Zancen Safwan ya tabbata don kuwa sati biyu bai cika ba Dije ta fara laulayi mai ɗan karen zafi, don kuwa ruwa ma idan ta sha sai ta amayesu, ga shi a lokacin Safwan ya fara zirga zirgar neman aikinshi, inda aka yi dace aka nemeshi Abuja interview, shiyasa ya mayar da ita wurin Hajiya amman ko da yaushe suna maƙale a waya har ALLAH ya dawo da shi, sannan ya kwashi Matarshi suka koma gida yana ci gaba da renon abarshi, don kuwa duk abunda take so baya jin nauyin dattijuwar da ke taya Dijen aiki yake zagewa kitchen ya yi mata, ko ba daɗi ta cinye tana santi daga baya kuma ta amaye tass!, Haka suke abu ƙaɗan ya ce sai sun je Asibiti an dubata don baya son ta zauna cikin gida da wata matsala a tattare jikinta, shiyasa duk wani abu sai ya nemi sani tare da shawarwarin ƴan Asibitin, duk da wani zubin yana biyewa son zuciyarta ya yi mata duk abunda ta ke so saboda kawai ta yi farin ciki, don ba ƙaramin jin jiki take yi ba, cikin haka ne Safwan ya tura direba ba tare da ta sani ba ya ɗauko su Baffah da Inna da Hansai da Usmanu don Gambo ta ce ita ta yi tsufa ba zata iya yin wannan doguwar tafiyar ba, duk da har a ranta ta so ace ta je ta dubo jikallenta, amman yanayin jikinta na tsufa yau lafiya gobe ciyo yasa ta haƙura ba don tana so ba.
Dije cike da mamakin ganin gidan wasu ƴan'uwansu Safwan da su Surayya a kitchen sai hidimar dafe dafe da soye soye suke yi, in sun sauke wannan su ɗora wancen gida ya runtume sai zuba ƙamshin garar da ake ta haɗawa su Inna ake yi, duk abunda aka yi sai an kawo mata ace ta ɗanɗana ta ji in ya yi, cike da mamaki take tambayarshi wai halan wasu baƙi ne zai yi masu muhimmanci shiyasa ake ta wannan hadahadar?, Yana dariya ya ce
"Ke dai ki ci ki ƙoshi ki sha maganin amanki ki je ki yi wanka ki tsalo kwalliyarki cikin sababbin ɗinkunanki"
Cike da jin daɗi ta fara cin wani dambun nama tana ci tana kaɗa kai alamun ya yi daɗi sosai, hannunshi riƙe da plate ɗin tana ci yana yi mata dariya, bayan ta ci abunda zata iya ci ne ya bata magani ta sha sannan ya je ya taimaka mata ta yi wanka, wanda ko shi ɗin sai da suka ɓata lokaci sosai sunata wasarsu ta ma'aurata, tare suka yi wankan suka fito sannan suka shirya cikin taimakekeniyar juna, kafin ka ce me sai ga su dukansu sun fito shar! Abunsu kowane sai tashin ƙamshi yake yi, duk da ta yi rama amman hakan bai hana kwalliyar ta yi kyau ba, don kuwa fatarta ta washe sosai ta yi haske dai dai jikinta, haka ma ta ƙara yin kyau masha ALLAH dukiyar fulaninta sun ƙara cikowa sosai a ƙirjinta, waɗanda a kullum baya gajiya da lalacewa akansu yana santin yanda suke ta ƙara hawa tamkar an hura masu iska ga taushi tamkar balombalom, dole ba don ta so ba take sakin jiki ta barshi ya yi abunda yake so don duk da ciyon ta wannan ɓangaren baya ɗaga ƙafa, a cewarshi wai duk wani maganin da zata sha bai kai wannan tasiri a jikinta ba, da wayo da lallami yake samun abunnda yake ƙulafuci, don idan ma ta ce zata yi tirjiya ma ba haƙura zai yi ba shiyasa take ta danne zuciyarta tana faranta masa, amman ita sam bata son damuwa a wannan lokacin da zai barta na tsawon watanni da tafi sha'awar hakan fiye da yanda yake manne mata akan biyan buƙatarshi.
Bayan sun gama kimtsa komi da ko'ina ne Safwan ya kawo falo ya ce ta zauna ta jirashi minti biyar kacal zai je ya tarbo baƙinshi ya dawo, aikuwa cike da mamakin da son ganin waɗanni baƙi ne haka?, Ta zauna tare da su Surayya suna kallo a falo suna fira jefi jefi, don ko ita ya ja kunnenta sosai akan kada ta sanarwa da Dijen zuwansu Baffahn ya fi so ta gansu unexpected, ai kuwa suna nan suka ji saukar motoci, Surayya ta yi tsalle ta kalleta ta ce
"Yau fa manyan baƙi ne da mu a garin namu"
Dije ta yi wata dariya tare da cewa "ai kam ga shi na ga alama don ko mu mun sheda da waɗannan manyan baƙi"
Surayya ta nufi hanyar fitq falon da sauri tana murna duk da itama cikin ne a jikinta, Dije ta bi ta da kallo ta ce
"Aunty Surayya dai ba'a girma ba har yanzu, da cikinki kike wannan uban rawar jikin ki je ki janyo muna jidali muna zaman zamanmu"
Surayya ta ɗaga murya kafin ta ƙarasa ficewa ta ce "ai sawun Giwa ya take na raƙumi wannan abun murnar dole ne mu nuna farin cikinmu"
Dije haka kawai ta ji ta kasa ɗauke idonta a ƙofar da ake shigowa falon, saboda jinta da take yi cikin ɗokin ganin su wanene waɗannan baƙin, ai kuwa sai ga Surayya riƙe da Abba yaron Usmanu wanda aka yiwa Baffah takwara da shi, cike da mamaki ta zaro ido cen sai ga Hansai bayan Surry, a zabure ta miƙe Baki a sake zata yi magana kenan ta hango Inna a bayan Hansai, aiko ba shiri ta fasa wata uwar kuwwa ta nufosu aguje tana kururuwa sai ga Baffah ta hango da Usmanu tare da Habibynta, cike da tsantsar mamaki ta dinga rufe ido tana budewa tare da murzasu tana faɗin
"Wayyo ALLAHna shin mafalki nike yi ko gaske?"
Hansai ta riƙo hannunta cike da jin daɗin ganinta ta ce
"Ido buɗe ne mune muka kawo maku ziyara"
Dije ta ruƙunƙumeta tana murna ta saketa ta nufi Inna ta faɗa jikinta tana ihun jin daɗi, ta saki Inna ta zo gaban Baffahnta ta riƙo hannunshi tana faɗin
"Ashe ko da gaske kai ne Baffahnah wayyo daɗi kasheni Ni Dije"
Usmanu ya hararota ya ce "ashe dai har yanzu da sauran hankalin?"
Tana dariya ta saki Baffah ta ce
"Yaya Usmanu ya zu fa na girma kai ma ka sani ai"
Surayya ta kai su Inna har falon sannan ta dawo ta ce da su Baffahn su shigo a gaisa kafin a kaisu muhallin da aka tanadar masu, Safwan dai tsaye kawai yake hannunshi a aljihu yana kallon Matarshi wadda ita har kullum bata gajiya da abun dariya, haka ma shagwaɓarta da wautarta suke ƙara dulmiyashi cikin ƙaunarta, waɗanda a cen inda aka fito yake ganin shirmenta amman sai ga shi yanzu sun yi masa rana, don kuwa salon ba ƙaramin burgeshi yake yi ba.
Bayan sun zazzauna ne aka sake sabuwar gaisuwa Dije baki yaƙi rufuwa saboda murna, Hansai kam sai yi take yi tana satar kallon falon saboda ganin tamkar ba a duniya take ba, don ko ita kanta Inna ta jinjina irin wannan daula da Dijenta ta ke ciki, shi kam Baffah ba ma maganarshi ake yi ba don sai hamdala yake yi cikin zucinshi akan wannan ni'ima da Allah ya wadata Dijenshi da ita.
Bayan an ƙare gaiigasawa ne Dukansu aka kaishi masaukinshi, Inna da Hansai aka kaisu wani ɗakin baki da ke cikin sashen Dijen, Baffah da Usmanu kam takanas Safwan ya yi masu jagora zuwa ɓangarenshi, inda aka kaisu wani ɗakin alfarma da aka haɗashi tamkar ɗakin wasu sarakuna don kuwa ya sha ado ta ko'ina sai ƙamari ke ta shi.
Sannan aka kawo masu abincinsu da aka tanadar masu kala kala, bayan sunyi Sallah ne suka fara lodawa cikinsu suna jinjina irin wannan uwar gara da aka tanada donsu kawai, Usmanu ya buɗe ƙafafuwa sai jan girki yake yi yana faɗin
"Ashe Baffah shiyasa kake ta farin ciki saboda kasan inda ka kawo ƴarka?, To Wallahi a ja kunnenta duk tsanani ta ci gaba da yi masa biyayya, don ko watarana ta yi masa shirme ya kaita ƙofar gida ya ce ya ce ta fi gida, to ta ce masa ita ba inda zata je don taga wurin zama, yana kaita tana dawowa har sai ya gaji don kanshi ya haƙura ya ƙyaleta"
Baffah nama cike da bakinshi ya ce "ba ma zata aika shirmen ba bale har akaita ƙofar gidan, don haka ka godewa ALLAH ka godewa Dijengalata don sanadinta ne kake cin wannan naman"
Haka suka dinga firarsu da suka saba cikin raha da tsantsar farin ciki da jin daɗin ganin Dijensu ta yi dacen aure.
Inna Kam da Hansai su ma suna inda aka saukesu Hansai tare da yaronta sai jan gara suke yi Inna kam cike da jin nauyi take tsakura abincin, Dije tana kallonta cike da jin daɗi ta ce
"Inna ki saki jikinki don ALLAH ki ci abincinki, ba fa kowa daga Ni sai ku ko Surayya ta barku ku ji daɗin cin abincinku cikin nutsuwa"
Inna ta maka mata harara tace "don ma kin ci sa'a na zo? Ba yanda banyi da Baffah'nki da Mijinki ba akan a barni ba sai na zo ba suka ce dole da ni za'a yi tafiyar, Ni ban saba da wannan rashin kunyar ba ta ƴan zamani, zuwa gidan Suruki har da zube ɗuwawu a cenye abincin Suruki, kai Ni Hasiya wannan zamani ina zaka da mu? Kin ga Inna Tumba har ALLAH ya yi mata rasuwa bata taɓa tako ƙafarta ɗakina ba" cewa da Mahaifiyarta da ta haifeta ma'ana kakar Dijen.
Dije tana dariya ta ce
"Cabɗi to ai Ni Inna duk wanda ma zai auri ɗiyana dole ne ma ya yi man nawa ɗakin a gidanshi yanda ya yiwa Mahaifiyarshi"
Inna da Hansai suka zaro ido, Dije ta ƙyalƙyale da dariya ta ce "ALLAH kuwa zama zan yi yanda ta zauna idan aka muzgunawa ƴata in fito mu raba gari Ni da Uwarshi WALLAhi"
Inna ta ce "laaa! Na ga aya ashe Dijen har yanzu ba ta yi hankali ba, to ai sai ki janyo a tattaroki tare da ƴar a watsoku waje da kayanku kusan na yi WALLAhi"
Dije da Hansai suka dinga dariya Surayya ta shigo da wasu sauran kulolin itama ta zauna aka ci gaba da firar da ita anata dariya.
Da ƙyar suka ciyo kan Inna ta ci abincin sai dai ta ƙi cin sauran abubuwan a gaban Surayya da Hansai, saboda surukutar da ke tsakaninsu, ganin haka yasa Dijen ta ja Hansai ɗakinta suka bar Inna nan ita kaɗai sannan ta cisgi garar itama cikin ɗar! ɗar! don kada a risketa bata sani ba.
****
Zee kam a ranar bata kwana gidansu ba don kuwa Baaba Asabe ta kwasheta da kayanta suka nufi gidanta, suna shiga tashin farko ta ce da ita
"Bani wayarki"
Zee ta ce "ai Ni tun ranar da na bar gidan ban sake ganinta da idona ba, tana cen Yola a falona ban sani ba ko ya ɗauke mani ko kuma ma an sace oho"
Baabaah Asabe haɗe da fuska ta ce "to je ki kai kayanki ɗakinsu Inna Dela ki dawo ki ji"
ZEE ta zaro Ido waje ta ce "Inna Dela fa kika ce Gwaggo?"
Kai tsaye ta ce "eh ita nace ko a cikin halittar jikinki akwai abunda su babu irinsu jikinsu?? "
Zee ta girgiza kai tare da sosa kai murya ƙasa ƙasa ta ce "ƴan aiki ne fa Gwaggo, Ni dai don ALLAH ki barni ko ɗakin waje ne zan zauna amman ba ɗakinsu Dela ba"
Baabaah Asabe ta katsa mata wata arniyar tsawa ta ce "za ki je ki kai kayan ko sai na haɗaki da buloli yanzu?"
Zee ta zabura aguje ta nufi inda ɗakin na ma'aikatan gidan yake saboda tsabar tsoron Baabaah Asaben da take yi, tana tafe tana gunguni Baabaah Asabe ta ɗaga murya ta ce
"Ai da kin tsaya ki nuna man banbancinki da ƴar aikin, to ai gara su basu shuka tsiyar da kika shuka a gidan mazajensu ba amman ga su a matsayin yan aikin, to ke in Baki yi a hankali ba yan aikin ma sai su fiki daraja a idon duniya, don ko wannan bankaɗa da kika janyo aka yi wa zuri'armu kawai hakkinmu ya isheki ballantana haƙƙin ɗaukar rai da kika so ki yi, in banda ALLAH ya tarfawa garinki nono da yanzu kin janyo muna bala'in da bamu san inda zamu jefa kanmu ba, don haka WALLAhi Ni banu wani ragi tsakanina da ke a gidan nan don yan aikin ma sai sun fiki daraja a wurina"
Har Zee ta ajiye kayan ta fito bata daina sababin faɗa ba, haka ta zaunar da ita tana ta tsara mata abunda zata yi a gidan tun daga safiya har dare, hankalin Zee bai ta shi ba har sai da ta ji wai har da wanki zata dinga yi kullum, wankin ma kuma na samarin ƴaƴanta da suka balaga wasu ma har suna zancen aure amman ace har da su zata dinga yiwa wanki,cike da ƙuncin zuciya ta kwana tare da cin alwashin muddin ta ji za'a kasheta WALLAhi dole ta tsere ta bar mata gidanta, don bazata zura ido aiki ya kassarata ba tunda daman cen ita ko undies ɗinta wanke mata ake yi, ba abunda ta iya in banda dafa indomie ko shi don watarana in an dafo mata tace bata yi mata daɗi ba, Mahaifiyarta tace ba mai sake dafo mata wata in tana so ta je ta dafa da kanta, to da hakan ne ta iya dafata saboda Daddynta ya ajiye mata masu aikin da suke yi mata duk abunda take so, to yanzu ga shi Baabaah Asabe zata sakata shiga uku.
Don kuwa tun da sassafe ta tadota daga baccin da ta koma na bayan asuba, ta fito ta kaita wajen tulin kayan wanke wanke ta ce ta fara idan ta gama ta je ta share gidan lungu da saƙo, cike da fargaba da tsananin tashin hankali ta ke ƙarewa ƙaton gidan kallo, tana nazarin ko rabinshi aka sakata sharewa ai an so kasheta bale duka, sai ga muryarta a saman kanta tana faɗin
"Zaki fara wanke wanken ko sai na fara sauke maki bulalata a jikinki?"
Zee jiki yana rawa ta fara harhaɗa kwanonin Baabaah Asaben ta ce da wata matashiyar ƴar aikinta ta nunnuna mata yanda zata yi, tana tsaye har aka nunawa Zee komi ta fara m wankewa tana hawaye sannan ta bar wajen, ta dawo falo ta zauna zuciyarta cike da jin daɗin yanda ta yi nasarar da Daddyn Zee ɗin ya gano kuskuren da ya tafka akan tarbiyyar ɗiyarshi, tare da jin daɗin amincewar da ya yi akan ta zo da ita hannunta ta zauna don bai san ƙudurinta akan Zee ɗin ba, da wataƙila ba zai yi saurin amincewa ba duk da kuma yasan ba zata yi mata ta daɗi ba, amman bai taba tunanin irin wannan azabtarwa zata yi mata ba.
Zee Kam haka aka yini ana aiki wankin samarin ma sai da ta yi sai dai su ma kansu ba da son ransu ba don dai Mahaifiyarsu ta yi masu jan kunne da kashedi sosai akan duk abunda suka ga ta saka Zee iyakacinsu Ido, Dole Suka zura ido suna kallon yanda take ta yi masu wankin, cikin ƙankanin lokaci hannunta ya yi ja ya saluɓe aiko ta fara yarfa hannu tana kuka, ganin haka yasa aka canza mata wani aikin ko da dare ya yi ta kwanta ko'ina nata ciwo yake yi, da ciwon jiki ta kwana kan tabarma tana haki tana juye juyen wahala.
Sorry Zee😢 Wai ko dai in zo in gudu dake ne🙊 gidan mum Irfaan ko gidan Daughter Rufaida ko wurin ƙanwata Asiya? Ki yi shawarar inda kike son zuwa kafin in dawo🏃🏻♀️🏃🏻♀️🏃🏻♀️🏃🏻♀️🏃🏻♀️🏃🏻♀️🤣
Akafta😊
D/AUTA CE✍🏻
*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*
*NA HADIZA D/AUTA*
*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*
*Don Allah masu neman book ɗin Ƙarangiya daga farko ku yi haƙuri idan an kammala za ku sameshi a complete ɗinshi, plss ku yi haƙuri kunji😢saboda anyi nisa sosai kuma bana son kuna tambaya baku samu ba😆*
*Lamba 68*
Daren ranar Dije da Inna sai hira suke ta zubawa, don ita Hansai tun da ta ji cikinta ya ɗauka ta baje abunta sai sharar baccinta take yi ita da yaronta, ganin dare ya miƙa ne Inna ta ce da Dijen ta tashi ta je wurin Mijinta, Dije tana zumɓuro baki ta ce
"Anan zan kwana Inna mu yi ta firarmu Ni da ke Inna, sabida ALLAH yaushe rabon da mu ga juna an daɗe fa? Ni dai don girman ALLAH Inna ki barni in kwana abuna anan ɗakin"
Ta ƙare maganar tare da zubowar wasu ƙwallah, Inna ta gyara ta yi kwanciyarta tana faɗin
"To Ni dai bacci nike ji idan ke baki gaji da firar ba ki ci gaba ai akwai aljanun dare suna saurarenki zasu tayaki yin firar"
Dije ta zaro ido tuno abunda ya taɓa faruwa a school ta yi saurin kwanciya bayanta ta ƙudundune tana faɗin
"Inna ki yi man addu'a kar su kamani don ALLAH"
Inna ta miƙe zaune cike da mamaki ta ce "zaki ta shi ki je wurin Mijinki ko ko so kike yi ya ɗaukemu waɗanda basu san abunda suke yi ba?"
Dije ta miƙe tana kallon ƙofa tace
"To mu je ki rakani WALLAHI tsoro nike ji"
Inna ta riƙe baki cike da mamaki ta ce
"Tunda kike gidan baki ji tsoro ba sai yanzu da kika ga mun zo ko? To ya yi insha ALLAHu gobe tun da sassafe mu zamu bar maki gidanki tunda so kike yi ya ɗaukemu mutanen banza"
Dije ta miƙe ta fito Inna ta rufo ɗakin zuciyarta cike da nauyin kada Safwan ɗin ya ga sun riƙeta, aikuwa Dije cikin sanɗa ta ke tafiya tana waige sai jin ta yi anyi caraf da ita, ba shiri ta yage baki da nufin fasa ƙara taji bakin Malaminta cikin nata, gano shine yasa ta ƙara ruƙunƙumeshi jikinshi tana faɗin
"Mu je ɗaki tsoro nike ji"
Cike da jin daɗi ya sake manneta jikinshi suka yi ɗakinshi, ganin da gaske tsoron take ji yasa ya fara tambayarta abunda ya tsoratata, cikin murya ƙasa ƙasa ta yi masa bayanin yanda suka yi da Inna, cikin dariya ya ce
"ALLAH ya biya Inna da gidan Aljannah don Ni ta kyauta man, saboda tun ɗazu da na dawo wurinsu Baffah nike ta juye juye Ni kaɗai akan gado, dole na fito falo na zauna ina kallo nan ma na ji ba daɗi na kashe ina tunanin yanda zan yi in ce ki zo, ashe Inna tasan ƙishina shiyasa ta koro man ke waje"
Dije ta tureshi cikin fushi ta ce "tunda haɗe man kai kuke son yi ai ku je ni ma gobe wurin Hajiyarmu zan kwana "
Safwan ya janyota jikinshi ya ce "ai Hajiyarmu ma ba zata so ki bar Mijinki shi kaɗai ba yana kewa ba"
Haka ya hilaceta ya gwangwaje abunshi tare da sassafta murya wurin sambatun da ya saba, don gudun ya tafka abun kunya gaban surukai.
Tun da Sassafe aka kammala masu komi na breakfast ɗinsu tare da taimakon wasu yan aiki biyu da Hajiyar ta ƙaro masu, bayan sun karya ne aka sake wata sabuwar gaisawa sannan Safwan ya kwaahesu zuwa gidansu su gayar da Hajiyar, tarba ta mutumci Hajiya Mama ta yi masu fuska cike da fara'a tamkar cewa da man cen ƴan'uwanta ne, Inna da Baffah suka yi godiya sosai akan yanda take kulawa da Dije tamkar itace ɗiyarta ba Safwan ba, Inna da Hansai da Dijen sun daɗe gidan tare da Hajiya Mama sannan Safwan ya dawo da su Baffah da ya je kaisu yawon ganin gari, marece sakaliya ya ɗaukesu ya kaisu gidan Mijin Surayyy, inda itama ta yi masu tarba mai kyau tamkar kar su rabu saboda kirkin Surry ba ƙaramin burge su Inna yake yi ba, sai gaf da magriba suka dawo gidan inda suka taradda an haɗa masu abincin dare mai rai da lafiya, tuwon farar shinkafa da miyar agusi ta ji zuƙa zuƙan namomi tare da lafiyayye ferfesun kajin turawa masu manyan tsokoki, bayan sun ci abincin ne aka koma yin firar bankwana saboda tun da sassafe zasu juyawa inda suka fito, tun cikin daren Safwan ya tanadar masu duk abunda zai ba su ya basu, Hajiya Mama ma da nata kalar tsarabar Surayya ma da tata, haka suka yi ta godiya kamar ba gobe, don kuwa su kansu sun san ba ƙaramin arziƙi suka yi ba,saboda bancin sutura kuɗi tsabarsu dubu ɗari Safwan ya baiwa Baffah, Inna dubu Hamsin Usmanu da talatin Hansai ashirin yaronta goma, bayan suturar da aka cikasu da ita da turaruka da sabulai kala kala, yaron Hansai kanshi ledar kayanshi daban aka siyo mashi masu ɗan karen kyau.
Tun cikin daren Dukansu suka saka Dije tsakiya suna yi mata nasihohi tare da jan kunne akan ta ninka wa mijinta da Mahaifiyarshi biyayyar da take yi masu, haka ma ƴan'uwaanshi ta riƙesu tamkar yanda zata riƙe nata, in ma da hali su fi natan don kawai ta sami zaman lafiya da kwanciyar hankali a gidan aurenta, anan ne take sanar da su gumurzun da aka yi da Zee akan kashe sun da ta so yi tare da ƙudurinta da ta yanke akan muddin Zee ta dawo to ita zata bar mata gidan, cikin fushi Usmanu ya ce
"WALLAHI kika kuskura kika bar wannan gidan akan baƙin shirmenki sai na saki jiki na lakaɗa maki shegen duka"
Inna tana harararta ta ce "to bari ki ji da kyau muddin kika taka ƙafarki kika bar gidan nan bada izinin Mijinki ba to ki sani ban yafe maki ba"
Baffah ya yafito Dijen ta zo gabanshi ta zauna tana zimɓoro baki yana dariya ya ce
"Shin Ina Dijengalata?? "
Hawaye suka zubo mata ta ce
"Gani Baffah".
Yace "to ki ajiye komi ki yi zaman aurenki tsakani da ALLAH, ki sa a ranki duk duniya babu wanda ya isa ya yi maki abunda ALLAH bai yi maki ba, haka ma kaf mutanen duniyar nan idan ymza su taru akan sai sun kasheki to basu isa su kasheki ba har sai kwananki ya ƙare, don haka ki ɗauka cewa duk abunda kika ga ya sameki daga ALLAH ne, abunda ma ya kuskure maki shi ma daga ALLAH ne da kin yi hakan shikenan kin ci maganin matsalarki, ALLAH ya saukeki lafiya ke da ƴar uwarki kuma ya baku zaman lafiya a gidajen aurenku"
Dije ta rufe fuska cike da jin kunya ta ce "Ameen" cikin maƙoshi, haka suka dinga nusar da ita abubuwa da yawa masu amfanarwa sannan ta saki jiki ta dawo dai dai aka ci gaba da fira cikin raha da annushuwa.
Dije ta ce su gayar mata da Gambo da su Ladiyo, ta ɗauko sako ta bayar ta ce akai masu ace in jita, don kuwa su Ladiyo kowa dubu bibbiyu ta bada akai masu Balan duduwa dubu biyar tare da Duduwar itama dubu biyu, sannan saƙon Maigari da Matanshi na shadda da atamfofi, Malaminta na makarantar allo ma da saƙonshi tare da ɗalibanta na makarantar da ta baiwa sababbin goma goma ta ce a raba masu su yi mata addu'a, abun dai masha ALLAH gwanin burgewa Dukansu kowane zuciya cike da tsantsar farin ciki da jin daɗi, tare da yi wa ALLAH godiya da ya baiwa Dije miji ɗaya tamkar da goma kuma ya haɗasu da mutanen kirki.
Tun cikin daren su Hajiya Mama suka zo suka yi sallama da juna shiyasa tun da sassafe suka fara shirin barin garin, Dije sai kuka take ci ana lallashinta har motarsu ta ɗaga ta faɗi ƙasa tana ta kuka gwanin ban tausayi, sai da Malaminta ya yi mata jan ido sannan ta fara shiga taitayinta, don ya yi mata alƙawarin in dai har ta bar kukan to itama zai kaita idan cikinta ya yi ƙwari ta je ta ganosu, sannan ne ya samo kanta ya koma aikin ban baki tare da daɗin baki kala kala.
Sati ɗaya a tsakani takardar samun aikinshi ta fito inda kai tsaye aka postershi Abuja, tare da zunzurutun albashi mai tsoka da kyautar sabuwar mota da gida a garin Abuja, mutane da yan uwa sai murna ake yi masu don Lawi kanshi sai da ya zo ta ya murna tun daga Gombe har Yola tare da Amaryarshi da tuni itama ta kusa zama Mama, don kuwa ɗauke take da cikinta ɗan wata biyar itama kyakkyawar bafulatana da ita masha ALLAH, kwanansu ɗaya a gidan suka koma cikin kewar juna, saboda jinin matar Lawin mai suna Maryam da ya haɗu cikin lokaci ƙanƙani da na Dijen Baffahn, saboda itama ba laifi akwai barkwanci da son wasa da dariya gata da saurin sabo.
Lokacin da aka ɗibar masa da ya cika ya fara zuwa aiki, fiddo da wasu dattijai biyu suka dawo gidan suna taya Dijen Baffah zama, atakure ya yi sati ɗaya ya dawo Yola cike da ɗokin Matarshi, don ba ƙaramin sabo ya yiwa kanshi da ita ba, shiyasa ya ji gaba ɗaya zama garin bai masa daɗi ba, dole ya kwashi Matarshi suka nufi garin Abuja a gidansu da aka basu, don ya so har sai ta haifu sannan su dawo nan ɗin , to amman ya ga hakan bazata samu ba don sabon da ta yi masa kanta, ga shi kuma shi matan banza basu gabanshi don ko na kwarai ɗin baya kula shirginsu bale har na banzan.
Aunty Ummi da su Husnah sai murna suke yi Dijen ta dawo kusa da su, shiyasa kullum suna tare basu wannan wurin shaƙatawa basu wurin ciye ciye da tanɗe tanɗe da lashe lashe, kafin ka ce me idon Dijen sun ƙara buɗewa cikin garin Abuja, don kuwa ita kanta tasan wurare da yawa.
Da zama ma ya yi daɗi sai ga shi da koya mata driving, tana jin tsoro tana fargaba haka yake koya mata ita duk da bata so, saboda bala'in tsoron da ta ke ji amman a hankali ko wata biyu basu rufa ba a garin ta fara iyawa, don ya ce da ta iya zai siya mata tata idan ALLAH ya sauke ta lfy, ko don ta fara zuwa makarantar da take kwaɗayi ba tare da takura ba, don saboda busyn da yake yi a wurin aikin nashi kullum, gashi kuma yana son ta yi karatun don shine babban gatan da zai mata a rayuwa, saboda akwai rayuwa akwai mutuwa in mune yau ba mune gobe ba, Yana da kyau mace ta dogara da kanta ko don ranar da kika rasa mai tallafa maki ki kula da kanki da yaranki da iyaye da ƴan uwanki duka.
****
ZEE Kam tun bata saba da aikin wahala ba har yanzu ya fara zame mata jiki, don ta yi ta tserewa tana zuwa gidajen yan uwa ana dawo da ita wurin Baabaah Asaben, don kowa cike yake da haushinta ba kaɗan ba musamman ƙin Aminu da ta yi tare da abun kunyar da ta janyo masu, Mahaifiyarta kanta da ta je gidan take korota ta fito tare da yi mata kashedi da gargadin cewa duk ta yarda Daddynta yasan halin da take ciki a gidan gwaggonta sai ta tsine mata, tana kuka take komawa yanzu har ta haƙura don kanta ta daina gudun, ganin hakan yasa Gwaggon ta fara sassafta mata daga matsin lambar da take yi mata, don kuwa ta ladaftu sosai kuma ta gano irin kuskuren da ta so aikatawa, ta yiwa ALLAH godiya da yasa Ruma bata bari ta aikata mugun abun da ta yi niyya ba, ga shi ta rasa Safwan ɗin kuma Aminun ma ta rasa shi don kuwa yanzu haka ƙawarta Sadiya yake aure, don Ruma ya so aura ta nuna masa amincinta da Zee bazata iya aurenshi ba, Sadiya kam hannu biyu ta karɓeshi yanzu haka da ƴarsu tana nan mai sunan Mahaifiyarshi.
Zee ta shiga damuwar rashin jin Safwan ɗin da kullum take tsumayin zuwanshi gareta ya ce ta dawo, amman shirun da ta jini yayi yawa ne ta fara tunanin binshi da kanta, don laifin da ta aikata masa ko ma wanene dole ne ya sallamata, kasancewar tasan numbarshi akanta yasa da Ruma ta zo ta ari wayarta ta kirashi, kasancewar baya da layin Rumar a lokacin shiyasa daga baya ya bi miss call ɗin da ya gani kusan goma sha bai ma san an kira ba, sai dai jin murya Ruma yasa ya yi saurin faɗin
"Wacece ??"
Jikinta yana rawa ta ce "Rumasa'u ce ƙawar Zee don ALLAH ka yi haƙuri da abunda ta aikata ita ce ta kiraka ɗazu da naje wurinta ta ari wayar ta kiraka baka ɗaga ba, saboda WALLAhi yanzu Zee ta canza sosai kuma ta yi nadamar abunda ta aikata"
Cike da mamaki ya ce
"Daga ke har ita kada ku sake nemana matuƙar kuna son kanku zaman lafiya"
Ƙittt! Ya kashe wayarshi gaba ɗaya cike da jin haushinsu duka, Dije da ke shigowa ɗakin da tiren coffee'nshi ta ajiye tiren akan stool ta ɗauki cup ɗin ta zauna tana kallonshi tare da nazarin yanayi shi, sannan ya zura hannu da nufin ya karɓi kofin ta riƙe gam idonta a kanshi ta ce
"Wa ya taɓo man Habibyna? Don haka na fita na barshi ba plss ka yi haƙuri ko ma mene saboda zama cikin mutane sai da kai zuciya nesa Mijina"
Cike da jin daɗin kalamanta ya duƙo ya kurɓi coffee'n sannan ya ce, "waɗannan ba irin mutanen da kike tunani bane, ki share da su kawai don na riga da na shafe babinsu a rayuwata"
Dije ta miƙa masa cup ɗin ya karɓa ya dinga sha a hankali har ya shanye, sannan ta karɓi cup ɗin ta ajiye ta kalle da kyau ta riƙo hannunshi ta haɗe da nata ta dunƙule waje ɗaya ta ce
"Wacece ta kiraka?"
Cikin diriricewa ya ce
"Ruma ce ƙawar Zee take rokona akan inyi haƙuri in yafe wa Zee wai ta yi nadamar abunda ta aikata"
Dije ta ji wani ɓacin rai ya ziyarci zuciyarta, amman ta yi dubarar ɓoye damuwarta ta ce
"To kai kuma me ka ce?"
Ya ɓata fuska tamkar a lokacin sannan ya sanar da ita abinda ya ce da ita, Dije ta ɗauko hannunshi ta ɗora a saman cikinta da ya fara turowa kaɗan, ya bita da kallon ƙarin ba'asi sannan ta kashe masa ido ɗaya ta ce
"Nasan kana sonshi ko?"
Ya maka mata wata harara, ta zunɓuro baki ta ce "Ni dai ka daina hararata amsa nake nema"
Ya yi saurin faɗin
"Yo idan ma ba don kina son kawo man reni ba ta ya zaki kalli tsabar idona ki tambayeni ina son abunda Ni da kaina sai da na zuba ƙarfi kafin in sameshi?, Kin fi kowa sani kaf duniya babu wanda zai fini son abunda ke cikinki ko da ko ke ɗin ce da zaki haifo man shi"
Dije ta ƙumshe dariyarta ta ce "au abun har ya kai cen?"
Yana dariya ya ce "ya ma wuce ai" tace "well yanzu idan na ce ka yi mani wata alfarma saboda son da kake masa zaka yi?"
Cikin sauri ya ce
",Me zai hana in dai har hakan zai faranta ranki da unborn ɗina"
Ta ce "to in ko haka ne bari in zube ƙasa in rok'i alfarmar don ina son ayi saurin amsa mani"
Ta sauko ƙasa zata durƙusa ya riƙo hannunta tare da dawo da ita kan gadon ta zauna ya ce
"Faɗi buƙatarki kawai ba sai kin cutar man da abun ciki ba"
Dije ta yi dariya cike da jin daɗi sannan ta riƙo hannunshi ta matse gam ido cikin ido ta ce
"Daga Ni har babynka Muna so ka dawo muna da Aunty Zee ko don mu sami abokiyar shawara tunda har an ce ta yi nadamar abunda ta aikata"
Cike da ƙunar zuciya ya ƙwace hannunshi tare da miƙewa tsaye ya kalleta ranshi a ɓace ya ce
"Wannan rana da wannan lokaci su zamo na ƙarshe da zaki sake tunkarata da wannan zance"
Yana ƙare faɗar hakan ya fice ɗakin fuuu ya barta zaune sake da baki, zuciyarta cike da tabbacin abunda Inna ta nusar da ita wanda ita ta kasa gano hakan sai yanzu da ta tabbatar da hangen nesan Innarta, cikin tsananin farin ciki tace
"ALLAH ya ƙara maki tsawon rai innata"
To Ameen Dijen Safwan tare da namu Innonin duka kuma ya ƙaro masu lafiya mai ɗorewa Amee🤲🏻.
Akafta🥰
D/AUTA Ce✍🏻
*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*
*NA HADIZA D/AUTA*
*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*
*Don Allah masu neman book ɗin Ƙarangiya daga farko ku yi haƙuri idan an kammala za ku sameshi a complete ɗinshi, plss ku yi haƙuri kunji😢saboda anyi nisa sosai kuma bana son kuna tambaya baku samu ba😆*
*Lamba 69*
Duk da take cikin farin ciki haka ta fito ɗakin haɗe da fuska ta zo ta zauna tana shan ƙamshi tare da mayar da hankalinta ga kallon tv'n da ke ta aiki shi kaɗai, don shi kwance yake tare da rufe fuskarshi da hannu alamun yana cikin damuwa a zahiri, jin motsin shigowarta yasa ya buɗe ido yana kallonta, ganin yanayinta kuma ta ƙi kulashi yasa ya ji ba daɗi, ya miƙe zaune yana kallon yanda ta haɗe fuska tamau ba alamun wasa, cikin danne dariya ya taso ya zo gabanta ya yi tsugunno tare da riƙo hannunta yace
"Wai ke wace irin mace ce ke? Ni dai nasan kowace mace tana kishin mijinta amman ke har ingizashi kike yi akan ya yo maki kishiya"
Dije ta zare hannunta a hankali zata miƙe tsaye ya yi saurin dafeta ya ta shi ya zauna kan kujerar ya rungumota jikinshi ya ce
"Ki ji tsoron Allah kar ki jefa Mijinki a damuwa saboda macen da bata san muhimmancin kanta ba ma bale tasan na wani, kina kallo gaban idonki ta so kashemu da ma bata sami sa'a ba wuƙa ta ɗauko da nufin ta soka man, yanzu irin wannan matar kike so in sake dawo da ita cikinmu?"
Dije ta riƙo hannunshi ta ce "ba laifi bane don an yi maka laifi ka yafewa wanda ya cutar da kai, don ALLAH da kanshi haƙuri yake yi da mu da halayenmu saboda darajar fiyayyen halitta Annabinmu Muhammadu s.a.w da muke cin albarkacin shi, kuma a shirye yake da ya yafe muna a duk lokacin da mu ka yi tuba zuwa gareshi, tunda haka ne mu me zai hana mu yafe mata akan abunda ta aikata muna a baya?, Don ALLAH ka yafe don ni tuni na yafe mata ka sake bata wata dama matuƙar ka tabbatar da ingancin nadamar da ta yi "
Safwan ya sauke ajiyar zuciya yace "zan dawo da ita kamar yanda kika nema in har na tabbatar da gaske ta yi nadamar, amman da sharaɗin bata zo nan Abujar ba sai dai idan har ta amince zata zauna Yola, don bazan haɗaku waje ɗaya ba ta je ta koya maki mugun hali"
Dije ta ji wani sanyin daɗi ya ratsa zuciyarta cike da tsantsar farin ciki tace " ina sonka Mijina ALLAH ya baka ikon yin adalci a tsakaninmu"
Ya lakuce mata hanci
"Ya ce Ameen Matata ke ma ina sonki son da Ni kaina ban san iya adadinshi ba, na godewa ALLAH da ya azurtani da samun mace irinki, wadda take da wankakkiyar zuciya mai sowa wata abunda ta sowa kanta, don ba kowa ce mace zata iya yin abunda kika yi ba, ALLAH Ubangiji ya yi maki albarka ya kuma saukeki man ke lafiya tare da Babyna"
Cike da jin daɗi take ta faɗin "Ameen Ameen Habibyna, tom kirata yanzu ka sanar da ita ta dawo ka yafe mata"
Ya maka mata wata uwar harara ya ce "su kenan ba sai an tantance ba? Ai WALLAHI sai na tabbatar da lalle ta gyaru sannan in ce ta dawo, don bazan taɓa yarda in siyowa kaina rariyar da zata yi man asarar ruwa ba"
Dije ta ƙyalƙyale da dariya ta ce "uhummm har na tuna lokacin da ake yi man kashedi akanta, daɗin abun da dai komi yake wucewa don yanzu ga shi kai da kanka ka bayyana mata matsayina bayan ka gama yi mata ɓoyo, ai WALLAHI kai ma da naka laifi Malamina don da tun farko ka sanar da ita da abun bai yi tsananin irin wannan ba, don da ace ta kashemu da shikenan mun tafi bamu bar masu yi muna addu'a ba"
Ya sosa kanshi cike da jin nauyin maganar tata ya ce "Ni dai bana son tone tone idan abu ya wuce a dinga barinshi a matsayin ya wuce, ki ta so mu je dai ki ji wata magana dare ya fara tsalawa"
Ta bishi da wani kallo tana ƙumshe dariyarta tace
"Ni yau anan ma zan yi baccina na gaji da kwanciya akan gadon nan"
Ba shiri ya waigo ya ce "Ashe ko da ke ce zaki wahala don WALLAhi in Banda tausayin abun cikina da kinsha mamakina, amman tunda hakan kike so bari in zo daga baya na baiwa abun cikina haƙuri"
Sanin halinshi yasa ta yi saurin tashi tana dariya ta ce "mu je Ni dai yasin idan na koma haifuwa garinmu sai na yi kusan shekara ban dawo ba"
Ya riƙo hannunta yana dariya ya ce "ki ce kawai in rubuta takardar barin aiki don kin san ƙafata ƙafarki kuma idan sun gaji da halina sai su korani in koma Yola dolena"
Ta yi masa wani mintsina a gefen ciki tana dariya ta yi ɗakinta da sauri tana faɗin "banji bakinka ba WALLAhi, Ni da nake shirin zama student kake so ka yi man ciki baƙi?"
Ya bita yana dariya ya ce " to Alhudahuda ai dai kya bari ki haife man abun cikina ko?"
Haka suka dinga wasarsu cikin raha har suka kwanta bacci bayan sun gama farantawa juna cikin tsantsar ƙaunar juna.
****
Ruma kam jikinta yana rawa tun da sassafe ta je ta sanarwa Zee abunda ya faru bayan barinta wurinta, cikin sanyin jiki da zubowar hawayen tausayin kanta ta karɓi wayar ta sake kiranshi, sai dai ta yi rashin sa'a wayarshi a kashe lokacin suna gudanar da wani meeting, ganin ta ƙi samunshi ne yasa ta rubuta masa saƙo ta tura masa kamar haka
_Aslm_
_Plss my Man Ni ce Zee don girman ALLAH ka yafe mani abunda na yi maka WALLAhi na yi nadama kuma na yi godiya ga Allah da ban ci nasarar abunda na so aikatawa ba, don yanzu haka Daddyna yana kwance har yanzu bai koma dai dai ba, kuma Mummy ta tsaneni ko kusa da ita bata bari inje, gani gidan ƙasar Daddy sai azabtar da ni take yi da ayyuka kala kala don ALLAH ka taimaki rayuwata ka ce in dawo ɗakina, WALLAhi na yi alƙawarin ba zan sake_ yin abunda bai da ce ba, plss ka yafe mani mu cuddle bear wallahi sonka ne ya
rufe mani ido ya janyo
na so aikata duk abunda ka gani, don ALLAH ka ce ka yafe mani in dawo don ALLAH my Bobbie.
Tana kuka take rubuta text ɗin bayan ta tura kuma ta sake bi da kira amman kuma bata shiga ba, saboda bai buɗe wayarshi ba har sai ya dawo gida ne bayan ya gama komi sannan ya buɗe, aiko buɗewar ke da wuya sai ga saƙon Zee ya danno kai, ba ɓata lokaci ya duba duk da ya tausaya mata amman hakan bai sa ya mayar mata da amsa ko ɗaya ba, asali ma goge text ɗin ya yi gaba ɗaya a wayar, sannan ya mayar da hankalinshi akan sauran saƙonnin da suke ta shigowa.
Zee ta gaji da jira ta sake gwada kiran sai ko ta yi dace ta shiga cike da tsananin jin daɗi ta yi wani ihu saboda murna, yana ɗauka ta daburce tana ta kame kame ganin bata da abun faɗa ne ya sa ya katse kiran, cikin sauri ta sake binshi da wani kiran har sai da ta tsinke bai ɗauka ba, bata gaji ba ta sake kira ganin zata dameshi ne yasa ya ɗauka, cikin rikicewa ta fara rawar murya tana faɗin
"Don Allah ka yi haƙuri ka yafe mani my Bonnie plss"
Cikin ko in kula ya ce
"Ni fa yanzu matata ta isheni bana fatar haɗata da kowace mace a matsayin kishiya ballantana mai som ta kashe mu Ni da ita, don haka ki ƙara haƙuri sai na yi shawara in ta amince tukunna"
Yana kare faɗar maganar ya kashe wayar, Zee ta fashe da kuka cikin tsananin takaicin kanta da har ta yi abunda ya janyo mata faɗuwar daraja warwas, don daman cen ya lafiyar kura ballantana yanzu ta ci sarauta?, Dole sai haƙuri cikin kukan ta sake kiranshi caraf ya ɗauka cike da Muryar kuka ta ce
"Ko a ƴar aikinta ka ce in zo Zan zo idan har zaka yafe man abunda na yi maka"
Safwan ya ɓata fuska kamar yana ganinta ya ce "kina da labarin ina Abuja yanzu ko?"
Ta ce "a'a bani da labari" ya ce "Ok tom yanzu haka ina Abuja Ni da Matata nasami aiki ne a cen, idan kin shiryawa zaman Yola to ki tattaro kayanki ki koma, amman ki sani weekend kawai zai dawo da ni Yola idan kin amince shikenan fine, idan kuma kin ji ba zaji iyawa ba Tom sai mu sahalewa juna"
Cike da jin daɗi bakinta yana rawa ta ce
"Na amince My Man amman don ALLAH ka ce ka yafe man, itama ka nemar mani tafiyarta kafin ku haɗu"
To kawai ya ce ya kashe wayar, Zee ta yo sororo da waya a hannu tana kallon Ruma ta ce
"Ya ce in koma amman har yanzu bai ce ya yafe mani ba"
Ruma cike da tausayinta ta ce "kada ki damu a hankali yafiyar zata biyo baya in har ya fahimci kin canza ba Zee ɗin da ya sani ba ce a cen baya, fatana kawai ki san yanda zaki taushi zuciyarki saboda tsoron aikata abinda za'a azo ana da ansani daga baya"
Zee ta share hawayenta ta ce "Ai Ni tuni na gano cewa zafin nema baya kawo samu, don da banda ke da yanzu Ni kaina bana duniyar an riga da an kasheni, wanda ta sanadin haka ina da tabbacin Daddyna ma zai mutu itama kanta Mummy zata shiga muwuyacin hali, saboda gorin mutane ƙarshe itama ta bimu, Nagode sosai Ƙawata lalle ke ƙawar amana ce ALLAH ya bar zumunci kuma ya baki miji nagari ke ma ki je ki yi aurenki ki huta"
Ruma ta ce "Ameen"
Tare suka je suka samarwa Baabaah Asaben abunda ke faruwa cike da jin daɗi ta nufi gidamsu Zee ta sanarwa Mahaifin Zee saboda murna sai gashi da tashi zaune ba shiri zuciyarshi cike da jin daɗin jin wannan abun farin ciki, Mahaifiyarta ma ba ƙaramin daɗi ta ji ba da jin maganar, shiyasa ta nemi alfarmar ganinta ba ɓata lokaci Baabaah Asaben ta kira wani yaronta ta ce ya ɗauko Zee ya kawota.
Satinta ɗaya gidansu Mahaifiyarta tana nusar da ita tare da nasihohi kala kala da misalan abubuwa da yawa wadañda suka faru a duniya masu daɗi da akasinsu, sannan aka fara gyarata na tsawon kwana uku sannan Mahaifinta ya yi mata huɗuba sosai da kanshi ya ɗauketa ya kaita gidansu Safwan wurin Hajiya Mama ya bada haƙuri sosai sannan ya ɗauketa ya kaita gidan Safwan da hannunshi tare da yi masu addu'ar zaman lafiya.
Satinta biyu a gidanshi ba tare da ya waiwayota ba, har sai da Hajiya Mama ta nuna masa rashin kyautawarshi sannan ya baro Abuja ya nufo Yola ranshi ba daɗi, don in ta shi ake bi abarshi da Dijenshi ta isheshi rayuwa a duniya.
Ko da ya shigo garin sai da ya je wajen Hajiyarshi suka gaisa ya bata tsarabarsu sannan ya ɗan taɓa fira da fiddo da Surayya da aka dawo da ita haifuwa saboda Mijinta da baya nan, bayan sun gama tambayar juna bayan rabuwa ne ya miƙe zai tafi Hajiyarmu ta ce
"Ka kula da matarka don na hango shiriya a idanuwanta, kuma ka yi haƙuri da ni don nasan ba da son ranka ba biyayya ce kawai kake yi man, to ka sani duk lokacin da wani ya sami shiriya ta sanadinka ba ƙaramar lada zaka samu a wurin Ubangiji ba, shiyasa duk da nasan ta aikata mummunan laifi amman hakan bai sa na barka ka yi abunda ka so ba, don ina jin tsoron ka sake auro wadda zata aikata abinda yafi wanda ya yi muni, don gara ita da kishinta yake a fili yake kowa zai gani, saɓanin wasu da suke ɓoyewa a fili su nuna ba komi kuma su bi ta ƙarƙashin ƙasa su wargazaka daga kai har matar taka, to ko a hakan ma ka godewa ALLAH da baiwar da ya yi maka tunda bai haɗaka da mace mashurika ba mai biyar bokaye, wadda ba matarka ba har Ni da na haifeka da ƴan'uwanka duka zata iya rabaka gaba ɗaya"
Cikin sanyin jiki ya ce
"Na gode Hajiyarmu ai nasan daman ke baki ɗora wani ma a hanyar da bata dace ba bale ɗanki da kika haifa, Ubangiji ya ƙara bar muna ke ya karo lafiya da nisan kwana Hajiyarmu, na gode sosai kinga na manta da tsarabar da ɗiyarki ta bada in kawo maki"
Ya kalli fiddo ya ce "ke zo mu je ki karɓo na tafi Hajiyarmu sai na dawo"
Fiddo ta biyoshi zuciyarta cike shakkun abinda zata faɗa cen dai ta danne ta ce "big bros yaushe zaka je da Ni Abuja wurin Khadija?"
Ya waigo Yana yi mata wani kallo ya ce "Ba ma maraba da gulma idan har itace zata kaiki don nasan Zee ce taki don haka ki tattara kayanki ki je ki tayata zama idan na koma, ko ko karatu na ki ya zaki yi da shi idan kin je cen?"
Ranta a ɓace ta ce "Ni dai yayanmu cen nike son zuwa don ALLAH ka je da Ni in zaka koma yanzu, sai ka sakani makarantar a cen don nafi son inyi karatuna a cen"
Ya miƙo mata ledar saƙon da Dijen ta aikowa Hajiyar yana faɗin "lalle baki da hankali kina year 2 ki nemi barin makaranta saboda daɗin da ya yi maki yawa ko? To ki jira idan kin fara aiki sai ki koma cen da karatun kina biyawa kanki, Ni matsa ki bani gu tun ban hanɓarar da ke ba"
Fiddo ta yi cikin gidan tana gunguni don ita zaman garin ne ya gundureta, saboda in suna chatt da Husnah tana turo mata pictures ɗinsu in suna shaguna ko wuraren shaƙatawar da suke yawan zuwa, abun yana burgeta sosai shiyasa tasawa ranta itama zata koma cen a fantama da ita, amman dai ga shi ya gwasaleta a tashin farko.
Ya fisgi Motarshi ya nufi gidanshi, haka kawai yake jin baya son shiga gidan don ya daɗe zaune a parking space yana firarshi da ma'aikatan gidan, don ko jakarshi tuni aka shige da ita ciki sannan ya fito ya nufi sashen Zee ɗin zuciyarshi a cunkushe, sai dai yanayin da ga Zee ɗin yasa ya yi saurin sakin fuskarshi saboda ba ƙaramin bugawa zuciyarshi ta yi ba, ganin yanda ta yi baƙi ta rame sosai amman a hakan har da fara'a kwance a fuskarta da ta rame sosai tana yi masa sannu da zuwa.
Ya zauna tare da bin falon da kallo kamar mai neman wani abu sannan ya dawo da kallonshi gareta ya ce
"Ke fa? me ya sameki kika rame irin haka??"
Ta duƙe hawaye suna zuba ta fara wasa da yan yatsunta, cike da tausayinta ya ce
"Zo zo inji me ke faruwa ne?"
Zee ta durƙushe ƙasa tare da riƙo ƙafafuwanshi tana wani irin kuka take faɗin
"Plss ka yafe mani don ALLAH nasan ban yiwa kaina adalci ba, don ALLAH ka ce ka yafe mani ko da zuciyata zata yi sanyi"
Safwan ya ɗagota ya zaunar da ita kan kujerar da yake yana share mata hawayen ya ce "komi ya wuce ki daina wannan kukan yanzu ba gamu tare ba?"
Zee ta sake fashewa da kuka tana faɗin "na cutar da kaina da hannuna don ALLAH ka yi haƙuri"
Dole Safwan ya ajiye komi ya fara lallashinta, sannan ta kaishi ya yi wanka ta rakoshi diny inda ta shirya masa abinci mai kyau, yana ci yana janta da fira saboda ganin har lokacin bata daina hawaye ba.
Cikin dauriya ya bata kulawa ba yabo ba fallasa haka suka kwana kowa da tunanin da ke cike cikin zuciyoyinsu, ita tana ganin kamar yana riƙe da ita shi kuma yana tunanin irin lalacewar da ta yi.
To mu dai sai dai muyi maku fatar ALLAH ya bada zaman lafiya da hkr😝
Akafta😊
D/AUTA Ce✍🏻
*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*
*NA HADIZA D/AUTA*
*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*
*Aski ya zo gaban gashi Mutanena💃🏻*
*Lamba 70 *
Haka dai suka kwana ba natsuwar zuciyoyi, bayan SALLAHr Asuba Safwan ko da ya dawo masallaci ya taradda Zee tana ta karatun Qur'ani, abun ya buregeshi kuma haka ya ba shi mamaki sosai, saboda sanin da ya yi mata ada da ƙyar ma take tashi yin SALLAHr a lokacin, sannan idan ma ya matsa mata ta yi tana kammalawa take yin kwanciyarta ko addu'ar kirki bata tsayawa yi, amman yanzu ita ce har da su karatun Qur'ani, cike da jin daɗin sauyin da aka samu ne ya zauna kan gadon yana ƙarasa addu'o'inshi na azkar, har bacci ya fara janshi ya kwanta ba shiri saboda baccin da ya fiegeshi ba tare da ya shiryawa hakan ba.
Misalin ƙarfe takwas ya falka saboda ƙamshij abun break ɗin da take haɗa masu, mamaki ya sake kamashi ya fito ɗakin ya nufi kitchen yana kallon yanda take ta hadadarta, cikin shigar wata doguwar riga ƴar kanti, tana ganinshi ta diririce tana gayar da shi cikin ladabi, bayan ya amsa ne zuciyarshi cike da jin daɗin sauyin da ta samu, ya fice kitchen ɗin zuwa sashenshi saboda zuciyarshi da ke ta kwaɗayin son jin muryar Uwargidanshi, don tun yana kan hanyar shigowa garin da suka yi waya ta ji ya sauka lafiya ta kashe wayarta, saboda kishin da ke cin zuciyarta game da zuwanshi wurin Zee, da abun ya kwana a ranshi saboda ya yi ta kiran wayoyinta a kashe ta Husnah ma a kashe, cikin takaici ya kira Aunty Ummi ya ce ta haɗashi da ɗaya daga cikinsu yana son yin magana da Dijenshi, Aunty Ummi ta nuna masa dare ya yi sosai ya dai haƙura sai da safe, saboda a lokacin ƙarfe sha biyu da mintuna dole ba don ya so ba ya haƙura amman zuciyarshi cike fal da son jin dalilin da Dijen ta aikata hakan.
Shiyasa ko da ya shiga sashenshi ko wanka bai yi ba ya fara nemanta a waya, aka yi da ce ta shiga itama caraf ta ɗaga sai dai shirun da ya ji ta yi masa ne yasa shi saurin faɗin
"Me na yi maki kika horani da rashin jin muryarki?"
Sheshshekar kukan da ya ji ne a kunnenshi yasa ya yi saurin sake wata maganar a rikice ya ce
"Subhanllah me ke faruwa ne? Me aka yi maki? Wa ya taɓa man ke don ya ga bana nan?"
Dije ta sake fashewa da kukan gaba ɗaya cike da ruɗewa ya ce
"Plss babyluv don ALLAH ki daina kukan nan ki sanar da ni abunda ya faru idan har kina son ganin natsuwata"
Cikin kukan Dije ta ce
"Ka gaisheta"
Tana ƙare faɗar hakan ta datse kiran, cikin wani sabon tashin hankali ya sake bi da wani kiran amman har ta tsinke bata ɗauka ba, ganin hakan ya sa ya dinga kiran Husnah kira bayan kira, tana bacci dole ta miƙe ta ɗauka ya ce da ita ta kaiwa Dijen, ta miƙe cike da jin haushin katse mata bacci da aka yi, sai dai kukan da ta tarar tana yi ne yasa jikinta ya yi sanyi, ta miƙa mata wayar ta fito zuciyarta cike da jin zafin kukan da ta ga Auntynta tana yi, don tun jiya take lallashinta akan ta yi haƙuri ta daina kukan da ta ke yi na rashin Auncle ɗinsu, ta yi kamar ta haƙura ashe bata haƙura da kukan ba.
Dije ta kara wayar a kunne tana share hawayenta ta ce
"Ba wani abu fa kaina ne yake ciyo"
Daga cen ɓangaren ya sauke ajiyar zuciya yace, "haba haba My luv to meyasa ba zaki sanar da ni ba kike wahalar man da kanki da Babyna? Yanzu ki shirya Aunty Ummi zata zo ta kaiki Asibiti sannu kin ji? ALLAH ya baki lafiya"
Ta ce "Ameen" cen cikin maƙoshi sannan ya sake cewa "ya kwananki da na Babyna?"
Ta ce "ƙalau"
Cike da mamakin yanda take ta ba shi amsa a taƙaice ya ce "Babyluv ko na yi maki wani abun ne ban sani ba?"
Ta ce "A'a" yace 'to wacece kike cewa da ni in gayar?"
Ta murguɗa baki kamar yana gabanta ta ce "wadda ka je wajenta ko ba'a buƙatar gaisuwar tawa ne?"
Ba shiri ya rufe bakinshi saboda fahimtar inda ta dosa, cikin dariyar da ta so kufce masa ne ya ce
"Ana buƙata kuma an karɓa hannu bibbiyu ALLAH ya saka da aljannah, amman fushin na minene? ko kin manta Umurninki na bi? To yanzu kuma tunda an yi maki abunda kike buƙata kuma ta dawo kamar yanda kika roƙar mata alfarma Ni kuma mi ye laifina a ciki?"
Ta ce "ba ko ɗaya hasali ma ka yi abunda ya dace" zai sake yin magana ne Zee ta turo ƙofar ɗakin ta shigo da nufin sanar da shi komi ya yi ready, ganin yana waya ya sa ta yi saurin juyawa da nufin komawa, ya yi gyaran murya ta waigo ya yafitota ta ƙaraso wurinshi, ya miƙa mata wayar cikin jarumta ya ce "kHadija ce ku gaisa"
ZEE ta karɓi wayar cikin sanyin jiki tana shirin yin magana ta ji Dijen tana faɗin
"Dawo da itan ai abu ne wanda ya dace, kuma kai kanka zaka gano alfanun yafiya ga wanda ya yi maka laifi, saboda ladarka tana wurin Allah Kuma insha ALLAHu za ka ga sakamakon abun alkhairin da ka yi, fatana kawai ALLAH ya baka ikon yi muna adalci, kada don an sami ta ƙarfen a juyawa ƴar ƙauye baya"
Zee ta yi saurin faɗin
"Insha ALLAHu in dai ta ɓangarena ne matsala ta ƙare, da ni da ke yanzu mun zama abu ɗaya babu wani gorin asali ko wani fifiko, a zahirance ma kin sha gabana don kin riga da kin yi man fintinkau tunda har kike da zuciyar imani, kika ɗora Mijinki akan hanyar dawo da ni cikinku duk da abunda na aikata maku a baya, don ALLAH ki yafe mani kinji insha ALLAHu zan yi ko yi da kyakkyawar zuciya irin taki, saboda yanzu na gano cewa ko wane mutum da kalar baiwar da Allah ya yi masa, sau da yawa wanda ka ke renawa sai ya zo ya fi ka ta hanyoyin da kai ko da kuɗi ba zaka iya binsu ba, matuƙar sheɗan yana buga ganganunshi saman kanka, na gode sosai da taimakon da kika yi mani aka dawo da ni, kuma ki sa a ranki cewa kina da ƴar'uwa saboda yanzu Zee ta ɗaukeki tamkar ƴar'uwarta ta ciki ɗaya tunda har na gano ke ɗin alkhairi ce garemu ni da shi"
Tana ƙare faɗar maganar ta miƙa masa wayar ta fice da sauri tana kuka, ya bita da kallo sannan ya sauke ajiyar zuciya yace
"Babyluv sannu da namijin ƙoƙarinki, lalle ke alkhairi ce ga rayuwata, ina ta ya ƴaƴana farin cikin samun uwa ta gari irinki, fatana kawai a yanzu ALLAH ya sauke man ke lafiya ki bani Babyna a hannu in ɗauka"
Dije ta goge ƙwallarta ta saita natsuwarta ta ce "Insha ALLAHu ƴaƴa har sai ka ce in tsaya haka nan in huta , don in na Fara watso maku su sai ka rasa da hannun da zaka riƙe sauran"
Safwan ya fashe da dariya cikin dariyar ya ce "au watsosu ma zaki yi don salon mugunta?, To bari ki ji ko da jefosu zaki yi ta yi duk bayan minti biyar Habibynki ba zai taɓa rasa hannun da zai karɓesu ba, ke dai kawai ki natsu ki sako man su sannu a hankali ina karɓewa cikin farin ciki ba tare da gajiyawa ba ko ƙosawa"
Haka suka yi ta firarsu mai cike da barkwanci da raha har dukansu suka daina jin damuwar rashin ganin juna, sannan Dije ta daƙile firar dolenta don bata son ta shiga haƙƙin Zee, ba don ya so ba suka yi sallama cikin kewar juna tare da kwaɗayin ganin junansu, saboda mugun sabon da suka yi wa juna da kawunansu.
Har ga ALLAH Safwan ya ji daɗin yanda Zee ta dawo macen kirki, shiyasa cikin dauriya da kai zuciya nesa ya mu'amalanceta har lokacin barin garin ya yi ya tattara kayanshi ya koma Abuja, wurin Matarshi da ya ke jin a duniya kaf ba ya da matar da zata kamo ƙafarta ma bale ta kamota, ko da ko akwai ɗiyan lu'ulu'u da murjani a cikin.
****
Haka rayuwa ta yi ta shurawa sannu a hankali har cikin Surayya ya isa haifuwa ta haifo ƴarta mace masha ALLAH da ita.
Cikin zumuɗi Dijen ta yi ta murnar zuwa Yolar sai dai idan ta tuna da zata ga Zee sai jikinta ya yi sanyi, dole dai haka ta daure ta matsa masa ya barta ta biyo su Aunty Ummi suka nufo Yola, saboda a lokacin shi ana tsaka da aiki don during working hours ne, cike da jin daɗin yarinyar Dije ta fara santi tamkar ta sace yarinyar take ji saboda sonta da take yi, Hajiya Mama da su Surayya sai dariya suke yi mata ganin yanda ta maƙake yarinyar bata son kowa ya ɗauketa, don har goyeta take yi sai Hajiya ta yi faɗa take sauketa, Zee ma kullum tana zuwa da ita ake komi shiyasa Dijen ta rage kishinta da take ji aranta, saboda ganin yanda ta ke ta haba haba da ita tamkar cewa babu abunda ya taɓa shiga a tsakaninsu, haka ma da yanda take ta janta a jiki tana nuna mata cewa ai an zama ɗaya babu zancen wata kishiya shiyasa itama ta ajiye komi suka fara ɗasawa, wanda hakan ba ƙaramin daɗi ya yi wa Hajiya Mama ba, ta ƙara godewa ALLAH da har ta jajirce Safwan ya dawo da aurenta, don tasan dole ne sai ya nemi wani auren tunda har ya saba da mace biyun, kuma da wacce ba'a san halinta ba gwara wadda daman cen an san halinta sai a ci maganin matsalar.
Aka yi taron suna lafiya cike da ƙayatarwa yarinya ta ci sunan uwar Mijin Surry ana yi mata laƙabi da ilham, bayan suna Safwan ɗin ya zo ya yi kwana biyu sannan ya kwashi Matarshi suka koma Abuja. kawosu ita da
Sannu a hankali itama Dijen cikinta yana ta miƙawa har ya kai watannin haifuwa, Hajiya Mama ta matsa masa akan dole ya dawo da ita wurinta ta haifu, amman ya nuna shi dai ya fi son idan ta haifu sai su dawo yolar, saboda cen ɗin tana samun kulawar manyan likitoci a Asibitin da take awo, sai da Hajiya Mama ta yi masa jan ido sannan ya kwasota da himilin uwar siyayarta da ta jaririn da za'a haifo masa, don daman cen shi rabuwa da ita ne ba ya so saboda ko da take da titsetsen cikinta idan jarabarshi ta motsa tasan ta yanda zata faranta masa har ta gamsar da Habibynta.
Shi yasa ko da suka zo Yolar ya kasa ya tsare gidan Hajiya Mamar ya ƙi barin garin har sai da korashi saboda yanda ake ta nemanshi a ma'aikatar ta su, saboda muhimmancin da yake da shi dole ne wani abun sai da shi.
Satinta ɗaya a Yola ta fara jin sign na naƙuda, Hajiya Mama tana bata kula sosai da sosai don itama ɗin har nurse's ta samo mata masu duba mata ita har gida ba sai anje Asibiti ba, Zee kanta kullum tana gidan ana renon cikin da dakon zuwan haifuwar, sai ko ga shi cikin ikon ALLAH wata ranar juma'a Asubar farin ta fara naƙuda, jikin Hajiya Mama yana rawa ta saka direba ya kwasheta da kayan da duk za'a buƙata suka nufi wata babbar Asibin da ke garin yolar, cikin nasara kwata kwata bata yi minti goma da shigarta labour room ba ta haifo santalelen yaronta Mai kama da Ubanshi sak, fari jajir har wani yalo yalo yake yi saboda tsabar farinshi, ga shi ƙatoto da shi masha ALLAH tamkar ba haifuwar Dijen Baffah ba.
Farin ciki wajensu Hajiya Mama da fiddo da ma Zee ɗin abun ba'a magana, saboda har rige rigen ɗauka ake yi tsakaninsu su biyu, Surayya ma rufe ido ta yi tace tunda da ita yaron yake kama itace zata riƙeshi, Hajiya Mama dai sai dariya take yi masu idonta akan ɗakin da Dijen take tana ta baccin sauke gajiyar naƙudar da ta sha.
Ango ƙarni kam daman yana kan hanyar zuwa Yolar sai ga kiran Fiddo ya shigo wayarshi cikin kuwwa da ihun murna take sanar da shi an samu Baby boy, ba shiri shi ma ya buga wata ƙatuwar kabbara ya ce
"ALLAHU Akbar? Alhmdllh! Shikenan na zama Baba, Little sis kina da tukuici mai tsoka a wurina, to ya ita Mamar boy ɗin lafiyarta ƙalau dai ko?"
Cikin murnar albishir ɗin da ya yi mata na tukuici ta ce "fine take big bros bacci ma ta ke yi yanzu haka"
Baki a washe ya ce
"Ok Ina Kan hanya daman ganin na kusa ƙarasowa garin ki shafa man kan babyna"
Cike da jin daɗi fiddo ta koma ɗakin tana dariya ta ce "Wayyo daɗi Ni ce na yiwa yayanmu albishir ya ce in tsumayi tukuicina"
Surayya da ke ta faman murnar ta sameshi a wayar da nufin ta riga kowa sanar da shi ba shiri ta kashe wayar tana harararta ta ce
"Ai WALLAHI kin ƙware da mugunta yanzu don salon yaudara shine kika fice waje kika rigani to ai dole mu raba koma minene"
Zee sai dariya take masu Hajiya Mama ta kira cen garinsu Dijen ta sanarwa da su Baffah, sannan ta dinga kiran mutane yan'uwa da abokan arziƙi tana ta sanarwar haifuwar, kafin ka ce me Asibitin ta cika da yan taya murna kowa baki har kunne.
Angon ƙarni ma ko da ya zo ya taradda mutane ciccike sai tayashi murna ake yi, sai washe baki yake yi amman idonshi suna cen wajen dubo ta ina zai hango kyautar da ALLAH ya yi masa?, Aiko sai ga shi ya hango babyn hannu wata dattijuwa tana tofeshi da addu'o'i.
Cikin sauri ya nufeta ba kunya ya saka hannu ya karɓe yaron tamkar ya yi ihu saboda daɗin ganin yaron a hannunshi, ba tare da tuna da inda yake ba ya kaiwa yaron kiss a goshi da baki, sannan ya hankalta da mutane bakinshi ya ki rufuwa saboda dariyar kanshi da jin daɗin ganin ɗan shi,sannan ya miƙa yaron yana tambayar Hajiya Mama Dijen ta yi masa nuni da ɗakin da take hutawar, ya nufi ɗakin zuciyarshi fess da farin cikin hangota kwance har a lokacin tana ta baccinta, ya tsaya jikin gadon ya shafo kanta tare da duƙowa ya yi mata kiss sannan ya riƙo hannunta, cikin sauri ta buɗe idonta ta saukesu a kanshi ba shiri ta washe baki da murmushi akan fuskarta ta ce
"Habiby"
Ya riƙe hannunta duka biyu ya ce "sannu da ƙoƙari kin ji? ALLAH ya biyaki da gidan Aljannah, naga yarona Masha ALLAH har ya fiki kyau"
Ta ɓata fuska tare da turo baki ta ce
"Saura ƙiris in fara kishi da shi yasin"
Yana dariya mai cewa cike da zallar ƙaunarta tare da shauƙin sonta da ke ɗibarshi, ya duƙa ya tsotso leɓenta sannan ya ce
"I love You so much my heart desire, ke mahaɗina ce idan ina kusa da ke kina sakani susucewa, don haka kada ki janyo in yi abunda za'a ga na yi rashin kunya"
Dije ta yi masa wani fari da ido ta rausayasu sannan ta ce "ina sonka Habiby"
Cikin zurmawa da salonta ya ce "ina son matata kuma ina son kasancewa da abuta a kullum a koda yaushe kuma a kowane lokaci, amman yanzu sai na yi zaman jira kenan ko? Kwana nawa ne ma ake yi wai?"
Dije ta rufe fuska cike da jin nauyin maganar ta ce "kwana dubu uku ne ake yi ai nasan Habibyna jarumin gaske ne zai iya yin fiye da kwanakin ma "
Ya zaro ido waje baki buɗe ya ce "A wannan karon kam dole ne kowa sai ya gano ragwantakata, cabɗi ki ce in mutu kawai kafin zuwan lokacin"
Dije zata yi magana wata Nurse ta shigo tana dariya musamman ganin yanda suke riƙe da hannun juna gam gam tace
"To luv bird's zaku iya tafiya gida tunda har ta gama hutun, sai ku je cen ku ƙarasa soyayyar"
Dukansu suka kalli juna suna dariya Safwan ya saka hannu aljihu ya fiddo kuɗi bai ma tsaya lissafi ba ya miƙa mata yana faɗin
"To ga goro a tayamu da du'a'in dawwama cikin farantawa juna"
Ta karɓe tana jin daɗi ta fice bayan ta gama zuba masu addu'o'in.
Haka aka tattaro da maijego da jinjirinta da masu zuwa ta ya murna aka nufo gidan Safwan, saboda Hajiya Mama ta ce akai Dijen ɗakinta saboda danginta idan sun zo ta ji daɗin tarbarsu, kuma duk wanda bai san muhallinta ba ya gani, amman ta saka wasu dattijai masu kula da ita waɗanda za su yi mata komi kamar a gabanta, cike da jin daɗi Safwan ya fice bayan ya saukesu ya faɗa shaguna yanata lodo kaya har na hauka, bayan waɗanda suka sissiyo a Abuja sai da ya yiwa Dijenshi set biyu na jakunkuna masu samfurin akwati tsadaddu masu shegen kyau, kowace jaka maƙare da kaya na alfarma sannan ya yi wa boy na shi set guda shi ma tsadaddun kaya, Zee ma da nata set sannann ya yi wa su Hajiya Mama da su fiddo su ma, ya sa aka kwaso masa kayan suka nufi gidan Hajiya Mama ya zubesu gabanta, duk da ta ji daɗi amman ta yi masa faɗan almubazzaranci ba kyau, yana dariya ya ce
"Duk abunda na yi maku Hajiya ai kun fi ƙarfinshi wajena, amman insha ALLAHU zan kiyaye a gaba, don ko wannan don naga khadija ko lefe ban yi mata a lokacin aurenmu ba"
Ta sauke ajiyar zuciya ta ce To ALLAH ya rufa asiri ya ƙara buɗa maka kuma ya baka ikon sauke ɗawainiyar gidanka gaba ɗaya "
Ya ce '"Ameen"
Sannan ta ce idan duhun dare ya shigo ya zo ya kwashi kayanshi ya kaiwa Matanshi, sannan ta yi masa godiyar na su da ya siyo masu tare da saka masa albarka, da addu'ar kariya daga sharrin ko mi ƙankantarshi.
Dije kam tana cen ita jaririnta sun sha wanka sai ƙamshi suke yi, Surayya ta haɗa mata tea mai shegen kauri ta shanye saboda saukowar ruwan nono da wuri, sannan dattijan suka baje wajen da aka keɓe don kawai irin wannan lokacin, anata hidimar dafe dafe da dama mata kunun jegon da Hajiya Mama tasa aka dako tun lokacin da aka yi haifuwar.
Ko da ya dawo gidan ya taradda Zee da su Surayya ɗakin sunata firarsu suna shewar jin daɗi, Dije riƙe da kofin kunun tana sha a hankali saboda zafinshi, ya ƙaraso cikin ɗakin ya kalli Zee da ke goye da yaron ya ce
"Naman boy Daman cen kin iya goyon ne?"
Tana dariya ta juya kanta baya ta kallo yaron ta ce
"Ka ga alama don kuwa ga yarona nan yanata baccinshi don shi ma yasan Uwa ba wasa ba ce"
Gaba ɗaya suka fashe da dariya wajen dariya har Dijen ta ƙware da kunun da ta cika bakinta, sai ga shi da kaiwa wurinta ba shiri yana bubbuga bayanta yana hura mata kai tare da faɗin
"Sannu baby sannu"
Hankalinshi bai kwanta ba har sai da ya ga ta dawo normal sannan ya fara dungure mata kai ya ce ,. "Idan kin san ba zaki natsu ba to ki koma wani gu sai kin shanye kunun ki dawo don bana son wasa da lafiya"
Dije ta yi masa wani kallo cikin marairece fuska sannan ta riƙe kunnenta ta ce
"Am sorry habi....."
Ta kallo Zee ta yi saurin datse cikon maganar, Zee tana dariya ta ce "biby"
Surayya da fiddo suka fashe da dariya saboda yanayin da Zee ta yi maganar tana marairece fuska tana lanƙwashe wuya tare da murguɗa baki, sannan ta kalli su Surry ta ce
"Ku zo mu basu waje tunda a gabanmu ma ba za'a yi muna kawaici ba"
Su Surry Suka fice ɗakin suka barsu sunata kallon Zee cike da dariyar da ta suƙesu, Safwan ya kalli Dijen ya ce
"To Ni yanzu ya zaku yi da ni? Babyna na zo gani na taradda an wani duƙunƙuneshi a baya, ƙarshe ma ga yanzu kin janyo an fice da shi bamu gaisai ba"
Dije ta ɗauki kunun ta kurɓa sannan ta haɗiye ta ce "kun fi kusa ka je ka karɓo tunda baka godewa kulawar da yake samu ba"
Ya kalleta da kyau ya ce "haka ma zaki faɗa?"
Ta sake kurɓa kununta sai da ta cika bakinta sannan matso jikinshi ta janyoshi ta riƙo kanshi ta tallafo ido cikin ido ta goga hancinta da na shi sannan ta nufi bakinshi kamar wani sakarai ya buɗe bakin ta juye masa kunun sannan suka fara zuƙe kunun tare har suka shanye, sai ga shi sun buge da dulmiya cikin wata sabuwar duniya sun manta shaf da cewa ba su kaɗai suke ba har sai da suka ji kukan yaron sannan suka dawo hayyacinsu.
Sai ga fiddo ta zo rungume da shi ta ce tsohuwa ɗaya daga cikin dattijan ta ce ta ba shi nononshi ya tsotsa, Dije ta zaro ido waje ta ce
"To Ni ina nasan yanda zan bashi ??"
Safwan ya karɓi yaron Fiddo ta fice ya sakarwa yaron kiss sannan ya kalleta ya ce
"Oyo bari Abban boy ya koya maki riƙe man shi anan"
Ta karɓa ta rungumeshi ya ɗaga rigarta ta ƙasa ya fito da nonuwan, cike da zallar maitarsu a fili ya shafosu duka ta yi saurin lumshe ido, sannan ya ɗago kan yaron ya saita bakinshi ga ɗaya aiko yaron ya fara tsotsa zumui zumui tsut! tsut! Ta cije baki tana faɗin
"Da zafi Habiby kuma ma WALLAhi ba komi a ciki don ALLAH ka bari har ruwan ya zo a hakan zafi kawai zan sha"
Yana ƙumshe dariyarshi ya cire nonon a bakin yaron ya karɓeshi ya ajiye sannan ya je ya rufo ƙofar ɗakin, ya dawo yana wata dariya ya yi durƙuso a gabanta ya sunkuya ya kai nonon a bakinshi ya fara tsotso cikin mugunta, ta fara tureshi amman hakan bai hanashi tsotse ɗaya tas ya saki ya kama ɗayan ba, sai da ya ɗauki lokaci yana zuƙo nonon sannan ya saki, Dije tana hawaye wahala ta ce
"Shi dai mutum ya kamata yasan ya fara girma, a gaban yaro ko kunya baka ji ba kake wannan halin?"
Yana dariya ya sake ɗauko yaron ya ajiye a gabanta ya saita bakinshi ya saka masa nonon, yaro ya ci gaba da tsotsa har da su sauke ajiyar zuciya, Dije ta bi shi da harara ta ce
"Yasin zaka janyo in horashi tunda akanshi ne ake yi man mugunta"
Yana dariya ya ce "wuta bal bal cin zalin yarona ko a bayana ne ku wa"
Ta murguɗa masa baki tana cije leɓe saboda zafin da take ji yana ratsata, haka yaron kam ya sha iya son ranshi sannan ya koma bacci, Safwan ya karɓeshi ya kwantar da shi ya zauna suna firarsu mai cike da nasu salon son, har sai da suka ji ana ƙwanƙwsa ƙofar ne ya buɗe ya fice su Surry suka shigo suna yi mata tsiya.
Ko da dare ya yi Safwan ya kawo masu kayansu Dukansu sunyi farin ciki ba kaɗan ba, musamman Dije da har sai da ta yi kukan daɗi saboda ganin himilin kaya kuma wai duk nata ita da yaronta, ba shiri ta rungumeshi tana kuka tana yi masa godiya.
Mai jego muma dai kam mun tayaki murna😊
Akafta🤪
D/AUTA Ce✍🏻
*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*
*NA HADIZA D/AUTA*
*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*
*ALHAMDULILLAH!!!!*
*Lamba 71*
Dije da yaronta suna samun kulawa sosai tamkar a gaban iyayenta ko ma fi, don ta ɓangaren cima mai daɗi bata da wani aiki sai na cin daɗi, saboda har rago biyu ya sa aka yanke aka soye mata wani bayan an sarrafa sauran kala kala aka tasata gaba ta yi ta kwasar gararta, kwana biyar da haifuwarta ne ƴan'uwanta suka diro Yola ƙatuwar Bus cike da mutane har da masu zuwa ganin ƙwam, don kuwa izuwa lokacin Dije ta yi wata daraja da ƙima a idanuwan yan garin nasu, saboda mutumci da Safwan ya siya mata a wurinsu ba tare da ma ta sani ba, wanda ya janyo har su kansu Inna da Baffah yanzu sun zamo wasu mutane masu daraja a cikin garin na su ta sanadin hakan.
Dije murna baki har kunne saboda jin daɗin ganin ƴan'uwanta da abokan arziki a cikin gidan aurenta, sai haba haba take yi da su cikin mutuntawa tare da girmama matsayinsu a wurinta, wuri na musamman aka keɓe masu ana ta basu kulawa ta ɓangaren abinci da abinsha sai sambarka suke ta yi da sa albarka, Dije kam farin cikin fal ranta bakinta ya ƙi rufuwa saboda ganin Abokanta na ƙurciya, waton Ladiyo Jummala da Lanti da Mune sai Hansai da ta zame mata tamkar ƴar uwa tuni, saboda auren Usmanu da ta ke yi sannan kuma ga shi tana kyautawawa Innarta shiyasa ta ke jinta ta daban a wurinta.
Mutanen garinsu Dije kam sai mamakin ganin yanda ta koma ƴargayu suke yi, don tuni ta sade da su ba zaka taɓa ganinta ka gano cewa wai tashin ƙauye ba ce, ta burgesu sosai musamman yanda ta ke nuna masu kulawa babu ƙyama bale nuna wariyar launin fata, ganin haka ne su Surayya da Zee da ita kanta Fiddon suke ta Nam nan da su su ma.
Tun ana gobe suna aka watsawa aka fara hidimar bikin don kuwa gidan cike yake fam da mutane ana ta hada hadar bikin, tsakanin soye soye da dafe dafe bayan wanda aka kai wani guri ayo ammsn duk da hakan mutane sai ɓarkowa suke yi.
Ranar suna maijego da yaronta da ya ci sunan Mahaifin Safwan ana kiranshi da Sayyid shi ma kanshi ya sha gayu bayan an ɓata lokaci wajen tofeshi da addu'o'in kariya daga sharrin mutum da na aljan, don farinshi yasa ko wa ya ganshi dole ne ma sai ya maganta, musamman yan ƙauyensu Dijen da suke ganinshi tamkar ba Dijen ce ta haifoshi ba, saboda ganin yanda yake tamkar ɗan indiyawa saboda kyau da fari.
Dije tare da su Surry da sauran mutane sai ɗaukar photuna ake yi cen na hango wata tawagar mutane ta doso Dijen ko da na duba da kyau na hango Shaharrun marubutan nan masu ji da kansu da amfani da lokacinsu wajen farantawa al'umma irinsu
Hannah Suhana (Hajiya Duduwa)da Billy s fari Ayusher Muhammad, tare da Ummi Garkuwa, Nimcyluv, Maizafafa, Oum Mumtaz, Ummu Najma, Salaha Muhammad, sai Mmn Musaddiq, Firdausi mrs shugaba, Ameera Adam, Mmn Shaheed, Mmn Maleek, Autar manya, tare da Ummu Ja'afar.
Ganin yanayin takunsu yasa ta gano su ɗin ba ƙananun mutane ne bay yasa ta sa aka tanadar masu wurin zama na musamman, sannan ta je rungume da Sayyid tana gaisawa da su ɗaya bayan ɗaya sannan kowacensu ta gabatar mata da kanta cikin raha da wayewar kai irinta Marubutan, sannan suka dinga ɗaukar photuna da ita tare da Baby, sai ga shi na hango ana rigimar karɓar Sayyid tsakanin ƙannena biyu Billy s fari da Hajiya Duduwa, ko wace ta na faɗin ita ce zata ɗauka sannan dai Ƙanwata Ummi Garkuwa ta raba gardamar wajen shiga tsakiyarsu ta riƙe yaron aka fara ɗaukar photuna.
Tana cikin marubutan ne Fiddo ta zo tana haki ta ce ta zo ga wasu gungun mata cen su zo suna nemanta, Surry ta ce ta je ita zata ji da su aiko ta saki jiki ta dinga lodo masu abinci da abinsha da maƙulashe ko wace ta ci ta sha sannan ta cika mas ledodinsu na kayan bikin kala kala.
Dije ta je ta sauyo wasu kayan cikin wani arnen tsadadden less wanda yaji shuwari stone ta ko'ina sai walwalniya suke yi, ta fito tana takun ƙamshi ta nufi inda ake nemanta, sai ko ga Maryam Omee ta yi saurin zuwa wurinta ta rungumeta tana faɗin
"Oyoyo Dijeta Barka da arziƙi"
Dije ta saki baki tana dariya tace "yawwa Barka dai Auntyna" duk da bata ganota ba amman ganin zallar ƙaunar da ta nuna mata yasa ta ji itama ta kwanta mata a rai, Omee ta waigo bayanta tana kallonsu Mmn irfaan da ke tsaye suna kallonsu ta ce "mun yo tattaki ne takanas daga group mabanbanta saboda kawai mu tayaki murnar zuwan wannan rana mai cike da farin ciki a garemu duka, saboda haka yanzu zan yi maki bayaninsu filla filla"
Ta nuna Mmn irfaan da ke tsaye tana wara idon ta ina zata hango Zee ta ce
"Wannan itace Mmn irfaan sai wannan Mmn ss, Ummu Afrah, Fati Ghana, Oum Suhail, Hauwa Zubair, Deejerlee, Mum Sayyid, Sa'ar Bukar, Faeexe, Najida Aliyu, Daughter Ummi Khatsina, Rufaida idris, Hamida Ƙaura, Jamila Haidara, Mmn Ra'ees, A'isha Yola, "
gano hakan yasanMmn Heedaya, Zainab Garba, Aunty Sady,Rahina, Glam By hajia sumy,Ummu Rauda, A'isha kishoor, Amrah barrister, Mmn Beaty, Mum of 3full H, Ummu Muhammad, Aisha S yamm, Subai'a Hussaini Gwandu, Hannatu Umar, Saratu Nakura, Zee MD, Hannatu Ahmed, Ummu deedat, Firdausi Muhammad sani, Rukynamango, A'isha Muhammad, azrarrfa8, Fatima sani mmn Masoyi, Princess N, Nakura, Ummin Sadiq, Ummi Sajida, Mmn meenat, mmn Yusuf, Hannatu Garba, mmn inty&Anwar, Shafaatu Aminu, Halima Gwani, Mmn Moh'd, Tamasu, mmn basma, mmn Hafsa, mrs Kamal, Aisha mada, Ummu Aisha, Ummu Haidar, Fatima Bello maimaita, mmn Abdu, Nasmie mafara, i lv u mum,Mummyn Nasrin, Jamila Isa, Aunty Islam,mmn Husnah,Mummyn annur, mmn shuraim, Ummul adnan,Amina Abdullahi.
Cikin sauke numfashin wahala Omee ta dafe goshi ta ce "wai ALLAH yasin muna da yawa in nace in ta zayyanosu zamu kwana anan bamu tantance ba,don haka don ALLAH ku yi haƙuri saura abun ne da yawa...."
Tana cikin maganar ne maganar ta tsaya saboda hango Asiya Umar A ya yarda, da tayi ta shigo gidan cikin gayunta tana wara idon ta ina zata hango idon sani, Omee ta washe baki tare ta dafe goshi ta ce
"Wayyo rimatyna ta ƙasaro"
Dije ta yi dariya ta ce dasu gaba ɗaya tana yi masu sannu da zuwa sannan ta jasu suka yi ciki inda ta yi masu masauki a ƙaton falon nata, Dukansu suka shishigo kowace tana samun wurin zama inda wasu ma har ƙasa suka zube abunsu saboda yawa su yasa falon yana so ya yi masu kaɗan.
Nan fa aka shiga yi masu tarba ta musamman, don su yawansu bai hana kowacensu ta yi ƙat ta yi hani'an ba saboda anyi komi a wadace.
Ana cikin cin abincin ne naga ɗiyar ɗakina Mmn irfaan da Daughter Rufaida da ƙanwata Asiya Umar sun haɗa kai suna ƙusƙus, sai ga shi naga suna ta zarmewa da ɗaya ɗaya suka fice falon, aiko na biyo bayansu sai naga sun nufi sashen Zee, na bisu cike da mamaki a raina nace
"Lalle so duk so ne amman son kai ya fi yau ko ga shi na gani da idona"
Ina biye da su har falon Zee inda na hangota cikin shiga ta alfarma tana ta hidima da ƴan'uwanta da suka zo daga Gombe, abun mamaki Asiya naga ta manna da gudu ta rungumeta tana ihun faɗin
"wayyo Aunty Zee Ina yinki WALLAhi"
ZEE tana dariya ta bi Asiya da kallo ta ce "Ni ma haka ƙanwata saukar yaushe?'"
Asiya ta washe baki ta ce "mun jima munata neman inda zamu ganki tare Ni ke da ƴan'uwana suma masoyanki ne na haƙika kamar Ni, don lokacin da wannan ƙaddarar ta sameki mune muka yi ruwa kuka yi tsaki akan kare maki martabarki agun abokan adawa"
Zee ta sake rungume Asiya cike da jin daɗin maganar tata ta janyo hannunta ta ce
"Oya ku zo mu je masaukinku na daban ne ai"
Ɗiyar ɗakina da Daughter Rufaida Suka biyo bayansu suna dariya, aiko sunga tarba kuma sun ga gata don kuwa Zee komi nata na tarbon baƙint ta yi abunta daban bayan na gidan.
Shiyasa suka baje suka kwashi Gara abunsu ina yi ina haɗiyar yawu saboda ina jin tsoron in fito su gano leƙen asirinsu na zo yi.
Haka aka yi taro cikin farin ciki da annushuwa kowa ya tafi yana murna saboda anyi masu komi a wadace babu ƙwange hannu a cikin lamarin ko kaɗan.
Taro ya watse lafiya kowa ya nufi gidajenshi anata yabawa sannan da yi wa jariri da Mahaifiyarshi addu'a, da yi masu fatar ƙarin buɗi mai alkhairi ko don wasu su amfana.
Don yan garinsu Dije daren da zasu koma gida ne Safwan ya cikasu da abun alkhairinshi, suka ruɗe sai zuba godiya suke yi, haka ma ZEE ta yi masu alkhairi dai dai iyawarta suna ta godiya da yi masu addu'ar zaman lafiya ga junansu.
Dije da su Ladiyo suna ɗakinta ana firar bankwana Ladiyo ta kalli Dije cike da urgewa ta ce
"Ai ke Dije yanzu ba abunda ya rage maki a duniyar nan illah ki cika da imani ki je lahira ki sami aljannah, don WALLAhi duk abunda ake yi ALLAH ya yi maki saboda haka ki godewa ALLAH"
Dije ta yi dariya ta riƙo hannunta ta ce "Alhmdllh K'awata wannan kalmar itace kalmar da kullum nake yawan faɗa a bakina, saboda Ni kaina sanan ya yi man baiwar da ba kowa ya yi wa irinta ba"
Jummala ta ce ", TABBAS ke ƴar baiwa ce a cikin mata don ga shi ko mu yanzu ta sanadinki mun fara zama ƴaƴan baiwar, don kuɗin da kika aiko muna kwanaki wallahi Ni dai sun yi man tsanin alkhairi Ni da Garbatina, don kuwa yanzu haka birni yake zuwa yana siyar da fitullu kala kala na zamani masu batur da masu aiki da zuƙar nefa, kamar da wasa ya fara kasuwancin sai ga shi yanzu kullum abu sai haɓaka ya ke yi, WALLAhi mun gode sosai mukam"
Lanti da ta yi tagumi ta ce "ai Ni bance komi ba Dije don WALLAhi har zaucewa na so yi lokacin da Usmanu ya kawo man su har gida ya ce in jiki wai mu ja jari, haka naga abun kamar almara WALLAHI"
Dije cike da mamaki ta kalli Hansai saboda neman ƙarin bayani don ita bata ma san kan zancen ba, kuma bata da masaniyar komi akai, Hansai ta yi dariya ta ce
"Habibynki ne ya turowa wani saƙon ya baiwa Baban yaron nan ya kawo muna ya ce in ji ki abamu mu abokanki"
Dije ta ji wata ƙwallah ta sauko mata cike da jin ƙara ƙaunar mijin nata, saboda ita ko kaɗan bai sanar da ita anyi hakan ba sai yanzu da ta ji a bakunansu, Mune ta sauke ajiyar zuciya ta ce
"Dole ki yi kuka don farin ciki ya yi a rayuwa, ALLAH ya ƙara buɗe maku hanyoyin samu ta ko'ina ko don mu na kusa da ku mu amfana"
Gaba ɗaya aka ce "Ameen"
Dije ta share hawayenta tana dariya ta ce "Mune naga yanzu kin rage surutu mi ye sirrin halan?"
Mune ta yi dariya ta ce
"Hmmmmmmmm ai ke dai in ana SALLAH ba'a magana, don kuwa akan halin har sakina ma Ummaru ya yi na dawo gida, saboda wani faɗa da na haɗa tsakanin matan yayan Ummaru, duk da a zahiri Ni iya gaskiyata ce na faɗi, amman duk wanda ya ji zai ɗauka cewa munafucci ne"
Lanti tana dariya ta ce
"To da gaskiya ta bayyana ai ALLAH ya wankeki ko? Kuma ki godewa ALLAH tunda har hakan ya zamo sanadin shiriyarki kika daina yawan faɗi ba'a tambayeki ba"
Dije ta kalli Jummala ta ce "me ya faru halan"
Ladiyo ta fashe da dariya ta ce "ki tambayi ƴar gidan taki mana sai ta fi iya bada labarin yanda ake so"
Mune ta cire taguminta ta ce "Matan yayan Ummaru ne suke ta faɗan kishi kullum a tsakaninsu, shine ranar na ji ɗaya tana faɗawa wata abokiyarta cewa zata sakawa abokiyar zaman shinkafar ɓera a abinci ta mutu, to shine Ni kuma na ji tsoro na je na sanarwa wadda ake so akashen, aiko ta sanarwa da mijinsu sai ko ga shi wadda ta ci alwashin ta kawo mata abinci ta ce bazata ci ita sai ta ci ta ƙi ci, daman an shirya hakan mijin ma ya kafe akan dole sai taci abincin ta ƙi ci, rigima ta rikice gida ya cika da mutane ƙarshe dai abu har gaban Maigari, aka baiwa kyanwa ta ci bata yi komi ba itama aka tilastata dole sai da ta ci, abun mamaki ba abunda ta yi shine aka fara kuka ta ce daman na ce sai na ƙalla mata sharri, nan mutane suka yi ta tsine mani ana cewa da ni daman cen Ni Munafuka ce, gashi yanzu zan haɗa rigima don kawai na tsani ɗayar, ke a taƙaice dai akan hakan Ummaru ya sakeni na koma gida sai daga baya da gaskiya ta fito aka gano makirci ne ta ƙulla ashe ta ji lokacin da nike faɗawa waccen ɗin, shine ta liƙaman sharri sai cikin ikon ALLAH bayan bana gidan faɗa ya haɗasu ta ɗauko taɓarya ta ce sai ta kashe kishiyar, da komi ya lafa aka gano gaskiya don ta yi iƙirari da bakinta akan cewa itace ta faɗa na ji a lokacin, shine fa ya dawo da ni gidanshi bayan an ja kunnena da faɗi ba'a tambayeka ba, to tun daga haka na kame bakina ba ruwana da faɗin abunda bai shafeni ba, kinji mafarin shiriyata, yanzu ko a gabana aka yi abu WALLAhi ba abunda ya dameni bale in fad'a"
Dije tana dariya ta ce "Alhmdllh ƙawata baki dadi wallahi yanzu ki ce ko a gabanki mu yi kashinmu ba zaki faɗa ba? "
Mune tana dariya ta ce "tabbas Ni ce ma zan sakayaku in yi maku labule don kar a ganku"
Gaba ɗaya aka saka dariya, haka suka yi ta tuno baya suna mayar da zance suna dariya, sun ɗauki lokaci sunata firarsu har dare ya raba sannan suka je suka kwanta.
Tunda sassafe suka yi sallama da kowa suka kama hanyar zuwa inda suka fito, da nufin sati yana zagayowa itama zata bi su ta je wankan gida a garinsu .
Haka ko aka yi Satin yana zuwa Fiddo da Zee da wata dattijuwaar da zata dinga taimakonta suka rakata zuwa garinsu ta jirgin sama da zai rage masu hanya zuwa sannan su ci gaba da motar, saboda kawai Yaron Safwan da ko ƙuda baya son su hau kanshi bale wahalar doguwar tafiya irin wannan.
Ko da Jirgin ya saukesu motar tana jiransu saboda tuni ta taso sannan su daga baya suka biyo hanya, kasancewar an samu ci gaba sosai a babban birninsu Dijen har cikin ƙauyensu, shi yasa basu sha wata wahala ba suka isa ƙauyen ƙiriu garinsu Dijen Baffah.
Mamaki bai kashe Dijen ba har sai da suka isa ƙofar gidan nasu taga kamar ma ba nan ne ba, don kuwa gida ne na alfarma Safwan ya ƙyanƙyara masu saboda kawai ya basu tukuicin faranta masan da ƴarsu take yi a kullum, ga kuma hasken solar ta ko'ina tun daga ƙofar gidan har cikin gidan fes yake masha ALLAH tare da sabon fentiin da ya ƙara fito da kyawon gidan.
Baki sake Dije take kallon gidan don ko kula da masu yi mata sannu da zuwa bata yi ba har suka isa cikin gidan ita da su Zee, Baki bud'e ta ƙura wa inna ido cikin shiga mai kyau ta buɗe wata doguwar freezer tana fito da wasu gorunan ruwa tana saka wasu, bakinta washe ta ke faɗin
"Sannunku da zuwa mutanen Yola sannu da zuwa"
Fiddo kanta mamaki abun ya bata saboda tasan yanda gidan ya ke acen baya, Zee kam wasar bakinta kawai ta ke yi har suka shiga falon Inna da ya ƙawatu da kujeru irin na ƴan gayu, Suka zazzauna Dije kam ƙurya ta shige saboda kukan da ya zo mata kuma ba zata iya danneshi ba, haka ma bata son ta yi shi a gaban Zee ta fahimci wani abu.
Inna ta fara jera masu abinci kala kala da ruwa da lemuka tana faɗin "ku sha ruwa kun kwaso hanya kam"
Fiddo ta karɓi Sayyid hannun Zee ta ce
"Inna ba zan baki yarona ba tunda har baki yi murna da zuwanshi ba"
Inna ta rufe Baki tana dariya ta ce "ku yi ta kaya Ni mai Malam me zan yi da wannan mijin cikin zane komai sai anyi masa?"
ZEE ta ɗauki ruwa tana tsiyayawa a kofi tace "ai dai inna shi sabon miji daban yake tsoho, idan kuma kika bari ya yi fushi ya ce ya fasa kuma shikenan sai mu nemo masa wasu matan"
Shigowar Hansai cikin tsantsar farin ciki yasa Inna Bata Sami damar mayar masu da amsa ba, Hansai ta karɓe yaron tana ihun faɗin
"Wayyo daɗi ɗanmu ya zama ɗan turawa Inna duba ki gani"
Inna ta ƙarɓeshi da bisimillah tana faɗin
"Waɗannan uwayen dai akwai kuri, to ALLAH yasa kafin ku haifu wasu sun rigaku haifuwar"
Ta ƙare maganar tare da zaunawa tana gyara masa hannun rigarshi ta kayan sanyin da ke jikinshi ya sauko ƙasa ya rufe tafinshi, Zee tana dariya ta ce
"Mu dai na mu muka sani Inna don zamu iya bugun ƙirji mu ce namu ya fi na kowa"
Inna tana dariya ta ɗagashi sama tana yin miƙa yana wani botsarewa alamun ya ji daɗin hakan, Inna ta kalli Fiddo ta ce
"Ku ne da yaron amman baku iya renon ba, to ku biya kawai a tayaku renonshi kawai"
Dattijuwaar da suka zo da ita tana dariya ta ce "Mutum da Matarshi har sai an biya? To a biyosu bashi idan ya girma sai ya biya da kanshi"
Sai ga sallamar Baffah ya shigo Dije da ke ƙuryar ɗaki tana kuka Hansai na lallashinta Muryar Baffah ta sa ta fito da saurinta ta taryeshi cike da jin daɗin ganinshi ta durƙusa tana gayar da shi, cike tsantsan farin ciki ya ke amsawa sannan ya tsaya bakin ƙofar falon ya gaisa da su Zee, sannan ya yi masu sannu da zuwa tare da tambayar mutanen gida, bayan sun ƙare gaisawar ne ya yi ɗakinshi Dije ta biyoshi zuciyarta cike tsantsan farin cikin ganin yanda yayi ƙiba hankalinshi a kwance, ta zauna tana wasa da yan yatsunta suka sake gaisawa a tsanake sannan ya kalleta yana ƴar dariya ya ce
"Wa ya taɓa man Dijeta daga zuwanta?"
Dije ta share hawayenta tana dariya ta ce "naga gida ya yi kyau Baffah ashe haka ka gyara gidan?"
Yana dariyarsu ta manya ya ce "na gyara ko aka gyara man? ki yi haƙuri shi ya ce kada a sanar da ke sai in kin zo kin gani da idonki, don yanzu haka bamu fi wata uku da tarewa ba, saboda cikin ƴan watanni aka yi komi aka gama, mutane da yawa sunyi mamakin yanda aka kammala ginin cikin lokaci kaɗan, Alhmdllh kam mun godewa ALLAH da ya had'amu da mutanen kirki masu mutunci da sanin Yakamata, da ace duk sauran mutane haka su ke da ina tabbatar maki mabuƙata ba zasu taɓa yin kuka ba, to matsalar da aka samu irinsu ƙaɗan ne a cikin al'umma"
Dije ta share hawayenta ta ce "Ni ban ma san mi zan ce ba Baffah saboda tun da naga wannan gyaran nasab aikinshi ne, haka fa ya aikowa da su Ladiyo kuɗi Ni banma sani ba ya ce in jini su ja jari"
Baffah ya yi murmushi mai cike da jin daɗi ya ce "daman ita addu'ar a kullum mutum ya yi bata faɗuwa ƙasa banza, don haka muka roƙa kuma ga shi ALLAH ya cika muna gurunmu fiye da yanda muka yi tsammani, da ina da iko da na tara mutane na sanar da su cewa kada su gaji da yiwa ƴaƴansu addu'a, duk halin da suke a kullum su ci gaba da yi masu addu'ar shiriya saɓanin faɗin aibinsu a bakinsu, saboda addu'ar iyaye bata da shamaki wajen Ubangiji, da sunyi take tafiya sai dai ayi jinkiri wajen ganin sakamakon addu'ar, yanzu ga ki kamar ba ke ba kin natsu kin ajiye shirme da tsokana, kin ajiye jan faɗa da abun maganar da kike ta janyo muna a cen baya, ga shi Sakamakon haƙurin da muka yi ALLAH ya mayar muna da alkhairin da bamu zato ba bale tsammani"
Dije ta ce "hakane Baffah ALLAH ya ƙara shirya maka Ni"
Ameenn 🙏🏻
Akafta🤪
D/AUTA Ce✍🏻
*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*
*NA HADIZA D/AUTA*
*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*
*ALHAMDULILLAH!!!! ALHMDLLH!!! ALHMDLLH!! GIDAN AURE shine sunan book ɗina da zanyi a gaba, wadda take buƙata zata biya kuɗinta 300 kacal ta hanyar transfer ta wannan account ɗin HADIZA D AUTA 1230094555 access Bank, idan kuma kati ne zaki turo aritel ko mtn na ɗari uku to za'a turo ta wannan numbar 09032685442*
*Ƴargata Maman Sultan Ubangiji ya baki lafiya yasa kaffara, Mrs Naseer ina miƙo gaisuwata zuwa gareki akan namijin ƙoƙarinki ga book ɗina, my Ambash ALLAH ya saukeki lafiya mu zo mu ci rangyem, Asma'u Umar ki yi haƙuri na goge laifina🤗*
*Lamba 72 last page*
🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚
Baffah yana murmushin jin daɗi ya ce "Ameen Dijengalata amman fa ko haka aka tsaya Alhamdulillahi, don ba abunda za mu ce wa ALLAH sai godiya ALLAH ya sawa aurenmki albarka ya baku zaman lafiya ke da Mijinki da abokiyar zamanki duka, kuma ya baki ƴaƴa nagari masu albarka waɗanda zasu yi maki fiye da abunda kinka yi muna na alkhairi"
Dije sai "Ameen Ameen" take faɗi zuciyarta cike da jin daɗin samun iyaye nagari, sai da suka ɗan taɓa fira sannan ta dawo falon Inna suna cin abincin ana ci gaba da fira cikin raha da barkwanci.
Kwanansu Zee ɗaya direba ya kwashesu suka suka koma suka bar su Inna da kewarsu tare da jinjina lamarin Ubangiji, ganin yanda dukansu daga Zee har ita Fiddon sun saki jiki da su kamar cewa daman cen ƴan'uwan juna ne.
Bayan su Inna sun dawo daga rakiyarsu ne Hansai ta goye Sayyid ta yi ɓangarenta, Dije ta faɗa kujera tace
"Wash ALLAHna WALLAHI Inna gaba ɗaya jikina ciyo yake yi"
Inna ta zauna tana ƴar dariya ta ce "sai kin yi haƙuri kam don yanzu jikinki yake haɗewa daga ɗaukar ciki da haifuwar da kika yi, wani zubin ma har zazzaɓi wasu su ke yi a wannan lokacin"
Dije ta dafe goshinta ta ce "ai kam dai nima ina jin abinda nike ji a jikina"
Inna ta kalleta da kyau sannan ta ce
"Naji daɗin yanda yarinyar nan ta sauko kuka fahimci juna ga shi yanzu zamanku gwanin burgewa"
Dije ta yunƙura ta ta shi zaune sannan ta kalli Inna ta ce "kin dai gani Inna ga shi yanzu kamar ba'a yi ba ashe da kirkinta sharrin sheɗan ne da kuma mugun kishin Abban Sayyid da take yi"
Inna ta sauke ajiyar zuciya ta ce "duk macen duniya dole zata yi kishin mijinta, ke ba mijinta kawai ba duk abunda kake so a rayuwa dole ka yi kishin ganin wani ya raɓeshi, sai dai na wani ya fi wani don kowa da kalar dauriyarshi, shiyasa kika ji na ce da ke duk runtsi ki sa ya dawo da ita a matsayin matarshi, saboda ko da ta fita dole ne ya auri wata, kuma ita zata iya shigowa gidan da shirinta ƙarshe ma ta janye maki Mijin ya koma gareta a barki da cizon yatsa, amman in ita ce sanadiyyar wannan abun da ta aikata zai dakushe mata karsashi akan ko ma aikata wani mummunan abu saboda ganin igiya ɗaya ce ta rage a tsakaninsu, saɓanin wacce zai auro ba ita, don ba lalle bane ba ace ku fahimci juna, bale kuma ta barki ki ji daɗin zama gidan aurenki ko zama da Mijinki lafiya, don wata mace sharrinta ko sheɗan ya sarawa bala'in da ke tattare da ita, amman yanzu kin ga komi ya zama tarihi kuna zaman lafiyarku Masha Allah, wanda hakan da kuke shi zai ƙara farantawa mijinku rai ya ji daɗin kyautata maku"
Dije ta cire tagumin da ta yi ta ce "Lalle Inna na yarda da aka ce abunda babba ya hango yaro ko da ya hau sama bazai iya hangowa, kuma naji daɗin biyayyar da na yi wajen sakashi dawo da ita, yanzu ga shi abun Ni ma ya zamo mani alkhairi don baki ga yanda ta ke son Sayyid ba, bata bari ya zauna hannuna matukar ba abincinshi zai sha ba, kuma ina bashi take sake karɓeshi su tafi, shi kanshi Abbanshi sanadin wannan halin kirkin da take yi ne yasa ya sake mata sosai suna ɗasawa, sai dai wani lokacin ina jin ba daɗi idan naga yana kulata Inna, Amman idan na tuno da cewa itama fa Matarshi ce kamar Ni sai in baiwa zuciyata haƙuri don bana son ta fahimci ina jin zafinta"
Inna ta yi shiru sannan ta ce "hakan da kike yi ya yi kuma shine abunda ya dace ki yi, don yanda kike ji haka itama take ji amman ta ke haƙura saboda neman zaman lafiyarku, ALLAH ya baku haƙurin zama da junanku itama kuma ya bata nata rabo"
Dije ƙirjinta ya buga amman ta daure ta ce "Ameen inna Bari in je in kwanta Wallahi wani bacci nike ji a idona"
Inna ta bita da kallo cike da jin daɗin ganin yanda hankali ya shige Dijenta, sannan ta ce
"Duk baccin da ki ke son yi ai wannan baturen baya barinki sai dai in bai rikice ba"
Daga cen cikin ɗakin Dije ta ce "WALLAhi sai in tafiyata gidan Gambo in sha baccina in barku da shi ku yi ta fama"
Inna tana dariya ta ce
"Ai duk inda zaki je ki ɓoye sai an kai maki shi acen tunda mu bamu da abunda zamu ba shi"
Dije ta yi saurin faɗin
"Gaskiya Inna uwaye suna shan wahalar renon ƴaƴa a rayuwa"
Inna ta fashe da dariya ta ce
"Kamar yanda aka sha taki ba ai duk uwar da kika gani da ɗanta to ita kaɗai tasan wahalar da ta sha da abunta lokacin da yana ƙarami har girmanshi, ALLAH dai ya jiƙan iyayenmu da rahamomi Wallahi"
Dije ta ce "Ameen" sannan ta yi kwanciyarta aranta tana jinjina irin yanda iyaye mata suke shan wahalar reno musamman farkon haifuwa, wanda ita sai yanzu ta gano cewa ashe ba ƙaramin haƙuri Inna ta yi da ita ba, cikin zuciyarta sai addu'a take zubawa Innar saboda tuno irin abun maganar da ta yi ta janyo masu a baya, tana cikin tunanin ne wani ta yi dariya wani ta ɓata fuska har bacci ya yi awon gaba da ita.
****
Rayuwa mai daɗi Dije ta yi a gidansu saboda komi yi mata ake yi aikinta bacci da cin abinci sai kuma baiwa Sayyid nono, sannan da baiwa Malaminta dama wajen ƙara macewa kanta, don kuwa suna maƙale a waya ko wane lokaci yana nuna mata irin kewarta da ya yi, tare da sanar da ita da ta cika wata ɗaya a garin zai zo ya kwashesu su koma, cikin dubara take ta hilatarshi har ya bar zancen don bata son ya gano bata son komawar a lokacin, kada ya ga kamar ita bata yi kewarshi ba kamar yanda kullum yake sanar da ita irin damuwar da yake ciki, don Zee ta so binshi acen Abujar ya ce ta jira anan Yolar zai dinga zuwa akai akai wurinta, dole ta haƙura amman ba don ranta ya so ba sai don samun zaman lafiyar da ko kaɗan bata son abunda zai janyo wata fitina a tsakaninsu.
Satin Dije Uku a garin ta yi ɓul ɓul daga ita har yaronta gwani sha'awa saboda kulawar da suke samu wurin Inna da dattijuwar matar, a gefe ɗaya kuma Gambo da bata gajiya da dafa mata abubuwa tana shanyewa, don wani zubin acen ma take kwanciyarta daga ita yaronta da dattijuwar, ga Yan garin na su kowa sai nan nan ake yi da ita da kuma yaronta, don ma Gambo bata son ana yawan fita da shi don ƙa'ida ne kullum sai ta tofeshi da addu'o'in tsari, sannan ta ce dole itama Dijen sai ta tosheshi da addu'o'in saboda kariya daga sharrin mutum ko aljan da wasu masu kambun baki, saboda farin yaron da yanda yake kyakkyawa ga shi ɓul ɓul dole ne mutane su yi shaawarshi, sannan uwa uba ga shi fes fes kullum cikin shiga ta alfarma kuma irinta wayayyun ƴan birni.
****
Wasa wasa Dijen Baffah sai da ta yi wata biyu a garinsu sannan Angonta ya garzayo ya kwashi Matarshi da yaronshi suka koma Yola, suka bar su Inna da Baffah da mutanen garin da kewar Dijen da ɗan baturen yaronta mai kama da indiyawa samfurin larabawa kalar yan Ethiopia.
Hajiya Mama ba ƙaramin daɗi ta ji ba da ta ga yanda yaron da mamarshi suka yi sharr abunsu, cike da tsananin farin ciki ta karɓe shi tana ta yi masa wasa yana wasar baki, Fiddo ta karɓeshi tana faɗin
"Coming to your mama my beautiful boy"
Hajiya Mama ta kalleta tana dariya ta ce "in dai ɗanku ne ga shi nan don ma na yi maku kara na ɗauka?"
Fiddo tana dariya ta ce "WALLAhi Hajiyarmu son yaron nan Nike yi, don ALLAH ki ce da Yayanmu su tafi da Ni Abuja don bana son a rabani da shi ALLAH"
Hajiyar tana dariya ta ce "ki jira idan kunyi jarabawar ƙarshe sai ki tattara inaki inaki ki koma cen duka tunda ke baki fatar ki je naki gidan mijin sai taya wasu zaman aure"
Dije dai dariya kawai ta ke yi cikin dariyar ta ce "ai Insha ALLAHu acen ma zamu yi mata aure don bama fatar a raba uwa da ɗanta"
Safwan da ke shigowa ɗakin ya ce "ba inda zata je don tana kammala karatunta zamu auradda ita"
Fiddo ta zumɓuro baki ta ce "to ai Ni bani da miji"
Dije ta dafe baki ta ce "Mukhtar ɗin fa? Ko an ɓata?"
Ta miƙe tana dariya ta ce "yarona zo mu je tunda yau haɗe man kai ake yi a gidan"
Ta fice suka bita da kallo Safwan ya ƙaraso ya zauna suna ci gaba da firarsu kafin lokacin tafiyarsu ya yi suka tafi duka har Fiddon cen gidan nashi, inda Surayya da wasu yan'uwa suke acen suna tsumayin zuwansu.
Aiko shigarsu gidan mutane suka zo tarbarsu cikin farin ciki ana yi mata Barka da dawowa, Zee ta karɓe yaron tana ta juyi da shi Safwan ya riƙo hannunta ya yi mata raɗa ta yi saurin rufe ido, Dije ta bisu da kallo cikin gefen ido sannan ta shige sashenta tare da mutane tana dariyar yaƙe, Zee tayi sashenta da Sayyid tana ta murnar dawowarshi.
Dije kam tana shiga ta faɗa toilet tana share ƙwallar kishin da ya turnuƙota, sannan ta watsa ruwa ta ɗauro arwallah, bayan ta fito ne Surry ta ce "haba Hajiya daga zuwa ba wani jira sai shige abunki ki barmu a falo muna jiranki?"
Dije ta washe baki cikin ƙarfin hali ta ce "Tom bari in shirya in zo inji me da me aka tanadarwa baƙuwar?"
Surry ta riƙo hannunta ta ce "ki daina ɓoyo nasan me ke damunki to Aunty zee dai ciki. E da ita shiyasa kika ga yayanmu ya hanata wannan tsallen da take yi don kada ta janyo muna aiki, saboda haka plss a yafewa yayanmu don ALLAH, kada a lalace masa wannan dare da yake ta tsimayin zuwanshi"
Dije ta rufe baki cike da jin kunyar ganotan da surry ta yi ta ce
"Bafa wani abu Ni daman cen ban ji komi ba Aunty Surrynmu"
Surry ta fice tana dariya tace "ki dai zo ga delicious cen mun haɗa ma ku yana jiranku ke da Big bros"
Dije ta bita da kallo tana dariya sannan ta fara shiryawa tana jin daɗin cikin da aka ce ZEE tana da itama, don ƙaunar Sayyid da take yi yasa ko kaɗan bata kishin abunda zata haifo itama, Shiyasa ta yi mata fatan alkhairi a zucinta.
Bayan ta yi sallah ne tashirya cikin wani voil da yaji aiki tun daga sama har ƙasa sannan fara fesa turare sai ga Safwan ɗin ya shigo ɗakin, yana hangota ya ƙaraso ta bayanta ya rungumota a jikinshi, sannan ya sunsuno dogon wuyanta tare da sauke masa wani wawan kiss, ba shiri ta zabura tare da ɗauke wuta na wuccin gadi, sannan ta kai kallonta jikin madubin tana ƙare masa kallo cikin wani sihirtaccen kallon da shi kanshi baisan ta iya shi ba, ba shiri ya ji yar ya jikinshi tsikarshi ta miƙe, ya yi saurin kwantowa bayanta yana sauke hannunshi akan dukiyar fulaninta da suke cike fam, ta yi saurin runtse ido tace
"Da zafi fa"
Ya juyota a zafafe ya dinga tsotse mata baki tamkar zai cire mata shi, da kyar ta samu ya ta ƙwaci leɓenta sannan ta ɗago tana kallonshi ido cikin ido da wasu jajayen idanuwanshi da suka rine a lokaci daya, sannan ta ce
"Mu je mu ci abinci yana jiranmu"
Tana gama faɗar hakan ta zille ta fice ta bar masa ɗakin ya bi bayanta da kallo tare da dafe jarumarshi da ta miƙe tana kallon gabanta, ya nufi toilet minti biyar a tsakani sannan ya fito ya fice cikin wata kasala da ta diro masa.
Har suka ci abincin suka ƙare ba wata walwala a fuskarshi, yana ƙarewa ya shige ɗakinshi na sashen Zee sai dare sosai ya dawo sashen Dijen, inda ko da ya taradda ita har ta yi bacci ita da yaronta, cikin dabara ya ɗauke yaron ya kaishi cikin gadonshi ya ajiye sannan ya dawo kan gadon ya janyota jikinshi sai rawa yake yi,
Cikin bacci ta jiyo saƙonshi yana sauka ta ko'ina cikin jikinta, dole ta wartsake ta karɓi mijinta hannu bibbiyu suka dinga farantawa juna cikin farin ciki da ɗokin juna, ALLAH ya taimakesu yaron ya basu haɗin kai domin shi ma kanshi a gajiya yake shiyasa yake ta baccinshi su kuma suna ta shan soyayyarsu kan kari, don Safwan ya susuce akanta sosai sai zuba santin daɗi yake yi yana nishi saboda irin bala'in daɗin da yake ji yana ratsa koina na jikinshi, sun daɗe suna abu ɗaya har sai da Sayyid ya falka sannan suka haƙura ba don sun so ba.
Da safe ma ba ƙaramin rawar jiki ya yi akanta ba don ma yana kawaici baya don Zee ta ganoshi, gudun janyo wata sabuwar fitinar yasa kwanansu biyu a Yola ya tattara Matarshi da ɗan shi suka koma Abuja, inda suka ci gaba da jiyar da junansu daɗi tare da tarairayar juna kamar yanzu ne suka yi sabon auren, a gefe ɗaya kuma suna renon yaronsu da ko kaɗan basu son ganin kukanshi don inda hali ma ƙuda basa son ya hau kanshi.
Watan Sayyid huɗu Dije ta fara zuwa school saboda ƙulafucinta akan makarantar, dole aka nemo mata wadda zata dinga kula da Sayyid saboda hidimar karatun ba wasa ba.
*****
Bayan shekara biyar Dijen Baffah ta yi karatunta ta ƙare har ta sami aiki a wata babbar Asibitin da ke Abuja, sannan ALLAH ya sake bata wata haifuwar inda ta sami ƴa mace aka saka mata sunan Hajiya Mama ta ci sunan Sayyada, Zee ma ta yarinyarta ɗaya mai suna Ummusalmah itama tana aikinta acen Yolar cikin amincin ALLAH, Fiddo ma anyi mata aure har ya haifi ɗanta masha ALLAH, Surayya ma yaranta uku Husnah ma ta yi aure da ƴarta mai sunan Nasiba.
Zamansu lafiya har lokacin saboda akwai fahimtar juna sosai a tsakaninsu, shi ma kanshi Uban gayyar ya zama ƙaton Alhaji don kuwa daga shi har Matanshi duka sun sauke farali, Inna da Baffah ma da Gambo da Maigari duka sun je, a gefe ɗaya kuma Dije daga lokacin da ta fara karbar salary ne ta fara asusun gina makarantar boko da islamiya garin na su, ga alkhairin da take yi wa yan garin da guminta bayan na Maigidanta, izuwa lokacin su Ladiyo kansu sun zama wata tsiya a sanadin Ƙawarsu Dijen Baffah, sai dai kwatsam ALLAH ya aikowa Gambo rasuwa bayan gajeruwar jinyar da ta sha, Dije ta yi kukan rashin Gambo saboda wani jigo ce ta rayuwarta, akan hakane ta yi ƙudurin gina masallaci a ƙauyen hadiyya zuwa gareta, ALLAH ya taimaketa Alhaji Safwan ya dafa mata ta cika gurinta, mutanen garin sai sambarka suke yi tare da godiya ga Ubangiji da ya sanya Dijen da suke aibatawa a baya itace yanzu ta zamo silar jin daɗinsu, Usmanu ma ya zama babban ɗan kasuwa yana samu daidai gwargwado don ya riki kanshi da Iyayenshi har ma wasu suna jin dadi ta sanadinshi.
Dije ma Cikin ƙashin kanta da shekaru suka ja ta biyawa Usmanu da Hansai Hajji, bayan sun dawo ne wata shekara suka yi haɗaka da Malaminta suka biyawa ƙawayen Dijen, Ladiyo Jummala Lanti da Mune tare suka je da su ma ɗin kansu suka sake komawa tare da su.
Wata shekara ma da kanta ta biyawa uwargidan Maigarin hajjin ta je don har abada bata mance karayar da ta janyo mata ta yi a lokacin gudun kura da suka yi.
Hajiya Dije da ALHAJI Safwan a ƙauyensu Dijen mutane sai turuwar zuwa gayar da su ake yi a ƙofar gidan Maigarin da suka fara zuwa domin su gayar da shi, sai ga wasu yan bautar ƙasa an turo tare da doguwar takardar da aka ce akawowa Maigarin, Maigarin ya karɓa yana kallon Dijen da ke dariya cikin ƙasaita saboda tuno abunda ya faru a baya, Dije ta karɓa ta dinga karantawa cikin harshen turancinta irin na ƴan America, bayan ta kare ta fassara masu duk abunda takardar ta ƙunsa, gaba ɗaya wurin manya da yara samari da ƴanmata aka dinga yi mata tafi ana yi mata kirari irin na mutuntawa da zayyano irin halayen kirkinta ita da Mijinta, zuciyarta cike fess da farin ciki ta tashi ta fara nuna jin daɗinta a fili sannan ta yi kira sosai ga mutanen garin akan su jajirce su dinga saka ƴaƴansu a makarantar boko da islamiya, saboda su ma su waye su zamo dai dai da kowa adaina yi masu kallon ƙauyawa, ta yi masu nuni da kanta da irin nasarar da ta samu duk a sanadin bokon wanda su kansu shaida ne ba sai an sanar da su ba, sannan ta yi kira ga iyaye sosai akan su dinga haƙuri da halayen ƴaƴansu musamman marasa ji, Baffah'nta ma ya tashi ya yi dogon jawabi akan alfanun yi wa ya'ya addu'a kuma kada a gaji da yi madu addu'a aduk wani rashin ji ko wani abu mara kyau da suka aikata, don ALLAH maji roƙon bawanshi ne kuma aduk lokacin da aka roƙa zai amsa sai dai jinkirin sakamakon a wani lokaci, mutane da dama sunyi alwashin jajircewa sosai akan karatun ƴaƴansu, kuma sunyi godiya da abun alkhairin Dije da Mijinta garesu, nan suka fito da kuɗi suka rarraba wa mutane duk wanda Allah ya sa da rabonshi ya samu, don ko yan bautar ƙasar ma sai da Suka wankesu da alkharinsu da suka saba.
Tammat bi hamdullah anan na kawo karshen littafin na *Dije ƙarangiya* masu comments masu masu yiman addu'a da masu yiman sharing book din a groups Kuma na gode sosai sai mun hadu a littafin na kuɗi mai suna *GIDAN AURE* littafi ne wanda ya kunshi rigingumun gidajen aurenmu a yau da kuma ma wasu abubuwa da baki bazai iya faɗa ba, masoyana masu son bin books ɗina a Koda yaushe idan kuna buƙata zaku sameni ta wannan numbar sai mu yi magana 09032685442 sai kuma na Free da zanyi don ku masoyana shi ma mai suna *SHAGALLIYA* wanda shi ma ɗin cike yake da barkwanci da nishaɗi ba kaɗan ba kusan ince fiye ma da Dijen Ƙarangiya, don haka ku ci gaba da bibiyata Ni *HADIZA IBRAHIM D/AUTA wadda wasu suka fi sani da PRINCESS DIJA* zaku iya nemana ta wattpad kamar haka *Princessdija246*
INA SONKU SOSAI MASOYANA ADUK INDA KUKE KUMA A DUK INDA KUKA KASANCE🤝🏻