Thursday, September 30, 2021
BA GIRIN GIRIN BA Page 1 to 10
Share this
Thursday, September 16, 2021
Inna lillahi wa inna ilaihir raji'un! Allah ya ma shahararren jarumin Kannywood, Alhaji Yusuf Barau rasuwa ɗazu a Kaduna.
Yusuf Barau, wanda tsohon ma’aikaci ne a Hukumar Wasanni, Al’adu da Yawon Shaƙatawa ta Jihar Kaduna, ya rasu a yau a asibitin Isolation Centre da ke Down Quarters, Kakuri, Kaduna.
Marigayin ya rasu ya na da kimanin shekara 61 a duniya.
Haka kuma ya rasu ya bar ‘ya’ya takwas da mata ɗaya
Yusuf Barau ne ya kai kan shi asibiti da kan shi, inji aminin sa
Aminin sa, fitaccen ɗan wasan ban Malam Musa Mohammed Abdullahi, ya shaida wa mujallar Fim cewa shi marigayin da kan sa ne ya kai kan sa asibitin.
Za a yi jana’izar sa bayan sallar Isha’i a gidan su da ke garin su, Zariya, inda wan sa ya ce a kai gawar a rufe shi a can.
Haƙiƙa rasuwar Alhaji Yusuf Barau ta kaɗa hankalin ‘yan Kannywood, musamman abokan aikin sa, wato waɗanda su ka yi aiki da shi a industiri ko a Hukumar Wasanni, Al’adu da Yawon Shaƙatawa. Duk jikin jama’a ya yi sanyi. Kowa ya na ta yi masa addu’ar samun rahama
Share this
Monday, September 13, 2021
Hotuna: Shin Adamar Kamaye ta yi ‘wuf!’ ne? Hira da jarumar
WASU hotuna da su ka karaɗe soshiyal midiya a yau sun haifar da raɗe-raɗin cewa jarumar nan ta Kannywood, Hajiya Zahra’u Saleh, wadda aka fi sani da Adama matar Kamaye, ta yi miji.
A hotunan, an ga Zahra’u tare da wani matashi a tsarin miji da mata, wanda hakan ya sa ake zaton ko jarumar ta samu yaron mijin aure ne samfurin zamani, wato ‘wuf!’
Bayan ɓullar hotunan, mutane sun ta yi wa Zahra’u addu’ar sanya alheri, yayin da wasu ke tambayar idan jarumar cikin diramar ‘Daɗin Kowa’ ɗin ta yi aure ne a asirce.
To amma ba haka abin ya ke ba, kamar yadda mujallar Fim ta binciko.
Don tabbatar da gaskiyar labari, mujallar Fim ta ji ta bakin Hajiya Zahra’u Saleh, inda ta ce, “Wannan hotunan na biki ne wanda amarya da ango su ke ɗauka kafin biki, wato ‘prewedding’, amma kuma a cikin fim.
“Wallahi ba aure na yi ba. Wannan hotunan fim ɗi na ne wanda zai fito kwanan nan mai suna ‘Matar Yaro’. To sakamakon haka ne ya sa mu ka fara motsa jam’iyya da yaɗa manufar mu ta cikin wannan hoto da mu ka ɗauka sannan mu ka fara sakin sa duniya ta gani.”
Ta ƙara da cewa, “Fim ɗin zai kasance mai dogon zango kuma ni ce wacce na ɗauki nauyin shirya abu na da kai na.”
Jarumar ta yi farin cikin jin yadda ake ta yi mata fatan alheri. Ta ce, “Na ji matuƙar daɗi ganin yadda mutane su ka fara karɓar wannan fim tun kafin ya fito kasuwa. To hakan ya na nuna alamun kwalliya za ta biya kuɗin sabulu. Don haka su jira, nan ba da jimawa ba fim ɗin zai fito.”
Game da yadda masoyan ta su ke yi mata fatan ta yi aure, ta ce la shakka ta kusa yin auren.
Zahra’u ta ce, “Kamar yadda kowa ya ke ta magana, da man kuma ai duk ɗan aure ba ya ƙin aure, kuma shi aure ai lokaci ne, idan Allah ya kawo shi, aure da likkafani ai ba a tanadin su, ko da kuɗi ko babu idan Allah ya ƙadarta dole za ka yi shi.
“Don haka ina nan da niyyar yin auren ma; kawai dai a jira lokaci.”
Wakilin mu ya gano cewa sunan jarumin da su ka yi hotunan da shi shi ne Mudassir Muhammad, kuma an ce ɗan asalin garin Dutsin-ma ne na Jihar Katsina
Share this
Sunday, September 12, 2021
Martani: Naziru Sarkin Waƙa da Aminu Saira ba su da laifi ko kaɗan!
SALAAM mujallar Fim. Na karanta wani labari naku mai taken “Naziru Sarkin Waƙa Ya Hayaƙa ‘Yan Jarida” wanda da dama mutane su ka mayar da martani a kafafen sadarwa, inda su ka bayyana abin da fitaccen mawaƙin ya yi a matsayin tozarci ga ‘yan jarida.
Babu shakka, masu wannan ra’ayi su na da nasu hujjojin, bai kamata a ga laifin su ba, sai dai ni na bambanta da mafi yawan ra’ayoyin nasu. Amma na fi karkata kan ra’ayin Malam Nazifi Dawud, wanda ya nuna yadda ‘yan jaridar da kan su su ke wulaƙanta kan su.
A iya sani na dai, aikin jarida aiki ne mai ɗimbin ƙa’idoji da ‘farillai,’ ‘mustahabbai,’ ‘makaruhai’ da kuma dabaru masu yawan gaske. Muddin har mutum ya kuskure su, ko ya jahilce su, shakka zai faɗa cikin matsala, har ma ya jawo wa kan sa da ma sauran masu sana’ar jangwangwama.
Kan haka ne na ke ganin akasarin masu kiran kan su ‘yan jarida a yau su ke cikin garari.
To, bari mu koma kan zancen da Sarkin Waƙa ya yi a cikin fim. Abu na farko da za mu kalla shi ne labari ne ya bi a matsayin sa na jarumi a cikin shirin. Wanda kuma a farkon farawa ma, wasu gogaggun marubuta ne su ka raba dare, su ka jajirce su ka tsara shi. A cikin su ma, har da ma wasu manyan ‘yan jaridar. Saboda haka, ni ban ga dalilin da za a ɗora laifi kan jarumin ba.
Abin da ya kamata a yi shi ne a fahimci cewar Naziru Sarkin Waƙa fa ‘script’ ɗin labarin ne ya bi, kamar yadda aka tsara, aka ba shi.
A gani na, da yawa daga cikin masu wancan ra’ayin su kan fassara rayuwar mawaƙin ne na zahiri, wanda a ganin su wataƙil zai iya wulaƙanta mutane saboda sun san attajirin mawaƙi ne, wanda kuma hakan babban kuskure ne!
Na biyu kuma dasu danganta laifin da darakta Aminu Saira, su ma alwalar tasu ta sami ‘lam’a’. Domin kuwa kafin a shiga lokeshin, sai da marubuta labarin da ma’aikata shirin gaba ɗaya, da ma wasu ƙwararru, su ka zauna su ka yi bitar sa daidai gwargwado.
To, idan mu ka tattaro waɗannan hujjojin, babu yadda za a yi mu danganta laifin ga waɗannan bayin Allah.
Ta yaya za mu kalli aktin ɗin jarumi a cikin fim, mu yanke masa hukuncin zahirin rayuwar sa? Kenan duk labaran da wasu jaruman su ka yi a kan wasu gungun mutane, su ma sai an yi musu hukuncin furucin su kenan? Sau nawa ake nuna gurɓatattun ‘yan sanda a fim? Sau nawa ake nuna alƙalai marasa adalci a wasu kotunan a fim? Shin mun taɓa jin wani ɗan sanda ya fito ya ce an ci zarafin ɗan sanda a cikin fim? Tilas ne a nuna ‘character’ a cikin fim, mai kyau ko akasin hakan, domin wataƙila a cikin fim ɗin har a bayyana wa masu kallo dalilin bijiro da ‘character’ ɗin.
Ba mamaki a cikin fim ɗin za kuma a samar da wani ɗan jaridar da ba ya tsayawa ya karɓi na mota a wulaƙance.
Yanzu bari mu koma zahirin rayuwar wasu ‘yan jarida a wannan zamani. Dukkan mai hulɗa da ‘yan jarida a yau zai yarda da ni cewa Naziru Sarkin Waƙa, ko kuma in ce fitaccen darakta Aminu Saira, sun yi daidai, saboda ko shakka babu akasarin masu aikin jarida sun koma tamkar maroƙa da sunan aikin na jarida.
Mafi yawa ba su da ƙwarewar aiki, sun ɗauka aikin jarida wata dama ce ta tara dukiya ko neman arziki ko ta halin ƙaƙa!
A matsayi na na ƙaramin ɗan jarida, ina ƙyamar masu aikata hakan, kuma wannan lamari da ya faru, ya hasko min wata hanya zan jajirce wajen gina labari kan gurɓatattun ‘yan jaridar, waɗanda a duk san da su ka yi aiki, ba za su kama gaban su ba, sai su koma gefe su na jiran na mota!
Share this
Naziru Sarkin Waƙa ya hayaƙa ‘yan jaridaa
Naziru Sarkin Waƙa
WASU ‘yan jarida sun mayar da martani ga kalaman da fitaccen mawaƙi kuma Naziru M. Ahmad (Sarkin Waƙa) ya furta a kan ‘yan jarida a cikin dirama mai dogon zango ta ‘Labari Na’.
Ana haska shirin ne a tashar talabijin ta Arewa24 a duk mako.
A cikin mako na 11 na shirin, wanda aka haska a jiya Juma’a, an nuno wani matashin ɗan jarida ya je ofishin Sarkin Waƙa don neman ƙarin haske a kan sabuwar waƙar da ɗaya daga cikin ma’aikatan sa, Sumayya (Nafisat Abdullahi), ta fitar mai taken ‘Dawo-Dawo’.
A ƙoƙarin ɗan jaridar na samun labarai tare da samun bayanin wanene Mahmud ɗin da aka fitar da waƙar a kan sa, ya yi wa Sarkin Waƙa ‘yan tambayoyi, shi kuma ya ce masa ba shi ne ya ke da hurumin bayar da amsa ba, sai dai ya tuntuɓi Sumayya ɗin.
Da za su rabu, sai Sarkin Waƙa ya yi umarnin da a nema wa ɗan jaridar kuɗin mota, bai ko yi sallama da shi ba ya haye motar sa, direba ya ja su ka tafi.
Ƙalubalen Hidaya Ahmed ga ‘yan jarida
Wannan maganar ce ta fusata wasu daga cikin ‘yan jarida a soshiyal midiya, musamman a Facebook, inda su ka bayyana rashin jin daɗin su da kalaman na jarumin ya furta a fim ɗin.
Karanta kuma Ali Nuhu: Yadda zan gudanar da aikin jakadanci da Jami'ar Skyline ta ba ni
Mujallar Fim ta tattaro wasu daga cikin ra’ayoyin da ‘yan jarudar su ka wallafa.
Shugabar sashen labarai da al’amuran yau da kullum na gidan rediyon Aminci FM da ke Kano, Hidaya Salisu Ahmed, ta buɗe muhawarar da cewa: “Kamar ‘yan jarida ba ku ji an ce wa ɗan’uwan ku a nema masa kuɗin mota ba a wani wasan Hausa? Menene matsayar ku kan wannan kalamin da Naziru mai waƙar nan ya yi?”
Ita kuma wata mai fafutikar kare haƙƙin mata a Jihar Kano, Zainab Nasir Ahmad, cewa ta yi: “Ko mu da ba ‘yan jarida ba abin bai mana daɗi ba. Akwai raini da ƙasƙanci a abin da su ka yi. Wani mawaƙi da ba a da shaidar kwalin sa na difloma bai kamata ya raina ma’aikacin jarida ba.”
Shi kuwa Auwal Mahmoud Durumin Iya cewa ya yi, “Shirmen banza ne kawai. Ai duk lalacewar ‘yan jarida ba su kai matakin lalacewar da Naziru ya kwatanta su ba a jiya. Babu shakka mu na Allah-wadai da wannan ‘scene’ ɗin da aka gabatar cikin shirin ‘Labari Na’ na jiya. Babban mai laifi kuma shi ne Aminu Saira, tunda shi ne ya bada umarni.”
Karanta kuma Sabbin hotuna masu zafi na Rahama Sadau da ƙannen ta
Saƙon Auwal Mahmud Durumin Iya
Aminu Ibrahim Rimin Keɓe kuma ya ce: “A matsayi na na ɗan jarida, na yi Allah-wadai gami da tir da waɗancan kalaman na Naziru Mai Waƙa. Duk lalacewar ɗan jarida ya wuce a yi masa waccan rashin darajar.”
A ra’ayin Nazifi Dawud kuwa, wanda tsohon ma’aikacin jaridar Daily Trust ne kuma mawallafin jaridar Daily Focus, “Tsuntsun da ya ja ruwa, shi ruwa ke duka. Ai da ‘yan jaridan ba su wulaƙanta kan su ba, da babu wani mahaluƙin da ya isa ya raina su.
“Mu ‘yan jarida mun san yadda wasu daga cikin mu su ka ƙasƙantar da darajar aikin su, su ka maida kan su almajirai. Kullum su ke nan bin ofis-ofis na ‘yan siyasa da manyan jami’an gwamnati da sunan neman labari.
“Da yawa daga cikin mu ba su iya yin labarai na bin diddigi (investigative journalism) saboda kada su ɓata wa wasu manya rai a daina ba su abin da ake ba su. Idan waɗannan ‘yan jarida su ka halarci taro, sai su tsaya bayan an gama don a ba su kuɗin da bai taka kara ya karya ba. Wasu ma har faɗa su ke yi a kan wannan kuɗi. Kuma mutane na kallon su.
Karanta kuma 'Yan Kannywood sun yi tir da kalaman Ummah Shehu
“Saboda haka ai maimakon mu zo mu na ɓacin ran banza a kan abin da mu ka san mu na aikatawa, ai gwara mu yi amfani da wannan damar mu gyara aikin mu, mu guji kwaɗayi. Da ba su ga mu na wulaƙanta kan mu ba, wallahi da ba su isa su yi mana wannan cin zarafi ba. Allah ya ganar da mu, ya ba mu ikon gyara wa.”
Abin da Ibrahim Aminu Rimin Keɓe ya ce
To sai dai mujallar Fim ta lura da cewa abin dubawa shi ne rashin albashi mai kyau, da rashin cikakkiyar kula da walwala, da kare haƙƙoƙin ‘yan jarida a Nijeriya na daga cikin manyan ƙalubalen da ma’aikatan aikin yaɗa labarai ke fuskanta a ƙasar nan.
Duk da cewa masu ruwa da tsaki a ɓangaren kamar majalisar kula da ayyukan ‘yan jarida ta ƙasa, da ƙungiyar editoci, da kuma ƙungiyar ‘yan jarida ta NUJ, har ma da masu sharhi da rajin cigaban aikin jarida a Nijeriya sun daɗe su na gwagwarmayar wayar da kan hukumomi game da muhimmancin samar da tsarin da ya dace ga ‘yan jarida, amma har yanzu a iya cewa kwalliya ba ta kai ga biyan kuɗin sabulu ba.