Saida ya gama fad'in abin da ya faru kafin ya d'ora da "Wallahi Mama Khadija ta bani mamaki, wai ni Khadija zata kalla ta dinga fad'awa duk abin da ya zo bakin ta, saboda kawai na mata kishiya saita raina ni, ko kuma dan na mata magana akan abin da tayi bata kyauta bane, wannan abu ya b'ata min rai sosai, shine dalilin da ya sa nacr ta zo gida saina neme ta, banyi haka dan cin mutumcin ta ko cin zarafinku ba, sai dai nasan dole anan akwai wanda za su fad'a mata kuma ta saurare su, dan naga yanzu kishi ya rufe mata ido gaba d'aya."
Malam ne yace "Kai dallah rufewa mutane baki, koma menene ai sai kayi hak'uri, duniyar nan uban waye baisan halin mace ba akan kishi, ko kai kana ganin kamar uwarka ba ta da kishin ne, ita kan ta mahaifiyar ta ta da ka ke magana akai ai tasan zafin shi, kenan sai ka yi hak'uri ka d'auke kan ka dukansu na d'an lokaci ne za su yi, in banda rashin hankali irin na ka da can farko ta ma ka haka kafin zuwan amaryar?"
Murmushi Mama ta yi tace "Alhaji ka k'yale shi haka, to idan yace ya saka mu su ido suyi yanda su ka dama suna fakewa bayan kishi, ai kuwa kullum da tsiyar da za su b'ullu da ita a gidan, hakan zaisa ba za'a zauna lafiya ba, ni banga laifin shi ba dan hakan shine daidai, ka na ji ko." Mama ta fad'a ta na kallon shi cike da kulawa, kallonta ya yi take kuma ya sunkuyar da kan shi k'asa, d'orawa ta yi da "Ka yi hak'uri dan Allah akan abin da ya faru, insha Allahu zan ja mata kunne hakan ba zai sake faruwa ba, abinka ne da d'an yau ka haife shi baka haifi halinshi ba, babu irin tausar zuciyar da ban mata ba, amma ba ta ji ba ko kad'an, amma ka yi hak'uri kaji, insha Allah za ta kiyaye a gaba."
Kallon malam ta yi tace "Bara na kira mu ku ita sai ku tafi ko." Cike da dattako malam yace "Shikenan Hajia mun gode sosai da karamci, Allah ya bar zumunci."
Mama na wucewa d'akin Khadija dake ta cika ta na batsewa Usman ya d'ago kai a hankali ya kalli su Ashir da duk su ka hakimce su na kallon shi, d'auke kan shi ya yi dan gani yake kamar za su rufe shi da duka, dan ko basu fad'a ba kasan ba haka su ka so ba, musamman Naseer da Habeeb da bakin su ke ta motsi😂, a d'aki kam tuburewa Khadija ta yi wai babu in da za ta je, saida Mama ta fara nuna b'acin ran ta kad'ai ta fito ta na kumburo baki, wajen yan uwan ta ta tsaya ta ja birki ta na kallon su, Naseer ne yace "Ki yi hak'uri kinji auta, Hajia tace ba ta yarda mu ce komai ba."
Kallon Usman ta yi da shima yake kallon ta, har ga Allah kafin ta fito ya ji ya na son ya koma tare da matar shi, amma ya na ganin ta yanzu sai ya ji kamar yace ta yi zamanta ko kuma ya rufe ta da duka, haka kawai ya ji ranshi ya b'ace ko da ya ganta, amma sai ya dake ya mayar da hankalin shi kan Mama da tace "Maza ki bawa mijin ki hak'uri yanzun nan, sannan ki mi shi alk'awarin hakan ba za ta sake faruwa ba, in kuma ki ka sake to fad'an ni da ke ne ba da shi ba."
Kamar za ta yi kuka ta kalli Mama tace "Mama, wai ni ce ma zan ba shi hak'uri? Har fa mari na ya yi mama, kuma dama duk na ji abin da ka fad'a ina d'aki." Ta fad'a ta na mayar da hankalinta kanshi, ci gaba ta yi da cewa "Bansan me ya sa za ku yi tunanin na lalata abincin yarinyar nan ba, domin Allah ku dube ni da kyau ku dubi Haseenah, ace na rasa ta yanda zanyi na yi maganinta akan kishi saita hanyar zuba gishiri a abincin ta, haba dai kuma, wannan ai abune da hankali ba zai d'auka ba, kenan ma ta gagare ni?"
"Khadija." Mama ta fad'a cikin tsawa, shiru ta yi ta kalli Mama, cikin b'acin rai tace "Rashin kunyar da ya fad'a mana ki na masa ita ce za ki nuna mana sanfurin da ki ke ma sa?"
A hankali ta durk'usa duka gwiwoyinta biyu tace "Ki yi hak'uri Mama."
"Ba ni za ki bawa hak'uri ba, mijin ki ne gashi nan."
Saida ta had'e hawayen ta kad'ai ta kalle shi tace "Ka yi hak'uri." Yanda ta turo baki ne ya sa Mama cewa "Anya kuwa Khadija ke ce? Ke ce Khadija auta ta da na sani."
Kallon maman ta tayi ta sake kallon Usman ta saisaita murya tace "Ka yi hak'uri Abban Bilal, insha Allah ba zan sake ba."
Da k'yar ya iya k'arfin halin k'ak'aro mata murmushi yace "Ba komai ai ya wuce, ni ma ki yi hak'uri abisa marin ki da na yi, kuskure ne da b'acin rai."
'Anzo wajen." Cewar Naseer, d'agowa ya yi daga jinginar da ya yi a bayan kujera yace "D'an uwa Usman dan Allah a dinga kiyayewa, shi duka a fuska ya na da had'ari sosai, mari kan iya jayo makanta, mari ya kan iya sanadin rasa ji, mari zai iya sakawa haure ya fita, mari kan saka kai ya yi ciwo, dama wasu matsaloli da dama, ka ga sai a dinga sanin me za ayi idan rai ya b'ace."
Yasan ba lallai Mama ta yi shiru ba, dan haka ya na fad'a ya tashi ya bar falon ya nufi b'angaren shi, da murmushi Usman ya bishi ya kalli sauran yace "In Allah ya yarda ma ba za ta sake faruwa ba, wannan ma tsautsayi ne."
"Allah ya kiyaye gaba." Cewar Ashir, haka suka tashi su ka koma gida, saida ya ajeta gida kafin ya wuce ya kai malam, Bilal ya yi farin cikin ganin mahaifiyar shi, Haseenah kam ba ta ji dad'i ba ko kad'an, sai dai tasan nan ba da jimawa ba za ta koma tunda yanzu sai yanda ta yi da Usman.
A matsayin kwanan Khadija ne yau ta shirya ta kuma je har d'akin shi kamar yanda ta saba, tabbas ya kwana d'akin, amma da kwanan shi da rashin kwanan duk d'aya, dan kuwa baya ya juya mata ko uhum ba ta ji daga bakin shi ba har ya yi bacci, amma ita ba ta yi baccin ba sai nafila da ta kwana ta na yi ta na kaiwa Allah kukanta, har asuba tana nan kafin ya tafi masallaci ita kuma tayi sallah, bayan ta kammala ta shiga madafa ta d'ora girki.
Usman kuma na dawowa daga masallaci d'akin Haseenah ya nufa su ka gaisa, daga nan ya fad'a mata gobe fa zai yi tafiyar nan ta shirya in tana zuwa, amma bayan tunani da tayi sai taga za'a zargeta idan suka tafi tare, dan haka ta marairaice tace "Um,um gaskiya ni na fasa tafiyar ma, ka ga kai kasuwancin ka ne zai kai ka, bai kamata muje tare ba kuma na hana ka sabgar gaban ka, kawai kaje Allah ya tsare mana kai, ranar da na haihu sai mu tafi tare da yaronmu mushak'ata."
Saida ya rumgume ta yace "Gaskiya ban ji dad'i ba, Haseenah ba zan iya farin ciki ba ki na nesa da ni, me ya sa ba za ki je ba? Zan iya yin wata d'aya fa ko sati uku ban dawo ba, ki na ganin zan iya rik'e kai na bayan na saba da ke a d'an lokacin nan."
Cike da gatsali tace "To ba ga aunty Khadija ba, ku je tare mana, ni kuma sai mu zauna abunmu ni da yarona Bilal, ko ya ka ce?"
Tunda ta ambaci sunan ya ji kamar ta jefe shi da mashi akan tsohon ciwon shi, b'ata rai ya yi yace "Ya ina magana da ke za ki kawo min maganar matar can? Gaskiya ba na so kar ki sake."
Saida ta shafi fuskar shi tace "To shikenan yi hak'uri ba zan sake ba."
"To yanzu fad'a min za ki je ne?" Ya fad'a ya na k'ara cukuikuyeta, ba alamar wasa tace "Gaskiya ba zan je ba, kawai ka tafi kai kad'ai."
"Shikenan, amma taya zan barki ki zauna tare da matar can? Na ga fa ba wani sakin jiki ki ke da ita ba."
Shiru ta yi ta na tunanin abinyi ita ma, da sauri yace "Ko na kira Hajia ta turo mi ki Aziza? Tunda kinga dama ita ce ke zuwa nan idan zanyi tafiya."
Wani murmushi ta yi da bai kai ciki ba tace "To shikenan ba damuwa, hakan ma ya yi ai."
Da haka ya fito ya shiga d'akin shi ya yi wanka ya shirya ya fito kan teburi, saida Haseenah ta fito kafin su ka fara cin abincin, tabbas daga yanda ya ke cin abincin za ka san ya masa dad'i, amma da zaran ya had'a ido da wacce ta dafa abincin saiya d'aure fuska, haka su ka gama ya tashi ya fita su ka bishi da addu'a, Khadija da ta bi bayan shi har wajen mota sannan ya juyo ya kalle ta yace "Ya dai malama ki ke bina haka?"
Murmushi ta yi tace "Abban Bilal hushi ka ke dani har yanzu akan abin da ya faru?"
Wani d'auke kai ya yi yace "Mtsss, ba komai kawai, kawai dai ki na ba ni mamaki ne."
A hankali ta janyo hannun shi ta na shafawa, in da shi kuma ya ke jin kamar hannun wuta ne da ita, cikin taushin muryar da tasan ta na tasiri akan mijin ta ta fara magana "Dan Allah ka yi hak'uri ka yafe min, insha Allah ba zan sake b'ata ma ka rai ba, ka ji? Ka yafe min, kasan hankali na ba ya kwanciya idan ina ganin ka haka."
Saida ya raba hannunshi da na ta yace "Shikenan ba komai, Allah ya sa haka."
Juyawa ya yi zai shiga mota tace "Shikenan kuma ba komai za ka tafi."
"Kamar me fa?"
Cikin yanayin jan hankali tace "Ba rumgumewa, ba sumbata, abun ba armashi."
Kasak'e ya yi ya na kallon ta da tunanin abinyi, matsawa ta yi kusan shi ta shafo fuskar shi, a hankali ta kai bakin ta kan na shi ta zura harshenta cikin bakin shi, harshenshi ta kama tana wasa da shi in da ta kai d'aya hannun ta cikin rigar shi ta na murza k'irjin shi, d'aya hannun kuma shafar sumar kan shi take ta na yamutsata, tunda ya lumshe ido ya rasa kuzarinshi, hak'ik'a ya na son abin da take ma sa sosai d'in nan, amma ya na jin ba zai iya biye mata ba, amma da ya ke Khadija bala'i ce saida ta watsa mi shi duk wani lissafin shi da nutsuwa ya ma manta ina ne ya ke yanzun, me kuma zaiyi ko ya ke yi, saida ta ji jikinshi ya saki sosai sai wani gurnani da yake ya na k'ok'arin kai hannayen shi cikin rigar ta kawai ta raba kan ta da shi, wani arnan kallo ta masa da manyan idon ta a cikin gilashi kafin ta kashe mi shi ido d'aya, wata yar mik'a ta yi tare da fad'in "Ashhhh."
Bye bye ta mi shi ta juya da nufin komawa ciki, wata karairaya ta dinga yi wanda ya sa hankalin Usman k'ara tashi saboda yanda take juya jikinta, wata zabura ya yi saboda wani zirrrrr da ya ji tun daga k'asa har sama, fitowa ya yi daga motar ko rufewa baiyi ba ya bi bayan ta har da gudu ya na so ya kamo ta, ta na shiga falon ta ga Bilal zaune sai kawai ta wuce d'akin ta, Bilal na ganin baban shi ya bi bayan maman shi sai kawai ya mik'e ya fita, wajen mai gadi ya zauna su na hira ya na kallon hanya, Usman na shiga wani k'arfi ne ya zo mi shi cikin sauri ya ke son aika sak'on shi, haka dai al'amari ya yi nisa sosai suka gangara, tabbas tun bakin k'ofar za ka ji abubuwa kala kala masu rikatar da mutum, amma ya na k'arasa shiga ciki sai ya ji wani b'acin rai da rashin ma'ana da...abubuwan ma dayawa, da k'yar ya k'arasa abin da ya fara cikin d'an lokaci ya samu nutsuwa ya tashi ya yi wanka ya saka kayan shi, ko kallon ta baiyi ba ya wuce abin shi ya na jan tsaki ya na gunguni.
*A gurguje*
Bayan ya fita gida ya nufa in da ya aje mu su duk wani abun buk'ata, sannan ya fad'awa Hajia ta tura Aziza can ta taya Haseenah kwana, tunda yamma ko da Haseenah ta karb'i girki Usman ya zo gidan, bai bari ta yi aikin ba ya zura ta d'aki ya na ta huce haushin shi na safe, har saida ta kai ita kan ta Haseenah ta fara nadamar kan ta dan ba k'aramar wahalar da ita ya yi ba, hakan ya sa ko da dare ya yi yace ta shirya suje cin abinci, saida su ka shirya za su tafi ya shigo falon Khadija yace Bilal ya zo su fita unguwa, sam ba ta yi tunanin har da Haseenah ba, har su ka fita sune sai sha d'aya da rabi na dare suka dawo, kai tsaye kowa falon shi ya nufa, sai lokacin ne Bilal ya fad'a mata har da auntyn shi su ka tafi, ba ta nuna mi shi komai ba, amma ta na shiga d'aki ta yi yan dabaru ta ci abinda ya sawak'a saida ta zubar da hawaye, har ta yi bacci ba ta ga Usman ba da sunan zai mu su saida safe.
Misalin *08:10* ya shigo falon ta cikin shirin da gani ba tambaya kasan tafiya zaiyi, tare suke da Haseenah dan Bilal na d'aki har yanzu ya na shiri, kud'i ya mik'o mata yace "Ga wannan kya yi anfani da shi, ni yanzu zan wuce Niamey zuwa asuba kuma jirgin mu zai tashi, nasan akwai komai babu wani abin da za'a buk'ata, sannan maganar kai Bilal makaranta na barwa amarya ta duka makullan motar da tawa da taki, idan za ku yi anfani da su sai ki mata magana, saina dawo."
Ya na fad'in haka ya juya rumgume da Haseenah a jikin shi, suna fita saida ya gama shinshine ta da lalabe lalabe kafin ya fito da enveloppe ta kud'i har jaka d'ari biyu ya bata, zo kaga murna ga yar matsiyata an bawa Khadija jaka talatin an bata d'ari biyu, 😂 da k'yar ya fita Murtala ya d'auke shi ya tafi cike da kewar amaryarshi.
Sai da rana Aziza ta zo gidan da kayan ta, lokacin Khadija na zaune ta na waya da wata yer uwar ta (cousine) ta na mata k'orafin ta daina zuwa wajen ta, *Aishatu* ce tace "Aunty Khadija na zo Allah ko, ba dai ni nace mi ki na zo ba."
"Hum, yaushe to?"
Daga d'aya b'angaren ne Aishatu tace "Idan na sa lokaci na sanar da ke."
"To ina jiran ki." Ta fad'a su ka yi sallama tace ta gaishe da su aunty (k'anwar maman ta).
Ta ga shigar Aziza b'angaren Haseenah amma ko a jikin ta, ta na jin su suna aiki a madafa amma bata kula da tsiyar su ba, har lokacin d'auko Bilal ya yi daga islamiyya, Ashir ta kira a waya bayan sun gaisa ne tace "Yah Ashir wata alfarma a gurin ka dan Allah?"
Saida ya yi murmushi yace "Auta ai babu alfarma tsakanin mu, fad'i me ki ke so yanzun nan a mi ki shi?"
Cikin sanyin murya tace "Al'amarin Abban Bilal ya na buk'atar addu'a, na sani mijina ba ya hayyacin shi, yanzu haka ya yi tafiya, amma ni saida safen nan na sani, kuma ya tattara makullan mitar shi da tawa ya bawa yarinyar nan, yace sai dai idan ina buk'ata na karb'aa wurin ta, a gaskiya yah Ashir hakan zubar min da mutumci ne, na tabbata sai mun samu matsala da ita akan haka, yanzu haka Bilal na ismaliyya ba'a d'auko shi ba, shine na ke so ka samar min wanda zai dinga kai shi ya na d'auko shi har lokacin da zai dawo, tunda ka ga ma nan da kwana kad'an za'a koma makaranta (school)."
Duk da ya ji ba dad'i amma cewa ya yi "Kinga kar ki damu da wannan, barta da makullan ta had'iye su in za ta iya, yanzu zanje na d'auko Bilal d'in na kawo shi gida, ba buk'atar sai an d'aukar mi shi dreba, ba wai dan ba za'a iya biyan kud'in ba, sai dan darajar Bilal ta wuce haka a wajen mu, kamar yanda na ke kai yara na da kai na haka zan dinga biyowa ina d'aukar shi shima, ko da babu mazauninshi a motar shi to za'a siyi sabuwar mota ne saboda shi kawai, motar tsiyar me da har za'a mi ki iko da ita."
Ya na fad'a ya kashe wayar bin wayar ta yi da kallo tasan ranshi a b'ace ya ke, amma ta ji dad'i kuma da Allah ya bata yan uwa masu huce takaici, baifi minti sha biyar ba saiga Bilal ya shigo gidan da k'atuwar leda da kayan mak'ukashe a ciki, Haseenah da kallo ta bi shi har ya shiga tana mamakin waya kawo shi, ya na shiga ya aje ledar gaban Khadija ya shiga dan sauya kaya, ba jimawa ya dawo da wayar shi a hannu ya shiga latse latse ya na korawa da kayan mak'ulashen shi, sai daf da la'asar Aziza ta shigo wajen Khadija kawo mu su abinci, ko kallon Allah ya isa ba ta ishi Khadija ba har ta aje ta fita, ta na fita Khadija ta d'auki wayar ta kira *Hafsatu* Mak'wabciyar ta tace ta aiko yara ya amshi abinci, ba jimawa yarta ta zo Khadija ta juye mata shi a kwano d'aya ta tafi da shi, dan ita dai ba za ta ci abincin Haseenah ba in dai har za ta fitar mata da na ta da d'an ta a had'e, sai dai kome zai faru ya faru.
*Tun daga wannan rana* Ashir ne ke zuwa ya d'auki Bilal da kan shi tare da yaran shi da na yan uwan shi, dama shi ya d'orawa kan shi alhakin kai yaran, sai dai ba kullum yake zuwa d'aukar su ba sai dai ya sa a d'auko su, amma yanzu da ya zamana akwai Bilal a cikin tawagar da kan shi ya ke d'auko su, hakan ya sa har yanzu bakin Khadija da na Haseenah bai had'u ba da sunan magana, ta yi shiru ta rik'e makullai ta na jiran ace kawo ta yi rashin kunya, Khadija kuma ta nuna mata ita ba bak'uwar mota ba ce, ana cikin haka hutun k'arshe ya k'are na makaranta, yara da manya aka fara hada hadar komawa, Ashir ne ya wa Bilal komai kama daga sababin kaya da abin da zai buk'ata a sabon ajin shi, har zuwa kud'in makarantar shi ya biya ba tare da sanin ma Khadija ba, saida aka kawo kayan kad'ai ta ji kuma ta gani, Usman kuma dama ba kiran ta ya ke ba, idan ma ta kira shi zai ce ta kashe zai sake kiran ta yana cikin mutane ko wani abu, sai in ya kira Bilal ne kad'ai yace ina maman ka yace gata nan, to lokacin zai ce bata waya kuma har su jima suna magana ya na tambayar ta abubuwa.
Zaman Aziza da Haseenah ma ba laifi, a fuska faran-faran take mata, amma da ta bada baya za ta bita da harara dan duk ta gundureta, sai dai kuma har yanzu ba ta bar yiwa Khadija bita da k'ulli ba, duk ranar girkin Khadija idan ta aiko mu su da shi bata nunawa, dan dama Aziza sai ta tafi islamiyyar su ta dawo wacce Haseenah ce ke bata kud'in adaidaita dan ta yi nisa daga nan, kullum sai kusan k'arfe d'aya take dawowa, Khadija kuma na gama abinci da wuri tun kafin Bilal ma ya dawo, hakan ya sa da an kawo mata zata zauna ta ci ta k'oshi tasha ruwa, sauran kuma komai yawanshi da kyawunshi sai dai ta shek'a mi shi ruwa ta zuba wajen wanke wanke, da Aziza ta dawo za ta nuna ba'a basu abinci ba, haka za ta aikata ta siyo mu su awara ko soyayyan dankalin hausa, wata rana kuma su dafa indomie ko suyi taiba, kullum a takarce suke hakan ya sa Aziza da taje gida ta fad'awa Hajia, a wannan karan kam Hajia ta yarda tunda Aziza ce ta rantse ta fad'a mata, da farko ta so ta kira Usman ta fad'a ma sa dan ya mata magana, amma sai tayi tunanin ja mata matsala, dan haka saita shirya taje gidan da kan ta da nufin yi mata magana cikin ruwan sanyi, amma abun mamaki a gabanta ta zubawa su Haseenah na su abinci kwanon miya da na tuwo ta bawa Bilal ya kai, ita ma saida aka zubo mata ta ci ba wani sosai ba kafin ta mata sallama za ta tafi, saida ta shiga da nufin yi wa Haseenah sallama ta samu Aziza sun ware sai shigar tuwo suke kamar 'ya'yan yunwa, nan fa Aziza ta shiga cewa wallahi dan ta ga Hajia e ta zo ta zubo mu su, kuma d'ari bisa d'ari Hajia ta yarda, haka ta tafi gida ranta ba dad'i ta na ji a ranta Khadija ta bata kunya, *Khadija baiwar Allah* ba ta san ma tsiyar da suke ba, dan ita abincin Haseenah ma idan ta aiko kullum saidai ta kira mak'wabtanta azo a d'auka, ita kuma haka za su yi ta yan dubaru ita da d'an ta.
*Yau sati biyu* kenan da tafiyar Usman, kuma jibi ne komawa makaranta, hakan ya sa Usman kiran Khadija a wayar ta, ta yi mamaki dan abu ne da bata tab'a gani ba tunda ya tafi, ta na d'auka suka gaisa a gajarce ya d'ora da "Na ga yara na ta shirin komawa makaranta, amma saboda banda girma da mutumci a idon ki ban isa ki fad'a min ba ko da wani abu da ku ke buk'ata."
Murmushi kawai ta yi tace "Allah huci zuciyar ka ranka shi dad'e, ai akwai hikima sosai a cikin hallitar kowane bawa da iyaye biyu, naga ba ka gari ne kuma kullum cikin aiki ka ke, ba ka da lokacin waya dani bare har mu yi magana da ta shafi d'an ka, shi ya sa ni kuma na mi shi duk wani abin da zai buk'ata, har kud'in makarantar ma na biya."
Duk da ya ji wani abu a zuciyar shi a game da ita, amma basarwa ya yi yace "Uhum." Kashe wayar kawai ya yi, take ya durmiya cikin tunani, Khadija kud'in da ya bata babu abin da za su mata, amma da su take buk'atunta har ta biyawa yaro kud'in makaranta, amma kuma Haseenah daya lodawa masu yawa yanzu haka zaije ya tura mata kud'i ne dan tace suna buk'atar kud'i, dan haka ya kasa nutsuwa ya kira Aziza ya tambaye ta da gaske Haseenah ta na bata kud'in adaidaita, bud'ar bakin ta cewa ta yi "Eh yah Fodio, ta na bani na zuwa da dawowa, har da ma d'an na kashewa, kuma kullum fa sai mun siyi abinci in dai ranar girkin Khadija ne, kuma jiya masu karb'ar kud'in ruwa sun zo dole sai aunty Haseenah ce ta basu."
Duk da ya yarda da Aziza dan abu d'aya suka fad'a amma Haseenah ba ta fad'a mi shi suna siyen abinci ba, haka dai ya sa Nura ya kawo mata kud'in sannan ya kira ya tambaye ta K'arin haske akan abin da Aziza ta fad'a, cikin marairaicewa tace "Kawai ba na so ne wani abu ya faru kuma ace ni ce sila."
"Shikenan to ya yi kyau." Ya fad'a ya na kashe wayar, wayar Khadija ya kira dan jin dalili, amma suna gama waya ta farko Aishatu ta kira ta tace ga ta k'ofar gida mai gadi na mata iskanci, dariya Khadija ta yi kafin tace ta na zuwa, Bilal ta aika sai gasu sun shigo tare, Aishatu budurwace da ke da larura ta iska, hakan ya sa komai nata daban ne, fad'a da masifa kamar shan ruwa ne a wajen ta, tunda su ka shigo tare da Bilal ta ke zagin mai adaidaitar da ya kawota wai yace sai dai ta bashi arba'in ita kuma ishirin ta bashi, hakan ne ma ya sa sam Khadija ba ta ji kiran Usman ba saboda wayar na (vibration) ne, aifa nan hira ta b'arke suna ta yi kamar wanda aka jonawa lantarki, tunda wuri kamar yanda ta saba suka shiga girkin yamma, kuma yau ta yi niyyar yin waina dan akwai wa abokanan mahaifin ta, saboda sabo ya sa ba wani wahala tasha ba musamman kuma ga mai kamawa, sai salade da shima aka siyo mata suka gyara abinsu, Bilyamin ta kira ya kai wainar in da ta zubawa Haseenah na su tace ya kaii, da sauri Aishatu tace ya jirata su tafi tare ta ga amarya, nan fa gaban Khadija ya shiga dukan uku uku, dan ba lallai ta shiga lafiya ta fito lafiya ba, k'aramin aikinta ne ta k'arewa Haseenah kallo tace au dama wannan ce amaryar? Saida Khadija ta rik'e hannunta tace "Dan Allah idan ki ka je ku gaisa kawai ki juyo ki dawo, ba na son tashin hankali ko kad'an."
"Wai amaryar 'yar akuya ce kenan? To ai sai ki fad'a mata ki na da irin mu 'ya'yan busurai, mu za ta wa iskanci?" Cewar Aishatu har tana gaggawar tafiya, rik'e ta Khadija tayi tace "Ni fa ban fad'a mi ki haka ba, kawai dai ku gaisa ki juyo ki dawo, kar ki ce za ki tsaya wani abun da bai shafe ki ba."
Saida ta fizge hannunta tace "Naji dallah."
"Kinyi alk'awari?" Cewar Khadija ta na binta da kallo, k'ala ba tace ba ta bi bayan Bilal su ka shiga, Bilal ne ya yi sallama amma shiru, bubbuga k'ofar ya yi ya sake jin shiru, sai Aziza ce ta lek'o daga sama ta hangeshi tace "Bilal ga auntyn ka nan sama."
Daga nan yace "Abinci ne na kawo mu ku."
"Kawo nan." Cewar Aziza, kallon Aishatu ya yi tace "Muje saman na ganta, ai ko saman bakwai take sai na ganta yau."
Can suka nufa, Bilal na isa ya aje abincin sai aishatu da ke k'arewa Haseenah kallo ta hakimce akan kujera ta na latsa waya, kallon Aziza ta yi tace "Ke na ganeki k'anwar Usman ce ko?"
"Eh, ina wuni." Cewar Aziza wacce ba tun yau ba tasan Aishatu farin sani, mayar da kallonta ta yi ga Haseenah ta na wani murmushi tace "...
*Allah fidda A'i daga rogo.*
15/02/2020 à 13:58 - 💋😘💋: 💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
*KALLON KITSE*
_(Ake wa rogo)_
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
_SAMIRA HAROUNA_
*Litattafan marubuciyar*
*1* _KAUSSAR_
*2* _D'AUKAR FANSA_
*3* _BA SO BANE_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI_
*6* _JIHADI_
*7* _K'ANGIN RAYUWA_
*8* _ITACE K'ADDARARMU_
*9* _KAWU NA NE_
*10* _MAATA_
*11* _KALLON KITSE..._
*SADAUKARWA GA*
_MATAN FARKO_ 🧕🏼 *(UWAYEN GIDA)*
🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_🤜🤛
```Fatan alkairi masoya```
_Bismillahir rahamanir rahim_
*26*
"Wai ke ce dama amaryar da ya yi? Kai, amma dai wallahi maza ba su da tabbas, yanzu shi dan Allah rufe mi shi ido ki ke kayi? Ko kuma tallarki aka mi shi?"
Bilal ne ya kalle ta yace "Aunty Aishatu mu tafi ko."
Bushewa ta yi da dariya tace "Bilal barni na k'are kallon amaryar Baban ka, wannan mace haka sai kace kaza ta ga wuk'ar yankanta."
Wata dariyar ta saka mik'ewa Haseenah ta yi da nufin magana sai Aziza ta rik'e hannun ta, girgiza mata kai ta yi alamar a'a ta rabu da ita, ganin hakane ya sa Aishatu cewa "Da kin barta ta fad'i abin da ke ran ta ai kar ta zama ajalin ta, ni ma saboda ba zan iya yin gulmarki bane ya sa na fad'i abin da ke raina tun a gaban ki."
Iza k'eyar Bilal ta yi tace "Mu tafi kai yaro ka ji, Allah ya tsigewa Babanka rigar wahala, wannan mata kafin ya sa k'asusuwanta su cika ai sai mai kampanin gidan shinkafa na *oriba* ya san da zaman shi."
Ta na wucewa Haseenah tace "Ita kuma wannan mahaukaciyar fa? Wacece ita?"
Ajiyar zuciya Aziza ta sauke tace "Hum! Cousine d'in Khadija ce, mahaukaciya ta sawa a gidan gaba, wallahi da kin biye mata ina tabbatar mi ki yau a gidan nan sai kinga motar masu kashe gobara."
Tab'e baki ta yi tace "Kin dai gani Aziza da idon ki, duk wanda ya zo gidan nan wajen ta sai ya zo ya ci mutumci na, ba na shiga sabgarta amma ita sai ta san yanda ta yi ta tsokane ni, yanzu wannan da me ya yi kama?"
"Ki yi hak'uri dan Allah ki rabu da ita, can aniyarta ta koma mata." Cewar Aziza, Haseenah ce tace "Mu sauka k'asa kawai dan magriba ta gabato."
"Gaskiya kam." Aziza ta fad'a ta na d'aukar kwanon abinci ta na fad'in "Ta mayar da mu mabarata k'arfi da yaji, in dai ta yi abinci ran alhamis da juma'a to ranar za mu samu abinci, saboda ta na yin abincin da take rabawa mutanen ta, shi ma fa ba kullum ba sai taga dama."
Kallon ta Haseenah ta yi ta wutsiyar ido a zuciyar ta tace "To ai saboda ki na gidan a wannan ranakun shi ya sa ba na iya zubar da shi, sai kin fita kad'ai na ke samun wannan damar."
Tunda Aishatu ta koma take mita akan amaryar Usman, har akayi sallah magrib da isha'i su ka ci abinci, anan take tambayar Khadija za ta je bikin *Saratu* (kamar jikanya take ga mahaifiyar Khadija), zaro ido ta yi tace "Wai yaushe ne bikin Saratu?"
"Jibi mana." Cewar Aishatu tana shirgar wainar ta, cike da mamaki Khadija tace "Wallahi na manta, kuma Mama ba ta sake tuna min ba, amma dai bara na kira Abban Bilal na fad'a mi shi yanzun nan, dan zan iya mantawa, kuma tafiya ce da ba nan cikin gari ba akwai buk'atar ya sani da wuri."
Saida ta d'auki wayar ta ga kiran shi har uku ba ta d'aga ba, maida kiran ta yi kamar kuma jira ya ke sai kuwa ya d'auka dan ya zazzage kwandon bala'i, cikin sa'a sai Aishatu ta d'aga murya tace "Gaida min shi, ki ce na ga amaryar shi ina taya shi murna."
Dariya Khadija ta yi tace " bara na baki sai ki fad'a mi shi." Bata wayar ta yi, kasancewar akwai fahimtar juna tsakaninsu ya sa su ka dinga hira ta na tsokanar shi shima haka kafin Khadija ta karb'i wayar, ta na d'orawa a kunne tace "An wuni lafiya saraki."
"Lafiya lau, anga damar d'aukar wayar?"
Murmushi ta yi tace "Ka yi hak'uri, ina aiki ne a lokacin ban lura ba, yanzu ma na d'auko wayar ne zan nemi izinin ka sai na ga kiran."
"Izinin me kuma?"
"In ba ka manta ba wata biyu da ya wuce na baka goron Saratu? To bikin ne ya taso yanzu ni har na manta ma saida Aishatu ta tuna min."
"Yaushe ne?"
Ta na wasa da yatsunta tace "Jibi, ranar da su Bilal za su koma makaranta."
"Amma ai ba cikin gari bane?"
"Eh hakane."
"Shikenan, Allah ya tsare, zan kira Mama na tambaye ta shirye shiryen tafiyar." Ya na fad'in haka ya datse kiran, ita kam bata wani damu ba tunda dai ya barta, sai wajen tara na dare Khadija ta ma Aishatu kyautar fitar hankali kafin ta bar gidan.
B'angaren Haseenah kam tunda ta ci wainar nan dayawa sai ta tayar mata da zuciya ta dinga kelaya amai, sosai ta galabaita har Aziza ta tashi hankalin ta, dare na sake yi kuma sai zazzab'i da ciwon kai, Hajia su ka kira aka fad'a mata tace su shirya su fad'awa Khadija tunda ita ta iya mota saita kai ta asibiti, ira kuma za ta same su asibitin yanzu, har Aziza za ta tafi wajen Khadija kawai Haseenah ta rik'e hannunta tace kar taje, "Me ya sa to?" Ita ce tambayar da ta mata.
Cikin galabaita tace "Kawai ba na so tasan halin da na ke ciki, ko ta taimaka min ba dan Allah bane, dan ta samu mafakar da za ta yak'eni ne."
Da mamaki tace "Amma Haseenah dan ta kai mu asibiti miye a ciki?"
Kallonta ta yi tace "Aziza in za ki samo mai adaidaita ki samo, in ba za ki sami ba ki bar shi, yanzu haka da yan uwa na za su san ina cin abincin ta wallahi da sun tofa min yawu, mutum fa ba abun yarda bane, kuma ke kinfi kowa sanin ta ai."
"Gaskiya ne kuma." Cewar Aziza jiki a sanyaye, haka suka shirya suka fita a hanya suka yi sa'ar samun adaidaita su ka hau, asibitin kud'i aka kai da ke nan kusa da su ta *Clinique Alheri*, tun kafin su ka likitan Hajia ta k'araso ta na waya da Usman da ta sa aka kira shi take fad'a mi shi, aifa kamar ya taso ya zo ya ke ji ance amarsu ba lafiya, ko da su ka ga likita ya mu su albishir da ta na da ciki amma k'arami, nan dai aka mata allura tare da bata magunguna, bayan sun biya kud'i tsagaga su ka dawo gida da rankiyar Hajia, kwance Haseenah ta yi Hajia ta kalli Aziza tace "Da na ce ku fad'awa Khadija ta kai ku me ya sa ba ku mata magana ba ku ka hau adaidaita?"
Aziza ce "Hajia zan..." Da sauri Haseenah ta mata alama da hannu kan ta yi shiru, duk da Hajia ta gani amma da tace "Me ye ta yi shiru?"
Cike da tausayi tace "Hajia kawai ku bar maganar, tunda dai gashi mun tafi kuma mun dawo lafiya."
Shiru Hajia ta yi da mamaki, kallon ta tayi tace "Kun ci abinci?"
Kallon juna su ka yi sai Haseenah ce tace "Wallahi wata waina ce aunty Khadija ta aiko mana, ko gama ci banyi ba zuciyata ta tashi sai amai."
"Yanzu ta na aiko mu ku da abincin kenan?" Cewar Hajia ta na kafesu da ido, Aziza ce tace "Hajia bata aikowa fa, sai kamar irin wannan ranakun alhamis ko juma'a, shi ma sai in ya na girkin ta ne."
Kallon Haseenah ta yi tace "Ki fad'awa Aziza idan za ki ci wani abu mai sauk'i saita d'ora mi ki kafin ki sha magani, ni yanzu gida zan tafi dare ya yi."
"To." Ta fad'a ta na yamutsa fuska, Hajia na fita tasa Aziza ta d'ora mata zallar shayi tasha kafin tasha magana, kiran ta Usman ya yi suka dinga hira har saida tace za ta yi bacci, Hajia kuma na fita ko kallon b'angaren Khadija ba ta yi ba saboda ran ta ya sake b'acewa a game da ita, adaidaita ta hau ta koma gida, ba ta yi nauyin baki ba wajen fad'awa malam abin da ake ciki, sai dai shi baiji komai ba a zuciyar shi, sai dai yafi mayar da hankalin shi kan Usman da ya ke d'an ganin canji a tare da shi yanzun, da haka suka kwanta da fatan ganin wayewar gari lafiya.
Tunda safe Hajia ta had'a abin kari ta bawa Nura ya tafi ya kai ma su Haseenah, a lokacin Khadija na madafa da doguwar rigar bacci a jikinta Nura ya shigo, da kallo ta bishi har ya wuce b'angaren Haseenah kai tsaye kamar yanda Hajia ta fad'a mi shi, amma bai jima ba ya dawo dan gaisawa kad'ai ya yi da Haseenah ko jiki bai tambaye ta, falon Khadija ya lek'a sai Bilal kwance akan kujera, baisan da shigowar shi ba yace "Yarima barka da safiya."
Juyowa ya yi yace "Tonton Nura, ina kwana?"
"Lafiya lau, ka tashi lafiya?"
"Lafiya lau."
Ba tare da ya shigo ba daga k'ofar yace "Ina maman ka?"
"Ta na madafa." Ya fad'a da ma sa nuni da yatsarshi, hannu ya d'aga ma sa yace "Ina zuwa to." Madafar ya nufa da sallama, ya na ganin Khadija yace "Uwar gida ran gida, uwar gida sarautar mata, kowa ya shigo gida ke ya tarar, ko mai gida sai kin lamunce ya shigo, sannu da aiki."
Da wuk'ar hannunta ta nuna shi tace "Bansan dad'in baki, fad'i abin da ka ke so na ma ka."
Cikin had'e rai yace "Kamar ya? Ban gane me ki ke nufi ba?"
Kallon shi ta yi tace "Ai dana gan ka gidan ka to da dalili, bugu da k'ari kuma gashi har da min wani kirari kamar marok'i."
Dariya ya yi yace "Lallai uwar gida daban ki ke da kowace mace, cikin sakan biyar har kin fahimci akwai abin da na ke buk'ata ki min ko?"
Hararan wasa ta mi shi tace "Yau da gobe ai bata bar komai ba, karfa ka manta a hannu na ka k'arasa girma."
B'ata rai ya yi yace "Haba kema, basar mana."
"To naji, me ka ke so."
Saida ya matso kusan ta yasa hannu ya na cakurar dankalin da take soyawa ya na jefawa baki yace "Aunty Khadija maganar fa mai mahimmanci ce."
"Uhum, ina jinka."
Saida ya saci kallon ta yace "Aure na ke so."
Da sauri ta dakata daga abin da take ta kalle shi tace "Me? Aure fa ka ce Nura?"
"Eh mana, ko ban isa ba?"
Zaro ido ta yi tace "Ni bance ba, amma dai me zai hana ka bari kad'an k'ara mallakar hankalin kan ka, Nura aure fa ba iya abin da kawai ka ke tunani bane."
Kamar zaiyi kuka yace "To ni me na ce mi ki ina tunani?"
Mirmushin gefen labb'a ta yi tace "Ba ma irin wannan hirar da kai, amma na tabbatar ba zai wuce wutar balaga ce ke fizgarka ba."
"Kinsan me?" Ya fad'a ya na rik'e k'ugu, "A'a sai ka fad'a."
"Mijin ki ma haka yace da na masa magana, wai na bari har nan da ko shekara biyu, a gaskiya kuma ni ba zan iya ba, aunty Khadija wallahi gaskiya na ke fad'a mi ki, na fad'awa su Baba sunce ba ruwansu na fad'awa Usman tunda shine zai min auren, shi kuma yace ba yanzu ba."
Ajiyar zuciya ta sauke tace "Yanzu me ka ke so na ma ka?"
Cikin sigar rarrashi yace "Ki daure dan Allah ki taimaka min ki ma sa magana, wallahi nasan zai saurare ki, ni fa har mun gama magana da iyayen yarinyar ma, sunce kawai na turo manya na."
"Babbar magana." Cewar Khadija, "Haba wannan k'arama ce, yanda na san ki da Abban yarima ai sha yanzu mgani yanzu ne."
"Sanin da ka yi mana ada ne wannan." Cewar Khadija a zuciyar ta.
Basarwa ta yi tace "Shikenan kar ka damu, zan jaraba na gani, amma ba lallai ya amince ba tunda har ya nuna bai yarda ba tun farko."
"Zai ma amince in dai ki ka masa magana wallahi." Da haka ya bar gidan ita kuma ta shiga tunanin yanda za ta fara tunkarar sabon Usman d'in ta da maganar nan, ba ma lallai ya saurare ta ba bare har ya amince da abin da Nura ke tsammani.
Ta na gama abin karin ta bawa Bilal na su Haseenah ya kai mu su, suma ko da su ka kammala suka fito farfajiyar gida, Bilal na yawo da moton shi a tsakar gidan Khadija zaune da waya ta na tunanin ta kira ko karta kira, ta na haka sai kiran shiya shigo wayar ta, yau ma mamaki ta yi ganin kiran shi, hakan ya sa ta d'auka ta aza a kunne, ba sallama bare gaisawa yace "Na kira Hajia akan maganar tafiyar nan, sai ki shirya da wuri ki same su can gida dan sun ce Naseer ne zai kai su."
"H...hello." Ta fad'a da sauri saboda jin zai katse kiran, cike da k'aguwa yace "Ina ji? Lafiya?"
Cikin fad'uwar gaba tace "Lafiya lau, dama ina son yin magana da kai ne."
"Magana akan me kuma?"
Murya k'asan mak'oshi tace "Nura ne dama ya same ni akan maganar aure da ya ke so, amma yace ka ce ba yanzu ba, shine..."
"Shine za ki sani na yarda na mi shi auren ko me?" Ya fad'a cike gatsali, kamar ta kashe wayar sai kuma ta daure tace "A'a ba haka bane, ya fad'a min ne saboda shi a tunanin shi Khadija tafi k'arfin komai a gurin Abban Bilal, ya zo da buk'atar shine gare ni saboda sanin da ya mana ina iya shawartarka akan al'amura har na cikin gida ma kuma ka yi aiki da ita, ya fad'a min ne ba dan tunanin zan saka ka dole ba, sai dan cewa kamar ina da mahimmanci da kima a wajen ka da zan iya nemawa wani alfarma a wajen ka, sannan ni a gani na ba wani abu bane idan an mi shi auren, matashi kamar Nura ya kalli iyayen shi yace ya na son aure, ina ga a mi shi auren shi yafi kwanciyar hankali."
Har k'asan zuciyar shi maganganunta sun ratsashi, amma saiya dake yace "Me Nura ya sani a game da aure da za ayi mi shi? dan ya na da abinyi ba shi ke nuna zai iya rik'e mace ba."
"Amma ai ko neman auren ya tafi daga cikin tambayoyin da za'a masa akwai son sanin abin da yake, hakan kuma nasara ga d'an uwan mu da ya zamana ya na da aikin yi, ko ba komai zai ciyar da ita, zai shayar da ita da tufatar da ita, sannan ina da yak'inin zai kula da ilimin ta ko wane iri ne, sannan zai iya biya mata buk'atar ta."
Saida taji sautin sauke ajiyar zuciyar shi a kunnenta kafin yace "Bansan me ya fad'a mi ki haka ba da ki ka yarda da shi, gashi har kinsa nima na ji banda wata hujjar hana shi auren, ki fad'a ma sa na amince, amma dole ya jira ni na dawo sai ayi duk wacce za ayi, idan kuma ba zai iya jira ba sai ya turaki ki nemo masa auren."
Ya na fad'a ya kashe wayar, ita kam dad'i ne ya sata bushewa da dariya saboda abin da ya fad'a a k'arshe, wayar Nura ta kira ta fad'a ma sa yanda su ka yi da shi, sosai ya yi murna tare da binta da addu'a Allah ya barta da yayan su, suna gama waya ta ji wayar Bilal na k'ara, hannu ya sa a aljihu ya fito da ita ya d'auka, take ta fahimci Abban shi ne ya kira shi, suna nan zaune Hajia ta shigo gidan da sallama saboda ganin su, da farin ciki Khadija ta mik'e ta tarbe ta tana mata sannu da zuwa su na gaisawa, Bilal ma saida su ka tab'a hira irin ta kaka da jika kafin ta kalli Khadija tace "Ina yer uwar ta ki ta na ciki?"
"Eh Hajia su na ciki."
Nufa b'angaren ta yi ta na fad'in "Bara mu gaisa."
"A fito lafiya." Cewar Khadija, ta na shiga su ka gaisa kafin ta tambaye ta sun ci abinci ai? Eh, shine amsa da su ka bata, kallon Aziza ta yi tace "Ke ki zauna gidan to, ke sai ki tashi mu koma asibitin."
Dama a shirye take, hijabi kawai ta saka suka fito tare da Hajia da ke rik'e da katin likita a hannu, "Hajia har kun fito? Gida za ku tafi ne?"
"A'a." Ta fad'a kai tsaye, ganin Haseenah tare da ita ya bata mamaki, musamman da taga ta na gaba ta na binta, "Hajia lafiya kuwa? Ko ba ta da lafiya ne?"
Sai kawai Hajia ta ji haushin wannan tambayar, bud'ar bakinta cewa ta yi "A'a lafiyar ta k'alau, akwai in da za mu ne."
Da ido kawai ta bisu ta na mamakin kamuwar Hajia ita ma da wannan cuta ta 'ya'yan ta, ido kawai ta zuba mu su har suka dawo lokacin ta na madafa ta na girki, lokacin ne kuma 'yan uwan Haseenah da ma 'yan uwan Usman d'in suka fara zuwa ganin ta, ita dai ta na kammala girki ta fitar mu su ta bayar aka kai, sai dai ta yi niyyar ko ciwon ajali ne Haseenah keyi ba za ta je ta duba ta cikin mutane, tunda ta lura b'oyewa ake ba asa ta sani saboda tunanin wani abu.
Da yamma Haseenah ta karb'i girki, amma 'yan uwan ta ne suka shigar madafar suka yi yanda su ke so, sai dare su ka bar gidan Khadija ta shiga dan samun abin da za su ci, yanda ta ga madafar abin ya bata mamaki da dariya, saida ta gyara ta sosai kafin ta samu abin da za su ci, ko da su ka kammala suka kwanta abin su.
*Hummmmmmmmmm.*
Tunda asuba Khadija ta shirya tare da Bilal suka yi karin kumallo, sai da ta kira Usman tace ta na si ta aje Bilal a gida, amma sai yace "Me ye haka Khadija? Gidan nan fa akwai mutane, ya ki ke so ki nunawa yaron banbanci a zahirance."
"Shikenan ka yi hak'uri." Ta na fad'a ta kashe wayar ita ma, zuwa k'arfe *07:15* suka fito, saida su ka shiga d'akin Haseenah da sallama suna falo ita da Aziza ita ma ta na shiri, "Antashi lafiya?"
"K'alau." Cewar Haseenah, Aziza ce tace "Ina kwana."
"Lau." Cewar Khadija, kallon su ta yi tace "Dama zan tafi Tessaoua ne wajen biki, na kulle d'aki na, ga kayan Bilal idan an dawo da shi sai ya canza wannan, sai na dawo."
Hannun shi ta kama su ka fita, Aziza kam cewa ta yi "Ka ji matar nan sai ka ce akwai bawanta anan d'in."
"Ke kuwa miye a ciki? Bilal ai d'an mu duka, Allah dai ya kaita lafiya."
Saida ta gama shiri suka karya tace"Idan na tafi zan tsaya gida na wuni, na san dai saida dare ko na dawo gida."
Da haka su ka yi sallama ita ma ta tafi makaranta, Khadija ma ko da suka isa Ashir ne ya kai su makarantar duka, su kuma zuwa tara Naseer ya d'auke su suka tunkari *Tessaoua*.
*Me kuma zai faru yanzun?*
16/02/2020 à 13:20 - 💋😘💋: 💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
*KALLON KITSE*
_(Ake wa rogo)_
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
_SAMIRA HAROUNA_
*Litattafan marubuciyar*
*1* _KAUSSAR_
*2* _D'AUKAR FANSA_
*3* _BA SO BANE_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI_
*6* _JIHADI_
*7* _K'ANGIN RAYUWA_
*8* _ITACE K'ADDARARMU_
*9* _KAWU NA NE_
*10* _MAATA_
*11* _KALLON KITSE..._
*SADAUKARWA GA*
_MATAN FARKO_ 🧕🏼 *(UWAYEN GIDA)*
🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_🤜🤛
```Fatan alkairi masoya```
_Bismillahir rahamanir rahim_
*27*
Sha biyu Ashir ya d'auko su Bilal, suna hanya Khadija ta kira shi su ka gaisa, gida aka aje shi kafin suka wuce, k'ofa mai gadi ya bud'e masa ya na fad'in "K'aramin Alhaji har an taso?"
"Eh, ya aiki?" Ya fad'a da fara'a, shi ma da fara'a ya mayar masa da "Alhamdulillah."
Ciki ya shiga kai tsaye kuma b'angaren Haseenah ya wuce tunda yau ita ce maman shi, sallama ya dinga rabkawa amma ya ji shiru, saida ya bud'a k'ofar falon ya shiga kad'ai ya ga takalma alamar bak'i amma kuma ba kowa a falon, kujera ya samu ya zauna ya ciro wayar shi ya na dannawa da chocolat a hannu ya na sha, minti talatin ya d'auka a falon sai dariya da shewar su Haseenah ita da Zeinab wacce daga makaranta take ita ma ta ratse nan, tashi ta yi ya nufi d'akin na ta ya k'wank'wasa k'ofa duk da bud'e take, shiru su ka yi kafin tace "Waye?"
A hankali ya yaye labulen ya kalle ta yace "Aunty sannu, ni ne."
Fuska a d'aure tace "To, yaushe ka shigo gidan?"
"Na jima zaune a falo, yanzu ma dan na ce ku bani kaya na ne zan canza wannan."
"Ka je idan na fito zan baka kayan." Ta fad'a ta na mayar da hankalin ta kan Zeinab, har ya juya zai fita tace "Kai zo nan."
Dawowa ya yi jiki a sanyaye ya tsaya gaban ta, kud'i ta mik'o mi shi tace "Ka wuce maza kaje ka siyo min katin waya na airtel."
"To." Ya fad'a ya na karb'ar kud'in ya fice, ta k'aramar k'ofa ya bi zai fice mai gadi yace "K'aramin Alhaji fita za ayi?"
"Eh." Kawai ya fad'a a tak'aice ya na zura duka hannayen shi biyu cikin aljihun doguwar rigar shaddar shi wacce ka na gani kasan ta ji kud'i, a k'afa ya taka har ya iso bakin titi, ya jima tsaye kafin ya samu ya tsallaka saboda akwai ababen hawa sosai a wajen musamman da ya zama ranar farko ta komawa makaranta, siyowa ya yi ya dawo gidan ya kawo mata, falo ya dawo ya zauna amma bai jima ba aka fara kiran sallah, tashi ya yi ya fita a panpo na daf da shigowa gidan ya yi alwala ya tafi masallaci, daya dawo wajen mai gadi ya zauna shi ya na sauraren redio shi kuma ya na kallon hanya, tsawon lokaci ya d'auka nan zaune kafin ya ji cikin shi na neman agaji, cikin gidan ya koma ya samu su Haseenah har yanzu a d'aki amma su na cin soyayyen k'wai da indomie, ga lemu a gefe suna korawa mai sanyi, cikin muryar tausayi yace "Aunty abi..."
Kallon da ta ma sa ne ya sa ya yi shiru, Bilal yaro ne miskili da bai cika magana ba, in kaji yawan maganar sa to da iyayen sa ne idan suka had'u, jin ya yi shiru ya sa tace "Me ye kuma? Kayan ka na ce ka jira ni na tashi sai na d'auko ma ka, ka gansu can gefen gado, banyi niyyar tashi ba yanzun."
Juyowa ya yi ya sake fitowa daga d'akin, Zeinab ce tace "Kin bashi abincin shi?"
"Wannan d'in?" Ta nuna Bilal da ya fita da yatsa, d'orawa ta yi da "Ai munafiki ne da ki ke ganin shi kamar uwar shi, ba sa cin abinci na fa, yanzu in d'auka in bashi wani abu ya faru ace ni ce, yanda duk na ke k'ok'arin jingina mata laifukan nan ai kinga kashina ya bushe, kuma wallahi ni har ga Allah ma na manta da ya na gidan."
Da haka su ka ci gaba da hirar su Bilal kuma na fita ya samu mai gadi shi ma ya gaji da jira ya siyo wake da shinkafa, a hallitar Bilal bai tab'a cin wake da shinkafa ba, amma yau da ya ke jin yunwa sosai kuma mai gadi yace su ci, sai kawai ya sa hannu su ka ci abincin tare, saida su ka gama su ka sha ruwa, sun d'an fara tab'a hira Bilal ya ji cikin shi ya fara k'ullewa, a hankali ya fara dafe ciki ya na d'an matsa shi, amma sai abun ya fara k'amari sosai, mik'ewa ya yi kawai ya koma cikin gida kai tsaye madafa ya nufa, jar kanwa ya samu ya samu kofi ya sa ruwa ya jik'a yasha kamar yanda wani lokacin idan cikin shi na ciwo maman shi ke bashi, har zai fito sai ya ji ciwon ya fi na baya ma, dafe ciki ya yi sosai ya na murd'awa har ya sulale k'asa, jin azabar ciwon na k'aruwa ya sa shi tafiya wajen Haseenah, falo ya same su wannan karan su na kallo ana hira, a dafe da ciki ya tsaya gaban ta yace "Aunty ciki na ke ciwo, dan Allah ki bani magani idan ki na da?"
A wulak'ance ta kalle shi tace "Cikin ka kuma? To miye a ciki ya wuce kayan zak'in da kullum uwayen ka ke siyo ma ka ne ka na had'iya, sune kawai za su tambaye ka, ni ba na da magani."
Ganin idon shi cike da hawaye ne ya sa ta d'auki kud'i ta mik'a mi shi tace "Je ka siyo maganin bakin titi sai ka sha."
Karb'a ya yi ya fita ya na duk'e-duk'e, mai gadi na ganin haka yace "K'aramin Alhaji lafiya ka ke, ya na ga ka na dafe ciki? Ko ciwo ya ke ma ka."
Cike da k'aguwa yace "Ba komai." Ya wuce abinshi, da k'yar ya kai kan shi shago ya siyo maganin ya juyo ya dawo, madafa ya zarce ya samu ya sha maganin sannan ya wuce d'akin Haseenah, kwance ya yi bawan Allah akan kujera sai Haseenah tace ai ya sauko daga kan kujera ko ubanshi bai tab'a kwance anan ba, k'asa ya kwanta babu ko tapi (carpet) shinfid'e in da ya ke.
Ko dare Haseenah ba ta yi girki ba ta na hutawar ta, Bilal na gefen ta kwance ya galabaita dan babu abin da ya yi sauk'i daga ciwon cikin, sai ma kumbura da cikin shi ya yi kamar zai fashe, hakan ya sa zazzab'i sauko mi shi mai zafin gaske, yamma lis ta kalli Bilal da ke ta rawar d'ari tace "Kai zo amshi nan ka karb'o mana salade wajen mutumin can na tsallaken titi."
Da k'yar ma ya iya bud'a idon shi ya kalle ta sunyi jawur, rarrafawa ya yi ya zura mata hannu ya karb'i kud'in da take mik'o mi shi, da wuya ya iya mik'ewa tsaye ya fita sai rangaji ya ke, k'wafa ta yi tace "Munafiki, ciwon k'arya ne ka ke k'irk'irowa saboda kawai ka jaza min masifa."
An fara kiran sallah magriba kenan sai ga Khadija ta sallamo gidan, daga jakar ta sai ledar da tayowa d'an gudaliyar ta tsaraba, kai tsaye b'angaren ta ta fara bud'awa ta shiga, uwar d'aki ta shige ta cire kayan jikin ta ta saka doguwar riga ta atamfa, lokacin kuma Aziza ita ma ta sallamo gidan dan Hajia tace ta zo ko aiki ta kama ma Haseenah, zaune ma ta same ta tace ba ta d'ora komai ba, amma ta bada a siyo mu su salade su ci, Khadija kuma jin shiru ba motsin d'an gudaliya ya sa ta sallamo falon Haseenah, "Sannun ku da hutawa."
Haseenah da gabanta ya shiga fad'uwa dan ta d'auka ma can za ta kwana, Aziza ce kad'ai tace "Sannu aunty Khadija, har kin dawo?"
"Na dawo yanzun nan, ya gida?" Ta tambaya ta na kai kallon ta kowace kusurwa na falon, kallon Aziza ta yi tace "Wai ina Bilal? Ko ba'a dawo da shi ba."
Cikin rashin sani Aziza tace "Eh...to, ban dai..."
Jin kakarin amai a k'ofar d'akin ne ya sa Aziza yin shiru yayin da Khadija ta fita da sauri dan ta gane ko muryar waye, da sauri ta rumgumo shi jikin ta duk da aman da ya ke bulalowa, take idon ta suka kawo ruwa ta kalle shi tace "Bilal, me ya same ka? Me ka ci ka ke amai haka? Lafiya?"
Da k'yar ya iya kallon ta da ido dishi-dishi cikin muryar galabaita yace "Mummy, ke ce? Ki kai ni likita Mummy, ciki na ciwo ya ke."
Kuka ta fashe da shi ta manna kan shi a k'irji kamar za ta bashi nono tace "Bilal me ya same ka? Halan ka ci wani abu da ya b'ata ma ka ciki?"
Shiru ya yi sai numfashi da ya ke saukewa na wahala, fitowar su Aziza da Haseenah ne ya sa ta kalle su tace "Na d'auka za ku kula da shi ba sai na ce na bar amanarshi a hannun ku ba, amma shine ku na kallon shi a wannan halin, ya yi kyau, ki bani makullin mota na kai shi asibiti." Ta fad'a ta na kallon Haseenah.
Cike da gadara Haseenah tace "Ki yi hak'uri, gaskiya ba zan iya baki makulli ba, ko da ya bar shi a hannu na baice na ba ki ba, cewa ya yi idan buk'atar aiki ta tashi da mota sai ayi, kuma akwai wanda zai dinga fita da su."
D'auke kan Bilal ta yi daga k'irjin ta cikin hushi ta mik'e tsaye tace "Ina tunanin na jima da fad'a mi ki ba na so ana min wasa da d'ana, wallahi ba ke ba ko Usman ne ba zan lamunci ya min wasa da lafiyar shi ba bare ke, domin kuwa har yanzu shine kad'ai gare ni, shi kad'ai na mallaka a duniya sab'anin Usman da zai iya haifar wasu yaran da wasu mata, misali ke, dan haka ki ban makullin mota yanzun nan kafin kisa hankali na ya bar jiki na miki dukan mutuwa a gidan nan, kinga sai ayi biyu kenan dan na fahimci so ki ke ki kashe min d'an nawa."
Jin haka ya sa Haseenah juyawa ta koma falo, da sauri Khadija ta biyo bayan ta tasha gabanta ta shak'i wuyan rigar ta, janta ta yi har saida ta kai ta d'akin ta ta wurga ta kan gado tace "Maza tashi ki d'auko makullin ki bani."
Haseenah da ta ji mararta ta d'aure kasa tashi ta yi sai dafe mara, hakan ne ya sa Khadija cire d'an kwalin atamfar dake kan ta ta d'aure k'ugu da shi tace "Na rantse mi ki da Allah idan ba ki tashi kin d'auko min ba ko, wallahi gidan nan sai dai ya kama da wuta amma banga wanda ya isa ya shiga tsakani na da ke ba, Haseenah yaro na ne fa kwance babu lafiya, ga abin hawa a cikin gida kuma na iya sarrafa shi amma ki ce ba za'a hau ba, ba dan larura ce ba ma ni ko kallon motar na sake yi bare har na yi sha'awar hawan ta, dallah ki tashi ki d'auko min."
Jiki na rawa Haseenah ta mik'e da k'yar saboda sosai ta ke jin ciwo a marar ta, d'aukowa ta yi ta mik'a mata ta fizga ta juya za ta fita tace "Lokaci zai zo da za ki gane mahimmancin d'a da kuma zafin haihuwa."
Ta na fitowa k'ofar d'akin ta yi karo da Aziza da ta k'i shiga saboda tsoro, saida ta kwance d'an kwalin ta ta d'aura akai ta kalli Aziza da kyau tace "Aziza ba ni ki ka cutar ba, kan ki kika cutar, ba ni ki ka azabtar ba, d'an ki kika azabtar, hak'ik'a na ji ba dad'i a zuciya ta, amma ki sani bai kai wanda d'an d'an uwan ki ya ji ba, wannan yaron ko d'an mak'wabta ne ina tunanin zai iya samun tausayin ku a matsayin ku na 'yan adam kuma mata masu d'aukar ciki da haihuwa, amma kash an rasa wannan tausayin daga gare ku ba dan komai ba sai dan kawai ku na so wai ala dole sai kun cuzguna min, to bari na tuna mi ki wani abu, Bilal d'an ki ne domin kuwa ciki d'aya ku ka fito ke da mahaifin shi, Aziza rayuwa ba ta da tabbas, watak'ila wannan yaron da ki ke nunawa k'iyayya yanzun sai kin fini cin moriyar shi ni da na haife shi, idan ki na ganin kamar zanji zafi saboda kun cuta mi shi, to ki sani fa ku sai kun fini cutuwa, domin wannan yaron d'an uwanku ya na son shi fiye da komai a rayuwar shi, sannan abu d'aya da ku ka manta shine, ko a makaranta ana kiran shine da sunan *Bilal Usman Ali* ba wai *Bilal Khadija*, da yau mahaifin shi zai fad'i ya mutu, to ko shakka babu ke d'in nan Aziza zaki fini iko da shi ta wani b'angaren, da ace yau zanje nemawa Bilal aure a wani gidan, daga cikin tambayar da za'a mana ita ce *ina dangin mahaifin shi*? Domin kuwa kune shak'ik'an shi, kuma wallahi ina tabbatar mi ki ke d'in nan kawai idan na nuna a matsayin k'anwar mahaifin shi zai iya sawa a bamu aure, dan haka ku farka daga baccin da ku ke, duk abin da kukawa Bilal zai koma kan ku ne da d'an uwanku, ke ma kuma mace ce, nan da wani lokaci za ki yi aure kije gidan miji, ba zan mi ki fatan samun matsala a gidan auren ki ba, amma zan so ko na wuni d'aya ne ki fuskanci irin rayuwar da na fuskanta a dalilin ku, kinsan me Aziza? Na fi jin zafin juyawar bayan ki a kai na fiye da sauren 'yan uwan ki, kinsan me ya sa? Saboda ke ba baya kad'ai ki ka juya min ba, har da cin amana da yaudara, Allah ya ganar da ku gaskiya, za ku gane waye ya mallake d'an uwan ku."
Da sauri ta juya ta koma kan Bilal da ke kwance k'asa har yanzu, da gudu ta d'auko mayafin ta ta d'auke shi tasa mota suka bar gidan, asibitin da aka kai Haseenah ta kai shi, saida suka ciri tikitin ganin likita kafin suka samu aiki, bawan Allah saida aka saka mi shi k'arin ruwa sannan ya sabu bacci, kan shi na kan k'afafun Khadija ta na shafa kan shi, hawaye ta ke saboda tunanin irin halin da d'an ta ya shiga saboda wata tsinanniya a cewar ta, Habeeb dake ta faman kiran wayar Bilal dan su gaisa ne amma ba'a d'agawa, hakan ya sa ya kira Khadija sai lokacin suka san abin da ke faruwa, kafin ki ce kwabo asibitin ta samu hallarar 'yan biyar da mahaifiyar su, iya abin da ta sani kawai ta fad'a mu su, saida Bilal ya farka a bacci ne ya kora mu su jawabin duk abin da ya faru tun daga zuwan shi gidan har wannan lokacin, kuka Khadija ta yi sai Mama ke bata hak'uri, haka dai dare ya yi ko da ruwan suka k'are aka sallame su suka koma gida.
*Bayan fitar* Khadija sosai Aziza taji ba dad'i tare da jin nadama, amma bata gama gane halin da take ciki ba taji ihun Haseenah daga d'aki, sosai Haseenah ke murk'ususu tana kiran cikin da marar ta, waya Aziza ta d'auka ta kira Hajia ta fad'a mata, ana sallah isha'i Hajia ta zo gidan dan ganin lafiya, amma ganin irin azabar da take sha ya sa ta tambayi dalilin abun, Aziza ba ta yi magana ba sai Haseenah ce tace Khadija ce ta yi niyyar kashe ta yau a gidan, saboda kawai tace ta bata makullin mota tace Usman bai yarda ba haka kawai, ran Hajia ne ya b'ace saida Aziza tace " Amma fa likita tace za ta kai Bilal da ba shi da lafiya."
Cikin b'acin rai Hajia tace "Daga haka kuma sai tace saita nemi kashe ta, yanzu dubi ta'asar da take shirin yi."
Kama Haseenah ta yi suka tashi aka tafi asibiti, adaidaita na aje su suka shiga ciki, Aziza kad'ai ta lura da motar Khadija a k'ofar shiga amma banda su da basa hankalin su, saida akawa Haseenah éco aka duba cikin na ta, a cewar likitan "Cikin ta lafiyar shi k'alau, amma fa a kiyaye dan yanzu haka jijjiga ce ta sa take jin wannan ciwon, ayi hankali sosai in ba haka ba cikin biyu za ayi d'aya, ko dai cikin ya zube ko kuma ya bar mahaifarta ya koma bayan mahaifa, dan haka a kiyaye sosai."
Nan aka rubuta mu su magani za su koma gida Aziza tace "Hajia kinga motar aunty Khadija har yanzu su na nan, mu shiga mu ga jikin Bilal mana."
A tak'aice Hajia tace "In ke za ki shiga ban hana ki ba, ni ma ai marar lafiyar na kawo."
Ba dan ta ji dad'i ba suka wuce gida bayan sun siye maganin a pharmacie, Hajia da kan ta ta fad'awa Usman halin da ake ciki, kuma yanda take magana zai nuna ma ka cikin hushi take, shi ma dai tunzura ya yi har yace "Zan shigo garin gobe, ba zan yarda da wannan iskancin ba dan naga abun nata rashin mutumci ne."
"Ai kam dai gwara ka yi ka dawo, dan nima na fara gajiya da wannan al'amarin." Aziza da jikin ta ya yi laushi ce ta kalli Hajia tace "Amma Hajia fa makullin mota kawai ta amsa ta kai yaro asibiti, me ye laifi a ciki?"
"Yarinya ce ke Aziza, ba wai makullin kawai ta amsa ba, ta so ace tsotsayi ya gifta cikin jikin ta ya zube, dan haka gwara ya zo ya wa tubkar hanci."
Saida su Ashir suka rankosu har gida, canzawa Bilal kaya ta yi sannan ta kwantar da shi akan gadon ta, ita ma shirin baccin ta yi su ka kwanta bayan ta jima tana tofesu da addu'a.
*Washe gari da safe* Gidan kamar ana wani sabga, dangin Khadija sun hallara dan ganin jikin Bilal, dangin Haseenah ma da dangin Usman sun hallara dan ganin jikin ta, duk da kowa na b'angaren da ya kawo shi amma ka kan iya jiyo hayaniya ta ko ina, a lokacin ne kuma Usman ya diro garin ba dan ya shirya zuwa ba sai dan amaryar shi na wani hali.
*Allah kare k'aramin yak'i.*
17/02/2020 à 21:31 - 💋😘💋: 💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
*KALLON KITSE*
_(Ake wa rogo)_
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
_SAMIRA HAROUNA_
*Litattafan marubuciyar*
*1* _KAUSSAR_
*2* _D'AUKAR FANSA_
*3* _BA SO BANE_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI_
*6* _JIHADI_
*7* _K'ANGIN RAYUWA_
*8* _ITACE K'ADDARARMU_
*9* _KAWU NA NE_
*10* _MAATA_
*11* _KALLON KITSE..._
*SADAUKARWA GA*
_MATAN FARKO_ 🧕🏼 *(UWAYEN GIDA)*
🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_🤜🤛
```Fatan alkairi masoya```
_Bismillahir rahamanir rahim_
*28*
Saida ya fara ganin Haseenah ya tabbatar komai lafiya kafin ya nufo wajen Khadija da nufin bala'i, ya na shigowa falon sai ya yi sanyi ganin mutanen dake d'akin, a hankali yake takawa ya na kallon Bilal dake k'afafun Mama ta na bashi magani, Khadija ma da mamaki take kallon shi kamar ba ta tab'a ganin shi ba, da sauri ya k'arasa ya zauna gefen Khadija ya na fad'in "Yarima, bashi da lafiya ne? Me ya same shi?"
Shiru Khadija ta yi sai Mama ce tace "Bashi da lafiya ai tun jiya, amma da sauk'i sosai."
Hannu ya zura ya kamo shi kamar d'an shekara biyar haka ya rumgume shi a k'afafun shi ya na shafa shi yace "Yarima ba ka da lafiya? Ya jikin na ka da sauk'i ko?"
Da kai kawai ya ma sa alamar eh, rumgume shi ya yi a jikin shi ya kalli Khadija yace "Amma ya akayi ba ki kira ni kin fad'a min ba?"
Cikin hushi tace "Saboda kai ne silar shigarshi wannan halin, kuma ma naga me za ki yi mana idan na fad'a ma ka? Tunda ba damuwa ka yi damu..." Da sauri Mama ta kalle ta tace "Khadija."
Kallon Mama ta yi ta na kumburo baki, Mama ce ta d'ora da "Subhanallah, Khadija haka ki ka koma magana da mijin ki? Ki na hauka ne?"
Shiru ta yi sai Usman da ke murmushi ya kalle ta yace "Me ya sa ki ka yi tunanin haka? Taya zan zama sila baya bana nan."
Shiru kawai ta yi saboda Mama ta mata magana, mik'ewa Mama ta yi ta d'auki gyalenta ta yafa ta d'auki jaka ta kalli su Naseer dake gefe kamar sun zo neman aure tace "To sai ku tashi mu tafi ko, ko kuma nan za ku tabbata?"
Mik'ewa su ka yi a tare da d'ai d'ai suka bawa Usman hannu su ka yi sallama kafin su ka fita, ta na ganin fitar su ta kalle shi tace "Dama na bar Bilal gida ne saboda umarnin ka, amma ka sani ba zan sake wannan kuskuren ba wallahi, tunda dai na gama lura matarka ba imani ne da ita ba, sannan daga yau wallahi ba zan sake d'agawa kowa k'afa ba, duk wanda yace zai min kan kara to tabbas sai nai masa na itace."
Mik'ewa ta yi saida ta zo gaban shi ta karb'i Bilal ta d'ora a kafad'a saboda k'arfin halin kafin ta nuna shi da yatsa tace "Da nace kowa ina nufin kowa ma, ba sauk'i a al'amarin."
Za ta juya ne taji sallamar su Hajia da sauren yaranta mata biye da ita, tsaye ta yi ta na kallon su har su ka k'araso su ka zauna, Hajia ce ta kalli Bilal da ke kafad'ar ta tace "Kai namijin duniya ya jikin na ka?"
Wani irin mamaki ne ya bayyana a fuskar Khadija ta sunkuya ta aje Bilal ta kalle ta da kyau tace "Hajia, ya jikin shi fa ki ke tambaya? Hakan na nufin dama kinsan ba ya da lafiya amma shine bai samu kimar da za ku zo ku duba shi ba tunda ku ka shigo gidan nan, tunda rana fa na ke iya jiyo hayaniyar ku a gidan nan, amma sai yanzu za ku zo ku tambaye ni lafiyar shi, hum, to ba ni ku ka wa ba, kan ku kuka wa."
Juyowa ta yi ta d'auki Bilal za ta wuce d'aki Aziza tace "Aunty Khadija ga kayan shi in ji Haseenah."
Juyowa ta yi fuska a had'e tace "Bilal na da kayan da a shekara baya saka su, ku mayar mata ta mayarwa da bokan nata tace ba ma so."
"Khadija, wai baki da hankali ne? Ke kad'ai ki ka fi kowa baki anan da za ki zaunar da mu ki na fad'a mana magana, so ko ke kice dole ke ce akawa laifi kenan bayan duk abin da ki ka aikata, me ki ka d'auke ni ne da har za ki tsaya ki na fad'awa 'yan uwa na magana kuma daga ciki har da mahaifiya ta, ko kinsan da hushin ki na dawo garin nan? Amma shine za ki nuna ke ce ma akawa laifi, to ya isheki haka, maza wuce ciki zan zo na same ki."
Yanda ya ke maganar ne ya sa ta yi dariya tace "To ka had'iye ni mana kaga shikenan sai ka huta."
Ta na fad'a ba ta tsaya sauraren shi ba ta shige ciki da Bilal a hannu, tana shigewa Hajia tace "Haka kuma abin nata ya zama? Lallai mutum bashi da kama, yanzu waye zai iya cewa Khadija za ta yi abin da ta yi."
Rabi'a ce tace "Hum, dama ai sai anyi yunwa halin kowa ke fitowa."
"Gaskiya ne, yau na tabbatar da hakan." Cewar Hajia, Usman ne ya kalle su yace "Hajia ku yi hak'uri dan Allah, kar ku damu da abin da ya faru."
"Ya kar a damu, ba ka ji maganganun da ta fad'a mana bane, nan gaba mu ka san me za ta fad'a ko ta yi mana, za ta iya cewa ma Bilal d'an ta ne ita kad'ai."
Mik'ewa su ka yi su na fad'in "Sai anjiman ku."
Tafiya su ka yi Aziza ta koma wajen Haseenah, shi kuma d'akin Khadija ya koma, ya na zuwa ta kwantar da Bilal yace "Ya kamata kisan ina d'aga mi ki k'afa ne saboda abubuwa dayawa, amma naga sam kin kasa fahimta sai ma son wuce gona da iri, Khadija wannan fa mahaifiya ta da ki ka tsaya ki ka fad'a mata magana son ran ki, me ki ke ji da shi? Rashin kunya ko fitsara?"
Tsaye ta mik'e tace "Kalle ni da kyau kaga da me ya kamata ka kira ni."
Da yatsa ya nuna ta yace "Na zo ne dan na fad'a mi ki wani abu, wannan ya zama na k'arshe da hannun ki zai sake tab'a jikin Haseenah, in kuma ba haka ba wallahi zan d'auki matakin da ba lallai ya mi ki dad'i ba, kinji na fad'a mi ki."
"Haseenah? Haseenah fa ka ce? To in har kaga hannu na bai tab'a jikin ta ba ka tabbatar ba ta min rashin kunya ba, wallahi ko yanzu tace za ta min abinda ba zan d'auka ba ni kuma can ci uwar ta a gidan nan kuma a gaban ka."
Daf da ita ya matso cikin d'aga murya yace "Saboda ki nuna min kin rainani? Ban isa na fad'a mi ki kiji ba kenan?"
Kafin ta yi magana ya sake k'ure ta da fad'in "Bak'in ciki ki ke da ta samu ciki za ta haifa min wasu yaran? Shi ya sa ki ka yi k'ok'arin zubar mata da ciki, wallahi Allah ne ya ceceki cikin nan bai zube ba, da sai na sa kinyi aman duk wani abu da ke cikin ki kema."
Rasa abin fad'a ta yi saboda kukan da ke son taho mata, rab'awa ta yi da nufin shiga ban d'aki ya rik'o hannun ta ya nufi k'ofar fita da ita yace "Muke ki bata hak'uri, 'yan uwan ta ma na nan suna tsammanin jin hukunci daga gare ni, ba zan barki haka ba, amma da farko ki ba su hak'uri."
Jin wani sabon rainin hankali ya sa Khadija fizgo hannun ta da k'arfi tace "In kuma ka ga haka ta faru to tabbas ba ta hanyar aure aka haife ni ba."
Juyowa ya yi ya na kallon ta ita kuma ta gyara tsayuwa tace "Wallahi na rantse da sarkin daya busa min numafshi ko za ka kashe ni ba zan bawa uban kowa hak'uri ba, Usman." Ta kira sunan shi cikin d'aga murya ta d'ora da "Karfa ka yi tunanin sanin da ka min da, wallahi yanzu walkice ni daidai na ke da k'ugun ko wace shegiyyy..."
Marin da ya zabga mata ne ya sa ta fad'i gefe har gilashin ta na fita daga idon ta, dafe kunci ta yi ta d'ago kai ta kalle shi, cikin fitar hayyaci ya shak'o wuyan rigar ta ya mik'ar da ita tsaye yace "Wuce muje na ce."
Ba tate da tayi yunk'urin k'watar kan ta ba tace "Ba zan je ba wallahi, banga laifin da na yi ba da zan bawa wani hak'uri."
Wani marin ya sake kifa mata da k'arfi da ya sa Bilal zabura ya tashi zaune, sake dafe kunci ta yi ta na kallon shi dishi-dishi, da hannu ya nuna mata k'ofa yace "Wuce muje."
"Ba zan je ba." Ta fad'a ta na k'ok'arin tashi tsaye, a karo na uku ya sake gwab'a mata wani marin ya na fad'in "Ai kuwa za ki mutu kamar yanda ki ka ce, tunda taurin kai ne da ke."
*Lovely sister kin tuna ko? Ki ci gaba da hak'uri komai zai wuce da ikon mai kowa mai komai.*
Bilal na ganin haka ya sauko daga kan gado ya rik'e hannun mahaifin shi ya na hawaye yace "Abba dan Allah ka daina, ka bar dukan ta."
Ture shi ya yi gefe d'aya ya na fad'in "Kai bar ni na nuna mata na fita taurin kai, zuciya ai ba ki fini ba." Ya k'arashe da kifa mata wani marin, a tak'aice saida Usman ya mata lafiyayyun mari har guda takwas a kumatu kamar ya samu jaka, da ta kasa tashi ne gashi ba ta iya jin komai ba ta ganin komai ya sa take zaune har yanzu k'asa, cikin hargagi ya ke fad'in "Wai ba za ki tashi ba?" Ya fad'a ya na zura k'afa ya na kai mata hanb'ara, Bilal ne ya rik'e shi ta baya ya na kuka sosai ya na fad'in ya k'yale mi shi Mummyn shi, Usman kam ido sun rufe rai ya b'ace bai ma san me yake yi ba sai harbinta ya ke da k'afa ya na had'awa da hannu ya na nausarta, da sauri Bilal ya zo ya rumgume ta ya juyo da kan shi ya kalli Usman yace "Abba na tsane ka, ba na son ka, ka fita ka ba mu wuri, Allah saiya sakawa Mummy na."
Cak ya tsaya da hannun shi sama daga d'agawar da ya yi zai dake ta, duk da ya ji kalmar tsanar har k'asan zuciyar shi amma saiya basar ya nuna ta da yatsa yace "Yanzu hankalin ki ya kwanta da ki ka ji d'ana ya na fad'in ya tsane ni? To ki zuba ruwa k'asa kisha dan farin ciki, ni ma kuma Allah ne zai saka min da har ki ka yi sanadiyar da d'ana ya furta min kalmar tsana, munafuka kawai shed'aniya, kuma ki sani wallahi in har ki ka ce wannan halin za ki ci gaba da nunawa a gidan nan kenan, to ki na tare da wahala wallahi."
Juyawa ya yi ya fita, d'auko gilashinta Bilal ya yi ya saka mata, mik'ewa ta yi ta shige ban d'aki ba dan tasan in da take saka k'afar ta ba, zaune ta yi bakin bahon wanka ta kunna ruwa suna zuba ta fashe da kuka, tabbas yau tabbatar da Usman baya hayyacin shi tunda har zai iya mata wannan dukan a gaban d'an su, mutumin da magana marar dad'i ba ta tab'a shiga tsakaninsu ba amma yau har da kiran ta munafuka, ta jima zaune ta ci kukan ta kafin ta mik'e ta wanke idon ta ta kashe ruwan ta fito, lokacin fuskar ta har ta kumbura kamar an hura balam-balam, jakunkunanta ta d'auko ta d'ura duk wani abun buk'atar ta a ciki Bilal na kallo, hijabi ta saka ta kalli Bilal tace "Bilal."
Cikin muryar kuka yaron ya amsa da "Na'am Mummy."
Cikin muryar da tasha kuka tace "Tafiya zanyi Bilal, ka zauna gidan mahaifin ka dan ba na jin zan iya dawowa gidan nan, amma ka sani ina tare da kai kaji ko."
Da sauri ya taso yace "A'a Mummy, ni dai dan Allah ki tafi da ni, wallahi ba zan zauna nan ba, yanzu Abba ba ya so na, aunty amarya ma ba so na take yi ba, ni dai wallahi binki zanyi."
"Bilal ba zan iya tafiya da kai ba, ba wai dan ba na so na tafi da kai d'in ba, sai dai nasan mahaifin ka ba zai bari ba, ka tuna ranar ma da zan tafi shi ya hana na tafi da kai? To ka yi hak'uri ka zauna kaji, idan ba ka jin dad'in zaman nan sai ka ce ya kai ka gidan su Hajia."
Cikin kula yace "Ni dai ba na so Mummy, idan kuma ki ka tafi ki ka bar ni wallahi guduwa zanyi daga gidan nan."
Cikin sanyin jiki tace "Shikenan je ka had'o kayan ka."
Ya na fita ta zauna bakin gado ta zuba tagumi ta na fitar da wasu hawaye masu zafin gaske, ba wani jimawa Bilal ya dawo da k'atuwar jakar shi shima ya sanyo duk wani abun buk'atar shi, kallon shi ta yi tace "Ka d'auko kayan makarantar ka?"
"Eh, suna ciki." Mik'ewa ta yi ta kashe duk wutar d'akin ta kile da makulli suka fita, a hankali cikin sand'a ta isa ga k'ofar da za ta shigo da mutum falonta da falonshi ta kulleta kafin suka fita ta d'aya k'ofar, nan ma rufewa ta yi kafin tace Bilal ya kira mai gadi k'ofar gida sannan ya tsayar mu su da adaidaita sahu, ba wahala kam mai gadi ya shigo har in da take ya tsaya yace "Mai adaidaitar na k'ofar gida Hajia."
"Yawwa karb'i nan." Ta fad'a da bashi jakunkunan tace "Ka fitar mana da su muna zuwa yanzun."
"To Hajia." Ya fad'a ya na d'aukar jakunkunan ya jasu Bilal ma ya ja tashi jakar, saida ta lek'o ta hangi motar Usman alamar ya na gidan, saida taga ficewar mai gadi kad'ai ta fito ita ma ta fita, har an yiwa kayan nasu wuri dan haka za ta shiga mai gadi yace "Hajia, lafiya dai ko? Ko tafiya za ku yi ne?"
Juyowa ta yi ta kalle shi tace "Ka yi hak'uri Baba mai gadi, duk da dai abin da ya faru yanzun sirrine na gida na, amma kai ba yau muke tare ba, tunda na dawo sabon gidan nan na tarar da kai, tun Bilal na jinjiri, matsala ce ta faru da tasa dole sai na bar gidan nan na wani lokaci, ku yi hak'uri, na bar ka lafiya."
Ta na gama fad'a ta shiga adaidaitar suka wuce, da kallo ya bisu ya na fad'in "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un, ita kuma amaryar da abin da ta zo da shi kenan? Wannan wace irin jaraba ce, mata da mijin ta kullum cikin farin ciki, idan ka ji hayaniya to suna wasa ne kamar yanda su ka saba, amma yau gashi su na shirin rabuwa dalilin wata, kai Allah ya kyauta."
Usman na ciki shi da Haseenah bai san tsiyar da ake ba, ba jimawa kam adaidaita ya sada Khadija da gidan su, Mama na ganin su da kaya ta fara salati da sallalami, kai tsaye d'aki ta nufa ta aje kayan ta ta wuce d'akin ta, tashi Mama ta yi tabi bayan ta sai matan yan uwan ta ne su ka bisu da ido, matar Habeeb ce kad'ai ta iya cewa "Aifa lokacin ya yi."
Shiru sauran su ka yi dan suma kawunan nasu a rarrabe suke, kowa da b'angaren da yake saboda suma akwai uwayen gida akwai kuma amare.
Babu abin da Khadija ta b'oyewa maman ta duka ta fad'a mata, duk da taji ba dad'i sosai amma sai bata nuna mata ba, kallon maman ta tayi tace "Dan Allah Mama taimaka min da maganin ciwon kai."
Tashi kawai Mama ta yi ta d'auko ta kawo mata tasha ta kwanta, matar Mansur ta shigo d'akin dan su kwashi labari sai dai ta samu Khadija har ta fara baccin wahala da fuska har yanzu a sumtume, sam Mama ba ta fad'awa 'yan uwan ta ba ko a waya sai dare da suka dawo su ka tarar da wannan abin takaici, lokacin Khadija zazzab'i ya sake rufe ta, Naseer har da k'walla ya yi da ya kalle ta, yanda ya sunkuyar da kai ne ya sa Habeeb dafa shi, goge fuskar da ya yi ne ya tabbatar musu kuka yake, Bashir ne yace "Kai haba dai maza, kuka fa? Ai ba kai ya kamata ka yi kuka shi ya kamata ya zubar da hawaye."
Wasu hawayen ne suka sake taho mi shi yace "Yanzu domin Allah me ya sa Usman ya yi haka? Mufa mun bashi ita ne da tunanin zai kula da ita, me ya sa zai mana haka yanzu? Saboda kawai ana ganin ita marainiya ce mahaifin ta ya rasu."
Sun jima d'akin ta suna tattaunawa in da take kwance ta dunk'ule, saida dare ya yi suka tashi suka koma nasu dak'unan, saida tasha magani kafin ta sake kwantawa, sai dai ba ta yi bacci ba har aka kira sallah asuba, sallah ta yi ta sake komawa ta kwanta ta na istigfari tasbihi da hailala da hannun ta na dama.
Ko da Usman ya fahimci basa gidan haka kawai yaji bai wani damu ba, hakan ya sa ma da safe ko da ya je gida ya samu su Hajia da maganar ya kuma fad'a mu su kar suce za su je su dawo da ita, harda had'a su da Allah akan su barta harta shiga hankalin ta, Bilal kuma d'an shi ne ba ta isa ta raba shi da shi ba, amma malam yace sam ba da shi za ayi haka ba, a k'arshe ma tambayar su dalilin faruwar haka akayi, fad'an Hajia shine "Makulli Usman ya bawa Haseenah ta aje na mota da zai tafi, ita kuma ta tashi fita tace ta bata, shi kuma yace kar aba kowa idan za'a fita a fad'a mi shi zai aiko da wani ya kaisu duk in da za su je, shine ta turmushe yarinya da k'aramin ciki ta karb'i makullin, dalilin hka fa ya kusa sawa ta yi b'ari."
Duk da jin haka yace zaije ya dawo da ita gidan ta, kuma kamar yanda ya fad'a ya cika maganar shi, amma maganganu mabanbanta ya ci karo da su, musamman da suka fad'a mi shi har da duka, har d'akin Khadija aka mi shi jagora ya ganta kwance da k'arin ruwa a hannu, dan tunda ta yi sallah asuba zazzab'i ya sake rufe ta, hakan ya sa Naseer ya d'auko likita har gida aka dubata, sosai suka nuna mi shi b'acin rai da cewa ba za ta koma ba har sai Usman ya dawo hankalin shi, baiga laifin su ba kam dan ya sa dole wata rana zai neme ta, haka malam ya juya rai b'ace da kuma kunyar abin da ya aikata, tun a hanya yace Usman ya same shi gida za su yi magana, da "To Baba." Ya amsa.
*Ku na ganin zaije? Yanzu fa Haseenah ita kad'ai ce.*
Saida ya sake wanka ya shirya yace "Amarya ta zanje gida na dawo, amma ba zan jima ba kinji, ki kula da kan ki."
Kallon shi ta yi ta na k'ara rufe jikin ta da zanin gado tace "Gida kuma? Na d'auka d'azu ka ce min gida ka tafi, ya da wuri haka za ka koma."
Ya na gyara zaman hular sa yace "Eh wallahi Baba ne wai ya ke son gani na, amma na san ba zan jima ba ai zan dawo."
Shiru ta yi a zuciyar ta tace "To idan fa yanzu ma dawo da Khadija za su tafi? Dole na yi wani abu."
Shagwab'e fuska ta yi tace "Yanzu tafiya za ka yi ka barni a haka? Ba ka da matsala kenan tunda ka samu biyan buk'atar ka ko?" K'ok'arin saukowa ta fara daga kan gadon ta na fad'in "Shikenan ai ka tafi."
Matsowa ya yi kusan ta zai kamo hannun ta ta kubce ta shige ban d'aki, bakin k'ofar ya tsaya yace "Haba ke kuwa, kar ki yi hushi mana, kinfa san ba na son b'acin ran ki ko kad'an."
"Ahhhhhhh, wayyo Allah ciki na, marata." Fad'in Haseenah daga cikin ban d'aki, bai tsaya tunanin komai ba ya kutsa ciki ya same ta zaune dafe da ciki alamar fad'uwa ta yi, bai tsaya komai ba ya d'auko ta sai kan gado ya dire ta, kallon ta yake ciki da damuwa ya na rik'e da hannayen ta yace "Garin yaya ki ka fad'i haka? Haseenah karfa ki mana asarar kyautar nan da Allah ya bamu, kinfi kowa sanin lokacin da na d'auka ina fatan Allah ya sake bamu haihuwa, ina son na ga gidan nan ya cika da yara kuma ya zamana ke ce uwar su."
Yanda ya k'arashe maganar kamar zaiyi kuka ne yasa tace "Ka yi hak'uri dan Allah, ni ma santsi ne kawai ya kwashe ni, ban kula ba sai ji na yi na fad'i saboda rai na a b'ace yake."
Kallon ta ya yi yace "To me ya b'ata mi ki rai haka da har ki ke neman ja mana babbar asara."
Cikin turo baki tace "To ba kai ne ka ce zaka fita ka bar ni ba, ni kuma wallahi ba na so ka tafi, satin ka biyu fa baka gari, kasan dai dole munyi kewar ka mu na buk'atar ka a kusa da mu, shine kawai daga ka samu yanda ka ke so sai ka ce za ka fita."
Da rawar jiki yace "Ai dai fitar ce ba kya so ko? To na fasa, kin gani ma? Zan kira Baba na fad'a mi shi ya yi hak'uri zan je anjima, shikenan kinji dad'i?"
Dariya ta yi ganin ya cire hular shi da takalma ya fasa tafiyar, ko farfajiyar gida babu wanda ya lek'a a cikin su suna d'aki suna soyayyar su, hatta abinci sai dai ya kira Bilyamin ya siyo ya kawo mu su, haka dare ya yi amma Haseenah na jikin Usman, da ya yi maganar tafiya wajen Baba za ta fara shagwab'a wai zai barta ita kad'ai, haka ya k'arar da wunin na shi bai je kiran Baba ba kuma bai kira shi a waya ba.
Tunda malam ya ga shiru ya tabbatar da zargin shi na cewa akwai abin da ke damun Fodio, ganin har dare ya yi anyi shirin bacci ya sa malam samun Hajia a d'aki har ta fara bacci ya tashe ta, saida ta wartsake yace "Bacci fa bai kama ki ba, tashi ya kamata ki yi mu duk'ufa da addu'a, dan shakka babu Fodio ba kan shi d'aya ba."
Saida ta k'ara murza ido tace "Malam, ban gane ba, me ya ke faruwa da Fodio kuma?"
"Shiga gaba." Ya bata amsa kai tsaye kafin ya d'ora da "Na yi mamakin da ku ka kasa fad'a min gaskiyar abin da ya faru a gidan shi, kun fad'a min ta karb'i makulli da k'arfi, amma ba ku fad'a min ta karb'a bane saboda za ta kai Bilal asibiti, yaron da aka barwa Haseenah ya wahala saboda babu mahaifiyar shi nan, sannan shi kuma Fodio bai fad'a min ya daki Khadija ba, ke ma kuma ba ki fad'a min ba."
"Duka malam?" Ta fad'a da dafe k'irji, d'orawa ta yi da "Wallahi ban sani ba ni ma, bai fad'a min ba ko alama."
Gyara tsayuwa ya yi yace "Har da duka, kinga yanda ya kumburawa yarinyar nan fuska da kin tausaya mata, tun jiya ta na kwance babu lafiya har zuwa safiyar nan da na je gidan ana k'ara mata ruwa, wannan abun kunya da me ya yi kama? Kinga yanda ran 'yan uwanta ya b'ace su na cewa ba za ta koma ba si in ya zo ya nemi ta koma tare da alk'awarin ba zai sake tab'a lafiyar jikin ta ba, kuma ni banga laifin su ba ko kad'an dan su na da gaskiya."
Shiru Hajia ta kasa magana saida malam ya sake cewa "Na fahimci yarinyar nan ta na biyar shi da sharri, ba kuma alkairi bane ya kawota gidan nan, dan haka k'arya take tace za ta cutar da ahalina wallahi, ko da boka take yawo ni nan zanyi maganin ta, Allah ya fi k'arfin ta wallahi."
Kallon Hajia ya yi da zufa ta rufe ta yace "Ke ma ki taya d'an ki da addu'a."
Fita ya yi daga d'akin ita kuma ta k'ara gudun masuburbud'ar sanyin dake d'akin, ta jima bacci bai sake d'aukar ta ba ta na tunani akan abin da malam d'in ya fad'a, anya kuwa Haseenah za ta iya yin haka? Yarinyar da a zahirance ita ake cutawa, taya za ace kuma ta cutar da wani? Kai da kamar wuya gaskiya.
*Da kamar wuyar zata kassara ku.*
21/02/2020 à 19:15 - 💋😘💋: 💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
*KALLON KITSE*
_(Ake wa rogo)_
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
_SAMIRA HAROUNA_
*Litattafan marubuciyar*
*1* _KAUSSAR_
*2* _D'AUKAR FANSA_
*3* _BA SO BANE_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI_
*6* _JIHADI_
*7* _K'ANGIN RAYUWA_
*8* _ITACE K'ADDARARMU_
*9* _KAWU NA NE_
*10* _MAATA_
*11* _KALLON KITSE..._
*SADAUKARWA GA*
_MATAN FARKO_ 🧕🏼 *(UWAYEN GIDA)*
🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_🤜🤛
```Fatan alkairi masoya```
_Bismillahir rahamanir rahim_
*29*
Sai k'arfe *10:25* suka tashi daga bacci, Usman ne ya fara shiga wanka da tunanin ya gaggauta shiryawa dan ya fiya kiran malam, ya sakarwa kan sa ruwa kenan Haseenah ta shigo ban d'akin, bahon wanka ta cika da ruwa ta had'a sabulu a ciki ta cire d'aurin k'irjin ta, da k'arfi ta jashi su ka famtsama cikin bahon su biyu, dama abin da take so kenan, shi ya sa ma ta yi anfani da damar wajen b'ata lokaci suna wanka da 'yar shiriritarsu irin ta amare, sun d'auki lokaci kafin su ka fito haka nan ma wajen shiryawa saida su ka jima, suna fitowa falo cikin shiri ya kalle ta yace "Mummyn beby yau ma ba ki dafa mana komai ba fa, ya za mu yi kenan?"
Zaune ta yi akan kujera tare da d'ora k'afa d'aya kan d'aya ta d'auki masarrafar telebijin (remonte) ta kunna tace "To ai ina ganin ba sai na yi girki ba, tunda kaga amarci mu ke ci, ko ba haka ba?"
Zaune ya yi kusan ta ya na fad'in "Kuma fa da gaskiyar ki, dan mafiya yawancin lokuta idan na dawo daga tafiya sai dai muje cin abinci kawai."
Cike da izza ta na karkad'a k'afa ta kalle shi tace "Oho, kenan aka ake yi, amma shine ni ba za ka iya d'auka ta ba muje?"
Waya ya ciro daga aljihu yace "Yanzu dai bara na fara kiran Bilayamin ya kawo mana na karin kumallo, anjima da dare sai muje mu ci ko, hakan ya mi ki?"
"Ba damuwa." Ta fad'a cike da k'asaita, ta na ji ya bawa Bilyamin sallahun abin da suke buk'ata su ci, bayan d'an lokaci Bilyamin ya iso da abincin, ya na karb'owa kai tsaye kan teburi ya nufa da shi ya d'auki faranti ya zuba ya kalle ta daga in da ta ke zaune yace "Madame ki taso abinci na jiran ki."
Tashi ta yi cikin tako d'aya bayan d'aya ta isa, zaune ta yi akan cinyar shi ya dinga saka mata abincin a baki, saida su ka gama ya tashi zai fita tace "Babban mutum ni fa gida na ke so ka aje ni, idan za ka shigo da dare sai ka biya mu taho tare."
"Gida kuma?" Ya tambaya da mamaki, "Eh, gida." Jim ya d'anyi dan gaskiya a tsarin shi ba'a mi shi haka ko kad'an, ace sai yanzu ne kawai za ta fad'a masa ta na so ta fita kuma yanzu yanzu saboda raini, had'e fuska ya d'anyi yace "Ki yi hak'uri mana Mummyn beby, ki bari har gobe sai kije."
Yamutsa fuska ta yi tace "Gaskiya yanzu na shirya tafiya, in kuma ka hana ni wallahi kuka zan kwana ina yi a gidan nan." Ta na gama fad'a ta mik'e ta nufi hanyar falon ta, ganin fa da gaske ranta zai b'ace ya sa ya yi saurin rik'o ta ya had'a da jikin shi yace "Shikenan to naji, ran gimbiya ya huce, je ki d'auko hijabin ki sai mu tafi."
Cikin farin ciki tace "Da gaske kake?" Cike da tabbatarwa yace "Sosai ma, ai ba na da wani abu da ya fi min ke mahimmanci, zanyi hidimar ki kafin na yi tawa, ki yi sauri ki je."
Cikin d'an lokaci ta d'auko hijabi da jaka da takalma duk kala d'aya suka tafi, ba jimawa ya sauke ta gida tare da bata kud'i kafin su ka yi sallama, mahaifiyar ta kad'ai ce a gidan a farfajiyar gida zaune, bayan sun gaisa sosai suka fara tab'a hira, anan ne mahaifiyar ta tambaye ta ko ta na anfani da magungunan ta, bud'ar bakin ta cewa ta yi "Eh, ina sha Mama, amma fa akwai matsala."
"Matsala kuma? Tame?"
Cikin sanyin jiki tace "Mama wannan layun da aka aje na duba su ban gansu ba, kuma gashi har yanzu ana tsorata ni a cikin dare."
Da al'ajabi dattijuwar tace "Toh! Amma abun da mamaki, to ina suke? Kuma kin tabbatar an aje su in da ki ka duba?"
"Wallahi Mama wajen ne, su aunty Mariya fa da kan su su ka aje su, amma da na duba babu komai a wajen."
"Toh." Ta fad'a ta na girgiza kai kafin tace "Lallai wannan abu ya wuce duk in da ake tunanin shi, amma bari Baban ku ya shigo sai na fad'a mi shi komai."
Sosai ta ji dad'in wannan wunin da ta yi a gida, gashi ana ta bata kulawa a matsayin ta na mai k'aramin ciki, sai abin da take so ake bata ta ci, har mahaifin ta ya zo aka fad'a mi shi abin da ke faruwa, a cewar shi ta kwantar da hankalin ta zai sake karb'o mata wasu, sannan ta ci gaba da addu'a komai zai wuce.
A b'angaren Khadija kam ganin jikin ya k'i kyau ya sa Mama cewa "Khadija."
"Umm." Ta fad'a ta na d'an gyara kwanciyar ta, "Khadija ba ki da ciki kuwa?"
Murmushi ta yi tace "Ciki Mama? A'a, ba na da komai wallahi, kawai dai zazzab'in wahala ne."
"To Allah ya tabbatar da alkairi." Cewar Mama, Bilal ne ya shigo da sallama ya na cire jakar makarantar shi, kusan maman shi ya je ya sumbace ta da fad'in "Mummy ya jiki? Kinji sauk'i?"
"Na ji sauk'i yarima, har kun taso?" Saida ya fara cire rigar shi yace "Eh Mummy, kawu Ashir yace na mi ki sannu da jiki ba zai shigo ba ya na sauri."
Mama ce ta katse shi da cewa "Kai d'auki tarkacan kayanka ka wuce da su d'akin ka, kar ka kuskura ka min tsirara a tsakiyar falo."
Matsowa ya yi kusan ta ya yi tsaye yace "K'arasa cire min kayan ma in ki na son samun lada."
Rufe fuska ta yi tace "Kai b'ace min da gani kaji ko."
Fad'awa ya yi jikin ta ya sumbaci kumcinta ya na fad'in "Ina son ki Hajia ta."
Rumgume shi ta yi ita ma tace "Ni kuma ba na son ka yau, dan nasan akwai abin da ka ke so waje na."
Kallon ta ya yi yace "Me ki ka dafa yau?" Hararan shi ta yi tace "Uhum, nifa na san za'a rina dama, ina ka fito ci ina zaka ci, to wake na dafa."
Dariya Khadija ta yi tace "Mama ta na so ta sake kumbura ma ka ciki ne."
Juyowa ya yi ya kalle ta yace "Kema kin zama aunty amarya muguwa?"
Daruya suka saka sai Mama ce tace "Ai ni mugunta ta ma sai tafi ta ta, dan kuwa idan ka gama ci ba ruwa zan baka kasha ba, sai dai na ba ka kwanan nan fura ka kora da ita."
D'aukar kayan shi ya yi ya nufi d'aki ya na fad'in "Kuma idan na mutu ke ce za ki fara zubar da hawaye."
"To ba dole ba, na rasa miji na uban 'ya'ya na, idan kai ma na rasa ka ai zan shiga cakwakiya."
Usman ya je gida bayan ya aje Haseenah, Hajia kad'ai ya samu dan rana ta take sosai zaiyi wuya ka samu namiji gida a wannan lokacin, bayan sun gaisa ne Hajia tace "Amma me ya hana ka zuwa tun jiya da aka kira ka?"
Cikin rashin gaskiya yace "Wallahi Hajia wani d'an aiki ne ya taso min, kuma yarinyar nan ba ta ji dad'i ba, saida ma na kai ta asibiti aka rubuto mana magani."
_Daga cikin bala'in da asiri ke iya jawa mutum akwai k'arya, zai iya k'arya dan ya kare kan sa ko kuma wanda ya ke so, akwai rashin kunya ga wanda baya hayyacin shi, abune mai sauk'i miji ya tub'ewa mata kayan ta ya mata wulak'anci a gaban 'ya'yansu, kad'an ne daga aiki sihiri daina ganin girman wanda ka ke ganin girman shi, akwai wasa da addini wanda za ka ga wani ya na sakaci da shi, illolin fa dayawa yan uwa, fatan mu Allah ya k'ara tsarkake mana zuk'atanmu._
Take Hajia ta fahimci k'arya ya fad'a, amma saboda kunya ta dake tsakanin uwa d'an fari sai kawai ta share tace"Allah ya sawak'e, gashi kuma yanzu malam d'in har ya fita, sai dai in za ka same shi can shagon."
Cikin sunne kai yace "Ba damuwa sai na je can d'in ai."
Ba tare da ta kalle shi ba tace "To ya maganar Nura, ya fad'a min sunyi magana da Khadija kuma tace ka amince, amma a bari sai ka dawo, gashi kuma ka zo ba ka ce komai ba."
"Eh Hajia, ya na ina ne Nuran?"
"Ya na shago mana."
"Shikenan zan kira idan na fita saiya same ni ko can shagon Murtala ne."
Cikin had'e tafukan hannayenta tace "Hakan ma ya yi."
Kallon ta ya yi yace"Hajia me zai hana ku je ku d'auko Bilal?"
Sai lokacin ta kalle shi tace "Ban gane na je ba? Kai me zai hana ka tafiya? Kuma ma ka na nufin ba za ka je ka dawo da mahaifiyar shi ba kenan?"
Cikin b'acin ran an ambaci sunan Khadija yace "Hajia ni babu in da zanje, ita ta tafi saboda ta na so, dan haka taje can ta k'arata, ni yaro na ne kawai matsala ta."
Karo na farko a rayuwa da Hajia ta iya d'agawa Fodio murya, cikin jin haushi tace "To ba zan je ba, ranar da ka shirya ganin d'an na ka sai kaje ka d'auko shi da kan ka."
Kallon ta ya yi shima, amma saboda ran shi a b'ace ya ke da maganar Khadija sai kawai ya mik'e cikin kumburo baki yace "Ni zan wuce, sai anjima."
Da kallo kawai ta bi shi har ya fita daga gidan, girgiza kai ta yi ta na mamakin wannan canjin daga Fodio, mik'ewa ta yi ta shiga d'aki ta na fad'in "Ai kuwa da alama gaskiya malam ya fad'a, amma koma menene zan wa tubkar hanci."
Daga nan wajen malam ya zame, k'ofar shagon ya samu malam zaune akan bacci shi da wani suna hira, har k'asa ya durk'usa ya gaishe su kafin malam ya sallami waccen, mayar da kallon sa ya yi kan Usman da ke durk'ushe yace "Fodio sai yanzu ka zo kiran nawa? To nagode."
"Wallahi Baba..." D'aga mi shi hannu ya yi alamar ba ya son ji kafin ya d'ora da "Jiya na je gidan su Khadija, kuma naji duk abin da ya faru, Fodio ka bani mamaki sosai da na ji ance wai ka d'aga hannu ka daki Khadija, wannan abun kunyar har yaushe da irin shi, duka! Kai a matsayin ka na mai hankali da ilimi, a shekarun ku na k'uruciya haka ba ta faru ba sai yanzu da girma ya fara riskar ku, wanda ya kamata ace yanzu ne soyayya take da tausayin juna, amma ace ka dake ta akan abin da ma k'arya ake mata da sharri, kawai rud'in zuciyar ka ne ka biyewa da kuma wata banzar hud'uba da wasu sakarkari suka ma ka, kasan me ya sa ta karb'i makullin motar? To saboda ta kai yaron ka asibiti ne, yaron da ya wuni da yunwa alhalin ya na gidan uban shi wanda ke wadace da kayan abinci sama da na shekara d'aya, amma wai akan hakane har ka d'orawa baiwar Allah laifi har ka iya dukan ta, ni ko a gani na ko taka Haseenah ta yi ta mayar da gabanta gabas ta yanka ta da wuk'a za ka iya mata uzuri, uzurin kuwa shine za ka duba dalilin da ya sa ta yi haka tunda ita uwa ce, amma ba komai, ka je gidan ka gani yanda ka lalata mata fuska da rashin hankalin ka, tace ba za ta dawo ba kuma na yarda da abin da ta fad'a, dan haka kaje kai da amaryar taka ku cinye kan ku, amma ka sani wallahi Fodio ina jin tsoron ranar da za ka yi nadama, dan alamu sun nuna *kallon kitse ne ka ke wa rogo*, tashi ka bani wuri."
A hankali Usman ya d'ago kai ya kalle shi tabbas ran shi ya b'ace sosai, cikin taushin murya yace "Dan Allah Ba..."
"Nace ka tashi ka bani wuri ko." Cewar Baba, mik'ewa ya yi ya juya zai shiga mota malam yace "Ji nan." Juyowa ya yi ya matso ya sake zubewa durk'ushe, d'orawa ya yi da "Har yanzu ita matar ka ce, kuma d'an ka ya na tare da ita, ban kuma yarda ka ce za ka d'auko yaron nan ba saboda banga alamar zai samu kulawa ba, dan haka umarni ne daga gare ni ya zama wajibi a wajen ka kai mu su kayan abinci da basu kud'in da za su yi sauran buk'atun su, ka ji da kyau?" Ya fad'a da kama kunnen shi.
Cikin sunkuyar da kai Usman yace "Na ji Baba."
"Tashi ka b'ace min da gani." Cewar malam ya na gyara zaman shi, tashi ya yi ya shiga mota ya wuce kamar zai fasa ihu saboda sharudd'an malam, amma kuma ba yanda zaiyi dole ne ya yi hakan d'in.
Yamma sosai Haseenah na kwance d'aki ita kad'ai Mariya ta kira ta, bayan sun gaisa ne take tambayar "Wai ni kam ya ku ka kare da rigimar ku da matar nan? In ce dai Usman ya d'auki mataki?"
Wata shak'iyar dariya ta yi tace "Ai tuni ta kama gaban ta, yanzu haka ni kad'ai ce a gidan, kwananta biyu yau ba ta gidan."
Daga d'aya b'angaren Mariya tace "Ke Haseenah! Da gaske ki ke?"
"Eh mana, zan mi ki k'arya ne?"
"A'a, amma Haseenah ki na ganin abun baiyi yawa ace ta bar gidan?"
"Baiyi ba, tunda ba ni na fitar da ita ba, bansan akan me su ka tattauna ba da har ta bar gidan, kuma shi ma ba na tunanin shi ya kore ta tunda har na ji yace tunda haka ta zab'a matsalar ta ce."
Cikin sanyin jiki Mariya tace "Toh, yanzu me ye abunyi? Ba za ki bashi hak'uri ba ya dawo da ita tunda ya na jin maganar ki yanzu."
Ba tare da tunanin komai ba tace "Abin da na ke so yanzun bai wuce ki zo gida ki same ni ba na baki kud'i ki kaiwa malamin nan ya sake mana wani aikin."
"Wani aiki kuma?" Ta fad'a da k'arfi, cikin sassauta murya tace "Idan fa ta dawo da matsala, so na ke kawai ta ci gaba da zama acan har mala'ikan mutuwa ya same ta."
Cike da gargad'i Mariya tace "Ke Haseenah ba ruwa gaskiya, me ya sa za ki yi haka? Me ya yi zafi? Na ga dai Usman ne kuma kin same shi, ina ganin ai zafi idan ta na gidan za ki fi k'unsa mata bak'in ciki, amma a dawwamar da ita a gidan su gaskiya abun ba dad'i."
Cikin gaggawa tace "Kinga, kedai idan kin samu dama ki zo gidan ki same ni sai muyi magana."
Shirun da Mariya ta yi ne ya sa Haseenah cewa "Ki na ji na?"
Abin da ta lura a lamarin na Haseenah shine akwai alamun rashin kunya, amma saita dake tace "Shikenan na ji, idan na fita gobe siyan kaya zan biyo."
"Ok." Kawai ta fad'a ta kashe wayar, nan ta ci gaba da zama har saida aka kira sallah magrib ta fito, kuma kamar yanda su ka yi da Usman bai dawo sai bayan isha'i, lokacin ta shirya sosai dan dama da kayan kwalliyar ta a cikin jaka, daga nan restaurent *Kebab* suka nufa cin abinci, rayuwa kenan, rayuwa ta juyowa Haseenah kam yanda ta ke so, gashi kuma ta na garata son ran ta, daga nan ma *plaza* su ka wuce suka siyi ice crime da sauran kayan mak'ulashe kafin su ka wuce gida, wangale k'ofa mai gadi ya yi amma ko kallo bai ishi dukan cikin su duk da gaisuwar da ya ke mu su, girgiza kai ya yi cike da takaici kafin ya rufe k'ofar.
*Washe gari* bayan fitar Usman Mariya ta zo gidan, bayan Haseenah ta bata kud'in ta mik'e za ta fita, gwangwanin madara ta gani na *lacstar* aje, kallon ta ta yi tace "'Yar k'anwar tsakura min mana ko a leda ne na d'an kaiwa 'ya'yan ki."
Cikin b'acin rai tace "Ba fa na san haka gaskiya, jiya ne fa na fasa madarar nan, idan na ce na dinga rabarwa ai ba za ta min ko sati ba."
Waro ido ta yi tace "Sati fa? Yanzu wannan sai ki shanye ta a sati ke kad'ai?"
Wata irin dariya ta yi kafin tace "Ai kamar kunu haka nake damata ina sha, kuma shine yace ta zama abinci na saboda ya na son ganin yaron da zan haifa kamar d'an turawa." Ta k'arashe da shafa cikin ta, tab'e baki Mariya ta yi tace "Yanzu ni dai sammin na tafiya ta."
Saida taja tsaki kafin ta samo 'yar leda ta zuba mata cokali uku ta mik'a mata ta na fad'in "Karb'i nan ta isheki, ba na so yace ina almubazzaranci da kaya wallahi."
Ganin 'yar madarar da ta zuba mata ya sa ranta b'acewa ta aje tace "Ki had'a kawai kisha, Allah ya raba lafiya."
Ko a jikin ta ita kam har suka fito farfajiyar gidan Mariya tace "To ai kya bani ko na adaidaita ko?"
'Yar k'aramar jakar hannun ta ta nuna mata tace "Kin ganta wallahi k'ananan kud'i a ciki ita ce jaka biyu (maybe dubu d'aya yanzun, dan farashin kud'in ya sauya), amma ki bari idan ki ka dawo daga wajen malam d'in saina baki."
Saida ta kalle ta sama da k'asa ta fice ko sallama ba ta mata ba, tun a hanya Mariya ta yanke hukuncin ba za ta je wajen malam d'in ba tunda ta lura iskanci ne abun na Haseenah, dan haka ma ta wuce gida kai tsaye ta fara tunanin abinyi da kud'in wanda zai anfane ta, a k'arshe ma dai jarin ta ta k'arawa yawa wajen k'ara siyo wasu kayan gwanjo.
Yamma lik'is saiga Bilyamin ya sallama gidan su Khadija nik'i-nik'i da kayan abinci da na masarufi, hakan baiwa mutanen gidan dad'i ba saboda a ganin su za su iya ciyar da kamar Khadija d'ari ma bare ita kad'ai, amma da Mama ta fahimtar da su sai suka mayar da wuk'ak'en na su, in da Khadija kuma tunanin ta kenan ba zai zo ba ya na nufin na yi ta zama a gida.
Gida Usman ya koma dan sanar da su ya tattauna da Nura kuma za su je neman masa aure, har d'aki ya samu iyayen na shi ya sanar da su yanda ake ciki, ya d'an jima suna tattaunawa akan lamarin kafin ya fara yunk'urin tafiya, "Karb'i nan."
Cewar malam, kallon malam ya yi ya kalli kofin hannun shi, ruwa ne dai fari k'al da su, kallon malam ya yi yace "Baba wannan fa? Na miye?"
"Karb'i kasha, na tsari ne." Ya fad'a ba alamar wasa, hannu ya sa ya karb'a ya yi bismillah ya kifa kai ya shanye, aje kofin ya yi ya musu sallama ya fita, bayan shi Hajia ta biyo saida ya zi gaf da d'akin ta tace "Bismillah nan." Saboda ba za ta kira sunan shi ba, bayan ta kawai ya bi suka shiga, ya na shiga ta mik'o mi shi roba da nono a ciki da abun magani tace "Shanye ka bani roban, kuma ka hi bismillah, sannan kasha zuciyar ka d'aya ba tare da tunanin cutar da wani ba ko wata."
A raunane ya kalle ta yace "Hajia shi kuma wannan na miye?"
Wani kallo ta watso masa amma ba tace komai ba, sanin ma'anar kallon ya sa ya kifa kai nan ma saida ya shanye kad'ai ya mik'a mata robar ya mata saida safe ya fito, haka ya d'auki hanya ya na tunanin abin da iyayen shi ke nufi da shi, da haka ya isa gida ya samu Haseenah yau dai ta yi girki kam, amma badan ranshi na so ba ya ci abin da ta dafa d'in har suka kwanta.
Bayan tafiyar shine Hajia ta ji kamar ta yi kuskuren rashin sanar da shi wani abu, amma ta yi niyyar fad'a mi shi gobe da safe idan ya zo, sai dai kuma ta makara kam, dan Usman ya jima baiyi bacci ba ya na dafe da cikin shi, da Haseenah ta tambaye shi kuma bud'ar bakin shi cewa ya yi "...
_Mu tara a shafi na gaba insha Allah._
*Ku yi hak'uri da ni mutane na abisa jinkira na, hakan na faruwa ne saboda sauyawar yanayi na.*
~*LUVE U ALL*~🥰😘
23/02/2020 à 13:03 - 💋😘💋: 💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
*KALLON KITSE*
_(Ake wa rogo)_
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
_SAMIRA HAROUNA_
*Litattafan marubuciyar*
*1* _KAUSSAR_
*2* _D'AUKAR FANSA_
*3* _BA SO BANE_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI_
*6* _JIHADI_
*7* _K'ANGIN RAYUWA_
*8* _ITACE K'ADDARARMU_
*9* _KAWU NA NE_
*10* _MAATA_
*11* _KALLON KITSE..._
*SADAUKARWA GA*
_MATAN FARKO_ 🧕🏼 *(UWAYEN GIDA)*
🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_🤜🤛
```Fatan alkairi masoya```
_*Lubabatu Shehu shayi*, ina ganin sak'onninki sosai, lallai ke masoyiya ce ta hak'ik'a, tun a gidan Raheenat muke tare, kuma gashi har yanzu kina tare dani a gida na na kallon kitse, Allah ya bar k'auna._
*KALLON KITSE FAN'S 1&2*
💑 _Wannan sadaukarwar taku ce, kuyi yanda kuke so da ita._💑
_Bismillahir rahamanir rahim_
*30*
"Wallahi kawai wani kindirmu ne Hajia ta bani nasha, gaba d'aya ya na neman lalata min ciki ma." K'aramin tsaki ya yi, ita kam da mamaki tace "Kindirmu kuma? Haka kawai?"
Kamar wanda aka takura dole yace "Ina jin ko magani aka saka a ciki kome, ban dai sani ba ni dai kawai ya lalata min ciki sai tayar min da zuciya yake."
Cike da kissa ta shafo shi tace "To in hakane kar ka sake sha mana, tunda ya na tayar maka da zuciya, zai iya saka ka amai ma fa."
"Ina tunanin haka nima." Ya fad'a ido rufe, kallon shi ta yi tace "To wai ma maganin meye aka baka? Ba ka da lafiya ne dama ban sani ba."
Bud'e ido ya yi ya kalle ta yace "Ke kar ki tsora ta, lafiya ta k'alau mana ke shaida ce, tace dai ko maganin tsarin jiki ne da kuma...mtss na manta dai, kawai share."
Tashi tayi zaune ta na kallon shi idon shi rufe, tabbas in dai har hakane to iyayen shi sun fara hango wani abu kenan, d'aukar mataki shine abin da ya kamace ta kawai, dan haka tace "To beby in hakane me zai hana ka karb'o maganin, kaga sai ka rik'a sha anan zaifi da sai kaje can, koya ka gani."
Cike da damuwa yace "Kar ki damu kan ki, ni fa ba wani shan shi zan dinga yi ba, ina addu'a na tsarin jiki hakan ma ya isa, kawai ki rabu da su, kinsan tsofaffin nan da tame-tame."
Murmushi ta yi tace "Duk daha beby, idan ma ba za ka sha ba ai sai ka karb'o shi, dan in har ya na wajen su to ba fashi sai ka sha shi ko da za ka mutu ne."
Shiru ya yi ya na tuna lokacin da ya tambayi Hajia amma ta yi banza da shi, hakan na nufin dole dai ya sha ba makawa, dan haka yace "Ba tabbacin za su k'ara bani, amma in har sun bani na sha to zan karb'o shi daga wajen su na taho da shi."
"Gaskiya kam, da ba zan so wani abu ya samar min miji ba uban 'ya'ya." Ta fad'a ta na gyara kwanciyar ta, daga haka babu wanda ya sake magana har bacci ya d'auki dukan su.
*Yau kam* Alhamdulillah Khadija ta tashi jiki da sauk'i sosai, da kan ta ta gyara d'akin ta da na Bilal da ma na Mama, zuwa k'arfe goma kuma ta fita madafar da matan gidan ke aiki, da kan ta ta fara girkin rana kafin matan yan uwan ta suka fito su ka kama aka k'arasa, *12:10* yaran su ka fara shigowa da sallama wasu kuma da gudu, kowa wajen tashi uwa ya nufa kafin suka wuce d'aki dan cire kaya, lokacin ne Khadija ita ma ta shiga d'aki dan ta yi wanka ta yi alwala, ta na d'aure da k'irji za ta shiga ban d'aki wayar ta tayi k'ara, dawowa ta yi dan d'auka amma har ta tsinke, d'aukar wayar ta yi ta duba mai kiran, sunan k'awar ta ne Kaltume, aje wayar ta yi da niyyar idan ta fito ta kammala za ta kira ta, har ta aje ta yi sauri ta sake d'auka saboda idon ta da ya sauka kan kwanan (date) wata, dubawa ta yi da kyau taga tabbas yau wata na da kwana *21*, kai da kawowa ta fara yi tsakiyar d'akin ta na tunanin yanda ta kasa ankara da lokacin al'adarta har wata ya ja haka, sai lokacin kuma ta iya tunawa fa tunda Usman ya yi aure ma bata sake ganin jinin ta ba, to me hakan ke nufi? Ta tambayi kan ta.
"Kenan ciki gare ki kamar yanda Mama ta tambaya?" Da sauri ta zo gaban madubi ta janye d'aurin k'irjin ta tana shafa marar ta, tabbas sai lokacin kad'ai ta iya fahimtar tudun da mararta ta yi, a hankali ya fad'a kan gado ta yi zaune ta rufe ido, wasu hawayen farin ciki ne suka zubo mata ba tare da sanin ta ba, hannu ta sa ta share ta d'aga hannu sama ta furta "Alhamdulillah Allah, Allah kaine Allah, kuma kai ka ce mu rok'e ka za ka amsa mana, Allah nagode ma ka abisa wannan baiwar da ka min, Allah ka tabbatar min da alkairi."
Saukowa ta yi daga kan gadon ta shiga wanka, da sauri ta k'arasa ta fito ta saka kaya ta yi sallah, gyalen ta ta saka ta d'auki jaka tasa takalma ta fito, da kallo Mama ta biyota tace "Ke kuma ina zuwa haka da rana patsal-patsal haka?"
Kasancewar duk matan gidan na d'akin ya sa ta matsa kusan amaryar Ashir tace "Duk cikin nan ke ce babba, dan haka ke ce zan iya fad'awa dan ba na jin kunyar ki."
Rad'a ta mata a kunne kafin ta fice daga d'akin da sauri, dariya amaryar Ashir ta yi ta kalli Mama tace "Mama wai kinsan me?"
"Sai kin fad'a mana zan sani." Cewar Mama, saida ta jinjina kai tace "Ai Mama sai kin bani goron albishir kafin na fad'a."
"Ita goron ki ka bata kafin ta fad'a mi ki? Ai naga kyauta ta fad'a mi ki."
Dariya matar Bashir ta yi tace "To ai Mama shugaban k'asa ya hana aikin banza."
Tab'e baki Mama ta yi tace "To can ku k'arata ku da shugaban k'asar na ku, ku rik'e sirrin ku ba na son ji."
Dariya amaryar Ashir ta yi tace "Mama Khadija fa cewa ta yi ta na zargin ta na da juna biyu, yanzu ma za ta je asibiti ne a tabbatar mata da gaskiya."
Waro ido Mama ta yi tace "Ke *Safiya* ba na son k'arya, da gaske ki ke?"
"Wallahi kuwa Mama haka ta fad'a."
Wani murmushin farin ciki Mama ta yi kafin tace "Allah ya tabbatar da alkairi, *wani hanin ga Allah baiwa ne*."
"Hakane Mama." Suka amsa da shi.
Khadija na fita cikin sauk'i ta samu adaidaita sahu ta kai ta *Clinique tattali*, kamar yanda ta yi tunanin kam hakane ta faru, dan kuwa ta samu k'awar ta ce akan aiki mai sunan *Maryama*, kasancewar babu mutane a asibitin ya sa suka fara tab'a hira kafin ta fad'a mata abin da ya kawo ta, nan ma saida aka sha wata hirar kafin ta mata gwajin fitsari, ko da ta duba dan ta ga sakamakon Khadija tace"Dakata."
Kallon ta ta yi ita kuma tace "Kawai ki min murmushi idan har gaskiya ne tunani na, in kuma babu to ki had'e rai."
Dariya Maryama ta yi tace"Kaga wani sabon gwajin ciki kuma, to bara na gani." Ta na dubawa kam ta ga ciki dai ya tabbata, haba wa ai sai ta washe mata hak'ora tace "Ke kiyi farin ciki, wallahi ciki ya tabbata, kai Khadija na miki murna wallahi."
Rumgume juna su ka yi cikin farin ciki, ba ta jima ba ta mata sallama ta bar asibitin, daga nan kuma gidan k'awar ta ta wuce Kaltume dan sanar da ita, da shigarta gidan ta ji sun k'ara birge ta abun sha'awa, dan farko *Madina* kishiyar Kaltume ta so ita ma ta yi kalar nata iskancin, sai dai ina tuni Kaltume ta nuna mata ruwa ba sa'an kwando bane, sannan shi kan shi mijin na su *Alhaji Ibrahim* yasan da ya fad'a tarkon Kaltume da babu mai k'watar shi idan ba ubangiji shi ba, a k'arshe dai Madina ta fahimci tazara mai tsayi ce tsakanin su da ita dole ta hak'ura, musamman da ya zama babu mai iya bata shawara ga yanda za ta mu'amulanci rayuwar gidan ta, cikin sauk'i sai suka zauna lafiya kamar ba kishiyoyi ba, yanzun ma saida suka gaisa sosai ita da Khadija har suka fara tab'a hira kafin Kaltume tace su je daga ciki, nan fa ta fad'a mata ta na da ciki kar kuso suji bud'ar da Kaltume ta rabka har k'ofar gida, tsabar nuna farin cikin ta ya sa nan take ta bawa yara kud'i tace su siyo alawa mai tsada su rabawa yara, anjima kuma da yamma za ta yi fanke na sadaka da godiya ga Allah, Khadija dai kallonta kawai tale ta na k'ara k'aunar Kaltume, tabbas a rayuwa bata da yar uwa mace amma Kaltume ta zame mata komai, har kusan yamma kafin ta bar gidan saboda kiran ta da Mama ta yi, haka ta koma gida nan ma Mama da aka k'ara tabbatar mata gaba d'aya gida ya d'auka Bilal zai samu k'ane ko k'anwa, in da Mama ke binshi da gwalo ta na fad'in "Tuzurun wofi, yanzu dai sai naga k'afafun uban wa za ka hawa ko kuma wanda zaka wa shagwab'a, dama can rashin ganin wani ne a gaban ka ya sa ka wannan iskancin."
Shi kam cewa ya ke to sai me, ai k'ane za'a mi shi dan haka bai damu ba, kuma idan ya na son hawan k'afafu ga nata nan zai hau, da haka har 'yan biyar su ka zo suma suka d'ora nasu farin cikin ana addu'ar Allah ya sauketa lafiya.
*Mu ma dai munce ameen.*
Kamar kullum Usman ya je gaishe da iyayen sa, kuma kamar yanda ya saba riska yau ma malam baya nan, sai dai ya bar sak'on wannan ruwan addu'ar a bashi ya sha, saida ya shanye Hajia ta fito daga ban d'aki tace "Tashi kaje ka yi wanka ruwa na nan na had'a ma ka."
Kasa magana ya yi saboda mamaki da kuma rashin sanin abin da zai fad'a, saida ta maimaita da "Ko ba ka ji ba ina magana?"
Saida ya gyara zama ya kalli jikin shi da kyau yace "Amma Hajia na yi wanka fa, wane irin wanka ne zanyi yanzu kuma?"
"Ka tashi ka shiga lokaci tafiya yake." Marairaicewa ya sake yi yace "Amma Hajia wai dan..." Katse shi ta yi da "In za ka tashi ka tashi kafin ka b'ata min rai."
Tashi ya yi kamar zai k'urma ihu saboda haushi, ya rasa irin wannan sabon al'amari na iyayen shi, haka ya tub'e kayan da ya sanyo yanzun ya yi wanka da wannan hakukuwan na magani, haka ya sanyo kayan ya fito duk ruwan jikin shi sun tsaya a kayan, ya na fitowa Hajia kuma ta bashi damammiyar fura da maganin jiya a ciki, saida ta masa jan ido yasha dan cewa ya yi jiya baiyi bacci ba, hakan ya sa ta bud'e mi shi ido sosai sannan ya sha, wata 'yar kwalba ta d'auko bak'a mai d'auke da maganin *jibda* a ciki, da kan ta ta lak'ato a hannu ta shafa mi shi a wuya zuwa kai da hannuwan shi har zuwa damatsenshi, bashi ta yi tace ya d'iba ya shafa a cikin shi har zuwa k'irji, kamar zaiyi kuka ya kalle ta yace "Hajia wai duk wannan na miye haka? Wannan abun nan amai zai saka ni, sam warin shi babu dad'i."
Shiru kawai ta yi ba tace komai ba dole ya shafa yanda take so, mik'ewa ya yi yace "Hajia ko za ki bani magungunan sai ki nuna min yanda ake sha, ina ga kamar hakan zaifi ko?"
Kallon shi ta yi tace "Alhaji, kai ka haife ni ko ni na haife ka?"
Cike da ladabi ya rusuna yace "A'a Hajia ki yi hak'uri, ban fad'i haka dan b'ata ran ki ba."
"To ka wuce ka tafi in da za ka je kawai, sannan ba na so ka fad'a wa wani ko wata batun magungunan nan, ko da kuwa matan ka ne ban yarda ba, kaji ni ko?"
"Naji Hajia, amma wallahi da gaske na le idan ki ka bani zanyi aiki da su, Hajia ki duba kiga hakan zaifi a gani na, misali yanzu na wankan nan, idan da a waje na yake da haka ba za ta faru ba, amma idan ya na nan zai zamana kullum sai na yi wanka anan kenan, sannan idan na yi tafiya za'a dakatar da maganin kenan har sai na dawo, sannan Hajia..."
"Dakata dallah." Ta katse shi tare da d'aga hannu, shiru ta yi ta jima ta na tunanin abin da ya fad'a kafin ta gamsu ta d'auko duka magungunan ta bashi, saida ya karb'a ta nuna mi shi yanda zaiyi aiki da su kafin ta sake jadadda mi shi bata so ko matar shi ta sani, alk'awari ya mata babu wanda zaiji dan haka ta bashi ya tafi, aljihu ya saka su ya fita daga gidan ya shiga harkokin gaban shi, sai yamma ya dawo gida cin abinci, zai shiga wanka ne ya fito da komai na aljihun shi ya na ajewa akan gaban madubi, ya na aje ledar maganin Haseenah ta kalle shi tace "Oga wannan fa na miye haka?"
Ba tare da wani damuwa ba yace "Um, ba na fad'a mi ki zan karb'o wannan maganin ba a wajen Hajia? To ai sune na karb'o d'in, da k'yar ta bani su bayan na mata alk'awarin ba zan bari kowa ya sani ba."
Ya na fad'a ya shige wanka, zaune ta yi tana kallon magungunan har ya fito, cikin taushin murya tace "To yanzu ya za ka yi da su kenan? Za ka ci gaba da sha ne?"
Da k'arfi yace "Wa? Ni! Haba dai Hajia, kinga kawai d'auke su ma daga nan ki zuba su shara danni ko d'aya ba zanyi anfani da su ba."
Mik'ewa ta yi da wani mirmushin mugunta a fuskar ta ta kalle shi tace "Haka na ke son ji dama, dan ba na son namiji mai tsirfa kamar mace."
*Da dare* Usman da malam da kuma rakiyar Murtala da d'aya abokin nashi mijin Hajia Salamatu wato *Alhaji Salisu* suka je aka nemowa Nura auren sahibar shi *Choukra*, cikin girmamawa aka yi abin da za ayi aka gama kafin abin da zai biyo baya, ko da su ka dawo har gida suka fara aje malam in da ya umarci Usman da ya shigo su yi magana, suna shiga ya bashi ruwan addu'a yasha, ganin Nura a gidan ne ya sa yace ya je gida gobe da safe ya same shi kafin ya fita, da "To yah Fodio." Ya amsa kafin ya fito suka wuce.
*Washe gari* da safe Hajia Sadija ce ta yi sallama gidan surukan Khadija in da Mansur ke binta a baya, tarba ta musamman suka samun daga wajen Hajia da malam d'in kafin su ka nutsu, cikin dattako Mama tace "Nasan za ku yi mamakin gani na da sanyin safiyar nan, to ba wani abu bane dama face wani alkairi da ya tunkaro mu, shine na ce ba za mu yi farin cikin mu kad'ai ba, kuma da kuma Usman d'in ku na da hakk'in ku san me ke faruwa."
Malam ne yace "To gaskiya dai ba mu yi mamaki ba, abu d'aya da na ji shine fargaba, kuma bai wuce fargaban tunanin makomar auren yaran mu ba."
Murmushi ta yi tace "Malam kenan, kamar yanda na fad'a ne a farko alkairi ne ke tafe damu, kuma insha Allahu babu abin da zai shafi makomar auren yaran nan, yanzun ma k'addara ce kawai ta gifta a tsakanin su, amma komai zai daidaita da yardar Allah."
"Allah yasa haka Hajia." Cewar malam yayin da Hajia kuma tace "Allah ya yarda, ya kuma kawo mana k'arshen matsalar."
"Ameen ya Rabbi." Mama ce ta d'ora da "Dama dai ba wani abu bane Bilal ne za'a wa k'ane ko k'anwa idan Allah ya amince."
Da sauri duka suka kafe ta da ido kowa da mamaki, Mansur ma da kallo ya bita da mamaki, dan sam bai d'auka abin da zai kawosu ba kenan, amma ya zaiyi shiru ya yi ya na sauraren ikon Allah, Hajia ce tace "Wai Hajia ki na nufin Khadija juna biyu ne da ita?"
Dariya mama ta yi tace "K'warai kuwa."
Da tsantsar farin ciki tace "Kai Alhamdulillah, Allah abin godiya, Allah mun gode ma ka, gashi bayan shekaru goma sha uku za ka k'ara azurta baiwar ka da ni'imar ka wacce babu wanda ya isa ya bawa wani sai kai, baiwar da kud'i basa sayanta kuma alfarma bata bayar da ita."
Malam da hak'oran shi ke waje ya na faffad'an murmushi ne yace "Tabbas hakane, arzik'i ne da imanin ka ko kafircin ka bai isa ya baka shi ba, sai mai bayarwa ya ga damar baka."
"To wannan dai shine dama na ce bara mu zo mu fad'a mu ku, dan bai kamata ku kasa sani ba."
Malam ne yace "Gaskiya ne Hajia, kuma mun gode da wannan girmama mu da ku ke yi, Allah ya saka da alkairi."
"Ba komai wallahi." Mama ta fad'a ta na mik'ewa ta na gyara mayafin ta tana ci gaba da fad'in "Mu zamu wuce, dama zanje 'yar kasuwa ne na ce mu fara biyowa ta nan d'in."
Mansur mik'ewa ya yi suka mu su sallama, har k'ofar gida malam ya rakaso in da ya sake jadadda ba su hak'uri akan abubuwan da suka faru, sannan yace a gaishe mi shi da su sosai, da haka su ka wuce shi ma ya dawo gida suka k'ara jinjina al'amarin, suna haka Nura ya sallamo d'akin tare da Aziza cikin shiri, har k'asa suka gaishe da iyayen su kafin Nura yace "Zan aje Aziza makaranta ne daga nan na biyo gidan yah Fodio, jiya yace na je gida na same shi."
Malam ne yace "To shikenan Allah ya tsare, Allah ya mu ku albarka."
"Ameen Baba." Su ka amsa suna mik'ewa, Hajia ma d'orawa ta yi da "Allah ya tsare, sai kun dawo."
"Ameen Hajia." Cewar Aziza suna ficewa.
Mansur na d'aukar hanya ya kalli Mama yace "Hajia ta, dama abin da ki ka zo fad'a mu su? Wallahi ko kad'an banyi tunanin haka ba."
Ba tare da ta kalle shi ba tace "Kenan da ka sani da ba zaka kawo ni ba?"
Dariya ya yi yace "Wane ni, ni d'in banza na kasa kai ku in da ku ke so."
"Dan haka ka ja min bakin ka kayi shiru, in kuma ranka ya b'ace to rufe ni da duka." Ta fad'a ba alamar wasa, dariya ya sake yi shi dai yace "Allah ya huci ranku Hajia ta, ban fad'i haka dan b'ata ran ku ba wallahi, amma a gafarce ni."
Shiru ta yi basu sake magana ba har ya kawo ta yar kasuwa wajen *Nasruminallah* ta fita ta lek'o tace "Zan d'auki lokaci anan, saboda akwai atamfofin da zan duba, idan ka na da aikin ke ka wuce kaje in da za ka."
"To Hajia ta ame za ku koma kenan?" Kai tsaye tace "A adaidaita mana."
Waro ido ya yi yace "Ah haba dai, Hajia ki na da mu a cikin garin nan mu barku ku hau adaidaita sahu, haba dai wuce nan ai wallahi, Hajia ta shiga kusha zaman ki, zan jira ku har lokacin da ku ka gama."
Sai lokacin ta masa murmushi mai tsada cike da so da k'auna tace "Allah ya bar min kai."
Cikin jin dad'i shi ma yace "Ameen Hajia ta, ai wannan addu'ar kad'ai ma ta isa tasa na kwana wajen nan ina jiran ku."
Dariya kawai ta yi ta shiga shagon da ya kawo ta, shi kam gyara zama ya yi ya k'ara sautin wa'azin da ya ke saurara, ya na haka Bashir ya kira dan tambayar in da ya kai mu su uwa su, nan ya fad'a mi shi komai ai sai Bashir ya fara zazzaga fad'a wai akan me Hajia za ta mu su haka, ai sai su d'auka ko wani abu suke so a gurin su ko kuma su na son amayar da yar uwar su ne, Mansur kam da ya ji ya cika mi shi kunne kuma ya na gaba da shi babu rashin kunya tsakanin su sai raha, hakan ya sa yace "To yallab'ai Bashari ni zan kashe wayar sai ka kira wayar Hajiar ka fad'a mata haka."
"Wallahi zan wulak'ance idan ka sake kira ni da Bashari, fitsararre kawai, shine ma har za ka ce na kira Hajiar, wato so ka ke kaga ta yi hushi da ni ko? To ba zan kira ba."
Cikin dariya Mansur yace "Dan haka ni ma sai ka shafa min lafiya da surutun nan naka." Ya na fad'a ya kashe wayar ya na ci gaba da dariya, dan ya san in ya koma gida sai su sake wata badak'alar akan kashe mi shi waya da ya yi, shi kam Bashir jefar da wayar ya yi ya na ci gaba da mita, Aisha dai na saurarn shi dan yau ya na d'akin ta har ya shirya ya fita su ka gaosa da Khadija bai daina mita ba.
Nura na aje Aziza ya wuce gidan dan dama babu nisa sosai daga nan, saida sula gaisa sosai da mai gadi kafin ya wuce ciki, Haseenah na madafa ta na soya dankali saboda wuyar da take ji, Usman kuma na d'aki ya na bacvi dan lokacin tashin shi baiyi ba, har saida Nura ya tsaya k'ofar shiga falon Usman ya tsaya ya d'an fara bubbugawa, Haseenah dake kallon shi tana ta fad'a wai miya kawo shi da safiyar nan, sai lokacin ta lek'o ba tare da tunanin rigar baccin da ke jikin ta ba tace "Sannu ko?"
Juyawa Nura ya yi ya sauke idon shi a kan ta, d'auke idon shi ya yi lokaci d'aya sai dai ya na shakku ko ita ce amaryar ma ko ba ita bace, dan shi dai dama ba wani saninta sosai ya gama yi ba har yanzu, musamman kuma yanzu da yake ta taso daga bacci ne duk a hargitse take, hakan ya sa ya ga ta masa wani irin muni kamar tsohuwar akuya,😂 Nura bala'i, a tak'aice shi ma yace "Sannu, mai gidan fa?"
Cikin yamutsa fuska tace "Alhaji ya na bacci, kuma lokacin tashin shi baiyi ba, sai dai ko za ka dawo wani lokaci."
Wani kallo ya mata sama da k'asa yace "Da alama ba ki gane wane ne ni ba, amma ko Khadija dake gaba da ke na zo gidan nan tana taso min in har ina son ganin shi, amma bara ki gani."
Wayar shi ya ciro daga aljihu ya danna lambar Usman ya doka masa kira, murmushi ta yi tace "Ni Hassenah suna na, ita kuma Khadija sunan ta, kaga dole hallayar mu da d'abi'ar mu za ta banbanta, ba lallai abin da ta maka ba ni ma shi zan maka, dan haka na fad'a maka Alhaji na bacci."
Ta na fad'a ta fito daga madafar ta bud'a k'ofar falon ta shiga, ta na shiga Usman kam bacci yake hankali kwance, kai tsaye wajen wayar shi ta nufa dan ta na nesa da shi kuma ta na vibration, d'auka ta yi ta kashe wayar gaba d'aya sannan ta aje ta fito, ta gaban Nura ta sake wucewa ta koma madafa ta ci gaba da aikin ta, shi kam ko da ya kira ba'a d'aga ba kuma da ya sake kira ya ji a kashe yasan ita ce, rai b'ace ya juya ya fita dan a cewar shi in ya tsaya ya na kallon ta to tabbas zai d'auki man da take suya da shine ya k'ona mata fuska da shi, dan haka ya fita daga gidan.
Ko da ta kammala abin da take wanka ta yi ta shirya ta taso Usman, taya shi ta yi ya yi wanka ya shirya ya fito suka fara kari, cike da kasala ya kalle ta yace "Wai ina waya ta ne ban ganta ba?"
"Ta na d'aki." Ta fad'a a tak'aice, wata hamma ya yi ya kalle ta yace "Wallahi gaba d'aya jiki ba dad'i, ba na da ra'ayin fita yau kam."
Murmushi ta yi tace "Zan so kasancewa tare da kai na tsawon wunin nan, idan haka ta faru zan ji dad'i sosai."
"To shikenan, yanzu kije ki fito min da k'ananan kaya na canza wannan manyan da na ji dad'in zaman gidan."
"To." Ta fad'a da azama ta nufi d'akin shi, d'orawa ya yi da "Ki biyo min da waya ta dan Allah."
"Ok." Ta fad'a ba wani fargaba a tare da ita, ba jimawa ta dawo da kayan da wayar, da ka ta ta saka mi shi kayan ta ninke waccen ta mayar d'aki, ta na shiga d'akin ya kunna wayar ya fara kiran wayar Bilal, ya yi mamaki da yaron ya kasa d'aukar wayar shi, dole ya hak'ura ya barshi sai lokacin ya ga sak'o da ke nuna Nura ya kira shi bai samu ba, kiran Nuran ya yi wanda har yanzu yake cika ya na batsewa cike da haushin Haseenah, a kakkauce suka gaisa kafin Usman yace "Jiya na ce ka zo ka same ni gida, akan wani dalili ne ba ka zo ba, ko ka na so ka nuna ban isa bane?"
Cikin b'acin rai Nura yace "Kuma yaya, ka tambayi wannan shed'aniyar amaryar ta ka mana, tunda safe na zo amma tace ka na bacci wai ba za'a tashe ka ba, ni kuma naga ko shugaban k'asa ne kai tunda har kai ka ce na zo ai dole a barni na ganka, amma ta rufe ido wai ita mai miji." Ya k'arashe maganar da k'wafa, Usman da ya yi shiru ya na sauraren shi zuciyar shi na tafasa saboda ya tab'o masoyiyar shi, tabbas da ya na tsaye gaban shi wallahi da ya sai ya mare shi, dan haka ya gyara zama daidai lokacin kuma Haseenah ta fito daga d'akin, cikin b'acin rai Usman ya fara fad'in "...
*Yan uwa ku taya ni da addu'a, bébé Abdul Latif ba lafiya, Allah ya bashi lafiya.*
24/02/2020 à 21:49 - 💋😘💋: 💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
*KALLON KITSE*
_(Ake wa rogo)_
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
_SAMIRA HAROUNA_
*Litattafan marubuciyar*
*1* _KAUSSAR_
*2* _D'AUKAR FANSA_
*3* _BA SO BANE_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI_
*6* _JIHADI_
*7* _K'ANGIN RAYUWA_
*8* _ITACE K'ADDARARMU_
*9* _KAWU NA NE_
*10* _MAATA_
*11* _KALLON KITSE..._
*SADAUKARWA GA*
_MATAN FARKO_ 🧕🏼 *(UWAYEN GIDA)*
🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_🤜🤛
```Fatan alkairi masoya```
_Bismillahir rahamanir rahim_
*31*
"Yanzu Nura ni ka ke kallo ka ke fad'a ma haka? Ko dan ka na ganin a waya ne shine ya ba ka damar fad'a min abin da ka ga dama? Lallai wuyan ka ya isa yanka Nura, har ni za ka bud'a baki ka aibata matata a gaba na a dodon kunnuwa na, to nagode, kuma ka yi hak'uri idan ran ka ya b'ace saboda kiran da na ma ka, ni dama ba aikin ka zanyi ba, na ce ka zo ne dan na baka kud'in da za ka fara shirye-shiryen bikin ka tunda an riga da an gama magana, amma tunda har ka ci mutuncin matata a gaba na ba tare da fargaba ba, to na fasa sai ka je ka samu malam saiya ma ka komai, ko kuma ka je ka fad'awa wacce ta sanya aka nemo ma ka auren ka ga saita d'auki nauyin komai."
Ya na fad'a ya kashe wayar ya jefa kan kujera, zaune ta yi ta na kallon shi tace "Ya dai babban mutum na ji ka na waya haka kamar ka na fad'a? Kai da wa ne haka?"
Cikin fusata yace "Ni da wannan banzan Nura fa, wai har ni zai kalli tsabar ido na ya na fad'a min magana har ya na ci mi ki mutunci, amma ba laifin shi bane laifi na ne da na sakar mu su fuska har su ke samun damar fad'a min abin da duk ya fito bakin su."
Cikin ladabi tace "To me yace ma ka?"
"Ki barshi kawai, ban san tunawa." Matsowa ta yi kusa da shi ta b'alle mab'allin rigar shi ta sa hannu ta na shafa k'irjin shi ta na fad'in "Na fi ka sanin cewa yan uwan ka ba sa so na, musamman yanzu da aunty Khadija ba ta gidan nan, wallahi gaba d'aya haushi na suke ji, gani su ke kawai laifi na ne ni ce silar barin ta gidan, amma ka sani ba zan tab'a damuwa da hakan ba in dai har ka na tare da ni."
Rumgume ta ya yi yace "Kar ki damu Mummyn beby, babu abin da zai raba ni da ke saboda ina bala'in son ki sosai."
Nura kam shi ma cikin hushi ya aje wayar shi ya ci gaba da aikin da ke gaban shi ya na balbala masifa shima, bai damu ba dan yace ba zai bashi gudummuwa ba, dan dama a shirye ya ke kafin ma ya fara maganar auren, dan haka ya yi niyyar yi wa kan shi komai ba tare da jiran taimakon wani ba, sunyi mai wuyar tunda sun nemo mi shi auren.
Har ya gama abin da ya ke ya dawo gida kowa bai fad'awa abin da ya faru ba, dan Nura mutum ne mai zuciya da kuma rik'o sosai, wannan abun da ya faru ko da an yafi juna zaiyi wuya ya d'ora idon shi akan Usman ba tare da ya tuna wannan ranar ba, uwa uba kuma Haseenah da ya ke da tabbacin ita ce silar faruwar komai, har ya yi wanka ya ci abinci zai fita Hajia tace "Wai kai ya ku ka yi da Fodio da ka je gidan?"
Fuska a had'e yace "Ba komai Hajia, dama wani sak'o ne zai bani na kai wani wurin."
"To ai ni na d'auka ko maganar auren ta ka ce za ku tattauna." Hanyar fita ya nufa ya na fad'in "A'a ba ita bace."
Har ya kusa kaiwa k'ofar fita ta sake cewa "Zo ka kira min shi a waya, ni tun yamma na ke kira ba na gane me ake fad'a, kuma har yanzu bai shigo gidan ba har dare ya yi." Dawowa ya yi ya karb'i wayar ya danna kiran lambar Usman ba tare da yace komai ba, wayar na k'ara a lokacin amma ba'a d'auka ba.
Manne suke da juna basu rabu ba, sai dai ta samo mu su abu su tab'a kawai su yi sallah idan lokacin ya yi, mai gadi bawan Allah sam sun ma manta da a al'amarin shi bare a aika mi shi da abinci, sai dai ya siyo kawai ya ci amma ran shi bai mi shi dad'i ba, a haka har dare ya riske su Usman sai amsa waya ya ke musamman abokan shi na rashin ganin shi yau da ba ayi ba a waje, wani ikon Allah kuma saida su ka yi shirin kwanciya sai ciwon mara ya hana Haseenah sukuni, cikin rud'ewa ya d'auke ta su ka nufi asibitin da aka fara duba ta tun farkon rashin lafiyar ta, suna gaban likita lokacin kiran Hajia ya shigo wayar shi, kasa d'auka ya yi ya mayar da hankali kan abin da likitan ke fad'a cewa ta daina duk wani aikin wahala, in fa ba haka ba zata iya yin b'arin cikin nan, haka aka sallamo su suka dawo aka ce ta ci gaba da shan magungunan da aka bata na farko, tun cikin mota yake fad'in "Wallahi ba za ki k'ara dafa ko ruwan zafi ba a gidan nan, ke baki san yanda na ke son abin da ke cikin nan naki ba, amma bari cikin ki ya k'ara k'wari wallahi k'asar waje zan fita da ke ki haihu acan, dan ni ban ma gamsu da likitocin nan d'in ba, daga yanzu kuma zuwa lokacin zan samo mi ki yar aiki ko kuma Aziza ta dawo nan ta dinga aikin gidan."
Ita dai ta na sauraren shi dafe da marar ta har suka isa gida, da kan shi ya canza mata kaya ya kwantar da ita ya bata magani tasha sannan ya rufe ta da zanin rufa, k'ura mata ido ya yi ya na kallo har bacci ya d'auke ta, wani bala'in tausayinta da kuma son ta ne ke k'ara gyauraya da jinin shi, ta yanda yake jin kamar ya mayar da cikin jikin shi saboda ta samu sauk'i, ya jima zaune kafin ya fito da wayar shi ya ga kiran Hajia, fita ya yi falo ya sake maida kira cikin sa'a kuma Hajia ta d'auka, a d'an kakkauce suka gaisa kafin ta tambaye shi ya yi aiki da magungunan nan, "Sosai ma Hajia, ai duk na yi aikin da su." Cewar Usman fa, tambayar shi ta kuma yi me ya hana shi zuwa yau? Malam ma ya bayar da ruwan addu'a a abashi amma bai zo ba, haka kawai ya tsinci kanshi ya sharara k'arya ta hanyar fad'i "Hajia ai wani abu ne ya d'an taso da ya sa dole sai da na je *katsina*, kuma sai bayan isha'i na dawo ina zuwa na gaji sosai kawai na d'an kwanta, yanzu ma ina bacci ne na farka sai kuma na ga kiran ku."
Cike da gamsuwa Hajia tace "Ah to shikenan, saida safe, Allah hutar da gajiya."
"Ameen Hajia, nagode, saida safen ku." Ya na fad'a ya kashe wayar ya shiga uwar d'akin shi ya canza kaya kafin ya dawo d'akin Haseenah.
Washe gari da safe kafin malam ya fita saida ya sake bayar da ruwan addu'a, Hajia dai ba ta ma fad'a mi shi na jiya na nan ba kawai ta amsa, sai kuma akayi sa'a Usman ya zo gidan, shi ma kuma ya zo ne da maganar Aziza ta koma can da zama ta na taya ta aiki, kasancewar ba sabon abu bane ya sa Hajia cewa idan malam ya zo za ta fad'a mi shi, idan ya amince saita kira a fad'a mi shi, nan ta d'auko ruwan duka biyu ta bashi ya shanye kafin ya fita, daga nan wajen Murtala ya nufa su ka d'an tab'a hira har ya na tsokanar shi wai amarya da uwar gida sun hana shi fita ko ina, nan ya kalle shi ya tab'e baki yace "Wace uwar gida kuma da ba ta nan?"
Da mamaki Murtala yace "Ban gane ba ta nan ba, to ta na ina?"
K'ara tab'e baki ya yi yace "Ta na gidan su mana."
"Gi me?! Murtala ya fad'a da k'arfi har da dafe k'irji, a wulak'ance ya kalle shi yace "Gida na ce, gidan iyayen ta, ko tafi k'arfin zuwa gida ne?"
Kai tsaye ba tare da fargaba ba Murtala yace "Ta fi k'arfi, wallahi in dai Khadija ce tafi k'arfin haka aboki na."
Sake tab'e baki dai ya yi yace "Sai kuma ka yi kan ka ake ji." Dafa shi Murtala ya yi yace "Wai dan Allah in tambaye ka mana? Ka na nufin ta tafi gidan su saboda ganin damar ta? Ko kuma kai ka kora ta gida? Ko kuma ma dai wasa ka ke min?"
Cikin hassala yace "Ya zan ma ka wasa da wannan maganar, wai ita Khadijar nan me ku ke d'aukar ta ne da ba za'a hukunta ta ba?"
Wani kallo Murtala ya ma sa yace " Mun d'auki Khadija a matsayin rayuwar Usman, sannan Khadija ita ce sirrin duk wata nasara ta Usman, kar ka manta da haka aboki na, duk abin da ka zama yau Khadija ta taka muhummiyar rawa a zuwan ka wannan matakin, amma gaskiya abin da ka yi yanzun kasa ni kai na na fara jin kunyar had'uwar da ita da iyayen ta da kuma 'yan uwan ta, shin aboki na yanzu da wane irin ido za ka iya kallon Ashir idan kun had'u ko da bisa hanya ne?"
Cikin b'acin rai ya kalle shi yace "Da wane ido fa, da idon da ya ke kallon na shi 'yan uwan matar wacce ya saka lokacin da zai k'ara aure, Rahama ba, ka tuna da ita? To ai gwara ma ni tunda ba sakin ta na yi ba, kuma ita ce ta d'auki kayan ta ta tafi ba ni nace ta tafi ba."
Murmushi Murtala ya yi yace "Kafi kowa sanin dalilin da ya sa Ashir ya rabu da Rahama, ta yi ikrarin in har ya k'ara aure to ba shi ba kwanciyar hankali, sannan daga lokacin ta dinga nuna raini akan mutanen da suka fi komai daraja a wurin shi, mahaifiyar shi da kuma Khadija, wulak'anta su da ta fara yi ta na kallon su kamar sune ke zugashi ya sa ya kasa jura ya sallame ta, amma kai kuma fa? Fad'a min tayar ma ka da hankalin da ta yi."
Tsaki ya yi yace "Kaga, ni ban zo nan ba saboda jin wannan maganganun, kawai..."
Dafa shi ya yi cikin nutsuwa yace "Me ya ke damunka aboki na? Fad'a min miye matsalar mana? Khadija ce fa, matar nan da ba ka son komai sama da ita, ina wannan soyayyar? Ina wannan k'aunar? Ko da yake ma bai kamata na tambaya ba, nasan har yanzu ka na son ta."
"Ba gaskiya bane, ni yanzu ba na son ta." Ya fad'a ba alamar wasa, murmushi Murtala ya yi yace "Ka rufe idon ka, sannan ka saurari zuciyar ka ita kad'ai, kar ka bari wani tunani ya shiga tsakanin ka da zuciyar ka, ina tabbatar ma ka hoton Khadija za ta gani."
Ya na fad'a ya mik'e ya shiga cikin shagon shi dan ya ba shi dama, Usman kuma na ganin haka saiya mik'e ya tashi ya shiga motar shi shima ya bar wajen, gida ya koma ya na zuwa mai gadi ya bud'e masa k'ofa ya shiga, har ya aje motar a muhallin ta kalaman Murtala na masa yawo, hakan ne ya tilasta masa dafe sitiyari ya rufe ido ya na mayar da nutsuwar sa gare sa, ya jima a haka kafin ya zuba ya bud'e ido saboda ganin Khadija da ya yi cikin doguwar riga bak'a, gefen ta Bilal sai dariya suke suna kallon wani abu da ya birge su, amma ko da ya bud'e ido ya na tuna fuskar ta saiya k'ara had'e fuska, tsaki ya yi kawai ya fito daga motar ya wuce wajen amarya.
Da shigar shi ya samu Haseenah na waya da Mariya akan maganar su, kasancewar a shirye take ya sa tace ta karb'o sak'on ta zo ta amsa ko ta aiko a karb'ar mata, a cewar Haseenah "Zan kira yah Mubarak ya je ya amso min." Da "Sai ya zo." Mariya ta amsa su ka datse wayoyin.
Wanka ya fara shiga ya yi ya fito d'aure da abin tsane ruwa a k'ugu (towel), wayar shi ya d'auka gaban madubi ya danna kiran lambar Bilal, a daidai lokacin Bilal na zaune gaban Khadija su na karatu, ya na fito da wayar daga aljihu ya datse kiran saboda ganin mai kira, irin shi ma wai an tab'a mi shi mahaifiya d'in nan, ganin hakane ya sa Khadija kallon shi tace "Bilal, ba kiran ka ake ba na ga ka na katsewa? Waye haka?"
Turo baki ya yi gaba baice komai ba, dariya Khadija ta yi tace "Ko dai surukata ce ta ke kiran shi ya sa ba ka so ka d'auka gaba na?"
Kamar zai fashe da kuka yace "Mummy."
"To waye ke kira?" Ta fad'a ta na d'aukar wayar da ya aje saman gado, tana dubawa ta ga mahaifin shine ya kira ya katse, da mamaki ta d'ago ta kalle shi tace "Bilal! Mahaifin ka ne dama ya kira ka ke katse shi?"
Kafe ta ya yi da ido, cikin tsawa tace "Da kai na ke magana ka na jina ka yi shiru, ina so na ji hujjar da tasa ka ke datse kiran shi ba ka d'auka."
Cikin turo baki yace "To Mummy ba Abba ne ya daina son mu ba, kuma a gaba na fa ya dakkk..." Kashe shi ta yi da marin da ya sashi saurin dafe kumci ya fashe da kuka, cikin zafin rai ta d'ora yatsanta akan bakin ta tace "Shiiii, kar ka bari na ji sautin muryar ka har zuwa lokacin da zan gama magana."
Gimtse kukan shi ya yi ya na kallon idon ta tace "Bilal matsala ta ce fa da mahaifin ka, kai miye na ka a ciki? Me ya shafe ka da har za ka juyawa mahaifin ka baya a kai na? Kasan me ya faru ne a tsakanin mu? Ko kuma na fad'a ma ka ba na son mahaifin ka ne? To maza kafin na k'irga uku ka kira mahaifin ka ka bashi hak'uri sannan ka nemi gafararsa."
Da sauri ya d'auki wayar ya mayar da kira, Usman da ke cikin saka kaya ne ya ga kiran Bilal, d'auka ya yi kafin yace wani abu Bilal yace "Assalama alaikum, Abba ina wuni."
Wani murmushi Usman ya saki tare da sak'awa a ran shi tabbas Khadija ce ta sashi ya kira shi, dan ya na da yak'ini akan Khadija wajen tarbiyar Bilal, bai iya amsa sallamar sai cewa ya yi "Yariman hushi ka ke da Abban ka?"
Jiki na rawa Bilal yace "A'a Abba ba hushi na ke da kai ba, dan Allah ka yi hak'uri ka yafe min, ba zan k'ara ba insha Allah."
Murmushi ya yi yace "Ba komai yarima ya wuce, ya ka ke? Ya karatu?"
"Lafiya lau Abba." Ya yi maganar ya na kallon Khadija da ta kafe shi da ido, ta na ji su na wayar su kafin daga bisani Usman yace "Yarima yaushe za ka zo mana gida? Kasan fa mu na kewar ka."
Cikin turo baki yace "Gaskiya Abba ba zan je gida ba ba tare da Mummy ba, kawai kai ka zo nan."
Ba tare da damuwa ba yace "Shikenan to, amma idan naje makaranta zan gan ka?"
Cike da k'aguwa yaron yace "Abba! Me ya sa ba za ka zo gida ba?"
"To to shikenan, na ji zan shigo gidan zuwa gobe."
"Wane lokaci?"
Saida ya d'anyi tunani kafin yace "Umm, ina ga zuwa dare zan shigo."
"To Abba." A hankali Usman yace "Saida safe ko, ka yi bacci lafiya."
"To Abba, ga Mumm..." Bai k'arasa fad'a ba ya ji ya datse kiran, kallon maman shi ya yi yace "Mummy ki yi hak'uri to, Abba ya hak'ura."
Janyo shi ta yi ta rumgume hawaye na fita a idon ta tana fad'in "Bilal ba na so ne abin da ke tsakani na da mahaifin ka ya shafe ka, idan ba ka manta ba a baya haka bata faru ba tsakanin mu, yanzu ne haka ta fara faruwa saboda dama ita rayuwa ta gaji haka, ba lallai mutum ya tabbata cikin farin ciki ba, zan iya cewa a rayuwa ta ban tab'a fuskantar matsalar da ta sani bak'in ciki ba kamar wannan, dan haka zanyi hak'uri da jarabawar da Allah ya d'ora min har na cinye ta, ko da kuwa hakan na nufin k'arshen zama na kenan a gidan mahaifin ka."
Da sauri ya d'ago yace "A'a Mummy, gaskiya ba za ku rabu ba, ni dai wallahi idan ku ka rabu to ba za ki sake wani aure ba." Zaro ido Khadija ta yi ta na kallon shi da mamaki tace "Kai kuma a ina ka samu wannan tunanin?"
Cikin shagwab'a yace "To ba *Beby* (d'iyar Ashir ta farko mai sunan maman su) ce tace mana Maman su za ta yi aure ba."
Girgiza kai ta yi tace "Kenan idan ban koma gidan sa ba saina tabbata a cikin d'akin nan? Kai ba ka kishi na ne? Ko ba kaga shi mahaifin naka ya k'ara aure ba, me ya sa ba ka hana shi?"
"To Mummy ai shi namiji, ni kuma ba na so ki sake min wani Abba, na fi so ku zauna ku biyu abunku yafi dad'i." Shiru ta yi tunda shekarun shi basu kai tace dole saita fahimtar da shi ba, sannan ita kan ta tana wa Usman kishin kan ta ta yanda take fatan ya zama mijinta har abada, da haka suka ci gaba da karatun su har dare ya yi su ka kwanta.
*Washe gari* da safe gidan ya yi shiru sosai aka amshi bak'uncin Murtala, dan gaskiya abun bai masa dad'i ba sosai, a falon Hajia suka zauna tare da Khadija da Hajia ya na basu hak'uri da nuna mu su rashin jin dad'in sa, sannan ya d'ora mu su da sam bai sani ba sai jiya, cikin fara'a suka nuna mi shi babu komai haka Allah ya hukunta, kuma ai da sauk'i tunda ba saki bane Allah zai iya daidaita lamarin, haka dai ya tafi abun ba dad'i sai hak'uri kawai.
Yau Usman ya samu malam a gida bai fita ba saboda jiki da jini, saida ya sha ruwan shi kafin ya mik'e zai bar gidan Hajia ta tambaye shi ko yaje ganin Khadija? A cewar shi dai "A'a ban je ba, amma na ce yau zanje anjima."
"To aiko gwara ka tafi dan kasan halin da take ciki." Da mamaki ya kalli Hajia yace "Hajia wani abun ne ke faruwa da ita?"
Cikin murmushi tace "Ai Khadija Allah ya..." Da sauri malam ya d'aga mata hannu alamar ta yi shiru, girgiza mata kai ya yi kawai bai ce komai ba, jin ba tace komai ba ya sake mu su sallama ya fita, Hajia kuma malam ta kalla tace "Me ya sa ba ka so ya sani? Ya na da hakk'in sani fa."
"Ki barshi kawai, idan ya je saita fad'a ma sa idan ta so ya sani, idan kuma ba ta so ba saiya gano da kan sa." Har ya mik'e zai fita Hajia tace "To amma ni banga anfanin b'oyewar ba."
Juyowa ya yi ya kalle ta yace "Ni kuma na gani, in dai ina fad'a aji to ban yarda ki fad'a ma sa da bakin ki ba, dan halin da Fodio yake ciki yanzu ba ya iya rik'e sirrin kan shi ma bare na wani, a gaskiya ni ban yarda da amaryar nan tasa ba."
Da *yamma* Khadija su na farfajiyar gida yara duk sun cika gidan da hayaniya suka ji sallama, amsawa akayi tare da masa izinin shigowa, Bilal na ganin shi da gudu yaje ya rumgumr shi, Khadija ma na juyowa ta mik'e ta na dariya saboda farin cikin ganin shi ta na fad'in "...
*Addu'ar ku tamkar takobi ce a gare ni mafi kaifi a duniya, ina k'aunar ku masoya.*
25/02/2020 à 21:16 - 💋😘💋: 💑💑💑💑💑💑💑