Ango kai ne a gidan namu, lallai babban bak'o, amma dai da alama hanya ce ta d'auka ka ya sa ka biyo nan, ba dan haka ba ni dai na san ka da tsoron bayar da kud'in cefanai."
Dariya ake in da ta nufi falon Mama ta na fad'in "Bismillah Nura shigo." Bayan ta ya bi ya na rik'e da hannu Bilal, saida ya gaisa da mutanen da ke nan kafin ya k'arasa shiga ciki, zaune ya yi akan kujera ita ma ta zauna bayan ta aje ma sa ruwa da lemu, kallon ta ya yi yace "Ke haka ake sai ki tarfani a gaban manyan mutane, sai kisa su d'auka gaske ne abin da ki ka fad'a."
"Au! Ba gaske bane kenan? To ka na bayarwa ne? Yanzu fad'a min yaushe rabon da ka zo gidan nan?" Sosa kai ya yi yace "Gaskiya na kwana biyu, yanzu kuma da na samu labarin ki na nan wallahi kunya ce ta hanani zuwa."
Murmushi ta yi tace "Ba na son ku na fad'in haka wallahi, kenan idan k'addara tace za mu rabu da Usman ba da shi kad'ai zan rabu ba har da ku?"
"Ah haba dai, ai ba za mu tab'a bari ki fita a cikin dangin mu ba wallahi, ke fa alkairi ce a cikin mu, shima yasan da haka, wannan mai k'afafun angulun ce ta sauya mi shi tunanin shi."
Bilal ne ya bushe da dariya yace "Aunty amaryar ce haka?" Kallon Bilal ya yi ba alamar wasa yace "Kai k'yale shegiya mai suffar kwad'o, ai fata na ke Allah ya had'a ni da ita wata rana ta nuna min rashin kunya, wallahi ko kallon da raina bai so ba ta min sai na karya mata k'afa, yar banza hanci kamar bakin sahani (buta) amma sai iya shege a k'ugun ta."
Khadija in banda dariya ba abin da take kafin ta yi shiru tace "Kenan ni ma haka ka ke shammace ni bayan ido na?" Kallon ta ya yi yace "Ah haba dai, ke ai ko mutuwa ta na kunyar idon mahaifi, kin wuce nan wallahi."
Nan fa Nura ya kwashe duk abin da ya faru ya fad'awa Khadija tare da d'orawa da "Kin ganta fa da kod'add'iyar fuska kamar an tafasa kabewa, wai Alhaji ya na bacci, kuma lokacin tashin shi baiyi ba, sai dai ko za ka dawo wani lokaci, ke kinji bak'in cikin da ya taso min a lokacin, kamar na d'auki man da takr suyar da shi na bad'a mata a fuska ta k'arasa sulala."
Rik'e ciki Khadija ta yi tace "Dan Allah bar maganar nan kafin ciki na ya k'ulle, wallahi ba zan iya da masifar nan ta ka ba."
Gyara zaman sa ya yi ya saita nutsuwar sa yace "Kinga ba wannan ba, ni fa dama na zo ne na fad'a mi ki jibi za'a kai kaya na, kuma ke ce wacce na ke so ta shige gaba a komai, dan ni a wuri na kamar ke ce ki ka min auren nan wallahi."
"Ba damuwa Nura, insha Allah zan kasance a duk wata hidima ta auren ka." Sun jima su na hira cikin d'aki kafin ya tashi tafiya bayan ya mata alk'awarin kawo mata amaryar shi bayan an kai kaya, haka ya tafi ya bar Khadija da Bilal da dariya duk sanda su ka tuna iskancin da ya sokawa Haseenah.
Da yamma Usman da kan shi yaje ya d'auko Aziza ya kawota gidan, suna zuwa sun tarar da Mubarak ya kawowa Haseenah maganin ta, Mariya kuma dama maganin mata ne da take anfani da shi ta bado a kawo mata, d'ayan tace ta had'a da madara tasha zai k'ara mata haiba ne da kwarjini a wajen shi, d'aya kuma tace ta binne a cikin gidan, hakan zaisa Khadija ko ta dawo ba za ta iya zama ba saita koma, dan ta k'ara rubtawa da ita kuma tace kafin ta binne ta samu takardar da alk'alami ta rubuta sunan Khadija akai,😂 *yaro man kaza*, Mubarak na tafiya bayan Usman ya gwangwaje shi da kud'i wai ya sa mai a moto, a lokacin anata kiran sallah magriba, Aziza ma alwala ta yi ta kabbara sallah hakan ya bawa Haseenah damar fitowa da maganin ta je wajen wata pliwa mai kyau mai bayar da sanyi wacce ke kusada panpon dake farfajiyar gida, nan ta durk'usa ta sa wuk'a ta tona rame ta binne ledar maganin, duk abinda take a idon mai gadi da yake fitowa daga ban d'aki da buta a hannu ya na kurkure baki, da sauri ya sake komawa ban d'akin ya na lek'owa dan tabbatar da abin da ya ke gani, ya na kallo har ta tashi ta koma d'aki ta yi alwala ta yi sallah, mai gadi ma alwala ya yi a gaggauce ya wuce masallaci, bayan magriba Usman ya shigo saboda zaije ganin Bilal, tun a bakin k'ofa mai gadi ya tsayar da shi ya fad'a mi shi fa da matsala a gidan nan, ya ga wani abun da bai yarda da shi ba, Usman da ya nuna kamar bai yarda ba sai ya ja shi har in da aka binne abun ya kuma sa hannun shi ya tone ya nuna mi shi, warware takardar ya yi duk da baisan me aka rubuta ba, nunawa Usman ya yi yace "Kune yan boko, ko za ka iya gane me aka rubuta anan?"
Da wani yamutsa fuska yace "khadija aka rubuta, sai me?"
Abu dai ya tumbatsa hakan ya sa Usman k'walla kiran Haseenah yace ta zo, nan ta same su tsaye gaban ta na tsananta bugawa tace "Gani."
Nuna mata takardar ya yi da ramin yace "Ke ki ka aje abin nan a ciki?" Da mamaki ta kalle shi tace "Ni kuma? Inji wa?"
Nuna mata mai gadi ya yi, nan fa Haseenah ta shiga rantsuwa ba ita bace Garba ma ya rantse yace da idon shi ya gani, k'arshe dai makirci ne ya yi aiki saboda kuwa kuka Haseenah ta saka ta na fad'in dama kowa ba k'aunarta ya ke ba, kowa bayan Khadija yake kuma ana d'ora mata laifin fitar Khadija daga gidan, dan haka ita ma barin gidan za ta yi in ya so saiya zauna shi kad'ai, hakan zai sa ba za'a zargi kowa ba, haba wa ai sai hankalin maza ya watse ya rasa nutsuwarsa amarsu tace za ta tafi, take a wajen yace mai gadi ya bar mi shi gida tunda dai shima ba k'aunar shi yake ba kuma munafiki ne, sam Garba baiji wani zafin korarshi da akayi ba, dan ya na da yak'inin akwai abin da ke damun ogan shi, dan haka ya kalli Haseenah yace "Kibi a sannu duniya ce ba matabbata ba, tabbas ni ina b'angaren Hajia uwar yarima, kuma wallahi d'an halak ne ni, dan haka zan mata hallaci a lokacin da babu wanda ya yi tsammani."
Juyawa ya yi ya bar gidan bayan ya tattare nashi ya nashi, shi kuma ciki suka shiga saida ya k'ara rarrashin ta ya nuna mata babu fa wanda ya isa ya b'ata ran ta kuma ya yi shiru, saida ya ga murmushin ta kad'ai ya shirya ya kama hanya, anyi sallah isha'i kenan ba jimawa Usman ya zo, k'ofa ya aje mota ya sallamo farfajiyar, yara ne ke ta wasa abinsu kasancewar gobe ba makaranta kamar sallah ce a gurin su, yaran na ganinshi su ka rumtuma wajen shi su ka rufe shi suna gaishe shi, farar ledar hannun shi ya fito da ita ya bawa kowa rabon sa mai alawa da mai chocolat, bawa Bilal sauran ya yi ya shafa kan shi yace "Kawunan ka na nan?"
"Kawu Ashir da kawu Habeeb ne su ka shigo, kuma su na b'angaren su." Wata ajiyar zuciya ya sauke dan ba ya son ganin su ko kad'an, cikin rad'a yace "Hajia fa?" Nuna masa ya yi yace "Ta na falon ta."
Hannun shi ya kama yace "To muje ka rakani na gaishe ta saina koma, sauri na ke." Falon Hajia su ka nufa da sallama su ka shiga ta amsa ta mu su izinin shigowa, zaune ta ke kan kujera cikin riga da zani mai kama da siket, kallo d'aya Usman ya mata ya d'auke kan shi saboda kwarjinin da matar ke ma sa baya iya had'a ido da ita a baya ma bare yanzu da ya san shi mai laifi ne, duk da dai dattakon matar na birge shi matuk'a, dan mace ce mai kamar maza wacce kusan gaba d'aya tarbiyar yaran ita ce ta yi ta, a kunyace su ka gaisa ita kam ganin haka ya sa ta saki fuska sosai fiye da ma farko su na gaisawa, mik'ewa ya yi cike da kunya ya na fad'in "To Hajia ni zan koma, dama ina sauri ne nace dai bara na biyo."
Gyara zama ta yi tace "Maman shi ai ta na ciki, ka wuce ku gaisa sai ka wuce ko." Da wutsiyar ido ya d'an saci kallon ta ya na sosa kai, kama hannun shi Bilal ya yi sai cukuikuyeshi ya ke, kallon shi Mama ta yi ta harare shi tace "Kai dallah miye haka malam sai wani cakumar shi ka ke kamar wani wutsiyar shi, dawo nan ka zauna har ya fito."
Ta nuna mi shi kusa da ita, mak'ale kafad'a ya yi yace "Wai ke ina ruwan ki, ba Abba na bane, karfa ki ga idon Abba na ki b'ata min rai, sai na ce na fasa dawo da ke d'akin ki."
Rufe baki Mama ta yi tace "Ka ji masharranci kuma, to yaushe ka kore ni da har yanzu ba ka dawo dani ba?"
Dariya Bilal ya yi yace "Ka ji ko tsohuwar nan, wato so ki ke Abba ya bani hak'uri na dawo da ke, to na k'i d'in sai kinyi sati d'aya babu kud'in cefanai."
Usman da ke dariya shi dai cewa ya yi "Ka na manta wani abu yarima, na fad'a ma ka kafin ma Mama ta san da kai mu ta fara haihuwa, shin ka na ganin duk yawan mu za mu iya barin ta da yunwa? Abu ne da ba zai yiwu ba ai."
"Ah to fad'a mi shi dai, kuma da ka gan shi nan cika bakin ne kawai, gishiri wannan na dala biyar bai tab'a bayarwa aka siya ba, watak'ila ma ko sabon bebe da zai zo yanzu na yi miji idan na ga ya fika k'ok'arin cefanai."
Dariya Bilal ya yi yace "To ai dai sai na sake ki sannan za ki koma gare shi, kuma idan fa aka haifo min mace ya za ki yi?"
Shiru kawai Mama ta yi sai murmushi da take ta na kallon shi, gwalo ya mata yace "Yeeeehooo, na rufe mata baki, ai ba'a aure akan aure, kuma nasan ke kishi ya mi ki yawa."
Sai lokacin Usman ya juya ya nufi d'akin Khadija, Bilal kuma zaune ya yi kusan Mama ya d'ora kan shi akan k'irjin ta, ture shi ta yi tace "Kai d'aga min nono malam, k'walelen kare da hantar kura fa, tom."
Saida ya sa hannu ya tab'a nonon yace "To me zanyi da wannan tsohon nono, abin duk ya yamutse, ga na Mummy ta nan sabo dal a leda."
Bushewa su ka yi da dariya dukansu ta janyo shi jikin shi su ka rumgume juna, tabbas kamar yanda ta ke matuk'ar k'aunar Khadija matsayin ta na mace, haka a cikin jikokin ta ma take matuk'ar k'aunar Bilal saboda wayon shi, yaro ne mai shiga rai dan shi ko irin mahaukaciyar k'uruciyar nan baiyi ba, hasalima cikin yara za ka ga shi wasan shi ta dabance, sannan bai cika son hayaniya ba kuma baida yawon surutu, idan kaji bakinshi cacaca to sun had'u ita da shi ne.
Tun kafin Usman ya shiga ya ke tunanin abin da suka fad'a na maganar bébé da haihuwa, me su ke nufi? Khadija ciki gare ta kenan? Dama k'ofar a bud'e ta ke dan haka k'arasa tura ta kawai ya yi ya shiga, zaune take akan gado da littafin *hisnul muslum* ta na karantawa, ta na kallon shi ta d'auke kai ta mayar kan littafin tace "Me ya sa ba za ka nemi izini ba kafin ka shigo?"
Saida ya k'arasa shigowa har ya zo daf da gadon yace "Saboda da kai da kaya duk mallakar wuya ne."
Kallon shi ta yi fuska ba annuri tace "Kan na iya zama na ka amma banda kayan saman shi."
Murmushi kawai ya yi yace "Haka ake tarban bak'o a garin ku?"
"Duk bak'on zai iya shiga kowane lungu da sak'o na gida ba bak'o bane, musamman ma irin ka da ba sa neman izini kafin su shiga, kuma ina da tabbaci ba waje na ka zo ba, dan haka me zai sa na damu kai na?"
Kafe ta ya yo da ido ya na kallo kamar ya na karatun wani abu, jin shirun ya yi yawa ne ya sa tace "Bilal fa ya na farfajiyar gida."
"Na gan shi ai." Kallon shi ta yi tace "Hajia kuma ai ta na falo." Saida ya zura hannayen shi aljihu yace "Ita ma mun gaisa."
Mayar da hankalin ta tayi kan littafin ta tace "Da kyau." Ci gaba ta yi da karatun ta shi kuma yace "Ya beby ya ke?"
Cak ta tsaya amma ba ta kalle shi ba sai rarraba ido da ta fara yi, tambayar da take wa kan ta ita ce ya aka yi ya sani? Dan ba ta san Mama ta je ta fad'awa su Hajia ba, rasa abin fad'a ya sa Usman zaune kusan ta ya na k'are mata kallo yace "Kenan da gaske ne? To amma me ya sa ba'a fad'a min ba?"
Kallon shi ta yi cikin dagiya tace "Waya fad'a ma ka ina da ciki? Ko kuma ka na so ka b'ata min rai ne?"
"Ban gane ba? Bayan da kunnuwa na naji Mama ta na fad'a, gashi kuma na tambaye ki amma duk alamu sun nuna gaskiya ne."
Murmushi ta yi tace "Ka taya ni addu'a Allah ya bani nawa nima, amma yanzu ai amaryar ka ce ke da shi, duk da ka ce ina mata bak'in ciki."
Kafe ta ya yi da ido yace "Ki rantse da Allah ba kya da ciki." Cikin mamaki tace "Rantsuwa kuma? To miye na rantsuwar? Abin da na ke nema ido bud'e zan samu kuma na kasa fad'a ma ka."
"Ba ki ke nema ba dai, mu ke nema, kar ki manta da haka, har yanzu ina son sake ganin abin da zai fito daga tsatsonki." Kallon shi kawai ta yi shi kuma ya mik'e yace "Kin dai tabbatar ba ki da komai?"
"Eh." Ta fad'a, sake jajjadawa ya yi "Kin tabbatar babu?" Cikin k'osawa tace "To! Na ce babu, babu, idan ba ka yarda ba ka je ka tambayi su Maman ka ji, su a zatonsu ne ciki gare ni saboda rashin lafiyar da na yi, ni kuma wahala ce ta sani wannan rashin lafiyar na dukan da ka min."
Murmushin gefen labb'a kawai ya yi ya sunkuyo da kan shi kusan fuskar ta yace "Kin tabbatar dai ba kya tare da ciki na ko?"
K'asa ta sauke idon ta hakan ya sa yace "Sai kin kalli ido na." Kallon shi kam ta yi tace "Eh, babu komai." Tsaye ya mik'e yace "Shikenan, amma ki tabbatar duk ranar da na ji labari yasha bambam wallahi sai kin gane kurenki."
Saida ta sake kallon idon shi tace "Na yarda." Jinjina kai ya yi yace "Shikenan, saida safe."
Juyawa ya yi ya fice daga d'akin ta bishi da kallo, saida ta tabbatar ya bar gidan ta fito ta samu Mama ta tambaye ta, ba ta b'oye mata komai ba hakan ya sa tace dan Allah kar su sake ya san ta na da ciki, dalili Mama ta tambaya saita nuna mata kawai ba ta so ya sani yanzu, dan ta na tsoron rashin imanin yarinyar nan matar shi.
*Bayan kwana biyu* an kai kayan Nura, kuma kamar yanda ya fad'a Khadija ma saida ta halarci kai kayan, kuma da yake a dangi ma ba kowa bane yasan abin da ya faru, Haseenah dama ba ta je ba dan haka ma ba su had'u ba, anje lafiya kuma ayi duk abin da ya dace, lokaci kawai za'a jira *wata uku* mai zuwa lokacin hutun farko na yan makaranta, duk lokacin da biki ya taso irin haka akwai wanda Khadija ce ta ke mu su d'inkin anko, yanzun ma ba ta gaza ba ba ta kuma duba abin da ya faru ba, haka ta d'inka kaya kala takwas ta aikawa kowa na shi daga ciki har da Hajia da kuma k'annan ta guda uku, k'annan Baban Usman biyu sai wasu tsofaffi biyu suma, kamar yanda Nura ya yi alk'awari ya kawo Choukra ta wuni gidan su Khadija, sai dare ya zo ya d'auke ta su ka koma bayan tasha goma ta arzik'i.
*Haka* abubuwan suka ci gaba da tafiya da dad'i ba dad'i, Khadija na kula da cikin ta cikin kulawa sosai, Bilal na karatun shi hankali kwance ba tare da matsala ba, ranar da babu karatu kuma Khadija na kiran Nura ya zo ya d'auke shi ya kai shi wajen su Hajia, amma basu tab'a katarin had'uwa da mahaifin shi saboda yanzu gida sai su yi sati kwana shida ko biyar basu gan shi da idon su ba, wayar ma sai da k'yar ake iya samun shi wani lokacin, kuma har yanzu bai san Khadija na da ciki ba, dan malam yace ba ya so ya sani sai in Khadija ce ta fad'a mi shi ko kuma ya gani da kan shi, a haka har aka cinye wata *uku* wanda ya yi daidai da fara shagulgulan bikin Nura, a lokacin Khadija har ta fara zuwa awo dan cikin ta na wata *biyar* ne har ya fito ta yanda duk wani mai ido zai iya ganin shi, tun kwana biyu saura Khadija ta turo Bilal ya kwana nan har zuwa ranar bikin tare da gudummuwarta da na Mama da kuma ta su Ashir, gudummuwar da suka bayar ko yan uwanshi babu wanda ya mi shi wannan bajin ta.
Wajen Haseenah ma haka abin yake, abin da ranta ya so ta ke ci tasha wanda ya mata, Aziza tuni ta jima da gane kurenta, dan kuwa duk aikin gidan ne ita ce ba dare ba rana, idan ba ta yi ba Usman ya balbale ta da jaraba, Haseenah na zaune ta na gatsar 'ya'yan itatuwa, sa'a d'aya shine ba'a cika yin girki a gidan ba kusan kullum saida a siyo daga waje, wani lokacin Aziza ta ci idan an siyo ko kuma ta d'ora wani abu ta ci, duk wannan bai cika damunta ba kamar yanda ta ga Usman ya zama kamar karan farautar Haseenah, in dai ya na gari to ya na gida nanak'e da ita ko gajiya ba ya yi, duk bak'on da zai zo wajen ta to fa haka zai dinga rawar jiki ya na aikawa ana siyo musu abin tab'awa, idan sun tashi tafiya kuma ya wadata su da kud'i da sunan kud'in taxi, haka ita kan ta Haseenah kud'i yake kashe mata kamar ba gobe, a wata *ukun* nan sai Haseenah ta shirga wata murgujejiyar k'iba, masha Allah ko fa kai mak'iyinta ne ka ganta dole k'ibar da ta yi ta burge ka dan ta mata kyau, hakan kuma ya sa Usman sake narke mata dan abun har kusan haukata shi take, ga magunguna da take aiki da su, ga k'iba (wanda kowa yasan akwai sirrin dake tattare da k'iba ba) ga kuma ciki, duk tsiyar nan da ake tsulawa Aziza ta kasa fad'awa kowa saboda kunya, to idan ita ma tace ta mallake shi kenan tsakanin ita da Khadija wacece ta mallake shi? Hakan ya sa ta yi shiru, ko gida taje idan aka tambaye ta wai ya na nan sai dai tace eh, idan ya na nan d'in, dan yanzu ko balaguro ya yi da k'yar yake iya sati d'aya zuwa kwana goma ya dawo, shiru take yi ba ta fad'a mu su komai inda su kuma su ka damu sosai su ka fara maganganu akai.
*Yau* Alhamis ya rage nan da kwana biyu za'a d'aura auren Nura, su Rabi'a sun hallara ana ta kujuba-kujuba Aziza ta shigo gidan, dukan su kallon ta su ka yi da mamakin ganin ta ita kad'ai, Husseina ce tace "Aziza ke kad'ai ki ka taho?"
Saida ta nemi gurin zama tace "Ni kad'ai na taho."
"Ina Haseenah?" Cewar Rabi'a, tab'e baki ta yi tace "Ta na gida, wai ba ta jin dad'in jikin ta."
Hajia da ita ba wannan ne damuwar ta ba cewa ta yi "Ina shi Alhajin ya ke?"
"Ya na gida na baro shi, na ji ya na cewa ko zai kai ta asibiti." Girgiza kai Hajia ta yi tace "Allah ya kyauta, gaba d'aya ta mayar da shi wani sha-katafi, ko motsi taji a cikin ta sai ta fad'a mi shi shi kuma sai yace aje asibiti."
Tab'e baki Aziza ta yi tace "Ai kam ba shi da maraba da shanyayye."
"To ai ba kama bace, duk alamu sun nuna shegiyar yarinyar nan ita ce mai laifi, wallahi sai yanzu ne nake na tabbatar da tun farko *kallon kitse mu ka yi wa rogo*."
Nura da ke fitowa daga d'akin shi cikin sauri ne ya kalle su dukansu yace "Ku sai yanzu ma ku ka sani kenan? To mu zuba zuwa mu ga mu da ku waye zaiyi nasara, 'yan bayan Khadija ko 'yan bayan wannan mai kama da agwagwar."
Hajia ce tace "Abun bak'in cikin ma wallahi ta yanda gaba d'aya ta raba shi da mutane, d'an taimakon da muke san mu mi shi bamu ma gan shi ba bare mu taimaka d'in, amma ba dan haka ba da yanzu nasan komai ya wuce, kuma kinga shi malam ya ma bar maganar kamar baisan me ke faruwa ba."
Nura dai ficewa ya yi ya kama sabgar gaban shi sai Rabi'a da tace "Ai kuwa ba za mu yarda ba wallahi, ni zanje gidan na ga me ke faruwa, wallahi saina fad'a mata magana."
"Ai kuwa in ban cire ki a cikin dangin shi ba to tabbas zaki sha dukan tsiya." Cewar Aziza, da mamaki Rabi'a tace "Kamar ya duka? Ba shi da lafiya?"
Aziza ce tace "Lafiyar shi lau, amma babu mai tab'a ta ya yi shiru, akan haka fa ya kori Garba mai gadi."
Hajia ce tace "Ni kai na da zan ganshi da sai ran shi ya b'ace, tunda aka fara hidimar nan har yanzu banga k'eyar shi gidan nan ba, kuma ni har yanzu daga Nura har malam banji wanda yace ya bashi gudummuwar bikin nan ba, akwai abubuwa dayawa wanda da shi ne mu ka dogara, ba dan Allah ya rufa mana asiri ba yanzu yarinyar nan sun aiko da wannan gudummuwar ta su da ya za mu yi."
Hassana ce tace "Bai fa bayar da komai ba hajia?"
"Ni dai bai bani ba, kuma Nura da malam ba su fad'a min ba, kinga ko abune mai wuya ace sun kasa fad'a min."
Husseina ce tace "Ah ba ma ta yiwu ai, in har ya bayar dole sai ki sani Hajia."
"To me ya ke nufi? Ba zai bayar ba ko ta hana shi?" Cewar Rabi'a, Hajia ce tace "Gidan fa da za akai amarya ma Murtala ne ya bashi gidan, da ina jin har yanzu ba mu san ina za su zauna ba."
"Wallahi sai naje, sai dai ya kashe ni." Cewar Rabi'a cikin b'acin rai ta na mik'ewa ta yi kam ba b'ata lokaci ta saka hijabin ta, Hassana ce tace ita ma za ta je ta jira ta, Husseina dai cewa ta yi "Allah ya kad'e hau." Ko amsata ba su yi ba su ka tafi, cikin k'ank'anin lokaci su ka isa gidan, sunyi nasarar samun falon Haseenah bud'e, shiga su ka yi da sallama amma ba kowa sai telebijin ita kad'ai, zaune su ka yi sai Rabi'a da ke ci gaba da rumtuma sallama dan suji su fito.
*Alhamdulillah Ala ni'imatul islam.*
27/02/2020 à 13:42 - 💋😘💋: 💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
*KALLON KITSE*
_(Ake wa rogo)_
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
_SAMIRA HAROUNA_
*Litattafan marubuciyar*
*1* _KAUSSAR_
*2* _D'AUKAR FANSA_
*3* _BA SO BANE_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI_
*6* _JIHADI_
*7* _K'ANGIN RAYUWA_
*8* _ITACE K'ADDARARMU_
*9* _KAWU NA NE_
*10* _MAATA_
*11* _KALLON KITSE..._
*SADAUKARWA GA*
_MATAN FARKO_ 🧕🏼 *(UWAYEN GIDA)*
🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_🤜🤛
```Fatan alkairi masoya```
_Bismillahir rahamanir rahim_
*33*
Tun su na sallama har su kai su ka yi shiru babu wanda ya amsa, suna magana k'asa kasa su ka ji an bud'a k'ofa, mayar da kallon su su ka yi ga mai fitowa, wa za su gani in ba Usman ba da doguwar riga kamar wanda ya taso daga bacci, da kallo su ka bishi har ya k'araso ya zauna ba su daina kallon shi ba, cikin wani cijewa yace "Ashe kune? Daga ina haka?"
Hassana ce tace "Ina wuni?" Bai amsa ba sai shafa kan shi da ya fara yi, Rabi'a ce tace "Dama Hajia ce tace mu zo mu ga ko kuna lafiya, daga kai har Hassenah ta jima ba ta gan ku ba."
Kamar wanda aka takura wajen maganar ya ke fad'in "Tsohin nan matsala ce da su wallahi, ko shekaran jiya fa na je gidan mun gaisa, lafiya k'alau na ke ni, ita ce ma dai ba ta jin dad'i, yau lafiya gobe ba lafiya."
Hassana ce tace "Shi ya sa har an fara shagulgulan bikin nan amma har yanzu babu wanda ya gan ta? Yah Fodio ka na ganin hakan ya yi daidai domin Allah, akwai fa abubu..."
"Ke dakata." Ya katse ta ya na mik'ewa tsaye, da yatsa ya nuna ta yace "Ke ma 'yar hassadar ta ce kenan? To da alama ba Hajia ce ta turo ku ba kun zo ne ku min rashin kunya, to ba na da lokacin ku, idan kun gama ku rufe mana k'ofar."
Ai kuwa ya na gama fad'a ya koma in da ya fito ya bar su nan, kallon juna su ka yi Rabi'a tace "Kutumar bala'i, yanzu haka abin ya zama dama? Lallai."
Mik'ewa Hassana ta yi tace "To ai sai mu tafi ko? Tunda ba gidan uban mu bane."
Fita su ka yi su ka bar gidan ba yanda su ka iya, ko da su ka je gida nan fa aka bud'a sabon shafin hira akan abubuwan da ke faruwa, duk da haka kuma Aziza babu abin da tace dan ita dai kam kunya ma take ji, ana sallah magrib Usman ya dokowa Aziza kira wai ta zo gida ya na son ganin ta, gabanta ne ya dinga fad'uwa tunanin ta kar ace ya yi tunanin ita ta fad'a mu su wani abu, da k'yar ta kimtsa ta fito jiki na rawa ta zo bakin titi kuma ta kasa samun adaidaita da wuri, hakan ya sa ta sake b'ata lokaci kafin ta je, ta na zuwa gidan ran Usman ya gama b'aci saboda Haseenah ce ke neman ta amma ta b'ata lokaci, dan haka ta na shigowa falon saukar mari ne ya mata maraba, bai tsaya iya nan ba saida ya dinga masifa wai ta na can ta samu gulma ta bar aikin gida anan, Haseenah na zaune kan kukera ta kalle su tace "Kai ba ka yi mamakin zuwan su Hassana ba? Ai bayan fitarta ne su ka zo ma'ana ta fad'a mu su wani abu, suna can gidan ku sun baza tabarmar gulmata su na yi da ni, dan nasan dama babu mai so na kafatanin ahalin ka."
Ido ya rufe ya dinga zagin Aziza kamar ba ciki d'aya su ka fito ba, kafin daga bisani yace ta wuce ta gyarawa Haseenah d'akin ta, da "To." Ta amsa, ta na kallo ya kama hannun Haseenah suka nufi falon shi, ta na ganin haka ta shiga d'akin da take kwana ta gama had'a kayanta ta fito ta bar gidan, tunda ba za ta iya rama marin ta ba amma kuma in ba ta bar gidan ba tasan dole wata rana za ta jiwa Haseenah ciwo, dan haka ta bar gidan ba tare da sanin su ba ta koma gida.
Bayan sallah la'asar aka ce ana sallama da Khadija, da mamaki ta fita amma wa za ta gani sai Baba Garba mai gadi, da fara'a kamar za ta had'e shi ta mi shi izinin shiga ciki, har falon Mama ta saule shi in da Mama ke zaune ita ma, gaisawa su ka yi sosai kafin ya fara da "Hajiar yarima bayan barin ki gidan nan abubuwa da dama sun faru, tabbas mijin ki ba'a hayyacin shi ya ke ba, shiga baga ne kawai, amma insha Allahu komai ya k'are tunda har na je gida lafiya na dawo lafiya, kin gan shi nan abin da ya tsayar da ni." Ya fad'a ya na mik'o ma Khadija wani k'ullin magani k'arami, karb'a ta yi ta na kallo kafin ya d'ora da "Wannan maganin na karya sihiri ne, wani kaka na ne ya ke bayar da shi, maganin ya na da wuyar samu sosai, hakan ya sa ya ke da tsada ga wanda zai siya duk da dai ba ya da farashi, amma ke kyauta na karb'o mi ki shi saboda girman ki, Hajiar yarima wannan maganin da ki ka ji da ganin shi wallahi na rantse mi ki ko da bokan india mutum ke tink'aho to anfani da shi saiya karya komai, ba na da tamtama akan shi, tabbas na ke da, ki jaraba shi ki gani da yardar Allah za'a dace."
Ba tare da ta daina kallon shi ba tace "To amma ya ake anfani da shi?"
Da yatsa ya ke mata alama cewa "A buta za'a zuba maganin sai a saka ruwa ya yi wanka da shi, idan ya fito ya tsane jikinshi sai a samu garwashin wuta kuma a zuba maganin ciki a turara, ba dole sai ya shak'a ba ko yaje kusa da wutar, jikin shi ne kawai ake so hayak'in ya shafa lokacin da babu sutura a jikin shi, sai kuma wannan." Ya fad'a ya na sake mik'o mata wata ledar yace "Wanna kuma a tabbatar ya shak'a a hanci sau uku, insha Allahu idan ya shak'e shi zaiyi atshawa, to da izinin Allah duk wani bala'i dake kansa zai bar shi ko ba'a so."
Daga Khadija har Hajia godiya su ke masa amma ya na cewa ba komai, haka ya tashi tafiya su ka bashi kud'in mota ma amma ya k'i karb'a yace ya yi ne saboda Allah kawai, sai lambar shi kawai sabuwa da Khadija ta karb'a ta na ci gaba da k'ara masa godiya, nan su ka shiga tattauna yanda za su saka Usman yin wanka da maganin nan, gaba d'aya kan su ne ya kulle dan haka Mama tace kawai ta bari har bayan bikin Nura in ya so sai su san abinyi, haka akayi Khadija ta kai maganin ta nasa a cikin jakar ta da ke kusa da gado, bayan sallah magrib kuma su ka yi waya da Bilal har ya na fad'a mata shi gaba d'aya surutun gidan ya dame shi, tunda yamma ake ta maganar Abban shi da matar shi har ya fara jin haushin mutanen, hak'uri ta bashi tare da cewa ya fita waje yanzu ai da malam ya shigo zai zauna k'ofar gida, haka akayi kam sai k'ofar gidan kad'ai ya samu nutsuwa.
Ko da Aziza ta zo ana sallah isha'i lokacin malam da Bilal na masallaci, da kuka ta shigo gidan aka tarbe da tambayar lafiya? Nan ta fad'a ma Hajia abin da ya faru kuma ran ta ya b'ace sosai, wannan karan an tab'a mata autar ta dan haka dole rai ya b'ace, ji ta yi ba za ta hak'ura ba dan haka ta kira shi a waya, ya na d'auka ita ma ta zazzage shi da masifa har ta na fad'in ya zama lusari yarinya k'arama na juya shi, shi dai k'ala bai ce ba har ta gama ta kashe wayar, sai lokacin ne su ka san Aziza ba ta gidan, ko a jikin su kam dad'i ma su ka ji da ta tafi d'in.
*Washe gari* ta kama juma'a, malam na sallah asuba ya dawo gida ya canza kaya ya fita, a k'asa ya ke tafiya cikin nutsuwa ya na zikiri har ya yi doguwar tafiya, tashar mota ya isa da ke *'yar sonita*, mota ya samu da babu komai a ciki ya fad'i garin da za shi, saboda biyan buk'ata yace shata ya ke so a kai shi a dawo da shi, dama garin ba wani nisa ne da shi ba, nan ya shiga tare da dreba su ka d'auki hanyar da zai sada su da wani k'auye da ake kira garin *Bamo*, har k'ofar gida aka aje shi ya kusa yi sa'ar samun wani tsoho da ba za su gaza wari ba a k'ofar gidan akan tabarmar kaba, daga yanda suka gaisa suke dariya zai nuna ma ka ba sanin yau bane ko kuma ma abokai ne, zaune su ka yi daga cikin wata runfa dake gefe akan wata tabarmar da ke d'auke da buzun akuya, nan ne har tsohon ya ke fad'in "Mu muna shirin tafiya garin auwa yamma kuma kai sai ka ga, lafiya kuwa?"
Ajiyar zuciya malam ya sauke yace "Lafiya ba lafiya ba *Lawali*, halin da gidan nan ke ciki ne ma ya sa na kasa hak'ura har yamma ta yi ka zo ni na zo da kai na."
Cikin nutsuwa yace "Toh, me ya ke faruwa ne haka malam Ali?"
Nan dai bai tsaya b'ata lokaci ba ya fad'awa tsohon abin da ke faruwa a gidan na shi, malam Lawali ne yace "Amma yanzu har wannan iskancin na faruwa amma ka kasa sanar da ni, wannan shegentakar har ta bar kan wasu ta dawo kan yaran mu, gaskiya banji dad'i ba da sai yanzu ka ke fad'a min."
"Da farko na d'auka abun na ta ba zaiyi k'amari haka ba, amma daga yanda ta raba shi da kowa na shi ne ya nuna min ita d'in dama ba mai son shi da arzik'i ba ce, na fara bashi taimako da kai na wanda na san zai warware komai cikin sauk'i, to matsalar da aka samu baya ma zuwa gidan akai akai bare har maganin ya karb'i jikin shi, shi ya sa na ce to bari na sada matsalar nan da kai."
Cikin b'acin rai Lawali ya mik'e ya nufi cikin gidan shi ya na fad'in "Ina zuwa bani minti biyu, wannan ai maganar banza ce da wofi, mu za'a kawowa iskanci har gida, yo badan ma yaran sun zama 'yan zamani ba basa son shan saiwa na tsarin jiki yo da ko kusa da shi ta isa ta zo ma, kuma kai ma da ka fad'a min da wuri da ko kwana d'aya ya yi a cikin tarkon ta, ga dukkan alama ba ta san wata aura ba shi ya sa, mu da ake baro k'asa mai tsarki azo neman taimako wajen kuma a dace da yardar ubangiji shine har d'an mu zai shiga wannan halin kuma ya kwashe watanni a kasa fito da shi, aikin banza aikin wofi." Haka ya shiga gidan ya na ci gaba da bambami har ya shiga d'akin shi ya d'auko wasu sayun magani fari dogaye ya fito da shi, kawo mi shi ya yi yasa a leda ya zauna kan kujera ya juya bayan shi ya d'auko robar lemu sai dai ruwa ne a ciki fari tas ya bashi yace "Da wannan ruwan za'a jik'a magani, ruwan da ya yi alwalan sallah magriba da su sai ka cire maganin a zuba ruwan alwalar, idan ya yi sallah sai ya yi wanda da su amma a buta za'a zuba ruwa."
"Na fahimta, nago..." Katse shi ya yi da cewa "Kar ka fara min godiya, in ba haka ba maganin ba zaiyi ba ma, ko ka manta wanene kai a wuri na?"
Dariya malam Ali ya yi ya mik'e, saida ya shiga cikin gidan su ka gaisa da matan kafin ya fito ya samu dreban nan su ka wuce da cewa sai sun zo suma wajen bikin Nura, kamar bai je ko ina ba sai gashi ya dawo ko rana bata gama haska duka gari ba, jika maganin ya yi da wannan ruwan kafin ya shiga wata sabgar ba tare da ya fad'awa kowa ba.
*Yamma* lik'is Khadija ta fito bayan ta biya ta karb'owa Bilal sabon d'inkin shi sannan ta zo gidan, ta na sallama kam gida dama ya samu hallarar dangi har an fara d'ora tukunyar abincin d'aurin aure, nan fa kowa Hajia Khadija Hajia Khadija, sosai ta gaisa da mutane kafin ta wuce d'akin Hajia, abun mamaki sam Hajia kasa had'a ido ta yi da ita sai haka suka gaisa cikin kunya, su Hassana ma da Rabi'a haka, sai ma wani sabon al'amari daga gare su na kowa ya na son ya mata magana, wurin zama suka samar mata tare da kawo mata ruwan sha da lemu, sai dai suma ba kowa ke kallon ta ba, ita kam ko a jikin ta sai dai ba ta sakar mu su fuska ba, kuma ta zo gidan nan dan ta ga malam ta bashi wannan maganin, dan ita bata san yanda za ta sa shi ya yi wanka da shi ba, ganin sun baibaiye ta ya sa ta fito tace su yi aiki, sai lokacin Bilal ya shigo Khadija ta tambaye shi ina malam? A cewar shi ya na k'ofar gida tare suke da shi ma, aika shi ta yi ya yo ma sa magana, a soron gidan su ka had'u da malam in da ta bashi magungunan ta fad'a mi shi duk yanda akayi, murmushi malam ya yi ya mata godiya tare da fatan alkairi, ciki ta koma ta yi zaune su na b'are tafarnuwa, malam kuma na fita ya kira Usman a waya ya na d'auka yace "Duk abin da ka ke ka zo gida yanzu ka same ni."
Usman da ke tsaye gaban gado ya na kallon Haseenah ta na shiri zai kai ta can ne yace "To malam, dama yanzu za mu taho gidan."
Datse kiran kawai malam ya yi yayin da ya bi wayar da kallo, kallon Haseenah ya yi da ta mik'e ta saka hijabin da ya dace da kayan ta haka ma jaka da takalmi, a gaskiya ta yi kyau sosai cikin wani bak'in leshi mai ji da kud'i da kyau, kwalliyar da ta yi kai kace yau ne bikin kuma ba aiki ne za ta tafi kamawa ba, wayoyinta biyu ta d'auka duka a hannu ta rik'e suka fito, da kan shi ya bud'e mata k'ofa ta shiga kafin ya ja suka bar gidan yamma ta k'ara yi sosai.
Daga nesa ne aka fara kiran sallah hakan ya sa Khadija tashi ta yi alwala ta shiga d'aki dan yin sallah, ta na shiga d'aki ta kabbara sallah ta ji sallamar Usman, saida gaban ta ya fad'i kafin ta saita nutsuwar ta ta ci gaba da sallar ta, gaisawa ya yi sosai da mutanen da ke wajen in da Haseenah ke gaishe da mutane ciki-ciki, fita ya yi tare da malam ysu ka yi alwala in da malam ya tara ruwan shi ya aje suka nufi masallaci, mata ma alwala suke su na sallah, Khadija na fitowa daga d'aki Haseenah za ta shiga, dukansu gadara su ka nuna in da Haseenah ta had'a da girman kai da raini, babu wacce ta matsawa wata dan ta wuce hakanne ya sa su ka bangaji kafad'un juna su ka wuce, tsaki Haseenah ta k'ara da shi wanda ya sa Khadija jawo hijabin ta ta kalli fuskarta tace "Kamar tsaki na ji kinyi ko? Da ni ki ke?"
Cikin nuna isa tace "Sake min hijabi malama." Dawowa Khadija ta yi cikin d'akin yanda ta ke fuskantar ta da kyau, k'ara shak'o hijabinta ta yi za ta yi magana Hassana ce ta shiga tsakani tace ma Khadija "Dan Allah yi harkar gaban ki, kinsan sai ka kula kashi ka ke jin warin shi, kare kuma ai ba ya haushi shi kad'ai."
Kallon ta Khadija ta yi tace "Ta ci albarkacin ma su albarkaci." Ta na fad'a ta fito daga d'akin ta na mu su sallama, Haseenah kam kallon Hassana ta yi wato ma ita ce karyar? K'wafa ta yi a ran ta ta zauna ko sallah ba ta yi ba, ta na kaiwa k'ofar fita malam ya tiso k'eyar Usman zuwa d'akin shi, tsaye ta yi su ka yi sallama da malam Usman kuma idon shi na kan cikin ta dake cikin hijabi ya ke ganin kamar gizo, shigewa malam ya yi Usman kuma ya tsaya bakin k'ofar k'ik'am, rab'awa Khadija ta yi za ta wuce sai kawai ya had'a ta da bango ya rufe kamar zai rumgume ta, kallon fuskar ta ya ke cikin wata irin murya yace "Me na ke gani a jikin ki ne haka?"
Fuska a had'e ta kalle shi ta na sake gyara hijabinta tace "Me ka gani?" Hannu ya zuro zai tab'a cikin ta yi saurin bige hannun shi ta ture shi ta kalle shi tace "Ka zama mai d'a'a mana, haka kawai sai ka tab'a jiki na."
Za ta fita ya rik'o hijabin ta yace "D'a'a? Ni ne marar d'a'ar?" Kafin ta yi magana ya fizgo ta ya had'a da bango, saida ta rintse ido tace "Ashhhhh." Saboda zafin da taji, hannu ya sa cikin hijabin ta ya na fad'in "Bara kiga rashin d'a'a, ke da kinsan ba na da d'a'ar kuma ki ka aure ni? Yanzun ma fitsara za ki min kenan." Da sauri ta rik'e hannun shi da ke shirin shafa cikin ta, kallon idon ta ya yi yace "Ban sani ba ko gizo ne ido na ke yi min, amma sai na ke gani kamar ciki ne a jikin ki."
Shiru ta yi ta kasa d'ago kai ta kalle shi, hannunta da ta rik'e na shi hannun ya kama yatsunta sosai ya na murzawa tare da juyasu son ran shi, tun ta na jurewa har ta fara matse ido saboda mugunta ce yake mata, jin idon ta na neman kawo ruwa ne ya sa ta kalli cikin gidan tace mi shi "Malam fa na jiran ka."
Da sauri ya saki yatsunta ya d'an ja baya ya juya ya kalli cikin gidan shi ma, ta na ganin haka ba ta b'ata lokaci ba wajen takawa da sauri ta bar soron gidan, juyowa ya yi dan ya kalle ta sai ya ga wayam, cije leb'e ya yi tare da k'wafa yace "Wato ni za ki rainawa hankali ko, ki na d'auke da ciki na amma ki na b'oye min, wallahi na tabbatar da gaskiya sai ran ki ya yi mugun b'aci, sai kin gane ba'a min haka a zauna lafiya."
Ciki ya shiga ya samu malam a d'akin shi, abun mamaki shine izini da malam ya masa ya shiga ban d'akin shi ya yi wanka da ruwan da ke cikin bokiti, idan ya gama sai ya d'auki wanda ke cikin buta suma ya yi wankan da su, yanda fuskar malam ke had'e ya sa dole bai iya tambayar komai ba face shiga ya yi abin da aka ce, tunda ya yi wanka da ruwan cikin bokitin nan ya ji kan shi ya masa bala'in nauyi, jiri ne ya dinga d'ibar sa har saida ya rik'e kan panpo kafin ya ji ya fara masa sauk'i, butar ya d'auka ita ma ya kwararo ruwan daga sama har k'asa, rawa ya ji jikin shi ya d'auka kamar mazari, bala'in da yake ciki ne ya sa ya kasa sako kayan shi sai towel d'in malam da ke rataye ya d'auro ya fito, malam na zaune ya na jiran shi da kaskon garwashin wuta, har zaiyi zaune saboda abin da yake ji sai malam yace "Dakata."
Tsaye ya yi malam yasa maganin nan ya na kewara shi da shi, Usman da hatta numfashin shi ya fara canzawa kasa tsayuwa ya yi sai kawai ya fad'i k'asa kwance ya na rawar d'ari, k'amk'amewa ya yi sosai ya na rawar d'ari, sunkuyawa malam ya yi yace "Fodio lafiya ko? Me ka ke ji?"
Cikin hard'ewa da hak'oran sa keyi ya iya had'a kalmar "S...ss..an..yi...na..ke.ji." Aje kaskon malam ya yi ya shiga uwar d'aki ya d'auko mi shi bargo ya na zuwa ya rufa ma sa, d'auko wannan garin maganin ya yi ya zauna k'asa kusa da shi ya bud'e ledar ya dangwalo da yatsunshi biyu ya kara masa a hanci yace "Shak'a, shak'a Fodio kaji."
Shak'awa ya yi duka hudar hancin shi kafin yaja zanin rufar ya sake rufe kan shi, mik'ewa malam ya yi amma shi kan shi saida ya yi atshawa guda hud'u, Usman kam da ya kama atshawa tun ya na yi daga zaune har saida ya bud'e rufar ya tashi zaune, atshawar da ya yi ba iya ka kafin ta tsagaita mi shi, jingina ya yi da kujerar da ke bayan shi ya na dafe da kan shi, da k'yar ya fara furta "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un, inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un, la'ilaha illalah, Muhammadur- rasulillahi sallalahu alaihi wassalam."
Matsowa malam ya yi kusan shi yace "Fodio ya ka ke ji yanzu?" Ya na dafe da kan shi cikin yamutsa fuska yace "Gaba d'aya ji na ke kamar ba ni ba, kamar na farka daga wani mummunan bacci na ke ji."
"Alhamdulillah, Allah kai ne abin godiya." Cewar malam kafin ya mayar da kallon sa ga Fodio yace "Ka tashi ka saka kayan ka sai ka samu ka je gida ka kwanta ka huta ko, amma dan Fodio a daina wasa da addu'a, ba zance sakaci da addu'a bane ya ja abin da ya faru, saboda kuwa na sanka sosai ba ka wasa da ibada, amma dai ka sake zage damtse ka ji."
Mik'ewa ya fara yi da k'yar yace "Insha Allahu Baba, amma wai me ya faru da ni ne?"
"Idan ka je gida ka huta mayi magana wani lokacin."
Jiki a matuk'ar sanyaye ya sanya kayan shi ya fito daga d'akin wanda ya yi daidai da fara kiran sallah isha'i, haka ya wuce ba tare da ya kula kowa ba saboda abin da ya ke ji, a k'ofar gida ya samu Bilal zaune akan tabarmar malam ya yi alwala, shi ma alwalar ya yi suka nufi masallaci tare, bayan sun fito ne Usman ke tambayar shi "Wai ina sarauniya ne ban gan ta ba?"
D'aga kai Bilal ya yi ya kalle shi kafin yace "Mummy na na gida ba ta jima da tafiya ba." Ji ya yi sam babu wani abun da ya ke iya tunawa ma a kan shi a halin yanzu, kallon Bilal ya yi yace "To ni yanzu gidan zan tafi, za ka je ne ko kuma na barka?"
"Um um, Mummy tace na zauna nan sai an gama bikin kawu Nura." Shafa kan shi ya yi yace "To shikenan ni zan tafi, ka kula da kan ka kaji ko."
Saida ya sunkuya ya sumbace shi kafin ya shiga motar shi ya wuce gidan shi saboda tunanin shi Khadija na can,😂 tsohon zance, ai kuwa da ya je dai bai samu samu kowa a gidan ba, kiran Khadija ya yi yace "Ki na ina ne?"
Da mamaki Khadija tace "...
*Lokacin Haseenah fa ya fara fan's, yanzu nasan za ku ji dad'i.*
_Ma chérie *Hakeema* barka da samun k'aruwar 'ya mace, Allah ubangiji ya raya mana ita akan sunna, zafa musha shoki yan uwa😎 nasan baku tab'a gani na ina kwaso shoki ba._
01/03/2020 à 14:18 - 💋😘💋: 💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
*KALLON KITSE*
_(Ake wa rogo)_
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
_SAMIRA HAROUNA_
*Litattafan marubuciyar*
*1* _KAUSSAR_
*2* _D'AUKAR FANSA_
*3* _BA SO BANE_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI_
*6* _JIHADI_
*7* _K'ANGIN RAYUWA_
*8* _ITACE K'ADDARARMU_
*9* _KAWU NA NE_
*10* _MAATA_
*11* _KALLON KITSE..._
*SADAUKARWA GA*
_MATAN FARKO_ 🧕🏼 *(UWAYEN GIDA)*
🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_🤜🤛
```Fatan alkairi masoya```
_Wannan page ta ki ce ke kad'ai mahaifiya kuma maman mu da tafi kowa, my sweet and lovely ki bayar da wannan page ga *Momy na*, Allah ya k'ara girma da lafiya mai anfani._
_Bismillahir rahamanir rahim_
*34*
"Ban gane ina ina ba?"
Cikin tausasawa yace" To ranki shi dad'e Hajia uwar yarima ina aka je ne?
Saida ta furzar da iska tace "Ka fad'a min abin da ya sa ka kira ni amma ba wannan ba."
A hankali yace "Nana Khadija ina k'ofar gida yanzu haka kuma babu kowa a ciki, sannan daga gidan su Hajia na ke ba kya can, yarima yace min kin zo gida amma kuma ban same ki ba, ina ki ka je ki fad'a min?"
"To me za ka min da ka damu da sai ka ganni?" Ta fad'i hakane saboda tasan in har cikin jikin ta to fa ta shiga uku, dan sai ya yi mata abin da yace zaiyi, shi kam a cewar shi "Ina son ganin ki ne, ki fad'a min ina ki ka na je na d'auko ki tunda na ga motar ki aje."
Haushi ne ya kamata tace "Kaga malam ina d'an wani aiki, sai anjima." Datse kiran ta yi ya bi wayar da kallo, a hankali ya furta "Me ya samu Khadija ta ne haka? Ba ta min irin haka fa."
Shawara ya yanke ya kira wayar Hajia, ta na d'auka yace "Hajia Khadija na ce ko ta na nan gidan?"
Da mamaki Hajia tace "Khadija kuma, ai ko da ta yi sallahn magriba ta tafi gida."
"To Hajia kuma gani a k'ofar gidan ba ta nan, na kira ta kuma ta k'i fad'a min in da take."
Yanda ya ke maganar cikin damuwa ya sa Hajia cewa "To ka shiga cikin gidan mana sai ka tambayi Hajiar ta, ita ai ba za ta kasa fad'a ma ka ba, ita ma nasan ba ta fad'a ba ne saboda ta na jin haushin ka."
Da mamaki fal a fuskar shi yace "Hushi da ni kuma? Hajiar ta? Hajia wai me ki ke fad'a ne? Ban gane ba sam wallahi."
Fahimta da Hajia ta yi akwai abin da ya faru ne ya sa tace "Yanzu dai in ganin ta ka ke so ka yi ka je gidan su, ni kaga ina wasu harkokin."
"Hajia wai me ta ke yi a gidan su? Dan Allah ki fad'a min ko na ji sauk'i, wallahi ji na ke kamar na tashi a bacci."
Shiru Hajia ta yi ta na tunanin abin da za ta fad'a ma sa, kamar zaiyi kuka yace "Hajia ki taimaka ki fad'a min mana, dan Allah ki ce ba wani mugun abu na yi wa Khadija da har ya sa ta tafi gidan su, Hajia kinfi kowa sanin Nana ita ce rayuwa ta, dan Allah ki cire ni a duhun nan."
Cike da k'aguwa Hajia tace"Fodio, na ce ka je godan nasu ka same ta ko."
Ikon Allah sai kawai Usman ya ji hawaye a fuskar shi, cikin rawar murya yace "Hajia sakin ta na yi?"
Jin muryarshi ya sa Hajia jikinta yin sanyi, tabbas sunyi kuskure a baya da su ka nunawa Khadija k'iyayya, gashi alamu na nuna cewa Khadija dai ita ce rayuwar d'an su, jin shiru ya sa yace "Hajia na shiga uku idan sakin ta na yi, Hajia tun yaushe ta ke gida?"
Kashe wayar kawai Hajia ta yi ta aje gefe ta fito waje su ka ci gaba da harkokin gaban su, sai dai kuma hankalin ta ya koma kan Usman da abin da ke faruwa, Haseenah na d'aki zaune ba aikin fari bare na bak'i sai kallon mai bisa ruwa takewa kowa, Usman kam daga nan baiyi k'asa a gwiwa ba wajen wucewa gidan su Khadija ya na addu'a a zuciyar shi "Allah ka sa ba wani abu nayi wa Khadija ba, Allah na rok'e ka kasa ba fad'a mu ka yi ba." Wani lokacin kuma mamakin kasa tuna komai ne ke damunshi, da haka ya isa gidan ya paka mota a k'ofar gidan, zai sallama sai ga Bashir zai fito daga ciki, gaisawa su ka yi cikin mutumta juna kafin yace ya wuce ciki Hajia na nan shi zai fita ne, ba musu ya wuce dan dama ba tsayawa zaiyi ba, Hajia na zaune tsakiyar less da atampopi ya sallama tace ya shigo, zaune ya yi k'asa kamar yanda ya same ta a k'asa ita ma, gaisawa su ka yi kamar kullum kafin ya d'anyi shiru ya na tunanin ta'inda zai fara, shiru ne ya ratsa d'akin kamar ba kowa a ciki, a hankali Hajia ta kalle shi da murmushi tace "Komai lafiya dai ko?"
Saida ya rarraba ido kafin yace "Mama, wani abu ne ya ke faruwa da ni da na ke so na samu amsar tambayoyi na anan, dan Hajia ta ma k'i saurara ta bare ta fad'a min me ke faruwa, dan Allah Mama ki taimaka ki fad'a min ina Khadija take? Sannan meya faru tsakani na da ita da har ya sa take zaune gida?"
Jim Mama ta yi ta na tunanin to in har iyayen shi ba su fad'a mi shi ba me zaisa ita ta fad'a, murmushi kawai ta yi ta kalle shi tace "Ba komai Usman, ka wuce ta na ciki yanzu mu ke zaune tare da ita ta shiga ta yi sallah."
Damuwar kan fuskar shi ce ta k'aru yace "Mama, dan girman Allah ki fad'a min meya faru tsakanin mu, Mama idan ma sakin ta na yi wallahi tallahi bansan na yi ba, shi ya sa na ce mu ku wani abu ne ke faruwa, gaba d'aya na kasa tuna komai ji na ke kamar daga dogon bacci na tashi."
Ganin kamar zai mata kuka ya sa ta saki fuska tace "Kar ka damu Usman, ba wata babbar matsala ba ce, ka shiga ka same ta a ciki ku yi magana, idan har ka na so ma za ka iya tafiya da matar ka gida yanzun."
Sai lokacin murmushi ya bayyana a fuskar shi yace "Mama da gaske zan iya tafiya da ita? Kai Alhamdulillah Allah na gode ma ka."
Dariya Mama ta yi ta na kallo ya shiga ciki, dama k'ofar ba rufe ta ke ba kamar yanda tafi barinta mafi yawan lokuta, ya na tura k'ofar ya shiga ya yi daidai da Khadija ta idar da sallah ta mik'e tare da cire hijabin ta, riga ce jikinta ruwan madara mai k'ananan hannuwa wacce ta kama ta, sai bak'in siket da ya bud'e sosai bai kama jikin ta ba, saida gabanta ya fad'i ganin mutum kawai a d'akin, amma kuma saita kasa motsawa saboda tasan yau ta ta kam ta k'are dan idon shi na kan cikin ta, Usman da tunda ya d'ora idon shi akan cikin ta yaji k'wak'walwar shi ta fara tuna ma sa da wasu abubuwan, mamaki ne fal a fuskar shi har ya fara matsowa kusan ta, ta na ganin haka ta fara ja da baya a hankali shi ma ya na bin ta, daf da ban d'aki ta juya da sauri za ta shige ciki da azama ya rik'o hannun ta.
Janyo hannun ta ya yi har saida ya zaunar da ita bakin gadon ya tsaya gabanta sank'am kamar zai fad'a mata ya na kallo, kan ta k'asa ta kasa had'a ido da shi kafin yace "Ya mu ka yi da ke?"
D'agowa ta yi tace "Akan me fa?"
Had'e rai ya yi yace "Kar ki raina min wayo mana, Khadija me ye hujjar ki na b'oye min ki na da ciki? Akan me za ki min haka?"
Mik'ewa ta yi tace "Kaga malam dan Allah kar ka d'aga min hankali, ni babu wani ciki da na ke da, ko kai ka ga na yi ma ka kama da masu ciki ne?"
Wani bala'in haushi ne ya taso mi shi amma sai ya share yace "Tashi wuce muje gida sai mu yi maganar acan."
"Wane gidan kuma?" Ta fad'a ta na kallon shi, kai tsaye yace "Gidan ki mana."
Wani murmushi ta yi tace "Ni ai duk filaye ne gare ni har yanzu ban gina gida ko d'aya ba."
Cile da k'aguwa yace "Haba uwar yarima, gidan mu fa na ke nufi, ki tashi mu tafi mana."
Cikin nuna rashin damuwa tace "Au! Ai wannan gidan ka ne ba nawa ba, idan da nawa ne ma ai da ba ka yi abin da ka yi ba har na baro ma ka gidan."
A hankali ya durk'usa kan gwiwoyinshi ya rik'o hannayen ta yana murzawa yace "Khadija fad'a min me na mi ki in ba ki hak'uri? Ke kinsan ba zan iya cutar da ke ba, tunda mu ke da ke ba mu tab'a samun sab'anin da yasa mu ka raba shinfid'a ba bare gida, dan Allah ki fad'a min sai na baki hak'uri yanzu kuma mu koma gida tare, sanin kan ki ne ba zan iya bacci ba alhalin ke ki na nan."
Ajiyar zuciya ta sauke tace "Ka na nufin ka ce ba ka san ma me ka min ba?"
Kamar zaiyi kuka yace "Wallahi na manta Khadija, komai ya dawo min kamar sabo a rayuwa ta." Tab'e baki ta yi tace "To kaga ka tashi dai yanzu ka koma gidan ka kafin amaryar ka ta fara neman ka."
Tsaki yaja yace "Ina mi ki magana mai mahimmanci ke ki na magana akan wata, dallah malama ki tashi ki wuce mu tafi gida."
Waro ido ta yi irin mamakin nan tace "Eyee! Lallai ma mutumin nan, to ba zan je ba ina nan gidan mu."
Ba alamar wasa yace "Haka ki ka ce?" Ita ma ba tsoro tace "Eh, haka na fad'a."
Yatsunshi ya sa biyu ya kama agarar (jijiyar da ke bayan k'afa kusa da diga-digi) ya dinga murzawa da zafi, da sauri ta janye k'afar ta sai kuwa ya rik'e k'afar ya na fad'in "Ba dai kinfi son na mi ki hukunci a gidan ba? To ai sai mu zuba ni da ke, na ga wanda ya isa ya k'wace a hannu na yau."
K'ok'arin k'watar k'afar ta ta shiga yi amma ya hanata dama, idon ta ne suka cika fal da ruwa ta na so ta bashi hak'uri amma ta k'i magana, shi kam ko a jikin shi har cije leb'e yake ya na fad'in "Uhum! Da dad'i ko? To yaya yanzu za ki fad'a min dalilin ki na k'in fad'a min ki na da ciki?"
Jin zafi ya kai mata ya sa ta bud'a baki da k'arfi tace "Mamaaaaa, ki zo ki taimake ni."
Bushewa ya yi da dariya yace "Kuma a zaton ki za ta zo? Kar ki wahalar dani a banza ki fad'a min abin da na ke son sani."
Jin bala'in na k'aruwa ya sa Khadija fashewa da kuka irin na sangartattun yaran nan ta na fad'in "Dan Allah ka yi hak'uri zan fad'a ma ka, wallahi zafi ke akwai, dan Allah ka daina zan fad'a."
D'an tsagaitawa ya yi yace "To ina jinki." Saida ta fara goge hawaye tace "To d'anyi baya mana ka matse ni sosai."
Kallon da ya mata ya sa ta d'an matsa baya amma sai ya sake binta ba tare da ya mik'e tsaye ba, shiru ta yi shi kuma ya sake kamo k'afar ta yace "Ke fa na ke saurare, muguwa kawai, da meye nufin ki to? Ban cancanci zama uban d'an ba ko kuma ke kad'ai ke da shi? Allah sai kin fad'a min dalilin ki ko na rabu da ke."
Tangale kanta ta yi da hannayen ta ta rufe fuska ta na tunani, a hankali taji ya d'an d'ago ya zauna bakin gadon ya rumgumota jikin shi, cikin taushin murya yace "Nana, ki fad'a min komai da ya faru mana, meye ake b'oye min haka da ba'a so na sani? Kowa na tambaya sai ya yi shiru ba ya son fad'a min komai."
D'agowa ta yi daga jikinshi tace "Kaje ka tambayi Hajia ko Baba su za su fad'a ma ka komai."
"Ban damu da sanin komai ba Khadija, na fi damuwa da sanin abin da ya sa ki ke zaune gida."
Tallabo fuskarta ya yi yasa idonta cikin na shi yace "Khadija me nai mi ki da zafi haka?"
Kamar za ta fashe da kuka tace "Mun samu sab'ani ne da kai akan amaryar ka, sab'anin da ya sa ka yi abin da ba ka tab'a yi ba a rayuwar ka, shine ni kuma na dawo gida gaba d'aya a lokacin ba ka buk'ata ta a gidan ka."
Da tsantsar mamaki yace "Sab'ani? Amma me na yi to?"
"Duka, duka na ka yi." Ta k'arashe da sunkuyar da kan ta k'asa tana hawaye, dafe kan shi ya yi yace "Duka? Ni da hannu na?"
Tsaye ya mik'e jiki a sanyaye ya sake sunkuyawa gabanta ya d'ago fuskarta yace "Ki yi hak'uri Khadija, wallahi Allah bansan na yi ba sai yanzu da ki ke fad'a min, ki gafarce ni dan Allah kar ki hukuntani da laifin da bansan na aikata ba, yanzu haka kunyar had'a ido na ke da ke da ahalin ki."
Ya na fad'a ya tashi ya fita ko juyowa baiyi ba, Mama ya samu a in da ya barta da alama kan ta ya d'au zafi, sunkuyawa ya yi yace "Mama, Khadija ta fad'a min abin da ya faru, Mama ina mai baku hak'uri da gaba d'aya zuciya ta, ku yafe min dan Allah, ba dagangan na yi ba, kuma banyi dan cin zarafin ku ba, hasalima abu ne da sam banyi tsammani ko tunanin faruwar shi ba."
Mik'ewa ya yi tare da cewa "Saida safe Mama." Ya fad'a ya na barin falon ba tare da jiran me za ta ce ba, Mama kam sai taji tausayin shi ya kamata sosai, watak'ila har ya yi anfani da maganin da Garba ya kawo cewar Mama a zuciyar ta, Khadija ma tausayin mijin ta ne ya sa ko fitowa ba ta yi ba ta kwanta daga nan kuma bacci ma ya d'auke ta.
Kai tsaye gida ya sake komawa ya samu malam zaune k'ofar gida sai Bilal gefen shi da wayar shi a hannu, zaune ya yi akan tabarmar ganin haka ya sa malam cewa "Fodio lafiya dai na gan ka haka?"
Idon shi cikin na malam yace "Ba lafiya Baba, Baba ka fad'a min dan Allah me ya faru da ni ne? Sannan me na aikata a lokacin da na rasa tunani na? Kawai ganin abubuwa na ke kamar sabi kuma kamar a almara."
Tank'washe k'afafu malam ya yi yace "Fodio, abubuwa sun faru da dama, idan da ka nutsu kai da kan ka za ka iya tuna komai, amma ka kasa kwantar da hankalin ka ma bare har ka samu nutsuwar."
Cike da damuwa yace "Baba ina maganar nutsuwa ga wanda ya na kallo rayuwar shi ke barazanar fita daga gangar jikin shi, a yanzu haka fa Khadija na gidan iyauen ta zaune da kuma ciki na a jikin ta, Baba ban ma san tsawon lokacin da ta d'auka acan d'in ba."
Murmushi sosai malam ya yi yace "Watan ta uku yanzu."
"Wata uku?" Ya fad'a da k'arfi da zaro ido kafin ya d'ora da "Baba da sakin ta na yi fa da yanzu ta kammala idda kenan? Kutumar bala'i, Allah ya ceceni."
Dariya malam ya yi kafin yace "Ai kam dai, dan ni dai ka ganni nan ba zan tashi zuwa yi ma ka biko ba da girman ka da komai."
"Yanzu dai malam ku fad'a min abin da ke faruwa da ni, ina so na sani."
Gyara zama malam ya sake yi bayan dogon tunani da ya yi kafin yace "Abin da ya faru da kai ba zamu dangana shi da kowa ba, dan har yanzu ba mu san mai wannan alhakin ba, dan haka kai ma ba na so ka d'auki laifin ka d'ora kan wani ko wata, ka barwa Allah kawai shine zai ma ka sakayya." Jinjina kai Usman ya yi alamar gamsuwa kafin malam ya ci gaba da bashi labarin iya abin da ya sani kawai daga barin Khadija gida zuwa yau d'in nan, sosai al'amarin ya girgiza Usman tare da bashi mamaki, to shi kam waye abokin gabar shi da har zai mi shi haka? Kasa tunawa ya yi sai kuma zuciyar shi tafi ta'allak'a mi shi komai da Haseenah, dan a ganin shi ita ce za ta iya sawa ya manta da Khadija dan ta bar gidan ita ta zauna, to amma kuma malam yace kar ya d'orawa kowa laifi, ya barwa Allah zai ma sa sakayya dan haka ya ja baki ya yi shiru, amma kuma abin da ya ji yanzun ya sa ya tuna da abubuwa dayawa da su ka faru, sai dai ba duka ba, saida safe ya mi shi dan lokacin har bacci ya d'auki Bilal daga nan, ganin zai shiga mota ya sa malam cewa "To matar ta ka fa wa ka barwa ita anan? Ko nan za ta kwana ne?"
Zaune ya yi cikin motar ya kira ta a waya yace ta fito, ba wani jimawa ta fito cikin takun k'asaita da izza dan dama zaman gidan ya isheta, kafe fuskata ya yi da ido har ta k'araso, tabbas ba munin fuska ba ko munin halitta, sai dai wani abun al'ajabi wani irin haushin ta ne yake ji na taso mi shi, wanda ko farko duk da ba wani son ta yake sosai ba amma dai ba ya mata irin wannan k'iyayyar, zagayawa ta yi ta shiga suka d'auki hanya ba tare da sunwa juna magana ba, jin shirun ya yi yawa kuma ya d'auki hanyar gida ya sa tace "Kasan fa ba mu da abin da za mu ci a gida, ka siya mana kafin mu wuce ko."
Cikin isa da gadara ya juyo ya kalle ta, a hankali kuma ya d'auke kan shi daga kallon ta cikin mak'oshi yace "Uhum."
Saida ya tsaya ya siya mata iya cikin ta kafin suka wuce gida, suna shiga ya nufi k'ofar na shi falon, da sauri tace "Beby, ina kuma za ka je?"
Juyowa ya yi yace "...
*Gidan uban da ki ka aike shi mana.*🙊🙈
04/03/2020 à 19:43 - 💋😘💋: 💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
*KALLON KITSE*
_(Ake wa rogo)_
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
_SAMIRA HAROUNA_
*Litattafan marubuciyar*
*1* _KAUSSAR_
*2* _D'AUKAR FANSA_
*3* _BA SO BANE_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI_
*6* _JIHADI_
*7* _K'ANGIN RAYUWA_
*8* _ITACE K'ADDARARMU_
*9* _KAWU NA NE_
*10* _MAATA_
*11* _KALLON KITSE..._
*SADAUKARWA GA*
_MATAN FARKO_ 🧕🏼 *(UWAYEN GIDA)*
🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_🤜🤛
```Fatan alkairi masoya```
_Bismillahir rahamanir rahim_
*35*
"Zan d'an shiga ciki na kwanta ne saboda na gaji, ki ci abincin kawai dama ni na k'oshi."
Sake juyawa ya yi zai wuce tace "Amma yau d'akin ka za ka kwana ne?"
"Eh." Ya fad'a a hassale tare da juyowa ya na kallon ta ya ci gaba da cewa "Kuma ke ma ina so ki kwanta d'akin ki dan ba na son takura."
Da mamaki tace "Takura kuma? Ni ce ma zan zama takura a gare ka? Babban mutum wai lafiyar ka k'alau."
Ajiyar zuciya ya sauke irin ta takura masa d'in nan kafin yace "Lafiya k'alau, na yau kawai na ke so ki bar ni na kwanta ni kad'ai, ki yi hak'uri." Ya fad'a ya na wucewa ciki ya barta nan, mamaki ne ya kama ta sosai da tunanin ko lafiyar shi? Ita dai a saninta lafiya lau suka je gida, amma daga lokacin da ya shiga d'akin malam ba ta ma san da tafiyar shi ba sai da taji kamar su na waya da Hajia duk da dai ba ta da tabbacin da shi su ka yi wayar, ita ma d'akin ta ta nufa ta cire kaya ta yi wanka kafin ta ci abinci ta kwanta, sam ba ta samu wata damuwa ba wajen baccin ta, dan kuwa ba jimawa baccin ya d'auke ta.
A wajen Usman kuma kasa bacci ya yi ya na tunanin abin duniya, da farko dai da kunya ce ke neman sa shi yin k'asa a gwiwa, amma kuma saiya duba ya ga ai ba a sanin shi bane komai ya faru, sannan bai saki matar shi ba bugu da k'ari ta na d'auke da cikin shi, da haka kuma sai ya ji ya ma k'agu gari ya waye ko ya sake komawa wajen Dije, ba kuma zai gushe ba har sai ta dawo gare shi, saboda fatan dacewa ya sa ya d'auro alwala ya shiga fad'awa Allah kukan shi tare da neman taimakon ubangiji.
*Washe gari* da safe d'aurin aure, sammako sosai Usman ya yi ya hallara d'aurin auren bayan yace wa Haseenah ta yi k'ok'ari taje da wuri ita ma, haka ya fita kamar shine angon cikin babbar riga da 'yar ciki farare, ya na isa a k'ofar gida ya tsaya saboda mutanen da ya samu a wajen, nan su ka shiga gaisawa da mutane har lokacin da motar Naseer ta kutso cikin taron jama'ar, mazauni aka samarwa da motar kafin Mama ta bud'e ta fito daga ciki, Usman na ganinta ya tafi da azama dan kwasar gaisuwa sai ya ga Khadija ta fito a matsayin dreban da ta tuk'o motar, tsaye ya yi ya kasa k'arasawa saboda haushi, tabbas yasan ta na fita da gyale sai dai yau ne ya fara jin haushin haka, domin kuwa ta na fitowa gyalen ma a kafad'ar ta yake, duk da doguwar rigar shadda ce jikinta wacce ta fito da d'an cikin ta na wata biyar, amma dai baiji dad'i ba duk da ya ga sai gyara gyalen take, har saida su ka zo daf da shi kafin ya sunkuya ya gaishe da Mama ta amsa cikin sakin fuska, wucewa Mama ta yi shi kuma ya mayar da kallon sa kan Khadija da ita ma shi take kallo yace "Ke ba ka iya gaisuwa ba ne ko me?"
Cikin tsiwa tace "Um ban iya ba, ko ka koya min ne?"
Gyara tsayuwa ya yi ya na k'ara sab'a rigar shi a kafad'a yace "Uwar yarima wai yaushe ki ka raina ni ne haka?"
Ta na kallon idon shi tace "Tun ranar da ka fara wulak'anta ni saboda ka yi amarya."
Wani kallo ya mata kafin ya d'an saci kallon mutanen da ke wajen yace "Yanzu ko albarkacin mutanen nan ba zan ci ba na ga murmushin nan na ki mai saka ni bacci."
'Yar siririyar dariya ta yi tace "Toh fa Alhaji mai babbar riga, kai da za ka je d'aurin aure kuma me ya had'a ka da bacci? To ka farka idan mafarki ka ke, kai da sake ganin murmushin Nana Khadija kuma sai dai ko a lahira, a lokacin da aka min umarni da na shiga aljanna, to zan iya juyowa na kalle ka dan na ma ka bye bye, to fa zai iya yiwuwa a lokacin ne za ka ga murmushin."
Shi maganar ta dariya ma ta bashi, da sauri ya rik'o hannunta ya matso daf da ita yace "Ki na so ki ce ni kuma zan zauna har sai kin riga ni shiga? Ko kuma nufin ki ni ba ma zan shiga ba?, ai k'afar ki k'afa ta insha Allahu, in kuma ba haka ba to sai dai ki same ni a ciki kewaye da sabbin mata na."
Fizge hannunta ta yi tace "Ka na dukan nawa ne kuma ka ke tunanin za ka shiga aljanna."
Wucewa ta yi ta bar shi nan tsaye ya na ta dariya shi kad'ai, Murtala ne ya k'araso wajen shi yace "Mijin Khadija lafiya ka ke dariya kai kad'ai?"
Hararan shi ya yi yace "Ni kad'ai ka gani a wurin? Ba ka ga wacce na gani ba."
"Na gani kam, ince dai kun sasanta za ta koma?" Kallon shi ya yi sosai yace "Da alama fa sai ka tayani bata hak'uri, ran 'yar aljanna ya b'ace sosai."
Zaro ido Murtala ya yi yace"Wa? Ni! Sam ba dani ba, kai dai da ka mata laifi ka bata hak'uri amma banda ni."
"Au! Yanzu ka na nufin ba za ka tayani ba kenan? To nagode, ai na d'auka zan iya yin zaune gida ma kai kaje har sai ka dawo min da ita, ashe ba haka bane."
"A'a ni ba haka na ke nufi ba, kasan dai maganar nan ta manya ce ba iri na ba, kuma tsakanin ka da Khadija ma ai ba ta b'aci."
Ba jimawa da shigar Khadija mutane aka fito dan tafiya wajen d'aurin auren, daga ciki har da Mama dan dama d'aurin auren take son samu, nan aka shiga motoci aka wuce d'aurin auren, Khadija na zaune d'akin Hajia Nura ya shigo da sauri ya na kiran sunan Hajia, ya na ganin Khadija yace "Uwar gida yane, ke ba ki je d'aurin auren ba?"
Hararan shi ta yi tace "Wa? Allah ya sawak'e, me zanje na yi a d'aurin auren kishiya, ai ina daga nan ina aika mu ku da addu'a."
"Yawwa hakan ma ya yi ai, addu'ar ita mu ke buk'ata ai." Cewar Nura ya na kallon Hajia da ta fito daga d'aki, cikin k'aguwa yace "Hajia takalma na da na baki jiya na ke nema."
Ledar hannun Hajia ta mik'o mi shi tace "Dama nasan su za ka nema ka ke min wannan kiran."
Bud'ewa ya yi ya saka takalman kafin ya juya zai fita yace "Hajia ku fara tausar min k'irjin ta kafin na dawo."
Haka suka wuce wajen d'aurin aure gidan waliyin Choukra, kuma ba'a b'ata lokaci ba waken yin abin da ya kai kowa wurin, nan aka d'aura auren *Nura Ali* da amaryarshi *Choukra Sabi'u*, bayan taya juya murna da farin ciki ne abokan ango su ka nufi inda za su ci su sha, manyan mutane kuma suka dawo gidan su ango dan cin abinci suma.
Bayan tafiyar 'yan d'aurin aure ne ba jimawa kuma Haseenah ta zo ita ma kamar yanda Usman yace ta zo da wuri, a d'akin Hajia suke zaune nesa da juna amma babu mai kula wani, haka suke zaune Khadija na hira da mutanen da ba su je d'aurin auren ba, Hajia ce ta fito daga uwar d'aki ta kalli Khadija tace "Nana wai kinga Bilal kuwa?"
"A'a Hajia, ya na ina ne?"
"Ai tare da malam su ka shirya su ka fita, kin ganshi kamar shine angon sai rawar k'afa ya ke, saida na gargad'e shi dai kan karya kuskura ya kalli wasu mata."
Dariya kawai ta yi ba tace komai ba har mutane su ka fara shigowa aka fara hayaniya, nan su Hassana da sauran mutane suka fara raba abinci ana kaiwa mutane.
Bilal ne ya shigo tare da malam kai tsaye wajen mahaifiyar shi ya nufa ya zauna kan k'afafun ta, wanda hakan ya yi daidai da shigowar Usman da kwalbar lemu a hannun sai malam a biye da shi, kwantar da kan Bilal ta yi a k'irjin ta tana sumbatar shi tace "Yarima na yi kewar ka fa, kwana uku ka na nesa da ni."
Bilal kenan d'an gata sai kuwa ya sake wani cakume ta kamar zai sa nonon ta a baki yace "Mummy yunwa na ke ji fa."
Lek'a fuskar shi ta yi tace "Ban gane ba, ba ka ci abinci ba ne a waje?"
Cikin shagwab'a yace "Ban ci ba, to duka fa manya ne a wajen."
Murmushi ta yi tace "To yarima na k'arami ne? Yaro ana bikin kawun ka ace ka na rasa abin da za ka ci, to ba ka had'u da Abban ka bane?"
K'ara tusa kanshi ya yi cikin jikin ta yace "Um um."
D'ago kan ta tayi za ta yi magana sai ga Usman tsaye gaban ta ya na fad'in "Yarima yanzu da girman ka za ka hau k'afafu haka?"
Da sauri Bilal ya d'ago ya na ganin Abban shi ne ya yi tsaye ya mak'ale mi shi a wuya, rumgume shi ya yi shima yace "Me ya ke faruwa ne na ga ka na ta zuba shagwab'a haka?"
Khadija ce tace "Bai ci abincin bane, amma kuma kai ga hannun ka nan har da lemu ma ka ke korawa."
Kallon ta ya yi yace "To yanzu shan lemun nawa ya zama haramun ne ko me?"
"Ya zama mana, taya za ka jefa loma bakin ka ba ka san gudan jinin ka ya ci ko bai ci ba." Yanda ta had'e fuska ne ya sa ya ga ko ya fad'a mata shi ma bai ci abinci ba ba yarda za ta yi ba, dan haka ya juya da Bilal d'auke da shi yace "Yarima muje ka zab'i abin da ka ke so ka ci, rabu da mahaifiyar nan ta ka yau tunda safiya ta waye ta tashi da masifa, can ta k'arata da masifarta."
Shiru ta yi sai kallon k'eyar shi da take, shi kam jin ta yi shiru ya sa ya juyo dan ya san ta na nan ta na kumbura, wata irin harara ta dalla masa da tasa shi b'arkewa da dariya yace "Yi hak'uri Hajia, nasan me ye matsalar ki, ki ba ni hak'uri sannan ki lallab'a ni sai na mi ki magani."
Yanda ta motsa bakin ta ya sa ya fahimci me take nufi, dan haka ya mata gwalo yace "Idan kin kamani ki mayar da gabana gabas ki yankani."
Da haka ya fita su ka bar gidan, tun lokacin ba ta sake ganin Bilal ba har biki ya yi biki ana ta bayar da zafi, Haseenah na d'akin Aziza kwance sai narkewa ta ke, sai dai kuma abin ya d'an dameta na yanda kowa baya ma kula ta, sai wanda ya ganta ne dole ya ke iya gaisawa da ita, amma har Aziza sai ta shigo d'akin ta fita ko kallon in da take ba ta yi ba, haka yamma ta yi aka raba abinci, kasancewar a d'aki take ita kad'ai ya sa aka rabe abinci ba'a ma san da ita ba, babu wanda ya damu da hakan sai ma ran su Hassana da ke k'ara b'aci.
Da dare mutane duk sun tafi gidan amarya da ango, Khadija ce d'aki ke gaggauta shirya dan tafiya tare da masu jiranta a waje tunda ta zo da mota, sai Haseenah da tun sallah magriba ta tafiyar ta gida, Hajia na zaune kan katifa gyangyad'i na neman fizgar ta Khadija tace "Hajia bacci ne?"
Kallon ta tayi tace "To tukuna dai."
Saida ta gyara jakarta a kafad'a tace "To ni zan tafi, kuma ina ga daga can gida zan wuce, sai dai gobe idan Allah ya kaimu."
"To Allah ya yarda Khadija, Allah hutar da gajiya, angode sosai Allah ya saka da alkairi, saida safe." Duk ta na maganar ne saboda Khadija har ta kai bakin k'ofa ta na amsa mata, za ta bud'a labulen d'akin Usman ya sallamo, kaucewa ta yi da tunanin ya wuce amma saiya wani tsare ta da ido yace "Hajia ke kuma wannan kwalliyar fa? Duk ta zuwa kallon ango da amaryar ce?"
Kallon Hajia ta yi sai ta ga ita ma su take kallo dan haka ta share shi kawai, hannu ya sa aljihu ya ciro da hankici (hankiciep) ya kai a bakin ta zai goge mata jan baki, da sauri ta ja baya ta na rufe bakin tace "Ya za ka goge min? Yanzu fa na saka shi, kuma ina da bak'o ne a gida."
Wani kallo ya mata yace "Bak'o kuma? Wane irin bak'o?"
Ba alamar wasa tace "Bazawari nn..." Bugun da ya kai mata a baki ne ya sa ta saki k'ara ba ta shirya ba tare da rufe bakin ta durk'ushe kan gwiwanta, Hajia da ta zabura ne ta kalle shi tace "Alhaji meye haka? Me tai ma ka?"
Zaune ya yi akan kujerar da ke iya fuskantar Khadijar ya na hararan ta, cikin d'aga murya Hajia tace "Fin k'arfi ne ko me? Dallah malam ka bata hak'uri ko."
Rai b'ace ya kalli Hajia yace "Hajia ba ki ji me yarinyar nan ta ke fad'a ba ne, ina matsayin mijin ta za tace wani wai bak'o na jiran ta, har da cewa wai bazawarinta." K'wafa ya yi hakan ya sa Hajia kallon Khadija da har yanzu ba ta motsa ba tace "Yi hak'uri kinji Khadija tashi ki tafi abinki, ba zan iya tashi bane saboda k'afafu na amma da na rama mi ki dukan ki, ki yi hak'uri kinji."
D'agowa ta yi a hankali ta sauke ido a kan shi sun mata jawur, murmushi ta yi ta kalli Hajia tace "Saida safe."
Mik'ewa ta yi ta fice daga gidan, ta yi k'ok'ari ta sauke ma su jiran ta a waje gidan amarya amma ita ba ta tsaya ba ta wuce gida.
*A gurguje*
A kwana biyu zuwa lokacin da aka kammala sabgar bikin Nura Usman ya shiga taitayin shi, dan ko wayar shi Khadija ba ta d'auka bare ta saurare shi idan ya zo, hakan ya tab'a shi sosai dan ya damu, haka ma Haseenah ta fara damuwa sosai akan lamarin na shi, dan har yanzu ba su kwana d'aki d'aya ba, gari na wayewa kuma zai buga sammako yaje gida ya na lallab'ar malam ya je ya dawo da Khadija, sam ba ya da lokacin wata Haseenah yanzun, abinci ma idan ta dafa sai dai ta ci ita kad'ai amma ban da shi, ba ya son zuwa gidan saboda ba ya son ganin Haseenah da idon shi, ya na iya k'ok'arin shi sosai wajen b'oye k'iyayyar da yake mata, ya rasa dalilin da ya sa ya ke sake jin tsanar ta a kullum idan ya ganta, ba ya son jin muryar ta ko ganin giftawarta a gidan, duk da ba ya da kokwanto akan cikin da ke jikin ta cewa na shi ne amma dai ba ya jin ya na k'aunar abin da ke cikin ta kamar yanda ya ke k'aunar wanda ke cikin Khadija, a haka har aka kwashe *sati biyu* babu abin da ya sauya.
A sati biyun nan ne Usman ya yi tattaki har k'auyen su Baba Garba mai gadi ya je ya bashi hak'uri akan abin da ya farusannan ya nemi da ya dawo bakin aikin shi, ya hak'ura ya kuma nuna masa komai ya wuce shi dama bai rik'e ba saboda ya san ba laifin shi bane, amma dai ba zai iya komawa aiki ba saboda jiki da jini, amma idan ya amince akwai d'an shi da ke neman kangarewa zai iya had'a shi da shi saiya zauna a mazaunin shi, ya amince ya taho da yaron mai sunan *Rabe*, tabbas ya fara aiki yanda ya kamata sai dai burin Usman akan yaron ba wai ya zama mai kula da pliwoyin (flawers) gidan shi bane da k'ofa, ya na so a gama wannan zagon na karatu sannan ya d'ora shi ya ci gaba da karatun shi tunda ya na yi ya dakatar saboda shirme, duk da haka kuma Usman bai daina bibiyar Khadija ba, yanzu haka har ya gaji da sawa Bilal na rok'on ta akan ta dawo, Hajia da malam dama sun ce ba ruwan su, a k'arshe ya samu da k'yar ya lallab'a Murtala ya je ya mata magana, nuna masa ta yi ba komai za ta koma, amma ya na barin gidan tace ba yanzu sai ya sake shiga hankalin sa, jin shiru shiru ya sa saida ta kai ga Usman ya turo Nura da Kabir da kuma Mannir su ka je bata hak'uri, sai lokacin Mama tasan da irin tsiyar da Khadija ke tsulawa, dan sam babu wanda ya tab'a ce mata ya zo bata hak'uri dan ta koma, Usman kuma idan ya zo ta kan basu wuri ne dan su tattauna, kuma ba ta nuna mata wasu alamu na rashin jituwa, hakan ya sa ba ta san me ke faruwa ba, shi ma Usman ya so ya b'oye mata ne dan yasan za ta iya tirsasata akan ta dawo, duk da ya na matuk'ar so ta koma amma ya fi so ta koma dan ganin damar ta, kuma har yau ba ya ganin laifin ta akan hukuncin da take masa, dan kuwa babu abin da ta rage shi da shi a rayuwa amma ya mata kishiya, sannan ya rasa meya shiga kan shi da ya dinga cin mutuncin ta, dan wasu abubuwan sai yanzu ne idan ya na rarrashin ta take iya fad'a mi shi irin abin da ya mata, bugu da k'ari kuma bata gama hucewa ba ya zo ya bugar mata baki har saida ya kumbura, wanda kullum mitar hakan take masa, nan Mama tace su koma Khadija za ta dawo gidan ta ba jimawa, sun tafi da farin cikin samun nasara amma sam Khadija tace ba yanzu zata koma ba, da Mama ta fara fad'a kuma sai 'yan biyar suka tausheta suka ce tunda ba yarinya ba ce kawai a rabu da ita, hakan ya sa a ranar Usman ke ta zuba idon ganin Dije amma shiru, ko bacci baiyi ba a ranar ya na sak'awa ya na warwarewa, washe gari da dare ya je gidan da kan sa, a falo ya samu duk 'yan biyar d'in da wasu daga cikin yaransu, Mama na d'aki hakan ne ya sa ya zauna suka gaisa sosai, Naseer ne yace "Auta kam ta na ciki, amma kafin ka shiga ciki ka kawo kud'in ganin ta."
"To in dai hakane me zai hana ka fad'a min gaba d'aya farashin da zan biya, kaga sai ka d'auke ta da kan ka ka kai min ita gida na." Cewar Usman cikin raha, dariya su ka yi sai Habeeb ne yace "K'anwa ta fa tsada ne da ita, farashin ta baya fad'uwa."
Cikin zolaya yace "To kunga, duk cikin kun nan naga babu wanda zai iya taimaka min, dan haka ni zanje na yi yak'i na ni kad'ai, in har k'anwar ku bata koma gida na zuwa gobe ba to ku canza min suna."
Cike da cika baki ya mik'e zai nufi d'akin Khadija Naseer ya bushe da dariya yace "Wane sunan za mu saka ma ka to?"
Juyowa ya yi ya harare shi yace "Ka zab'a da kan ka mana."
Bashir ne ya yi saurin cewa " sai mu saka mi shi *Mani*."
Komai baice ba ya wuce d'akin, ko sallama baiyi ba yau dan al'amarin ba sauk'i, kuma cikin sa'a saiya samu Khadija tana ban d'aki, murmushi ya yi kafin ya cire hular kan shi ya aje gefe ya kwanta kan gadon ya yi d'a-id'ai, kusan minti biyu ya d'auka kafin Khadija ta fito daga ciki d'aure da k'irji, kasancewar cikin ta ya sa ya d'age sosai daga sama har ya kan iya hango cinyoyinta, ita kam gilashin ta ne take gogewa ta na k'ok'arin sakawa, ta na sawa ta ja ta tsaya da tsoro fal a idon ta, bud'ar bakin ta cewa ta yi "A'uzu billahi mina shaid'anir-rajim, innahu min Suleimana wa innahu bismillahir-rahamanir-rahim."
Ba tare da damuwa ba Usman yace "A kan ki, wato na ma zama shaid'an ko?"
Wata ajiyar zuciya ta sauke ta matso kusan shi tace "...
*Ina k'aunar ku.*
06/03/2020 à 12:54 - 💋😘💋: 💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
*KALLON KITSE*
_(Ake wa rogo)_
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
_SAMIRA HAROUNA_
*Litattafan marubuciyar*
*1* _KAUSSAR_
*2* _D'AUKAR FANSA_
*3* _BA SO BANE_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI_
*6* _JIHADI_
*7* _K'ANGIN RAYUWA_
*8* _ITACE K'ADDARARMU_
*9* _KAWU NA NE_
*10* _MAATA_
*11* _KALLON KITSE..._
*SADAUKARWA GA*
_MATAN FARKO_ 🧕🏼 *(UWAYEN GIDA)*
🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_🤜🤛
```Fatan alkairi masoya```
_Bismillahir rahamanir rahim_
*36*
"Malam lafiyar shigo min d'aki haka kawai, wa ma ya baka izinin shigowa nan?"
Kamar ba dashi take magana ba ma saiya share ta, ta jima tsaye ta na kallon shi ganin bai damu da tsiyar da take ba ya sa ta juya ta isa gaban madubi ta fara shafe shafe kamar yanda ta saba, lokaci lokaci takan juyo ta kalle shi amma abun mamaki shi kuma hankalin na ga waya ya na dannawa, saida ta gama ta nufi wajen kaya ta d'auko riga, ba tare da ta cire d'aurin k'irjin ba ta saka wando da rigar nono kafin ta saka doguwar rigar, juyowa ta yi ta kalle shi tace "To malam, idan ka gama da d'akin sai ka rufe min ko, ni zan fita."
Gyale ta d'auka ta fesa turare ta juya zata fice, da sauri ya duro daga kan gadon yace "Ina za ki je?"
Ta na kallon idon shi tace "Bak'o..." Sai kuma ta yi shiru saboda tuna ranar da ya kwamtse mata baki, rik'e k'ugu ta yi tace "Ka ban hanya mana zan wuce."
Rumgumo ta ya yi jikin shi ya dawo da ita ya zaunar akan gado, ture shi ta yi tace "Malam ka daina tab'a ni mana."
Sosai ya kalle ta yace "Khadija, har yanzu fa ni mijin ki ne, a labarin da ki ka bani ba ni ne na kore ki ba, amma Khadija ki na hukuntani abisa laifin da na ke tunanin ko da na aikata shi ne dadangan za ki yafe min, me ya sa haka Khadija? Kin daina so na ne yanzu? Ko kuma ba kya son ki tsufa a gida na ne yanzu kamar yanda ki ke fad'a min."
Mik'ewa ta yi tsaye tace "Ni dai kawai ka fitar min daga d'aki, so ka ke mutane su d'auka wani abun ne ke faruwa anan? Dan Allah ka tashi ka fita."
Yau fa ya yi niyyar ba zai bar gidan nan ba babu wani sakamako mai kyau, dan haka ya haye gadon ya gyara kwanciya ya kalle ta yace "Ba zan fita d'in ba, idan kuma ki na ganin za ki saka k'artin 'yan uwan ki ne su fitar da ni to bismillah."
Mamaki ne ya sa ta zaro ido tace "Abban Bilal, yan uwan nawa ne ma k'arti? To ai ko ba k'artin banza bane tunda su na ciyar da duka girman gidan nan dama wasu dake kewayen shi."
Hararan ta ya yi yace "Ni kuma na gaza ko? To ki jaraba kiran su ki gani mana idan za su iya."
Rumgume hannaye ta yi tace "Amma dai kasan tsaf zan iya saka su kefa min kai cikin kwalbatin unguwar nan ko?"
Wata irin dariya ya bushe da ita yace "To ki kira su mana, na fad'a mi ki ina tsoro ne."
Fitowa kam ta yi daga d'akin amma abun mamaki ba kowa a falon har telebijin ma an kashe, mayar da d'akin ta yi ta rufe ta dawo ta zauna kan kujerar da ke gaban madubi, kallon ta ya yi yace "Hajia ko za ki iya samo min kayan bacci a gidan nan?"
A harzuk'e ta kalle shi tace "A ina zan samo ma ka kayan bacci? Na wa zan d'auko ma ka?"
Har ta yi shiru shi kuma ya fara dariya sai kuma ta kalle shi tace "Wai ma tsaya, idan na d'auko ma ka kayan baccin me za ka yi da su?"
Ba alamar wasa yace "Nan zan kwana yau, tunda na fahimci ba za ki koma gidan ki ba, kinga saina raba mu ku kwana, biyu a nan biyu a can."
Tasowa ta yi ta kamo hannun shi ta na fad'in "A'a wallahi, akan me? Haka kawai kasa a kafa min hak'ora, kwana a nan saboda me?"
Fizge hannun shi ya yi yace "In dai ba kya son na kwana nan to ya zamar mi ki dole ki had'a kayan ki yanzun nan mu tafi na mu gidan."
Cikin b'acin rai tace "Wallahi babu in da zanje, haka ake kawai ka b'ullo min ta wannan hanyar."
A nutse ya kalle ta yace "Na fad'a miki ki bani hak'uri tare da lallab'a ni dan na mi ki maganin matsalar ki, amma girman kai ya hana ki ko? To ba damuwa mu ci gaba da zama a hakan tunda haka ki ke so, yarinya sai taurin kai."
"Ni na fad'a ma ka wani abu na damu na?" Ta fad'a ta na nuna kan ta da yatsa, saida ya tashi zaune yace "Ke kuwa ke da damuwa, gata nan b'aro-b'aro ina gani a idon ki."
Duk da idon na ta na cikin gilashi amma saida ta mitsika idon ta kafin tace "Ban gane ba fa."
Kashe mata ido ya yi yace "Yaushe rabon ki da ni? Yaushe rabon da na yi wasa da ke? Hajia Dije yaushe rabon da ki ji zallar ingantacciyar madara a jikin ki?"
Shiru ta yi kawai sai kallon bangon d'akin da take, murmushi ya yi yace "Shi ya sa yanzu zuciyar ki ta cika saurin hawa, ki ka cika masifa da jaraba, sannan ba kya da kuzari kamar yanda ki ke a baya, sannan hakan zai shafi lafiyar abin da ke cikin ki, saboda ni d'in nan da kika raina to lafiyayyen abincin shi na jiki na, za ki iya haifar yaron ki babu kazar-kazar a jikin shi da walwala kamar sauran yara, saboda ya rasa wani muhimmin abu da ya kamata ya samu amma kin hana shi saboda ki na bak'in ciki."
Juyawa ta yi ta kalli agogo ta ga har k'arfe goma ta soma wucewa, dan dama shi ma tara ta wuce ya shigo, kallon shi ta yi tace "Dan Allah babban mutum ka tashi ka tafi dare ya yi, ni kai na bacci na ke so na yi."
"Wasa ki ke ko Khadija? Yanzu ki na nufin ba ki yarda da abin da na fad'a mi ki ba kenan? To shikenan, ni dai na yi niyyar kwana anan, idan ke ki na jin kunyar kar mu wayi gari mu fito a d'aki d'aya to ki je d'akin Bilal ki kwanta."
Dafe goshi ta yi tace "Na shiga uku na, Abban Bilal ya ka ke so na yi ne?"
Wani kallon mamaki ya bita da shi, saukowa ya yi daga kan gadon ya tsaya daf da ita yace "Khadija, ke da kan ki, ke ce yau saboda takura da gundurar da na mi ki har ki ke iya fad'a a cikin ido na cewa kin shiga uku, Khadija me nai mi ki da zafi har haka? A gaskiya ban yi tsammanin jin wannan maganar daga bakin ki ba."
Juyawa ya yi cikin sanyin jiki ya d'auki hular shi yasa ya kalle ta yace "Shikenan uwar yarima, ni zan tafi, bana iya ce mi ki ga ranar da zan dawo ba, dan gaskiya kin kashe min k'warin gwiwa na, tunda ba kya son komawa zan rabu da ke, idan kin haihu kuma sai ki min magana idan ki na buk'atar takardar ki."
Kama hanya ya yi zai bar d'akin Khadija da idon ta su ka cika taf da hawaye ji ta yi kamar ta k'urma ihu, saida ya kama hannun k'ofar zai murd'a ta yi k'arfin halin janyo rigar shi da k'arfi, baya ya yo kamar zai fad'i tare da kallon ta, kafin ya ankare ta hankad'a shi kan gadon ya fad'a da k'arfi, da iya k'arfin ta ta fad'a kan shi ba tare da tunanin cikin jikin ta ba, rufe shi ta yi da duka tako ina kamar Allah ne ya aiko ta, kallon ta kawai yake bai hana ta ba sai murmushi da yake dokawa, ita kam kuka take ta na fad'in "Aikin banza kawai, ashe dama ba so na ka ke ba shi ya sa har za ka iya saki na, so ka ke kaje kai da amaryar ka ku ci amarcin ku."
Ganin sosai ta ke kukan da gaskiyar ta ya sa ya kwantar da ita a k'irjin shi ya na shafa bayan ta ya na fad'in "Kinji yanda zuciya ta kuwa ta buga lokacin da na ambaci kalmar takardar nan, dan Allah Khadija ki daina azabtar da ni haka, gaba d'aya kinsa na zama kamar mahaukaci saboda k'ok'arin ganin kin dawo gare ni, ki tausayawa uban yaran ki mana."
Luf ta yi a k'irjin ta na share hawayen ta, sun jima a haka kafin yace "To ya ake ciki yanzu? Za ki koma ne ko ko sai na aiko mi ki da takardar har gida?"
Wani naushi ta kai mi shi a ciki wanda ya sa shi bushewa da dariya ya dafe ciki, tashi ta yi zaune kafin ta kalle shi tace "A gaskiya ba zan iya binka ba a daren nan, kawai ka je gobe na dawo da kaina."
Dariya ya yi ya kamo kunnen ta ya rad'a mata "Ashe yarinya ta na so na mata b'arin madara."
Murmushi ta yi tace "Matsala ta da kai rashin kunya."
"Um hakane, amma ai ke ki ka koya min."
Tashi ya yi yace "Da gaske za ki dawo gobe?"
"Zan dawo mana, ba ni na fad'a ba."
"Idan ma ba ki dawo ba wannan karan su Hajia Kaltume da Turai zan aiko su d'auke ki su kai min ke."
Kallon shi ta yi tace "Turai dai? Lallai."
Tsaye ya mik'e yace "Yanzu kira min Bilal da shi zan tafi, dan nasan dole ma ki dawo idan na tafi da shi ai."
Ita kam saboda ta yi niyyar komawa ya sa ta mik'e tace "Muje idan ka d'auke shi sai ka wuce."
Tare suka fita daga d'akin su ka nufi d'akin Bilal, idon shi biyu ya na rik'e da wayar shi a hannu, nan ta canza mi shi kaya su ka tafi da niuyar za ta zo mi shi da sauran kayan, saida ya shiga d'akin Mama da ta jima da bacci ya tsokane ta yace ya tafiyar shi, idan ta damu da shi ta je ta yi bikon shi ita ma, saida ta rako su har k'ofar gida Bilal ya bud'e motar ya shiga, Usman na ganin haka ya damk'i Khadija da wata wawar sumbata da ta rikita su dukansu, da k'yar ya sarara mata kafin ya kalle ta da jajayen ido yace "Ki yi sauri ki zo da wuri, ina buk'atar ki kusa da ni Hajia ta."
Motsa bakin da ta yi ya sa ya yi murmushi yace "Na ji dai idan kin kama ni ki yankanin amma fa bayan kin shayar da ni ruwan ki."
Dungure mi shi kai ta yi tace "Wai kai ka manta da ka tsufa ne, watanni kad'an fa su ka rage ma ka ka cika shekara *arba'in da biyar* cif a duniya, amma ka na abu kamar wani tsohon bazawari."
Saida ya sa hannu ya na shafar k'irjin ta yace "Kafin na cika hamsin da biyar kuma sai kun haifa min yara goma, kin ga ai ba na mayar da kai na tsoho ba, kuma ma ai ba daga nan abun yake ba, k'arfi da mazantakar na nan." Ya mata nuni da zuciyar shi.
Da haka suka rabu ya tafi da Bilal, yau kam Khadija ta yi bacci cikin nutsuwa saboda burin ta ya cika, ta juya Usman son ran ta ta hakane ma har ta gano yanzun Haseenah ba ta da wani girma a idon shi, dan haka ta yi bacci da zumud'in gari ya waye ta fara shirin komawa.
A wajen Usman kam Haseenah ba ta san da shigowar shi ba saboda har ta yi bacci ita ma, saida ya shinfid'e Bilal a gadon shi kafin ya wuce d'akin ta ba dan komai ba sai dan ganin halin da take ciki kamar yanda yake yi kullum, bud'a k'ofar da ya yi ne ya sa ta tashi ta na murza ido, kallon ta ya ke sosai ya na jin wata sha'awar na sake fizgar shi, sai dai kuma ba ya so ya neme ta saboda ba ita ta taso shi ba dama, da k'yar ya iya cewa "Ki yi hak'uri na tashe shi ko? Ashe hr kin kwanta ma, yau kam ban shigo da wuri ba."
Gyara zama ta yi tace "Sannu da shigowa."
"Yawwa sannu, ya ki ke?"
Kallon shi kawai ta yi ba tace komai ba, juyawa ya yi zai fita yace "Saida safe ko, yau ma zan kwana a d'aki na saboda muna tare da yarima ne."
Da mamaki tace "Yarima kuma?"
Juyowa ya yi yace "Eh, Bilal ba."
Wani haushi ne taji ya kamata, saukowa ta yi daga kan gadon tace "Kenan a gidan na su ka yi dare haka? Babban mutum ka na ganin abin da ka ke yi ya dace kenan? Wannan fa ba adalci bane, ka daina kula ni, ka daina min magana, ba ka cin abinci na, sannan ba ka kwana a d'aki na, me nai ma ka hakane da ka ke min irin wannan hukuncin? Ni ba wani abu bane a gare ni dan na durk'usa har k'asa na ba ka hak'uri, ka fad'a min dan Allah."
Gyara tsayuwa ya yi ya na kallon ta, hak'ik'a komai gaskiya ta fad'a, sai dai baisan me zaice ba domin kuwa ba zai iya fad'a mata haka kawai ya ke jin tsanar ta ba, cikin taushin murya yace "Kinga ki yi hak'uri da duk abin da ke faruwa, kawai harkoki ne su ka d'anyi tsamari, amma insha Allahu komai ya kusan zuwa k'arshe, ki k'ara hak'uri kinji ko, saida safe."
Ya fad'a ya juya kenan ta sake cewa "Shikenan ka je ka kwana da Bilal, dad'inta dai ba ya da abin da ni ke da shi, komai daren dad'ewa nasan dole ka neme ni a duk in da na ke."
Juyowa ya yi ya kalle ta da mamaki yace "Da Bilal d'in za ki yi kishi? D'ana ne fa shi, kinsan mahimmancin shi a gare ni kuwa? To shi d'in kamar rayuwa ta ne, ina k'aunar sa fiye da komai, ki iya bakin ki in dai akan iyali na ne, ba na juran b'acin ran su ko kad'an."
Idon ta cike da ruwa tace "Usman ba ka adalci wallahi, kullum nunawa ka ke Khadija da d'an ta sune rayuwar ka, kullum sune ma su mahimmanci a wajen ka amma ni ko oho, to kasan ba ka so na me ya sa ka aure ni?"
Girgiza kai ya yi yace "Ni bance ba na son ki ba, sai dai abin da na sani kawai shine ina son iyali na, idan ki na son zama da ni ki so su kema, kuma kar ki d'auka Khadija kishiyar ki ce ki yi kishi da ita, maganar gaskiya ta wuce nan a wuri na, Bilal d'ana ne da ya fito daga jiki na tsatsona, amma ina wa mahaifiyar shi son da bana ma sa, kinsan me ya sa?"
*Ita rayuwa dama haka take, da kin zauna da su lafiya da wannan ranar ba ta zo ba, kuskuren da mu mata keyi wani lokaci shine, ba ma fahimtar abin da mazajenmu suke so, idan har ki ka fahimci mijinki na bala'in son mahaifiyarsa ko yan uwansa ko yayansa, sai ke ma ki bishi ki nuna musu so na gaskiya, ba dan komai ba dan kawai ki faranta mi shi, hakan zaisa ya dinga kallonki da daraja da kima, saboda kina son abin da yake so, amma kishi da hauka da wauta sai ta saka mu rufe idonmu mu nuna k'iyayya da kishi kan abinda suke so, yanzu dai gashi kalaman da a baya bai iya fad'a mata yanzu gashi ya na kallonta ya fad'a mata, kenan ta jima ba ta mutu ba, Allah kasa mufi k'arfin zuciyarmu.*
D'orawa ya yi da "Saboda da ita na fara had'uwa, ita Allah ya fara bani kafin ya bani Bilal, ita ce wacce Bilal d'in ya fito daga jikin ta, shi ya sa na ke mata k'aunar da ko shi Bilal ba na masa, zanji zafi matuk'a idan aka ce yau na rasa Bilal, amma kuma zanyi farin ciki idan na waiga naga Khadija a gefe na, ba dan komai ba saidan nasan za ta sake bani wani Bilal d'in."
Ya na gama fad'a ya juya ya bar d'akin ya koma na shi ya kwanta ya rumgume Bilal kamar zai had'e shi, ya na shafa shi har bacci ya d'auke shi shima, Haseenah kam kuka ta fashe da shi mai tsanani, wai abin da a baya yake ma sayawa baya fad'a yau gashi ya fad'a, kai lallai abin nan bana lafiya bane, tunaninta ne ya bata duk wani shiri da tayi a kan shi ya wargaje, dan haka dole ta sake sabo, da haka ita ma ta yi bacci da tunanin kiran Mariya idan gari ya waye.
*Luv u all.*😘
09/03/2020 à 15:01 - 💋😘💋: 💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
*KALLON KITSE*
_(Ake wa rogo)_
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
_SAMIRA HAROUNA_
*Litattafan marubuciyar*
*1* _KAUSSAR_
*2* _D'AUKAR FANSA_
*3* _BA SO BANE_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI_
*6* _JIHADI_
*7* _K'ANGIN RAYUWA_
*8* _ITACE K'ADDARARMU_
*9* _KAWU NA NE_
*10* _MAATA_
*11* _KALLON KITSE..._
*SADAUKARWA GA*
_MATAN FARKO_ 🧕🏼 *(UWAYEN GIDA)*
🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_🤜🤛
```Fatan alkairi masoya```
_💕 Masoya wannan littafi wannan kyautar ku ce, nagode da soyayyar da kuke nuna min ni da kaya na😚, Allah ya barmu tare._💞
_Bismillahir rahamanir rahim_
*37*
Ko da gari ya waye Bilal ya shirya cikin k'ananan kaya dan yau alhamis ce ba karatu, Usman ma kamar kullum cikin shadda ruwan madara ya shirya, tare suka fito falon Haseenah sun same ta zaune tana waya da Mariya, bayan ta fad'a mata akwai matsala ne Mariya tace ta sake fito da kud'i kawai a mata aiki, kafin ta yi magana ta ji fitowar su hakan ya tilasta mata aje wayar, juyowa ta yi ta na kallon su, duk da cikin hushi take amma tabbas tasan an samo Bilal ne daga Usman, dan zubin hallitarsu ma iri d'aya ce, duk da ba ta zauna da yaron sosai ba amma ta fahimci ya na da miskilanci fiye da ubansa, kai tsaye teburin cin abinci su ka nufa dan ba su ma lura da ita a zaune ba, saida ta ga sun zauna ta taso ta nufo su dan zuba mu su abinci, sai dai ta na mamaki yanda yau Usman zai ci abincin ta tunda ya jima baici ba, shi kuma zai ci ne kawai saboda Bilal na gidan yau, amma sam baya sha'awar cin abincin ta tunda ya lura kullum abinci kala d'aya ta iya sarrafawa, tun kafin ta tsaya wajen Bilal yace "Aunty ina kwana?"
Cike da makirci ta shafo kan shi tace "Yarima, ashe gidan mu ka kwana jiya, lokacin da ku ka shigo har na yi bacci, ya ka ke?"
Shi kam yaron fuskar shi ba fara'a yace "Lafiya lau."
Kallon Usman ta yi wanda ke kallon cikin ta shi ma tace "Ina kwana babban mutum?"
Ba walwala a tare da shi yace "Lafiya lau, ya jikin na ki?"
Da murmushi ta amsa da "Da sauk'i sosai." Shayi ta fara had'awa Bilal ta aje ma sa kafin Usman d'in, tare su ka karya dukan su bayan sun gama Usman ya mik'e zai fita, hannun Bilal ya kamo yace "Muje ko yarima, yau da kai za mu fita."
Da zumud'i ya mik'e tsaye dan bin mahaifin shi amma sai Haseenah tace "Haba dai babban mutum, wannan ma ai son kai ne wallahi, yaushe rabon da na ga Bilal, yau ya zo kuma shine za ka fice da shi, gaskiya ni dai ban yarda ba."
Kallon ta ya yi yace "To ya ki ke so ayi?" Kallon Bilal ta yi tace "Ka bar min shi mana, anjima idan ka dawo sai ku fita tare."
Duk da ya samu labarin dalilin da yanzun mahaifiyar shi ke gida, amma kuma ba ya jin akwai wani abu da za ta iya yi wa Bilal tunda ya na gari, ajiyar zuciya ya sauke ya kalli Bilal yace "Yarima, ka zauna tare da auntyn ka kaji, zan fita amma ba zan jima ba zan dawo, idan kuma ka gaji da zaman gidan ka na iya fita k'ofar gida wajen Rabe sai kuyi hira."
Saida Bilal ya kalli Haseenah kafin ya kalli Usman yace "To Abba, amma fa kar ka jima sosai."
Dafa kan shi ya yi yace "Ba zan jima ba insha Allahu."
Saida ya sumbace shi kafin ya kalli Haseenah yace "Ba wani abin da ki ke buk'ata?"
Sosa kai ta yi irin na kunyar nan ta kasa magana, hannu kawai ya sa aljihu ya fito da kud'i ya bata, karb'a ta yi ta mi shi godiya kafin tabi bayan shi har ya shiga mota, Rabe da ke zaune da littafin karatu (dan tunda aka ce za'a maidashi makaranta abun ya sake shiga ran shi) ya taso suka gaisa kafin ya bud'e mi shi k'ofa ya fice ya na binshi da addu'a, rufewa ya yi har ya zauna Haseenah ta k'wala mi shi kira ya zo, tsaye ya ke kamar yanda take su na kallon juna tace "Wannan pliwoyin ka basu ruwa mana, ya ka ke abu kamar ba ka san aikin ba ne."
Wani kallon raini ya mata dan babu abin da bai wani ba game da ita kafin yace "Tofa, to na ji zan ba su ruwan, shikenan?" Ya na fad'a ya juya ya bar mata wajen, ciki ta koma ba ta damu da shi ba dan a cewar ta k'aramin arne ne shi ba ta shi take ba, yau dai ba wata matsala tsakanin ta da Bilal, ya na zaune gefe ta na zaune ita ma sai dai su kalli juna, dan dama ba tace ya bar shi bane saboda ta na da wani nufi akan hakan, kawai ta fahimci ta b'ata mi shi rai ne jiya saboda abin da ta fad'a, ana hakane ta shiga madafa d'ora girkin rana, ba jimawa da fara aikin Bilal ya shigo da sallama, amsawa ta yi tace "Ya dai?"
Cikin ladabi yace "Aunty dama zanje gidan aboki na *Abdallah* yanzu zan dawo."
"To shikenan sai ka dawo, amma kar ka jima kuma uban ka ya dawo ya min tijara." Ta fad'a ta na ci gaba da aikin ta, da sauri ya fita ko amsa ta biyi ba, ashe Bilal moton shi ya d'auka ya fita da shi Haseenah ba ta ma sani ba, Rabe kuma tunda bai san ba'a barin shi fita da shi ba shima bai hana shi ba sai ma bin moton da kallo da ya yi har ya daina ganin Bilal kafin yace "Kai, Allah ka bamu kud'i mu ma muji dad'in rayuwa."
Wannan addu'a fa bana bari ta wuce ba ni kai na, dan haka na amsa da *ameen*, Bilal ya je gidan su Abdallah da babu nisa sosai da nan d'in, sunyi farin cikin ganin juna dan sun jima basu had'u ba, amm bai yarda ya jima ba ya mu su sallama ya juyo ya dawo, *tsautsayi fa ance idan ya wuni baya kwana*, rabon ayi Bilal su ka had'e shi da wani mai mota a lokacin da zai shigo kwana, mutanen dake wajen ne da su ka ankara wasu kuma akayi gaban idon su ya sa suka rabka salati tare da sallalami, tuni aka rufe wajen ana jimami tare da taimakawa Bilal da tuni baisan in da kan shi yake ba, a daidai lokacin motar Usman ta shigo layin, dan gaba d'aya hankalin shi ya kasa kwanciya, yanzun ma ya taho ne da nufi ya d'auke shi ya tafi da shi duk in da ya saka k'afar shi, ganin wannan taro yasan had'ari ne dan haka ya tsaya tunda dai a unguwar su ne abun ya faru, tashin hankali da ba'a saka mi shi rana, sai ga Usman ya ga Bilal hannun mutumin da ya bige shi jina-jina kamar babu rai a tare da shi, kallon shi ya kai kan moton shi daya wargaje abinka da dama roba tafi yawa a jiki, wani irin duka ne gaban shi ya fara yi yayin da zuciyar shi kamar za ta fito, a hankali ya ke kutsowa cikin mutanen wanda ke ta hayaniya kowa da abin da yake fad'a, wasu na fad'in sun san shi za su je su fad'a a gidan su, in da wasu suka dakatar da su da cewa kar aje babu namiji a gidan mata ba lallai su rik'e kan su ba idan su ka ji irin wannan labarin, hannu Usman ya zura ya karb'o Bilal daga hannun mutumin da ke kallon shi da mamaki, yana amsar shi wayar Bilal ta fad'o daga aljihun shi ta fad'i k'asa, d'aya daga cikin mutanen wurin ne yace "Mahaifin shi ne."
Motar shi mutumin ya bud'e da nufin a saka Bilal ciki amma sai Usman ya nufi tashi motar da shi, amma daga ganin yanda ya ke takawa jikin shi sai b'ari yake haka ma hannayen shi, dan yanda ya ke kallon Bilal baya jin zaiyi rai, sosai jikin shi ke rawa har ya na neman fad'uwa da Bilal d'in, da sauri wani mutum da shi ma anan unguwar yake ya karb'e shi a hannun shi ya na fad'in "Ayi hak'uri Alhaji, ayi hak'uri, insha Allahu zai tashi."
Zagayawa mutumin ya yi ya kwantar da Bilal sai Usman da ya shiga ya tayar da mota, wanda ya bige shi ne ya bi bayan shi har suka isa asibitin da tafi kusa da su, amma ganin halin da Bilal ke ciki ya sa suka tura su babban gida (Hôpital), nan aka karb'e shi da taimakon ubangiji aka bashi taimakon daya dace.
Usman na zaune akan wani banci amma da simitin aka yi shi ya na tunani, shin dama Haseenah na da burin kashe ma sa d'an sa ne kome? Yanzu taya zan fara fad'awa Khadija maganar nan? Sai ta ga kamar da ni aka had'a baki ma aka cutar da shi, wata zuciyar ce tace mi shi, haba dai, ba ma za ta yi tunanin haka ba, nauyayyar ajiyar zuciyar da ya sauke ce ta sa wanda ya bankr Bilal d'in kallon shi, dafa kafad'ar shi ya yi yace "Dan Allah ka yi hak'uri, abun ya faru ne a bazata, bansan..."
Kallon shi ya yi yace "Ba komai malam, tsautsayi ne da baya wuce ranar shi, nima ina da abin hawan nan, kuma hakan na faruwa sosai."
Jinjina kai ya yi yace "Allah ya tashi kafad'un shi."
Da k'yar Usman ya iya cewa "Ameen." Likita ne ya fito daga d'akin ya na cire abin da ke rufe a hanci shi, hannu ya ba Usman da ya mik'e yace "Mu gode Allah, ya na samun lafiya in Allah ya yarda, ya na bacci yanzu."
Sanyayyar ajiyar zuciya ya sauke yace "Alhamdulillah, nagode sosai likita, Allah ya saka da alkairi."
"Ba komai." Cewar likitan ya na shirin shiga ofishinshi, Usman d'in ne yace "Likita za mu iya ganin shi kuwa?"
Juyowa ya yi yace "Eh, za ku iya." Da sauri Usman ya nufi d'akin, Bilal ne kad'ai a ciki kwance jiki duk bandeji, k'arasawa su ka yi kusan shi suna kallon yanda Allah ya canza hallitar shi cikin k'ank'anin lokaci, mutumin ne ya mi shi sallama tare da cewa saiya dawo, ya na tafiya ya kira malam ya fad'a mi shi, zuwa bayan sallah azahar d'akin da Bilal ke ciki ya cika da yan uwa, sai dai wajen su Khadija har yanzu ba su san me ke faruwa ba, duk suna zaune jugum har yanzu Bilal bai farka ba wayar Usman ta shiga kururuwa, cikin sanyin jiki ya fito da ita ya duba, take gaban shi ya tsinke ya fad'i saboda ganin sunan *uwar yarima*, kallon Hajia ya yi da ke fuskantar shi, har wayar ta tsinke bai d'aga ba saida tace "Ka d'auka mana, wa ya ke kira ne?"
Cike da damuwa yace "Khadija ce." Malam ne yace "Ka d'auka mana sai ka fad'a mata wani abun, inyaso sai kaje gidan ka fad'a musu a nutse."
Khadija da ke tare da k'anwar Mama da kuma Kaltume zaune kasa hak'ura ta yi ta sake aika wani kiran, dan gabanta ne taji ya tsananta fad'uwa haka kawai, ta kira Bilal kuma ba ta samu ba shi ya sa ta kira Abban shi, d'auka ya yi cike da son b'oye halin da ake ciki yace "Uwar yarima ya ake ciki? Har kinyi kewata ko?"
Hajia dake kallon shi mik'ewa ta yi ta fita saboda kunya, inda Khadija ta amsa da "Na yi kewar ka mana, kai fa?"
"Kema kinsan na yu kewar ai, yanzu fad'a min kin shirya ne na zo na d'auke ki?"
Dariya ta yi tace "Haba dai, da rana haka patsal-patsal, ai ko zan shigo saida dare."
"Kamar wata marar gaskiya, to me ya sa?"
"Saboda lokacin da za'a kaini gidan ma da daddare aka kai ni, dan haka yanzu ma sai da dare zan koma."
Murmushi ya yi yace "To da da d'in da yanzu d'aya ne? A lokacin fa kina sabuwa ne fil a leda, yanzu kuma na bi ta ciki na fito, sannan Bilal ya fito ta nan ga kuma k'annan shi ma na shirin fitowa."
Duk da ya sassauta murya saida Hassana taji me ya fad'a, kallon shi ta yi ta kuma sunne kanta k'asa ta rufe baki cike da kunya, Khadija kam cewa ta yi "Matsala ta da kai fa kenan, yanzu dai ba wannan ba, ina yaro na yake? Ina kiran shi amma ba a samu."
Wani tsam yaji a jikin shi kafin ya daure yace "Bilal ya d'an fita tare da Murtala, mu na shago ne, watak'ila cajin wayar ne ya k'are, amma zan..." Kasa k'arasawa ya yi saboda rawar da muryar shi ke yi, da k'yar yace "Zan kira ki saina baki shi."
Ba tare da damuwa ba tace "Shikenan sai na jika, sai anjima."
Cike da zolaya yace "Au! dama muryar d'an ki kawai ki ka kira kiji? To ya yi kyau."
Dariya ta yi tace "To meye a muryar ta ka da za ta dame ni? Bayan anjima kad'an za mu kasance tare da kai."
Da haka sukayi sallama bai nuna mata komai ba, sai lokacin ne malam yace ya kamata su san halin da ake ciki, fita ya yi da niyyar zaije ya samu Ashir ya fad'a masa, hakan kuwa akayi dan ba jimawa ya isa in da Ashir ke harkokinshi, bayan sun gaisa ne ya fad'a masa abin da ke faruwa, ya jinjina al'amarin tare da tashin hankali, amma sai Usman yace "Idan dai har kai za ka d'aga hankalin ka to ya mahaifiyar shi kenan? Na zab'i na fad'a ma ka saboda ka san ta hanyr d za ka kwantar mata da hankali."
Shiru Ashir yayi kafin daga bisani yace "Hakane Usee, insha Allahu zan fad'a mata yanda za ta fahimta, kar ka damu."
Hannu ya bashi su ka yi sallama yace zai wuce gida ne, shi ma Ashir d'in gidan ya nufa daga nan dan fad'a musu, Mama ya fara fad'a ma tasan halin da ake ciki, ita kanta Mama da k'yar ta iya fad'awa Khadija, cikin tashin hankali tace Ashir ya kaita asibitin taga d'an ta, a hanya ma kuka take ta na fad'in kawai laifinta ne da ta yarda ta bashi yaron, Mama ce ta dinga tausarta da kalamai masu kwantar da hankali da k'arfafa gwiwa, suna isa asibitin aka nuna musu d'akin, da sallama su ka shiga amma Khadija na ganin Bilal kamar ba shi ba sai ta yi shiru, da k'yar ta isa ga gadon ta zauna ta na shafa fuskar shi, hawayen da suka taho mata ne ya sa malam cewa "A'a Khadija dan Allah, kar ki masa kuka mana, k'addara ce da kuma tsautsayi, ki masa addu'a Allah ya tashi kafad'un shi."
Hassana ce ta yi tsaye kanta tana shafa bayan ta tana bata hak'uri ita ma, sun jima a haka kafin ta kalli Nura tace "Har yanzu bai farka ba?"
Cikin sanyin jiki yace "Bai farka ba har yanzu, amma dai likitan yace an masa allura ne."
Cikin zubo da wasu hawayen tace "Ko dai ya mutu ne? Dan Allah ku fad'a min idan ya mutu, wallahi zan d'auki dangana."
Hajia ce tace "Haba Khadija, idan ya mutu za mu saka shi gaba ne haka, da ran shi mana gashi ma ya na numfashi."
Haka suka zauna jugum sai wasu dake tafiya wasu na zuwa, sai yamma kad'ai Bilal ya farka idon shi har sun kumbura, bud'ar bakin shi da "Mummy, Mummy." Ya fara, dama ta na kusa kam ta rik'o hannun shi tace "Gani nan Bilal, bud'a idon ka."
Bud'a ido ya yi ya kalle ta sosai, hawaye ne suka taho mi shi yace "Mummy ina Abba na?"
Saida ta mayar da na ta hawayen tace "Ya tafi gida yanzu zai dawo."
Da k'yar yace "Mummy, ciwo na, ki bani ruwa na sha." Ruwa ta d'auka ta bashi, komawa ya yi ya kwanta yanda ya ke har bacci ya sake d'aukar shi.
*B'angaren* Usman kuma tun a hanya yake tunani dama Haseenah ta shirya raba shi da yaron shi, in ba haka ba me ya sa ta hana shi ya fita da shi? Kawai makirci ne ta shirya mi shi dan ta raba shi da Bilal d'in shi, tunda ai tasan baya bari Bilal ya fita da moton shi, ko a k'afa bai cika son ana aikan shi ba wajen ti-ti, da wannan tunanin ya k'araso gida dan d'aukar mataki akan amarsu.
_Ita dama rayuwa haka take tafiya, ka shuka alkairi saika girbi alkairi, a baya mutane suna ganin laifin Khadija saboda makircin Haseenah, wanda ita Khadija a kan gaskiyarta take, yau kuma gashi Haseenah ita ma bata da niyyar cutar da Bilal, amma sakkayar Allah dama haka take, gashi ita ma yanzu za'a hukunta ta akan laifin da bata san hawa ba bata san sauka ba, Allah ka mana agaji da kan ka._
Haseenah da ke madafa a lokacin da waya a kunne ta kira Mariya ta na tambayar ko za ta zo? Cewar Mariya "Haseenah ba zan samu damar zuwa ba wallahi, saboda kwana biyun nan munyi hidimar biki, ko na tambayi Abban Fadila ma ba zai bar ni ba, amma ke ki zo ki kawo kud'in, idan na samu dama sai naje wajen malam d'in."
Cikin damuwa tace "Haba aunty Mariya, na fad'a mi ki fa halin da nake ciki, wallahi Usman ko magana ba ya son yi min, ina ga fa Khadija wani asiri ta masa ya juya min baya, kuma yace za ta dawo gidan, jiya ma kar ko so kiji maganar da ya fad'a min akan Bilal, to ina ga ta dawo gidan? Ai sai dai ya sake ni."
Mariya ce tace "To ya za ayi? Ni dai yanzu na fad'a mi ki uziri na ai, kinga kuwa dan na gyara aurenki ai bana b'algace nawa ba."
Ajiyar zuciya ta sauke tace "To shikenan, bara ya shigo saina tambaye shi naji idan zai bar ni, ko zuwa gobe sai naje na kai mi ki kud'in, amma fa aunty Mariya wannan karan so na ke gaba d'aya a zautar da shi ya zama ba komai a gabansa sai ni, sannan ba shi kad'ai ba har iyayen shi da yan uwan shi ina so a rufe bakin su, su zama babu ruwansu da harkar shi bare har wani ya yi tunanin taimaka masa da ko da addu'a ce."
Da matuk'ar mamaki Mariya tace "Ke Haseenah, a ina ki ka koyi mugunta haka? Yaushe zuciyar ki ta zama marar imani haka? To kinga gaskiya no ba zan iya wannan aikin ba, dan in na biye mi ki mu ka yi haka to kashin mu zai bushe wallahi."
Cikin rashin nuna damuwa tace "Me ki ke nufi? Kamar ya banda imani?"
Muryar Usman ce ta bata amsa da "To ki na da shine imanin?"
Bata san lokacin da ta saki wayar ba ta juyo da k'arfi, hannu tasa ta rufe bakinta matuk'ar tsoro a fuskarta, tabb', lallai yanda ta ga alamunshi ta san yau babu tsumi ba dabara, amma duk da haka bara ta jaraba lallab'a shi ko Allah zaisa a dace, a cewar ta fa, durk'ushewa ta yi ta had'e hannayenta ta kalle shi tana hawaye tace "Dan Allah dan girman Allah Abban Bilal ka yi hak'uri, wallahi tallahi sharrin shaid'an ne da zugar aunty Mariya, ka yi hak'uri ka yafe min dan Allah ko dan cikin nan dake jiki na, wallahi na ma ka alk'awarin haka ba za ta sake faruwa ba."
Takowa ya yi har kusanta ya sa hannu ya kashe wutar gas d'in, tsayawa ya yi ya na k'are mata kallo, wai yarinyar da ya aura saboda nutsuwarta da hankalinta, ita ce ta yi sanadiyar faruwar abubuwa marasa dad'i irin haka a rayuwar shi, ita kam kallon da yake mata ne ya sa ta sake cewa "Dan Allah babban mutum ka yi hak'uri, wallahi ba laifi na bane, wall..."
Marin da ya zuba mata ne ya sa ta kwamtsa wata k'ara ta fad'i kwance, duk'awa ya yi ya d'ago ta cikin zafin rai ido jawur yace "Haseenah me nai mi ki a rayuwa? Me ya sa ki ka cutar dani? Me ya sa Haseenah?"
Cikin duburburcewa tace "Wallahi ba ni bace, ka yi hak'uri dan Allah, ba zan.." Shak'e mata wuyan da ya yi ne yasa komai nata tsayawa idon ta fitowa waje, cikin fitar hayyaci Usman ke fad'in "Haseenah ke annoba ce, jaraba ce kuma masifa ce ke da bala'i, barin irin ki a doron duniya wallahi japa'i ne, wallahi da zan kashe ki amma ba zan iya ba saboda cikin da ke jikin ki, Haseenah banga anfanin zama da ke ba a rayuwa ta, kin raba ni da hankali na da ubangiji na, kin raba ni da iyaye na da 'yan uwa na, kin raba ni da matar da nafi so a rayuwa ta, sannan kin raba ni da d'ana da ya fito daga ciki na, Haseenah ni kam ya zanyi dake? Wane irin hukuncin ma zan mi ki ne da zai sa na huce abin da ki ka min."
Haseenah dake ta fafutukar neman rayuwa ya na sakin ta ta samu ta sauke wasu numfarfashi, mik'ewa ya yi tsaye ya juya baya ya cire hular kan shi yana shafa sumar shi kamar zai cire kan, sake juyowa ya yi ya nuna ta da hannu yace "A dalilin ki yanzu haka Bilal na kwance asibiti, bansan ko zai rayu ba saboda yanda jikin shi yake, dan haka Haseenah ba zan iya ci gaba da zama dake ba, kije gidanku kawai na sake ki saki biyu."
Wata k'ara Haseenah ta yi ta d'ora hannu akai tace "Ahhhhhhh, na shiga uku na lalace, dan Allah Usman ka rufa min asiri ka yi hak'uri ka yafe min, wallahi ba zan sake ba na rantse ma ka, ka taimaka min mana ka dubi cikin nan dake jikina, kar ka mayar dani bazawara tun yanzu Usman ko haihuwar fari banyi ba."
Girgiza kai yayi ya tab'e baki yace "Hum, ai ko meya faru ke kika jawa kan ki, dan haka ki tattara naki ya naki ki bar min gida na, idan ki ka bari na dawo gidan nan na same ki wallahi saina lahira ya fiki jin dad'i."
Yana fad'a ya fice daga madafar ya shiga b'angaren shi, rage kayan jikinshi ya yi ya shiga ya watsa ruwa saboda yaji sanyi, yana fitowa maganin ciwon kai yasha kafin ya canza kaya ya bar gidan ko kallon b'angaren Haseenah baiyi ba, a tunanin shi ma tana barin gidan zai ruguza wannan b'angaren dan ya zauna lafiya, dan ba zaisake bari zuciyarshi ta raya mi shi sake k'ara wani aure nan gaba, lokacin har an fara kiran sallah la'asar sai kawai ya tsaya ya yi sallah kafin ya isa asibiti.