Tana cikin tunanin ne saiga kiran UMMAKATIN ya shigo wayarta. Cikin lumshe ido da wani hali tad'auka da cewa.. "Yanxu nake shirin kiranki.
UMMAKATI ta sauke ajiyar zuciya da fad'in. "Da fatan dai kinkai gida lafiya, duk hankalina ya tashi danaji wani abokin Alhajin nan ya kirasa yana gaya masa abubuwan da suka faru, nan gabana ya fad'i yace min karna damu ai koda anyi wanda yafi hakan bincike bazai zo inda muke ba, shine nace bara ke nakira naji ko kinkai gida lafiya.
Jan numfashi RAHMA tayi da cewa. "Nakai gida lafiya dan yanxu haka ma ina kwance ne. "Toh bari na barki sai mun had'e da safe dan dak'ar nake miki magana. "Eh, ai naji hakan, sai da safe.
RAHMA na fad'in hakan takashe wayar dajan bargo tana lumshe ido cikin matuqar jin bacci.
Shiko ABDUL sanda ya tabbatar da nan ne gidansu sannan ya kad'a kan mashing d'in yabar layin nasu.
Bai wani sha wahalar gane hotel d'in ba, dan wani police ya tambaya ya mai kwantance ammafa sanda ya bashi kud'i, Allah ya kyauta.
AMEER ya kallesa bayan shigowarsa d'akin da aka saukesu yace. "Ka kaita lafiya. "Eh. Ammafa yarinyar bata da kunya. Wallahi da qanwata ce baqaramin wahala zatasha aguna ba.
Dariya AMEER yayi da qara jan bargwan jikinsa yace. "Ai sufar yanayinta ya bayyana kansa. Zatayi shagwaɓa da rashin kunya wannan babu makawa😀.
Sanda ABDUL yayi sallah raka'a biyu ya rok'i Allah kan ya kintsar dasu sannan ya saka qaunarsa cikin zuciyar mahaifiyarsa kana ya kwanta. Wannan itace addu'ar ABDUL ako-da yaushe.
Eh, gaskiya RAHMA bata wani damu da sallah akan lokaci ba can ba🙁, Zatayi ammafa ba akan lokaci ba, kuma hakan ya faro asaline lokacin data fara fanɗarawa.
Yanxu haka sallar asuba sai kusan qarfe bakwai da rabi tahau yinta, dan anyi mata tashin duniya taqi Tashi, bayan ta'idar ne sai tanufi wajen mahaifinta danta gaida shi, saidai da damuwa ko akan fuskarsa ya amsa mata yana meci gaba da cewa. "Yanxu Mamana ban isa na gaya miki magana kiji ba kenan ko, duk abinda nake gaya miki baya shiga kunnanki ko,
Ahankali ta ɗago da fararan idanta tace. "Tome kuma nayi yanzu, nifa banyi komai ba, "ina nufin jiya da kika dawo ƙarfe ukun dare ina kikaje.
Sosa ƙeya tayi da cewa birthday ɗin wata ƙawarmu mukaje nida UMMAKATI, Wallahi Baba tana sa kirki sosai yarinyar.... "Wane birthday ɗin arziƙine za'a yisa cikin dare, wato baza dai kiji abinda nake gaya miki ba ko. Kina dai ganin yanda kowa yake nuna miki tsana agidan nan amma kinkasayin hankali ko.
"Toh kayi hak'uri Babana bazan sake ba kaji, Allah bazan sake ba. Ta katse shi da faɗin hakan cikin raunin murya da shagwaɓa.
Hmm haka dama al'amuran suke, cikin ƴaƴanka dole kafi San wani, kafi ƙaunarsa, kamar yanda na gaya muku mahaifin RAHMA yana bala'in santa da ƙaunarta, koda ya shirya mata faɗa fata fata tana bashi hak'uri yake haƙura.
Dama shi irin iyayen nan ne waƴannan basu zafi kuma basa duka, Sam baya duka ko kaɗan, dan haka cikin saka mata albarka dayi mata fatan kintsuwa yace taje Allah yayi mata albarka..
Dataje gaida mamanta ko muguwar harara ta auna mata tace "gidan uban wa kikaje jiya dahar kika kai ƙarfe uku na dare. Wato bazaki dena yawan dare ba ko, wato sam ke ba'a isa dake bako.
Turo baki waje RAHMA tayi da cewa, "Toh kiyi hak'uri bazan sake ba.
"Toh kiyi hak'uri bazan sake ba,🙁 maman ta mai-mai ta abinda tace cikin takaicinta kana taci gaba da cewa.. Wallahi RAHEEMAT kima kanki fad'a, idan yau mune gobe bamu bane, yanxu ke ko kishin kanki bakyayi ace cikin gidanku ke kad'aice kika fitta zakka, kowa baya sanki baya qaunarki kuma baki damu ba.
"Toh ai y'an uwan nawa ne kad'ai basu sona, muta nan gari suna sona suna qaunata Wallahi dan baki fitta zuwa wajejen da nake zuwa ne dasai kin sha mamakin yanda ake ƙaunar ƴarki...
Saurin bige mata baki maman tayi afusace tace, "Allah yamin tsari da yawan gurare irin naki yawan gantali, nan har wani abun arziƙi ne ace jama'ar wasu gune suke ƙaunarki ba danginki y'an'uwanki ba, yanxu ko mutuwa kikayi ke dai kam wannan mala'ikan rubuta kyawawan d'abi'un mutane bazai samu kyawawa daga wajen y'an uwanki ba sai munana,
Wallahi RAHEEMAT kima kanki fad'a ki canja hali, yanzu bazaki San darajar fad'an da nake miki ba har sai kinga babu raina tukunna zaki san darajarsa, Yanxu maza ficce min daga d'aki mutuniyar banza kafin nayi boll dake..
Turo baki taqarayi gaba☹ da ficce daga d'akin mahaifiyar tata dan RAHMA ta tsani fad'a a rayuwarta..
Subaiba yarinyar matar babansu ta hud'u ta kalleta da kyalkyalewa da dariya tace. "Hmm Allah ya kyauta. Tana fad'in hakan taci gaba da karatun novel nata na online na wannan marubuciyar UMMU BASHEER wato *KE HASKE CE* labarin yana mata dad'i sosai..
Amma me😳 sam batayi tsambani ba saiji tayi fauuuu🙁 RAHMA ta fallata da mari, kanta saita tunaninta nan taqara kai mata wani Marin gauuu kamar tasamu jikin dotse😨.
Kan kace me🤔 nan fad'a ya kaure tsakaninsu kamar a filin dambe. Dake Subaiba ma ba'a barta a baya ba wajen qarfi nanta kwashe RAHMA sai ganinta kawai nayi a qasa.
A rayuwar rahama sam ta tasani a kadata a fad'a dan haka bata ba Suwaiban damar hawa ruwan cikinta ba, nan tayi kukan kura ta d'aga Subaiwan daga ƙasa ta nunama Allah ta nanata da ƙasa,
Habawa nan suka dinga birgima a ƙasa suna masu yakushin juna da kaima juna juka kowane iri.
Subaiwa ta d'auki wani takalmi me tsini ta kwantarawa RAHMA aka, zahiri taji zafi sosai hakan yasa tayi saurin rarumo wani takalmin itama me tsini na ummi ta kwantara mata itama aka, saidai nata yazo da akasi dan a goshi ta kwantara mata, nan wajen ya d'an fashe jini ya fara zuba, amma saboda shed'an ya kad'a musu ganga nan sukaci gaba da faɗan Cikin jin matuƙar ƙiyayyar juna.
Dake ba kowa a d'akin su suke amansu suke lashewa.😀
Can matar baban nasu ta uku tazo waccewa ta d'akin nasu, nan taji ana gurnani da nishi irin na wahalar nan saita leƙa taga meke faruwa😂. Ai nan taga Suwaiba kan RAHMA tana kici kicin kwaye mata fuska.😨. Bata samu dai nasara ba dan wani juye RAHMA tayi da ita wanda yasa nan take itama ta haye ruwan cikinta tahau falla mata mari da make mata baki tana cewa... "Dan uwarki wa kikema dariya"
Salati Iyami tasaka tana cewa jama'a kuzo zasu kashe kansu🙆🏼♀
Kan ka kace me🙁 nan jama'ar gidan sukayo d'akin. Still wannan karan ma daqer aka d'aga RAHMA daga ruwan cikin Suwaiba.
Da kuka RAHMA take bada labarin wai dariya Subaiwan tayi mata dan kawai taga ta shigo d'akin da b'acin rai, Kowa salati ya kamayi awajen suna masu cewa "Yanzu ke dan tayi miki dariya shine kika hauta da fad'a haka kamar ba Yayarki ba😨
Murgud'a musu baki RAHMA tayi da barin gidan gabaki d'aya tayi gidansu UMMAKATI
Maman UMMAKATI na ganin RAHMA tasakar mata murmushi da cewa "Ha'a, yana ganki ke d'aya ina ƙawar taki.
RAHMA ta kalleta da b'acin rai tace "Bata dawo bane.
"Eh, aina zata tana gidanku anan takwana.
"aa acan na barota hotel d'in Sharna" "Ok, ba mamaki ki ganta yanxu.
Shuru RAHMA tayi mata. Jin hakan sai yasata lura da yanayinta, nanta gano kamar akwai abinda ya faru da ita yanxu, dan haka sai taci gaba da cewa, Me ya faru ne naga kamar antab'amin ke. Cikin qara turo baki RAHMA tace "Ba Subaiba bace daga ganina na fitto daga d'akin mamammu kawai saita hau yimin Dariya.
"Wato ita dai Suwaiba bata San zaman lafiya sam, banda haka miye nayi miki dariya. "Aunty ki barta kawai zan gyara mata zama dan Wallahi wata rana Allah b'allata zanyi.
"Ki daiyi hak'uri dan sun rasa yanda zasuyi dake ne shiyasa baqin ciki yake kamasu har su dinga neman tsokanarki, ki barsu kawai kidena shiga harkarsu.
Shuru RAHMA tayi dan da gaske ranta ya b'aci da dariyar da Suwaiban tayi mata.
Can saiga UMMAKATI ta shigo gidan, da Murmushi ta kalli RAHMA da cewa. "Yeee qawata ammafa gaskiya alhajin nan bashi da dama.
mamanta ta kalleta tace "Wane Alhaji.
Maida kallanta kanta tayi da matsawa kusa da ita tace. "Wani ne mana mama, yana da kirki sosai, kinga har dubu ishirin yaban yace na baki.
Nan maman tata ta waro ido cikin murna ta amshe kud'in daga hannun UMMAKATIN tana cewa "Kai ammako nagode Allah ya saka masa.
Tashi UMMAKATI tayi da kama hannun RAHMA tace "zomuje dakina mana kiji, nan ko RAHMA tabita d'akin nata wanda yake d'auke da qaramin gado da katifa sai kayayyakinta na sawa, bayan sun zauna kan gadan zuge Jakarta tayi da fito da wani kud'in ta nunama RAHMA tana cigaba da cewa, duk shi yaban, wato RAHEEMAT Alhajin nan yayi, gaya min ya kika gaya da naki.
Jan numfashi RAHMA da cewa "Ni sai yanxu ma na tuna dashi, ban karb'i ko sisi agunsa ba, amma yanxu bara ki gani.
Nan RAHMA ta lalubo numbarsa ta tura masa waƴannan hotunan nan tana me gaya masa gaskiya taji dad'in harka dashi cikin wannan dare, ga hotunan data d'aukesu nan sai maimaita kallansu take, Dan Allah yayi hak'uri tatafi batare data tsaya ya dawo hayyacinsa ba bare ya bata wani abu, amma yanxu tasamu nutsuwa ga A/C num nata nan tana buqatar ya turo mata da dubu d'ari yanxu zatayi wani abu ne da ita..
Lokacin da sakwan ya iske wannan Alhaji a fusace ya kira RAHMAN yana ce mata, "Ke qaramar y'ar iska, karki nemi ki raina min hankali, danna gama tunani tsaf na gayane babu wani abu daya shiga tsakanina dake har zuwa lokacin da bacci yayi awan gaba dani, dan haka babu abinda zan turo miki dashi..
"Gaske.... Ta katse shi da faɗin hakan tana me murmuwa tare da yima UMMAKATI sigina cikin wani salo taci gaba da cewa, Babu abinda zai hanaka turomin da kud'in dana buqata, eh da gaske babu abinda ya shiga tsakanina dakai, saboda ina da wayo, nasan sarai abinda kake nema aguna ba abu bane na banza, wannan dalilin yasa nayi amfani da damata danna b'ata tunaninka, wato kayi kuskuran neman harka dani, hotunan dana turo maka idan baka turomin da kud'in da nake buqata ba Wallahi nan take zan turasu yanar gizo kowa ya gani ya abinda babban mutum kamarka yake aikatawa.....
"aa aa dakata, kin san koni waye da kike shirin aikata hakan agareni, zan turo miki da kud'in da kika buqata yanxu sai dai daga shi babu ni babu ke, Ya kai qarshen zancen gumi na tsattsafo masa.
Dariyar mugunta RAHMA tayi da cewa. "Wannan ne dai kuma kayi qarya, dan zan nemeka aduk lokacin da nake bukar kud'i, na barka lafiya sai naji shigowar sakwan.. Tana fad'a mishi hakan ta kashe wayar da kallan UMMAKATI wacce ta zuba mata ido kawai tana kallanta. RAHMA ta kalleta da cigaba da cewa, abin ya birgeki ko, hmm Wallahi kima kanki fad'a kidena bama mazaje kanki kamar wata shashasha, dan tatse miki komai zasuyi kije gidan mijinki da saura, ni tanadin danama mijin Aure na babban danadi ne, dan zanyi mai mugun bazata nanuna masa BARIKI IYAWA CE, in sashi qaryata kalaman da y'an uwa suke fad'a na wai karauwanci nake yi,
Toh waima tayaya mahaifiyata tana min addu'a dare da ranah ace addu'arta baza tayi tasiri a akaina ba, kawai nafi yarda da cewa ni d'in bani jin magana amma tawajen aikata zina zan karema Mahaifiyata wannan mutuncin, dan mijin Aure na yayi mata kallan mutunci,
Jan numfashi UMMAKATI tayi da cewa, "zanyi k'ok'ari sosai wajen ganin na zama kamarki, kuma insha Allah zan dena bama maza kaina, dan gaskiya ne idan naci gaba a haka ba makawa bazan kaima mijin Aure na abin kirki ba, yanxu dai yunwa nake ji dan ban tsaya na karya a hotel d'in ba, bara naje na dafa indomie da kwai ko naji qarfin jikina.
"Owkie, ki dafa dani dan nayi fad'a da Suwaiba,
yanxu," wannan yasa bazanci abincin gidan ba,
"Toh shikenan bara na dafa mana, UMMAKATI tafad'i da tafi ta nufi kitchen d'insu.
Nan RAHMA ta baje kan gadan nata tashiga tunanin ABDUL, k'amshinsa ya tsaya mata arai, tana lokacin data rungumesa ta baya ba qaramin dad'i taji ba, kowane lungu da sak'o na jikinsa qamshinsa ne ke fitta, gaskiya koma waye shi ya had'u, yana da tsafta da aji, ga muryarsa me sanyi, saidaifa yana da saurin hannu, bazata tab'a manta marikan da dinga dirka mata ba, "Harfa sau biyu ya maran, wallahi Allah ya qara had'ani dashi ba abinda zai hanani ramawa, Ta faɗi hakan a bayyane batare da tasan ta fad'i a bayyanan ba,
By AUNTYN LUV💋
`☆´-`☆´-
☆“˜•☆•
¸☆“☆ª☆_☾`☆•
❉ *.¸¸.*♠*.¸¸.*🙆🏻♂*.¸¸*❆ *.¸¸.*⚫.¸¸.*♠
☆
*TANTIRANCI KO KARUWANCI*☆
*.¸¸.*♠ *.¸¸*❆ ¸¸.*⚫¸*♠ *.¸¸.*🙆🏼♀*.¸¸*❆
`☆´-`☆´-
☆“˜•☆•
¸☆“☆ª☆_☾`☆•🤱🏻
{Fad'i alkairi ko kayi shuru)🤫
A true life story
*Follow me on Wattpad @rahamanalele*
Labari da rubutawa zuwa ga tsarawa.. ☾•Rahma Muh'md Rufa'i Nalele..☆
https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R
” بسم الله الرحمن الرحيم
Page 11
Suko su ABDUL gari na Wayewa suka hau shirin barin garin na jos, wanda sukazo garin dan shi ya nuna buqatarsa nasan harka dasu, har yana nuna musu zai iya biyansu fiye da yanda ogansu wanda ya turasu wajensa yake biyansu,
Saidai baisan yaran suna da wayo me yawa ba, hakan yasa sukace mai ya tintib'i ogan nasu idan ya amince su dinga harka dashi zasuyi dashi sam basu da matsala da hakan, yace muku zai tintib'eshin...
Bayan sun iso garin Nasu na kaduna kallan AMEER ABDUL yayi da cewa. "Duniya ta cika da rashin gaskiya, ka duba ogammu ya yarda da wannan mutumin amma yana san ya saye dan mu bijire masa mu koma aiki dashi.
AMEER yace "Bar banza mana, ya d'auka mu yara ne, san kud'in kawai mukasa a gaba bama duba mutuntuka.
ABDUL yace "Na yanke shawarar gobe kawai mu antaya garin na Lagos mu aiwatar masa da aikinsa koya kagani.
"Hakan yayi saimu fara shiri tun daga yau.
Da dare ne da misalin qarfe d'aya da rabi na dare mijin Salisu ZAINAB ya dawo gida a d'an bige, da alama watace can wajen iskancin nasu ta b'ata masa rai, dan haka sai kawai yazo ya sauke akan ZAINAB d'in....
Tana kwance har bacci ya fara kamata kasancewar yau kwata kwata bata jin daɗin jikinta, kawai basai yahauta da duka baji ba gani ba, wai dan iskanci tanaji yana sallama amma tayi biris dashi, toh dama gaskiya ZAINAB bata tab'a yin bacci idan har Salisu bai dawo ba, to da wannan yayi amfani yake ganin kamar yau iskanci take ji, shine yace bara ya sauke mata shi😀...
Sai d'auketa yake da mari yana kai mata naushi kamar ya had'u da saransa.
Ba qaramin wahala yake san bata a wannan dare ba, dan haka sai tayi yanda tayi ta ficce daga bedroom d'in, taci nasarar d'aukar wani hijabinta afalo tayi saurin bud'e kofa ta ficce.
Haka jiri na ibanta cikin daran nan haka tayo gidansu tana me addu'ar Allah yasa kartayi gamo da aljanu, dan tunda take gujema mijin nata bata tab'a guduwa cikin nisan dare haka ba.
ALLAH ya sota lokacin ABDUL suka dawo daga yawan nasu daran.
Saidai bai bugu sosai kamar yanda ya saba buguwa ba, saboda yayi alk'awarin denawa gabaki d'aya ahankali-ahankali, saboda ganin RAHMA da Yayi cikin wannan yanayi,
Dama Hajjiya Kakah tasakama y'an gidan dokar kar taji wani cikinsu ya kullema ABDUL ƙofar gida, wannan dalilin shiyasa ABDUL baya fargabar dawowa akowane lokaci, dan yasan k'ofar a bud'e take,
Ta kusa isowa kofar gidan nasu kenan saiga su ABDUL sun tsaida motarsu a kofar gidansu AMEER,
Nan suka fito da mamaki suna kallanta kallan tuhuma, AMEER ya bugu sosai dan haka saiya rufe baki da waro ido waje yace.. "Kai ka kai kai🤭, AUNTY ZAINAB me kikeyi acikin wannan daran haka, baki tsoran aljana takama ki😨, kut.. waya miki duka haka naga fuskarki ta kumbura,
Zainab ta kallesa dakyau ganin jini a rigarsa, shima ABDUL ga jinin ajikinsa tace, "yanaga jini a jikinku, meya faru daku.
Lumshe ido AMEER d'in dai yayi da bud'ewa yana layi irin na bugaggu yace da ita... "Al'ada muke😨 yana faɗin hakan sai kuma ya waro ido da maida kallansa ga ABDUL yaci gaba da cewa, aa ina nufin fyed'e mukayima mata,
Da sauri ZAINAB ta waro ido😳 nan take taji qarfi yazo mata, cikin tashin hankali tace "what,😳 fyeɗe...
Da sauri ABDUL ya make bakin AMEER d'in tare da waro nasa idan yana cewa, "kai😳.. Wallahi AUNTY qarya yake yi,
AMEER yayi dariya yace, "wallahi AUNTY qarya nake yi.
Maida kallanta tayi ga ABDUL tace, "toh gayamin, meya sameku da har jini ya tab'a jikinku,
Yace, "wasu ne sukayi fad'a harda yanke yanke shine muka rabasu,
Jan numfashi ZAINAB cikin rashin yarda dan ganin duk abuge suke ba mamaki ko duk qarya suka sharara mata, amma Allah ya kaimu gobe zata jisu ne ai, dan haka saita ce dasu "Allah ya shiryeku... Tana fad'in hakan ta shige gidan nasu, sanda ta b'ata lokaci tana bugama Hajjiya Kakah kofa kafin ta bud'e, tana ganin itace dama tasan abinda ya korota, dan haka nan tabata hanya ta wucce ciki.
ABDUL ko da bacci a idansa shiyasa daya kulle gidan nasu kawai shashinsa yayi baibi takan AUNTYN tasu..
Haka acikin wannan dare ma RAHMA da UMMAKATI a jos dai-dai wannan lokaci suma suka dawo daga yawan nasu daran, saidai basu shirya had'uwa da kowa ba kawai dai sunje sharholiyarsu ne, yawan rawa da shaye shaye, ba qaramin buguwa sukayi ba, wasu samarinsu ne suka kawosu har gida,
Dama iyayen RAHMA sunsan bazata dena dan furucin da tayi agaresu ba, amma suna mata kyakkyawan zaton zata dena, wannan yasa suka qara k'aimi cikin addu'o'in da suke mata,
Aikinsu kenan hana kansu bacci har sai sunji dawowarta,
Washe gari a Kaduna bayan ABDUL ya kintsa d'akinsa wanka yayi ya feshe jikinsa da turara ya nufi d'akin Hajjiya Kakah danya karya, anan yaga manyan iyayan nasu maza sun saka Hajjiya Kakah da ZAINAB a gaba suna jin abinda ZAINAB d'in take gaya musu kan abinda mijin nata yake mata,
Qare mata kallo ya shiga yi, gaskiya ba qarya ta bugu sosai dan ga shaida nan ta nuna kan fuskarta duk ya kunbora mata fuskar.
sosai ABDUL ya nutsu ya gane duk abinda take fad'i akan mijin nata, hmm ransa ya b'aci matuqa, sam baya san abinda zai tab'a mishi lafiyar kakarsa babansa ZAINAB d'in, danko mamansa babin takanta yake ba, wannan dalilin yasa yaci alwashin yau saiya koyama mijin nata hankali, badai ya iya dukan mata ba, to shi kuma ya iya dukan maza,
Dan haka shuru yayi abinsa ya jawo kwanan sha me d'auke da kunun gyaɗa gefe guda kuma ga wani fulas me d'auke da ƙosai me zafi, dan haka nan ya koma kan kujera ya hauci dan yasan nasa ne.
Lokaci lokaci sukan had'a ido da Babah Shehu sai kaga Baba Shehun yayi saurin kawar da kallan nasa yana me nuna alamun tsoro.
Murmushi kawai yake yi yana cewa aransa na saka maka tsorona Baba Shehu, dan haka sai haƙuri..
Bayan ya gamaci gidansu AMEER ya nufa ananya gansa d'akinsa yanata sharar bacci hankali kwance, AMEER yana kyau daidai nashi, yana da wani jiki wanda mata masu aji suke so wato kamar dai yanda ABDUL ya haɗe....
Kallan agogwan hannunsa ABDUL yayi yaga k'arfe takwas ne da minti arba'in da d'aya ne, dan ya d'akama AMEER d'in duka yana me cewa, Dallah tashi d'an iska, qilama ko sallar asuba bakayi ba.
Tashi AMEER yayi yana murza ido yace "Allah nayi, dan Dady ne yazo yasani agaba.
"Wallahi AMEER kama kanka fad'a yanxu sallar ce har sai anwani zo an saka a gaba"
"Kawai ka share abokina, yanxu dai ya take ne, har yanxu tafiyar tamu nanan ne kodai zamu bari sai gobe"
"Idan kana san abari sai goben ai sai'a bari, kaga nima nasamu damar cin uban mijin AUNTY ZAINAB dakyau"
Waro ido😳 AMEER yayi da wastsakewa sosai yace, "Yauwa kamar jiya naganta cikin dare kamar ma magana tashiga tsakanina da ita ko"
Murmushi ABDUL ya mai da cewa, "Kawai guy ka kwafsa abar batun kawai, nan AMEER ya mararrarcema ABDUL kan dan Allah ya gaya masa me yace ne a cikin daran,
Share shi da batun ABDUL yayi ya shiga kiran abokansu cikin wayarsa ya shaida masu yana san sunemo masa mijin AUNTYNSA ZAINAB aduk inda yake sukai masa shi d'akin huronsu, Nan suka amsa mai da ladabi kan yanxu ko zasu nemosa.
AMEER yace "Yau Salisu zaici ubansa" Murmushi ABDUL yayi da faɗin "kadai bari"
Sallama Abida tayi tashiga d'akin da tira abincin kayyawan AMEER ta dire a kan wani tebur anan cikin d'akin ta kalli ABDUL tace "Ya ABDUL ina kwana" "Lafiya my dear kin tashi lafiya"
"Lafiya lau, ga breakfast nan momy ta had'a harda kai tana tunanin ko zakaci.
"Wayyo momy data bari, dan yanxu na gama karyawa d'akin Hajjiya Kakah, yanxu zubama AMEER nasa kitafi da sauran. "Toh, tace mai cikin ladabi ta aiwatar da abinda yasatan.
Bayan tatafi ne AMEER ya kalli ABDUL yace, "kaga wani group da aka sakani ciki, waishi YARA MASU AJI, ya kai qarshe zancen nasa da nunama ABDUL d'in gaban wayar tasa dan ya gani.
ABDUL ya karb'i wayar da cewa, Nima d'azu naga ansani ciki, da alama y'an group d'in zasuyi surutu.
"Au, haba kana ciki ashe, AMEER ya fad'i yana me janyo abin Karin nasa.
Bashi wayar ABDUL da bashi amsa wajen cewa duba kaga, ni ina ganin ma yanxu fitta daga cikinsa, dan bani san group d'in da aka cika surutu da yawa.
Bayan AMEER yaga ABDUL na ciki ya gane wanda ya sasu cikin group d'in, wani abokin ABDUL ne wanda sukayi fad'a dashi kwanaki, amma yanxu sun shirya saidai basu cika harka dashi kamar da yanda suke ba, to shine fa yaketa wani shish-shige musu, sun gane yana san su dawo harka dashi kamar da ne, kuma ya nuna musu yayi nadama sosai, dan haka yanxu cema ABDUL AMEER yayi "kawai ɗan'uwa kashe, jeeboy ne ya bud'e group d'in yasamu, please karka fitta dan zaiga kamar basu kwata kwata bamu san wata wuld'a dashi ne,
Kan ABDUL ya bashi amsa sai kiran abokan nasu ya shigo wayar ABDUL d'in ya d'auka yana me cewa, "kun kai min shi d'akin ne.
Nan suka bashi tabbacin hakan, dan haka saiya kashe wayar da tashi yana cigaba da cewa , sunkai min shi AMEER bari naje namai yanda bazai qara tab'amin lafiyar my AUNTY ba,
Murmushi AMEER yayi kawai sai ABDUL d'in ya ficce.
Yana nan zaune kan wannan dai kujerar da aka d'aure Baba Shehu wancan lokacin to abinda aka masa shima haka aka masa, sun d'auresa tamau fuskar nan tashi a rufe ruf.
Nan Abdul ya bud'e mai fuskar tare da watsa mishi ruwan sanyi bayan ya farfad'o ya sakar mai murmushi da cewa, "Mema sunanka"
Da matuƙar tsoro Salisu ya haɗiye yawu yace "Me make faruwa ne, me zaka min, suwaye suka kawoni nan,
falla masa mari ABDUL yayi yace "Ya za'ayi ina tambayarka kaima kana tambayata.
_Na shiga uku ni Salisu, meya shigo dani hannun ABDUL D'AN KASADA, TANTIRI a y'an daba,_ Salisu ya fad'i hakan aransa da matuqar tashin hankali, afikiko cewa yayi, "Sunana Salisu"
"Toh miye dangantakar ka dani"
"Babu wata dangantaka, nidai nasan ina Auran ƙanwar Babarka ZAINAB"
"Masha Allah, " Zanso naji dalilin dayasa kake dukar Auntyna ZAINAB dahar kake bari take baro gidanka cikin dare batare da hakan ya dameka ba"
Gumi ne ya karyoma Salisu, tabbas yau me rabasa da ABDUL sai Allah, dan yafi kowa sanin TANTIRANCI irin nasa da AMEER tun yana zuwa wajen ZAINAB zance.
Cikin muryar rauni yace "A gaskiya bani da wani dailin dayake sawa nake aikata mata hakan"....
"Da gaske😀! ABDUL ya katseshi da fad'in hakan.
Shuru Salisu yamai, shima ABDUL d'in shurun yayi yana kallansa kawai.
Can sai Salisun yace "Kamin aikin gafara Wallahi na tuba bazan sake aikata mata hakan ba, idan na sake aikatawa kamin duk abinda zakamin.
Murmushi ABDUL yayi da cewa, "wato Salisu, giya da kwaya da kayan maye suna da matuqar dad'i ga wanda yake shansu, suna saka mutum cikin nishad'i da annushuwa adai dai lokacin daya shasu, bayan kana shansu kana had'awa da iskanci wanda kawai ganin damarka ne yake saka kake dukan ZAINAB badan ka bugu ba, kana dukanta ne dan jin daɗin kanka badan buguwa ba, kana dukanta ne dan cin zalinta ba dan buguwa ba.
Bazaka nunamin shaye shaye ba, saboda yanxu idan nagaya maka giyar da nake sha da kwayar da nake sha mamaki kasheka zaiyi, amma hakan baya sani dukan kowa sam babuma wani sinadarin da yake saka mutum duka acikin kayan maye, duk wanda kaga yana duka yayi dan qarin samun nishad'in kansa ne.
Ba abinda zai hanani hukunta yau kan dukan daka mata a daran jiya, ABDUL na fad'in hakan nan ya hau zane Salisu yana ihu saiya make masa baki.
Sanda ya tabbatar ya masa dukan gobe ka k'ara sannan yabar dukan nasa,
Sai ya zaro wata qaramar wuqa me kaifi ya kama kunnansa na dama zai gutsire masa kunnan aiko nan Salisu ya kwalla wata qara da salati yana masa magiyar karya gutsire masa kunnansa dan soyayyarsa da manzan Allah😂..
Jin ya ambaci manzan Allah saiya fasa gutsire masan amma sanda ya d'an tsagasa masa shi, nan take ko Salisu ya sume, ABDUL murmushin mugunta ya qara yi da yayyafa masa ruwa ya farfad'o da gumin azaba, nan ya dinga hawaye yana rokwarsa kan ya barsa haka, Wallahi yayi nadama ba kuma zai sake ba, dan Allah karya qara masa wani abun,
Kauda kallansa yayi daga kansa yace, "Idan na qara maka wani abu mutuwa zakayi ba suma ba, dan haka bazan qara maka komai ba, dan ina San ganin AUNTYNA cikin farin ciki, idanko na kasheka bazan yafema kaina ba,
Kaci sa'a zamuyi tafiya gobe, dan haka zan kunceka a goben, daba dan haka ba Wallahi sai kayi sati biyu ina baka shaqi iskar waje ba. Yana faɗin hakan ya kulle masa baki da ficcewa daga d'akin.
Anan jos ko haka su RAHMA ma suka tashi sukaga anjefasu cikin wannan group d'in da aka jefa su ABDUL. Sam basu san wanda ya bud'e group d'in ba, amma su k'awarsu Aliya itace tasasu,
Group d'in yazo da farin jini awajen RAHMA da UMMAKATI, musamman jama'ar cikin group d'in, duk wanda aka sashi ciki sanda yaji shauqin san group d'in,
Gabaki d'aya y'an group d'in basu wucce su saba'in ba, amma kaf ci babu wani meji acikinsu.
Duk marasa ji ne aka had'a cikin group d'in,
Wanda ya bud'e group d'in yayi qoqari sosai dan group d'in ya dace da mutunan da suke cikinsa.😂
"YARA MASU AJI. RAHMA ta fad'i cikin jin daɗin sunan group d'in,
Da san mutane da yawa acikin group d'in kuma duk masu aji ne irinsu.
Wannan dalilin yasa ta fantsama cikin group d'in tafara zuba hira kamar me, kan kace kwab'o nan Yawancin way'anda suke online acikin group d'in suka santa, wayanda ko dama sun Santa nan hira tafara aikinta, haka ma umma kati nan sukayi qawaye maza da mata,
Dama suna d'akinsu Rahma na y'an matan gidan ne UMMAKATI ta kalli RAHMA tace "Alama tanuna kinji dad'in group d'in nan. Murmushi RAHMA tayi da bata amsa tace, da farko danaga group d'in wallahi gabana ya fad'i, dana shiga cikinsa naga dake aciki ga kuma qawayenmu sai naji group d'in ya kwanta min arai, kuma ki lura yaran masu ajine cikin group d'in bakiga kowa ya sake ba.
UMMAKATI taja numfashi tace, " ammafa gaskiya naji wani iri a jikina kamar wani abu zai faru damu acikin group d'in"
"Ke dalla tafi can matsoraciya, ba wani abinda zai faru damu insha Allah" RAHMA tafad'i hakan da ajiye wayarta bayan ta kashe datan ta..
By AUNTYN LUV 💋
`☆´-`☆´-
☆“˜•☆•
¸☆“☆ª☆_☾`☆•
❉ *.¸¸.*♠*.¸¸.*🙆🏻♂*.¸¸*❆ *.¸¸.*⚫.¸¸.*♠
☆
*TANTIRANCI KO KARUWANCI*☆
*.¸¸.*♠ *.¸¸*❆ ¸¸.*⚫¸*♠ *.¸¸.*🙆🏼♀*.¸¸*❆
`☆´-`☆´-
☆“˜•☆•
¸☆“☆ª☆_☾`☆•🤱🏻
{Fad'i alkairi ko kayi shuru)🤫
A true life story
*Follow me on Wattpad @rahamanalele*
Labari da rubutawa zuwa ga tsarawa.. ☾•Rahma Muh'md Rufa'i Nalele..☆
https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R
” بسم الله الرحمن الرحيم
Page 12
*Read more 12 nayi muku danna wanke kaina agareku y'an hannuna*😂
Jan numfashi UMMAKATI tayi da cewa, "To shike nan Allah ya dafa mana", "Amiin, RAHMA tace mata
Direct gidansu ABDUL yayi, anan yaga ZAINAB ta ritsashi d'akin Hajjiya Kakah tana me tambayarsa meya faru dasu jiya taga jini ajikinsu, kodai da gaske fyaɗen sukama mata kamar yanda AMEER yace.
Kallanta ABDUL yayi da ɗan murmushi yace, "Allah da gaske ba fyaɗe mukama mata ba, wasu ne suke fad'a muka rabasu, dake faɗan na wuk'ane shiyasa kikaga jini ajikinmu, kuma Aunty kinsan duk rashin jina bana kula mata, dan Allah kiyarda da abin dana gaya miki
"Owkie, na fahimta, amma dan Allah kudena faɗace-faɗacen nan da yawan dare, wallahi bashi da amfani dan Allah kuma kanku fad'a"
"Yayi Auntyna, insha zamu rage, am yaushe zaki koma gidanki"
"Abdul nagaji da iskancin Salisu bazan iya da abinda yake min ba, nina hak'ura da Auran dashi, kana dai gani har yanxu bai biyoni ba, inda dane iyanxu yana gidan nan tun safe zaka gansa yazo ba Hajjiya Kakah haƙuri, amma yau dake yana jin iskanci kaga har yanxu baizo ba,
"Aunty gaya min har yanxu kina san mijinki, Ya katseta da faɗin hakan
Cikin wani hali tayi shuru tana tunani, can tace "Ina sanshi har yanxu ABDUL, ina san rayuwa dashi, Amman wannan shine zai kasance karo na qarshe dazan qara zuwa gida saboda matsalata dashi.
Damma su Babah Shehu sun qara bani hak'uri ne kan na koma idan yazo dan suga kozai canja halinsa, banda hakan nina cema Hajjiya Kakah kawai suraba Auran d'azu.
"Toh kiyi hak'uri insha Allah zai canja miki, ina tabbatar miki da hakan, dan yana sanki, zabai so rabuwa dake ba, musamman idan yaji abinda kikacema Hajjiya Kakah d'azun.
"Toh Allah yasa, yanzu ina zakaje, "kawai na dawo gida ne.
"Hakan yayi"
"Yauwa dama ina san nagaya miki zamu Lagos gobe nida AMEER, bazamu wucce sati biyu ba zamu dawo"
"Lagos kuma, ABDUL me zakuje kuyi a Lagos" "AUNTY wani aiki oganmu yasamu, ba wani dad'ewa zamuyi ba" "Wai waye wannan ogan naku ne dazai dinga turaku gari gari kuma wane aiki kuke masa" ZAINAB ta tambayesa cike dasan jin abinda zaice mata
Tashi yayi yana bata amsa da, "Bawani aiki bane Auntyna, kawai ki share basai kinji ba" "Ban gane in share ba, idan wani mugun abun yake saku kuyi fa, ai kaga na nuna muku illarsa.
"Toh nidai bazan gaya miki ba, dan ba wani mugun abun bane, kuma ma aunty yanzufa na girma ba wani abu dazan aikata wanda za'a kirasa da mugun abu.
"Amma ABDUL kana....
"Amma ABDUL me, dan Allah karkice min baki san naje Lagos d'in nan, dan ina san zuwa, musamman ma da ban tab'a zuwa ba, ABDUL yayi saurin katseta da faɗin hakan.
Shuru tayi mai ganin hakan sai ya sulale yabar mata d'akin, dan yasan halinta sarai bata san yawan yawan nan da ogansu yake turasuyi.
Sanda yayi sallar warha sannan ya baje kan katifarsa ya bud'e data yana san ganin me duniyar yanar gizan take ciki...
Sannu a hankali yake bin hirarrakin da y'an group d'in nan da aka sashi sukayi, "kai amma wannan yarinyar tacika surutu, ka duba yanda taketa sakar zance kamar wata aku....
"Kai dawa kakeyin magana, AMEER ya katse shi da faɗin hakan yana me kwanciya shima akan katifar tashi. Murmushi ABDUL yayi dace mai, "Sam banyi tsammanin abayyane nake zancen ba, hirarrakin da y'an group d'in nan sukayi nake gani...
"Akwai wata RAHEEMAT da UMMAKATI sunfiya surutu kai musamman ma RAHEEMAT d'in.. AMEER ya qara katseshi da faɗin hakan
ABDUL yace "eh, naga tafi kowa magana, wannan da alama idan tabar group d'in surutun sauran zai ragu,
AMEER yace "kwarai da gaske, yanxu dama nazo na gaya maka ne munyi da oga kan jirgi zamubi gobe qarfe bakwai, dan haka saika tashi muje muyi ciki cikin samu.
Sun samu yanda suke so dan haka qarfe taran dare ABDUL yaje ya saki Salisu, amma kafin ya sake shi sanda yaja mishi kunne Wallahi ya dawo yasamu labarin ya qara dakar masa Aunty saiya mishi abinda yafi hakan, Salisu najin hakan yace ya yarda, nan ABDUL ya make qeyarsa nan take ko ya sume, saiya kira abokansa kan su fidda shi su kaisa can gidansu,
Haka ko akayi dan gidansu Salisun suka kaisa suna masu cewa wai ganinsa sukayi a yashe kan hanya, suna gaya muku hakan suka barsu da d'ansu.
Nanko ZAINAB sai zaman jiransa takeyi, can dataga baida niyar zuwa saita kunne idanta bacci yayi awan gaba da ita.
Su RAHMA ko awannan ranah bikin wata qawarsu Salima sukaje, biki ne na yara yaran mata irinsu, yaran da suka amsa sunansu wayayyu, duk wanda kagan shi a wannan biki toh ka tabbatar wani ne TANTIRI ko watace MARA JI.
Bad'ala dai iri iri anyi awajen fatyn nan, dan maza da mata ne suka haɗe suka cure waje guda aketa dirkar rawa, ba sallah ba salati sai tashin muryar Arna kakeji tana rera musu waqa, RAHMA ta iya rawa ba lefi shiyasa mazajen wajen sukefi liqe mata wajen rawan.
Basu suka dawo gida ba sai wajen qarfe goma da rabi na dare
Duk sai warin giya sukeyi, hakan yasa RAHMA tayi wanka agidansu UMMAKATI tasaka wani kayan kana tayi gidansu.
Girgiza kai maman tayi dacewa "Allah ya shiryamin ke kidena yawace yawacen nan da kikeyi, Wani Yayanta dake tare da maman yace "Ameen,
RAHMA da sanyin jiki daje ta shige jikin maman nata tace, "Wallahi mama zan dena dan Allah kayi hak'uri kinji, tace " Ya zanyi dake RAHEEMAT, ai tsakanina dake addu'a ce, Allah Yayi miki albarka, dan dadai hankali na bazan jefeki da mugayan maganganu wanda zasu qara fanɗarar min dake ba.
Washe gari Daqer da siɗin goshi Hajjiya Kakah ta harda da tafiyar dasu ABDUL zasuyi, dan kuka tasama ABDUL tana cewa saiya gaya mata aikin da ogansun yake turasu yi gari gari, shidai bai gaya mata ba amma Yayi qoqari sosai wajen shawo kanta, nan tayi musu fatan alkairi suka antaya airport sai garin abuja, anan suka qara yankar tikiti zuwa kudu Lagos,
Bayan tafiyar su ABDUL iyayen Salisu ne sukazo bikon ZAINAB suna masu gaya musu wai Salisun baya jin daɗi ne, wani hatsabibi aka samu yayi mai dukan tsiya shekaran jiya😂 yanxu haka ma yana gida ana jinyarsa.
Jin hakan sai yasa hankalin Hajjiya Kakah ya tashi ita da ZAINAB nan suka bar batun wani biko tace da ZAINAB tashirya ta koma d'akinta tayi jinyar mijinta.
Haka ko akayi, haka ZAINAB ta koma gidan aka kawo mata Salisun ba lefi jikin nasa da d'an sauqi,
Amma tayi mamakin yanda yana cikin ciwo amma yake wani janta da hira har yana bata hak'uri kan bazai sake aikata mata abinda yake aikata mata ba, dan Allah tayafe mai.
ZAINAB taji dad'i sosai hakan yasa tayafe mai suka rungume juna cikin so da qauna,
******
Su ABDUL sun sauka lafiya anan sukaga wasu sunzo daukarsu, ba lefi dan hotel d'in da suka saukesu ya had'u irin sosai d'in nan, anan bayan sunci abinci sunyi sallah hutawa suka hau yi.
Akalla sanda suka kai kwana uku kafin wani ya basu hodar dafara yimusu jagora zuwa ga waƴanda zasu bama.
Idan dai hodar iblis tashiga hannun ABDUL da AMEER duk iya kwafkwafinka baka isa ka ganeta a jikinsu ba.
Saboda kayan da suke sawa na musamman ne ajikin nasu yayin harkar, dan idan hodar nan takai akwati uku irin wanda ake saka hodar aciki tsaf suke sakawa jikin wannan kayan nasu.
Wannan dalilin yasa sam ogansu baya kawo matsala awajensu.
Haka wannan ɗan jagoran ya dinga sadasu da manya manyan sheɗanu a harkar suna masu basu hodar, su kansu duk da sun d'auki shekaru a harkar sanda salan su ABDUL ya birgesu, suka dinga mamakin yanda suke Yawo da hodar a jikinsu amma babu wanda zai kawo cewa akwai hodar jikinsu bare ayi ram dasu.
Su ABDUL suna san kwarewa a harkar, dan haka bayan sun gama rabama mutanan ogan nasu hodar sai suka shige jikin sheɗanun nan suka nuna musu suna san qara kwarewa a harkar kafin su tafi, jin hakan ko yama waƴannan dad'i dan haka nan suka d'orasu akan tasu harkar,
Gaskiya da wahala dan nasu ba irin nasu ABDUL bane, dan ankusa kamasu lokacin da zasu kaima wani babban mutum da irin salan ba mutana sai kuma Allah ya kare. Nan suka qara tabbatar da cewa Nash salan daban yake dana kowa.
Sun dai yanke shawarar wata biyu zasuyi su dawo gida.
Ayanxu watansu d'aya a garin na Lagos, Toh suna harkar aikin nasu suna kuma yawan daran nasu na bin club, gaskiya club a garin Lagos ba qaramin yawa bane dasu, gasu gurare ne masu kyau sosai da tsari, ba lefi su ABDUL suna jin dad'in garin sosai, dan sun qara samun wayewa fatarsu ta qara gogewa, dan wahalar da suke sha bata yawo arana bace,
AMEER dolensa yabar batu akan harka da mata, dan matan nan ba irin na arewa bane, haka y'an garin suka gaya masa, suna masu tabbatar masa da cewa zai iya d'aukar cuta idan har bai kula ba, dan matan ba gaya masa zasuyi ba, ABDUL najin hakan ya kalli AMEER d'in da cewa, saika hak'uri mukoma gida ka d'ora aya tunda lamarin ya zamar maka jiki.....
______________________________
Suna dai hira cikin wannan group d'in amma ABDUL sama sama yake magana ciki, kuma shi yana magana da maza y'an uwansa ne, sam wata magana bata tab'a had'asa da wata mace a group d'in ba, amma kunga AMEER har yayi sabo da RAHMA da UMMAKATI hira suke kamar sunsan juna....
Kaf RAHMA a y'an group d'in nan ba way'anda bata sani ba, tasan way'anda sufa fiye magana aciki, tasan way'anda basa magana, tasan mazan da suke magana idan sunga mata na hira, tasan mazan da suke magana idan sukaga maza y'an uwansu na hira, to tagane AMEER yana san hira da mata, gashi ya iya hirar dasu, sai kuma ABDUL, tagane sam mata basa gabansa, dan bata tab'a ganin ranar da Magana tashiga tsakaninsa da wata mace cikin group d'in ba, ta lura ko maganar zaiyi yanayi ne da maza y'an uwansa, gashi matan way'anda suka sanshi y'an garin nasu na kaduna sai suta masa shishshigi wajen d'ura maganarsu akan maganar da yakeyi da mazan y'an uwansa, sam bai tab'a ba wata mace amsa ba, alamar dai abayyane take, kaf y'an group d'in Suna masa kallan me aji, musamman idan sukaga yanda wasunsu suke shige masa.
RAHMA faɗi take aranta gaskiya mutumin nan yanaji da kansa, ka duba yanda ake binsa yana wani share mutane, su kuma dan tsabar zubar da aji ahakan suke qara shige masa, RAHMA takanja tsaki cikin b'acin rai aduk sanda taga ana binsa yana wani share mutane....
******
Yau da misalin qarfe goma da rabi na safe RAHMA tabud'e datanta inda taci karo da wani sak'o da aka tura mata ta prvt anan WhatsApp, nan ko ta share ring groups da dama, group d'in YARA MASU AJEEY yana d'aya daga cikin way'anda taturama,
Toh alokacin ABDUL yana online, dan haka akan idansa taturo da sakwan, nan yabi yana karantawa, irin sakwan nan ne da ake alaqanta manzan Allah dashi ace idan baka tura ma group kaza ba wani abu zai faru dakai, ko kuma ace wani ya fad'i maganar banza akan manzan Allah ga yanda abin ya kasance dashi, ko kuma ga wata tataka qur'ani tana me nunawa musulmai dan ransu ya b'aci, sam ABDUL baya bin takan way'annan zancikan, dan haka karan farko maganarsa da wata mace a online bama a cikin wannan d'in ba yayima RAHMA magana akan wannan sakwan data turo wajen cewa, _Bai dace kudinga irin wannan post d'in ba RAHMAT, ya dace da'aka turo miki kijama wanda ya turo miki kunne wajen karya qara turo miki, amma bawai yasaki yad'a abinda aka b'ata manzan Allah akansa ba, ya dace kima karatun kyakkyawar fahimta kigane kawai b'atanci ne irin na yahudawa dan kawai sudinga amfani damu wajen yad'a manufofinsu, na gaya miki gaskiya ne dan bana san kiraqa shere ring ma kowa._
Shuru RAHMA tayi bayan ta gama karanta abinda yace mata, azahirin gaskiya sai yanxu tagane turawan bashi da amfani, har zata sharesa sai kuma tace mai _Naji nagode_
Ahankali Ahankali ABDUL da RAHMA suke d'an magana, can da tafiya tayi nisa sai suka zama kamar abokai, dan idan RAHMA taga ABDUL na hira da maza y'an uwansa shiga takeyi ayi hirar da ita, haka shima idan yaga tana hira da abokan nasa yana shiga ayi hirar dashi sab'anin da da'idan yaga tana hira dasu baya shiga
Yau saura kwana biyu su ABDUL subar garin na Lagos, dan sun qara wata d'aya akan wata biyun da sukayi niya,
Toh yau d'in ta kasance Asabar da misalin qarfe goma sha d'aya, ABDUL ne da abokansa suke hira cikin group d'in harda RAHMA da UMMAKATI da qawarsu Yahanasu, k'arfin hirar dai akan Yahanasun ce da wani surayinta dake nan cikin group d'in,
Toh ana wasa ne irin na wasa😀 Amma mezai faru😳, dama su takwas ne suke hirar, sai wanda ya bud'e group d'in yace "Yau ranar masoyace ta duk duniya, dan haka Dan Allah mu da muke online ayanxu mud'an tab'a wasan soyayya, mukuma tura group group dan muji comments d'in da za'ayi kan suwaye sukafi iya soyayya acikinmu, dan haka kowa ya zab'i budurwarsa acikinmu muyu wasan soyayyar yanzu dan a tantance,
UMMAKATI tace, "kaji ka da wani zance, idan mukayi hakan miye fa'idarka,
Kanya bata amsa sai RAHMA tace, "koma dai miye fa'idarsa ai wasa ne, miye dan munyi wasan soyayya cikin group, nidai na tabbatar koda waye aka had'ani sai mun cinyeku a soyayya🙈 ta fad'i hakan da kai qarshen zancenta da saka wannan birin me rufe fuska🙈👈🏻
Kowa dariya yama zancen nata,😀 Yahanasu qawarsu tace "um um RAHMA bar cika baki fa😀,
Tace "Allah da gaske nake kuma a fara a gani"
AMEER yace "toni na zab'i Yahanasu, sai Wanda ya bud'e group d'in yace, "ni kuma na zab'i UMMAKATI, ABDUL yayi murmushi duk da cewar gabansa ya fad'a amma haka ya share yace, "Nina zaɓi RAHEEMAT,
sai sauran biyun kasancewarsu dukkansu maza sai sukace, "Toh mune y'an sa ido👀 masu tantancewa, dan haka a kafta,
Nan wanda ya bud'e group d'in yace da UMMAKATI, "tun ranar dana fara ganinki ban qara samun kwanciyar hankali a rayuwata ba, wato UMMAKATI kin tafi da zuciyata, kin b'ata tunanin kwakwalwata, jina nake tamkar wanda bashi da hankaki, na kasa nutsuwa, na kasa samun kwanciyar hankali dan Allah kice kina sona kin yarda dani a soyayya...
Jan numfashi UMMAKATI tayi da kallan RAHMA dake suna d'akin UMMAKATIN ne dama itama RAHMAN kallanta tayi nan take suka kwashe da dariya😆, RAHMA tace, "Dalla kibashi amsa.
Ahankali ko UMMAKATI tahau bashi amsa wajen cewa, "Hak'ik'a nima zuciyata bata dare da nutsuwa tun ranar dana had'a ido dakai, jeboy ina sanka ina qaunarka da fatan zamu gina rayuwarmu rayuwa irinta cikakkun masoya....
Sai AMEER ya karb'a yana cema Yahanasu, "wato matata ayanda nake samun farin ciki agunki bana tananin akwai wani wanda yake samun irin hakan agun matarsa, gaskiya babu qarya ina MASEEFAR sanki da qaunarki, dake kad'ai zan iya rayuwa ina fatan har a gidan aljanna ki kasance matata,
Murmushi Yahanasu tayi da cewa "Nima haka Abban Anisa, ina fatan qara zama matarka a gidan aljanna, ina sanka mijina ina qaunarka dan kaci gaba daji dani har bayan qarshen rayuwa bama qarshenta,
"Zanji dake matata nidai kawai kiyarda dani, "nayarda dakai mijina...
Ayanzu ABDUL da RAHMA ne suka rage aji irin nasu salan,
Sam ABDUL baisan me zaice ba, saboda shi bai iya soyayya ba, dan haka Ahankali ya kalli AMEER dake gefansa yana mai murmushin mugunta dan yasan indai ci akan soyayya to ABDUL dai bazai ci bah, dan bai iyata ba, baima san ya ake yinta,
Bayan ya gama fuskantar murmushin mugunta AMEER yake masa sai kawai yayi qaramin post ga RAHMA kamar haka, yace da ita "Kin tabbatar kina sona.
RAHMA taja numfashi tace dashi "Sosai ma kuwa, ina sanka ABDUL
Yace "toh muyi Aure mana.😊
RAHMA tace "zanyi farin ciki da hakan,
Yace "toh waye waliyinki
Tace "Ni kowama ya zama waniyi na.
Yace "kin amince, tace "kwarai ma kuwa na amince,
ABDUL yace to turomin da A/C number naki naturo miki da sadaki yazu.
Nan gaban RAHMA ya fad'i ta kalli UMMAKATI, itama UMMAKATIN kallanta takeyi ad'an tsorace irin me yake shirin faruwa ne😳.
Nan dai RAHMA ta tura masa da account number nata.
Shuru group d'in ya d'auka suna masu kallan ikwan Allah, nan RAHMA taga sakwan shigowar kud'i wayarta.
"Dubu shittin😳.. RAHMA ta bad'a a bayyane tana me kallan UMMAKATI daci gaba da cewa, sadakina ya turan da dubu sittin..
UMMAKATI ta waro ido tace, "Harya turo miki ne.
RAHMA tace "gashi ko nagaya miki.
"Owkie, ai sai kice masa ya shigo kuci gaba muga k'arshen naku salan.
RAHMA tace da ABDUL "My dear naga sak'on sadakina dubu sittin ya shigo yanxu. Anya baiyi yawa ba, kasanfa albarkar Aure suke buqata.
Murmushi ABDUL yayi da d'agama AMEER gira wanda ya saki baki yana kallan ABDUL d'in da qurama wayarsa ido yana san ganin ikwan Allah,
ABDUL yace... "Haba my Baby, sam baiyi yawa ba, Yanxu dai acikin Suleiman da Usman masu saka ido cikin wannan wasan namu wa kika zab'a ya zama waliyinki.
RAHMA tace "Na zaɓi Usman daya zama waliyina saboda nasan shi anan bayan layinmu yake.
ABDUL yace "gud hakan Yayi, nima na zab'i Suleiman dan shima yaran unguwarmu ne, yanxu sai kowa ya shaida dan yanxu za'a d'aura Auran namu..
Nan AMEER da jeeboy wanda ya bud'e group d'in suka ce sune shedu amma a jira sauran y'an group d'in suzo sai'a d'aura Auran,
ABDUL yace aa kawai a d'aura in yaso in sukazo saga komai..
Nan kamar wasa fa😳 suka d'aura Auran ABDUL da RAHMA, kowa ya shaida da auran. Kan kace kwabo nan su RAHMA suka cinye wasan.
Waliyansu suka basu making da yawa.
Yahanasu tace "RAHMA kin cika baki gashi salan naku ya cinye namu,
Yanzu wasa ya qare sai mujira comment d'in y'an group..
Aiko y'an group d'in suna zuwa nan suka dinga comments akan Auran nasu.
Wata acikinsu ana cemata Ashanty tawaro ido😳 a tsorace ganin abinda ya faru a group d'in tace, "Wallahi Auran gaske kukayi ABDUL da RAHMA kuje ku tambayi malamai na tabbatar zasu tabbatar muku da hakan, lallema, meya kaiku wannan kwamacalar😀.
Dake RAHMA tana online har lokaci nan tawaro ido itama waje tace, "What.. Aure na a group😨, ke dalla dakata malama wasa muke fah😀,
Ashanty tace "Wallahi bazan rantse miki a banza ba Wallahi tallahi kuje wajen malamai ku tambayesu na tabbatar ke matar ABDUL ce yanzu😂
Tashi RAHMA tayi a rikice cikin tashin hankali takalli UMMAKATI tace, "Tunani yana san hautsinewa, kwakwalwata tana san rikicewa, wai me Ashanty take gaya min ne.😨
UMMAKATI taja numfashi tace "abun abin a duba ne RAHEEMAT, nima yanxu hankalina ya tashi dajin abinda tace,
"Aurena ni RAHMA a group😨 RAHMA ta fad'i hakan cikin san fashewa da kuka, dan Wallahi ta tsorata sosai.
Nan ta d'auki gyalanta sai gidansu, a tsakar gidan taga mamanta na murja taliya, nan tazube ajikinta tana cewa, "Mama nashiga uku🙆🏼♀ Wallahi wasa muke yi bada gaske bane, dan Allah ki gaya min kice min wasa ne.
Maman ta kalleta da damuwa tace, "menene ya faru. Cikin kuka hannu aka RAHMA tace da itace. Aure aka d'aura min yanxu a cikin group kuma Wallahi DAGA WASA muka faru ni da shi, amma yanzu kinji wata Ashaty tace Wallahi Auran gaske mukayi, wai ba'a wasa da Aure....
Nan maman tatashi da zareta daga jikinta tadafe qirji tace "RAHEEMAT Aure ba abin wasa bane, tabbas yarinyar tafad'a muku gaskiya, shi kenan sai yazo ya d'auke ki ai kun kyauta... Maman takai qarshen zancen nata da murmushin yaqe.
Nan cikin RAHMA yad'au k'ogi ta qara d'ora hannu aka🙆🏼♀ ta kwalla k'ara tare da rushewa da kuka wiwi🤣 tana cewa "Na shiga uku an d'aura Aure na a group.....
Nanko take jama'ar gidan suka firfito maza da matan suna masu zaro ido da cewa me sukaji tana cewa, nan maman RAHMAN ta kora musu bayani kamar yanda tafad'a mata, basai kishiyoyin maman nata suka dafe qirji tare da qafa gwalalo ido har suna had'a baki wajen cewa "Munshiga uku😳, Aure, kuma Auran RAHMAN koba natan ba,
Mamanta tatabbatar musu da natan dai take nufi, nan suka hau salati suka wari rikice ba shiri ko waccen su tayi d'akinta tana cije yatsa, fad'i suke aransu tayaya hakan ta kasance, bayan bokansu yayi musu aiki akan ita da Aure har abada, idanko tayi to asirin da suka mata zai koma kan y'ay'ansu mata.
Nan suka dinga safa da marwa Suna kai kawo alamar ya zasuyi...
Hmmm, ita dai RAHMA in banda kuka ba abinda takeyi, duk ƴan uwan nata mata sakata suka agaba suna kallanta, mazan ko waƴanda suke gida girgiza kai sukayi da cewa "Allah shi qara.. Suna faɗin hakan suka koma kan abubuwan da sukeyi.
Hawaye dumu dumu a fuskar RAHMA ta lalubo numbar ABDUL danta kirasa...
Suko anan AMEER ne ya rikice dan nan take yahau kiraye kirayen numbers d'in mutane yana tambayarsu shin ana yin auran wasa🙁
Kowa tabbatar mishi yakeyi da cewa ba'ayin auran wasa, dan addinin musuluncin ba abin wasa bane..
ABDUL na jinsa sam bai wani damu ba. Saki ne dai idan tace ya saketa zai iya sakin nata dan dama ai shi mata bawai sun damesa bane🙅🏻♂.
Suna cikin hakan saiga kiran RAHMA ya shigo wayar ABDUL, ba suna dan dama bawai Yayi seven num natan bane.
Sam bai zaci ita bace ya d'auka, saijinta yayi cikin kuka tana cewa, "Haba ABDUL ya zakamin haka, kasan ba'a wasa da Aure kace muyi..... Ta qarashe da qara volume d'in kukanta.
Shuru ABDUL yayi, da farko dai kukan nata ya taɓa zuciyarsa, na biyu yana san tuno a inda yasan muryar tata, abu na uku bai taɓa jin wani yanayi agame da y'a mace ba kamar yanda yaji yanxu, ji yayi yana san taci gaba da magana, sannan kuma baya san taci gaba da kukan da takeyi,
Cikin sanyin murya yace, "Ina magana da RAHMA ne" afusace tace mai "Idan bada ita kike magana ba dawa kuke tsammanin kana magana adai-dai wannan lokacin, kawai so nake naji kace ka sakeni saki uku.....
"Da gaske...
Ya katseta da faɗin hakan dan yanzu ya gane muryarta sosai, itace dai yarinyar nan daya temaka a garin jos, tabbas kunnansa bazai manta da muryarta ba, Allah ya temaketa tamai rashin kunya ya nuna mata kuranta, dan haka cigaba yayi da cewa, idan naƙi sakin naki me zakiyi.
"Nemoka zanyi aduk inda kake, na cakume maka wiya wallahi ko kafi waye qoqari sai furta kalmar saki agareni.
"Yayi malama✋🏻 hakan yayi sosai👌🏻. Nayi miki alƙawarin nine zan kawo miki kaina har kofar gudanku danki aiwatar da abinda kikace agareni, idan kuma bakiyi ba, ni kuma zan kama hannunki nasaki amota na kawoki garinmu matsayin matar Aure nah?...
"Kayi kaɗan, Wallahi ƙaryarka tasha ƙarya, RAHMA ta katseshi da faɗin hakan tame tashi daga inda tare daci gaba da cewa, kana san ka nunamin kai TANTIRI ko, to bari kaji wallahi nafika TANTIRANCI, idan ka isa kai d'an halak ne kazo ƙofar gidan namu ba abinda zai hanani tabbatar maka da abinda nace maka, Ina garin Jos layin d'an k'arfalla, duk wanda ka tambaya wacece RAHEEMAT zai kawoka har kofar gidammu.
"Toh shi kenan, insha Allah nayi miki Alk'awarin zanzo, zamu bar garin Lagos yau idan muka koma garinmu Kaduna nayi miki alqawari kwana d'aya zanyi a kadunan na duro garin naku, wallahi sai naga qarshen TANTIRANCIN KI...
"Kodai naga qarshen naka ba, Allah ya kawoka kasan dawa kike wannan maganar, tana faɗin hakan ta kashe wayarta da kallan mahaifiyarta ta qara rushewa da kuka, tana meci gaba da cewa "nidai na shiga uku wallahi da wasa muka faru dashi😭.
Murmushi mahaifiyar tata tayi mata dayin d'akinta tana me neman number na mahaifinta tagaya masa abinda yake faruwa,
Itako RAHMA d'akinsu ta shige cikin tashin hankali, dan taji a jikinta ABDUL ya bambanta da samarin da take harka dasu, sam bataji wani alamun tashin hankali daga garesa ba, saima magana da yake mata cikin wani izza kamar wani tantiri, toh wallahi duk TANTIRANCINSA tafisa, yazo zaisha mamakinta...
ABDUL ajiye wayarsa yayi gefe yana murmushi, wallahi zai koyama yarinyar nan hankali, Allah ya kaisa gareta lafiya...
Kallansa kawai AMEER yayi ganin murmushi ma yakeyi, irin na wani abun da yake damunsa.....
Ina jiran comments
Muje zuwa y'an hannuna👐🏻. Karfa ku manta wannan labarin true life story ne, ku biyoni kuji yanda labarin zai kasance, shin da gaske Suna da Aure koko babu shi, By AUNTYN LUV 💋takuce....
`☆´-`☆´-
☆“˜•☆•
¸☆“☆ª☆_☾`☆•
❉ *.¸¸.*♠*.¸¸.*🙆🏻♂*.¸¸*❆ *.¸¸.*⚫.¸¸.*♠
☆
*TANTIRANCI KO KARUWANCI*☆
*.¸¸.*♠ *.¸¸*❆ ¸¸.*⚫¸*♠ *.¸¸.*🙆🏼♀*.¸¸*❆
`☆´-`☆´-
☆“˜•☆•
¸☆“☆ª☆_☾`☆•🤱🏻
{Fad'i alkairi ko kayi shuru)🤫
A true life story
*Follow me on Wattpad @rahamanalele*
Labari da rubutawa zuwa ga tsarawa.. ☾•Rahma Muh'md Rufa'i Nalele..☆
https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R
” بسم الله الرحمن الرحيم
Page 13
Sai yace dashi, "ABDUL ya dace muje mu tambayi malamai kan wannan batu, wallahi duk hankalina ya tashi"
"Hankalinka ya kwanta d'an uwa, Wallahi sam banji wani damuwa araina ba, ina san kaima kacire damuwar aranka" ABDUL ya katse AMEER da faɗin hakan.
Sai AMEER d'in yaja numfashi yace, "Yanxu ayau zasu bar garin nan kenan" "Eh, kawai mutafi yau d'in, dama ai ba jiran wani abu muke ba" Abdul ya qara katse shi wajen qara bashi amsa.
Haka ko akayi dan awannan lokacin suka had'a kayansu sukayi airport dan barin garin na Lagos...
_______
Sallah kawai RAHMA takeyi awannan ranah bacin haka ba wani abu da takeyi sai aikin tunani da kuka.
UMMAKATI tayi mata lallashin duniyar nan amma ko kallanta batayi ba, daga qarshe ma barinma UMMAKATIN tayi gidan nasu tayi gidansu UMMAKATIN, anan UMMAKATIN take qara gayama maman RAHMAN yanda abin ya faru, shuru kawai maman tayi tana nazari, ganin hakan sai UMMAKATI takoma gidansu tare daci gaba da bama RAHMA baki.
Ba kowa agidan nasu yanxu dan duk yaran gidan sun fatta da alama kowa yana da wajen zuwa ne, sai ya kasance daga maman RAHMA sai kishiyoyinta, nan tafito sanye da hijab danta leqa makwaftansu barka anyi aihuwa.
Sanda ta lek'a duk d'akunan kishiyoyin nata tace musu bara ta leqa makwafta barka, dama itace bata leqa ba.
Cikin jin daɗin zata fitta alokacin da suke buk'ata nan suka amsa mata da kulawa, tana fitta ko nan suka had'e a d'akin Lantana wato ta uku dan itace uwar sharri.
Iyami ta kalli Lantana tace, "Mun shiga uku, yanxu ya zamuyi, ina jin tsoran karfa abinda mukama RAHMA ya dawo kan y'ay'anmu kamar yanda boka ya shaida mana muddin aka d'aura Auranta asirin kan y'ay'anmu zai dawo.
Asabe tace "hmmm, aini duk narasa nutsuwata, hankalina duk ya tashi, Lantana kisama mana mafita dan kinsan yace idan ya dawo kan y'ay'anmu zasu aikata TANTIRANCIN dayafi na RAHAMAN, kinga tunkan hakan tafaru dan Allah muyanke abin daya dace.
Lantana taja numfashi tace "mafita d'ayace garemu yanxu, itace mukoma wajen bokan mu gaya masa komai, na tabbatar zai temakemu.
Iyami tace "amma yau zamuje garesa ko. "aa saurin me kikeyi ne, mudai bari citta maje tunda kunga ranar ne sunan Hauwa'u zamu fitta gabaki d'ayanmu, amma idan mukace zamu yau ai bazai yuhuba, sam babansu bayarda zaiyi mu ficce mu uku a alokaci d'aya ba, tambayarmu zai fara yi ina zamu mu uku haka kamar anyi mutuwa, amma kunga wannan dake sunan K'anwarsa ne zai barmu kunga daga can saimu sulale mubar maman nata muje garesa koya kuka gani.
Asabe tace "Zancenki hakk'un, mu bari sai cittan maje......
Gabaki d'aya wannan zancikan nasu akan kunnan maman RAHMA sukayi, dan tana fitta taci karo da Larai wata makwafciyarsu tafito daga gidan da zata shiga danyin barkan, saita tambayeta ina zata tace zata leqa gidanne tayima Furera barka, Sai Larai tace mata ai bata nan Fureran sunje asibiti da jaririya za'a mata allura kuma yanxu fitansu kenan saidai tabari idan tadawo tayi mata.
To shine maman RAHMA tadawo gidan nasu sai taga shigar iyami d'akin Lantana dajin abinda suke faɗi..
Har wani jiri ne taji yana iyabanta, ahankali dai tadafe bango ta shige d'akinta tana mamakin mugun hali irin na mutane, dan Kawai mahaifin yarinya na santa shikenan sai suje su aikata mata asiri, Innalillahiwainna'ilaihirraji'un duniya tazo qarshe. Nan hawayen baqin ciki ya zubo mata ta share tana tunanin me zatayi itako tarama abinda suka mata, nan tadinga tunani kala kala daga qarshe tayanke shawarar Auran RAHMAN shine kawai abinda zai wanke mata baqin cikin da suka d'auki shekara da shekaru suna bata, tasani Auran ABDUL d'in da RAHMAN akwai gyara cikinsa dan sadaki ya dace ya kasance a hannun mahaifinta ne ba'a hannunta ba, bari dai tabari ubanta ya dawo susan nayi, saidai bazata tab'a bari wannan damar ta wucceta ba, dan zatayi amfani da ita ne wajen ganin tadatse dukkan wani makircin da suka kullama RAHMANTA, tabbas dole ABDUL d'in ya zama miji ga RAHMAN, dan kawo qarshensu,.
Baban RAHMA nadawowa yahau tambayar maman RAHMAN kan wane batu ne take gayamai d'azu a waya, zaunar dashi tayi da bashi ruwa me sanyi sannan ta zaiyane masa komai, amma bata gaya mai abinda su Lantana sukama RAHMAN ba, saidai ta gyara zama ta tsaida dukkan nutsuwarta garesa tace dashi, "ni abin danaga ya dace anan shine, na lura Auran RAHEEMAT shine abinda ya dace, zai bamu farin ciki da nutsuwa da kwanciyar hankali, ko'a tarihi ban tab'a cin karo da yarinya maraji kamar RAHEEMAT ba, dan haka na yanke shawarar koda ace Auran nasu bai d'auru ba ak'ara d'aura musu wani. wallahi dama ni nagaji da halin RAHEEMAT.
Jan numfashi Baban RAHMAN yayi yace, "Banji dad'in wannan lamari ba, sam banji dad'insa ba, amma yanda kikace hakan za'ayi, saidai yanxu fara kiramin ita RAHMAN taban number na yaran na kirasa naji yanda suka d'aura Auran, idan da gyara sai kawai a gyara musu idan bai d'auru ba zanji tabakin yaran idan yana da ra'ayinta saina d'aura masa ita.
"Hakan yayi, maman tafad'i hakan tana me lalubar num na RAHMA danta kirata.
RAHMA na kwance gadan UMMAKATI sai aikin rahawaye take tana tsinewa ABDUL aranta, sai ganin kiran mahaifiyar tata tayi, bayan ta d'auka gaya mata tayi tazo gida yanxu tana nemanta, RAHMA najin hakan tatashi tayi gidan nasu, anan d'akin maman nata taga mahaifin nata, yace tabashi number na ABDUL, tana turo baki tabashi numbar ABDUL d'in, nan yace mata to tatashi taje dama numbar kawai zai karb'a, bayan ta fitta nan yakira ABDUL, lokacin suna airport basu samu jirji ba, saidai masu aikin wajen sun basu tabbacin gobe zasu samu me tafiya arewa qarfe shidda na safe. Dan haka sai suka nufo dawowa hotel d'in da suka sauka cikin jin haushi, bayan ABDUL ya d'auki wayar tasa ahankali yake gaisar da baban RAHMAN da tambayarsa waye shi, nan ya gayama ABDUL d'in shi mahaifin RAHMA ne, yana san jin yanda suka d'aura Auran nasu, nan ba b'ata lokaci ABDUL ya gaya masa yanda suka d'aura, murmushi baban RAHMA yayi yace mai yazo jos ya samesa, Amman yana rokwansa alfarma yazo da iyayensa maza dan yana so su qara tabbatar da lamarin saboda wani dalili nashi.
Nan cikin ladabi ABDUL ya amsa mai da cewa indai ya dawo daga Lagos zaizo insha Allah da iyayen nasa.
Sosai ABDUL ya kwanta aran mahaifin RAHMA, haka kawai yaji yana san yaran, yana fatan yazo garesa lafiya yaji waye shi.
Washe gari ko su ABDUL suka bar garin na Lagos, sun sauka a Abuja lafiya, saidai sanda sukayi kwana d'aya anan, washe garima sanda suka kai wajen qarfe biyar kana sukaje tasha suka hau motar Kaduna, lokacin da suka iso Kaduna qarfe goma sha d'aya na dare ne, ABDUL baiyi shashin Hajjiya Kakah ba, shashinsa yayi da zubewa kan katifarsa cikin jin daɗin yanda suka dawo lafiya, AMEER ne dai iyayensa suka san ya dawo, saboda bud'e gidan da sukaji anyi, nan sukayi kansa da fad'a wai akan meyasa zaiyi tafiya bai gaya musu ba, me yasa sam bai d'aukesu a bakin komai bane, karfa ya manta sufa iyayensa ne.
Shuru yayi musu kawai yana jinsu, sanda suka gama yace dasu Shifa yanzu ba Yaro bane, danya girma, sudena saka masa ido akan al'amuransa, tafiya ce dai yayi kuma bai gaya musu ba wani abu ne, yana gaya musu hakan yayi shashinsa cikin b'acin rai, dan sosai ransa ya b'aci da faɗan nasu garesa. (Allah ya shirya)...
Washe gari bayan ABDUL yayi wanka ya kintsa d'akinsa zuwa wajen mahaifiyarsa yayi ya gaisheta, saidai daqer ta'amsa masa, shidai ajiye mata tsarabarta yayi ya qara gaba shashin Hajjiya Kakah dan taganshi cikin yi mata bazata,
Anan yaga mahaifinsa, yako ji daɗin hakan,
Hajjiya Kakah taji dad'in ganinsa sosai, bayan sun gama gaisawa yayi breakfast kana ya sasu agaba ya kwashe komai daya faru tsakaninsa da RAHMA ya gaya musu, ya qara da gaya musu yanda sukayi da babanta.
Murna sosai Hajjiya Kakah tayi, nan tahau tunanin Allah yasa ko Auran nasu bai d'auru ba a sake d'aura wani, dan bazata manta da abinda malamai suka gaya mata kan tantirancin ABDUL d'in ba, na muddin aka mai Aure ba makawa duk asirin dake jikinsa zai karye...
Nan cikin zumuɗi Hajjiya Kakah tace da ABDUL d'in, "Dani za'a garin Jos d'in, zamu kwana gidan Hajjiya Saratu qawata, nasan zataji dad'i sosai dan rabona da ita yau shekara Hud'u kenan, cikakkiyar aminiyata ce aika santa tana kawomin ziyara,
Shuru ABDUL yayi yana san tunota, tabbas ya ganeta dan tun yana Yaro yake ganinta tana kawoma Hajjiya Kakan ziyara, amma shi bai tab'a ganin Hajjiya Kakan takai mata ziyaran ba, dan haka kallanta yayi da cewa, "Naganeta, dama kamar baki tab'a kai mata ziyara ba ko"
Murmushi tayi da bashi amsa, "Eh, sau biyu na tab'a kai mata ziraya, Auranta da aihuwarta ta fari, tasan lafiya bata isheni ba shiyasa bata damuwa da zuwana.
"Ok, Allah yabar qauna,
Mahaifinsa yace "gaskiya banji dad'in faruwar lamarin nan ba ABDUL, sam baku kyauta ba, dan ba'a wasa da addini, addini ba abin wasa bane, dan haka ku kiyaye nan gaba.
Cikin ladabi ABDUL yace mai, "Toh zamu kiyaye.
"Yanxu zan kira su Baba Shehu mu zanta yanda mukayi zan gaya maka da daddare.
"Toh, ABDUL yace mai da maida kallansa ga Hajjiya Kakah yaci gaba da cewa, Yanxu bara naje gidan AUNTY ZAINAB na gaisheta.
"Toh, adawo lafiya, Allah yay maka albarka,
"Ameen yace mata da ficcewa daga falan...
Sanda ya shiga gidansu AMEER ya gaishe da iyayensa sannan yay gidan ZAINAB d'in, Ya ganta a falo kwance kan kujera da alama zazzab'i ne yake san kamata danta dukunkune cikin wani qaramin tsaftacaccen bargwanta, d'akin nata sai tashin qamshin turare yake, ZAINAB tana da tsafta fiye da tunanin me tunani,
Tana ganinsa tayi qarfin halin tashi cikin murna take mai sannu da zuwa, Ahankali ya amsa mata yana me mata kallan wurillar san gano me yake damunta,
Ta tsargu da kallan da yake mata dan haka cikin alkarewa dashi tace, "Amai da gudawa nakeyi, ina ganin shi yake san sakamin zazzab'i,
Shuru yayi mata, itama sai tayi shurun,.
Can ya d'auke idansa daga fallanta yace "Aunty ko har yanxu kina da matsala da mijin naki ne, naga haskenki ya ragu. Gashi kinyi wata rama, akwai abin dake damunki ne.
Murmushi tayi mai da cewa, "wallahi ABDUL ban tab'a jin dad'in mu'amala ta rayuwa da Salisu irin na wannan karan ba, sam baya san b'acin raina ayanzu, sannan ya rage yawan daran dayake yi, kawai matsalata da danginsa ne ayanzu, ABDUL mahaifiyarsa aihuwa take so kamar me, gashi ni har yanzu aihuwar batazo gareni ba, qannansa zuwa gareni suke sumin rashin kunya akan hakan, kuma ba dama nayi magana dan nan take take zuwa tawankeni soso da sabulu, ABDUL ina san na haihuwa wallahi ina san yara, gashi yanzu tace mai wai dole ya qara Aure, ABDUL zanyi rayuwa da kishiya wallahi bana san hakan, bana san kishiya na tsaneta, haka kawai ina zamana da mijina sai tacemai yayi aure yayi min kishiya kuma kishiyarma y'ar uwarsa wacce take santa, wane baqin ciki zan gani, sam yarinyar bata da kunya bata da kamun kai, ina sha'awar rayuwa da mijina ni kad'ai, danna tara duk wani abu da d'a namiji yake buqata agun mace. ZAINAB takai qarshen zancenta da zubo da hawaye.
ABDUL yaja numfashi da kallanta yana me cewa, "Kiyi hak'uri my Aunty, komai yayi farko zaiyi qarshe, kuma kisaka azuciyarki haihuwa ta Allah ce, shi yasan me yake nufi da hakan daya hanaki yanzu da kike buqata, kinemi zab'inshi banaki ba kiga dai dai, na tabbatar zaki haihu Auntyna, zaki haifamin k'anne masu kyau kamarki, Wallahi Aunty zaki haihu, karki damu da abinda suke faɗi, dan basu tara sani da Allah ba, fatana kisaka Allahn agabanki ya isan miki kinji Auntyna. Ya qarashe maganar da sakar mata murmushi.
Murmushin itama tayi mai da cewa, "toh nagode, ya garin na Lagos kun dawo lafiya.
"Lafiya muka dawo Auntyna, saidai nazo miki da wani batu, nan ABDUL ya kwashe komai ya gaya mata na Auransa da RAHMA, sanda gaban ZAINAB ya fad'i, kuma bazatace ga dalilin faɗuwan gaban nata ba, ita dai taji dad'in lamarin dan dama rokwan Allah take kan ya kawo mata ranar Auran ABDUL d'in, dan asirin dake d'awainiya da shi ya karye, ahankali tace, "Gaskiya naji dad'in hakan, kuma idan aka tabbatar maka da cewar auren naku nanan dan Allah karka saketa, haka kawai naji ina santa, kai anya ma kuwa badani za'a garin na Jos d'in ba, dama ban tab'a zuwa ba, gashi ina fatan na had'u da wata marubuciya acen (RAHMA NALELE).
"Aunty baki jin daɗin jikinki, dan Allah karkice zaki kibari har gida zan kawo miki ita idan komai ya dai-daita.
Tace "amma zanso ayi komai agabana ai.
Yace "Kawai Aunty kishare, dan komai dazai faru zan gaya miki kamar akan idanki akayi.
Murmushi kawai ZAINAB tamai.
Kasancewar Dadyn AMEER amini ne ga Baban ABDUL nan ya gaya masa komai na Auran ABDUL d'in da RAHMA, yayi mamaki sosai dan haka yace goben dashi za'aje dama yana san ganin wani d'an uwansa,
Saiya kama mutum biyar ne zasu Hajjiya Kakah da baban ABDUL da Baba Shehu da qaninsa da Dadyn AMEER sai ABDUL da AMEER cukutan na bakwai,
washe gari ko da qarfe shidda suka antayo garin na jos, da motarsu suka tafi, da motar su AMEER da motar Dadynsa
Hajjiya Kakah dai motarsu AMEER tahau, su Baba Shehu ko motar Dadyn AMEER d'in suka hau.
Saidai sanda ABDUL yakira Baban RAHMA yazo ya kaisu gidan nashi, dan bazai iya gane gidan ba, kasancewar ranar daya kai RAHMA gidan da daddare ne, kuma daqer ta'iya kawosu gidan.
Abin mamaki baban RAHMA d'an uwa ne ga Dadyn AMEER, shine wanda Dadyn AMEER d'in yake faɗin zai duba,
Wannan abu ya basu mamaki sosai dan Dadyn AMEER yana kawoma baban RAHMAN ziyara lokaci lokaci, haka shima yana kai masa ziyarar lokaci lokacin. Dan y'an uwan juna ne na gaske ba gaji gare gaji gare ba, dan kakansu d'aya, shiya haifi iyayansu maza, Dadyn AMEER yana temakwan Baban RAHMA sosai arayuwa, hakan yasa baban RAHMA yake sanshi da qaunarsa.
A d'akin d'aya daga cikin y'ay'ansa ya saukesu, dama maman RAHMA tayi musu abinci nan da sukayi sallah sukaci sosai dan ta'iya abinci ba d'an kad'an ba.
Babu b'ata lokaci suka buqaci ABDUL da AMEER dasu qara musu bayanin yanda suka d'aura Auran,
Nan ko suka koro musu bayanin komai, gaskiya basu d'aura Auran dai dai yanda ake so ba, Auran yana buqatar gyara, musamman yanda sadakin baizo ta hannun mahaifin RAHMAN ba, wannan dalilin yasa dole Auran nasu yana buqatar gyara,
Nasiha sosai sukama ABDUL da AMEER kan karsu sake aikata ganganci irin wannan, sannan mahaifin RAHMA ya kallali ABDUL cikin so da qauna, yace "A zahirin gaskiya qaunarka tashiga raina, haka kawai naji ina qaunarka ina san na baka Auran RAHMA, duk da cewar ina da sani akan rashin jinka kai da AMEER abakin Dadynsa, dama kai ne dai ban sani ba, amma nasan AMEER sosai shima ya sanni dan ina zuwa gidansu lokaci lokaci kaima mahaifinsa ziyara, naso ace auran nan naku ya d'auru yanda akeyi, da wallahi bazance maka kasaki RaHMA ba, dan dakai tadace, b'cos aduniya banga mutumin daya tsayama RAHMA arai take kuka sanadinsa ba, amma kai kasaka mata tsoro aranta faɗi take tashiga uku ta abo ruwan dafa kanta dan kayi furucin bazaka saketa ba, da bakinta take gayama mahaifiyarta hakan, yanzu inasan nasan labarinka idan na gamsu nayi maka alqawarin baka Auran RAHMA.
Jan numfashi Hajjiya Kakah tayi tace da AMEER da ABDUL d'in su fitta daga d'akin zatayi magana da Baban RAHMAN.
Nanko su ABDUL d'in suka fitta, Yayan RAHMA Usman ya gansu suka gaishesa da kulawa yace suzo su shiga d'akinsa, nan suka shiga d'akin nasa dajin dad'in yanda yayi masu.
Hajjiya Kakah ko gyara zama tayi ta karanto ma mahaifin RAHMA Komai akan ABDUL bata b'oye masa Komai ba.
Nan ko ya jinjina lamarin nasa, musamman ma asirin dayaji yana d'awainiya dashi da tsanar da mahaifiyarsa take masa.
Kan yayi magana maman RAHMA taja numfashi da gyara nata zaman ta gaya musu rashin ji irin na RAHMA, daga qarshe ta qara da cewa, "Nima inaji a jikina idan aka d'aurama RAHMA Aure ba makawa duk wani rashin ji nata zaiyi sauqi, dan haka ina bada shawarar a had'a AURAN ABDUL da RAHMA dan ina kyautata zatan yin hakan zai kawo haske arayuwarsu.
Kowa awajen tattara nutsuwarsa waje guda yayi yaga dacewar shawarar tata, dan haka Baban RAHMA yace ya amince da Auran nasu, yanzu bara ya kira aminansa a d'aura Auran yanzu ba wani batun b'ata lokaci.
Nan ya ficce yaje ya kira aminan nasa, Hajjiya Kakah da maman RAHMA suka fitta daga d'akin Dadyn AMEER ya bada sadaki dubu saba'in batare da b'ata lokaci ba nan take aka D'aura Auran Abdullahi (ABDUL) da Rahma (RAHEEMAT)
Kowa cikinsu ya shaida wannan Aure, saidai me zai faru,🤔 tunda aka d'aura Auran ABDUL dake d'akin Usman ya fara jin wata hajijiya akansa, kamar ana kunce masa wasu notika a kansa, ya tashi yana rik'e kan nasa cikin wani hali yana cewa, "Kaina zan mutu, wayyo kaina zan mutu, kan AMEER da Usman suyimai wani abu tuni ya faɗa qasa sumamme. Nan cikin tashin hankali suka hau yayyafa mishi ruwa amma ina sam ko alamar motsi babu ga ABDUL, hankalinsu ya dad'a tashi nan sukayo d'akin da iyayen nasu suke suka fad'a musu ABDUL fa ya fad'i yanzun nan.
Hajjiya Kakah tace "Ai dama nasan hakan saita faru, kunga aikin asirin ko.
nan iyayen sukayi d'akin suna masu salati, saidai wani abu daya qara d'aure musu kai wanda ya furgitasu shine jini suka gani yana fittowa ta bakin ABDUL d'in da hankinsa tare da wani abu kore haka babu kyan gani.
Jinin sosai yake fitta fa😨.. wanda kallo d'aya zaka mai kasan idan har ya dad'e a hakan ba makawa mutuwa zaiyi, gashi shi ba motsi yake ba, amma haka jinin yake fitta daga jikinsa,
Ga RAHMA ko itama ga yanda nata lamarin ya kasance, dan tana gidansu UMMAKATI kwance a gadan UMMAKATIN tana shirya wulak'ancin da zatama ABDUL, Dan taji mamanta na fad'in yau zasuzo suna kan hanya, to shinefa da'aka qara d'aura masu Auran taji gabanta ya yanke ya fad'i, nan tatashi tayo tsakar gidan gidan hannunta dafe da qirji, ji tayi kamar an zare mata wani kayan nauyi akanta, nan take jiri ya abeta ta zube k'asa sumammiya,
Nanko maman UMMAKATI da UMMAKATIN sukayo kanta suna masu kiran sunanta, saidai ina tayi kamar babu rai ajikinta. Nan cikin tashin hankali maman UMMAKATI tahau yayyafa mata ruwa, amma ko alamar farfad'owa babu ga RAHMA itama, dan haka tace da UMMAKATI taje gidansu RAHMAN tagayama mamanta abin dayake faruwa
Lokacin data shiga gidan lokacin Usman da AMEER suke fitto da ABDUL ranga ranga dan sashi cikin mota su kaishi asibiti,
Babu b'ata lokaci nan tagaya musu RAHMA tafad'i kuma sunsa mata ruwa taqi farfad'owa.
Haka hankalinsu ya qara tashi suka tambayeta meya jawo mata fad'uwan, tace ita dai ganinta tayi ta fitto daga d'aki hannunta dafe da qirji daga haka saita fad'i..
Nan ko su AMEER sukayi gidansu UMMAKATIN suka d'auko RAHMAN itama suka sata a mota sai asibiti,
Matanity sunan asibitin da suka kaisu, kasancewar yafi kusa dasu, anan cikin gaggawa doctors suka hau yi musu binkicen gaggawa, ABDUL dai ya zubda jini sosai dan haka yana buqatar jini, babu b'ata lokaci haka sukazo suka gaya musu suna buqatar jini nan cikin gaggawa,
Baban ABDUL yace shi mahaifinsa ne ad'auki jininsa.
Abin mamaki😳 da'aka gwada jinin Baban ABDUL d'in saiya nunama doctor jininsu ba d'aya bane🙅🏻♂.
Baban ABDUL yace wannan zancen banza ne ai ABDUL d'ansa ne dan haka dole jininsu ya zama d'aya, dole yanzu su ibi jininsa su saka mai dan yana san d'ansa baya san ya mutu su'ibi jinin cikin gaggawa a saka masa yana san ganin d'ansa araye, su kuma sukace baza su iba ba, dan Komai yana da qaqida, idan dai yana san agwada jininsa dana ABDUL d'in ne sai'a gwada dan ashare mai tantama, aga d'ansa ne ko ba d'ansa ba.
Aiko yana jin hakan yace ya yarda agwada.
Doctor ya gwada jinin ABDUL dana Baban ABDUL d'in ya nuna masa ABDUL ba d'ansa bane🙅🏻♂...
Lokacin da doctorn yake gayama baban ABDUL d'in jirine ya nemi ibansa Allah dai ya kare aka taresa bai faɗi ba,
Dadyn AMEER yace a ibi jininsa a sakama ABDUL d'in saboda karsu rasa shi,
Doctor yana gwada jinin nasa yaga daidai yake dana ABDUL d'in, yaqara dai yimai babban gwaji wanda zai bada komai, nan sakamako ya bashi tabbaci kan ABDUL d'an Dadyn AMEER ne🤔
Doctor da mamaki ya kalli Dadyn AMEER bayan ya ibi jinin ya sakama ABDUL d'in yace dashi yasamesa a office d'insa,
Bayan Dadyn AMEER yaje garesa cemai yayi "Abin yaban mamaki, dan binkice ya nuna majinyacin d'anka, kuma gashi wancen mutumin yace d'ansa ne, koda yake binkice ya nuna ba d'ansa bane, Kai ne ubansa.
Cikin waro ido😳 Dadyn AMEER yace "Ban gane me kake nufi ba doctor, kana nufin ABDUL D'ANA ne.....
D'aga masa kai doctor yayi cikin tabbatarwa da cewa, "Haka dai binkice ya nuna"
Tashi Dadyn AMEER yayi dayin waje yaje ya kamo hannun AMEER yace "Doctor wannan shine d'ana, kuma Wallahi da mahaifiyarsa kad'ai natab'a mu'amala ta rayuwar Aure,
Doctor ya kalli AMEER Sosai yace "Gaskiya abin da rikitarwa, amma bara na gwada jinin shi wannan d'in nagani.
Shuru Dadyn AMEER yayi masa,
Haka sukayi d'akin gwaji da AMEER, shi kuma Dadyn yazo ya gayama su Baban ABDUL ada😀 cewa gafa abinda doctor yace, wai ABDUL d'ansa ne, tayaya hakan tafaru, bayan shi bai tab'ayin mata biyu, kuma mu'amala ta Aure bata tab'a had'asa da wata y'a mace bayan matarsa ba.
Wannan abu yaba kowa mamaki.
Nan Baban ABDUL yakira doctorn yacemai ya gwada jininsa dana AMEER yaga d'ansa ne..
Baban RAHMA yace me hakan yake nufi, yace kawai yaji aransa cikin Abdul da Ameer dole d'aya ya kasance d'ansa dan ƙaunar da yake musu bata wasa bace.
Baba Shehu yace wannan ba hujja ba, Dadyn AMEER yace aa ayi dai yanda yace...
Abin dai da kulle kai yake,🤔 dan bincike ya nuna ABDUL ɗane ga Dadyn AMEER, sannan AMEER ɗane ga Baban ABDUL..
Komai ya hautsine, dan gabaki d'ayansu sun shiga rud'u, hankalinsu ya bala'in tashi, tabbas akwai abin daya faru, kuma matansu su zasu gaya masu Komai,
ALLAH yasa suna da hankali ba irin mata ba, dan wani sab'ani bai shiga tsakaninsu a wannan lokaci ba,
Yau ce ranah tafarko da AMEER yayi nadamar abinda yake aikatama iyayen nasa arayuwa, dan tunkan asan bakin zaran zancen ya kama qafar Dadynsa ya fashe da kuka yana cewa Dady ka yafemin abinda nadinga aikata maka arayuwa, nasan koma wane labari za'a bada nan gaba nasan bazai kasance me kyau bane agareni, kaga farta min dan Allah, ashe duk wannan abun da nake maka ashe ni ba d'anka bane....
Hawaye ne ya zuboma Dadyn nasa da duk wanda yake wajen... sai rahma nalele tatsaida hannunta daga rubutun, da takema masoyan nata, tana me hararo abubuwan da zasu faru nan gaba...😀
By Rahma Nalele Auntyn luv💋
`☆´-`☆´-
☆“˜•☆•
¸☆“☆ª☆_☾`☆•
❉ *.¸¸.*♠*.¸¸.*🙆🏻♂*.¸¸*❆ *.¸¸.*⚫.¸¸.*♠
☆
*TANTIRANCI KO KARUWANCI*☆
*.¸¸.*♠ *.¸¸*❆ ¸¸.*⚫¸*♠ *.¸¸.*🙆🏼♀*.¸¸*❆
`☆´-`☆´-
☆“˜•☆•
¸☆“☆ª☆_☾`☆•🤱🏻
{Fad'i alkairi ko kayi shuru)🤫
A true life story
*Follow me on Wattpad @rahamanalele*
Labari da rubutawa zuwa ga tsarawa.. ☾•Rahma Muh'md Rufa'i Nalele..☆
https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R
” بسم الله الرحمن الرحيم
Page 14
*Masoyana ina dad'a baku hak'uri, lafiyace bata isheni ba, rahma nalele dai takuce ƴan hannuna*💋
D'agasa Dadyn yayi da rungumarsa yace "kai d'ana ne AMEER, hakan bazai tab'a canjawa ba" kuka sosai AMEER yakeyi yana cewa, "ka gafarta min Dady nayi nadama"
Kowa sai share hawaye yakeyi awajen tare da girgiza kai da tayin mamakin lamarin,
RAHMA tasamu kanta sanadin temakwan data samu wajen doctor, amma tatashi da mutuwar jiki, hutu take buqata sosai dan ji take kamar anlakad'a mata dukan tsiya,
ABDUL dai bazai samu kansa nan kusa ba, dan doctor ya tabbatar musu saiya kai awa Ashirin da hud'u zai farfad'o, ahakan ma zato yake yi, wannan dalilin shiyasa su Dadyn komawa gidansu RAHMA da RAHMAN.
Anan sukaba Hajjiya Kakah labarin abinda yake faruwa, nan take ko hankalin Hajjiya Kakah ya tashi, fad'i take, "nidai dan Allah dan annabi karku rabani da ABDUL, danya zama jinin jikina, idan bana ganinsa hankalina baya kwanciya,
Dady murmushi yayi mata kawai, ashe ba banza ba yake matuƙar ƙaunar ABDUL, tabbas kuma miye ya faru ba qaramin abu bane, Allah dai ya maidasu gida lafiya su zanta da matansu...
Haka sukaje suka kama hotel d'in Sharna suna masu addu'ar Allah yasa ABDUL ya farfad'o cikin gaggawa su koma gida dan su kawar da damuwa.
Hajjiya Kakah ko gidan Hajjiya Saratu tayi aminiyarta, aiko tasamu tarba mekyau agunta dan rasa inda zata sata tayi dan farin ciki, haka ta cika mata gabanta da kayan ci dana marmari, Hajjiya Kakah bata iya cin komai saboda damuwar dake cinta arai, wallahi bata san arabata da ABDUL dan tafi kowa sanin san ƴaƴa irin na Dadyn AMEER..
Nan ta gyara zama bata b'oye ma aminiyar tata komai ba tagaya mata damuwar dake damunta yanzu, dama ance abokin kuka shi ake gayama mutuwa, aiko Hankalin Hajjiya Saratu ya tashi, dan itama tasan ƙaunar da Hajjiya Kakah takema ABDUL, sam baza taso a rabata dashi ba, nan tadinga kwantar mata da hankali wajen nuna mata ABDUL bazai iya yada ita ba, dan yana matuqar qaunarta. Hajjiya Kakah ta gamsu da maganar Hajjiya Saratu, dan da wiya kam ABDUL ya iya yada ita.
D'akinta Hajjiya Saratu tabarma Hajjiya Kakah dan takwana cikinsa.
Dake maman RAHMA tasan RAHMAN tana fashin sallah sam batabi takanta dan tatashi tayi sallar la'asar bangariba i'sha ba, haka tabarta tadinga sharara bacci abinta, sai wajen karfe taran dare sannan ta iya tashi, amma tatashi da qarfin jiki sosai, dake a d'akin maman nata tayi baccin hakan yasa data tashi ta kalli maman nata tace, "Mama ruwan wanka,
"Au kin tashi ne, aidama nasan zaki buqata bara naje na juye miki dan dana gama tuwa na d'ora miki tuntuni, ina da tabbacin yama tafasa yanzu" maman nata ta bata amsa tana me tashi dan zuwa juye mata.
RAHMA tayi murmushi da cewa "Yauwa nagode mamana"
Bayan tayi wankan d'akinsu na y'an mata tayi dan saka kaya, ba kowa a d'akin da alama duk y'an uwan nata sun ficce wajen samarinsu, haka ta canja kayan ta koma d'akin maman nata dan taci abinci, tana cikin cin ne ta kalli maman nata tace, "Wallahi mamah sai nake jina kamar wata sabowa, gabaki d'aya jikina ya canja, kamar an d'auke min wani kaya me d'auyi akaina, sam ban tab'a jin hakan a gareni ba"
Maman taja numfashi tace, "Ai dama haka ne, wata ranah duk sai kaji kamar an zare maka wani abu ajikinka, dama ina san gaya miki maganar yaran nan ABDUL wanda kukayi Aure a group, nan take gaban RAHMA ya fad'i ita sai yanzu ma tatuna da batunsa, cikin sauri ta katse mahaifiyar tata da cewa, "Eh, meya faru,
Tace "ai d'azu iyayensa ne suka dawo dake gida daga asibiti" shima yana asibitin, nan anan ya fad'i.
"Ok, ashe sune iyayen nasa, wai mema ya jawo min fad'uwan ne dahar aka kaini asibitin"
"Oho, ina zan sani, UMMAKATI dai tace kawai ganinki tayi kin fito hannu dafe da qirji sai kuma kika fad'i"
"O, na tuna, tabbas anyi haka, dan haka kawai naji gabana ya yanke ya fad'i, sannan kuma dana fitto tsakar gidan sai naji jiri ya kamani, daga haka bansan meya faru ba, yanzu dai gaya min mama, ba dai wani batun Aure tsakani na dashi ko"
"Ai kunyi kuskure RAHEEMAT, Aure ya kwullu tsakaninku ke dashi, wallahi yanzu ABDUL mijinki ne, maman ta fad'in mata hakan dan tace bazata gaya mata cewar wani Auran aka d'aura mata dashi ba, dan tana san taqara tabbatar mata da cewa musulinci ba abin wasa bane.
Aiko nan take RAHMA ta zare hannunta daga cikin miyar tuwan da take ci, hankalinta tashe tace, "Na shiga uku ni RAHMA, wallahi bana sanshi, danna tabbatar bazai zamo d'aya daga cikin mazajen danake fatan na Aura ba, kuma ma ni yanzu ban shiryama kaina Auran yanzu ba, wallahi tallahi saiya sakeni danni ban shirya zaman Aure dashi ba.
Murmushin takaici maman nata tayi mata da cewa, "hmmm RAHEEMAT kenan, sam baki da hankali, kidai bi duniya ahankali dan ABDUL ya fiki rashin ji, yafiki TANTIRANCI ayanda naji labarinsa wajen kakarsa, sannan bazan so ya sake ki ba, dan ɗan uwanki ne, yaro ne ga ɗan uwan mahaifinki Alhaji Aminu wanda yake zama a garin Kaduna aikin sanshi sasoi dan yana zuwa nan kawo mai ziyara kamar yanda shima yake zuwa mai, wallahi RAHMA ki rufama kanki asiri karki bari aji kanki tsakaninki dashi, dan Auranki dashi babban rufin asiri ne, kuma ni haka kawai naji ƙaunarsa araina, ina san shi ina san kiyi rayuwa dashi, bana san naji kin tayar da wata fitina atsakaninku idan har kina san ganin farin ciki na, idan kuma baki so kiyi duk abinda zakiyi.
"Gaskiya mama saidai kiyafe min, wallahi ina ji araina bazan iya zama da igiyarsa akaina ba, dan kwata kwata banji ina sanshi ba, haka bazan tauyema zuciyata hakk'inta wajen rayuwa da wanda bata so ba, nidai kawai zance mai ya sakeni dan bana sanshi....
Ai bata ida zancen nata da numfashi ba nan maman ta make mata baki saiji kake gab🙁.
Aiko nan RAHMA tafashe da kuka da ture kwanukan abincin dake gabanta taficce daga d'akin tayi d'akin kwanansu.
Dama kishiyoyin maman nata yauce ranar da suka shirya zasu gun boka, sai kuma akayi rashin sa'a gidan qanwar baban RAHMAN da zasuje sunan taje asibiti dan ama jaririya allura sai likita ya riqesu wai jiririyar bata da ishash shan lafiya, dan haka an d'aga suna, Lantana tace to subarta ita taje wajen bokan duk abin da ake ciki in tadawo saita gaya musu,
Sun yarda da hakan, haka ta shiryama maman RAHMAN qarya wai zata duba mahaifiyarta jiki ya tashi, haka ya barta taje, toh bayan taje wajen bokan gaya mata yayi yanzu haka asirin ya koma kan y'ay'ansu, kuma makaryar asirin shine mutuwar Auran RAHMAN, muddin Auranta ya mutu toba makawa asirin zai karya, shi yanzu ba abinda zai iya yi musu akai dan san da yaja musu kunne, hankalin Lantana tashe tazo ta gaya musu, hankalinsu suma ya tashi sosai, nan dai suka d'aura aniyar kashe Auran RAHMAN kota halin qaqa...
Toh bayan dawowar Lantanan ne su ABDUL sukazo, toh sun kasa gane me yake faruwa sukaga baqi agidan nasu dan baban RAHMAN bai gaya musu zuwan nasu ba, suna tunanin magana dai ake akan Auran RAHMAN, sun dai kasa gane me yake faruwa, dan haka sai kowaccensu take a ankare tana me fatan tasan me yake faruwa, shine fa jin kukan Rahma da sukayi da shiganta d'akinsu na kwana sai kowaccensu tayi zarab ta shige d'akin cikin munafunci suka hau tambayan RAHMAN meya faru da ita take kuka, sam RAHMA bata gane munafunci ne ya kawosu ba, haka tasaki baki ta gaya musu wai Auranta da wannan yaran nan yana nan, ita kuma bata sanshi, aiko suna jin hakan suka hau zugata kan karta yarda da auran, dan bai dace ace Auranta yazo a haka ba,
Lantana tace "Ai munga wasu baqi sunzo wajen Babanku d'azu, harda Alhaji Aminu d'an uwan mahaifinki, kaidai baqin sune iyayen mijin naki"
Shuru RAHMA tayi mata, jin hakan sai Iyami ta amshe da cewa, "Kin manta Har da samari biyu, bashine har d'aya daga cikinsu ya fad'i jini ya dinga fitta ba"
Asabe tace "Haka ne, ina ga acikin samarin biyu qila da mijin nata a ciki ko" takai qarshen zancen da zubama RAHMAN ido cikin san suji tabakinta dan tabasu haske a hikimance,
Aiko RAHMA share hawayenta tayi dace musu, "eh, wanda ya fad'in shine mukayi Auran dashi dan shine naji mamana tace yana asibiti, kuma ma ɗane ga Alhaji Aminun d'an uwan baban namu"
Suna jin hakan sai suka dafe qirji, baqin ciki ya qara cika zuciyarsu, saboda sanin da sukama Dadyn AMEER shine me kud'i aduk cikin Y'an uwan baban su RAHMAN, Tab Wallahi da sake,🤔 wai bindiga a ruwa, ai dole Susan yanda zasuyi su raba Auran dan sam RAHMAN bata dace da Yaransa ba, y'ay'ansu sune suka dace dashi,
Nan suka dinga zugata kan karta yarda sam bai dace tana babbar yarinya kamarta Auranta yazo a haka ba,
Ji RAHMA tayi bata da masoya alokacin sai su, haka tadinga d'aukar zugarsu tana qara jin tsanar ABDUL cikin ranta..
Washe gari da qarfe 1:30pm Dady harda Hajjiya Kakah suna tare da ABDUL, har zuwa wannan lokaci bai farfad'o ba, hakan yasa sukayi masallaci danyin sallah, lokacin yayi daidai da sulalewar RAHMA daga gidansu tayo asibitin dan karb'ar takaddar sakinta gurin ABDUL d'in, nan tayi tambaya aka nuna mata d'akin da ABDUL d'in yake,
Hajjiya Kakah tagani a dukkin k'ofar tana sallah ita da Hajjiya Saratu qawarta, sai tayi saurin shigewa d'akin tana me wara ido dan taga ABDUL d'in.
Aiko tagansa kwance kan wani tsaftataccen gado hannunsa d'auke da robar qarin jini, gabanta ne ya fad'i, haka kawai taji wani yanayi yayi ram da zuciyarta, nan ta zuba masa ido tana me kallansa sama da qasa tare da mamakin kyau irin nasa, gay d'in ya had'u iya had'uwa dan ya tara abubuwan da kowace mace take buqata agun mijin Auranta, matsalar dai itace, ita ba yanzu tayi niyar yin Aure ba, kuma ABDUL yayi mata yaro, dan tana san Auran namijin daya zarce mata a shekaru Sosai, sam bata fatan ta Auri sa'anta ko wanda ya d'an girme mata da irin shekara d'aya haka ko biyu, to ABDUL ya cika duk wani abu da take buqata agun mijin Auranta saidai shekarunsa baza su wucce nata ba, wannan kad'ai ya isa ta iya sashi sakinta, dan aganinta idan ta Auri sa'anta bazata samu cikakkiyar kulawar data dace ba.
Jan numfashi tayi tare da matsawa garesa hancinta na bin k'amshin jikinsa, tare da tunanin a ina tasan qamshin.
Ahankali ta kara hancinta ga qirjinsa ta shaqi qamshin dakyau nan tatuna ajikin wannan saurayin daya dinga marinta tatab'a jin wannan qamshin, da gaske turaran yana da dad'in qamshi, haka ta d'ago da fuskarta dan d'auke kanta daga qirjin nashi, karab suka had'a ido, gabanta yayi mummunan fad'uwa, nan tayi saurin qarasa janye jikinta a rikice, cikin in ina tace, "Dama, da, mah, nabi qamshin turaranka ne dan naji kamar na tab'a jin irinsa jikin wani.
Shuru ABDUL yayi mata idansa nakan fuskarta, _Yarinyar tana da kyau_ ya qara faɗin hakan akaro na biyu cikin ransa,
Ganin yayi mata shuru yana kallanta sai taci gaba da cewa, takaddata nazo karb'a, sam ban shirya zaman Aure yanzu ba, dan haka saika bani takaddata dan Wallahi bazanyi rayuwar aure da sa'ana ba.
Ayanzu daga qasa ABDUL ya fara kallanta har zuwa sama, rigace da wando a jikinta, girar iya cikinta ta tsaya, sai wandan dogo har qasa, sai wani d'an figigin gyale data yane kanta dashi, ga alama ta nuna kitsan dake kanta kitsan qari ne, gashin ciko yayi aikinsa a kan, dan yasa kan ya cika tam irin na yara yaran mata masu aji mara ji kamarta, kayan sun matseta matuqa, dan sun bayyanar da sirrin halittarta, nan take wani abu ya caki zuciyar ABDUL, sam batayi kama da y'ar musulmai ba, dan shigar ita zata tabbatar maka da hakan.
Ahankali ya kawar da kallansa daga gareta tari ya kamasa sosai, nan ta rikice tad'auki ruwan swan wata dake wajen ta bud'e ba tare da tunanin komai ba ta d'ago da kansa tare da kwafa masa bakin goran, a nufinta yasha.
Nan ABDUL ya lumshe idansa sakamakwan jiyo qamshin jikinta da yayi, kad'an yasha ruwan saita maida masa da kan nasa kan filo a hankali, sannan ta maida ruwan gefe tare da maida kallanta garesa taci gaba da cewa, Sannu, Allah ya qara lafiya.
Shuru dai yayi mata, ita dai RAHMA haka take, sam bata san taga mutum bashi da lafiya, yanzu saita rikice, y'an uwanta sunyi mata wannan shedar dan ko tayi fad'a yanzu dakai taga baka da lafiya jikinta sanyi yakeyi, nan zata zuba maka ido tana mejin tausayinka, idan kuma bakuyi faɗa ba, haka zata zauna dare dakai tatace maka sannu cikin kulawa.
Yan zumma zubama ABDUL ido tayi cikin tausayawa, tunani take bai dace tayi masa maganar saki yanzu ba, ya dace tabarshi ya samu lafiya saita karb'i abinta....
"Zaki iya kira min doctor"
ABDUL ya katse tunaninta da faɗin hakan.
Nan taficce daga d'akin tayi inda take tunanin ganin doctorn,
Hajjiya Kakah taga fitowanta amma zatanta ko ma'aikatan wajen ne, musamman da bataga fuskarta ba.
Rahma tagayama doctorn ABDUL na San ganinsa, nanko ya tashi da murmushi akan fuskarsa yana tambayarta yanzu ya farka, eh tace mai, akan idanta ya shiga d'akin da ABDUL d'in yake, ganin hakan sai tabar asibitin tana me fad'i aranta bara dai tabari ya samu lafiyan, saiya bata takaddarta.
Doctor ya duba ABDUL sosai yaga baida matsala ayanzu, sam baya buqatar komai, dan jini ya wadaci jikin nasa, ma'ana dai ansamu yanda ake so,
Dan haka kiran Hajjiya Kakah yayi ya gaya mata jikin nasa yayi kyau sosai, ko yanzu za'a iya sallamarsa, tunda ba anan suke ba, amma zai basa magunguna Wanda zai shasu tsawan sati biyu. Saidai sukula dashi sosai dazaran sunga wani canja agunsa su maidashi asibiti,
Murna sosai Hajjiya Kakah tayi, nan tazauna kusa da ABDUL d'in tana me shafa fuskarsa cikin san taji ko jikin nasa da d'umi, Hajjiya Saratu tayimai sannu yayi mata murmushi da tashi yana kallan Hajjiya Kakah yace, "Kakah yunwa nake ji, zanso nayi wanka na wanke baki sainaci abinci.
Kan Hajjiya Kakah tace wani abu, saiga su Dady sun shigo d'akin suna masu murmushi ganin ya farka, nan suka mai sannu Hajjiya kaka tagaya musu abinda yace, sai sukace bara sukarb'i sallama suje can hotel d'in da suka sauka sai yayi wankan yaci abincin idan suka qara ganawa da iyayen RAHMAN sa tafi yau tunda da sauran lokaci,
Haka ko akayi, sun karb'i sallama AMEER ya kama hannun ABDUL ya sakashi cikin mota suka rankaya Sharna...
Wanka da ruwa me zafin gaske ABDUL yayi, ya tsaftace bakinsa da saban buroshin da makilin d'in daya gani cikin toilet d'in, sai yayi alwala ya saka kayan da Dadyn AMEER ya siya masa akan hanya lokacin da suke tawowa hotel d'in, kana ya rama sallolin dake kansa, sannan yaci abincin, haka kawai yake jinsa wani fayau haka, kamar an zare masa wasu kaya masu nauyi akansa, sanda su Dady suka tabbatar yad'an huta kana suka rankaya gidansu RAHMA, anan suke gaya mai an qara d'aura musu Aure shi da RAHMAN, amma ita RAHMAN bata san qara d'aurawa akayi ba, dan haka suna san jin ta bakinsa yana da ra'ayinta yana santa koko baya ra'ayinta Susan nayi tun yanzu.
Kunyarsu ta kama ABDUL matuqa, dan haka ce musu yayi shi ai d'ansu ne, bazai tab'a ƙalubantar duk wani abu dazasu zartar akansa ba, zai rayu da ita rayuwar da zasuji dad'inta, insha Allah baza'a tab'a samun matsala daga garesa ba.
Wannan kalami nasa ya qara saka qaunarsa a cikin zuciyarsu, nan suka saka masa albarka wajen yi musu fatan alkairi.
Sai maman RAHMAN ta roqi alfarma kan sud'an bar mata RAHMAN na d'an wani lokaci kad'an dan akwai shirye shiryen da zatayi mata, sai Dady yayi murmushi yace mata karta wahalar da kanta wajen yi mata wani abu, yana da wani gida daya gama gidawa danya koma saboda yana san qara Aure, kuma ba abinda baisa ba agidan, zai barma ABDUL gidan sai su zauna a gidan, dan haka karta damu yasaka komai na rayuwa agidan ba abin buqata sai kayan kitchen irin nasu na mata da kayan abinci, shi kuma wannan ba matsala bane akone lokaci za'a iya siya..
Murmushi tayi da cewa, toh angode amma duk da haka ad'an bata lokaci, kona wata d'aya ne, tayi alqawarin bazata qara ko kwana d'aya ba zata saka y'an uwa da abokan arziqi su kayo RAHMAN, dan Allah ita dai tana neman alfarmar.
Sunce mata toh ba komai Allah ya kawosu lafiya,
ABDUL yayi mamaki Dadyn AMEER sosai, Allah dai ya sakamai da alkairi dan yana nuna masa qauna akowane lokaci, hakankali ya kalli AMEER sai yaga hawaye na zuboma masa, da damuwa ABDUL ya tab'asa yana ce mishi lafiya, saurin goge hawayen yayi dacemai ba komai.
Shuru kowa yayi, dan ABDUL dai baisan me yake faruwa ba.
Nan dai dukkansu suka tashi dayima baban RAHMAN sallama sukayi mota, sai maman RAHMA ta tsaida ABDUL a zaure tana ta gaya masa irin tsanar da y'an uwan nata suke mata, da abinda kishiyoyin nata sukama RAHMAN, ta qara da cemai dan Allah karya saki RAHMAN idan tabuqaci hakan, tana san RAHMAN tayi rayuwar aure me d'orewa, dan Allah ya rik'e mata y'arta amana wajen qoqarin gyara mata rayuwa, ta lura shi kad'aine zai iya da ita, kuma tagaya masa komai ne dan tana san ganin qarshen makircin kiyoyin nata nan kusa,
ABDUL ya tabbatar mata bazai tab'a sakin RAHMAN danta buqaci hakan ba, zaiyi qoqari sosai wajen ganin yaba maqiyanta mamaki.
Maman taji dad'in furucin nasa sosai, tayi mai godiya dace mai ya tsaya taturo masa ita su gaisa ai baya tafi batare daya ganta ba, Har zaice mata ai d'azu tazo asibiti gunsa sai kuma ya fasa dan inda tasan taje garesa d'azun bazatace mai yanzu ya tsaya taturo masa ita ba.
RAHMA tana yatsina baki tayo zauran gidan nasu, ta kallesa sosai, _yafi d'azu kyau_ ta fad'i hakan aranta, a fili ko ce masa tayi, "Kawai kabani takaddata dan nagaya maka nifa basan Auran nan nake ba. Kuma gaskiya ni bana sanka kawai kaban takaddata.
ABDUL yayi murmushi yace "Nima sam bana sanki, dan bakiyimin ba, bakya d'aya daga cikin jerin Matan da nake so, sam baki taka ko farcen qafarsu a zubi me kyau ba, zan gaya miki wata gaskiga wallahi duk wanda kikaji yace miki kin cika mace kyakkyawa me aji, to wallahi qarya yake miki, dan ke mummunace abar ƴama cikin mutane, farkoma kije ki fara kallan kanki a madubi, sam bakiyi kama da ƴaƴan musulmai ba, kalli wani qazantaccen gashi da kika wani kasa akanki, wanda kike da tabbacin musulinci baice ki saka shi ba, kalli kayan dake jikinki, kallo d'aya me tarbiya zai miki ya gane sam ba ƴar musulmai bace, kin matse jiki gabaki d'aya kina nunama maza suzo ga haja kin bud'e, mata wayayyu irinki a harka irin wannan basa fitowa sununa haka' saidai sufito a nunasu, sam baki iya KARUWANCI ba, dan inda nine a matsayinki bazan dinga fitowa da kaya ajikina ba, kawai karuwancin zan saka a gaba, in fito da kayan da duk maseefar sheɗani idan ya ganni saiya shagaltu da kallona, wato da bireziya zan fito da d'an qaramin wando in nunama duniya ni TANTIRIYAR KARUWACE, abu na qarshe dazan gaya miki anan shine, Babu batun saki tsakanina dake, zan rayuwa dake rayuwa irin ta ma'Aurata da kalamai irin nasu badan ina sanki ba, saidan nanuna miki kuranki na baki isa kisani sakinki.. Yana faɗin hakan ya nemi ficcewa daga zauran, saidai ina.... Zuciyar RAHMA tacika tayi FAM da muggan kalaman daya jefeta dasu, dan haka shan gabansa tayi da cukume masa gaban riga tana wani fitta wani numfashi na baqin rai tace da shi, "Kai ka isa kazo har cikin gidamu kajefeni da muggan kalamai sannan kayi tunanin zaka fitta batare danace maka komai ba, eh, naji na yarda baka sona kamar yanda nima bani sanka bani qaunarka, batu kuma akan saka gashi danayi akaina, gani nayi ai kaina ne ba naka ba, kuma kai baka isa ka hanani sakawa ba, KARUWANCI kuma ai sani ne bakayi ba, ni tantiriyace a harkar, dan na zubba ciki sau goma sha shidda, bazan iya Yawo da kayan irin wanda ka fad'i yanzu da rana ba, dan kirana za'ayi da mahaukaciya ba tantiriyar karuwa ba, amma ina yawan bin club cikin dare kuma tsirara nake yawa gaban maza da mata sune zasu tabbatar maka da cewar ni ba qaramar tantiriya bace, wallahi kokafi waye qoqari saika sakeni dan rantsuwata bazata tab'a tafiya a banza ba"....
"Da gaske" ya katseta da faɗin hakan yana me dalla mata fararan idansa cikin nata, nan ko take kwarjininsa ya make ta, taji wani abu na fitowa daga idansa yana shiga nata, nan bata san ya akayi ba saijin hannunta tayi yana sakin rigarsa data cukume, cikin sauri ta kawar da fuskarta daga kallansa,
ABDUL yayi murmushi da janyota jikinsa... Nan ta kallesa a furgice, ya qara sakar mata murmushi da da zare d'an figigin gyalan data yana kanta dashi, nanko take kitsan dake kan nata ya qara bayyana, kitsone yafi dubu amma sam bai bashi sha'awa ba, ya tab'e baki daci gaba da cewa, Bana san mutum me qarya a rayuwa, idan da gaske ne abinda kikace, meyasa ranar dana ganki a club ban ganki a yanda kika fad'i yanzu ba, kawai ganin qaramin iskancinki nayi wanda kika zauna kan cinyar wani Alhaji yana me lalubar qirjinki kina me hanasa, shin tantiriya karuwa me yawo tsirara gaban maza da mata ya dace ta hana abukin iskancinta jikinta wannan lokacin da hankalin kowa bai tafi kansu ba".
Hararar tsana RAHMA ta galla masa da cewa, "Wato kaine wanda nake nema wanda ya dinga wanka min mari kamar yasamu jakarsa ko"
"Eh, nine mana, har kikace zaki nemoni ki rama abinki ba"
Wata hararar ta qara galla masa da cewa "Babu abinda zai hanani ramawa yanzu kuwa"
"ai dama ni bance karki rama ba, saidai idan kika min d'aya atake zan miki uku waƴanda sukafi naki"
"Wallahi na tsaneka ABDUL karkayi kuskuran barin akawo maka ni cikin gidanka, dan zanyi maka wani kisa ne irin wanda matan yanzu suke yima mazajensu da zaran anyi musu Auran dole.
Murmushi ya qara sakar mata da cewa, "common my Baby, zanso hakan kuwa, dan dama ni nagaji da rayuwar, amma gaya min, wane irin kisa zaki min aciki, zakimin irin wanda wasu matan sukeyi na sakama amzajensu guba ne cikin abin cinsu, koko zakimin irin wanda wasu matan sukeyi na dannama mazajansu fillo yayin da suke bacci, koko zakimin irin wanda wasu matan sukeyi nayima mazajen nasu yankan rago, koko cakamin wuqa zakiyi, koko Dakar wani shashi zakiyi cikin jikin nawa wanda zai baki damar gamawa dani"
"Babu d'aya da zanyi maka cikin waƴannan, dan nawa salan na musamman ne, salo ne na yara yaran mata masu aji yaran zamani, kisan zamani zanyi maka ABDUL" RAHMA tabashi amsa cike daqarin jin tsanarsa cikin ranta.
Qara jawota jikinsa yayi da cewa, kince na zamani zakimin ko, to ai nagano kowane iri zakimin, kina nufin ki kama gabana ki gille min da wuƙa ko".... Cikin sauri RAHMA tawaro ido😳 da girgiza masa kai a tsorace,
hakan sai ya qara tabbatarma da ABDUL ba tantama ko kusa RAHMA bata san kan iskanci ba🤣 kawai tsiwar da rashin kunyar ce ta iya, dan haka kai mata kiss yayi ga bakinta ya tsotsa da sakewa yaci gaba da cewa, ina jiran zuwanki gidana my Baby, sannan ina san wannan tsiwar taki irin sosai d'innan.
Yana faɗin mata hakan ya sake da ratsawa ta gefanta ya ficce daga zauran.
Tunda RAHMA take bata tab'a cin karo da d'an iska irin ABDUL ba, sam bata tab'a had'a baki da wani katan garde ba, takanyi dai kiss d'in na gefe da gefe sam ƴamar bakin mutane take, amma gashi yau ya had'a bakinsa da nata cikin lokacin da takejin kamar ta shaqesa dan tsana, batayi aune ba, saijin hawaye tayi ya zubo mata, nan tafashe da kuka wiwi ta koma gidan nasu tana cewa "Wallahi saiya sakeni😭😭😭....
ABDUL ko saurin shigewa motarsu yayi, ganin shi suke jira ashe tuntuni.
Haka suka d'auki hanyar kaduna cikin addu'ar Allah ya saukesu lafiya.
Aiko sun isa lafiya anan ba tare da b'ata lokaci ba, baban ABDUL da Dadyn AMEER suka had'a kan matansu sukayi asibiti dukkansu, sam basu gaya musu abinda yasa sukace sushirya zasu asibitin ba, haka ABDUL sam bai san me yake faruwa ba, sanda yaga an zuqi jininsa dana mahaifiyarsa da jinin AMEER dana momynsa harda na babansa dana Dadyn AMEER d'in, sannan ya kalli AMEER yace, "Wai meyake faruwa ne" gwajin me za'ama jininmu" shuru AMEER yayi masa, ganin hakan sai yayi shuru ya zubama sarautar Allah ido.
Sun shafe sama da awa d'aya a asibitin kana doctor yabama kowan nansu sakamako, bincike dai ya nuna ABDUL shine d'an Dadyn AMEER kuma momyn AMEER d'in ita ce mahaifiyarsa, haka AMEER ɗan baban ABDUL ne kuma maman ABDUL d'in itace mahaifiyarsa,
Tashi ABDUL yayi cikin matuqar mamaki, tare da kallan kowannansu da furgici baiyi aune ba, nan yaji jiri na kamasa, yayi baya luuuu kamar zai fad'i sai Dady da babansa sukayi saurin taro shi, cikin matuƙar kulawa.
Dake da Hajjiya Kakah akaje asibitin tana qara jin sakamakwan ta rabka salati, AMEER ko sai jinsa sukayi a qasa ya yanke jiki ya fad'i sumamme, hankalin mama Saude ya tashi sosai, sam batayi zatan gwajin tantancewa za'ayi tsaninsu ba, da Wallahi bazata yarda ayi mata ba,
lalle zataci uban ZAINAB dan ba makawa itace tatona mana asiri, Wallahi bame rabata da ita sai Allah...
Andai samu AMEER ya farfad'o, dan haka basu tsaya wani jin ba'asi kan lamarin a cikin asibitin ba, dan Dadyn AMEER cewa yayi subari su dawo gida su tattauna, amma yana so Dan Allah suzo gidansa ayi maganar anan, dan anan ne zasufi samun sakewa,
Kowa yayi na'am da zancen nasa
Sunyi faking a ƙofar gidansu ABDUL kenan saiga ZAINAB ta iso wajen tana kuka wiwi,
Nan suka firfito suna masu tambayarta meya faru, ko anyi mutuwa ne😨... Ita dai shuru tayi musu daci gaba da kukanta.
Mama Saude ta galla mata wata muguwar harara tace, "Dan ubanki yanzu kika fara kuka, bani zaki tonama asiri ba, Wallahi sainayi miki illah a rayuwa, kowa maida hankalinsa kanta yayi yana nazarin kalmominta,
Ganin hakan sai ABDUL yaje ya kama hannun ZAINAB d'in yace.. "Aunty koma me yake damunki ina san kiyi hak'uri dashi, Aunty ina cikin tashin hankali, halin da nake ciki ayanzu na tabbatar yafi damuwar da kike d'auke da ita.
Tace "aa ABDUL, wallahi nafika shiga damuwa da tashin hankali ayanzu, dan Aurena ne ya mutu😭, yau Salisu yayi min saki uku ABDUL ya zanyi, wallahi ina san mijina.
Dafe kai ABDUL yayi da cije bakinsa ya zare hannunsa daga nata wannan jirin ya qara kamasa, zai fad'i still Dady da Babansa suka qara taresa.
Su Hajjiya Kakah ko salati suka rabka,
ABDUL kallanta yakeyi cike da tausayi, nan take wani zazzafan zazzab'i ya kama sa, ya lumshe idansa cikin wani hali, ganin hakan sai Babansa ada da Dadynsa ayanzu suka riƙesa kowannansu niyarsa ya kaisa cikin gidansa.
Dan dukkansu hanyar gidansu suka nufa dashi.
Nan Hajjiya Kakah ta kallesu a kid'ime sai alokacin suka lura da yanda suka riqesa da niyar dake cikin zuciyoyinsu.
Ahankali cikin sanyin jiki baban ABDUL ya sake shi hawaye ya zubo masa yace da Dadyn, "Gidanka zakayi dashi ko nayi gidammu dashi,
Rintse idansa Dadyn yayi, gaskiya bazai iya yima abokin nasa kawaici akan ABDUL ba, Wallahi tun yanzu zai d'auke d'ansa, dan haka saiya bud'e idansa yace, "Kayi hak'uri abokina, ina san ainihin d'ana ya kwana cikin gidana yau kuma a d'akina...
ZAINAB najin haka tawaro ido😳 da barin kukan nata tace... "Shike nan Yayata yau asirinki ya tonu, dama wannan ne kike tunanin nina tona miki asiri, ko kad'an ni ban gayama kowa wannan sirrin naki ba, Allah ne dai ya tona miki asirin bani ba...
Shidai Dadyn AMEER gidansa ya nufa da ABDUL momyn AMEER tabi bayanshi.
Baban ABDUL ya share hawayensa, da kallan AMEER yace, "Ayanzu nine mahaifinka AMEER, shin zaka yarda dani, ka karb'e ahaka,
Kallansa AMEER d'in yayi da matsawa kusa dashi yace, "nayi nadama arayuwata, kuma ban tab'a yinta ba sai jiya da yau, kai mahaifina ne, kuma na yarda da hakan, zan bika duk inda kasa qasa, bazan tab'a guje maka ba,
Rungumarsa baban nasa yayi tare dajan hannunsa yayi gidan nasu dashi, anan wani d'akinsa ya zaunar dashi..
Anan waje ko, kasa shiga gidan nasu Hajjiya Kakah da ZAINAB sukayi, ita dai ZAINAB bata jin zata shiga gidan batare data qara ganin ABDUL ba, dan tana hango yanda yake lumshe ido da alama bayajin daɗin jikinsa Sosai, dan haka barin Hajjiya Kakah tayi anan tayi gidan Dadyn..
Anan falo taga sun kwantar da ABDUL, kansa na bisa cinyar momy yayinda Dadyn ya maida hankalinsa kan ABDUL d'in gabaki d'aya yana meyi masa sannu, hawaye ya zuboma ZAINAB, takai hannunta ga goshinsa nan taji zafi zau, tasan ABDUL bai iya ciwo ba, musamman idan wannan zazzab'in ne yayi ram dashi, dan tacema Abida takawo mata ruwan zafi,
Momy tace "dawai yanzu na kira doctor zaizo ya dubasa,
ZAINAB tace, "Ya saba irin wannan zazzab'in momy, kuma yana samun saukarsa da wuri idan aka gasa masa jikinsa da ruwan d'umi.
Shuru momyn tayi mata, haka Abida takawo ruwan da tawul d'in, nan ko ZAINAB tadinga goge masa jikin nasa, momyn na tayata, dan momyn tace mata tabari amma taqi,
ABDUL najinsu, sakin ZAINAB d'in ya tsaya masa arai matuqa, sannan ba wacce yake hangowa aransa yanzu sai Hajjiya Kakah, danya hango tashin hankali agareta lokacin dataga Dadyn yayiyo gidansa dashi. Ga mahaifinsa shima ya shiga tashin hankali, dan yaga zubar hawayensa.