Thursday, November 4, 2021
JARABTAR MU Page 1 to 10
Share this
Monday, November 1, 2021
Hukumar Hisbah ta kama matashin da ya yi yunkurin sayar da kanshi a Kano
Hukumar Hisbah ta jihar Kano, ta cafke matashin saurayin nan dan shekara 26 da hotunansa suka karade shafukan sadarwa bayan ya sanya kanshi a kasuwa da niyyar sayar da kanshi.
A wata hira da sashen BBC Pidgin suka yi da shugaban hukumar na jihar Kano, Sheikh Harun Ibn-Sina, ya tabbatar da faruwar hakan.
Shugaban hukumar ya sanarwa da BBC cewa sun cafke saurayin ne sakamakon abinda ya aikata ya sabawa koyarwar addinin Musulunci.
Ya ce a ka’idar addinin Musulunci babu wani dalili da zai sanya mutum ya sanya kanshi a kasuwa.
A cikin makon nan ne dai muka kawo muku rahoton yadda matashin mai suna Aliyu Na Idris ya yi yunkurin sayar da kanshi kan kudi naira miliyan ashirin (N20,000,000).
Ibn-Sina ya nuna rashin dacewar wannan abu da saurayin ya yi, inda ya ce hakan bai dace da koyarwa da dabi’ar addinin Musulunci ba.
Ibn-Sina ya ce:
“Tabbas mun kama shi jiya da daddare, kuma a wajen mu ya kwana, sai dai kuma har ya zuwa yanzu bamu yi hira da shi ba tukunna.”
“Sai dai za mu same shi domin jin ta bakin shi.”
Talauci ne ya tilasta ni
Aliyu Idris, ya bayyana cewa ya so ya sayar da kanshi a jihar Kaduna, sai dai kuma bai samu masu sayen shi daa daraja ba, hakan yasaa ya dawo jihar Kano, inda ya kara da cewa ya samu masu taya shi a farashi kamar miliyan daya daa dubu dari uku (N1.3m), amma bai sallama ba. domin ya kasafta kudin sa, idan aka saye shi miliyan ashirin (N20m), zai bawa iyayen shi miliyan goma, sai kuma miliyan biyar haraji ga jihar da aka saye shi, miliyan biyu ya bawa wanda yayi masa hanya aka saye shi, miliyan uku kuma zai bawa wanda ya saye shi ya ajiye masa, saboda wasu bukatu da ka iya tasowa nan gaba.
Wani mai suna Nura Isah, mazaunin jihar Kano ya yi tsokaci cewa bai kamata hukumar Hisbah ta kama shi ba. A cewar Nura mutane da yawa suna ganin cewa Aliyu wasa yake yi.
“Kamata ya yi Hisbah ta zaunar da shi su ji da gaske ya ke ko kuma wasa maimakon kama shi da su ka yi. Don ‘yan Kano da dama gani su ke yi wasa ya ke yi.”