Tsaye Abdallah yayi yana bin Ramlah da ido yadda take hawaye yasa jikinsa ya kama rawa, Yana jin wasu kalamai daga bakinta lokacin daya shigo masu kama da almara,yana jin furuci mai kama da rabuwarsa da jiddah....zuba hannu yayi a aljihu ya tsaya tsakiyar parlorn yana kallon Ramlah ...da sauri ta share hawayenta tayi murmushi kanta a kasa ta soma gaishesa "ina yini sir Abdallah"
"Lafiya... menene kike hawaye haka?ina gab da shigowa nakejin wani furuci masu kama da almara daga bakinki,ko zan iya sanin me kike fada?"
Ya zuba mata kyawawan idanuwansa da suke kara narkar mata da zuciya, girgiza kai tayi tana wasa da gyalenta kanta a kasa "babukomi magana ce mukeyi da ummah"
Cikin takaici ummah ta amshe "ki fada masa abinda kikasani karki boye masa saboda hakan cutarwa ne,tunda dama ga halin da muke ciki da iyayen yarinyar gara ki sanar dashi mu nemi mafita"
Girgiza kai ramlah tayi "ummah...ina gudun matsala banason abinda zai shafi auren jiddah. Domin itadin yar uwatace ina matukar kaunarta"...tana gama maganar ta zamo ta durkusa gaban Abdallah "dan allah kayi hakuri ka yafewa jiddah...kada hakkin aure ya kamata inason yar uwata"
Sai hawaye,saukar da ajiyar zuciya yayi,"a halin yanzun nida jiddah munkai matakin da iyayenta suke bukatar raba aurena da ita,wata kil hakan alheri ne dikda inajin sonta cikin zuciyata...babu abinda ya canja daga soyayyar da nakeyi mata,abu daya ne yajzun inaso insan me nakeji sama sama lokacin da nashigo...ki taimakeni ki sanar dani"
Hawaye ne suka zubowa ramlah tasa hannu ta share,ummah ta katseta "kina tunanin sanar damu abinda ke faruwa?kina ganin duniya zata zageki idan maganar ta fito ko?to kisani babu wanda zaisan da maganar nan saini da Abdallah"
Kallon gefen su rumaisa ummah tayi"ku shiga ciki"dik suka mike jiki babu kwari rumaisa bataso hakan ba taso a fadi komai suni,...afee kuwa bugun zuciyarta da furgicin da ta shiga yasa miyaun bakinta ya kafe motsi kwakwara ta kasayi balle ta mike ta shiga daki kamar yadda ummah tace"kece bazaki tashi ba? saina ci ubanki?"sai lokacin afee ta dawo hankalinta,da kyar ta mike jikinta na rawa,mamaki da al'ajabin Ramlah takeyi dama Haka duniya ta lalace?haka rayuwar ta koma?....jikinta na sassarfa ta mike dakyar take takawa tayi hanyar dakinsu.....
Juyowa ummah tayi "umhmmm ina saurarenki"
"Tun farko jiddah ta sanarmun da cewar Abdallah baida lokacinta,don haka ita zata soma hulda da mazan waje tunda komai tayi shi zaa rubutawa zunubin"
Wani irim zabura Abdallah yayi kamar mayunwacim zaki jikinsa na kyarma zufa kawai ke kwarara jikinsa kamar ana watsa masa ruwa jikinsa kamar ansa masa shocking....
********
Cikin sauri Bilal ya fito daga motarsa,ganin yayan jiddah a kofar gate tsaye yana danna waya ya karasa ya mika masa hannu cike da ladabi...
"Barka da yamma"yace yana kokarin mika masa hannu su gaisa,
Kallonsa yayi kamar ya taba ganin fuskar,"barka dai...ya aiki"
"Lafiya lau alhamdulillahi...."
Shiru ya biyo baya kansa a kasa yaya ibrahim yace "yadai...waye kake nema ko kana tambaya ne?".
Gabansa ya fadi,to me zaice masa?yazo wajen jiddah ko yaya?sosai keya yayi "ummm... nazo wajen jiddah ne"
Da sauri ya ya Ibrahim ya dubesa "tou daga ina kuma?a ina kasanta"ya kara jefa masa muguwar tambaya a karo na biyu,
Wani mawuyacin miyau bilal ya hadiye,gaba daya ya daburce "ehh ni abokin mijinta ne, Ina son magana da ita ne dama"
Shiru yayi yana kallom bilal tabbas shine wanda ya taba sauke jiddah a kofar gidan nan tace abokin mijinta ne"babu laifi mu shiga ko?"
Wani sanyi ne ya lullube bilal babu musu yabi bayan yayan jiddah har parlorn da suke sauke baki sanan ya wuce ciki ya barsa,
Zaune take tayi tagumi gaba daya tunanin bilal ya hanata sukuni,tunanin yadda zata ganshi takeyi ibrahim ya turo kofa "kinada bako a parlorn baki"..gabanta ya fadi,kasa tambayarsa waye tayi sai kawai ta sadakar da kila wani dan uwan Abdallah ne zaizo neman sulhu,hijab dinta dake rataye gefen ta ta zura ta fito....
Turo kofar tayi hade da sallama,suna tozali da idon juna ta kasa karasa sallamar kallonsa takeyi cike da mamaki da yadda akayi yazo har aka barsa ya shigo wajenta,to me yace musu?
"Karaso mana kika tsaya daga nan lil sis"...
Babu musu ta shigo kafarta na hardewa ta nemi gefen kujera ta zauna...yadda ya zuba mata ido yasa ta kasa sukuni ta sunkuyar da kai kirjinta bai bar bugawa sama sama ba,ita yake kallo tausayin ta ya lullubesa baiwar Allah batai saar miji ba,gashi yana hango tsantsar soyayyarsa a kwayar idonta....shin yanzun sanar da ita zaiyi shi din waye koko?idan be sanar da itaba tabbas lokaci yana gab da kurewa don ya tabbatar da ko ramlah bata fidda video ba tana can tana kokarin kashe mata aure,
Cije lebe yayi "barkanki da wanan lokaci"
Dakyar ta tattaro natsuwarta waje daya zuciyarta bata bar bugawa ba "barkan ka..."
Murmushi yayi "ina iya hango tsantsar mamakin yadda akai nasan inda kike ko?"
Gabanta ya yanke ya fadi,ta kasa magana sai kallonsa da tayi ta sadda kanta..."and kina kara mamakin yadda akayi na shigo gidan nan yayanki ya bari ko?"ya kara jefa mata tambaya cike da izza,
"Tou ba abun mamaki bane,idan na kwakulo ainihin gidan iyayenki na gaskiya...ba kuma abin mamaki bane idan nasan wancen gidan da nake zuwa gidan mijinki ne"
Wani zabura jiddah tayi tana kokarin mikewa ya dakatar da ita "kada ki mike...kada kije ko ina jiddah....yanzun ma na shigo gidan nan kai tsaye saboda na sanar da yayanki nidin aminin mijinki ne"
Zaro ido tayi tana kallonsa ido cikin ido...kallonta yakeyi yayi murmushi mai ciwo "kwarai dagaske nidin aminin mijinki ne bilal....wanda mijinki yake kira da man"
Zumbur tayi ta mike wanan karon jikinta na rawa tamkar an zuba mata shocking....."innahlillahi wa innah ilaihi rajiun"ta furta a fili tana girgiza kai,
Kujera ya nuna mata"ki zauna jiddah.....lokaci yayi da zan sanar dake nidin aminin mijinki ne,kuma dan uwansa wanda dik abinda yake faruwa tsakaninki da mijinki ina sane dashi"
Wani abu ne ya taso ya tokarewa jiddah kirji...nan da nan idonta ya kada yayi jajir bugun zuciyarta ya tsananta....
"Kanaso kacemun kasan ni matar aurece kake muamala dani?kanaso kacemun kenan kasan Ramlah kawata aminiyata wadda itace ta hadani da kai?"hannu tasa ta toshe bakinta kuka na neman kwace mata,
Gyada mata kai yayi "nasani jiddah...amma inaso ki yanke alakar kiran Ramlah da aminiyarki yar uwarki fyace maciyiya amanarki wadda take gab da kashe miki aure a yanzun haka,wadda take barazanar fidda video dina dake a lokacin da nake shan bakinki ina wasa da nipples dinki"
Wata kara jiddah ta saki wadda tabbas da akwai mutane wajen parlorn sai sunji"ya isheni haka....banason jin komi bilal...me kake fadamun kamar wanda yayo shaye shaye...wasu irin kalamai kake kokarin fadamun da suke barazana da tarwatsamun zuciya?"
Girgiza kai yayi cike da tausayin jiddah...zamowa yayi daga kujera ya zuba gwiwoyinsa a kasa yana kallonta cike da tashin hankali"ina sonki jiddah.....inda bana sonki bazanyi kokarin shiga wanan riskin dana shiga ba dan kadan ya rage duniya ta soma kallona da naci amanar abokina....nayi hakan ne saboda tabbas da wanine kike muamala dashi da tuni ya taka martabar aurenki ya kwanta dake"hannu jidda tasa ta shararawa bilal mari "me kayi kai?me kake shirin fadamun?kana kokarin fadamun cewar kai bakayi kokarin hakan ba?kasan kai aminin mijina ne kasa na fada soyayyarka?bilal ka cuceni.....wallahi ba ramlah bace ta cuceni kaine ka cuceni"ta fashe da kuka tana ja da baya,
Idanuwan bilal sunyi jajir yake kallonta,jikinsa rawa yakeyi meyasa jiddah bazata saurare sa ba?
"Ki saurareni jiddah... nasan haka zata faru kuma zaki tsaneni amma kafin ki tsaneni ya dace yanzun kiyi bincike kisan wacece ramlah aminiyarki dake kokarin mallakar mijinki a halin yanzu,wadda ta shirya fuskantar ko wani irin yaki don samun cikar burinta?....idan nabar nan zanje in sanar da iyayena komi da nayi dikda bansan da wace fuska zasu kalleni ba amma nasan iyayena sunsan koni waye"jikinsa na rawa ya mike....
Kallonsa takeyi parlorn na juya mata....dafe kai tayi tana wani irin kuka wani irin tashin hankali ne wanan ke shirin tunkararta?waye ya ja mata? Abdallah...ko bilal koko aminiyarta Ramlah?meyake shirin faruwa da rayuwarta a Aurenta na fari?da kuruciyarta?....
Tausayin jiddah ne ya lullube bilal ...shi kansa kasa jurewa yayi yana kokarin takawa yana hawaye ya tsaya kadan neda da ita ya soma magana....
********
Kuka sosai Ramlah keyi bayan ta sanarwa da Abdallah komi dake tsakanin jiddah da Bilal da chat din da sukeyi har dare....
Abdallah bakim ciki ne da zuciya yasa ya kasa magana,ummah ta shiga tafa hannu "kagani ko abinda nake fada maka,ni dama haka rayuwata take inhar na tsani mutum to tabbas idan aka bincika wanan mutumin ba mutumin arziki bane,wanan yarinyar zata aikata abinda yafi haka"
Dakyar Abdallah ya motsa bakinsa yace "biri yayi kama da mutum,no Wonder bilal yaki tako kafarsa zuwa gidana,no wonder bilal ya kasa fitowa daga cikin mota a airport yana gudun suyi wani abun da zan fahimci suna tare shida matata....aminina ke cin amanata da matata?aminina ke rungumar matata dakai hannunsa kirjinta"..durkushewa Abdallah yayi a kasa ya fashe da kuka,mai ciwo...dafe kirjinsa yayi wani irin heart break yasamu a wanan lokacin,
Ummah cikin tashin hankali tace "ba kuka zakai ba Abdallah mafita zaka nema ka makata a kotu daga ita har bilal din ka kamasu da cin zarafin aure"
Zaro ido ramlah tayi cikinta ya katsa ta shiga zare ido cike da tsoro,girgiza kai Abdallah yayi "baxan iya maka bilal a kotu ba kodan darajar abbansa da ummansa,da darajar kaunar da nakeyi masa saidai zan sakar masa jiddah ya aura kuma babuni babu shi"
Mikewa yayi yana gumi "gidan su jiddah zani ummah....ummah zan saki jiddah a yau ba sai an kwana ba idan abbah yazo daddare ki sanar masa da hakan don banajin zaku sake ganina sai dan wani lokaci....bayan nasaketa zan auri ramlah zanbar garin da ita"
Wani sanyi ne ya shiga ramlah....wani irin farim ciki ne yasa ta fashe da kukan dadi,wanda a tunanin Abdallah da ummah kukan jiddah takeyi
"Kidaina kuka Ramlah,nasan kina kukan zaa kiraki da cin amanar aminiyarki....ko daya dama inada niyyar aurenki saboda kyawawan halayenki da suka banbanta dana jiddah....zan saki aminiyarki wa aminina ya aureta kuma zan samesa har gida"... Yana karasa magana ya fice.......
*********
Ganin jiddah batada alamar magana yasa bilal ya tsagaita da kukansa "zan tafi jiddah....amma kisami inada burin taimakon ki a rayuwa saboda soyayyarki ke yawo a jinin jikina yanzun haka,kuma bam cire rai da aurenki ba"yana gama magana ya fice ya zura takalminsa....kallo tabisa dashi wani jiri ke kokarin kwasarta... Dole yau ta hadu da ramlah don ta kwance mata wanan kullin dake barazana da tarwatsa mata zuciya....
A kwanar shiga layin,motocinsu sukai kicibis da juna,bilal beko ga motar Abdallah ba amma Abdallah yaga motar bilal hakan ya kara harzukashi a guje ya Shiga layin yana tada kura kamar zai tashi sama.....
Tana nan zaune ta kasa tashi koda ya shigo bega kowa ba parlor da ya gani a bude ya bude labule yana ganinta ya shiga a fusace jikinsa sai rawa yakeyi....kallonsa takeyi jikinta na kyarma gaba daya kamannin Abdallah sun sauya jijiyoyin goshinsa sun fito sunyi rudu rudu idanuwansa da fuskarsa sunyi jajir kasantuwarsa farin mutum....mikewa tayi da niyyar ficewa saboda yadda ta furgita....daka mata tsawa yayi"ina zaki munafuka?....dole ki mike ki gudu tunda ya biyoki har gida ya tattabaki yadda ya saba zuwa gidan aurenki ya laguda ki"...cakkkk network din kanta ya tsaya,
Jin tashin magana yasa yaya ibrahim shigowa dakin da sauri "meke faruwa?"
"Kaine dama kake bukatar inrabu maka da kanwa ko?"Abdallah yace yana nuna ibrahim, ummah ce ta shigo da sauri da hijab jikinta,
"Tou gani nazo in sanar muku da na saki jiddah saki daya sakamakom cin amanata da sukeyi itada aminina Bilal...nasaki jiddah saki daya"
Dafe kirji jiddah tayi take duhu ya gauraye mata ido ta daina gani.....
*SLIMZY✍🏼*
[11/5, 7:40 AM] Mis Slimzy😍🥰: *💥💥AUREN FARI...💥💥*
*SLIMZY✍🏼*
_Wattpad@slimzy33_
*SADAUKAR WA:*
*HAUWAU MU'AZU AMIR RUMA...*
*19*
Wani mugun kallo yaya ibrahim yake watsawa Abdallah,huci yakeyi idanuwansa sun gama sauya kala zuwa launin ja...nuna Abdallah yakeyi da hannu yana takowa dab dashi har ya karaso gabansa ya tsaya,wani kallo yake watsa masa kafin ya cije baki ya shafa gemunsa ya girgiza kai "yaro yaro ne,kayi wawta Abdallah kayi wawtar da harabada bazaka sake irinta ba,sanan ka nuna mana dabbanci da rashin ilimin islamiyya da bai wadace ka ba,da kanada ilimi koda zaka rabu da matarka baxakazo gidan surukai kana wanan haukar ba...."kallonsa yake ido cikin ido "ka saki jiddah kace ko?tou dan allah gobe zan sameka a wajen aikinka ka rubuta a rubuce ka bani sanan ka shaida babu kai babu jiddah harabada kuma ka nuna kai din baka fito daga gidan mutunci ba"
Girgiza kai Abdallah yayi kamar zai bugi kirjin yaya ibrahim "niko na fito daga gidan mutunci sanan nidin banine na nuna halin dabbanci ba sai kanwarka da ta nuna ita din jaka ce da aurenta take hulda da aminina"
Cikin tsawa yaya ibrahim yake magana jikinsa har rawa yake "kada ka saki kanwata kace zaka bi ta da sharri wallahi zan maka ka a kotu ina mai tabbatar maka komi kudinka zanyi Sharia dakai"
Wata irin dariya Abdallah yayi ya dage kafadarsa ya kalli sashen da jiddah take tana rike a hannun abidah da ummah wadanda sukai mata kariya lokacim da take kokarin faduwa,
Zaiyi magana ibrahim ya katse sa da nuna masa kofa "fitar mana a gida mara mutunci kawai....kuma karka kuskura ko harabar unguwar nan inganka dabba"ibrahim ji yake kamar ya shake Abdallah irin kallom wulakanci da yake masa,
Shiko Abdallah mamakim cin mutunci da dan uwan jiddah yayi masa yakeyi zai kuma tabbatar masa da shi din mai zuciya ne....ace kanwarsu tayi masa laifi amma yake cin zarafinsa?haka ya fice dakyar yake taka kafarsa ko gabansa baya gani....
A fusace ibrahim ya juyo yana nuna jiddah da yatsa "kinga irin mijin da kika dauko ko?kinga abinda muke fada miki kinga sharrin da ya biyo baya ko yana zarginki da amininsa ina mai tabbatarwa wanda naganki dashi ne a gaban mota da wanda yazo dazun"....cikin tsawa ya daka mata "koba shi bane dan ubanki"parlorn ya amsa,dakyar ta daga kai tana sauke numfashi hawaye na ambaliya a fuskarta tace "shine....kuma yaya ku gafarceni"
Nunata da yatsa yakeyi yayinda ummah da abidah suka kafeta da ido "ku gafarceni...hakika na aikata babban kuskure na muamala da aminin mijina....amma wallahi bans..."
Bata karasa ba ummah ta sharara mata wawan Mari "hauwau me kike shirin fada?kinaso kice dagaske ne abinda Abdallah ya fadi kin aikata"
Dafe kumatu jiddah tayi tana kuka, rungumeta abida tayi tana kuka itama cikin tashi hankali ummah ke salati cikin kuka "jiddah kinci amanar tarbiyyar da muka baki....kuma bari mahaifinki ya dawo dole yasan yadda zaiyi dake"
Neman waje ibrahim yayi ya dafe kai....zuciyarsa nayi masa kuna,kalamam jiddah sun sagar masa da gwiwarsa dikda idan aka bincika yasan tafi Abdallah gaskiya amma meyasa zatayi haka?....
Gudu yake shararawa a mota hawaye ya wankewa Abdallah fuska,cije lebensa yayi fuskar jiddah ke yawo a idamuwansa,sa hannu yayi ya daki sitiyarin motarsa kamar wani mahaukaci haka ya karkata motarsa ya nufi gidansu bilal.....
Bilal kuwa hawaye ya hanashi magana daga zuhura har ummah da rufaida hankalinsu a tashe yake abincin da sukeci dik dire plate din sukayi, shasshekar kukan bilal ce kawai a parlorn sai karar fanka da Ac da falom ya dauki sanyi...sai kuma tv da yake aiki shi kadai,
Tsuru tsuru duka sukaiyi kannensa ummah kuwa hankalinta yakai kololuwa wajen tashi, tunda bilal ya taso bai taba kuka haka ba domin dan nata namijin duniya ne....",bilal....ka fadamun abinda ke faruwa,mai ke damunka na ganka cikim wanan halin?idan kanason kwanciyar hankalina to ka sanar dani abunda ke faruwa"...dago fuskarsa yayi kuka yakeyi harda majina ya maida kansa,idanuwan ummah akan sa,
Sallamar da akayi ce tasa duka suka juya "assalamu alaikum"Abdallah ya shigo dakin cikin karsashi,shima kukan yakeyi ...."innahlillahi wa innah ilaihi rajiun...meyake faruwa yara na naganku cikin wanan halin?wace irin masifa ce tasamu mazaje suke wanan kukan"
Karasowa Abdallah yayi har gaban bilal ya tsaya ya cakumo wuyansa ya dagosa,wani irin juyi bilal yayi ya bangaje Abdallah yaja da baya suna kallon juna suna zagaye parlorn,
Cikim daga murya ummah ke tambayarsu cikim tsananim tashin hankali "wai meke faruwa?menake shirim gani Abdallah da Bilal?meke shirin faruwa?abinda bakuyiba kuna yara shine kuke kokarinyi yanzun?meyake faruwa"tace tana daga hannu kamar mahaukaciya,
"Bilal.... kaci amanata,amma nazo in sanar maka da na sakar maka ita ka aureta maimakon taba mata nono da tsotson bakin matata da kakeyi a matsayinka na maci amana jahili Wawa"cikin tsawa Abdallah ke maganar yana kokarin cakumo wuyan bilal,
Cikim daga murya da karfin hali bilal ya soma magana yana nuna Abdallah"ka tafka babban kuskure na sakin mata kamar jiddah....sanan ina mai gargadinka da ka bar dagamun murya,kasani nasani ko uban daya haifeni da uwar data haifeni bata dagamun murya Abdallah..maganar neman matarka kuma taimakonka nayi a matsayinka na jahili wanda baisam darajar aureba da shika shikan aure"...cakumo wuyan bilal Abdallah yayi yana girgiza bilal "ni kake cewa bansan darajar aure ba da shika shikam aure...kaida kasan darajar musulumci ai ka isa gidan sunna ka taka martabar aure"yana maganar idonsa kamar zasu firfito yana daga murya,
Wani irim hankada bilal yayiwa Abdallah sai gashi ya fada kak centre table ji kake tasssss glass ya fashe,
Ihu da kururuwa ummah tasa "wani irin balai ne wanan nake gani da ido na?ban fahimci maganar da kake fada ba Abdallah dukanku kardai ace macece ta shiga tsakanim soyayya da kauna tum ta yarinta....bilal idan ka kara motsi ko kace wani abu Allah ya isa tsakanina dakai"ta nuna Bilal da yake kokarim nannade hannum rigarsa,...ja da baya yayi kawai ya tsaya ya jingina,
Cikim sauri ta dau waya ummah ta dialing kiran mahaifin bilal..
Tafe suke a mota shida mahaifin Abdallah,kiran momy ya shigo"barkanki da yamma uwar gida...kinji tsohom mijinki shiru ko munfita da aminina gamunan a hanyar gida zaa saukeni"
"Alhaji dik inda kake kayi sauri ka iso gida Babu lafiya,ina cikin tashin hankali da Bilal da Abdallah fada harda dambe"
Kallom sashen mahaifin Abdallah yayi sanan yace "what....ok gamunan zuwa'ya datse wayar,
"Alhajin allah maike faruwa ne?"
"Ban fahimci me take fada ba amma dai naji furucin babu lafiya Abdallah da bilal fada harda dambe"
"Driver take kafa please.....
******
Tunda Abbah ya shigo gidan yaji abinda ya faru yayi shiru hade da tagumi,wani irim radadi yakeji a cikim zuciyarsa saidai dik lokacin da ya daga ido ya kalli jiddah sai ya kasa magana,tausayinta yakeji sosai ya fahimci dalilin da yasa ta fada wanan halakar,dalili kuwa shine tayi bayani akan Abdallah baya biya mata hakkinta na aure bashida lokacinta....irin wanan case dim yanzun haka ake fama a wanan rayuwar,mazan aure basu dauki hakkin aure a bakim komiba face su tauyewa Mata hakki hakan yasa yanzun zinace zinace ba yan mata kadai keyi ba harda matan aure,na matan auren ma ya kazanta....sanan yasan tarbiyyar da yayiwa yarsa yasan wacece jiddah ko mutum ta kashe bazatayi denying ba bazata taba kim fada ba...
Gyaran murya abbah yayi dik yabi kowa dake parlorn da ido kafin ya gyara zama "tou wanan abu daya faru beyi dadi ba amma tabbas jiddah kin tafka kuskure saidai kome kikayi Abdallah ne sila shine ya jefaki cikin halim da kika shiga....abu na biyu kuma bakida masaniya akan da waye kike muamala da waye kike hulda,don haka nakeso kiyi hakuri ki kwantar da hankalinki,hannunka baya taba rubewa ka yanke ka yar don haka ko munki ko munso ke din tamuce babu yadda zamuyi koba haka ba?"ya dubi ya ibrahim,
"Haka ne Abbah"
"Tou ni a ganina jiddah jibi idan allah ya kaimu ki shirya kayanki zan kaiki wajen kanwata rashida can zaki zauna har ki fita iddarki sanan hankalinki ya dan kwanta ki numfasa"
Cikim kuka abida da Ashma suka hada baki "abbah kana nufin katsina Ablah zata koma?....dan allah kada ka rabamu da Abala muna sonta muna bukatarta"
Dafa kan ashmah ummah tayi cike da takaici "kuyi hakuri yan biyu hakan shine ya dace da Ablar taku insha Allah zata dawo garemu da ta gama iddarta"
Tausayin yaran yasa ibrahim ya mike ya fice sakamakom kiran sallar da akeyi,abbah ma be kara cewa komi ba ya mike ya fice,
Ruko hannun jiddah ummah tayi tana mikewa ta fada jikin ummah ta fashe da kuka....
*******
Shigarsu abbah parlorm cikin tashin hankali yasa Abdallah mikewa yana kallom mahaifinsa,"Abbah bilal yaci amanata neman matata yakeyi..."
"Yimun shiru wawa sai mace ta hadaku oya zomu tafi gida can zamuyi dan ubanka"ciki fushi abbah ya juya Abdallah yabi bayansa,
Abban bilal kuwa kallom tuhuma yakewa bilal cike da takaici,dakyar yace "ka bani mamaki bilal....yau kaine kake nannade hannu zakai dambe da Abdallah?...kuma daga gani bakada gaskiya...idan nayi catching maganarsa kamar yana nufin matarsa kake nema"
Sunkuyar da kai bilal yayi batare da yace komi ba,tsananin zuciya yasa da zarar yayi magana zai iya mutuwa....
Momy ce ta karbe zancen "ehh hakan ne Alhaji,gashi nan har cewa yayi wai Abdallah besan darajar aure da shikashikan aure ba yasa ya nemi matarsa idan banji da kyauba naji Abdallah na fadin kamar har dakin matarsa ya taka"
Jikin abbah rawa yake ya zare malum malum din jikinsa .."bilal....menakeji kamar a mafarki yaushe ka zama kwarto bansani ba?kwarton ma matar amininka dan uwanka kake nema?"
Hawaye ne ya shiga gudu a fuskar bilal take ya gurfana akan gwiwoyinsa "Abbah...nayi kuskure amma inada dalili da zansamu a saurareni da kun fahimci cewar ban aikata hakan dan take martabar aure ba abba.....abbah ban kwanta da jidd .."
"Da kata mun...karbi wanan"ummah taiwa bilal dakuwa idonta na ciccikowa da hawaye....
"Hajiya"cikin kakkausar murya Abbah ya kira mahaifiyar bilal "naam"cikin kaduwa ta amsa tana hango tsantsar fushi a kwayar idon abbah....
"Banason ganin bilal a kusa dani ...hanyar danabi kada ya sake bi,bazai yuwu in haifi kwarto maci amana ba"durkushewa bilal yayi ya ruko kafar abba,cikin rashim saa abbah yasa kafa ya kaiwa bilal hamb'ari sai a fuskarsa yayi yar kara...baiko sauraresa ba ya nufi sashensa....tashin hankali wanda baasa masa rana...bilal ya waiga ya kalli rufaida da zuhura dik kuka suke ta dalilinsa take yaji tsanar kansa ta dasu cikim zuciyarsa....
*******"
Mari uku masu kyau abbahn Abdallah yayi masa "wallahi Abdallah matukar baka je ka dawo da jiddah ba babuni babukai...idan kuma kace ah ah bismillah,sanan maganar aure ban hanaka ba amma tabbas ina mai umartarka da kaje ka dawo da jiddah kaji na fada maka"
Ummah ta karbe "haba Alhaji,yarinyar nan fa amanar yaron nan taci da aurensa take hada shimfida da wani wanin ma bilal amininsa"
"Hajiya,bakida tunani amma banga laifinki ba don dik abinda Abdallah yayi kece kikasa shi saboda kiyayyar yarinyar data darsu cikim zuciyarki saboda son zuciya irin naki don haka ina mai baki shawara da wallahi idan baki bar wanan halin ba zai kaiki ga danasani"...watsar da glass dinsa yayi ya fice a dakin,
Kallom ummah Abdallah yayi "ka kwantar da hankalinka,zai sauko nasan yadda zanyi dashi katashi kaje gida ka kwanta,sanan ka rubuta takaddar kafin kaje aiki tunda wan nata yace zaizo ya amsa"..amsa mata yayi da Kai,cikin takaici ya musu saida safe ya fice....ummah ta shiga kaiwa da komowar abinda zatayi akan wanan matsalar da auren Abdallah....
******
Karfe daya na dare...
Kwance jiddah tayi ta kifa ciki idanuwanta a lumshe...dik bugun xuciyarta da soyayyarsa takeyi amma can kasam zucuyarta tanajin wani irin zafinsa da wani abu mai kama da kiyayya....
Abdallah ya fado mata a rai ta juya ta dafe kai....hawaye masu zafi ke zubo mata take ta lumshe ido wani tunani ya fado mata,
Bayan aurensu da kwana biyu washe garin first night ... Abdallah ya nad'ota a towel yana mata light kiss a goshi yana tsaye rungume da ita kallom kwayar idonta yakeyi cike da shaukim soyayya...itama hakan ne,
"Baby.... fadamin wani alkawari kikeso inyi miki ya zama tukwici na budurcinki da kika mallaka mun?"
Lumshe ido jiddan tayi "kaimun alkawari aurena da kai babu saki ko wani irin laifi zanyi maka bazaka rabu dani ba sweet ina matukar kaunarka"....
Jinjina kai yayi "ko kashemum mutum kikayi bazam sakeki ba"ta jinjina kai ya shiga juyi da ita cikim bed room din...
Kuka ne ya kwacewa jiddah data dawo duniyar tunanim da ta shiga....hawaye suka cigaba da ambaliya a fuskarta....shikenan yau ta zama bazawara ... bawani bane ya jefata mai laifi sai kanta da ta dauki amana ta mikawa Ramlah...
Lumshe ido tayi bazatabar garim nam ba saita hada ido da ramlah....
Shasshekar kuka Abdallah yakeyi hannunsa rungume da pillow ya jingina rigarsa kawai ya cire sai singlet.....tunanin irim cin amanar da bilal da matarsa sukayi masa yake ya kara tabbatar masa da ya tambayi mai gadi shigowarsa ya sheda masa....hasko kansu yayi a jamia a london shida bilal kaya iri daya suke sawa,baya mance ranan graduation dinsu haka yake bim bilal dagudu da baloom hannunsa saida ya fasa masa a fuska shima ya bishi da gudu a harabar babbar jamiarsu dake kasar London....
Daddare Abdallah haka zai zama gaban computer yana research shiko bilal koda yaushe chat saboda yanason social media...
Lumshe ido Abdallah yayi ya murgina ya fashe da kuka akam gadonsa.....
Bilal kuwa zaune yake yana hada akwatinsa....kukan zuci yakeyi babu abinda yafi damunsa irim yadda jiddah ta kasa saurarensa,
Turo kofar momy tayi sanye da rigar bacci da zani a sama,dummm light ne tasa hannu ta kunna globe take haske ya gwauraye dakin...
Kallom momy yake itama kallomsa take tausayim da da mahaifi yasa ta kasa sukuni ta shigo....sakin kayan yayi ya karasa gabanta ya durkushe ya rike kafarta yana kuka "momy kiyafemun kiji tausayina nasam ko kowa bazai saurareniba nasan ke zaki saurareni"shafa kansa tayi ta dagosa suka karasa gefen gado ta zaunar dashi ya zauna,
"Bilal ni mahaifiyarka ce kada ka boyemun komi"tana fadim Haka bilal ya shiga share hawayensa,dakyar ya saita natsuwarsa ya kwashe komi daga farko har karshe har yadda sukayi da Ramlah ya fadawa momy,
Gumi ne ke ketowa momy cikim damuwa tace "lallai kum hadu da sharrim shedan dana mace....sanan na fahimci jiddah tayi wawta dom dik abinda tayi kawarta ce tasata.... gashi ta kaita ta baro"
"Momy....jiddah taki saurarena...momy ina som jiddah wallahi saina aureta koda zumuncin mu zaizo karshe tsakanina da Abdallah'... bubbuga masa baya momy tayi "ba wanan ba, yanzun Ina zakaje?...kake hada kaya",
Kallom momy yayi ya kauda kansa gefe "momy zan barwa daddy gidansa....daddy bazai saurareniba yanzun nasani kuma ya tsaneni baya son ganina shiyasa zan tafi katsina can....inzauna wajen dan uwanki daddy zangina"
Jinjina kai momy tayi "na amince da hakan amma kada ka wuce wata daya..."
Ruko hannum momy bilal yayi "nasan zaki goyi bayana...momy inasom jiddah inason taimakonta..inaso kafim im tafi in sheda mata soyayyar da nake mata da aurenta da zanyi"
Hannu momy tasa ta rufewa bilal baki"kada ka kuskura ka nemi aurenta cikim idda,idam kayi hakan bakuda aure....ko bazawara ce ko wadda mijinta ya mutu aka ganta ana som aurenta baa fada inba haka ba babu aure baa neman aure cikin iddah....sanan ka hakura da maganar ganawa da jiddah yanzun kaji?"
Hawaye suka sulalowa bilal....wani irim so yake wa jiddah haka yanzun shikenan haka zai tafi ya barta a garin nan?ya tafi katsina zama?...waye zai kula da ita ya daibe mata kewa?..
Katse masa tunani momy tayi "ka hada kayan bari inje in kwanta kuma insha allahu nasam ta inda zan bullowa lamarin,amma gobe zanje gidansu Abdallah....mikewa tayi ta fice,yabi bayanta da kallo ya lumshe ido yanajim soyayyar momynsa cikim zuciyarsa.....
Kasa baccin Abdallah yasa wajen karfe uku na dare ya dawo parlor....yana rubuta takardar sakim jiddah hawaye na diga a takardar.......
*TO YANZUN ZAA FARA WASAN FA.....*
*SLIMZY* ✍🏼
[11/5, 7:41 AM] Mis Slimzy😍🥰: *💥💥AUREN FARI...💥💥*
*SLIMZY✍🏼*
_Wattpad@slimzy33_
*SADAUKAR WA:*
*HAUWAU MU'AZU AMIR RUMA...*
😩😩Omo see love ina godiya masoya slimzy na WhatsApp da kewaye....sakwanni masu tarin yawa da akemun forwarding sun iso gareni...... *AUREN FARI* *FANS...* Bana cikin group amma sakwanni na yabo suna isowa gareni ina godiya🥰😃
Wanan shafin naku ne
*BARRYN SADEEK*
*MRS KAMAL MAGINA*
*EASHAH KADIR(BAE)* Allah ya kara miki lafiya masoyiyar usuli...
My lil sis *MAMMY* D love i have for you is endless🥰
*TEELARH* billahi ina kaunarki yadda kike kaunat...😩
*MAMAN SHARRIF*
*MARYAM NURA* ...ban mance daku ba ina sonku fisabilillahi wallah am speechless....😭
*20*
Washe gari....
Da wuri ramlah ta tashi,ta shiga kitchen soye soye takeyi cikin kwanciyar hankali zuciyarta falll tunanin Abdallah minti minti takan sauke murmushi mai kauatarwa a fuskarta,tanaji yau kamar haduwar farko zatayi dashi zuciyarta na azalzalarta da tsananin kaunarsa....
Karfe bakwai da minti sha biyar me napep ya sauke jiddah a kofar gidan su ramlah,tana sanye da hijab har kasa mai ruwan kasa,fuskarta tayi fayau sauri sauri ta shiga cikin gidan kasantuwar gidansu babu wanda ya tashi lokacin data fito ...cikin gidan su Ramlah shiru haka tayi sallama a sanyaye a parlorn su Ramlah nan ma shiru.....
Hango Ramlah tayi tsaye cikin kitchen gaban gas da alamar breakfast take hadawa,wani miyau mai kauri ta hadiye kafin ta karasa tayi masauki a jikin kofar kitchen din ta kurawa Ramlah ido zuciyarta ta tsananta harbawa wanda batasan dalilin hakan ba....
Ramlah kuwa farar vest ce jikinta da under skirt kasantuwar tayi wanka tun asuba,haka kawai ta jikin glass na windown kitchen take hango inuwar mutum a bayanta ...gabanta yadan fadi kafin tayi dauriya ta juyo wani irin shock tayi tadan ja da baya "malama....yaushe kika shigo kika tsaya a bayana kike shirin furgita ni?wallahi kinban tsoro...da asuba haka"
Cije baki jiddah tayi "bacci ne ya kauracewa idona sakamakon mummunan al'amari daya sameni wanda nake hasashe dikda nazo im tabbatar da cewar ancemun kece silar mutuwar aurena Ramla"
Wata irin shewa ramlah tayi ta juya tana kokarin kwashe dankalin dake cikin mai,ta kwashe tasss a kula batare da tacewa jiddah komiba sanan ta kashe gass din ta hada basket kafin ta dubi jiddah cike da izza da takama "muje cikinko,tunda baki ko jira mun gaisa ba kike mun wata magana me kama da soki burutsu"....wani takaici ne ya kara kule jiddah ta lura Sarai ramlah raina mata wayau take kokarin yi daga yanayin yadda take mata magana cikin ko in kula....batare da sun hada ido ba,hakanan tabi bayanta har cikin dakinta inda tayi masauki a gefen gado,
Ramlah kuwa jikin wardrobe ta karasa ta bude ta ciro kaya tana kokarim sawa...."magana nakeyi miki ramlah ki sanar dani abinda nakeso insani"
Batare da ta kalli jiddah ba ta amsa "mai kikeso kisani jiddah....ko kinzo ne ki tambayeni nasan waye bilal maska?"
Mikewa jiddah tayi jikinta na rawa "kenan kinada masaniya da masifar da nake ciki a yanzun?kece kikasani cikinta"
Wata yar dariya ramlah tayi "banina sakaki ba jiddah,dakikanci da rashin wayau irin naki yayi sanadiyyar jefaki cikin halin da kike ciki"
Cikim fusata jiddah ta mike "ni kike cewa dakikiya mara wayau.... Ramlah kece kuwa ramlah aminiyata yar uwata"gabanta na faduwa take tambayar ramlah ido waje...nan da nan idonta ya kankance yayi jajir,
"Ramlah...ta tashi daga Aminiyarki sai kishiyarki koda yake nasak cewar igiyar aurenki girgidi takeyi idan kuma ta tsinke ne ki sanar dani domin indaina shirye shiryen zama da kishiya"ido cikin ido ramlah keyiwa jiddah maganar,
Dafe kai jiddah tayi "innahlillahi wa innah ilaihi rajiun...."rufe ido tayi tana kada kai "allah ka farkar dani daga wanan mummunan mafarkin da nakeyi yanzun,nasan ramlah ta baxatayi mun haka ba ramlah masoyiyata ce mai son cigabana mai sona"
Zuge zip din rigarta tayi ta tsaya gaban madubi tana kokarin shafa hoda ta karbe zancen "nasan bilal ne yake kokarin sanar dake to dik abinda ya sanar dake hakan ne,amma bilal ya yaudareki ne ya kasa sanar dake shidin aminin mijinki ne yake tattabaki yana tsotseki yana jin dadinki....sanan note,kada kisake bakinki ya kirani da mai kaunarki don bantaba kaunarki ba jiddah kullum burina bai wuce insamu damar da zanzama koda kwatankwacinki ba kin kasa gane hakan,sai wawanci kikeyi anfada miki cewa ni zanso kiyi aure kinzauna gidan daula ni ina zaune a gida ba miji ne?....hmmmmm wanan sai ya zame miki darasi da dik wata mace ballagaza dakikiya irinki...ke dan allah ki fice mana daga gida don aiki zani yau monday as u can see shiri nakeyi ma"
Wata kururuwa jiddah tayi cikim tashin hankali jikinta har rawa yakeyi ta tunkari shake ramla,cikin azama ramla ta zabgawa jiddah marin da saida taga gilmawar wuta domin cikim karfinta tayi mata"....dafe kumatu jiddah tayi tana kallon ramlah cikin daukewar kwakwalwa jinta take tamlar baa duniyar nan ba,
Nunata ramlah tayi da yatsa "kada ki kuskura kiyi wanan gangancin,idan kikace zakiyi bakeba har zuriarku saina hanaku zaman garin nan don inada video dinki da yadda bilal ya tsotsi nonoki da zuwanku yawom shakatawa dik zan watsaki a duniya idan kinada shirin wani auren ma babu wanda zai kwashi kwartuwa"... kyalkyalewa da dariya ramlah tayi....
Cikim daga murya jiddah ta soma magana "lallai ramlah kin nunamin hali irin na dan adam kin kuma nunamin ke cikakkiyar mace shedaniya ce,inada tabbacin cewar shedan ma tsoronki yakeji ramlah.... maciyiya amana azzaluma muguwa,dake da zaman lafiya a gidan Abdallah harabada ....sai kinga sakamakom zalunci dan da izinin Allah Abdallah sai ya shayar dake gubar datafi tawa daci,sai ya miki ninkin abinda yamum harabada bazan sake yarda da wani dan adam ba a rayuwata......."
Sama sama mahaifiyar ramlah ke jiyo hayaniya,daga kai tayi ta kalli agogo takwas saura minti ashirin gashi tana jiyo maganganu harda muryar ramlah...dirowa tayi daga gadonta ta fito direct dakin ramlah ta fado....
"Jiddah lafiya?mekikeyi a nan da sassafen nan?"ko saurarenta jiddah batayi ba ta bi ta gefenta ta fice ko ganin gabanta batayi tamkar zata tashi sama saboda bakim ciki....."jiddah bake nake kiraba meyake faruwa meya hadaki da aminiyar taki?"cikim daga murya ta tsaya bakin kofa tanawa jiddah magana,
Komawa tayi daidai ramlah ta fito rataye da jaka tasha daurin dankwali me step bakin nan yaci maroon din jan baki sai sheki fuskarta takeyi"lafiya kuwa ramlah?meyake faruwa me jiddah tazoyi a gidan nan daidai wanan lokacin?"
Ajiyar zuciya ramlah tayi "ummah ki kwantar da hankalinki,nida aminiyata baajin kanmu fushi tayi saboda ance bata haihuwa tace in auri mijinta nayi gaddama ...kuma ummah ina gudun zagin da duniya zataimun ne"
Shiru ummah tayi kafin ta nisa "tou ba laifi amma dai kibita ku sasanta kanku naga ta fita tana kuka kuma daga gani jiddah tayi fushi ainun tunda ko saurarena takiyi"
Jinjina kai ramlah tayi"insha allahu idan antashi aiki zan wuce wajenta....saina dawo ummah am already late"tayi gaba ummah ta bita da addua "Allah ya tsare ya kare"
"Ameen ummah bye"ta daga mata hannu.....
**********
Zaune suke kan shimfidar cin abinci a parlorn suna breakfast,babu meyiwa wani magana ko wannensu fuskarsa babu wata walwala musamman momyn bilal....shigowa parlorn yayi sanye da farar shadda kansa babu hula gashin kansa ya kwanta lufffffff Yana haye da trolley dinsa ya dire a tsakiyar parlorn nan da nan kwalla ta cicciko a idon momy....beyi masauki a ko ina ba sai gaban dadynsu da ganinsa yasa ya kauda kai gefe,
Durkusawa bilal yayi kansa a kasa "daddy.....fatan ka tashi lafiya mahaifina"ko kallon bilal beyi ba ya cigaba da abinda yakeyi yana sanye da milk din jallabiya,
"Nazo a gareka na durkusa akan gwiwoyina ka yafemun abinda nayi daddy koda bazaka saurareniba domin a yanzun ina shirin bankwana daku zan nisanceku har zuwa lokacin da zaka sauko ka saurareni mahaifina"muryarsa na rawa yake maganar hannunsa akan cinyoyin daddy yana kallon fuskarsa da ko alamar murmushi babu,
Cikin karaya momy ta amshe maganar "kai mahaifi ne ga bilal,dik inda zashi idan har baka yafe masa ba bazai taba ganin dakyau ba Alhaji...dan allah ka yafewa bilal domin zai tafine ya bar mana gidan"...wani mugun kallo daddy yayi mai cike da kunar rai da bakin ciki ya jefi bilal da harara"tashi kaje kada ka cikamun kunne da maganganunka mutumin banza... kaje nayafe maka amma banason ganinka don niba mutumin banza bane"
Zuhura tana hawaye tace "ya bilal shikenan zaka barmu?"
Kada kai yayi alamar ah ah "zan rinka zuwa ganinku kannena ku kulamin da kanku"...ya dubi momy "zantafi momy kiyitamun addua"
"Allah yayi maka Albarka,ya tsare ka ya kiyayeka a dik inda kake"tana maganat hawaye ya wanke mata fuska....haka Bilal ya yunkura ya mike yaja akwatinsa... Zuhura da rufaida suka ruga suka rungumesa suna kuka shima dik dauriyarsa saida yayi hawaye.....
*********
Dakyar ta shiga gida koda ta sauka a napep tana shiga da ummah ta soma cin karo,kallon mamaki ummah taiyi mata don dik a tunaninta jiddah tana bacci a daki "daga ina kike kamar daga waje jiddh?kardai kicemun gidanki kikaje ya wulakantaki ko?"
Girgiza kai tayi ta fada jikin ummah ta saki kuka mai ban tausayi "ummah....ramlah ta cuceni"..cikin rashin fahimta ummah ta dago kanta "banganeba jiddah mekikeso kice?"
"Ramlah itace ta kashemun aure ummah... yanzun haka ita mijina ke shirin aure...ummah natsani kaina na tsani zaman garin nan ummah yau zanbar garin nan yau zantafi katsina"..ta rufa aguje ta fada dakinsu abidah kukanta yasa abidah ta zabura tana mutsika ido "lafiya..ya ya jiddah meke faruwa haka?"
Fadawa kan gado jiddah tayi tana kuka.....
****
A reception yaya ibrahim ya zauna,don tun sassafe ya iso wajen aikinsu Abdallah amma ance be shigo ba zaidai shigo hakan yasa ya nemi waje ya zauna,
Ramlah na maxauninta idonta na kan hanyar shigowa don tun isowarta be shigoba cikin tashin hankali take ta kosa tayi tozali da sanyin idaniyarta....cikin minti talatin sai ga Abdallah ya shigo...yana sanye da Ash din suit fuskarsa tamkar hadari....saida gabanta ya fadi jikinta ya kama rawa cleaner dake goge goge ya durkusa "barka da shigowa ranka ya dade"daga masa hannu,
Ganin Abdallah yasa ibrahim mikewa beko bari ya nufi office dinsa ba yasha gabansa "malam ba saika shiga ba kai nake jira ina takaddar kanwata"wani kallo Abdallah yayi masa cike da wulakanci kafin yayi jimmmm sanan yasa hannu a aljihun gaban rigarsa ya ciro farar takadda a ninke ya mika masa "gata...sai kuma me?"
Murmushin jin dadi ibrahim yayi "babukomi babu kare bin zago.."yasa aljihunsa ya gifta ta gabansa yayi wucewarsa, Abdallah yabisa da kallo,
Murmushin farim ciki Ramlah tayi....ta tabbata jiddah Babu aure tsakanin ta da Abdallah.....yanzun miji nata ne ita kadai abu daya ya rage Abdallah yace zai turo iyayensa gidansu....mikewa tayicike da karairaya ta karasa ta dan rusuna ",barka da zuwa sir Abdallah"ta mika hannu ta karbi jakarsa babu musu ya bata,wani dadi ne ya kara rufeta ji takeyi tamkar sun zama miji da mata.....
*******
Zugum zugum ummah da ashma sukayi yayinda Abidah ke taya jiddah hada kaya,
"Lallai ramlah taci amanarki jiddah....amma banga laifinta ba domin rabi da kwata na cin amanar da tayi miki yayi tasirine a gareki ta sanadiyyar yarda da rashin rike sirri irin naki kin amince da ita ta jefaki a rijiya mai zurfin gaske wadda fitarki cikinta sai kinsha wahala...don na tabbatar bazaki taba mancewa da tabon aminiya ba"
"Shiyasa tun farko ni wanan ramlat ban taba sonta ba dom natsaneta don ko abida zaku tambaya banason ganinta ko kadan"
"Allah shi kyauta....kifito kiyi breakfast,kafin ki kama hanya tunda kin dage yau zaki tafin kafin nan yayanku ya shigo"
"Assalamu alaikum"yaya ibrahim yayi sallama,
Duka suka hada baki suka amsa,gefen gado ya zauna ya ciro takardar a aljihunsa "ga takaddar shedar sakin hauwau na karbo wajen Abdallah,meke faruwa naga kuna hada kaya?ina akasaku kaya haka?"
"Kayan su ashma ne muka tsinta zata tafi dasu,tunda kaga baai maganar kwaso kayanta ba tukunna,amma idan ankwashi kayan sai a aika mata",
Jan numfashi yaya ibrahim yayi "badamuwa allah yasa haka shi yafi alheri,yanzun idan ta shirya sai muje insata a mota kawai"ya kama hanya ya fice dakin,
********
A kofar gidan su Abdallah driver ya sauke momyn bilal.....da sallamarta ta shiga gidan suka gaisa da mai gadi cike da mutumtawa....taku take cike da kasaita tana sanye da milk da brown lace ne mai shegen kyau da tsada,dinkin bubu na manyan mata akayi mata,
Dukkansu yan matan da mahaifiyarsu suna parlorn momy tayi sallama cikin faraa hakorin makkanta ya bayyana da makekiyar wushiryarta tace "oyoyo yarana"afee ce ta ruga ta fada jikinta "sannu da zuwa momy"
"Yauwa"tace tana kokarin shigowa,daga rumaisa har meenah kallon da ummansu tayiwa momyn bilal yasa suka kasa mikewa su gaida momy "zan gamu daku wato afee kadai taimun oyoyo"ta shigo tana kamshi na alfarma,
"Ah ah hajajju ashe kina parlorn,nasameku lafiya?"ta karkace tana gaida ummah sakamakom ummah ta girmeta,
"Lafiya ...kikasamemu"tana amsawa ta yunkura ta bar parlorn ....
Kallo momy tabi ummah dashi cike da mamakim yadda ta karbeta sabanin da idan tazo da ita ake rugowa ai mata oyoyo....to kodai abinda ya shiga tsakanin yaran ne yasa tayi fushi?koda yake Bilal keda laifi dole ta basu hakuri....amma zata jira taga me ummah ke nufi...zatai kokarin danne xuciyarta wajen basu hakuri da tattausan lafazi amma sanin hali irin na ummahn Abdallah idan tai mata hauka to fa zasu kwashe.....
Tafi minti goma zaune afee ta kawo mata drinks da meat pie ta dire ita kuma ta ciro wayarta tana kokarin kiran bilal taji lafiyarsa da hanya ummah ta shigo parlorn fuskarta kamar wadda aka aikowa da sakon mutuwa....
********
Tafe yake a mota gabaki daya bashida sukuni hankalinsa na wajen jiddah,yaso ace bebar garin kaduna ba saida ya hada ido da ita.....a fili ya furta "soyayyarki a jinin jikina take a halin yanzun hauwau,bazan taba daina sonki ba harabada.....daga ke babu wata ya mace kece nafara so zan dawo gareki jiddah.."
Gudu sosai mai mota ke shararwa kanta yana gefen window tana karewa dajika kallo amma hankalinta gaba daya baya jikinta maganganun ramlah keyi mata yawo akai.....mamakin wanan rayuwar me cike da alhini takeyi....ta wani bangaren kuma tunanin bilal ya hanata sukunishine yake mata yawo a kwayar idonta ko rufe ido tayi shi take gani,babbar damuwarta shine ta yaya zata soma rayuwa a katsina bayan ruhinta yana kaduna?soyayyar bilal ce tai mata dirar mikiya wadda ta haddasawa zucuyarta da gangan jikinta daukan zafi....soyayyar bilal ce ke dawainiya da ita,meya jawo hakan?kyautatawar da yayi miki da kulawa jiddah.....zuciyarta ta bata amsa,
Kwantar da kanta tayi zuciyarta tayi zurfi cikin tunani lokacin da taga welcome to katsina nan take ta tunada batasan address din inda zatajeba dikda ance zaazo daukarta har tasha amma dolene tasani saboda bacin rana....
Cikin sauri ta kira Ashmah
"Hello aysha...umm gani mun shigo kt ya sunan unguwar da gwaggo suke?"
"Ablah kunyi sauri masha allah,kinga sunan unguwar goriba road...ummmm ok street G suke amma,yauwa amma ai ummah tace sunyi magana zaazo daukarki"
"Ehh inaso insani ne kawai....nagode sai kunjini"
"Owk Allah ya tsare"
Wayarsa ya ciro a aljihunsa nan da nan ya shiga laluben layin momy bata zuwa tsuki bilal yayi shikadai a mota ya furta "nadaisan abbah zangina a goriba road suke amma bansan street din ba gashi wayar momy bata shiga....koda yake gidan bazai boyu ba ai"...ya maida hankaki driving dinsa.....
********
Cike da lallashi ramlah ta shawo kan Abdallah sai yanzun da azahar ta wuce yake cin breakfast din da ta kawo masa,shiru duka babu meyiwa wani magana saidai ita tana satar kallonsa lokaci zuwa lokaci..."ummmm inaso in aureki"
"Naam"tace kamar bataji shi ba...
"Nasan kinji Ramlah ke ba yarinya bace...i mean i love you and inaso in aureki cikin sati biyu.....wa zaagani idan zaaje neman aurenki?"
Sunkuyar da kai tayi tana wasa da yatsunta shiru sanan tace "zanyi magana da ummah na"
"Owk.... note....amma ba abbah na bane zai nemi aurenki kanin mahaifiyata ne zaimun jagora don abbah baxayiba....nafada miki ne kisani"
Wani abu taji ya caki zuciyarta kamar mashi...nan da nan fuskarta ta sauya kallo daya zakai mata ka hangi damuwa da tashin hankali.......
*MUJE ZUWA KU BINI YANZUN WASAN ZAI SOMA.....*
*SLIMZY✍🏼*
[11/5, 7:41 AM] Mis Slimzy😍🥰: *💥💥AUREN FARI...💥💥*
*SLIMZY✍🏼*
_Wattpad@slimzy33_
*SADAUKAR WA:*
*HAUWAU MU'AZU AMIR RUMA...*
*21*
Kare mata kallo Abdallah yayi yana karantar yanayinta yanayin nata ya nuna tamkar bataji dadin hakan ba,tou meyasa zataji rashin dadi?kenan idan Abbansa be nema aurenta ba ya zama damuwa?bema dace ta damu ba ai.....ture flask din yayi ya kurbi ruwan lipton "ki fadawa ummah...tayi magana da wadanda zasu amshi manena aure saiki sanar dani jibi da yamma karfe hudu zasuzo insha allahu"
Dakyar ta saita natsuwarta "tou shikenan badamuwa sir....zanyi hakan"mikewa tayi jiki babu kwari ta tattara kayan da yayi breakfast ta juya da niyyar ficewa , har ta kai kofa ya kira sunanta cikin wata irin siga "ramlah......"cakkk ta tsaya bugun zuciyarta ya tsananta,bata tabajin wanda ya kira sunanta yayi mata dadi haka ba,juyowa tayi ta amsa "naam...."
Shanyayyun idanuwansa ya zuba mata "idan mun tashi aiki zamu biya dake shopping koh?"
Wani dadi ne ya lullubeta kamar ta daka tsalle "tou sir Allah ya kara girma"
Jinjina kai yayi yana kokarin jawo laptop dinsa,karar rufe kofarta yayi daidai da sauke ajiyar zucuyarsa,pin na computer dinsa yasa yanada aikin da zaiyi kyakkyawan hoton jiddah ne a walpaper na laptop dinsa,kuri yayi da ido yana kallon hotonta,kamar me kokarin gano wani abu,wani daci ne yasa ya kasa yin abinda zaiyi ya kife laptop din ya kwantar da kansa a jikin kujerar da yake zaune.....
********
Momyn bilal na zaune ummah ta shigo parlorn sanye da lafaya dik tunaninta momyn bilal ta tafi ganinta yasa tadan ja da baya cike da mamaki sai kuma ta cijee"ashe kina nan baki tafi ba"
Yatsina fuska momy tayi cike da takaicin tambayar ummah "wani irin tambaya ne wanan hajiya?ya zaai intafi?bayan wajenki nazo mu tattauna akan abinda ya faru na lamarin yaran nan"
Dakyar umma ta zauna daya daga cikin kujerun tana rataye da jakarta "wani lamari Kuma kenan kike nufi"cikin ko in kula take maganar,
Kada kai momy tayi dik ta fahimci inda ummah ta nufa "abinda ya faru tsakanin bilal da Abdallah"
"Ohhhh kicemun cin amanar da bilal yayiwa Abdallah na keta masa haddi har gida na neman matarsa da yakeyi"
"Haba hajiya ya zakice hakan? yaran nan dai shedan ne ya shiga tsakaninsu wanda dik bamu da tsumi babu dabarar wanan kaddarar data fado mana...."
Gyara zama ummah tayi tana kallom agogon hannunta cike da bacin rai domin kalaman momy kara tunzurata sukeyi "kinga hajiya babu kaddara,inda dan uwansa ne na jini ai baxai masa hakan ba kawai dai yaci amanar abota to ya sakar masa ita yaje ya aura ya karasa dan babu abinda zaiyi da sauran danki"
Zuwa yanzun zuciyar momy tana kara zafi da kalaman ummah amma kasantuwar danta yaja mata yasa ta cije ta saita natsuwarta cike da izza tace "tou Alhamdulillahi babu wanda yafi karfin kaddara,don haka insha allahu tunda ya sakar masa ita zan tambayi bilal din idan ya taba kwanciya da ita idan ya tabayi idan ta fita idda sai suyi istibra'i suyi aure.....shikenan hajiya nagode sosai da mugayen kalamanki ba laifinki bane laifina ne dana tako kafata nazo gidanku"ta yunkura ta dauki jakarta ta nufi kofar fita,
Cikin daga murya ummah ke fadin "Allah ya raka taki gona bama bukatar gayyar na ayya arna a idi a zuriyar mu dama babu abinda muka hada daku kinzo kina fuffuka kina wata barazana kim sauko zinarin karya na bogi shashasha"
Da sauri afee tabi bayan momy har ta fice gate din cikin saa ansauke wata a makotansu momy ta tari me napep din ga wayarta dake faman ringing amma ranta a bace ko bude jakar ta ciro batayi ba "momy dan allah kiyi hakuri da abinda ummah tayi miki"afee ta ruko hannun momy cikin kidimewa,
Murmushin karfin hali momy tayi ta shafa kan afee "Allah ya miki albarka ummul khairi babu komi aiba laifinta bane laifin dana ne da kuma ni kaina,kamar yadda tace bamu hada komi ba insha allahu bazan kuma zuwa ba ummul khairi kiyi hakuri kinji"momy ta shige napep tace "muje wajen makarantar zabeeb collage malam....
Meya samu wayar momy nake kira tun dazun bata dauka ba kusan minti ashirin da isowata garin katsina nayi parking gefen titi ina jiranta shiru,ransa ne ya soma baci ga kansa dake matsanancin ciwo...ya Kara laluben wayarta,
Da sauri momy ta zage jakarta ta ciro waya ranta a bace ganin bilal ke kiran yasa ta dan ja numfashi cike da kulawa ta dauki wayar da sallama,
Cike da shagwaba ya soma magana "haba momy tin daxun ina cikin garin katsina na mance sunan unguwar da zani gashi kaina na ciwo inata kiranki kimun kwatancin gidan abbah zangina shiru"
Nisawa tayi cikin wata iriyar murya tace "goriba road suke street G numbet gidan 26 ne dan momy kayi hakuri wayar na jaka ne...kaji?"
Jimmm kadan yayi samm muryar momy shes not sounding normal "momy ya naji muryarki haka meyake faruwa?meyasameki"
Murmushi tayi cike da bacin rai "babu komi dan momy kaje idan ka sauka ka huta daddare zamuyi waya mu tattauna wata maganar"
"Owk"yace ya datse wayar yabi wayar da kallo,yasan akwai wani abu amma shi mutum ne idan ya tambayeka damuwarka kaki fada masa yana baka space,baxai takurawa momy ba yasan zata sanar masa,
Key yayiwa motarsa ya cigaba da tafiya....bin ko ina da kallo yakeyi haka kawai yake jinsa cikin nishadi,garin katsina gari ne mai kyaun gaske yana cikin garuruwan arewa da suke burgesa garin karamci da kara kenan ga kunya matan katsinawa uwa uba katsinawa kyawawa ne ga ilimi....kasantuwar lokacin damuna garin yayi tamkar hadari zaka dauka yamma ce tayi amma karfe biyu ne da wani abu na rana....yana karyo kwana ya shigo unguwar goriba road yaji faduwar gaba haka ya shiga kirga street har yazo street G kamar yadda momynsa tace manyan gidaje ne na alfarma na masu kudi haka yakebin numbobin gidan da kallo har yazo 26 a daidai 25 yaga wata mota ana shiga da wani akwati cikin gate din gidan wani dan saurayi ne yaketa murna yana fadin mutanen kaduna.....haka ya karasa gida na gaba daya kasance 26 nan ne gidan Abbah zangina inda yazo.....
Horn yayi mai gadi ya rugo ya leko ta karamar kofa yana kallom motar yana hangosa daga ciki yana karewa motar kallo alamar be gane waye ciki ba,murmushi bilal yayi haka kawai yake jin kansa cikin nishadi ko meye dalili oho?....zuge glass din yayi "nine baba"suna hada ido da bilal ya ganesa ya washe baki "barka da zuwa bila babban bawa"daga masa hannu yayi,
Bude masa gate yayi ya shige gidan,yana kokarin rufe gate din wata mace babba zatai saa da momynsa ta shigo gidan sanye da gyalenta da lace dinta ja daidai nan bilal yayi parking ya fito suna hada ido ya daga murya "oyoyo Ammiey.....oyoyo na iso"
Fadada faraarta tayi "oyoyo bilal....oyoyo mutanen kaduna yanzun nake maganarka da hajiya gwaggo makociyarmu itama tayi bakuwa daga kaduna nake cewa nima d'ana na tafe daga kaduna,kamar kun hada hanya da yarinyar"
Beko kula da me Ammiey ke fada ba cike da murna ya rungumeta sanan yadan rusuna "barka dai gwaggo",
"Mu shiga daga ciki mana bilal ai bama gaisa a nan ba,yan uwanka maza da mata dik suna nan anyi shirin zuwanka"
Daga bene wata kyakkyawar budurwa ta fito ta kwala ma Ammiey kira "ammiey"daga kai sukayi a tare sai kuma ta kwalla kara "oyoyo yaya bilal nina fara ganinsa"
Murmushin gefen fuska yayi suka kalli juna shida Ammiey "muje mana bilal kabar akwatin a nan zaazo a dauka"be ce komi ba yayi gaba ammiey na biye dashi,
A hanyar shiga gidan sukai kicibis da budurwar data leko daxun ta rungume bilal "oyoyo....",lakuce mata hanci yayi "kinfa girma zee baby umm banace kibar oyoyom nan ba"
Dan turo baki tayi tana kallon Ammiey suka shiga parlorn a tare aiko nan da nan hayaniya ta kacame cikin parlorn .....
********
Jiddah sallah tayi a dakin da aka sauketa,ta fito parlor inda gwaggo ke zaune da wata yarinya yar shekara sha daya suna kallo "ah ah hauwau kin fito?"
Sunkuyar da kai tayi ta zauna kasan carpet "tashi mana ki zauna kujera...ga abincinki nan ki bude kulolin wanda kikeso ki zuba kici,kuma kici sosai dan nayi waya da mamanki tacemun bakison cin abincu to zakicu anan dan zamu bata"murmushi tayi
Yar yarinyar ce tace "gwaggo....A nan zata zauna damu?"
"Ehh nafeesah,kinga kin samu abokiyar magana ko idan Aunties dinki sunzo kusha hira"...karamar yar gwaggo kenan sakamakon yaranta mata sunyi aure mazan ma biyu sunyi aure amma dai suna zuwa gidan....
"Anty barka da zuwa naji dadin zuwanki"nafeesa ta soma tsalle cike da murna,itama gwaggo dariya take,
"Jiddah Allah yasa kiji dadin zaman nan tunda ba mate dinki saidai makota akwai Yan mata dikda kindan girmesu zainab nasan zakiji dadin zama da ita zanyiwa Amminsu magana ta rinka shigo miki hira kema wataran sai kije musu ko?"
Gyada kai jiddah tayi ta zuba jealouf din couscous da hanta tasa farfesun kifi da zobo tana ci,
Sallamar da akayi a parlorn yasa nafeesa ta daka tsalle "ga Anty maryam ga Anty fatima.....Anty muma munyi bakuwa zata zauna damu"
Matashiya ce da bazata wuce shekara ashirin da takwas ba daga gani yar gwaggo ce don kamarsu daya da yaranta maza suka shigo suna ihu oyoyo oyoyo "ai na dauka bazakuzo ba ja'irai"inji gwaggo,
"Aiko zamuzo gwaggo"tace tana kallon jiddah cikin zare ido tace "gwaggo kamar jiddah yarinyar innah zainab"
"Ehh itace"
Cike da murna Anty fatima tace "masha allahu aiko dauke ta zanyi ingudu da ita gidana"
Nafeesa ta turo baki "tabdijan daga zuwanta yaseen bamu yarda ba"duka sukasa dariya Anty fatima ta zauna tana duban jiddah "yasu innah zainab,ina abida da aysha rigima,sholly gayu tana nan tanayi ko",jiddah na dariya ta amsa,...nan sukaita janta da hira dakyar tadan saki jikinta ...
*******
Misalin karfe hudu suka bar wajen aiki suna tafe a mota jiddah na satar kallom Abdallah Wanda yake tuki yana kallonta ta gefen ido,ganin kallon yayi yawa yasa ya juyo hade da kakalo murmushi yace "yadai....naga ana kallona na hadu ko?"ya tambayeta a dan sake,
Farr tayi da ido"sosai ma...amma meyasa ka tambaya?"
"Naga ana satar kallona ne shiyasa,ko har an tsunduma kogin sona?"ya dage mata gira amma Babu faraa,bata damu da yadda yayi maganar ba sai kawai tasa tafin hannunta cike da kunya ta rufe ido....cikin zuciyarta take fadin,da kasan yadda ka hadu da baka tsaya tambayana ba burina daya ne inganni a dakinka,inganni kwance a faffadan kirjinka kana zubamun soyayya ina maka shagwaba,da alamar Abdallah ka canja tunda har kakemun magana haka....
Parking yayi a wani shopping mall can wajen marafa .."tou sarkin kunya a bude idom mu shiga ko?kidau abinda kikeso kinji?"yayi maganar yana daga girarsa,babu wani jan aji ta amsa da "tou"tana bude kofar motar,
Da makociyarsu Abdallah sukaci karo itada mijinta sun fito,tana ganin Abdallah da ramlat ta zaro ido kadan ya rage bata fadi ba wajen kallonsu,
Kasa hakuri tayi ta dubi mijinta "honey kaga me nake gani?makocinmu ne fa da Aminiyar matarsa a wajen shopping"
Murmushi mijin yayi "ehh halan bakisan ya saketa ba ma,yana shirin auro ta wai yadda naji matar tasa kecin amanar mijin da amininsa"
"Ohhh nan ramuwar gayya ce kenan shima yake neman aminiyarta ....idan haka ne ya zama dabba ya kuma zama mace tunda mata akasani da halin ramuwa,amma honey wallahi banajin jiddah zatayi abinda kace,kawai dai ya saketa zaiyi auren cin amana....hmmmm wanan yarinyar zata dandana kudarta indai wanan miskilin ne...dubi yadda ya taho da ita fuskarsa kamar hadari ita kuma sai wani murmushi take tana biye dashi"taja tsaki ta bude mota....
Kaya na gani na fada Abdallah ya biya kudi Wanda jiddah ta zaba ita kanta mamakin yadda ya kashe mata kudi takeyi....hmmm koda yake dama jiddah ta fada mata Abdallah baya kyashin kashewa mace kudi itada yan uwanta...idan hakane ta tsinci dami a kala itada yan uwanta zasu huta ....
********
Ramlah ce bayan tayi sallar magriba ta samu ummahta a daki zaune kan dadduma ta zauna gefen gado,ummah na rike da carbi tace "yadai ramlatu"
"Ehh ummah magana nazo muyi"
"Ina jinki"
"Ummm....dama Abdallah zai turo iyayensa maganar aurena,to jiddah taimun magana shine shima dazun yace in sanar dake ki fadawa magabatana iyayensa zasuzo gobe neman aure inso samune nan da sati biyu sukeso"
Jimmm kadan ummah tayi tana tunani ta nisa "sati biyu ramlah?kamar ana gudu?ke har kin amincewa aminiyarki zaki auri mijin nata?kina ganin bazaa zageki ba?"
Dan bata fuska ramlah tayi "ke ummah ya zanyi tunda sun matsa gashi na amince,har mahaifiyarsa ta rokeni yanzun so kikeyi ince musu nafasa gudun ace naci amana bayan nayi alkawari na amsa?ki duba dazun fa tare ya kaimu shopping da jiddah....tou nima dai na sanar musu da hakan sukaki suka kafe kina ganin jiddah har fushi tayi gashi na amsa suzo din yanzun baki ganin rashin dacewar haka?"
Ajiyar zuciya ummah tayi "Abdallah mutumin kirki ne ana shedarsa,idan hakane kinyi dacen miji saidai ayi adduar allah ya zaunar daku lafiya keda Aminiyarki ya kauda shedan laananne ..amma ina jiye muku hada miji dik amintarku kishi ba abin wasa bane"
Mikewa ramlah tayi tana kokarin ficewa don ta gaji da maganar ummah "ni yinwa nakeji ummah bari inci abinci,saiki sanarwa da su abbah maganar(kanin mahaifinta)...
"Da safe zani insameshi infada masa sai suzo nan su amshesu tunda nan zasuzo"
Ramlah kamar ta taka rawa don dadi, Abu daya ne ke bata mata farin ciki idan ta tuna da Abbah baya sonta.....
********
Daddare su abida na zaune a parlor take cewa yaya ib "nafara missing Ablah wallahi"kafin ya bata amsa wayarta tayi kara tana dubawa taga itace ta daka tsalle "kaga ita ke kirana"ta dauka cike da zumudi
"Abla'ta Kira sunanta cikin daga murya, murmushin jin dadi jiddah tayi ta amsa nan suka cigaba da hira cike da nishadi dik saida ta gaisa da kowa na gidan....tunda ta soma waya nafeesah ta kafeta da ido har ta gama "Anty naji ankiraki da wani suna da kika kira waya",
"Ehh Abla"
Yatsina fuska nafeesa tayi "meke nan?"
"Elder sister,haka ashmah da abida suke kirana....idan kinaso kema zaki iya kirana hakan",
Jinjina kai nafeesah tayi "daga yau Ablah zan rinka kiranki since you are my elder sister ko!"
Gyada mata kai tayi kawai ta lura nafisa akwai som hira sai kawai ta kwantar da kai a pillow tayi lamo.....as usual tunanin dake hanata sukuni shi ya fado mata bilal.....gabanta ya fadi tarasa me yasa yake hana rayuwarta sukuni,ya kashe mata aure amma yana can ya mance da ita kuma ya zalunceta ya zuba mata soyayyarsa cikin zuciyarta.....
Hawaye ne ya gangaro mata ta gefen ido ta kwantar da kanta a pillow.....
********
Tunda safe umman Abdallah ta fita da wuri ta isa gidan kaninta ta sanar masa da zaije nemawa Abdallah aure sakamakon mahaifinsa yayi tafiya,kuma bata sanar dashi Abdallah ya saki matarsa ba don tasan yanada zafi.....nan tayi breakfast ta dawo gida cike da zumudi take sanarwa dasu rumaisa zaaje neman auren yayansu,
Murna suka hau yi da ihu da tsalle yayinda afee ta mike ta fice daga parlorn duka suka bita da harara "kyaji dashi zaki dawo hanya ma",....
Matar kanin mahaifin ramlah itace ta shiga masifa "anya maman ramlatu kunyi adalci kuwa idan ramlah ta auri mijin aminiyarta dikda kumce su suka nemi haka?aure fa ba abin wasa bane"
Hmmmm"banida yadda zanyi dan da idona Naga yarinyar tana kuka har gida tazo da asuba take rokom ramlah ta auri mijinta dadai ramlah taki amincewa ma fushi tayi koda na bi ta ina kira bata saurareniba "
"Ita aminiyar kinji daga bakinta ko ramlah ta fada miki hakan da kika amince?ina gudun ai miki hali irin na dan yau fa maman ramlah asaki a kwali azo ana zaginku"
Dan bata fuska umman ramlah tayi ta soma gajiya da wadanan maganganun na wanan matar "tou ni bani xaki tsare da wanan tambayar ba idan yar tazo zaki iya tambayar ta,don yadda kike tambayar nan haka nayi mata"
Ganin ran umman ramlah ya baci yasa tace ", Allah ya kyauta,ya tabbatar da alheri"taja bakinta ta tsuke .....nan kanin mahaifin ramlah ya fito shirye cikin manyan kaya,
"Barka da zuwa ranki ya dade,"yacewa uwar ramlah cike da faraa yana kokarin zama,
Bayan sun gaisa ne ta sanar masa da maganar data kawota,yayi farin ciki sosai take ya kira wani dan uwansu ya sheda masa neman aure da zaai suzo suka amince sanan umman ramlah ta baro gidan....
*******
Wajen 11 jiddah ta shirya tsaf sanye da milk din material ta fito parlor inda gwaggo ke zaune,
"Barka dai gwaggo"ta zauna..."barka dai jiddah,an fito"
"Ehh"
"Kinata kadaici ko?gashi yau su fatima bazasuzo ba, Bari in shirya in shiga makota insamu zee baby inzo miki da ita in hadaku kawance ko yadda zaki samu yar hira"
"Laaa gwaggo dama kinbari bakomi ni banma fiye son zama da mutane ba"a sanyaye jiddah tayi maganar,
Yunkurawa gwaggo tayi ta mike....."kinga bari ma in shiga Dole kisamu me debe miki kewa jiddah tunda kimzo ne ki mance damuwarki ki saki jiki bakyayi zaman kadaita ba bari ina zuwa"ta dau hijabinta da ta ajiye gefen kujera ta fice,
WhatsApp dinta ta bude haka kawai tasamu kanta da bude profile din bilal hotonsa ne da singlet ya gyara gashin yayi dariya,wani takaici ne ya lullubeta ta shiga tambayar kanta ke jiddah meye naki ma na bude hotonsa kina kallo mutumin da ya mance dake ma yanzun?hmmmm da sauri ta kife wayarta tana kokarin daukar remote......
Suna zaune parlor gwaggo tayi sallama,bilal ne gefe yana kallon hoto a wayarsa gwaggo tabi ta bayansa,hoton wayar idonta ya sauka kai amma bata lura ba ta shige "oyoyo gwaggo"inji zee baby dakewa kanwarta kitso,
"Keda nazo wajenki kuma na sameki kina kitso?"
"Gwaggo me zaai miki kinada aiki ne?"
Ammiey ce ta shigo parlorn "haba naji murya kamar hajiya gwaggo,barka da zuwa",
"Barka dai wajen zee nazo ai,inaso tazo muje gidana wajen bakuwata inaso in hadasu tadan saba da ita ko shigowa itama saita rinkayi",satar kallom bilal zee baby tayi"su yaya anata kallon waya an sharemu",
Murmushi yayi ya dubi gwaggo"ina yini"ya gaisheta,
Cike da kulawa ta amsa masa sanan yacewa zee "sa idonki yayi yawa kefa ma kawa kikayi fita zakiyi nima su sagir nake jira mu fita in zaga gari",
"Tou kujirani inje gidan gwaggo inga sabuwar kawata...idan nadawo sai muje tare"daga mata kain yayi ya mike ya bar parlorn tabi bayansa da kallo har ya bace,
Gwaggo da Ammiey sukayi yar hira har zee ta karasa kitso tabi gwaggo....
****
Zee da jiddah suna zaune shiru "ke kam bakuwa tunda na shigo nike zuba miki surutu ke baki magana ne?kodan ke kyakkyawa ce?"
Murmushi ne ya subucewa jidda "kema din kyakkyawa ce ai zainab....nice to meet you"
"Nice to meet you too,yanzun xantafi gobe zanzo muyi hira inaso zanbi brother na da kyakkyawan bakon gidan mu kamar ke zamu zagaya gari gobe zanzo muyi hira kema zakizo wajena ai wataran ko?"
Gyada mata kai jiddah tayi alamar ehh,zee tace "ko kuma gobe idan nazo da yamma zamuje ki gaida Ammiey kinga sai mudan taka ki mike kafarki ko?".kara gyada mata kai tayi tana murmushi,zee ta lura da jiddah tanada faraa amma batason yawan surutu daga ganin yadda komi saidai tayi murmushi.....sallama tayi mata,ta tafi....
*******
A parlor ta tarar da sagir da bilal sun fito har zasu wuce "au da tafiya zakuyi ku barni yaya bilal"cike da shagwaba take maganar,
Daure fuska sagir yayi "meye haka kamar wata jinjira"
"Ya bilal dan allah kujirani muje tare ...wallahi naje ne ina hira da sabuwar kawata saidai bata cika son magana ba "
Sagir ya amshe zance "gashi ta hadu dake aku ba"suka tuntsire da dariya shida bilal.... Bata fuska tayi "kasan me gata kyakkyawar gaske kamar ka ya bilal"
Daga gira daya yayi "really....takaiki?"
"Ina tafini kyau yaya hmmm kyakkyawar gaske ce fa,tafi budurwarka kyau ma"tayi maganar cike da son gano idan bilal nada budurwa don zuciyarta na raya mata abubuwa....
Jimmmm kadan yayi kamar me tuno wani abu,fuskar jiddah ya hasko.....anya akwai wadda takai hauwau sarauniyar mata kyau sarauniyar data zame masa sanyin idaniyarsa,wadda soyayyarta ta zama bishiya tayi rassa a zuciyarsa,akanta yake kallon ko wace mace a matsayin namiji.... kyawu na fuska irin na jiddah babu kamarta cikin mata kashi dari dakyar asamu kashi goma masu kyau irin nata....
"Kayi shiru",zee tace tana kallom kwayar idonsa cikin zullumi....kamar daga sama yace "babu macen da ta kai budurwata kyau...cikinko har kawar taki sabuwa"
Hmmmmm tace zuciyarta na harbawa "don baka ganta bane....amma zan shigo da ita ai"
"Ko kim shigo da ita bazan kalle ta ba",
Sagir ya katsesu "ke in zakibimu jeki shirya ki fito ki kuma tambayi walida idan zata dan kar Ammiey tace mun barta"
"Tou "tace ta shige....
*******
Sadakin ramlah dubu dari uku aka bada da kudin gaisuwa....nan akasa ranar aure sati biyu masu zuwa......
*SLIMZY✍🏼*
[11/5, 7:41 AM] Mis Slimzy😍🥰: *💥💥AUREN FARI...💥💥*
*SLIMZY✍🏼*
_Wattpad@slimzy33_
*SADAUKAR WA:*
*HAUWAU MU'AZU AMIR RUMA...*
*22*
Daddare Abdallah yana zaune a parlorn mahaifiyarsa kannensa suna zagaye dashi su meenah sarkin rawar kai sai wani surutai sukeyi "ya Abdallah kawai idan anyi aurenku da Anty ramlah ka hadamu da ita muje umarar tare tunda dama next month zamu tafi ko"
"Ehh ai taren zaku tunda lokacin sungama amarci,yauwa Abdallah nace akwai wata hidima ne da zakuyi na bikin mufara shirye shirye don yanzun ne zakai auren da zan nuna farin ciki"
Girgiza kai Abdallah yayi "babu abinda zanyi ummah,ai ba auren fari bane sanan kuma auren kinga yadda zaayishi babu wani shiri bare armashi"
"Haba Abdallah,ya xakace haka bayan yarinyar nan budurwa ce"..... Abbah ne ya fito daga sashensa ta kofar baya ya shigo parlorn sanye da riga da wando brown kaftani hannunsa rike da makullin mota da wayarsa,....dukkansu suka shiga taitayinsu banda ummah dako kallon inda abbah yake batayiba tunda yake fushinsa,
"Barka da fitowa abbah ina wuni"a sanyaye afee ke gaishesa,dan murmushi abbah yayi "barkanki ummulkhairi ya kike"
"Lafiya lau Abbah"ta amsa hade da murmushi,
Da rumaisa da meenah suka hada baki "barka da fitowa abbah"
"Barkanku ameenah da rumaisa"...ya amsa yana kokarin wucewa,
Tsugunnawa Abdallah yayi hade da kaskantar da Kai cikin faduwar gaba da fargabar ko zai amsa ya soma gaishesa, "Abbah barka da fitowa....ina wuni"..abbah beko san Abdallah na wajenba har zai fita ya dawo,
"Hajiya,wato bakida tsoron allah ke ko?ashe bakida hankali bakida tunani?har yanzun bakisan meke miki ciwo ba bakisan rayuwar duniya ba,amma kibi duniya a sannu kinji don zata karantar dake,yanzun nasan cewar ke kadaice kika haifi Abdallah habiba"
"Haba Alhaji....me kake fadi haka ya zakace haka?"
Cike da takaici yace "ehh ke kika haifesa kece keda ikon sashi yayi ko yakiyi,kinsashi ya saki matarsa kuma kina shirin aura masa wata cikin sati biyu,saboda ki ninamin iyakata ma dan uwanki kikasa yaje ya shiga gaba don nemawa danki aure ko habiba?tou kusani taron biki saidai kuyi a wani waje baa nan ba"
Gumi ne ya karyowa ummah ta sa hannu ta share cikin damuwa da tashin hankali take kallon yadda abbah ke magana cike da izza da isa,sanin halin Abbah yasa ta sunkuyar da kai batare da tace komiba zuciyarta ce kawai ke tafarfasa sanan a gaban yaranta yake ce mata batada hankali duniya zata bi da ita, matukar tace zatai masa musu to tasan zai mata abinda yafi hakan,
Har yakai kofar fita ya nuna Abdallah da yatsa,"banaso ka kara ganina a hanya ko a ina ka nuna nidin ubanka ne"cikin daga murya abbah ke maganar,..wata irin razana Abdallah yayi yana kallon Abbah cikin tashin hankaki ga gumi da dama ya gama jikewa dashi "ehh ka kalleni da kyau Abdallah munkai matsayin da zansa doka ka karya saboda ka dogara da kanka kasamu abun duniya...munkai matsayin da zanbaka umarni ka tsallake umarnina kabi umarnin mahaifiyarka,to da kai da ita dukkanku baku isa ba Abdallah kunyi kadan wallahi....dik abinda zakuyi kuje kuyi wani waje amma baa cikin gidana ba don nan munallina ne Abdallah"
Rugowa afnan tayi ta rike kafar Abbah ta fashe da kuka "dan allah abbah kayi hakuri ka yafewa yayah Abdallah da ummah"...kallon afnan yayi cikin takaici da bacin rai ya janye kafarsa ya fice.....
"Ummah,kibi abbah kintashi hakuri kinajin fa abinda yake cewa"rumaisa ke magana kamar zatai kuka cikin damuwa,
Nisawa ummah tayi "zai sauko haka yake idan yayi fushi"....
*******
Kaiwa da komowa ramlah keyi cikin dakinta da waya a hannunta,wayar Abdallah ta kara dialing a karo na biyu,
Yana kwance akan gado yana kallon ceiling kalaman Abbansa keyi masa yawo a tsakar kai,anya yayiwa Abbansa adalci Haka da yayi masa na nuna masa iyakarsa?kiran wayarta ne ya shigo,ya daga wayar a hannunsa ganin itace ya kife wayar yayi tsaki ya maida kansa kan pillow cike da damuwa,
Abbah ya kasa fahimtar abinda jiddah ta aikata yake kokarin sashi ya koma zama da ita,shi abbah meyasa zai yarda da jiddah fiye da yadda ya yarda da dansa na cikinsa,?wani abu ne ya taso ya tokare masa makogwaronsa,
Tsaki ramlah taja, shin ina ya shiga ne ina kiransa baya daukar wayata?ina lura da yanayinsa da take takensa a yan kwanakin nan....zuciyarta ke kara azalzalarta ta kara dialing numbersa a karo na uku,
Kiran wayarta ne ya shigo wayarsa,fusata yayi yana kallon wayar,besan meyasa wasu mutanen jahilai bane jakai,tayaya zaka kira mutum fiye da sau uku ka cigaba da kira,da zarar ka kira na farko baa dauka ba ka kira na biyu baa daukaba kasan mutum be kusa da wayar yana wani uzurin ne idan kayi na uku sai ka bari amma ka cigaba da kiran waya,
Katsewa wayar tayi ta sake kira,a fusace ya dauki wayar,ta gefen ramlah kuwa ajiyar zucuya tayi tace "hello....dear inata kiranka bak...m"bata karasa ba ya katseta "i don't feel like recieving your call ne shiyasa"yace cike da isa yana daura fuska kamar tana ganinsa,
Cire wayar ramlah tayi a kunnenta ta kalla anya Abdallah ne ta kira,ta kara maida wayar cikin rawar murya ta soma magana "ok am sorry please fatan ban bata maka rai ba ko?"a sanyaye tayi maganar tana cije baki,
Jin yadda ta bashi hakuri yasa jikinsa yadanyi sanyi dikda bacin rai da yake ciki ya danne "tunda kikaga ban dau wayarba inada uzuri....note idan kikamun misscall daya ban daukaba karki sake kibari wani lokaci. Ok?"yace ,daga kai tayi kamar yana ganinta tace "kayi hakuri dear"
"Don ko jiddah batamun call haka....."ya datse wayar,
Jefar da wayar tayi kan gado ta fada gado ta kifa ciki tana sauke numfashi sama sama,mamakin Abdallah ne ya lullubeta ji yadda yake mata magana cikin gadara ko a jikinsa,ta lura iya gaskiyarsa yake maganar.....juyawa tayi ta kwanta rigingine,sanan har ya fara mata misali da matarsa kenan har yanzun da guggubin son jiddah cikin zuciyarsa....kishi ne ya turnuketa taji kamar taje ta kashe jiddah ta huta wai meyasa jiddah ke neman zamar mata karfen kafa? Dole ma ka mance da juddah Abdallah don kai mallakina ne yanzun nikadai....a fili tayi maganar zan mantar da kai jiddah,zaka banbance tsakanin jiddah da Ramlah ba daya bane ko a alphabet na sunanmu akwai wadanda sukasha banban.....
Anya Abdallah ka kyauta abinda kayiwa ramlah kuwa?tana sonka sosai kuma yarinyar nan ita ta fargar dakai da wuri daga cin amanar da jiddah tayi maka ya dace itama ka bata wani gurbi cikin xuciyarka... jikinsa ne yayi sanyi....
********
Yau ta kama sati biyu yau ya kasance auren ramlah da Abdallah....
Kannen ummahn ramlah ne zaune a parlor suna gyaran cabbage da zaasa a jealouf umman ramlah ta fito tasha leshi sai daukar ido yakeyi "sannunku da aiki murja anata fama ko?"
Suka amsa "ehh wallahi,kaga uwar amarya gaskiya kinyi kyau sosai Allah yasa alheri"
Washe baki ummah tayi "Ameen"ta wucesu tayi waje tana kiran yaron kanin babansu ramlah "Ina mahmud din ga kudin lemo a karbo katan hudu"
Nan aka soma gulma masu yankan cabbage "murja,wanan wani irin biki ne babu armashi kamar bikin bazawara?wai ko kinsan jiya da zamusa ramlah a lalle babu wani Wanda yazo daga dangin yaron nan kuwa?"
Waigawa murja tayi "hmmm bareerah kenan,toni yadda naji ma ance uban dan beson auren gaba daya dan yanzun haka gidan angon babu wani shaani da akeyi shiru ne gwara ma mu nan munata shaaninmu"
"Tou meyasa hakan murja?ita maman Ramla dukiya ce ta rufe mata ido take kokarin mika yarta irin wanan gidan?ina jiye musu wulakanci kuwa"
Ramlah ce ta fito daga dakinta taci ado sosai tasha lalle tayi kyau na kece raini don Abdallah ya zubo mata kaya a akwati dan sha biyu ummah tasashi yayi,taji hirar da kannen ummanta keyi amma saita basar tayi gaba wasu kawayenta da sukayi makaranta tare su biyu suna biye da ita, suma karya ta zuga musu cewar dangin mijinta a Germany suke shiyasa bazaai wani taro ba sai sundawo.....
Karfe biyu da rabi na rana a kofar gidan alhaji Auwal aka daura auren ramlah da Abdallah inda mutane suka shaida aka danyi walima aka watse....
******
Mahaifin Abdallah kuwa yakai kololuwa a bacin rai hakan yasa yana sashensa yana harhada wasu takaddu da dama zaije dubai dasu nan da nan yakira waya akai masa booking private jet dan tafiya,
Ummah ce ta taso Abdallah yana sanye da blue din shadda me ruwan sararin samaniya da hula da takalminsa da agogo baki masu tsadar gaske suna shigowa abbah ya daka musu tsawa "ku ficemun a daki,me kuma kukazo kuyi mun a nan habiba?kamarni da girmana a cikin garin nan yau naje masallaci na jumaa duniya ke nunani ana daura auren dan dana haifa da wata nan mutane ke tsegumin cewa ban halarci wajen ba?duniya batasan da cewar dana zaiyi aure ba kamar auren sa na fari"
Tsugunnawa Abdallah yayi gaban Abbah "ka yafemun abbah....nayi kuskure amma...."daga masa hannu abbah yayi idanuwansa sunyi jajir "ya isheni haka Abdallah kayi abinda kakeso ko a lokacin da ka gadama,amma zaka nemeni nima a lokacin da babu abinda zan iyayi maka Abdallah,zakazo da kafafuwanka lokacin da gari ya waye maka,kabi mahaifiyarka ka ficemun a daki"..mikewa yayi ya bi bayan ummah wani irin zafi da tsanar jiddah ne yaji cikin zuciyarsa don dik saboda ita ne hakan ta sameshi.....
Karfe hudu na yamma ya dau waya yana tare da yan wajen aikinsa da sukazo masa allah ya sanya alheri ya kira wayar ramlah,
Tana cikin kawaye anata mata hoto taga kiransa,murmushi tayi "hello Angona"tace cikin kashe murya,
"Ummm,ya kike"yace a dakile kamar dole,
"Lafiya lau....ka kasa hakuri ne ka kira kaji muryata mijina?"tayi farrr da ido....
"Hmmm nakira ne,karfe shida zanzo mutaho gidan mu, saboda inada taro da zanyi da wasu turawa karfe tara na dare yau akwai contract da zasu bawa company namu to memakon inyi lattin zuwa daukarki sai inzo karfe shida na yamma ko?"
Shiru tayi,ji tayi kamar ya caka mata mashi a kirji nan da nan taji wani jiri na daukarta,meyasa Abdallah zaiyi mata hakan?daga ganin alama ma idan yazo ita kadai zai dauka,to kawayenta fa da zaai siyan baki?yan uwan mahaifiyarta fa da zasu kaita gidanta kamar ko wace mace?....
"Hello,naji kinyi shiru yadai"...kada kai tayi gabanta na tsananin faduwa,
"Kenan mu shirya karfe shida"tace cikin rashin kuzari,
"Ki shirya dai, don matata kawai zanzo in dauka itace dolena,don ni bana wanan al'adar ta hausawa kinaji ai"
Jimmmmm tayi ta kasa magana sai kallon gefe daya kamar gunki,saida yace "ko bakyajina ne"dakyar ta hadiyi wani miyaun bakin ciki "ehh inajinka...shikenan"be jira mezata ce ba ya kashe wayarsa,
Komawa yayi cikin abokanansa ya zauna,kallo daya zakaiwa Abdallah ka hango damuwa a fuskarsa ba kamar ko wani ango da zaka hango farin ciki ba a fuskarsa,
Kawar ramlah ce tazo ta rike kafadarta "yadai amarsu,ango ya hada mana karamin reception ne?"...jimmm tayi tai murmushi cike da kwarin gwiwa "hmmmm kinsan mutumin nawa dan boko ne,yacemun karfe shida zaizo ya daukeni"
"Ya daukeki?kintabajin inda ango yazo daukar amarya shikadai batare da abokai ba"kawayenta suka hada baki,
Yatsina fuska tayi ", surprise yamun wlhy karfe shida zaizo mutafi saboda Abuja zamu kwana gobe jirgin safe zamubi zakuje germany"
Tafawa kawayenta sukayi "kaji manya,amma ramlah kin caba kin fada gidan daula Allah yasamu a damshinki"mikewa tayi tabi wata kofa don taje sanarwa ummanta sakon Abdallah.....
Tsaye sukayi itada ummah,takaici yasa ummah tace "gaskiya ki fada masa baayin hakan ramlah wanan ai zagi zai jamun wajen mutanen kauye dukda dama kuss kuss sukeyi"
Cikin rashin jin dadi ramlah tace "kiyi hakuri ummah,ki sanar musu da yadda na sanarwa kawayena kinga kin kashe bakin kowa"nan ta kwashewa ummah yadda sukayi da kawayenta,..."naji amma banga jiddah ba tunda aka soma bikin nan ramlah anya kuwa?"
Gaban ramlah ya fadi tace "ummmah jiddah nacan da mutanen ta,dazun ta kirani aita. Kosa a daukoni bakiji yadda take zumudi ba ummah wlhy ni kunyarta nakeji ma na aure mata miji"....shiru ummah tayi taja ajiyar zuciya "tou ba giringirin ba tai mai dai",ta juya ta fice ramlah tabi ummah da kallo kafin ta zauna gefen gado tana jan ajiyar zuciya.....
********
Zee ce zaune da jiddah a garden din gidan gwaggo can gefensu nafeesa ce ke wasa da igiya da yamma bayan laasar,
"Waike jiddah tunda kikazo muke kawance baki taba zuwa gidan mu ba,sanan yau din nan ina miki kallom kamar wani abu na damunki"
Wani irin sanyi jikin jiddah yayi yau haka kawai takejin kanta cikin wani yanayi na damuwa da yafi da haka kawai takejin wani abu ne ya faru da ita,amma bataso zainab tasan rayuwarta "babukomi"ta kamo hannun zainab tace tana murmushi "kuma gidanku dama yau nace zan shiga inda badan ke da kikaxo ba"
Fuzge hannu zainab tayi cikin sigar fushin wasa tace "inda kinaso kije aida kin zo koda nazo sai kice muje ko?idan da gaske ne yanzun kizo mana muje?"
Murmushin karfin hali jiddah tayi haka kawai taji kwalla ta cicciko a idonta,shikenan tanaji a jikinta an kwace mata miji,idan har bata mance ba a lissafi yau ne bikin Abdallah da aminiyarta ...hawaye ya gangaro mata a fuska batare da tasani ba,itako zee kidimewa tayi ganin jiddah na hawaye ta girgiza ta "kiyi hakuri friend idan bakison zuwa gidan mu ne na hakura ni zan cigaba da zuwa inda kike badamuwa kamar yadda gwaggo ta bukata"
Girgiza kai jiddah tayi ta share hawaye da sauri "ba haka bane zainab,nikadai nasan abinda nakeji cikin zuciyata yau din nan....wani mummunan al'amari ne yasamu rayuwata"wasu sababbin hawaye suka kubuce mata,
Ruko hannunta zainab tayi kamar zatai kuka cike da damuwa "wani mummunan lamari kuma?meyasa zakice haka?haba jiddah meyake faruwa dake?banason ganin hawayenki idan nina bata miki rai kiyi hakuri"ta hada hannuwanta biyu tanabawa jiddah hakuri,
"Bake bace friend karki damu zan sanar dake wataran,tashi muje in cika miki burinki na zuwa gidanku inaso ingaida Ammiey ma"babu musu zainab ta ruko hannunta suka shiga cikin gidan gwaggo lokacin ta idar da sallah tana lazumi suka shiga,..
"Ah ah ina zuwa yan biyun gwaggo"
Shiru jiddah tayi ta sunkuyar da kai ta kasa fadawa gwaggo tana son zuwa gidan su zainab ne,ganin tayi shiru zainab ta kyalkyale da dariya
"Gwaggo,wai jiddah zataje gidanmu ta gaida Ammiey shine takasa bude baki ta fada miki"
"Laaaaa amma jiddah anyi yar banzar yarinya,kuje allah ya tsare a gaidata".....
Suna fitowa gate din gidan gwaggo saina su zainab coffe brown,wani irin faduwar gaba ne ya ziyarceta,take taji kafafuwanta sunyi mata nauyi,wani irin abu ke yawo a kanta wanda yasa ta ruko hannun xee ta dafe kirjinta lokacin da suka sako kafa a farfajiyar gida......tozali da bayan wani guy yana waya can gaban fulawoyi yasa taji wani abu ya caki zuciyarta take ta runtse ido,bayan bilal ta tuno lokacin da yazo gidansu na karshe da zai tafi yana hawaye,shine ta hasko yasa ta kara runtse idonta ta budesu akan hadadden farfajiyar gidan mai girman gaske daya wadatu da fulawoyi masu kamshin gaske can gefe fararen kujeru ne zagaye da table.....jikin jiddah ya soma rawa dakyar take daga kafa suka shigo zee ta rufe gate din da karfin gaske,
Tana hango Bilal ya rufe kunnensa da dayan hannunsa batare da ya juyo ba,dariya zee ta kwashe dashi "su yaya ana waya baaso a ji karar gate hmmm"tayi farrr da ido ta kalli sashen da jiddah ke tafiya"ya naga dakyar kike daga kafafuwanki?kodai kunyar shiga gidan mu kikeji?"... girgiza kai jiddah tayi gabanta na cigaba da faduwa "ah ah"
"Tou ga inda zamubi can ta bayan yaayah,wanan kofar kamar an rufeta"haka sukazo wucewa yana waya da ummah yake waya amma yana jiyo takun takalmi yasa yayi shiru har suka wucesa,zee ce ta juyo tai masa murmushi da dage masa gira daya,
Dariya yayi mata yana shafa sajensa.....wani kyau ya karayi dakyar ta kauda idonta....
Bilal kuwa nisawa yayi yaja numfashi a karo na farko gabansa ya fadi,dik maganar da momy takeyi baya jinta saboda yadda kamshin turaren jiddah ya bugi hancinsa da kahon zuciyarsa ya tafi kwakwalwar kansa yayi circulating....cire wayar yayi a kunne ya kalli hanyar da sukabi be gansuba, meyake shirin faruwa dashi?bata taba masa gizo ba sai turaren ta?wanan kamshin turaren jiddah ne ita kadaice yasani da wanan turaren,murmushi yayi mai ciwo take yaji farin ciki ya lullubesa,dikda yasan jiddah bazatazo nan ba amma yayi matukar fari ciki da yaji kamshin turaren annurin zuciyarsa farin cikin rayuwarsa.....dole yabi bayansu don tabbas yasan ba zainab bace me turaren nan da alamar su biyu suka wuce dole inje inga mai kamshin farin cikin rayuwata koda kamshin in shaka inji dadi.....
Tafiyar kasaita yakeyi wayarsa na hannunsa,sai lokacin ya tunada bai kashe wayar ba ya dubi wayar yaga momy ta kashe "i'm sorry momy its like naji kamshin hasken rayuwata ne,kamshin da ko a cikin bakin duhu na rijiyar turaruka najishi saina banbance kamshi irin na jinin jikina..... zuciyata ta tsunduma cikin kogin soyayyarki jiddatu....har yakai numfashina yana fita da soyayyarki ne ko wani second na rayuwata da zucuyata ke bugawa da kaunarki take bugawa"shi kadai yake magana cike da shaukin soyayya yasa hannu gefen kirjinsa "kinjiko yadda kirjina ke bugawa da kaunarki jiddah .....kiyafemun idan kin fita iddah in zama abokin rayuwarki a karo na biyu"....a kofar balcony na parlorn ya tsaya bugun zucuyarsa ya tsananta.....
*******
Tafe suke a mota ta sunkuyar da kanta jikinta yana fidda wani irin sihirtaccen kamshi wanda tun shigowarta cikin motar gaba daya motar ta gauraye da kamshin turaren Ramlah.....da kansa yake driving idanuwansa suna kan titi yana sarrafa mota amma ya dau hannunsa daya yakai kan hannunta ya rike yana murzawa yana shafawa laushin hannun Abdallah yasa ramlah taja numfashi wani abu yayi mata yarrrrrrr cikin jiki......kasa hakuri tayi ta dago idonta ta dora kan fuskarsa,ga mamakinta titi yake kallo bema ko san tanayi ba kenan yadai kai hannunsa jikinta ne ....murmushi tayi nasara ta farko kenan tunda har zai iya kasa jurewa yakai hannunsa jikinta ....
TOH FA GA RAMLAH GA ABDALLAH......
MUN TSUNDUMA CIKIN KUNDIN LABARI....YAYA ZAMANSU ZAI KASANCE?....YA ZATA KASANCE A GABA?
*ALBISHIRINKU MASOYA....AKWAI LITTAFIN IZZATA COMPLETE DA ZAINUL ABIDEEN MAI* *BUKATA TA TURA 300 CIKIN WANAN ACCOUNT DIN 2255398727 ZENITH BANK AMINA JIBRIL....IDAN DAYA* *ZAKI SIYA 200 KACAL.....KARKU MANTA SAYEN NA GARI MAIDA KUDI GIDA GA NUMBER* *TA 07042277401 GA MAI BUKATA.....*
*SLIMZY✍🏼*
[11/5, 7:41 AM] Mis Slimzy😍🥰: *💥💥AUREN FARI...💥💥*
*SLIMZY✍🏼*
_Wattpad@slimzy33_
*SADAUKAR WA:*
*HAUWAU MU'AZU AMIR RUMA...*
WANAN SHAFIN KACOKAN SADAUKARWA NE A GAREKI K'AWATA *FEEDHOM.....*💥 MARUBUCIYAR *MATAR ABDALLAH* ....KO KUNSAN YANZUN HAKA TANA NAN DA LABARI MAI KAYATARWA WANDA YAFI *KWAD'AYI* DADI DA ILIMANTARWA....KU GARZAYA DOMIN NAMU BA IRIN NASU BANE NAIRA 200 KACAL YA ISHEKI KI MALLAKI *SILAR* *WAYE?...* SON SO NAKEYI MIKI K'AWATA❤️❤️🥰🥰💋
*23*
Parking motarsa yayi a harabar gidan,bin cikin gidan ramlah takeyi da kallo babu abinda ya canja sai kyau gidan da ya kara mata dikda babu wani abu na gyara da yayi dangane da aurensa,kallonsa tayi suka hada ido ta sunkuyar da kai,karasa parking yayi ya dubeta "muje Ramly"yadda ya kira sunanta ba karamin dadi yayi mata ba,bude motar tayi ta fito wata irin iska mai sihirtaccen dadi ce take kadawa a garin sakamakon hadarin da akayi ruwa bai sauka ba....yana tafe tana biye dashi har suka karasa balcony din da zai sadaka da parlorn gidan.....yana kokarin bude kofa mai gadi ya karaso ya dan sunkuya "barka da zuwa ranka ya dade, Allah ya sanya alheri yasa albarka"
"Ameen baba,ammm a kunna tanki mana sanan zan fita ka kula da gidan inada meeting bayan ishai na awa daya,idan an dauke wuta a kunna gen"
"Tou ranka ya dade"....satar kallon ramlah mai gadi yayi hade da jinjina kai yana tafe yana waigensu har ya karasa wajen zamansa,
A parlor ta zauna ta sunkuyar da kai,kunna globes yayi ya kunna Ac hade da fanka ya wuce sashensa,minti kadan ya fito ya cire rigar shaddarsa sai farar singlet da wandon shaddar,
A gabanta ya sunkuya ya cire mata gyale,lumshe ido tayi yana karewa fuskarta kallo,gabaki daya ta sauya masa zuwa fuskar jiddah....da sauri ya kauda kai gefe cikin faduwar gaba,.... kusan minti uku suna a haka ta bude idonta taga kansa a gefe ga hannunsa rike da fuskarta,muryarta a sarke tace "yadai....dear"..."umm umm babukomi ramlay"dagota yayi ya rungumeta sosai a jikinsa ya zame dankwalin kanta yana shafa sumar kanta da tasha gyara yana shafawa wani sihirtaccen kamshi ke fita daga jikin ramlah,bugun zuciyoyin su a tare suke harbawa ramlah bata taba tsintar kanta cikin wani yanayi me kama da hakanba kissing din wuyanta yayi yana shafata a hankali ya rada mata a kunne "am sorry amaryata,banji dadi ba daya kasance yau kina amarya zan fita inje meeting headquarter dinmu amma banida yadda zanyi...inaso in gina mana rayuwa ne hope ranki be baci ba"
Yadda takeji yasa ta kasa amsa masa sai kada masa kai tayi alamar batayi fushi ba,kissing dinta yayi a goshi yaja ta ya Kai ta dakin ta wanda ya kasance tsohon dakin jiddah ada....
*******
Bilal karo sukayi da sagir a kofar shiga parlor "ya man,ina kokarin zuwa insameka sai gaka kuma?lokacin sallah ya karato muje masallaci ko?"
Shiru bilal yayi yana jiyo sautin dariyarsu a tare gabansa na cigaba da faduwa,yanaji muryar kamar ta jiddarsa saidai bayaso yayi abun kunya, tabosa sagir yayi "mutumina yane naganka hakan meke faruwa ne?"
. girgiza kai kawai bilal yayi"babukomi muje masallacin"
"Owk"a tare suka jero suka nufi massallaci,
Ammiey cike da tsokana tace "anya wanan bakuwar bazanyiwa dana kamunki ba kuwa?wanan kyau haka? Masha Allah tubarkalla amma ku fulanine ko?"
Sunkuyar da kai jiddah tayi tana murmushi "Ammiey abbana ne bafullatani mutumin ruma ne, mahaifiyata ma tanada dangantaka da fulani dan kakarmu mace bafullatana ce"
Zainab ta mike "bari inje inyi sallah nidai,don ke nadan kina onnnn koh?"tace cikin sigar tsokana,
Walida kanwar zee ta amshe "kedai yaya zee akwai tsokana ita bata cika son magana ba amma ke kiyita zuba"
Harara zee ta watsa mata sanan ta dubi ammie tace "ammiey kinajin me walida ke fada ko? tou wallahi zan ji mata ciwo don batada kunya"
"Kar insakeji walida,yayarki ce fa"...mikewa zee tayi "mu shiga ciki kinji idan nayi sallah sai muci abinci"
Babu musu jiddah ta takewa zainab Baya zuwa dakinsu na yan mata,
Tare suka fito jiddah tanayiwa Ammiey saida safe sagir ya shigo yacewa zainab "ke kawo mana lemo muna harabar gida ki hado da cake"
"Owk"zainab ta juya ta shiga kitchen cikin minti biyar ta fito hannunta dauke da tray ta dubi jiddah "muje inbasu sai in rakaki ko?sai ku gaisa dasu"
Tun daga nesa Bilal yake kallonsu saidai jiddah kanta a kasa take tafiya amma take ya hango fuskarta mikewa yayi tsaye kamar zararre yana nuna jidda da yatsa,sagir ya dubesa "yadai mutumin naga kana nunasu zainab da yatsa ko kaga wani abu ne?"girgiza kai yayi jikinsana rawa ya koma ya zauna,
Sunyo dabbb dasu gaban jiddah ya cigaba da faduwa "ammm kiyi hakuri zee"cakkk zee ta tsaya tana kallonta cike da tuhuma "yadai menene kike bani hakuri"
"Kafafuwana sunamin nauyi,banason ina kusantar inda maza suke saboda halin da nake ciki a yanzun"
"Yayyin nawa ne maza?bakiso ki gaisa dasu yaya sagir ko?hmmm kodai kunya kikeji ne?"
Muryarta ce ta soma rawa ta juya ta dan gifta tana tafiya batare da tako kalli inda suke ba,tabe baki zee tayi ta karasa inda su sagir ke zaune ta ajiye musu tray a gaban table dinsu ",barkanku da hutawa"
Satar kallon bilal tayi taga ya rike habarsa yana kallom wani sashi na daban,juyawa tayi tana kallon inda yake kallo bataga komi ba,zungurinsa tayi yadan juyo a furgice,ta dage masa gira daya "yadai.... naganka cikin wanan yanayin akwai damuwa ne?"tace cikin nuna damuwa,"babukomi kanwis....kawar taki ce waccen?"besan lokacin da tambayar ta kubuce masa ba,
Juyawa tayi ta kalli inda jiddah ta juya baya ta girgiza kai "nayi nayi da ita tazo ku gaisa dukkanku taki wallahi,kunya takeji sanan wai a yanayinta be dace tana kusantar maza ba"
Tsaki sagir yaja "aikin banza...mtswwww don tanada kyau ne yasa tace hakan?toko hurul ain suna kula mazan aljannah"kyalkyalewa zee tayi da dariya tana kallon sagir "haba yaya,kaidai bakasan uzurinta ba da tace hakan...ummm kunga tafiyata natafi in rakata nabarta tsaye"
Shafa kai bilal yayi hade da cije lebensa,zucuyarsa nada muradin ganin bakuwarcan kodan kamshin sanyin idaniyarsa da takeyi,ko wacece yana son ganinta amma bayaso ya nuna musu hakan don kada suyi zargin son ta yake don shi yanada wadda yakeso....
Karasowa zee tayi hade da kama kunnuwanta "afwan habeebty wlhy su yayah basuji dadi ba kinki zuwa gaidasu"...murmushi tayi "next time insha allahu"
Tare suka fice suka Shiga gidan gwaggo....
*******
A inda ya barta nan ya tarar da ita tana zaune ta kwantar da kai jikin kujera kanta babu dankwali, agogo ya kalla sanan ya dubeta "baki sallah ne?"
"Inayi dear"ta amsa a takaice idonta akansa sosai yayi mata kyau tabi pink lips dinsa da ido masu kama dana mata,
"Ramly zantafi, already nayi latti baxan jima ba awa daya na dawo nan hotel 17 zaai conference din kinji?hope babu damuwa"
"Babu Allah ya tsare"ta amsa hade da lumshe ido,ya sunkuyo yayi mata kiss sanan ya fice,bude idonta tayi nan da nan sukai jajir yana fita ta gyara zama "wani irin abu ne ranar auren mu ma sai yaje conference ?gashi nikadai ya bari cikin gidan nan da wanan daren?"....hmmm koda yake ya bani hakuri don baa son ransa bane,kuma yana sona tunda ita jiddah batasamu hakanba,
Mikewa tayi ta shiga dakin,bin ko ina da kallo take daki hadadde aljannar duniya wanda in ka kwanta baxakasan safiya tayi ba shine jiddah take kasa bacci kullum korafi,saboda batasan yadda zata shawo kan mijiba jaka kawai......
Tana zaune ta sauya wasu kayan a parlor tana kallon tv minti minti takan daga ido ta kalli agogo,shi da yace mata karfe tara zai dawo gashi har tara da rabi,idanuwanta ne suka cicciko "kadawo dear i miss u",ta furta a fili bata gama rufe baki ba taji horn din motarsa alamar ya dawo,murmushin jin dadi ne ya subuce mata mikewa tayi ta gyara zama da kyau ta cigaba da kallon tv,....yana shigowa ya tsaya daga jikin kofa yana kallonta tayi kyau sosai ashe wayayya ce tunda har ta iya yin wanka ta sauya kayan jikinsa ya furta a ransa,a zahiri kuwa hannunsa ya bude alamar ta taho mikewa tayi ta taho kallonta yakeyi take ta rikide masa zuwa jiddah wadda dik lokacin da yayi mata hakan take taku komi na jikinta na motsi musamman dirinta da ko kafarta ta motsa sai ya motsa,sabanin ramlah da batada hips nonon ma ba sosai take dashi ba,haushin kansa yaji meye nasa na tunawa da jiddah lokacin da ramlah ta fado jikinsa yaja tsuki,...da sauri ta dubesa ya kada mata kai "badake nake ba ramly...nadawo hold off ya tsareni a hanya"ya shafa kansa ya janyeta daga jikinsa suka karasa parlorn....kaza ya baje musu yana ci yana satar kallonta,ci takeyi tamkar baxataci ba tana yatsina,a ransa yace ",komi nata a yanga"....
Misalin karfe goma suka kwanta bacci,rungume yake da ita yana shinshinar jikinta yana shafa ko ina na jikinta cike da salonsa mai rikita mace,lasar wuyanta yake a hankaki Yana mata tafiyar tsursa a jikinta har ya zame rigar jikinta ya hade bakinsa da boobs dinta ya soma tsotsa a hankali....ai take ramlah numfashinta ya soma sauya salo wanda hakan ya tabbatarwa da Abdallah tana karbar sakkonsa ...cike da kwarewa Abdallah ya shigi ramlah inda nan ne ta soma kuka mai ban tausayi don ramlah dai bata taba sanin wani namiji ba,minti goma zuwa sha biyar Abdallah ya sauka daga kanta ya tallabota yana kallon yadda hawaye ke ambaliya a fuskarta....gumi ne ke karyo masa don samm besamu gamsuwa daga wajen Ramlah ba take first night dinsa da jiddah ya fado masa yadda ruwa ke bulbula a jikinta kamar an bude famfo sabanin ramlah da babu wani ruwa da yaji daga jikin nata gashi shaawarsa a motse take share mata hawaye yayi ya kwantar da ita ya fada toilet ya sakarwa kansa ruwa,
Yafi minti talatin sanan ya fito dik bashida kuzari haka ya dauketa ta kara wani makalkalesa tana shasshekar kuka, Abdallah sarkin miskilanci da zuciya take yaji ta bashi haushi....jiddah da kafarta ta taka ta shiga toilet dikda wuyar da ya bata a daren farko saida yayi round uku.....dakyar ta yarda ya gasata ya fito da ita suka koma suka kwanta,bacci ne ya gagari Abdallah ita kuwa rungumesa tayi tana shigewa jikinsa kamar mage.....
********
Hawaye ya gama jika pillown jiddah dik juyi idan tayi bakim ciki ne ke lullubeta na tabon da ramlah ta bar mata cikin zuciyarta,babbar damuwarta be wuce yadda takejin wani abu a zuciyarta ba musamman yadda take yawan faduwar gaba tun dawowarta daga gidan su zainab.....me hakan ke nufi?"
Wayarta ta janyo daga gefenta ta share hawayenta ta kira abidah a waya,
Bacci me nauyi abidah keyi lokacin da wayarta ta soma ringing...
Dauka tayi ",hello Ablah lafiya naji kina kirana da wanan dare?"
Shashekar kuka jiddah takeyi"babukomi abidah zuciyata tana cikin kunci"
"Kardai kicemun kina kunci ne saboda kinji yau aminiyarki ta angwance da mijinki....tou ki kwantar da hankalinki dan auren beyi armashi ba"
Bilal juyi yayi ya kalli agogo karfe biyu na dare babu alamar bacci a idonsa,yau kimanim wata kenan beji muryar jiddah ba,take zuciyarsa ke raya masa ya kirata wata zucuyar ta tuna masa gargadin momy na kada ya kuskura ya kirata ko yayi mata maganar soyayya don aure zai haramta a garesu.....ajiyar zuciya ya sauke i need to hear her voice koda bazance mata komiba zan kirata ta dauka ko hello tace,ya furta hade da jan numfashi....karamar wayarsa da sabon sim dinsa ke ciki ya daddana numbobinta yayi dialing......abun mamaki call waiting...mikewa yayi ya zauna ya kalli agogo,
Itako jiddah jin waya ta shigo wayarta yasa ta dubi agogo tadan dubi wayar taga bakuwar number saita maida wayar kunnenta ta cigaba da waya da abidah....
Bugun zuciyar bilal ya tsananta take yaji wani irin kishi ya taso masa,dawa take waya a wanan dare?kansa ya sara masa nan da nan ya soma masa wanan mahaukacin ciwon da yakeyi masa idan yana cikim damuwa ko bacin rai....rike kansa yayi ya watsar da wayar gefe ya rufe ido saboda duhu da yake gani ya kwantar da kansa a pillow....
Tana gama wayar ta dubi number gabanta ya fadi ta tambayi kanta waye yake kirana da wanan dare?....hannunta na rawa tayi dialing wayar,
Yana kallom wayar na haske yaga numberta ce yayi kuri da jajayen idonsa yana kallom wayar yakasa sa hannu ya dauka....hawaye ne kawai ke zarya a idanuwansa...
*******
Washe gari,
Misalin karfe sha daya na rana,zee ce ta gama breakfast ta fito daga kitchen da kuloli sai gumi takeyi,ya sagir ya tabe baki "mata fa sunyi aiki dubi yadda kike gumi dan allah jeki wanka"
Harararsa ammie tayi "banson wulakanci kajiko me kake nufi?"gumtse baki yayi batare da yace komiba,
"Ina bilal ya fito ayi breakfast"
Sagir yace "Ammiey bilal bashida lafiya,ciwon kai mai tsanani yake fama dashi yanzun hakan na baroshi a kwance"
"Innahlillahi wa innah ilaihi rajiun shine sagir tun fitowarka baka sanarmun ba?kai amma kai shashasha ne wallahi"mikewa tayi ta nufi bangarensu zee ta rufa mata baya,
Yana kwance idonsa a rufe suka turo kofar dakin,hannun ammiey tasa ta kunna wutar dakin,ta cikin idonsa yaga alamar haske a hankali yake bude idonsa har ya saukesu akan ammiey da zee dake tsaye "sannu bilal,ya jikin naka?meke maka ciwo yanzun"
Dafe Kai yayi cikin jin ciwo yace "aushhhhhhh Ammiey kaina ke ciwo sosai ko gani dakyar nakeyi don allah ki kiramin momy"
"Bazaa kirata ba a tada maka da hankali bilal yanzun bari akawo maka breakfast kaci muje asibiti"
Kallom zee ammie tayi wadda idonta sun kada kamar zatai kuka tausayinsa ya kamata ",jeki kawo breakfast dinsa nan yasamu yaci wani abu yasha panadol extra sai muje asibiti ko?"....bata ko amsaba ta fice da sauri dan aiwatar da umarnin ammie....
********
Ramlah ce kwance a doguwar kujera ta sauya kaya tayi wanka,kallon tv takeyi amma hankalinta na wajensa,mamaki takeyi yadda ya tafi aiki sakamakom yau monday ko tashinta beyi ba jiyafa aka daura musu aure....bata gama tunani ba ya kira wayarta cikin sauri ta dauka muryarta na rawa "dear...ina katafi ne natashi banganka ba"cike da shagwaba tayi maganar,
"Ehh naje aiki,naga kina bacci sai ban tasheki ba amma kinga breakfast a dining wanda ummaj tabawa driver ya kawo ko?"batako bi takan abinda yake cewa ba tace "amma baa baka hutu bane wajen aiki?...naga yau washe garin auren mu ne and i need u by my side"
Shiru yayi yana saurarenta kamar bazaice komiba harta cire rai zaiyi magana yace "amma dai kinsan nafada miki ban hada komi da aikina ba ko?...den why are u asking me such silly question bayan kinsan manyan mu daga headquarter abuja suna garin nan basu gama duba wurare ba"
Yadda yayi maganar yasa tace "kayi hakuri shikenan"muryarta na shakewa cikin zafin amsar daya bata,
Beko damu da yadda tayi maganar ba "banaso ki somamun korafi tun daga yanzun dan zamu saba nidake hope u are getting me"
Jinjina kai tayi kamar yana ganinta...."zandawo da wuri"
"Owk"tace batare da yace komi ba ya dire wayar...
Sallamarsu rumaisa ce tayi daidai da ajiye wayarsa,hannuwansu rike da kuloli masu tsadar gaske,shiru tayi tana kallonsu wani irin abu ne ya tokare mata wuya yasa ko sallamarsu ta kasa amsawa,
Gefenta duka sukai maxauni "Anty ramly amarya yadai bakijin muna sallama ne?"rumaisa tayi tambayar da ruko hannunta,
"Sorry ina jinku barkanku da zuwa"
Kallom juna sukayi ganin yadda ta amsa su,basu damu ba yasa suka hada baki ",barka dai amaryar yayan mu amaryar mu munata murnar zuwa mu ganki wooowwww gida ya zama namu"meenah ta buga tsalle ta fada kujera,
"Ke meenah meye haka kike ihu kamar ba mace ba?idan kika karya kujerar fa"tace a dakile tana kallon meenah ido cikin ido,
"Sorry Anty ramly"suka hada baki,
Dukkansu shiru sukai nadan lokaci kafin ramlah ta nisa tace "ya mamanku?"
"Lafiya lau ummah tace a gaisheki kafin tazo ganin yarta"
"Ummm ...aifa Allah sarki"ramlah ta basu amsa tana kokarin daukar remote,
"Meenah je kitchen ki mikomin plate in zuba abinci"ramlah tabawa meenah order tana kokarin canja chanel din tv.....samm dukkansu basuji dadin yanayin antyn nasu ba,a tare suka tafi kitchen din ta tabe baki ta furta "naga kashin awaki karewar hadin kai"
"Me kikace Anty"suka hada baki.... girgiza kai tayi alamar babukomi,
A kitchen rumaisa ta kasa hakuri "meenah,me akayiwa anty ramly...ki duba yadda take magana kamar wata sarauniya"
"Kinsan amare da mulki kyaleta kawai kila batajin dadin garin ne"meenah ta dau plate suka fito a tare suka tarar da ita inda suka barta,
"Gashi plate din anty ramly"...batako kalleta ba cike da isa tace "zubamun,in yayanki ne ai zaki zuba masa"
Basu kawo komiba sukai dariya "hooo Anty"yatsina fuska tayi...hmmmm a ranta tace bazan bari ku rainani ba don niba jiddah bace....
********
A parlor suke zaune dukkansu bayan sundawo daga asibiti bilal ne makale da waya,
Cikin damuwa momynsa tace "Bilal ka fadamun damuwar data tayar maka da ciwo kada ka boyemun"
Idanuwansa suka cicciko da hawaye ga kansa dake sarawa dakyar yake magana kasa kasa kamar wanda bayaso"momy ...babukomi kawai dai zuciyata ce take yawan tunani"
Tausayin bilal ya kamata tasani yana bukatarsu a kusa da ita amma batada yadda zatai,saidai dole ne tayi wani abu akai "kayi hakuri kadaina damuwa idan kanason kwanciyar hankalina da zamam lafiyata nima don in har bakada lafiya banida kwanciyat hankali kaji"
Cije lebe yayi "owk momy muyi magana anjima inadanjim ciwon kan yanzun",
"Tou ka gaida maman naka da Yan uwanka"ta kashe wayarz...ammie tabar parlorn,zee kuwa tana gefensa tana masa wani kallo mai cike da sakwanni,gaba daya cikin tashin hankali take don har boyewa tayi dazun tayi hawaye "yaya sannu ya jiki?da sauki'tambayarsa takeyi kamar zatayi kuka kasa magana yayi sai daga mata hannu yayi alamar da sauki ya dan kifa kansa a kujera ya lumshe ido ...
Gwaggo ce taga jiddah ta fito da gyale "ah ah gidan su aminiyar zaa ne yau baa ganta ba?"
"Ehh gwaggo zanje in dubata don nasan halin zainab tana shigowa gobe saitamun gori tace banje naga lafiyarta ba banganta ba kinsan mutuniyar tawa"dariya gwaggo tayi "kunfi kusa"
"Gwaggo ina nafeesa ne"
Sunfita da fatima sunje saloon kina bacci"
Bata fuska tayi "nima inason fa zuwa in wanke kai"
"Gobe keda zainab sai kuje ta rakaki ko"
"Tou gwaggo saina dawo"ta fice....
Zainab ta tasa Bilal tayi kuriiiii tana kallon yadda ya lumshe ido gashin girarsa sun kwanta lufffff luffff da eye lashes dinsa zara zara.....takun takalmin jiddah yasa zainab maida hankali a kofar dakin,
Tana bude labule kamshinta ta gauraye dakin yasa bugun zucuyar Bilal ya tsananta.... meyake shirin faruwa dashi da kamshin jiddah ke bibiyarsa kodai itace?...."assalamu alaikum"tace cikin muryarta mai sanyi....da sauri ya bude ido sukai ido hudu ya mike zumbur kamar mahaukaci yace "itaceeeeeeeeee".....suna hada ido da shi ta dafe kirji ta juya ta runtuma a guje,zainab tayi saurin bin bayanta a guje....ko kafin zainab ta fita karar rufe gate din jiddah taji garammmmmmmm
MASOYA KU GARZAYO DON SAMUN LITTAFIN IZZATA DA ZAINUL ABIDEEN KO WANNE COMPLETE DARI BIYU IDAN BIYU ZAKI SIYA A SAUKAKE KI BIYA 300 TA WANAN ACCOUNT NUMBER 2255398727 ZENITH BANK AMINA JIBRIL INA JIRAN KAUNA...BAXAKUYI DANASANIN SAMUN ZAFAFAN LABARAN NAN BA SAYAN NAGARI MAIDA KUDI GIDA GA NUMBERTA IDAN KIN TURA KUDI 07042277401
*SLIMZY✍🏼*
[11/5, 7:41 AM] Mis Slimzy😍🥰: *💥💥AUREN FARI...💥💥*
*SLIMZY✍🏼*
_Wattpad@slimzy33_
*SADAUKAR WA:*
*HAUWAU MU'AZU AMIR RUMA...*
*24*
Gwaggo tana zaune a kujerar roba a harabar gidan tana karanta hisnul muslim,da nafeesa da Anty fatima suna zaune gefen ta da yaran anty fatima jiddah ta turo gate a guje ta shigo ta ruga da gudu tayi cikin gida,a furgice nafeesa ta mike tana fadin "lafiya,meya faru Abla"
"Kee kee jiddah keda waye haka meyafaru?"gwaggo cikin tashin hankali take tambayar jiddah tana kokarin mikewa daga kujera,kallon juna nafeesa da fatima sukayi suna kokarin dunguma suyi cikin gidan saiga zainab ta shigo tana sauke numfashi,
Dakatar da ita gwaggo tayi ta hanyar saurin tambayarta "ke zainabu meyake faruwa ne?naga kawarki ta shigo ta shige cikin gida a guje kema gaki kin shigo kina haki"
Dafe kirji zainab tayi tana sauke numfashi,cikin damuwa tace "wallahi....gwaggo...nima bansaniba,ta shigo cikin gidan mu muna zaune a parlor tana shigowa ta runtuma a guje kamar wadda tayi gamo da dodo ko mugun abu"
Gaban gwaggo ne ya yanke ya fadi cike da dimaucewa ta soma salati "innahlillahi wa innah ilaihi rajiun,assha Allah ya rufamun asiri yarinyar nan ba gamo tayi da aljanun laasar ba"
Fatima ce tasa dariya "gwaggo akwai aljanun laasar ne,wallahi kinbani dariyar da ban shirya ba mudaije ciki muji menene hakan yasata shigowa gida a guje kamar an biyota"
Cikin sanyin jiki gwaggo ta sake duban zainab "kin tabbatar bawani abu kike boyemun ba,dan allah ki sanar dani gaskiya"
"Wallahi gwaggo gaskiyar kenan bansaniba nima"cikin damuwa zainab tayi maganar tana kallon hanyar da zata sadaka da parlorn gidan,
A tare duka dunguma sukai cikin gida ta wata siririyar hanya sukabi suma bullo ta babbar kofar patlorn,tun daga kofar parlorn gidan suke jiyo shasshekar kukan jiddah,cikin tashin hankali gwaggo ta nufi dakin ta dake ta cikin parlorn,
Kwance take ta kifa ciki ta dukunkune cikin bargo ta dora pillow a kanta tana faman kuka dukkansu gadon suka nufa cikin dimuwa gwaggo tace "lafiya jiddah? menene haka meke faruwa mai kikagani kikazo nan kika boye?ko wani abun tsoro kika gani ki sanar dani"
Hannu fatima tasa ta yaye bargon,ta cire pillown saiga fuskarta tayi jajir ta sharbe da gumi da hawaye daya wanke mata fuska....
Tabota fatima tayi tana kokarin tallabota "tashi jiddah kifadamun meke damunki meyafaru umm me kikagani?"
Jingina zainab tayi da jikin bangon dakin tana kallon jiddah,tana son gano wani abu gabanta ne ya tsananta faduwa lokacin data tuna da amsa kuwwar muryar yaya Bilal da yace itaceeeeee da karfi,to itace wa?meye tsakaninsu yasan ta ne?....gabanta na cigaba da faduwa,
Mikewa jiddah tayi ta zauna tana kokarin share hawayenta, zama gwaggo tayi "fadamun jiddah na menene kedamunki umm yar gwaggo me kika hadu dashi ko inyi miki addua a idonki ne?"
Girgiza kai jiddah tayi cikim kuka tace "nidai...."sai kuma ta girgiza kai "babukomi gwaggo"
"Ya zakice babu komi jiddah,kin tada mana da hankali ki sanar damu meke damunki mana"fatima ta amshe maganar,
Girgiza kai tayi lokacin da ta dago kwayar idonta ta dorasu akan zainab ta runtse idonta wani takaici takeji,ta sanadiyyar ta ne yau ta kai kanta inda ta ga bilal"nibakomi"
Kallon zainab fatima da gwaggo sukayi ganin yadda jiddah dayi data kalleta suka hada baki "kada ki boye mana komi zainabu ki sanar mana da abinda ya faru kawai saboda yanayin jiddah na nuna kamar kinsani"
Cije lebe zainab tayi gabanta na dukan uku uku,kodai bilal yasan jiddah da alakar soyayya tsakaninsu?tambayar kanta takeyi gwaggo ta kara katseta "kinyi shiru"
A sanyaye zainab ta soma magana "gwaggo abinda nasani shine, jiddah ta samemu a parlor da bakon gidan mu don bashida lafiya ma tana shigowa naga sun hada ido ta juya a guje....wallahi bansan komiba,kawai dai abinda zanyi recalling dana biyota naji shima yana fadin itaceeeeee"
Aiko kukan jiddah ya tsananta....yayinda gwaggo da fatima suka kalli juna cikin damuwa dukkansu sanan suka tsura mata ido yadda take kuka....
*******
Ammie kuwa fitowa tayi daga daki a guje jiyo muryar bilal,a tsaye ta sameshi jikin kofa yana maganganu hannunsa dafe da kansa
"Meyasa zaki gudu baki tsaya na ganki ba jiddah,ki tsaya Dan Allah in kalli kyakkyawar fuskarki ko zan samu sassauci a zuciyata....inajin ciwo sosai rashin ganinki bazan taba furta miki kalmar so ko aure ba don nasan zaki iya haramta a gareni"
Bazan iya furta miki kalmar so ko aure ba dan nasan zaki iya haramta a gareni kawai ammie taji,dan ja da baya tayi dan ba karamin furgita tayi da yanayin nasa ba, hawaye wani na bin wani ta gani kwance a fuskar bilal.... dafa kafadarsa tayi hade da ruko hannunsa "zo muje bilal....zomuje kasanar mun wanan sambatun na meye kakeyi,idan ba kunnena ba to tabbas naji wasu zantuka a bakinka masu kama da kanason wata amma kanawa kanka gargadi da bazaka fada mataba shin wacece"ta karasa maganar tana kokarin zaunar dashi a kujera,
Kallon Ammiy yakeyi yakasa furta komi banda kallonta da yakeyi fuskarta na sauya masa zuwa ta jiddah...hakan yasa ya kara kafeta da ido da har saida ta tsorata,gabanta na dan faduwa tasa hannu tayi masa waving sanan idanuwansa ya motsa su "yadai bilal....meke faruwa ka sanar dani,fadamun ko wacece zan nemo maka aurenta bazata haramta a gareka ba ko wacece idan har ta gida ce to ta zama mallakinka"...lumshe ido yayi zafafan hawaye na kara sauka a idonsa,
Ammie kuwa bugun zuciyarta ne ya tsananta ta kosa taji bilal nason zainab dinta,idan kuwa haka ne sai tafi kowa farin ciki,idan kuma ba zainab bace to zatayi bakin ciki kuma zatai kokarin nema masa farin cikinsa,
Walida kanwar zee tana labe jikin labule tana saurarensu,zuciyarta kamar ta fasa kirjinta ta fito saboda bugu,fatanta daya bilal yayi responding da zainab yakeso,
Kalle kalle bilal keyi kafin ya juyo ya ruko hannun ammiey..."Ammiey ina sonta wallahi ina sonta sosai,soyayyarta itace zatai ajalina matukar na rasata, gashi zuciyata nayimun barazana da kasa jurewa har saina furta na jawowa kaina"
Girgiza bilal amie tayi "is ok my son,fadamun wacece kake sonta?ni Kuma zanyi kokarin nema maka soyayyarta"
Lumshr ido yayi ya Kara budewa ya damke hannun ammiey jikinsa na rawa "ammiey...dan allah kada ki sanarwa kowa ya zama sirri tsakanina dake kinji Ammiey na"
Gyada masa kai tayi gabaki daya tausayinsa ya lullubeta"insha allahu bilal baka da uwar data fini don mahaifiyarka haifanka kawai tayi"
"Ammiey...ina son jiddah....ina matukar kaunarta amma da zarar na furta mata a yanzun to ta haramta a gareni"....
Jinjina kai Ammiey takeyi cike da alhini da damuwa cikin yanayi na sanyin jiki tace "wacece jiddah'
Sunkuyar da kai yayi "kawai zee ce...bakuwar da zainab ke zuwa wajenta a makota"
Walida dake tsaye ta dafe kirji ta zaro ido,ta manne da bango.....jiddah...ta furta a fili a hankali ta gyada kai sanan taja da baya ta koma daki,
"A ina kasanta bilal da har soyayyarta tayi maka tsiro da kake ikirarin zata illata maka zuciya?"
Murmushin takaici yayi don Ammiey batasan komiba tadai san cewar sun sami matsala da Abbansa ne yazo,
Nan ya kwashe mata komi dangane da jiddah be boye mata komiba harda dalilin da yasa ya nemeta a lokacin....sanan ya dora da "ammiey yanzun ta tsaneni ko ganina batayi dom zargina take da nine na kashe mata aure"
Ajiyar zuciya ammiey tayi "tabdijan,babbar magana dan sanda yaga gawar soja....amma abinda nakeso da kai ka kwantar da hankalinka...zafin mutuwar aure ce da tana ganin kana sane da gangan kai hakan don ka kashe mata aure,nasan ta inda zan bullo dikda baa neman aure cikin idda don haramun ne amma ka bar komi a hannuna,badai kacekana sonta ba ko?"..
Dai dai nan zainab ta shigo parlorn cikin rashin kuzari saidai taji lokacin da ammiey ke tambayar bilal din badai yana sonta ba kuma taga lokacin da ya gyadawa ammiey kai....wacece yakeso?kodai itace wadda yakeso?mafarkinta da burinta na gab da cika?...wucesu tayi batare da tace musu komiba ammie a fakaice ta kalli zee ta girgiza kai don ta dade da fahimtar yar tata tana son bilal tun zuwanta....
"Tashi kaje kayi sallah kaji?a dawo aci abinci asha magani"
Mikewa yayi dakyar yake taka kafarsa ya nufi sashensu.....binsa tayi da wani irin kallo mai cike da tausayawa ta kada kai"
******"
Wanka ramlah ta tsala ta sha wata doguwar riga da ta siya cikin kayan da aka kawo mata daga gida da yamma ta ciro ta tasanyata iya gwiwarta....saida tayi sallah sanan ta fito fuskarta sai sheki yake bakinta kuwa tamkar a nan akai kamfanin jan baki maroon wanda yayi matumar daukar fuskarta,
Su rumaisa suna parlorn ta fito,fuskarta adan daure ta kalli agogo sanan ta dubesu dukkansu ita suke kallo yadda tayi matukar kyau,
Kasa hakuri meenah tayi "kaiiiiii Anty amarya kinyi kyau sosai wanan gayu haka?hmmm ba kamar waccen jakar jiddah ba da batasa kananan kaya"
Gwasaleta ramlah tayi "ban tambayeki ba, banason jin suna mai kama da jiddah a bakinku don nan ba gidan ta bane gidan ramlah ne,ammmm nace baku sallah ne kuka tsurawa tv ido kamar wasu kauyawa?ai sai a tashi ayi sallah ai haramar tafiya gida ko naga yamma tayi"
Cikin yar faraa rumaisa tace "ai minsaba inhar mukazo gidan yayanmu shine yake kaimu gida idan ya dawo aiki tare da matarsa kinga yau ma sai ya kaimu saiki gaida ummah"
Kujera ta nema ta zauna sanan ta dubesu a wulakance "a wancen gwamnatin na jiddah kenan amma baa gwamnati na ba,ku tashi kuyi sallah ku kira driver dinku yazo kutafi gida dan akwai hadari ina bukatar kebewa da mijina"
Tabdijan meenah tace a ranta,sai yanzun ya fahimci dik abinda ramlah keyi musu tun rana tana sane...meenah kasantuwar tanada zuciya tadan shaka ta mike ta zari gyalenta,
"Tashi rumaisa,mu shirya mutafi mu hau napep"
"Ah ah mana meenah,mu kira shuaibu driver yazo ya tafi damukawai miyi sallah"
Meenah girgiza kai tayi 'baxanyi sallah ba gaskiya idan naje gida nayi,ammm idan zakiyi kiyi kizo mutafiko kin manta shuaibu yabar kwana kuma yanzun ya dade da wucewa gida",
Rumaisa shigewa tayi ta dauro alwala tayi sallah a patlorn tayi, ramlah kuwa kanta na tv amma hankalinta na wajensu don ta kosa su tafi aiko tana idarwa kamar an tsunguli meenah ta mike "antyn mu sai anjima"
Daga inda take zaune "mu jima da yawa,a gaida ummar"
Suka fice taja tsuki....
Sauri sauri suke sukai titi rumaisa tace "amma meyasa kika dage da mutafi ne meenah gashi nan mun fito muna kwasar kafa"
Batare data ko kalli rumaisa ba tayi banza da ita caannnn kamar an tsikari meenah tace "halan bakiga rainin wayaun da takeyi mana ba,da farko na dauka kawai mood dinta ne haka amma daga baya na fahimci kora da hali take mana"
"Niko naga ba haka halin ta yake ba...kodai yaayah ne yayi mata wani abun"
Tsaki meenah taja "su ta shafa"....
*******
Abdallah ne ya shigo rataye da jakar laptop dinsa da suit dinsa a hannu kallo daya zakai masa a kwayar idanuwansa da sukai jajir ka hango tsantsar gajiya da bacci,
Cikin karairaya d kissa ramlah ta mike ta amshi jakar hannunsa "barka da zuwa dear"
Kokarin zare takalminsa yakeyi daga tsaye ya mika mata jakar "barkanki....ya zaman gida"
Farrr tayi da ido "gashi nan munatayi"
"Koda yake su rumaisa ai sunzo sun debe miki kewa,da mukai magana da ummah ma take cewa zasu rinka zuwa miki har kisaba"
Ya dire takalmansa yayi gaba tabi bayansa,tabdijan ta furta a ranta...waige waige yayi "inasuke?...inata sauri inzo gida muci abinci sai mu kaisu gida ko?"
Zaro ido ramlah tayi cikin nuna damuwa da mamaki tace "au dama sun sai kaine kake kaisu gida kenan sukasani gaba wai zasu tafi su, sungaji karkaso kaga yadda mukai da yaran nan wallahi"
Cikin fusata yace "amma znci wa yaran nan mutunci,yanzun zuwanki ne zasu canja yadda mukeyi dasu koko wani munafurci sukeson hadawa kuma?"
Tabe baki ramlah tayi "kasan yan mata,musamman yadda sukaga sunti girma nidai naga meenah tayi waya shine sukace zasu tafi naita fama dasu sukaki"
Kwafa Abdallah yayi ransa a bace "aiki nake ban karasa bama sbd nasan suna nam da ba yanzun zan shigo ba wallahi...shiyasa nazo da laptop gida"
"Tou muje kayi wanka nasan ka gaji dear,aiki kuma ai dana koma zamu rinkayi tare"...wata harara ya watsa mata da batasan dalilin hararar ba yayi gaba wadda tasa tasha jinin jikinta daga baya ta rufa masa baya....
********
Cikin lallashi gwaggo tashawo kan jiddah tayi sallah,ta zauna a parlor inda suke zaune da nafeesa sai kokarin mantar da ita damuwarta sukeyi dikda gwaggo Allah Allah takeyi taji meye ke faruwa zata tuntubi ammie,
"Jiddo...jibi zaki bimu muje bikim yar aminiyata ko?"
Gyadawa gwaggo kai tayi idanuwanta a kumbure "zani gwaggo insha allahu "ta sunkuyar da kai,
*******
Yana gaban laptop dinsa ta fito sanye da wata rigar bacci iya gwiwa mai hannun vest shara shara ta daure kai da ribbom baki,
Yana ta aiki idonsa nakam laptop yasa siririn farin glass dinsa ya kurawa computer ido,ta dade tsaye kansa tana kallonsa sosai yayi mata kyau ashe yanasa glass haka,...karasowa tayi tana zuba kamshi ta zauna gefensa ta kwanto jikinsa tana shafa masa breast dinta a jikinsa ta kai hannu ta shafa kansa sanan ta kwantar da kanta a kafadarsa"dear...aikin ne haka?"tace cikin siririyar murya,
Tamkar wani kurma yace "ummm"kawai yana kokarin shigar da abu,
"Umm dear kasan me?"
Beko kalleta ba yace "saikin fada"takai hannu tana wasa da sajensa,
Tsaki yayi"wai meye haka ne,inajimki kince nasan me meye kikeso kice ne?"
Take fuskarta ta sauya yadda yayi mata magana tsawa tsawa ta dan tashi daga kwancen da take a jikinsa,"umm umm bakomi....nace naga 11 kazo muje mu kwanta"
Shiru yayi beko amsa ta ba,ta kuresa da wani mayen kallo da beko san tanayi ba,harta cire rai zai amsa sanan cike da dakilewa yace "idan kinajin barci ban hanaki ba kije ki kwanta"yace ko kallonta beyi ba,
Takaici ne ya lullubeta,gashi tasha wani abu dazun ta shiryawa dawowarsa dikda taji zafin abunda akayi mata sakamakon bata taba sex ba amma daga baya taji dadin abun dikda zafin da takeji..."amm yaushe zaka kwanta?"tace a sanyaye,
"Bansaniba ko nace kije ki kwanta bana bukatar komi kije kawai zan sameki"yace hade da mata wani kallo fuskarsa babu fara,a
A tsorace ta tashi da ganin yadda yayi magana cikin tsawa tsawa,dakyar take hada hanya ta shige daki ta rufo kofa ji kake garammmmm
Tsaki yaja...ya maida kansa ya cigaba da abinda yake,
Lumshe ido Ramlah tayi....i need u my husband lallai naji dadin yadda ka sarrafa jikina jiya,dikda jikin da naji amma kaidin namijin duniya ne ina ciki da bukatarka koda zanyi kuka yau din kamar jiyan amma nasan zanji kishiyar zafin.....murginawa tayi ta lumshe ido batare da tanajim bacci ba ta fada duniyar yadda yake tsitsa boobs dinta jiya....bude ido tayi ta furzar da iska ashe haka aure yake da dadi?take tambayar kanta....murginawa tayi ta kwanta rigin gine....tana shafa gashin kanta wani abu takeji yana yawo a jikinta ga pant dinta daya jike......
********
Dare ya raba zee juyi takeyi akam gado tanaso tasamu amsar da ammiey take tambayar bilal.... Allah yasa dai itace wadda yakeso,
Walidah na lura da yanayin nata,
"Yaya zee bakiyi bacci ba?"kwatsam taji walida ta jeho mata tambaya,
Dan juyowa tayi ta dago kai daga kwancen da take mamakinta walida ke zaune kan kujerar madubi "au ke ko kwanciyar ma bakiyi ba?hmmm banyi bacci ba wallahi nakasa kuma inaso inyi"cikin sanyin murya tai maganar,
"Tunanin yaya bilal ya hanaki bacci ko?"walida ta wurga mata tambayw,
Lumshe ido tayi daga kwancen da take batare da ta amsa ba,
"Hmmmm yaya zee wallahi akwai wadda yaya bilal keso Kuma nasanta"...
Mikewa zee tayi "wacece?nice yakeso?kifadamun a ina kikaji Kuma?"
Tausayin yar uwarta ya kamata don ta kama kiwon makahon kare don son maso wani masifa ne "ehh jiddah yakeso,naji yana fadawa ammie....banji sauran me suke fadi ba"
Dafe kirji zee tayi hawaye ne ya soma gudu a fuskarta....kishi ne ya taso mata ya tokare mata wuya ta koma ta kwanta tana kukan zuci,
Ganin zee na kuka yasa walida yin danasanim sanar mata,itama jiki ba kwari ta hayo kan gadon ta kwanta bayan zee tana jiyo shasshekar kukanta....
Lamo zee tayi cikin bargo har biyun dare batayi bacci ba,ga Ac da take bugata...ina son yaya bilal nasan yasan ina sonsa amma zanyiwa jiddah adalci bazan taba sanar da ita ina sonsa ba dikda alamu sun nuna kukan da takeyi akwai wani abu....itama sonsa takeyi kenan?hawaye ya gangarowa zee wani irin kishi ne ke taso mata....
********
*Bayan kwana uku*
Jiddah ta tashi da dan zazzabi ta kasa sakin jikinta tun daga ranar bata sake zuwa gidan su zee ba,ga mamakinta zee kuma batazo wajenta ba,gashi tanaso taga kawar tata amma batasan yadda zaai ta gantaba kuma batada number ta....
Tana cin abinci a parlor gwaggo da nafeesa sunyi shirun biki nafeesa tace "wayyoo ablah, gashi allah beyi zaki bikin ba saboda fever"
"Kizomun da dik abinda kikaci kinji kanwis"
Gwaggo tasha babban gyalenta tayi kyau yar dattijuwar "tou ki kula da kanki kiji motsin gida bazamu dade ba kome kike bukata akwai kafin mu dawo"
"A dawo lafiya"
Suka fice a kofar gate,gwaggo tayi karo da ammiey zata shigo "ah ah hajiya gwaggo ina wuni"
Washe baki gwaggo tayi farin hakorin makkanta ya bayyana "lafiya lau... halan kinzo wajena ne gashi zanje biki nan sabuwar unguwa"
"Tou badamuwa sai kundawo"kallonsu ammie takeyi bataga jiddah ba cikin hikima tace "ina bakuwar ko banda ita?"
"Ehh batajin dadi ne zamutafi da wuri zamu dawo"
"Wayyo allah ya bata lafiya,sai kun dawo"ammie ta koma ta shige gate dinsu,
Sagir da bilal sun fito zasu masallaci sallar azahar sukai kicibis da ammie suka gaisheta suka fita.....
Sagir ne ya gaida gwaggo tana kokarin shiga motar da babban danta ya turo mai kaita unguwa...."ina yini gwaggo"
"Lafiya lau sagiru"ta amsa cike da kulawa...bilal a sanyaye ya gaisheta ta amsa tana kare masa kallo kamar dan balarabe ta shige mota itada nafeesa.....kallon gate din gidan bilal yayi ya hadiyi wani mugun miyau gashi baa wani ja kofar ba kila sun mance...suka tafi masallaci
Zee kuwa bayan ta idar da sallar azahar ta fito sanye da bakar jallabiya ta dubi ammie "bari in je wajen jiddah"ammi ta amsa mata da kai,sagir na cin abimci sakamakon ya baro bilal waje yana shan iska,
Tana bude gate din gidansu tayi kicibis da bilal tsaye yana kallom cikin gidan da jiddah take ..ta juya baya tana zaune a kujera a harabat gidan tana kallom fulawoyi.....tsaye zee tayi tana kallonsa zuciyarta na harbawa idonta suka kada sukai jajir....hmmm yazo ganinta kenan...ta dade tsaye be sani ba,
Shiko kallonta yakeyi yana murmushi ko kifta ido bayayi kusan minti goma zee na tsaye kafin ta hadiyi wani miyau me kauri ta furta "excuse me"muryar zee jiddah ta jiyo ta juyo daidai nan bilal yaja da baya batare da ta gansa ba yana sauke numfashi ya juya da sauri ya shige gidansu....zainab ta bisa da kallon tuhuma wanda bema san tanayi ba,
Jiddah ko ta kasa daina murmushi ganin zee ta shigo tana kallonta,itako zee takaici yasa takewa jiddah wani kallo mai dauke da maanoni haka ta shiga gidan jiki sukuku ba kwari....ta rufe gate fin
*******
Ramlah na shan fruit salad taji tsayuwar mota da sauri ta dire don tasan ba Abdallah bane yana wajen aiki ta daga labule....daidai nan ummah ta fito daga mota itada rumaisa ne babu meenah tasha kwalliya sai walkiya leshin jikinta keyi.....wani kululun bakin ciki ne ya tasowa ramlah wato banje ba saida aka biyoni taja tsaki ta koma ta zauna hade da daura fuska ta dora kafarta daya kan daya.......
*Toh fa muje zuwa*