa, d'an kunne,sarka da warawarenta na zinare sai d'aukar idanu sukeyi saboda kyallinsu,fuskarta shar da kwalliya, bakinta yana kyallin jambaki ja.
Tazauna suna kallan juna "Zaujatiii...kinyi kyau dame kike son tukwuici?Tad'ora ha6arta a kafad'arshi tayi furucin da wani salon shagwa6a "agada(plantain) yajuyo yakalleta"kin cinye wannan agadan dana siyo miki ne?Ta amsa kai tsaye"wallahi tun jiya.Yabud'e baki dan mamaki saboda ada shi yake matsa mata tasoya musu dan ba wani dad'ata da k'asa yayi ba,amma a yan kwanakin nan cin agada takeyi kamar ta samu abincin gado,d'an kullum, ranshi yadad'e me martaba tuwo miyar kuka abincin hausawa.Kai shifa bai yadda ba sai da yaje yaduba in da suke ajiyewa yaga ba kome sannan yadawo yana cemata lallai kinyi k'ok'ari,yad'auki waya yana kiran wani mak'ocin shi da yau yatafi Jos kuma anjima zai dawo dan ALLAH yasiyo mishi agada.
Yasake kallanta bayan yagama wayar amma fa na d'auka bakya jin dad'i danaga tun safe kina ta bacci har shabiyun rana.Ai na fad'a maka lafiyata k'alau kawai ni dai nafiso in kwanta in yi baccine.Ya mata nuni da kazar.Tagirgaza kai dan ko sha'awar ci batayi,tad'auko lemun peach tana sha suna hira jefi-jefi suna kallansu har suka gama shirin,sannan yamik'e zai koma makaranta "adawo lafiya.Takashe kallan tad'auki wayarta ta kunna data zuwa duniyar yanar gizo...
Da daddare kafin yadawo daga sallar Isha'i Sudaida tayi baccinta a inda ta idar da nata sallar. Yatasheta"Zaujatiii...ga agadan an kawo.Dakyar tad'an bud'e idanunta da yanayin bacci takalleshi sai ta mayar ta rufe,tayi wani juyi tana dad'a shemewa a dadduma"barshi sai da safe ni bacci nake ji,tacigaba da baccinta sai kuma tamik'e zuwa d'akin bacci.
Yabita da kallo har tashige.Shi kad'ai yayi zaman D'akin-shak'atawa yaci abinci kad'an, yaje yahad'a shayin shi da baya gajiya dasha.Yagama yan rubuce-rubucen shi har zuwa sanda bacci yafara kawoma idanun shi ziyara,yashiga d'akin ta kashe wuta,yakunna fitilar wayar shi yana hasketa" tana kwance a k'asa kuma yau tsabar jin bacci ko kayan bacci bata tsaya sawaba,yad'anyi murmushi yana cigaba da kallanta numfashi na shiga da fita cikin kwanciyar hankali,sai tamishi wani irin kyau na musamman, ya dad'a gyara mata rufa dan yasan ko ya maida ita gadon to sai ta sauko wai ita k'asa yafi mata dad'i,yakashe fitilar yakwanta yana musu azkar d'in bacci.
Abinda yaketa maimaituwa kenan,kullum bata da kuzuri,bata san yin kome sai kwanciya,yau dai abin ya isheshi,dan haka yana dawowa daga Kaduna jakarshi kawai ajiye,yatasata agaba sai tashirya sun tafi asibiti dan daren jiya kusan kwana sukayi tana mishi wash...wash...mararta tana mata ciwo amma abin mamaki baturiya da suna manga gari na wayewa sai tamik'e wai ta warke,yanzu kuma yadawo ya ganta lamooo bata da wani kuzari sai bacci-dai bacci dai bata gajiya...Yabita d'akin tanata nuk'u-nuk'unta"Zaujatiii...hijab d'in ne baki gane ba kome?Tabud'e wardrobe tad'auko.
A k'ofar gida sukayi kaci6is da motar Musaddiq tsayuwar shi kenan suka fito shi da Hajiya. Sudaida tarungume ta tana murna"oyoyo Hajiyarmu sannu da zuwa,suka koma ciki.Julaibib yayi murmushi"yau farar ranace agaremu me kyakkyawar suna.Hajiya ta ajiye kofin lemun"to ance ka gaida me gaisheka,kunzo nan kun share waje kun manta da kowa kuna sha'anin gabanku.Julaibib yasa hannu yana shafa kwantaccen bak'in gashin kanshi "munata fama dai da ayyuka da d'alibai Hajiya.
Ganin Hajiya yasa Sudaida ta nemi kasalar data rufeta tarasa,tashige D'akin-girki tana k'ok'arin shirya musu abincin data cema Julaibib ita yau baza tayi wani girki ba,yad'an motsa kafad'a" duk d'aya 6arin manshanu a miya, dan shima ba kullum yake cin abinci me nauyi da daddare ba.Musaddiq dai bai tsaya cin wani abinci ba Sudaida tafito suka gaisa yamusu sallama suka fita da Julaibib.Har suka gama cin abinci bai dawo ba, takwanta suna hirarsu me dad'i da Hajiya,bacci yafara d'aukanta sama-sama, sannan taji sallamarshi yashigo musu da gashashshiyar kaza,bata tsaya ciba tamusu sai da safe taje tayi kwanciyar ta tana jinsu sunata hirarsu, ita kuma baccinta rabi-da rabi tayishi saboda ciwon maran d'aya matsa mata daren jiya to yauma daren yayi shine yace bari ya motsa.
Yadawo daga masallaci sallar asubahi yaganta tsugune a bakin famfo tana ta yunk'urin amai amma yak'i zuwa,Hajiya tana mata sannu,tarik'ota suka koma D'akin-shak'atawa takwanta a doguwar kujera jikinta a mace yake murusss"sannu ALLAH yasauwak'e"Hajiya ta zauna tana mata fifita ganin yadda tajik'e sharkaf da zufa kamar wacce tafita motsa jiki da sanyin safiya.
Yazuba mata idanu zuciyarshi ba dad'i saboda yadda take dad'a rintse idanunta tana mirgina kai gefen hagu zuwa dama tana yarfe hannuwa,tana ta6a mararta da take mata wata irin d'aurewa tamauuu...ita kad'ai tasan azabar da take ji, wucewar wasu dak'ik'u cikin ta ya dad'a yamutsewa ciwon yana k'aruwa,mararta kamar zata 6alle,Hajiya itama ta shiga cikin damuwa"Sudaida wai meke damunkine?wai!Wash...wayyohALLAHnan...uhhh...washhh.. tasake yarfe hannun hagu na dama na saman mararta,da kyar tayi furucin"Wayyoh! Hajiya marata ce take ciwo. Julaibib yajuya dan tsayuwar ba amfani, motarshi kuma ba ishashshen mai"Hajiya barin samu mai yanzu mutafi asibiti.Tagyad'a kai"to hanzarta dan naga abun yana dad'a k'amari.
Wayyo ALLAH! tafad'a a galabaice tayi nishin wahala...uhhh...Hajiya marata!"sannu Sudaida yanzun nan Julaibibi zai zo mutafi asibiti.Ta cije le6enta na kasa ta yunk'ura zata mik'e zaune amma ta kasa;Hajiya ta taimaka mata,tad'ora kanta a kafad'ar Hajiya idanunta na rufewa da bud'ewa cikin azabar ciwo,cikinta na cigaba da hautsinewa ciwo na k'aruwa,da marar tayi wata irin murd'ewa sai ta k'ank'ame Hajiya tana Istirja'i da salati, tasake k'ank'ame Hajiya iya k'arfinta tayi wani nishi sai kawai taji wani ruwa me d'umi ya 6alle mata da kyar taduba sai taga jinine,cikin yan dak'ik'u zanin jikinta ya jik'e sharkaf,zata tashi jiri luuu...yayi awon gaba da ita ta zube a jikin Hajiya cikin d'aukewar numfashi.
Hajiya ta rikice tashiga jijjigata amma ko motsi ga jini na cigaba da zuba, saboda rikicewa sai tarasa me ma za ta matane?Tana cikin wannan halin Julaibib ya turo k'ofar yashigo.Cikin tsinkewar zuciya yake kallansu saboda ganin Sudaida da yayi kwance cikin jini male-male,k'wak'walwarshi bangaren tunani da adana bayanai yafara tariyo mishi shud'add'en abinda yafaru a shekarun baya lokacin da Bilkisu take kwance sam6al cikin jini fuj'atan.Dammm...yaji ruguzowar wani abu a k'ahon zuciyar shi"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un...baiyi wata-wata ba yasa hannayenshi ya cicci6eta cikin tashin hankali yayi mota da ita,Hajiya tabiyo shi.
Sun 6ata lokaci suna dubata sannan wata ma'aikaciyar jinya takirasu"kaine mijinta? Yajijjaga kai kawai.Tad'an kalli Hajiya sannan tamaida kallanta gareshi"yarinyar nan gaskiya tana mugun jin jiki kuma matsalar ta fi k'arfin mu,tunda sai an mata aiki kuma likita baya nan,to sai ku gaggauta kaita wani asibitin,irin wannnan zubar jinin idan yazo da k'arar kwana sai a rasa mutum."ALLAH yabata lafiya yasa kaffarace.
Tajuya tayi tafiyarta.Hajiya ta kalli Sudaida bata san wanda yake kanta ba.Julaibibi mu san abinyi mana.Idanun shi sun kad'a jawur,yayi wani huci cikin tashin hankali sannan yaba motar wuta,a guje yafito daga harabar asibitin suka fad'a kwalta zuwa wani asibitin.
Dasauri suka d'auketa zuwa d'akin agaji da taimakon gaggawa suma sun 6ata lokaci sannan likita tafito suka bi bayan ta zuwa office suna tambayarta me yafaru?Yajikin na ta?Ku kwantar da hankalinku.Tadanyi rubuce-rubucenta a katin data shigo dashi tagama taturashi a aljihun Labcoat d'in ta, sannan tad'ago cikin natsuwa ta kalli Julaibib"ka gane ko,matsalar matarka sai an mata aikin gaggawa, idan ba haka ba za ta iya rasa ranta,saboda ciki tasamu amma ya zauna a bayan mahaifa.
Shi da Hajiya suka kalli juna sannan suka kalleta cikin murna da mad'aukakin mamaki.Yayi yar dariya"ciki likita?Tajijjiga kai"eh ciki.Suka shiga tasbihi ga buwayi gagara koya dan furucin likita ya zo musu a bazata."Julaibib yayi sujudush-shukri.Likitar ta cigaba to amma an samu matsala dan cikin har ya fashe, abinda yasa take wannan serious bleeding d'in kenan (rupture ectopic pregnancy)kuma wannan aikin dole sai Gynea Doctor(likitar dake mu'amala da abinda yashafi lalurorin mata)kana...Julaibib yatari numfashinta"to ke fa?
Ni nan da dak'ik'u talatin zan shiga wani aikinne(operation) amma karku damu dan nayi waya da Doctor Kagarko itama kwararriyace yanzu haka tana kan hanya.Tabud'e dirowa tad'auki wani fallen littafi tayi rubuta sannan ta fad'a mishi adadin kud'in da zai biya,tamik'a mishi wannnan fallen littafin kaje kabiya kud'in sannnan kaje a d'auki sample d'in jininka idan yazo d'aya danata basai an siyaba. Yamik'e yaje yabiya kud'in,kuma yasa hannu sannnan yawuce aka d'auki jinin shi ana dubawa akaga yazo d'aya sai aka wuce dashi laboratory dan tantance sahihancinshi kafin ak'ara mata.
Doctor Khadija Aminu Kagarko tak'araso, matar me hankali da natsuwa ga tarin ilmi da ya ratsata,ta gaishe da Hajiya cikin girmamawa"ki mana addu'a Ubangiji yasa a dace.Hajiya tagyad'a kai"ALLAH ya amsa yar nan.Hajiya da Julaibib sunata kai-kawo bakunansu d'auke da addu'o'i tunda aka shiga da ita d'akin theatre,har akayi aikin aka gama aka fito da ita agadon marasa lafiya ana turata a hankali dan zuwa d'akin hutu,idanunta a rufe bata san in da takeba,ta d'ashe saboda rashin ishashshen jini,yasauke gwauran numfashi"Alhamdulillahi an tsallake tsirad'i d'aya na yin aikin cikin nasara,saura na farfad'owarta,ALLAH yasa tafarfad'o cikin hayyaci da lafiya.
A sanda rana tatafi zata fad'i magriba na shirin kunno kai Sudaida tad'an motsa da alama maganin da suka ba ta na anaesthetic ya fara sakinta...wucewar wasu dak'ik'u kuma tayi motsi da fatar idanunta sai kuma tad'an bud'e idanun tana bin Julaibib da Hajiya da suke rige-rigen yi mata sannu,a hankali bakinta yamotsa tana salati, sai kuma ta yunk'ura zata tashi,yarik'eta da sauri "Zaujatiii... kiyi hak'uri kinga aiki aka miki kar a samu matsala,takoma takwanta ta damk'i hannunshi tamau tafara kuka mara sauti saboda jikinta ba k'wari"ni dai ku yafemin mutuwa zanyi furucin a hankali yake fita muryar kamar bana taba, sai kuma tafara sambatu
"Dan ban haihuba sai a dinga min cin kashi? Ni zan ba kaina haihuwa? Shima autan Inna ai ina jin haushin shi dan bai kawo min agada ba,har madidi nace yasiyo min amma yak'i...Hajiya cikina ciwo yakeyi marata... wai...wayyoh Zaujiii...ni fa ba na san wannnan kallan na ka dan haushi yake bani...kai fa ran...da sauri yasa tafin hannun damarshi yatoshe mata baki dan kartayi kato6arar da zai sa shi jin kunyar Hajiya tunda ba a hayyacinta take ba kome ya d'arsu a zuciyarta fad'arshi za tayi.Ganin tak'i sakin hannun Julaibib dan yakira likita yasa Hajiya ta tafi kiranta"to fa tashin hankali gobarar gemu...
Magani a shaka badan yunwa ba.
Kome tsawon giginya daga k'wallo tafara.
2 Rajab 1441
25 February 2020
We Ibrahim's Daughters👇
Asdilat KD...2geda with Ra'ibs.
DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION
{Da Inganci Mukayi Fintinkau}
Bismillahi wabihi nasta'in.
...GWAJIN DAFI💔
Almost true story
Daga alk'alamin🖊
Ya'yan Ibrahim
Saudat A.Baba (Asdilat KD)
Da
Bara'atu Ibrahim (Ra'ibs)
Shafi na ashirin da uku.
Kwanakin su uku Doctor Khadija Aminu kagarko tabasu sallama dan Alhamdulillahi ta samu sauk'i, wata ma'aikaciyar jinya tana tsokanar Julaibib saboda yadda yadamu da Sudaida,lokacin ba da magani (medication)nayi idan basu zo ba da kanshi za shi yakira su"ALLAH dai yasa d'an daza'a haifa yamaka kara yayi kama da kai dan ba k'aramar hidima kayi ba.Yayi murmushi kawai yana shafa kwantaccen bak'in gashin kanshi.Mutan Zonkwa ma d'ai-d'ai kune wad'anda basu zo dubiya ba a cikin yan'uwa da abokan arzik'i.
Doctor Kagarko takalli Sudaida cikin kulawa"ki kula da kyau kinga aikine a jikinki,banda aiki bare d'aukar abu me nauyi okey?Sudaida tagyad'a.Tarakasu har wajen mota, Sudaida tashiga tazauna sannan ta rufe musu motar, tad'an sunkuyo ta taga"Hajiya ALLAH yakiyaye hanya. Madam adinga kula da dressing d'in wajen yadda yakamata, kidawo akan lokaci kar fa kiyi sakaci.Tad'aga hannu tana musu adabo,suma godiya sosai suke mata.Doctor Khadija Aminu Kagarko ta san ya kamata.
Julaibib da Hajiya su suka cigaba da kula da ita da ayyukan gida.Watannin Hajiya hud'u tafara musu zancen tafiya.Sudaida tawani marairaice"Lillahi warasulihi Hajiya yanzu sai ki tafi kibarni?Tagalla mata harara"to da ni zan tayaki zaman auren?Taware yatsunta hud'u watannina haka a gidan nan,ai ko na yi iya abinda zan iya.Julaibib yagama abinci yazubo musu a faranti"sannu da aiki Zaujiii...Yayi murmushi kawai,yashige bayi yahad'a mata ruwan wanka
"Sudaida ga ruwan can kije kiyi wanka.Hajiya takama fad'a"kai Julaibibi bana ce kadaina kai mata ruwan wanka ba?Ruwan kawai da za ta bud'e famfo ta tara sai an mata kai haba,tanuna shi da yatsa "kazama jarumi dan a haka nasanka.Sudaida tamik'e kaji matar nan da wata magana to ko wankan ma idan takama ba shi zai min ba?Tamata dakuwa"ungo nan,zancen banza kawai dan an miki aiki shikenan kuma ke bazaki dinga motsa jikin kiba? Sudaida tawuce batayi magana.
Ita kuma Hajiya tana dad'a jaddada mishi gobe Insha-ALLAH zan koma in da nafi wayau Zonkwa.Yagyad'a kai sannan cikin girmamawa yace"ALLAH ya nuna mana goben da ran mu da lafiya...mungode kwarai Hajiya ALLAH yak'ara nisan kwana me amfani.To amin kaga ai kai ka san yakamata,ita wancan matar taka ai bata gode min, niko ba in da zan fara azumin watan ramadana sai a d'akina. Kiyi hak'uri Hajiya bari tafito ai dole kuwa tagode miki.
Suka cigaba da hirar su har Sudaida tafito,yad'ago yana kallan surarta a cikin hasken farin watan daya haskesu"kinyi kyau Zaujatiii...Hajiya tagalla musu harara musamman Julaibib daya kasa daina kallanta,takad'a kai"ba shakka ai kinji sauk'i tunda kika iya zama kiyi wannan kwalliyar abin ma bai tsaya anan ba kikabi jiki kika shafeshi da wannnan shu'umin humran me k'amshin fita a hayyaci,to ni kuwa zaman me zan kumayi?
Sudaida tayi lallausan murmushi"haba Hajiyarmu ban fa sanki da halin sa'idawa ba,yanzu har wani kwalliya nayi?Ko unguwa ai zan iya fita a haka.Eh to in dai kai kikaci(hauka)ai bazan musa ba.Suka kalli juna ita da Julaibib tamishi wani kallo ta kashe mishi ido...Yakai hannu yana shafa kwantaccen bak'in gashin kanshi a hankali ya motsa la66anshi,Sudaida ta matsa kusa dashi"ni dai Yaya D'ansarai ban gane me kake fad'a da la66a ba gaskiya.Hajiya tamik'e"abin nayi ne to ALLAH ya tashemu lafiya.Sudaida tace kai Hajiyarmu yau da wuri haka zaki kwanta?Eh dan gobe sammako zanyi Julaibibi sai da safe.To Hajiya ALLAH ya tashemu lafiya.
Washe gari tun daga sallar asubahi bai shigo gidan ba sai da hantsi yadubi ludayi da kaya nk'i-nik'i,duk suka bishi da kallo har yagama shigo dasu sannnan yazauna suka gaisa.Hajiya tace"ai na zaci guduwa kayi saboda kar in tafi dama nace anjima kad'an tafiya ta zan yi ko kadawo ko baka dawo ba tunda duk wayoyinka a guda kabarsu. Mantawa dasu nayi sai da nayi nisa da tafiya sannan na tuna.Jos natafi na miki siyayyan tsaraba dana azumi.Hajiya tabi manyan ledojin da kallo tana jinjina k'ok'arinshi tare dasa mishi albarka"Ubangiji yayi albarka, yabaku masu muku madallah nagode nagode Julaibibi. Yayi murmushi"ai ba kome Hajiya, yad'an kalleta cikin natsuwa "na so kwarai da dakaina zan kaiki to amma hakan bazai yiwuba saboda yanayin aiki,yanzu ma Kafanchan zan tafi amma na ma wani direba magana k'arfe d'aya na rana zai zo kutafi,yasake bata wasu kud'ade sannnan yamik'e dan shirin tafiya Kafanchan.
Sabo turken wawa...kowa yayi fushi da bak'o ya ji kunya,da Hajiya tatafi sai taji gidan ya mata girma gashi shima Julaibib ba ya nan tagaji da nazarin da takeyi a cikin na'ura me k'wak'walwa ta rufe, tasa bayan tafin hannunta na hagu tana Isti'aza tare da rufe bakinta saboda hamman da tayi.Julaibib yashigo da sallama, yazauna a kujera a gajiye lik'is yacire riga yabar farar singlet. Sannu da zuwa Yaya D'ansarai.Ya aikin? Yafurzar da iska tabaki ta hanci"aiki ba dad'i kuma ba dama a bari.Wayyo! neman halali da wuya,kowa ga ganshi a inuwa tabbasss ya sha rana sannu Zaujiii...nah,tad'an shafa kwantacciyar gargasarshi"ubangiji yak'aro lafiya ta gangar jiki da natsuwar zuciya,tad'ora ha6arta a kafad'arshi,tagewaye hannayenta tana mishi tausa. Yasauke numfashi yana jin gajiyar data lullu6eshi tana tafiya a hankali a hankali"Shukran jazilan Zaujatiii...Yad'an bud'e idanun shi daya rufe yakalleta "kin cinye agadan?A ah ai yanzu kad'an nake ci dan yafara fita kaina.Yayi murmushi.
Kafin tagama abinci takawo mishi bawan ALLAH har yafara bacci sai da ta tashe shi tana mishi dariya"yau baza ayi nazarin karatu anjima ba kenan?Yayi mik'a yana salati"gaskiya yau ba nazarin karatun dazanyi,kin san tun a office nake gyangyad'i saboda baccin da kika hanani daren jiya.Takama ha6a tana yar dariya"Kai Yaya D'ansarai nice na hanaka baccin?Yagyad'a kai.Tayi yar dariya"au to shikenan ta kwana gidan sauk'i daga yau bazan kuma hanaka bacci ba shikenan ko?Yamata wannan kallan da bata so yayi bismillah yafara cin abincin data zuba mishi.Takauda kai tana k'unk'uni dan wallahi haushi kallan yake bata.
Ramadan wata me albarka,wata me alfarma.Tana kwance ta kifa fuskarta a cikin matashin,ya san ba bacci take yiba tsabar jin jikine kawai,tunda ko da da take ita kad'ai azumi wahala yake bata bare yanzu ga ciki,bataji shigowar shiba sai da yazauna a gefen gadon yadafa bayanta "Zaujatiii... Tamik'e zaune dakyar tana kallan shi bata da kuzari kona sisin kwabo.
yakalli cikinta yayi girma yanayinta ya canja gaba d'aya,tausayinta da k'aunarta suka mamaye ilahirin gangar jiki da zuciyarshi "Zaujatiii... Ki hak'ura da azumin nan mana,kinga wahala kike sha,barin had'o miki shayi kawai.Tawani marairaice "haba Yaya D'ansarai kalli agogo kagani k'arfe uku saura kwata na rana sai in karya azumi? Uh to menene ai kina da lalurane.A ah kayi hak'uri ai azumin ma ya kusa k'arewa tunda nayi ashirin to ai ko tara ko goman dasuka rage bazasu gagara ba Insha-ALLAH za k'arasa dani,nima ina kwad'ayin dacewa da daren"lailatul qadri".Yagyad'a kai"Toh ALLAH yasa mudace da wannan dare daya bambanta da darare dubu a daraja,ALLAH yabaki nak'uda kafiifan(me sauki) Tayi murmushi"amin Yaya Julaibib.
Yarik'o hannunta tamik'e suka fito waje suna d'an tattaki har zuwa bayan gidan in da sukayi yan shuke-shuken su kamar su alaiyahu,ganyan ogu, timatir,attarugu,zogale,d'ad'd'oya(scent leave)da sauran su, dakyar ta zauna a d'an k'aramin dakalin wajen tasa hannu tana tsinkar lemar kwad'i/naman k'asa(mushroom)ya tsuguna yana tayata tare da tambayar ta"yau kuma me za kiyi dashi?
Tun safe natashi da sha'awar shan romon shi(mushroom sauce) yad'an kalleta"ni fa yau a tsarin abincin mu ba shinkafa.Toh Yaya Julaibib,ni ma ba da wani abu zan had'a ba haka kawai zanyi romonshi in sha. Suka gama tsinka sannan suka wuce D'akin-girki yakar6a yawanke ya yayyanka mata, yad'uko kaskon suya yazuba magyad'a kad'an yad'ora a wuta sannan yakalleta"to na miki me wuyan zo kibashi tsoro. Tad'an kalleshi a marairaice nagode,to amma Yaya D'ansarai...sai kuma tayi shiru"uhun menene kuma?
Tanuna mishi abinda take so yayi.Yad'auki wuk'a da albasar yana mita"ni fa a duk aikin gida ba abinda yake bani haushi irin yankan albasa,tagyad'a amma kuma kafi kowa san albasa me yawa a girki,jiyama ai miyar albasar kasani nayi dayake ba kai kake yankawa bako? Eh mana...sukayi dariya yana fara yankawa idanun shi suka fara ruwa, yarintse su"Zaujiii...Karfa kayanke"eh ai kin san zan iya yankewa amma kika sani,da sauri yayi yagama yana fad'in"kai gaskiyar bahaushe da yace albasa batai halin ruwa ba, yawanke hannayen shi da omo,yanad'e hannu riga toh aikin dai aikine an ba kuturu tallan jakai"yad'auko abin markad'e(blender)ina karas d'in dana gyara d'azu?Ai na had'a maka lemun,yana cikin fridge.Yawarware hannun rigar"yauwa Zaujatiii...Kin kyauta nagode ALLAH yamiki albarka.
Yanzu barinje in yi alwala lokacin tafsir ya kusa,kuma yau d'in nan Insha-ALLAH nake tunanin zamu rufe sai ALLAH ya kaimu ramadan me zuwa ga masu tsawon rai.Toh Yaya Julaibib adawo lafiya, kuma dan ALLAH ana idar da sallar magriba ka dawo gida da wuri kasha ruwa,tazuba mishi dabinon ajwa a aljihu daya manta bai d'iba ba kaji Yaya D'ansarai?Yad'an dafa kafad'arta"Insha-ALLAH nagode Sudaida.Tabi bayan shi da kallo cikin yaba k'ok'arinshi da wata irin k'aunarshi da take dad'a narkewa a sararin cikin zuciyarta.
Safiyar sallah garin yayi lullumi a sanda hantsi yadubi ludayi ta yi k'ok'ari tagyara gidan da taimakon shi,ko ina yana k'amshin turaren d'aki, sassanyar iska tana kad'a fararen lubayen da ratsin ruwan hoda saboda rashin nauyin su.Tana sanye da voil-lace ruwan sararin samaniya(sky blue)doguwar riga dan d'aura zani wahala yake mata yanzu,d'an kunne,sark'a da warawaran hannayenta da zobe na zinare,suna ta d'aukar idanu saboda kyallinsu,ga jan lallanta me yarfin bak'i da tayi k'afafu da hannaye sun k'ara haskata,bata d'aura dankwalin kayan ba sai tayafa k'aramin mayafi ruwan sararin samaniya me shara-shara,gashin kanta yasha gyara daren jiya a wajen gyaran gashi da Julaibib yarakata.
Takoma D'akin-shak'atawa tazauna tana kallan shirye-shiryen wasannin sallah a tashoshi mabambanta aranta kuma tana mita"Yaya D'ansarai ya hanata tafiya gida taje tayi sallah a cikin Iyaye, yan'uwa da abokan arziki,sannan tun d'azu aka sakko daga masallacin Idi ya aiko a kar6a musu tuwon sallah shi da abokanshi kusan awa d'aya kenan,taja tsaki ai ko danko sukeci yaci ace zuwa yamzu sun gama ya shigo,a hankali tazame takwanta a doguwar kujera tacigaba da kallan amma ranta sam ba dad'i.
Taji ana sallama tare da k'wank'wasa k'ofa, taja malalacin tsaki a yadda taji dad'in kwanciyar nan data sani tabar k'ofar a bud'e koma waye tad'aga murya tace a shigo,tamik'e dakyar taje tabud'e, bakinta yak'i rufuwa saboda mamaki sai bin yaran takeyi da idanu,suma sunata tsallen murna sunzo gidan Inna Sudaida,za suci dad'i,yarik'o hannun wasu daga cikin yaran"kai kuzo kawai in maidaku wajen Iyayenku dama daga masallacin Idi natarkato miki su,ban tsaya tambayar kowa ba,yad'aure fuska ganin sunk'i motsawa"mitafi nace ko? Wasu suka mak'ale kafad'a, wasu har idanun su yaciko da kwallah.
Tarik'o hannushi"haba Yaya Aminu talek'o ta koma kenan,yagyad'a kai" eh mana tunda baza ki bamu hanya mushiga ba basai mu koma in da mukafi wayau ba?Oh dan ALLAH kayi hak'uri murna da mamakin ganinku ne yamantar dani abinda zan yi tun farko,tamatsa yaran sunata rige-rigen shiga,suka zazzauna suna tsallan murna wasu suna fad'in su sun dawo nan gidan Inna baza su wani koma Zonkwa ba.
Yaya Aminu naji dad'i wallahi,tazauna suna gaisawa tare yima juna barka da sallah ALLAH yamaimaita mana na bad'in bad'in bad'ad'a...tana tambayarshi mutan gida.Kowa lafiya k'alau Sudaida, mutuniyarki Nasmat ta bani sak'o yana mota,yakalli yaran sun baje suna cin abinci, hakanan zuciyata taraya min dama kaje wajen Sudaida, nace musu nan zanzo shine suka dinga rok'ona ALLAH annabi wai suma za suzo.Tayi yar dariya"ai kuwa nagode daka zo min dasu ALLAH yabar zumunci,dama kad'aici ya dameni.Yakalleta cikin tausayi dan cikinta ya girma"sai hak'uri kanwata,kafin mu shigo na ga Julaibib d'in mutane sun mishi yawa,na san haka kawai bazai kyaleki ke d'aya ba.
To Yaya Aminu kaci abincin mana. Yad'auki wayarshi yana duba sak'on karta kwana da aka turo mishi"ke ni dama kunu kika kawo min. Takalleshi wani iri "kai dan ALLAH wani irin kunu yau take sallah fa.Yamaida wayar aljihu"uhun ba a shan kunu ranar sallah ne kome? Yayi bismilah loma biyar yayi a tuwon sannan yad'auki cinyar kaza yad'an gutsira yamayar ya ajiye dan baya wani jin yunwa,ai kin san halina ni nama ba d'ad'ani da k'asa yayi ba, wannan sai su autan Inna kura kyaci da gashi,tad'an yamutsa fuska"to ai bashi kad'ai bane har da Yaya Musaddiq, yakama ha6a wuuu...au haka ne?Babbar magana ance da mak'asau bawa,barin kama bakina.Tayi yar dariya.
Julaibib yashigo aka cigaba da hirar dashi, ranar wunin farin ciki sukayi,sai bayan sallar la'asar Aminu ya kwashi yaran dayazo dasu cikin mota,Sudaida takawo musu cin-cin,nama da goron sallarsu,kowa ta bashi a hannunshi,sunata murna da rige-rigen fad'in" Inna Sudaida nagode,ALLAH amfana. Takalli Aminu"na rasa me zan baka rabin raina. Julaibib yadafa kafad'arta"juye mishi ragowar kunun safen nan yatafi yayi farau-farau dashi.Tagalla mishi harara,yad'an d'age gira yana mata wannan rikitaccen kallan na shi"eyehhh...ni kike harara?Kinga Sudaida Aminu yakirata,tabishi da kallo daina hararshi haka,yad'auko sak'on Nasmat data rufeshi da wrapping sheet me zanen zuciya da rafar kud'i yan naira ashirin guda d'aya"nawa goron sallar.Julaibib yasa hannu biyu yakar6a"toh Yaya Aminu mungode ALLAH yak'ara bud'i,ALLAH yabarka da Siddiqa tazama tauraruwarka har gaban abada.Yadda yayi furucin yasa sukayi dariya.
Sudaida tarufe musu motar itama tana godiya,Julaibib yasunkuyo"toh kagaishe mana da Hajiyarmu kace mata munanan zuwa mata yawon sallah ta ajiyemin dambun nama,tasa amin kilishi me tsomen aya,yanzu ma zan kirata in fad'a mata. Yad'aura belt yana dariya"toh kura duk kai kad'ai? Yaran sunata tsalle daga cikin motar suna d'aga hannu sunama su Julaibib adabo,a hankali yaja motar suka bi danjojin motar da kallo har tayi nisa tasha kwana ta6acema ganinsu.
K'arfe hud'u na yammacin asabar motar Julaibib ta tsaya a k'ofar gidan Hajiya.A D'akin-shak'atawa suka sameta tana waya,tagama tasauke wayar a kunnanta tana murmushi"lale marhabun,yau ina da manyan baki. Takalli Sudaida cikin tausayi dan ta kasa zama a kujera, zama tayi ak'asa tana matsa k'afafunta da suka fara kumbura alamar ciki ya tsufa wash...tafad'a tana yamutsa fuska"sannu Sudaida ALLAH yaraba lafiya.
Kai Julaibibi Sudaida tadawo kenan sai ta haihu ko?A ah jibi zamu koma ni bazan tafi in bartaba. Hajiya tagyad'a kai"madallah,to idan haihuwar tazo sai kuyi yaya?Hala ka ta6a kar6an haihuwa ne? Yashafa kwantaccen bak'in gashin kanshi"wannan karan dai zanyi,Hajiya bar wannan maganar kinji,ai haihuwar ma da saura,yad'an kalleta kuma ni gaskiyar magana"I can't do without Zaujatiii... besides me.
Bashakka Julaibibi zama da mad'aukin kanwa...ni dai na sanka me kawaici amma wannan matar taka me suffar takand'a ta fara koya maka rashin ta'ido ko?To kaji dakyau baza tabikaba,to me zata maka da wannan tsohon cikin?Sudaida tayi murmushi tana zancen zuci"lallaima Hajiya ni ce na koya ma Julaibib d'in rashin ta'ido?Yaya D'ansarai wallahi gwani na gwanaye ne bar ganinshi haka Ustazu-Ustazu baya san magana hummm... takyalkyale da dariya tuno abinda yagama fad'a mata daren jiya data keta wani sha mishi k'amshi dan ta karance tsabbb...da abinda yake so.
Tad'an turo baki gaba"Hajiya ai gwamma in zauna a suffar takand'a da dai in zama tashi da nishi...bakiji kirarin muba?Bena bakya tsufa sai dai kiyi girgiza ki sake sabon gashi,kuma waya jazamin wannnan k'aramin jikin idan ba ke ba?Takalli Julaibib"Yaya D'ansarai...Kasha kuruminka k'afata k'afarka ai tare ta gammu.
Yauwa Zaujatiii...tabashi hannu suka tafa, tad'an yafito shi zo kaji,yamatsa kusa da ita tasaita bakinta a kunnanshi tana rad'a mishi wata magana, suka kalli juna,yad'age gira yana nunata da yatsa cikin yar dariya"da gaske Zaujatiii...? Ta amsa kai tsaye"na rantse maka da girman ALLAH.Hajiya takama ha6a ba shakka"wato ana nuna miki ma'aiki kina rintse idanu,da wannan tsohon cikin kike wannan iya shegen k'auri da kare? Tawatsa hannu"to ai shikenan jiki magayi baki kuma mafad'i.Yamik'e barinje shago wajen su Baba"ke sai na dawo zamu tafi gidan Kawu ko? Toh adawo lafiya.
Yana fita Sudaida tamatsa kusa da Hajiya takalleta cikin natsuwa"Hajiya na rantse miki da girman ALLAH nima na fiso in zauna a nan sai bayan na haihu,toh kin san halin Yaya D'ansarai da banyi haka ba ni zai rufe da fad'a,kilama yace nina kira a waya na fad'a miki,saboda ni ma ina ta damunshi ya dawo dani gida,shi kuma yana cemin a ah acan zan haihu,dana fara nak'uda wai asibiti za mutafi, mutumin da a wasu lokutanma har na fara bacci bai shigoba.
Kin san halin miskilancinshi idan suka motsa, maganar duniyar nan za ki mishi,sai dai yamiki kunnan uwar shegu,yasunkwui da kai bazai yi magana ba ko da me za kiyi,yamaida mutum kamar wanda yaci kai(hauka)to Hajiya me zuwa fada ga banza bare kuma Sarki na kira?Hajiya tajijjiga kai"eh lallai kinyi hikima da siyasar rayuwa a nan, dama idan kasan mutum to sai kaci maganin zama dashi, barni dashi zai zo zamu sake tattaunawa.
Suna cin abincin dare kiranshi yashigo tad'aga da sallama,ya amsa muryarshi a dake"har yanzu kina gidan Hajiya ne?Eh Zaujiii... dama yanzu zan kiraka dan na jika shiru...yatari numfashinta"kin jini shiru,ke makauniya ce dabaza ki iya tafiyaba dole sai da d'an jagora ko?Tad'anyi murmushi wannan fad'an dawalakin goro a miya,ba mamaki taran dangi aka mishi akan dole yabarta anan,sai ta fad'a a tausashe duk shi d'in yace ta zauna idan yadawo za suje gidansu"Esbeer Yaya D'ansarai nahhh...ganinan zuwa.Hajiya takalleta"karki nuna mishi kin fahimci abinda yasa shi a damuwa,tarataya jakarta"toh Hajiyarmu mukwana lafiya. ALLAH yasa Sudaida.
Da sallama tashiga D'akin-shak'atawar, yakalleta a d'age yakauda kai.Bismillah,wash...ALLAH! tafad'a sanda ta zauna a k'asa dirshan tana maida numfashi kamar wacce gudun famfalak'i"Yaya D'ansarai na dawo. Yayi kamar ba dashi take magana ba,ganin haka tasama ma kanta lafiya ta hanyar kunna data tana turama A'isha sak'o,wucewar dak'ik'u kusan arba'in sannan yamik'e zaune daga kwanciyar da yayi yakira sunan ta.
Takashe data tana amsawa da na'am.Kishirya gobe da sassafe zamu koma. Gobe kuma?To saboda me?Hummm...ki bari kawai wai har da Baba a fad'a min ya kamata a barki,ni kuma bazan iya ba, Sudaida ko baza kimin kome ba to ni dai ina san zamanki kusa dani,yabud'e idanun shi daya fara rufewa gaba d'aya a kanta"Zaujatiii... ina k'aunarki ba tare da wani dalili ba,zan cigaba da k'aunarki a kowani hali da yanayi na rayuwa kingane ko?Tajijjiha kai"na'am na gane Zaujiii...ALLAH yabarmu tare,mutu karaba takalmin kaza.
Ta sauke numfashi to amma Yaya Dansarai... wani hanzari ba gudu ba,Baba da duk wanda yace kabarni anan umarni suka ba ka ko shawara?Yad'ago yakalleta"shawarace ba umarni ba.Tawani marairaice"to in ko hakane bai kamata kawatsa musu k'asa a cikin idanu ba "Yaya D'ansarai tsakani da ALLAH ba wanda zai so ya haifi d'a a cikinshi bayan fad'i tashin da yayi a rayuwar d'an nan har yazama abinda yazama a doron duniya,sannan wani abun yata so,su bashi shawara a matsayinsu na masoyin shi da suka fi kowa k'aunar shi bayan ALLAH da manzon ALLAH amma yawatsa musu k'asa a cikin idanu ta hanyar kin kar6an shawarar da suka ba shi ace ransu bazai sosu ba?Duk fad'in duniya duk wani me da'awar yana k'aunar mu toh daga bayane sadaka da karuwa,dan da Iyayen na mu basu maidamu mutane a sanda bamu da kome baza mu iya amfana ma kanmu kome ba to da bamu girman da duk wani me son mu ya so muba.
Tasake tausasa murya"Zaujiii...gyara kayan ka baya ta6a zama sauke mu raba,nima yanzu d'an mune a cikin cikina,to ai baza muji dad'i mu bashi shawara bayan mun maida shi mutum yak'i kar6a,bayan kuma shawarar bawai ta sa6ama shari'a bane"Yaya D'ansarai kayi hak'uri kabarni anan d'in,na tabbatar dan haihuwar farice,amma da baza su d'aga idanu su kalli rayuwarmu da abinda yake gaban muba, in dai bamu muka fad'a musu dan neman shawara ko kuma addu'a ba.Zaujiii...Aljannarka a k'ark'ashin Iyayanka take sai ka bisu ka kyautata musu zaka sameta fa.Tayi murmushi kasha kuruminka mijin Sudaida ni zan dinga zuwa maka hutun k'arshen mako(weekend)a 6oye,wallahi ba wanda zai sani sai Yaya Aminu dan na san ba zai k'i kawo ni ba.
Kalaman Sudaida gaskiyace wacce daga k'inta sai 6ata,zuciyarshi tayi wasai,d'aya daga cikin jin dad'in doron duniya samun mace tagari "Zaujatiii...Ke macen alheri ce,ALLAH yamiki albarka. Kiyi zamanki ba sai kin dinga zirga-zirga tsakanin Zonkwa da Gidan-Waya ba ni duk lokacin dana samu sarari zan zo ko a k'arshen mako ko a ranakun mako(weekdays)ALLAH yamiki albarka yabaki nak'uda kafiifan.
Yana had'a kaya a jakar da zaiyi tafiya da ita yana dad'a jaddada mata"Zaujatiii...kullum fa kisha ruwan zamzam d'in nan,kici dabino,ki yawaita addu'a ba dare ba rana,gobe Insha-ALLAH zan ai ko miki da hulba ki fara tafasashi kina shiga,da kinji alamun nak'uda ki d'ibeshi ki had'a da zuma ki cakud'a kidaure kishanyeshi kinji ko?Jikinta yayi sanyi sai take ji kamar kar yatafi,ko kuma su tafi tare tana lumshe idanunta mak'alallun kwallan da suka cika su,suka samu damar zubowa sharrr...yayi kamar bai gani ba,yagama shirya kome a jakar ya rufe yatafi yayi wanka yashirya cikin shigarshi ta dogaye fararan kaya kanshi da hular dara bak'a.
Yagama d'aure bak'in agogo a hannun damarshi,sannan yagewayeta yana magana cikin tausayi da k'auna"haba Zautajiii...kuka kuma! yafara share mata hawayen ai ke macen albarkace Sudaida,ban ta6a nadamar zama dake ba ko na sisin kwabo...haba Sudaidan D'ansarai...Ki k'arfafamin gwiwa kamar yadda ki kayi jiya mana,wannan hawayen na ki sai su sa autan Inna a uku fa...yacikata da kalaman k'auna da kambamawa... Itama ta gewaye shi tare da d'ora ha6arta a kafad'arshi
"Zaujiii... na yi shiru...ALLAH yamaka albarka. Yayi murmushi"amin.ALLAH yatsare min kai, yakiyaye ka da kiyayewarshi,tasa hannu tad'an shafa k'asumbarshi...wucewar wasu dak'ik'u sunata kallan juna, a hankali suka saki juna yad'auki jakar shi sannan yad'aga hannu yana mata adabo...Yajuya yatafi sai ta d'aga labulan taga tana cigaba da kallan shi yashiga mota yad'aura belt yayi azkar yasa mukulli yatashi motar...har yabar haraban gidan tana cigaba da kallan danjojin motar yayi nisa ya6ace ma ganinta sai taji wasu zafafan hawaye suna zubo mata sharrr...shar...tasaki labulan takoma ta kwanta cikin kewar masoyiii...
Shekaru goma sha uku kenan cifff...da auren Julaibib Abdullahi D'ansarai da Sudaida Ibrahim Me-Lambu. A wad'annan shekarun ALLAH ya zurta su da Ya'ya sanyin idanu da Bilkisu...kyakkyawar yarinya data d'auko kyan Iyayenta,bak'in gashi me yawa da tsantsi irin na mahaifinta, sannan ALLAH yabata farar fatar da bana Iyayenta bane ganin damar Ubangiji ne kawai.Bilkisu yarinyace data yi farin jini a zuri'arsu kaafatan,gata da natsuwa bata da yawan magana kamar mahaifinta,idan kaji dariyarta toh dashi suke magana, ga ta da k'wak'walwa duk abinda aka koya mata sau d'aya toh ya zauna kenan ba ta buk'atar maimaici,tana da kaifin basira.
Bilkisu Julaibib D'andarai...
Shekarunta biyar a yanzu haka tana primary one a makarantar boko,bangaren Islamiya kuma tana da haddar Izifi goma sha biyar daga Yasin zuwa nasi duk in da kaja mata Insha-ALLAH zata cigaba.
Sai Maimunatu Julaibib D'ansarai... kanwarta takwarar Inna suna kiranta Walida me shekaru uku.Sai kuma wani cikin da take dashi.
Julaibib ya d'auki son duniya ya d'orama Y'ayan nan musamman Bilkisu son ta yake kamar me, saboda dalilai masu yawa,na farko ya sameta a sanda baiyi zato da tsammani ba,na biyu tayi kama da Innarshi,na uku sunan marigayi daya so auren ta kamar me amma ALLAH bai k'addari za suyi aure ba,na hud'u Sudaidan da yake so yake k'auna ita ta haifa mishi,na biyar yarinyar akwai ta da k'wak'walwa da sauransu da sauran...
A gajiye lik'is yashigo gidan da sallama,suka gewaye juna tana mishi tausa a hankali yalumshe idanunshi wata natsuwa ta mamaye ilahirin gangar jiki da zuciyar shi "Zaujatiii...ta iya biyar dashi da lak'antar abinda yafi kwantar mishi da hankali,yad'an shafa kanta"nagode Zaujatiii...Takawo mishi ruwa yasha,sannan yaje yayi wanka yasa kaya k'ananan wandon chinos ruwan k'asa da shirt mara nauyi fara, yazauna yana hutawa,Sudaida tabishi da kallo.
"Zaujiii...kayi kyau,sai ka zama wani d'an matashin saurayi.
Yayi yar dariya"wani saurayi kina ganin Zaujiii...gemu da k'asumbarshi duk furfura...Ni dai a ah ai bawani tsufa kayi ba gaskiya,kai dai girman kawai kake so.Sudaida ai ko girma ya zo gasu Baba ga ku ga sauran bataliyar daza ki haifamin...Yaran suka shigo da gudu dawowar su daga makaranta kenan,suka haye jikinshi suna mishi surutu.Tace"Oya to muje ku canja kaya...sai suka dad'a mak'alewa a jikin Julaibib "ku tashi mana.Julaibib yad'aga mata hannu"kyalesu sai sunyi wanka zasu canja kaya. Tagyad'a kai tatafi tacigaba da ayyukanta.
Tana aikin abincin dare Bilkisu tashigo D'akin-girkin tasha kwalliya da wata yar rigar turawa mara nauyi ruwan hoda da dogon wando da d'an k'aramin hijab ruwan hoda,tanata k'amshin arabi'an perfume d'in Julaibib fuskarta shar da kwalliya,tayi murmushi kawai dan ta san aikin shine,haka yake zama yamata wannan kwalliyar musamman idan tamata laifi tace baza tayiba,shi kuma zai rarrasheta yamata.
Tafara ta6e-ta6e irin na yara"Mama in dai tuwo za kiyi ni bazan ci ba na fad'ama Baba yace to ki mana doya da kwai da nama,kuma ki had'a mana lemun citta da karas,ni natsani tuwo tana wani yamutsa fuska.Sudaida tajuya takalleta"ALLAH Hajiya Bilkisu?Bilkisu tagyad'a kai tana sake fuska 6ata ALLAH kuwan Mama.Tayi yar dariya"Hummm wato ke dai kullum aci me dad'i ko?Kalleki kamar za ki fashe duk kin fi kowa na gidan nan ki6a,toh yau tuwon dawa miyar kuka nake yi,kuma ba lemu tuwo za a ci asha ruwa.Tad'an buga k'afa cikin shagwa6a "ni dai ALLAH bazanci wannan bak'in tuwon ba,gidan Inna zan ce Baba yakaini ai ita zata bani nama,Baba yace ni ce amaryar shi tana nufin Alhaji Abdullahi,shi kuma zai bani madara da yoghort da biscuit short cake.Tagyad'a kai"toh a sauka lafiya ni dai yau d'an gado nake yi.
Tagama kome tagyara D'akin-girkin sannan tafito tasame su yana koya musu aikin gida da aka had'osu dashi daga makaranta amma Bilkisu tanata ta6ara shi kuma yana wani lalla6ata,suka bata haushi kamar ta dake su.Bata dai kula suba itama ta zauna tana nazarin wani project...Basu gama aikin ba amma da Bilkisu tamatsa a tafi sai kawai yabiye mata taje tad'auko mukullin mota yakalleta"Megado nan da gidan Inna sai munje a mota? Tawani shagwa6e"eh Baba.Yakar6i mukullin to shikenan.
Zaujatiii...Za kije ne?Idanun ta na kan Laptop d'inta ta bashi amsa"uh uh adawo lafiya. Yakalleta na wucewar wasu yan dak'ik'u" Sudaida yakiraya.bata amsaba tad'ago suka kalli juna said yawani kashe mata ido d'aya,takauda da kai kamar bata gane me yake nufi da hakan ba.Yayi d'as da yan yatsunshi"kin ci bashi wallahi.Tagyad'a kai"eh ba kome bashi ai hanji ne yana cikin kowa,kafad'i ko nawane zan biya.Yajuya ba fashi kuwa ina dawowa za ki bani.
Tana jin barar"Allazi wahidin...tabud'e k'ofa takar6i robar almajirin tajuye mishi tuwon tunda d'uminshi dan ta san ko sun dawo shima ba wani ci zaiyi ba,wanda za taci kawai tabari,yakar6a cikin rawar jiki data murya"Iya ALLAH yabiya buk'ata duniya da lahira.
Har bayan sallar Isha'i shiru basu dawo ba, taja tsaki ranta ba dad'i abinda yake ma yaran nan yana neman wuce makad'i da rawa fa,haka Bilkisu take mata wannan iya shegen k'auri da kare in dai tayi tuwo kai bama tuwo ba ko menene in dai bata ga dama ba to baza taci ba,sai tace ita wani abu na daban take so,tana ganin ya dawo zata fara shagwa6a ita yunwa take ji Mama bata ba ta abinda take so ba...
Shi kuma sarki me Bilkisu sai yafara fad'a shifa baya so ta dinga bar mishi Megado da yunwa tunda ba ta son wannan ba sai a bata wanda take so ba? Ai Bilkisu yarinyace sai da rarrashi wata rana za ta daina,wani lokacin su shiga D'akin-girki yadafa mata abinda take so baya wuce soyayyen kwai,ko taliyar yara(indomie)ko yoghort da donut, wasu lokutan kuma yaje yasiyo musu gasassun kaji ko nama,itama mayyar naman ce haka za su zauna suci su k'oshi,shi yasa kumatu a wajenta har da na sai dawa,to ganin haka itama Walida ta ara tayafa in dai tuwo ne to baza su ciba sai dai in baya gari ta musu jan idanu shine zasu d'an tsakura su bar mata..
Ita har ga ALLAH tana ganin wannan abun idan aka d'ore a haka to za a samu matsala fa,ace kome yaro yake so sai an bashi?Haka yake so su taso su basu san babu a rayuwa ba?Wasu lokutan ko fad'a take musu sai yawani 6ata rai alamar baya son hakan duk da bai ta6a furta wa ba to amma ai labarin zuciya a fuska ma ana ganin alama,shi yasa ita kuma in dai Bilkisu ce za tace ayi kaza to baza tayi shi ba,kamar yanzu da tace atafi gidan Inna, tana son zuwa amma tace baza taba,shi dai Bilkisu bata laifi a wajen shi kome tayi,idan tafara mata fad'a sai yayi murmushi"haba Zaujatiii...Bilkisuna guda nawa take ne? Ai za ta bari wata rana.Toh yaushe ne wata ranar bayan kullum k'ara wayau take yi,dad'a sabawa da hakan take yi?Itace dai tun yana d'anye ake tank'warashi idan ya girma bazai tank'waru ba sai dai ya karye.
Dare ya farayi tayi tsayuwar motarshi, yashigo da Walida tayi bacci ya kwantar da ita ya koma yakulle gidan sannan yad'auko Bilkisu,ai yana kwantar da ita tafara mutstsuke idanu sai ta mik'e zaune"Baba ina sauran nama na?Naman ki yana nan kuje kuyi bacci dare yayi sai gobe za kici abinki ko? Tamak'ale kafad'a ni dai a d'akin baccinka yau zan kwana...
Yayi kamar baiji abinda tafad'a ba.Sudaida tayi murmushi a ranta tana fad'in"yayi kyau... Tarik'o hannunshi"Baba a d'akin baccinka zan kwana dan ALLAH.Yagyad'a kai"yashafa kanta na ji Megadona,to maza aje a wanke baki, tatafi dagudu ta d'auko brush da maclean takawo mishi, yamatsa mata taje tayi tanata tsallan murna "yau tare da Baba zata kwana, yarik'e hannunta suka tafi. Sudaida taje takwantar da Walida ta tofeta da azkar d'in kwanciya tagama abinda za tayi tanufi d'akin.
Suna kwance tamak'alk'aleshi tak'i yin bacci tana bashi labarin yan makarantarsu da Inna dasu Kawu Aminu,tabisu da kallo Bilkisu wai lallai sai ya mata tatsuniyar d'an fulani me kiwon shanu dayaje birni.Yayi hamma yasa tafin hannun dama yarufe baki yana Isti'aza"ni dai gaskiya ban iya wannan tatsuniyar ba Megadona,dan ban san abinda yayi a birni ba. Takyalkyale da dariya tana d'an bud'e idanu dan mamaki" Baba ba kace Innace Mamanka ba? Yakalleta da kulawa"eh Bilkisu itace Mamana.Yad'an yamutsa fuska"amma bata baka labari ba?To gobe zan rakaka wajenta sai tabaka labari ai muma ita take take bamu labari,har fa da tatsuniyar gizo da k'ok'i. Sudaida tace"Bilkisu surutun ya isa tashi kije ki kwanta...Julaibib yatari numfashinta"kyale ta bata jin bacci ko Megadona?Tagyad'a kai a shagwa6e"ai haka takeyi idan ba kanan wai muje mukwanta.Haushinsu yakamata kawai sai tajuya"dan ALLAH ku kwana kuna hira.
Sak'onshi yashigo wayarta"Zaujatiii... Kar kiyi bacci fa...ina lalla6atane.Takashe wayar tayi kwanciyarta"kai ka sani.Sai da baccin Bilkisu yayi ni sa sannan yabita...yakunna fitilar wayarshi yana haske mata fuska,tasa hannu takare fuskarta sannan ta bud'e idanu"Zaujatiii baki ga sak'ona bane? Na gani. Tafad'a a taik'aice...Sudaida ta kin fahimce ni amma kika share ni kina ji Bilkisu ta tasani agaba.Tadad'a gyara rufa"uh ai duk a cikin lokacin tane, yaushe ko za a bar ranta ya6aci sarauniya me D'ansarai.Yad'an daki bayanta yana matsa mata hannu a hankali"yau haka kike jin fad'ar sunan nawa D'ansarai gatsau ba ko sakayawa?Tayi shiru kamar ba da ita yake magana ba.
Yagewayeta"to gani na zo a bani bashi na... duk da ranta a 6ace yake amma bata hanashi abinda yake so ba...shima ya fahimci haka shi yasa yake jinta wata ta musamman a sararin zuciyarshi, Sudaida ba dama ne wallahi,ta gama lak'antar shi,a cikin ruwan sanyi take hukunta shi sai yazo yana bata hak'uri da bakin shi dan a zauna lafiya...Yawani narke kamar k'aramin yaro"Zaujatiii... Ina k'aunarki fa I can't do without you.Batace kome ba tacigaba da bashi wasu sak'onni sai shima ya biyema yarima su sha kid'a...
A safiyar asabar yara sun sami hutun makaranta Sudaida tamatsa sai sun tafi Zonkwa dan watanninsu biyu basu je,tagama shirinta tsafff sannan tashiga d'akin...baki bud'e take kallansu da mad'aukakin mamaki baccinsu sukeyi hankali kwance ya lull6esu da bargo,tun d'azu fa tahad'a ruwan wanka za ta musu yace tabari zai musu taje tahad'a musu abinda za suci suna gamawa sai tafiya amma shine bayan fitarta suka koma su kayi kwanciyarsu,wato sune masu idanun jin bacci ko? Tayaye bargon tana tashinsu ya bud'e idanu,ta6ata fuska "haba dan ALLAH Yaya D'ansarai kai bakiyi wankan ba,su baka musu ba?
Yaziro k'afafunshi k'asa"kin san akwai sanyi ban san sanda baccin yasake awon gaba dani ba barinje in yi...tunda yashiga wanka ta san ko ya fito bazai musu ba, dan haka tatashi Walida taje tamata sai da tagama shiryata sannan ta tashi Bilkisu tamata tad'auko shadda getzner ruwan makuba yasha aiki da zare ruwan zinare da wasu k'ananan duwatsu masu d'aukar idanu saboda kyallinsu riga da buje da d'an kwali,tana ganin kayan tawani shagwa6e fuska wai ita baza ta sa kaya irin na Walida ba wanda Baba yasiyo mata dayaje Umrah doguwar rigar larabawa shi za tasa.
Sudaida ta dafa kafad'arta da sigar rarrashi"kisa wannan kinga anko fa za kiyi ke da k'anwarki, yanzu zan miki wannan kwalliyar sai kuyi Selfie da waya ta.Walida tayi tsallan murna"Yehhh...ni ma na iya tsayuwa da shan baki a selfie,Bilkisu ta ta6e baki ita yar gata haihuwar samu sai kawai tafashe da kuka tana bubbuga k'afa ita fa dole rigar larabawan nan za a d'auko mata.Sudaida ta tsare ta da idanu"idan ban d'auko ba fa?Kawai sai ta kwanta a k'asa tana burgima tana k'ara fashewa da kuka dan ta san Julaibib zai shigo...Haushi yakama Sudaida tagyad'a kai "lallai mugun gata asara,rashin shi kwata-kwata illah...
Tanunata da yatsa"ke Bilkisu ki rufe min baki.Bilkisu tacigaba da ihu da burgima tana kiran Julaibib"Baba kazo ka d'auko min doguwar rigar larabawan daka siyo min,Mama wai bazan sa ba. Sudaida ta kifa mata mari ba za a d'auko ba... taduba yar k'aramar dorinar ta take musu barazana da ita tarasa kawai sai ta jawo wayar caja tanad'e ta a hannu"baza kiyi shirun ba ko?Ga mamakinta kawai sai tagyad'a mata kai alamar eh.Ai batayi wata-wata ba shaud'a mata iya k'arfinta caraf a kan idanunshi.
Bilkisu tagigice dan taji dukan yadda yakamata tak'ara fashewa da kuka kamar zata shid'e, ya d'auketa ya zubama wajen data shaud'a mata idanu,cajar ta fito rad'am da kwanciyar jini a wajen toh jikin hutu ko ina lukwui-lukwui da tsoka ga kuma farar fata,yakalleta fuskar shi ba wal-wala"Sudaida baki da hankali kasheta kike so kiyi? Dan tace ga kayan da take so sai yazama laifin da har sai kin mata wannan dukan?An siyo kayan dan ayi meye dasu?Ya rufeta da fad'a kamar zai daketa,Sudaida tayi shiru tana zancen zuci"wai ita ce za ta kashe mishi 'ya saboda ta daketa sau d'aya.
Tashi ki d'auko mata rigar.Takalleshi cikin idanu"na rantse da girman ALLAH ba zan d'auko ba!Yashare ma Bilkisu hawaye"to fad'a min in da take in d'auko...Cikin fushi tace"wannan rigar haramiyar ta har abadan duniya wallahi.Shima cikin fushi yajuya rungume da Bilkisu"kar ki d'auko ki dafa kici...
Sharrr...sharrr wasu hawaye masu d'umi suka zubo mata akan Bilkisu suke wannan ja-in-jar da Yaya D'ansarai?Ranta in yayi dubu ya 6aci wai shi wani irin so yake ma wannna yarinyar da har zai ga laifin ta amma yakasa tsawatar mata?Wannan makauniyar soyayyace wacce daga k'arshe baza ta haifar da d'a me idanu ba wai Zaujiii...Shine yake mata wannan hayagagar...za ta kashe mishi 'ya... tadafa rigar taci tunda baza ta bata ba...taci kukan ta ta k'oshi tayi shiru tunani barkatai ya cika k'wak'walwarta...yawa-yawan Ya'yan da suke samun matsala a rayuwar su to hakan yana samo asaline daga irin mugun gatan da ake nuna musu tun zamanin k'uruciya.
Sai da hantsi yadubi ludayi sannan Walida tashigo d'akin cikin wata shiga ta daban riga da wando da k'aramin hijab yan kanti...ran Sudaida ya kuma 6aci wato fitan da yayi sababbin kaya yayafi ya siyo musu kenan? Walida takalleta"kingani Baba ya siyo mana wasu kayan?Tagyad'a kai"na gani Walida. Mama kuma na ce mishi ALLAH amfana... tad'an shafa kanta"yauwa Innarmu ALLAH yamiki albarka haka ake so duk wanda yabaki abu kisa hannu biyu ki kar6a kuma kiyi godiya...tayi yar dariya"wanda yagode sai ALLAH yak'ara mishi haka kika fad'a min ko? Eh Innarmu ashe baki manta ba.To nagode da kike rik'e duk abinda nake fad'a miki. Tad'anyi jimmm...sannan ta kalli Sudaida"Mama ita Yaya Bilkisu fa da Baba yakawo sai tace wai basu da wani kyau sai da yahad'a mata lemun tuffa da karas sannan ta yadda tasa...wai ita dai na Umrah nan take so,shine yace sai ya koma wata Umrah,damu zai tafi muje can muza6a irin wanda muke so da kanmu...
Walida... Suka jiyo muryar shi daga D'akin-shak'atawa yana kiranta,sai ta d'an bud'e idanu "Mama...Baba ne yace wai kizo mutafi na manta... tafita da gudu tana amsa kiran na shi.Takoma tayi kwanciyarta"da bata hak'ura ba baza suyi tafiyar ba kenan kome?Tayi k'wafa"wallahi abu d'aya zai sa tabisu dan tafad'a ma su Baba abinda yake yi, da ba in da za taje,gwamma ayi ma tufkar hanci,ai gabama da gabanta aljani ya taka wuta,ita baza ta iya cigaba da ganin kayan takaicin nan ba nama na jan kare.
Ko kallanta bai yiba,to itama a cikin fushi take dan haka ba wanda yakula wani har suka isa Zonkwa. Inna taji dad'in ganinsu sai ina za a saka ina za a aje takeyi da jikokinta haka suka yi wunin farin ciki.Bayan sallar magriba Sagir k'aninta daya yazama matashin saurayi takira yaraka ta wajen gyaran gashi har Julaibib yadawo basu dawo ba shima yazauna ana ta hira,Bilkisu Megadon Zinare an samu abinda ake so dafadukar cus-cus me nama da kayan lambu take ci,ga Baba ya kawo mata yoghurt tana taci tana sha cikin jin dad'i da kwanciyar hankali.
Sai wajen takwas da rabi suka shigo Sagir yasake gaishe dasu Baba sannan yamusu sai da safe,ita kuma taje tayi sallar Isha'i ta zubo abinci tanaci;yad'an saci kallanta tayi kyau sosai amma ko nahiyar da yake bata kallaba har tagama ci takai farantin D'akin-girki sannan ta dawo ta zauna tad'an kalli yaran"kutafi D'akin-shak'atawa ku kalli wannan shirin na Balarabe da bai iya gaza gurasa ba...Suka mik'e da Sauri"ehhh kuwan Mama...
Tad'an sunkwui da kai cikin ladabi"Baba ina son magana da ku.Yagyad'a kai"to Sudaida... Julaibib yayi wani huci"me wannan yarinyar take nufi? K'arar shi za ta kawo wajen su Baba?Ina jinki Sudaida me yafaru?Muryar ta tafara rawa alamar zuciyarta ta karye"ni dai Dan ALLAH Bilkisu zata dawo gidan nan da zama zan had'o kayanta... Inna tace"ashsha to me yayi zafi idanu za suci wuta har haka Sudaida?Inna kusan kullum sai mun samu sa6ani da Yaya D'ansarai a kan ta,wai d'azu da safe har yana fad'a min zan kashe mishi 'ya saboda na daketa,kuma agaban idanunta ya rufeni da fad'a kamar zai dakeni,Lillahi warasulihi Inna ace kamar Bilkisu sai abinda take so za a dinga yi a cikin gidan nan?Sannan ita ba ta laifi, ba ta kuskure kome tayi dai-dai be a wajen shi, wannnan abinda yake yi ya dace da tsarin ingantacciyar tarbiyya!?
Ni dai ta zauna a wajenku kawai.Inna ta numfasa to me yakawo dukan?Sudaida duka ai baya ba da tarbiyya sai dai yakangarar,ni ma ba na son duka.Wani haushi yamamaye ta wallahi mantawa tayi kuka takawo gidan mutuwa"ai kamar yadda Bilkisu take hantar Yaya D'ansarai to haka abun yake a wajen Inna son ta take kamar me,shi yasa ba gidan da take son zuwa kamar nan dan Inna tana biye mata ne,yanzu ma abincin daren ta daban tadafa mata.
Tasa hannu ta share hawaye"shikenan Insha-ALLAH daga yau ba ruwana da duk abinda Bilkisu za tayi ai ALLAH yagani bani da wani k'arfi ne dan haka zan kyamaci kome a zuciyata.Auna had'a idanu ya gallamata harara"ai dukan yayi yawa ne har ciwo kika ji mata to me zaisa bazanyi fad'a ba.
Baba yayi tsaiii...yana nazarin kalamansu d'aya bayan d'aya,yakad'a kai"Maimunatu wannan hukuncin na ki na adalci ne kuwa?Tsakani da ALLAH Sudaida ta fiku gaskiya;kar k'aunar yarinyar nan tarufe idanunku fa,idan an ciza to yakamata a hura...yanuna Julaibib"Malam D'ansarai da ilminka da girmanka amma kana irin wannan abun?Kiwo aka ba ka game da sha'anin Iyalinka fa,shi itace tun yana d'anye ake tank'warashi...kana nunama Bilkisu tsananin gata amma ba kwa6a to an yi ba ayiba kenan...an 6ata goma biyar bata samu ba,dan me za tayi laifi ba za a hukunta taba?Mahaifiyar tace fa idan ba a nuna mata abinda takeyi kuskure ne tun yanzu ba,to a gaba ma cigaba dayi za tayi,kuma duk fad'an da zaka ma Sudaida to na rok'eka da girman ALLAH kadaina yi a gaban Ya'yanku,hakan yana gur6ata tarbiyyarsu,dan ALLAH Malam D'ansarai idan rai ya 6aci to bai kamata hankali yagusheba kaji ko?
Yanuna ta"ke kuma Sudaida ba ke za ki yanke hukunci na rad'in kan ki ba kome ya miki,tunda shine ubansu shine a hakku a kansu dan shine shugabanku ke da yaran gaba d'aya.Ubangiji ya muku albarka,sannan duk yadda ranki ya6aci kiyi hak'uri dasu kinga banji dad'in furucinki akan Bilkisu ba,ke uwace bakinki amsashshene akan ta,dan haka ki janye wad'annan kalaman na ba babu ruwanki da duk abinda za tayi,ai kece kuwa me ruwa da tsaki yaushe za ki biye ta wani D'ansarai Ya'yanki kadararki su shiga garari,duk abinda ya kumayi ki bugo waya ni dake ki fad'a min zai sha mamakin yadda zanyi wallahi ALLAH kinji na rantse ko?
Kalaman Baba sun tausashi zuciyarta"to Baba nagode ALLAH ya k'ara girma.Inna ma tajijjiga kai toh na gano kuskure na kiyi hak'uri Sudaida ALLAH yamuku albarka,ku tashi kitafi gida dare yana dad'a yi,ta lek'a D'akin-shak'atawa duk sun yi bacci Inna tace suyi tafiyarsu kawai.
Suna zuwa gida taje tayi wanka tayi kwanciyarta shi kuma yatafi D'akin-girki zai dafa shayin na shi na fama taja tsaki sai kaje kayita sha...takwanta cikin tunanin tsohuwar soyayyar su..ita dai ta san da son Julaibib ta girma kuma ba tajin da wani abu dazai rage k'aunarshi a sararin zuciyarta,to amma wannan yawan sa6anin da saka fara samu ita tata k'arfin k'aunar ta zuciyarshi ce ta koma kan Bilkisu da kuma kud'in da yakeji yayi?Ko kuma giyar Ilmi da dukiyace tafara bugar dashi...!?
Tad'auki wayarta takira"Umma kiyi hak'uri na kiraki da daddaren nan wata magana nake so muyi.Ba kome me yafaru ne?Hawaye suka zubo mata"Umma ni da Yaya D'ansarai ne...sai kawai tafara kuka,Umma bata hanata kukan taba sai da taci ta k'oshi tabari dan kan ta...Umma tasauke numfashi "Sudaida kiyi hak'uri ni bazan shiga tsakanin ki da D'ansarai ba ai kunfi kusa,kuma ai ba a ta6a zaman tare ace wani bazai sa6a ma wani ba...fuskantar matsalolin aure irin wannan ai dole ne dan haka ki k'ara hak'uri kuma ki yawaita addu'a kome yayi farko yana da k'arshe...kuma in dai akan Bilkisu ne to fa dole sai kin kawar da kai...ba kome za ki nuna ya dame ki ba...ki dai kiyi k'ok'ari ki jata ajiki kinga ai tafi shak'uwa dashi ko? Eh Umma...to ko ni nan a yanzu nagano wasu kura-kurai danayi game da tarbiyyarku to amma har kwanan gobe ina godema ALLAH ina godema Mama wacce ba dan ita ba da kuma kun samu tasgaro dan haka ki natsu ki san abinda kike yi game da sha'anin tarbiyyarsu...
haba Sudaidan D'ansarai kika juya shi yayi wasu abubuwan da bai so ba sai kuma wannan za ki fara raki? Ki bi dashi ta siyasar rayuwa ko bai daina wasu abubuwan ba to amma ai za ki samu sauk'in wasu,Umma tad'anyi murmushi"taurin kan Bilkisu da kafiya kema fa haka da kike k'arama kinyishi,shi yasa bana miki da wasa...ita kuma sai abun yahad'u mata da gata...
Julaibib yashigo lokacin suna sallama da Umma.Yakar6e wayar"k'arata kika sake kaiwa,me kika fad'a mata?Abinda kunnuwanka sukaji.Yayi murmushi"ALLAH ko?Tajijiga kai"bawai...yashiga rarrashi"kiyi hak'uri Sudaidan D'ansarai ni ma na gane kuskure na,bai kamata ace Bilkisu ce zata shiga tsakanin muba,ai tare tazo ta ganmu,lallai ke macen albarka ce dakika jajirce dan ganin na dawo kan hanya nagode Zaujatiii...ALLAH yamiki albarka ya saukeki lafiya.Sai taji zuciyarta ta yi wasai"ta marairaice Zaujiii..to idan banyi hak'uri ba me zanyi bayan mun zama k'arfe da mayen k'arfe,mutu karaba takalmin kaza...?Hummm fushin masoya hutuhhh...
Rawa da k'afa d'aya sai gwani.
Da ba 'yan koyo da gwanaye sun k'are...
5 Rajab 1441
28 February 2020
We Ibrahim's Daughters👇
Asdilat KD...2geda with Ra'ibs.
DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION
{Da Inganci Mukayi Fintinkau}
Bismillahi wabihi nasta'in
...GWAJIN DAFI💔
Almost true story
Daga alk'alamin🖊
Ya'yan Ibrahim
Saudat A.Baba (Asdilat KD)
Da
Bara'atu Ibrahim (Ra'ibs)
Shafi na ashirin da hud'u.
Gobe zan tafi Sudan fa...takalleshi wani iri" haba dan ALLAH shine baka fad'amin ba sai da daddaren nan?Yagyad'a kai"ai dan ma mun shiryane da sai na tafi zan turo miki sak'o ni nawuce sai ALLAH yamin dawowa. Tad'an harareshi"gaskiya banji dad'i ba,ba fa abinda na shirya maka.Uh bakome kibani abinda yasauwak'a,kin san ni bana raina kad'an"da hanau ai gwamma mannau. Tare suka shirya kayan tafiyar.Washe gari jirginsu yad'aga.
A wad'annan shekaru goma sha ukun Julaibib Abdullahi D'an Sarai ya taka matakai da yawa a bangaren ilmi har ya zama shehin malami ferfesa gangaran(Professor)Yasai k'aton fili yana gina had'ad'd'iyar makaranta ta zamani bangare biyu bangaren addini da bangaren boko,aiki tuk'uru ake yi k'asa tanata cin kud'i,makarantace tun daga matakin prenursery,nursery,primary da secondary,abubuwa k'alilan suka rage mishi a bud'e makarantar,yana kuma da buri nan gaba yad'ora makarantar zuwa Jami'a me zaman kanta, yana kuma fatan makarantar tacigaba har bayan rayuwarsu,Ya'yansu su cigaba har jikoki...ta shahara har zuwa sauran k'ananan hukumomi da jahar Kaduna da d'aukacin sauran jahohin dake tarayyar Nigeria.
Abubuwan rashin jin dad'in da suka faru kuma shine tun bayan yak'in Zongon-Kataf da yak'in da akayi a k'waryar cikin Kaduna na k'addamar da shari'ar musulunci wani hargitsi da kisan rayuka bai kuma faruwa a k'aramar hukumar Zangon-Kataf ba,to amma a 'yan kwanakin nan manyan kabilun yankin Bajju da Atyap da sauran kabilu da basa sallah sun fara neman hana musulmai rawar gaban hantsi,takalan fad'a ba irin wanda ba sayi to amma bai damu hausawa ba,saboda duk fad'in doron duniya kowa ya shaida duk in da kaga musulmi kuma bahaushen mutum to ba wani abu yakai shiba face neman ilmi ta yadda zai bautama Ubangiji ba tare da jahilciba,sai kuma neman kud'i,kuma musulmi na da sauk'in halin da basa son tarzoma,wannan dalilin yasa suka d'an sararama hausawa amma ba hak'ura sukayi gaba d'aya ba,aka cigaba da zama cikin aminci da amana kamar yadda zuciyar bahaushe take a ko ina.
Tana kwance a d'akin baccinsu lullu6e da bargo tana chat da Nasmat,video call d'inshi yashigo ta d'aga da sallama,ya amsa da wani salo irin nashi yana murmushi"eyehhh... kaga Hajiya baki da wata matsala.Tayi yar dariya"godiyar Ubangiji a kowani hali da yanayi Zaujiii...Yagyad'a kai"ina yaran?Suna gidan Inna wai a can zasu kwana,yad'auki kofin gabanshi ya kur6i abinda yake ciki yamayar ya ajiye. Me kake shane?Shayi tad'an yamutsa fuska"asha lafiya.
Zaujatiii...Yakirata.Na'am.Nayi kewarki, bakya barina inyi ayyukan dake gabana,gangar jikina ne kawai a Sudan amma tunanina da zuciyata suna gida wajenki,gashi kwanakin basa sauri,anya ba visa za kiyi ki taho ba?Tawani marairaice"ni ma nayi kewarka,Yaya D'ansarai...Esbeer kaji?Kamai da hankali akan aikin da kaje yi,ai kamar yaune zaka dawo gida katarar da zuri'a da Iyalinka cikin k'oshin lafiya Insha-ALLAH,ka yi kwanaki goma sha shidda,saura kwana hud'u kacal ai...
Zaujatiii...na rantse miki da ALLAH daga shi ba wani kece duniyata,ina k'aunarki fa.Tagyad'a kai cikin gamsuwa da kalamanshi bawai shaci fad'i bane"ni ma haka Zaujiii...Ina k'aunarka a kowani hali da yanayi, baka da abokin tarayya a irin k'auna da soyayyar da nake maka"in poor and in rich,in sickness and in health...till death due part us''Yaja numfashi yafesar da iskar ta baki ta hanci"oh ya rahman...wani shauk'i da d'okin ganinta yamamaye shi...sun dad'e suna musayar kalaman k'auna sannan suka fara magana akan kud'in daya turo aka sai wasu kayan aiki na ginin makaranta.
Hantsi yadubi ludayi tashirya cikin doguwar riga kamfala,tatafi gidan Inna suna tattauna wasu al'amura daya shafesu,Abu me aikin da Julaibib ya d'auko ma Innar tashi tashigo da sallama ta ajiye farantin hannunta a gaban Sudaida tana tsokanarta "uwar biyu tashi kici kwad'on zogale na miki naga kwanaki biyu in dai kinzo abinda kike tambaya kenan, yau kuma naji baki tambaya"tamik'e zaune dakyar tana murmushi"nako gode miki Abu ba kad'an ba,sannu da aiki,tad'iba da bismillah takai bakinta, tafara taunawa cikin gyad'a kai "gaskiyar magana wannan k'uli-k'uli akwai d'ankaren dad'i da d'and'ano, tasa hannu a jaka taciro dubu biyu tabata"yaba kyauta tukwuici Abu.Abu takar6a tana godiya "madallah ALLAH yak'ara bud'i,yasaukeki lafiya... tad'anyi murmushi kawai,sai Innace ta amsa da" amin. Abu tajuya takoma D'akin-girki tana yaba halin kirkin zuri'ar Hajiya.
Bilkisu tashigo cikin shagwa6a ta rungume Sudaida tabaya"Mama kince za ki kira min Baba mu gaisa.Tad'an harareta"kin fa dameni idan nace na fasa sai ayi yaya dani?Asma'u da shigowarta kenan ta amsa dama me hali baya fasawa"wallahi abu me sauk'ine muyi k'uli-k'ulin kubura dake.Bata kula Asma'u ba tafara kiranshi,cikin d'oki Bilkisu ta manna wayar a kunne"Baba afqadtuka(nayi kewarka) Yayi dariya ALLAH Megadona?ALLAH kuwan Baba jiya ma nayi mafarki wai ka dafa mana naman talo-talo naci nak'oshi...tanata mishi shirme yana dariya... toh ni dai gaskiya idan bazaka dawo ba zan sa Kawu Aminu yakawoni in da kake ai yasan wajen ko Baba?Eh yasani.Ina Walida?Tatafi da Kawu Aminu siyo kindirmo a riga ni dai nace baza niba,shine wai yace idan suka dawo suma bazasu sammin ba,Baba kace Mama yau ta soya min dankalin turawa da kwai. Yagyad'a kai"to Bilkisu na har da lemun kwakwa ko?
Tajijjiga kai tana tsallan murna"zan rage maka har kadawo,yaushe zaka dawo d'in?Insha-ALLAH gadan bil-lail.Tawani fasa ihun murna Sudaida takwace wayar ta buge mata baki"ban hanaki wannan ihun murnan ba?Kawai ki cika mana dodon kunne.Inna tafara fad'a"nifa Sudaida ban san sanda kika 6aci da saurin hannu ba,tad'anja tsaki"haba ina amfanin irin wannan?Tayafito Bilkisu da hannu"zo nan muga bakin...yauwa kingani ko har ya fara kumbura.Sudaida tace"kiyi hak'uri Inna,Inna bata kulataba sai da tagama lalla6a Bilkisu ta daina kuka sannan ta kalli Sudaida"ya wuce amma a dinga kulawa... tayi murmushi"to Inna a ranta tana fad'in "wuuu na manta ashe hantar Inna nata6a a gaban idanunta.
Dawowar shi da kwana biyu ya tasata a gaba wai dole sai ta raka shi wata seminar,sun gama abinda za suyi suka wuce kasuwa yasai kayan wuta na mak'udan kud'ad'e da za a sasu a makaranta.Sudaida tayi tsaiii...cikin tafakkurin abinda za ta sai ma Yaya Aminu wanda zai burgeshi har yayi amfani dashi,saboda abubuwa da yawa basu d'ad'ashi da k'asa ba.Zaujatiii...tunanin me kike yi haka?Takalleshi"Yaya Aminu na rasa me zan sai mishi bani shawara"yayi murmushi"turare da kayayyakin da yake ayyukanshi dasu(artistry equipment) sune kawai zai yaba ko?Yauwa Yaya Julaibib wannan shawara taka ta samu kar6uwa nagode.
Bayan sallar Isha'i taje gida tasame shi a D'akin-shak'atawa yana shan fura da nono,ya maida ludayin cikin kofin yana amsa sallamarta"Sudaida kece haka da daddaren nan,ina autan Innan?Ta zauna a k'asa tana maida numfashi kamar wacce tayi gudun famfalak'i saboda nauyin da cikin ta yayi"su Bilkisu yatafi d'aukowa a gidan Inna,ni kuma nagaji da jiranshi shine nayi tahowata.Da sauri ya d'auko ruwa ya zuba a kofi ya mik'a mata,har ta kai tsakanin la66anta da bismillah yasa hannu yakar6i kofin"yi hak'uri ina zuwa,bulkodi(glucose D) yad'auko yazuba mata babban cokalin cin abinci d'aya a cikin ruwan yajujjuya sannan yabata,ta shanye duka,suka kalli juna suna murmushi"yaya a k'aro?A ah Yaya Aminu nagode kwarai taurarona.
Yazauna"da kinyi zamanki, kina kirana a waya ai kin san bazank'i zuwa ba.Yaya Aminu ba kome ai nima ina motsa jiki ne.Ya kalli k'afafunta da suka kumbura,har ranshi yaji tausayin ta"mata suna shan wahala da ciki fa,duk mace me ciki ai kana ganin yanayin ta ka san abin ba a cewa kome"lallai biyayya ga mahaifa dolen-dole ne ga duk mai son gamawa a doron duniya lafiya".Sannu kanwata to baza kije asibiti su baki magani ba? Tayi yar dariya ganin yadda yadamu dama haka yake nuna mata tausayi duk sanda suka had'u,tasa hannu tana murza k'afafun"wannan ba kome bane,ba shi da wani magani wasu suna yi yayin da cikin su ya tsufa wasu kuma ba sayi,duk cikina bai wani girma amma gashi na fara wancan makon ma naje an dubani kome nawa lafiya lau.
Yakad'a kai"toh Ubangiji yaraba lafiya.Amin Yaya Aminu nagode"ga wannan.Yakar6i ledan, yad'ago yana murmushin jin dad'i bayan yaga abubuwan da suke ciki "yanunata da yatsa duka na Aminu ne shi kad'ai?Tajijjga kai.Toh nagode ba kad'an ba"ALLAH yamiki albarka Sudaidan D'an Sarai. Sukayi dariya.Sun d'an ta6a hira har zuwa takwas da rabi sannan yace ta tashi yarakata gida dare ya farayi,suka jera suna tafiya a hankali suna magana har suka zo k'ofar gidan"shige gida kinji dare na dad'ayi ga hasken farin wata kar yasa miki mura.Sai da safe ko?Tagyad'a kai"ALLAH ya tashemu lafiya tabi bayanshi da kallo har yasha kwana ya6ace ma ganinta.
Ranar wata laraba a watan Rabi'u Awwal kabilun garin suka tashi da neman rigima ba wanda yataka ko ya zubar musu suka fito suka dinga zage-zage da k'one-k'onan tayoyi nan da nan gari yafara rikicewa kowa yatashi a wajen sana'arshi sai gida hankali a tashe, basu suka daina wannan abun ba sai wajen k'arfe d'aya na dare.
Sudaida ta sauke gwauron numfashi "Zaujiii...garin nan yafara bani tsoro,sallolin yau gaba d'aya kowa a gidanshi yayi bayan ga masallatai nan, amma saboda tsoron wasu marasa sallah an rasa wanda zai fita?To wai me aka musu? Yayi murmushi "kome zai wuce Insha-ALLAH gobe za a tattauna da Agwam Bajju (Sarkin Bajju) kin san shi mutumne me san zaman lafiya na san kuma zai ja musu kunne Kwanta muyi bacci kinji"gobe asubanci zanyi zuwa Gidan-Waya, har Sudaida tayi bacci amma shi idanun shi biyu yana tunanin al'umara mabambanta, lokuta da dama shima yanaji kamar yatattara yabar garin,to amma idan ya bar garin ai anyi gudu ba a tsira bane"gudun da ba a tsira ba kuwa kwanciya ta fishi".
Gaba d'aya zuri'arsu a garin suke Iyaye da kakanni,ai duk in da za shi dole dai sai ya dinga zuwa duba Iyaye da yan'uwa dan ya san mahaifanshi ba yadda za suyi su bishi ba,yasauke numfashi "zaman su a garin Zonkwa cikin wad'annan kabilu muk'addari ne tun daga Lauhul-mahfuz, k'addara ta riga fata,sai dai ya kamata suyi ho66asa dan suna so su fara musu cin kashi, shekaru kusan goma da suka wuce haka suka zauna cikin fargaba saboda fad'an d'aya 6arke sakamak'on k'addamar da shari'ar musulunci da akayi a Kaduna, a cewar su wai an kashe musu mutane da yawa a Kaduna dan haka suma za su d'auka fansa a kan musulman da suke zaune anan,tsawon lokaci haka suka zauna cikin tashin hankali,har dai kuma Ubangiji ya kawo k'arshen abun ba tare da sunyi kome ba...da wannan tunane-tunanen bacci yayi a won gaba dashi.
Sai dai cikin baccin na shi yayi mafarkin daya dinga na shud'ad'd'en shekaru"Kasham dai yau ma yasake gani cikin shigar Fulani kirar kalangunta ya fito rad'am kamar dai wancan lokacin amma idan tayi magana sai yaji muryar Sudaida...ya farka yanata nazarin wannan mafarki"toh me yak'un sane?...baccin da bai kuma komawa ba kenan har aka fara kiraye-kirayen sallar asubahin farko...
Hausa/Fulani Community Development Association(HAFCODA)Taza6i manya daga cikin su, suka tafi fadar sarkin Bajju,ya kuma kar6esu cikin mutuntawa, sun gabatar da abinda yakawo su,nasan zaman lafiya,da hak'uri da juna,shima Agwam Bajju a zahirance dai ya nuna 6acin ranshi"dan sanin asirin ciki sai hanji,ya kuma tabbatar musu su kwantar da hankalinsu lallai zai tsawatar musu ta hanyar yin gargad'i a dukkan majami'u(churches)ga wad'annan samari yan zauna gari banza masu son tada hargitsi,idan kuma basuji ba to lallai zai buga musu sandar shi(a al'adarsu idan har agwam Bajju yace zai buga sandarshi to duk abinda mutum zaiyi to ba zaiyi nasara ba)
Wad'anda ba son zaman lafiyar suke yiba suka had'a taron su.Shugaban nasu yabisu da kallo d'aya bayan d'aya"kunji abinda yake faruwa, dama hausawa masu san zaman lafiya ne tunda duk abinda muke musu basu ta6a mai da martani ba...toh ni dai kawai bana son ganinsu a garin mune,kome sune suke dashi sama damu sannan hakan bai wadatar dasu ba kullum aure mana Ya'ya suke k'arayi,wani abin takaicin ko da wasa baza kaga wata yarsu kace kana sonta zaka aureta ta yadda da kaiba,sai tace bata yadda ba tunda baka yadda da addinin taba,kunaji suna fad'a kakar za6e me zuwa zasu za6i mutum biyu daga cikinsu su tsaya takarar Chairman to kuna gani za su yadda su sake dangalama wani na mu k'uri'arsune?Yaja dogon tsaki"infact I'm sick and tired of seeing all those masu sallah bounch of idiot,we've to do something,something seriously againts them.
Wani daga cikinsu me rangwamen kafircin yace"da munyi hak'uri kawai ai mun riga mun zama d'aya,ga Ya'yanmu a cikinsu idan munyi yak'i mun kashe mazaje to yaya zamuyi da tarin mata da Ya'yansu?Nifa Ya'yana guda uku ne masu sallah.Cikin fushi shugaban nasu ya daka mishi tsawa"enough of this stupidity,so bloody what da Ya'yanka uku ne a cikinsu? Ko akwai 'yata a cikinsu na rantse muku zan iya kasheta, ba sune shegu masu kwad'ayin abin hannun hausawa ba? To da irin suma zan fara kisa,so dubu nawa suna wulak'antasu? Yanuna mishi k'ofa yana mazurai"now get out! Kai baka cikinmu.
Yasake bin sauran da kallo,suma shi suke kallo suna jijjiga kai alamar gamsuwa da matakin daya d'auka,fuskokin nan babu rahama da tausayi kona sisin kwabo,idanuwa jawur saboda shan burkutu da hayakin maro."nayi dai-dai?Suka had'a baki wajen amsawa"kayi dai-dai.Yakyalkyale da wata irin gur6atacciyar dariya da bata da dadin ji saboda giya da hayaki sun gama lalata hunhunshi"that's very good of you... Suka rufe k'ofa suna cigaba da k'usk'us d'insu na yadda zasu canja salon takunsu akan hausawa, d'akin ya kaure da dariyarsu dan sun gamsu d'ari bisa d'ari da matakin da suka d'auka...
Hankulan jama'a ya kwanta an cigaba da harkoki kamar yadda aka saba,sai dai kuma watanni kad'an a hankali abubuwa suka fara rinca6ewa za a koma yar gidan jiya,aka sake komawa cikin zaman d'ar-d'ar,basu da wani kwanciyar hankali, harbin bindigogi daga daji haka yake shigowa cikin gari ba dare ba rana alamar suna koyan harbi amma abun duka ba sanda da yake kuma dama bahaushen me ban haushinne na tanko me kan bashi,hakan bai d'ad'asu da k'asa ba,su dai neman halalinsu kawai. Mtswww ALLAH yakyauta.
Gidan shiru saboda yaran yanzu a gidan Inna suke kwana a duk ranakun k'arshen mako,Julaibib ya d'auko musu abinci,tamik'e zaune dakyar suka faraci da bismillah yana kuma mata bayanin aikin kafa ma'adanar littafai(bookshelves)da aka fara a d'akin nazari da bincike na makarantar (library)Tayi lallausan murmushi"Ubangiji yacigaba da rufa mana asiri duniya da lahira,gaskiya naji dad'i wallahi.Amin Zaujatiii...
Cikin firgici ta farka daga bacci a sulusin daren,wasu irin munanan mafarkai takeyi duk dare,har fargaba duk lokacin da rana tatafi zata fad'i magriba ta kunno kai,saboda da zarar ta kwanta baccin dare zata fara wannan mafarkan masu tashin hankali da sanya damuwa a zuciya.Julaibib yana zaune yana cike wasu bayanai a na'ura me kwakwalwa yaji motsinta,yajuya yana kallanta,tana zaune a tsakiyar gadon ta kama kanta da duka hannayenta cikin maimaita Istirja'i,rigar shimin dake jikinta ta jik'e sharkaf da zufa"Sudaida lafiya?Zafi kikeji haka?
Yamik'e barin kunna miki mukayyib. Takalleshi a rikice"Yaya D'ansarai ba zafi nake jiba,jikinta yakama rawa"kasan abinda nake gani kuwa?Wai...yatari numfashinta ta hanyar sa tafin hannun damarshi ya rufe mata baki sannan yakalleta cikin kulawa"ba wai bana so inji abinda zaki fad'a bane a ah ina miki kwad'ayin samun lada saboda bin umarnin Manzon ALLAH dan yayi hani da bayyana mummunan mafarki,duk abinda kike gani to ki nemi tsarin ALLAH akan abinda kike ganin,kiyi tofi a gefen hagunki sau uku"A'uzu billahi minashshaid'anir rajim "sai ki juya daga gefen da kika kwanta zuwa d'aya gefen.Wannan shine abinda yadace.Ta rungumeshi tana sauke numfashi"nagode da wannan tunatarwan.
Ranar wata Litini aka bud'e makarantar Julaibib a zangon karatu na farko me suna...
"Alfurqan Science Academy.
Musulman Zonkwa sunyi murna da farin ciki da samuwar wannan makaranta,Ya'ya dayawa an ciresu daga wasu makarantu an dawo dasu nan.Julaibib ya so kwarai ya zauna da Iyalinshi dan bata jin dad'i,sai dai hakanshi bata tadda ruwa ba dan da yammacin ranar ya mata sallama yakama hanyar Gidan-Waya washe gari da sassafe zasu tafi Jos asibitin k'ashi na Bima abokin karatunsune yayi hatsari a hanyar shi takomawa garin na su na Jos yakakkarye.
Sai k'arshen mako yazo,gidan Hajiya yafara zuwa kamar yadda yasaba,su Hajiya an dad'a tsufa sai dai Alhamdulillah tsufa me amfani tayi dan bata rikice ba,tana gane kome da kowa,sun dad'e suna hairarsu kamar yadda suka saba.Bilkisu kuma tagaji da jiranshi kamar yadda Sudaida tace mata ta zauna ta jirashi ba sai ta bishi ba ai zo.Tanata k'unk'uni tana turo baki gaba,Sudaida tana shiga D'akin-girki Bilkisu tasa dogon hijab d'inta har yana jan k'asa,wai haka sabuwar malamarsu ta Alfurqan take sawa,shine tace lallai itama haka zata dinga sawa Julaibib kuwa yad'inka musu ita da Walida kala-kala,tayi sand'a tafice da sauri.
Hajiya tana ganinta tace kai wannan yarinya da gaggawa kike hannun hagu a romo"sarauniya me D'ansarai ai ban ce zan rik'e miki uba ba.Julaibib yayi yar dariya ya tuno da Sudaida itace me fad'a mata haka musamman idan tana jin haushin su.Bata kula Hajiya ba tarungumeshi tawani shagwa6e"Baba tun d'azu kazo kayi zamanka anan.Yashafa kanta "Esbeeer Megadona yanzu zamu tafi.
Takalleshi cikin farin ciki"Baba yau Mama ta barni ni na had'a maka lemun karas,kashu da citta"kaji d'and'anon kuwa?Yagirgiza kai.Wallahi sooo luciousss...yadda tayi furucin yabasu dariya. Shima yace"thank you sooo very much my dear Bilkisu. Yarik'o hannunta suka mik'e"Hajiya barinje in sha lemun nan tunda sanyin shi. Bilkisu tad'an zaro idanu tana kallan Hajiya"ALLAH na mantane amma yanzu zan kawo miki naki dama Mama bata san nafito ba.Hajiya tace"tafi can sai yanzu kika tuna dani to bana sha.Tabi Julaibib da sauri da yasa takalmanshi yafara tafiya"ALLAH kuwan sai kin sha idan ba haka ba nima bazan kuma shan dabgenkiba.
Da daddare Julaibib yatafi kai Bilkisu da Walida hutun k'arshen mako gidan Inna,Sudaida tana shan rake taji tauuu...tauuu...tauuu...!k'arar harbin bindiga har tana hango kyallinshi ta tagar da take bud'e,raken hannunta ya su6uce, tarintse idanunta cikin matsanancin tsoro duk da abin ya zame musu jiki to amma na yanzu ya firgitata wallahi, tana Istirja'i yashigo da sallama yazauna yana kallanta"lafiya kuwa?Tad'ago tana kallan shi cikin mad'aukakin mamaki"kai bakaji harbin bindigar da akayi yanzu a jere har sau uku ba?
Yaya D'ansarai anya garin nan za a samu kwanciyar hankali a cikin shi? Yamaida kai da bayanshi jikin kujerar yana murmushi"matsoraciya kawai...Ta tsare shi da idanu. Yad'an kalleta" ke ba kome fa na...Ta girgiza kai"ba kome fa kace?Haka shekaran jiya danaje gida muna magana da Baba shima yace wai ba kome,to ni abinda bangane ba,a ba kome d'in me yakawo wannan harbe-harben ba dare ba rana?Anya ba koyan harbin suke yi ba? Baza kusa yan lek'en asiri su binciko muku me ake ciki ba Yaya Julaibib? Yaciro wata takadda daga aljihun gaban rigarshi da biro yafara lissafe-lissafenshi a ciki"to me kika ga anyi?Koma me sukeyi bata shafe muba...tayi shiru tana kallan shi aranta tanata maimaita Kalmar"kome sukeyi bata shafe muba... Yagama ya bud'e Laptop d'inshi yayi yan rubuce-rubuce a ciki ya rufe sannan ya kalleta"gobe Insha-ALLAH zani Kaduna mun tura kud'in kayayyaki amma har yanzu shiru tun wancan makon muke waya da manager na wajen amma sai wani hanya-hanya yake mana toh zani inga koma meye ganin idanuna.
Takalleshi wani iri ranta ba dad'i"nifa tafiye-tafiyen nan naka ya fara shigar min hanci da k'udundune wallahi,yana hanani rawar gaban hantsi, jiya fa yakamata kazo garin nan baka zo ba,na kauda kai banyi magana ba,yau kazo sai kuma gobe kace Kaduna za ka tafi washe gari da sassafe ka koma Gidan-Waya?A k'arshen makon ma baka hutaba?Ni gaskiya ban yadda ba shi Yaya Musaddiq d'in yatafi mana.Yayi yar dariya"Zaujatiii...uwar gidata anan duniya har a aljannah;ai ko Musaddiq yaci ya huta ko da yaushe shi yake tafiya,rabona da inje Kaduna saro kaya na kusa shekara fa,ko wannan karon bashi yace inje ba nine naga dacewar hakan shima yad'an huta...Kyan rawa da makar6i,amma kisha kurumunki Sudaidan D'ansarai ai na kusa ajiye koyarwar da nakeyi in dawo kan wannan makarantar gaba d'aya, kinga tafi-tafiye ya k'are sai mu manne kamar k'arfe da mayen k'arfe kullum muna tare mutu ka raba takalmin kaza ko?Yad'age gira yana mata wani kallon k'auna.Tayi shiru ta kyaleshi,dan wannan tafiyar da zaiyi ta 6ata mata rai sosai wallahi.
Shi kuma yacigaba da maganar shi duk da bata kulashiba,ai ya san tanaji tunda ba kurma bace,ranar litini d'inma bazan bar garin nan ba har sai munje an sake miki scanning ni wannan girman cikin yana bani mamaki a watanni biyar kacal.Hummm kawai tace tazame ta takwanta dakyar.
Da safe suna karyawa yazuba mata idanu yana zancen zuci ganin ta tsame hannunta a abincin wai ta k'oshi kuma ba wani cin kirki tayiba "wannan cikin gaba d'aya ya canja mishi Sudaida,ga yawan laulayi,ga rashin samun ishashshen bacci saboda munanan mafarkai,ga wasu k'ananan k'uraje da suka fito mata a duka la66anta ba irin magungunan da bata shaba dan su warke amma abin yaci tura,tayi sanyi sosai.A hankali tajingina bayan ta da jikin kujera tana yamutsa fuska"wash ALLAH!... Zaujiii...bakaji bayana ba kamar zai 6alle.Yafara mata tausa "sannu Sudaida. Tad'an kalleshi kawai.
Aminu yashigo da sallama shima yakalleta cikin tausayi"Sudaida ko asibiti zamu tafi ne? Tad'an yi luuu...da idanunta kamar zata rufe sai kuma takalleshi"Yaya Aminu sai gobe za muje.To ALLAH yaraba lafiya,yamik'a ma Julaibib hannu sukayi musafaha sannan yazauna suka gaisa da Sudaida. Suna hirarsu da Julaibib amma suna sakota,wani abun tayi magana wani kuma ta musu shiru. Aminu yamik'a mishi katin za6enshi(voters card)ni dai wannan karan bazan yi za6e ba,tunda ko ka za6a wanda kakeso to a k'arshen wanda su suke so shine sai lashe za6en da kuri'a mafi rinjaye,magud'i kiri da muzu haka ake yinshi.Bai wani dad'e ba yamusu sallama yatafi.Shima Julaibib yayi shirin tafiya Kaduna.
Yazauna a hannun kujerar da take kwance suna kallan juna na wucewar wasu dak'ik'u, tarik'e hannunshi"ban so tafiyar nan ba har ga ALLAH, ina ji ajikina kamar ba zamu sake had'uwa ba, idanunta suka kawo ruwa.Haba Zaujatiii...me yasa kike wannan furucin? Insha-ALLAH kafin magriba ai na dawo,sharrr...hawayen suka zubo mata,yafara goge mata"kiyi hak'uri Sudaida kome ya kusa zuwa k'arshe,kullum muna tare har sai kin gaji da ganina,yazame hannushi daga cikin nata,yamik'e yana gyara kwalar farar rigarshi"zo muje kawai kiyi zamanki a gidan Inna ko gidan Kawu idan na dawo sai in tsaya in d'auke ki.Uh uh ba kome idan naji bazan iya zaman ba to sai in tafi,tawani marairaice"
Tafiyar za kayi Yaya D'ansarai? Eh Sudaida ina 6ata lokaci gwamma inyi maza in tafi tunda ba kwana zanyi ba.Yasunkuya yabata sumba,tashafa k'asumbarshi sukama juna adabo.Har yakai k'ofa takirashi"Yaya D'ansarai...yatsaya cak sannu yajuyo "na'am Zaujatiii...suka sake zubama juna idanu na wucewar wasu dak'ik'u,tasauke gwauran numfashi a sanyaye tagyad'a kai "shikenan adawo lafiya.
A gidan Inna ma Bilkisu kuka tasa mishi ita bazai tafiba,ta had'a kai da bango tana sheshshek'a,dakyar shi da Inna suka dinga lalla6ata sannan tayi shiru ita da Walida suka rakoshi k'ofar gida tana k'ananan hawaye,yashiga mota ya zauna yana d'aura belt tarufo mishi motar"Baba ALLAH yatsare a dawo lafiya...Walida ta koma Gidan-Waya da gudu ita bata wani damu sosai ba.Tad'aga hannu tana mishi adabo,yaja motar yatafi,zai sha kwana ya leko tana tsaye, tad'aga murya"Baba Qad uhibbbuka... shima yamata adabo sannan yasha kwana yana murmushi furucinta"My dear Bilkisu kenan nima ina k'aunarki.
Tafiya yake yi amma yanaji kamar yajuya wajen Iyalinshi,ranshi ba dad'i har yashiga Kaduna garin gwamna,kiran Sudaida yashigo yad'aga da karsash"Zaujatiii...gani a garin gwamna.Nayi tunanin dama yanzu ka shiga.To ya jikin? Ya tambayeta cikin kulawa.Da sauk'i yanzu bana jin wani ciwo sai dai na yau da gobe kawai irin na mace me juna biyu,yanzu ma na idar da sallah walha,na kuma maka addu'a ALLAH yatsare min kai a duk in da za ka shiga,nima na rok'i ALLAH yarabani da cikin nan lafiya,yabani nak'uda sassauk'a,sannan nace barin kira D'ansarai mijin Sudaida inji muryarshi da kalamanshi su k'aramin nishad'i.
Oh ya rahmanu rahim...nagode ma Ubangiji da yabani ke a matsayin mata,ke macen albarkace,kece uwargidata har a aljanah,yasake yin k'asa da murya yana fad'a mata wasu kalamai wanda sirrin sune,tako kyalkyale da dariya"kai Ustazu...? Shima dariyar yake yi"na rantse miki da girman ALLAH Zaujatiii...Ko baka rantse ba na yadda da kai,ba abinda yake fitowa daga bakin ka game da soyayyarmu sai gaskiya"ALLAH yamaka albarka Abu Bilqisss...sai ka dawo d'in.Ya amsa da to sannan sukayi sallama ya zubama tashi wayar daya cire a kunne idanu,yayi lallausan murmushi yana shafa kwantaccen bak'in gashin kanshi"Ummu Bilqisss...ya fesar da iska ta baki ta hanci,sannan yasa wayar a aljihu.
Duk yadda yaso ya koma gida a ranar hakanshi bata tadda ruwa ba, sai dai sun gama kome da Manager,ashe daga can Lagos aka samu matsala amma kome ya dai-daita.Washe gari kuma wayewar gari litini yana shirin barin garin gwamma gari yarikice anata k'one-k'onen tayoyi da kisan rayuka na babu dalili,cikin damuwa Sudaida takirashi"ka riga ka taso ne?A ah.Sukayi shiru na wucewar wasu dak'ik'u"to ALLAH ya sauwak'e wai meye musabbabin wannan fad'an?Sudaida ai kin san idan guguwar siyasa tafara kad'awa sai dai Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un"
Tagyad'a kai"hakane,muma nan d'in sai a hankali,wallahi mutane dayawa suna ta kwashe muhimman abubuwansu suna tafiya wai sai angama za6e kome ya dai-daita sannan zasu dawo,Abu me aikin Inna ma yanzu tazo tamin sallama zata tafi k'auyansu, hankalin jama'a da dama yak'i kwanciya tunda sukaji Kaduna ba lafiya,yanzu mu kuma sai yadda hali tayi kenan?Ta tambayeshi.Eh Sudaida amma nan in da nake ba a kome sai dai ansa matakan tsarone ba shiga ba fita, amma Manager yayi waya da babban d'an shi sojane yanzu zai zo yafitar dani tunda dama rigimar a cikin garine.Ta amsa a sanyaye"to ALLAH yasa.
Tana zaune cikin tsananin tsoro da damuwa na rashin mafita Aminu yashigo"ke Sudaida ki d'auki abinda zaki iya d'auka me mahimmanci yanzu zamu bar garin barinje in dawo...ta tari numfashinshi "har dasu Baba?Yakoma ya zauna tun safe nake magiya da rok'onsu su shirya mubar garin"gudun hijira wajibi ne idan kaga ba dama ka tsere...inji Garba Super,sunk'i toh ni dai gaskiyar magana tafiya zanyi dan wuya ko da magani ba dad'i, sunce basu hana duk me tafiya tafiya ba su dai sunanan,barinje ATM ki zama cikin shiri kafin in dawo. A sanyaye ta gyad'a kai sannan tasake kiran Julaibib sai dai tak'i shiga tabi D'akin-shak'atawar da kallo"to me zata d'auka?
To suma da suka ankare mutanan garin suna tafiya sai suka tare hanyoyi ba shiga ba fita dan suna da wani k'uduri a zukatansu amma a zahirance fad'i suke ba kome ba kome,dole Aminu ya hak'ura.Bayan sallar la'asar wata motar roka shak'e da abinci da mutane hanya tabiyo dasu ta garin suma da gani ba tambaya yan gudun hijirane ko da wani gari suka fito? ALLAH masani.
Direban a rikice yake sunata tsayar dashi amma yak'i tsaya"wanda maciji ya sare shi idan yaga tsumma sai gudu...Kawai yayi k'undunbala zai bi takansu sai suka tarwatse daga tsakiyar titin ya wuce cikin tashin hankali suka rufa mishi baya, saboda rikicewa sai sitiyarin yakwace mishi,take ta daki sabon masallacin mak'era da ake kan aikin ginawa, kowa yayi ta kanshi dan sun kusa cin musu,suka fantsama cikin gari gidajen mutane a kid'ime,su kuma ganin wannan ya dad'a tayar ma da mutane hankali musamman mata.Sudaida tashiga D'akin-girki ta sauke abincin data d'aura dan bata da kwanciyar hankalin da zata iya k'arasawa dama tun karin safe bata kuma sa kome a bakin taba.
Takira Julaibib amma yana ganin kiran yak'i d'agawa a k'arshema yasa wayar a yanayin shiru (silent)saboda d'azu ta sake kiranshi akan kar yadawo, yabari ko zuwa gobe ne dan suma garin ya fara rikicewa, sai yace mata bazai iya ba yau d'in zai dawo yana ma hanya ta kwantar da hankalinta ba kome fa,kuma ta dafata mishi shayi,tayi abinci me kyau yana azumi kome dare bazai yi bud'a baki da kome ba bayan dabino sai abincinta ko da bai shigo kafin magriba ba,bai jira amsawar taba yakatse kiran ya kira Musaddiq yana tambayar shi"wai meke faruwane Sudaida ta dameni kar in dawo?
Yayi tsaki"kai rabu da ita,da da wata babbar matsala ai dana fad'a maka,sun d'anyi zage-zagen sune d'azu ko dak'ik'u talatin ba suyiba suka koma k'auyukan su,in dai wannan hatsaniyar ne yau suka fara?Ka san halin mata basa raina abin tsoro,watama cinnaka za kaga tanama ihu da kururuwa a zo a kashe mata kar ya cijeta.Uh uh Musaddiq sharri dai ba kyau...to suwaye suke ta guduwa?Julaibib yasake tambayarshi.Masu guduwa dama yan ciranine amma ni dai a ganin idanuna banga wani zaunanna gari daya tafi ko mutum d'ayaba.To ALLAH yakyauta.Musaddiq ya amsa"Amin D'ansarai ka iso lafiya.Da wannan dalilin yasa yak'i sake d'aga wayarta.
Sai da yashigo cikin gari sannan ya d'auki wayarshi zai tsokani Sudaida,sai dai missed call d'ari da yagani yasa zuciyarshi bugawa da k'arfin gaske kira daga kowa na zuri'arsu lambar Inna yafara kira amma tak'i shiga,fargaba ta kamashi lallai ba lafiya...
A bakin hanya kuma sunyi kaca-kaca da kayan dake cikin rokan sannan suka banka mata wuta.Me neman kuka ne aka jefe shi da kashin a waki,wai saboda yak'i tsayawa suka fara k'ona shagunan bakin hanya...ALLAH Sarki shagon Ashiru Chindo suka fara k'onawa...Mtswww bahaushe me ban haushi na tanko me kan bashi...wai sai a wannan lokacin suka san eh lallai wad'annan mutanan da gaske sukeyi,suka fara neman mafita a sanda lokaci yariga yak'ure musu, dan ba a fafe gora ranar tafiya...kumamar tsanyar da wuri take tila...Dana sani mara amfani...suka cigaba da k'ona tayoyi suna watsa borkonon tsohuwa(tear gas)wallahi abu kamar wasa k'aramar magana ta zama babba,garin yayi bak'ink'irin ga har6e-har6en bindigogi ta ko ina.
Yana cikin wannan hali kiran Sudaida yashigo yad'aga da sauri,cikin rawar jiki data murya tafara magana"Yaya D'an Sarai na rok'eka da girman ALLAH karka k'araso garin nan...me yafaru ne?Yak'i a keyi ka koma dan wallahi sun fara kashe mazaje suna k'ona gidajeee...tak'arasa maganar cikin sarewa saboda harbin bindiga shima yaji hakan jin kunnuwan shi.Kina ji? Ta amsa da eh ina...in...inaji...yana d'ago kai yaga gungunsu sun mishi k'awanya...zufa tasake karyo mishi Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un yafad'a,a wayar kuma yana jiyo hayaniya da surutai barkatai... wasu suna ihu wasu suna kabbara,anan kuma suna jiran fitowar shi"gaba kura baya siyaki.
Sudaida tafi gidan Inna Insha-ALLAH zan zo in sameku a can yayi jarumtar fad'a mata haka. Tarintse idanunta saboda a zaba wai...wash...uhhh... bazan iya tafiya ba wallahi!wai...ALLAH na!Tafara nishin azaba Zaujiii...nak'uda nake yi haihuwa zan yi...wai...Wayyo!Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un dan ALLAH ka yafe min Yaya Julaibib mutuwa zan yi!A ah Sudaida ba nak'uda bane cikin naki fa watanni biyar ne...wallahi shine bakaji marataba!Tayarfe hannu. Yasake d'ago kai yakalleshi basu k'araso in da yake ba dan sun san ba ta in da zai gudu,yaga abinda bai gani ba d'azu bindigogi AK47,pistol, shar6a-shar6an wuk'ak'e gayama jini na wuce,adduna,tayoyi da jarka wanda ya tabbatar fetur ne a ciki,ga nishin da Sudaida takeyi cikin tsananin ciwon daya had'u da tashin hankali,sai yaji wasu zafafan hawaye sharrr... sun zubo mishi"yanaji yana gani amma ba shi da damar da zaije ya taimaketa...
Sudaida kiyi hak'uri kiyi addu'a ALLAH yana tare dake,bata amsaba nishin azaba kawai take yi tana kiran sunayen ALLAH wai...ALLAH ka taima... bata k'arasa wasu suka shigo gidan.Wayyo! Yaya D'ansarai ga sunan...wani yad'auki wayar dama a k'asa take ta bud'e maganar"me D'ansarai ya isa ya hanamu yi?Zuciyar Julaibib tafara lugude...malam karka ta6a min mata yafad'a cikin k'araji.Yakyalkyale da dariya "matsoracin banza matsoracin wofi kaje ka 6uya kana magana ta waya,to idan ka isa kazo gidan na ka muyi gaba da gaba mana,I swear a gabanka zan zamu mata yankan rago kai ma mu maka,wawa kawai"filthy bastard...
"Wallahi ALLAH ya fiku...yasake kyalkyalewa da wata irin dariya"eh ALLAH ya fimu mu kuma munfiku kaga dai mune zamuci gari,kabimu a hankali dan zakara a rataye baya caara.Bazan biku ba wallahi.Yajijjiga kai"that's very good,mun shigo gidan ka dan muyi bincike ance kuma kunada bindigogi to amma tunda kace bazaka bimuba za muyi maganin taurin kanka, kuma duk inda ka6uya a fad'in garin nan sai an binciko ka an kawo min kai gabana na maka yankan rago kamar yadda muka fara yima sauran tsinannun yan'uwanka.
Yakalli Sudaida da take durk'ushe tana matagugu dafe da ciki,yayi murmushin mugunta"sai nayi abinda naga dama da wannan banziyar matar taka, ya kyalkyale da dariya.Kalamanshi suka soke Julaibib da Sudaida suk'ar wuk'a a k'ahon zuciya. Ambaton ALLAH takeyi a galabaice dan zuwa wannan lokacin k'arfinta ya riga ya k'are,d'an cikinta ya dunk'ule waje d'aya,wucewar wasu dak'ik'u kawai sai jini ya 6alle mata,tana kwance ko motsin kirki ba tayi,idanunta sun fara canja kala kad'an kad'an bak'in ciki yake 6acewa.
Yayi jimmm...yana kallanta,yayi d'as d'as d'as da yan yatsunshi sannan yagyad'a kai bayan ya kalli sauran da suma shi d'in suke kallo"tunda kin min buk'ulun abinda nayi niyya to kema baki da sauran amfani a doron duniya,yad'aga bindiga yana gyara kunamar jiki(trigger)zan fasa k'ok'on kan matarka D'ansarai...Julaibib yafara karaji karka kasheta dan girman ALLAH kabari in zo ni ka kasheni a madadinta... yakyalkyale da dariya wannan daga bayane sadaka da karuwa...shege d'an iska ai kowa ya tuba dan wuya ba lada"may her gentle soul rest in hell...suka had'a baki wajen amsawa da"amennn...Dai dai da har6e kanta da yayi tauuu...tauuu...sai biyu jini yayi kaca-kaca a jikin bango rai yayi halinshi,suka zuba fetur sannan suka sake harba bindiga wuuuhhh...wuta ta tashi suka fita da gudu wayar ta katse.
Julaibib yashiga cikin tashin hankali,ya tabbatar sun kashe Sudaida.Yayi Istirja'i yana kiran sunanta,ihun kiran sunan yasa wad'anda suka mishi k'awanya suka bud'e motar suna mazurai suka jawoshi "da uban wa kake magana tun d'azu a waya? Ko kana fad'ama sauran yan'uwanku masu sallah su kawo muku taimakone?To su zo d'in ba abinda zasu iya mana dan munfi k'arfinku har abadan duniya, yabisu da kallo duk fentin da sukama fuskokin su bai hanashi gane suba, wasu mak'otan shine,wasu ma akwai kud'ad'en da suke binsu bashi,bazato yaji an buga mishi bakin bindiga"you're very stupid ka tsaremu da idanu ba tambayarka muke yiba?Yarintse idanunshi dan yaji bugun har k'wak'walwarshi,bai gama dawowa dai-dai ba suka rufeshi da duka, naushi da mangari baji ba gani.
Wasu tarin matasan hausawa suka hango sun samu mafaka,abinda yasa suka bar dukan Julaibib kenan suka rufarma wad'ancan.Julaibib yamik'a hannu yajawo wayarshi data fad'i yasa a aljihu,dakyar yashiga motar yatashe ta yana gani dishi-dishi saboda jinin da yake zuba dan sun farfasa mishi jiki bana wasa ba,yana zuwa k'ofar gidansu yaci burki wani abu mara dad'i yatsirga ilahirin gangar jiki da zuciyarshi"ina Innarshi? Baba?Walida da Bilkisun shi!?Zuciyarshi tana bugawa da k'arfin gaske saboda ganin gidan ya gama k'onewa har ya rufta,ya tabbatar koma menene a gidan ya k'one bashi da sauran amfani a doron duniya.
Yafito daga motar yana jiri yana bin bango har yak'arasa gidanshi,yana cikin tafiyar ya yanke jiki yafad'i,awanni nawa yayi a kwance a wajen bai sani ba,ya farkane yaji mutane nabi takanshi cikin neman ceton rai, yarik'o k'afar wani"dan ALLAH taimakeni in tashi,yafizge k'afarshi"wannan rana ce ta kowa yayi ta kanshi,kalleni da kyau harsasai guda takwas ne a cinyoyina amma ina tafiya sai kai kana kwance babu alamar rauni me tsanani a tare da kai?Yayi gaba dan ALLAH kayita kwanciya har su zo su same ka a wajen...ai bai san da gaske zai iya tashiba sai da yaji hucin wutar da suka banka ya ta6i jikinshi.
Dakyar da sid'in goshi yak'arasa gidanshi nanma ya gama ci da wuta,wani wajen kuma da sauran hayak'i,yana shiga D'akin-shak'atawar yaji kamar an sa adda an sare mishi k'afafu saboda tashin hankalin abinda idanun shi suka gani. Wayyooo...!!! Sudaida ce ta k'one k'urmus,maik'on jikinta male-male a wajen kamar anyi 6arin mangyad'a,tabbasss da a waje yaga k'onannan gawar nan to ba zai gane Zaujatiii...ce ba! Kuka yak'wace mishi jikinshi da zuciyarshi suka d'auki rawa"yanzu irin kisan gillan da akama sauran zuri'arsu kenan!?da sauran yan'uwanshi al'ummar Manzon ALLAH? Yahad'iye wani abu me zafin gaske kamar garwashin wutan da aka barbad'eshi da dakakken barkono d'an munci wayyo! Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un!!!Lahaula wala quuwata illah billahil aliyul azim!!! Idanunshi suka kad'a jawur sai yaji kome yafice mishi a rai... zafafan hawaye suna zubo mishi sharrr...! sharrr...!
kira yashigo wayar daya manta da al'amarinta yacirota a aljihu Musaddiq...yad'aga da sauri yana fad'in Musaddiq sun kashe Sudaida sun k'onata ina sauran Iyayan mune? Suna ina?Kaima kana inane?Musaddiq ya amsa cikin tashin hankali "saurara kaji abinda zan fad'a maka dan tun d'azu nake gwada kiranka bata shiga sai yanzu.Sun kashe su Baba a masallaci, gidajanmu, Iyayanmu, matanmu da Ya'yanmu sun banka musu wuta kafin sufito su gudu!Musaddiq yafara kuka sai dai mu bisu da addu'a kafin wa'adinmu yacika,D'ansarai sunci k'arfinmu, sunyi galaba...!D'ansarai bamu da abinda zamu kare kanmu dan nima haka nafito daga gida hannu rabbana...dakyar furucin nashi yake fita... Musaddiq me yasame kane?Saurareni kawai Julaibib meye ma bai sameniba!?Menene ban gani ba?Yak'ara fashewa da kuka"a gaban idanuna akama Adnan da Sagir yankan rago...!!!
Kaiii ALLAH yatsinema arna...Julaibib k'afafuna a karye suke ga sara ba adadi a jikina,ga harsashin da suka harbeni yana cikin cikina...dakyar yake furucin Julaibib yadad'a manna wayar a kunnanshi dan maganar tashi k'asa take dad'a yi,kaima sunata neman ka ruwa a jallo dan haka ni shawarar da zan baka idan kasamu ma6uya to wallahi ka6uya,tunda ba abinda zaka kare kanka dashi...yafara tari da nishi duk tarin da yayi jinine yake fita ta baki ta hanci,yafara numfarfashi sama-sama, numfashin yana san d'aukewa,yafara magana a fizge D'ansarai mu yafema juna...abinda duk yake tsakaninmu na kud'ad'e da sauran al'amuran rayuwa duk mu yafema junaaa...!rayuwata...ta...k'are ina ji ajikina bazan kuma rayuwa a doron duniya ba!Cikina kamar ana huramin wutahhh...!!! Wai...washhh,Yayi nishi me k'arfi...jini yana zubowa tabaki ta hanci.. Ju...l...lai...bib...kumaaa...ina!yayi iya yinshi furucin yak'i fitowa yana nishi cikin tsananin ciwo...
Kaskon wuta me wuyar tallafa.
Na gaban wuta shi yake jin d'umunshi.