M. Ahmad yace mai haja family name din mahaifiya ta ne bana aiki da sunan mahaifi na. Abinda na sani dai shine sunan mahaifi na jibril. Zaro ido likitan yayi yace jibril wa? M. Ahmad yace gaskiya sai na tambayi mahaifiya ta.
Nan sukayi sallama su m. Ahmad din suka tafi.
Bangaren su lud kuwa gidan umma suka nufa da niyar zasuyi Mata surprise tunda basu fada Mata zasu zo ba.
Taji dadin ganin su sosai haka suka dinga hira. sai yamma tukunna suka koma gida bayan an hadasu da abincin dare.
Kamin su tsafin ne sai ga mansura kuskus ta shigo tace ma marakisiyya mu ja labule. Suna kebewa marakis tace shegiya kede in irin harkannan ya taso kece a gaba gaba anji kunya.
Mansura tace ke de kika sani da babu irin mu AI da kin shiga matsala.
Nan ta fada Mata kayan itatuwan da zata samu sai ta hada da garin da ta bata shikenan ba wani kayan cutarwa a ciki. Godiya tayi Mata kamin sukayi sallama har suka rage Mata hanya.
Kamin su karasa ne take fada masa AI zata koma makaranta yace toh ba matsala. A take ya Kira driver din gidan su yace ya kawo masa motan marakisiyya su hadu NNPC gidan mai.
Marakisiyya kuwa ana komawa aka bude fridge akayi Hadi ta saka rabi a Kofi tare da zuba garin a ciki ta sha ta ajiye sauran. Aka je aka yi wanka aka sha turare.
In takaice muku magana bayan marakis ta sha hadi nan lud ya gane an Sami matsala, kamar yadda marakis ke tunanin tausaya Mata lud keyi toh shima lud din haka yayi tunani yau Dan sanda akayi tashin hankali.
Da kyar ta barshi yayi bacci shi kuma ya dage bazai bada gari yace ya gaji ba. Da mugun sanyin sadiya ya tashi ya gudu zuwa gidan su zannu Dan bayason ma ta tashi ta kawo masa wani sabon zance.
Yanzu shi kam Dan ba kara duk yadda zaiyi ya dinga arcewa toh zaiyi. Tunda ya gama bawa zannu labari ya zauna ya dinga masa dariya har ranshi ya soma baci. Tashi yayi yace in bakada shawara da zaka bani gara nayi tafiya ta.
Riko Rigan shi zannu yayi yasa fuskan tausayi yace my lud ina zaka? Wai shi.a dole zai kwaikwayi marakis ne. Jifan shi da takalmi lud yayi yace bana son wulakan ci fa. Dan kaga ina neman shawarar ka shine zaka na tsokana ta?
Kokarin danne dariyar sa yayi yace toh I am sorry a yafe min please da alamu dai wannan matar tafi karfin ka toh kawai ka fada Mata mana kaga sai ta na tausaya maka. Lud yace kai mutumin ba wasa bane fa.
Fada daban aikatawa daban. Zankai ga yadda za'ayi.
Marakisiyya kuwa ko da ta tashi taga lud baya nan ta Kira wayan sa bai daga ba kawai sai ta tashi tayi wanka bayan tayi order din abinci ta ci abinta.
Daukan tarkacen ta tayi sai makaranta kuma shirye take da duk abinda zata riska.
Shigan ta makaranta ke da wuya yan sa ido suka hanzarta suka zanzara wa class rep. Ai ga marakisiyya ta dawo. Nan fa makaranta aka dinga binta da ido wasu kuma suna yi Mata congratulation.
Koda m.ahmad ya shiga ajinsu domin ya koyar aa kin kallon inda suke zama yayi domin rabon da yasa ta a idonsa tun ranan da wannan abun ya faru.
Haka de marakisiyya ta dinga binsa da ido tama rasa me ke Mata dadi ita dai tana ganin kamar tana son lud amma kuma kyawawan halin m. Ahmad ke Jan hankalinta zuwa gareshi.
Bayan an tashi m. Ahmad ya koma zuwa ga likita saboda m. Salis bai tashi ba yana da lectures guda daya da zaiyi. Koda ya zo likitan na ganin sa yace ah malam Ahmad Kaine da war haka aiko kazo da sauri Dan yanzu nake shirin zuwa duba wani patient.
M. Ahmad yace jiya na tambayi mahaifiya ta take sanar min da cewa sunan mahaifi na jibril mustapha arancaba(Dan Allah in akwai me irin sunan ba shi nake nufi ba). Dafe kirji litan yayi ya ja shi suka koma office yace kai Alhaji arancaba ne mahaifinka? m.Ahmad yace eh likitan yace tashin hankali mahaifinka na daya daga cikin mutanen arewa na farko da sukayi luwadu a baiyane.
Lokacin da ake kokarin kera allurar da nake fada maka ai yana daya daga cikin Wanda suka saka kudi da komai nasu akayi. Innalillah wa inna ilaihi raji'un. AI ya mutu mutuwar wulakanci ma kuwa.
An boye mutuwar sa ne saboda in masu itin halinsa suka ji kila zasu gyara hali. M.Ahmad gaba daya ji yayi guiwan sa tayi sanyi yace toh yanzu ya za'ayi kenan? Dr yace karka damu akwai maganin allurar da akayi maka.
Saide baza'a samu anan ba amma nasan wani aboki na insha Allah har nayi masa magana tun jiya zuwa jibi ma allurar zai osoba sai kazo ayi maka daga nayi ma na kwana biyu shikenan ma.
Abinda yasa take da effect a kanka saboda kana jariri akayi maka ne kuma ina matukar zargin cewa shi ne ya Nemo ku kuma ya same ku amma bai nuna muku ya same ku ba shine ya biku a boye da mahaifiyar ka ta haife ka shine yasa akayi maka wannan allurar.
Amma ni dai bansan me yake nema ko ya shirya yi ba toh koma de wannene insha Allah ka tsira tunda de yanzu ya koma waken alkalin da babu ya shi. Nan m. Ahmad yayi masa godiya tare komawa gida ya fada ma mahaifiyar tasa. Harda hawayen farin ciki ta rungume shi ko ba komai Santa zai samu lafiya taga jikokin ta.
Haka rayuwa taci gaba lud yana gudun marakisiyya ita kuma tana tausaya mai bataso ya neme ta tace masa ta gaji shiyasa ta dage da gyaran jikin ta.
Ankai ankawo fa to the extend lud sai ya bari tayi bacci yake dawowa gida sannan kuma kamin ta tashi yake fita har ta fara tunanin kode baya dawowa ne? Kiran umma tayi umma tace Mata ai yana yawan zuwa ya yini amma dai in yazo gobe zata tamabaye shi.
Lud fa yanzu a wajen zannu yake biya gaba daya ya mugun ramewa ne ? Har duhu yayi banda komai sai hanci Allah sarki tun zannu yana masa dariya har ya fara jin tausayin sa.
Zama yayi ya dafa kafadar sa yace my man kaje gida mana kawai sai ka fada Mata ka dena gudu kasan itama tana da bukata kar ka sata a wani hali yau 4 days fa Baku hadu ba.
Ajiyan zuciya lud ya yi yace my guy, naji kamshin gaskiya a maganar ka Allah ya gani yau zanje na fada ma marakisiyya gaskiya komai ta fanjam fanjam ta tausaya min ta daga min kafa.
TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO
Miss untichlobanty 💕
26th September,2020.
[13/10, 2:00 am] Miss Untichlobanty💕: *🤍🏆🤍YA JI TA MATA🤍🏆🤍*
🖤🖤by miss untichlobanty🖤🖤
marubuciyar :
*1.YARINYAR CE TAYI MIN FYADE*
*2. KURUCIYAR MINAL*
Feel free to contact me on :
WATTPAD miss_untichlobanty
INSTAGRAM miss_untichlobanty
TWITTER, miss_untichlobanty
TELEGRAM miss_untichlobanty
WHATSAPP: 08146448881
Your little sis loves you and don't forget to follow me!
*🤍CHAPTER 50🤍*
*NOT EDITED*
Koda m.salis ya karaso wajen sa m. Ahmad yace gaskiya kana da kokari ba kadan ba kuma kana da hakuri. M.salis yace toh ya aka iya zata gane AI komai Dan lokaci ne. Haka suka fita suna hira su m.Ahmad bai tambayi m. Salis yadda ma ta kaya a daren jiya ba Dan yasan ansar tunda yaga jikin ta.
Haka dai har wajen azahar yan uwan jummalo suka San inda dare ya musu bayan m. Salis ya basu dubu biyar biyar m. Ahmad bai tursasa ya koma gidan sa ba Dan haka suka yi yawon su tare tunda weekend ne ba aiki gara ma m. Ahmad za'a iya neman sa a makarantan.
Da magrib lis m. Ahmad ya dawo da m. Salis domin a motar sa suka fita. Sallama sukayi m. Ahmad yace toh brother a kula da amarya sai munzo suna.
Baki m. Salis ya bude kamin yace kana nufin bazaka kara zuwa gida na ba? m.Ahmad yace toh ni me zanyi a gidan ka? M.salis yace ina brother baka isa ba AI kullum sai kazo m. Ahmad yace haba sai kace gida na? Barshi dai juma'a juma'a ina shigowa sai mu dinga gaisawa da amarya amma kullum AI muna tare a gidan mama.
M. Salis yace toh na yarda da wannan. Nan dai sukayi sallama m. Ahmad ya nufi gida m.salis shima ya shige gida. Sallama ya dinga zabgawa amma shiru ba amsa. Kara ya jiyo a dakin yaran hakan yasa ya fito yaje ya duba. Gani yayi jummalo da mando na cukun cukun cire hannunta da vacuum cleaner ya shanye.
Da sauri yaje ya kashe shikenan hannunta ya fita. ajiyan zuciya ta sauke tace kai kai kai gaskiya aradun Allah bani sake aiki da wannan abar kawai ni ka bani tsintsiya ta. Dafe kai m. Salis yayi Anya kuwa bai yi kuskure ba? Yace toh ya ma akayi kika sa yatsanki?
Turo baki tayi tace toh ba mando bane ya kai hannunsa wajen da yaji zubowa yakeyi shine Dan mugunta ice min in sa nawa ina karawa sai ya tura shine fa iskan taci gaba da jan hannun ga karhi ne da hi na kasa cire hannun nawa.
M. Salis yace toh ai ba'a saka hannu kinga yanda ake yi fa ba na koya miki ba? Saita komai yayi ya gyara dakin mando yace kinga yadda ake yi ba? Toh kema ki kiyi mu gani.
Daga nan ta kware tayi abinta mai kyau yace yauwa. Haka ya bita sukayi komai da komai tare domin kaman ba gidan amarya ba ita da mando daga gani kasan sunyi guje gujen nan nasu saboda me?
Parlourn gaba daya sun zubda cushion din, sun fado da labule daya gashinan gashinan dai. Yace Mata ga can dust bin a nan zasu dinga saka datti idan kuma danyan Abu ne asa a na kitchen mando ya dinga fitarwa ya zubar a can waje cikin babban dust bin din.
Tace menene dos bi kuma yace Dust bin akace ko trash bin shine kwandon shara. Bayan ta gyara ne yace sai anyi magana mutum da safe yace wa mutane yana da tsafta zaije yayi wanka.
Tace AI Dan bansan yadda zan gyara gidan bane hi yasa. Yace munji yana mai shiga dakinshi ya fada kan gado tare da rufe ido. Kamar Wanda aka zaune shi ya Mike yana kallon gadon a tsorace tunowa da basu gyara gadon inda ta bata ba kar yaje ya kwanta a kai amma sai yaga wayam.
Daidai lokacin ta shigo tana shan bakin shayi yace ashe de dagaske kina da tsafta? Tace ban fadi maka ba? Ai babu ya ni kaf kauyen mu aradu kayi dace. Nan ta zauna ta hau bashi labarin kauyensu bata ma San bacci ne ya dauke shi ba.
Sai lokacin sallah ta ga bai tashi ba anan ne da ta Kira sunan shi taji shiru nan tayi zuciya wai yace bakinta yana waring shiyasa ya kifa hula a fuskan sa yayi bacci. M. Salis Dan kar ya rasa sallah ne ya fice ganin in ya tsaya sai akai gobe bata sauko ba shi a dole za'a ce ya fadi abinda bai fada ba.
..........
M. Ahmad kuwa shima sanda yaje gida ne ya samu daman yin tunani ma. Dan gaba daya bai ma samu zama shi daya ba balle yayi tunani cikin bazance nazarcen sa ne ya tuno da sanda yaje gidan m. Salis din. Tare da tuno yadda jummalon ta bata jikin ta dadin abin m. Salis ya yaga Mata mayafi Dan idan da ta ita ne toh tabbas bazata saka komai ba.
Mikewa yayi ya zauna daga riginginen da yake yace idan kuma ba jinin al'ada bane fa? Toshe baki yayi kamar mace shima yace shege salisu ni wonder duk tsiyar da take masa ko ajikin sa.
Wani tunanin ne yazo masa wata zuciyar tace ina ruwanka? Kaide ka Samu ka nemi Mata kayi aure kamin kaji kanin ka yace ma zai zama uba kai ko mai gida baka zama ba.
Mahaifiyar sa ce ta bude kofa ita ma tana fadin baba na ashe ka dawo? Toh ka dai gani banson in takura ma amma kanin ka yayi aure kaima ka soma gyara naka gidan ka samu daga ka warke ka ajiye iyali.
M. Ahmad yace insha Allah mama AI nima gefen gidan sa ba siya gidana guda biyu zan fasa su koma gida sai na hade su. Tace masha Allah ka yi zurfin tunani toh Allah yayi albarka.
Yace ameen ba'a wani Dade ba aka Kira sallah hakan yasa shima ya tashi ya fita.
........
Bangaren su lud kuwa yanzu zaman lafiya ake ba tashin hankali. Marakisiyya ne ke saka musu kayansu da aka kawo daga wanki da guga yayinda lud ke zaune a kan gado yana neman aiki Wanda ya fara ne kwana biyar da suka gabata.
Tace wai har yanzu baka gama ba? Yace na kusa ina diba wani Abu ne. Bayan yan mintuna kalilan ya rufe laptop dinsa yace albishirin ki. Tace goro yace na samo mana gida Wanda yake daga nan ba nisa da gidan umman ki kwalta biyu ne.
Anguwan opposite din anguwan mu ne tsalle ta daka tana mai fadawa jikinsa tace kayi Allah kayi mijina Alhamdulillah! Nuna min hotan gidan ba gani.
Yace nope surprise ne kuma ban ma fara gyaransa ba jiya na siya yau muka gama komai. Tace gaskiya nayi farin ciki Allah yayi albarka ya kara arziki yace toh tashi. Tace menene? Yace da fari dai idan ba jariri kike nema ba ki tashi, na biyu kuma kalli bayan ki ta juya tace banga komai ba.
Tana Jan kwalar rigansa tace ko guduwa kake son yi? Yace ni zaki yi wa shagwaba? Young lady gyara muryanki ko kiyi shagwaba da dalili. Bude baki ta yi zatayi magana yace kalli kasa.
Dafe kirji tayi ta Mike tare da daka masa duka tace shine bazaka fadamin na barar da kayan ba? Yace kinci bashi dukan nan nawa da kika yi. Tashi yayi ganin lokacin sallah ya kusa ya bude kofa zai fita yace kuma yau bazan kwana a nan ba tunda abin harda mugunta.
Da tsawa tace baka isa ba kamin ta fashe da kuka tana mai fadin ka siyo min gasasshiyar masara. Dariya yayi yace na 'ki din mai hakwaran masara😂
INJI COMMENTS, VOTES SANNAN AYI SHARING KAMAR BA GOBE, IN AKAYI HAKA TOH ZATA FASHE AMMA ARZIKI NE ZAI FASO.
TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO
Miss untichlobanty 💕
9th October, 2020
[13/10, 2:00 am] Miss Untichlobanty💕: *🤍🏆🤍YA JI TA MATA🤍🏆🤍*
🖤🖤by miss untichlobanty🖤🖤
marubuciyar :
*1.YARINYAR CE TAYI MIN FYADE*
*2. KURUCIYAR MINAL*
Feel free to contact me on :
WATTPAD miss_untichlobanty
INSTAGRAM miss_untichlobanty
TWITTER, miss_untichlobanty
TELEGRAM miss_untichlobanty
WHATSAPP: 08146448881
Your little sis loves you and don't forget to follow me!
*🤍CHAPTER 49🤍*
*NOT EDITED*
Da sallamar su suka shigo BILKISU kawar maman Dan musa ne tayi musu iso kamin ta shiga ciki ta sanar da su jummalo. Fitowa sukayi da ita suka zauna m. Ahmad ne ya fara magana da innalhamdu lillah. Gaban ta ne ya fadi da ras.
Nasiha da duk wani Abu da ma'aurata ke bukata m. Ahmad yayi musu kamin ya Mike yana me kallon agogon dake sakale a hannun sa Wanda gashi ke kwance yace toh saida safin ku Allah ya bada zaman lafiya.
Maman Dan Musa ya kalla yace auntyn mu ga abincin ku a Kan dining table. Ita dai ta amsa da toh ne bawai Dan ta gane ko ta san menene dining table din ba.
Bayan ya fita ne su bilkisun suka nemi wajen kwanciyan su. Ango da amarya ma suka nufi nasu daki kamar yadda m. Salis yayi tunani. Domin da ya nufi hanyar daki ya dauka jummalon ta biyo shi.
Ha'a ya shiga daki ya juyo yaga wayam, sai yayi tunanin ko Wanda suka kawota wayaiyu be sun Dan yi Mata bayani ita kuma ta fahimta a baibai ta tafi dauko plate. Murmushi yayi yace a cici abin da ke ranta kenan.
Wasa wasa minti har 8 amma mutuniyar ku bata iso ba. Tashi yayi ya fita bayan ya ajiye hulansa da babban Riga gaban madubi, amma me? Sai ya ganta zaune inda ya barta.
Gefen ta yaje yana tunanin toh ko bacci ne ya kwasheta tun kamin sanda m. Ahmad me musu nasiha? Amma yana kiran sunan ta ta amsa da na'am. Yace na dauka bacci kike yi AI naga baki shigo ciki ba.
Tace ka fadi min ne ?ni da hiska ta ke cikin tsumma ta ina zan gani?yace gyale de ko? Tace koma wanne ne mu tahi saida safe sai yaga ta kama hanyar dakin da su ummu musa suke.
Yace ina kuma zaki? Tace bacci nikeji. Yace AI ga hanyar dakin mu. Tace dakin mu? Au haka fa ahe in anyi aure daki daya ake kwana. Mancewa nayi imin uziri.
Murmushi kawai yayi a ransa yana fadin AI tun ba yau ba nayi miki uziri. Bayan sun shiga daki sukayi sallah tare da cin duk abinda zasu ci. Banso my zurfafa dominn ko jummalo Sam nuna wa tayi bata San inda m. Salis ya nufa ba domin ita Sam banda rike hannu toh ko anyi aure ba abinda aka halatta sauran iskanci ne.
Ita kuma bata shirya mai garin su yasa ayi Mata bulala ayirin (20)ba kamar yadda sukeyi bisa dukan garin su ba wai bin Shari'a ba. Abinda bata sani ba shima m. Salis din bawai wani tsiyar zai Mata ba Dan ba narkewa ya gama yi ba yana dai son ya dinga rabarta ne Dan ya Saba.
Abin haushin ma ashe al'ada takeyi ta dinga basa ciwon kai Dan sanda akayi kusan minti 30 ana Abu daya. Daga karshe ya bata hakuri ya hau kujera yayi kwanciyar sa yana shawara shin ya fadawa m. Ahmad ko kuwa ya zama namiji kuma mai gida ya dinga samar wa kansa maslaha?
A haka har bacci yayi awon gaba da shi dukda ko yana jin jummalo dake watsa amaro tana juye juyen ta a Kan gado.
Washe gari ko da ya tashi ya samu tayi wargaje wargaje a kan gado gashi duk tayi staining wajen hakan yasa bai tashe ta sallah ba ya fice yana tunanin wato da ta fada masa tana al'ada gara ta nuna bata San komai ba.
Bayan ya dawo daga sallah ya dauko paper zai Mata rubutu akan kar su dafa komai dafe kai yayi tunowa da bata iya rubutu ba ma yace kai ina da aiki fa. Haka ya fice yana mai mika daganan ajiyan gidan sa hannun Allah.
Kar kamin ya dawo a kone masa ita😂. Bai ma yi nisa ba ya hango motan m. Ahmad hakan yasa shima ya juya suka dawo gidan tare.
Gaisawa sukayi m. Ahmad yace ango ango ango mijin amarya an tashi lafiya? Murmushi m.salis din ya yi yace Alhamdulillah! yana mai yiwa m.ahmad din iso zuwa cikin gidan.
M.ahmad yace wai ya naga da sanyi safiya ka fito ? M.salis yace wallahi abin Karin kumallo zan Nemo nasan yan kauye da tashin safiya. m.Ahmad gashi har mama ta hada muku kaga kun huta ma kenan saide ba nauyi fa shayi da bread ne sai kwai but tace karfe tara zan kawo muku gwaten wake.
Cikin fara'a m. Salis yace gaskiya muna godiya bari ma na bika Muje nayi Mata godi......kamin ya rufe bakinsa sai ga mutuniyar wato jummalo ta fito tana sose sose. Ba tare da ta kallesu ba tace wai ina zaka da sanyi sahiyan nan?
M.salis yace gidan mu zani,wuce su tayi zuwa kofar da zai kaita farfajiyan gidan tana leke leke. M. Ahmad yace ke wai baki iya gaida mutane bane? Kin fito ba Dankwali a kanki bayan sarai kinji muryar da ba ta mijin ki ba?
Har ya karashe zancensa bata juyo ba saide ta dena leke leken da takeyi fuskarta yayi ja a take. Tabbas tasan ba mijin ta bane kadai a gidan amma bata dauka m.ahmad bane.
Juyowa tayi tana kumbure kumbure tace barka da sahiya. Da gudu tazo ta rike hannun m. Salis cikin shashancin tace wai nikam so kake ka kahe mu ne? Ni banga rijiya ko tuka tuka a gidan nan ba da mi zamuyi wanka? Jiya ma da badan akwai ruwa cikin bokataye ba da hikenan bazamuyi alwala ba.
Shi kuma ruwan da ke cikin randar bahida yawa bai wuce Kofi daya ba. Kuma nasan duk hyawarar wannan yayan naka ne ko hiya wata(pure /sachet water) ai ka kawo mu hya.
M. Salis da tsikar jikin sa ke tashi tunda ta rikoshi yace muje kitchen in nuna miki. A Kitchen din ya nuna Mata bottle water da yadda ake budewa. Ya nuna Mata fridge da aikin sa.
Fitowa sukayi ya nuna Mata yadda ake aiki da su famfo Dan bai yi kama da normal famfo ba da yake akwai su control din shower amma yadda ake kunnan famfo kawai ya nuna Mata.
Dan abubuwa masu muhimmanci duk ya nuna Mata sannan yace shikenan an yafe min? Tace sosai ma kuwa ni na tahi yin wanka domin tsafta gareni. Tana kaiwa nan ta saki hannunshi ta shige daki yayinda m. Ahmad dake zaune yana kallon ikon Allah ya saki murmushin da bai ma San yayi ba yana tabe baki.
Koda m.salis ya karaso wajen sa m. Ahmad yace gaskiya kana da kokari ba kadan ba kuma kana da hakuri. M.salis yace toh ya aka iya zata gane AI komai Dan lokaci ne. Haka suka fita suna hira su m.Ahmad bai tambayi m. Salis yadda ma ta kaya a daren jiya ba Dan yasan ansar tunda yaga jikin ta.
TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO
Miss untichlobanty 💕
19 -
[13/10, 1:52 am] Miss Untichlobanty💕: *🤍🏆🤍YA JI TA MATA🤍🏆🤍*
🖤🖤by miss untichlobanty🖤🖤
marubuciyar :
*1.YARINYAR CE TAYI MIN FYADE*
*2. KURUCIYAR MINAL*
Feel free to contact me on :
WATTPAD miss_untichlobanty
INSTAGRAM miss_untichlobanty
TWITTER, miss_untichlobanty
TELEGRAM miss_untichlobanty
WHATSAPP: 08146448881
Your little sis loves you and don't forget to follow me!
*🤍CHAPTER 51🤍*
*NOT EDITED*
Da tsawa tace baka isa ba kamin ta fashe da kuka tana mai fadin ka siyo min gasasshiyar masara. Dariya yayi yace na 'ki din mai hakwaran masara😂
Tace ni ba hakwaran masara bane da ni kuma sai na fadawa umma na abinda kamin. Yace kice bakyason ki ci masara tace toh yi hakuri ka siyo min masaran kaji pleaaase! Yace zanyi tunani.
Jifan sa tayi da gajeran wandonsa dake hannunta. Da sauri ya rufe kofar yana dariya. Yauma kamar kullum ya hadu da wanna receptionist din suka gaggaisa ya bata kudi yace a kula masa da madam duk abinda take so a bata.
.......
Washe gari m. Salis ya fito ya samu jummalo tana ta kokarin dafa dankalin hausa wato sweet potatoes. M.salis yace matar ba gaisuwa ne? Ta sharesa. Dama ya lura tun jiya take sharesa in ba ya zama dole ba bata kulawa shi kuma ya gama nazarin sa bai ma San me yayi ba.
A ransa yace Allah gani gareka nikam na kasa gane Mata kuma inajin har na mutu bazan gane su ba, bansan de ko Dan ita yar kauye bane yasa take caja min kwakwalwa. Gaskiya ne da ake cewa aure sai hakuri kar nayi zuciya naki yi Mata magana abin ya koma gaba.
Matsowa yayi ya dafa kafadan ta yace matar magana fa nake tace Ayya abinka da yar kauye AI ban iya gaisuwa ba. Yace yaushe nace....? Sai kuma ya tuna da tunanin da yayi kila ya subuce masa ya fito ne ta ji me yace.
Yace Ayya uwar gidan salisu baki gane bane fa ni ba haka nake nufi ba... race kuma bana son na gane. Da kofar kitchen din ya jingina yana kallon ta ga yadda hannun braziyar ta suka baiyane yayi magana tace ya zageta gara ya bari in ta huce ya gyara Mata.
Sallaman m. Ahmad yasa m. Salis amsawa yana mai fitowa daga kitchen din tare da mika masa hannu. M. Ahmad yace ya na ganka haka baka shirya ba ? Au na mance ashe angwanci ake sha baza'a je makaranta ba. Abin yayi wa dalibai dadi.
M. Ahmad ya fadi hakan cike da tsokana murmushi m. Salis din yayi m. Ahmad ya kara da amarya ma ganin wanka fa irin wannan shadda haka da kasha ga kamshi da ke tashi. Allah dai ya bada zaman lafiya. M. Salis yace uhm ameen.
Da shike m. Ahmad din babba ne hankali ya fara jika shi hakan yasa ya fahimci akwai matsala. Yace kodai akwai matsala ne? M. Salis yace babu wata matsala yana juyawa Dan ya shiga daki.
Riko hannunsa m. Ahmad yayi yace haba bro bama boye boye AI kuma ba wani Abu da bai dace ka fada.kin na tamabaya ba. Kaga in da matsala ku warware tun da wuri daga tarewa har an fara da uhm? Ni shi yasa banso ka auri yar kauye ba amma ganin kamar tana da tarbiyya yasa na bada gari.
M. Salis zama yayi a hannun kujeran da m m. Ahmad ke zaune yace yaya Mata na da muguwar matsala muma muna da shi amma nasu yafi namu wallahi, ni fa ban ma San me nayi ba amma matar nan ko kallon inda nake batayi kuma ni yanzu na tamabaya ma ace nayi sabon laifi.
M.ahamd yace toh bari in tambaya ma. Shigowqn ta parlourn yasa dukan su biyu kaman masu jin tsoron ta suka gyara zama suma gyara zaman shaddodin da suka saka. Kamar surukar su ce ta shigo shi m. Ahmad kar ta raina shi kuma m.salis kar tace yayi wani abun.
Kallon m. Ahmad tayi tace sannu kamar bai ji ta ba ya dauke kai tabe baki tayi taci gaba da jera abincin da ta dafa. Ba tare da ta kalle su ba tace mijin yar kauye kaje ka shirya ka tafi makaranta kar daliban la yan birni suyi kewan ka.
Bude baki yayi zaiyi magana tace banson ji. Sum sum kamar danta ya tashi yana kallon m. Ahmad irin ka gani ko? M. Ahmad kamar baisan me ke faruwa ba ya tsare yaci gaba da daura idanun sa akan talabijin dukda baya gane me ke wakana a ciki ba ma.
M. Salis kuwa zama yayi a gado ma ya ciro wayar sa a aljihu ya fara buga "mortal combat" a ranshi yana fadin babban yaya na zaiyi maganin ki. Yadda yayi maganar har sanda na murmushi kamar wani yaro irin anci zalin sa ya Kira babban yayansan nan.
M. Ahmad kuwa yadda yaga tana kara hade rai yasa yace ke? Dagowa tayi yace jummai ko? Ta kara cin magani yace zo, sauna ina da magana da ke.
Zuwa tayi ta zauna yace me ya hadaki da Dan uwa na salisu kike ta har hade masa rai ke haka ake wa miji? Sai kuma yace zai kara aure nan zaki bugi kirji kice bai isa ba, me kika rage shi da shi ko?
Kananu tayi da ido yadda fulani ke yi in zasu yi masifa tace eh lalle ma, wato si wannan mijin nawa kara ya kai maka bayan si ne bashi da gaskiya ko?... hannu m. Ahmad ya daga Mata yace ni ba banbami nace kiyi min ki cika min kunne ba.
Nace me ya miki in bashida gaskiya sai nayi masa magana ba ku tsaya kuna share juna kamar yara ba. Tashi yayi ta tsaya tace kaima sawun kafar nashi zakabi AI ba sai ka fada ba nasan kun girman shi yasa zaku ci zalina. Ta karashe maganan tana bare masa baki.
Jin kukan ta yasa m. Salis fadin Allah ya kara yar banza dama ba cewa take na zageta ba ta hadu da daidai da ita indai bazata daina min abinda take min ba kuka ta dinga yi Dan dole ayi Mata fada saboda ta gyara hali.
Jummalo kuwa cike da turo baki tace yanzu da safen nan ba cemin yayi yar kauye ba wato irin yana da dalibai wayaiyu ko? M. Ahmad yace shi ya dada miki haka ? Tace da kunnena na ji shi kasa kasa yake magana ya dauka bazan ji ba.
M. Ahmad yace amma AI tun jiya kike kin kulasa tace jiya ne fa da yamma bayan ka sauke sa ina basa labarin garin mu kawai yasa hular sa ya rufe fuskan sa yayi bacci.
M. Ahmad yace ai bayaso yace miki bayason yaji labarin ne jiya ya gaji sosai shiyasa. Tace ba wani nan kawai de yana nufin ina warin baki ne Dan banayin bayush (brush) sai asiwaki.
Yace me bayush kuma? Tace kar ka canja zance ni bakina baya wari Allah baki na baya wari ta fada tana bubbuga kafa.
Dafe kai yayi Yace ni nace bakin ki yana wari ne? Ya za'ayi na sani ni da ban taba shinshina ba? Matsowa tayi tana fadin kaji fa.yayin sa take bude baki daidai lokacin m. Salis ya turo masa message.
Zaro wayan sa yayi a aljihu yana shirin bude sakon kawai yaji mutum a jikin sa tana fadin gashi kaima kana kauda kai yayin da tasa hannu take juyo da fuskan sa domin ta kalle sa.
TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO
Miss untichlobanty 💕
[13/10, 1:53 am] Miss Untichlobanty💕: *🤍🏆🤍YA JI TA MATA🤍🏆🤍*
🖤🖤by miss untichlobanty🖤🖤
marubuciyar :
*1.YARINYAR CE TAYI MIN FYADE*
*2. KURUCIYAR MINAL*
Feel free to contact me on :
WATTPAD miss_untichlobanty
INSTAGRAM miss_untichlobanty
TWITTER, miss_untichlobanty
TELEGRAM miss_untichlobanty
WHATSAPP: 08146448881
Your little sis loves you and don't forget to follow me!
*🤍CHAPTER 52🤍*
*NOT EDITED*
Zaro wayan sa yayi a aljihu yana shirin bude sakon kawai yaji mutum a jikin sa tana fadin gashi kaima kana kauda kai yayin da tasa hannu take juyo da fuskan sa domin ta kalle sa.
Kamar an jona masa transformer haka ya ji wani gumi ya karyo masa yayinda mutuniyar kuwa ta tsaya kallon sa tana fadin yaya Ahmad kaga na FISA gaskiya ko?
Ganin dai ya tsaya cak yasa itama ta tsaya tana kallonsa yayin da take kyakkayfta ido yar karamar kwakwalwar ta na tunanin ko lafiyan sa? Shi kuwa bai masa tana magana ba kawai Zane fulani ta dake gefen bakin ta yake kalla.
Tace ya Ahmad kaga na fisa gaskiya ba bakina baya wari ko? Bakin sa na rawa in ya bude ya rufe in ya bude ya rufe hakan yasa yace um. Ta cikin daga murya tace kaji ko mijin yar kauye bakina baya wari.
Cire hula m. Ahmad yayi da hannu yana Mata alamar tayi shiru yayin da yake fifita Dan numfashin sa dake dauke masa, bai taba sanin yana da asthma ba sai yau, bayida asthman de amma yaji yadda masu asthma suke ji. Murya na rawa yace Mata jummai,
Kallon sa tayi tana wangale masa baki yace jummai tace iye? Yace kar ki dinga... ya zan miki bayani ne? Kinsan me ake nufi da muharrami? Ta girgiza kai a ranshi yace salisu kana da aiki sai ka sakata makaranta.
Yace toh zan fadawa mijinki ya miki bayani, turo baki tayi tace ah ah ni kai zaka fada min yace mijin ki de ni gida zan tafi. Rike hannunshi tayi tana jijjiga tana Dan tsalle a dabara ya janye hannunsa tare da mikewa domin tafiya Dan yaga alamu ko magana bazai samu daman yi da mijin nata ba in ya tsaya sai ta sa ya sabwa Allah.
Daga samun lafiya sai ta wani zo tana latsa sa dukda ya lura cewa batasan ba daidai takeyi ba. Hakan yasa ya hade rai Tace zan fashe maka da kuka fa ince ma yaya salisu bakason ka koyawa matar sa karatu tsaki yaja yace karki dinga zuwa jikin maza kinji ? Sannan ki dinga rufe jikin ki in kina gaban namiji idan ba haka ba Allah wuta zai saka kj.
Zaro ido tayi tace amma ai mando kanina namiji ne, yace banda kanin ki yana kaiwa nan tayi sauri ya fice saboda yadda gaba daya hannun riganta ya zame Wanda bata damu ta gyara ba ga tsalle da ta tsaya take masa bai taimakawa lamarin ba.
Yana fita ya sauke ajiya zuciya yana jinjina kai yace a ransa yace gidan nan ba gidan zuwana bane har sai matar nan tayi hankali. Amma kuma wani bangare na ransa yayi wasai ko ba komai yanzu yasan ya Sami lafiya.
Bayan ya shiga motan sa har ya five a gidan ne ya Kira m. Salis yace masa ga matar sa nan ya Mata fada shima ya Dana Mata nasiha sannan ya sakata a makaranta bai jira mai m. Salis din zaice ba ya kashe wayar sa.
Jummalo na shigowa daki m. Salis ya Mata murmushi yake tayi masa da sauri ta zaro hijabin ta ta zabga ta nemi waje ta dake. Kallonta yayi yace kin huce ? ni dama ban dau fushi ba kawai naga kana zagi na ne Dan kaga banida wayo banje makaranta ba.
Yace yanzu dai kin hakura ko? Tace eh yace toh ya kika zauna a nesa? Bata kulashi ba tashi yayi ya matso kusa da ita ta matsa ya matso ta matsa har ya tsargu tashi yayi ya shiga ban daki ya shinshina jikin sa yaji dai baya wari ya kalli kansa madubi komai normal.
Batasan ya fito ba sai ki tayi yazo ya rungume ta ta baya yace haba matar salisu fishin ya isa mana. Tsalle tayi ta fita da gudu kamar me aljanu tana fadin kar ka tabani.
Haka suka dinga kewaye gidan wai bazai tabata ba. Shidai yace yaga ta kansa da wannan Mata sai kace annoba?
Har dare ma tace ya jira ta a daki da ta hada abincin sai taje ta kwankwade dakin sa ta sanar dashi sannan ta shige nata. Bayan ya gama ci ne ya shiga dakin ta lokacin tana wanka fitowanta daure da zani gashin hamtanan nan suna fadin excuse me taga mutum yayi tsam Alan gado komawa tayi da sauri tana leko kai tace ya salis me kake nema?
Yace sai ina neman Abu ne zan shigo dakin matata? Tace toh nide ka juya zan hito na sa tufafi ba musu ya juya ta fito tare da zura dogon Riga. Juyowa yayi bayan ta bashi dama yace jumy wai me ya sameki ne? Ni, ni na kasa gane kanki tunda aka miki fada shikenan ko kinada aljanu ne?
Dafe kirji tayi tace Allah ya rabani da segun nan aljani wai, no banida wani aljani me ka gani yace toh AI naga sai gudu na kike yi. Tace ba fa gudun ka nake ba nasiha ne ya amadu yayi min cewa in dinga rufe jikina kuma in daina zuwa kusa da maza sai muharramai na.
Yace toh AI gaskiya ya fada miki nu ma AI muahrramin ki ne. Tace um um ni mando kawai yace min banda shi ku ba muharrami na bane, m. Salis yace ya Ahmad din ne ya fada miki hakan? Tace Itoh hide haka na fashinta(fahimta).
Tana kaiwa nan kuwa ta bude kofa ta tura sa ta Dane gado sai bacci. Zuwa asuba ta rataya kafafu a kallon gadon m. Salis kuwa yana shiga dakin sa ya Kira m. Ahmad yace ka janyo min matsala brother ka ware wani ka daura wani.
M. Ahmad yace me ya faru? M. Salis yace gobe ka dawo kawai Dan Allah gobe ka dawo da sauran rina a kaba. M. Ahmad yace Allah bani zuwan gidan nan.
Salis yace Please brother Ahmad yace ba inda zani fa yana kaiwa nan ya kashe wayar yana sauke ajiyan zuciya. Kiran m. Salis din da ya kara shigowa wayan sa ne ya tsinka masa zuciya har sanda gaban sa ya fadi.
Kin dauka yayi m. Salis ji yake kamar ya mutu ya rasa inda zaisa kansa. Hakan yasa wata dabara ta fado masa ya yanke shawarar TV zai dinga kunna jummalo ta dinga kallon American films hakannan tunda su ba kunya suke da ita ba sai kuma ya sa m. Ahmad yace Mata ta dinga yi ma m. Salis din duk abinda ta gani a film.
Da wannan shawarar yayi bacci kansa na Sara masa saboda ciwon kan da ta basa.
............
Bangaren su lud kuwa yau shopping da yawon shakatawa yakai marakisiyya bayan ya dawo saide kuma ya rasa game kanta Dan kamar mayya batada aiki sai cin masara da naman kaza nace Ayya you don't know what is going on😂
Shida da rabi na yamma a hanya ta musu lokacin gari ya fara duhu taga wani me balangu yadda ta riko hannun lud har sanda gaban sa ya fadi yace menene ya faru cikin murya kamar zata fashe da kuka tace balangu!🥺
Ajiyan zuciya ya sauke yace haba baby yanzu yadda kika sa nayi birki da na daki motan wani fa? Har kin tsinka min zuciya tace toh yi hakuri zaka siya min balsn gun? Yace kina ta kashe min kudi na yaushe yaushe na bude.... sai kuma yayi shiru tace ka bude me?
Riko hannun ta yayi yace kinga boutique dinnan da muka je? Daga kai tayi yace nawa nesting da ya wuce na bude dama surprise naso na miki in mun koma gida yanda daga na fada miki sai ki bani balangu.
Tace au haka fa toh baka siya mana balangu ba ta yaya ni zan baka,yace ba wannan balangun make nufi ba, race toh wanne? Yace kawo kunnenki.
A hankali yayi Mata rada Wanda tsabar girman maganar sanda ta rufe baki tace na shiga uku ni karka koyamin tambada. Da rashin kunya nan ya dinga tsokanan ta suna dariya suka siya balangun suka tafi.
Saide me bayan sun fara ci ne suka lura akwai tsutsa a ciki marakisiyya ce ta gane da yake dukda dubun motan taji tafiyan Abu a hannun ta. Tana haskawa taga tsutsa take ta shararo amai tsikan jikin ta ya fara tashi Allah ya taimaka shna saitin chemist.
Maganin tsutsa ya siya ya bata a take ta sha shima ya sha Dan ya ci guda daya Wanda dakyar ya samu ta tsamma sa a hakan ma tana korafin ya cije ta.
Reverse lud yayi a ba tare da bata lokaci ba sai tungan me balangu. Gefe ya ja shi ya nuna masa yace menene wanna? Saboda shi lud yaso suyi magana asiri a rufe yayi masa nasiha da nuni cewa abin da yake yi zalinci ne.
Sannan yasa shi ya zubda naman yau gaba daya kar ya siyar ya bada wani abun ma saboda ya rage asara. Saboda shi mai laifi in ya tuba sai a taimaka masa wajen gyara kuskuren sa.
Amma me mutumin nan ya rufe ido yace Sam Sam shi ba tsutsa a naman sa shekara 4 hudu kenan yana sana'ar nan ba musu lid ya matso gaban tukuban mutanae da sukayi layi sunzo siya ya dauko wayar sa ya haska wake yace kowa ya matso AI kuwa yana haskawa wata tsutsa na kwana kwana tana lakwashewa jin an haska ta yasa tace hello tare da tsayawa tana kallon mutane😂
Nan fa akayi wa mutumin ca daga karshe yasha duka Dan lud shi gaba yayi abinsa yana shiga motan yaga marakis tana sose sose yace menene? Tace ina da alaji (allergy) ma abin Khan kyami ta fadi hakan bakin ta na rawa.
Fita yayi ya kewaya ta bangaren ta ya bude kofa ya fito da ita gare da wanke aman da ke jikin kayan ta da yake ta tsallake motan su yake hakan yasa hayaniyar da ake na tittinnikan me balangu be dame su ba.
Baya ya bude ya saka ta a ciki shima ya kewayo ya shiga bayan tare sa ware labulen motan sa irin bakin nan na jikin glass sanna ya kunna haske gaba daya fatar ta tayi ja ja wur domin kuwa marakis ta fishi haske.
Kuka ta fara masa tare da kiransa da sunan da take tsokanan sa har yabi bakin ta wato ustazu. Tace ustazuuuu😭 jikina kaikayi ka Sosa min.
Fara Sosa Mata yayi tace mu cire Riga na shiga uku na. Kamin kace me marakis ta dawo daga ita sai lingerie dinga kawai, daga ta janyo kaza sai ta janyo kaza tana sose sose. Lud da yaga abin da gaske ne ya zare belt dinsa ya saka wajen karfe ya Sosa Mata jikin nata har ta bashi tausayi.
Lokacin da abin ya lafa kuwa kwantawa tayi a jikin sa Wanda a yanzu bashida Riga kuma in zaka kashe sa baisan yadda akayi rigan ta bar jikin sa ba saide ya yi karya. Jin kamar tayi bacci yasa tsaya da sosawan.
Kama hannunshi tayi ta gurza alamun yaci gaba da sosawa har dariya taso ta bashi yanda ta larme kamar jaririya. A hankali yace baby? Tace ummm? Yace mu tafi gida ko? Ta girgiza kai hakan yasa yaci gaba da Sosa Mata bayan nata har tayi bacci kamin ya kwantar a hankali ya nufi hanyar gida yana yiwa mai balangu Allah ya isa Dan shi ba haka yaso ba.
Washe gari......
CHAPTER NA GABA ZAI FASHE FA DAN ZAFI NE GARESHI, GA CITTA HARDA KANIMFARI😂
NAJI RUWAN COMMENTS DA VOTES SANNAN AYI SHARING KO KUMA NA FASA YIN ME SWEET.
TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO
Miss untichlobanty 💕
[13/10, 1:53 am] Miss Untichlobanty💕: *🤍🏆🤍YA JI TA MATA🤍🏆🤍*
🖤🖤by miss untichlobanty🖤🖤
marubuciyar :
*1.YARINYAR CE TAYI MIN FYADE*
*2. KURUCIYAR MINAL*
Feel free to contact me on :
WATTPAD miss_untichlobanty
INSTAGRAM miss_untichlobanty
TWITTER, miss_untichlobanty
TELEGRAM miss_untichlobanty
WHATSAPP: 08146448881
Your little sis loves you and don't forget to follow me!
*🤍CHAPTER 53🤍*
*NOT EDITED*
Kama hannunshi tayi ta gurza alamun yaci gaba da sosawa har dariya taso ta bashi yanda ta larme kamar jaririya. A hankali yace baby? Tace ummm? Yace mu tafi gida ko? Ta girgiza kai hakan yasa yaci gaba da Sosa Mata bayan nata har tayi bacci kamin ya kwantar a hankali ya nufi hanyar gida yana yiwa mai balangu Allah ya isa Dan shi ba haka yaso ba.
Washe gari m. Salis justin duniya yayi akan m. Ahmad ya taimaka masa yaje ya gyara lamarin m. Ahmad yace babu ruwan sa. Kullum Abu daya ake yi har abin ya fita akan m. Salis ya fawwala wa Allah lamarin sa.
A kwana a tashi rayuwa na tafiya m. Ahmad ya samu sauki sosai likita yace masa daga sun dawo wani sati ma an sallame sa in babu wani matsala. M. Salis kuwa an sallamesa sati biyu ma da suka wuce sai de har yau jummalo ana gidan jiya ta daina saka hijabin amma banda rike hannun bata yarda aje ko ina yau ne ma aka yarda aka masa bye bye hug shi da ya tashi fita film me zafi ya saka Mata dukda bata jin yaren.
Yaga alamu tana daukan lecture ita ba iya aiki zatayi da waya ba, Shiyasa bai batawa kansa lokaci ba ma. M. Ahmad zaune a office dinsa yana tunani shi wace irin kaddara ce dashi komai NASA a bai bai? Yanzu Matar da yake so din ma tana da aure.
Ajiyan zuciya ya sauke yana mai fidda rai akan auren marakisiyya domin taga yadda kwana biyu take farin ciki sosai yasa tana jin dadin zama da lud din. Jummalo ta fado masa baisan sanda ya saki wata mai jegon dariya ba.
Dai dai lokacin yaga computer dinsa tayi haske duba email din yayi yaga letter of promotion ne sanda gaban sa ya tsinke. Karantawa yayi yaga ya samu Karin matsayi ne daga level coordinator zuwa HOD farin ciki kamar me amma kuma tunowa da bazai dinga ganin marakisiyya yasa yayi tunanin kila addu'ar sa ta karbu zai daina ganin baibai shiyasa Allah yasa aka daukesa daga inda zasu na haduwa sosai Dan ya manta ta.
Murmushi yayi yace marakisiyya allah ya albarkace rayuwarki yasa.... fadowa office dinsa da m. Salis yayi babu ko sallama yasa bai karashe addu'ar sa ba.
Rungume sa m. Salis din yayi yana fadin Alhamdulillah bro allah shine abin godiya duba ka gani ya nuno masa laptop dinsa yace yanzunnan nayi receiving letter dinnan rungume juna suka kara yi suna yiwa Allah godiya.
M. Salis yace bro saboda wannan ya kamata yau kazo gida na muci girki ko ya kace? M. Ahmad bayaso dai m. Salis yaga kamar rashin kirjinsa yayi yawa gashi abin farin ciki ya samesu kawai sai yace na yarda amma da shararo ka kirata kace zamuzo tare.
M. Salis yace batada waya AI ko ka mance ne? Shiru kawai m. Ahmad tayi yana nadamar amsa gayyatan da yayi yace toh shikenan matar taka ce sai shiriyan Allah. Shida m. Salis gani yake ya ma m. Ahmad wayo nidai kawai murmusawa nayi.
.........
A hanyan su na tafiya gidan ne m. Salis yace bari ya siyo kayan miya da nama Wanda zasu ajiye Dan kayan miya kudin su ya hau musamman ma albasa.
M. Ahmad yace um mu ina muka San wannan ? Daga company ake kawowa gida mama na ta dafa mana abinci Dan taki na kawo Mata yar aiki wai tana son ta dinga mota jiki kar in tsufa ya kamata ta zauna gaba daya.
Dariya sukayi m. Salis yace gaskiya kam mama batason tsufa ya kamata abin da ta Saba yi kasan Allah da fari da kace min tana shiga gym room dinka tayi exercise ban yar da ba.
Nan suka cigaba da hira har suka iso gidan m. Salis mai gadin makwabta su Wanda kwana biyu shi yaje bude ma musu gate saboda kirkin m. Salis din ne ya bude musu. Toh tunda zama zai ti ta yi a gidan da take gadin Dan masu gidan basu kauro ba, gara yayi aikin lada.
🖤❣🖤
Jummalo tunda m. Ahmad ya fita tace toh yau kuma me ya kunna min ? Anya kiwa ya Ahmad ne yace ya dinga saka min fina finan yahudu yanzu yanzu ana yaki, anjima suhau rungume rungume bari muga na yau kuma me za'ayi a ciki?
Kai ni sunan fin (film) din da ya Samin din ne wahalar fada gare ta wai dilobats(the love birds. BAN SAN KO AKWAI FILM ME SUNAN SA BA DAN BANA KALLO SAI YA KAMA DAN HAKA HADA SUNAN NAYI) sai kace jamusanci.
Matar salisu fa kallo yayi dadi taga an fara kauce hanya da sauri ta rufe ido tare da buga salati ta sauko daga kan kujeran tana gyara zani kasan center table ta shiga tana leke. Can dai ta fara jin wani irin kamar yadda taji sanda ta fada jikin m. Ahmad tana masa hauka.
A lokacin tayi tunanin ko tsoransa yasa taji hakan. Fitowa dai tayi ta nutsu harda tashi ta dauko coke a karamin fridge dinsu da ke parlourn.
Nazari ta fara yi yanzu wai haka zatayi wa mijin ta kawai ta hau tsoran bakin mutum sai kace mayya? (Note: normal film kawai take kalla ba zina ba)
Rufe ido tayi tana gwadawa a jikin Goran ta kawai sai ta tuntsire da dariya abin ya Mata sugar, tace kai gaskiya bazan iya yi idona biyu ba saide in ido na a rufe.
Hakan yasa ta tashi ta shiga daki ta dauko bakin Dan kwali ta ajiye a gefen ta. Duk abin da akayi sai tayi imagining tace kai ahe mu yan kauye an barmu a baya, shehu shiyasa naga duk yan garin mu cewa suke aure suke so.
Allah sarki ni jummalo an barni a duhu, toh wa zai fada min ni da ko kasance ba'ayi da ni. Da saide Bello na.... shiru tayi ji a karo na farko da tayi tunanin Bello bata ji komai a ranta ba kawai tace Allah ya ji kan ka.
Ta shi tayi tunowa da yau bata ji motsin msndo ba kar yazo ya kalls ba da ita ba hakan yasa ta sa pause kamar yadda m. Salis ya koya Mata. Tace la ai kuwa sun tsaya sun dena motsi.
Fita tayi zuwa dakin mando ta samu ya shanya baki sai bacci tace kai yaron ba ba dai asara ba sai ya yini yana basshi kamar gawa.
Komawa tayi taci gaba da kallon ta tsalle ta daka tace ase I lo yu (I love you) din da nikeji saratu na fada a cikin salurar ta ahe turanci ne, she masoyi ake fada wa. Ko menene ma'a nar sa? Zan tambayi ya salisu in ya dawo.
Can sai ta jiyo shigowar mota lekawa tayi taga m. Salis yana kokarin shigowa hannun ta har rawa yake ta daure idon ta bayan ta tsaya inda ta tabbatar in ta tsaya kofa bazai hambare ta ba.
Su m. Ahmad kuwa har zasu shigo ya tuna da kayan miyan da ke booth mikewa m. Ahmad mukulli yayi yace bro kayi gaba bari nasa su tumatirin nan a deep freezer dake baya na shinfida albasan nan a kasa sai na shigo.
Kar fa ka fada Mata surprise din, m. Ahmad yace ni na isa na shiga sabgata Mata da miji ? Allah ma yasa bata parlourn karban mukullin gidan yayi yayin da m. Salis ya juya tare da komawa.
Mukulli m. Ahmad yasa ya bude.....
MU HADE A CHAPTER NA GABA IN AKAYI RUWAN COMMENTS DA VOTES NAYI UPDATE DA WURI NAJI SHIRU KUMA KUJI SHIRU😁
TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO
Miss untichlobanty 💕
[19/10, 10:50 am] Miss Untichlobanty💕: *🤍🏆🤍YA JI TA MATA🤍🏆🤍*
🖤🖤by miss untichlobanty🖤🖤
marubuciyar :
*1.YARINYAR CE TAYI MIN FYADE*
*2. KURUCIYAR MINAL*
Feel free to contact me on :
WATTPAD miss_untichlobanty
INSTAGRAM miss_untichlobanty
TWITTER, miss_untichlobanty
TELEGRAM miss_untichlobanty
WHATSAPP: 08146448881
Your little sis loves you and don't forget to follow me!
*🤍CHAPTER 54🤍*
*NOT EDITED*
M. Ahmad yace ni na isa na shiga sabgata Mata da miji ? Allah ma yasa bata parlourn karban mukullin gidan yayi yayin da m. Salis ya juya tare da komawa.
Mukulli m. Ahmad yasa ya bude yaji an daka tsalle an fada jikin sa ana fadin baby oyo oyo kamin yace wani Abu ta hade bakinsu.
A cikin makokoron sa yake jin bugu zuciyan sa yayin da ya saki mukullin da ke hannun sa yayi mutuwar tsaye saide kash jummalo bata zo da sauki ba, caraf ta riko harshen sa.....
Saide haka kawai take mamakin yadda taji banbancin jilin mijin nata kamar ya Dan kara tsayi sannan kuma haka kawai taji tana so ta zauna a haka har ta mutu, wannan ne yasa ta fara tunanin ko ta fara son m. Salis din ne?
Murmushi ta tayi a wannan yanayin tana kara narkewa a jikin m. Ahmad din Wanda Allah sarki bata San shi bane. Hannun hagun tasa ta lankayo wuyan sa yayi da tayi anfani ta da hannun daman ta tasa cikin rigan shi.
Wani numfashi m. Ahmad yaja Dan shi gaba daya ya daina tunani ma da kwakwalwar sa kawai ya tsaya ne kamar gunki.
Ba abinda ke tada masa tsikan jikin sa kamar turaren da ta fesa, a yau ne ya yarda babu sarki sai Allah, a yau ne ya yarda akwai yanayin da Dan Adam ke shiga ya kasa aikata komai da jikin ya ma kasa banbanci fari da baki, ya kasa banbanci me ya faru da shi, me kuma ke faruwa da shi.
(Toh toh toh ga m. Salis nan zuwa Dan! Dan!! Dan!!! WASA NAKE HAR KUN WANI DAFE KIRJI KUNA ZAZZARE IDO😂)
sakan masa baki tayi tace I lob yu sannan ta fara kai hannun ta wajen maransa. Flash din wuta ya gani a idonsa hakan ya baisan dalilin da yasa ya dura Mata yawun sa Dan ta sake sa ba saide kashe da alamu bai yi aiki ba Dan ji yayi tace kara min.
Yasan in yayi kokarin yin tsawa ma maganar a rada zata fito hakan yasa ya yanke hukunci kawai ya since Mata idanu kila Allah ya kawo masa agaji.
Mugun nauyi hannunsa ya masa ji yake ko biro bazai iya rikewa ba amma a haka ya ja gyalen nata Wanda hakan yasa idan sa fadawa kan kirjinta da mugun sauri ya rufe ido daidai lokacin hawaye suka sauko mai kuma shima baisan na menene ba.
Mutuniyar ma tana ganin sa tasha jinin jikin ta. A second daya tana kyafta ido yakai sau 10. Baki na bari tace yyyyy...yya...ya ah..Ahmad? Bude ido yayi suna hada ido wani Abu ya soke ta.
A zuciyar sa addu'a daya yake iya yi Wanda banda ita ba abinda ya tuna
"أعوذ بكلمات الله التامة من شر ما خلق"
"a'uzu bi kalmatil lahi tâmmati min sharri ma kala'ka"
Tsoro yasa tayi saurin sakin sa ta fada daki tana daura hannu a ka shikenan ta zama yar wuta ta shiga uku!
Shima m. Ahmad din juyawa yayi ya fice da gudu sukayi karo da m. Salis wartan mukullin motar sa ya yi ya bude gate kamar mahaukaci ya kunna motar sa ya fice.
Dan ma gidan su kusa yake da tabbas babi shakka sai yayi hatsari saboda a seconds baifi biyar ba ya isa gida. A kofa ya bar motan ya bawa mai gadi mukullin kawai ya wuce.
Koda ya fada parlour sanda gaban mahaifiyar sa ya tsinke ganin yadda yake sauke numfashi ga wani gumi da ya hada yana sauri ya shige daki.
Biyo shi tayi tana Kiran sunan shi tare da tambayar sa ko lafiya? Bai ma San ta zo ba kawai zama yayi sai a lokacin ma kwakwalwar sa ta fara tunani.
Lissafi ya fara wai me ma ya kaida gidan wannan yarinyar ? Kai ya shiga uku wayar sa ya janyo tare da shiga Google yayi searching me yake nufi idan zuciya mutum yana bugawa da sauri in ya kalli wani?
Amsan da ya gani yasa idon sa fitowa kamar wani karamin yaro.
Yace abubuwan da ke janyota in kana tsoron mutum ko kana son shi? Yayin da ka fada son mutum system ma gangan jikin mutum yana sakin abinda ake Kira 'Epinephrine' da kuma 'norepinephrine' lokacin da adrenal medulla na cikin kwakwalwar sa ta saki sinadarin 'catecholamines' cikin hanyar jinin Dan Adam hakan yasa bugun zuciyar mutum ke karuwa.
Hannu m. Ahmad yasa ya rufe baki shikam wannan tirka tirka ya zaiyi da ita? Gaskiya untichlobanty bata kyauta masa ba. Ta tasa Wanda zata saka ya so sai matar aure? Rana hakan ya wuni ko sallah ya ki ya fita Dan gani yake za'a gane.
Shida m. Salis bai ma San me zaiyi ba tunda bai gane me ke faruwa ba bayan yabi motan m. Ahmad da ido baki na tabo kasa sai ya shiga ciki. Mutuniyar ma ya ji dakin ta a kulle yace iko sai mahalicci na.
Ko de rashin kunya yarinyar nan ta yi masa? Kai amma ba halin Dan uwa bane ya dauko zafi har haka tunda ba yau suka fara ba. Knocking ya fara tana ji da sauri ta Mike ta fada bandaki tana mai safa da marwa Dan tasan in ta bude wannan kofar toh lalle ne babu wata shakka tabbas sai tayi sibyl da baka cikin tsoro ta fadi abun da ya faru.
Hannu ta daga tace Allah kar ka nuna masi cikin mafalki. Ni jummalo na siga uku na. Zama kawai a parlour m. Salis yayi a ransa yana fadin zadai ki fito ko Dan cikin ki muji me ya faru. Nace uhm ba za dai kaso jin abin da ya farun ba.
Zuba abincin sa yayi ya fara ci tare da saka wa'azi Dan shi kallo ba wani damun sa yayi ba saboda hadura dake cikin sa kalle kalle duk shi ya jefa arewa cikin masifa. Daga kallon film din India ana kantire kantire, kuci kuci hotahei. Cori cori wa ya mutu wa ya tashi.
Su yan kantire kantire suka kyankyaso mana growers din kannywood kuma gashinan dai yanzu yan matan mu ko wace budurwa da ta taso ta rasa abin yi ba arabi ba boko in tana neman suna asan da ita shikenan sai ta shige wasan kwaikwayo sai kace abin da aka aikota yi a duniya kenan.
Kayi magana mutane suce a barsu sana'ar su ne. Yo in ba munafurci ba in de kunsan sana'a ce kuje ku aure su mana. Ko zunubi ne mutum yayi sana'a. Yanzu wani har mutuwa sai yayi akan wata mai tallan kanta yar film, bashi nan da shekara 10 ko 15 in ka kawo masa ita ko sadaka ne na rantse da Allah bazai karba ba.
Dama can ba sonta yake ba. Ana dai binta a social media accounts dinta ne kawai Dan ta basu show, toh yanzu babu kayan show din sama sunyi jaka kasa tayi buhu dama can kuma fatan an kwaile ta shine sai kaga mutum ya da dawo kamar mazaunan biri.
Mu Mata baza mu yi tunani ba? Bazamu hankalta ba? Yanzu Wanda suke fitowa a matsayin stars a 2000 AI yanzu ba su bane stars yanzu an gama miki mutunci ki fito a bazawara ko aunty. Saboda yanzu anyi sabin kyankyasa yan 17 18 ke kin zama guntun shago.
I am telling you, ko yan Mata da ke ta slay queen, slay queen a Instagram haka nan zasu kare yo ni akwai Wanda na sani dayawa, fake shigan tsirai co amma ko FOLLOWERS Dina ba ta da su. Wai yan guda dari waye din ma sai ta burge su.
Ikon Allah yo to ko kece "Kim Kardashians" familyn da kowa celebrity wata rana sai kin hakura Dan suma yanzu tsufa ta fara baiyaniwa da surgery din da komai.
Ba su kadai ba har matan auren namu na San akwai ba wai babu ba. Eh ku de kunsan kanku masu hoto da gyale sandar wuya duk a bude a yi posting a status kuma Allah na ganin ku.
Kar ma ki bani wata hujja cewa gyale AI mayafi ne munji gyale na iya zama hijab ne a waje daya idan kaza Riga mai fumdum fumdum mara nuna jiki mara likewa mara shape. Ga ke matar aure kam ko kin ki ko kin so bazai yuwu ki sa gyale ba dole ki sa hijabi har da nikam Dan ke yanzu taken ce ko fuskar ki ma ta wani ne.
Nasan akwai masu cewa kai ni niqab dinnan in nasa yana rike min numfashi ko kuma AI ni mummuna ce ba wani kyau bane da ni. Yadda baki da kyan nan dai a haka mijin naki ya auro li AI ko? Toh bayida wayo ne ya auri mummuna?
In kuma kince kyan hali na da addini na ya duba kamar yadda manzon Allah yayi Umar ni toh shikenan sai ki nuna masa baiyi zancen tumun dare ba dagaske na kwarai ya auro ki rufe jikin.
Kuma masu cewa niqab na sarke musu numfashi a hakan nan dai kika saka face mask da covid 19 ok? Da shike wannan kala baba Buhari ne kin bi amma bazaki bi Umarnin mahalicci ba.
Sai masifa ya fado wa jama'a kinci kowa makokoro waken cewa Kin shiga uku kin lalace toh dakata hajiya da saura baki ga komai ba tukun continue Allah, Arrahman ya ishi kowa har yayi yawa.
Mu dai gyara hali wallahi nutsu musan me muke yi. Yanzu duk mawakan nan ku duba ba dawwama suke yi ba da kazo zaka tafi ne wata rana, ok a Dade ko ajima a baka shekaru dari biyu za'a neme ka a rasa da kai da murmushin ka.
In karya nake ku fada min ba sai anyi da nisa ba. Shekaru 50 kamin su shata su waye mawaka? Kamin azo su barmana coge ko barmala take su waye yan farkon? Toh amma malaman addini fa? Har yau har gobe suna nan daram.
Yanzu mu duba Abu abdullah, Muhammad bn isma'il wato imam al bukhari daga sanda ya mutu (1st September, 870 AD) zuwa yanzu 2020 shekaru 1150 kenan amma kamar sa'an kakan mu haka mukaji tsabar yadda aka sanshi kuma ake kara saninshi.
Toh mu nan yan arewa sai mu gama tsiyar tamu ko wasu yan kudu ma dake cikin kasar mu basu San mu ba balle yan wata kasa. Shiyasa ko me zakayi kayi Dan Allah sannan kasan hukuncin Allah akan Abu kamin ka aikata shi kamar yadda me alkhdari ya sanar da mu.
Wallahi in kabi Allah abin zaka samu duk abinda kake so Wanda baka nema ba ma zai baka. Amma mum tsaya muna ta bata lokaci da ga kwalliya sai yawo kullum a tafe yau ta kula wancan gobe ta kula wancan ga shegen maula da tumasanci ta zubda martaba ta da na baban ta. Ga gungumemen zunubi tana yawo da shi akai.
In fa Baku sani ba ku sani balle ma na San kun sani Dan ahaka ku kara sani dai dai da wannan turare da ake fesawa fa ku sani daga sanda aka sa aka bar cikin muharraman har a dawo kamar kina zina haka ake rubuta miki.
Kinga in yini kikayi a unguwa kin yini kina zina. Nasan sarai kuma kaso 90 sun sani, wannan kafa da ake gani abar banza ba abar banza bace ita kanta dole wanjibun compulsory ne ki saka safa ko kin ki ko kinso Dan shima tsiraici ne amma AI wanna ka ya zama ruwan dare a ustazan ma masu Dan kokarin sa hijabin ba kowa ke sakawa ba.
Ga wani rashin tunani da naga Mata ke yi shiyasa ko wani namiji da ya taso sai yace Mata basuda zurfin tunani. Yo wai ya za'ayi kullum kisa hijabi sai kuma ranan da zaki gidan biki ko suna ki bude tsiraici ga zuwa wajen zunubi ga ka aikata zunubi.
Akwai Wanda Laura ke kaisu gidan suna kamar yan Mata masu matsowa masu iyaye mamar ki ta dage sai kinje fada mata gaskiya sannan ki baza hijabin ki kuje wata rana zata ji ta dena tursasa ki in ma bata denw ba Allah ya gani kinyi naki daga kinyi aure shikenan dama ta samu kiyi barka ki yi zaman ki gidan mijin ki ba me cin kwalar ki yace baki zo ba.
Ba sani yanzu zaki ce toh AI nima in wani Abu na ya taso baza'a zo ba, toh dama ance azo ne? AI taron suna da bikin aure da waye din babu kyau Dan ba'azo ba daidai kenan shine abinda ake so ai.
A gaskiya matsalar mu tayi yawa in nace sai na rubuto komai toh lalle dole za'a fasa rubuta ya ji ta Mata kenan. A haka bacci ya kwashi m. Salis din yana lissafe lissafen sa.
OYA OYA OYA COME AND COMMENT OOO KAR A.MANTA DA YIN VOTING. WACCE BATAYI FOLLOWING DINA BA A TAIMAKA AYI.
TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO
Miss untichlobanty 💕
[6/11, 10:50 pm] Miss Untichlobanty💕: *🤍🏆🤍YA JI TA MATA🤍🏆🤍*
🖤🖤by miss untichlobanty🖤🖤
marubuciyar :
*1.YARINYAR CE TAYI MIN FYADE*
*2. KURUCIYAR MINAL*
Feel free to contact me on :
WATTPAD miss_untichlobanty
INSTAGRAM miss_untichlobanty
TWITTER, miss_untichlobanty
TELEGRAM miss_untichlobanty
WHATSAPP: 08146448881
Your little sis loves you and don't forget to follow me!
*🤍CHAPTER 55🤍*
*NOT EDITED*
Da wanna tunane tunane har bacci ya kwashe m. Salis bai sani ba. Hakan yasa bai samu yin sallar magrib ba sai hada ta yayi da isha'i.
Shida abin har ciwon kai ya fara bashi Dan baiga m. Ahmad a masallati ba, kai me jummalo tayi ne wai? Ko da ya shiga gidan mama kamin ya karashe sallama ta nufo sa kamar zatayi kuka tana fadin salisu wai me ya Sami Dan uwan ka ne?
Yace mama nima abin da nazo ji kenan tun dazu na kasa gane kansa na ga ko masallati bai zo ba. Abin har ya fara bani tsoro ma wallahi.
Dakin m. Ahmad din suka sake nufa sukayi knocking har suka gaji amma shiru ya ki ya bude. Jiki a sanyaye ya nufi gida yana shiga kamar zai wuce dakin jummalo wani Abu yace mai ya duba dai. Muryan mando ya jiyo Wanda ke kwance akan kujera.
Mando yace ina wuni ya salisu? Gaisawa sukayi tare da yin musbah kamin m. Salis din ya nemi waje ya zauna a gefen sa.
Mando yace ya salisu wai adda ta tafi anguwa ne naga bata daura abinci ba kuma yunwa nake ji. M. Salis yace tana nan ba ta jin dadi ne mu je mu siyo abin ci ko?
Rufe gidan m. Salis yayi tunda ba sa gida akwai hatsari amma ya bar Mata mukulli ko da wani bukata zai taso na dole sai ta fita Allah ma ya tsare.
Bayan kamar minti 20 suka dawo, mandi har yaci abinci yayi bacci amma jummalo bata fito. Ganin fa zata kashe kanta ya saka m. Salis ya tafi ya fara Nemo inda ya ajiye mukullan gidan da kyar ya samo shi a madabak ina nufin kitchen.
Ko da ya bude tsamo tsamo yaga tana zazzare ido tare da girgiza kai kamin ta fara fadin wallahi ni ban San shi bane Allah bansan ya Ahmad bane.
Dafa kafadan ta m. Salis yayi yace kwantar da hankalin ki jummai haba ya kika azalzali kanji kamar wacce tayi kisa? Baki na rawa tace ba.. ba zaka dakeni ba?
Gira daya m. Salis yayi yace me zai sa in dake ki? AI baki yi min laifi ba. Ajiyan zuciya ta sauke kamar ba ita ba ta washe baki tace 'kanhin abinci nake ji me ka sayo mana ?
Yace yauwa yanzu naga jummalo na. Shredded chicken salad da kebab na siyo. Tace tab wannan sunan AI kai kasan abin ka ni yunwa nake ji.
......
Wasa wasa m. Ahmad ya rubuta letter ya dauki hutu na sati biyu ya kulle kan sa a gida kullum bashi da aiki sai addu'a na Allah ya yaye masa ko ma wani masifa ce ke tare da shi ya kuma tsare sa daga cikin Wanda zai fada.
Haka m. Salis take zuwa makaranta shi daya ya zama abin tausayi. Jummalo ma dai duk sanda ya fita toh ta dinga fadawa tunani iri iri wasu masu ma'ana wasu kuma dai... kin dai San mutuniyar.
.....
Yau an yashi a makaranta marakisiyya, habiba sa mansura suna shirin tafiya suka hadu da m salis. Beeba ce fara ta gaisheshi kamin marakis ma ta gai da shi sama Sama Dan basu wani Saba ba.
Mansura kam dauke kai tayi kamar bata Ganshi ba. Beeba tace malam dama naga kenan biyu malam Ahmad baya zuwa lectures dinsa da muke da su shine nace bari mu takabaye ka muji ko lafiya.
Kasa kasa mansura tace ki tambaye shi de, uwar iyayi sannan ta tabe baki. Da ido marakisiyya ta Mata alamun irin me haka? Ba dadi fa. Kafada ta daga alamun ita ba abin da ya dame ta.
Murmushi m. Salis yayi ma beeba yace lafiya kalau kawai tafiya ce yayi zai dawo soon. Yana kai wa nan ya shige motan sa yayi gaba Dan kare mutun cin sa.
Motar sa na barin wajen ms madeena wanna me son m. Ahmad din ta bullo gaban beeba tazo ta aika Mata wani kallo tace katuwar banza kawai, ke shugaban aji ce zai dame ki in malamin ki bai zo ba.
Marakisiyya ne tayi taku daya wato one step forward tare da daga gira daya yanda lud keyi Mata yare da Dane baki wanda bata ma San ta koya ba tace toh sannu magajiya in ita karuwa ce, ni ban masan me ya samu idon Wanda ya dauke ki aiki ba. Mtsww! Banes muje Dan Allah.
Nan suka bar madina ta ma rasa me zata ce tana kumfa Dan taso ta ci mutuncin beeba ba kadan ba. Bayan sun Dan yi nisa ne sun kusa zuwa inda motan su yake mansura tace duk ai laifin ki ne me na wani tambayan inda m. Ahmad yake?
Beeba tace kawai mutumin burgeni yake shine Dan na tambayi inda nake nayi laifi? Mansura tace ba tambayan bane damuwa ta, ki rasa aanda zaki tambaya sai wannan mutumin?
Marakis tace beeba kin dai yi sa'a yanzu banason m. Ahmad da na bige miki baki ke kuma mansura me naki da salis dinnan bai rike miki komai ba kawai ki kullaci mutum?
Mansura tace ni fa mutumin ne kawai bai yi min ba, mutum yana Abu kamar mace sanyin sa yayi masa yawa haba Dan Allah, ji yadda yake da ido sanda yake mana nagana Lamar na cokale.
Marakis tace ni kinga bazaki zo gefen mu kici mutuncin musulmi ba, kin dai San bazamu biye miki muyi gulma ba. Ajiyan zuciya mansura ta sauke tace bazaki gane bane ni Allah banaso ko mace naga ta fita sanyi ana dannar ta balle namiji. Ko Dan yaga yana da hakan fata ne oho.
Murmushi beeba tayi tace AI kuwa sanda kika fada na gani wallahi ya kai marakis ma haske ya ma fi Ahmad, awwn! Waiyo kyau. Dungure Mata kai mansura tayi suka fashe da dariya marakis tace kede farin namiji ne ajalin ki.
Beeba tace haba kema kin San kawai ina fada ne amma AI a aure ba a suba wadannan indai mutum zai bi shawaran annabi Muhammad SAW shi yace muyi aure ne saboda addini da kyawawan halin mutumin ko matar toh amma yanzu fa ba haka bane abin jama'a sunyi cilli da shawarar ko ince umarnin sa sun koma yin aure Dan wani abin duniya.
A hadisin da Abu hurairah ya karbo manzon Allah tsira da abincin Allah su tabbata a gareshi yace
Ana auren mace ne saboda Abu 4, dukiyar ta, nasabarta, kyawunta da kuma kyawun addinin ta. Sai yana yin nuni ko ishara ga me addini.
Hadith na 4802 a sahih bukhari, kuma hadith na 1466 a Muslim.
Mansura tace saide kuma kinsan wasu fa sun fahimci hadisin nan a baibai wasu suna ganin manzon Allah yana fadin mutum zai iya auran mace saboda wannan abubuwan ne wasu kuma suna ganin ma dole sai tana da duka kamin a aure ta.
Dariya mansura tayi tace ba San ba abin dariya bane amma ya ban dariya wallahi. Marakis tace abin fa me sauki ne. Kawai manzon Allah yana fadan fact na dalilan da yasa mutane ke aure ne sai ya bawa musulmai shawara cewa su me addini zasu aura.
Beeba tace ni abin da ke ci min rai, ke ci min turo a kwarya wai sai wasu mutane suce ma AI shawara ce alhalin wasu mala ma suna ganin umarni ce. Mansura tace toh idan ma shawara ce AI dole is dauka.
Yanzu ko Abu zakayi idan mahaifiyar ka ta baka shawara kuma bai Saba addini ba in kana da mutun ci AI shi zaka dauka balle shawaran manzon Allah. Wato dai a takaice in aka fassara aikin su fa kamar manzon Allah yace ka auri me addini su kuma suna cewa mun ji mun gode amma me kudi zan aura ko kyakkyawa zan aura ko yar babban gida zan aura.
Marakis tace ba laifi bane in ya kasance ta samu daya daga cikin wadannan ko duka indai tana da addini Abu ne mai kyau Romo ce Allah ya ga daman bawa mutum.
Jan kumatun ta mansura tayi a muryar tsokana tace irin baby lud ko? Yayin da beeba ke Mata signa da gira sannan suka fashe da dariya. Mansura tace ni Dan tuna min wani hadisi ne ma yayi magana akan abin da ake bukata a gaban miji.
KWANA DAYAWA YAN UWA BA MU HADE BA DON ALLAH A SAKA NI A ADDU'A INA DA PHYSIC RANAN MONDAY.
INSHA ALLAH IN NA HUTA KO TALATA NE ZAKU JI NI. KAMIN MU SAKE NITSAWA CIKIN KARATU.
TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO
Miss untichlobanty 💕
[21/11, 8:42 pm] Miss Untichlobanty💕: *🤍🏆🤍YA JI TA MATA🤍🏆🤍*
🖤🖤by miss untichlobanty🖤🖤
marubuciyar :
*1.YARINYAR CE TAYI MIN FYADE*
*2. KURUCIYAR MINAL*
Feel free to contact me on :
WATTPAD miss_untichlobanty
INSTAGRAM miss_untichlobanty
TWITTER, miss_untichlobanty
TELEGRAM miss_untichlobanty
WHATSAPP: 08146448881
Your little sis loves you and don't forget to follow me!
*🤍CHAPTER 56🤍*
*NOT EDITED*
Jan kumatun ta mansura tayi da muryar tsokana tace irin baby lud ko? Yayin da beeba ke Mata signa da gira sannan suka fashe da dariya. Mansura tace ni Dan tuna min wani hadisi ne ma yayi magana akan abin da ake bukata a neman miji.
Haka dai suka ci gaba da hiran su har suka rabu ko wacce tayi gida. Marakis na shigowa dakin su ta samu lud yana saka Riga tare da daukan mukulli.
Tace ustazu ina zuwa ? Yace zanje na duba gidan mu ne naga progress din. Tace ko na zo mu tafi tare pecking goshin ta yayi tare da shafa kanta yace karki damu wifey ki yo hutawan ki I want to surprise you.
Gyada kai kawai tayi ta sake taje masa gashi bayan ta ajiye jakan ta sannan ya fita.
........
M. Ahmad ne zaune a dining table din gidan m salis yana shan shayi kamin jummai ta fito daga kitchen dauke da farantin abinci dauke da ciki niki niki.
Da sauri ya taro ta tare da karba yana fadin yi a hankali matar my kar kiyi mana asara. Kasa kasa tayi da murya tace hmm gara da kashe matar ku kam da naka Mata kuma nashi.
M. Ahmad yace ni kam har yau ina nadaman abinda na aikata amma naga ke ko da damun ki baiyi ba. Tace toh in na damu ma mai zai shanza? Ni fa kai Nike so kawai dai Dan na aure shi ne.
M. Ahmad yace nikam aure zanyi gaskiya, wani harara jummalo ta aika masa tare da cin kwalar sa tace ka kara maimata wannan magana a bakashin danka. Indai ina raye baka isa ka auri wata ba.
M. Salis da ya sako kafa daya ne yayi mutuwar tsaye kamin yace me kike nufi dansa. Jummalo da idonta ya rufe da kishi batasan sanda tace yo danshi mana ko da anshe ma danka.
Wani kwallo m. Salis yayi da ita ta kifa kan titsetsen cikin ta ba tare da bata lokaci ba jini yayi Male Male.
A zabure m Ahmad ya tashi daga mummuna mafarkin da ya fara yi yau kwana uku kenan, gaba daya ya jike da gumi sai haki yake kamin yayi addu'a ya sauko daga gadon sa ashe lokacin sallahn la'asar ne yayi.
Sallah yayi tare da addu'a sosai kan Allah ya sa shawarar da ya yanke ita ce mafita a gareshi akwatin shi ya hada tare da zama ya rubuta letter ma mahaifiyar sa tare da sanar da ita kar ta sha wahalar neman shi zai nemeta in yabar kasan sannan ya saka akwatinshi a mota ya dauki duk documents da yake bukata. Ya kama hanyar birnin taraiya domin tafiya Chicago Dan samo karatun PhD wanda ya nemi admission kuma ya samu.
Wajajen magrib m. Salis ya shigo domin gaida mama sannan ya samu ya duba Dan uwan nashi. Bayan sun gaisa da mama tace bari ta kawo masa ruwa yace tayi zamanta bari ya dauko da kansa. Jiki a sanyaye ta ga m. Salis ya fito gaban ta yayi mugun fadi Dan tayi tunanin ko cutar da ta kama m. Ahmad ce ta kama shi.
Mikewa tayi tana fadin salisu kayi wa Allah karma ka fara kaga Ahmad ma daga haka ya fara. Miko Mata papern kawai yayi kamin ya zauna ya saka hannun sa cikin tafukan hannunshi.
Umma kam kin karantawa tayi tace ni fada min abinda ke ciki banshirya hawan jini ya bige ni ba. Haka ta dinga magana har ta cure rai cewa m. Salis zai kulata kawai sai taga ya dago idon sa abun tsoro yayi ja sosai dukjijiyan jikin sa sun tashi kamar zai zubda hawaye yace ya bar kasan.
Tace wa? Waye ya bar kasan? Kallon kofar dakin m. Ahmad yayi da sassarfa ta bankada AI kuwa bayanan. Tace kai salisu Kira min shi, ka Kira sa nace.
M. Salis yace yace karma mu Kira shi.
Daukan wayanta tayi ta lafta masa Kira har ya datse bai dauka ba zata sake Kira m. Salis ya karbi wayan yace in kika fiya Kira zai kashe wayar tunda dai a bude take na San me zanyi.
Wayarsa ya dauko ya tura ma m. Ahmad din sako cewa mama ta yanki jiki ta fadi. Cikin minti biyu m. Ahmad ya Kira sa ysna dauka yace masa ya jikin nata ? kun kaita hospital? Me likitan yace? M salis da ransa ya baci saboda yadda m. Ahmad din ya musu yace ka damu da mahaifiyar taka shine ka tattara zaka bar kasan?
M. Ahmad sanda yaji tsoron m. Salis ya shiga zuciyar sa Dan basu taba ganin ranshi ya baci ba kullum abun tausayi kuma unserious. Mama ne tace kai salis karkuyi fada kawai kace masa ya dawo gida.
M. Ahmad yace dama karya kayi min? Salis ashe zaka iya min karya kuma karyan ma da mahaifiya ta? M. Salis yace au kai abinda ya dame ka ma kenan? Ahmad nace abinda ya tsaya ma a rai shine nayi maka karya? Kai da ka bar mu fa? Ashe dama zaka iya barin mu ba ko sallama bare bayani?
Me aka ma? Me aka rageka da shi me ka nema ka rasa da zaka bar gida kuma harda rubuta letter na jinginar da aiki? Toh indai Allah ne ya halitta min hannuna toh ba shakka ni dai bazan kai wannan letter ba. Cikin daga murya m. Salis din yace wai me ka nema ka rasa ne duk kabi ka tada wa mutane hankali ka zama kamar zaucacce?
Cikin daga murya shima m. Ahmad yace MATAR KA ko zaka bani ne? Salisu nace ko saka bani ne? Na tabbata in naci gaba da zama ina kallon ku dayan biyu ne ko na cuci kowa ko na cuci kaina.
Shiru ba Wanda yayi magana har lokacin da m. Ahmad ya ji ana ce mai your call credit has been exhausted and your call is terminated, dial.........
Sauke wayar yayi daga kunnensa yana mai goge kwalla dake kokarin sauko masa sannan ya ja akwatin sa ya shige hotel domin samun makwanci kamin su daga washe gari da daddare.
Shi kuwa m. Salis tunda yaji kalaman m. Ahmad ya saka wayar sa yayi a aljihu bai damu da ya kashe ba sannan ya nufi gidan sa yabar mama tsaye ta ma rasa me zatayi ko tace dukda ko bata ji me suke cewa ba.
Yan wattpad please don't forget to VOTE and comment ooo, that's my only motivation.
TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO
Miss untichlobanty 💕
[27/11, 2:25 pm] Miss Untichlobanty💕: *🤍🏆🤍YA JI TA MATA🤍🏆🤍*
🖤🖤by miss untichlobanty🖤🖤
marubuciyar :
*1.YARINYAR CE TAYI MIN FYADE*
*2. KURUCIYAR MINAL*
Feel free to contact me on :
WATTPAD miss_untichlobanty
INSTAGRAM miss_untichlobanty
TWITTER, miss_untichlobanty
TELEGRAM miss_untichlobanty
WHATSAPP: 08146448881
Your little sis loves you and don't forget to follow me!
*🤍CHAPTER 57🤍*
*NOT EDITED*
Shi kuwa m. Salis tunda yaji kalaman m. Ahmad ya saka wayar sa yayi a aljihu bai damu da ya kashe ba sannan ya nufi gidan sa yabar mama tsaye ta ma rasa me zatayi ko tace dukda ko bata ji me suke cewa ba.
Kawai zama tayi ta fara cin abinci Dan kar ta daga wa kanta hankali, Abu daya da ta sani shine komai rintsi wata rana zai wuce kuma ba yadda za'ayi danta ya barta har abada.
M. Salis kuwa yana zuwa gidan sa ya samu mando na zaune a gefen jummalo ya baza tagumi yana tambayar ta wai me ya faru kwana biyu bata wasa da shi kamar yadda ta Saba ko Dan tayi aure ne?
Girgiza kai kawai tayi ta barsa ya ma rasa abin cewa. M. Salis zama yayi ta dago ta kalleshi shima itan yake kallo bai yi magana ba itama bata ce komai ba. Tace na kawo maka ruwa? Jingina yayi da kujera tare da daga kai sannan ya sauke ajiyan zuciya.
......
Bayan ya sha ruwan mando ya Mike ya basu guri domin sun gaisa lokacin da jummalo ta tafi kawo masa ruwa. Zama jummalo tayi a gefen sa ya Dan matsa Wanda bata ma lura ba.
Tace wai mi ya faru ko wani Abu ya samu mama ne? Kace min zaka je gaishe ta yanzu kuma ka.dawo min a haka. Bai ce Mata komai ba tana ta zuba saida kaf ta tsayar da maganan ta lokacin da taji yace KINASON YAYA NA? Kyakkyafta ido ta fara da sauri tana kallon shi tace mi kashe?
Mando dake labe a bayan kofa yayi saurin toshe bakin sa Wanda ya kasa rufewa tare da zaro ido. M.salis yace yanzu ace idan na mutu zaki iya auren ya Ahmad?
Tace chabdi jan ya amadu da yake shewa ina da rawan kai din ni gaskiya bana sonshi gara dai kai din zan iya zama da kai har in fara sonka. M. Salis yace idan kuma yana da wata cuta Wanda sai dole kin aureshi zai warke fa?
Tace eh toh wannan lokacin zan aure shi Dan in taimaka mishi saide.... hannu ya daga Mata yace kar kice saide shikenan dama Ansar ki nake son ji.
Tashi yayi ya shige dakin shi jummalo da ta rike saide dinta ne ta karashe... saide idan ya min ba daidai ba zan Rama.
Sansadawa mandi yayi zai shige dakin sa dake waje ya bige kwandon shara. Jummalo tace toh zo nan munafuki Allah ya kama ka. Shigowa tayi har ya fara hada gumi tsamo tsamo da shi sai kace beran da ruwan sama yayi masa duka.
Tace duk maganar da nayi maka shewa babu kyau sauraran maganan da bai shafe ka ba baka daina ba ko? Yace kiyi hakuri adda juma na daina.
Hararran sa tayi tace zan kamaka fita kamin inyi kwallo da kai. Fita yayi da gudu Dan yasan halin ta yanzu sai tayi masa dukan.
M. Salis ne ya fito da wani karamin jaka a hannun sa ya mika Mata hijab tace muje. Tace ina ? Bai kulata ba ya fice dakin mando ya shiga yace masa ya dauki kayan sa guda uku ya sa a jakar da ya ajiye masa a gado sannan ya fita.
A mota ya samu jummalo ta kalle sa kamar zata yi magana wani Abu ya gwabe ta. Mando ne yazo shima tsilif ya shige m. Salis ya tsaya a gidan mama ya sauke mando tare da mika masa dubu biyar yace masa zasu yi tafiya ne zasu dawo ga wannan koda zai bukaci wabi Abu.
Godiya yayi ya karba sannan ya sauka daga motan sallama suma suka yi wa mama m. Salis ya shiga dakin m. Ahmad bayan kamar minti Goma ya fito daga nan suka hau babban titi sai birnin taraiya. Jummalo tun tana rike maganar ta taga fa kai bazata iya ba hakan yasa tace wai me ya faru zamu tafi birnin taraiya ? Ina ne shi wannan garin ?
Kawai kallon ta yayi kamin ya dauke kai wani Abu ya sauka a fuskan sa shi ba murmushi ba shi ba kuka ba shi ba farin ciki ba haka shi ba bakin ciki ba yace gyara zaman ki.
Tace ba kai kace in ina tare da kai in saki jiki na ba? Yace AI yanzu a mota muke. Ganin bai bada wani kofar yin magana ba yasa ta gyara zaman nata.
Kallon window ta fara tana kirga bishiyoyin da suke wucewa a haka har bacci ya kwashe ta ba tare da ta ankare ba. Hakan ne ya bawa m salis daman kare Mata kallon tare da tsaida zuciyar sa kan abin da ya yanke.
Wajen 2 dare suka isa Federal capital territory Dan haka m. Salis ya nema musu makwanci. Washe gari da sassafe ya tafi neman Wanda zasuyi masa tracking din numbar m. Ahmad duk sai suke cewa wayan sa a kashe babu location.
Paper da ya gani a dakin m. Ahmad din ya ciro daga aljihun sa ya bude tare da sake kallon lokacin da jirgin su m. Ahmad din zai tashi da kuma airline din da zai bi.
Wata dabara ne ta zo masa bayan yayi sallan magrib yace a nema masa inda wannan wayan tayi aiki last nan aka fada masa gaban hotel din da m. Ahmad take. Da hanzari yaje ya dauko jummalo tana kallon sa kamar ta mai duka saboda ya taso ta daga baccin ta mai dadi saide ganin yanda yake ta sauri yasa ta Dan fara damuwa ko wani Abu mai muhimmanci ne ya taso.
Ko da suka je reception na hotel din suka bukaci sanin ko m. Ahmad na ciki receptionist tace wannan hotel din suna da tsauri wajen bada information na client dinsu. Menene alalakar su? M. Salis yace AI m. Ahmad din Dan uwan sa ne kuma ya manta staff ID Card dinsa ne.
Tace saide ta duba in m. Ahmad din yana ciki ta Kira musu shi. M. Salis yace ba matsala a ransa kuwa yace indai mun tabbatar yana ciki sai mu jira a waje har ya fito. Dubawa tayi tace minti 30 da suka wuce yayi signing out.
Da sauri m. Salis ya riko hannun jummalo ya wulla ta a mota suka sake kama hanyar airport Dan shi m. Salis yaso su rike sa tun daga hotel din ne amma da alama sunyi latti toh sai su same sa a can. Duba agogon sa yayi yaga saura awa 2 su tashi Wanda chances din su hadu da shi awa 1 da rabi ne.
Kuma daga inda suke zuwa airport zai dauke su kusan awa 1 Dan haka minti 30 suke da shi idan yayi sauri kenan. M salis yace ma jummalo ta koma baya ta kwanta. Ba musu tayi hakan tana turo baki tace ni AI nayi fushi ma ina cewa ka siya mmn farin abin nan ka ki ka siya min.
Yace kada ki damu zai siya miki a inda zamuje. Tace wa? Bai bata amsa ba saima gyara zaman belt dinsa da yayi tare da godewa Allah a Nigeria babu speed limit. Kunna injun motan sa yayi ya bata wuta yace ki rike kujeran nan gam gam kuma kar kiyi min ihu.
Kawai ya finciki motan a wani gudun da shi kansa bai San nawa yake tafiya ba kila 180 ko 200 Abu daya da ya sani shine yana shan gaban motocin da ke gaban sa ne yadda ake shan gaban napep marasa yin sauri dukda ko babu Wanda yakai yan Abuja bawa titi wuta. KOMIN RINTSI SAI YA HANA M. AHMAD TAFIYA DOMIN SHI YA TAIMAKA MASA YA ZAMA MUTUM.
KAMAR DE YANDA AKA SABA KAR A MANTA DA YIN VOTING DINNAN SABODA SHI KE SA WATTPAD SU NUNA MA WASU LABARIN PLEASE AYI SHARING DA FRIENDS. GODIYA MARA ADADI GA MASOYA NA.
TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO
Miss untichlobanty 💕
[2/12, 12:40 pm] Miss Untichlobanty💕: *🤍🏆🤍YA JI TA MATA🤍🏆🤍*
🖤🖤by miss untichlobanty🖤🖤
marubuciyar :
*1.YARINYAR CE TAYI MIN FYADE*
*2. KURUCIYAR MINAL*
Feel free to contact me on :
WATTPAD miss_untichlobanty
INSTAGRAM miss_untichlobanty
WHATSAPP: 08146448881
Your little sis loves you and don't forget to follow me!
*🤍CHAPTER 58🤍*
*NOT EDITED*
Abu daya da ya sani shine yana shan gaban motocin da ke gaban sa ne yadda ake shan gaban napep marasa yin sauri dukda ko babu Wanda yakai yan Abuja bawa titi wuta. KOMIN RINTSI SAI YA HANA M. AHMAD TAFIYA DOMIN SHI YA TAIMAKA MASA YA ZAMA MUTUM.
Jummalo kam mikewa tayi Dan bata da tsoron mota ta fara washe baki wani nishadi na sauka Mata a rai ganin yanda suke ta wuce motoci abin yana Mata sugar ta mirror m. Salis ya hango ta ya murmusa tare da dauke tunanin daga kansa ya mayar da hankalin sa ga tukin da yake yi.
Idan su air port m. Salis ya bude kofan bangare da jummalo take da sauri, da yaga ta tsaya kalle kalle zata bata masa lokaci kawai ya riko hannunta ya janyo ta da gudu suka tafi wajen clearance tun daga ne sa suka hango m. Ahmad na kokarin wucewa kamin su iso ya wuce.
Kokarin tare su security yayi Wanda m. Salis yasan za ayi haka Dan haka ya shirya kawai hankada jummalo yayi bayan ya ture security, suna gudu ana biyo su har security 6.
Jummalo sai lokacin ta hango m. Ahmad Dan haka cikin jin dadi ta bude murya tana danna masa Kira YA AHMAD! YA AHMAD! MUNZO MU TAFI DA KAI GIDA!
Bata ma San sanda ta cire hannun ta da ke cikin na m. Salis ta kara gudu ba.
M. Ahmad kuwa bayan anyi clearing dinsa ya wuce yana tunanin gara da ya tafi hakan shine zai gi zaman lafiya ma kowa, hara shi daya ya wahala saura su Sami natsuwa Dan yaga alamu zuciyar sa na kokarin kawo tashin hankali a cikin gidan su ya raba sa da kanin sa.
Kamar daga sama ya jiyo muryanta tana danna masa Kira murmushi yayi Dan a tunanin sa kawai imagination ne. Jin talun takalmin ta da kuma sautin takalma dayawa da alamu ana kokarin tsayar da wasu yasa ya tsaya cak.
Sautin ne ke kara matsowa kusa da shi Dan haka ya juyo domin ya tabbatar da abin da yake tunani AI kuwa itace dauke da wannan murmushin nata Wanda ke sa ta zama kamar wata shashasha tana ta dago musu hannu yayinda m. Salis ke tsaye yana kallon su wani security na masagana kuma bai ma San me yake cewa ba.
Sauran biyar din kuma suka ci gaba da bin jummalo Wanda ita ma bata San suna yi ba. Cire takalma tayi duk Dan ta kara sauri tana isowa gaban sa ya daka tsalle zata dale jikin sa tana me fadin ni da ya salis ne muka zo zamu tafi da kai.
Baya ya ja tare da yi Mata murmushn me boys damuwa yace bakyajin magana ko? Ba nace miki ki dena taba maza ba? Sosa kai tayi tace au mancewa nayi tsabar jin dadin ganin ka. Kasan wahalar neman ka da mukayi kuwa?
Tana mai nuna wa da hannu ta ce ga can ya salisu yana kiranka zo mu tafi gida. M. Ahmad yace ai ni bazan koma gida ba kasan zan bari karatu zanje nayi.
Ta dafe kirji tace barin kasar kuma? Yaya Ahmad me muka maka? M. Salis ne ya karaso inda suke ganin securities na kokarin su taba jummalo da ke ta yi wa m. Ahmad karadi.
Rike hannun security din yayi tare da bashi hakuri sannan yayi masa tuni cewa musulmai ba kowani namiji ke taba mace ba. Da yake security din mai fahimta ne yace ba damuwa amma sun karya doka su koma daga baya.
M. Salis yace ya basu minti biyu yanzu zasu fita hakan yasa security din ya sanar da sauran securities cewa su koma zai fito da su.
M. Salis bai ce wa m. Ahmad komai ba kawai ya fanki hannun sa ya fara Jan sa . Kafewa m. Ahamd din yayi yace brother ku koma gida kawai ba za biku ba. M.salis bai kulasa ba yaci gaba da Jan sa. M. Ahamd yace ka dai na dagewa brother ka San bazan biku ba na Riga da na yanke shawara.
Ganin dai m. Salis yayi kunnan uwar shegu yasa yace brother ka San dai dalilin da yasa zan bar kasarnan in ina zaune son matar ka zai cigaba da nanaye min zuciya ne ni da kai mu dinga jiwa zuciyoyin hunan mu ciwo ka barni na tafi.
Ya karasa zancen yana fincike hannun sa. Cikin tsawa m. Salis yace IDAN KUMA NACE NA SAKETA FA? Shiru wajen yayi security dake kokarin ce musu minti biyun su ya cika shima tsayawa yayi da maganan sa makale a bakin sa.
Dai dai kun mutane da akayi clearing suma tsayawa kallon ikon Allah sukayi. Abun dai kamar a da wasa. Tsaki m. Ahmad yayi tare da juyawa zai koma m salis ya riko hannun sa yace brother wallahi Allah da gaske nake na saketa kuma ni kai nake so ka AURETA bayan ta kammala iddan ta.
M. Ahamd yace kai salis kana da hankali kuwa? Kai wai yaushe zaka girma ne ka dauka komai abin wasa ne? Kawai zaka saki matar ka kace na aura? Yaushe ma ka sanni? Daga wajen aiki muka hadu har muka kulla zumunci shine....
M salis ne ya datse ta hanyar cewa toh AI shine abin da nake fada mun kulla zumunci mun zama yan uwan juna mun zama daya. Matsowa tayi daf da fuskan m Ahmad din tare da rike wuyan track suit dinsa amma ba shake sa ba yace tun ranan da na fara aiki ka shiga raina.
Kai ka sani a da ba soyaiyar Dan uwa nake maka ba soyaiyar abokin rayuwa nake ma kuma ka fahimta shiyasa kaki la bari na shiga jikin ka ashe kaima kana dauke da lalura, daga baya da ka ga matsalar mu daya ce muka hada karfi da karfe muka samu lafiya a sanadin ka ne yau na zama mutum cikakke da zan bigi kirji nayi alfahari da badan haka ba da yanzu haka ina tare da wani katon banza muna....
Hannu m. Ahmad yasa ya rufe masa baki yayinda girard sa ta hade suna kallon juna ido cikin ido kowa ya kafe yana nuna taurin kansa. M. Ahamd yace na San da wannan salis, look brother na San son da kake min ka juya ka mayar da shi na yan uwan taka amma me mutane zasu ce dukda ni abinda zasu ce bai dame ni ba.
Haka zamu ci gaba da rayuwa kenan? Duk abin da kake sa shi idan ina so sai ka bani? Tunda ka iya bani Mata na San ba abinda bazaka bani ba, nagode da soyaiyar ka gareni amma inajin nauyin na karbi kyautar ka domin a kowani lokaci idan na kalle ta sai naga kamar banyi maka adalci ma.
Yana kaiwa nan ya dauke hannun sa daga.bakin m. Salis din ya juya domin ganin idanun dukan su biyu na kokarin bada maza. Ba jikin sa kadai ba har zuciyan sa sanda ya tsaya lokacin da yaji m. Salis ya rungume sa ta baya tare da fadin bro karka tafi ka barni.
Wallahi in ak tafi Jima barin garin zanyi domin ban San inda zan sa kaina ba. Ni duk in da kake nan nake son kasancewa, kwanaki kadan dinnan da na daina ganin ka baka ga yadda nake ji ba kawai jarumta nake yi Dan akr mama jikin ta yayi sanyi.
Wannan kalaman yasa m. Ahmad juyowa yana kallon m. Salis da ya makale shi. Tabbas ya Dan fada ba karya yayi ba. Ajiyan zuciya m. Ahmad ya sauke tare da share ma m. Salis hawaye yace shikenan toh Dan kani na na yarda.
SHIN KUNA GANIN YA DACE DA M. AHAMD YA YARDA? SHIN DA GASKE YA YARDA KO DAI WAYO YAYI MA M. SALIS
DON'T FORGET TO FOLLOW ME, VOTE BY CLICKING THE STAR BELOW AND COMMENTING YOUR THOUGHTS !
Miss untichlobanty 💕
[9/12, 1:44 am] Miss Untichlobanty💕: *🤍🏆🤍YA JI TA MATA🤍🏆🤍*
🖤🖤by miss untichlobanty🖤🖤
marubuciyar :
*1.YARINYAR CE TAYI MIN FYADE*
*2. KURUCIYAR MINAL*
Feel free to contact me on :
WATTPAD miss_untichlobanty
INSTAGRAM miss_untichlobanty
WHATSAPP: 08146448881
Your little sis loves you and don't forget to follow me!
*🤍CHAPTER 59🤍*
*NOT EDITED*
Wannan kalaman yasa m. Ahmad juyowa yana kallon m. Salis da ya makale shi. Tabbas ya Dan fada ba karya yayi ba. Ajiyan zuciya m. Ahmad ya sauke tare da share ma m. Salis hawaye yace shikenan toh Dan kani na na yarda.
Murmushi ne ya fadada a fuskan m. Salis din yace da gaske? Shima m. Ahmad din murmushi yayi masa tare da gyada kai yace ni matsala na da kai baka girma Abu kadan sai ka fara yin kuka rungume juna sukayi tare da fita daga area din jummalo na biye da su.
Da gudu ta rufe wajen m. Salis yace yanzu zaka siya min gurgurun? Yace a ina kika gani da yatsa ta nuna. M. Ahamd yace toh sauke hannun ba'a nuna Abu a cikin mutane kar wani ya dauka shi kika nuna ya gutsire miki yatsa.
Da sauri ta dauke hannun ta m. Salis yace ina zuwa kamin ya nufi wajen da ake sayar da abubuwa dayawa ya sayo musu apple pie, drinks tare da gurguru wato pop corn din jummalo.
M. Ahamd kuwa shiru yayi toh me ma zai ce Mata? Kawai kallon ta yake tana waite waige daga yaga zata juyo sai dauke kai. Saide a karo na uku bai yi sa'a ba domin kuwa ta kama shi dumi dumu yana kallon ta.
Hade rai tayi cikin hausan ta na fulani tace la kallo na kake? Kaga na zo binnin taraiya na kara kyau ko? Gira daya ya daga tare da ninke hannu a kirjin sa ya gyara tsayuwa yace wani kyau kike magana ? Kyan Kayan jikin ki?
Tace lallai ma Dan uwan ya salis dinnan kana nuhin kaya ya hini Kyau? Yace yanzu ko sunan nawa ma baza'a iya Kira ba ? Jummalo tace kashe min mummuna sannan na Kira sunan ka?
M. Salis da ta hango rike da ledoji yasa ta mance da zancen da suke yi taje ta karba ta fara ci a wajen. Gutsiran farko tayi ta sauke ajiyan zuciya tace kai aradu kaman kasan yunwa na bugu na.
Dariya sukayi kamin suka nufi inda m. Salis ya bar motan shi suka shiga domin tafiya su Sami makwanci.
......
Bayan dawowa su komai ya dawo normal m. Ahmad ya koma aikin sa yanzu kawai jira ake yi jummalo tayi jini uku a tsarki na hudu a daura musu aure. Saide kuma ana wata ga wata, don kuwa ana dara ga dare yayi amma kamin nan.....
(Akwai wani Abu da mutane dayawa basu fahimta daidai ba game da idda, wato shi wata 3 da aka ce AI ana nufin jini uku ne duba da cewa yawanci wata wata ake al'ada yasa wasu masu fadakarwa dunkule maganan da wata uku. Toh wasu sukan yi jini a 20 20 dan haka su a wata biyu ma suke kare idda saide ance rashin sani yafi dare duhu.... duba da cewa maza na karanta littafin ina ganin kar na zurfafa ga duk mai bukatan Karin bayani ko take da wani Abu da ya rikita ta ko yake daure Mata kai game da al'ada ko ma wani hukunci na daban ta tuntunbe ni ta numba na.)
Dalilin da yasa kuwa nace ana dara ga dare yayi hajiya mansura fa ta fara zuba ido taga ra ina ciki zai billo amma shiru shikam oga lud ya ci gaba da karatun sa tare da nuna Mata yaushe ma akayi auren da har Dan bata Sami juna biyu ba zata tada hankalinta?
A makaranta kuwa miss madeena kullum tana cikin zirya a office din m. Ahmad dukda ko tasan cewa zai yi aure ita dama ba alkhairi ya kawo ta ba. Ita dai burin ta sai ta maida shi Dan wuta ta hallaka sa ta tsoma kansa a ruwa, ita dai sai ta hallaka al'umma ta shiga cikin masu cewa Allah kayi mana kyautar masifa ko Rabin ludayi ne.
Saide Allah cikin ikon sa bata samun sa domin kuwa yayi busy sosai amma kamar maiya kai tafi maiya ma naci. Ban garen kawayen madam mansura kuwa suna nan yadda suke saide wani hanzari ba gudu ba.
Yanzu m. Salis ya fara daukan su wani course a semester din Dan haka kullum su marakis ba suda kwanciyan hankali Dan beeba ta dinga tsaki tana yatsine.
Har ta kai ta kawo indai suna da ajin m.salis toh ba sa zama waje daya Dan bata bari su riban ta da abin da ake koya musu kuma dai physics ne.
A kwana a tashi tau da gobe lud ya gama gidan su kaf sannan suka kaura. Masha Allah gidan su daidai da su kuma tsarin ginin irin na m. Salis ne saide paint da irin su kofa da window ne ya sha ban ban.
Da daddare maraki na zaune a parlour tana da CDS dayawa a gabanta tana nazarin wanne zata zaba ne ? Tafsir ok hadith kuma na wani malami? Ko kawai ta hau you tube ne ma? Ji tayi an kwantar da kai a cinyanta amma ko kallon sa bata yi ba Dan tasan inda zancen zai kare duk sanda ya fara like like da bin jiki kamar kulya.
Ganin ta shareshi yasa ya ja zirin gashinta da ke reto bige hannunshi tayi yayi dariya yace madam wai me nayi ne? Tace Maltina zan sha yace toh shine like hade rai tashi yayi ya dauko musu a fridge ta ce Kofi nan ma ya je ya kawo.
Tace zata ci kwai ya soya Mata ya kawo sanda tayi nat sai ta Mike kamar zata kitchen tayi masa gwaliyo tare da fadin ni bana sallah ma. Dariya yayi yace toh AI kinyi a banza Dan dama ni din ma ba wani Abu nake nema ba.
Ko banida ikon na kula da Mata ta sai ina neman wani Abu? Ya fada yana daga gira daya. Jikin ta ne yayi sanyi ta dawo ta zauna har ta mance ta ji caraf ya riko hannun ta yace wa na kama? Tace waiyo Allah na zata gudu yace ke wasa nake matsoraciya.
Dauko musu pop corn yayi suna ci suna kalle kallon su can yace why not gobe mu gaiyaci su umma da kawayenki da aminina suzo su saka ma gidan mu albarka? Tace hakan ma yayi amma de ni kar suzo tare da umma una so randa umma na zata zo mu kadan mu ne ta yini min.
Yace ji bakin wai umma na sai kace nata ne mutum da mamar sa a kwace masa. Tace AI nima mama na ne kuma kowa ya San da hakan. Dungure Mata kai yayi yace tafi can da wani goshin ki a wajen. Washe gari kuwa haka akayi suka gaiyaci friends din su.
Su mansura ne suka fara zuwa suka gida suka yaba domin kuwa ba almubazzaranci a ginin komai daidai misali. Suna cikin cin cup cake din da marakis tayi oga lud da aminin sa zannurain suka yi sallama lokacin mansura taje dauko musu cups da zasu sha kunun aya.
Gyara hijab dinsu suka yi. Kamin suka basu daman shigowa. Zama lud yayi a gefen marakis tace matas karde aiki suka sa min ke naga kin gaji. Zannu yace my guy basai ka tuna min banida aure ba. Mansura tace a yi zuciya toh.
Mansura ne ta shigo parlourn tana masifa wai garin wanke Kofi ruwa ya taba Mata waya. Hakan yasa bata ma lura da su lud da ke parlourn ba.
Beeba tace ke mansura kyankyaso tace a ina, marakis tace danger dago kai tayi daga wayanta ta kalli beeba ita kuma beeba da ido ta Mata alama tana kallon inda ta nuna taga lud, marakis ne ta wulla Mata hijab dinta ta saka daidai lokacin suka hada ido da zannurain.
Da sauri ta dauke kai har tana hardewa take fadin bari na karo cups. Zannu ne ya kalli lud yace Allah yayi lokaci ya kawo mu yana kallon marakis da sauri ta nuna masa lud da yatsa.
Lud yace ni bana ciki tukunna ma mune kyankyaso? Dariya suka kyalkyale da shi 😂ya matso kusa da kunnenta ta yace bashi kika ci. Kwaduwa kawai.😂
PLEASE KAR A MANTA DA YIN VOTING DA COMMENTING SAURA CHAPTER DAYA YA KARE ME DA ME KUKE SO NA RUBUTA? DUKDA DAI NA SHIRYA ME ZAN RUBUTA AMMA INA SON JIN RA'AYOYIN KU.
GA WANDA BASU YI FOLLOWING DINA BA FATAN ZAKUYI BADAN HALINA BA😉
TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO
Miss untichlobanty 💕
FINAL CHAPTER IS LOADING........
[10/12, 1:02 am] Miss Untichlobanty💕: *🤍🏆🤍YA JI TA MATA🤍🏆🤍*
🖤🖤by miss untichlobanty🖤🖤
marubuciyar :
*1.YARINYAR CE TAYI MIN FYADE*
*2. KURUCIYAR MINAL*
Feel free to contact me on :
WATTPAD miss_untichlobanty
INSTAGRAM miss_untichlobanty
WHATSAPP: 08146448881
Your little sis loves you and don't forget to follow me!
*🤍CHAPTER 60(FINAL)🤍*
*NOT EDITED*
Lud yace ni bana ciki tukunna ma mune kyankyaso? Dariya suka kyalkyale da shi 😂ya matso kusa da kunnenta ta yace bashi kika ci. Kwaduwa kawai.😂
Zuba kunin ayan sukayi zasu sha saide marakisiyya na kawo shi kusa da bakin ta ta fara makakin amai nan zannu yace my guy what's up ban gane ba. Lud yace nima ban gane ba tana kallon marakis daga hannu tayi sama tace kaina a cikin bakin leda a bakin tsumma a kasan gado. Mansura tace za ma ki since.
Nan suka tattara kowa ya watse su lud suka tafi asubiti tsabar a zarbabi daga mamakin amai😂
.......
Bayan wani Dan lokaci jummalo ta kammala iddan ta Dan haka m. Salis yace Mata za'a saka ranan sabon auren ta. Cike da murna tace da gaske sake aure na zakayi? Na dauka laihi nayi ai.
Murmushi yayi yace a ah ba sake auren ki zanyi ba ina dai son in tamabaya ki in kian so na zama waliyin ki ne. Tashi tayi ta shige dakin ta tare da cewa in de ba gidan ka zan koma ba ni bani so aradu bani auren kowa.
Mama dake zaune a parlourn ne tace au kainsalisu dam abaku taba yin maganar da ita ba sai yau? Kai haka ake ka saki mace ko dalilin ma baza ka fada Mata ba? Ko Dan kaga bata wayo shine kuka miyar da ita tamaula wanna ya buga ya bawa wannan?
Yace mama ba haka bane kawai ban Sami lokaci bane shiyasa tace toh AI shikenan nide na cire hannuna amma kar ka kuskura ta kawo karar ka waje na tace ka Mata dole ku lallaba ta kusan yadda zakuyi ku shawo kanta ko ku canja shawara.
Daga nan ya tashi ya shige dakin m. Ahmad. A kan gado ya same sa kamar kullum yana aiki da computer dinshi sallama yayi masa kamin ya shiga ya zauna. M.ahmad yace ya kuka yi da ita? M. Salis ya gyara hulan sa tare da fadin tace nan da kwana uku take so a daura amma kar kowa ya Mata zancen wai kunyar mama take ji.
Murmushi m. Ahmad yayi yace ja'ira daga baya kenan kamar ba ita bane ranan da kace ta dawo gidan mama ta makale maka wai a gidan ka zata zauna. Dan zun kudawa yayi yace amma tsaya idan har ta makale maka ranan AI yana nufin bata so ku rabu kenan.
M. Salis yake yayi yace haba dai ta dauka guduwa nima zanyi shiyasa wai ita me wayo ta makale min. Haka dai duk sanda m. Ahmad ya kawo kokonto sai m. Salis ya kafta masa karya.
.....
Bayan kwana daya da zuwan su lud asibiti aja ce suzo result ya fito da murna suka shiga office din likitan saide yadda suka ga fuskan shi yasa jikin su yin sanyi.
Bayan sun gaisa yace look nasan ku musulmai ne kuma kuna da tawakkali ba zan tsaya yi muku boye boye ba in nayi haka na cuce ku ku sani abin da zan fada cikin ikon Allah a samu canji amma gaskiyan lamari matarka bazata taba iya haihuwa ba idan ko aka dage ko ta samu cikin ma mutuwa ce!😳😟🥺😭
......
A kwana a tashi a kwana a tashi har Rana na uku ya zo mama ma bata San da auren ba sai daren washe gari take cewa Anya babu wani Abu a kasa kuwa me na gaggawa. Ni gaskiya ban yarda da ku ba bari na tambayo ta.
Koda taje domin ta tambayi jummalo ta Riga da tayi bacci hakan yasa ta kalleta Dan da ta tashe ta ma surutai take Mata ta fillanci. Haka dai tace toh zata sanar da jama'a Wanda zasu samu halar ta gobe.
Wajen karfe 8 na safe bayan jummalo ta ci abinci ta koma bacci abinta bayan ta tashi ma bata fito ba Dan an siya Mata waya an Dan koya Mata tana can tana buga game abinda tafi koya kenan😂 tunda ba wai tayi boko bane balle tayi su chatting.
Guda da ra ji ana yi yasa ta fito Dan ganin me ya faru Dan ta dauka ihu ne. Ta na fitowa taji manyan Mata sun damko ta ana fadin ga amar yar nan ma da ake fadin a damko mana ita.
Bude baki tayi zata tambayi me ake nufi aka danna Mata wasu gumba wai taci da kyar ta hadiye daga zatayi magana sai a dura Mata wani Abu ko ace kar ta damu AI ansan tana Jin kunya.
Ganin Abu yaki karewa yasa ta Mike ta warce hannunta daga wajen mai lalle tace wai mi ake nufi ne ba nace ni bazan aure hi ba ? Mama tace kamar ya bazaki aure shi ba ince ke da salisu kun tattauna kika ce a daura auren a kwana 3?
Dafa kirji tayi tace ba shiga uku ni ni jikan barmoji yaushe mukayi wagga zanshe da ya salisu? Hajiya lawisa kawar mama tace aikuwa yanzu zance ya kare Dan tun karfe Goma aka daura auren ku yanzu sha daya da rabi ihu ta fasa tare da musu zaman daba tace wallashi Allah ni bana son ya Ahmad ni wajen ya salisu na zan koma ya Ahmad cin zali na yake yiiii😭
Waya mama ta dauka ta Kira m. Salis tace maza maza ka zo ina neman ka da matsala, kamin ta kashe wayar ya jiyo Muryan jummalo tana fadin ita ko zata mutu bata zuwa gidan m. Ahmad hakan yasa cikin gaggawa ya Kira m. Ahmad ya fada masa gaskiya tare da yanayin da ake ciki a hanyarsa na komawa gidan.
M. Ahmad da ke shopping din akwati Wanda zai saka lefen sa ya hada wiri ya nema ya zauna gumi ya fara karyo masa yaran shagon suka zo suna fadin Alhaji lafiya? Ince lafiya dai ko?
.....
M. Salis na zuwa mama tace fara bayani, tsamo tsamo yayi a gaban matan kowa na jiran yaji me zaice kawai jikin sa ta dauki rawa ga jummalo na ta bori a gefe tayi cilli ma da ribbon dinta fuska shame shame da hawaye. Bayani ya fara musu cewa yasan m. Ahmad yafi son jummalo fiye da yanda yake sonta shi kuma farin cikin ta yake so.
Yasan tana son m. Ahmad ganewa ne bara yi ba tace karya ne, aradu karya ne kar ku yarda ni shi nake so hajiya saude tace oh ni yar mutum biyu jikan mutum hudu jimin diya da baki kamar gwazarma ba kunya kike cewa shi kike so?
Tace i, aradu ni hine ya min ko a auran shi ko nayi juyun dan dabas... wayan m. Salis ne tayi ringing na farko ya SHARE bai dauka ba a karo na biyu ne yaga m. Ahmad ne yasa ya dauka yace bro....kamin ya karashe zancen yaji ance Dan Allah kasan me wannan wayar ? Yace eh yaya na ne.
Ta dayan bangaren akace toh Allah yayi masa rasuwa Dan yanzu yayi hatsari wayar sa ma tayi raga raga sim din sa muka saka a wata waya sai muka ga numbar nan yayi saving da jinin jikina mun dauka matar sa ce.
Zama m. Salis yayi yace mene? Ban gani me kake cewa ba kana nufin ya ara muku wayar sa ku Kira wani kuka yi kuskure dai ko? Mutumin ne yace look, baqan Allah nasan kana da kusanci da mutumin nan amma hakuri zakayi ya rasu ina ne gidan ku zamu kawo muku shi yanzunnan.
Baki na rawa m. Salis ya fada mika wa hajiya altine ba tare da ta San wa ya bawa wayan ba yace fada musu gidan nan. Karba tayi ta kwatanta gidan tare da tambayar me ya faru, mutumin yace hajiya danki ne ya rasu saboda hatsari.....
Bata gama ji ba ta zauna tare da cillar da wayan tana fadin a'uzubillah minasshaidanir rajim. Hajiya saude tace menene? Tace shireman banza ake fadi wai Ahmad yayi hatsari ya mutu. Ji fa wani zance. Jummalo da ke kururuwa sai aka ji tsit yayin da mama ma tayi zaman dirshan tana fadin innalillah wa inna ilaihi raji'un, saltine kice wasa kike min.
......
Yau kwana biyu kenan da ahalin lud suka Sami mummanan labari na jarabta da Allah yayi musu Wanda abin ya taba su sosai. Marakis zaune a cinyan lud ta sakala kafarta a kugunsa yayinda kanta ke kirjinsa tana matsar kwalla tace AI shiyasa tun da fari ni jikina ke min wani iri naji ina son na haihu ashe bazan iya haihuwa ba.
Shafa kanta lud yayi yace toh ya isa mana kiyi hakuri baki ji me likita yace ba? Kila allsh ya canja mana kaddarar mu. Volume ta kara tace banason in fadi maganar ba amma dole sai na fada kawai ka auri kawata habiba ta Haifa mana yara😭
Yace baby ya kike magana kamar yarinya ne wai umm? Kawai Dan ba kya haihuwa kamar duniya ne zai tashi? Ko zaki haihu ko bazaki haihu ba ni ina tare da ke kuma idan ina da ke banida bukatar wata mace idan bukatar ya samu kinsan zanyi ba wai bazan yi ba.
Batun haihuwa kuwa ba sai muje ayi incubating mana ba? Kawai a saka mana a machine shikenan Tunda AI ba daga kwanki bane matsalar mahaifin ki ne ke da rauni kuma baki ji dalilin ba? Saboda wani maganin period pain da kika dinga sha ne cikin rashin sani ya miki illan shiyasa ake son kamin mace ta sha wani Abu ta nemi shawaran likita.
Da sauri ta Mike tace daga yau ni magani ma na daina sha tana turo baki tare da rugawa da gudu daki tana fadin tsaya na saka abaya na mu tafi asubiti dariya yayi yace kai na shiga uku. Bayan ta fito tace muje yace nawa zaki biya?
Tace na me? Yace ni sinadarin haihuwa na da zan bayar ance miki kyauta ne? Jifanshi tayi da remote tace AI in dan ya fito ba nawa ni kadai bane. Zama yayi a kujera yana alamun ya gaji yace kai ni banida nourishment ma dayawa kar a hada miki da nakasasshe.
Dunkule hannu tayi cikin kankanin ido tace in baka tashi min tafi ba I will kill you. Yace da na huta. Ficewa tayi kamar zakanya tana fadin I hate you yace I love you too baby yana Mata dariya kamin ya dauki key yabi bayan ta.
........
Zuwa yanzu kowa yayi jugum jugum ana jiran gawan m.ahmad karan ambulance da suka ji shi ya tabbatar musu da cewa ba fa mafarki suke yi ba.
Koda aka shigo da gawan an rasa Wanda zai bude fuskan sa m. Salis ne tayi ta maza yaje ya bude fuskan sa ba abinda ya same ta sai ma Dan murmushi da yake yi sai bandeji da aka daura masa Wanda an daura ne kamin ya cika a cewar wadanda suka kawoshi.
Rarrafowa jummalo tayi ta sanda tazo daf da shi ta kalleshi ta kalleshi kowa ya dauka zata fashe da kuka sai ta kyalkyale da dariya tace karyan banza anshe muku wasan kwaikwayo nake kallo ne wai?
Kawai a daura min aure da mutum yanzu kashe min ya mutu? M. Salis ne tace jummai nasan abin ya tabaki amma ya zama dole muyi hakuri kema wata rana....daga masa hannu tayi tace ba sani ba sai anje wata rana ba inde ya amadu ba zai tashi yanzu to nima kawai ku kashe ni. Ba kowa sai ya saki baki ba kai kace ba ita ta gama musu bori da shan majina ba.
Rike hannun m. Ahmad tayi tace yanzu kai in ba rashin mutunci ba sai ka mutu ? M. Salis yace ke kul fa tace yanzu da ka mutu idan nayi girki waye zaisha baiyi dadi ba? Idan nayi brush ta yaya zan nuna ma Dan kar ka kara yadda bakina ya wari? Waye zai she min ina kama da kulya amma kwakwalwan kihi gareni? Yanzu sabon dinki da nayi niyar sawa in nuna ma ina da kyau hikinan bazaka gani ba? Farar lace ne fa? Kalar kayan da naji kana cewa ya salisu kana so kaga mace a ciki.
Toh yanzu hikenan ka tahi ba ko sallama? Haka lokacin ma ka gudu daga gida ko Hodi min bakayi ba? Yanzu in nayi maka Allah ya isa da ka barni kashe banida kunya ko? Allah ka tashi ko in mintsine ka😭
M. Salis yace gani zan miki duka har fiye da Wanda yake miki ba dama cewa kika yi bakya son shi ba? Tace toh yanzu ina son shi sai aka yi kaka? Jijjiga m. Ahmad tayi tace ka tuna duk sanda nayi shirme ko abinda bai dace ba sai ka make 'keya ta kashe min behes (behave; usually used instead of the complete sentence BEHAVEYOUR SELF) ta karashe tana dungure masa kai.
Hada kai da guiwa tayi tana shessheka kuka taji an make keyarta tare da fadin behave. Da sauri ta dago AI kuwa taga m. Ahmad zaune yana Mata murmushi da sauri ta rungumeshi tana kuka tace ni dama nasan baka mutu ba kawai wasa ka ke min kun gani ko na fada muku bai mutu ba.
Yace toh AI in ban mutu ba yanzu kta jasgeni da wannan makure ni da kika yi sakin sa tayi ta Mike wai tayi zuciya m. Salis tace toh yanzu dai kina son shi ko? Tace ah ah kawai na fadi ne Dan ya tashi kuma ya tashi.
Kowa da kowa da ke dakin har mutanen da suka kawo gawan m. Ahmad Wanda dama abokan aikin su ne suka hada baki wajen maimata maganan ta KARYAN BANZA ANSHE MIKI WASAN KWAIKWAYO MUKE KALLO NE WAI?😂
Da gudu ta shige daki hajiya zuwaira Wanda bata yi magana ba tundazu tace ja'irar yarinya hajiya lawisa tace yar butan shayi kawai😂 nan aka fara cin abinci rayuwar kowa Normal
......
Marakis zaune tana ta tsittsilla ido lud rike da hannunta likita ne ya fito tare da fadin daga yau kisa a eanki kina da ciki nan da wata tara ki zo ki karbi danki tsalle ta daka ta fada jikin lud cikin murna suka tafi gidan umma.
Sannan suka sake sanar da aminan su cewa suzo gidan su for a sleep over wato suzo su kwana musu a tattauna rayuwa sosai nan suka amince.
A gidan su umma suka hadu duk Sanda mansura da zannu suka hada ido sai su dauke kai suna murmushi kamar wasu shashashu. Wajen 8 na dare suka nufi gidan su lud , marakis da ke jin hayaniya da guda a dayan makotan su na dama Wanda gidan m. Ahmad ne yayinda gidan m. Salis ke hagun su tace oh gaskiya wannan watan anyi aure kamar kaji muma ga daya mun samu.
Shiga gida sukayi inda takalmin beeba ya tsinke ta tsaya gyarawa jakan kayan su da take rike sa shi ya zube. Gyarawa ta tsaya yi bayan ta gama tazo zata shiga taga mutum tsaye a gefe yana kuka a tunanin ta shine angon.
Tace a iya sani na dai amare ke kuka toh bansan ko wannan angon yana kuka Dan bayida abokai bane juyowa tayi zuciyar sa na tsinkewa Wanda ya rasa dalili gani beeba ne yasa a ransa yace no wonder gaban sa ke fadi Dan yasan irin tsanar da tayi masa har tsoro take bashi.
Bai bari ta ga fuskan shi ba yace AI ba ni nayi aure ba yaya na ne. Tace na sanka? Yace kila kin sanni tace toh kai yayan ka yayi aure kai kuma ka labe kana kuka? Labari ya zezara Mata kaf har yadda suka yi wa jummalo dabara ta gane tana son m. Ahmad.
Ajiyan zuciya tayi tace ashe dai kai mutumin arziki nake jin haushin ka babu dalili, yace kin gane ni ne? Tace an ce ma irin jumman ku ne me kwakwalwar kifi? Dariya sukayi dukan su biyu tace oya man up ka shiga tunda kayi sacrifice kila ma ka samu me auren ka.
Yace wa ? Tace duba ka gani murmushi yayi yace zanyi tunani sannan sukayi sallama lokaci daya taji tsanar da take mai ya koma kauna kuma tasha alwashi indai da rabo zata aure shi.
Shi kuwa bai San menene a zuciyar sa ba kar ya yaudari yar mutane ya aminta da ita kawai Dan ya manta da jummalo saide abinda ya sani shine dole wata rana zaiyi aure kuma in wannan lokacin yazo toh ita zai fara nema.
Da asuba bayan anyi sallah a masallati m. Ahmad ya fito zai koma gida yaga kamar ba takalmin sa bane size din yafi nashi. Daga kai yayi yaga mutumin da ya saka nashi sallama yayi masa yana juyo suka kalli juna kallon kallo sukayi kamin lud yace Kaine? M. Ahmad yace nine musabaha sukayi tare da yin magana da ido.
Kawai kuma sai sukayi dariya m. Ahmad yace ya wuce lud ma yace da izinin Allah ga gida m. Ahmad yace kace makota na ne kai. Tafawa sukayi lokacin da kowa zai shiga gidan sa lid yace abi amarya a hankali makiyi na. M. Ahmad yace mai hali baya canja hali kaima a fito lafiya. Zannu ne ya rufe da gudu yana fadin my guy amana ta zaka ci ka barni a masallati zaka yi sabon amini? Lud yace kaga laifi na? Tare da shige yace ka dai rufe min kofar gida.
ALHAMDULILLAH! FATAN KUN ILMANTU KUMA KUN NISHADAN TU DA WANNAN LITTAFI AYI MIN AFUWA NA WAHALAN DA NA BAWA MASOYA NA BA SON RAINA BANE HAKAN YANAYI NE YA KAMA.
INSHA ALLAH BAYAN NA DAN HUTA ZAN GABATAR MUKU DA SOBON LITTAFI NA MAI SUNA (SARKI YACE A KASHE YARIMA) FATAN ZAKUYI MARABA DA SHI FIYE DA TUNANI NA. NA GODE DA KAUNA ALLAH YA BAR ZUMUNCI.
TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO
Miss untichlobanty 💕