Thursday, October 7, 2021
Pherty tace"hmm bara nakawo muku abinci
Baran ma kai gauro".
Amsard yayi murmushi tare da fadin"ai sai nabaku mamaki domin inna tashi hudu zan jera".
Usman yace",kaga nima nasamu damar kara daya.Daga karshe yakarasa da dariya".
Pherty tagallawa usman harara tare da fadin"kanku dai akeji tayi tafiyarta".
Usman yace"kaga har nakashe mata baki".
Dukansu suka sheke da dariyar mugunta.
Bayan wasu yan mintuna sai ga pherty tadawo dauke da abinci.
Tafara zuba musu tuwon shinkafa ne sai drinks din abarbA.
Bayan ta zuba ne tace"oya su malam gauro azo aci abinci kai kuma honeyna ga namu nan".
amsard yace"aiko indai hakane kuci kayanku tunda ni wareni za'ayi kuma in baki kama kafa dani ba sai nasa ankaro miki biyu."
pherty tayi dariya sannan tace haba yayana nasan barakamin haka ba.
Kumama ni wasa nake ga abincin ku nan kuci".
Usman da amsard suka saka dariya tare da cewa" dole amana biyayya".
pherty dai dariya take domin tasaba da zolayar sa.
Sai da sukaci suka k'woshi sannan Amsard yace"bara yatafi hotel domin aceb zai kwana".
Usman yace"kai haba abokina mu kwana anan mana ga dakuna anan ".
Pherty mah tace"haba ya amsard ka tsaya anan mana".
Amsard yace"kwaji dashi dai domin nasan azuciyarku kunata sauri natafi neh".
Pherty da usman suka fashe da dariya.
Sannan usman yace" baka dai son kwana ne kawai".
AmSard yaCe"hmm wallahi inada wani aikine kuma nafison nasami nutsuwa nikadai".
Pherty tace"kodai za agun yayata kuma kawatace?.
amsard yace kedai sai ahankali nalura damuwar ki kawace kawai kuma kinkusa samu na huta".
Pherty tayi dariya sannan tace "aiko da ka huta sosemah".
usman yace"gobe dai ka fito da huri to damin mukarasa da sauri".
Amsard yace"insha Allah kuwa .
Usman ya"Allah yasa".
Tare da fadin Ameen dukansu".
Sannan sukayi sallama cokin farinciki da begen juna.
Da fitar Amsard yanufa hotel domin sai sukayi sallah tun askul.
**************
Aban karaen fayal kuwa har yanzu tana nan da kudurinta azuciya.
Sai kitse kitse take ta hanyar da zata rama abin da Amsard yamata.
misalin karfe bakwai na dare dadyn fayal ya iso gida .
Dashigowarsa yaga momy da Amnah neh kadai afalo .
Bayan yayi sallama sun amsa suka masa sannu da dawowa.
Sannan yaduba Amnah yace "ina kawartaki neh ko yauma yan abun sun motsa ne?
Amnah dai tayi murmushi sannan tace" tana daki".
sannan momy ta kwashe duk abinda yafaru tsakanin fayal da lecture ran su .
Kwatakwata dady bai ji dadin abin da yar tasa ta aikata ba.
DAn haka yace"amnah ta kira masa fayal .
Bayan taje kiranta ne suka tawo tare.
Fayal tageshe da dadynta sannnan yafaramata magana".
fayal gaSkiya yau banji dadin abin da kika aikata ba.
kinsan dai karatu ba abin wasa bane ko?.
Banaso inkarajin wani makamancin hakan yafaru ".
Fayal ta sunkuyar da kanta domin jin fadan dadynta.
sai da yamata fada meshiga jiki sannan ta d'ago tace" masa ta godE tare da alkawarin insha Allah barata karaba".
Dadynta yaji dadin hakan sannan yasamusu Albarka ita da Amnah .
sannan sukaci abinci tukun kowa yakoma daki domin kwanciya.
*WASHE GARI*
da safe amsard yafara shirin tafiya skul .
Su fayal ma sun shirya.
Atare suka isa skul motar su fayal nagaba ta Amsard kuma abaya .
Fayal takinta take yadda tasaba kamar ba titi tahau ba.
AMsard yanata horn Amman duk da haka fayal ta kara gudun motarsu ba .
Ran Amsard ya matukar baci dan haka yatsaya da tukin domin ganin kosuwaye zasu fito amotar nan.
Tsayuwarsa kedawuya yaga anyi paking .
*WA zai gani?*
*WAni mataki zai dauka?*
*PAGE* 13,14.
---------------------------------------------------------
Fitowar Fayal kenan daga mota .
Tana yatsina fuskar nan kaman yadda tasaba.
Amsard kawai tsayawa yayi domin abin mamakima yabasa"wato ma abin yarinyar nan har yakai haka!.
Yake fada azuciyarsa.
ita kuwa batamasan dawani abayanta ba tafiyarta take cikin isa da k'asaita.
Amsard yafito shima sannan yanufa wajen usman.
Dazuwansa bayan sun gesa da usman sai yace"usman wai dama haka yarinyar nan take?.
Ita yar wayema wai agarin nan?."
Usman yanunfasa sannan yace"hmm daga maganar nan take nagane wa kake nufi
Domin nasan inba fayal ba ba wace zata nemi b'atama rai".
Haka take kuma wallahi karkayi tunanin wai iyayen ta ne suka goyamata baya domin wulakanta mutane.
Aa ba haka suke ba domin su kullum fatan ta gyaru suke domin su kansu basa ganewa halayenta ".
Karkaji mamaki innacemaka bata da samari domin ita aganinta soyayya bakomae bace bace wahala .
Batasan cewA *BABU RUWAN SO* ba ita tadaukesa amatsayin shirme".
Amsard ya nunnfasa tare da fadin"hmm A lallai wannan tacika miskila duk miskilancin dasu momy sukecewa inadashi insuka wannan yarinyar sai sun sara mata.
Domin komai nata nadaban ne .
Amman insha Allah ni nadau Alkawarin sai na chanja mata hali kai dama rayuwarta ta gaba daya".
Usman yayi murmushi sannan yace"anya kuwa abokina baka fada ba?".
Amsard ya sheke da dariya sannan yace "haba kai kam usman me zanyi da ita kawai dai inaso na nuna mata *BABU RUWAN SO* ne.
Sabida takiyaye wulakanta masu sonta".
Usman yace"aa fa dai kar azo daga baya akamu kuma".
Amsard yayi murmushi'sannan yace kadai ka tsaya kaga dramar nan .
Domin yanzu za,a fara".
usman yace"toh shikenan fatan alkairy nakewa abokina".
Amsard yacewa usman"yagode sannan yakarasa maganar dacewa su tashi su tafi domin fara aikinsu".
ita Kuwa fayal tine taje tasamu waje tazauna sai alokacin Amnah kecewa"fayal kinsan kuwa dazu wannan lecturern abayanmu kuwa kikaki matsa me"?.
Fayal ta dago sannan taja dogon tsaki tare da cewa"ai gwanda haka indai ko shine yanzu yafara ganin abubuwa kala kala sai randa yabar makarantar nan zai rabu da jarabawata".
Amnah batasan sanda ta shek'e da dariya ba sannan tace"lallai ynzu kinaso ki taro wanda yafi karfinki, anya ma kin kallesa Da kyau kuwa?.
Fayal tace"toh uwar kalle kalle ni me zan kalla ajinkisa me yake dashi".
Amnah ta karAshekewa da dariya sannan tace"amman gaskiya zanji dadin wannan dramar taku .
Za,asha kallo awanga makaranta.
Fayal tace"kyaji dashi dai nikam wlh duk akan mutumin nan kwanann sai magana nake mtsww".
Ita dai Amnah dariyar ta take domin taga tun ynzu yar uwarta ta tafara magana inaga in aka fara dramar?.
Hmmm kallo nagaba kubiyoni danjin yadda zata kaya.
Amsard ya usman sun shiga domin fara practical.
Shigarsu keda wuya kawai Amsard yaga fayal azaune .
Abin yabasa mamaki azuciyarsa yace"toh yar girman kai yau anzo kenan.
Sunfara practical dinsu cikin nutsuwa ita kanta Fayal sai dataji farinciki tanata tunani ashe fa jiya tayi missing sose,wata zuciyar kuma tace sai me? mtsw".
Suna kammalawa fayalce tafara fita aiko da amsard yaga haka sai yayi sauri yabita.
Tashiga mota tanajiran amnah .
Shiko Amsard yana zuwa yahau motarsa sannan yasha gaban tata.
Fayal tace"owk wato mutumin nan adole shima so yake ya rama abinda name dazu ko?
Alallai naga alamon cewa bai san wacece fayal ba,
Amman yaro kakusan sanin ni wacece yadda inma kaganni barakaso karasawa inda nke ba balle ka kalleni".
Tana maganar nan Amnah nashiga motar aiko ta figa motar da gudu.
Amsard yana ganin haka shima yafara gudu.
Fayal tayi tayi yadda zatayi ta huce Amsard Amman takasa gashi daman ita ba iya gudu sose tayi amota ba.
Aiko ananne ranta yakara baci batasan sanda ta figi motar da mugun guba.
Aiko karaf sai gashi tayi gware da motar Amsard .
Amnah tun tana magana tana ta"haba fayal kiyi ahankali mana ko kibani nayi driving din.
Duk magiyar nan da Amnah tayiwa fayal Amman bata saurareta ba hasalima batasan me take BA.
Aiko amnah naganin sunyi karo da mota ba abinda take fada sai" innalillahi-wa'inna -illaihir-raji'un".
Ita kuwa fayal ko numfashima batayi bare motsi.
Shiko Amsard yabuga kansa ajikin madubin mota kansa sai zubar jini yake.
Amnah gaba daya tarasa ta yadda zata fara dominga fayal nan kwance ko motsi babu .
*PAGE* 15,16
-------------------------------------------------------------
Dasauri Amsard yafito amotarsa domin duba motar su fayal.
Yna zuwa yaga Amnah sai kuka take tana salati.
Dasauri yataimaka mata suka fito da fayal .
Sannan yakaita motarsa domin daman shi ba abin da yasami motar tasa sai dai kansa dake zubar da jini.
Tuki yake Amman duk hankalinsa baya jikinsa gabadaya ya rikice kawai tuk'i yake.
Da isarsu asibiti akazo domin awa fayal taimakon gaggawa .
Sannan shima Amsard yaje aka me treatment din kansa.
Ita kuwa Amnah ba abinda yasameta dan haka ta kira momy awaya domin sanar da ita halinda ake ciki.
Aikuwa da fadarta momy tace"gatanan zuwa ".
Bajimawa sai ga momy ta iso adaidai wannan lokacin kuwa fayal ta farfado.
Momy tashiga dakin tasamu fayal da Amnah tace"wai ya akayi haka neh?.
Amnah tabude baki zatayi magana fayal tamata alama datayi shiru.
Aiko Amnah tayi tsit domin tasan halin fayaL.
Fayal tace"uhymm momy wata motace abayan mu tana gudu nikuma kinsan ban iya gudu ba shine fa kawai mukaci karo".
Momy tace"hmm toh shikenan dai Allah yakyauta abinma yazo da dan sauki".
Amnah tace"Ameeen".
Fayal kuwa tayi dogon numfashi domin ta tsira da kyar dan tasan in momy tasan gaskiya bazataji da dadi ba.
Doctor yazo yaduba su sannan yace" ga takardar sallamarsu nan angama komai".
Momy tace"toh ai ban biya ba ".
Doctor yace"ai wanda yakahosu ne yabiya".
Momy tace"owk ko zan iya ganinsa?.
Doctor yace"a'a ai ankirasa wai yana sauri shiyasa ma bai tsaya muku sallama ba".
Momy tace"owk to mungode Allah yabiya".
Suka kare dacewa"Ameeen".
momy ko dady bata kira ba suka tattara suka nufa gida domin fayal ta dan warware.
Shiko Amsard yana tafiya ashe managen sa na chan malesia ne yakirasa domin wani aiki na gaggawa wanda dole sai da shi abin zai tafi dai'dai.
Su fayal na tafiya Amota Amman kwatakwata hankalinta baya jikinta gaba daya tunanin irin wulakacin da zatawa Amsard take.
Batama jimamin jikinta sai wani jarabar datake tarawa.
Ita aganinta ma wato ya rainasu ne da har zai biya musu kudin asibiti.
Watomah yadaukesu matsiyatane ko?.
Hmmm duk dai wannan maganar datake ta zuciya ce dan haka babu me bata Amsa.
Amsard sauri sauri yake yakira usman yace masa"su hadu a airport domin ko katsina bazai koma ba malesia kawai zai huce" .
Shiyasa yace"yazo yakarba motar .
Aiko nanda nan sai ga usman yazo.
Usman yace"kaiiii Amman gaskiya banji dadin abunnnan ba nida naketa shirin kallon dramar miskili da miskila".
Amsard yayi murmushi sannan yace"oh yaro ai kabar dadi tun yau mukafara dramar kuma gashi kayi missinh" .
Usman yace"oh haba dai abokina bani labari mana".
Amsard yaduba agogon hannunnsa sannan yace kaga yanzu jirginmu zai tashi kabari sai munyi waya koma hadu a whatsApp.
Kuma ma ai ba dadewa zanyi ba karka damu kakusa zama drectorn dramar mu".
Usaman yashek'e da dariya hade da cewa"lallai kam toh adawo lafiya actor na actress".
Shima Amsard yayi dariya sannan yace"toh sai na isa kajini ko?.
SUKa gesa tare da yin sallama.
Amsard yahau jirginsu suka tashi.
Yayinda shima usman yahau motar domin komawa gida.
SU fayal sun isa gida adai dai lokacin da daddy yadawo .
Fayalce tafara fitowa tare da Amnah data rike mata hannu.
Daddy abin ya razanasa domin bai san meke faruwa ba kuma gashi yaga yarshi ba dai dai ba.
DAddy yace"fayallllllllll kala..... sai da yaja numfashi sannnan yakara cewa"fayal kalau kuwa?
*PAGE* 17,18
----------------------------------------------------------------------
Daddy yazo yatallafawa fayal domin shiga cikin gida.
Suna shiga ya kwantar da ita akan kujera domin ko bed room basu karasa shiga ba afalo suka tsaya.
Bayan yan wasu daki k'u ne daddy yaja numfashi sannan yacewa momy"wai ya akayi ne? meyafaru?".
Momy itama sai da taja mufashi sannan ta kwashe duk abinda yafaru ta fadawa daddy.
Daddy yadanyi murmushinsu na manya sannan yace"kice ma abin yatsageta kennan kuma gashi ansamu dan albarkan yaro .
Domin na tabbatar da wasu ne guduwa zasuyi".
Momy tace"wallah kuwa ninaso ma nagansa domin namasa godiya amman ba dama".
Daddy yace"ai nima inason ganinsa insha Allah duk randa Allah yayi zan gansa sai name halallaci kamar yadda yamin".
Ita dai fayal jinsu take Amman zuciyarta cike take da bak'in ciki .
Ita kuwa Amnah suna zuwa tayi kichin domin daurA musu abinci.
💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖
Amsard ya isa malesia lafiya da isarsa bai nufi ko ina ba sai Amsard special hospital .
Yana isa managen sa yazo yamasa bayanin komai.
Ashe wata yarinya aka kawota sunyi hatsari gaba daya namomin kafarta sun fita sai jijiyoyi kawai ake hangowa.
Sannan kuma yar Nigeria ce ankasa aikin ananne aka turasu malesia.
Batare da bata lokaci ba Amsard yaje yayi wanka sannan yayi sallah yana idarwa yaci abinci sannan yasaka kayan aikinsa.
Sukaje domin farawa yarinyar nan aiki.
Batare da bata lokaci ba yafara aikinsa cikin zafin nama da kwarewa.
Aiko aikin nasu da alamon nasara aciki domin kosu yan malesia sai da suka jinjina masa.
*KATSINA*
Gidan su Amsard.
Sahalace tabiyo sameer da gudu tana fadin"uhymmm hajiya momy kice yabani abuna".
Sameer yayi sauri ya dane ajikin hajiya momy yana fadin"uhymm hajiya momy nawane fa ba nata ba ".
Hajiya momy tayi murmushi tare da fadin"kai sameer fa kaine babba kabawa yar kanwarka Aro mana".
Sameer yace"uhumm to gashi kuma in bro Amsard yasiyomin kayan wasa bazan baki ba ".
hajiya momy tace"oh kun tunamin mah bara nakirawosa.
Domin yacemin zai koma malesia Yau.
Momy taceWa sahala tadauko mata wayarta domin ta kira Amsard.
Sahala tadauko sameer yace"ai shi zai kira Amsard tindama bros dinsa ne".
Sameer yakira Amsard har sau ukku bai dauka ba.
SAhala sai dariya take masa.
Momy tace"rabu da ita sameer dina inaga aiki yake kuma ma nasan inyadawo zai kiramu".
Haka dai hjy momy tata fama da rigimarsu sahala.
Har daddy yadawo sannan tasamu sauki suka koma kansa.
💖💖💖💖💖💖
Amnah tagama abinci sannan tayi sallah aka taimakawa fayal ma tayi sannan suka zauna domin cin abincin.
Daddy sai jan fayal yake da magana Amman samm taki .
shiko da hike yasan halinta bai damuba domin yasan koda lafiyarta kalau ba sakewa zatayi ba inaga bata da lafiya.
Dakyar fayal tadan chakali abinci sannan suka tashi sukayi sallah .
Kowa yayi bed room dinsa.
💖💖
Abangaren AMsard kuwa sai yanzu yasami kansa .
Bayan yayi sallahne yaduba wayarsa yana dubawa yaga missed call din hjy momynsa.
AIKO batare da bata lokaciba yakirata .
Sameer ne yafara dauka suka gesa sannan yabawa sahala suka gesa.
BAyan su gama masa shirmensa ne suka bawa momy wayar .
DASuka gesa hjy momy tace"dazu kar dai har kunfara aikine?".
Amsard yafadawa hjy momy duk abinda yasami yarinyar nan
Hajiya momy ta matukar tausayawa yarinyar nan.
SUKayi sallama sannan kowa ya kwanta.
*PAGE* 19-20
------------------------------------------------------------------
*WASHE GARI*
su fayal suntashi da huri domin tafiya scul
Domin daman yau ne zasu gama practical dinsu.
Bayan sun kammala komai sunyi wanka sannan suka shirya cikin shiga iri daya bak'a doguwar riga tare da farin gyale farin takalmi da farar jaka.
Amnah ce kadai ta tsaya yin kwalliya duk da dai bame yawa tayi ba itako fayal daman ba yi take ba iyaka karshen kwalliyarta shine tashafa farar hoda da farin manbaki.
Amman duk da haka kyanta kara fitowa yake sai kaga kamanma intayi kwalliyar muni zatayi.
Bayan sungama shirine sukayi breakfast karfe takwas daidai sannan suka nufi mota domin fayal jiki yayi sauki sose kaman ba ita bata jiya ba lafiya.
Amnah ce ke driving dinsu itako fayal sai tunanin abinda zatawa Amsard yau take.
Da isarsu makaranta akace musu ae yau lecturern bazai samu damar zuwa ba yayi tafiya so dole sai yadawo sucigaba.
Dan haka ynzu zasu cigabada lectures ne.
Ita dai fayal bataso haka ba domin kuwa yau taxomasa da tsarabar rashin mutunci ita practical dinma bai dame taba akan shirinta daya baci.
Fayal tacewa Amnah"kinga fa mutuminnnan baida mutunci fa".
Amnah tace"haba fayal yanada uxurine fa".
Fayal taja tsaki sannan ta huce ajinsu.
Sannan Amnah tabi bayanta.
💖💖💖💖💖💖💖💖
*malesia*
Amsard ne zaune adakinsa yafito DAga wanka yashirya cikin kananun kaya bak'in wando bluen riga sannan yasaka glass dinsa na likitoci.
Ankawo masa abincinsa sannnan yaci .
Bayan yagamane yadauko wayarsa yakira usman.
Bayan sun gesane usman yace"yauwa yallabe bani labarinku kai da madam".
Sai da Amsard yaja numfashi domin shi harma yamanta dawata wai fayal.
Sannan yace"kai dai baka mantuwa wallah".
Usman yasheke da dariya sannan yace"eh din naji nidai abani labari".
Amsard yakwashe duk abinda yafaru tsakaninsa da fayal yafawa usman.
*PAGE* 21,22
-------------------------------------------------------------------
Bayan yagama fadawa usman abin dayafaru tskaninsune.
Usman yace"oh Allah dai yakiyaye gashi yanzu baka da numberta balle muji yajikin"
Yakarasa maganar tare da dariyar mugunta.
Amsard yace"kai kama sameni wallahi yaushe zan karba number wannan jaririyar ai kabari kawai sai na nuna mata *Babu ruwan so* alokacin ne zata nemi numberta kai yarma dani gabaya".
Usman yakara dariya sannan yace"kaiiiii oga adaiyi magani awannan miskilancin naka".
Amsard yace"hmm usaman kennan karka damu kabi dramar nan asannu zatazo karshe bakaji yadda bature yake cewa *wonder shall never end* ba dan haka karkayi mamaki daga karshe"
Usman yace"toh shikenan oga Allah dai yaba da sa'a dawasa wasa hakan yazama gaskiya yatashi daga drama".
Amsard yace"kai dai baka da damuwa wallahi gwara kai ma bara natashi domin zamu shiga aiki".
Usman yace"toh yaushe zaka dawo neh?
Amsard yace"wallahi daga zuwana har aiki yamin yawa Amman karka damu inaga jibi nazo".
Usman yace"owk Allah yakaimu".
Amsard ya amsa da "Ameeeen".
Sukayi sallamah sannan kowa yayi wajen aikinsa .
💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖
Lectures akema su fayal Amman ita gaba daya hankalinta baya jikinta sai tunani take .
Ita kadai sai yatsina fuskarnan take .
Abinda akasaba bara adaina ba dai.
Tun 8 suka shiga lecturers Amman sai 4 akabarsu sufito domin sallah hada azhar da la'asar sukayi.
Fayal sai mita takeyi akan anki bari su huta itako Amman sai dai ta kalleta domin ita tariga tasaba da hali irin na fayal.
Aiko suna idarwa ba abarsu sunci komai ba suka koma lectures .
Gaba daya sun galabeta sai wajen 6.10pm suka fito wasu masallacinma har Anfara kiran Sallah.
Suna fitowa suka nufi motarsu domin komawa gida bashiri Fayal tamikawa Amnah key din motar domin acewarta tagaji bazata iya komai ba.
Aiko Amnah gudu take Amotar domin ita kanta tagaji ga azababbiyar yunwa Anhanasu ko cin abinci.
Suna isa megadi yabude musu get suka shiga sannan Ammnah tayi paking fayal ko daukan jakartama batayi ba tashige gida .
SAi Amnah ce ta dibomusu dukansu.
Fayal tanashiga tayi sallama tageshe da momy daga nan bata kara cewa komai ba tayi cikin dakinsu.
sannan Amnah tashigo da sallamarta bayan sun gesa da momyne .
Momy tace"sannu da alama yau practical din yabaku wahala".
Amnah tace"ai bama practical din mukayi ba domin lecturan bai zo ba.
kinsan mun kwana biyu ba lectures shiyasa yau muka dadde".
MOmy tace"owk toh sannun ku nima yau aiki yamin yawane wallahi sai yanzu nashigo naga bakwanan gashiba abinci".
Amnah tace"to bara nadaura mana momy".
Momy tace"kema fa kingaji da kin huta kawai anyi ordering ".
Amnah tace"A'a momy kinsan fayal batacin abinci waje bara kawai nayi".
Momy tace"oh Amnah kincika san sisternnan taki ".
Amnah tayi murmushi.
MOmy tace "to dai Allah yayi muku Albarka kuma Allah yakaramiki hakuri da juriyar zama da fayal".
Amnah ta Amsa da Ameeen .
SAnnnan ta tashi tashiga daki tacire kaya tasa wasu tayi sallah tukun tashiga kichin.
Batare da bata lokaci ba ta fere doya sannnan tawanke tukun tasa atukunya ta daura agas .
BAyannnan tayi gretin din kayan miya tafara soyawa ba mai bayan yadan soyu tazuba kwai.
Kafin tagama miyar har doyar tayi dashike agas neh.
Bayan takammala doya da miyar sos ne tukun ta hada musu fruit salat.
Tana kammalawa anakiran sallar isha tuni taje tayi wanka sannan tadawo domin shiryamusu abinci a dainin.
💖💖💖💖💖💖💖💖
Amsard yana cikin aiki chuku chuku har yanzu dai anata fama akan kafar nan duk da alamun sun fara samun nasara.
*PAGE* 23.
-------------------------------------------------------------------------
sai karfe 10pm su amsard suka samu fitowa daga dakin ofireshon .
Suna fitowa yanufi gidansa sannan yayi wanka tukun ya gabatar da sallah.
Yana idarwa yanufi kicin domin shi inba girkin hajiya momy ba gwara yayi da kansa inkaga Amsard yaci abincin waje to fa ba yadda ya iyane.
Dan haka bai damu da gajiyar dake jikinshi ba yafara aiki .
yadaura sanwar wake sannan yadaura shinkafa adayan gefen gas din .
sannan yakoma yafara gretin din kayan miya.
Batare da bata lokaciba shinka far nan suka tafaso dan haka yasauke su duka sannan ya wanke .
Ya zuba su a abin tsamewa .
Yadibo kayan miyannnan yasa atukunya asoyasu sose da manja sannan yazuba su kayan dan'dano .
Bayan yazuba ruwan yatafasa sannan yasa su shinkafa da waken nan.
yatafi fallo domin huta wa bai fi 40minit ba aiko yafara jin kamshi alamun abincinsa yadahu
Yaje yasauke sannan ya samo plet yasa .
yakoma falo.
Sannan yake firish dinsa yadauko drinks na lakaseraH
Yazauna dominci.
Arayuwar Amsard acikin abinci ba wanda yakeso fiyeda dafa dukan shinkafa da wake.
Adrinks kuma lakaserah.
Shiyasa ba ya kyashin yima kansa girki komai dare.
*PAGE* 24,25.
-----------------------------------------------------------------------
Amsard yagama abincinsa yaci kuma sannan yayi lafila tukun ya kwanta barci.
Suma su fayal sunci abinci tukun sukaje kwanciya.
Anan ne fayal take ta tunin Amsard dayaki zuwa azyciyarta tace kodai ma tsoro yajine yace zai tafi wajen aiki ana nemansa tana ta tunani dai iri iri daga karshe kuma tace"toh ma ina ruwana dashi mtsw".
Batasan maganarma tafito fili ba sai ji tayi Amnah ta shek'e da dariya .
Sannan tace "aiko da ruwanki tunda kina tunaninsa".
Rain fayal yabaci dan haka taje dogon tsaki sannan ta kwanta.
Sai tajima ita kanta haushin kanta take.
****WASHE GARI******
💖💖💖💖💖💖💖💖
Da Asusuba Amsard yatashi yayi sallah sannan yayi wa kansa breakfast .
Yayi wanka sannan yashirya tukun yayi break kafin 7 har ya kammala komai nasa sai tafiya asibity.
Da isar sa asibity akasanar masa Da ai feshen din sa ta farka .
Aiko yayi farinciki da jin hakan .
Batare da bata lokaciba yaje yaduba sannan yamata tambayoyi tukun yakoma office dinsa.
yau gaba daya fayal ta tashi jiki ba kwari ita kanta batasan meke damunta ba ita dai kawai taji jikinta ba kWAri .
Dan haka tanayin wanka ta zumbula doguwar riga sannan ta dauko hijab da glass dinta tasa .
Ko breakfast dinma takasa yi su momy sun tambayeta menene Amman sai dai tace musu bakomai.
Tun suna tambayarta har suka gaji sukayi shiru.
Ahaka suka tafi skul itada Amnah .
Fayal sai faman tsaki take wanda ita kanta batasan dalilin hakan ba.
Ita kuwa Amnah me zatayi banda kallo .
Azuciyarta kuwa cewa take"da alamu kinkusa chaza hali mu huta dan inAga kinkusa fadawa tarko".
Afili kuma tayi murmushi abinta.
Fayal ko sai sake yamutsa fuskarnan take ga tsaki.
Ahaka suka isa skul ba mai wa wani magana .
duk da dai daman hakan dabi'ar fayal dince .
Amman nayau din yafi nakullum.
Sun isa skul wajen 8 dan haka har anfara lectures ma Amnah tashiga sannan tace"excuse sir".
Sai da yabata izinin shiga tukunna tashiga .
Ita kuwa Fayal batama fito amotar ba sai ynzu duk da tasan sunyi letti Amman ko ajikinta .
Tafiya take kamar bazata taka kasa ba .
TaNa zuwa tashige lecture room din ko sallama babu.
Shiko lecture yace"tafita mai a aji tabari sai takoyo sallama tukun tadawo.
Aiko hakan ko ajikinta Dan hakama yasa tacigaba da tafiya kamar wadda kwai yafashe mata aciki.
kowa yakoma da kallonsa gareta ahaka har tabar ajin.
shiko lecturern sai da yazabga tsaki sannan yace"wallahi duk mace me irin wannan halin tausayima ni take bani gwara ku gyara halayenku ku huta.
Sannan yacigaba da lectures dinsa.
Amnah azuciyarta kwatakwata bataji dadin abin da fayal tayi ba domin koda yaushe infayal tayi wani Abu kanta yake dawowa sai yan ajin sutamata habaici.
Itakuma batason hakan
Shiyasa kawarta guda dayace akaf makarantar.
Fayal tana fita tayi mota tabude baya ta kwanta abinta ita har taji makarantar tafitan mata akaima.
KOMai yasa?
Ohooo Amsar da taba kan ta kenan.
Ahaka har tafara barci abinta.
💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖
Amsard yaga yau ba aiki sose a office dan haka yafara shirin komawa nigeria gobe.
MIsalin karfe 2 Yakira usman yafada mai insha Allah gobe zai dawo .
SAnnan usman yace"toh Allah yasa nidaman na zaqu kadawo aciga ba da drama domin naga mutuniyar ma amota ita kadai
DA alama dai yau ma ankuma da wani kenan".
Amsard yace"hmmm ai wannan yar sai dai Allah yakyauta Amman fa karka damu nakusa saita ta".
USman yasa dariya sannan yace"toh nidai kullum inama fatan sa'a ".
Amsard yayi dariya shima sannan yace"kadai ji dashi ageshemin da uwargida".
USman yace"aiko zataji domin nafara bata labarin dramar ku".
Amsard yace"kace kasani a faifai kenan".
Usman yasa dariya.
SAnnan AMsard yace"nidai sai anjima inashiri ne".
Sukayi sallamah.
*PAGE* 26,27.
----------------------------------------------------------------
Bayan usman sunyi sallama da Amsard .
Sai Amsard yacigaba da shirinsa nakoma wa nigeria.
Abangaren fayal kuwa tun karfe 9take barci sai 1 tafarka daidai da fitowar su Amnah kenan.
Amnah nafitowa ta hango motarsa abin yabata mamaki dan batayi tunanin ganin fayal ayanzu ba.
Batama ga abin mamaki ba sai da taga fayal da alamun tashi daga barci.
Azuciyarta tace"ikon God".
Niko nace sai kallo.
tana zuwa tace"fayal lafiya kuwa".
fayal ta yamutsa fuska har kungama kenan?
Amnah tace "eh wlh lecture usman ma yasanar damu insha Allah jibi zamu cigaba da practical dinmu".
Fayal tace"kwaji dashi dai".
Amnah tace"hhhh ai shiyasa kikaga mun fito da huri yau yasin da sai 6 inaga har sai kingama kumburah ma'.
Fayal taja tsaki sannan tace"ni kishigo mutafi ko malama".
Ita dai Amnah dariya take da dariyarta tashiga mota suka nufi hanyar gida.
Sun isa gida bakowa dahike momy ta tafi aiki shikuma dady yayi tafiyama.
Dan haka suna isa fayal tayi sallah tukun tadawo kichin domin daura abinci.
Duk irin halin fayal na kyaliya hakan baisa iyayenta sun sakalta ta ba .
Aduk sanda momy zatayi girki sai ta tabbatar da su fayal da Amnah na wajen.
Dan haka fayal tashiga kichin domin musu girki .
shinkafa da wake dafa domin itama shine abincin datafi so arayuwarta.
Tana kammala momy tadawo dan haka suka hadu a dainin domin cin abinCi.
Ananne momy tace"yadai maganar practical dinnaku gashima naga yau kun dawoma da huri".
Amnah tace"umm momy wai jibi zamu cigaba kinsan gobe sunday shiyasa kawai akabari sai monday inAga yau me practical din zai dawo shiyasama yau bamu jima a lectures ba".
Momy tace"owk su fayal ansha aiki ko maganar ma baza amin ba".
Fayal ta yamutse fuska sannan tace"hmmm momy".
Daganan bata kara cewa komai ba .
Sukuwa momy da Amnah suna hira sunacin abincinsu.
Itakuwa Fayal yadda batason yin magana haka bataso nakusa da itama su cika yi dan Haka da anfara cin abinci taga su momy sunfara bude dandalin hira sai tayi sauri tabar wajeN.
Toh yau mah haka tayi tayi tatashi tabar wajen.
Dashike sunsaba da halinta hakanma baya damunsu.
Fayal tana shiga daki Tadauko wayarta tafara game.
Domin datayi magana gwarah tata karatu ko game.
Suko su momy sai dasukaji sunyi nak tukun Amnah ta kwashe kayan da tA bata tatafi wanke'wanke .
Sai momy afalo dake danna wayarta.
Megadi yashigo da sallamarsa.
Momy ta Amsa.
Sannan me gaji yace"wai wani ne yace nakira masa fayal".
Shikansa asanyaye yake maganar domin yasan halin ta sarai.
Bayau akasaba zuwa wajenta ba tana hulakanta mutane .
Amman duk da haka kaman karuwa masoyanta suke.
Sai da momy taja dogon nufashi.
Domin ita kanta tsoron yartata take.
Sannan tace"waye ke kirinta?.
Megadi yace"wani ne yazo amota yana waje ".
MOmy tace"owk kace tana zuwa".
Megadi yace"toh sannan yatashi yatafi jikinsa asanyaye.
Momy takasa motsi sai tunanin yadda zata bullowa yartata take.
Daga karshe dai kawai ta yanke shawarar zuwa tasanar mata.
Momy nashiga ta tarar da fayal kwance tana game awaya.
TAyi sallama sannan fayal ta dago tukun ta Amsa.
MOmy tace"fayal ".
Fayal ta dago.
Tukun momy takara da cewa dadynki ya aiko wani dan abokinsa kije ku gesa".
fayal ta yatsina fuska sannan tace momy ni wallahi agajiye nake kawai Amnah taje su gesa".
DAkyar momy tajawo hankalin fayal dataje su gesa tukun tayarda.
Momy tabar dakin gaban ta sai faduwa yake.
Azuciya kuma tana addu'ar Allah yasa adace yau".
FAyal tadauko hijjabinta harda daukowa Amnah likaf tasa.
Tana fita!.
BABU RUWAN SO Page 1 to 10
*PAGE 1*
----------------------------------
Fayal ce xaune akan kujera futo war su kenan daga lectures ita da kawarta Amnah chating take yi ciki 'kware wa Amnah ta kalle ta tace. ‘’ Fayal wai me zakicine mukazo nan nikam kitashi mutafi gida mana.‘’
magana take mata amman kaman ba da ita take ba tawani hada rai tare da bada hankalinta ga waya Da take hannun ta Amnah tasan halin kawarta ta sai tayi shiru bata kara cewa komai ba.
Wani saurayi ne yadau wanka yaci fararen kaya shiba mummana ba kuma bara ace mishi kyakkyawa ba.
Da sallamarsa yataho garesu. Amnah ce tace. ‘’ walaikumussalam.‘’ kujera ya samu ya zauna Alokacinneh Amnah ta tashi tabar gurin domin tasan halin kawarta da disga mutaneh bataso ta tsaya agabanta ta hulakanta wannan mutumin ba.
Saurayi yace. ‘’ To nidai sunana auwal Ana kiranah da Arfan kuma ni dan garin katsina ne babana ne sarkin katsina nine d'ansa nafari.‘’Duk maganar nan dayake bata dago ta kallesa ba balle tasan waye.
Yacigaba da cewa. ‘’Dan Allah ko dan iya sanin sunanki.‘’Bata dai kulasha ba sannan shikuma be gaji ba yace. ‘’ sonki nake da aure so na gaskiya.‘’ 'Dauko eye pices dinta yi tasa akunneh Sannan ta tashi tabar gurin wanda har ta tashi ko kallon inda Auwal yake batayi ba.
Tabar shi zauneh awajen abun da tayi masa ya matukar basha mamaki irin hali da miskilanci na yarnan Ko kalloma be shita tayi mishi ba da tunani iri iri yatashi yabar wajen motarsa ya je ya hau ya bar gun aguje.
Fayal tana tashi tanufi inda sukayi paking din motarsu domin tasa Amnah na ciki
Tana zuwa ta hau Amnah da fad'a tace. ‘’ amman dai kinsa bana son irin wannan abunko kawai kinbarni dawani kato yazo yanatamin zuba kamar parrot?
Amnah tace. ‘’Nasan hula 'kantashi zakiyi shiyasa na bar gun, har yanzu kin ki chanjaa halinki,wallayi Fayal ina kujemiki ranar da zaki fara son wanda bai ma da lokacin ki, ki tuna fa kamar yadda kikema wasu haka za,a miki,Fayal tace. ‘’ Ke dalla cen meye ma wai so hmm wallahi ni banga wani abu asoyayya ba inbanda bata lokaci dan haka ni dakika gannin nan ban da lokacin da har zan tsaya batawa akan wani banxa .‘’
Amnah takara ka da baki tace. ‘’ A bi dai ahankali domin wataran ke zaki zubda hawaye kamar yadda wasu suka zubar akanki.‘’
Fayal tace. ‘’ hmm suma wallahi suna daurawa kansu wahala ne bani na nace suxo susoni ba ai ko?
Dan haka kowa yayi takansa banzaYe wahallalu dasu,Nikam mikwomin key mutafi dan wallahi har kinsa nagaji domin nayi magana dayawa yau.‘’
*zamu gani shin tusa zata hura huta kuwa wane rayuwa fayal zata tsinci kanta*
PAGE 2
-------------------------
Fayal driving take kaman kaman bazatayi ba.
amnah tace. "Haba fayal bakiga lokaci yanata kure manah bane?
Haba Dan Allah kiyi sauri mana kinsan halin mumy fa
Duk maganar nan da Amnah take Fayar ko sauraranta batayi ba.
Amnah batagaji ba takara ka da baki tace. "magana fa nake miki inkuma baraki iya yin sauri bane ki tsaya ni nasauka na hau adedeta kawae.
Sannan Fayal tace. "oh kekam baki da hakuri kinsan dae banason yawan magana ko? hmm Kayi hakuri dai ai munkusan isa ko.?
Duk irin miskilanci da kyaliya irinta Fayal tana ragawa Amnah domin ita kadai ce tasan halinta kuma ta karance ta
Amnah tace."shikenan amman wlh kome mah mumy tace ke ce da laifi ba ni ba.
Ahaka su fayal da Amnah sukA isa gida batare da k'ara yima wani maganah ba.
Da isarsu mai gadi yaxo yabude musu get sannan fayal tayi paking.
suka shiga cikin gida da sallamar su
Momyce zaune tana kallon Tv.
Tace. "wa,alaikumul salam.
Fayal dakinta tanufa batare da ta tsaya sun gaisa da mumy ba.
Ita kuwa Amnah taje tageshe da mumy kafin ta nufi d'akinsu.
Mumy tasan halin yarta ta shiyasa ko damuwa batayi ba da tun tana damuwa yanxu kuwa abin yaza me mata jiki sai dai kullum tana taya yartata da addu,a
PAGE 3
--------------------------------------
Daga shigar Fayal daki har tanufi toilet ta dauro Alwalah sannan tayi sallah tana idarwa bata nufi ko ina ba sae gado..
Ita kuwa Amnah tana idar da Sallah ta nufi shashin Momy domin taci abinci sannan ta tayata aikin gida.....
Dazuwanta tace."momy ina food dina?
Momy da dan murmushinta tace."gashi cen a kichin
Amnah tace."ok momy
Taje tadauko abincinta ta ci sannan suka shiga kichin ita da momy dan d'aura abincin dare.
Sunayi suna yar firarsu,,
Momy tace."Amnah yau kuma fayal tayi wani aikine Askul?.
Amnah tace."hmm momy wallahi bawani aiki datayi illa abinda tasaba kuma shine wai nasata tayi magana dayawa....
Momy Tace."hmm to dai Allah ya shiryata domin narasa gane hali irin na fayal nidai da abbanta ba haka muke ba
Amnah tace."Toh Ameeen dai momy ni abinda ma nafi jiye mata tsoro kar daga karshe tafAda tarkon wani..
Da wannan hirar suka kammala girkinsu
***********
wani saurayi na hango zaune afalo yanata murmushi nikai na dana ga irin kyansa sai da nace masha.. Allah hajiya ce tafito tana fadin."a Amsard Yaushe ka iso ko maganah babu?
Sannan saurayin nan yad'ago" oh my hajiya yanzu na iso fa ina hutawane kinsan da jirgi yasauka a airport nina driving kai na xuwa gida shiyasa nagaji....
Hajiya tace."owk to welcome my son yanzu tashi kaje kai wanka sai muci abinci ko?
Amsard yace." ok hajiya nah
yanaji gidan shiru neh?
Inasu salaha da samir
Hajiya tace."suna makaranta
Amsard yace."oh hakane fa namanta ne yana maganar yana tafiya shashinsa.
Dashigar Amsard yashiga toilet yayi wanka sannan yayi sallar la'asar da hike yayi azahar tun amota bayan ya idar da sallar yasaka kananun kayan sa pink din riga tare da farin wandon jeans .....yafeshE jikin sa da turare sannan yanufo shashin hajiya..
Dashigarsa yatarar duk sun dawo daga skul...
Yashiga da "sallamarsa
Su sahala suka amsa tareda rungume yayan nasu
Amsard."yace a su sahala an girma anbar fitina kenan
Sahala.Tayi murmushi
hajiya tace."to kuxo muci abincin tunda dai duk kun dawo..
Suka nufi daining table tareda fara cin abinci
Sahala sai surutu takewa yayan nata shiko ba mai son magana bane sai dai kawai yamata murmushi
Sahala tace."uhummm hajiya kinga yaya amsard yaki kulani ko?
Hajiya tayi murmushi tace."kema dai kinsan halin yayannan naku shi magana ma wahala take masa keko bakya gajiya da zuba kamar parrot....
Sahala tace."hhhhh lallai matar yaya zatasha wahala dashi wlh tab
Nidai bazan yarda da hakan ba...
Shiko Amsarda,,murmushinsa yake tare da cin abinci
Ahaka suka kammala cin abinci kowa yayi dakinsa
PAGE 4
------------------------------
WACECE FAYAL?
Sannan wanene Amsard???...
Fayal y'ace Wajen Alhaji Mohammed Mai zinare
Alhaji Mohammed dan garin jigawa neh sannan shi babban dan kasuwane.Abinda yasa akece Masa mai zinare yana safarar sark'wokin zinare neh daga kasashen waje.
Matarsa daya wato hajiya Amina Mata mai kirki da son yan uwanta tare da karramah mutane
Yarsu daya aduniya wato Nusaiba Mohammed wacce ake kira da fayal
fayal yarinyace kyakkyawa fara tas kamar ataba ta jini yafito kana ganinta kaga jinin fulani domin tana da wadatace ciyar suma
Sannan fayal tana da miskilanci wanda baran iya misalta muku ba ga kyaliya da rashin son magana sannan tana da wulakanta duk wani namiji da yanufe ta da kalmar so domin ta tsani wannan kalmar...
Acewarta so wahala ne dan haka batada lokacin yi...
Adalilin hali irin na fayal ne momy tadauko yar kanwarta domin taga sun dan shaku da fayal ita kadai
take sakewa fuska...
Ayanxu fayal Tacika shekarah Ashirin tana universty ajigawa karantar likitar mata take...
Wannan kadan kenan daga tarihin fayal...
WANENE AMSARD?
Amsard d'ane ga Alhaji Abubakar ,,,,,,,Alhaji Abubakar minister ne na mai ..
Suna xaune Agarin katsina..matarsa daya wato Hajiya maryam tana da mutuncinta tare da son mutane kuma yar kasuwace Tana fita kasashen waje domin siyo kaya....
yaran Alhaji Abubakar 3 Amsarda ne dansa nafari......Amsarda ba fari bane sannan kuma ba baki bane shi wankan tarwa ne Amman duk da hakan Baya hana kyahu irin na amsard fitowa asalin sunansa Abdulazeez Abubakar Ana kiransa da Amsard...
Amsard bai cika son magana ba duk da yammata dayawa nacewa suna son sa Amman hakan bayasa sa wulakantasu...
Insuka fada mai sai dai kawai yayi murmushi yace ya gode tahanyar da yake rufe ma yan mata baki kenan duk da sun san hakan zai fada Amman hakan baya hanasu cewa suna sonsa....
shiko yamakansa alkawarin bazai auri wace tace tana son sa ba sai yasamu wadda tamai..... tunda hajiyA maryam ta haifi Amsarda bata kara haihuwa ba har Amsarda yakai shekara 20...
Sun cire rai da tunani samun wasu yaran Amman duk da haka basudai nah Addu,a ba ahaka har Allah yabawa hajiya ciki ta haifi yan biyu mace da namiji sahala da sameer....
Amsarda da iyayensa sunyi mutukar farinciki
Yanxu Amsard yagama karatunsa A Ummaru Musa Yar Adu'a dake katsina sannan yakoma malesia domin masters dinsa....
ayanzu yazama cikakken medical Doctor kuma yana da asibitinsa a malesia inda yake aiki shin acen
Kadan daga cikin tarihin Amsard kenan
PAGE 5
-----------------------------
CIGABAN LABARIN
Abangaren Fayal tunda ta kwanta bata farka ba sai dataji ana kiran sallah magriba.
Tana tashi tanufi toilet ta dauro alwala sannan tayi sallah.
hakama su momy sun riga da sun idar da sallar su.
Har sunfara shirya abinci akan daning table.
Suna cikin shiryawa sai ga fayal ta fito tana yatsina fuska. daman wannan d'abi'ar tace.
Momy da Amnah suna ganin fayal suka fara mata murmushi.
Tare da fadin."fayal din momy kin tashi ne?.
Alokacin fayal tadan k'akulo murmushin dole tace." good evening mom and amnah?.
Su momy sukayi murnushi tareda fadin."
evening fayal.
Alokacin dady yayi sallama.
Su momy suka Amsa.
Fayal tayi gudu taje gun dadynta.
Tareda fadin."welcome dady.
Dady yace."how are u daughter?.
Fayal."am normal dady
Dady yace."dax gud
Sannan momy."tace to ai sai kuxo muci abinci ko?
Dady yayi murmushi tareda fadin."oya daughter tashi muje.
da isar su daning Amnah tafara geshe da dady.
Ya amsa mata cikin sakin fuska.
momy tayi serving din su sukaci abinci cikin farinciki da annashuwa.
fayal Ce tafara tashi tareda fadin."gudnight momy daddy amnah.
Momy tace."haba dai wai harkin k'woshi?.
Kafin fayal taba momy amsa har daddy yafara magana.
"haba daughter wai ke har yanzu bazaki fara cin abinci yadda kowa yake ci bane?.
Fayal ta yatsine fuska sannan tace."uhumm momy dadu fa naci.
Nikam byeeee tanufi dakinsu.
Bayan tafiyar fayal daki.
Dady yace."Ni Wallahi har yanzu narasa gane irin hali na fayal.
Momy tace."hmmm Sai dai kawai mucigaba da tayata da Addu'a domin abinnan nata bana wasa bane.
dady yace."to dai Allah yakyauta.
Alokacin Amnah tabudi baki tace Ameeeen ni wallahi ma dady abin da yafi bani tsoro shine yadda take wulakanta maza.
INajiye mata kar taje ta wulakanta wanda batasan zuciyarsa ba.
Kokuma wataranah takamu da son wani wanda bazaiso ta ba.
dawannan hirar suka kammala cin abinci.
SAnnan Amnah tamusu sallama kowa yatafi daki.
WASHE GARI
Bayan su Fayal sunyi sallah Asuba basukoma barci bA.
Suka shiga kichin domin daura breakfast tunda yau da safe suke da lectures.
Shiyasa koma barcinma basu koma ba
*********
Abangaran Amsard mah yagama Shirinsa domin yau yanaso yaje ziyarah jigawa wajen abokinsa dake karantarwa acen universtyn.
Kamar karfe 7 Amsarda yafito yana fitowa yatarar da su hajiya da Alhaji na break fast sukuma su sahala da sameer har driver yatafi kai su skul.
Alhaji yace."oh Amsard yaushe agari?
Amsard yasosa k'yaya tare da fadin"ina kwana Alhaji?
Ina kwama hajiya?
duka suka Amsa cikin sakin fuska.
Sannan hajiya tace." ai tun jiya yadawo da rana. kai kuma bakanan shiyasa nabari inma suprise .
Alhaji yayi murmushi tare da fadin aiko kin kyauta dole inmiki kyauta ganin my son.
Sunfara cin abinci kenan.
Amsard yace."Alhaji jigawa fa zan tafi ana nemana a universtyn da usman abokina yake koyarwa.
Hajiya taci"oh kai kam dai baka gajiya kuma baka zama waje daya.
Alhaji yace gashima ko yar hira bamuyi ba.
Sai alokacin Amsard yayi murmushi tare da fadin."ai inaga bazan kai kwana 3 bama zan dawo indai nagamah.
Bayan sungama yin breakfast yamusu sallama suka mai addu'a.
yadau hanyar jigawa.
*******
su fayal sun shirya da huri domin suna tunanin yau sunada practical shiyasa suketa sauri.
Da fitowarsu Amnah tace nikam fayal bani keyn motar nan dan nasan inna biye miki sai kibatamana lokaci.
Fayal ta mika mata key din batere da tayi magana ba domin ita kanta Saury take taga sun isa skul din.
PAGE 6
---------------------------------
GODIYA AGAREKU LODI LODI DOMIN KUKE DAURANI AKAN HANYA hassan atk.Real shaxee.princes dija inayinku irin totallyn nan
Amnah tuki take cikin sauri dan ita aganinta sunyi letti mah.
Amsard kuwa shima yana shiga mota yafara sauri domin yanaso ya isa kafin 10pm
Tuki yake cikin sauri.
Dadai karfe 8.00pm su fayal suka isa domin suna da nisha da makarantar .
Amnah tace."kingama fa wai dan nayi sauri kenan nasan dakece da sai munkai 10 kafin mu iso.
Fayal ta yatsine fuska tare da jan dogon numfashi irin damwarkin nan.
Atare suka fito domin nufar inda sukaga students na zaune.
Da isarsu wajen amnah ce ta nufi wajen wata class mate dinsu tare da fadin"wai daman ba afara bane?
Tace"hmm eh wlh wai bai iso ba ashe yanada nisa.
Amnah tace"kai gaskiya amman su azabtar damu sunce mu fito da huri Amman gashi shi bai zo ba.
Takoma wajen da fayal ta tsaya domin kuwa fayal bata kula kowa askul din inkaga tayi magana da amnah take toh .
Shiyasa tun wasu nashishshige mata har sun gaji sun rage shiga harkarta domin kuwa yan kwana su take.
Da ta iso guri zakaji Anfara cewa ga yar girman kai nan tazo kowa yana fadan albarkacin bakinsa.
Wasu suce tana birgesu .
Wasu kuwa haushi take basu .
Amnah nazuwa tace."hm wai ashema bai iso ba.
Fayal tace"what!
Duk sammakon nan dakikasa mukayi?
Alallai ma wannan mutum min ya isa.
Ai naga ba dole bane practical dinko?
To wallahi baranyi ba nafasa komawa gida zanyi.
Nina tsani wulakanci arayuwata yawani sa an ajiye mutane kaman kaji..
gashi har rana tafara fitowa mtsw.
Amnah tace."haba fayal kinama mutane uxuri mana .
Kinsan mai yatsayar dashi kuwa?
Fayal tace"mtsw nikinga tafiyata wallahi har kai na yafara ciwo.Innaje zan turo driver yakawo miki motar.
Amnah tace."hmmm shikenan ai .
Fayal ta."figa mota aiko duk tabade mutanan gurin da kurah.
Mutane suka fara cewa."tir dai da hali irin naki
Ita kuwa batama san mai suke ba tayi tafiyarta.
ita kuwa Amnah ta koma wajen wata yar ajinsu Khadija suka zauna.
Fitar fayal keda wuya Amsard yashigo makarantar.
Da shigowarsa usman yazo yashiga dashi ciki.
Khadija kawar amnah tace"kai Amnah gaskiya yayarnan taki batada hakuri gashi daga fitar ta har ya iso.
Amnah tace."hmm wlh haka take ni bansan wani irin hali fayal kedAShi ba.
Suna cikin hira akazo kiran mutane domin shiga bayan kowA yashiga.
Amsard yaga wajen mutum daya babu yace"wa usman gurin waye wannan?
Sannan usman yayi bincike akaga ashe wajen fayal ne.
usman yazo Yafadawa Amsard fayal ce.
dakuma dalilin tafiyarta.
Ran amsard yayi mutukar baci domin yatsini mace mai girman kai.
Acewarsa matan mesukedashi da hardasuyi girman kai.
Yayi murmushi yacewa usman kabarni da ita i will teach her a lesson
DAMUGANI KOWANI MATAKI AMSARD ZAI DAUKA AKAN FAYAL??
PAGE 7
------------------------------------
INAKIKE MY SOUL BAN MANTA DAKE BA KUMA BARAN TABA MANTAWA DAKE TARE DA AMSARD DINA NA GASKIYA INA MUTAKAR ALFAHARY DAKU NUSAIBA MUHD AUWAL AND DAN MATASHI NAH
GODIYA GAREKU MASOYA WANNAN LITTAFI INAJIN DADIN BADA HADIN KANKU GARENI ANA MATUKAR TARE.
Da isar fayal gida ta tararda momy adaki tana duba wasu takardu .
Tashiga da sallamarta.Domin ita kanta tasan bata da gaskiya yau.
Momy tana raga mata aduk abinda take amman banda ta fannin karatu.
Dan haka take tsoro.
Momy tadago tare da fadin"wa alaiku mul salam
Fayal tayi sauri domin nufa dakinta momy ta dakatar da ita.
"ina zaki kuma?
Faya tace"fa.......
Momy tace"tsaya banason wannan maganar banzar taki mekika dawo yi?
Fayal tace"momy shifa lecturern da akace daizo yamana yaki zuwa.
Momy ta nufasa hadi da cewa"hmmm naga yanzu ma 10:am tayi.
Fayal nifa nagaji da rashin hakurinki.
Wai ke ko karatun ma barakiyi hakuri ba dan kisamu?
duk maganar nan da momy take fayal takasa dago ido domin tasan bata da gaskiya.
Momy tace"ki huce kibarmin gida kikoma inba haka ba kuma kema kinsan sauran wallahi.
Atake fayal ta juya domin komawa skul.Amman ba dan ranta yaso ba .
Dan haka ma ahankali take driving kamar wata mara laka ajiki.
Abangaren su Amsard kuwa yace"sufara
Yayinda aka fara practical gadan gadan .
Kowa adaliban yanajin dadin yanayin practical din domin yana musu yadda zasu fahimta.
Gashi duk yan matan shige masa jiki suke.
PAGE 8
--------------------------------------
Sunata shigewa Amsard jiki da tambayoyi shiko sai dai yayi murmushi sannan yabasu Amsa.
Domin Amsard yana da hakuri sose Amman in aka kuresa bara ataba jin dadi bah.
Fayal ta iso skul kamar yadda tasaba fuskar nan ayatsine amman nayau kam daban ne domin yatsinar yau tafi ta kullum.
Duk da haka bayasa kyahunta yaragu sai dai karuwa.
Tafiya take kamar bazata taka kasa ba.
Tana isa tashiga cikin lap din dazuwanta bawanda yakulata.
Sai masu gulma,Wasu nacewa yau anrage girman kan kenan.
Wasu ko ce suke oh tir dai anyi ba ayi ba miye amfanin dawowar.
Kowa na fadan albarkacin bakinsa.
Ita kuwa Amnah cewa take. "Fayal ga wajen kinan.
tukun tajuyo tanemi waje tazaune daidai da dawowar Amsard domin yaje yadauko abune Amotarsa.
Yaga fayal shikansa saida yace. "Masha Allah azuciyarsa.
Amman afili yace. "ke lafiya zaki shigo mana waje bakiga muna aiki bane?
Fayal batamasan yanayi ba domin ko kallonsa batayi ba bare har tasaurari maganarsa.
Amsard abin yamatukar bata mai rai dan haka yayi magana da tsawa"keee get out of my class!
Fayal tajuyo arazane domin ita arayuwarta bawani namiji daya taba daga mata murya bare tsawa.
Shiyasa tajuyo arazane domin inba dan yamata tsawa ba da saidai inyagaji da maganarsa yatafi yabarta.
Fayal."tace what!!!!!!
Amsard yace."i said get out of my class .
Aji yayi shiru domin yau fayal tagamu da gamota wasu sai dariya suke aboye.
Dan haka fayal tamike ta tashi domin baran ajin.
Jiki asanyaye domin ita abinma mamaki yabata.
sukuwa sauran yan ajin suji mamaki dasukaga fayal tayi shiru bata kara magana ba ta tashi ta tafi.
Duk ji da kan nata yau ina yake?‘’
Fayal tana isa mota tafara kuka ba kakkautawa domin ita gani take ayau anmata tozartar da bata taba tsammani ba.
Amsard yaji mamaki datakasa bada hakuri bare yaji tausayinta tayi .
Yacewa usman. "Lallai kuna fama da yan girman kai amakarantar nan wlh indai zanyi sati amakarantar nan sai na gyarama kowa zamansa.
Usman yace. "Hmm ai wlh indai fayal ce tafi hakama ninaji mamakima da bata fadama wata bakar magana ba.
Amsard yace"hmm ai wallahi kaima kasan banason raini da ta fadamin wata bakar magana .Da daga yau barata kara wulakanta wani namiji ba.
usman.Yace"hmm kai dai bari kawai .
Fayal kuwa tana nan amota takasa tukin ma balle taje gida sai kuka take tare da mamakin abinda Amsard yamata
PAGE 9,10
--------------------------------
Amsard yaciga ba dayiwa student bayani.
Amman acikin zuciyarsa tunanin fayal yake.
Oh afili kuma yace"oh wai nikam ma ina ruwana da ita.
Miye damuwata ai ita tawa kanta.
Mtws.
Usman yace"yadai amsard naji kaman kana magana.
Amsard da baima san maganar zuci ta fito fili ba.
Yayi murmushi sannan yace" aa no bakomai.
Ahaka sukagama practical dinnan Amman Amsard yarasa me yasa yake tunanin fayal.
Duk yadda yaso yabari amman yakasa.
Awata zuciyar kuwa cewa yake inaga dai tausayinta nake.
Yanata sake sake azuciya.
su amnah sun fito kenan ta hango motarsu.
Dan haka ta nufa wajen domin ita atunaninta driver ne yazo daukanta.
Tana zuwa taga abin mamaki abin da bata zato.
Fayal ce zaune tazuba uban tagumi tana kuka.
Arikice Amnah tashiga tare da fadin"yaya dai fayal lafiyan ki kuwa kike kuka haka?.
Fayal takasa magana saima wani kukan dayagara tawowa.
Bashiri amnah tafara driving .
Gudu take akan titi domin jikin fayal yadau d'umin zazzabi tafara.
Fayal rawar sanyi take matuka.
Domin yau tayi kukan da bata tabayi ba tunda tazo duniya .
Niko nace wace take ganin magana aikin wahala ne inaga kuka?
Hmm.
Da isarsu gida Amnah tashiga domin sanar da momy.
Momy tafito arikice domin shiga da fayal cikin gida.
Ita kuma Amnah takira family doctorn su domin yazo yaduba jikin fayal.
Kafin likita yazo har momy tafara d'uma ma fayal jiki da ruwan zafi.
Har zazzabin yafara sauka.
Sai ga doctor Abdulrahman ya iso.
Isowarsa keda wuya yashiga dubata .
Sannan yasa abata koda tea ne tasha yamata allurar barci.
yana mata kuwa tasamu yin barci.
Bayan doctor yatafi ne momy tafara"Tambayar Amnah wai meyafaru ne?
Batare da bata lokaci ba Amnah tama momy bayanin yadda komai yakasance.
Momy taji dadin abin nan ba duk da tasan laifin yartace Amman bataji dadin hakan da amsard yamata ba.
Allah sarki uwa da y'a kenan.
Momy tace"hmm to dai Allah yashiryamin ke fayal bansan ya zanyi dake ba sai dai mucigaba da addu'a .
Amnah tace"Ameen momy.
bara nayi sallah sai indaura mana abinci.
Momy tace"ok nima bara nayi sai mushiga kicin din tare.
Suka tashi domin sallah bayan sun idar suka nufa kichin domin daura abinci.
Fayal barci take Amman ganin abin da yafaru take acikin idonta.
Afirgice tafarka tare da fadin"wai ni yau wani zai wulakanta!!!!!
Wallahi wallahi sai sai na rama abin da yamin.
Yanzu zan fara asalin wulakanci tunda da ance INayi nikumA banga hakaN ba.
DAn hakA yanzu da afara.
Hmmm niko nace kome da afara?
Sai kubiyo ni Aysherth(preety xayeesherth)
Domin sannan me za afara cewAr fayal.
Bayan su momy sun kammala girkinne suka fito .
Fitowarsu keda wuya sukaga fayal zaune afalo.
Da alamu dai tunani take.
ko tunin me take? ohoo dai.
Amnah ce tafara magana"fayal kin tashine?
Ya jikin?
Sannan momy tace" sannu fayal.Ya jikin dai?.
duk maganar nan bata dago ba sai daga baya ta yatsina fuska tare da fadin dasauki.
Tun daga nan bata kara cewa komai ba.
Suko su momy da hike sunsan haka halin fayal yake sai abin bai damesu ba.
sabida hakan yabi musu jiki.
Tafiya sukayi suka fara jera abinci adainin.
Bayan su kammala ne sukace da fayal tazo taci abinci.
taje tazauna Amman tunani take.
Har yanzu abin yaki bace mata a ido .
Niko nace ai ke kikajawa kanki.
anzuba mata abinci amman takasaci.
Momy ta lura da hakan Amman tashareta.
SAi Amnah ce ta ka da baki tace."fayal bazaki ci abincin bane?
FAyal"ta yatsine fuska.
Sannan tace na k'woshine fah.
Sai alokacin momy ta bude baki tace"wallahi indai yau bakici abincinan ba sai dadynku yaji abinda kika aikata askul .
Kinsan dai inasane dakomai ko?
Fayal ta girgiza kai tare da fadin "aa danci.
Ahaka faya ta chacchakula abincinan tabari wai adole taci.
Domin ita dama asalinta cin abinci wahala yake mata.
Suna gama ci FAyal taje tayi sallar la'asar sannan takoma gado.
****
Abangaran amsard kuwa sun koma gidan usman dake jigawa .
SUNa isa yatarar da matar usman phertymerh sai fara"ah take.
Dasauri tazo ta karba jakar mijinta tanamai sunnu da zuwa.
Amsard kuwa murmushi yake.Domin usman da pherty na birgeshi.
Pherty tace"ah kacemin yau munada babban bakwo agidannan .
Amsard yace"oh sai yanzu kikaganni ?
Bayan kingama karban mijinki?
Pherty tayi murmushi sannan tace"hmm ai kasan halin naku ne sai ahankali inmuka sake sai amana kari.
Amsard da usman suka sheke da dariya .
sannan Amsard yace"ashe dai anajin tsoronmu.
pherty tace"ai dole munma wallahi harda gudU.
Shidai usman ba abinda yake musu banda dariya.
Pherty tace"gwandama ogana fa ashe tunda kai har yanzu ko budurwar ma babu.
Antsaya anamin bakin cikin samun kawa.
Share this
Wednesday, October 6, 2021
Shin Ko Kunsan Adadin Kudin da Ake ba Wadannan Fitatttun Jaruman idan Sun fito a cikin Film?
Shin Ko Kunsan Adadain Kudin Da Ake Ba Wadannan Fitatttun Jaruman Kuwa Idan Sun Fito A Cikin Fim.?
Wadannan Jaruman Sune Manyan Jaruman Da KannyWood Ke Ji Dasu Yanzun, Kuma Sunfi Wasu Jaruman Da Yawa Samun Kudi Idan Sun Fito A Kowane Fim Din KannyWood,
Domin Sanin Nawa Ake Biyansu Bayan Shirya Ko Wane Film Shiga Ku Kalli Wannan Videon Anan.
Share this
Tuesday, October 5, 2021
Ba'a Shan Zuma Page 51 to 60(The end)
Bayan sun gama ta wuce ta
fesa wanka, ta dau gayu na
musamman domin taryar rabin
ran nata.
K'arfe biyu da kwata dai dai
suka iso gidan, da sallamarshi
ya shigo palon babu kowa sai
Mahmoud yaron Hafsat yana
kallon cartoon a MBC3. Da
gudu ya taso ya rungume
Nawap yana cewa
"ga Uncle ga Uncle."
D'aga shi sama Nawap yayi,
yana fadin "my boy, ka zama
babban mutum"
Dariya ya kyalkyale da shi,
"sosai ma, har na kai nursery 2
fa uncle"
"Smart boy" Nawap ya fada
yana dariya, sannan ya sauke
shi, ganin Deedo na saukowa
fuskarta kunshe da wani
murmushi na ban mamaki.
Karasawa yayi inda take tsaye
ta nannade hannayenta, ya
kalleta yace "yan mata na,
yakike?"
"Ina wuni" ta fada, yayin da ya
ansa a daburce, "na same ku
lafia?"
"Lafia lau, ya hanya?"
"Alhamdulillah, ina ta sauri na
zo nayi tozali da abin k'aunata
"
Rufe fuskarta tayi, alamar
kunya, tayi gaba tana cewa
"muje ka ci abinci, dan na san
yanzu haka ko breakfast baka
yi ba"
Bayanta ya biyo yana cewa
"banda abinki waye zai ba
gauro abinci"
Dariya tayi lokacin da suka iso
kan dining table din, sai da ta
rage muryanta, sannan tace
"just two weeks ya rage, ka
daina zama da yunwa in sha
Allah"
Ta juya ta cigaba da serving
dinshi, inda shi kuma yana
murmushi yace "I trust my
baby doll"
Ta kalle shi ta murmusa,
sannan ta mika mashi plate din
abincin, ta wuce kitchen domin
kwaso drinks.
A haka Hafsat ta tarar dasu
yana cin abincin, yayin da
Deedo ke zaune gefenshi suna
tadinsu cikin jin dadi.
Suka gaisa dashi, yana
tambayar
"ina mama small" tace
"dak'yar na lallabata, tana
sama tana bacci."
Sannan ta wuce cikin palon
inda Mahmoud yake a zaune.
Tunda Nawap yazo kullun
suna manne da Deedo, shi ke
kaita skool, sannan ya jirata
office din Dr. Kashim, har sai
ta fito exams, sannan ya dauko
ta su dawo gida kullun, har
zuwa yau da take gamawa.
A hanya take ce mashi
"Ummi ta fada maka da su Yaa
Hafsat zamu tafi?"
"Me zasuyi mana ne in mun
tafi dasu? Me sa Ummi take
mun haka, bata son ina
ke6ewa da matata" ya dan ja
tsaki, ya kara gudun da yake,
yace "ke kuma me kika ce
mata?"
Dariyar da take ta dan
tsagaita, tace "ni har na isa
ince wani abu ne bayan Ummi
ta gama yanke hukunci, lallai
ma"
"Duk ke kika ja mana ai da
kika fada mata"
"Zan bi wani ne ba tare da
sanin Ummi na ba aka fada
maka" tana yi tana kallon
yadda yayi kicin kicin shi dole
ga wanda aka shiga hakkinsa.
"Zaki maimaita ranar da kika
zo hannuna yarinya, dan sai
kinyi wata biyu baki ga Ummin
taki ba" ya fada a dai dai
lokacin da suka iso kofar gida,
ya fara danna horn kamar
wanda ya d'auko majinyaci.
Ita dai dariya kawai take,
yana yin parking ta fito zata
shige, yace "wa kika bar ma
wannan tilin books din naki?"
"Wa fa in ba mijin yar auta
ba" ta shige tana ta dariyar
mugunta.
Yayi kwafa, ya kwashi k'atin-
k'atin din text books din har
guda ukku, shi kanshi sai da
hannuwansa suka k'age, ya
zube mata su a palo, yana
banbami "koma ya ake tana
daukan books din nan, gata dai
abu kamar a karya ta"
Mahmoud yace "uncle kai da
wa kake fada?"
Yace "wannan yar siririyar
auntyn taka mana, ta sanya ni
daukar books masu nauyi"
Yayi dariya, yace "ai idan ta
dauka zasu fadar da ita ne shi
yasa, kai kuma kana da k'arfi
kaga"
Shafa kanshi yayi, ya wuce
kitchen ya dauka robar ruwa,
sannan ya wuce side dinsa.
[24/04 21:45] Nty Lubiee:
BA'A SHAN ZUMA…
108
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
®NWA
K'arfe goma dai dai na safe,
kowa ya gama shiryawa tsab,
suna zaune a palo suna jiran
fitowar oga Nawap wanda yake
ta faman cika yana batsewa
shi dole an takura masu, za'a
hana su sakewa shi da Deedo.
Karasowa yayi, ya dau wanka
cikin farar gezna, hularshi da
takalminshi har ma da agogo
duk bak'ak'e, yana ta kanshin
Tom Ford Velvet Orchid,
Mahmoud kawai yai ma dariya,
ya kama hannunsa suka fita.
Deedo da Hafsat da suke
kunshe dariya suka kyalkyale,
sannan Deedo ta sa6i mama
small suka fito, yayin da Saude
take kwaso kayan da zasu tafi
dasu tana lodawa a boot.
A gaba suka zauna ita dashi,
sai mama small a hannunta,
yayin da Mahmoud da Hafsat
suke a baya. Haka suka fara
tafiyar kamar kurame, in banda
Mahmoud da mamah da suke
yan surutansu na yara.
* ********
K'arfe d'aya na rana Nawap
yayi parking motarsa a kofar
wani kwarmad'ad'd'an gida
wanda yake da tabbacin tabbas
nan ne gidan Goggo, domin ko
ba zai taba manta gidan da ya
fara ganin mamallakiyar
zuciyarsa ba.
Kallon Deedo yayi, yace
"kamar munyi batan kai
ko?"
"Anya kuwa?" Bari dai in shiga
mu ga"
Ta 6alla murfin motar ta fito,
yayin da shi ma ya bude nashi
kofar ya bita a baya.
Cikin gidan wanda ga
dukkan alamu rabon da ya ga
shara akalla anyi shekara
hud'u, domin ko yadda kasan
kango, haka bola ta samu wuri
ta basar, suka kutsa kansu,
Nawap ya kalle ta
"Bana tunanin akwai dan
Adam din da yake rayuwa a irin
wannan wurin, fito mu shiga
makwabta mu tambaya ko sun
koma wani wuri ne"
Basu ankara ba suka tsinkayi
murya daga cikin dan akurkin
dakin da Deedo take da, wanda
shi kadai yayi saura a cikin
dakunan da suke gidan, domin
kuwa sauran duk sun rufta,
kana iya hango komai daga
inda suke a tsaye.
"Wane dan banzan ne nan?
Iyii? Ko bakwa ji na ne
la'anannu"
Ta fara laluben sandarta,
dakyar ta dafa bango ta mik'e
tsaye, tana bin bangon ba tare
da sanin ta ba ta taka wani
kwano, aiko ba tare da 6ata
lokaci ba ta fadi kasa, ji kake
wani rigijib!!!
Nawap da Deedo da suke
tsaye bakin dakin suka yi
saurin kutsa kai ciki, amma
wani mahaluk'in k'arni tare da
wani gagarumin wari ne suka
yi ma hancinsu sallama nan da
nan suna rige-rige suka yo
waje da gudun bala'i, Nawap
ya rik'e cikinshi wanda yake
murd'a mishi, nan take ya fara
shek'a amai ba k'akk'autawa…
"Allah dai ya tsine muku, wai
su uban waye a nan?" Ta
cigaba da laluben inda ta
wurga sandar, ko Allah zai
taimaketa ta fita ta warci daya
a cikin irin yan iskan yaran da
suke shigowa suna tsokanarta
ko wacce rana.
(Nayi iya kokarina na karasa
labarin nan yau, amma hakan
bai samu ba, I promise yu
zuwa gobe in sha Allah.
Thanks y'all for the love. I love
yu too)
BA’A SHAN
ZUMA…
109-111
BA'A SHAN ZUMA… 109
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
®NWA
Hawaye masu azabar zafi suka
gangaro a fuskar Deedo ganin
halin da kanwar mahaifinta ke
ciki. Hannu tasa ta share, ta
juya tana kallon Nawap wanda
yake goge bakinsa da
handkerchief, karasawa tayi,
gabanshi
"Sannu Yaa Nawap" ta fada
yayin da take waige waige ko
me take nema,
"Kaje waje, bari nayi magana
da ita"
Goggo wadda ta rarrafo ta turo
kanta kofar dakin, tace
"Wai muryar su waye nake
ji nan? Iyii? Ko baza kuyi
magana bane tambadaddu
ya'yan fata, Allah dai ya tsi… "
Nawap ya katseta ta hanyar
cewa,
"Goggo Nawap ne, wannan
kuma Deedo ce, dago ki ganta"
"Deedo? Nawabu? Ku ne? Ko
dai tsinannun ya'yan unguwa
ne suke tsokanata"
Ta fada yayin da ta dago kanta,
ko Allah zai sa ta hango
kyallin wani abu wanda zai
tabbatar mata da cewar su din
ne.
A tare suka toshe bakinsu da
hannu, suna fadin
"innalillahi wa inna ilaihir
raji'un!
Goggo!"
Ganin kwantsa mai kama
da mugunya, har da wasu yan
tsutsotsi suna fita daga idanun
Goggo, idon ya ca6e, ya
cakwale, Allah kadai ya san iya
shekarun da ta dauka tana tare
da wannan azabar.
Lalube ta cigaba da yi, inda
ta jawo 'yar k'afarta guda daya
da tayi mata saura, ta fito da
ita wajen dakin dak'yar,
"'Ya'yan nan ku fada mun
gaskia, Deedo ce wannan a
gaba na da gaske?"
Tasa hannu tana lalube ko
zata samu damar ta6a Deedon.
"Nice Goggo, wai me yake
faruwa da ke ne? Bakya gani
ne ko ya akayi?"
Kuka mai sauti Goggo ta
saki, sai dai kash, kukan babu
ko alamar hawaye, amma duk
wanda ya ganta zai tabbatar
kukan nadama Goggo take
rerawa.
"alhakinku ne yake bibiyata
Deedo, dake da malam Ilu,
wanda bakin cikina yayi
sanadiyyar barin shi duniya, na
shiga ukku ni Batula,"
Abinda Goggo take nanatawa
kenan, yayin da ta dauki
hamnuwanta ta dora bisa kai,
tana kurma ihu kamar
mahaukaciya.
Ihun da Goggo ta kurma,
shi ya jawo hankalin su Hafsat,
da Mal. Labarin makwabcin
Goggo wanda shi kadai ne
mutumen da ya rage wanda ke
taimaka mata a unguwar,
kasancewar kowa ya san bakin
hali da bala'i irin na Goggo,
shi yasa babu mai kallon inda
take, anan inda take a zaune
zata yi kashin ta da fitsari,
haka kuma idan malam
Labaran ya miko mata dan
abinci, anan din dai zata cinye
shi, ba tare da wanke hannu ko
kashin da yake jikinta ba.
Da azama suka yo cikin gidan,
ganin yanayin yadda wurin
yake yasa Hafsat dakatawa,
hannunta rik'e da na Mahmoud,
yayin da Mal. Labaran ya
karasa yana fadin
"Samari daga ina? Lafiya
kuwa?"
"Lafiya lau mal., ina wuni"
Cewar Deedo, inda shi kuma ya
cigaba da kare mata kallo
kamar ya santa.
"Deedo ce" ta fada tana kallon
goggo,
Nan ya fara salati yana
sallallami
"Deedo? Ina kika shiga?
Wanene wannan din shi
kuma?"
Anan suka gaisa da Nawap, yai
mashi bayanin kanshi, mal. Ya
kara da tambayar "kai kuma ina
ka santa?"
Nawap wanda baiyi kasa a
gwiwa ba ya labartawa mal.
Yadda akai ya san Deedo, har
ma da yadda akai ya tafi da ita.
Goggo wadda ta daskare tun
lokacin data tabbatar da Deedo
din dai ce a wurin, ta kara
kurma wani sabon ihun, a
yayin da Mal. Labaran ya
kwashi sabon salati yace
"Eh lallai dole kike shiga
wannan halin Batula, ka ganta
nan" ya fada yana kallon
Nawap tare da nuna Goggo da
yatsa, yace
"Wannan matar bayan tafiyar
Deedo, duk wanda ya
tambayeta ina yarinyar nan
take, ce mashi take ta tafi
yawan karuwanci, ashe ke da
hannunki kika dauki diya kika
bayar, chabdi! Lallai Allah yana
son ki Batula, tunda har ya
baki damar sake ganin Deedo
don neman gafararta"
Cigaba da jinjina kai yayi, ko
a film bai taba jin irin wannan
tsantsan rashin imanin na
Goggo Batula ba.
[26/04 01:21] Nty Lubiee:
BA'A SHAN ZUMA… 110
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
®NWA
Deedo wadda take shar6ar
kuka domin jin bayanin mal.
Labaran nan da nan taji wata
sabuwar tsanar Goggo ta karyo
mata, ba don kanwar ubanta
bace, da babu wani abu da zai
kara hada su, duk uwar azabar
da ta gana mata bata isheta
ba, har sai da ta zubar mata da
duk wani mutuncinta daga idon
mutanen garin.
Nawap ne ya lallabata har tayi
shiru, sannan ya kai dubansa
ga mal. Labaran wanda har
yanzu bai daina mamakin
makirci da mugun hali irin na
Goggo ba,
"Mal. To ita menene
musabbabin dawowarta haka?
Ina yaranta suke ne basu kula
da ita?"
"Chabdi! Dogon labari
kenan,"
Cewar mal. Labaran, sannan ya
cigaba
"Abinda yayi sanadin
dawowarta haka baya rasa
nasaba da dan ta shehu,
wanda tun yana dan shekara
sha biyar ya zama tataccen
dan daba, inda ya shiga wata
kungiya ta wasu mutane masu
yanka mutun su gudu. Haka ta
faru da shi bayan ya soka ma
wani yaro wuka a ciki, ya gudu
ya bar garin, yan sanda suka
nemeshi suka rasa, har suka
kame ita Batular, inda wani
bawan Allah da bata san ko
wanene ba yayi belin dinta, to
bayan an sako ta daga caji ofis
din ne ta taho gida mota tayi
ciki da ita, wanda hakan yayi
sanadiyyar rasa kafarta guda ta
dama"
Mal. Labaran ya dan
tsagaita, sannan ya dora,
"To ita kuma waccen Hadizar,
babbar 'yar tata kenan, da tana
kula da ita, daga k'arshe sai
abin ya dawo kamar ta dan
samu ta6in hankali, kullun in
banda kuka da kiran shehu
bata da wani aiki, nan zata yi
kashi, tayi fitsari, bata iya
motsawa ko kadan, ana haka
duk Hadizar na taimaka mata,
kwastam, sai aka wayi gari aka
ga Hadiza da katon ciki wanda
babu wanda ya san inda ta yo
shi, kuma ita dai ba aure akai
mata ba, nan fa yaran unguwa
suka dinga jifarta, suna
zaginta, itama daga nan aka
nemeta aka rasa. To ni dai a
ganina kukan rashin ya'yanta,
da kuma iftila"in da ta jefa
mutane, shine yayi sanadiyyar
rasa ganinta, ana haka kowa ya
watse babu ko wanda yake
kallonta, sai fa ni din nan, nima
dan dai kawai in sauke hakkin
makwabtaka, amma in ba haka
ba, babu abinda zai sa na kalli
mai mummunan hali irin na
wannan matar"
Ya karasa maganar, yana
mai nuna ta da yatsarsa.
"Hasbunallahu wa ni'imal
wakil"
Shine abinda Nawap yake
maimaitawa, yayin da yayi
saurin dauke idonsa akan
Goggo, wadda yake jin kamar
ya shaketa ya hada da bango
ta mutu kowa ma ya huta.
"Sai ki nemi yafiyar yarinyar
nan, tunda Allah ya taimaka
miki gata a gabanki a karo na
biyu"
Cewar mal. Labaran kenan
yayin da yake kallon Goggo.
"Na yafe mata ni kam, mal.
Ko yadda Allah ya mayar da ita
ai ya isa ishara gareta, da duk
wani mai hali irin nata, fatan
dai Allah ya yafe mana baki
daya"
Deedo ce take wannan jawabin
a lokacin da take share kwallan
idanunta.
"Amen" duk jama'ar wurin
suka ansa da.
Goggo dai banda wasu
surutai, da wasu yan bige bige
kamar wadda sauro ke cizo
babu abinda takeyi, sai kuma
lokaci zuwa lokaci kaji ta
kurma wani gagarumin ihu,
babu Allah, bare kuma salatin
annabi a bakinta.
Kofar gidan suka fito gaba
dayan su, in banda ita da bata
iya takawa sai dai
rarrafe.
Gaban mota Nawap ya
bude, ya fito da kudi wanda
bansan adadinsu ba, mik'awa
mal. Labaran yayi,
"A taimaka a gyara mata
ginin nan da ya rufta, sannan a
dinga sai mata abinci, inda hali
a samu wanda zai rinka
tsabtacce mata wurin, ni zan
rinka biya in har an samu
wanda zaiyi hakan, mun gode
mal., Allah ya kara girma, ya
kuma baku ladar abinda kuka
yi"
"Amin" ya fada, sannan
sukayi musayar number shi da
Nawap, ya wuce zuwa cikin
gidan shi, inda shi kuma ya kai
kallonsa ga su Deedo da sukai
jugum,
"Sai ku shiga mu wuce"
Babu gardama, duk suka
shige suka dau hanyar
komawa.
Sai da suka shiga Bauchi
sannan suka tsaya, domin
neman abinda zasu ci, anan
Deedo ta kira hally, tai mata
kwatacen gidanta suka je, nan
ta tarar da ita har da dan
yaronta mai shekara daya da
rabi, suna cikin fira take shaida
mata halin da Goggo take ciki,
addu'a dai sukai mata, inda
daga bisani ta fada mata
bikinsu kwana goma masu
zuwa. Hally kuma tai mata
alkawarin zuwa in har Allah
mai kowa mai komai ya bata
iko, sukayi sallama, sannan
suka dau hanyar Kaduna.
[26/04 02:05] Nty Lubiee:
BA'A SHAN ZUMA… 111
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
®NWA
Har suka iso gida firar da suke
ta irin mutane masu halayya
irinta Goggo ce, Hafsat wadda
abin ya zama sabo a wurinta
tace
"Allah kenan, buwayi gagara
misali, yanzu ji yadda matar
nan ta dawo, ko duniyar da
take ma hadama ta juya mata
baya, suma ya'yan da ta
musguna ma wasu saboda su
sun gudu sun barta, kai Allah
dai ya sa mu cika da kyau da
imani,"
"Amen" suka ansa da shi,
lokacin da suka iso kofar
gidan, ana ta faman kwalla
kiran sallar maghriba.
* *******
Kwana ukku da dawowarsu,
su Ummi suka dawo, inda tayo
siyayya ta ban mamaki, sun
hado mata lefe dai dai
gwargwado, babu karya, babu
kuma karanta a ciki, sai dai
san barka, haka kayayyakin
daki ma sun siyo dai dai
iyawarsu, inda suka karasa
siyen sauran anan gida
Nigeria.
Bayan Ummi ta natsu, ta
huta duk hankalin kowa ya
dawo jikinshi, anan take
tambayar Deedo yadda akai
bata je Ningin ba, ta kara da
cewar
"Ba dai mutumin can ne ya
hure maki kunne ba?"
Ta fada tana kallon Nawap,
Murmushi Deedo tayi, tace "ko
daya Ummi, munje ai"
Nan ta labarta duk abinda ya
faru, bata rage komai ba,
Salati Ummi tayi, sannan ta
kara da "Allah kasa my gama
da duniya lafia"
Suka ansa da amin gaba dayan
su, inda suka d'auko wata firar,
wadda yawanci duk labarin
yadda za'a tsara bikin ne suke.
Biki dai sai matsowa yake,
inda yau rage kwana hud'u a
fara. Kasancewar Deedo bata
da tarkacen kawaye, hakan ya
bata damar kammala duk wani
rabon invitation da zata yi,
wanda dama duk course mates
dinta ne ta gayyato, sai fa yan
mutanen da baza a rasa ba,
wanda suke gaisawa a
makaranta.
Hakan ya bata damar
natsuwa wuri guda, tana
daukar gyara a wurin matar da
Ummi ta dauko takanas, daga
Niger republic. Haka Hafsat ma
ba a barta a baya ba, itama da
nata sinadarin gyaran na
daban, wanda ya kasance
tsakanin ta da Deedo ne, sirrin
kissa da kisisina, da iya rik'e
miji kawai take dora mata,
yayin da Deedo take kwashe su
a kwakwalwarta kamar tana
rubutawa. Domin ko zamanin
nan dai sai da kissar, amma
sai kaga mace a harbutse, ko
magana bata iya ba, sai kuma
idan mijin ta ya kyallo wata
abun ya zama bala'i, a daure a
koyi sirrikan mazan aure
yanuwana.
Rana bata karya, wai sai dai
uwar diya taji kunya! Inji
Hausawa. Haka aka fara bikin
Deedo da Yaa Nawap dinta,
amarya sai kyalli take tasha
dilka, tayi kyau har ta koshi da
shi.
Daga su sai su suke bikin
nasu, dangin Maman ta ne, sai
kuma dangin baban su Nawap,
sai 'yan gayun kawayenta
wanda duka duka basu wuce
mutun sha biyar ba, biki ne
suke hankali kwance ba tare da
hayaniya ba, babu wata bidi"a,
illa kyakkyawar dinner da za
suyi a gobe, sai kuma daurin
aure.
Amarya ce ta fito cikin light
brown din gown mai asalin
kyau, wadda ta dace da kirar
jikinta, yayin da KHADY'S
MAQUILLAGE ta gwangwaje ta
tsararran make up mai daukar
hankali. Tayi kyau dai dai
misali, haka angon ya fito a
cikin danyar farar shaddar
Sheraton, wadda taji lafiyayyan
aiki da light brown din zare,
hularshi da takalmansa, gami
da agogonsa duk light brown
din, sunyi kyau kamar a sace.
Bayan sun shigo hall din Kabir
Gymnasium, inda ya kasance
can ne aka tanada domin
gabatar da dinner, nan fa aka
fara sakin flash, masu video
coverage suma suka cigaba da
dauka, yayin da zaka hango
farin cikin da yake kwance a
fuskar Ummi domin ganin
wannan kyakkyawar rana.
Haka aka cigaba da
rakashewa, ana gwangwajewa
yadda ya kamata, har aka gama
lafia, kowa ya kama gabansa.
Washe gari da misalin k'arfe
1 na rana aka Daura auren Dr.
NAWAP KHAMIS, & FIRDAUSI
KABIR SANI, akan sadaki mafi
daraja, wanda ya ta'allak'a
akan koyarwa ta ma'aiki
(S.A.W).
Bayan daura auren da
misalin karfe shidda na yamma
aka dauki amarya sai gidanta
dake Sultan Road. Komai ya ji,
babu abinda Ummi bata yi ba,
sai kuma fatan zuri'a mai
albarka.
Kwanansu biyu a Kd, sannan
suka tattara suka wuce Abuja,
kasancewar hutun da Nawap
ya dauka ya kare. Rayuwarsu
abin sha'awa, soyayya suke ta
ban mamaki, kowa kokari yake
yaga ya faranta ran dan
uwanshi, dan haka suke zama
na jin dadi da salama.
Satinsu biyu a Abuja su
deedo suka koma hutu, bata da
yadda zata yi, dole ta dawo Kd,
da sabuwar Mercedes-AMG
dinta wadda Nawap ya bata
tukwicin amarci.
BA’A SHAN
ZUMA…
K’ARSHE
BA'A SHAN ZUMA… 112
NA LUBABATU MAITAFSIR
&BENAXIR OMAR
®NWA
Shi da kanshi ya tuko su,
gidansu suka zarce ko da suka
shigo Kd, wanka sukai suka
gabatar da sallar maghriba
wadda tai musu a hanya,
Deedo ta fito cikin wani skinny
long skirt, da yar top dinta,
gashinta, ta tara shi wuri daya
ta daure, kitchen take k'ok'arin
shiga domin ta sama masu
abinci, a dai dai lokacin Nawap
ya fito palon shima cikin blue
din jeans da red din t-shirt,
gabanta ya karaso, ya mika
mata agogon dake hannunsa,
sannan ya miko hannun, yana
kallon ta.
Ansa tayi, tana tura baki tace
"Abinci fa zan girka mana,
kuma ka zo zaka tsaida ni"
Dariyar yadda tayi da bakinta
yayi,
"Gobe kaman haka baza ki
ganni ba, balle har na tsaida
ki"
Ya fada yana langabar da kai,
Itama fuskan tausayin tayi,
tunowar da tayi gobe fa ita
kadai ce; babu yayan ta.
"Yi sauri dauko hijab dinki
muje gaishe da Ummi, can sai
mu samu abinda zamu ci"
Ya fada yana kallon console
mirror din dake makale a palon,
yana gyara collar rigarsa.
"Da gaske Yaa Nawap?" Ta
fada cikin zumudi.
"Zan ce na fasa ko ki wuce
kizo mu tafi"
Da dan gudu ta shige daki tana
fadin "I'm sorry Mon amour",
Bata wani dade ba ta fito
sanye da dogon hijab har
gwiwanta, suka rufe gidan suka
shige mota sai gidan Ummi.
Taji dadin ganinsu sosai, sun
kuma yi sa'a tana zaune a
dining table tana cin abinci,
dan haka ba tare da bata lokaci
ba suka zauna suma, Deedo ta
zuba masu, suka cigaba da ci
suna fira.
Sai wurin goma da rabi,
sannan suka yi mata sallama
suka wuce gida.
A palo suka zauna, firar
yadda zasu yi missing juna
suke ta yi, a haka har sha daya
da rabi, inda Deedo ta fara
hamma, bata ankara ba ta
bingire a wurin ta cigaba da
bacci. Juyowar da Nawap zai
yi ya ganta sai bacci take,
murmushi yayi, don ya zata
baccin karya ne, saboda haka
take mashi, sai ya dauke ta ya
kaita daki sannan ta mik'e.
Shigewa yayi ya gama shirin
baccinsa, ko da ya fito dai a
haka ya tadda ta, dan haka ya
sa6i abinshi suka wuce dakin
baccinsu.
Tun karfe biyar na asuba
suka tashi, wanka suka yi, tare
da alwallah sannan ya ja su
sallah, bayan sun gama suka yi
adduoin da suka saba, Nawap
ya mike ya koma gado, inda ita
kuma ta wuce kitchen ta shirya
breakfast mai sauki, sannan ta
shirya jikinta da jeans wanda
ya matse ta tsaf, ta samo top
dinta mai fadi ta dora, tayi
kyau sosai, sannan ta matsa
inda yake a kwance, lokacin
karfe bakwai dai dai, fuskarsa
take shafawa har ya buda
idonsa,
"7:am har yayi kana bacci, ka
manta akwai aiki yau ne? Nd
flight din karfe takwas zaka bi"
Ya mike tare da salati,
"Ai duk lefinki ne"
Ya fada yana cire kayan jikinsa,
Ta mika masa towel, "je ka
shirya idan ka fito sai kayi
banbanmin" ta fada tana fita
daga dakin.
K'arfe takwas saura suka fito,
jikinta sanye da doguwar
abaya, ta yane kanta da gyalen,
ita ta kaishi har airport, sannan
ta dawo, tana mai cike da kewa
da maraicin mijin ta.
Daga nan ita ma skool ta
wuce domin sun fara lectures
tun satin da ya wuce.
BAYAN SHEKARA HUD'U
Deedo ce ta fito daga babban
asibitin gwamnati na garin
Kaduna, atamfar super wax ce
jikin ta dinkin riga da skirt, sai
dogon hijab dinta, hannunta na
dama sagale da farar riga ta
likitoci (lab coat), yayin da
dayan hannun yake dauke da
jaka, da kuma katon littafin
(text book) mai hoton
kwakwalwar dan Adam a jiki.
Gaban motar ta kirar BMW
M4 ta isa, ta juye tarkacen
hannunta a baya, sannan ta
bude bangaren driver ta shiga
ta bata wuta, ta wuce
hankalinta kwance.
Cikin unguwar rimi ta nufa
dai dai kan alkali road, naga
tayi parking gaban wani asibiti
wanda aka rubuta TAIMAKO
SPECIALIST CLINIC, lab coat
dinta ta buda bayan motar ta
dauka, yayin da ta shige cikin
asibitin kasancewar wayar da
aka mata kan tayi sauri tana da
marassa lafia. Cikin k'warewa
take bin gadajen marassa
lafiyar, a bayanta kuma nurse
ce tana dauke da file na
kowanne patient a wurin.
Gadon wani dan tsoho ta isa,
wanda yake fama da ciwon
zuciya, ta duba file dinshi, ta
juyo da kallonta gare shi
"Baba akwai gwaje gwaje da
zanyi maka, akwai kuma na jini,
sannan kuma zan duba bugun
zuciyarka, amma sai kayi
hakuri fa"
Cikin ciwo tsohon yace
"Kuma duk a nawa zakuyi
wannan aikin? Ni fa wlh ba
kudi ne da ni ba, sai da nace
su kaini na gwamnati, amma
suka kawo ni nan, ni ban san
ya zanyi ba 'yar nan"
Da murmushinta, ta kalle shi
"Kar ka damu Baba, domin
kuwa babban dalilina na bude
asibitin nan ba komai bane, sai
dan na taimakawa marassa hali
irin ka, in sha Allah za ayi
komai, ba kuma tare da ko
sisinka ba"
Ta mik'awa nurse din file
dinshi, sannan ta wuce zuwa
gado na gaba, haka har ta
gama round dinta, ba ita ta bar
asibitin ba sai misalin karfe
biyar na yamma.
[26/04 09:40] Nty Lubiee:
BA'A SHAN ZUMA… 113
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
®NWA
Tana shiga gidan ta zube a
palo saboda tsabar gajiyar da
ta kwaso, hannuwanshi taji ya
ziro ta kafadarta yana danna
mata su a hankali, lumshe ido
ta fara yi, tana jin tamkar a
mafarki,
"Likita bokan turai" shine
abinda ta ji an fada, wanda
yasa tayi firgigit ta juyar da
kanta tana kallonsa.
"Yaushe a gari?"
Ta fada tana kare mashi kallo,
murmusawa yayi,
"Ko 30 mins banyi da
shigowa ba, na gaji da missing
matata bazan iya daurewa har
sai Friday kafin na ganta ba"
Ya zagayo inda take a zaune
ya zauna a gefenta,
hannuwansa cikin nata.
Bude bakinta zata yi magana
wata kyakkyawar yarinya mai
asalin kama da Nawap, ga dan
banzan wayo, duk da
shekarunta basu wuce biyu ba,
ta rugo da gudu ta fada kanta,
tana shashshekar dariya.
"Mammy sannu da zuwa" ta
fada cikin maganarsu ta yara,
lokacin da ta mik'e ta rungumo
wuyanta, tana mai nuna farin
cikin ganin Mammyn tata.
Sama Deedo ta daga ta,
tana fadin
"Thank you Ummina "
Nawap ya jawosu jikinshi
yace "Ummi har kin manta da
ni ko, dan kinga mammy ko?
Gobe ma zan koma bazan kara
wasa dake ba"
Suka kyalkyale da dariya ita
din da Deedo, yayin da ta
zaunar da ita a tsakaninsu, ta
mika hannu ta rungumo
Nawap, shima haka yasa
hannunsa ya k'ank'amesu yana
jin soyayyar matarshi, da tilon
'yar tasa, har cikin birnin
zuciyarsa.
ALHAMDULILLAH, anan na
kawo karshen wannan labari,
kuskuren da nayi Allah ya
gafarta mana, Allah kuma ya
amfani abinda na fada dai dai,
ya bamu ikon amfani da
darasin da yake ciki.
This is a dedication to a sis
from another mother (FEEDO-
DEEDO) thank you 4 been
there always.
Special thanks to Aysha
Chuchu, Jam33la & Ummu
Ahmad, 4 loving this story like
no one.
Nagode kwarai da hakurinku
akan jinkirin da aka samu kafin
kammaluwar wannan labari. Ku
cigaba da kasancewa tare dani
a labarina na gaba wanda ya
ansa sunan K'ADDARAR
AURENA!
Lubabatu Maitafsir & Benaxir
Omar muke yi maku fatan
alkairi a koda yaushe.
Complied by Princess Aysha Muhammad