Sunday, October 3, 2021
DAN MINISTER Page 1 to 10
Share this
Saturday, October 2, 2021
Ko duk duniya za su guji Maryam Yahaya, ni ba zan guje ta ba – Cewar Maryam KK
Fitacciyar jaruma Maryam Yahaya na daga cikin jaruman da suka fito suka nuna kishin su kuma ta nuna murnar ta da zagayowar wannan rana, kuma jarumar tayi hakan duk da cewa tana fama da rashin lafiya, amma dai alamu na nuni da cewa sauki ya fara samuwa.
Kawarta da suka saba hotuna tare a irin wannan rana jaruma Maryam KK ta nuna rashin jin dadinta kasancewar abokiyar ta bata da hallin raya wannan rana tare da ita a wannan shekara.
Wannan dalili ya sanya ta wallafa hotunan kawartan na shekarar da ta gabata gami da wasu kalamai masu ratsa zuciya.
“Ko duk duniya za su guje ki ni bazan guje ki ba domin ke yar uwa ta ce musulma kuma cuta ba mutuwa bace kaddara da jarabawa bata wucewa kan kowa ✊🏽”
Sai dai bayan wasu lokuta Maryam Yahaya ta lallaba tayi hotunan murnar samun yancin kai duk da halin rama da rashin karfin jiki da take fama dashi.
Jim kadan da wallafa wadannan hotuna na ta masoya da ‘yan uwa da abokanan arziki suka yi ta sanya albarka kuma suna yi mata addu’ar samun lafiya kan wannan rashin lafiya da ta shafe tsawon lokaci tana fama da ita.
A wani rubutu da fitaccen marubucin nan na shafin sadarwar Facebook, Datti Assalafiy ya wallafa a shafinsa na, ya caccaki masana’antar Kannywood, kan halin da suka sanya fitacciyar jarumar nan Maryam Yahaya, wacce a yanzu haka ke kwance a gida babu lafiya.
A rubutun da ya wallafa Datti ya bayyana cewa jarumar ta shafe kusan watanni uku tana kwance cikin matsanancin hali, inda ya ce yanzu haka ko waiwayenta mutanen da suka sanya ta cikin wannan hali ba sa yi.
Ya ce saboda mawuyacin halin da ta shiga ya sanya ba zai iya bayyana irin rashin lafiyar da take fama da ita ba.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.
Share this
Aisha Dan Kano ta tafi ta dawo, yadda Zee Dan Kano ke shirin maye gurbin mahaifiyar ta
Kamar yadda bayan rasuwar Marigayi Rabilu Musa Ibro, dan sa mai suna Hannafi Rabilu ya daura damarar maye gurbin sa, alamu na nuni da cewa marigayiya Aisha Dan Kano ma za ta iya samun mai gadon ta idan hali ya yi.
A ‘yan kwanakin nan wasu bidiyo suka fara yawo a shafukan Instagram da tiktok na wata matashiya mai tsananin kama da Aisha Dan Kano, wacce ke yin koyi da muryar ta.
Kamannin wannan matashiya mai suna Zee Dan Kano dana marigayiya Aisha Dan Kano ya yi yawa sosai, inda hakan ya sanya ya dauki hankulan al’umma suka dinga mamaki, sai dai kuma bayan bincike da Tashar YouTube ta Tsakar Gida ta yi ta gano cewa Zee diya ce ga marigayiya Aisha Dan Kano.
Duk da dai Zee ba ta nuna ra’ayi na maye gurbin mahaifiyarta ba alamu na nuni da cewa inda za ta yi hakan za ta bada kwafin mahaifiyarta kwabo da kwabo, sai dai kuma mafi yawan tambayoyin da ake yi mata a shafin ta kan za ta fara fim ne? ba ta bada amsa ba.
Amma tambayoyi da suka shafi dangantakarta da Aisha Dan Kano, ta bada amsa da cewa mahaifiyarta ce, inda mutane da dama suka dinga addu’ar fatan rahama ga mahaifiyarta.
Ga kadan daga cikin bidiyon ta:
Share this
Friday, October 1, 2021
Maryam Malika – Raina na matukar baci idan naji ance matan Kannywood basa iya zaman aure
Fitaciyyar jaruma Maryam Malika, wacce kanwace a wajen marigayiya jaruma Balaraba Muhammadd ta samu tattaunawa da BBC Hausa, a cikin shirin da suka saba gabatarwa na “Daga Bakin Mai Ita”.
Jarumar ta samu damar amsa tambayoyi masu yawa, wadanda suka shafi sana’ar ta da kuma rayuwarta, inda a cikin amsoshin da ta bayar ta bayyana cewa babu ranar da baza ta taba mantawa da ita ba, kuma ranar da tafi kowacce farin ciki a rayuwarta kamar ranar daurin aurenta.
Haka kuma jarumar ta bayyana cewa kalmar da aka sanar da ita da tafi kowacce yi mata dadi a rayuwa ita ce kalmar da mijin da ta aura ya fada mata, wanda ya bayyana mata da aure yazo neman ta ba da wasa ba.
Maryam Malika da Balaraba Mohammed
Balaraba Mohammed da kanwarta Maryam Malika
Hakaa zalika Maryam ta bayyana cewa kaddara ce ta raba ta da mijin ta, haka kuma bata da burin da ya wuce ta samu wani mijin na gari ta aura.
Bayan haka kuma Maryam Malika ta bayyana rashin jin dadin ta kan yadda mutane ke zagin ‘yan fim da kumaa tada cece-kuce kan basa iya zama a gidan miji, inda ta ce addu’a ya kamata su yi musu ba maganganu marasa dadi ba.
Ta ce ta dawo harkar fim ne saboda mutuwar aurenta, wanda hakan ya faru ne ba wai a son ranta ba, ta ce yanzu babban burinta shine ta sake samun miji ta yi aure kamar kowacce ‘ya mace.
Maryam Malika ta ce mutane da dama suna yi mata kallon ita masifaffiya ce, inda ta ce suna cewa daga ganin idon ta bata da kunya, saboda idonta a tsaitsaye yake, ta ce kwata-kwata ba haka take ba.
Malika ta ce abin bakin ciki daa baza ta taba mantawa dashi ba a rayuwa shine, lokacin da kanwar abokin mijinta ke yin aure, suka je biki, lokacin da zaa a kai amarya, ‘yan uwanta suka taru za su kai ta, abinda ya bata mata rai shine, ita bata da su, ta ce a lokacin tana tunanin da yayarta Balaraba na nan da ita ma haka za ayi mata.
A wata hira da BBC Hausa ta yi da tsohuwar jarumar Kannywood Sadiya Kabala, a cikin shirin su na ‘Daga Bakin Mai Ita’, Sadiya ta amsa tambayoyi da dama bisa ga yadda shirin yake, an yiwa tsohuwar jarumar tambayoyi da suka shafi sana’arta, rayuwar ta, da dai sauran su.
Sadiya Kabala ta bayyana mutuwar auren da tayi a garin Jos, wanda a cewar ta akwai wani abin bakin ciki da ya faru wanda har ta koma ga Allah ba za ta taba mantawa da shi ba, inda hakan bai rasa nasaba da irin rabuwar da suka yi da mijin bayan wata biyu zuwa uku da yin auren.
Idan ba a manta ba, jim kadan bayan mutuwar auren ta, Mujallar Fim ta yi hira da tsohon mijin na ta, inda a cikin hirar ya bayyana cewa Sadiya maza take kawo masa gida shi yasa ya sake ta.
Sai dai wannan labari ya dauki hankulan mutane matuka, domin kuwa jarumar tayi ta jin maganganu daga bakin mutane kala-kala marasa dadi, yayin da wasu kuma ke ganin laifin mijin na yi mata bita da kulli bayan saki ya bita da bata suna.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.
Share this
Innalillahi Wainnailaihir Raji'un Adam A Zango da Ado Gwanja Suna Bukatar Adduar ku
Innalillahi Wainnailaihir Raji'un Fitactun Jaruman nan kuma Mawakan Kannywood Sun hadu da Iftila'i A Hanyar su ta Zuwa Kasar Nijar
Suk da Jaruman Basu bayyana me ke faruwa ba ko wani hali suke ciki, Sai dai Jarumi Adam A Zango Ya wallafa a shafinsa na istagram inda yasa
Share this
Sabon kace-nace ya balle a shafukan sadarwa kan sabuwar wayar iPhone 13 ta Ummi Rahab
Sabon kace-nace ya balle a shafukan sadarwa kan sabuwar wayar iPhone 13 ta Ummi Rahab, wannan na zuwa ne jim kadan bayan dambarwar da ta faru tsakaninta da tsohon uban gidanta Adam A Zango.
A makon da ya gabata ne dai kamfanin Apple suka fitar da sanarwar fito da sabon samfurin wayar iPhone 13, wanda aka karade shafukan sada zumunta da zancen zuwan wayar wacce take da nau’i uku.
Farashin wayar ya daga N460,000, zuwa N930,000, hakan ya danganta da kasuwa da kuma irin yanayin wayar da mutum ke so.
Tuni dai mutane suka fara rububin sayen wayar duk da tsadar da take da ita, ga kuma ganin cewa ko shekara ba a cinye da kasuwar wayar kirar iPhone 12 ba, wacce a yanzu ta zama tsohon yayi.
Ummi Rahab na daya daga cikin jaruman Kannywood da suka fara mallakar wannan tsaleliyar waya, inda ta wallafa hotonta da bidiyo a shafinta tana murnar samun wayar.
Sai dai wannan bidiyo da ta wallafa da hoton waya, ya raba kan mabiyanta, inda wasu ke fatan alkhairi, wasu kuma na maganganu marasa dadi ga jarumar.
Idan ba a manta ba ko a lokacin da dambarwar da ta faru tsakanin ta da tsohon uban gidanta kuma masoyinta Adam A. Zango, bayani sun nuna karbar irin wannan manyan kyautuka na wadanda kudi da mota na daga abin da ya fara haddasa sabanin a tsakanin su. inda wannan yasa masu goga mata magana suka samu abin fada.
Ummi Rahab
Ummi Rahab rike da sabuwar wayar iPhone 13 – Photo: Instagram