Tsakar tare ta miƙe ta hura wuta ya kama sosai ya yi jan garwashi, wani garin magani ta ɗauko ta bula akan wannan gaushi, nan wani haske ya bayyana a cikin dakin, wasu maganganu Asabe ta hau fadi gami da ambatar sunan Samima.
Samima dake bacci ta ji kamar ana mitsininta, a firgice ta farka ta hau juyi bakinta na fitar da kumfa, ihu take yi sabida azabar da take ji, kamar ana gasa mata ƙashi da fatar jikinta, ihu take yi tana murƙususu, zuwa wani lokaci ta galabaita ta fara ficewa daga hayyacinta, wani razananniyar kara ta kara sakewa wanda ya yi sanadiyyar farkawar iyayenta daga bacci suka tashi suka fito a razane, bude kofar da zasu yi suka ga wani zureriyar wutsiyar maciji tun daga bakin kofar, Ihu Umma ta saka ganin Samima tun daga kugunta abun da ya yi kasa ba mutum bace, cikinta abun da ya yi sama su ne mutum, Baba salati ya fara ya ma rasa me zai yi, sunan Samima ya ambata wacce bata san a wace duniyar take ba, ga b'arin da jikinsu ke yi, sun kasa karasowa inda take, a dayan bangaren kuwa Asabe tana kan zuba surkullenta tana ganawa Samima azaba, wani ihu Samima ta sake sakara nan take fatar hannunta ya fara sabulewa, tashin hankalin dasu Umma suka shiga abun ba a magana, nan take Samima ta yi wani juyi da gurnani inda ta koma wata katotuwar macijiya ta tumbatsa ta yi kan iyayenta, rufe ido Umma ta yi domin har ta sadakar kawai, da sauri Baba ya ja Umma sannan ya datse Samima a daki, parlour suka fito da Umma rungume a jikinsa, ɗagota ya yi ya ga ashe ma ta suma ne, ya rasa yadda zai yi, ga shi ba abun ya fita neman taimako ba, ga yarsa a daki ta koma macijiya ga matarsa ta suma, kuka ya saka mai ban tausayi ya fuskanci gabas ya kifa goshinsa a ƙasa yana ci gaba da kuka.
🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
A lallaba.
Sai Allah ya kaimu. 🏃🏻♀️🏃🏻♀️
UMMU AHLAN TAKU CE👍🏻
[02/09 à 08:45] 🌹🌹Flower 🌹 🌹: *SAMIMA* 🐉🐍
( _macijiya ce_)
Na
*ZAHRA ABDUL*
(MOMYN AHLAN)
Gajeran labari.
SHAFI NA HUƊU. ✍🏻
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association
*____________________________________*
*_YA ALLAH KA BARMU DA MASOYAN'MU 🥰🥰 WALLAHI MASOYA DADI GARESU, INA ALFAHA DAKU MASOYANA, KU CI GABA DA SHARHI DUK INA BIYE DAKU, KARKU GA BANA REPLY ABUBUWA NE SUKA MIN YAWA, AMMA KU SANI SHARHI DA SAKONNIN KU SUNE KARFIN GUIWATA HAR NAKE SAMBAƊO MUKU LITTAFIN SAMIMA, AHA MASOYANA INA GODIYA FA IRIN SOSAI DIN NAN, ALLAH YA BAR KAUNA SON SO DOMIN ALLAH_* 🥰🥰
🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
Addua Baba ke yi yana kuka sosai har izuwa karfen ukun dare, yana jin buge-bugen Samima a cikin daki, amma ba abun ya budeta ba, har wajan gefen asuba kafin ya miƙe da kyar ya ɗauro alwala ya tada Sallah yana gayawa Ubangijinsa da ya kawowa ɗiyarsa dauki, sanyin asuba ne ya farfaɗo da Umma, a firgice ta farka ta cakumi Baba tana cewa "Baban Samima, ina Samima? Ina ƴata?" hanyar daki ya nuna mata, ta tashi da sauri, shima cikin hanzari ya riƙota yana girgiza mata kai alamun karta je, sannan ya umarceta da tayi alwala, jiki ba kwari ya do shi hanyar toilet, bayan tayi suka tada sallah, nafila suke yi babu tsagaitawa, har aka yi asuba, sannan Baba ya ja su suka yi,dan ya ma kasa fita zuwa masallaci, nan suka zauna su na lazimi har garin Allah ya waye, misali karfe bakwai da rabi Baba ya ji wayarsa na ruri a daki, ya kalli Umma ya ce "Zulaiha ɗauko min wayata" tashi Umma ta yi jikinta duk ba kwari, dan hankalinta yana kan Samima, dan bata san a wani hali take ciki ba, ɗauko wayar ta yi ta duba ta ga Nuren ne ke kira, kawo masa ta yi ta ce "Nuren ne" karba Baba ya yi, ya ɗaga wayar Nuren ya masa sallama gami da gaishesa, amsawa Baba ya yi murya a raunane daga ji kasan muryar wanda yasha kuka har ya godewa Ubangijinsa ne, Nuren ya ce "Baba, wallahi jiya ban iya bacci ba, ban san me yasa ba, ina Samima?" Nuren ya tambaya, nan hawaye ya shiga wankewa Baba fuska cikin muryar kuka Baba ya ce " jiya mun ga tashin hankali Nuren, jiya naga masifa ido da ido, da badin karfin imani ba, inaji da na zauce Nuren" cikin kuka Baba ya bawa Nuren labari, sannan ya kara da cewa "ina gani yarinyata ta rikiɗe a gabana ta koma Macijiya!!" a firgice Nuren ya miƙe ya zari car keys dinsa yana cewa "Innalillahi wainna ilayhirrajiun!! Baba yanzu ina Samiman? Ina dai bata fita ba ko?"
"Nuren nima ban sani ba, dan bamu kara bude dakin ba"
"To Baba karku buɗe gani nan zuwa" ya katse wayar sannan ya fito ya shiga motarsa, tun kafin ya data motar ya fara dannawa mai gadi horn ya bude masa gate, yana daukar tiri ya dannawa Suhail kira, sai da ya yiwa Suhail kira uku ana hudu ya dauka cikin magagin bacci Suhail ya ce "Nuren lafiya kuwa?"
Nuren ya ce "ka fito kofar gida zan daukeka yanzun nan, gani nan kusa da gidanku" bai jira amsar Suhail ba ya katse wayar, da kyar Suhail ya miƙe ya zari jallabiyarsa ya saka ya fito, fitowarsa ya yi dai-dai da tsayawar motar Nuren " shiga muje" Nuren ya fada yana budewa Suhail mota.
"To ina zamu je kuma haka da sassafen nan Nuren?"
"Gidan su Samima"
"Yin me? ba Malam ya ce muje da rana bane?, ko dai ya canza ne?"
A wannan karon Nuren bai samu damar ba wa Suhail amsa ba, ban da ɗibar titi da yake yi, cikin mintuna sha biyar sai gasu a kofar gidansu Samima, su na isa a hargitse Nuren ya fito daga mota ya b'urma gidan, Suhail na biye da shi a baya, su na shiga parlour suka samu Umma da Baba zaune ko wannensu da hannu a kumatu sun rafka tagumi, Nuren ya ce "tana dakin har yanzu?" hannu Baba ya ɗaga a sanyaye alamun basu sani ba, Nuren ya ce "ina zuwa bari na duba" a razane Suhail ya ce "wai menene?" Umma ta ce "Samima ce jiya ta koma macijiya" wani wawan tsalle Suhail ya yi zai zura da gudu, cikin zafin nama Nuren ya cafkosa ya mai dasa kujerar da ya tashi yana galla masa harara, nan take Suhail ya fara goge gumi, Nuren ya wuce a hankali yana addua yana tura kofar dakin Samima gabansa na faduwa har ya gama bude dakin, can kasa ya sameta zaune kusa da toilet ta haɗa kai da guiwa tana ta faman rusan kuka, da sauri Nuren ya karasa gareta yana cewa "Subhanallahi!! Ƙanwata!! Samima!!? Me ya saka ki kuka? Wa ya tabamin ke?" ya durkusa a gabanta ba tare da yana jin tsoronta ba, ga jikinta duk a yakushe kamar an yaguneta, rinannun idanuwanta ta ɗago ta kallesa ta ce "YAYANA, da gaske ya tabbata cewa ni ba mutum ba ce? Ni macijiya ce?" Nuren bai san lokacin da yasa hannu ya jawo Samima jikinsa ba, wasu zafafan hawaye suka hau wanke masa fuska, sosai Samima ke kuka a jikin Nuren, dan kuwa a jiya ta ga lokacin da kafafunta suka miƙe sambal, suka koma zureriyar wutsiyar maciji, a parlour jin shuru yasa Baba cewa " anya lafiya kuwa? naji Nuren shuru? Kai bari dai mu duba kar wani abu ya samu dan mutane" Baba ya kalli Suhail ya ce " ka zauna bari na duba na ga ko lafiya" jinjina kai kawai Suhail ya yi, yana goge zufar da yake wanke masa fuska, Umma ta miƙe ta ce "muje tare" Baba ya ce " a'a Zulaiha ki jirani" a raunane ta ce "ni fa Uwa ce, ba zan iya jurewa ba" jinjina kai Baba ya yi, sannan ya yi gaba Umma ta bi shi a baya, har sun kai jikin kofa zasu bude sai ga su, su kuma suna shirin fitowa, Umma na ganin Samima ta yi saurin rungumeta, suka saki kuka mai ban tausayi da tsuma zuciya a tare, sosai Umma da Samima suke kuka, babu wanda ya hanasu sai da suka yi mai isarsu sannan suka yi shuru, Nuren ya ce " "BABA, UMMA, ina ga kawai yanzu ku shirya bari muje muma mu shirya sai mu dawo mu wuce gidan Malamin Abbana" suka amsa masa da to, sannan ya kalli Suhail ya ce "muje ko?" da sauri Suhail ya miƙe suka fice, sai da ya fara ajiye Suhail a gida sannan ya wuce gida, bangaren iyayensa ya fara shiga ya same su dukkansu zaune a dinning table su na breakfast, har kasa ya duƙa ya gaishesu suka amsa masa cike da kulawa, Momy ta ce "Nuren, ina kaje ne da sassafe?" zama ya yi kusa da kujerar da take zaune fuskarsa dauke da damuwa ya ce "gidansu Samima" nan ya labarta mata halin da ake ciki, Momy ta ce "Wayyo Allah ni Amina,yanzu ya ake ciki?" numfasawa Nuren ya yi ya ce "na zo ne nayi wanka muje wajan Malam" Abba ya ce "jiya ya gaya min ai akan cewa kun je kun same shi" Nuren ya ce
"Eh Abba, ya ce muje da rana, yanzu kuma ga shi karfe sha ɗaya saura, nasan kafin mu gama shiryawa na sake zuwa na dauki Suhail sannan muje na daukesu Baba, nasan sha biyu zata yi" Abba ya jinjina kai "eh hakane kuma, to Allah ya bata lafiya, ya za a yi da Gwaggon nata to"
"Abba ban sani ba tukunna, ina so ne muje muji me Malam zai ce kafin nan" Abba ya jinjina kai alamun gamsuwa, Momy ta ce "Nuren ka ci abinci tukunna ko?"
" to Momy" Nuren ya fada amma har cikin ransa baya jin cin abinci, Momy ta zuba masa ta tura masa gabansa ci ya fara yi da sauri, tuttura abincin ya din ga yi dan ya samu ya tashi, yana gama ci ya tashi ya wuce part dinsa ya shirya, kafin ya gama shiri su gama magana da iyayensa ma sha biyun ta yi, dan haka a hanzarce ya fito ya shiga mota ya tada ta mai gadi ya bude masa gate ya fice yabar gidan, yana daukar titi ya kirawo Suhail "Hlo Suhail, ka shirya ne?" shuru Suhail ya dan yi kafin ya ce "anya zan iya zuwa kuwa Nuren? Ji nake kamar bani da lafiya fa" tsaki Nuren yaja dan ya gama fahimtar Suhail a tsorace yake ya ri ga da ya gama tsorata ne, "ka ga Malam, idan ma baka shirya ba, to ka shirya dan gani nan zuwa" sannan ya katse wayar, jiki ba kwari Suhail ya tashi ya shirya, sai da Nuren ya shigo ya gaisa da iyayen Suhail kafin suka fito suka yi gidansu Samima, sun same su sun ma sun shirya tuni dan haka basu zauna ba, nan suka shige mota suka dauki hanyar gidan Malam Habibu, ko da suka isa sun kai kusan awa daya kafin su samu ganinsa, inda aka musu iso har izuwa babbar dakin da yake ganawa da mutane masu laluri, su na shiga Malam suka yi musabaha da Baba, sannan sukayi da Nuren da Suhail, Umma ta gaishe da Malam, Samima ce karshen gaishesa, su na hada ido ta yi saurin kauda kanta gefe, gaban Malam Habibu ne ya faɗi ya sake kallon Samima, sannan ya ce Samima da Mamanta su fita waje yana so zasu yi magana ne da Baba da Nuren da Suhail, jiki a sanyaye Umma ta kama Samima suka fita waje, Malam Habibu ya ce "Innalillahi wainna ilayhirrajiun!!" da sauri Nuren da Baba suka ce "Malam lafiya kuwa?"
"A gaskiya ba lafiya ba,idan ma za ace lafiya to ba za ace kalau ba, kallo ɗaya nayi wa yarinyar nan naga tana cikin halin ha'ula'i, kuma gaskiya bazan boye muku ba, tana bukatar taimakon gaggawa, ni a gaskiya bazan iya tunkarar miyagu kuma baƙaken aljanun da aka tura mata ba,baƙin sihiri mai guguwa ne tattare da ita, sai an haɗa da manyar Malamai, hakika kafin a karya sihirin dake jikinta za a sha matuƙar wahala sosai, kuma dole wacce ta yi mata sihirin ita ce zata iya warware shi, dan kuwa dole ita zata faɗi inda ta binne wani garin maganin da aka yi siddabarun mai tsaurin gaske, ni a ganina zan haɗaku da babban malaminmu yana maiduguri ne In sha Allah shi zai san yadda za ayi" wani zufa ne ke ketowa su Baba, sannan Malam Habibu ya daga wayarsa ya kira Babban Malaminsu bai boye masa komai ba ya masa bayani, nan *MALAM ABBA ALBANY* ya bawa su Baba kwanaki akan cewa su zo nan da kwana uku yanzu baya gari, suka amsa da to sannan suka yi masa godiya, wani magani Malam Habibu ya bawa Nuren ya ce "ga wannan a din ga mata hayaki da shi, kuma a gaskiya Samima tana da ɗan sakaci da adduoi duk da tana da ibada, amma ibada ba zai yu ba sai da addua, ya kamata ku sakata a gaba ta dage " suka karba sannan suka masa godiya har sun miƙe zasu fita Malam Habibu ya ce "amm Alhaji Nasiru, ka bani lambar Baba Malam wanda ku ka kai masa Samima daga farko, dan ina so mu haɗu da shi akwai wata yarinya da mayu suka sakata a gaba, kwanan nan ma suka kashe Yayarta shine yanzu suka sake komawa kan Ƙanwar su na so su lasheta" salati Baba ya saka cike da alhini ya ce "kaii jama'a, inda ranka da sauran kallo, idan bawa bai ji tsoron Allah ba hakika yana tare da babban aiki ko nace asara a rayuwarsa, duniya tazo karshe" Malam Habibu ya ce "ai wani abun idan ka jisu ma sai ka mutu da al'ajabi, mu Malamai mu ne muke ganin zahiri, amma duk abun da za ace maka ya faru to wallahi karka karyata dan lalacewar mutanen duniya ya wuce duk tunanin mai tunani, kuma yana daga cikin alamomin tashin duniya, Allah dai yasa mu gama lafiya" suka amsa da Ameen Baba ya bawa Malam Habiba lambar Baba Malam sannan suka yi sallama suka tafi, gida suka koma, sai yamma kafin su Nuren suka fara yiwa su Umma sallama akan zasu wuce, Samima ta ce "Yayana gobe ina son zuwa skull fa, ina da pepar ga shi ina son zuwa shagona" ta fada kamar zata yi kuka, sosai tausayinta ya kamasa, baya so tana fita balle kuma yanzu da jama'a aka gano ita ba mutum ba ce, cikin sanyin murya ya ce.
"To ƴar Ƙanwata, idan kin shirya ki kira Yayanki ya zo ya kai ki, sannan ya jiraki ki gama ku dawo tare"
"To ba zaka je office bane?"
"Zan je mana, ko da dare ma zan iya zuwa, karki damu kinji?" ta gya ɗa masa kai ta kalli Suhail wanda yau kwata-kwata bai kulata ba, ta ce "Ya Suhail wai yau meke damunka ne? Na ga ka ƙi kulani kuma sai guduna kake yi, ko dai kana jin tsorona ne sabida ni macijiya ce?" daga yadda ta yi maganar mai cike da karya zuciyar mai sauraronta, da sauri Suhail ya ce "no Samima karki sake wannan tunanin kinji ko? Ai kema ba yin kanki bane,kuma ni har yanzu ban yarda ke macijiya ba ce tinda ban taba gani ba, dan haka karki saka a ranki, kinji beauty?" da shike haka yake kiranta musamman ma idan su na shago, dan murmushi kawai ta yi mai dauke da wasu fassarori, jiki a sanyaye Suhail ya fice, Nuren ya bi bayansa su Umma suna yi musu godiya, bayan sun shiga mota Nuren ya tada suka fara tafiya ya kallesa ya ce "yanzu fisabilillahi Suhail baka ji kunya ba?"
[02/09 à 08:45] 🌹🌹Flower 🌹 🌹: *SAMIMA* 🐉🐍
( _macijiya ce_)
Na
*ZAHRA ABDUL*
(MOMYN AHLAN)
Gajeran labari.
SHAFI NA BIYAR. ✍🏻
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association
*____________________________________*
"Ni kuwa naji kunya, amma wallahi Nuren ba zan boye maka ba, da na kalli Samima sai naji jikina na rawa"
"Daure wa zaka yi, ka zama Namiji, haba ni wallahi har kunya kake bani"
Dan murmushi Suhail ya yi ya ce "to ka ga laifina ne?"
"Eh to ba zan iya yanke hukunci ba" hira suka ci gaba da yi har Nuren ya ajiye Suhail a gida suka yi sallama shi ma ya wuce gida, da washe gari Nuren ya shirya ya zo gidansu Samima dan ya kai ta skull, sun fito kenan zasu shiga mota sai akan idon Sha'awa, ganin yadda Samima da Nuren suke tafiya su na murmushi tamƙar masoya, wani ƙululun baƙin ciki da kishi ne ya tirniƙe mata zuciya, da mugun gudu ta juya tana kuka ta yi hanyar gidansu, Nuren ma kam basu san da ita ba, mota suka shiga ya dauki hanyar skull din su Samima, su na tafiya su na hira, yawancin hirar tasu kuma akan Show din da za ayi ne, bayan ya ajiyeta ya ce " Ƙanwata ina jiranki a mota, shiga idan kin gama lecture din naki sai ki fito mu tafi gida ko?" da kyakkyawar murmushin nan akan fuskarta ta gya ɗa masa kai ta juya zata tafi ya ce "amm plss ban da shiga hidimar mutane, idan suka kulaki plss karki kulasu kinji?" sai da ta sunkuyar da kanta kasa kafin ta amsa a sanyaye ta dauki hanyar department dinsu,tana zuwa ma ta samu lecturer din bai shigo ba, kujerarta can baya ta samu ta zauna ta yi shuru, yawancin wa inda suke ajin su na kallonta ya yinda wasu yan mata biyu suka miƙo mata hannu su na gaisawa "Samima Nasiru kwana biyu? Ya gida?" cikin fara'a ta amsa da.
"Wallahi lafiya lau Alhamdulillah Sauda, yasu Sally?"
"Tana lafiya, yau sati daya kenan da haduwar'mu da ita, take gaya min akan cewa wannan Babban Show din da za ayi na fashion dress designer har dake an zabe ki ta uku ko?" Dariya Samima ta yi ta ce.
"Eh wallahi Sauda, ni ce ta uku"
"Kai Ma sha Allah abu ya yi kyau, ai har na gayawa Mom dina zamu zo, dan mu gani, idan muka ga wa inda muke so zamu siya, kuma Brother yana ƙasar USA zan tura masa ya miki talle na tabbata zasu so fashion dress din ki" sosai Samima ta ji dadi ta din ga yiwa su Sauda godiya, da haka Teacher ya shigo ya ɗibi kusan mintuna 30 yana musu darasi inda suka yi paper biyu kafin ya fice wani ma ya sake shigowa suka yi kusan awa ɗaya, tana yin lecture din ne kawai amma hankalinta yana kan Nuren dake zaune a mota yana jiranta, bayan wannan lacturer din ya fita shi ne su ma suka dan fito hutun rabin sa'a inda suka fito a tare su na hira dasu Sauda, ba karamin dadi ta ji ba, dan yau kusan wata daya kenan rabonta da ta shiga cikin mata yan uwanta ko cikin mutane ma su yi hira, sai dai ta din ga tsintar kanta a jeji da wasu halittu mugaye masu azabtar da ita, idan sun gama su mai do da ita gida, hanyar parking space suka ɗauka Sauda ta ce.
"Yo Samima ina zamu je ne na ga kin yi damu hanyar parking space? Na dauka zamu je mu ɗan yi bitar karatun Mr Josep ne fa,kin san baya da mutunci ko kadan" Sarah ta ce.
"Hummm, ni wallahi duk ran da muke da papern'sa gabana ya din ga faduwa kenan"
"Ni kuwa kun ga ba ruwana da shi, duk wannan masifa da rashin arziƙin da yake yiwa dalibai bai taba min ba" cewar Samima, Sarah ta ce.
"Ai da shi ke ,ke din kyakkyawace,kinsan Allah wasu Malaman nan yan iska ne" Sauda ta ce.
"Hakane maganarki wallahi" Samima ta ce.
"Allah dai ya ganar da masu ganewa, marasa ganewa kuma Allah shi kadai yasan yadda zaiyi dasu, ni dai yanzu wajan Yayana zanje tare muka zo da shi, zanje nace masa ya dawo ya daukeni da yamma ne, shi ya wuce office, tun da nasan yanzu kam sai mun kai yamma, ita wacce ta gaya min muna da paper ban ma ganta ba"
"Wacece ta gaya maki?" cewar Sarah.
"Hidaya Abbas"
"Kaii kice min mss love" suka yi dariya, dai-dai inda suka hango motar Nuren.
"Kaii amma dai Yayankin nan fa yana ji dake" cewar Sarah.
"To muje mu ma mu gaishesa ko?" cewar Sauda tana kallon Samima"
"Okay ai ga shi muna kan zuwa"
Nuren na kwance a cikin mota tun da Samima ta shiga class yake addua Allah yasa kar wani ya tabata dan kar yan makaranta su fara ganewa har ta samu lafiya, ya yi zurfi cikin tunani ya ji ana kwankwasa masa glass din mota a hankali ya buɗe kyawawan idanuwansa ya ɗaura akan kyakkyawar fuskarta tana masa murmushi, ƙasa ya yi da glass din ta dan turo baki ta ce.
"Sorry Yayana" dan murmushi shi ma ya yi ya ce.
"Sorry 4 what?"
"4 keep u waiting..."
"Haba wa ai girmanki ne shaleleta" ta saki dariya Sauda ta ce.
"Kai anya kuwa? Ko dai-ko dai?" hararar wasa Samima ta yiwa Sauda ta ce.
"Malama bana son gulma, kodai-kodai me?"
"Ahh mu dai ba zamu ce komai ba" su na dariya suka gaishesa ya amsa cikin sakin fuska ta ce.
"Yayana, kawai ka tafi da yamma ka dawo ka daukeni, idan kuma hakan bata yu ba, zan hau abun hawa na koma gida" shuru na dan wani lokaci Nuren ya yi, yana nazari kafin ya ce.
"Zan dai dawo na dauke ki din, if you done let me know ok?" ta gya ɗa masa kai ya kalli su Sauda ya ce.
"Plss ga amanata na baku, dan Allah am serious karku ga kamar da wasa nake yi, wallahi da gaske nake yi, kar wani ya kulata,itama karku bari ta kula wani, dan Allah zaku iya min wannan taimakon?" wuff Sauda ta ce.
"Ai karka damu, an gama In sha Allah ba zata kula ba, ka kwantar da hankalin ka ta hanyar kai kanka office lafiya zamu kula da ita" dan murmushi ya yi ya kalleta ya ce.
"Pls ina kara jaddada maki fa ban da kula kowa uhum?"
"To Yayana, In sha Allah a dawo lafiya" motarsa ya kunna ya ɗaga musu hannu ya yi hanyar fita gate, sai da ya fita kafin su ma suka kama hanyar zuwa inda ya kamace su, a hanya Sauda ke cewa.
"Samima, tsakaninki da Allah ciki ɗaya ku ka fito da Nuren?" da sauri Samima ta kalli Sauda.
"Me yasa kika yi min wannan tambayar Sauda?"
"Sabida akwai abun da na lura ne, dan Allah nima ki faɗa min, Yayanki ne Uwa ɗaya Uba ɗaya,ko kuwa cousin brothern ki ne?" dan yatsine fuska Samima ta yi dan ta tsani tambaya, amma ta ce.
"No ba ciki ɗaya muka fito ba"
"Haba wa ko da na ji" cewar Sarah su na haɗa ido da Sauda, Sauda ta ce.
"To dai wallahi, idan baku soyayya da Yayanki to yana matuƙar kaunarki, kalli ki ga fa, sai kara maimaita mata yake yi, kar ta kula kowa, kiji wani love mai haɗi da kishi,na ban mamaki da sha'awa " dan murmushi Samima ta yi, a ranta ta ce.
"Rashin sani yafi dare duhu, da yanzu za ku san ni wacece da yawanku guduwa zasu yi su barni,wasu ma shirin kasheni zasu yi" a fili kuma ta ce.
"Eh gaskiya kam, yana sona sosai, nima kuma ina son sa" tana gama faɗi ta yi gaba dan bata so su kara jijjib'o mata wani maganar, waje suka samu suka zaune su na duba litattafansu, sunyi zurfi cikin karatunsu, Samima bata an kara ba ta ji an wafce mata littafinta da karfi bisa alama da wuya idan bai yage ba, dan yadda ta ji karar book din nata, a harzuƙe ta miƙe tana kallon wanda ya fizge mata littafi, dogon tsaki taja ta ce.
"Kaiii!! A rayuwa indai aka ce maka mutum dabba ne, duk shekarun da zai yi a cikin mutane ba zai taba zama mutum ba...."
"Keeeeeee!!!" ya katseta da kakkausar murya.
"Samima ni kike kira da dabba?"
"An kira ka din, abun da yafi dabba ma zan iya kiranka da shi tunda ni dai ba tsoronka nake ji ba, wai shin me ka dauki kan ka ne kam Amir? Kana taka yan mata yadda ka so, to wallahi ni kam karka sake ka ce zaka shigo gonata, kuma idan har ka yaga min littafina sai ka biya ni" sosai ran Amir ya b'aci dan babu yarinyar da ta taba murzawa idonta kwalli ta samu kwarin guiwar gaya masa wa innan maganganun ba, matsowa ya yi kamar zai rungumeta saitin kunnenta ya ce.
"Wallahi!! Wallahi!! Wallahi!! Ki rubuta ki ajiye yau sai kinyi nadamar haihuwarki da Uwarki ta yi" a hasale Samima ta ce.
"Wallahi ba dai Uwata ba, sai dai Uwarka!!!" nan Amir ya yi kan Samima, Sauda ta fara ba shi hakuri dan Amir bai da mutunci da imani, nan wasu mazan skull suka rirriƙe Amir ana ta faman ba shi hakuri, Samima dake tsaye ko gizau bata yi ba, illa kwayar idanunta da suka fara riƙiɗewa suka koma jajur dasu, da kyar su Sauda suka ja ta dan lokacin komawa class dinsu ya yi,su na zuwa suka samu ma Mr Josep ya shigo har ya fara darasi, dan haka suka zauna suka hau daukar darasi su ma, basu da fitowa ba tun shigarsu sai uku da rabi, su na fitowa masallaci suka nufa suka yi sallar azhar da basu yi ba, nan suka zauna su na jiran la'asar tun da sun gama lecture din yau, cikin damuwa Sauda ta ce.
"Samima?"
"Na'am, ya aka yi?"
"Samima kina ganin rigimarki da Amir babu matsala kuwa?"
"Wace irin matsala kuwa?"
"Ni dai gaskiya a tsorace nake, dan ba shiga hidimar mutane kike yi ba, amma Amir baya da mutunci ko kadan" Sarah ta ce.
"Nifa wallahi Samima kin burgeni, haka kawai ka addabe mu a skull sai ka ce ɗan ido, bai isa ya miki abun da Allah bai miki ba" ita dai Samima bata sake shiga hidimarsu ba dan wani bala'en'en ciwon kai ke addabarta kamar gefen kanta sai faɗo ƙasa, sabida tsananin sara mata da yake yi, da haka har aka yi sallar la'asar suka gabatar, su na nan zaune drivern su Sauda ya zo daukarta,bayan Sauda ta tafi ba jimawa aka zo aka dauki Sarah, ta rage ita ɗaya zaune a masallaci, duba agogon hannunta ta yi ta ga hudu har da rabi da sauri ta fito tana waiwaye, har ta je parking space bata ga motar Nuren ba, duba ƴar wayarta da take zuwa da shi skull din ta yi a cikin jakarta, nan ta tuno ta bar shi a gida da take shiryawa, salati ta hau yi ta samu guri ta zauna jiransa, dan tasan cewa zai zo tun da ya ce mata zai zo, ba mamaki aiki ne ya riƙesa, shuru-shuru har biyar da rabi ga shi yunwa take ji, a ranta ta ce.
"Idan bai zo ba shidda ta yi,nikam tafiya gida zan yi" ai kuwa har shidda bai zo ba ta tashi ta dauki hanyar fita gate tana tunanin to ina Yayanta yake, har ta fito wajan gate tana neman abun hawa bata samu ba, ga shi ji ta yi ma a gajiye take, da kyar take iya ɗaga kafarta sabida yunwa dan ko a gida tea kawai tasha kuma bata ci komai a makaranta ba, tana kan tafiya a hankali bata ankara ba ta ji an cafkota an dannata a mota, ihu take son yi amma sai ta ji saukar wuƙa a saman bakinta gami da ce mata "shiiiiii!!" ɗaga idon da zata yi ta ga su Amir da abokansa su biyar.
"Ina zaku kai ni?" ta tambayesu hankalinta a tashe.
"Zamu je mu koya miki hankali ne, nan gaba idan kinga budurwa tana yiwa saurayi rashin kunya sai ki haneta" zare ido Samima ta yi ta ce.
" bangane ba, kamar ya? yanzu shi kenan budurwa bata da yancin kanta? Sabida tana tsoron shashashu b'ata gari irinku, sabida kawai......" saukar mari ne ya dakatar mata da sauran maganganun nata ba dan ta gama su ba, hanyar wani gida suka dauka inda Samima ta fara yunkurin ihu, suka toshe mata baki.
🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
Ta ɗayan bangaren lokacin da Sha'awa ta koma gida da ihu da kuka take gayawa Mamanta akan cewa ta ga Samima da Nuren sun fita a mota, kamar ma yawon shaƙatawa suka fita yi, dan rabon da Sha'awa ta je skull tun tana primary, Asabe ta dunƙulo wata uwar ashariya ta zundumawa Samima gami da cewa.
"Wannan yan iska masu zubin Aljanu ba zasu fita rayuwata na huta ba ko, to wallahi sai nayi maganinsu daga ita har uwarta da munafukin ubanta, kwantar da hankalinki shaleleta, ba dai Nuren da Samima ba? Yi shuru abun ki"
"Ni dai Inna bana so a taba min Nuren Samiman dai"
"Ahaf karki damu shalele, tun da suka je yawon shakatawa zata ga shakawata ganin idanunta, dan kuwa...." sai kuma ta yi shuru ta ce.
"Ta shi kije abunki shaleleta" cikin murna Sha'awa ta miƙe ta fice a gidan inda Asabe ta ce.
"Hakika Nuren zai shakata da macijiya idan ma bai sani ba ya sani, ta yi yunkurin siddabarunta amma ya ƙi yi, sabida ba ya yi da rana sai dare, nan tasa ayi mata bincike idan Samima bata dawo gida ba, dan ta ƙudirtawa ranta sai ta mai da Samima Macijiya a gaban Nuren da mutanen da suke gaban su,in da ta sakawa ranta ra magriba ta yi, zata fara surkullenta.
Hakan kuwa ta kasance dan kuwa gefen magriba da zata fara a lokacin su Amir sun kundume Samima, suka kaita wani gida su na kokarin rabata da mutuncinta, ihu Samima ke yi tana neman taimako amma babu mai taimako wanda zai taimaka mata, nan suka fara zage mata kayan dake jikinta, Asabe kuwa ta haɗa wutar sihirinta inda ta fara siddabarun surkulle tana ambatar sunan Samima da ta koma Macijita ta kashe duk wanda suke tare da ita, amma ban da Nuren, Samima wacce take cikin tashin hankali jin su Amir sun kwantar da ita su na shirin farke mata siket ta saki wani razananniyar kara, wanda sai da gidan ya amsa gaba ki daya, wani raɗaɗi da azaba ta ji, ba shakka tasan riƙiɗewa zata yi ta koma Macijiya, su Amir ihun da Samima ta yi yasa suka tsorata suka saketa da sauri suka koma gefe su na kallonta yadda take murƙususu, tana juyi, rungume hannayenta ta yi a ƙirjinta tana kakkarwar azaba, gurnani ta fara kafin fatar jikinta ya fara sab'a yana sabulewa,daga kafafuwanta ne ta fara rikiɗewa, nan wutsiyar macijiya ya fara bayyana, ihu su Amir suka saka suka fara neman hanyar guduwa ga shi su da kansu ne suka rufe kofa, kafin suyi kokarin budewa Samima ta koma hamshakiyar maciji sai huci take yi, nan ta yi kansu Amir inda ta fara binsu da sara, ta ko ina saran su take yi.
🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
*KUYI HAKURI NA RASHIN JINA JIYA, DA BA KUYI BA, NAGA SAKONNIN WASUN KU HARDA KIRAN WAYA MA, WALLAHI YARINYATA CE TA JI CIWO A HANNU, KUNSAN YADDA ƳAƳA SUKE A WAJAN IYAYE BARIN MA UWA, GANIN YADDA JINI KE ZUBA SHINE HANKALINA YA TASHI NA KASA KOMAI, NA GODE MUKU DA KULAWA, M AHLAN INA GAI DA MASOYANA A DUK INDA SUKE*🤝🏻🤝🏻
[02/09 à 08:46] 🌹🌹Flower 🌹 🌹: *SAMIMA* 🐉🐍
( _macijiya ce_)
Na
*ZAHRA ABDUL*
(MOMYN AHLAN)
Gajeran labari.
SHAFI NA SHIDDA. ✍🏻
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association
*____________________________________*
*_ashe da rai na ke son ku masoya ba da zuciyata ba 🥁💃🏻 komai ruwa da iska a kan ku bazana na daina kewa ba, idan na samu zarran samunku ba zana na tanka kowa ba, ni ban ga mai harara ba, bare na waiwaya haaa 🥁💃🏻 indai akanku ne zana jure yin typing....... da an taba ku ajirani dan ko tilas na zo na na ɗau fansa, jimirin jira kuke yi nazo na kawo muku Samima, ta gani 🙋🏻♀️🤣🥁💃🏻 indai akanku ne nayi nisa dan ba kiran da zan ji, tilas a ganmu tilas a barmu, kaunarku tun nai nisa typing..... ba batun na fasa ko da ace in ba aron birona 😜😜, kaii aradun Allah na gaji da wakar nan, nayi kokari ko? Wannan wakar sabida farin cikin sharhin da na gani ne a grp da dama da kuma wanda aka min ta pc, gsky ina godiya masoya, shiyasa naji karfin yi muku typing... Karku ga bana reply duk ina sane wanda suke min sharhi wallahi, am very busy ne shiyasa, masu min cmmnts da tnx ko strks ko hummm🙁☹️hummm🙁☹️ na kusan fara rubuta zallar tnx nima._*
🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
Nuren hankalinsa tashe yake ganin magriba ta yi, bai je ɗauko Samima a skull ba, ga mahaifinsa wanda yake kwancea jikinsa har yanzu baya motsi bai dawo hayyacinsa ba, ga shi yana ta faman kiran wayar Samiman bata ɗagawa, ga shi yana ta kiran wayar Suhail dan ya je ya ɗauko Samiman a skull amma shima wayarsa baya zuwa ko kaɗan, a gidansu Samima kuwa Umma ganin har magriba Samima bata dawo ba,abun ya dameta sosai, ga faduwar da gabanta ke yi, amma idan ta tuno tare suka fita da Nuren sai ta dan ji sauki a ranta, har Baba ya dawo yake tambayarta ina Samima, take ce masa, basu dawo ba, Baba yake cewa watakila sun biya gidan Alhaji Ibrahim ne, mahaifin Nuren, dan wani lokacin idan Nuren ya ɗauko Samima daga skull Momy ta kan ce ya kai mata ita, da dare sai ya mai da ta gida, da wannan tunanin su Umma suka shiririce, basu nemi Nuren ko Samiman ba, har aka yi sallar isha'i Umma ta shiga dakin Samima dan ta dauki chazar Samiman ta sawa Babanta chaji da shi nan ta ci karo da wayar Samima wanda take tafiya da shi skull yana ruri, mamaki ne ya kusan sumar da Umma ta dauƙi wayar ta duba sunan mai kiran ta ga an rubuta *YAYANA 4 LIFE* gabanta ne ya faɗi dan ta tabbata Nuren ne mai kiran, har wayar ta katse, ta ga miss calls din Nuren 57, tana shirin kiransa sai ga wani kiran na shigowa, Umma ta ɗaga kafin ta yi magana Nuren ya ri ga ta da cewa.
"Hlo, Ƙanwata kina lafiya?ina kika shiga ne ina ta kiranki ba ki ɗagawa, hankalina ya yi matuƙar tashi, kiyi hakuri nace zanzo in daukeki, inata jiran kiranki ba ki kirani ba, ga shi Abba muna fitowa daga masallaci munyi sallar la'asar ya yanki jiki ya faɗi asthman shi ce ta tashi tun dazu har yanzu wallahi baya motsi, hankalin ya kasu kashi biyu bana tare da natsuwa, ga Dr ya ce yana raye amma har yanzu bai motsa ba, ina ta faman kiran wayar Suhail ya je ya dauko min ke amma kwata kwata wayar shi bata shiga ban san inda ya shige ba, kin koma gida ne?" duk a kiɗime Nuren ke magana, tun da Nuren ya fara magana idon Umma ya fara zubar da hawaye, jin shuru yasa Nuren cewa.
"Hlo Babyna ba ki jina ne? Ko dai fushi kikayi da Yayanki? Kiyi hakuri plss kema kinsan ba zan ƙi zuwa daukarki ba"
Muryar Umma na b'ari cikin kuka ta ce.
"Nu...Nu...Nuren..Samima bata dawo gida ba, kuma bata tafi da wayarta ba, ni ban san bata tafi da shi ba sai yanzu da na shigo daukar chazarta zan sakawa mahaifinta chaji da shi na ga wayar na ruri" Umma tasa kuka mai sauti, da karfi Nuren ya furta.
"Innalillahi wainna ilayhirrajiun!!" ya katse wayar da sauri jikinsa na kyarma, ga mahaifinsa kwance akan kafarsa baya motsi likita yana kan aikinsa, a fili ya ce.
"Innalillahi!!!! Ƙanwata ina kika je? Idan wani abu ya sameki bazan taba yafewa kaina ba, dan zan samu rauni na alkawarin da na dauka" Nuren ya rasa me zai yi kawai yasa kuka, sai wajan karfe tara da rabi kafin Abba ya farfaɗo, yana farfaɗowa ya ga gudan jininsa na kuka, cikin muryarsa na marasa lafiya wanda suka ji jiki ya ce.
"Nuren? Me ya faru? Meya same ka?" cikin kuka Nuren ya ce.
"Abba Samima ce"
"Ya salam!! Me ya faru da Samiman?"
"Nima Abba ban sani ba, munyi da ita akan cewa zan koma na ɗaukota a skull ne, ina ta jiran kiranta ban jita ba, nayi tunanin idan aka yi la'asar zata kira ni, ashe bata ma tafi da wayar ta wanda take zuwa skull da shi ba, bayan mun fito daga salla la'asar kuma ina da niyyar zuwa, ciwon ka ya tashi, ba hali na tafi na bar ka cikin wannan yanayi, ga inata kiran Suhail wayarsa bata shiga, sai yanzu Umma ke sanar dani wai bata koma gida ba Abba"
Cikin kuka Nuren ke magana sai ka ce karamin yaro, Abba ya ce.
"Subhanallahi!! Nuren ai da ka hadani da Likita ka tafi abun ka, ko kuma ka kira Mom din ka"
"Abba kasan Momy tana da hawan jini, da yau na kirata, ta zo ta ga halin da kake ciki itama ciwonta zai iya tashi, tun 4 fa sai yanzu aka samu kanka" Abba ya numfasa da kyar ya ce.
"To shi kenan, now am ok, kira Mom din taka, kai ka tafi neman Samiman, Allah dai yasa tana lafiya" da sauri Nuren ya ajiye kan Abba bisa pillow ya gyara masa kwanciya sannan ya kira Momy ya gaya mata halin da ake ciki, sannan ya fice da sauri, motarsa ya shiga yana driving yana kuka, skull dinsu Samima ya koma amma fesss, bai ga wanda zai iya tambaya ba, zama ya yi a kofar gate riƙe da kansa yana hawaye, mutanen da suke ɗan wuce wa ya fara tambaya amma kowa ce masa yake yi bai sani ba, mota ya koma ya kifa kansa ya ji wayarsa na ringing yana dubawa ya ga Baba, mahaifin Samima, sai da ya share hawaye kafin ya ɗaga, hankali tashe Baba ke magana ya ce.
"Nuren, ya ake ciki? Ka ga Samiman?"
"Gani ina hanyar skull din nasu Baba, ku kwantar da hankalinku In sha Allah tana lafiya zan dawo da ita" da kyar Nuren ya dan lallab'a iyayen Samima ya zauna a mota shuru sai aikin goge hawaye da yake yi, har wajan goma da rabi yana zaune a wajan, ga shi baya da lambar ƙawayenta na dazu balle ya tambayesu ko taje gidansu ne,duk da hakan ba halin Samima bane, wayarsa ce ta kara ringing yana dubawa ya ga Suhail ne, yana ɗagawa ya hau wanke Suhail da ruwan masifa, ido rufe Nuren ke zubawa Suhail balbalin bala'i, Suhail ya ce.
"Nuren, ka yi hakuri ban sanar da kai ba, na ɗan yi yar karamar tafiya ne, kuma tafiyar ban san da ita ba, Abbana ne ya aikeni can cikin ƙauyen adamawa wajansu Gwaggonina, kuma wallahi basu da nertwork shi yasa, ban jima da shigowa gida ba, ko abinci ban ci ba, balle na watsa ruwa, yanzu kana ina ne?" Nuren sai da ya ɗibi 5min kafin ya ce.
" gani a gate din skull dinsu Samima"
"Okay, ka jirani gani nan zuwa yanzu" Suhail ya faɗa yana ajiye wayar ya fita ba shiri ya bar gida, bai tafi da motarsa ba, mashin ya hau yace a kaisa city university, cikin yan mintuna ƙalila aka kawosa, yana zuwa kuwa ya tarar da motar Nuren, bayan ya sallami mai mashin da sauri ya karasa jikin motar ya kwankwasa glass, Nuren ya ɗago ya ga Suhail ne buɗe masa motar ya yi, ya shige sannan ya ce.
"To yanzu ta ina zamu fara?" cikin kuka Nuren ya ce.
"Ban sani ba, ban sani ba Suhail, kaina duk ya kulle, tsorona kar wani abu ya samu Samima" Suhail ya ce.
"Koma gefen mai zaman banza, ka bani motar naja, kawai mu shiga gari dubata" Nuren ya matsa gefe Suhail ya karbi motar, nan suka shiga gari, duk in da ta kama dubawa kawai suke yi, har wajan sha ɗaya da rabi na dare.
🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀