"What the....... Harith meye haka?" na fada ina hararan shi, ya sake ni tare da jingina da mota. "ina so ne muyi magana in secret, can idanun mutane yayi yawa shi yasa" nace "shine kuma sai ka tsorata ni?" ya daga kafada, "sorry ok! Ikram tana hango mu fa, muje" muka fito daga wajen da yaja mu muna dan dariya muka tsaya a daidai inda zata dinga hango mu sosai, Harith ya kai hannun shi kamar zai yi cupping din fuskata., "Nafeesah?" Husky voice din Abbu ya sankame ni a wajen, bayan kamar sakan goma na juya a hankali kuma cike da tsoron irin fahimtar da zai mana. Tsaye yake a gefen mu sanye da shadda light brown da hula a kan shi, kallonmu yake daga ni har Harith din cikin alamun tambaya da kuma bacin rai. Take naji jikina yayi sanyi, na kalli Harith da a lokacin hankalinshi ya tafi da Ikram wadda ta juya zuwa cikin hall din kamar tana share hawaye daga karshe ma sai ya bi bayanta. Na kalli Abbu da har lokacin kallona yake yi, idanunshi suna fitar da wani irin tartsatsin abu cike da alamun bacin rai, ya dan matso kusa dani yace "me kike yi anan?" na dan ja baya kadan saboda kusancin dake tsakanin mu kafin in ce "umh, dama na fito ne zamu gaisa da saurayin......" wani irin kallo daya watso min ne yasa nayi shiru jikina ya dauki rawa, me ke damun Abbu ne yau? Na daure na karasa ".... Ramlah kawata" sai lokacin na ga ya dan sassauta muryar shi idan ban yi mistake bama har da sighing yayi softly wanda na lura dashi ta yanayin yadda kirjin shi ya sauka a hankali. Ya katse shirun da muka yi ta hanyar cewa "kin yi kyau sosai yau.... Kodayake kullum ma haka kike" nace "hmmm" kawai saboda gabadaya na rasa abin cewa it's really unlike him. Na sha jin kalmar yabo daga gareshi amma ban taba jin makamanciyar wannan ba don haka naji abun so strange. Yace "zaki koma cikin hall din ne??" na gyada kaina da sauri, yace "k, ni zan koma ne yanzu" na kalli agogon hannuna kafin in kalleshi, "karfe tara ne fa kawai Abbu zaka tafi tun yanzu" yayi er dariya data saka ni shagala da kallonshi, "ban cika halartar ire-iren wadannan abubuwan ba Nafeesah.... Wannan din ma ya zamar min dole ne, naso ganin wani very badly kuma babu hanyar ganin nashi sai ta nan shi yasa" na gyada kai kamar na fahimce shi, sai dai maganar gaskiya na kasa processing maganganun shi a cikin kaina, babu abinda nake fahimta a lokacin irin daddadan kamshin turaren shi dake tashi da yadda zuciyata take bugu. Ya zura hannu a cikin aljihu ya ciro rafar kudi sababbi kar dasu ya miko min, naki saka hannu in karba har sai da yayi magana, "kudin liki ne ba wani abu ba, karbi" da sauri na hau girgiza kaina, "ina dasu nima Abbu ka bar kudin ka" ya hade fuska "akwai abinda na taba baki a duniyar nan ba tare da kin min gardama ba kuwa?" nace "Abbu Allah ba gardama bace, kawai akwai kudin likin a wajena ne nima" yace "to tunda na baki ai sai ki amsa koh?" na bude baki zan yi magana ya sake hade muryar shi, "Nafeesah karbi kudin nan kafin raina ya baci fa" yana iya? Sai kawai na saka hannu biyu na karba har da dan dukawa nace "Nagode sosai Abbu Allah ya saka da alkhairi" yace "Ameen.... Go back" ba musu na mishi sai da safe na wuce, ina jin idanun shi a kaina har na shige cikin hall din. Na koma wajen su Ramlah na zauna, lokacin da aka kira amaren suka fita wajen rawa muma muka tashi muka je muka fara liki. Sai sha biyu saura aka tashi daga wajen dinner dinnan, an daiyi komi lafiya an gama. Kafin mu isa masauki sai wajen karfe daya aikuwa mun sha fada sosai wajen Anty Ameenah kamar me! Washegari aka kai Amaren gidajen su na aure, ita Sa'adiya tana Lamido Crescent Ni'ima kuma suna Zoo road. A gidan Sa'adiya ne muka hadu da Ikram, mun gaisa da ita sama-sama tana ta wani shan kamshi ni kuwa ina mata dariya a ciki don nasan dalilin hade fuskar, sai a lokacin naji ashe cousin din mijin Sa'adiya ce. A washegari naso komawa gida Anty Ameenah tace ina! Ai sai na cinye sati daya din da aka bani daga gida, ban yarda da gaske take ba sai data dauke min jakar kaya ta kulle a bedroom dinta, ni wallahi dariya ma ta bani. Dole haka nan na zauna, dama kwana biyu suka rage min. Naje gidan Anty Haleemah da Anty Raliya, washegari kuma direban gidan Anty Ameenah ya kaini gidan Abbu. Da yake ranar Lahadi ce na samu Abbu a gida, na ga tarbar data bani mamaki kam. Tun daga bakin gate su Hafsy suka taro ni suna ihun murna har cikin falo. Gidan yana nan kamar yadda na tafi na barshi, matar gidan tana uwar daka. Na shiga har ciki muka gaisa na koma falo wajen su Hafsy, nan suka fara ajiye min tarkacen kayan makulashe muka shiririce anan muna hirar mu har aka kira sallar Axuhur, Abbu ya fito daga dakinshi sanye da jallabiya ruwan toka da alamun masallaci zai je, na zamo daga kan kujerar da nake zaune na gaida shi, ya amsa tare da wuce mu su Abdullahi suka tashi suka bi bayan shi ni da Hafsy kuma muka shiga dakinta muka yi tamu sallahr.
Abbu ya mana odar abinci daga restaurant muka ci namu ni da Hafsy a daki. Ina nan a gidan har yamma tayi, direban Anty Ameenah ya dawo daukata, na je nawa Anty Mubeenah sallama muka fita zuwa inda direban yake jirana cikin rakiyar su Hafsy. Abbu yana zaune akan kujera da laptop a gabanshi akan dan karamin table yana ta danne-danne a ciki. Na fasa shiga motar da nayi niyar yi na taka zuwa gaban shi, ya dago ya kalleni yana murmushi. Na sadda kaina kasa cike da kunya, "Abbu zan wuce" ya gyada kai, "gobe zaki koma koh?" na gyada kaina, yace "nima ina so zan shiga Kadunar gobe in shaa Allah. I'll drop you off goben, that is idan tafiyar tana nan" na kalleshi fuskana dauke da alamun tambaya sai dai na basar, ai yace akwai abinda zai kaishi kuma ma cewa yayi sai idan tafiyar tana nan ne sannan zai ajiye ni. Nayi murmushi nace "to Abbu, na tafi" ya gyada kai yana jifana da murmushin nan nashi, "ok Nafeesah! Mun gode da dariya" na danyi murmushi tare da juyawa na tafi. Muka sake yin sallama dasu Hafsy na shiga mota muka tafi, daidai saitin Abbu na dan saci kallonshi, idanunshi suna kaina yana kallona da wani irin yanayi da kallo with so much affection, nayi saurin sadda kaina kasa ban dago ba har sai da muka bar layin.
*******
Na fito jaye da trolley dina, Anty Ameenah tana zaune akan kujera a falonta ta kalleni tana murmushi, "tun kafin yamma tayi har kin gaji damu koh Nafeesah?" na girgiza kai ina murmushi nima "haba Anty ba haka bane, karfe hudu fa tayi already kuma kinsan akwai tafiya a gaban mu" tace "haka dai kika ce. Mun gode sosai duk da haka" na fara tafiya yayin data tashi ta biyo bayana. Abbu yana tsaye a jikin motar shi Toyota yana jiran fitowar mu. Hasken ranar dake haska shi ya kara haskaka shi cikin shigar Dogon wandon jeans baki da bakar shirt, hakan ya haskaka shi ba kadan ba. Kyawun shi da cikar kamalar shi suka kara fitowa sosai, ban san cewa na shagala a kallon shi ba sai da naji Anty Ameenah ta dan zungure ni, a matukar kunyace na sadda kaina kasa. Ya Allah! Abinda Bawan nan naka yake saka ni yi!! Ya bude booth muka saka akwatina a ciki. Na bude gefen mai zaman Banza na shiga na zauna, Anty Ameenah ta leko tana min addu'ar a sauka lafiya har Abbu ya shiga shima ya tashi motar muka tafi. Tuki yake yi a nutse kuma cike da kwarewa, baka jin motsin komi a cikin motar kamar babu abu mai numfashi a ciki. Ya kunna kira'ar Sudeis cikin Suratul Maryam, na dan kwantar da kaina a jikin kujerar. A matukar takure nake ji na, it felt so awkward for me, to be hooked up with someone you so much cherish, wanda nake hangowa a matsayin mijin da zan aura, wanda da kyar nake hana kaina throwing my self to him a duk lokacin dana ganshi, yanzu da muke tafiyar nan sai nake jin wani iri a jikina, gashi duk yadda naso koda barci ne inyi abun yaci tura. Muna barin cikin gari Abbu ya ware injin mota, lokaci zuwa lokaci za a kira shi a waya ya daga da wannan damar nake samu in kare mishi kallo. Abbu is really good looking and handsome man. Wajen karfe shida muka fara shiga Kaduna, na dan sauke ajiyar zuciya a hankali ina jin kamar in bude idona in ganni a tsakiyar gidanmu. Well, it has really been a hell of a ride (-Justin Bieber). Can u believe that tunda muka shiga mota kalma daya bata hada mu dashi ba?? Suddenly naga yayi parking din motar a gefen hanya, wani dan karamin daji ne gab da za a shiga Kaduna. Inda yayi parking din motar gaban wata korama, reflection din rana da take kokarin faduwa ya fita zane a Vikings, the view was wow! Gashi wajen babu hayaniya sai ta ababen hawa dake ta wucewa a guje. Na daga idona na kalleshi cike da mamakin dalilin da yasa muka tsaya anan, idanun shi suna ga koramar dake gaban mu, he seems out of the world, ya shige duniyar tunani. Na dan yi gyaran murya tare da cewa "Abbu.., laa.... fiya muka.... tsaya??" a hankali, bai kalleni ba, haka bai yi magana ba. Sai na tsaya kawai ina son in ga abinda xai faru. Lokaci mai tsayi muna a yanayin da muke har hasken rana ya fara daukewa duhu ya fara shigowa, tsoro ya fara shiga ta. Abbu ya kira sunana a hankali kamar mai rada, "Nafeesah!!" na kalli sashen da yake tare da amsawa, shiru ya sake biyo baya na kimanin minti guda. Kamar daga sama, kamar a duniyar mafarki naji saukar maganar, "Nafeesah! Zaki Aure ni??!". Tsabar firgita da mamaki sai da kaina ya buge da glass din motar, ban damu da zafin da naji ba Abbu kawai nake kallo kamar wata sabuwar mahaukaciya ko kuma shine nake wa kallon sabon mahaukaci?? Ganin expression din dana nuna yasa ya dan kauda fuskar shi daga kallona, "Nasan baki taba tsammanin faruwar hakan ba Nafeesah, na sani. Ni kaina nayi hesitating fada miki maganar nan yafi sau dari, sai dai I couldn't anymore. Auren ki nake son yi Nafeesah da gaske, ina kuma fatan cewa zaki aminta da hakan?" ya juyo ya kalleni. Allah ne kadai yasan yanayin da nake ciki a lokacin, baki nake so in daga a lokacin in amsa mishi da YES! Da duk karfin da Allah ya bani, in gaya mishi nima burina kenan sai dai ina! Na ma manta yadda ake yin magana a dan lokacin. Wasu kyawawan mintuna biyu suka wuce a haka, wasu masallatan har an fara kiran sallar magriba. Abbu yace "look Nafeesah! M not forcing you into this kin gane? Zan baki lokaci kiyi tunani da kanki don bana so in tauye miki hakkin ki Nafeesah, idan nayi haka na cuce ki. I just..... M just tired Nafeesah. I want us to get married ASAP. Hell, idan kika amsa min yanzu m ready to marry you tomorrow Nafeesah.... Na baki lokaci ki samu time ki yanke shawara akan abinda kike gani sai dai kada ya dauki lokaci pls, sannan ina so kiyi duba da Allah da soyayyar da Iyalina suke nuna miki Nafeesah, we really need u in our lives". Da wannan ya tashi motar muka kara gaba, duk yadda naso in dawo cikin natsuwata abin yaci tura, yes! I was shocked beyond my imagination. Har yayi parking a kofar gidanmu, ina jin yana gayawa Mai gadi da yake kokarin buddy kofa ba shiga ciki zai yi ba, Mai gadin yazo ya bude saitin kofar da nake yana jera min sannu da hanya. Kamar wadda aka daddaba daga barci, sai lokacin duniyata taci gaba da juyawa da dai tsayawa tayi cak. Na zura kafana daya waje da niyar fita, Abbu ya tsayar dani ta hanyar kiran sunana. Na dakata ba tare dana juya na kalleshi ba, bani da kuzarin kallon shi, ina tsoron abinda kallon fuskar shi zai haddasa min. Nasan zan iya amsa mishi da yes a take a lokacin. Yace "please think about US carefully Nafeesah, ina fatan jin daddadan labari daga gare ki" na karasa cira daya kafar na fita daga motar. Mai gadi ya maida mishi murfin motar ya rufe, ya sungumo trolley dina ya biyo ni dashi. Da kyar nake daga kafa ta. Taimakon Allah ne kadai ya kaini cikin gida, Mommy ta fito da saurinta tana min oyoyo, gani na a haka sai data yi turus. Ta matso tana tambaya na lafiya na lau kuwa? Da kyar na iya daga baki nace mata "gajiya" tace "shine kuma kika yi zuru-xuru haka? Wuce kije kiyi sallah kici abinci sai ki kwanta" babu musu na shige dakina. Na dauro alwala nayi sallah, yadda nake jin cikina a cike nasan babu abinda zan iya ci a lokacin. Ko kayan jikina ban cire ba na haye gado tare da lashes wutar dakin. Ina jin lokacin da Mom ta leko dakin ta maida min kofar dakin ta rufe. A gajiye nake, barci nake ji, sai dai awa daya kenan da kwanciyata babu alamun barci a tattare dani. Maganganun Abbu suke replaying a cikin kwalwa ta over and over, for once in my life da naji farin ciki yana so ya saka ni kuka, sai dai shima kukan yaki zuwa. Ya Allah!! What in the world am I suppose to do??! Ranar nasan dama babu barci, ina zan iya barci dama idan har na cigaba da hango ni zaune akan gado a cikin gidan Abbu lullube da gyale???
*♡Jeedderh♡
*NI DA ABOKIN BABA NA....!*
*©°•Jeedderh Lawals•°*
*34*
Da murmushi na tashi akan fuskata, rabon da inyi barci mai dadin na yau har na manta. Naje nayi brush na fito falo, babu kowa a falon dama nasan ba lallai in ga kowa ba saboda karfe goma sha daya na safe ne lokacin. Break fast na fara yi kafin na shiga dakin Mommy na gaida ta. Tace inje in shirya zata aikeni gidan Aunty Uwani, da saurina naje na watsa ruwa na shirya na fito. Turaren wuta ne da kayan labule da bed sheets ban san dai kona waye ba sai da naje can take ce min na diyar kanwar mijinta ne. Can kuryar dakinta na shige na nade akan gado ina kara tunanin makomar zancen Abbu a cikin raina, wani bangare yana shawarta ta da in kira shi a yanzu in fada mishi na amince, wani kuma yana gaya min hakan bai dace ba, wani kuma yana ce min in dan bashi lokaci dai gabadaya na rasa wanda zan dauka, a haka barci ya dauke ni saboda rashin barcin da ban samu a daren jiya ba, sai wajen karfe uku Anty Uwani ta tashe ni nayi sallah, bayan la'asar na musu sallama na wuce gida. Ina zuwa na ba mommy sakon data bani in kawo mata na wuce daki, ba a jima ba na fito muka shiga kicin da ita muka fara girki.
Kamar yadda yake Al'adar gidan mu, bayan an gama muna haduwa a dakin Daddy a yawancin darare, wani lokaci muyi kallo wani lokacin hira, sometimes ma musamman idan daddy yana ayyuka zaku ga kowa abinda ke gaban shi kawai yake yi. Ina zaune a kasan kujera ina browsing Mummy kuma tana kan kujera a xaune, Daddy ya fito daga bedroom din shi ya zauna a kusa da Mommy. Daddy ya kira sunana in a serious tone, "Uwata" na amsa a nutse tare da kallon shi, yace "last two weeks da suka wuce Ibrahim ya same ni da wata magana mai Muhimmanci" yayi shiru yana kallona yayin da zuciyata ta hau duka kamar zata fado kasa, ya cigaba da magana "Yace wai Yana So Ya Aure Ki! Ni kuma nace mishi sai naji daga bakin ki don bana son tursasa ki akan abinda baki da niyar yi, me kika ce? Zaki Auri Ibrahim?" Na sadda kaina kasa ina wasa da yatsun hannuna, ban san abinda yakamata in ce ba, ina son Abbu kuma Ina son Auren shi? Ina son Abbu amma ina tunanin auren shi is not a good idea? Ko kuwa me zan ce?? Mommy tayi saurin riga ni magana, "Haba Abban Ummiey, kaima kasan cewa wannan ba abu bane mai yiwuwa. Shi bai yi tunanin abinda zai zo ya dawo bane ya kirkiro wannan magana? Wannan abu ba zai yiwu ba sam!" duka ni da Daddy muka kalleta, fuska a hade sosai take yin maganar, daga ganin yanayin idanunta nasan cewa she is strongly against it, sai jikina ya kara yin sanyi akan na da. Daddy yace "me kike cewa ne haka Habibty?" tace "Abinda ya kamata mana, Idan shi idanun shi sun makance da cin Amana bai kamata naka su rufe ba Abban Ummiey. Haba! Ace daga tura yarinya yin IT na wata shida kawai sai aji wai ta buge da aure mai gida? Kaima kasan cewa wannan ba abu bane da zai yiwu ba, sai dai idan so kake ka saka mu a bakin duniya kuma" Daddy ya danyi murmushi, "sai dai idan basa son junan su Habibty, amma idan suna so then who cares about what people will say? Su mutane ai aikin su kenan ina tabbatar miki idan kika ce zaki biye ta mutane to numfashi ma sai sun miki izinin kiyi kenan?" Mommy ta hade fuska "na kula ga gaskiya nan kana gani kuru-kuru amma kana takewa, son Kai ne ko me? Aure dai Nafeesah da Ibrahim babu shi!! Ba zan taba bada hadin kaina ga cin amanar wannan da kuke shirin yi ba" Daddy yace "ke kuma kin ki fahimtar abinda soyayya zata yi da wannan ba zata iya ba, baki tsaya kinji ta bakin yarinya ba kin zauna kina ta tada jijiyoyin wuya, be it zaman aure ko cin amana kamar yadda kika ce don ni dai ban ga komi ba a ciki, ina ga ai ya rage ga yarinyar koh?" Mommy tace "ni nasan Ummiey ba zata taba aminta da hakan ba, ga samari nan bila adadin suna karakaina a kanta sai ta buge da wani can, ga mata ga 'ya'ya, abokinka kuma for that matter, anya Abban Ummiey ka duba maganar nan sosai?" Daddy ya kalleni yace "Uwata!" na daga kai na kalleshi, yace "kada ki damu da abinda take fada kin ji? Just tell me idan kina son Ibrahim kuma zaki iya auren shi" na kalli Daddy na kalli Mommy, toh fa! Ga sanyin Idaniyata guda biyu a gabana, ko wanne ya zuba min ido yana jiran amsa ta wanda nasan cewa amsar da zan ba daya daidai take da bacin ran daya, abinda na tsani gani da ji kenan a duniyata ace daya daga cikin Iyayena yana cikin bacin rai sabida ni. Abinda Mommy take fada gaskiya ne, shima Daddy akan gaskiyar shi yake, to me zan yi kenan? M I going to disappoint one of them? Ya Allah!! M extremely confused! Na samu kaina da girgiza kai wanda ni a karan kaina ban san dalilin yin hakan ba, Daddy yace "me kike nufi da girgiza kai, eh ko aah??" na sake girgiza kaina, "ban sani ba Daddy!" Daddy ya kura min ido na tsawon lokaci, yace "tashi ki tafi kawai Uwata, Allah ya zaba mana mafi alkhairi" ba musu kuma ba tare dana kara uffan ba na musu sai da safe na wuce dakina. Hannu dafe da kai na fada kan gadona na kwanta, na gaji! Na gaji haka nan. Haba! Kwana biyun nan kaina har ciwo yake yi tsabar tunanika da suka hana ni sukuni, abin ya ishe ni haka nan. Tashi nayi na fada toilet na dauro alwala na fito na haye kan Abin sallah, sallah na fara jerowa, dana gama na roki Allah akan yayi mun zabin abu da yafi alkhairi a cikin rayuwata, na gama nayi shirin kwanciya barci na kwanta zuciyata cike da sake-sake.
*****
Tsawon sati guda Daddy bai sake min zancen Abbu ba Mommy ma haka, haka a tsayin lokacin nan ban sake ji daga Abbu ba. Mun koma makaranta don dama ba wani hutu aka bamu mai tsayi ba. Ranar Asabar ina kwance a dakina da hantsi, mun gama waya da Harith kenan yana gaya min yadda suke shan fada shi da Ikram akan wai ni budurwar shi ce ni kuma ina ta shan dariya, na ajiye wayar tare da kurawa ceiling ido ina kallo. Wani kiran wayar ne ya dawo dani cikin hankalina, na mika hannu a sanyaye na dauki wayar. Ban san lokacin dana zabura na tashi zaune dangargar ba, Abbu. Kallon wayar kawai na dinga yi har kiran ya kusa karewa, in daga in ce mishi me? Koda yake na riga na gama yanke shawarar abinda nake ganin daidai ne a rayuwata so let's just finish this once and for all kawai, na karfafawa kaina gwiwa. Nayi gyaran murya tare da daga kiran na kara wayar a kunnena......
(Sorry for the short Chapter, m kinda busy this days wallah..)
So Kafin in tafi let me ask you this:
~Me kuke tunani game da Littafin Ni Da Abokin Baba Na so far?
~Me kuke gani ya kamata Nafeesah tayi a wannan lokacin, Accept or Reject?
~Who's siding with Mom, Dad? Raise your 👐 so I can count you guys lol
~Stay blessed and cool, see yah
Lots of Hearts and Flowers #teamAbbu 💞💞💐💐
*♡Jeedderh♡*
*NI DA ABOKIN BABA NA....!*
*©°•Jeedderh Lawals•°*
*35*
"Assalamu Alaikum" sansanyar muryar shi ta doki kunnena, duk wani karfin gwiwa dana tanada da kaudin da nake na cewa Abbu ya daina firgita ni ashe aikin banza nake yi, a take muryar shi tayi raga-raga da naman jikina, yayi gyaran murya tare da ambatar sunana, na amsa a nutse kuma a hankali cikin muryar rada, shiru ya biyo bayan hakan na lokaci mai tsayi, baka jin komi sai karan iska dake wucewa ta cikin wayar. Yace "Nafeesah! Ya muka kare da maganar mu ne?" nayi shiru ina zare idanu, da me na shirya zan ce ne? Gabadaya komi ya fita daga cikin kwakwalwata, yace "umh?! Ina sauraron ki" na bude baki zan yi magana sai dai sautin dake fita kawai shine "ermm.... ermmm" na kasa yin takamaimiyar magana. Abbu ya tausasa murya, "look Nafeesah. I don't have much time yanzu, mintuna kadan suka rage min in tashi zuwa Vancouver zan yi wani four months course acan so please do tell me, me kike tunani? Ina son ayi ayi auren mu dana dawo Nafeesah, da so samu ne a gare ni da tafiyar nan dake zan yi ta a matsayin mata ta Nafeesah don ba wani tsayawa zan yi bata lokaci wajen soyayya kamar yaro ba, kin san na tsufa da hakan koh?" wata hudu a Vancouver? A perfect timing!! Yace ina jin ki Nafeesah, an fara kiran fasinjoji, me kike tunani? Zaki iya aure na??" na lumshe ido a hankali zuciyata na suya a kirjina kamar an tsoma ta a ruwan zafi, "I Am Sorry Abbu...... I can't!" shiru ba magana daga bangaren shi yayin da kowace wucewar dakika zuciyata take nunka gudunta har na fara tunanin idan na kara minti daya a wannan lokacin zata iya bugawa gabadaya. Bayan kaman wucewar lokutan dana kasa lissafawa, yayi gyaran murya, muryar shi lullube da wani irin embarrassment da daci yace "zan kira ki idan muka sauka Nafeesah" a hankali hannuna da wayar suka sauka akan gadona kamar wadda aka zare mata numfashi. Nayi imanin da ace Duniya da lokaci suna tsayawa da sai ince nawa sun tsaya, komi nawa ya tsaya cak. Bana fahimtar komi sai daci da sanyin jiki dana ji suna fita daga bakin Abbu, ban yiwa kaina adalci ba, sai dai ina bukatar sanyin rai dana zuciya. Ina bukatar farin cikin iyayena, nasan cewa definitely Mommy zata yi farin ciki da hakan Daddy ne dai ban sani ba, ni kuma I only need those four months, In shaa Allah kafin lokacin ya cika, "I'll over come it!" na fada a fili cikin karfafawa kaina gwiwa. Karan bude kofa yasa nayi firgigit na kalli kofar, Mommy ta shigo tana kare min kallo, tace "kin yi bakuwa Ummiey" na kalleta da sauri, "bakuwa, wacece?" ta dan maida kanta wajen kofa tare da furta "shigo" Ikram ta shigo dakin bakinta dauke da sallama, da sauri na tashi tsaye ina amsawa, iso na mata zuwa gefen gadona ta zauna, Mommy ta juya ta fita ta barmu muna gaisawa, ruwa da lemu na dauko mata a fridge na dawo, muka zauna shiru a dakin saboda ba wani sabo muka yi da ita ba dama, can na katse awkward silence din nace "so???" ta sadda kanta kasa tana wasa da yatsun hannunta ta kasa magana, na dan yi murmushi nace "Kina son tambayar Abinda ke tsakani na da Harith koh?" ta kalleni cikin mamaki kafin ta gyada kai, nace "magana ta gaskiya Ikram babu abinda yake tsakani na dashi, duk abinda kika ga mun yi was just a plan, yana so ne yayi provoking dinki" ta nuna kanta da yatsa, "ni kuma? Why??" na zayyane mata labarin duk abinda kenan, Ikram tayi shiru kanta a kasa har na gama. Tace "yaki ya fahimce ni ne kawai, shekaru biyu kadai suka rage min a karatuna, menene a ciki idan ya hakura zuwa shekarun biyu?" nace "Ikram kina son Harith shima yana son ki saboda haka ni ban ga abin tada jijiyar wuya a wannan maganar ba. Shawarar da zan baki shine to just go for it, karatu baya hana aure kamar yadda aure baya hana karatu idan har kika maida hankalinki akan hakan" tayi shiru kamar mai tunani kafin ta kamo hannuwana ta rike, "nagode sosai Nafeesah. In shaa Allahu zan zauna in duba hakan, nagode" na danyi rubbing hannunta dake kan nawa ina murmushi. Mun dan kara hira da ita kafin ta min sallama ta tashi, na raka ta har bakin titi ta samu abun hawa ta tafi ni kuma na koma gida. Da dare Daddy yake gaya min an sai min DE form a BUK, na turo baki nace "Daddy ni fa ABU nace maka ina so" yace "sun riga sun rufe saida basically ne shi yasa nasa aka nema miki BUK din" nayi shiru ina tunani, wannan shine kaka-kara-kaka din fa, ina gudun Abbu shi kuma yana kara bibiyata, nace "ni dai kawai na hakura sai next year" daga Mommy har Daddyn kallona suka yi, Mommy tace "sai mu saka ki a gaba muna kallo har shekara koh?" Daddy yace "Duk maganar zama bata ma taso ba, tunda an samu admission din ki daure ki tafi can din kawai" nace "amma a cikin hostel zan zauna koh?" Mommy tace "to in ba can ba ina? Dole can zaki zauna" Daddy ya daga baki kamar zai yi magana sai kuma yayi shiru kawai. Daga haka aka fara processing din nemar min admission a BUK. A gefe daya kuma naci gaba da karatu na.
Sati daya, biyu, uku suka shude babu alamun kiran Abbu a cikin wayata, ban kuma sake jin magana game dashi ba. Tunanika iri-iri game da hakan babu kalar Wanda ban yi ba da wasi-wasi, kila ya hakura ne, kila maganar da nayi ta bata mishi rai, kila dama ba sona yake yi ba.
*♡Jeedderh♡*
[14:40, 12/18/2017] +233 50 348 1936: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*
*©°•Jeedderh Lawals•°*
*36*
"So sai kawai kika yi rejecting din golden opportunity like that?" cewar Ramlah. Zaune muke a lecture hall dinmu bayan mun gama lectures. Kwana biyu bana cikin natsuwata, walwala ta min kaura kamar yadda fara'a tayi kaura daga fuskata., a duk lokacin dana samu na kebance babu abinda nake yi sai tunani, Ramlah ta kula da yanayin da nake ciki yau dai ta rike ni sai dana fada mata abinda ke faruwa, ko babu komi naji dadin fada mata din da nayi. Tunda abin ya faru babu wanda yaji maganar, ni kadai nake juya abun a cikin raina. Fadar irin mamakin da Ramlah tayi ma bata baki ne, data hangame baki sai dana cika mata shi da popcorn sannan ta rufe. Na kai popcorn bakina tare da gyada kai, "babu wani zabi daya rage wannan Ramlah, kema kin sani" ta kura min ido, "akwai so many and n much more choices Babe, ke ce dai baki so zaba ba". Muka yi shiru na dan lokaci, ta sake cewa "wai ba kince kina son shi ba?" na gyada mata kai, "then why did you do it? Bayan kin san zaki kasance cikin damuwa?" na kalleta sosai, "Ramlah, ina cikin rudani wallahi" ta girgiza kai, "no! Ki kike confusing din kanki dai, wannan abu ne mai sauki da cikin kiftawar ido zaki magance shi. Kina son mutum, then marry him mana, meye matsalar ki wai? You once fall for the wrong person yanzu kuma right person din yana sonki kina gudu da kafafun ki? Me kike so ne?" nace "so, kulawa, zaman lafiya Ramlah" tace "A cikin abinda kika lissafo wanne ne ba zaki same shi ba wajen Abbu?" nace "duka..... Ban sani ba ko Abbu yana so na ko baya sona ba. Ban sani ko dangin shi zasu karbe ni ko ba zasu karbe ni ba, ban sani ko iyayena zasu yi farin ciki da haka ko ba zasu yi ba...." ta katse ni, "wait don Allah. Shi Abbu da bakin shi yace baya son ki?" na girgiza mata kai, "ko Kadan. Yanayin acting dinshi towards me ne yake nuni da hakan. Ki duba ki gani tunda muka yi maganar nan dashi yau an wuce wata biyu amma koda wasa bai kira ni, bai taba nuna yana sona ba, bai taba furta cewa yana so na ba, a haka zan aure shi kuma? To ince nayi auren me?? Bayan haka alakar shi da matar shi is not in a good condition wanda hakan ya saka ni zargin cewa saboda ita yake so ya aure ni...." na zayyane mata duk irin yanayin zaman su dana sani da challenge dinsu akan karo aure, tayi shiru tana saurare na har na dasa aya. "shine nake jin tsoron na amince dashi kuma daga baya in zo ina dana sani" Ramlah hararata take yi kamar wata wadda na kashe mata da, tace "kin san Allah? Da ba don ke bace? Da sai na dalla miki mari. Wai me yasa ke kullum tunanin ki daban yake dana normal mutane?" nima na harareta, "kin fara ko? Meye laifina anan to?" ta dafe kai, "saboda kin kasa fahimta. Sai me idan Abbu baya son ki? At least yana so ya aure ki which means ko yaya ne yana admiring dinki., kuma ko ba jima zai fada tarkon son ki girl balle ma na riga dana san tuni ya fada" nace "me yasa kika ce haka?" tace "yadda ya dinga kallonki with so much tenderness and affection in his eyes ranar dinner din su Ni'imah, ke ko ba wannan ba kallon da mutumin nan yake miki da gaske na so ne" na girgiza kaina, "I doubt it Ramlah" wayana tayi karan shigowar sako, na ciro ta daga cikin jakata tare da bude sakon bakuwar number ce kuma har da karin alamun + wanda yake nuni da cewa sakon daga wajen Nigeria ne, cewa aka yi., 'Let's have a talk later please, I'll call you nine pm on dot in shaa Allah. -Galadanchi' hannu yana rawa nayi niyar maida mishi amsa Ramlah tayi saurin rike min hannu, na kalleta "meye?" tayi rolling idanu, "haba babe! Bashi kamar minti goma mana zuwa ashirin kafin kiyi reply?" nace "ban gane ba? He sent me a message, let me reply please" ta kwace wayar daga hannuna, "kin ce kin fada mishi baki son shi, then me kike so yayi tunani yanzu? Ya turo miki text, within a second kin maida reply as in you care dinnan, kinsan Allah mazan yanzu ba a musu haka koda kuwa wanda yake son ka ne balle ke da kike ikirarin kina son shi" na sadda kaina kasa, "Ramlah kin san halina sarai. Ban iya boye so ba kamar yadda bana iya boye ki, bazan iya yiwa Abbu haka ba" tace "at least try mana. Be like the classy girl you are, wannan yana da banbanci da son da kike yiwa normal mutane, ina gaya miki ta haka ne kadai zaki gane yana son ki ko baya son ki" na gyada mata kai a hankali. Ta dafa kafadata tana dan bubbugawa, "ban san irin son da kike mishi ba Nafeesah, amma zan baki shawarar ki dinga Addu'ah. In shi alkhairi ne a gare ki Allah ya baki shi, idan kuma ba alkhairin ki bane Allah ya canza miki da mafi Alkhairi" nace ina yi wallahi Ramlah, tace sai kici gaba dayi. Na gyada kai, "in shaa Allah, nagode sosai. Baki ji dadin da naji ba dana gaya miki wallahi" tace "kar ki damu, what are friends for after all? Naji ance BUK zasu fara registration da lectures dinsu next month, haka ne?" hirar mu ta koma ta makaranta, da yake ita university of Abuja zata koma, mun dan kara mintuna kamar ashirin muna hira kafin muka mike, na mata sallama na wuce gida ita kuma ta wuce hostel.
Ban maidawa Abbu reply dinshi ba, amma tun kafin karfe tara ta cika na samu waje na zauna ina jiran shigowar kiran Abbu. Kamar yadda yace, karfe tara tana cika kiran shi ya shigo wayata. Na daga wayar tare da mishi sallama ya amsa, a nutse na gaida shi nan ma ya amsa tare da tambayar karatuna, ya dan ja ni da hira kadan kafin ya dulmiya cikin maganar data saka shi kira na. "Nafeesah ranar nan muna waya na katse sai kuma ban sake kira ba, na kara miki lokaci ne wanda zaki yi tunani a nutse don a tunani na a wancan lokacin baki zauna kinyi tunani bane shi yasa. Ina fata in ji different amsa daga gare ki wannan karon". Nayi shiru ina tunani, wata marubuciyata tace wai 'Opportunity comes once (Dama tana zuwa ne sau daya -Takori)' ni kam yau dai ina so inyi wasa da tawa damar. Masu karatu kar kuga laifina. I am a girl in her twenties, a irin wannan age din babban abinda 'ya Mace take bukata daga kowane namiji shine kalmar so, sai dai ni yana proposing din aurena ne kawai ba tare da nasan ainihin abinda yake cikin ran shi ba. In amince da auren shi ince nayi auren me? I can't risk my happiness akan son zuciya irin nawa. Nayi gyaran murya a nutse nace "kayi hakuri Abbu, ina kan bakana har yanzu" ina dire aya ya tare ni, "why?" nayi shiru, yace "me yasa baki son Aurena ne?" nace "it's obvious, saboda kai baban Hafsy dasu Abdullahi ne, kai Mijin Aunty Mubeenah ne, you are Niimah's brother, Abby you Are My Father's Friend.... How are you expecting me to accept your offer?" yace "just because of that?" na gyada kai kamar yana gani na, "yace but is it a sin? Abubuwan nan da kika lissafo dukan su ba wasu obstacles bane da zasu hana ni auren ki Nafeesah! Just tell me ba kya so na shi yasa ba zaki iya aure na ba" nayi shiru zuciyana tana bugawa, ina zan Iya furta wadannan maganganu? Yace "tell me Nafeesah!" cikin husky voice nashi wanda ya fara gauraya da bacin rai, nan ma shiru kawai nayi, zan iya karya akan komi amma banda karyar kin Abbu, ba zan iya ba. "Goddammit Nafeesah! Me kike son nayi for goodness sake?!" wannan Karon bacin ranshi ya fito baro-baro, ya cigaba "kina bukatar ki ganni akan gwiwa na ina rokon ki akan ki aure ni? Ko kuma so kike yi in dinga binki sahu-sahu kamar yaro ina shelantawa duniya ina son in aure ki sannan zaki yarda?" na danyi chuckling a hankali, that is so childish. Yayi shiru kafin inji ya fara magana wannan karon a hankali kuma very calm, "ok, ok. Maganar su Hafsy da kike yi Nafeesah ina tabbatar miki they will be more than happy idan suka ji cewa zaki auri baban su saboda suna Son ki Nafeesah, sun dauke ki da muhimmanci sosai fiye da tunaninki, haka ma su Ni'imah, Dad dinki kuwa has already given us his Blessings. M just trying to be a nice guy anan kin gane? Bana so ne a miki abinda ba kya so ne kawai shi yasa, Mubeenah kuma wannan ba damuwar ki bace, ba lallai sai da blessings dinta ne zamu yi aure ba, Are we good now?" nace "still Abbu....." ya katse ni, "kina da wanda kike so ne?" nayi shiru ban amsa ba, jin shirun da nayi yasa ya sha jinin jikin shi, "akwai kenan koh?" nan ma nayi shiru, yayi kwafa "just wait till I come back. I will not let you go that easily Nafeesah, Aure a tsakanin mu kamar an daura ne Nafeesah coz you are mine! Saboda ni aka halicce ki ba dan wani ba. Zan baki sauran watanni biyu da suka rage min anan don ki tsara yadda Rayuwar ki a gidana zata kasance. Ina dawowa daurin auren mu ba xai dauki lokaci ba Nafeesah in shaa Allah.... Bari in barki haka, sai da safe" da kyar na iya daga baki nace "A tashi lafiya" kusan a lokaci daya muka katse wayar dashi. Na kai hannuwana duka biyun na tallabo kumatuna dasu, Abbu da gaske yake. Wani bangare na zuciyata yana murna da hakan yayin da wani sashen yake jimami da tantama, tantama akan in amince ko inyi akasin haka? Jimami kuma na ya makomar rayuwata zata kasance idan na amince din???
Daga wannan ranar kusan kullum sai mun yi waya da Abbu, yawancin lokuta zai kira ya tambaye ni karatuna da sauran su, bai sake tada min zancen auren ba, hakan shi yake kara jefa zuciyata cikin wasi-wasi. I mean yadda nake ji ana fada ko kuwa dai mostly yadda ake yi a cikin film, a situation irin haka zaku ga Namiji ya shiririce a gefen mace going to the moon and black, proposing ta hanyoyi daban-daban, amma shi Abbu babu alamun haka a tattare dashi. Idan text ya turo min babu kalmar so ko daya da nake tsinta a ciki haka ma idan muka yi waya dashi, amma kulawa kam ina shan ta, kullum cikin tambayar lafiyata da Al'amuran rayuwata yake. Hakan shi yake kara jefa ni cikin tunani., Abbu Wane irin mutum ne shi kam??
#TeamAbbu
*♡Jeedderh♡*
[14:42, 12/18/2017] +233 50 348 1936: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*
*©°•Jeedderh Lawals•°*
*37*
High waist blue jeans, shabby coffee color T-shirt, black veil rolled, black and white kimono, jakar poshter rataye a kafada, one last look a jikin mirror na tabbatar dana fita yadda nake so. Yau ne ranar da zan zana exam dina na karshe a Kasu, probably rana ta karshe da zan taka kafana zuwa cikin makarantar idan ba da wani dalili ba dai. Na saka sneakers a kafada baki tare da daukar wayar hannuna na fita, karfe tara lokacin dana fita bakin titi, kafin in isa Kasu tara da rabi tayi already don haka exam hall dinmu kawai na wuce. Kyawawan awanni biyu suka wuce kafin mu fito, daga nan bankwana muka yi da abokanan nan mu muka wuce gida, Ramlah tun a ranar ta wuce Kano zata je ta fara shirin wucewa Abuja. Nima nasan lokacin da nake dashi a Kaduna ba mai yawa bane kafin in wuce Kano saboda BUK tuni sun fara lectures dinsu tun kimanin satika biyu da suka wuce. Na koma gida na samu tarba ta musamman a wajen Iyayena, wata kwaryar liyafa suka hada min inda en uwa suka taru wajen taya ni murnar kammala karatuna, I didn't expect it but I was happy and touched. Soyayyar da Iyayena suke min abu ne mai matukar wahala in iya fayyacewa masu karatu irinta. Kwana biyu ina gida bana fita ko nan da can ina aikin barci da relieving din stress din exams. Bayan na huta completely na fara shirye-shiryen wucewa BUK tare da iyayena. Ranar Lahadi da misalin karfe hudu na yamma, tafe muke a kan titin daya dauki hanyar fita Kaduna zuwa Kano a cikin motar Daddy Hillux, tare da Mommy, Anty Uwani da Sultan. Duk wasu abubuwa da zan bukata suna bayan motar da muke ciki, komi game da karatuna ya riga ya hattama a waje guda, abinda ya rage kawai shine shiga dakin daukar lacca a gobe litinin. Anty Uwani da Mommy bakinsu yaki rufewa wajen bani lecture Akan zamantakewar cikin makaranta, rayuwa ce da zan hadu da mutanen da ban sani ba kuma inyi rayuwa dasu, nasihohi da shawarwari dai. Mun shiga cikin BUK da misalin karfe biyar da rabi. Mommy da Anty Uwani suka taya ni shirya dakin da aka kaini, mun samu occupant daya a dakin luckily musulma ce kuma bahaushiya da alamun kuma zata yi kirki. Su Mommy suka taya ni gyara kayana da hattama su waje guda. Sai bayan sallar Magriba sannan suka juya, ni da Firdausi roommate dina muka musu rakiya har parking lot. A gabanmu Daddy yaja motar suka tafi muna daga musu kallo, ina kallon su har Motar ta bace mana daga gani. Iyayena suka tafi suka barni a bakon gari, bakon waje, again, for the second time. Na kai yatsa na dauke siririyar kwallar data tarar min a ido, wannan yana daya daga cikin challenges da 'ya mace take fuskanta a rayuwarta, wannan temporary ne ma fa, zan iya zuwa in gansu a duk lokacin dana ga dama kuma na bushi iska, to ina ga nayi aure kuma? Muka juya muka koma cikin hostel Firdausi na min dariyar kukan da nake. Sallah muka yi naci abinci na jira aka kira isha'i nayi kafin nayi shirin kwanciya barci na kwanta. Sai dana janyo wayata kafin naga alamun shigowar sako, ban san yaushe ya shiga ba amma ina tunanin lokacin da nake sallah ne. Zuciyata ta shiga bugu da tsallen murna lokacin dana ga sakon daga Abbu yake, yaushe rabon da inji muryar shi? Tunda muka fara exams ya daina kirana sai dai yana turo min text akai-akai. Yau ma kamar koda yaushe ko ince ko wane lokaci, ya nake? Ya su Daddy na? Ya kara da min lale maraba da zuwa makarantar BUK sai abu d'aya daya kara, cewa yayi; "Kar in saba da zaman hostel dinsu da wuri, saboda soon.... Very soon zan bar hostel din, saboda yana dawowa zai dauke ni daga hostel din" na turo baki kamar yana ganina, "wai ya daukeni kamar wata er tsana" sai kuma na kwashe da dariya ina birgima akan gadona, Abbu bai san cewa nima jiran dawowar tashi nake yi ba ne kome? He kept bragging about it, koda yaushe cikin zancen in jira dawowar shi yake making me go curious akan me zai faru idan ya dawo din. Ina lissafe da kwanan wata, ya daura akan wata hudu din da yace zai yi. Mommy ta kira ni muka gaisa tare da tambayata yanayin wajen nace mata lafiya, bamu yi wani hira ba saboda yadda nake jera hamma tace inje in kwanta kawai, nan muka yi sallama tare da kashe wayar. Addu'ar kwanciya barci nayi tare da lumshe idona, a tunani na barci zai kwashe ni a take saboda yadda nake a gajiye amma ina! Rayuwata a gidan Abbu, iyalinshi dashi kanshi, tun daga ranar dana fara ganin su har zuwa yau ta fara min yawo a idanu, nayi juyi akan gadona a karo na barkatai ina tambayar kaina tambayoyin dana kasa samun amsar su suma a karo na barkatai, will it be okay? Zan iya kuwa?
*NI DA ABOKIN BABA NA....!*
*©°•Jeedderh Lawals•°*
*Wannan shafi na Sadaukar dashi ga Marubuciya SADNAF da MAKAWA, I really appreciate you guys with your cheerful and concern, thanks. Sauran Marubuta ina gaishe ku sosai tare da duk wani Makamancin littafin Ni Da Abokin Babana!*
*39*
Muna fitowa daga lectures masallaci na shiga nayi sallar La'asar daga nan na wuce flower Garden. Anty Ameenah tana zaune a daya daga cikin kujerun da aka tanada, tana hangoni ta fara waving dina tana murmushi, nima murmushin nayi na karasa gareta, kujera naja na zauna ina fuskantar ta, na gaisheta ta amsa tana tambayata abinda nake so a kawo min nace a bani egg roll da lemu don tun safe da zan fita dana sha shayi ban kara komi a cikin cikina ba, aka kawo mana egg roll, meat pie burger da lemun peach. Anty ta kalleni tace "Allah yasa ban takura miki ba da nace ina son ganin ki?" nayi saurin girgiza mata kai, "haba ko kadan wallahi" tayi murmushi tare da gyara zamanta akan kujera, "da farko ban yi niyar sa baki ba akan maganar wannan sai dai ina ga lokaci yayi daya kamata in saka baki, ba shisshigi nake miki ba amma ina so inji inda maganar ku ta kwana?" na dubeta cikin mamaki, "Anty wace magana kenan?" tace "maganar ku da Ibrahim mana!" sai dana kusa zubdo da abinda nasa a bakina saboda maganar da naji cikin bazata. Ta miko min tissue na goge bakina tare da korawa da ruwa, Anty Ameenah tace "m sorry idan baki so hakan ba" kai kawai na girgiza mata, amma a kasan raina ina mitar me yasa don kawai Abbu yana son aurena sai kowa a cikin dangin sa ya sani? Kamar wadda take karanta mind dina, tace "kada fa kiyi zaton Ibrahim ne ya gaya min ko ya turo ni, bashi bane. Kwanakin baya dai ya taba neman shawarata akan cewa yana so ya aure ki, me nake gani? Naji dadin hakan sosai, wallahi abu ne wanda ya jima yana min amsa kuwwa a cikin kaina, tun ranar farko dana fara ganin ki Nafeesah na yiwa Ibrahim sha'awar kasancewar ki matar shi, sai dai sanin halin Ibrahim yasa na kame bakina nayi shiru. Ba tun yau ba nake mishi maganar kara aure amma sai ya wawantar da maganar, ba ni Kadai ba Hajiyar mu ma tayi nata kokarin ganin irin zaman da yake yi da matar shi but to no avail. Amma jin da kanshi yazo yana ce min yana sha'awar kara aure nasan cewa da gaske yake, Ibrahim baya nuna bukata akan abinda yasan baya so, musamman akan zancen nan Nafeesah, I've seen something different in him. To kuma tun daga lokacin har yanzu ban sake jin yayi magana game da hakan ba, last time dana mishi maganar ma sai ya sake wawantar da ita, ni kuma gaskiya na kasa mantawa da zancen shi yasa nace bari in tuntube ki da kaina inji" nayi shiru tare da sadda kaina kasa, ince me? Tunda ni a karan kaina ban san ya muke ciki ba. Anty Ameenah ta kamo hannuna ta rike cikin nata, "look Nafeesah! I am not trying to persuade you or something else.... I just.... I mean ina cikin eagerness nason ganin rayuwar kanina tayi haske, ya samu farin ciki da kwanciyar hankali a cikin rayuwar auren shi. It has been good thirteen years tun auren shi da Mubeenah, aure ne aka musu na zumunci, ita diyar wani abokin Alhajin mu ne. Tun daga auren su Ibrahim ya rasa farin cikin shi, he was young, amma bai dandani abinda matasa kamar shi suke dandana idan suka yi aure ba. Ya rasa jin dadin yarintar shi a wajen yarinyar da bata san darajar shi ba saboda kawai bata son shi. A matsayin Ibrahim na namiji ya hakura da auren dole din da aka mishi amma ita ta kasa hakura, a wajen Mubeenah ne kadai na karyata maganar bahaushe da yace duk kiyayyar da mace take wa namiji da sun fara haihuwa take dawowa so, a gareta kam sai kiyayyar ta koma har kan 'ya'yan shi. You wouldn't believe me Nafeesah, lokacin da ta samu cikin Abdullahi da kyar ta iya haifeshi, Allah ne kawai ya nufa zai zo duniya amma sai da tayi attempting din zubar da cikin sau biyu, haka aka zo aka sha dabi da cikin Qaseem, daga haihuwar Hafsat taje aka saka mata loop a cikinta ba tare da sani ko yardar Ibrahim ba. Bata dauke mu a tsiyar komi ba, sai mu hadu da Mubeenah a hanya idan ba dama ta gani ba ba zata mana magana ba, idan mu mun mata sai ta ga dama take amsawa. Babu yanda bamu yi da Ibrahim ba akan ya kara aure amma ya ki, yace baya so yaci amanar da marigayi mahaifin Mubeenah din ya bar mishi akan ya kula da ita da farin cikinta, shi a ganin shi cin amana ne idan ya kara aure. Haka Ibrahim ya rayu tsayin shekarun nan, ya danne farin cikin shi saboda matar da bata san yana yi ba, wadda bata appreciating dinshi da dangin sa har ma da 'ya'yan shi. Wallahi baki ji farin cikin da nayi ba lokacin da naji cewa ya shirya fitowa daga cikin ukubar daya sa kanshi a ciki ba, shi yasa kwata kwata naji na kasa yin hakuri in zuba ido ki kubuce masa Nafeesah" jikina gabadaya yayi sanyi, ban taba sanin cewa irin rayuwar da Abbu yayi ba kenan, koma yake kan yi. Anty Mubeenah kam wace irin mace ce? Anya akwai sauran mata irin ta a duniyar mu ta yanzu? Anty Ameenah ta shafa hannuna tace "kinyi shiru?? Baki son shi ne ko kuma ya miki tsufa??" na girgiza kaina ina dan murmushi, "ban taba mafarkin kasancewar wani mutum a matsayin mijina ba sai Abbu Anty" farin cikin dana hanga a cikin idanuwanta abun baya misaltuwa, na sadda kaina kasa cike da kunya ina jin kamar kasa ta tsage in shige. Tace "amma me yake hana ki cika burin ki?" nace "ina jin tsoron abinda zai je yazo ne, my mom seems to be strictly against it. Sannan ban san me zai je yazo ba a rayuwar auren Abbu da Anty ba, bana son abinda zai tarwatsa musu rayuwar auren su da kan iyalinshi" Anty tace "believe me Nafeesah! You are not. Allah kadai yasan iya ceton ran da zaki yi, wallahi babu abinda zai faru a rayuwar gidan Ibrahim sai ma farinciki dana san zai wanzu in shaa Allah, ke kadai ce wanda zaki iya yin wannan aikin saboda na tabbata Ibrahim yana son ki. This the first time in my life da naga Ibrahim wanting something very badly kamar ki, na tabbata idan ya rasa ki sauran rayuwar shi will be shattered to pieces. Naji dadin wannan lamarin sosai, ina tabbatar miki da cewa you are the perfect match for Ibrahim. You suits each other, na tabbatar da zai kula dake, zai so ki. Kada kiyi zaton saboda shi kanina ne wai nake koda shi, ba haka bane. Saboda na yarda da Ibrahim na kuma yarda da halayen shi. Ki kwantar da hankalinki In shaa Allah babu abinda zai faru sai Alheri, in shaa Allah ba zaki taba yin nadamar Auren Ibrahim ba kamar yadda na tabbata zaki kasance a cikin farin ciki matukar kina amsa sunan Matar shi. So dear, stop holding yourself in and just go for it, kiyi abinda kike son yi kafin lokaci ya kure miki, Allah ya Albarkaci rayuwar ki" na sadda kaina kasa ina jin wani irin confidence da kwarin gwiwa yana shiga ta. In shaa Allah ba zan kara rike kaina ga yin abinda nake son yi ba, da yardar Allah zan zama mallakin Abbu tun kafin ya subuce daga hannuna ya sa in tagayyara. Anty Ameenah ta kara bani shawarwari kafin muka mike muka fita daga cikin garden din, har inda tayi parking din motar ta na raka ta. Ta bude motar ta shiga, ta mika hannunta baya ta dauko Leda mai dauke da tambarin kamfanin shop rite Ta miko min, naso nokewa in ki karba amma ya kamo hannuna ta dora min ledar a tafin hannu dole na karba tare da mata godiya, tace "babu komi Ameenah, and please make sure to make it very fast" na sunne kaina a kasa ita kuma ta tashi motar ta tafi.
Tarkacen kayan makulashe ne ta kawo min, dambun nama, cookies da tarkacen biscuits sai turare masu kamshi a cikin ledar. Na bude biscuit din short bread na kai bakina na cinye tare da korawa da lemu, kwana biyun nan abubuwan dana mayar abincin cina kenan. Bayan nayi sallahr Isha'i na gama shirin kwanciya, na kwanta akan gadona tare da janyo pillow na rungume a kirji na, Maganganun Anty Ameenah suka fara dawo min a cikin kaina. Na tsinci kaina cikin mutuwar jiki tare da jina ina narkewa akan katifar da nake kwance. Allah sarki Abbu! Ban taba zaton cewa rayuwar auren shi munin ta yayi yawa har haka ba, na kara juyawa a akan gadon. Poor Abbu! Da yardar Allah sai na zama dalilin sharewar hawayen shi da yayi ta zubarwa a shekarun baya, in Allah ya yarda sai na zama haske da fitila a cikin rayuwar Auren shi. Da haka na lumshe idanuna barci ya dauke ni, idanuwa brown masu sheki da kyalli suna gagari a cikin duhu.
*******
Da kuzari sosai na tashi a cikin jikina ranar, tunda nayi sallahr Asubahi ban koma barci ba saboda ina da laccar safe, nayi wanka na shirya abin karyawa kafin na shirya jikina cikin riga da siket na leshi ruwan ganye dinkin yayi min cif a jikina, shi bai yi yawa ba kuma bai yi kadan ba. Ina cikin karyawa dinne na kira gida muka gaisa dasu, anan ne Daddy yake fada min cewa result dinmu na KadPoly ya fita kuma yayi kyau sosai, nayi hamdala tare da godewa Allah. Yace ya riga daya turawa Abbu da result din don a kammala shigar da takarduna a cikin BUK tunda dama awaiting result ne, nace mishi babu damuwa, daga nan ya ba Mommy muka gaisa da ita har take fada min ansa auren Hansa'u diyar Kawun su Daddy nan da watanni hudu, na musu fatan alkhairi sannan muka yi sallama da ita. A gurguje na karya naja gyale yellow mai yalwar fadi da flat din takalmi shima yellow sai jakar littafai da wayar hannuna na tafi. Kimanin mintuna arba'in muna jiran zuwan Mrs Adayi matar da take daukar mu Intro. Physiology amma shiru bata zo ba har karfe tara tayi laccar daya kamata ace tun karfe takwas aka fara ta. Na kalli agogon hannuna tare da dan jan tsaki, bana son abinda zai bata min lokaci duk da cewa bani da wani class din sai two, amma ina son ganin Abbu kafin ya tafi gida wanda nasan cewa muddin ta shigo sai ta cinye lokacin data batar a waje. Wajen karfe tara da rabi class rep yayi announcing din isowar lecturer din, nan da nan ajin yayi shiru daga hayaniyar daya dauka. Kofar hall din ta bude aka shigo, cikin takun nan nashi mai cike da kasaita da natsuwa ya taka har zuwa gaban allo. Ina jin irin sautin woah! Daya dinga fita daga bakin mates dina mata da kuma kus-kus din da suke yi sai dai hankali na baya kansu, yana gaban allo ina kallon halittar dake tsaye, sanye cikin suits navy blue da farar shirt sai navy blue din neck tie kafar shi sanye da bakin cover shoe, fuskar shi mai cike da kwarjini da ilhama tana ta shinning a cikin hasken ranar daya shigo, nasan dole dama enmatan ajinmu su rikice da ganinshi a yadda yayi kyawun nan, looking soo take away. Daga sama na dinga jin muryar shi lokacin da yayi introducing kanshi as Doctor Ibrahim Galadanchi, zan koya mana course din a madadin Mrs Adayi wadda ta samu accident din mota a daren jiya, zai daukeni course dinne har zuwa lokacin da zata warke. Ya lalubo idanuna ya rike da nashi idanun na en sakanni kafin ya janye idanunshi zuwa ga sauran dalibai yana wani smirking, "alright, can we start now?" gabadaya ajin ya dauki sowar "yes" Ya Allah! Ni kam na kasa tantance a wata duniya nake, har ya gama gabatar da darasin ranar cikin kwarewa da tataccen turancin nan nashi babu abinda na iya tsinta sai idanunshi dake karakaina a jikina suna kara hana ni natsuwa, A Father's Friend! A Lecturer! Way to go Nafeesah!! Ta yaya zan iya dealing da responsibilities dinnan?? Ya rufe littafin hannunshi tare da maida marker dinshi cikin cover dinta yana kallon en ajin, "let's call it a day here" kowa ya fara maida littafin shi cikin jaka, ba bata lokaci ya dauki brief case dinshi ya tunkari kofa bayan ya haske ni da wani irin kallo wanda yasa naji gabban jikina sun koma kamar ruwa, Abbu will really be the death of me!! Dalibai suka fara fita daga cikin class din amma ni ina zaune kikam kamar gunki, sai da Jalila wadda muka zauna seat daya da ita ta dan daddabe ni sannan na dawo cikin natsuwata, tace "Nafeesah lafiya? Tun dazu na kula kamar baki cikin natsuwar ki" na girgiza mata kai, "lafiya ta lau, kawai na dan gaji ne" tace muje koh? Na jinjina kai tare da mikewa tsaye, ina tashi karan shigowar message a wayata ya tsaida ni; Abbu ne. Cikin rawar hannu na daga, "meet me at room 13, Dept of Physiology, lecturers lounge" abinda yace kenan, na kalli Jalila ina dan murmushi nace "sorry, ku tafi kawai, akwai inda zan biya yanzu" tace ok, tare da wucewa. Ni kuma na tafi zuwa kiran Abbu. Ofishin shi shine na karshe cikin jerin offices din lecturers din dake wajen, na tsaya a bakin kofar ina kara kallon name tag dinshi dake rataye a jikin kofar an rubuta 'Dr. Ibrahim Mas'ud Galadanchi' na shafi sunan da hannuna tare da lumshe idanuna ina dan murmushi, Abbu! What have you done to my innocent soul?? A hankali nayi knocking a bakin kofar, cikin husky voice dinshi yace "yes come in please" na tura kofar a hankali na shiga, kafafuna suka nutse a cikin wani tattausan zagayayyen carpet an rubuta welcome a jiki, tattausan kamshin air freshener da sanyin split suka doke ni har sai dana saki ajiyar zuciya saboda sanyin dadin daya ratsa ni. Yana zaune a gaban desk top yana aikin typing, ya cire suit din jikin shi sai shirt din kawai ya bari, you have no idea irin kyawun da yayi mun a lokacin. Ofishin nashi babba ne, shelves shelves ne na littafai tun daga na bokon har na Arabi a kowace kusurwa ta Ofishin, sai desk da dai duk wasu tarkace da zaka samu a cikin Ofishin manyan laccarori da boko ta gama ratsa su. Ya dago kyawawan idanunshi daga kan desk top din da yake aiki a kai ya kalleni, murmushi ya saki mai sanyi wanda ban san lokacin dana mayar mishi da martani ba. Ya nuna min kujera alamun in zauna, ba musu naje na dan dosana kamar wadda za ace mata ar! Ta karta a sukwane. Na nutse nake bin Ofishin nashi da kallo, baby wasu tarkace da zasu saka mutum ciwon kai, komi a shirye kuma cikin tsari. A hankali ya daga baki yace "plss make me a cup of tea" na daga kai na kalleshi a hankali, ya wani langwabar da kai gefe kamar wani karamin yaro saura kiris in kwashe mishi da dariya. Na ajiye jakar hannuna akan kujerar na mike na kunna electric kettle dana gani a jikin socket, ya nuna min inda cups da sauran kayan shayin suke ruwa yana tafasa na hada mishi na kai na ajiye mishi, ya kalleni "thanks.... Ke fa?" na girgiza mishi kai. Aikin shi ya komawa yana yi yana dan sipping din shayin nima na koma na zauna. Ban jima ba naji ya kashe computer din, karan matsawar kujera alamun ya tashi daga inda yake, ya zauna akan kujerar shi wadda take fuskantana. Shayin shi yaci gaba da kurba idanuwan shi suna kaina, kaina yana kasa ina wasa da yatsun hannuna, ji nake kamar wanda rami zai bule daga cikin fatar fuskana saboda zazzafan kallon Abbu a kaina. Ya ajiye cup din akan teburi tare da dan matsowa daga kan kujerar da yake, yace "toh Nafeesah, yau dai ina so inji abinda kika yanke game damu, ya ake ciki? Na fada miki na gaji da jiran ki haka nan, na gaji da yawo da hankalin da kike min. This is the last time da zan tambaye ki, bayan shi ba zan kara ba Nafeesah I promise you don ni dai ba karamin yaro bane, so m asking you, me kike yanke game damu??" Zuciyata was beating very fast and erratically kamar wadda tayi gudun marathon, kaina, yatsa, gangar jikina da komi ma na jikina sun yi mun wani irin nauyi marar misaltuwa amma duk da hakan ban fasa daga kaina na nake jin ya koma kamar wani gingimemen dutse ba na kalleshi, fuskar shi was mixed of emotions, fargaba, hope, plead, idanunshi da suke matukar burge ni sun shige ciki, nasan da ace idanu suna magana dasu ne zasu yi rokon da nake gani akan fuskarshi tunda bakin shi ya gaza furtawa. A lokacin na gama yin concluding cewa farin cikina koma ince namu a yadda na karanci fuskar Abbu a lokacin, yana tattare damu ne, yayin da makullin kofar take hannuna, that means ni kadai ce zan iya bamu farin cikin da muke bukata kenan??
A hankali na sadda idanuna kasa, na tattaro duk kwarin gwiwa na tare da gyada kaina a hankali.....
#TeamAbbu
#OneLove
#AnaTare *Ni Da Abokin Babana!* Fans
*♡Jeedderh♡*
*NI DA ABOKIN BABA NA....!*
*©°•Jeedderh Lawals•°*
*40*
Na kasa tantance abinda ke zane akan fuskar Abbu a lokacin, murmushi yake yi sosai, amma zan iya rantsewa akan cewa na hango alamun moistness a cikin idanunshi, ban san me zai faru ba nan gaba, ban san ya zamu kare da Mommy ba sai dai irin farincikin dana gani a tattare da Abbu yasa naji duk wata fargabata ta barni, idan dai har zan dinga ganin irin wannan kallo daga Abbu to ban damu da duk abinda zai faru ba, nasan cewa murmushin Abbu ya ishe ni. Ya dauki mintuna da dama bai yi magana ba ina jin yana containing farin cikin dake cin shi ne, yayi gyaran murya yace "nagode sosai Nafeesah, amincewar ki da yardar ki a gare ni sun dadada min sosai you have no idea, in shaa Allah na miki alkawarin ba zaki yi nadamar aurena ba, Mrs. Ibrahim Galadanchi!" na kai hannuna biyu na rufe fuskata dasu ina dan murmushi yayin da naji Abbu yana er dariya, yace "why? Baki son sunan ne ko me?" naki bude fuskata balle in kalleshi, yace "idan baki son sunan it's okay, but bude mun fuskar ki plss" na kara kankame fuskar tawa, ina zan iya fuskanta Abbu a yanzu? Ina jin lokacin daya tashi daga inda yake ya dawo gefena ya zauna kamshin turaren shi ya cika min hanci, yace "zaki bude da kanki ne ko sai na janye da kaina?" a hankali na janye hannuwan nawa sai dai fuskana tana kasa, a yadda nake jina a lokacin nasan ba zan taba iya hada ido dashi ba. Ya rankwafo da kanshi saitin fuskata, da sauri na daga kaina na kalleshi cikin sa'a muka hada idanu dashi, wayyo Allah! Kasa tsaye in shige. Ban taba ganin Kwarjinin da yayi mun a lokacin a tattare dashi ba, wani irin magnet naji ya fara fuzgata yana kokarin hada ni dashi, da sauri na mike tsaye ina lalubar jakata tun kafin in kai ga yin abinda zan zo ina dana sani gwara in bar office din. Abbu ya bini da ido yana frowning, na tsaya a gaban shi ina rataye jakata a kafada kaina a kasa, nace "umh.... Zan tafi... In... na da class anjima" ya kalli agogon hannunshi tare da dan jan siririn tsaki, "so nayi mu tattauna game da yadda zamu tsara rayuwar auren mu dake fa, amma ba komi there's always a second time. Amma zan sanar da Daddynki dai" na kalleshi da sauri ina zaro idanu, "tun yanzu?" yayi scrunching din brows dinshi, "tun yanzu? Me kike nufi?" nayi kasa da kaina "na ga kamar yayi kusa ne" ya girgiza kanshi "bai yi kusa ba Nafeesah, na gaya miki na kagauta ki zama mallakin, ni da so samu ne ma sai ince satin sama a daura mana aure in killace ki a gidana, Ya Allah! Na tabbata burina ya gama cika, I wouldn't ask for anything sai dawwama dake a gidan Aljannar Firdaus" sai kawai na daga kafa na fara tafiya, Anya Abbu ne? Ban san me ya shiga kan shi da kwalwar shi ba a Kwanakin nan sai ya dinga min wasu maganganu da suke saka ni cikin ramin matsananciyar kunyar shi. Ya mike tsaye, "tunda baki son yin hira dani bari in maida ki hostel to" na fita na tsaya a bakin kofar Ofishin ina jiran shi, ya fito daga ciki ya rufe office din yayi gaba na bishi a baya har inda yayi parking din motar shi. Muka shiga yaja motar, a hankali muke tafiya yana ja na da er hira. Duk yadda nake kauce-kauce da kare-karen fuska sai dana dawo ina dariya, kafin mu karasa hostel na sake daga awkwardness din daya dabaibaye ni, a cikin motar ma mun jima muna hira a gaban hostel dinmu har sai da aka fara kiran sallar azuhur sannan muka yi sallama. Na bude murfin motar ina ce mishi ya gaida su Hafsy, yace "me zaki ce musu bayan tunda kika zo baki ziyarce su ba? Fushi ma take yi dake don ki sani... Koda yake ai na kusa ciccibar ki in kai mata ke cikin gidan gabadaya, ki fara haifo mata kanne nasan zata yi farin ciki sosai, zan gaya mata ta daina fushi dake haka nan" ni dai na ida sa kafata waje na fita ina dan murmushi, da gaske Abbu ya canza daga cool and calm Abbun dana sani zuwa Romantic, wanda yake fadar duk maganganun da suka zo bakin shi ba tare da yayi la'akari da cewa sun girmi kunnuwana ba. Ya dan leko da kanshi ta cikin motar, "baki ce komi ba fa" na dan juyo na kalleshi tare da haske shi da murmushi na juya na shige cikin hostel, ina jin hot gaze dinshi a kaina har na yi nisa a cikin hostel din, na tura kofar dakin na shiga. Firdausi na zaune akan kujera da littafi a hannunta tana karatu, ta dago tana min sannu da zuwa na amsa, kallona ta cigaba dayi kamar wadda taga wani bakon abu a jikina, na rataye jakar hannuna a jikin hanga na kalleta, "wannan kallon naki lafiya dai koh?" tayi murmushi tace "you are blushing! Did someone propose to you??" na kalli kaina a cikin madubi, I couldn't help the chuckling daya fito min, na kalleta ina murmushi "Ina ga dan zafi zafin da ake yi ne kawai" ta kalleni tana murmushi tare da gyada kai ta maida Idanunta ga littafin hannunta. Nima nayi murmushin na fita naje nayi alwala na dawo nayi sallah, kafin in gama Firdausi ta dafa mana indomie ina gamawa muka ci na sake fita wajen lecture.
A daren ranar sai ga wayar Daddy ta shigo, na daga wayar cikin sanyin jiki da faduwar gaba. Ina gaida shi ya amsa ya dora da fadin, "Ibrahim ya kira ni yanzu yana fada min wani labari" na sadda kaina kasa kamar ina gaban shi, "kayi hakuri Daddy" ya danyi murmushi, "meye kike bani hakuri dear? I just call to know that you are okay with it. Are you sure zaki iya?" na gyada kaina amma ban yi magana ba, yace "naji dadin zabin da kika yanke sosai Uwata, naji dadin cewa mutumin da kika zaba ya zama abokin rayuwar ki Ibrahim ne, naji dadin cewa zan barki a hannu na gari kuma na kwarai, nasan ba zan taba yin fargaba game da yadda kike ba saboda na yarda da Ibrahim. Allah ya miki albarka Nafeesah" naji hawaye suna kokarin cika min ido, da ace ina kusa dashi da sai na rungume shi, nace "I love you Daddy, nagode" yace "You are all we have Uwata, dole mu so farincikin ki, ina Alfahari dake" nace "nima haka Daddy.... Amma Mommy fa?" yayi kasa da murya nasan sirri yake nufi, "Mommy dinnan taki fa sai a hankali, tun dazu take hawa tana kumbura kamar fulawa daga mata maganar wae ai ita bata yarda ba cin amana zata yi, shine nace mata idan haka ne itama za a turo mata yarinya kamar ki idan tayi watanni sai in aureta, don Allah ba anyi 1-1 ba?? Sai kawai ta hau kumbure-kumbure, yau ko magana bata min ba dana dawo daga aiki" duk da banji dadin abun ba sai dana yi er dariya nace kai Daddy! Yace "it will be better idan baki kira ta ba for two days, zan yi kokari in ga cewa na ganar da ita abinda take fahimta" nace toh Daddy. Yace good girl, kije kiyi alwala ki kwanta, nasan kina da darasi da safe nace "exactly Dad, goodnight" muka yi sallama na ajiye wayata jikina a sanyaye. Na jima a zaune ina tunanin yadda zan yi idan Mommy taki bamu albarkarta game da auren nan, ni dai nasan cewa ba zan iya auren Abbu ba tare da yardar Iyayena ba gaskiya. Na tashi naje na dauro alwala nayi shirin kwanciya barci. Dana daga wayata naga message din da Abbu ya turo min mintuna biyar da suka wuce, cewa yayi; "A lokacin da kowa yake neman makwanci da niyar warware gajiyar data addabe shi, a daidai lokacin bawan Allah Ibrahim yake karawa kan shi wani tarin gajiyar, why? Saboda bashi da makwanci kwanciya balle filon tada kai. Ina fata wadda take karanta sakon nan zata yi gaggawar kasancewa tashi ko zai samu sanyin rai dana zuciya a tare dashi. Sai da safe, lots of love and kisses" n zan iya rantsewa naji saukar lebba a kumatuna, na kai hannu na dafe wajen ina duba gefe na, dariya na saki tare da dan dukan goshi na, silly me! I am even expecting him to kiss me, woah!! 'Goodnight' kawai na tura mishi as a reply na kwanta tare da lumshe idanuna. Barci mai dadi cike da kyawawan mafarkai ya daukeni ni.
~So how are you doing outta there Abbu and Nafee's fan??
#TeamAbbu
#OneLove
*♡Jeedderh♡*
*NI DA ABOKIN BABA NA....!*
*©°•Jeedderh Lawals•°*
*♡41♡*
Kwana biyu kuwa ban yarda na latsa sunan Mom a wayana da sunan kira ba sanin halinta na sauka daga fushi da kanta idan ta hau don sau tari idan tana fushi bata cika son ana bin kanta ana bata hakuri ba ma, she prefers a kyaleta har sai ta sauka don kanta, don haka ban tarki kiranta ba sai dai na tura mata text message which of course bata yi replying ba.
Ina fitowa daga class na koma daki, su Ni'ima suka kira ni suka ce suna dakina. Ina shiga suka tare ni da shewa ni har suka sa gabana ya fadi ina tunanin ko zancen mu da Abbu ya kai kunnensu ne, sai da muka gaisa har muka fara hira naga basu yi maganar ba sannan na dan saki jikina. Na kunna stove ina kallonsu, "me zan dora muku?" Ni'ima tace Indomie noodles, Sadiya kuma tace Spaghetti, na kallesu "guys, idan zaku daidaita akan abu daya ku daidaita don kun san bani da lokacin yin girki biyu" suka kwashe da dariya, Sadiya tace "dora mana noodles, wannan maman Babyn ba zata barmu mu shaki iska mai dadi ba idan ba a dafa noodles dinnan ba" nace "kema ai Maman Babyn ce" ta wani zare ido, wa?? Muka kwashe mata da dariya ni da Ni'ima. Nan da nan na dora Indomie na ta dahu na juye mana a tray muka fara ci. Muna cikin ci kiran Abbu ya shigo wayata, na kalli wayar tare da kallon su Ni'ima dake kallona suma, na ci mur tare da janye wayar na kife ta akan gado, suka yi sharing glancing a tsakaninsu. Sadiya ce tace "wai ni me ke tsakanin mutanen nan biyu ne? I've started putting a big question mark a tsakanin su" Ni'imah tace "kamar kin shiga zuciyata wallahi... Ni kaina na kasa fahimta" na kara hade fuska ina cusa indomie bakina ba tare da nayi magana ba, sam bana so maganar mu da Abbu ta fita ta shiga cikin dangin sa don tsakanina da Allah ban san da wani ido zan kallesu ba, ban shirya ba. Ni'imah tace "idan tayi wari dai mun ji" ni dai na kyale su ban tankasu ba. Muka gama na wanke kwanuka na kai mana soft drinks muka sha, daga nan na koma class bayan nayi sallah na bar su a dakin, dana dawo ban same su ba sun bar mun sako dai kan cewa sun tafi. Da dare Abbu ya sake kirana, na daga wayar da sallamata ya amsa ya dora da cewa "me bawan Allah yayi aka ki daga kiran shi dazu" nace "bana kusa da wayar ne Abbu.... Ina yini?" ya amsa, anan yake fada min wae washegari zai tafi Ilorin zai yi sati daya a can. Yace "me zai hana idan na dawo kawai a daura mana aure Nafeesah?" nace "Abbu baka tunanin it's too sudden?" yayi sighing, "Nafeesah, y do u always keep saying yayi sudden? Kina tunanin haka zan ci gaba da kallonki Ina kauda kai har zuwa yaushe? Har ki gama makaranta ko me?" nayi kasa da murya nace "at least in dan yi nisa a karatu na mana!" yace "really? Kin san? Ko session dinnan ba zan bari ya kare ba ba tare dana aure ki ba Nafeesah, idan kuma ba so kike yi in..... God! Nafeesah wae me kike nufi da rayuwata ne??" muryar shi ta dan fara yin sama alamun ranshi ya fara baci, nayi shiru ban bashi amsa ba. Lokacin dana gama yanke shawarar yarda da Abba, kamuwa da son shi da amincewa akan cewa zan aure shi, ban yi tunanin zancen aure ba, ban yi tunanin cewa zai taso zancen aure nan kusa ba, ban yi tunanin zai so ya aure ni ina cikin karatu na ba, nayi tunanin zai bar ni in karasa karatuna ko kuma at the very least ya bari sai na kusa kammala karatuna sai kuma gashi yana zancen aure in the next two weeks when I'm not even ready for it, hell ban ma san meye ma'anar auren ba, me zan yi kenan?? Ga zancen mu da Mommy ga.... Ya katse ni ta hanyar cewa "just forget about it Nafeesah, bana son tursasaki yin abinda baki yi niyar yi ba. Na hakura da zancen auren, idan muka ci gaba da zama a haka ma ya ishe ni, I want your happiness" naji kwallah ta tsattsafo min a idanu, nace "Abbu kayi hakuri" yace "don't mind Amour, na fahimce ki" nayi murmushi mai sauti wanda na tabbata ya jiyo sautin shi, ya maido min da martanin wani wanda yasa naji gwiwoyin kafana sun yi wani sanyi, yace "Pretty na tana ta cigiyar ki, yaushe zaki zo ki ganta?" na zaro ido kamar yana gabana, har sai da naji gabana ya fadi nace "ni?? A'ah gaskiya" ya danyi er dariya, "tsoron me kike ji ne? Na manta ma dazu in fada musu you are now my wife to be" nayi saurin cewa "pls Abbu no! Don Allah ba yanzu ba!" yace y? Na dan turo baki, "ni dai don Allah a'ah" yace "naki, sai na fada musu" na kula tsokana ta kawai yake yi don haka na kyale shi yayi ya gaji sannan muka danyi hira kafin muka yi sallama na mishi Allah ya kiyaye hanya muka ajiye wayar. Abin mamaki sai ga kiran Mommy ya shigo wayana, nayi tsuru Ina kallon wayar kamar ba zan daga ba, Ina tsoron abinda zai faru idan na daga kiran. Sai daya kusa tsinkewa sannan na daga, a hankali kamar mai tsoronta nayi sallama tare da gaida ta, cikin usual tone dinta ta amsa yadda take min, ta tambayeni karatu da sauran abubuwa duk na amsa mata da lafiya lau, tace "naji abinda kika yi Nafeesah, kina ganin daidai ne hakan?" nace "Mommy kiyi hakuri don Allah" tayi shiru kafin tayi ajiyar numfashi, "to tell you the truth naji haushin Abin daga farko, daga baya sai naga cewa abinda kike so kenan and I don't have the right da zan hana ki yin auren da kike so ba Ummiey. I really hope decision din da kika yanke shine daidai kuma zai kawo miki farinciki mai dorewa a cikin rayuwar auren ki" naji zuciyata tayi wani irin sanyi, na saki sansanyar ajiyar zuciya Ina jan hamdala a cikin raina, nace "Mommy nagode sosai" tace "Ni me ma zaki ce mun ne? Kwana biyu baki kira ni ba saboda kina gudun kar in hana ki yin soyayya ko?" nace "mommy ba haka bane" tace "idan haka ne ma ya zanyi? Tunda daddyn ki ya kitsa miki kin hau kai kin zauna, ina jinshi ai yana baki shawarar kar ki kira ni shine ke kuma kika ki kirana" na sake cewa "kiyi hakuri" ina danne dariyar data taso min, ta kuta, "he was even threatening me wai zai iya karo aure, bai san cewa abinda matar shi Ibrahim din zata yi da halin da zata shiga idan taji zancen auren bane nake gujewa ba, yayi zaton son raina ne nake shirin shiga tsakaninki da abinda kike so ba. Ummiey mata da kike gani baki san irin tashin hankali da fargaba da suke shiga idan suka ji zancen kishiya ba balle ita data zauna dake a gida daya ta rike ki cikin amana, dare daya ace zaki aure mata miji kin san ba zata ji dadi ba dai koh?" jikina yayi sanyi na sadda kaina kasa, wannan yana daya daga cikin abinda ya saka ni hesitating at first amma ya zamu yi? Ba zamu danne farinciki cikinmu don faranta ran wadda bata san namu farin cikin ba. Mommy tace "kada ki damu fa, kuma kada ki saka maganar a cikin zuciyar ki babu abinda zai faru da yardar Allah. Amma ya miki zancen aure? Yaushe yace za ayi?" nayi wuri-wuri da ido, tace "baki sani bane? Zan yiwa Daddyn ki magana, ya kamata ace anyi auren nan kawai" nayi saurin cewa, "Mom, ba zaku bari in gama karatu bane?" shiru ya biyo baya kafin tayi magana, "kina da hankali kuwa Ummiey? Shekaru nawa suka rage miki kafin ki gama karatunki, kina tunanin zamu zuba miki ido ko kuma shi Ibrahim din ne yace sai kin gama karatu?" nace A'ah, tace "to ai ko shine Ummiey ba zamu zuba miki ido ba, zan yiwa Daddynki magana a zauna ayi maganar auren ku don gaskiya hankalina ba zai kwanta ba kina karatu a Kano shima wanda ke son naki yana Kano mu muna nan Kaduna bamu san abinda ke faruwa ba a yadda duniyar nan ta baci" nace "Mommy baki yarda dani bane?" tace na yarda dake Ummiey, nasan irin tarbiyar dana baki, but still, hankalina ba zai kwanta ba gaskiya" nayi rolling eyes, "ai shikenan Mom" tace "zan dai tuntubi Daddynki inji, goodnight baby" na mata sai da safe tare da kashe wayar.
Babu ranar da bamu yi waya da Abbu ba tunda ya tafi, idan ma bamu yi wayar ba muna tare ta hanyar text message yana kashe ni da dadadan kalamai da suke kara narka zuciyata zuwa gare shi. Sai a dan tsakanin na fahimci ainihin ma'anar Soyayya, ashe da shirme nayi, ashe ba son Muneer nake yi ba tunda ko a lokacin dana yi tashen son shi ban taba kawowa raina bazan iya rayuwa idan babu Muneer ba, amma a yanzu, na tabbata cewa muddin babu Abbu a cikin rayuwata to tabbas rayuwa ba zata yiwu a gare ni ba, ko zan yi ta to mara gardi da dandano ce. A yanzu bana taba iya tunanin runtsa idanu matukar ban ji muryar Abbu a yini ba saboda nasan cewa ba zan iya barci ba, nayi wani irin sabo da muryar Abbu wanda sau tari hakan yake bani mamaki. A kowace rana kuma a kowane lokaci wata kofa a cikin zuciyata sai ta bude da sunan Abbu rubuce a jikinta Ina da tabbacin nan da dan lokaci kankani kila numfashina ma idan aka kula sunan Abbu ne zai dinga fita daga cikin shi. Duk da dai ance wai sanin gaibu sai Allah amma zan iya cewa ta bangaren Abbun ma hakan take koma fiye da haka. A yadda na fahimce shi cikin dan lokacin, yana daga cikin mutanen da baiyana halin da zuciyoyin su ke ciki abu ne mai matukar wahala da wuya a gare su, sai dai su baiyana shi through their actions kawai. Baya zama yana wani tsara min kalamai na soyayya kamar yadda yace bai iya irin wannan Abun ba but I am comfortable da yanayin yadda yake tafiyar dani, yadda yake tattalina da yadda yake nuna kamar duk duniyar nan babu wata 'ya mace mai gashi a cikin idanun shi sai ni, wannan kadai ya ishe ni numfashi mai dadi a rayuwa sanin cewa abinda nake matukar so da qauna shima yana sona da kaunata equally. Shi yasa ko a lokacin da Mommy ta sake tuntuba na da zancen aure a karo na biyu, tace "bikin Hansa'u yana matsowa, me zai hana a hada auren ku gabadaya kawai a daura a can Malumfashi? Bai fi watanni biyu ba za a daura in yaso ko bayan kun karar da session dinnan ko semester din sai ayi biki da tarewa ko?" nace "Mommy sai wani saurin ku aurar dani kuke yi kamar wadda kuka gaji dani? Wane irin aure ne kuke shirin yi mun haka daura aure kafin tarewa?" tace "to ai gani nayi hakan zai fi mana sauki da mutanen da zasu zo daurin auren, ace anyi aure da wata daya wasu ko gama kafe gajiya basu yi ba a sake juyowa yin wani auren kin ga ai akwai takura, ba gwara ayi a wuce wajen ba?" nace "Mommy ni bani da zabi, kuyi duk abinda kuke ganin daidai ne" tace "to Allah ya miki albarka, Yasa hakan shi yafi alkhairi.... Oh su Ummiey za a zama matar aure!" da sauri na kife wayar a kan gado na fara juyi akan gadon idanuna akan fuskata kamar Ina gaban ta. Abbu ya kira ni a daren ranar cikin tsananin farin ciki da murna, yace "kin gama yi mun komi Nafeesah, kin saka zuciyata cikin farincikin da bata taba shiga ba, Allah ya miki albarka Nafeesah! I'll definitely compensate you Amour, yau zan ma iya barci kuwa saboda murna?" da wadannan kalamai nashi na kwanta suna min amsa kuwwa a cikin kaina, tabbas I'll be the luckiest bastard on earth matukar na auri Abbu, Abbu!! Allah ya nuna min ranar da zan zama matar shi lalle zan kere sa'ah.
Bayan kwanaki biyu Abbu ya dawo daga Ilorin, da yake dawowar safe yayi gida ya wuce ya dan huta ya shirya kafin ya shigo cikin makaranta, lokacin muna cikin lab muna practical don haka yace in same shi a office dinshi idan mun gama. Sai karfe biyar muka fito, ban tsaya yin komi ba na tunkari ofishin Abbu cikin wani irin doki, ji nake kamar in yi fuffuke ko in bude idanuna in ganni a gaban shi, in dora idanuna akan kamilalliyar fuskar shi mai saka ni cikin nishadi, nayi kewar shi, ban taba kewar abu a rayuwata har nake ji numfashina yana daukewa saboda rashin wani abu kamar yadda nayi kewar shi ba, how I can survive without Abbu a rayuwata yanzu, only Allah knows. Jikina har rawa yake lokacin dana hau corridor da jerin offices yake ba, naja nayi burki a kofar ofishin shi Ina kokarin saita kaina kila idan na shiga kai tsaye a yadda nake zai iya zaton ko gudu nayi naxo gare shi. Na daga hannu da niyar yin knocking na jiyo wata murya tana magana, cikin Jan hankali, cikin kissa da kisisina, cikin wata murya dake baiyana tsananin bukatuwa da roko..... Zuciyata ce ta bada wani irin sauti da naji shi tamkar saukar aradu......
~Me kuke tunani game da chapter din Yau?
~Mommy fa? Ya kuka gani? Ta burge ku??
~Keep voting, sharing and commenting word by word dearies,
#TeamAbbu
#OneLove
*♡Jeedderh♡*
hh[12:19PM, 2/18/2018] +234 703 300 1537: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*
*©°•Jeedderh Lawals•°*
*42*
"Dr. Ibrahim baka tunanin lokaci yayi da xaka yi recognising din soyayya ta zuwa gare ka? Kana sane da halin da ruhina yake ciki saboda kai, soyayyar ka na azabtar da zuciyata a kowace rana amma kayi kunnen uwar shegu dani kana nuna kamar baka san komi ba, haba Ibrahim, ka tausaya min mana please!!" kafafuna suka shiga rawa na kasa yin knocking din da nayi niyar yi, a hankali na matsa ta jikin tagar office din da yake a bude take. Abbu yana tsaye ya juyawa tagar baya, ya rungume hannayen shi a kirji yana fuskantar ta yayin da ita kuma take fuskantar tagar duk da cewa dai bana iya hango fuskar ta amma yanayin shigar da tayi m not satisfied with it. Ko dai tayi kwalliya ne don tayi seducing din Abbu na ko kuma ta saba yin tambadaddiyar shiga ta marasa mutunci kamar yadda tayi yanzu. Abbu yace "Dr. Luba Ina ga wannan abu ai yana gare ki ne, ba tun yau ba na riga da na fada miki cewa Ina da aure har da 'ya'ya...." ta katse shi, "nima ai nace maka zan iya aurenka a hakan, meye hadina da matar ka ni? Kai zan aura ba ita ba!" yace "am getting married, in the next two months in shaa Allah!" ta laulayo wani ashar ta maka, "says who? Karya ne Dr Ibrahim, wallahi Karya ne! Babu 'ya macen data isa ta aureka Ina tsaye Ina kallo, idan ma wasa kake yi tunda wuri ka fadi kafin in aikata abinda ran mu ba zai mana dadi ba" yace "me yasa zan miki wasa? Ba tsoron ki nake ji ba kuma ba shakkar ki nake yi ba, ban san ko sau dubu nawa kike so in fada miki cewa bana son auren ki ba, you are not my type Ramlah" tace "but you are my type, and there's no way da zan zauna ina kallo a gaban idona wata ta dauke abinda nake so ba, Karya ne wallahi...." ta kara taku zuwa gaban shi ta kai bakin ta daidai kunnen shi, ban san me ta rada mishi ba, naga dai taja da baya yayin da Abbu yayi shiru kawai, can kuma naji yace a hankali, "get out please Dr Luba" tace "ba kai kace in zo ofishinka ba ra'ayin kaina ne, don haka idan zan fita ma yanzu sai nayi ra'ayi, gashi kuma ban gaji da ganin fuskar ka ba, ya za ayi kenan?" na hangame baki cike da tsananin mamaki, lallai duniyar Allah mai fadi, xaka ga mutane daban-daban masu hali iri-iri, ita kuma wannan wacece? Zuciyata ta hau wani suya kamar zata fito daga kirjina, ji nayi kamar in banka kofar ofishin in shiga in jawo ta by her hair in fada mata Abbu nawa ne, in ma ta kai ga tofa mata yawu a fuska duk zan yi matukar zata fita daga cikin rayuwar Abin sona. Na koma ga kofar na fara knocking da karfina kamar zan balla ta, Abbu ne ya min izinin shiga. Na tura kofar na shiga with full of attitude and Charisma, so that wadda take ikirarin mallakar Abbu na ta karfi da yaji taga cewa am not the type of people da ake musu kwacen abinda suke so, abinda suke Jin cewa ba zasu rayu ba tare dashi ba right in front of their eyes ba tare da sun yi abu ba. Abbu ya juyo yana kallona, murmushin daya saki kadai yasa naji wani irin kwarin gwiwa ya mamaye ni, naji duk wata fargabar kada fa matar dake gabanshi ta kwace min shi ta tafi ta barni a take, tabbas Abbu shine mahadin rayuwata. Nima na mayar mishi da martanin murmushin wanda yake kunshe da zallar so da nuna tsananin kewar shi da nayi kafin idanuna suka sauka akan matar dake ikirarin claiming din abinda yake nawa. Ta sha uwar kwalliya a fuska saboda tsabar kwalliya ba zaka tantance ainihin kala ko kamanninta ba, tasha adon izgar doki wanda ya sauko a kafada da gadon bayanta, wani material ne a jikinta an mishi wani irin watsattsen dinki na Allah wadai wanda ya fito da shafaffen kirjinta kamar shafaffen silifas, dinkin ya matse ta tun daga kirjinta har cinyoyinta, ta wani kalleni tun daga sama har kasa yayin da nake kallonta disgustingly cikin nuna kyama kamar wadda taga abin kyankyami wanda na tabbatar da cewa sai ya kada mata 'ya'yan hanji. Abbu ya katse mana kallo-kallon da muke wa juna ta hanyar cewa "Dr Luba meet my dearing wife, Nafeesah. Nafeesah she's my co worker" nace "sannu, ya kike?" ta tabe baki tana wani yamutse fuska, "wannan abar ce dama kake wani tada jijiyoyin wuya kana cewa wai zaka aura? Me ta fini dashi?" Abbu yace "ko zaki iya bamu waje, Ina son sirri" ta buda kofofin hanci har suna naso, "ko baka ce ba yanzu zan bar maka ofishin ka kafin ka wulakantani a gaban wannan er yarinyar, sai dai kada kayi tunanin na hakura ne, ko ta halin yaya sai na mallake ka Ibrahim saboda kai nawa ne!" ta warci jakar hannunta ta fita tana murguda kugu kamar wani shafaffen plate saboda rashin cikowar shi, na bita da kallo Ina murmushin mugunta, matar nan ta rainawa kanta hankali da yawa, ni ta kira da yarinya koh? Allah ya kara hada ni da ita wani lokacin, ni kuma nayi alkawarin nuna mata aikin yarinta. Na maida kallona ga Abbu lokacin data fita daga office din ta maida kofar tayi banging kamar tashin duniya. Murmushi na sakar mishi softly, duk da cewa har zuwa lokacin zuciyana tana itching game da Luba ce ko Bana yace sunanta? Bana so in sani. Yaja kujera ya zauna a kusa dani tare da nuna min wata kujerar nima na zauna, yace "kiyi hakuri da abinda ya faru, kada kuma ki sa maganar ta a cikin ranki, ta saba irin wadannan maganganun duk burga ce da tauna tsakuwa don aya taji tsoro" nace "wai wace? Ni ban ma fahimci abinda take fada ba balle in saka shi a cikin raina...," ya kura min idanu yana murmushi, "kin san abinda yasa nake kara jin ki a cikin raina kenan? Nafeesah my other being" na sadda kaina kasa Ina dan murmushi, Abbu with his flirtations, a hankali nace "sannu da dawowa, ya hanya?" yace "it was tiresome, amma yanzu na dawo normal dana gan ki, my wife!" wayyo kunya! Na rufe fuska ta da hannuwana ina er dariya, shi kuwa dariya ya saki sosai, a tausashe. Nayi shiru Ina jin dariyar da yake yi, he sound so relieved and happy, and I feel proud knowing that ni ce sanadin farincikin da yake ciki.
Cikin barci na kai hannu kasan filona na lalubo wayata dake vibrating, duka-duka karfe goma ne da rabi na safiyar ranar Assabar, da yake ranar hutu ce kuma ban samu nayi barci da wuri a daren jiya ba shi yasa na ke jina kamar wadda ta kwanta a lokacin saboda tsabar barci. Ban ko tsaya duba caller ID ba na dauka, muryar Sadiya ce ta doki kunnena, "Asslm, Nafeesah hope ban katse miki barci ba?" cikin muryar barci nace "kin katse min mana" tace "sorry, dama muna nan AKTH ne shine zan fada miki" na tashi zaune a sukwane nace "Teaching Hospital kuma? Waye babu lafiya?" tace "Ni'imah ce wallahi, ta samu miscarriage yau da safen nan" jikina yayi sanyi sosai, Allah sarki Ni'imah. Nace "ki turo min da number din dakin da kuke, gani nan zuwa" na ajiye wayar tare da dirowa daga kan gado. Wanka nayi na fito na Karya, ban wani tsaya yin kwalliya ba na saka kayana kawai na fita, sai a cikin mota ne na kira Ramlah Ina fada mata, tayi jimamin abin sosai tace zata kira ta mata jaje. Ban samu Sadiya ba a dakin da aka ajiye su lokacin da naje, Anty Ameenah da Anty Rayyah suna nan a dakin tare da wata dattijuwa sai kannen Bashir mata su biyu, Ni'imahr na kwance tana barci an sa mata drip, ta wani dashe tayi fari tas kamar wadda babu jini a tattare da ita. Muka gaisa dasu Anty Ameenah cikin mutunci har tana bani hakuri akan wai an taso ni daga makaranta, nace a kunyace haba Anty, Ni'imah tafi karfin haka a wajena ai.... Allah ya mayar mata da mafi alkhairi, suka amsa da ameen. Sadiya ta shigo dakin hannunta rike da na Jameel dan Anty Jameelah wanda yake tafiyar ta-ta-ta, muka gaisa da ita itama na musu jaje, naja Jameel a jikina ina tambayar shi inda yaje yana ta min gwaranci ina murmushi. Ni'imahr bata farka ba sai bayan azuhur, su Anty Ameenah suna waje suna sallah da yake ni fashin ta nake yi, na matsa gefen gadonta Ina mata sannu tare da tambayar ta abinda take bukata? Kuka kawai ta saka tana shafa cikinta, na rungumo ta a jikina ina dan jijjigata kamar nima in rushe da kukan nake ji, it's not easy ka dauki cikin abu ka raine shi, bayan ka gama kwallafa ranka a kanshi kuma sai Allah ya jarabce ka da rashin sa, hakika Allah kadai yasan irin sakayyar daya tanadarwa irin wadannan matan. Nace "kiyi hakuri Ni'imah, haka Allah yaso. In shaa Allahu zai kawo miki mafi alkhairin sa, stop crying please kinji?" ta jijjiga kanta. Naje na xubo mata ruwa a cikin cup ta kurba, lekawa nayi na gaya musu ta farka sai gasu sun duro cikin dakin, kowa sannu yake jera mata tare da nasihar fawwalawa Allah lamuranta, nan aka zuba mata abinci muma muka zuba namu muka ci. Da yamma sai ga Bashir din yazo ashe ma baya gari saukar shi kenan daga Abuja, bawan Allahn nan har da hawayen shi abin gwanin ban tausayi wallahi. Bayan Magriba su Anty suka yi haramar tafiya gida, Anty Rahina tace in zo ta sauke ni a makaranta mana nace mata ai ni anan zan kwana, tace inah! ga Sadiya nan da Gwoggo Hinde sun isa in zo ta maida ni makaranta kawai, nace mata ni fa anan nayi niyar kwana. Tayi shiru tana kallona ganin na kafe kafin tace "kin fadawa iyayen ki?" nace "zan fada musu anjima dai" tace ai shikenan, Gwoggo Hinde zo mu wuce gida dake kawai. Da haka suka mana sai da safe suka tafi bayan sun ajiye mana duk abinda zamu bukata. Na shiga bandaki na gyara jikina, ban taho da panties bama sai dana fita waje na sayo wasu pad ce ma ban nema ba da yake ni ma'abociyar ajiyar su ce a cikin jakata saboda emergency. Na fito daga bandakin ina gyara zaman rigar jikina, daidai lokacin Abbu yayi sallama ya shigo cikin husky voice din nan nashi Hafsy na biye dashi a baya, zuciyata tayi wani irin fari da ganin shi kamar zata haske duniya da abinda ke cikinta, gabadaya ranar ban ji muryar shi ba mun dai yi exchange din messages a tsakaninmu da rana, fuskar shi ta nuna zallan mamaki da ganina kafin baiyanannen farin ciki daya kasa boyuwa ya nuna akan fuskar tashi, na ja kujerar kusa da gadon Ni'imah din na zauna. Na Kalli Hafsy dake tsaye a bakin gadon Ni'imah na mika mata hannu alamun tazo ina murmushi, ta makale kafada tare da kara lafewa a jikin Abbu alamun ba zata zo ba, na janyo ta jikina tana kokarin kwacewa amma na hana ta, nace "haba Hafsy na ni dake bata baci, Waye ya tabo min ke?" ta turo baki tana nuna ni da yatsan ta, nace "ni da kaina? Me na miki?" tace bake bace ba kike kin zuwa ki gaida ni, kullum sai nace kizo ki ganni amma baki taba zuwa ba! Na dan saci kallon Abbu dake gaisawa da kannen shi amma idanuwan shi suna kanmu yana mana dan murmushi, na janye tare da kallonta nace "kiyi hakuri kinji? In shaa Allahu zan dinga zuwa Ina ganinki, so stop frowning and smile kinji?" tace "promise?" na gyada mata kai. Aka kwala kiran sallahr Isha'i a daidai lokacin, Abbu ya zube min wayoyin hannunshi a gabana ya fita da niyar yin sallah.....
~Nasan zaku ce chapter din yau ma yayi kadan, amma ya zanyi? Wallah bani da lokacin yin typing da yawa Ne shi yasa
~Lots of love and Hearts Ni Da Abokin Baba Na Fans
#TeamAbbu
#OneLove❤❤
#AnaTare🤝🤝🤝
*♡Jeedderh♡*
[12:19PM, 2/18/2018] +234 703 300 1537: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*
*©°•Jeedderh Lawals•°*
*44*
Kwanci tashi asarar mai rai, biki yana ta kara matsowa yayin da muke ta shirye-shiryen rounding off din semester dinmu. Tuni Ni'imah ta warware har ta fara shigowa school abinta, cikin Sadiya yana ta kara fitowa ni kuwa gandoki har na fara tanadar kayan jarirai, lol.
☆☆☆☆☆
Cikin mamaki na daga wayata dake ringing bayan na duba sunan wanda yayi kiran, “Yau ko dai batan lamba waya kayi Harith?" tunda ya samu aiki a Ibadan ya tarkata ya tafi zumuncin dake tsakaninmu yayi kasa, shi aiki ni kuma karatu don haka we were not in contact recently, yace “haba Nafeesah, har ke kina da bakin magana? Sau tari zan tura miki sako ta whatsapp amma bana ganin reply dinki, anya idan da amana ruwa ya dafa kifi??" nayi dariya nace “kasan rayuwar dalibai sai a slow wallahi, shi yasa. Ka yini lafiya?" yace “yeah, Alhamdulillahi..." nan muka gaisa dashi da tambayar juna kwana biyu, yace “Sis take fada min ranar nan wai ai an saka miki ranar aure, shine nace bari in kira in tambaya inji laifin me nayi da ban samu labari ba?" nayi murmushi nace “to kuma kawai daga sa min aure sai in hau shela? Kaima ai naji ance ka kai kudin aure gidan su Ikram" yace “yeah... Amma ya aka yi kika sani? Ko abokaina basu san da labarin ba" nace “nima a gari naji, amma daga majiya mai tushe, Ikram din ce da kanta take fada min" yace “iye lallai naga nuna wariyar jinsi, so u guys have been in contact with each other amma shine kike fada min wai wani rayuwar dan makaranta and stuffs ko?" nayi dariya nace “ai kasan zumuncin mata ko ta yaya dai in a week ba su rasa yin waya shi yasa... So what's up?" yace “mun shigo workshop ne cikin Kano, shine nace bari in tambaye ki idan ziyara is allowed, zan leko mu gaisa" nace “why not? You are welcome!" yace “to ba laifi, goben idan zan shigo I'll inform you" daga nan muka yi sallama kowa ya ajiye wayar. Firdausi ta dago kanta daga typing din da take yi a cikin laptop dinta ta kalleni, tace “ni yanzu meye makomar ki idan an miki aure? Zaki ci gaba da zama cikin hostel ne ko kuma zaki zauna tare da kishiyar ki ne tunda har yanxu ba a gama gyara inda zaki zauna ba?" na zauna a gefen gadona ina sighing, “ban sani ba nima wallahi, but kila, may be in ci gaba da zaman hostel" tace anya? I doubt idan mijin nan naki zai yarda, na harareta “me kuke nufi wai? Abinda Sadiya da Ramlah suka ce kenan dama" tayi dariya, “to ai yadda yake nunawa ne, he's barely holding it in, a dokance yake kuma a kagauce da auren nan, azo kuma ace an daura amma ya barki ki zauna a hostel? Ni dai a ganina da kyar ya bari" na dauki dan karamin filo na jefeta dashi, “ke fa m dinki karama ce wallahi, sam baki da kunya" ta fashe da dariya ni kuma na maida bayana kan gado na kwantar ina kara juya maganganunta a cikin raina, gaskiya a son samuna koda ace gyaran gidan da za a ajiye ni bai kammala ba to Abbu ya barni in ci gaba da zama a cikin hostel abina har sai an gama don ni fa har ga Allah ban shirya fuskantar Anty Mubeenah a matsayin kishiya ba balle har ta kaini ga zama a gida daya da ita a matsayin kishiyoyin juna, woah! Ko ya zaman zai kasance?? Na gyara juyawa a kan gadon tare da janyo face mask na rufe idanuna, a hankali barci ya dauke ni.
Washegari lecture din Abbu gare mu, da wuri na tashi na shirya cikin jallabiya brown mai kwalliyar light ash a jikinta, ban yi wata kwalliya ta sosai ba na yi rolling gyale ash mai dan fadi, na zura takalmin vincci flat na fita da dan saurina, takwas saura ina cikin hall din, nayi ajiyar numfashi lokacin da nake zama a kan seat, Abbu baya tolerating late coming ko da wasa, minti biyar ya kara akan karfe takwas to ka hakura da lecture dinshi na ranar kawai, na tuna lokacin dana taba yin nauyin barci ban tashi da wuri ba, na isa wajen six minutes past eight na tarar da kofa a rufe, kuma fa Abbun yana kallona a tsaye a kofar class din amma yayi biris dani tare da sauran dalibai abokan latti na, haka muka gaji da jira muka kama gaban mu.... Na ciza bakina cike da takaici, har yau idan na tuno abinda ya faru sai naji kamar inyi me, kuma fa sabida shi nayi makarar, shi ya kira ni a daren ranar ya tsare ni da hira har dare ya tsala., ai kuwa dai da kyar ya samu ya shawo kaina. Na saki dan murmushi a hankali dana tuno irin bidirin da muka sha a lokacin. Ajin yayi tsit lokacin da Abbu ya turo kanshi cikin ajin, yayi shigar wani danyen vowel ruwan hanta, bai saka hula ba sai dai ya taje sumar kanshi da yake shi ba ma'abocin saka hula bane. As always, yayi kyau kamar ka lashe shi. Ya fara searching din hall din da idanun shi a hankali har ya lalubo ni, ya sakar min murmushi very soft and lovely, ban bata lokaci ba wajen mayar mishi da martani, yayi gyaran murya amma fa jefi-jefi idanunshi kan kalloni kamar yadda koda wasa nawa basu bar shi ba.
Muna gama lectures muka fita, tun saura minti sha biyar mu gama dama Harith ya min text kan cewa ya shigo cikin makatantar ina zai sameni, na tura mishi text din inda muke yace xai zo, don haka muna fita na hange shi inda ake ajiye motoci. Murmushi nayi na karasa wajenshi, ya wani kara fari ya kara zama magidanci kamar ba Harith din dana sani ba watanni hudu da suka wuce, shima mamakin da yake yi kenan yace wai na kara yin kyau nayi fresh, nan muka tsaya muna gaisawa sosai mun fara hira sama-sama ya kalli agogon hannunshi yace “I gotta go, Abuja zan wuce daga nan" nace “za aje a ga Amarya kenan? A gaishe ta" kamar ance in waiga bayana, ina juyawa na hango Abbu yana nufo mu, na zaro ido tare da juyawa ina kallon Harith dake kallona shima, fuskar nan ta Abbu a hade take murtuk, lallai yau kishin maza ya motsa. Sam banyi zaton har lokacin yana cikin department dinmu ba saboda ban ga motar shi ba, ai da banyi gangancin tsayawa da Harith a wajen ba. Harith yace “da alamun wanda zaki aura ne ke tunkaro ku" nace “ya aka yi ka gane? Ka san shi ne dama?" yace “not at all, but hararar da yake jefo min kamar zai kawo min naushi irin wadda nake wa duk namijin dana gani tsaye da Ikram" nayi er dariya, “he's cute, isn't he?" daga bayana naji anyi magana, “well, look who's calling who cute" he sounds so close alamun yana bayana kenan, na ja gefe da dan saurina ina dariya cike da jin kunya, Abbu ya mikawa Hatith hannu fuskar shi babu yabo babu fallasa babu fara'ar nan dake tattare a fuskar shi, “Ibrahim Galadanchi" abinda yace mishi kenan coldly, ina ganin yadda yake glaring din Harith da hot gaze dinshi wanda zai iya grilling din kifi, da sauri Harith ya mika mishi nashi hannun suka yi musabiha yace “Harith, fiancé din Ikram cousin din Sulaiman mijin Sadiya" sai lokacin fuskar Abbu ta dan warware kadan daga hadeta din da yayi amma bata koma normal ba har lokacin, suka dan gaggaisa a tsaitsaye ya dawo da kallonshi gareni da tun da naja gefe ban yi magana ba, kallon daya jefe ni dashi sai da yasa naji alamun kadawar ‘ya‘yan hanjina, yace “ki same ni a mota" da kyar na samu na iya daga mishi kai, ya wa Harith sallama ya nufi wata bakar Land Rover dake kusa da inda Harith yayi parking din tashi motar, haba ba mamaki ashe ya canza mota ne? Na kalli Harith daya jefe ni da murmushin mugunta, na harare shi ya wani yi shrugging yana daga gira sai kawai na girgiza kai don bani da lokacin biyewa tsokanar Harith, godiya na mishi muka yi sallama na wuce inda Abbu yake jirana na bude motar na shiga. Ina shiga yaja motar muka fara tafiya ba tare da yace uffan ba, na kalli fuskar shi har lokacin babu fara'ah a tattare dashi, da alamun na bata mishi rai sosai. Jikina yayi sanyi, na maida kallona ga tagar motar ina jin kamar in fita ta ciki, da alamun yau Abbu na baya cikin walwala, duk saboda ni!!
#TeamAbbu
#One Love
#AnaTare
*♡Jeedderh♡*
[12:19PM, 2/18/2018] +234 703 300 1537: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*
*©°•Jeedderh Lawals•°*
*_Wannan shafi dungurungum na marubuciya RUFAIDA UMAR IBRAHIM ne. I was touched and impressed lokacin dana ji cewa cikin masoya kuma makaranta littafin Ni Da Abokin Baba Na kina ciki. Sauran Marubuta dake bibiyar littafin ina gaishe ku, wadanda suke kan posting nasu littafan ina musu fatan alkhairi. Masoyan Ni Da Abokin Baba Na ina gaishe ku a duk inda kuke. #OneLove_* ❤❤❤
*43*
Suka kalli juna kafin suka kalleni, Sadiya ta dage gira daya "me kenan?" "me fa??" na tambayeta ina wani fuskewa ni ala dole ban fahimceta ba. Tace “ki wani daina fuskewa malama, mun san abinda ke faruwa tsakanin ku biyun nan" na kada mata idanu innocently, “ni da wa??" ta kai min duka a kafada, “zaki sani ne maras M, ace kamar mu kuna cikin relationship da Yayan mu mu kasa sani?" na kallesu su duka biyun ina so in karanta yadda suka amshi zancen, ban karanci komi ba sai dai murmushin dana gani kwance akan fuskar su na farin ciki ne bana embarrassment kona takaici bane, naji sanyi ya lullube min zuciya, at least abotar mu dasu tana nan. Ni'imah tana murmushi tace “Sady ke kike wani tsayawa ma kina neman karin bayani, ni fa dama tun ba yau ba na harbo jirgin su ita dashi, they were making it obvious shi yasa ni ban tsaya jira a fada min ba nayi jumping into conclusion" na dan harareta cikin wasa nace “ni kar ki mun sharri wallahi" tace “ba wani sharri sai gaskiya. Irin kallon da kuke wa juna dama tun ba yau ba be it kuna cikin mutane ko ku kadai ne wallahi na soyayya ne, ai Anty Rahina tace an kusa yin auren" na dafe kirji ina zaro idanu, nace “su Anty har sun sani??" dariya suka saki suna kallona kamar wata kuntacciya dinnan, “Allah kina kwafsi matar Babban Yaya, tunda har muka sani ai dole su Anty su sani kuwa" na rufe fuskana ina diddira kafafuwa a kasa, “Ya Allah! Da wani idanu zan kallesu ni kam?" suka sake kwashewa da dariya har da tafawa, na hade fuska ina kallonsu, “this is not funny fa!" na fada in a serious tone don su san ba wasa nake yi ba, amma ko a jikinsu sai ma wata dariyar da suka kara sawa. Ganin zasu sa min ciwon kai naja Hafsy data fara gyangyadi a zaune muka koma kan spare gadon dake dakin na zauna ita kuma ta kwanta kanta a kan cinyoyina. Hira nake janta dashi duk don in janye hankalina daga shakiyancin dasu Sady suke min, cikin dan lokaci barci ya dauketa. Na maida hankalina wajen buga game bana ko kallon inda suke, har suka gama shiriritar su da tsara yadda bikin zai kasance suka yi shiru, dinner ma sai da aka tsara kala biyu, luncheon da parties kuwa wai har da Tea Party, fruits party, Arabian nights dasu Fulani day da tarkace, ina jinsu dai ban saka musu baki ba sai dariya da nake musu kasa-kasa, da alamu wani noti a kansu ya kunce kila saboda murnar auren Yayan su ne ko wani abu? Muna nan su Abbu suka dawo daga masallaci shi da Bashir, sallama ya musu ya matso inda muke ya dauki Hafsy a kafadanshi ni kuma na kara gyara zaman gyalena na kwashi wayoyin shi nabi bayan shi. Ya bude seat din baya ya kwantar da Hafsy, ya maida seat din ya rufe tare da jingina da motar yana kallona, na sadda kaina kasa ina dan tapping kafafuna a kasan, akwai wadataccen haske sosai a wajen shi yasa naji na kasa sakewa in kalleshi, tunda maganar auren nan ta shiga tsakaninmu na kasa sakewa in kalleshi sosai koda yake ko a da can dinma idan muka yi kallon ido da ido sai dai by mistake, balle yanzu. Yace “gobe in Allah ya kaimu zan samu Alhaji Babba yayan Alhajinmu da maganar zuwa a tambayo min auren ki, zasu kai kudin na gani ina so za kuma a saka ranar auren gabadaya” nayi shiru kaina a kasa, me zan ce mishi? Shi Abbu bai san irin matsananciyar kunyar shi da nake ji bane da zai dinga zama yana tattauna maganar aurena dani ba. Ya kara jingina da jikin motar yayi alamun tagumi, “ni ai shikenan tawa ta same ni kuma. Son maso wani nake yi ko kuma ba a shirya aurena har yanzu bane?" na saci kallonshi, ba karamar dauriya nayi wajen danne dariyar data taso min ba, ya wani yamutse fuska kamar yaron dake shirin fashewa da kuka, nace “me nayi ni kuma?" yace “baki son maganar auren mu mana. Da nayi sai ki wani hade fuska kamar wadda ake tursasawa, ji yanzu ma na gaya miki magana maimakon ko ameen ki ce shine kike wani sadda kai kasa" na girgiza kaina ina dan murmushi, Abbu da rigima yake wani lokacin kamar karamin yaro haka yake. Kwanan nan haka yake, gaba daya ya zama very open to me, baya shakkar fada min duk maganar data fito bakinshi, wata rana ta saka ni jin kunyar shi duk da cewa abin yana burge ni kuma na kula hakan yana kara ja na zuwa gare shi. Nace “to ameen Abbu" yayi murmushi, “datz you my Amour.... Amma tsaya...." na kalleshi, yayi frowning face “yaushe ne kika ce kin daina kiran sunana da wani Abbu? Na gaya miki Abbu na yara na ne ba naki ba" nace “ai nace zan daina fa! amma ba yanzu ba" ya wani langwabar da kai, “har sai yaushe?" nayi shiru, ya sake cewa “ko sai mun yi aure?" na gyada mishi kai, yace “ba laifi, ni ai bawan Allah ne I can wait" nayi dan murmushi, “datz you kaima.... Wai don Allah meye ma'anar Amour?" yace “Love in french" na sadda kaina kasa ina blushing, da gaske ni Love dinshi ce? Nace “amma sauran messages da kake tura min shima French ne? Me suke nufi?" ya girgiza kai, “naaa! Ba zan gaya miki yanxu ba, zan dai koya miki French din sai ki karanta da kanki. Idan muka yi aure ma a Kasar Faransa zamu yi honeymoon dinmu ai, kila kafin mu dawo sai kin koyi yaren sosai, sai mu dinga canza yare a gaban mutane abinmu koh?" na kai hannu ina rufe fuskata ina dariya, can kasan zuciyana kuwa fata nake ina ma zan bude ido in ga har watannin da suka rage in zama mallakin Abbu sun zagayo? Ya kara jingina da jikin motar yana murmushi “ke da kunyar nan taki kuna birge ni, sai dai it's way too much gaskiya, kiyi kokari ki rage ta ko kuma ni da kaina inyi wannan aikin...!" na kara dukunkune fuskana wannan karon a cikin gyale ma. Yayi dariya son ranshi kafin yace “ina tunanin raba muku gida ke da Mubeenah, me kike tunani?" nace “idan hakan yayi maka bani da damuwa da hakan nima" amma a can kasan raina ba karamin dadin hakan naji ba, har ga Allah dama can bani son zama gida daya da Anty Mubeenah har yanzu ina jin kaina guilty wani lokacin, har yanzu kuma ban san da wane ido zan kalleta ba balle har inyi tunanin zama a gida daya da ita, duk lokacin da nayi tunanin na kan ji hankalina bai kwanta da hakan ba. Yace “hakan ya min perfectly, zan samu inci amarcina cikin dadin rai da kwanciyar hankali abina. Amma na dan lokaci ne fa, don tuni an fara mana sabon gini" nace “sabon gini kuma?" yace “yeah, inda zamu koma da zama mu dukan mu har yaran da zamu haifa nan gaba. Da wancan gidan na gina shine a matsayin inda zan rayu da matar aurena ne, ban taba kawowa raina kara yin aure ba sai da kika shigo cikin rayuwata sannan na fara samun second thoughts. A yadda nake so kuma ki cika min gida da yara inda muke zaune yanzu ya mana kadan. Ina so iyalina su tashi da hadin kai ba tare da banbancin komi ba Nafeesah, ina fatan zaki bani goyon baya wajen ganin hakan ya tabbata?" muryar shi ta tabbatar min da cewa da gaske yake, tausayin shi ya kama ni Allah sarki Abbu na! Da haka yaso ya karasa rayuwar shi cikin takaici da rashin kulawar matar aure? Ta wani fannin sai na tsinci kaina da godewa Allah daya kawo ni cikin rayuwar su, ko babu komi nasan zan kawo haske cikin rayuwar Abbu kamar yadda name tabbata cewa shima zai kawo haske a tawa rayuwar. Nasan cewa shawarar daya yanke is not a bad idea, ni kaina nasan ba zan juri ganin rabuwar kan yayanmu ba kuma da yardar Allah ba zan bada gudunmawa wajen ganin rabuwar kansu ba kamar yadda wasu iyalan suke, na gyada kaina nace “In shaa Allah Abbu, zan yi iyaka bakin kokarina" yace “Nagode sosai Nafeesah. Allah ya bani ikon faranta miki rai kamar yadda kike iyaka bakin kokarinki wajen ganin cewa kin faranta nawa ran" na sadda kaina kasa ina murmushi, daya daga cikin halayen Abbu dake matukar burge ni kenan, saukin kai da saurin fahimta. A kasan raina kuma na amsa Addu’ar da yayi da “Ameen”.
Bamu ankara da lokaci ya ja ba sai da muka ga Basheer ya fito zai tafi sannan Abbu ya duba agogo yaga karfe goma ta wuce, Abbu ya kama baki cike da tu'ajjibi yace “haka lokaci yake gudu dama?" na sadda kaina kasa ina magana a hankali yadda ba zai ji ba “kaine dai baka kula da lokaci yana tafiya ba saboda love ya rufe maka ido" ya mikawa Basheer hannu suka yi musabiha na mishi sai da safe nima ya karasa wajen abin hawan shi ya tafi, Abbu ya bude motar ya shiga ya zauna, ya kalleni yana kokarin yiwa motar key, “naji abinda kika fada sarai, zaki zo hannu ne ai zaki yi bayani by then" na ja da baya ina er dariya, na maida mishi murfin motar na rufe, yace “any thing for me?" na girgiza mishi kai, “babu, sai da safe Abbu na!" na juya da sauri na fara tafiya ba tare dana jira abinda zai ce ba, ina jin shi yana en maganganu har na mishi nisa kafin naji alamun yaja motar, na saki dariya a hankali. Ina shiga daki suka min caaa da magana, ni dai er dariya kawai na dinga yi da kyar na samu na kashe musu baki, Sadiya ta miko min leda mai dauke da gasasshen kaji da yoghurt, na zauna ina ci muna hira dasu har wajen karfe goma sha biyu Ni'imah tayi barci, sannan ne muma muka kwanta don dama duk saboda ita ne muke yin hirar don kar muyi barci mu barta ita kadai kadaici ya dameta, muka gyara daya gadon muka kwanta mu ma. Washegari wajen karfe goma Basheer ya kawo mana abin kari da kayan da Ni'ima zata canza, bayan su Anty Rahina sun zo mun gaida su nabi Sadiya gidanta muka je muka yi wanka muka canza kaya, sai kayan Sadiya na saka saboda ban tafi da wanda zan canza ba. Muna komawa muka tarar an sallame su, nan muka hada kaya muka wuce gidan Ni'imah. Muka gyara mata gida da komi muka mata girki, su Anty Ameenah ana kiran sallahr la'asar suka wuce, ni dai daga nan na musu sallama don a ranar zan koma makaranta. Sai bayan tafiyar su ne sannan na kira Mommy na fada mata abinda ya faru, sai da nasha fadan wai ban gaya mata da wuri ba sannan tace in hada ta a waya ita da Ni'imah, no dai na bata hakuri kafin in ba Ni'imah wayar Mommy ta mata jaje tare da kara mata da nasihu daga nan ta maido min wayar, na amsa, anan take fada min cewa wakilan Abbu zasu je gida Malumfashi tambayar aurena, nayi shiru ina gyada kai kawai, ta mim addu'ar Allah ya sanya alkhairi muka yi sallama da ita. Nima ba a jima ba na musu sallama na koma makaranta. Bayan kwana biyu aka sanya ranar auren mu ni da Abbu watanni biyu masu zuwa yayin da biki da tarewa kuma za a bari sai na gama exams dina. Wannan kenan!!
~Hii! This is just to tell u that u people r really amazing, I want u to know that I really love and appreciate ur love and affection towards me and my write up! Thank u very much and stay blessed!! 🧡🧡🧡
#TeamAbbu
#AnaTare🤝
*♡Jeedderh♡*
[12:19PM, 2/18/2018] +234 703 300 1537: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*
*©°•Jeedderh Lawals•°*
*45*
Shiru muna cin abinci a cikin restaurant din da muke zuwa lokaci zuwa lokaci, baka jin karan komi sai karan cokali da plate din dake gaban Abbu yana cin abinci yayin da na kurawa nawa plate din idanu kawai, duk yunwar da nake ji sai naji ta tafi, babu space din komi a cikina a lokacin sai na numfashin da nake shaka. Fushin Abbu ya takura ni, ya tsorata ni, gabadaya na rasa abinda yake min dadi a lokacin. Tunda ya sadda kanshi ga plate din gabanshi bai dago idanunshi ba, na kula yana gudun kallona ne kamar yadda na kula cusa abincin kawai yake yi ba wai don yana jin dadin shi ba. A hankali nace “Abbu!" ya dakata da cin abincin da yake yi kafin ya dago ya kalleni, kyawawan idanuwan shi da a koda yaushe suke farare tas-tas suna sheki suna kallona cike da so da kulawa, sun rine daga ainihin kalar su zuwa ja-brown, gaba na ya fadi sosai ban taba ganin wannan kamar ta Abbu ba, ya maida kanshi kasa ya cigaba da cin abincin. Nace “Abbu don Allah kayi hakuri kar kayi fushi dani, kawai Harith yazo ne mu gaisa ba wani abu ba please" bai yi magana ba kamar yadda bai dakata da abinda yake yi ba, na sake cewa “kaji?? Please Abbu na!!" duk da cewa sau tari ya kan nuna bai son sunan amma na kula jin sunan daga bakina yana dadada mishi rai sai dai da alamun hakan bai yi tasiri ba yau, babu murmushin nan daya saba yi, bai yi scowling dinnan ba yana kallona dangerously kamar zai zuke ni da idanunshi, instead sai kawai ya kalleni yayi wani murmushi da bai ma gama hade fatar bakin shi ba balle fuskarshi, muryar shi tayi can kasa kamar wanda yake suffering daga cutar mura yace, “eat, Nafeesah!" ya cigaba da cin abincin, sai kawai naji gwiwoyina sun sage, me ke damun Abbu ne yau? Gabadaya ya wani rikice min kamar ba Abbun dana sani ba, ban taba ganin wannan Abbun da yake gabana ba don haka ne naji nima na gigice sosai. Na xuba duka tafukan hannuwa na biyu a cikin kumatuna kawai na kura mishi idanu, ban damu da cewa hakan zai takura shi ba ko kuma idon mutane dake cikin restaurant din, ni dai fata na da burina shine in karanto abinda yake damun Abbu inyi gaggawar magance mishi koma meye sai dai ban karanci komi ba, ya gama cin abincin ya dago ya kalli plate dina sai kuma ya tashi, yaje ya biya kudin abincin suka dawo tare da yaron wajen aka maida nawa abincin cikin take away muka fita daga restaurant din. Ko a cikin mota ma haka tafiyar ta kasance, yayi wani kicin-kicin da rai kamar wanda aka aikowa da sakon mutuwa. Har muka je bakin hostel ya samu waje a parking lot yayi parking. Na dan saci kallonshi kafin na yunkura da niyar fita daga cikin motar ya katse ni ta hanyar kiran sunana, “Nafeesah!" na dakata amma ban juya na kalleshi ba, na tsani ganin expression din fuskar shi kamar yadda na tsani mutuwata. Murya a hankali yace “kiyi hakuri don Allah" cike da tsananin mamaki na juya na kalleshi, fuskar shi nuna how apologetic he was, nace “me ya faru?" ya girgiza kanshi, “na saka ki cikin damuwa saboda son rai irin nawa, you didn't do anything wrong amma na saka ki gaba ina hade miki fuska, na..." ya sadda kanshi kasa saboda maganar data kakare mishi ni kuma na kura mishi idanu, he looks soooooo lovely and adorable, Anya soyayyar Abbu zata barni in rayu cikin dadin rai?? Ya sake dago kanshi ya kalleni, wannan karon babu bacin rai dake tattare dashi sai idanuwanshi dake nuna tsananin so, kauna, kulawa da wani abu kamar tsoro? I'm not sure. Yace “I was afraid" cikin mamaki na kalleshi nace “of what?" ya girgiza kanshi, “I don't know. Kawai tunda na ganki da wani a tsaye naji wani tsoro ya dabaibaye ni, I really cherish you alot Nafeesah, I was afraid of you leaving me ko wani ya juye miki tunani daga gareni, idan hakan ya faru ban san ya zan yi ba!" wannan ba Abbu Baban su Hafsat da Abdullahi bane, wannan Ibrahim ne a zamanin da yake kan ganiyar kuruciyar shi, na muskuta ta yadda zan fuskance shi sosai, “ni ko wanene kwanakin baya yake cewa ba zai zauna yana soyayya irin ta yara ba? I wonder ko wace kalar soyayya ce wannan?" ya dan jefe ni da harara, na danyi murmushi kafin nace “nima idan hakan ta faru ban san yadda tawa rayuwar zata kasance ba Abbu, idan hakan ta faru I'll be more shattered than u, gwanda kai kana da mata da ‘ya‘y'a ni kuwa dama daga kai sai Mommy da Daddy nake dasu" ya kura min idanu kaman wanda yake kokonton abinda nace, na saki murmushi reassuringly “kada ka damu Abbu, in shaa Allahu abinda kake tsammani ba zai taba faruwa ba, I am yours, and I'll always be in shaa Allah!" ya lumshe idanunshi for a second, daya bude duk wani duhu da rikicin dake cikin idanunshi sun yaye, damuwar data lullube shi ta tafi, Abbuna ya dawo kamar yadda yake, ya saki kayataccen murmushin nan nashi, “you are almost mine dai but at least am relieved, God! Kin tsorata ni wallahi, amma do you really mean what you said?" wai sai a lokacin naji kunya ta dabaibaye ni, nayi gaggawar Kai hannu na rufe fuskata, ina jin er dariyar da yayi, “ana so ana kaiwa kasuwa.... Zaki yi bayani ne idan aka miki snatching" fuskana na cikin tafukan hannuna nace “ai babu wanda ya isa ya kwace min abinda nake so!" ya rankwafo kanshi kusa dani yana wani smirking, ina kallonshi ta yatsun hannuna, yace “Ashe dai ana so na?" da sauri na bude murfin motar na fita na barshi yana dariya, da alamun abin ba karamin dadi yake mishi ba, haka kawai naji murmushi ya subuce min. Ya fito daga cikin motar shima, “tambayar ki fa nayi baki amsa min ba" inaa, ai nayi gaba abina. Yace “to tsaya ki amshi abincin ki" naja tunga na tsaya, ina ji ya bude motar ya dauko takeaway din ya tako zuwa inda na tsaya ya miko min, nasa hannu na karba ina wani sinke fuska, ya wani kuta kamar gaske “zaki yi bayani ne wallahi, sai ki wani dinga sinke fuska kina cuta na wai ke kunya, Allah ya kaimu ranar da zaki shigo hannuna" na saki murmushi, yace “dariya ma kike yi koh? Allah Nafeesah kina bukatar in gyara miki zama, dazu kin ce wai I was cute, yanzu kince ina soyayyar yara and ina magana kina dariya koh?? Sai na tabbatar dana hukunta bakin nan naki da baya jin magana wata rana" dariya na dan saki kasa-kasa, da alamun yau en rigimar ne akan Abbu. Naci gaba da tafiya abina, ya tsaya a inda yake yana magana cikin korafi, “wato ma tafiya kika yi kika barni koh? Ba komi, sai kinyi sati biyu baki sake ganin mai kama dani ba, kai sai ranar auren mu zaki sake ganina ma" na juyo ina kallonshi nace “to ka gaida gida dasu Hafsy" yayi wani irin chuckling daya sa ni bude baki ina kallonshi, ji nayi kamar in ruga da gudu in fada cikin faffadan kirjin shi, sai nayi murmushi kawai tare da girgiza kaina na wuce cikin hostel. Kafin in karasa daki kiran Anty Raheena ya shigo wayata, na daga muka gaisa da ita. Tace wai kira tayi in fada mata size dina zasu siyo under wears da za a saka a cikin kayan lefena, ni wallahi kunya ma ta bani. Da kyar na iya bude baki na fada mata, ko sallama bamu yi ba na kashe wayar.
Bayan kwana biyu aka kai akwatina gidanmu, guda takwas sai kit, sai ta waya Anty Uwani ta turo min akwatunan na gani, wasu azababbun akwatuna kirar kasar Italy na zallan fata kalar pink ne, kayan dake ciki kuwa kama daga shadda, lace, materials, atamfofi, takalma ma kadai daga na kamfanin vincci, dg, poshter, ga jakunkuna da jewelries duka babu kanana gaskiya ba karamin kokari Abbu yayi ba wajen hada kayan nan, na dinga gyada kai kawai lokacin dana dinga duba kayan, ‘kaya kam sun yi kyau gabadaya babu na yar wa sai dai fatan in more su a gidan aurena cikin tattali da soyayyar juna ni da mijina'., a cewar Anty Uwani, ni kam na amsa da ameen a cikin raina.
☆☆☆☆☆☆
A hankali ya gangara motar shi cikin gareji yayi parking, “Amour, sai anjima, take care" nace “toh Abbu na, take care too" yace “mimm, wai Abbu" dariya kawai na saki wadda nasan tana saka shi cikin nishadi na kashe wayar, yayi murmushi yana bin farar Toyota data shigo cikin gidan tayi parking a daidai inda yayi parking din tashi motar. Saddiqa babbar Yayar su Mubeenah ta fito daga cikin motar, shima fita yayi ya gaidata cikin girmamawa, ta amsa a tsaitsaye tana kumburi kafin ta wuce shi fuu, ya bita da kallo cike da mamaki, matar tana da kirki unlike sauran kannen Mubeenah da ita kanta Mubeenar, duk cikin danginta daga ita sai Shafa'atu ne masu sanyin hali a cikin su, yau kam ko mai ya hau kanta? Ya tabe baki ya wuce wajen maigadi suka dan yi en maganganu ya shige cikin gida. Tun daga cikin falo yake jiyo hayaniyar dake tashi daga can dakin Mubeenah. A can dakin na Mubeenah kuwa akwatuna ne a tsakiyar dakin manya har guda shida, Saddiqa na tsaye a gabansu ta kama kugu tana kallon Mubeenah dake kwance akan gado tana latsa waya, tun kayan barcin ranar data tashi dasu ne a jikinta bata canza ba gashi lokacin har karfe hudu na yamma, gashin kanta ya cukurkude ya cure waje daya, Saddiqa ta saki kugu data kama ta fara tafa hannayenta tana sallallami bayan ta gama sauraren abinda kanwar tata Mubeenah ta fada mata, “Innalillahi.... Mubeenah?! Anya kina da hankali kuwa? Kishiya ake shirin miki amma what?? You are cool with it?? Wai ke wace irin mahaukaciyar yarinya ce Mubeenah??" ta dago ta kalli Yayar tana gunaguni, “ni fa wannan aure za zai yi gaba ya kaini ba baya ba, kina kallon akwatunan daya zube min shake da kaya a matsayin kayan fadar kishiya, 5 millions ya bani in kara jarina bayan haka yana nan yana sake gina mana sabon gida kuma ya min alkawarin zai canza min kayan daki sababbi, bayan haka ita yarinyar da zai aura ta zauna damu anan, na riga da nasan halayenta ciki da bai na tabbata da cewa ba zata taba cutar dani ba balle ‘ya‘ya na ke in fact na tabbata Ibrahim ba wai don yana son ta zai auro ta ba sai don kawai ya bani haushi kamar yadda yake fada tun ba yau ba, to kin kuwa ga menene nawa na yin fushi ko in wani kama bori kamar yadda kike cewa inyi? Kin ganni nan wallahi ko a kwalar rigata, in dai aurene yaje yayi tayi ga fili ga mai doki" bayani take zubawa tun karfinta babu ko digon aya balle comma, yayin da Saddiqa ta sake baki da hanci tana kallon kanwar tata kamar wadda tayi gamo, ta jijjiga kai cike da takaici tace “naji dai ana cewa ke mahaukaciya ce, amma ban taba zaton cewa haukan naki ya kai mataki na farko ba sai yau. Ke don kaza kazar ki, (ta kawo zagi ta lailaya mata), kowace mace tana shiga cikin tashin hankali da fargaba idan za a mata kishiya, amma ke kina zaune hankalinki kwance kina gaya min wai an baki jari kuma za a miki sabbin kayan daki. Kudin banza kudin wofi? Ke don ubanki kin manta yadda muka sha dabi da amaryar Abban mu?" ta kuta, “koda yake kina yarinya dama ya za ayi ki tuna? Ga kuma wata irin kwalwa ta kifaye da Allah ya halitta miki?" ta wani cuno baki gaba, “Na gaya miki yarinyar tana da kirki sam ba halinta daya da sauran matan da kike fada ba..." Saddiqa ta warci kofin dake kan mirror ta saita bakinta ta jefeta dashi Allah yasa ta kauce da sauri, da sai ya dauke mata hakoran gaba biyu, Saddiqa tace “banza mahaukaciya wadda bata san inda yake mata ciwo ba. Kina ta daga murya kina wani fadan cewa kin san yarinya, kin san halinta ko tasan naki halin? Tazo gidanki ta zauna ta gama sanin sirrinki dana gidanki ciki da bai, taga weakness dinki taga komi naki, taje ta gama damarar kwace miki miji daga hannun ki amma kina zaune hankalinki kwance har kina da confidence din daga min wannan bakin naki ki ce wai kin san halinta?" da alamu ko kadan maganganun Saddiqa basa shiga kunnen Mubeenah, tace “ke ce kika kasa fahimtata dai, ni nasan Abinda nake yi. Da wadda ban sani ba ai gwara wadda na sani, ko babu komi yarinyar tana da biyayya sau da kafa, hakan zai bani damar juyata yadda nake so!!" Saddiqa ta dafe kanta da hannuwa biyu kamar zata kurma ihu, Mubeenah ta kalleta cikin mamaki, “wai ni kam don Allah menene damuwar ki akan maganar auren nan, ke za a yiwa kishiya ko ni?" Saddiqa tace “Yi miki kishiya fa kamar yi mana ne, kin sani kamar yadda nima na sani, Ibrahim zama yake yi da ke kawai ba wai don yana jin dadin zama dake ba, kin sani" Mubeenah ta katse ta, “ni nasan Ibrahim yana so na" Saddiqa ta daka mata wata tsawa data sa tashi zaune dangargar akan duwawunta babu shiri, tace “ki min shiru Mubeenah!! Ke ce banza da kika kasa tantance so da dole, idan kika kuskura kishiya ta tako kafarta cikin gidan auren ki wallahi ina mai tabbatar miki da cewa kashin ki ya bushe, idan kin san ma'anar OUT to tsab zata yi waje dake kuma ina mai tabbatar miki da cewa idan har kika sa kafa kika bar gidan Ibrahim to ki tabbata cewa kinyi sallama da aure, I am as sure as hell babu wanda zai yi marmarin daukar ki a matsayin mata a yadda kike dinnan, wallahi Ibrahim kadai ne rufin asirinki" Mubeenah tace “Ibrahim yana so na, ku daina cewa wai baya so na, auren da zai yi babu abinda zai ragu daga son da yake yi min" Saddiqa ta juya ta kara juyawa a cikin dakin kamar wadda take fareti, “idan na gama da case din auren ki I'll make sure to take you to psychiatrist for sure. Amma kafin nan bari inje in samu Haja (mahaifiyar su) babu macen data isa ta shigo gidannan wallahi" ta sa kafa ta bar dakin fuuu a matukar fusace kamar guguwa, Mubeenah ta daga kafada ta koma ta kwanta abinta. Saddiqa na fita taci Karo da Abbu a tsakiyar falo, bata damu da cewa yaji maganganun su ba ko bai ji ba ta shura kafa ta bar gidan. Ya girgiza kan shi a hankali yana murmushi amma fa can kasan xuciyar shi ji yake murmushin yafi mishi madaci ciwo, zuciyar shi kamar ana diga masa ruwan dalma saboda yadda take azalzalar shi da kuna, me yafi ciwo irin kaji cewa matar aurenka bata kishin ka??
~So what did you think about today's chapter?
~Kuna tunanin akwai mata irin Mubeenah a cikin duniyar nan kuwa? Idan akwai, wane irin hukunci kuke ganin ya dace da ire-iren su??
#TeamAbbu
#OneLove
#AnaTare🤝🤝
*♡Jeedderh♡*
[12:22PM, 2/18/2018] +234 703 300 1537: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*
*©°•Jeedderh Lawals•°*
*46*
Na cewa Jalilah class mate dina, “ki wuce hostel kawai, akwai inda zan je" tace toh sai kin dawo. Har ta fara tafiya sai kuma ta juyo tace “naji wani rumor yana yawo a cikin class dinmu, wai zaki yi aure?" na dan jijjiga mata kai ina murmushi, tace “amma gaskiya ban ji dadi da baki fada min ba" nace “sorry, auren ne kawai za a daura kin gane? Shi yasa ma ban wani yi shela ba saboda ina makaranta ma za a daura" ta matso da bakinta saitin kunnena cikin rada, “amma naji ana cewa wai wani lecturer ne anan zaki aura, da gaske ne??" na zaro ido cike da mamakin yadda aka yi zancen ya isa garesu, koda yake dama an ce zancen duniya baya buya. Nace mata “rumors ne kawai amma ba haka bane" tace “idan ma hakan ne meye na wa ko na mutane a ciki? Allah ya baku zaman lafiya mai daurewa" na mata murmushi ina kokarin boye dariyar data ciwo ni don nasan magana ce ta fada min, nace Ameen. Ta juya ta tafi abinta. Na duba agogon hannuna naga karfe sha daya ne da rabi lokacin, da sauri na dauki hanyar da zata kaini ofishin Abbu don nasan yana can yana jira na, ranar juma'ah ce ga masallaci ga kuma cinkoson ababen hawa. Na tura kofar office din na shiga fuskana dauke da murmushi, duk lokacin da zan ga Abbu sai in dinga jin wani irin doki da farin ciki a cikin raina kamar wadda ta shekara bata ganshi ba, alhalin duka duka jiya alhamis har karfe tara na dare muna tare dashi, ranar ta Jumma'ah da safe wayar shi ta tashe ni daga barci, muka gaisa ya maimaita min how eager he was to have me as his, farin cikin da yake ciki saboda samuna da yayi a cikin rayuwar shi. A gare shi wadannan kalmomin kamar wasu routine words ne da ya saba fada min a duk sanda muke tare, a gare ni kam they were far more than golden and diamond words, suna saka ni cikin tsananin farin ciki da jin dadi, suna hana duk wata damuwa da bacin rai samun matsuguni a cikin raina, they were my remedies. Ya juyo daga gaban book shelves din dake kusa da desk din computer dinshi, wani tattausan murmushi ya sakar min da suka sa naji alamun butterflies na yawo a cikina, sanye yake da wandon jeans blue da knit shirt mai kama da sweater, irin shigar da naga samarin zamanin nan nayi kenan a wannan lokacin, shima sai ta maida shi kamar wani saurayin bayan kyawun data mishi, Abbu yasan kan fashion kamar wani fashionista shi yasa ko wane irin kaya ya sanya suke haska shi. Ya maida littafin dake hannunshi cikin jerin littafan dake cikin shelves din, ya juyo gareni gaba daya yana murmushin nan nashi dai, kallona yake kamar wanda zai tsuke ni ta cikin idanuwanshi, it was so intense and disconcerting sai dana ajiye idanuwa kasa ina jin kamar kasa zata tsage in shige, yace “tun dazu nake jiran ki yanzu nake shirin biyawa ta library din in duba ki" nace “ban kula da cewa lokaci yaja bane, sorry!" ya dauki wata jaka mai kama da box dinnan akan tebur ya miko min, nasa hannu na amsa ina kallon shi cikin alamun tambaya, ya dan jingina jikinshi da teburin yace “akwai reception da aka hada mana ranar Sunday, kayan da zaki saka ne" na bude jakar na kalli kayan ciki, shadda ce bugaggiya ruwan kasa mai haske sai jaka, takalmi, da gyale su kuma dark brown kalar zaren da aka yi amfani dashi wajen yin surfani, na kara kallon shi nace “ranar Monday fa zamu fara exams dinmu" yace “ba zai taba karatunki ko jarabawar ki ba I promise, ni kaina ban san da zancen ba sai da suka riga suka shirya komi sannan suka sanar dani. I don't want to disappoint them, please help Nafeesah kinji?" yadda ya wani rausayar da kai yana kallona pleadingly, who m I to say no to him a yadda yayi dinnan taking my breath away?? Sai kawai na girgiza kai ina murmushi, nace “Allah ya kaimu ranar" yayi murmushi “Ameen Amour.... Mine" na sunke kai a cikin hijabina, ya wani kuta, “just wait till tomorrow, war haka kin zama tawa, mallakina ta har abada, wannan kunyar taki sai nasa kin neme ta kin rasa" ya saki murmushi mai sauti, “Allah ya kaimu goben nan dai, I really can't wait baby" na kara kanannade fuskata a hijabin, jin abin nake yi kamar a mafarki, mafarkin ma wanda ba zai zama da gaskiya ba, wai goben ne daurin Auren mu? Oh, zan zama matar Abbu, Abbu na wanda so da qaunar sa suka mamaye jini da jijiyoyin jikina, na kauda tunanin daga cikin raina bana so in fara fayyace matsayin da gobe take a gare ni don nasan ba zan gama da wuri ba. Ya dauki key din motar shi muka fita, na jira ya rufe office din kafin muka fara tafiya a hankali zuwa inda ya ajiye motar shi. Ya bude motar ya shiga ciki ya juyo ya kalleni, “sorry, bazan iya maidaki hostel ba saboda sai na biya na dauki su Abdullahi sannan mu wuce masallaci" nace “babu komi, a gaida su" ya gyada kai, “zan kira ki anjima" na maida mishi murfin motar na rufe, ya mata key ya tafi ina daga mishi hannu, sai dana ga fitar shi sannan na daga kafa da niyar tafiya. Kamar daga sama naga tsayuwar mutum a gabana, naja baya a dan tsorace har ina dafe kirji ina jan salati, Matar nan da muka hadu da ita a ofishin Abbu ranar nan ta bayyana a gabana, da alamu shigar rashin mutunci da na ganta da ita ranar a jininta take don kuwa lokacin ma irinta ce a jikinta, zan iya cewa ta ranar tafi ta waccan lokacin bayyana surar jiki ma. Hararata take yi tun karfinta da gwala-gwalan idanuwanta da suka sha uban eye shadow da girar kanti in ka ganta kamar wata doll. Nima na mayar mata da kwatankwacin hararar da take jifana dashi, “Malama lafiya zaki tare min hanya?" ta kama kugu tana wani jijjiga jiki, “ina so ne in fada miki ki rabu da Ibrahim" nayi fuskar alamun tambaya “me yasa?" ta dan daga murya, “saboda nawa ne! Na sha alwashin babu wadda ta isa ta aure shi muddin ina raye" nace “da alamu baki samu labarin cewa gobe ne daurin auren mu dashi ba, na tabbata da kin sani kam da ba zaki tare ni a hanya kina barking kamar tsohuwar karya ba" a girmame matar ta girme ni nesa ba kadan ba, sai dai ni a rayuwa na sau daya zaka zubda daraja da kimarka a idona, abin na matar yayi yawa, ko a lokacin da nayi shirmen son Muneer ban taba tunanin zan yi kwatankwacin abinda take yi yanzu ba, bin kan namiji yana wulakanta ni kamar karya amma in ki in hakura har ta Kai ni ga bibiyar wadda zai aura ina threatening dinta. Fuskar ta tayi looking so pale saboda maganar da nayi, “ni kika kira da karya? just wait, in har ina raye sai na mayar dake abin kwatance, sai na muzanta ki fiye da kare, I'm warning u, ki fita daga rayuwar Ibrahim kafin in mayar dake abin kwatance!!" na daga kafada, “I'm not stopping you from doing whatever you will do, kawai abinda nake so yanzu shine ki matsa ki bani hanya in wuce" ta hasala iya hasala, hannu ta daga kamar zata mare ni, kallonta nake yi kamar wata kayan kashi a yatsine, ita da kanta ta janye hannunta ta maida shi kasa, nayi murmushin mugunta nace “kece kike ta shirme kina bin namijin da yake kin ki, tunda yace baya yi let him be, ana so dole ne malama?" ta wani zare ido tare da buga tsawa “ke...!!" nayi saurin katseta kafin ma ta gama fadin abinda tayi niyar cewa ta hanyar zare ido nima, nace “malama kin ganni nan ban yi kama da matan da threats dinki zasu yi tasiri a kan su ba, kiyi duk abinda zaki yi wanda kike ikirarin mallaka ba zaki taba mallakar shi ba saboda ba don ke aka yi shi ba, a shawarce zan gaya miki ki fita daga rayuwar shi, Idan kuma kin ki ji sai dai kiyi mutuwar da kike ikirarin yi! Abbu ne kamar na aure shi na gama" naja tsaki tare da zagayawa ta gefenta ta wuce abuna ina muttering kalmomin dani kaina bansan me nake fada ba duk don in yi provoking dinta, na kuwa yi nasara. Ina bada baya naji sautin karan data saki cike da takaici, na kuwa saki murmushi kamar zan sheke da dariya.
Washegari da misalin karfe daya aka daura auren a babban masallacin juma'ah dake garin Malumfashi. Muna zaune a dakinmu Ni'imah ta kawo wata yarinya tana min kunshi wanda hakan umarnin Abbu ne, text dinshi ya shigo wayata. Na mika hannu na da nake jin shi kamar ba a jikina yake ba na dauki wayar, kai gabadaya ma sauran sassan jikina haka suke tunda garin ranar ya waye, ina ji Niimah da Firdausi suna ta hira amma na kasa saka musu baki duk da cewa rabin hirar a wajen tsokanata ne. Text din cewa yayi, “Alhamdulillah. Yanzun nan aka shafa fatiha, kin zamo tawa ta har abada. Ina taya junanmu murna da farin cikin mallakar junanmu, Allah ya bani ikon rike ki cikin amana da kulawa Nafeesah" sai kuma wani da yace, “Wannan ranar rana ce da ban taba tunanin zata Riske ni ba, ranar dana mallaki abinda ban taba kawowa raina zan mallake shi ba. Jina nake kamar wani sabon halitta saboda tsananin farin cikin da nake ciki wanda na kasa misalta shi, Nafeesah kina da gurbi mai matukar girma da fadi a cikin zuciyata, na roki Allah mai Girma akan ya bamu zaman lafiya mai dorewa. You've Completed My Puzzled and Shattered Life, I really Cherish You Nafeesah" naji hawaye sun cika min idanu, nayi saurin runtse idanun ina kokarin maida hawayen, Allah abin godiya da Girmamawa, wai ni ce yau na zama matar Abbu?? Naji ina narkewa kamar wata jelly akan kujerar da nake zaune, na tabbata da ace ina tsaye ne da sai na fadi. Rangadediyar gudar da Ni'imah ta rangada ce ta dawo dani cikin tunani na, guda take tun karfinta da waya a hannunta ta hau kiran waya tana bada albishir din an daura aure. Wayana ya shiga kara na daga, Daddy ne. Cikin rawar hannu na daga, “Uwata! Amarya!!" abinda na fara dokar kunnena kenan, na kasa magana sai kai dana jijjiga, yace “Nagode Allah da yasa naga wannan rana, ranar dana damka amanar ki a hannun wanda na tabbatar zai rike ki dari bisa dari, dama babu burin duk wani uba na kwarai daya wuce wannan. Yau dai kin zama matar Ibrahim, kin fita daga karkashin kulawar mu kin koma karkashin shi, yanzu shi zai yi sanadiyar ki zuwa gidan Aljannah wadda nasan babu haufi zaki sameta da yardar Allah uwata, Allah ya miki Albarka, Ya Albarkaci Rayuwar Auren ki, Allah ya baku zuriya Dayyiba!" muryar shi tayi kasa can kamar wanda yake so yayi kuka, ni kam kasa daurewa nayi kawai na fashe da kuka, gabadaya wani iri nake jina a tunanina idan nayi kukan zan samu sanyin zuciya. Ya shiga lallashina har na samu nayi shiru kafin ya min sallama. Yana kashe wayar kiran Mommy ya shigo, itama dai Addu'ah ta min kamar yadda Daddy yayi, zuciyar Mace mai rauni, sai tasa kuka, nima kukan nake yanzu sosai su Ni'imah na aikin bani hakuri, ina ji daga wayar Anty Uwani da muryar wasu mata suna ba Mommy hakuri, Anty Uwani cikin fada tace “sai kisa hankalinta ya tashi ai, gashi nan itama kin sata kuka, ina amfanin haka?" tace “kukan farin ciki ne" tace “ai godiyar Allah ya kamata kiyi ba wai kuka ba, shima Abban nata yanzu na baro shi a waje yana share kwallah Allah yasa ba ita ya kira yana kukan ba.... Wannan ai sai ku sanyayar mata da gwiwa...." daga haka dai suka kashe wayar. A hankali nima nawa kukan ya fara yin kasa har ya dawo shessheka kafin nayi shiru ina ajiyar rai. A ranar dai har ba zan iya lissafa iyaka mutanen da suka kira ni suna taya ni murnar yin aure ba, tun daga kan abokaina da yan uwa har wasu daga cikin abokan Mom. Da yamma sai ga Ramlah ta dira a Kanon kamar daga sama, muka yi tsalle muka rungume juna ni da ita muna ihun murna, watanni biyar ciff tunda muka rabu da ita bamu sake haduwa face to face ba sai dai a Video call. Muka zube akan gado muna maida numfashi daya bayan daya, kallona take tun daga sama har kasa ta kyalkyale da dariya, “kaga Amarya a gidan Ibrahim Galadanchi, kin ga wani kyau da kika yi kuwa??" na kai mata duka ina dariya, “meye haka zuwa babu sanarwa?" tace “surprise, dazu na dawo har mun yi hutu abinmu" nace “kun huta ku kam" nan muka shiga hirar yaushe gamo, tana nan tare dani har aka kira sallar magriba, ganinta ne yasa na warware har na samu naci abinci. Nan dai ta min sallama ta tafi akan cewa zata dawo Washegari, bayan na rakata zuwa bakin kofar hostel din na koma daki nayi sallar isha'i, bayan na gama na zauna nayi ta jero addu'o'i game da neman albarkar Allah da zaman lafiya a cikin sabuwar rayuwar da nake tunkara a cikin rayuwata. Abbu ya kira ni yace yana jirana a parking lot inda muka saba tsayawa, na tsinci kaina cikin faduwar gaba da sanyin jiki, cikin sanyin jikin na tashi na gyara zaman hijabin jikina na sauka kasa. Jingine yake da motar shi yana danna wayar shi, sanye yake cikin shadda ruwan Makuba yau kam har da hula a kanshi, akwai wadataccen haske a wajen hakan ne ya bani damar ganin fuskar shi sosai kamar cikin rana. Tunda na hango shi naji kafafuna sun fara hardewa, ban taba tsintar kaina cikin fargaba da tsoron fuskantar Abbu ba tunda nake a rayuwata sai ranar, da kyar na iya karasawa gaban shi ina maida numfashi kamar wadda ta sha gudu, babu abinda yayi motsi a jikinshi sai idanun shi da suke kare min kallo tun daga sama har kasa, kafafuna ba zasu taba iya daukana a haka ba sai nima na jingina da jikin motar ina kallon zara-zaran yatsun kafar shi da suka fito ta cikin kyakkyawan bakin budadden takalmin kafar shi yana ta sheki.....
~Yau dai Allah yayi Dare Gari ya waye An Daura Auren Nafeesah da Abbu, Woah!
~Me zaku ce game da Shafin yau??
~Lots Of Love and Hearts
#TeamAbbu
#OneLove
#AnaTare...