A tsakiyar term su inna suka zo min visiting suma. Sadauki ne ya tuko su amma babu Baffa kuma babu Ummah sai Asma'u Mama da su Rumaisa. Nace "ayyah, Inna da kun sani kun taho da Ummah, nayi missing dinta" babu wanda yace dani ci kanki a cikin su. Ranar nayi murna har na rasa inda zan saka kaina, su kuma suna ta yimin dariya. Suka zo da abinci kula kula muka hadu muka ci tare ana ta hira, amma Sadauki tunda muka gaisa ya koma mota, sai da muka gama cin abincin sannan na zuba na kai masa, ina mika masa kuwa inna ta kira ni in dawo haka na taho bamuyi magana ba. Sai da zasu tafi ya dauko bakar leda ya miko min yace inji Ummah, garin karba naji ya saka min takarda a hannu na sai nayi sauri na saka ta cikin aljihuna, yayi murmushi kawai ya daga min hannu suka tafi.
Bayan na koma hostel ina jejjera kayan dasu Inna suka kawo min, na duba ledar da sadauki ya bani naga dambun nama ne da yaji attaruhu da tafarnuwa, just the way I liked it. Nayi murmushi na dauko takardar daya bani na bude ina karantawa.
My dearest star.
Am sorry ba mu sami damar magana ba, but ganin kina lafiya kadai ya ishe ni farin ciki. Ga dambun nama nan inji Ummah tana gaishe ki.
PS
I love you.
Na dora takardar a kirjina ina jin wani iri. Na sani cewa akwai wani abu a tsakani na da Sadauki amma bai taba furtawa direct ba sai yau. And it feels great. A hankali nace "I love You too Aliyu".
Haka rayuwa ta cigaba da kasance wa, har cikin ikon Allah muka shiga third term na js1, a lokacin shi kuma Sadauki suke zana ssce dinsu. Kullum in naga yan ss3 dinmu suna exam sai inta yiwa Sadauki addu'a, Allah ga Sadauki nan, Allah ka bashi sa'ar exam din nan. Wannan term din gaba daya baizo min visiting ba. Sai ranar da mukayi hutu suka zo daukana shida Baffa, ko dan ma kwana biyu ban ganshi ba? Sai naga ya kara girma ya kara kyau.
Naje na shige gaban mota na barshi da daukan kaya yana sakawa a booth, Baffa kuma ya tafi zaiyi signing dina out. Na dauko powder da lipstick ina shafawa wai duk kyalliyar zuwa gidan ne, sai kawai naji kamar ana kallona, nayi sauri na kalli mirror muka hada ido dashi, ya tsaya da jaka a hannunsa kawai ya zuba min ido ta mirror, muna hada ido sai kuma kunya ta kamashi yayi saurin dauke kai kunya a rubuce a fuskarsa. Dariya kawai nayi wai namiji da kunya.
A cikin hutun ne muna gida na fara period. Ranar ina kwance a dakin Ummah ina tashi kawai naji danshi a kasana, na saka hannu na shafa kawai sai naga jini a hannu na, na kalli Ummah naga itama ni take kallo. A lokacin Sadauki yayi sallama nayi sauri na koma na zauna ina boye hannu na a baya na, ya tsaya daga bakin kofa yana kallona yace "ke kuma lafiya kike rarraba ido kamar bera a buta?" Ummah tace "ina ruwan ka da ita, tsabar sa ido me kazo yi ma gida a yanzu?" Ya shigo yana cewa "babu aiki a garejin, shine nazo gida in huta. Diyam tashi ki bani abinci" na kwabe fuska kamar zanyi kuka Ummah tace tana nuna masa kofa "tashi ka fita" yace "Allah ya baku hakuri, daga tambaya?" Sai ya mike ya fita yana waige na.
Yana fita Ummah tace "tashi in gani" na mike, tace "kin san menene?" Na gyada mata kai. Tabbas nasan jinin haila da hukunce hukuncen sa tun a islamiyya, na kuma kara sani a kansa a makarantar boarding. Akwai yan ajin mu da suke yi, kuma seniors din mu ma sunayi dan sukan aike ni wajen wata matron in siyo musu pad, amma ban taba tsammanin zaizo gare ni ba ni Diyam, at least not now, ni ban shirya girma ba gaskiya. Ummah ta saka ni naje drawers dinta na dauko wasu undies data siyamin da niyyar in zan koma makaranta zata bani, ta saka na dauko pad itama a dakinta takoya min yadda ake sakawa sannan tace min inje toilet in gyara kaina. Ina dawowa na tarar ta gyara inda na bata a kujerar ta, sai kuma ta zaunar dani ta sake yi min bitar wankan tsarki da sauran abubuwa da suke shafi haila, ta kama kunnena tace "babu wasa da maza daga yanzu, babu wasa da Sadauki" nayi kyar kara sannan ta cika min kunne na. A lokacin Sadauki ya shigo yace "ya naji ana ambatar sunana?" Sai kuma ya kalli irin zaman da mukayi yace "hirar me kuke yi ne haka?" Na tabe baki zan saka masa kuka ya juya yace "na fita, in tayi tsami zanji".
Sai da muka gama maganganun duk da zamuyi da Ummah sannan tace min in tashi inje in gayawa Inna. Na zaro ido nace "Inna? Ni bazan iya gaya mata ba" tayi dariya tace "ai kuwa sai kin gaya mata. In baki gaya mata ba ke da ba'a gida kike zaune ba ta yaya zata sani?" Nace "dan Allah Ummah kije ki gaya mata" tarike baki tace "ni? Babu ruwana, ke zaki gaya mata da bakin ki" naji duk hankalina ya tashi, sai tace "bara in baki shawara. Kinga, yanzu ki tafi dakin ta, ki saka pad a jikin pant ki ajiye akan gado inda tana shigowa zata gani. Da kinji ta taho sai kiyi sauri ki shiga toilet ki buya".
Haka nayi kuwa, na ajiye akan gado sai da naji ta taba kofa sai nayi sauri na shige toilet. Na jima aciki,a tunani na ta fita sai na fito ai kuwa sai gata azaune a kan gado ta tasa pant dina a gaba, nayi sauri zan koma toilet tace "ke! Zo nan" na dawo ina karkarwar jiki na tsaya. Ta nuna pant din tace "wannan na waye?" A hankali nace "nawa ne" sai kuma tayi shiru tana kallona sannan tace "yaushe kika fara?" Nace "dazu" sai ta zaunar dani itama ta dora daga inda Ummah ta tsaya a nasiha da bayanan sabon yanayin dana samu kaina a ciki. Sai data gama sannan tace "saura kuma in sake ganin kun rike hannu ke da wancan bakin munafikin".
Muna gab da komawa hutu exam din su Sadauki ta fito. Alhamdulillah, ya samu nasara sosai. Duk da dai ba distinction ya samu ba amma ya samu credits a duk subjects din daya kamata. Mukayi murna sosai. Sai da jamb ta fito sannan murnar mu ta koma ciki, yayi kokari nan ma, sai dai bai samu points din ake bukata ba a mechanical engineering wanda shine abinda yake so ya karanta. Ranar haka ya wuni ransa babu dadi, ni kuma harda kuka na zauna inayi masa, Ummah kuwa dariya tayi tace "wa kuka taba ganin ya samu abinda yake so lokaci daya? Kuje jami'ar ku tambayi daliban kuji wadansu da yadda suka samu admission din. Ko kuma ku samu mutumin daya ke da daukaka ya baku labarin yadda ya samu daukakar tasa. Babu wani abu mai kyau da ake samun sa cikin sauki".
Baffa yana duba takardar yace "babu komai Sadauki, kar ka damu, akwai next year ai insha Allah sai ka sake gwadawa. In the meantime kuma zan nema maka computer school kayi diploma kafin ka sake jamb din".
Ayi hakuri da wannan.
One love 馃槝鉂わ笍 DIYAM 鉂わ笍
By
Maman Maama
Episode Eighteen: Saghir
Assalamu alaikum masoya littafin Diyam. Kafin mu cigaba zan danyi wani jan hankali a game da masu cewa in bar labarin da muke akai yanzu in koma gurin Bassam da Diyam. Ina so ku fahimci wani abu, shi littafin nan gabaki dayansa labarin rayuwar Diyam ne da irin wahalhalun da tasha har ta kai stage din data hadu da Bassam, wanda kusan shine karshen labarin. Na fara ta can ne saboda ina so ku samu glimpse of yadda rayuwa ta juya mata saboda in kara increasing curiosity dinku.
PLEASE stop asking me to summarize and get back to labarin Bassam. This story is not about Bassam but about Diyam.
Shekara tazo ta wuce. Lokacin na cika shekaru goma sha uku shi kuma sadauki yana sha tara. A cikin ta babu abinda ya ragu sai ma karuwa da abubuwa suke yi a tsakani na da Sadauki, musamman yanzu da yake jin sa ya kara zama saurayi tunda gashi har ya kammala diplomar sa a computer science. Ya sake zana jamb, kuma wannan karon yaci abinda ake bukata din, sai dai kuma cikowar dalibai masu neman admission da kuma rashin hanya yasa ya gaza samun admission din, Baffa yaji takaicin wannan abin dan yana ganin hakan kamar gazawa ne daga bangarensa a matsayinsa na uba.
Ni kuma a bangare na, na kammala jss2 lokacin ina da shekara goma sha uku amma ina nan jiya i yau, babu abinda na kara a girman jiki sai dan tsaho da kuma hankali. A lokacin kam zan iya cewa duk wanda yake tare damu ni da Sadauki yasan something is going on, including Baffa, Ummah da Inna. Baffa baice komai ba, haka ma ummah, basu taba encouraging din mu ko discouraging din mu ba. Babban problem din, kamar yadda duk muka yi tsammani shine daga gurin Inna dan sosai take nuna kiyayyar ta ga tarayya ta da Sadauki.
Hutun da muka zo na third term din jss2, ina shiga palon Ummah hannuna rike da Asma'u da take ta murnar gani na, na tarar da akwati a ajjiye a kofar palo. Bayan na gaisheta nace "Inna wannan kayan fa?" Ta hade rai tace "naki ne, hutu zaki tafi" naji zuciyata ta buga nace "hutu Inna? Ban gama ganin ku ba fa ina zan tafi hutu kuma?" Ta harare ni tace "gidan Alhaji Babba zaki tafi, in muna son ganin ki mu zamu zo mu ganki" nayi ajjiyar zuciya a boye, dan dai sharada? Nasan Sadauki ko da adungure zai je ya ganni. Kwana na daya a gida na tafi sharada. Ni da Rumaisa ne zamu je muyi hutu a can yayin da Inna ta yi mana rakiya. Rumaisa tana ta murna saboda ita kam tana son zuwa gidan Alhaji Babba. Ni kuma ina yake saboda kar Inna ta harbo jirgina na plans din da mukayi da Sadauki.
Now, let's talk about Alhaji Babba da family dinsa.
Kamar yadda na fada Alhaji Babba shine babban yayan su Baffa, shi ya fara zuwa Kano neman kudi kuma a lokacin yafi dukkansu dukiya, dama baffan mu ne baya. Allah ya jarrabi Alhaji Babba da mugun son yaya maza sai kuma ya hana shi su, wannan yasa ya kasance mai aure aure duk a tunanin sa da burinsa hakan zai saka ya samu cikar muradinsa. Matarsa ta farko yar uwa ce daga Kollere, ya daya ta haifa masa Adda Zubaida, daga nan bata sake haihuwa ba sai ya auri Hajiya Babba wadda tashin farko ta haifa masa muradinsa na 蓷a namiji wanda muke kira da hamma Saghir. Hajiya Babba jinin sarautar kano ce, hamshakiyar macece mai mulki da izza wadda hatta kishiyoyinta inka gansu a gabanta zaka iya dauka cewa yaranta ne. Bayan shi ta sake haihuwar mata biyu, Aysha da Salma. Daga Hajiya Babba kuma sai Hajiya Yalwati wadda tafi duk sauran matan yawan yaya kuma wannan shine kadai abinda yake zaune da ita a gidan. Hajiya Yalwati kawar Inna ta ce dan haka duk sanda muka je gidan a dakinta muke zama, kuma nima saboda babbar kawata a gidan, Murja, yar Hajiya Yalwati ce dan haka nima na zama yar dakinta. That plus daga ni har Inna babu wanda yake iya jurar mulkin Hajiya Babba. Sauran vacant space din guda daya kuma na mai rabo ne, wannan ta shiga wannan ta fita.
Hamma Saghir shine da daya tilo da Allah ya bawa Alhaji Babba, dan haka zama bayyana cewa dan gata ne bata lokaci ne. An haife shi tun kafin Baffa na yasan zai auri Inna ballantana a haife ni, dan a lissafi ya bani shekaru goma sha shida da watanni. A kullum idan naji mata suna lissafa siffofin mijin da suke so su aura sai inga kamar lissafin kamannin hamma Saghir suke yi, fari, dogo, kyakykyawa, mai saje, marar son surutu, mai kudi, mai class blablabla. Hamma Saghir is all that and more. Labari ya zo min cewa makarantar da hamma Saghir yayi ma kanta daban take da ta sauran yaran gidan dan Alhaji Babba cewa yayi "a samo min makarantar da yayan masu kudi suke zuwa a garin nan, ita zan saka Saghiru" a haka yayi primary da secondary dinsa, sannan aka saka shi a buk yayi degree a economics ya fita da pass. Alhaji Babba yace "ba wani abu, dama an saka ka a makarantar ne saboda ka samu ilimin juya dukiya ba wai dan ka nemi aiki da takardun ka ba". Sai kuma Alhaji Babba yayi masa irin abinda Hardo yayi masa shima. Ya debi dukiya msi yawa ya bashi yace "tafi ka nemi arzikin ka" Saghir ya gyara zama yace "China zan tafi Alhaji, tunda can ne cibiyar kasuwanci ta duniya a yanzu. In naje sai in nemi Company in saka hannun jari a ciki. Maybe kafin shekara sai kaga nazo na bude nawa Companyn"
Haka ya shirya aljihu fal kudi ya tafi China, daga nan ba'a kara jin labarinsa ba har sai da ya shekara uku sannan sai gashi ya dawo daga shi sai jakar kayan sa yace "yan damfara na hadu dasu Alhaji, gaba daya kudina sun salwanta da kyar na tsira da kudin jirgi na dawo gida" Alhaji Babba yace "kasuwanci ya gaji haka dama, yau riba gobe faduwa hakan kuma ba zai saka mu karaya ba" sai ya debi wadandu kudaden ya kuma bashi, shi kuma ya karba yace "Dubai zan tafi wannan karon inke saro kaya ina aikowa dasu gurinku kuna siyar min". Wannan karon ma tunda ya tafi ba amo ba labari ko waya babu, amma sai iyayen suke boyewa kullum suna nuna kamar yanayi musu waya "abubuwa ne suka yi masa yawa amma yace yana gab da zuwa gida". Yazo gidan kuwa bayan shekara biyu, sai dai wannan karon ko akwatin kayansa bai dawo dashi ba ballantana kudi "Dubai bata karbe ni ba Alhaji. Kudi na gabaki daya sun salwanta ba bu abinda ya rage a hannu na" Alhaji Babba yace "kasuwanci bai karbe ka ba Saghiru. Dole sai mun zauna munyi maka adduoin neman sa'a sosai. Kuma ina kyautata zaton akwai nasara sosai a rayuwar ka shiyasa kake samun tangarda" Hajiya tace "musamman ma shi da yake da tarin makiya, gaskiya kam sai an hada da addu'a".
Bayan an gama rarraba wa malamai kudi sunyi adduoi, sai kuma Alhaji yace "gwara ka zauna a kasar nan saboda muke ganin abinda kake yi muna kuma baka shawara" amma sai Saghir yace "gaskiya Alhaji ko zan zauna a kasar nan to ba'a Kano ba, saboda anan an saka min ido dayawa". Haka rayuwa ta cigaba masa, yau yana wannan garin gobe yana wancan duk da sunan neman kudi, in kudin hannunsa sun kare ya dawo Kano ya karbi wadansu ya kara mai.
Tunda nake bazan iya cewa ga ranar da hamma Saghir yazo gidan mu ya gaishe da Baffa wanda yake kanin babansa ba ballantana Inna da take cousin din babansa kuma matar kanin babansa. Ni kaina ganin da nayi masa a duniya a lokacin bashi da yawa sai dai a jikin katon hoton sa dake kafe a main palon gidan.
A ranar da muka je gidan, kamar yadda muka saba, part din Hajiya yalwati muka fara zuwa muka ajiye kayayyakin mu muka huta sannan muka fita muka zagaya muka gaishe da sauran matan gidan. Bayan mun dawo palon Hajiya Yalwati ne Inna take tsokanar Murja "Murja ya na ganki a daki ne yau kamar matar kulle? Tunda muka zo gidan nan banga kin fita ko babban palo ba?" Hajiya Yalwati tace "uhmm ina zata fita taje, boss din su yana gidan? Tun safe nace musu suyi zamansu a daki kar wadda ta fita in ba haka ba sai kiga an dawo da kumburarriyar fuska ya kama su ya mara, komai akayi ai shi laifi ne a wajensa, magana ma mai karfi in sunyi cewa zaiyi sun hana shi bacci duk ya hada su yayi musu duka. Kuma ban isa inyi magana ba" Inna tace "wai Saghir kike nufi? Yazo garin kenan. Oh ni yaushe rabon da inga Saghir?" Kamar da hadin baki kuwa sai gashi ya shigo palon. Ya dafa kujera daga tsaye yace "Hajiya barka da gida" Hajiya Yalwati tayi yake tace "Barka kadai Saghir, anzo lafiya" yace shortly "lafiya lau" sai ya juya zai fita, Hajiya Yalwati tace "ga gwoggonka fa, gwoggo Aminan baffa Usman" ya dan juyo yana shafa kai yace "lah gwoggo ai ban lura ba. Ya gida? Ya Baffa?" Inna tayi murmushi tace "lafiya lau Saghir, ya kasuwa? Allah yayi jagora" yace "ameen" sannan ya fice ba tare daya ko kalli inda muke zaune ni da Rumaisa muna kokarin gaishe shi ba.
Yana fita Inna ta juya tana kallon Hajiya Yalwati tace "kai masha Allah. Saghir ya zama babban mutum sosai" Hajiya Yalwati ta tabe baki tace "eh fa. Yo mutumin da yake kokarin cika shekara talatin a duniya ai kuwa dole a kira shi da babba. Ni in dai gatan gaskiya kuke yi masa ma aure ya kamata kuyi masa maybe ko ya haifa muku jika namiji" Inna tayi dariya tana tafa hannu, Hajiya Yalwati tace"a'a to bai isa auren bane ba? Ko dai kuyi masa aure wallahi ko kuma ya dauko muku abin kunya dan duk abinda yake aikatawa a garuruwan da yake zuwa muna sane, in munyi magana kuma ace hassada muke yi masa" Inna ta watso mana harara ni da Rumaisa, sum sum muka tashi muka basu guri dan munsan ma'anar hararar.
Muna fita Rumaisa tace "zo mu tafi palon Hajiya Babba" na makale "ke ni bana son zuwa gurinta tayi ta mulka mutane tana kallonsu sama sama" ta kuma jan hannu na "dalla can kizo muje, wani abu zan nuna miki". Muka je muka sameta a dan karamin palonta tana kishingide yar aikinta tana yi mata tausa. Muka sake gaisheta sannan muka zauna a gefe muna kallon tv. Muna zaune ya shigo, yana shigowa na kama hannun Rumaisa da niyyar ta tashi mu basu guri amma sai ta rada min "ki bari muyi kallo" na koma na zauna na zubawa tv ido. Ya zarce gaban Hajiya ya zauna. Tace "kaje duk ka gaishe su?" Ya yamutsa fuska yace "naje" sai kuma yace "Alhaji har yanzu bai fito bane?" Tace "na gaya maka ai baya jin dadi ya kwanta. Wani abu kake bukata?" Yana shafa kai yace "dama kudi nake nema, akwai wasu kayana da aka kawo min daga porthercout shine nake so inje in karbo" tace "kaje drawer ta ka gani ko zasu ishe ka" ya mike zai tafi Rumaisa tayi sauri ta gaishe shi, ya dan bata rai yana kallon ta sannan ya amsa, wannan yasa nima na gaishe shi, ya amsa a ciki ciki irin irritatingly dinnan. Hajiya tace "ba ka gane Diyam ba" ya juyo ya kalle ni yana yamutsa fuska yace "bangane taba. Yar uwar mu ce?" Hajiya ta danyi dariya tace "Diyam fa, babbar yar baffan ka Usman" ya danyi shiru sannan yace "ohh, that little baby da akayi jegon ta anan? Wannan mai cika mana gida da kuka?" Hajiya tayi dariya tace "ita fa" ya dan karkata kai yana kare min kallo sannan yace "sam ban gane ta ba. Bata kama da iyayenta" Hajiya tace "ai kuwa Diyam kamar su daya da innar ta, dan karamin jikin ne dai ta dauko na babanta" ya sake kallo na yace "no Hajiya, gwoggo Amina ai kyakykyawar bafulatana ce, wannan kuma sai naga tana min kama da bararoji" gaba dayan mu sakin baki mukayi muna kallon sa har hajiyan, tace "bararoji kuma Saghir? Diyam kuwa ai kowa yana yaba kyanta" ya sake kallona sannan ta tabe baki yace "still, ni ban gani ba".
Another character added. Saghir. Tell me your feelings about him[1/18, 9:45 PM] Zuraiyah Zuzu 馃専: 鉂わ笍 DIYAM 鉂わ笍
By
Maman Maama
Episode Nineteen: Inna
Haka ya shige daki ya bar mu da budadden baki. Na kamo hannun Rumaisa muka fito da sauri.muna fitowa nace "what? Lallai ma mutumin nan" Rumaisa tana murmushi tace "ya hadu ko? Shi yasa nace miki kizo muje mu ganshi" nace "au wai kina nufin saboda mu ganshi kikajawo ni dakin nan? Meye abin kallo a gurinsa? Wai dan wulakanci nice bararoji" Rumaisa tayi dariya tace "au wai haushi kikaji? Ke baki san wasa ba? Wasa fa yake miki dallacan" na bata rai nace "it doesn't look like wasa yake min, har cikin ransa abinda yake nufi kenan" Rumaisa ta bagarar da maganar tace "to ya kika ganshi? Ya hadu ko?" Na tabe baki nace "ko kusa da haduwa baije ba" tace "ko dai don idonki ya rufe, Sadauki ya tare gaba ya tare baya" nayi murmushi ina jin sanyi a raina nace "yanzu kika kamo hanya yar gari" ta bani hannu muka tafa. Rumaisa ita kadai ce wadda nake zama muyi hirar Sadauki sosai da ita, tasan komai akan yadda muke ji a zukatan mu. Muka samu guri muka zauna, na bata labarin tsarin da mukayi da sadauki na cewa zai ke zuwa zance gurina a matsayin saurayina. Ta rike baki tana zaro ido tace "Diyam? Ba kwajin tsoro? Ba kya jin tsoron a kama ku?" Nace "relax. Kinsan dai gidan nan akwai yammata da yawa ko? Kuma duk suna fita zance so babu wanda zai gane, he will be just one saurayi among others, kuma I will make sure duk wanda yasan fuskarsa bai ganshi ba, ballantana kadan ne a gidan nan suka sanshi".
Ranar da Sadauki ya fara zuwa gurina a ranar na bashi labarin encounter dina da hamma Saghir. Ya bata rai yace "kar ki sake shiga harkar sa, duk hanyar da kika san yana bi ma karki kara bi ta gurin ballantana ya sake gaya miki wata maganar banzan". Duk sanda yazo zai gaya min next time da zai sake zuwa, dan haka ni nake fita da kaina in shigo dashi. A gefen dakin mai gadi muke zama, wanda yau da gobe sai muka zama very friendly dashi. Duk ranar da Sadauki yace min zaizo bai taba sabawa ba, koya wuce time din da yace zaizo to kuwa yan minutes kadai zai kara saboda traffic. A wannan lokacin na kara fahimtar cika alkawarin Sadauki, in dai yace zai yi abu to kuwa tabbas zaiyi din sai dai in wani abu ya faru beyond his ability.
Tun ranar da hamma Saghir yace min bararoji bamu kuma haduwa ba, nabi shawarar Sadauki dan haka ko muryarsa naji a guri to bana shiga, inkuwa tsautsayi ya biyo dani ta hanyar da yake to zanyi saurin chanza hanya. Rumaisa ce mai nacin zuwa gurinsa wai burge ta yake yi. Sai ranar nan bayan nayi ten days a gidan, muna tafiya da Rumaisa zata rakani in shigo da Sadauki sai muka hango Saghir a can packing lot, yasha farin voile sai kyalli yake yi kuma daga inda muke muna jin kamshin turarensa sannan muna jin muryarsa yana ta sirfawa baba audu zagi akan wai bai wanke masa motar daya saka shi ba, dan tsohon Allah sai hakuri yake bayarwa kansa a kasa amma kamar kara zuga saghir yake yi "tsabar iskanci da rashin mutunci wajan awa guda kenan nace ka wanke min mota ta amma saboda ban isa ba shi yasa kaki wankewa ko?" Baba Audu yace "kayi hakuri yallabai, Alhaji ne ya saka ni in gyara masa gurin da yake shan iska yana so ya fito anjima" yace "dalla yi min shiru, wallahi in kayi wasa kafin in koma porthercout sai kabar gidan nan. Ka kiyaye ni wallahi" dan dattijo ya durkusa yana ta bada hakuri. Ban san lokacin da naja wani uban tsaki ba, Rumaisa tayi saurin toshe min baki ta jani bayan flowers "rufa ma kanki asiri Diyam. Tsaki? Hamma Saghir? Wallahi in yaji ki zai balla ki" nace "ai kuwa daya gane cewa shayi ma ruwa ne" ta girgiza kanta tace "Sadauki ne dai takamar ki ba wani ba, amma kiyi tunani, do you really want to get him involved with hamma Saghir?" Na juya ina kallonsa, tabbas Sadauki na is very brave and fearless, amma saghir is not his match dan at least ya bashi shekaru goma, ga kudi ga kuma gata. Dan haka hada shi rigima da Sadauki will be like putting Sadauki in trouble. Na ja bakina nayi shiru sannan muka zagaye ta bayan sa muka fita daga gidan.
Sai three days to resumption date din mu sannan Baffa yazo da kansa ya daukeni zuwa gida. Matan gidan sun hada min goma ta arziki wai tsarabar boarding. Amma ni sai naji duk boarding din ta fara isata amma inaji inagani haka aka daukeni aka mayar dani. Sanda muka dawo next holiday shima ina zuwa na tarar da kaya na a ajiye, ban damu ba na shiga harkokina ina tunanin ai sharada ba nisa amma sai naga inna tana hada nasu kayan ita da Asma'u tace "Kollere zamu tafi, mun kwana biyu bamu je mun gaishe su ba musamman yan uwana da muke uba daya nan take naji bakin cikin duniya ya ishe ni amma haka Baffa ya debe mu a mota gabaki daya har su Ummah muka tafi, naji dama dama saboda ganin da Sadauki ne, amma bayan munje mun kwana daya a gidan Hardo da sabuwar matarsa sai naga su Baffa suna shirin komawa suna ta sallama da mutane, na bishi soro da gudu na rungume shi ina kuka nace "Baffa dan Allah zan biku mu koma tare" ya rike fuskata yace "kiyi hakuri uwata, ba tare daku zamu koma ba ku zaku zauna ku zagaya yan uwan innarku na gurin babanta" ai kuwa a take na kara wani kukan dan ni in akwai abinda bana so a lokacin to zama a Kollere ne. Suka tafi, Baffa da Ummah da Sadauki, suka barmu ni da Asma'u mun rike juna muna kuka, Inna ta tabe baki tace "sai suje ai suci uwar da zasu ci a gidan".
Mune daga wannan gida mu koma wancan mu kwana anan mu tashi anan muna ta ziyarar yan uwa har sai da muka yi sati biyu, Asma'u ta dan ware amma niko alamar warewa banyi ba, ranar da muka cika sati biyu Baffa yazo daukarmu ashe wai yayi wa inna waya akan mu shirya zaizo mu tafi ita kuma taki. Yana zuwa ta lissafa masa sauran gidajen da bamu je ba shi kuma yace baisan magana ba, "Diyam makaranta zata koma nan da sati daya, kamata yayi taje gida ta huta tukunna" Inna tace "wanne hutu zatayi a gidan? Taje dai gida mayun gidan su cigaba da lasheta" Baffa ya gyada kai yace "in har mayun gidan basu cinyeta ba a tsahon wadannan shekarun, to kuwa ke a garin wannan yawon naku zaki kaita gurin mayun" nan take sai rigima, inna tace ai Baffa yace yan'uwanta mayu ne. Hardo ya goya mata baya yace "to in bata kaisu sunga yan'uwanta yanzu ba sai yaushe?" Wannan yasa Baffa ya shiga motarsa yayi tafiyar sa, yace duk sanda muka gama yawon ma taho a motar haya.
Bamu koma ba sai two days to komawa ta makaranta, dan haka a gurguje na shirya shima kuma dan na samu Ummah ta fara harhada min wasu kayan kafin inzo. Dan haka wannan hutun ni da Sadauki sai gani da ido.
A hutun second term ne Baffa ya buga kafarsa yace babu inda zanje hutu, shima yana so ya zauna dani. Nan take rikici ya balle a gidan mu, Inna ta fito da abinda yake zuciyarta na kiyayyar ta a dangane da dangantaka ta da Sadauki, tace "sai dai bayan raina wallahi, wannan yarinyar indai ni na haife ta ba zata auri wannan yaron ba" Baffa yace "saboda me? Menene dalilinki na cewa haka?" Tace "Saboda bana sonsa, na tsane shi tamkar yadda na tsani uwarsa kuma bazan taba yarda in hada jini na da nasu ba" Baffa yace "to shikenan dalilin naki? Kishi ne kawai dalilin naki? To kuma in Allah ya riga ya rubuta akwai aure a tsakanin su fa? Fada min ya zakiyi?" Tace "sai in sallama ta, in dai ta aure shi to babu ni babu ita har abada sai dai ta nemi wata uwar bani ba" na durkushe a gurin da nake ina kuka kamar raina zai fita. Ina da karancin shekaru a lokacin amma nasan muhimmancin Inna a gurina, nasan darajarta ta wuce in hada tada kowa a sauran mutane, amma kuma nasan irin zafin son da nakeyiwa Sadauki, nasan irin soyayyar da shima yake yi min da kuma irin kyawawan halayensa shida uwarsa. Menene laifinsa.
Ta cikin hawayena na hangoshi ya shigo gidan da kayan da yake zuwa gareji dasu a jikinsa duk sunsha bakin mai. Ya tsaya yana kallon mu kawai, Ummah tayi masa alama da hannu cewa ya fita, sai ya ajiye kayan hannunsa ya juya har yakai bakin kofa sai kuma yajuyo yana kallona fuskarsa cike da concern.
Wannan hutun sam ba ajin dadi nayi shiba dan sai dana gwammace ina ma wani gidan aka kaini dan sosai Inna ta mayar dani matar kulle, ko tsakar gida bata bari na in fito daga dakin mu sai palon ta, Baffa ma sai dai in ya shigo in ganshi in kaishe dashi. Yar islamiyyar da nake zuwa in nazo hutu itama ta hana ni zuwa. Asma'u ce kadai abokiyar hira ta duk da ita lokacin bata da hankalin fahimtar me yake faruwa sosai. Rannan ina kwance a daki sai gata da takarda a bakin zanin ta ta miko min a hankali tace "inji Sadauki, yace kar Inna ta gani wai zata dake ki" na karba da sauri zuciyata tana muradin jin abinda yace, na bude na karanta, kalma uku ce kawai "how are you?" Naji hawaye ya taho min, shi concern dinsa akai nane, shi halin da nake ciki shine damuwarsa.
Ranar nan muna gab da komawa makaranta Baffa yana palon Inna yana cin abinci ni kuma ina zaune kusa dashi na dora kaina a kafadarsa, a gurinshi ne kadai nake samun hope. Sallamar Sadauki muka ji a bakin kofa, nayi saurin kallon kofar amma sai naji Inna tace min "tashi ki shiga daki" kamar zanyi kuka na shiga dakin amma sai na makale a bayan labule. Ina kallonsa ya shigo ya durkusa a gaban Baffa ya ajiye wasu takardu yana yi masa bayani akan wata mota da suka siya zasu gyara su siyar. Amma ni ba abinda yake fada nake ji ba fuskarsa kawai nake kalla, sai naga ya kara kyau fuskar ta dan canza min, sannan na lura da abinda ya chanza, ya fara tara saje. Nayi murmushi na durkusa a gurin ina cigaba da kallon sa har ya gama maganar da yakeyi. Sannan ya juya side Inna ya gaishe ta duk da yasan ba amsawa zatayi ba. Bata amsa din ba har ya mike, sai daya je bakin kofa sannan ya juyo ya kalli kofar dakin mu, muka hada ido sai ya lumshe idonsa ya bude sannan yayi murmushi ya fita. Yana fita Baffa yace wa inna
"Amina ni dai bazan gaji da gaya miki cewa ba kya kyautawa ba, kina dora kiyayya akan tushe marar dalili. Su yan uwan namu da suke kara zuga ki kike ganin kamar baki da masoya kamar su duk ranar da babu raina su zasu fara gudun ki keda yayanki, zasu fara ganinku kamar wasu responsibilities a gurin su. Ina ji miki tsoron wannan yaron da kike wulakantawa shine zai zama gatanki ke da yaranki watarana idan babu raina. Shi 蓷a na kowa ne."
Sai da lokacin komawa ta makaranta yayi sai naji sam bana son tafiya, duk da cewa zaman gidan kamar zaman kurkuku nake jinsa amma haka nan naji bana son rabuwa da gidan. Kamar ko wanne term, wannan karon ma Baffa da Sadauki ne suka tafi dani. Sai bayan da muka dauki hanya sannan Baffa ya fara magana
"Sadauki, Diyam ku bude kunne sosai kuji abinda zan gaya muku. Tun a gida naso yin magana daku amma saboda rigimar iyayen ku yasa na bar maganar nace mayi a hanya daga ni sai ku. Na farko, kun bani mamaki gaba dayan ku kuma kun bani kunya, yanzu har kunyi girman da har za ace an fara rigima akan auren ku? Yaushe aka haife ku gabaki dayan ku? Waye kuke tunanin zai yi muku aure yanzu? Ba dai ni ubanku ba. Musamman kai Sadauki kai da kake namiji, so nake kayi karatu mai zurfi kazama wani yadda wata rana zan kalle ka ince 'yes, that's my son'. Ke kuma Diyam, ko a ranki kada ki saka cewa zanyi miki aure yanzu. Sai kin gama makaranta kin shiga jami'a sannan in Allah ya kawo miji a lokacin sai inyi miki aure da sharadin zaki kammala karatun ki a gidansa, in kuma mijin bai samu basai kin kammala duk lokacin da Allah ya kawo shi sai ayi miki auren" yayi shiru muma duk mukayi shiru, sannan ya dora "in Allah ya kaimu lokacin, kun zama abinda nake fata zaku zama, kuma ya kasance har lokacin kuna son auren junan ku, to ni zan yi supporting dinku. Saboda dukkanin ku yaya nane, nasan halayenku kuma zanyi alfahari daku a matsayin surikai na. Kuma hausawa sunce da arziki a gidan wani gwara a gidan ka. Amma ku sani, daga ni sai Zainab ne zamu goyi bayan wannan hadin, ke Diyam a gabanki kinji kalaman da innarki ta fada, kuma da gaske take, kuma ni bazanyi miki fatan kiyi aure babu saka albarkar mahaifiyarki ba dan haka wannan shine challenge dinku ku tabbatar kafin lokacin dana fada muku kun yi kokari kuma kun dage da addu'ah kun juyo da hankalin ta ta amince."
[1/19, 11:35 PM] Zuraiyah Zuzu 馃専: 鉂わ笍 DIYAM 鉂わ笍
By
Maman Maama
Episode Twenty: The Two Corpses
Tunda muka koma school nake lissafin kwanaki ina jiran zuwan Sadauki dan nasan wata daya yake yi yazo ya ganni, kuma nasan bashi da karya alkawari sam. Lissafi na yana cika kuwa na fara saka ran ganinsa. Ina zaune kuwa a class sai ga baba mai kiran alkhairi yazo kirana. Na tashi na bishi da sauri jidda tana tsokana ta dan tasan lissafin zuwan wanda nakeyi. Muna fita daga class din na tsaya na kara gyara fuskata ta glass din window, ina lura da yadda sabon kitson da na saka akayi min jiya ya kara fitowa wa da kyawun fuskata. A gefen staffroom na hango shi a kasan bishiyoyi kamar kullum in yazo. Sai dai amma dama matsa kusa sai naga kamar ba shiba, kamar Sadauki na baikai wannan girma da iya daukar wanka ba. Sai na tsaya daga dan nesa nayi sallama. Ya juyo kyakykyawar fuskarsa dauke da murmushinsa mai kyau, na rufe baki ina dariyar murnar ganinsa nace "ashe da gaske kaine, sai naga kamar ba kai ba" ya harde hannayensa a kirjinsa yana kallona yace "lallai Diyam girma yazo, yau ke ce da yi min sallama bayan da tahowa kike da gudu ki wuce kirjina?" Na dan jawo hijab dina na rufe fuskata ina jin kunyarsa, ya saka hannu ya bude fuskar yace "yanzu in taho gari ya gari dan inga fuskarki kuma sai kiyi min rowarta ki rufe? Kinyi min adalci kenan?" Na danyi murmushin jin kunya sannan na kalle shi daga sama zuwa kasa. Ya zama cikakken saurayi sosai, hatta sajen sa ma ya zama complete kuma yayi masa kyau sosai. Gani nake duk samarin duniya babu wanda ya kaishi kyau a lokacin.
Sai kuma na rike baki nace "wai!! Sadauki ina zaka kai girma ne? Sai wani jin karfi kake kamar zaka dauki duniya" yace "ya kika ji sunan? Aliyu fa aka ce miki. Kin manta shi asalin mai sunan duniya kaf ta shaida karfinsa da jarumtakarsa? Sannan kuma akayi min lakani da Sadauki, kin san kuwa ko a cikin mayaka to duk wanda aka kira da Sadauki ina nufin jarumi ne shi a cikin jarumai. Ingarman namiji kenan" nayi dariya ina rufe baki, yace "what's funny?" Nace "wai ingarma, sai kace wani doki" shima sai ya tayani dariyar.
Na sunkuyar da idanuna ina wasa da fingers dina, mukayi shiru na wani lokaci sannan na dago kai na muka hada ido, na turo baki na buga kafa a kasa nace "ni ka daina kallona haka" yace "fada min menene shirrin, sai wani kara kyau kike yi kullum" na bata rai nace "bayan bana girma. Kuma wallahi ina cin abinci sosai" yayi dariya yace "girman zaizo ne Diyam. You won't know sanda zaki girma kawai sai dai ki ganki kin zama katuwa" nace "ni tsoro nake ji?" Ya bata rai yace "tsoron me? Nace "kai gashi nan ka zama kato, gashi kuma zaka tafi jami'a, kar kaje kaga manyan yammata kace ka fasa dani" ya jingina da jikin bishiya yana kallona, yace "Diyam" na dago muka ido yace "you have no idea how much I love you, do you? Ke din fa zuciyata ce, sonki kuma jinin da zuciyata take bugawa ne yana zagaye ilahirin jikina. Ta yaya mutum zai iya rayuwa babu zuciyarsa. Idan kinga Sadauki ya daina sonki to numfashin sa ne ya bar jikinsa. Idan kinga na rabu dake Diyam to kirjina aka tsaga aka cire zuciyata daga ciki. Nine ya kamata in kasance cikin tsoron watarana zaki rabu dani, ina tsoron idan innarki ta ki amincewa dani Baffa zai hanani aurenki, ina tsoron in kin girma zaki samu wani wanda ya fini kudi wanda ya fini asali kice kin fasa dani" na girgiza kai na nace "never, ba dai Diyam ba, Diyam ai kai take so tun kafin ta san menene so, da kai ta saba da kai kuma za tayi rayuwa insha Allah. Rayuwa babu kai will not be only unbearable but also unimaginable. I can't imagine Diyam without Sadauki" sai ido na ya kawo kwalla, yace "zaki fara kukan ko? I am here and I am going no where"
Muka zauna akan bench ya fara bani labarin gida, ana yake gaya min Baffa ya siya masa fili, yace "filin fa babba ne sosai, wai ashe for years yana tara min kudin aikin da nakeyi masa a garage shine yakara akai yasiya min. Yace duk sanda natashi yi mana ginin gidan mu sai inyi akai. Sannan kuma ya fara bani salary a garage kamar sauran ma'aikata" nayi murmushi nace "inye, kaga masu albashi" ya daga gira yace "ya kika gani?" Nace "Baffa ya kyauta. Allah ya saka mishi" yace "ameen. Problem din da nake fuskanta daga Ummah ne, tun ba yau ba kinsan nake fama da ita akan ta kaini dangin babana taki, ni kuma yanzu ina ganin kamar har da rashin su a tare dani ne yake kara kiyayyata a zuciyar Inna, ina so su shiga rayuwata Inna ta gansu tun yanzu amma kullum Ummah tana ce min wai ba yanzu ba, wai lokaci bai yi ba. I just hope ba zai zama too late ba" nace "it won't be, ni nasan Ummah kuma na tabbatar tana da dalilinta".
Ya sunkuyar da kai yana kallon kafarsa fuskarsa da alamun damuwa, naji nima zuciyata babu dadi sai nayi niyyar saka shi dariya nace "Sadauki kaga wani kwaro zai shigar maka ido rufe idonka inga ni" sai kuwa ya biye min ya rufe idonsa, sai kuma na shagalta da kallon fuskartasa. Fuskarsa bata cika tsaho ba kuma ba za'a kirata da zagayayyiya ba. Gashin girarsa mai cika ne da laushi kamar yadda gashin kansa yake, dogon hancinsa da kofofin suke budewa da sauri da sauri a yanzu alamun bugun zuciyarsa ya karu, madaidaicin bakinsa mai dauke da lips a slightly lighter than his dark skin color kuma suke zagaye da kyakykyawan sajensa mai laushi da kyalli, abinda yafi 蓷aukan hankalina a fuskarsa sune zarazaran gashin idonsa da suka yi kama da irin wanda yammata suke sakawa a gidan kwalliya.
Sai kuma nayi dariya, ya bude idonsa yana kallona yace "what? Ya fita?" Nace "wallahi gashin idonka irin na yammata ne" ya bata rai yace "Diyam kin raina ni Wallahi, dan kinga gurin kwana na ko?"
Sanda aka zo min general visiting sai naga anxo har da Ummah wannan karon, abinda ba'a taba yi ba. Naji dadi sosai muka zauna mukayi ta hira, muka ci abinci har da Baffa. Da zasu tafi kawai sai na fara kuka, abinda na dade banyi ba. Baffa yace min "ki zama yarinyar kirki Diyam, ki rike addinin ki kuma ki dage da addu'a akan komai ya same ki. Allah yayi miki albarka" sai na rungume shi ina kuka, yana dariya yace "yau kuma shagwabar kaina tazo?" Ya cire hannu na daga jikinsa, Ummah tace "zo ni ki rungume ni tunda shi baya so" na sake shi kuwa na tafi na rungume ta, sannan na juya na rungume inna itama. Ina kallo suka shiga mota suka tafi, sai naki kamar wani part nawa ya tafi tare dasu.
Kafin muyi hutu Sadauki ya sake dawowa. Wannan karon shida wani abokinsa suka zo kuma shine karo na farko da Sadauki ya fara introducing dina a gurin abokinsa, Ahmad Muhammad, na rike sunan ne saboda a ranar mun jima muna musu akan Ahmad da Muhammad duk suna daya ne. Sai kuma mukayi hirar carrier, shi Ahmad yace babu abinda yake so ya zama inya girma irin dan sanda, yace "duk ranar da na zama commissioner of police duk wadannan yan iskan da suke yawo a gari sai na rufe su" Sadauki kuma yace "ni kam whatever zan zama nan gaba a rayuwa will have to do with cars. Ni ina da wani passion sosai akan motoci" sai suka tambayeni ni kuma fa? Na girgiza kai na nace "I don't know gaskiya" Ahmad yace "with time zaki yi finding your place in the society kema".
Tunda hutu ya kusa nake jin babu dadi kamar wadda zanyi rashin lafiya amma kuma ciwon yaki zuwa, haka nayi exams din duk babu dadi. Ko kitson hutu banyi ba. Ranar hutun kuwa sai jidda ce ta hada mana kayan mu ta kai mana bakin gate. Har ta dawo ina kwance akan gado kawai naki hawaye yana bin fuskata, tazo ta tsaya tana kallona tace "kuka kuma Halima? Wani abun ne yake miki ciwo?" Nace "zuciya ta ce babu dadi jidda, ji nake kamar bani da lafiya amma kuma lafiya ta kalau, gaba na sai faduwa yake yi jidda" tazo ta rike ni tace "to ai addu'a zaki ke yi, innalillahi wa inna ilaihir rajiun , ba wai kuka ba" na fara yi kuwa sai naji naji dadi. Muka fito tare akayi assembly aka sallame mu kowa yana murna bandani.
A ka'ida duk ranar hutu kafin a bude gate su Baffa suke zuwa, amma yau sai naga an bude ana ta daukan sauran dalibai bandani. Na samu kofar wani class na zauna idona akan gate din makarantar amma ko motar da tayi kama da tamu ban gani ba. Har aka zo daukan jidda tazo tayi min sallama ta tafi. Har akayi sallar azahar shiru. A lokacin I was beyond crying kawai dai a zaune nake kamar mutum mutumi. Can sai ga wani malamin mu yazo inda nake yace "Halima? Ki zo anzo daukanki" na mike jiki ba kwari na bishi ina ta baza idon ganin Baffana ko Sadauki. Muna shiga staffroom sai naga Abba, baban su Rumaisa. Na tsaya kawai ina kallonsa yace "Diyam babu gaisuwa?" Sai na durkusa na gaishe shi malaman gurin suna ta kallona. Ya tashi da kansa ya zuba min kayana a motarsa sannan yace min inzo mu tafi, sai da muka shiga mota sannan nace "Abba ina Baffa yake?" Ya dauke kansa yace "sun taho motar su ta samu matsala, shine yayi min waya ni kuma na taho daga gumel yace dan Allah in biyo in taho dake" na gyada kaina kawai ina forcing zuciyata ta yarda da maganar sa.
Har muka shiga Kano bamu kara magana ba, na kwantar da kaina na rufe ido na kamar bacci nake yi amma ido na biyu. Na bude ido na kallon inda muke naga ba hanyar gida bane ba nace "Abba ba gida zamu tafi ba?" Yace "zan karbi wani sakona ne anan akth" na koma na kwanta. Ina ji muka shiga asibitin har mukayi packing, na daga kaina kadan ina kallon inda muka tsaya "Accidents and Emergencies" sai kuma ido na ya hango min wata kamar Aunty Fatima a tsaye a kofar gurin, sai na bude kofa na fita idanuna suna kara tabbatar min ita din ce amma zuciyata ta kasa yarda. Ina zuwa kusa da ita na lura kuka take yi, na bude baki zanyi mata magana sai na hango Inna a cikin hall din, Mama ta rike ta tana ta rusa kuka kamar ranta zai fita. Kamar mutum mutumi haka nake tafiya har nazo kusa dasu, sai naji muryar Ummah daga gefena tace "Diyam!!" Na juyo na zube idanuna a kanta, she looked old, ban taba ganinta a irin wannan yanayin ba amma kuma babu hawaye ko digo a idonta, "Diyam" ta sake fada sanda ta karaso kusa dani ta miko hannu da niyyar rungume ni amma sai ta sulale ta fadi kasa ta suma akan kafafuwana.
Tsayawa nayi kawai ina kallonta yayinda jama'a da ma'aikatan asibitin sukayi kanta. "Addah" naji muryar Asma'u a bayana, na juyo lokacin data karaso da gudu ta rungume ni
"addah mun shiga uku, Baffa da Sadauki sunyi accident kuma duk sun mutu"
Na cire hannunta daga jikina na dan tura ta kadan ina kallon fuskartada take cike da hawaye, sai kuma naji wani abu yana fusgata zuwa wani daki da naga wani doctor ya fito daga ciki yanzu. Na tura kofar dakin ina kallon gadaje guda biyu da suke a cikin dakin, sannan na kalli wadanda suke kan gadajen. Gadon farko wanda yake kai an lullube shi har fuskarsa. Gado na biyu kuma an rufe shi zuwa kirjinsa. Sadauki. Daga inda nake ina iya hango jinin daya jika sumar kansa ya bata katifar da yake kai.
[1/21, 2:47 PM] Zuraiyah Zuzu 馃専: 鉂� DIYAM 鉂�
By
Maman Maama
Episode Twenty One : The Two Corpses 2
Na dauke idona daga fuskarsa na mayar kan daya gadon da yake gaba na, sannan a hankali na taka na isa gaban gadon na saka hannu biyu na yaye sheet din da aka rufe mutumin. Idona ya sauka akan Baffa, kamar Sadauki shima gashinsa a jike da jini amma fuskarsa tas da ita babu emotions kamar mai bacci, na jima ina kallon sa dan ina jin ban taba yi masa cikakken kallo irin na yau ba. Kofa aka bude daga bayana wata nurse ta shigo da sauri tace "what .. ?" Sai kuma tayi shiru, ta karbe sheet din daga hannuna ta mayar ta rufe shi sannan ta kama hannuna ta jani kamar wata robot ta fita dani. Gurin su Inna ta kaini, wadda har yanzu take jikin Mama tana ta kuka, hannun ta daya rike da Asma'u. Nurse din tace "tare kuke da wannan yarinyar?" Inna ta kalle ni, da alama sai yanzu ta lura da zuwa na asibitin, tayi sauri ta jawo ni tana gyada wa nurse din kai tace "yata ce, yata ce" cikin kuka. Sai kuma ta rungume ni tana kara sautin kukanta.
Mama tace "haba addah, ya zaki saka yara a gaba kiyi ta wannan kukan haka? Da wanne zasu ji. Dan Allah ki rage wannan kukan inba so kike kema ki yanke jiki ki fadi ba" ta jawo ni daga jikin Inna ta zaunar dani a kan benchi ta rike fuskata tace "kai kiyi kuka kinji Diyam? Kiyi ta karanta innalillahi wa inna ilaihir rajiun" na gyada mata kai ina kallonta. To ni kukan me zanyi ne bayan nasan mafarki nake yi? Yanzu zan farka amma bana so in farka din sai Baffa da Sadauki sun tashi.
Wata nurse naga ta fito daga wani daki da sauri ta kira doctor sun koma tare, sai na samu kaina da mikewa na bisu amma ban shiga ba sai na tsaya a bakin kofar ina kallon ciki ta glass din jikin kofar. Ummah na hango akan gado, nurses biyu da likita daya a kanta suna ta kokarin bata taimako. Sai kuma ta fara convulsing, idanunta suka kakkafe doctor din yana ta kokarin reviving dinta amma sai jikinta ya saki. Ina kallo suka yi ta aaunata sannan doctor din ya kalli nurse din data dauko takarda da biro yace "time od death: 4:35" sannan ya bude kofa ya wuce ni jikinsa duk a sanyaye.
"Death" na maimaita. "Ummah, Baffa, Sadauki" na fada a hankali ina jin kaina yana juyawa. Na bi bayansa a hankali naga ya tafi gurin su Inna yayi musu wata magana, sai naga Inna ta saki hannun Asma'u da sauri ta rufe bakinta ta durkushe a gurin, Mama tana ta salati ita ma su Aunty Fatima suna tayata. Da sauri Inna tazo ta wuce ni ta shiga dakin da Ummah take sai kuma ta sake fitowa da sauri ta hada kanta da bakin kofar tana kuka kamar ranta zai fita. Tunda nake a lokacin ban taba ganin Inna cikin tashin hankali irin na yau ba.
Muryar yaya ladi na jiyo ta shigo gurin. "Innalillahi wa inna ilaihir rajiun. La haula wala quwata illah billah. Wayyo Usumanu wayyo Aliyu, yanzu aka kira ni akace sunyi hatsari an kawo su nan. Ya jikin nasu? Ya kuke ta kuka haka?" Kowa ya kalleta sai dai ya kara kukansa, ta rike kafada ta "Halima? Ina marasa lafiyan suke? Ina Zainabu kuma? Ya banganta anan ba?"
Nurses ne su biyu suka zo suka kamata suka jata gefe, duk suma a diririce suke suna yi mata magana, bana jin me suke cewa amma can naji ta saka wani kuka mai ban tausayi sannan ta wuce mu da sauri ta shiga dakin da Ummah take. Alhaji Babba ne da kawu Isa suka shigo gurin, Alhaji Babba yana fada
"menene hakan duk kun cika asibiti da koke koke? Kukan zai dawo dasu ne? Kun kuma san babu kyau yiwa mamaci kuka ko? Fatima ki riko yaran ke kuma Hafsa ki kamo Amina mu zamu taho da gawawwakin ayi musu wanka ayi musu suttura tun kafin magrib tayi".
Wannan maganar tasa ita ta dawo dani cikin hayyacina, lokaci daya naji reality din mutuwar ya doke ni. Na juya da sauri ina kallon kofar dakunan da gawawwakin suke. "Baffa!!" Na fada da iyakacin karfina "Sadauki!! Ummah" Aunty Fatima tayi saurin rufe min baki na da hannunta tace "kul Diyam, ba'a yiwa mamaci ihu". Sai na mayar da kaina jikinta na kwanta na rufe ido ba tare da na sake cewa komai ba. Nasan dai mun shiga mota sannan mun fita, sai kuma naji mun shiga gida mun shiga daki an zaunar dani akan kujera. Sannan ne na bude ido ana ganni a palon Inna, Asma'u tana zaune kusa dani tasha kuka ta koshi, ina jiyo tashin sautin kukan Ummah sama sama amma ban juya ba ballantana in kalli inda take.
Muryar Alhaji Babba naji ya shigo gidan, ya daga labilen palon Inna yace "a dauke carpet din palonsa sai muyi masa wanka a can" na runtse idona ina so hawaye ya fito min amma babu. Muna nan zaune sai muka ji hayaniya kuma, muryar Alhaji Babba "ku fita da ita daga gidan nan, ai tun sanda ya aure ta mun gaya masa babu mu babu ita, dan haka yanzu ma babu mu babu ita" sai muryar yaya ladi tana kuka. Ji nayi kamar in tashi in shake shi, how dare he said that a ranar da Baffa ya bar duniya? A ranar da Ummah ta bar duniya?" Rigima sosai har makota suka fara taruwa, sai ga dattijon mutumin da har yau yaya ladi take gidan sa yazo yace "a gidan aurenta za'ayi mata suttura kamar kowacce matar aure, kai kuma baka isa ka hana ba in kuma zaka iya to ka dauko yan sanda" ganin mutane suna ta kallonsa accusingly ya saka Alhaji Babba ya ja baya ya bari aka shigo da gawar Ummah. Na tambayi kaina to ina Sadauki kuma?
Tare akayi musu suttura, shi a palonsa ita a nata, sannan aka zo aka fita dasu ta gabanmu a tare. Na bi su a baya nayi musu rakiya har bakin gate sannan na tsaya ina kallo aja jera gawawwakin su akayi musu sallah a tare aka dauke su zuwa gidan su na karshe.
Na koma gida ina tafi ina hada hanya. A tsakar gida na durkusa a cure a guri daya ina kara tambayar kaina ina Sadauki? Ji nake nima inama dai mala'ikan mutuwar zai zo ya hada dani. Mama ce tafito ta ganni a gurin, sai ta dauko tabarma ta shimfida mana muka zauna ta jani zuwa cinyarta na kwanta. Anan mukayi sallar magrib, sai ga yaya ladi ta fito tazo inda nake ta shafa kaina tace "sannu Halima, Allah yaji kansu yayi musu rahama, shi kuma Aliyu Allah ya bashi lafiya" na dago kai da sauri na ina kallonta sai naji tace wa Mama "zan koma asibiti inga halin da yake ciki" Mama tace "to Allah ya jishe mu alkhairi" nace da Mama "waye a abibitin?" Tace "Sadauki mana" naji wani abu mai nauyi daya tokare tun daga zuciyata zuwa makogwarona ya janye, numfashi na ya fara fita da sauri nace "Sadauki? Ba tare suka mutu ba? Na dauka ko an kai gawarsa wani gurin" ta rike hannuna tace "Sadauki bai mutu ba ya samu buguwa ne a kansa shi yasa doctors sukayi sedating dinsa. Baffanku kuma tun kafin a kawo su asibiti ya cika, Ummah kuma tashin hankali ne ya saka ta yanke jiki ta fadi, jininta yayi mugun hawan da cikin yan mintina ta mutu" naji wani abu yana sauka daga kai na zuwa kafafuwana. Sadauki is alive. Then there is hope for me.
A daren ranar banyi bacci ba, muna kwance ina rungume da Asma'u da take ta jera ajjiyar zuciya saboda kukan da tasha, sai da naga ta samu bacci mai nauyi sannan na zame jikina na fita palo, Inna na gani zaune akan sallaya ta rufe fuskarta da hannayenta tana kuka a hankali, sai na wuce ta na shiga toilet nayo alwala nafito nima na tayar da Sallah, yau shine daren Baffa da Ummah na farko a kabarinsu kuma nasan suna bukatar adduoin mu sosai. Har na idar da sallolina Inna tana kuka, sai na kwanta akan sallayar na dora kaina akan cinyoyinta sannan nima na samu kuka yazo min.
Washegari yan Kollere suka zo, gida ya cika taf ana ta karbar yan gaisuwa amma babu wanda naji ya kuma maganar halin da Sadauki yake ciki, yaya ladi ma kuma ban kuma ganinta ba duk kuwa da cewa jama'ar Ummah suna ta zuwa gaisuwa suma. Inna dai kam tayi kuka kamar idonta zai fita kowa yashigo gidan sai ya tausaya "uwargidan sace kuma uwar yayansa". Sai dare na ajiye tsorona na tambayi Inna "Inna ya jikin Sadauki kuwa?" Ta kalle ni ta dauke kai, "ban sani ba" ta fada tare da cigaba da jan carbin ta.
Ranar da akayi sadakar uku ranar munga mutane, dan ko ranar mutuwar gidan baiyi wannan cikar ba, ranar yaya ladi tazo akayi adduoi da ita, sai da aka gama ta tashi zata tafi na bita a baya nace "yaya ladi ya jikin Sadauki?" Ta juyo ta kalleni tace "da sauki Halima, jikinsa da sauki" sai ta juya tayi tafiyarta. Alhaji Babba ya shigo bayan an gaishe shi yace "Amina zamu saka a gyara muku guri a can gidana, idan anyi bakwai sai ku koma can ku zauna ke da yara saboda nan din ba zaku ji dadin zama ba ku kadai. Allah ya ji kansa" akace ameen sannan akayi masa godiya ya tashi ya tafi.
Zuwa yamma I have taken all I can, ji nake nima kamar nawa jinin zai hau irin na ummah nima in mutu, an gama adduoin kuma an mayar da gidan kamar gidan biki sai ciye ciye ake da hira da dariya. Na shiga dakin inna na bude jakar ta na dauki kudi na saka hijab dina na fixe ba tare da kowa ya lura ba. Adaidai na hau direct na tafi asibitin malam, naje har emergency room nayi sa'a kuma visiting hours ne dan haka na tambayi nurses Aliyu Usman Kollere nake nema sai suka ce inje aminity room 3. Da sauri na na tafi, zuciya ta tana jin kamar zata kara sauri tayi gaba ta riga ni shiga dakin.
A kwance na same shi da drip a hannunsa daga alamar har yanzu allurar baccin akeyi masa, fuskarsa da dan fada kuma tayi haske, kansa a nade da bandage. Babu kowa a dakin sai shi kadai. Na karasa ciki inajin wani irin tausayinsa yana saukar min, na zauna a gefen gadon na kamo hannunsa nayi intertwining fingers din mu. Ya dan bata rai sai kuma yayi blinking ya bude jajayen idonsa yana kallona, ya kakalo murmushi mai nuna yana jin ciwon yinsa yace "you are here" na gyada kai nace "am here" yace "waye ya dauko ki daga school?" nace "Abban su Rumaisa" yace "good" mukayi shiru kuma can sai yace "ya jikin Baffa?" Gabana naji ya fadi na zuba masa ido, wato bai ma san abinda yake faruwa ba? Ya sake cewa "yaya ladi tace min ya samu karaya ne shine aka kai shi asibitin kashi. Shine kuma duk kuka tafi gurinsa ko?" Ya sake kirkiro murmushi "dama nasan Ummah tafi son Baffa akaina shine ta tafi jinyarsa ta barni, in kin koma ki gaya mata nayi fushi, nima tawa matar tazo ta ganni" na cije lebena ina danne kukan da yake so ya kwace min, sai yace "don't cry please, everything will be alright"
Na gyada kaina nace "yes Sadauki, everything will be alright. Ka koma kayi baccinka" ya lumshe ido yana kara rike fingers dina a cikin nasa. Mun jima a haka ina kallon fuskarsa ina jin wani irin yanayi yana kara shiga ta a kansa, nayi kokarin zare hannuna daga nasa sai ya kara rikewa a hankali cikin bacci yace "don't leave me please, stay with me please" sai ya dora hannayenmu akan kirjinsa sannan ya dora daya hannun ya sake rike wa.
A haka yaya ladi ta shigo ta same mu, ta tsaya tana kallon mu sannan ta girgiza kanta tace "an mutu an bar muku gadon wahala".
[1/21, 10:27 PM] Zuraiyah Zuzu 馃専: 鉂わ笍 DIYAM 鉂わ笍
By
Maman Maama
Episode Twenty Two : Birthday Gift
Abinda na tarar a gidan mu dana koma banji dadinsa ba, harkoki kawai ake yi ana wadaka da abinci, wato shi wanda akayiwa mutuwa shi kadai ta shafa ko? Shi kadai yasan me yake ji? Wato mutuwa ba zata zamo izna ga sauran mutane su nutsu su daina biyewa duniya ba? An bubbude koina har palon Baffa mutane ne a ciki, bedroom dinsa ne kawai a rufe.
Dakin mu na wuce da niyyar in kwanta inji da abinda yake damuna amma sai na tarar da yammata ne fal a dakin, suna ta dauke dauken hotuna da kallon videos a waya suna kyalkyatar dariya. Ko magana banyi musu ba na fito da shiga part din Ummah, babu kowa anan kofar palon ma a saye take dan haka na tura na shiga na mayar na rufe. Direct dakin Sadauki na tafi na bude na shiga. Dan karami ne dai dai size din dakin mu ni da Asma'u, katifa ce kawai a dakin sai wardrobe, standing fan, sai kuma tarkacen takardu a gefe. Sai hoto guda daya a jikin bango. Na tsaya a gaban hoton ina kallonsa kamar yau na fara ganinsa, Ummah ce da Baffa a zaune akan kujera, sai Sadauki a durkushe a gaban baffa sai ni kuma akan cinyar Ummah da shubeya a hannu na.
Na tuna sanda aka dauki hoton da wata sallah ne lokacin Inna tana da cikin Asma'u, babu yadda Baffa baiyi ba ita ba akan tazo ayi hoton taki tace sai dai yaje mu dauka daga ita sai shi sai ni. Shi kuma yaki. Na zauna a gaban hoton ina jin kewarsu tana kara mamaye ni, ina jin kamar inyi rewinding din rayuwar mu ta dawo baya in cigaba da ganin su, in cigaba da ganin Sadauki a gidan mu. Inna tuna cewa Sadauki bai san anyi mutuwar nan ba sai inji zuciya ta duk ta narke, bansan yadda zai dauke ta ba, ina gudun kar wani abun ya same shi shima. In na tuna yanzu bashi da kowa a duniya sai inji kamar in tashi in koma asibitin in zauna a wurinsa. Hope dina daya shine na yaya ladi zata kaishi gurin mahaifinsa tunda nasan dole zata san waye shi, in ma bata sani ba shi wanda ya hada auren ai zai sani. Amma kuma in nayi wannan lissafin sai inji zuciya ta ta kara tsinkewa saboda tunanin rabuwa da Sadauki. Kuma what if shi uban baya bukatarsa? What if shine yakori Ummah da jariri yace baya so?
Anan dakin bacci mai nauyi ya dauke ni saboda kwana ukun nan duk bana samun bacci mai nauyi. Na jima ina yin baccin sai naji magana kamar a tsakiyar kaina ance "Diyam? Uban me kike yi anan?" Na tashi zaune ina mitstsika ido amma na kasa bude idona saboda fitilar da aka haske ni da ita. Aunty Fatima tazo ta kama ni muka mike "tun dazu ake ta neman ki, babu inda ba muje ba duk hankali ya tashi mun dauka an sace ki ne" nace "kuyi hakuri, bansan bacci ya dauke ni ba, hayaniya ce ta yi yawa acan ni kuma ina so in zauna ni kadai" sai kuma sukaji tausayina, amma inna sai da tace "kuma ki rasa inda zaki je ki kwanta sai nan dakin? Ba gwara ki tafi makota ba?".
Sai da aka sake kwana biyu sannan na kuma samun dama na tafi dubo Sadauki, wannan karon tare da Rumaisa muka tafi kuma sai da na saka tayi min al茩awarin ba zata gaya wa kowa ba. A zaune muka tarar dashi yaya ladi tana ta fama dashi akan yaci abinci. Tun a fuskarsa na gane yaji dadin zuwana sosai. Yace "kun taho da waya? Ina son in kira Ummah, ina so kuma inji ya jikin Baffa" na girgiza masa kai nace "bani da waya ai ka sani, kuma bansan zaka bukata ba shi yasa ban karbo wata na taho da ita ba" ya jingina kansa a jikin gado yana runtse idonsa yace "a gurin da muka yi accident aka dauke min waya ta, ita kuma wannan tsohuwar wai tata ta lalace" na jawo kujera na zauna ina karbar kwanon abincin daga hannun yaya ladi nace "duk suna lfy Sadauki, ummah cema tace inzo in duba mata kai. Kasan ba zata iya barin Baffa ba Musamman yanzu da bashi da lfy" ya gyada kai yana murmushi yace "ji nake yi kawai ina so in ganta" ina kallon Rumaisa ta tashi ta fice daga dakin. Na zuba masa tuwon alkama miyar danyar kubewar da yaya ladi tayo masa na zauna ina bashi a baki, ba musu yake karba idanuwansa a kaina ko kiftawa baya yi har sai da ya cinye wanda na zuba masa tas, yaya ladi tace "oh, tun safe nake fama da shi akan yaci abinci yaki ci, shifa yace inyi masa tuwon amma shima ya bar ni da abina, amma da yake ke kece gashi nan ai ya cinye tas" ya juya yana kallonta yace "baki iya tarairayar miji ba ne shi yasa" da alama so yake suyi wasa irin yadda suka saba amma sai ta kasa mayar masa, sai ta hau tattara kayan gurin ta fita dasu.
Na saka tissue ina goge masa bakinsa sai ya rike hannun yana kallona cikin ido yace "kin rame, kinyi duhu, idonki sun kumbura" na kirkiro murmushi nace "ka manta daga makaranta na dawo, kuma exams muka gama bama samun isashshen bacci" ya saki hannuna yace "fada min gaskiya, ya jikin Baffa, is it bad? A ina ya karye?" Na kasa kallon idonsa nace "a hannu ne kuma da sauki" yace "hannu kuma? I thought kafa ce ma saboda shi yake driving" na dago ina kallonsa da mamaki dan nasan Baffa hardly drives in dai da Sadauki a motar. Nace "me ya faru?" Ya sunkuyar da kai yace "rami muka daka sai taya ta fashe, daga nan motar ta fara a dungure akan titi, sai data daki wata bishiya sannan ta tsaya" na gyada kaina ina rike hawaye na.
Muna komawa gida muka tarar da inna a tsakar gida tana alwalar magrib tace "daga ina kuke?" Rumaisa tace "makota muka shiga". Shikenan bata kara ce mana komai ba.
Washegari bayan nayi sallah na kwanta akan kujera amma ba bacci nake yi ba, na rufe idona ne kawai saboda bana son kowa yayi min magana a lokacin. Ina ji akayi ta hidimar abinci sannan aka fito palo aka baje kowa yana ci ana ta hira, cikin hirar naji Inna tana bawa yan uwanta da suka zo daga Kollere labari:
"Wallahi in gaya muku, daga zuwanta da yaron nan ya dauki son duniya ya dora akansa, komai Sadauki komai Sadauki, ni na dauka ko rashin haihuwa ne ya saka haka amma sai gashi bayan na haifa masa yaya har biyu amma sadaukin nan dai ya fiye masa duk su biyun. To in ba asiri ko maita ba me zai jawo haka? A ce agolan da aka haifa a wani gidan koma a wani titin ne oho, tunda babu wanda yasan ubansa amma ace yafi yayanda mutum ya haifa da cikin sa? Ai shari'a tsakani na da zainabu sai a lahira za'a karasa ta. Tun yaron nan yana dan mitsitsinsa aka fara bashi mota a gidan nan, kullum 'sadauki zo ka kaini guri kaza, Sadauki zo muje guri kaza' nayi magana amma a banza tunda dama ni ba jin magana ta yake yi ba. Shine ranar nan yace "Sadauki zoka kaini Taura mu dauko Diyam' to gashi nan bai kaishi taura ba ya kaishi lahira" naji kaina ya sara, ina so in tashi in gaya mata cewa ba Sadauki ne yake driving a ranar ba amma nasan ba yarda zata yi kuma zata tambayeni wa ya gaya min.
Wata ta tambayeta "to ina yaron yake yanzu?" Tace "yana asibiti yana karbar magani, kinsan irinsu bada wuri suke mutuwa ba" sai na tashi tsam na wuce su na shiga daki. I can't take sunan sadauki da sunan mutuwa a sentence daya, not now da nake ganin ya samu sauki sosai. Not now da nake ganin nafi bukatar safiye da koyaushe.
Washegari akayi sadakar bakwai. Jama'a sun taru sosai bangaren Baffa da na Ummah, ga kuma makota da abokan arziki. Yaya ladi ma da sassafe tazo ta bude dakin Ummah inda mutanen su suka zauna. Ana gama yin adduoi aka yi sadaka sai kuma kowa ya fara watsewa, har yan Kollere ma duk sun gama shirin su ana gama wa suka yi sallama suka dauki hanya. Muma kuma sai Inna ta fara hada mana kaya amma ni sai na koma na zauna a tsakar gida na takure a guri daya ina sheshshekar kuka. Yanzu shikenan barin gidan mu zamuyi? Gidan da aka haife mu muka tashi a ciki, me yada zamu barshi mu koma gidan wasu mu zauna a karo? Bayan muna da rufin asirin mu. Ina kallo aka fara fita da kayan mu ana zubawa a motar da Alhaji Babba ya aiko da ita.
A lokacin ne kuma ya shigo. Kansa still a nade da bandage hannunsa kuma sanye da carnula. Ya tsaya yana rike da kofa for support idanuwansa a kaina, na mike nima ina kallonsa ina hango tsantsar tashin hankali a idonsa. Ko ba'a gaya min ba nasan ya sani. "Ina Ummah?" Ya tambaye ni da wata irin murya, sai na fara sheshshekar kuka na kasa ce masa komai. A lokacin ne Inna ta fito da wani akwati a hannunta ta ajiye tana kallonsa tace "sun sallamo ka kenan, dama yanzu nake tunanin yadda za'ayi a fitar maka da kayanka zamu rufe gida" ya kalleta kawai sannan ya sake mayar da dubansa kaina yana kallon yadda nake kuka babu sauti, hawaye wani na korar wani. Sai ga yaya ladi ta shigo afujajan, tana ganin shi ta sauke ajjiyar zuciya "yanzu shine ka fito daga asibitin ka taho nan Aliyu?" Kallo daya yayi mata sai ta saka kuka itama.
Na tafi a hankali har inda yake tsaye na rike hannayensa a nawa, sai kuma na dora kaina a kirjinsa a hankali nace "Sadauki Ummah ta tafi ta barmu, Baffa ma ya tafi ya barmu, sun mutu Sadauki ba zamu sake ganin su ba. Mu dasu sai dai muyi musu addu'a kuma sai kuma a lahira in munje muma"
Baice min komai ba bai kuma yi magana ba amma ina jiyo yadda zuciyarsa take bugawa kamar zata bar jikinsa, ya saka hannu ya ture ni daga jikinsa ya fara tafiya kamar zai tafi dakin Ummah sai kuma ya juyo, yayi kamar zai fadi na tafi zan rike shi sai ya dakatar dani da hannu daya daya hannun kuma ya dafe kirjinsa dashi. Ya dan jima a haka sannan ya sake straightening ya doshi hanyar waje, da sauri ni da yaya ladi muka rufa masa baya muna kiransa amma sai Ummah ta damko rigata a dawo dani baya "in kika bar gidan nan sai na kakkarya ki" ta harari waje "muma duk marayun ne, mun rasa iyayen mu kuma mun hakura".
Sai daga baya na fahimci ashe wasu kawayen Ummah ne suka je duba shi a asibiti shine suka yi masa gaisuwa, basu san cewa bai sani ba, shine ya gudo daga asibitin ya taho gida dan ya tabbatar. Ni dai a bangare na zan iya cewa tunda akayi rasuwar nan banyi kuka mai yawa irin na ranar nan ba dan a tsakar gida na zauna nayi tayin abu na, ina kukan tausayin kaina ina kuma kukan tausayin Sadauki. Menene makomar mu ? Menene makomar soyayyar mu? Babu wanda ya kula ni sai Asma'u da take makale dani tana taya ni kukan itama.
Can naji Inna tana cewa "su kenan kayan sun kare, in muna bukatar wani abu ko Diyam sai tazo ta daukar mana tunda babu nisa" Mama tazo ta tashe mu ni da Asma'u "ku daina kuka kunji? Ai ba barin gidan kuka yi ba gaba-daya zaku dawo in innar ku ta gama takaba" na gyada mata kai kawai. Muna ji muna kallo aka tisa keyar mu zuwa waje aka rufe gidan, a raina ina tunanin kayan Sadauki fa? Kayan Ummah fa? Ai bamu kadai muke da gidan ba tunda dai a tunani na Ummah tana da gado dan haka Sadauki ma yana da gado kenan.
Ina shiga mota kamar ance in kalli side sai na hangoshi a tsaye a jikin bishiyar da take opposite gidan mu, hannayensa a rungume a kirjinsa, idanunsa a cikin nawa. Nayi kamar zan fita sai Inna ta tura ni ciki ta shigo ta rufe kofa. Driver kuma ya tayar da mota muka tafi. Na juya waiwaya baya ina hangoshi ya matso tsakiyar layin mu yana kallon motar mu har muka sha kwana na daina ganinsa. Na juyo idona ya sauka akan dashboard din motar, agogo na kalla,time 3:15 date 25th August and it occurred to me cewa yau ne ranar Birthday dinsa, a yau ya cika shekaru ashirin cif a duniya. So young and so alone. Sai na rufe fuskata da hannayena ina sake wani sabon kukan.[1/22, 11:13 PM] Zuraiyah Zuzu 馃専: 鉂� DIYAM 鉂�
By
Maman Maama
Episode Twenty Three : Shared Strength
Assalamu alaikum wa rahmatullah
Ina neman afuwar wadanda littafin Diyam ya saka kuka a kwana biyun nan, ina rubutu ne dan in faranta muku badan in bakanta muku ba. Amma ina so ku sani ita rayuwa is full of ups and downs dole sai ansha wuya sannan za'a sha dadi. Ina so duk sanda kuke karatu ku saka a ranku cewa kirkirarren labari ne, non of this happened in real life duk da cewa zai iya faruwan. But labarin Diyam kirkirarren labari ne.
Daki ne aka bamu a gidan Alhaji Babba, dakin a babban palon gidan yake. Ciki daya ne da ban蓷aki mai dauke da gado da wardrobe a ciki, asalin dakin an yi shine saboda baki in sunzo daga Kollere anan suke dauka amma sauran matan gidan kowa in tayi baki to part dinta suke tafiya. Muna zuwa matan gidan duk suka firfito harda Hajiya Babba da kanta, aka zauna a palo ana ta kara yiwa juna gaisuwa da kuma jajanta abinda ya faru sannan aka saka yan aiki suka kara gyara mana dakin aka kai mana kayan mu can sai kuma kowa ya watse ya bar mu mu kadai.
Nina fara tashi na shiga dakin da aka bamu ina kare masa kallo, babu laifi yana da girma kuma da toilet a ciki amma kuma it doesn't change the fact that aro aka bamu, aron kuma da nia ganina bama bukata. Na tuna yawan dakunan da suke gidan mu, Inna daki biyu da palo, Ummah daki biyu da palo sannan ga dakin Baffa ciki da palo ga kuma dakin waje, amma wai duk mun ajiye su mun dawo daki daya mun zauna da sunan taimako, taimakon me? In taimaka mana za'ayi ni a ganina ai food stuff ya kamata ake kai mana can gidan mu kamar monthly haka ko duk sanda aka samu dama, ko ake bamu kudi muna siyan abin bukatun mu da kan mu amma ba gurin zama muke bukata ba. Kuma ko kudin ne ma ni aganina zamu iya kula da kan mu ba sai mun dogara da kowa na. Yes, Baffa ya mutu amma bai bar mu fakirai ba, ya bar garejin sa da yake running for over twenty years, zamu iya cigaba da running kayan mu da kan mu, Sadauki can do that tunda yasan komai dashi ake komai kuma duk costomers din Baffa sun san shi.
Ni a ganina da mun yi zaman mu a gidan mu mun dora Sadauki akan komai kuma nasam as hard working and dedicated as he is zai iya yin komai. Ya cigaba da zamansa a gidan for security tunda za'a ce ba zamu zauna mu kadai babu namiji ba, in ma kuma Inna bata son zamansa a cikin gidan tana ganin ba muharramin mu bane ba zai iya zama a dakin waje ai, kuma yadda yake da kwarjini din nan babu wanda zai kawo mana raini a unguwa. Sadauki yana da gado a gidan da garejin, so it will be a mutual relationship wanda ni nake ganin mu zamu fi benefitting akan sadauki.
Ina ta tunanina har Inna ta shigo tana ta jera mana kayan mu a wardrobe din dakin, Asma'u tana tayata tana kuma mitar cewa wardrobe din tayi mana kadan sai dai mu bar wasu kayan a cikin akwati. Bayan sun gama na tashi na sake goggoge dakin na wanke toilet na jera mana toiletries dinmu da kuma kayan shafe shafen mu, sannan nayo wanka da alwala nazo nayi sallah tare da jera adduoin neman nasara akan Inna in samu ta saurare ni ta kuma yadda da shawara ta.
Da dare sai ga kwanukan abinci nan daga duk matan gidan kowa ta zubo ta aiko mana dashi, Inna ta karba tayi godiya amma daga ni har ita ba wani cin kirki mukayi ba Asma'u ce ta danci da yawa. A lokacin da muke cin abinci ne naga chance dina na magana da ita dan haka na zayyane mata duk tunani na da plans dina na kara da cewa "inna in mukayi hakan kamar mun dogara da kan mu kenan, ba ruwan mu da abinda za'a bamu da abinda ba za'a bamu ba. Duk wanda ya ke ganin zai taimaka mana saboda zumunci sai yaje har gidan mu ya taimaka mana in ma ba'ayi mana ba bamu da damuwa tunda muna da abin hannun mu. Inna dan Allah ki duba maganar nan".
Tunda na fara ta ajiye spoon dinta tana kallona har na gama sannan ta fara girgiza kai tana kallona tace "yayi daidai Diyam, ya kamata a jinjina wa wannan tsarin naki. Amma bara in tambayeki, sanda kike yin wannan tsarin mune a ranki ni da Asma'u ko kuma bakin yaron can? Iye? Wato bakin cikin ki shine mun taho nan gidan an raba ki da shi shine kike so mu koma saboda ku cigaba daga inda kuka tsaya ko? Kuma ke yanzu a tunanin ki duk duniya in rasa wanda zan dauki ragamar rayuwata ni da yayana in bawa sai wannan yaron? Bani da yan uwane? Ko shi mahaifinku bashi da yan uwan da zasu kular masa da sana'arsa su kuma kular masa da iyalinsa? Ai ina sane na karbi shawarar Alhaji Babba ta cewa mu dawo gidan sa mu zauna saboda in raba ki da wannan yaron. Ina so ki saka a ranki cewa Alhaji Babba yayi mana mutunci yayi mana karamci daya dauko mu ya kawo gidan sa cikin iyalinsa saboda baya son mu zauna mu kadai cikin kunci da kewar mahaifinku dan haka daga ni har ku kamata yayi mu gode masa mu kuma yi iyakacin kokarin mu gurin faranta masa. Maganar gareji kuma shi Alhaji Babba da yake da mutum ne mai budadden ido kuma wanda ya san mutane na tabbatar zai san abinda ya dace ayi dashi. Magana ta karshe Diyam, daga yau sai yau, kar ki sake yi min maganar yaron nan".
Bayan na kwanta na jawo bargo na lulluba sai na tambayi kaina ko a ina Sadauki zai kwana? Ko a wanne hali yake ciki? Sai kawai naji baccin ya dauke daga idona baki daya. Babu abinda ba zan iya bayarwa ba a lokacin dan in samu in san halin da yake ciki.
Kwanan mu biyu gidan Alhaji Babba kuma so far bamu da matsala. Muna samun kulawa da sympathy sosai daga jama'ar gidan amma ni a gurina na gaji da "Allah sarki" da "kuyi hakuri kunji" da kullum akeyi mana wanda babu abinda yake rage min a zuciya ta sai ma kara karyar min da ita da yake yi. Sannan kuma ga tunanin Sadauki daya addabi zuciya ya kullum sai karuwa yaje yi har cikin baccina wanda da kyarnake samu nake yi amma mafarkin Sadauki ne, ko inyi mafarkin rayuwar mu a baya ko kuma inyi mafarkinsa wai shi kadai a titi, har ganinsa nake yi a kwance abskin hanya ruwan sama yana dukansa duk kuwa da cewa nasan yaya ladi ba zata rabu dashi a titi ba, akwai makotan mu da akayi zaman mutunci dasu nasan ba zasu barshi a titi ba, akwai kuma marikin Ummah nasan shima ba zai bar Sadauki a titi ba, wannan sai yasa nayi tunanin to in duk wadannan ba zasu barshi a titiba why Inna? Ita me yasa ta barshi a titin ba tare da ko kayan sawa ba, wacce irin zuciyace da ita? Me yayi mata mai zafi haka?
Bayan mun kwana hudu Mama tazo dan ganin yadda mukayi settling down, ta kuma taho mana da yan abubuwan da take ganin zamu bukata. Bayan sun kebe da inna ne take cewa "ni kuwa Adda ina so muyi magana dake a kan yaron nan dan wajen zainabu. Wallahi ranar nan ba karamin tausayi ya bani ba ke kuwa dan Allah ki sauko da zuciyarki akan sa, ji nakeda zainabu kukayi kishin ku kuma zainabu yanzu kasa ta rufe fuskarta haka zalika shima wanda akayi kishin a kansa, shi kuma yaron ina ruwansa?".
Inna ta kuta tace "ni yanzu wani abu kika ga nayi masa, ko kallon banza banyi masa ba ballantana tsawa ko hantara. Abinda nace shine babu ruwa na dashi yayi gabas inyi yamma tunda wanda ya ha蓷a din ya raba yanzu. Ba shikenan ba." Mama tace "amma at least magana mai dadi ma ai sadaka ce musamman ga maraya, yaron nan bashi da wani gata fa yanzu sai Allah" Inna tace "wai ni Hafsa kin manta da irin wahalar da nasha ne a dalilin uwar yaron nan, kin manta da irin kiyayyar da aka nuna min saboda ba'a aure ta ba? Saboda ita ake so bani ba? Kin manta? Kin manta har sakina akayi a kanta aka kuma dauki yata aka bata. Babu irin kokarin da banyi ba dan in jawo hankalin mijina zuwa gareni amma har ya bar duniya idanunsa ita suke kallo, zuciyarsa baki daya tana gunta duk kuwa da cewa nice uwargidan sa, nice uwar yayansa, ni ce yar uwarsa kuma ni ce wadda ya aura a budurwa ita kuma bazawara. To yanzu sai kiga laifina dan nace bana bukatar duk abinda ya shafe ta? Dan nace bana son ganin abinda zai tuno min da ita?"
Mama tayi ajjiyar zuciya tace "shikenan. Allah ya kara sanyaya miki zuciyarki amma zan sake tuna miki da cewa yaron nan yana da gado a dukiyar da hamma Usuman ya bari, dai dai abinda zaki samu shima haka zai samu shida yaya ladi. Dan Allah Adda a fitar musu da abinsu a basu kinsan shi gado wuta ce, annabi ya fada cewa da mutum yaci gadon maraya gwara ya cika cikinsa da wuta." Inna tace "wannan kuma masu rabon gadon ai sunsan wannan karatun, kuma nasan zasu basu abinsu duk samda aka zo rabawa" Mama tace "yaushe za'a zo rabawar? Ai yanzu ne yake bukatar su, tunda kin ki daukarsa ai kamata yayi a raba gidan a bashi kason uwarsa sai ya fitar da kofa ya zauna a ciki" Inna tace "wai ni Hafsa ki gayamin kina baya na ne ko kina bayan yaron nan ne?" Mama tace "ina bayanki Adda, wannan kuma shi yasa nake gaya miki gaskiya".
A haka mukayi sati biyu a gidan, kallo daya zaka yi min kasan gabaki daya hankali na baya tare dani duk na kara ramewa dama ni ba jiki ba, kullum ina cikin tunanin halin maraicin da muka shiga ciki da kuma tunanin halin da Sadauki yake ciki. Ko wajen gate bani da damar fita saboda kullum ina tare da Inna ko aike na waje ba'ayi saboda akwai yan aiki da masu gadi. Rannan naji Hajiya Yalwati da tazo dakin mu tana cewa "wannan yarinyar kuwa anya ba sai anyi mata rubutu ba? Ita kadai sai inga kamar tana zabura" Inna tace "haka take yi wallahi, ina lura da ita ko baccin kirki bata yi" nan Hajiya Yalwati ta saka ni a gaba da nasiha akan yarda da kaddara mai kyau da marar kyau sannan tace inzo muje dakinta ta bani littafin wasu adduoi da zasu taimaka min. Naje na karba kenan na taho ina hanyar dawowa sai ga Murja da sauri tazo gurina tace "Diyam wai kizo wani yana kiranki a waje" nayi sauri na toshe mata baki muka matsa can gefe na tambayeta waye "to ni ina zan sani, mai gadi ne dai yazo ya a kiranki sai ya ganni ya fada min, wai wannan wanda yake zuwa gurinki sanda kika zo hutu" naji wani adrenaline rush yazo min, nayi kamar zan tafi dakin Inna sai kuma na dawo da baya na zare hijab din jikin Murja na saka nace "Please kar ki gaya wa kowa yanzu zan dawo" sai na wuce da sauri ita kuma ta bini da ido.
Da sauri na nufi inda muke zama in yazo, ji nake kamar inyi tsuntsuwa ko zanfi sauri. Tun daga nesa na hangoshi kuma na gane shi sannan naji dadin ganin sa sosai. He looks good, and that was all that matters to me a lokacin. Ina karasawa na lura da kayan jikinsa sababbi ne kuma masu kyau, he smells good too. Sai dai fuskarsa ce tayi betraying emotions dinsa dan idonsa ya fada ciki sosai kuma zagayen idonsa yayi baki alamun baya samun isashshen bacci. "Sadauki" na kira sunan sa da karyayyiyar murya, bai amsa ba sai murmushi da yayi min mai kokarin boye damuwarsa. Muka karasa zagayawa bayan dakin maigadi, Sadauki ya zauna akan ginin suckaway, wannan ya bani damar ganin gefen kansa inda akayi masa dinki. Na zauna nima a kusa dashi ina fuskantar sa kawai sai hawaye suka fara zarya a kumatu na, bai hanani kuka na ba sai ma ya miko min handkerchief dinsa na cigaba da kuka na, sai dana gama na share hawaye na sannan yace "dama mai neman kuka ne aka jefe shi da kashin awaki, ke din dama kuka baya miki wahala" nace "Allah yaji kan Baffa da Ummah" yace "ameen. Naje na kai musu ziyara kaburburan su. Suna kwance a sides din juna kuma ina fata da zaton suna aljanna a tare" sai naji dadi sosai a raina, dadin yadda naga ya dauki abin nima sai naji na samu courage din facing rayuwa a koya tazo min. Nace "kai kuma fa? Wanne hali kake ciki? A ina kake a zaune?" Yayi murmushi yace "ina gurin Alhaji Bukar (mutumin da yaya ladi take gurinsa) and they are treating me well, too well even. Ya gaya min cewa zai kaini gurin mahaifina, ya san shi ashe" na bude ido da baki "wow. Congratulations Sadauki, yaushe zaku je?" Ya girgiza kansa yace "I don't know. Ban san shi ba Diyam, bansan waye shi ba and for all I know zata iya yiwuwa ma bai san nayi existing ba, zai iya yayi denying dina yace ni ba dansa bane ba" Nace "amma ta yaya zaka sani in baka je ba? Nasan Sadauki na babu abinda yake tsoro just go kayi clearing doubt dinka and move on" ya gyada kai yana kallona yace "so I have your blessings kenan ko?" Nace "of cause you do".
Sai kuma na tambayeshi abinda yake raina tunda na ganshi "Sadauki me yasa kazo? Bayan abinda Inna ta tayi maka bayan yanzu babu Baffa kuma gashi ka samu wani mai rikon gashi kuma zaka je gurin babanka, me yasa kazo gurina? Ba ka gudun a wulakanta ka?" Ya dan bata rai yana kallona yace "me yasa ba zanzo ba to? For starters I love you, always have and always will. Na biyu duk abinda ya faru dani babu abu daya da yake laifinki dan haka baxanyi fushi dake akan abinda ba ke kika yi min ba. Na uku Baffa, a gurina darajar Baffa ta wuce in yi fushi da iyalinsa dan babu ransa, sannan........" Sai yayi shiru yana kallona, nace "sannan me?" Ya sauke idonsa kasa Yace "sannan lokacin da mukayi accident din, he looked at me straight in the eyes ya ce in wani abin ya same shi in kula daku ke da Asma'u".
Na sunkuyar da kaina inajin sabbin hawaye suna zubo min. Yace "amma bansan ta yadda zan iya kula daku ba Diyam, innar ku bata so na na sani, bansan ta yadda zan iya juyo da hankalinta ta soni ba tunda bansan abinda nayi mata wanda ya saka bata son nawa ba balle in daina. Diyam ina tsoron kar lokacin auren ki yayi in nema a hana ni akan dalilin da ni kaina ban sani ba, I don't think my heart can take that". Mun jima muna hirar yadda future dinmu zata kasance, sai daga baya yace "bara in tafi Diyam kar in jawo miki fada. I just want you to know cewa am okay, dan haka kema ya kamata ki rage wannan koke koken haka ki tsayar da hankalinki guri daya. And everything is going to be alright" nayi murmushi nace "ai na samu strength daga gurinka Sadauki, kayi sharing strength dinka dani" ya mike tsaye yana kallona yace "Aliyu shine sunan, Sadauki shine inkiyar, so ofcause am going to be alright". Muka yi sallama yana yi min alkawarin in sun saka ranar zuwa gurin babansa zai zo ya gaya min saboda inyi masa addu'a.
Shine a gaba ni ina binsa a baya, muna fitowa yayi hanyar gate ni kuma nayi hanyar cikin gida ina waigensa, a lokacin ne kuma aka budewa Alhaji Babba gate ya shigo gidan sukayi clear da Sadauki kafin Sadauki ya fita. Na kara sauri kafin yayi packing Ina jin bugun zuciyata yana karuwa amma ina kama handle din kofa naji muryar Alhaji Babba a baya na yace "Diyam, zo nan"
Not edited. In anga typos ayi hakuri Please.
[1/23, 10:35 PM] Zuraiyah Zuzu 馃専: 鉂わ笍 DIYAM 鉂わ笍
By
Maman Maama
Episode Twenty Four : Red Handed
Na juyo na ganshi a tsaye a gaban motarsa yana kallona, na dawo baya a zuciya ta ina karanto duk addu'ar da tazo bakina na durkusa a gabansa nace "gani Alhaji" ya nuna hanyar gate "waye wancan da na ganku tare?" Nayi shiru kaina a kasa "ya sunkuyo yace "ba'a koya miki in manya suna magana ba'a yin shiru a rabu dasu ba?" Na sake yin shiru ina jin hawaye yana taruwa a idona, ya kama kunnena ya murda, nayi kara na mike tsaye yace "waye wancan nace miki" cikin azaba nace "Sadauki ne" ya sake ni ya kwalla wa maigadi kira, baba audu ya taho dagudu ya durkusa a gabansa yace masa "wanene yace kake barin 拼a拼an iska suna shigo min gida?" Dattijon ya kalle ni sannan yace "bansan baka so ya shigo ba Alhaji, da yake naga duk sanda tazo gidan nan yana zuwa gunta ne na dauka dan uwanku ne" Alhaji Babba yace "babu abinda ya hada mu dashi, daga yau in ka sake barinsa ya shigo gidan nan a bakin aikin ka. Ina fatan ka fahimta" yayi saurin gyada kai "na gane Alhaji, insha Allah hakan ba zai kuma faruwa ba, ayi hakuri Alhaji".
Alhaji Babba ya juyo kaina yace "ke kuma muje gurin Amina ta gaya min idan da saninta kike shigo min da kattin banza cikin gida" na juya da sauri ina tafiya blindly, kafafuwana suna hardewa kamar zan fadi har na shiga dakin Inna na tarar da ita ita kadai da charbi a hannunta tana lazumi, ta dago tana kallona da mamaki "ke kuma lafiya kamar wadda aka koro? Me ya faru" ban bata amsa ba Alhaji Babba ya shigo dakin, ta mike da sauri dan hardly ne ka ganshi ya shigo cikin main gidan saboda part dinsa a waje yake. Yana nuna ni yace "kinsan Sadauki yana zuwa gurinta?" Ta bude baki tana kallona da mamaki sannan ta fara tafa hannu tana salati "Diyam? Yanzu sai da kika jajibo mana yaron nan har gidan nan? Wato duk abinda nake fada ta bayan kunnenki yake bi yake wucewa ko?" Yace "mai gadi yace min dama ya saba zuwa gurinta a duk sanda tazo gidan nan. Wato yar mitsitsiyarta da ita har ta fara jawo mana yaran banza marasa asali da tushe zuwa gida ko?" Inna tace "Alhaji kayi hakuri, anyi an gama insha Allah ba za'a sake ba. Yarinyar nan bata jin magana, babu yadda banyi da ita ba akan yaron nan tun kafin ta kai haka amma taki rabuwa dashi. Yadda kasan yadda Zainabu ta shanye marigayi haka shima yaron nan ya shanye Diyam" Yace "au kice min tafi 茩arfin ki kenan bata jin maganar ki" ya kuma kama kunnena, na saki karar azaba yace "ni in nayi magana ba'a tsallake ta a gidan nan, daga yau sai yau babu ke babu Sadauki" ya sake ni ya juya yana cewa "shi kuma duk sanda ya sake zuwa gidan nan sai ya gane bashi da wayo, sai na rufe shi naga wanda zai fito dashi, sai naga wanda ya tsaya masa a garin nan".
Bayan ya fita Inna ta bini da kallo ina rike da kunnena ina kuka, ta koma ta zauna a bakin gado tana kallona ina jiran ta dora daga inda Alhaji ya tsaya amma sai naji tayi tsaki tace "ba kya jin magana Diyam. Ke indai akan wannan yaron ne ba kyajin magana wallahi" ta dauke kai ta cigaba da jan charbin ta sai kuma tace "zo inga kunnen" na rarrafo nazo gabanta, ta duba kunne na ta shafa min vaseline.
Ranar haka na karasa ta cikin kuncin rai da kunan zuciya tare da fargaba, ni bawai fadan Alhaji Babba ne ya dame ni ba illa furicin da yayi akan sadauki, cewa da yayi zai sa a kama Sadauki duk sanda ya sake zuwa gidan nan, na kuma san alkawarin da Sadauki yayi min cewa zai dawo yayi updating dina akan duk abinda ake ciki dangane da mahaifinsa kuma nasan Sadauki baya karya alkawari idan yayi kuma bana jin zai fara daga yanzu. Option dina daya ne dole in nemi Sadauki in yi warning dinsa kuma in hana shi zuwa duk da cewa hakan yana nufin zamu kara nisanta da juna, amna gwara hakan akan abinda za'ayi masa in yazo din.
Bayan kwana biyu duk na kara diriricewa, ko yaya naji hayaniya a waje sai inji gaba daya hankalina ya tashi inyi tunanin ko Sadauki ne yazo aka kama shi. Rannan dai sai wata dabara ta fado min. Da daddare muna zaune da Inna nace mata "ni kuwa Inna ina so in tambayeki ko muma za'a saka mu a islamiyya ni da Asma'u. Kinga duk ana wuce mu a karatu muna zaune a gida" Inna tace "Wallahi nima zancen islamiyyar nan yana raina tunda muka zo na dauka za'a saka ku amma har yanzu shiru. Amma bari in hafsa tazo sai insa Mukhtar ya kai ku ko kuma in saghir ya zo gari in roke shi ya saka ku" nace "Inna yanzu islamiyya ma sai mun jira wani yazo ya saka mu? In kin yarda kawai in bi su murja in tambayi malaman abinda ake bukata na sabon dauka" ta danyi tunani tace "shikenan, ki bisu din". Ai kuwa na samu chance.
Washegari na shirya na kama hannun Asma'u muka je islamiyya na tambayar mana komai aka yi min bill, kamar yadda nayi tunani sai yasaiyadin yace mu shiga aji mu zauna, dai na tura Asma'u ajin su ni kuma nace zan je in dauko Alqur'ani na daga nan sai na kama hanya. Bani da ko kwandala dan haka na dauki hanya a kafa ina ta zabga sauri kamar zan tashi sama amma a raina sam banga nidan tafiyar ba, nasan gidan Alhaji Bukar inda yaya ladi take anan bayan layin mu yake dan haka nan na dosa, a ringa bi ta lunguna in tsallaka wannan titin in shiga wannan lokon bansan cewa na gaji ba sai da na ganni a kofar gidan, na tsaya a gaban mai gadi ina haki shikuma yana kare min kallo, sai da na gama tsaida numfashi na sannan nace "dan Allah baba Sadauki nake nema. Allah yasa yana nan" ya ajiye radiyon hannunsa yace "dazu ya shiga, bara in dubo miki shi" sai naga ya doshi boys quarters ana jima wa sai gasu sun fito a tare Sadauki ya doso ni da sauri fuskarsa cike da damuwa "Diyam? Lfy? Daga ina kike haka?" Na danyi masa murmushi sai naga yayi ajjiyar zuciya, ya kalle ni yace "kar dai kice min a kafa kika taho" na gyada masa kai sai ya jani zuwa kujerar mai gadi na zauna shi kuma yayi kneeling a gaba na yana mammatsamin kafata yace "me yasa kika taho a kafa Diyam? Ko menene ba zaki bari inzo ba sai ki gaya min? Yanzu da wani abin ya same ki kuma fa?" Nace "You don't understand, gaya maka zanyi kar kazo din ai" sai na bashi labarin abinda Alhaji Babba yace.
Sai naga fuskarsa ta chanja gaba-daya yace "Diyam mai nayi wa mutanen nan ne wai? Su kansu ba zasu taba iya fadar abinda nayi musu ba haka nan kawai suke ji a ransu basa sona" ya dago kai yana kallona yace "Diyam ni nasan ba zasu bani ke ba" nayi saurin girgiza kaina nace "da sauran lokaci ai Sadauki, ka tuno abinda Baffa yace? Sai na gama makaranta na shiga jami'a tukunna? Kafin nan zasu chanja ra'ayinsu zasu fahimci ko kai waye ne. Yanzu ka yarda Alhaji Bukar ya kai ka gurin abbanka tunda wannan zai kara sassauta zuciyarsu tunda suna cewa baka da asali" ya gyada kai yace "you are right. Gobe dama nayi niyyar zanje in gaya miki cewa jibi zamu tafi. Maiduguri yace zamu je" na bude ido ina mamaki, sai kuma na fara sharar hawaye, yace "sarkin kuka, kukan menene kuma kike yi?" Nace "Maiduguri fa da nisa" yace "kuma ce miki akayi a can zanyi ta zama. Nima ai bazan iya zama a can ba zanje in gansu ne kawai in dawo nan ko dan makaranta ta ma" sai kuma ya bani labarin wani abokin Baffa da Baffan ya hada su dan yayi masa hanyar admission, yace "ranan nan bayan nayi welcome back din layina sai ya kirani yayi min gaisuwar Baffa yace min insha Allah wannan admission din dani a ciki. Kinga zan dawo ko dan makaranta ta, besides, ni bazan iya rayuwa nesa dake ba"
Na makale kafada nace "Allah yasa dai kar Borno tayi dadi ka manta da Diyam" yayi murmushi yace "maganar kike so, sau nawa zan gaya miki cewa babu rayuwa a tare da Sadauki in babu Diyam ba. Life without you will not be just unbearable it is unimaginable. I can't imagine me without you". Sai kuma muka shiga hira kamar bamu da wani problem, yana ta tsara min yadda yake yana planning din rayuwar mu tare, hatta fasalin yadda zai gina mana gidan mu a filin da Baffa ya siya masa sai da yayi min. Ga iskar gurin tana yi mana dadi. Jin mu muke a saman gajimare, tamkar together zamu iya facing duk mutanen duniya
Mun jima tare sannan ya duba agogon hannunsa yace "Diyam, tashi maza in raka ki ki hau daidaita ki tafi, ashe lokaci ya tura bamu sani ba". Sai naji kuma kamar bazan iya tafiya ba kamar inyi zamana a gurinsa mu tafi Maidugurin tare amma nasan hakan ba zai yiwu ba, shima ganin yadda na damu sai duk jikinsa yayi sanyi. Ya dauko biro ya kama hannuna ya rubuta min number dinsa yace "ga numberta nan, ba wai rubutawa zakiyi a wani wajen ki boye ba a'a haddacewa zakiyi a kanki, if anything happens kafin in dawo, if you need anything ko menene ki samu aron waya ki kira ni. Kafin ki koma makaranta insha Allah zan dawo. Ki ringa yi mana addu'a" na gyada kai ina karajin jikina yana kara sanyi.
Ya raka ni waje ya tarar min adaidaita ya bashi address ya biya kudin, sai kuma ya tambaye ni in inason kudi. Na girgiza masa kai, kamar ba zai matsa ba yana kallon fuskata sai da mai adaidaitan yayi masa magana tukunna sannan ya ja baya muka tafi. Na waiga ina kallonsa sai yayi murmushi ya daga min hannu.
Daga dan nesa da gidan Alhaji Babba nace a sauke ni, ina sauka na juya da niyyar in karasa sai naji daga bayana ance "Diyam daga ina kike?" Na juya muka hada ido da kawu Isa shida wani mutum suna tafiya a kasa, na durkusa na gaishe su fuskata cike da rashin gaskiya, ya sake maimaita min tambayar, cikin in ina nace "Inna ce ta aike ni gidan Mama" ya gyada kai yace "to ki gaisheta, amma dan sahun ai daya karasa dake ciki" sai nace "zan biya ne ai ta islamiyya in tafi da Asma'u".
Nayi sa'a ina zuwa gida na tarar an taso yan makaranta na shiga cikin su muka shiga cikin gida. Bana jin dadi kuma bana so Inna ta gane dan haka nace da Asma'u ta tafi ta gaya mata mun dawo ni kuma na bi Murja muka tafi part din Hajiya Yalwati. Muna zuwa na kwanta a kujera ina jin kamar zanyi zazza蓳i, Hajiya Yalwati ta tambayeni "lafiya?" Sai na gyada mata kai inajin kamar zanyi kuka, sai kawai ta rabu dani tana tunanin ko Baffa na tuno.
Kwana biyu bayan nan, ranar da nake lissafin su sadauki sun tafi Maiduguri, mun fito zamu tafi islamiyya sai muka tarar da Alhaji Babba, kawu Isa, Inna da Hajiya Babba suna zaune a babban palo da alama magana mai muhimmanci suke yi. Muka gaishe su har zamu wuce sai ji nayi kawu Isa yace "Amina ki daina aiken Diyam ita kadai gwara kiyi wa Hafsan waya ta bawa Mukhtar ko menene ya kawo miki" na kara sauri kamar zan tashi sama, na kusa gate kenan naji an kwalla min kira, na runtse idona na kasa motsi, "Diyam ki zo ana kiranki" murja ta dafa ni tace "number dinki ta fito, good luck, ni nayi gaba"
[1/24, 9:57 PM] Zuraiyah Zuzu 馃専: 鉂わ笍 DIYAM 鉂わ笍
By
Maman Maama
Episodes Twenty Five : A Day To Remember
Na juya ina kallon kofar palon amma na kasa motsa kafata ballantana in tafi, Inna na gami ta budo kofa a zuciye tana kallona "ba kiranki ake yi ba?" Na taho a hankali ko wacce gaba ta jikina tana rawa, ina shiga Inna ta tunkuda keyata na durkusge a tsakiyar palon kaina a kasa. Kawu Isa yace "Diyam, shekaran jiya da na ganki kin fito daga adaidaita sahu daga ina kike?" Ban amsa ba kuma ban dago ba, Alhaji Babba yace "idan anayi miki magana kina yin banza da mutane sai na kakkarya ki anan gurin, ba zaki ansa ba" na fara rera kuka "dan Allah kuyi hakuri kar ku dake ni, dan Allah" Kawu Isa yace "ba zamu dake ki ba indai kika gaya mana gaskiya. Ina kika je ranar nan?" na cigaba da kuka na "wallahi Kawu na daina bazan sake fita ba". Na dago kai muka hada ido da Inna ta rafka tahumi tana kallona, nayi sauri na sunkuyar da kaina, tace "ba zata fadi inda taje ba fa, amma ni nasan inda taje, ba zai wuce gurin wannan bakin mayen ba" ta juya tana kallon Alhaji Babba tace "rannan ba kace in ya sake zuwa gidan nan sai ka kama shi ba? To shine ita ta tafi gurinsa tunda shi an hana shi zuwa. Wato dalilin da yasa kika nace sai na saka ku islamiyya kenan ko?" Na girgiza kaina da sauri "wallahi Inna ba haka bane ba, ranar nan ne kawai naje kuma bazan sake zuwa ba" Kawu Isa yace "to me kika je yi ranar? Me ya kaiki gurinsa?" Ina sheshsheka ina kuma wasa da fingers dina nace "ce masa nayi kar ya kuma zuwa gidan nan" Alhaji yace "au saboda nace zan saka a kama shi shine kika je kika gaya masa ko? To in nayi niyyar rufe sadauki kaf garin nan akwai wanda ya isa ya hana ni ne? Yanzun ma kuma zan tura har gidan da yake takama dasu din insa akama shi a dan lallasa min shi yadda nan gaba ko kince masa zaki je shi da kansa zai hana ki" Kawu Isa yace "tashi ki tafi" nayi sauri na mike nayi hanyar waje sai Alhaji Babba ya ce "kar ki fita daga gidan nan. Kin gama zuwa islamiyya ai. Zo ki wuce ciki" na juya na bi inda yake nuna min, muka hada ido da Hajiya Babba wadda tun da aka fara maganar bata ce komai ba tana dai bina da kallo kawai.
Kitchen din gidan na shiga, na rakube a jikin kofa na cusa kaina a tsakanin cinyoyi na, me yasa ni bani da sa'a ne? Me yasa duk sanda nayi wani abu sai an kama ni? Karya sam bata karbe ni ba? Sai kuma na kama addu'ar Allah yasa Sadauki ya tafi dan kar Alhaji Babba ya aikata abinda yace.
A palo bayan na tashi inna tace "na rasa yadda zanyi in raba yarinyar nan da wannan nataccen yaron wallahi. Nayi nayi, Allah ma ta gani nayi iya kokarina amma abin ya faskara, ni farko na dauka soyayyar yarinta suke yi, na dauka in suka fara hankali zasu saki hannun juna amma kamar kara tunzura su ake yi" Alhaji Babba yace "wai soyayya suke yi?. Diyam din yanzu harta isa yin saurayi? Shekarar ta nawa?" Inna tace "sha hudu zata yi nan da wata daya" ya gyada kai yace "ta isa kam. Matanen mu na ruga basu kaita ba ma ake musu aure. Kuma wannan tunda har tasan a raba ta da saurayi ita kuma ta dauki hanya ta bishi to lallai ita ma ta isa auren" inna tayi 茩o茩arin kare ni "ya shanye tane fa, babu maganar wanda Diyam takeji sai tasa" Alhaji Babba yace "anyi daya ai, ba za'a sake biyu ba, mu ba zamu kuma hada jinin mu da mayu ba, yadda bakin cikin Manu ya kashe Inno ba zamu bar bakin cikin Diyam ya kashe Hardo ba dan haka kija mata kunne. Babu ita babu shi, in taki kuma duk abinda ya biyo baya ita ta jawo wa kanta".
Shikenan kamar magana ta wuce, zuwa washegari na shiga harkokina sosai kamar babu abinda ya faru amma cikin raina kuma cikin sallolina ina yiwa Sadauki addu'ar samun nasara, sai inke tambayar kaina ko ya samu mahaifin nasa? Ko wacce irin karba a samu daga danginsa? Hankalina rabi yana tare dani rabi kuma yana gurin Sadauki har ya kwana uku da tafiya. A ranar da daddare aka aiko Alhaji Babba yana kiran Inna, ta dauki hijab dinta ta fita shiru shiru har na gaji da jiranta mukayi shirin bacci ni da Asma'u muka kwanta, amma sai na kasa baccin kuma nayi ta juyi ina jin wata irin muguwar faduwar gaba. Na rasa me yake yi min dadi kawai na tashi na zauna na rafka tagumi sannan sai gata ta shigo, sai kawai naga idonta kamar wadda tayi kuka amma sai ta maze tace "ke kuma me kike yi har yanzu bakiyi bacci ba?" Nace "bana jin dadi ne kawai Inna. Baffa nake tunowa" sai kuma na fara matsar kwalla, ta dauke kai tace in an tuno mamaci addu'a akeyi masa ba kuka ba" sai ta wuce can karshen gado ta zauna ta jingina kanta da jikin gadon, naso in tambayeta in wani abun yana damunta amma nasan ba lallai ta bani amsa ba dan haka sai nayi shiru na koma na kwanta ina kalllon ceiling, mun jima a haka sannan tace min "Diyam Baffanku ya mutu ya huta, mu da muke duniyar mu mune cikin wahalarta" na runtse idona ina tunanin ma'anar maganar ta ta.
Washegari bayan na tashi da assuba nayi sallah sai na koma baccin safe, cikin bacci na kawai naji muryar mama a dakin na farka ina mamakin me take yi a gidan da sassafe? Sai naji Inna tana cewa "ni wallahi Hafsa kinfi kowa sani, bana son yaron nan sam zuciya ta bata sonsa ballantana har inyi sha'awar ya zama surukina amma duk da haka saghir fa...." Sai kuma suka ga ina kokarin mikewa sukayi shiru. Na tashi na gaishe da Mama, sai naga fuskar Inna still akwai bacin rai idonta kamar batayi bacci sosai ba, sai kawai naji ina son inji maganar da suke yi. Sai na bude toilet na shiga na rufe na kunna pampo kamar zanyi wani abu amma sai na dawo na sakakunne na a jikin keyhole.
Sai naji Mama tana cewa "wannan gajeriyar matar tasa ce zata kissima masa, shi kuma ya hau ya zauna saboda son kansa, amma suma kansu sunsan ai Diyam ba sa'ar auren Saghir ba ce ba, ya ninka ta a shekaru fa, gashi da budadden ido ita kuma fa? Yarinyar da junior waec kawai ta rubuta? Akwai cutuwa sosai a hadin su" Inna tace "babu fa abinda ban gaya masa ba jiyan, sai yaji haushina ma wai ina so in nuna ni na haifi Diyam basu ba, wai ita suke wa gata, wai baza ta taba samun miji irinsa ba, wai gata suke yi mata albarkacin zumunci albarkacin maraicinta" ta danyi tsaki tace "ni da ace Diyam ta fi haka girma ne, da ace misali ta gama makaranta ne wallahi da bani da dumuwa. Ni yanzu abinda nake so kice masa idan kinje shine, ki roke shi a bar yaran su daidaita kafin ta gama makaranta".
Na sulale ma zauna a kasa a jikin kofar. Naji dai suna maganar aure, kuma naji sun ambaci sunana sun kuma ambaci sunan Saghir. To tambaya ta anan itace auren wa za'ayi? Aurena za'ayi ko auren saghir za'ayi? Dan kaina ba zai iya daukan aurena da saghir a sentence daya ba ballantana 茩wa茩walwa ta ta fahimci cewa aure za'a hada ni da saghir. Na wanke fuskata nayi brush na fito ina murmushin yake, suma duk yaken sukayi min har na zauna na fara breakfast sai na lura duk sun zuba min ido suna kallona. Sai na samu kaina da tattauna abincin amma makogwarona yakasa budewa ballantana in iya hadiyewa.
Muna nan zaune babu mai magana sai ga aike aba kiran Mama inji Alhaji Babba, ta tashi ta tafi muka cigaba da zama ni da Inna sai ga wani aiken wai inna taje itama, tana tafiya na rufe abincin gabana na tashi na kwanta a kan gado trying hard not to think, trying hard not to let my brain assess maganar da naji su Inna suna yi. Ba zan iya tuna adadin mintina ko awannin da suka wuce ba sai ga yarinya an aiko wai inzo inji ana kira na a palon Alhaji, na tashi na saka hijab dina still trying not yo think na fara tafiya blindly zuwa part din Alhaji Babba.
Na murda kofar na shiga da sallama. Duk suka dago kai suna kallona kamar yadda nima nake bin su da kallo. Alhaji Babba, Hajiya Babba, Inna, Kawu Isa da kuma Mama. Na durkusa na gaishe su da muryar da a kunnena naji kamar ba tawa ba. Suka amsa sannan duk suka zuba min ido suna kallona. Alhaji Babba ne yayi magana "Diyam a matsayin mu na iyayenki wadanda baki da wadanda suka fimu kaf duniyar nan mun yanke shawara a kanki. Zamu hada auren zumunci tsakanin ki da yayanki Saghir".
"Dama an jima da bani shawarar cewa babban abinda zai saka Saghir ya zauna a guri daya ya nutsu shine in na samu kyakykyawar yarinya na aura masa, tun a lokacin Diyam ce ta fado min a raina na kuma kuduri aniyar hada su aure in ta isa auren, to kuma yanzu ganin har ta fara iya bin saurayi zuwa gidansu na fahimci ta isa auren a yanzu, dan haka za'ayi yanzu. Diyam zaki cigaba da karatu kamar yadda mahaifiyar ki ta bukata, amma ba zaki koma makarantar kwana ba, za'a saka ki a day ki karasa secondary, in kin gama in mijinki ya yarda sai ki cigaba in bai yarda ba kuma shikenan. Bamu saka rana ba tukunna, na kira shi Saghir din nace masa lallai ya hawo jirgi yazo ya gobe ina nemansa, in yazo sai muji tsare tsarensa sai mu samu saka lokacin. Shikenan abinda zan ce miki Diyam, tashi ki tafi".
Na tashi kamar yadda yace, amma sai kafafuwana suka lankwashe na fadi a gurin, Inna da Mama suka yo kaina a tare amma kafin su karaso na sake mikewa na kama hanyar na fice. Bansan ya akayi nazo ba kawai sai gani na nayi a dakin inna, na durkusa a gaban gado gabaki dayan jikina yana karkarwa kamar ana kada mazari amma idona babu hawaye, lallai wani tashin hankalin yaji gaban kuka. Baffa naji ya fado min arai, na tuna maganar sa sanda yake mana fada ni da sadauki "waye kuke tunanin zaiyi muku aure yanzu? Ba dai ni babanku ba" ashe haka maraici yake? Ashe haka rashin gata yake?
A gefe na naga handbag din Mama, na dauka da sauri na bincike da dauko wayarta, babu tsoro ko kadan a raina nayi dialing number din da Sadauki ya bani.
Ring biyu ya dauka, muryarsa as clear as yana gabana a tsaye wannan yasa na samu relief na san at least lafiyar sa kalau. Yayi sallama amma ni sai na kasa magana saboda karkarwar da baki na yake yi, sai kuma kuka ya kwace min. Na fara rera wa ba kakkautawa nan take ya rikice "Diyam?? Ya Salam Diyam kiyi min magana menene? Me ya faru Diyam? Please talk to me" shima kamar zaiyi kukan, na tsagaita nace "Sadauki ka taimaka min, Sadauki aure za'ayi min wai" yayi shiru kamar baiji ba sannan yace "what?!!!" Nace "yanzu suka kira ni suka gaya min, aure zasu yi min Sadauki, wai hamma Saghir zasu aura min" yace da sauri "su? Su waye su? Diyam kar kiyi min wannan wasan bana so" na lissafa masa duk wadanda suke gurin sanda akayi maganar nace "da gaske suke Sadauki, wallahi da gaske suke, Sadauki mutuwa zanyi ka taimaka min". Yace cikin muryar da ban taba jin yayi magana da irinta ba "Diyam listen to me, zan ajiye duk abinda nake yi zan taho kano gobe and I promise you I will not let anything bad happens to you".
Kofa ta bude inna da Mama suka shigo fuskarsu babu yabo babu fallasa, sai kuma suka tsaya suna kallona da waya a hannu ina kuka. Na sauke wayar daga kunne na ina ji a raina bana jin wani tsoro kuma, wanne punishment za'a yi min wanda yafi wannan da aka riga akayi min?
[1/25, 11:53 PM] Zuraiyah Zuzu 馃専: 鉂わ笍 DIYAM 鉂わ笍
By
Maman Maama
Episode Twenty Six : Forever and Ever
Alherin Allah ya kai gun masoya na a duk inda kuke. Ina gani, ina karantawa kuma ina godiya da duk comments dinku, it kept me going.
This page is dedicated to duk wadda za'ayiwa ko kuma aka taba yiwa auren dole.
This page is dedicated to duk saurayin da aka raba shi da budurwarsa ba tare da wani cikakken dalili ba.
This page is dedicated to duk iyayen da suke da ra'ayin yiwa yayansu auren dole. Ina fatan wannan labarin zai saka ku chanza ra'ayin ku.
Ku fahimce ni sosai, auren dole nake nufi bawai auren ha蓷i ba, akwai banbanci tsakanin arranged marriage da kuma forced marriage.
Mama ta shigo ta karbi wayar daga hannuna tayi cutting kiran. Bata ce min komai ba ta saka wayar a jakarta ta harhada sauran kayanta ta rataya jakarta. Inna tace "ba dai tafiya zaki yi ba" Mama tace "tafiya zanyi, ni ba zan iya kallon wannan kayan takaicin ba, Allah ya bamu alkhairi". Ta juya da sauri ta bar dakin. Inna tayi ajjiyar zuciya dan ta fahimci Mama fushi tayi akan magana ta, tazo ta zauna a bakin gado daga gefena tace "shi kika kira ko? Diyam taurin kanki ne yake jawo miki koma menene akeyi miki. Ke ba kya jin magana ta, da ace tun farko da na hanaki kulashi kin daina ai da bata kai ga haka ba" tayi shiru tana sauraron kuka na, sannan tayi tsaki tace "nima zuciyata ba son hadin nan naki da saghir tace ba kawai dai dan babu yadda zanyi ne, ba wai saghir din ne bana so ba a'a auren ki ne yanzu bana so, duk da dai kamar yadda Alhaji ya fada ana yiwa wadanda basu kaiki bana aure kuma su zauna amma nasan da babanki yana nan da bazai miki aure yanzu ba. To ni wannan shine damuwata. Amma in kika duba ta wani bangaren fa zaki ga gata akayi miki, Saghir yafi wancan yaron da kike ta naci komai, yafishi kudi ya fishi kyau ya fishi asali ya fishi shekaru ya fishi hankali ya fishi wayewa sannan uwa uba gashi dan uwanki. To me kike nema kuma bayan duk wannan" a hankali cikin dasashshiyar murya nace mata "bana son shi Inna. Bana son Saghir Sadauki nake so, bana son aure yanzu karatu nake so. Inna ki taimaka min kar kuyi min auren dole" sai na dora kaina akan cinyarta na cigaba da rera kuka, ta dora hannunta a kaina tana shafawa, a hankali tace "gata akeyi miki Diyam, yanzu ba zaki gane ba sai nan gaba".
Kafin azahar zazza蓳i mai zafi ya rufe ni, ko palo ban kuma lekawa ba ina kwance daki a kudundune ina karkarwa. Ina jin yan gidan suna ta zuwa dubani kuma nasan da yawa daga cikinsu tsegumi ne yake kawo su. Ina jin Hajiya Yalwati ta shigo itama suna ta magana da Inna "amma dai Amina in kika yarda da wannan hadin kun zalinci yarinyar nan wallahi. Saghir in ana so ya shiryu ai gagarumar mace wadda taga jiya taga yau za'a samo a hada shi da ita ba yar mitsitsiyar Diyam din nan ba, ya zata yi dashi?" Inna tace "to wai Yalwati ya kuke so inyi ne da raina ne? Nima fa ba son abin nan nake yi ba amma ya zanyi? Yanzu zan iya cewa da Alhaji Babba ba zai aurawa Diyam Saghir ba? Duk duniya tana da wadanda suka fisu ne ko kuma ni duk duniya ina da wadanda suka fisu ne? Hakuri kawai zatayi nima kuma inyi hakurin sai mu hadu muyi tayi musu addu'a. Duk wannan koke koken nata daga anyi auren fa shikenan. Yara nawa ne akayi musu auren irin haka kuma gasu nan har sun hayayyafa sunyi zaman su" Hajiya Yalwati tace "to ba dole suyi zamansu ba tunda sun hayayyafa? Amma kije ki tambayesu kiji idan har yau abin baya musu ciwo a ransu. Kije ki tambayesu kiji irin wahalar da suka sha kafin su hakura din. To wannan fa wai ina yi miki magana ne akan in mace bata son miji aka aura mata shi to ina ga in shi din ma baya sonta? Kar ki manta Saghir fa bashi yace yana son Diyam ba. Kinsan kuwa ciwon auren wanda baya sonka? Kinsan kuwa irin bakin cikin da zai ta kunsa maka?"
Inna ta dauke kanta gefe tana jin kamar bakar magana ce Hajiya Yalwati take gaya mata. Ita kuwa ita tasan bakin cikin auren wanda baya sonka don har yau tana iya tuno farkon aurenta da Baffa ko kallo bata ishe shi ba, sai gabanta ya fadi data tuno Saghir, idan har Baffa daya tashi ya kuma yi karatu a kauye yayi mata wulakanci saboda baya sonta to ina kuma ga Saghir din da ya gama bude idonsa a kasashen turawa?
Da yamma Aunty Fatima autar su Baffa tazo, ita ta tashe ni zaune tana taba jikina tace "Amina anya kuwa wannan yarinyar ba za'a kaita asibiti ba, jikin ta yayi zafi da yawa fa?" Hmmm shine kawai abinda inna tace tana jan charbi, Aunty Fatima ta bani magani na sha na koma na kwanta tana cewa "wallahi baki ji irin dadin da naji ba dazu da Alhaji Babba ya kira ni take gaya min wannan labarin, kai amma Allah ya sanya alkhairi shi kenan munyi abinmu tuwo na maina. Dama tunda Hamma Manu ya rasu yaran nan Diyam da Asma'u suke raina ina ta tunanin su kinga yanzu shikenan, in akayi auren dai ta dauki kanwarta suje can suyi zamansu kema kin huta, duk inda zai tafi yawon nasa ba sai ya saka matarsa a gaba su tafi tare ba? Itama ma a hakan zata waye din ai" a raina nace kaji wata kuma, ita wayewa ce damuwarta.
Washegari da safe jikina ya danyi sauki sai wani matsanancin ciwon kai da nake ji. Inna ta saka na tashi da kyar ina shan kunun gyadar da Hajiya Babba ta aiko min dashi wai taji ance naki cin abinci. Ina cikin sha aka budo kofar dakin kamar za'a balla ta, duk muka tsorata muka daga kai sai idona ya sauka akan Hamma Saghir da yake haki kamar wanda yayi tseren gudu, Inna tana yake tace "a'a Saghir saukar yaushe?" Ya dauke idonshi daga kanta ba tare daya amsa mata ba ya kalle ni cikin ido yace "dan ubanki, tun wuri kije ki gaya musu cewa ba kya sona tun kafin a makala min ke ki zokina nadama" ban dauke idona daga kansa ba har ya juya ya fice ya bar mana kofa a bude, na sauke kaina kasa na ajiye kunun hannuna, ina jin Inna ta tashi da sauri ta fita tana salati. A hankali naji wata irin tsana, tsanar da ban taba tunanin it is possible ba tana shiga zuciyata a game da Saghir, abinda ya fada bashi yafi bata min raiba akan ambaton ubana da yayi.
Na jawo pillow na kwanta sama sama ina jiyo hayaniya a palo, naji Inna tana tsara musu abinda Saghir yace, muryarta har kakkaryewa takeyi kamar zata yi kuka, sai kuma naji Alhaji Babba yana magana shima amma bana fahimtar me yake cewa sai can naji yace "kai ka haife mu ko mu muka haife ka? To sai an aura maka ita din in yaso in an kaita gidan naka ka kasheta kakawo mana gawarta".
Na runtse idona na jawo wani pillown na dora a kaina na toshe kunnuwana.
Da yamma Mama ta sake dawowa gidan. Inna ta tsara mata abinda dazu ya faru da Saghir. Mama tace "to dama ni abinda ya kawo ni shine in gaya miki in anjima Sadauki zai zo, ya sake kiran layi na yace min zasu zo shida dan uwan mahaifinsa da kuma Alhaji Bukar na garin nan. Abinda nake so ince miki shine dan Allah idan sunzo kema ki fito ki nuna cewa ba kya son hadin Diyam da Saghir, ki karbi Sadauki sau daya dai a rayuwarki ko dan yarki" Inna ta fara girgiza kai "na gaya miki Hafsa, kin sani kuma bana son yaron nan bana kaunarsa" Mama ta fara daukan zafi "Yanzu kinfi son ki hada Diyam da mutumin daya kalli cikin idonki ya gaya miki baya kaunar yarki akan wanda yake binki kamar zai lashi takalmin ki saboda ki bashi yarki? Wacce irin zuciya ce dake Adda?" Amma inna sai ta cigaba da girgiza kanta kawai.
Ni kuma jin maganar Mama sai naji hankalina gaba-daya ya koma kan Sadauki. Sadauki zaizo da gaske? Kuma tare da dan uwan babansa? Kenan ya ga babansa da gaske. Amma kuma har zuciya ta ina tsoron yadda zata kasance tsakanin su da Alhaji Babba.
Muna nan zaune kuwa sai ga kira a wayar Mama, ta amsa sai ta tashi tana saka hijab dinta tace "sun zo, bara inje" amma inna bata motsa ba, ni dai ina zaune ina jin jira, irin jiran da akuya take yi lokacin da aka kaita mayanka. Har wani daci daci nake ji a bakina.
Abinda ya faru a waje kuma shine; Mama ce da kanta ta shigo da Sadauki tare da wani mutum da zuka zo tare daga Maiduguri. Babban mutum ne sosai kuma kana ganinsa kaga babarbare harda tsagun su a fuskarsa. Sai kuma Alhaji Bukar wanda shine asalin wanda ya aurar da Zainabu. Suka shigo tayi musu iso har palon Alhaji Babba ba tare dashi Alhaji Babban yasan ko su waye ba ballantana abinda yake tafe dasu. Sai da yaga Sadauki sannan balli ya fara tashi yace a fitar masa dashi daga gidan sa. Mama ta roka dan Allah a tsaya a saurare su tunda dai suka taho kafa da kafa tun daga Maiduguri ai sun chanchanci a saurare su. Mutumin da hausa bata ishe shi sosai ba sai yana hadawa da turanci ya fara bayanin cewa mahaifin Sadauki ne ya turo shi yayi representing dinsa saboda shi baya kusa, gurin nemawa Sadauki auren Diyam kamar yadda shi Sadaukin ya nema. Nan take Alhaji Babba ya basu short ansa da cewa "ba za'a bashi dinba, kuma Diyam mun riga munyi mata miji. Na gama baku amsa ku tashi ku bar min gidana tun kafin in kira muku yan sanda" Alhaji Bukar yace "shikenan dai? Shikenan maganar 'yan sanda dai?" Alhaji Babba yace "ai gida na kuka shigo, dan haka duk abinda nace kunyi min ya zauna kenan" Alhaji Bukar yace "ai kai abinda baka sani ba shine, in kai baka rufe mu ba mu sai mu tufe ka kuma muga wanda zai tsaya maka ya fito da kai" Alhaji Babba yace "anji din, aure dai ba za'a bayar ba in kaji haushi kamar yadda kayiwa zainabu aure dan munki yarda Manu ya aureta to shima Sadauki ka daura masa aure gobe mu gani" Alhaji Bukar yace "tabbas nayi wa zainabu aure, aure kuma wanda manu baiyi irinsa ba, amma kuma da amincewar ta ba wai tilasta mata nayi ba kamar yadda kake da niyyar tilastawa marainiyar Allah ta auri lalataccen danka. Wallahi indai kayi mata wannan auren sai Allah ya kamaka da hakkinta tun a duniya ba sai kunje lahira ba". Ya mike tare da dayan mutumin daya ke ta mamaki yana tambayarsa dama haka mutanen suke? Anan kuma Aliyu ya girma?
Amma Sadauki sai yaki tashi daga inda yake a durkushe. Sai ya rarrafa gaban Alhaji Babba yace "Alhaji dan Allah, nasan nine ba kwaso na yarda kuma ba zaku aura min Diyam ba amma dan Allah, dan Allah Alhaji kar kuyi mata aure, in dai saboda nine to na hakura na janye neman aurenta please ku barta tayi karatunta, ku barta ta girma ta zabi wani da kanta" Alhaji Babba ya dauke kansa, Sadauki ya sake cewa "in kuma lallai sai kunyi mata aure please not Saghir, ga Mukhtar nan" ya fada yana nuna Mama, "ku aura mata Mukhtar indai har sai kunyi mata auren yanzu but please banda Saghir".
Alhaji Babba ya mike "kai a matsayin ka na waye zaka gaya mana wanda zamu aura mata da wanda ba zamu aura mata ba? To albishirin ka, Saghir din zamu aura mata kuma rana ita yau za'a daura auren idan kaji haushi kaje ka fada rijiya ka mutu".
Ina daki a kwance, na bude idona a hankali ina kallon dakin na lura Inna bata nan. Sai na tashi zaune haka kawai naji ina son in fita waje. Na fito palo sai naga Inna da amaryar Alhaji Babba a can gefe suna magana kasa kasa amma basu ganni ba, sai na wuce su na bude kofar palon na fita waje ina karewa compound din kallo, haka kawai naji zuciyata tana gaya min in tsaya anan wajen. Ban jima ba kuwa sai na hango su sun fito daga part din Alhaji Babba su hudu, manyan maza guda biyu da Mama sai kuma mutumin da ko cikin duhu na hango shi zan gane shi. Sadauki. Su biyun sauri suke yi shi kuma a hankali yake tafiya yana ta waige waige, sai kawai na sati handle din kofar na fita da gudu na tafi inda yake, tun daga nesa ya hango ni sai ya juyo ya bude min hannayensa ni kuma na wuce direct zuwa kirjinsa ya mayar da hannayen ya rufe. Na fashe da kuka ina kankame shi.
A hankali yace "shshshsh, ya isa haka kukan, stop crying please. Wai litre hawaye nawa zaki zubar ne a cikin wata daya?" Sama sama naki hayaniya a compound din amma sai nake ji kamar wani background noice ne akan maganar da Sadauki yake gaya min. "Be strong Diyam, you are stronger than this. Ki zama jaruma ki bude hannayenki ki karbi duk wata kaddara da Allah zai dora miki ki dauke ta a matsayin jarabawa, ki dauka cewa Allah yana jaraba ki ne dan yaga how strong are you for the blessings He plans a head for you. Ki sani cewa Allah yana tare dake a ko da yaushe, kuma ki saka a ranki cewa ni Sadauki zan kasance tare da ke a koda yaushe, this is my promise to you, I will be with you forever and ever, I will love you forever and ever. Always ki saka a ranki cewa an angle is watching over you. Always. No matter what happens and no matter how long"
Hayaniya ake yi sosai yayinda ni kuma nayi luf a kirjinsa ina jin kamar anan aka halicceni, ina jin muryar Inna "ba zaka shika ta ba? Maye" Alhaji Babba "kuyi ta dukansa har sai ya sakar mana 'yarmu" dan uwan baban Sadauki "kar wanda ya taba shi, wallahi duk wanda ya taba shi sai yayi nadama".
Lokaci daya kuma sai Sadauki ya sake ni, ya rike fuskata yana kallona idonsa cike da wani yanayin da ban taba gani ba and then without another word ya kama hanyar waje da sauri, ina jin Alhaji Babba yana bawa yaran gidan umarnin su dake shi amma sai naga kawai kaucewa suke suna bashi guri har ya fita. Ni nasan a wannan yanayin da yake ciki da wani ya taba shi da tabbas in bai kaishi lahira ba to kuwa zai kaishi asibiti.
Yana fita daga gidan naji wani nauyi a zuciyata, wani duhu ya mamaye idanuwana, sai kuma kafafuwana suka lankwashe na zube a gurin unconscious.
Hope ba kuyi kuka sosai ba. Lol.
Love you all.
Chears[1/27, 9:17 PM] Zuraiyah Zuzu 馃専: 鉂わ笍 DIYAM 鉂わ笍
By
Maman Maama
Episode Twenty Seven : Acceptance
Na bude idona a hankali ina kallon ceiling kamar mai son fahimtar yadda aka tsara shi. Kaina yayi min nauyi haka kirjina. Sheshshekar kukan da naji a kusa dani ce ta sakani waigawa ina kallon mai kukan, Asma'u, tayi sharkaf da hawaye da majina da gumi sai kukanta take yi bil hakki. Na tashi hannuna dafe da kaina nace "Asma'u?" Sai ta juyo da sauri ta rungume ni "Adda dan Allah kema karki mutu ki barni" na rungume ta ina dan jijjiga ta nace "bazan mutu ba kinji, ina nan tare dake" sai ta daho kai tana kallona tace "Adda wai Sadauki ya tafi da gaske? Inna tace wai ya tafi kuma ba zai kuma dawowa ba" naji gaba-daya abinda ya faru yana dawomin kaina kamar film, wani kuka ya taho min amma sai na rike shi a nace mata "zai dawo kinji Yar Asama (sunan da yake tsokanar ta dashi) zai dawo wata rana".
Na gyara mata kwanciyar ta a jikina naja bargo na lullube mu tare, sai kuma na fara bitar abubuwan da suka wakana, na hango fuskar Sadauki a idona da irin bacin ran dana gani a idonsa, na tuno kalaman daya gayamin a kunnena. "Be strong" he said, but how can I be strong without him bayan shi din shine strength dina? Yace in bude hannayena in karbi duk wani abin da ya tunkaro ni but how can I do that bayan ya sabar min da kasance wa shield dina? Shi yake tsayawa a gabana ya kare ni daga duk wanda yayi niyyar zalintata, shi ya shagwaba ni inyi duk abinda nake so saboda ina takama ina da Sadauki. Yanzu banj da Sadauki kuma. I felt so exposed. So alone. So scared. Ji naui kamar duk mutanen duniya ne suka hada kansu suke nema su zalince ni. Suddenly sai naji duk duniyar ta ishe ni, to menene amfanin zama a cikinta? Me zan tsinta a cikin rayuwar indai har aka aura min wanda bana so aka ce in cigaba da zama dashi har karshen rayuwata? Sai naji feeling irin feeling din da yammatan da suke kashe kansu saboda auren dole suka ji kafin su kashe kan nasu. Sai naji feeling irin feeling din da yammatan da suke guduwa daga gaban iyayensu suke shiga duniya suke ji kafin su gudu din, ashe dai laifin su kadan ne, ashe dai tura su akayi zuwa limit din da shaidan ya kada musu gansar sa su kuma suka bishi.
Sai dare sannan na tashi na hada sallar magrib da isha saboda wani irin zazza蓳i da ciwon kai da nake yi. 茦wa茩walwa ta ta zama blank kamar babu komai a cikinta saboda na rasa wanne tunanin zanyi. Ni dai bana so in shiga duniya saboda I might end up never seeing Sadauki again tunda bansan inda zan same shi ba. Ba kuma naso in kashe kaina saboda nasan wuta zan tafi. Bani kuma da wanda zan kai kara gurinsa saboda su masu shirin yi min auren nan su ne dangin uwata kuma sune dangin ubana, dan Alhaji Babba a lokacin zan iya cewa shi yake juya kowa a family, saboda shi yake da naira. Sai na dora goshina a kasa na fara gayawa Allah, ina rokon sa ya sakamin ga duk wanda ya zalince ni, ina rokonsa kuma ya bani karfi da juriyar daukan duk wata kaddara daya rubuta min.
A kan sallayar na kwanta na lulluba da hijab dina, ina jin Inna ta shigo ta taba wuya na sai kuma ta fita, sai gasu sun dawo da Hajiya Yalwati da Murja, ina jin su suka kamani suka saka ni a mota sannan naji muna tafiya, na dago kai na kalli Hajiya yalwati data rungume ni a cinyar ta nace "Hajiya, dan Allah bana son auren hamma Saghir". A asibitin muna zuwa suka bamu gado, sunce temperature ta tayi sama da yawa dan haka sai na kwana a gurinsu for monitoring, suka yi min allurai ciki har dana bacci dan haka na samu nayi bacci amma cike da mafarkai. Cikin mafarkan da nayi harda wanda na ganni na soka wa hamma Saghir wuka a ciki.
Washegari aka sallamo ni tare da warning cewa jini na yana neman hawa, as young as I was. Muna dawowa gida Hajiya Yalwati ta zauna tana jera wa Inna bayanin likita Inna ta fara sharar hawaye tana cewa "ni in kuna wannan maganar sai inga kamar kuna dora min laifi ne, ni ya kuke so inyi ne wai? Ta yaya kuke tunanin zan je gurin Alhaji Babba in ce masa ba zai aurawa Saghir Diyam ba? Ta yaya? Ga Hafsa ma tayi fushi dani tunda ta tafi jiya har yau taki daukan wayata" Hajiya Yalwati tace "kamar yadda shi da matarsa suka so kansu suke neman hada Diyam da tantirin dansu kema haka zaki so taki yar kice ba za'ayi ba" Inna tace "yanzu zumunci har ya kai haka lalacewa? To ku ku gaya masa mana? Ku gaya masa Diyam tace bata so gashi har tana neman salwanta saboda haka" Hajiya Yalwati ta rike baki tace "ni asu wa? Ina magana cewa za'ayi kishi nake da bakin ciki".
Da rana sai ga abinci kala kala wai inji Hajiya Babba, ko kallon inda suke banyi ba. Ana jimawa sai gata tazo, tunda muka zo gidan ban taba ganinta a dakin ba sai yau. Ta zauna a bakin gado suna gaisawa da Inna sannan ta data jikina tace min "sannu Diyam" kai kawai na gyada mata, tace da Inna "ba zai wuce malaria ba fa, ita ake ta fama yanzu" Inna ta kauda kai tace "likita yace jininta ne yake neman hawa, hawan jini ne yake kokarin kamata" Hajiya Babba ta bude baki tace "hawan jini kuma? Wa likitan ya gayawa?" Inna ta ce "Hajiya Yalwati, ita ta kaita asibitin ai" Hajiya Babba tayi murmushi tace "hmmm, neman magana ne kawai irin na Hajiya Yalwati. Babu wani hawan jini ni na sani" sai kuma ta kauda maganar "kinga fita ma zanyi nace bara inzo in duba ta. Kinsan dazu da safe Alhaji ya siyasa Saghir gidan da zasu zauna, shine yanzu zanje in ga gidan sannan inyi lissafin duk kayayyakin da za'a siya. Wannan abu ai tuwona mai na ne. Kar kiji komai duk abinda ake yiwa yarinya na gata to za'a yiwa Diyam a dakinta. Ni da kaina zan siyo komai tun daga kayan daki har kitchen".
Tana fita Inna ta bita da harara tana magana kasa kasa. Sai kuma ta dauki waya ta kira zuwa can aka dauka ta fara magana "haba Hafsa, wai dame kike so inji ne, da mutuwar mijina ko da auren dolen da za'ayiwa Diyam ko kuma da fushin da kike yi dani? Yanzu Hajiya Babba take gaya min wai an bata kudi zata siyo wa Diyam kayan daki, saboda Allah bake da Fatima ya kamata kuyi wa Diyam siyayya ba? Wannan ai ba hurumin ta bane ba. Gaskiya kizo kije gurin Alhaji sai ki nuna masa kamar baki san maganar ba ki tambayeshi ya bayar da kudin kayan dakin Diyam zaki je ki siyo mata" sun jima suna ta mayar da magana sannan suka yi sallama.
Mama bata zo gidan ba sai washegari, shima tana zuwa tace "ni fa ba wannan maganar ce ta kawo ni ba, zuwa nayi in duba jikin Diyam. Su je suyi ta siya mata koma menene ba damuwa ta bace wannan. Ni damuwa ta shine in dauko yaron nan kafa da kafa in kawo shi har gidan nan amma a wulakanta su har dake a ciki, ni da ban shi nake yi ba dan Diyam nake yi. Kuma wallahi yadda naji takaicin abinda kukayi wa yaron nan ko wallahi da niyya nayi in bashi auren Rumaisa, dan dai kawai yace min a'a ne wallahi da sai dai kawai ki gansu tare da Rumaisa sai kuma inga yadda zaki yi da shi. Suma kuma yan uwansa suka ce a'a ba yanzu zasuyi masa aure ba wannan ma dan rana daya ya tayar da hankalinsa suma kuma ya tayar musu shi yasa suka taho nema masa". Haka ta gama fadanta ta tafi babu wanda ta gaisar a gidan.
Washegari na dan samu sauki babu laifi. Amma zuciyata babu sauki a tare da ita sai ma kara zafi da takeyi kamar ana hura min wuta a cikinta. Inna ta matsamin dole nayi wanka wanda rabona dashi tun ranar da Sadauki yazo gidan. Na fito daga toilet na tsaya a gaban mudubi ina kallon kaina. I can't believe how many things ne sukayi changing a rayuwata in just few weeks? Har yanzu fa ba'ayi arba'in din baffa da Ummah ba amma wai har mutane sun manta dasu, har an shafe babinsu an bude sabon babi na yiwa yarsa aure a shekara goma sha hu蓷u. Nayi wa yarsa auren da aka san inda ace yana da rai babu wanda ya isa ya ko tunkare shi da maganar danshi ba damuwa yayi da kudin mutum ba ballantana mutum yace ya daina bashi.
Ina cikin saka kaya ne naji hayaniya a palo har da gu蓷a, sai kuma gasu Murja nan sun shigo inda nake suna ta murna da dariya. "Amaryar Hamma" Salma autar Hajiya Babba wadda ba'a jima da bikinta ba ta fada. Sai kuma suka kwashe da dariya. Kusan duk yayan Alhaji Babba wadanda suke aure dama yammata da suke gidan duk suna nan. Na dauke kaina ba tare dana kula su ba na zauna ina daura dankwali na, "munga kaya masha Allah, kaya sunyi kyau, ko dan gidan gwamna ne iya kacin kayan lefen da za'a kawo kenan" naji wani suka a kirjina "lefe? Nawa?" Sai na kwanta a kan gado na rufe idona. Ina jin murja tace "ku bata so fa, kar ku saka ta kuka" Suwaiba tace "bata son wa? Hamman? Anya kuwa akwai macen da zata ce bata son hamma komai kyanta? Kunya ce dai kawai take ji amma babu ma zancen wai bata sonsa" Aysha tace "ni kam zan so inga yayanku, wow, Diyam kyau hamma kyau, in ina da ciki zanke zuwa gidan ku dan in haifi yaya kyawawa nima" na juya baya na jawo hijab dina na rufe fuskata a raina ina cewa 'ya'ya kuma? Ni da Saghir? Tabbas nasan me akeyi ake samun yayan but I will die first kafin in barshi ya taba ni. For I thought I belong to one, and one alone. Sadauki. Sai kawai tunanin matan da suke kashe mazajensu cikin dare yazo min and it didn't look so bad.
Adda Zubaida ce ta shigo ta kore su gaba-daya. "Manya manya daku kunzo kun saka yar karamar yarinya a gaba kuna tsokanar ta" Salma tace "yar karama ce amma ta kusa shiga layin manya" suka fice suna dariya. Adda Zubaida ta zauna a kusa dani ta dafa ni taji ina sheshshekar kuka tace "kiyi hakuri Diyam kinji? Kiyi fatan wannan hadin ya zamo miki alkhairi. Duk sanda kike bukatar wani abu ko wata shawara ki neme ni kinji? Karki dauka cewa ni yayar Saghir ce ki dauka cewa ni yayarki ce kinji" na gyada mata kai.
Ina nan kwance aka yi ta shigowa da akwatinan ana jere wa a gefe, ina jin daya daga cikin yan aikin gidan da suke shigowa da kayan tace da dayar "ai ga amaryar nan a kwance" sai kuwa suka hada baki suka rangada min wata uwar guda a kaina wadda naji kamar zata tsaga min kan. Sai bayan da kowa ya watse sannan Inna ta shigo ita da Asma'u. Ta tashe ni zaune tana murmushi "tashi Diyam, tashi kiga kayan lefen ki" ta fara bubbudewa, "kinga wadannan sarkokin? Wannan zata yi miki kyau. Kinga pearls din da kike ta nacin in siya miki. Kinga wani lace? Dankari! Wannan ai na zuwa gidan biki ne. Ga takalmin can mai tsini irin wanda kike so" ni dai kallon ta kawai nake yi ko kadan banji zuciyata tayi sha'awar wani abu a cikin kayan ba, na kalli Asma'u data baje a gefe tana ta zaben kayan kwalliya wai duk tana so in bata. Sai kuma ina ta tashi ta fita ta bani guri. Na kalli kayan, akwatuna ne set hudu, pink, purple, peach da blue kowanne kuma da kyar ake rufe shi saboda kaya. Na mika hannu na na dauki wata bra ina kalla a raina nace "ko me suke tunanin zan saka a cikin wannan brazier? Na mayar da ita na ajiye na koma na kwanta na juya wa kayan baya.
Kwana biyu bayan nan ina zaune ina cin abincin da yanzu kullum sai Hajiya Babba ta girka ta aiko min dashi Inna kuma sai ta matsa min naci, sai ga Murja nan ta shigo "Diyam Alhaji yace ki shirya zamu fita yanzu gaba daya" ban kalle taba nace "babu inda zanje" ta daga hannu tace "ni dai yar aike ce". Sai kuma ga Hajiya Babba nan tazo da kanta, taci kwalliya kamar mai shirin zuwa gidan biki tace "innar Asma'u Alhaji yace Diyam tazo muje ganin gida da ita, in yaso in da akwai wani abin da take so sai ta fada a siya" tana fita Inna tace "ki tashi maza ki shirya ku tafi" na bata rai "Inna ni babu abinda nake so, in na gani ma babu abinda zan ce su kara" ta watsa min harara dole na tashi na shiga toilet na wanke fuskata na fito na saka hijab tace "kuma ko dan mai ba zaki shafa ba?" Na dawo na lakuci mai na shafa na juya tace "au dan nace mai shine kika shafa man shi kadai?" Nayi kamar zanyi kuka tace jeki.
Ina fita na tarar da yayan gidan suna ta shiga mota, matan gidan kuma suna gefe a tsaye suna hira. Na tsaya daga gefe ina kallon compound din, na kalli dai dai inda muka tsaya da Sadauki rannan sai naji ina ma dai ranar zata dawo in sake ganin sa at least koda sau daya ne. Na kalli gurin motoci sai idona ya sauka a kansa, cikin normal shigarshi ta dogayen kaya yayi kyau sai kyalli yake yi amma fuskar nan babu annuri ko digo a cikinta. Kallo daya nayi masa naji kamar duniyar ce take kara kuntatamin dan haka na juya na bar gurin na tafi inda yara suke shiga mota sai kuma naji kira da muryar Hajiya Babba "Diyam, ki dawo nan tare zamu tafi dake" na juya kamar zanyi kuka na koma, sai naga sun doshi motar da yake tsaye a kusa da ita, anti amarya tace "Diyam shiga gaba mu sai mu zauna a baya" na tsaya kawai ina kallon su kamar in rufe su da duka har suka gama shiga, shima ya shiga seat din driver ya zauna ya tayar da motar, sai da suka sake yi min magana sannan na kama handle din kofar jishi a rufe ni kuwa na koma da baya na nade hannu na a kirji. Hajiya Yalwati ta leko. "Ki shigo mana Diyam, ke fa muke jira" nace "kofar a rufe take Hajiya" ina jin Hajiya Babba tana yi masa magana, ya dauke kai kamar bai jita ba sannan kuma bayan wajan minti daya sai ya bude lock din. Na bude na zauna a makale a bakin kofa ba tare dana ko kalli side din da yake ba.
A hanya naji Hajiya Babba tana yiwa kishiyoyinta bayani "kunsan halin Saghir da rashin son hayaniya, wai shi ba zai zauna a cikin gari ba saboda kar mutane su dame shi, nace to kai me kanne da yawa? Namiji tilo a cikin mata? Ai dole ko gari ka bari sai kannenka sunje gidan ka, shine Alhaji ya biye masa aka siya masa gidan a can wajen gari, unguwar tokarawa acan zasu zauna" a raina nace 'wato yadda zai samu damar kasheni hankali kwance' ni a lokacin ban ma san unguwar ba sai dai naga mun dau hanyar barin gari, sai da muka wuce 'yan kaba sannan muka sauka daga titi muka shiga unguwar dana lura kamar sabuwar unguwa ce. Tun daga nesa na gane gidan. A house fit for the only son of Alhaji Babba amma ko kadan banji kyan gidan ya burge ni ba. Mukayi packing kusan a tare dasu Murja, na fita na tafi gurin su muka shiga tare amma sai na zame na zagaya bayan gidan nayi zamana akan veranda r backdoor din gidan. Ina jiyo su suna ta hayaniya da iface ifacen su alamar suna cikin nishadi amma ko sha'awar inje inga gidan banyi ba, addu'a nake a raina kar Allah yasa ina da rabon ganin cikin gidan nan in dai a matsayin matar Saghir ce. Naji wata irin kewar Sadauki ta taso min, sau dubu gwara ace in zauna da Sadauki a gidan kasa me yoyo akan in zauna da Saghir a wannan gidan.
Kamshin turare naji, na daga kai sai na ganshi a tsaye yana kallon gefe da alama bai san ma ina gurin ba. Fuskar nan kamar an aiko masa da mutuwa. Nayi saurin share hawayen fuskata saboda bana son ko kadan yaga weakness dina ballantana ya kara rainani. Motsin da nayi ne yasa ya juyo ya kalli inda nake, sai kuma naga ya tako cikin gadara yazo gabana ya tsaye ya kara tamke fuska yace "ke! Me na gaya miki rannan? Ba zaki je ki gaya musu ba sai kin je kin daukowa kanki abinda ba zaki iya ba ko?" Na mike tsaye na karkade hijab dina na juya zan bar masa gurin, ya damko hijab dina ya juyo dani yace cikin barazana "ba dake nake magana ba?" Na zabga masa hararar da nasan ba'a taba yi masa irinta ba nace "su wadanda kake magana a kansu ai sunfi kowa sanin cewa bana sonka, sunfi kowa sanin ina da wanda nake so wanda kuma yake sona, asalima dan su raba ni dashi ne suke neman makalamin kai"
The Game Has Began
It is such a long episode ko?