Saurin zaro ido waje Rabi tayi tana mai girgiza kanta. “Wlhy ba haka bane ranki ya daɗe. Mizaisa na aikata hakan ga Nu'Aymah. Bayan sikari da Lipton sai ruwan dana dafashi da shi ne kawai a ciki”.
Wani irin tafasa zuciyar Yoohan takeyi daga can, ji yake kamar ya ziro hannu ya shaƙo wuyan Rabi ta cikin system ɗin, sai dai babu dama.
Little bee zatai magana Bily ta dakatar da ita ta hanyar ɗaga mata hannu. “Inaga ku maidata inda aka ɗakkota tukkunna”.
Babu wanda ya iya cewa komai a cikinsu. Sai tasa ƙeyar Rabi da aka saka wani jami'i yay tana kuka aka maidata inda aka ɗakkota.
Bayan fitarsu ajiyar zuciya bily ta sauke tana rubuce-rubuce. Kusan mintuna biyu kafin ta ɗago ta kalli Yoohan da zuciya ta kume daga can. “I'm sorry Dear wannan case ɗin duk yanda kuke tunaninsa ya wuce haka. Akwai wani abu dana fahimta dangane da wnanan matar wanda sam na kula ku duk baku gansaba. Kodai ya kasance amfani akeyi da ita a gidan batare da ita kanta ta sani ba. Kokuma tana kan sani ta fi yarda ta shanye duk wata azabar data fuskanta anan danta rufama wancan asiri. Kokuma an mata gargaɗi mai girma da tsoratarwa akan sanarwa tun ba yanzuba.
Dole wannan wayar tata na buƙatar sabon bincike. Sannan waɗannan voice recording ɗin suma zamu sake bincike sosai a kansu, idanma har ba'ita ɗin bace zamu gano ainahin mai muryar insha ALLAHU”.
Dukansu sun fahimceta. Hakan yasa Yoohan tabbatar musu da shima zai shigo Nigeria zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu, kuma harda Nu'aymah. Dan ya fahimci lallai wasan na gaske ne.
_____________★★
Tunda ya shigo gidan yau taketa faman binsa da kallon mamaki. Dan tun randa ya dawo daga 9ja ta kasa gane kansa gaba ɗaya. Kullum yana cikin ƙunci da tunani, baya son yawan magana, sai su yini su tashi har dare magana sau biyar bata shiga tsakaninsa da shi ba. Tayi tambayar harta gaji tayi fushi ta ƙyalesa. Daga ƙarshe ma sai ya koma fita asibiti. Idan ya tafi tunda safe sai tayi barci zai dawo. Ta fahimci yana hakane duk dan karta cigaba da masa tambaya akan abinda ke damunsa. Dan idan ya fita yata yawan kiranta kenan wai yaji yaya take ita da Unborn ɗinsa.
Hakan data ƙara fahimtane ya sata sake tattare maganar damuwar tasa ta watsar gefe. to shinefa aɗan kwanaki ukun nan ya fara sakin jikinsa yana kuma dawowa gidan kafin tayi barci. Yau kuma abin mamaki sai gashi kusan ƙarfe uku ya shigo mata.
Yanda batai maganaba shima baiyiba. Sai dai kallonta yake cike da tausayawa a gareta. Tana zaune ne a kujera ta miƙe ƙafafunta bisa centre table ɗin falon. Sai filo ƙarami a cinyarta ta ɗora lap-top a kai tana sauraren lecture da akeyi daga can school ɗinsu.
A ɗan kwanki goma sha huɗu ɗin nan duk ta rame saboda damuwarsa da itama ke damunta. Hakan yasa cikin nata ɗan watanni bakwai sake fitowa sosai gamai kallo. Musamman yanzuma da take sanye da skirt na atanfa da t-shirt mai ƙarancin girma. Sai dai ta ɗara waɗanda take sawa a da kafin samuwar cikin da girmansa. plate ne a cinyar tata shima gab da cikinta ɗauke da green apples a kai, sai ɗaya dake a hannunta da ƙaramar wuƙa tana yanka tana ci a hankali.
Sassanyan numfashi ya sauke da lumshe idanu ya sake buɗewa a kanta. sai kuma ya shiga takowa har inda take dan ganin taƙi daina kallonsa. Gefenta ya zauna daf da ɗora hannunsa akan fuskarta ya juyar mata da kanta ta koma kallon lap-top ɗin.
Cike da sanyin murya yace, “K da kike ɗaukar Lecture miye na zubamin ido kuma?”.
Uffan batace masa ba, sai iska data furzar daga bakinta. Itama da sanyin muryar tace, “Lafiya naga ka dawo da wuri haka?”.
Ajiyar zuciya ya sauke a karo na biyu, ya dora kansa a kafaɗarta tare da kamo hannunta dake riƙe da yankan apple ɗin ya kai bakinsa. Bata musaba ta saka masa itama. Sai da ya tauna ya haɗiye yana kallon lecturer ɗin shima sannan yace, “thanks you Sweet girl” ya ƙare maganar da kaima kuncinta sumbata, ya kuma tura hannunsa a rigarta yana shafa cikinta cike da ƙwarewar likitanci.
Kamar koda yaushe kuwa sai ga cikin na motsi. Dan duk sanda zai masa irin wannan shafar sai kaji ya motsa. Har mita Aymah ke masa akan ita miyasa cikin baya mata haka sai idan yaso motsinsa da kansa yakeyi. Kokuma idan tanajin matsanancin yunwa nanma yana motsawa.
A hankali yace, “Sheikh ɗin Daddy ga daddy ya dawo gida. Ina fatan bakai fushi da canjawarsa ba?. kana kuma cikin ƙoshin lafiya zinarin zuciyata”.
Fuska Aymah taɗan taɓe tana ɗauke kanta ta maida ga lecture ɗin da sam yanzu ma ba fahinta takeba ita.
“Jealous ɗin ya motsane madam?”. Yoohan ya faɗa a cikin kunnenta cike da neman tsokana.
Hannu tasa ta ture nasa da zuba masa harara. “Tunda Jealous ɗin nakeyi mizai hana a ciremin na huta”. Gimtse murmushin dake neman kufce masa yayi yana taɓe baki da ɗage gira ɗaya sama. “Silly girl, ai idan kinga mun barki sai mun cika watanni tara da kwanaki tara ciff insha ALLAH. magajin Uncle na zuwa kuma wata ƙwallon zata kuma faɗawa rag.....”
Lap-top ɗin da take shirin saukewa a jikinta yay azamar riƙewa dan yasan sotake ta gudu. “Oh am sorry sweetheart wasa nake fa ni. Mu mun isa miki gadara bayan yanzu kece boss ɗin gidanma, kammu bisa wuya Mie-mie. Nifa namazo miki da wani albishirne mai daɗi”.
Batare data tanka masa ba ta sake yunƙurawa zata tashi. “ALLAH seriously Sweet girl”.
Ajiyar zuciya taɗan sauke kaɗan. Sai kuma ta kallesa, “To ka bari naje na kawo maka ruwa”.
“Okay harda abinci. dan yunwa nakeji”.
“Ai baka da kaso anan gidan malam”.
Tai maganar tana shigewa kitchen. Murmushi yayi mai faɗi daya jima ba'a gani a fuskarsaba. Ya jingina da kujera yana furzar da zazzfar iska. Shi kaɗai yasan mi yakeji a ransa. Yana daurewa ne kawai saboda fahimtar halin da yake ciki na ƙuntata ta itama. Shikuma bayason haka kodan yanayin da take ciki........
“Uhyimmm! An tafi tunanin ko?”.
Saurin dubanta yayi yana ƙoƙarin canja yanayin fuskarsa, Aymah da idanunta suka cika da ƙwalla ta ajiye tiren data ɗoro masa plate ɗin abinci da ruwa sai kofin lemo ɗaya. Saurin riƙota yayi ganin zata gudu. Ya ɗorata a cinyarsa duk da tanata ƙoƙarin ƙwace kanta ga hawayen sun fara sauka a kumatu da gudu. Matseta yay da ƙyau ya lumshe idanunsa, tun tanason ƙwatar jikinta harta haƙura tayi luf a jikinsa tana shashshekar kuka da sauke ajiyar zuciya.
“Am sorry Zeeynab. I'm very sorry. Nasan tabbas ina ƙuntata rayuwarki da laifin da banakiba. Nima bada son raina bane, ina cikin tashin hankaline mai tsananin ruɗani Nu'aymah.......”
“Shine ka zaɓi ka ɓoye min saboda ni banda matsayin sanin sirrinka? Amma ni har sirrin daya kasance na family ɗina mun baka dama ka shiga tsundum saboda baka darajarka, sai ni da.......”
“Shiii!!!. Wlhy bani da wani sirri a duniyar nan sai ke Nu'aymah. Da ana buɗe zuciya ma'abocin kallo yaga sirrin dake cikinta dana buɗe miki tawa kin gani Zeeynab. Da kinsan wacece ke a gareni da dukkanin tasirin da kikayi a rayuwata da bazaki taɓa yin tunani irin wannan ba. Amma kiyi haƙuri nasan da laifina. Laifina shine ɓoye miki damuwata. Bana ɓoye miki dan baki isa bane, na ɓoye miki ne saboda al'amarine mai girma a gareni. Ki tayani da addu'a ke dai kinji. Ki kuma cire komai a ranki, ki yarda ke ta dabbance ga mijinki. Bakiga duk yanda kika rameba, hakan na tayarmin da hankali.....”
“Yah Yoohan amma ai......”
“Oh my Cutie karkice komai Please. Yanzu dai mu ajiye wancan batun bashi da wani muhimmancin cigaba da hargitsa mana rayuwa da tunani ok?. Ina miki albishirin zuwa Nigeria gobe insha ALLAHU ”.
Duk da kewar ahalinta da ɗokin son zuwa garesu da takeyi sai taji kamar tafiyar bata lafiya bace, musamman da tasan yace itada 9ja ɗin sai ta shiga watan haihuwa lokacin sun sami hutun ƙarshen shekara da Christmas.......
“Tunani again baby?”.
Numfashi ta kawo tana kallonsa. Kallo irin na tambayoyin da baki ya gaza furtawa.
“To ko a fasa nayi tafiyata kawai ni kaɗai”.
Da sauri ta girgiza masa kanta alamar a'a. Ya ɗan murmusa da sumbatar laɓɓanta. “Karfa kisa komai a ranki surprise ne kawai”.
Duk da bata yarda da shiba haka ta shanye abinta a rai. Sai dai ta masa maganar karatunta yace babu damuwa ko suna a can zata cigaba da ɗaukar lectures ta online ɗin. Daga haka suka fara shiri a ranar, duk da daima bawani sun haɗa kaya bane dan bama zasu tafi da kayanba tunda akwaisu acan babu buƙatar hakan.
A dai ranar duk wani abu da zai iya lalacewa sun fitar da shi. Suka ɗan fita shopping na abinda zata iya buƙata saboda lalurarta. Ranta cike yake da ɗokin Isa ga ahalinta bayan rabuwa da su tsawon watanni tara. A gefe kuma cike take da fargabar sakamakon abinda zataje ta tarar.
*_WASHE GARI_*
Washe gari safiyar juma'a jirgin su Nu'aymah ya sauka a ƙasar haihuwarsu batare da kowa yasan da zuwan nasuba. Sai da taimakon Yoohan ta sakko a jirgin saboda ƙafafunta da sukai mata tsami da kumburi. Sai faman taɓe fuska take kamar zatai kuka. Shi kam dai ga tausayinta ga dariya na cinsa a rai. a zuciya ya ayyana, ‘Abufa yazo ga ma'iya’.
Bayan shigarsu texi taji yace a kaisu hotel. Ai babu shiri ta kallesa, “Hotel kuma Yah Yoohan? Gidan papa ɗin fa?”.
Cikin jin zafin dake taso masa a rai ya girgiza mata kansa. “Zamuje, amma yanzu muje ki huta ko?”.
Hankalinta tashe akan tunawa da hoton nan da sauri tace, “A'a ni dai gaskiya inba gidan papa ba sai dai ka sani a motar kano na wuce. Yaya gamu da gidan iyaye mu kama raɓe-raɓen hotel kamar wasu marasa galihu. Kayi haƙuri gaskiya ni dai bazanje hotel ba”.
Duk yanda yaso lallashinta akan suje hotel ɗin dan shi bayason zuwa gidansu. Ko sha'awar kallon fuskar Momy bayayi sam. Amma Nu'aymah ta tubure duk da bawai dan tanason zama gidan bane itama. Tana son sujene saboda hoton nan. Gara suje tun a yau ta ɗauka kafin papa ya farga suna ƙasar tunda ya bada kwangilar kasheta. Daga lokacin da matsaloli suka fara kuma ai maganar hoto sai tasha ruwa.
Badan Yoohan yaso ba dole yasa mai taxi ɗaukar hanyar anguwarsu dan kuka Aymah ta sanya masa rirus babuko kunya. Sam baya buƙatar damuwarta a irin wannan lokacin. Dan yama fahimci jininta yayi sama saboda wannan tafiyar mai nisa da sukayo. Daga haka kuwa bai ƙara maganaba, sai dai ya sakata a jikinsa kawai yana shafa bayanta alamar lallashi. Saiko faman cijar lip ɗinsa na ƙasa yake da ƙoƙarin danne abinda ke taso masa a rai.
Har ciki mai taxi ɗin ya shiga dasu, koda maigadi ya leƙi yaga Yoohan sai ya koma da sauri ya buɗe gate ɗin ransa fal murnar ganinsu. Da taimakonsa Aymah ta fito yanzunma. yayinda gaba ɗaya Guards ɗin gidan suka rufu musu a ka suna kwasar gaisuwa bakin kowa a washe na murnar ganinsu. Zuciya kam fal gulma ganin Nu'aymah da ciki. Musamman ma Solomon daketa faman zare ido.
Solomon ɗinne ya amshi ƴan kayansu dake a trolly ɗaya sai lap-top bag ɗin Yoohan. handbag ɗin Aymah kuwa tana a hannun Yoohan ɗin ɗayan hannunsa kuma riƙe da nata.
Da Gebrail suka fara cin karo zaune a dining yana lunch ɗin daya makara baiyiba. Idonsa na sauka a kansu kuwa ya sarƙe da abinci har sai da Blessing ta fito daga kitchen a guje dan jin mahaukacin tarin da yakeyi. Ko kallon inda yake kuwa Yoohan da Aymah basuyiba.
Wani bala'in waro idanu Blessing tayi tare da daka tsalle gefe hannayenta duka a saman kai tace, “Heeyyy!!! Ahhhhhh!! Emiiii!!!”.
Dariya ta bama Aymah sosai. Hakan ya sakata darawar kuwa. Yoohan kuwa daya zaunar da ita a kujera ko kallon Blessing ɗin baiyiba. Sai durƙusawa yay a gabanta ya kama ƙafafunta ya zare takalman da take sanye da su masu taushi, amma saboda tsabar hawa da ƙafar tayi sun manne mata har sunyi mata sayi. Matsa mata ƙafar ya farayi a sannu-sannu ransa fal tausayinta duk da yasan bawai wata matsala bane. Yanayine kawai da wasu masu cikin kan shiga.
Ihun Blessing ne ya fito da Joy da Miracle daga ɗaki suma a guje. Sai ga Victoria dasu Favour da har yanzu su suna abuja basu koma ƙauye ba. Makaranta ma Yoohan yace zai duba musu anan, sai kuma aka samu akasi wancan matsalar ta faru Yoohan yabar ƙasar babu shiri.
Da gudun bala'i su Destiny sukayo kan Nu'aymah da itama take kallonsu fuskanta washe da dariyar Blessing data gama kwasa...
A wani zabure Yoohan ya miƙe yana dakatar dasu, amma ina sukam idonsu ya rufe yau saboda farin cikin ganin auntynsu da kullum suke nacin son dawowarta. Gata kuma da ciki zata haifa musu baby a gida.
Goshi kawai Yoohan ya dafe yana faɗin, “Oh GOD!”.
Itako Aymah da dama ba hankalinne ya gama isartaba oho. Tuni ta tarbi ƴan yaranta da suka nuna mata ƙauna zalla a gidan babu algus. Sai da Yoohan yaga lamarin nasu bana ƙare bane yasa hannu ya fara ɗagasu ɗai-ɗai daga kan Nu'aymahr.
Ihun su Destiny ne ya farkar da mama debora a barcin da takeyi. Ta fito jikinta na rawa dan ta ɗauka wani abunne ya faru da yaran. Kaɗan ya rage bata bangaje su Joy da Miracle tai suman gigitaba ta tarota. Kota kansu batabiba ta fara sauka a benen da gudu zane a hannu.
Wani bala'in waro ido tayi akan Nu'aymah tana faɗin, “Jesus John matarka ne da ciki? Cikin jikana ɗanka. Kaima zaka haifi yaronka John ?”. Sai kuma ta nufeta cike da Sassarfa. A take annurin fuskar Aymah ya ɓace ɓat, hakama Yoohan kallon kakar tasa yake yaga mizatayi. A mamakin kowa sai mama debora ta fashe da kuka tana rungume Nu'aymah. Sai kuma ta durƙusa ƙasa ta ɗaura hannunta akan cikin Aymah tana sambatun zance da yare wanda sam Aymah ba ji takeba. Sai dai yanda taga Yoohan ya langaɓe kai yana kallon kakar tasu fuskarsa da murmushi ya sata fahimtar ba mummunan abu mama debora ke faɗi akan gudan jinin nasu ba. Tabbas duk wanda ya kalli mama debora a wannan lokacin yasan farin cikine na gaske tattare da ita. Ba komai yay silarsaba kuma sai cikin jikin Nu'aymah ɗin. Dan kanta batasan yaya akai ƙaunar cikin ta saukar mata ba lokaci ɗaya tare da Nu'aymahn kanta. (Nace Ƙarfin addu'a ce mama debora).
Tana faman sharar ƙwalla ta kamo hannun Yoohan ta zaunar a kusa da Nu'aymah. Ta haɗa hannayensu cikin na juna sannan tai Kneeling a gabansu tare da rufe idanunta duka ta ɗaga hannaye sama ta fara raira waƙar addu'a da yare tana hawaye, ganin hakan yasa su Victoria ma durƙusawa tare da Blessing suka fara tayata suma duk idanu a rufe.
Cike da zaro idanu Nu'aymah ta kalli Yoohan kamar zatai kuka. Dariya taso kufce masa. Amma sai ya gimtse yay murmushi kawai. A cikin kunnenta yace, “Karki damu addu'ar kariya sukema baby dakema ALLAH ya saukeki lafiya cikin ƙoshin lafiya”.
Duk da tasan su ba musulmai bane ta ɗanji sanyi a ranta tunda ba wani tsafi baneba dai. sai kawai ta ɗora kanta a gefen hannunsa tana mai addu'a a ranta itama ALLAH yasa sunada rabon musulinci. Dan tabbas yau taji gaba ɗaya haushin mama debora da takeji ya kwaranye. Dama ance mai ɗa wawa.
Bayan sun gama addu'arsu sun zauna, mama debora nata wani ji da Nu'aymah. Ita dai abin har dariya yake bata. Hakam Yoohan dariya kakar tasa ke basa da gaske. Ta dungure masa kai tana faɗin, “Mara mutunci. kasan matarka nada ciki baka taɓa faɗama kowaba. Yarinyata watansa nawa?”. Ta maida maganar kan Nu'aymah bayan ta zubama Yoohan dake kumbura mata fuska saboda mangarar masa ƙeya da tayi harara.
Haka kawai sai Aymah taji nauyin faɗa. Sai Yoohan ɗinne ya bata amsa. Sai kawai ta tashi ta kama rawa tana waƙar yarensu irinta tsoffi.
A wannan yanayin papa da Madam Chioma da basa gidan suka shigo suka samesu. Gaban Nu'aymah yay mummunan faɗuwa. Da sauri ta shiga karanto addu'a a cikin ranta. Sannan ta yunƙura ta miƙe kamar yanda taga Yoohan ya miƙe fuskarsa a tsuke saboda ganin Momy.
Da wani irin kallo papa kebin Nu'aymah da cikinta. madam Chioma kam Yoohan take kallo kamar wata tsohuwar mayya. Dan sam hankalinta bai kai kan Aymah ba tukkunna.
Cike da farin ciki Mama debora ta nufi papa tana rera waƙarta da ke nuna tana a tsantsar farin ciki na haƙiƙa, hannunsa ta kamo ta nufi inda Nu'aymah take. Da sauri Madam Chioma takai dubanta inda mama debora ta nufa da Papa. Aiki idanunta sukai mata mummunan gani. Da tsanin gigita ta furta, “What??! Impossible!. Na rantse da ALLAH impossible!!!”.
A kusan tare kowa dake a falon ya kalleta, sai kawai ganinta sukai a ƙasa ta sulale sumammiya.
A guje su Destiny sukayi kanta da papa. Yoohan kam fuska ya kauda gefe cike da ƙunar zuciya. Nu'aymah da tasan ba sonta madam Chioma keyiba dama can sai bata ɗauki hakan komaiba face ƙiyayyar da take nuna mata dama can.
Mama debora kam wani irin taɓe baki tayi da faɗin, “Aiko Chioma zaki mutune a haifamin jikana duniya. Kujimin yarinya da baƙin halin baƙin ciki. Ke sanda kika haifi John nayi miki hassada ne? Bandama inada zuciya me ƙyau ai saina saka ayar tambaya a kanki dan Yoohana baya kama dake, nayi shirune kawai dan yana kama da yarona, amma kekam ai kamarma ba ɗanki ba. Sai shi yanzu zaki baƙin ciki matarsa zata haifa masa ɗa. Kema sai kinji abinda naji na rabani da ɗana da kikayi......”
A guje Blessing ta kawo ruwa aka yayyafama Madam Chioma. Tako fasa wata razananniyar ƙara da miƙewa zaune tana nuna Nu'aymah. “Wannan ba cikin yarona bane, kufitarmin da ashawo ɗinnan a gida, na rantse da ALLAH john wannan ba cikinka baneba. Dan hakan bazata taɓa kaswncewaba. Idan baku fitarmin da ita a gidaba zan kasheta. Ku kaita can ta nemo uban cikinta dan bana John bane. Darling narsantse damfararmu yarinyar nan zatayi cikin nan bana John bane. Sun tsafemin yaro sun rabani da shi. Yanzu zasu manna masa cikin kuma da ba nasab.......”
Yanda take surutan zaka ɗauka bata da hankalima sam. Yoohan da takaici ya kume yaja hannun Nu'aymah suka haye sama abinsu batare da yayi ko tariba. Mama debora ma wani dariya da ihu ta sanya tana tafa hannaye. “Chioma kishi da matar ɗanki yasa kin haukace gaskiya. Tunda ni kakar John na yarda cikinsa ne koke da goshpower kukaƙi yarda nasan kishi ne. Yanda nasha baƙin cikin rabani da ɗana da kikayi kema sai kinsha fiye da wannan baƙin cikin na rabuwa da John. Wuuuuuuu!!! She she Shem!!! Wuuuuuu!!!! Hhhhhhhh!!!! Anji kunya uwa mai kishi da matar yaronta!!!!”.
Hankalin papa ya sake tashi da abinda mahaifiyarsa keyi. Dan har cikin zuciya shima a kiɗimen yake game dayin tozali da wannan cikin da ko a labari bai taɓa sanin akwaishi ba. Lallai wannan shine lokacin daya kamata a fara yaƙin na gaske. Dan tura takai bango anzo dai-dai wajen.
Madam Chioma kam ihu takeyi da kururuwa har su Yoohan dake sama na jiyota.
Idanun Aymah da a yanzu sam batason yawan hayaniya cike da ƙwalla ta kalli Yoohan daketa kai da kawowa a cikin falon. “Yah Yoohan Please ka barni na wuce kano kawai zaifi. Wannan wane irin tashin hankaline? Maimakon ciki ya zama abin farin ciki sai kuma a maidashi tashin hankali? Kayi haƙuri mahaifiyarka ce, amma ina tsoron ta cutar dani nikam gaskiyar magana”.
Kallonta kawai Yoohan yake ransa na ƙara zafafa. Sai dai sam baiji zafin kalamanta ba, dan yasan gaskiyarta take faɗa. Shi kansa a yau ɗin nan ya sake shiga ruɗani dangane da halin mahaifiyar tasa. Wace irin uwace ita? Miyasa halayenta suka banbanta dana sauran iyaye? Tunba yanzuba wasu abubuwan nata suke dama masa lissafinsa da zurmasa a yawan tunani. Sai dai bai taɓa zaman musu fashin baƙiba saboda karta munana a cikin idanunsa. A wannan karon kam yaji bazai iyaba, dolene ko yanaso ko bayaso yasan dilin da yasa mahaifiyar tasa zafafa abubuwa akansa bayan kuma bashi kaɗai bane gudan jininta........
“Yah Yoohan maganafa nake”.
Nu'aymah ta dawo dashi hankalinsa saboda riƙe masa hannu da tayi. Nannauyan numfashi ya sauke tare da rungumota jikinsa yana sauke tagwayen ajiyar zuciya. Sunkai tsahon mintuna uku a haka sannan ya ɗagota, fuskarta cikin tafin hannayensa yana mai kallon ƙwayar idanunta data cika da hawaye. “Nima nafi aminta da tafiyarki Kano baby love, amma ina roƙonki kiyi haƙuri da safe idan ALLAH ya kaimu sai mu wuce kinji. Karkuma ki damu da zantukan Momy babu abinda zatai miki ɓacin rai ne kawai yasata faɗinsu itama kinji Heartbeat ɗina”.
Duk da bata gamsu baneba sai ta ɗaga masa kanta dan babu abinda take hange a cikin idanusa sai tsantsar tashin hankali da damuwa, itakuwa indai akan iyayensane bazata bari ya shiga tashin hankaliba insha ALLAH.
Yaji daɗin yanda ta nuna ta amince. Dan haka ya zaunar da ita duk da akwai ƴar ƙura a falon. Fita yay da kansa. Bai iske Momy ba da papa a falon, da alama sun shige daga ciki. Sai mama debora dake waya tana masifa da alama da ɗaya a cikin su momy Destiny take wayar, dan tana faɗa mata abinda ya farune.
Baibi takantaba itama yay kiran Blessing dasu Destiny suzo su musu gyara. Tare ya koma dasu, ya zauna yana mammatsama Aymah ƙafa daya tarar tana matsawa, su kuma suka fara aikin gyaran.
Koda suka kammala ɗakinsa ya janyeta sukai wanka a tare. Suna fitowa babu jimawa Blessing tai knocking. Jallabiya ya zura ya fita danya duba wanene?. Samunta yay tsaye da ƙaton tire ɗauke da abinci. Hanya ya bata ta shiga. Ta ajiye tiren a dining sannan ta fita kanta a ƙasa. Ƙofar ya maida ya rufe, yaje ya ɗauki tiren ya nufi ɗakinsa da shi.
Nu'aymah na kwance a gado ko towel ɗin jikinsa ta kasa cirewa saboda gajiya da barcin dake ci mata idanu. “Kefa yanzu kin zama raguwa Sweet girl. Tashi to ga abinci”.
Tashi tai zaune fuskarta da murmushi itama. Tace, “Duk ba ɗanka bane ya maidani hakan? Nida naci burin duk randa nazo 9ja yawo sai inda ƙarfina ya ƙare. Amma gashi tun ba'aje ko inaba lalaci ya fara mamayeni”.
Ƴar dariya yayi yana miƙa mata t-shirt ɗinsa mai girma sosai. Ta amsa ta saka sannan tazo inda yake zuba abincin. Tasan Blessing ce tai girkin shiyyasa zataci. Da taimakon Yoohan kuwa taci ta ƙoshi tai nak, shima ta bashi yaci sai dai kaɗan yaci dan sam zuciyarsa bata cikin jin daɗi. Yana dannewane kawai danya ƙarfafa Nu'aymah.
Suna gamawa gadonsa ta haye ta kwanta saboda uban barcin dake cimata idanu. Bai hanataba, saboda shima yafi buƙatar tayi barcin a yanzu. Babu jimawa kuwa barci mai nauyi yay gaba da ita.
_________★
Tunda Blessing mai kawoma Omar rahoton gidansu Yoohan ta kirashi ta sanar masa da abinda ya faru game da isowar su Yoohan ɗin hankalin Umar yay ƙololuwar tashi. dan shi kansa da yasan Yoohan gidansu zai wuce da Nu'aymah ba hotel ba ko kano da bazai bariba. Dolene shima yau ya kwana abuja kuwa dan harga ALLAH lamarin papan Yoohan yanzu tsoro yake bashi harma Momyn, bai ƙara tsinkewa da al'amarinsu ba sai akan abinda ya faru tsakanin Yoohan ɗin da Momy. duk da su hasashe sukeyi tunda su su Blessing bawai sunga komai baneba akan idonsu.
A take ya bincika ko akwai jirgi mai tashi zuwa abuja. Yakoyi sa'ar samun mai tashi nanda sa'oi biyu, dama shekaran jiya ya baro Abujan ai. Bai kira Yoohan ba, dan yafi son ya gansa tsulum kawai a bazata.
___________★
Shiko Yoohan yana samu Aymah tayi barci saiya fito zuwa sashen papa. Zaune ya samesa a falo yana waya. Yana ganin sa kuma ya yanke wayar. Ko a jikin Yoohan, dan ba wannan ne ya kawosa ba.
Zama yay a kujera, batare da ya dubesa ba yace, “Good afternoon”.
Papa ya danne abinda ke a maƙoshinsa da ƙyar ya amsa masa. Ya ɗora da faɗin, “Saukar yaushe haka babu labari. Aini nazata yanzu ni narigada na haifama Sheikh Sooraj ne kai?”.
Shiru Yoohan yayi baiyi magana ba. Hakan sai ya ƙara harzuƙa papa matuƙa. Cikin tsagwaron masifa yace, “Ina magana da kai kamin banza. Wato na fahimci dama nika maida ɗan iska game da cewar wani aiki kakeyi akansa. John dolene yau insan minene tsakaninka da Sooraj?”.
A matuƙar ɓacin ran da Yoohan shima baisan dalilinsaba, cike da suɓutar baki yace, “Papa nima inason sanin shin da gaske Momy itace ta haifeni? Dan ban taɓa jin mai halin uwa irintaba. Inhar ka amsamin wannan tambayar ni kuma na maka alƙawarin sanar maka alaƙata da Uncle Soorajidden Hashim jibiya. Sannan kama matarka gargaɗi, wlhy inhar wani abu ya samu cikina ko matata a gidan nan komaima zan iya aikatawa..”
Yana kaiwa nan ya miƙe fuuuu ya fito yana huci. Da sauri madam Chioma dake bakin ƙofar tsaye tai baya ta bashi hanya cikin matuƙar rawar jiki da tsagwaron tashin hankali. Dan taji komai daya gudana tsakanin papa da ɗan nata.
Wani irin zufar tashin hankalice ta shiga karyoma papa. Jikinsa na rawa ya zamo ƙasa daɓas kan carpet ya zauna. Gaba ɗayama duniyar sai take juya masa. Yau John ɗinsane ke kallan cikin idanunsa yana faɗa masa magana irin haka babu kunya babu tsoro. To tayaya hakan ta faru? Minene kuskurensa? Karfa ace lokacin da yake jira domin nasara ne ke shirin masa juyen ruwan hadarin da ba'a tsammaci zuwansa ba. cikin rawar jiki ya miƙe ya nufi bedroom ɗinsa batare da ya kula da madam Chioma dake a tashin hankalinba itama. A gurguje yay shiri ya fito daga ɗakin. Idonsa a rufe ya sake bangaje madam Chioma ya wuce dan harga ALLAH bai gantaba yanzuma, idanunsa har wani yana-yana suke masa saboda jirkicewar ƙwaƙwalwa dana tunani...........✍
ZAFAFA BIYAR 2021
Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
(Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗
Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗
Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗
Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋
Duka akan farashi mai rahusar gaske.
Kamar haka👇🏻💃🏻
Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇
ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇
0903 234 5899
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇
09033181070
💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍
ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.[7/6, 9:38 AM] +234 913 412 2711: *_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.
No. 72
...........Washe gari bayan sallar asuba Nu'aymah ta ɗorama Yoohan karatu kamar yanda suka saba. Daga haka ya shiga ɗakin motsa jikinsa. Ita kuma sai tayi amfani da wannan damar ta shiga ɗakinta domin ɗakko hoton nan. Duk da ta jima bata shigesaba ta fahimci an canja mata zaman wasu abubuwa da dama. Wasuma babusu. Bata bar hakan ya dametaba ta nufi Wadrobe direct inda ta ajiye hoto. Sosai gabanta ya faɗi ganin yanda kayanta suka koma a harmutse ba yanda tasan sukeba. Cikin gigita ta shiga tiɗosu ƙasa tana faman zazzagewa. Sai dai kamar da wasa babu hoto babu labarinsa. Hankalinta ya tashi, har takaita da duba indama tasan bata ajiye ɗinba amma ko mai alamarsa babu.
Jagwab ta zauna a bakin gado tanabin ɗakin da kallo daki-daki, dan sai a yanzune ma harmutsewarsa ba yanda ta barsaba yake dawo mata a zuciya daki-daki. Yoohan ta fara kawowa a zuciyarta. Sai kuma ta girgiza kanta dan bata tunanin zai mata bincike. Can ƙasan zuciyarta yace, ‘Omar ne. Bashi kika sanarma maganar hotonba’. Nanma da sauri ta girgiza kanta alamar a'a. Gebrail. ‘Kai bazai zama shiba. Dan shi manufarsa daban data masu hankali. Wannan bashi da man kai akan hakan’. Madam Chioma. Nanma a fili tace, ‘Kai ina bana sata a wannan layin dan kanta baya ja tacika kidahumanci kamar kifi’. ‘To wa zan zarga?. Ko dai papa ne?’. Mikewa tai da sauri tana kaɗa kanta hannayenta duka biyu a saman cikinta. ‘Lallai tabbas shine abin zargina, musamman daya kasance ya riga yabi diddigina akan shigar masa ɗaki da nayi, zai iya kasancewa tunaninsa ya basa zuwa nan yamin bincike. Shin minene wannan mutumin ke ɓoyewane akan mijina? Lallai ya kamata na sani kafin na sake barin ƙasar nan’. Sai kuma ta dafe goshi cike da damuwa. ‘Hoto shine kawai hope ɗina. Gashi yanzu ɗan barahazar ya sace min, bayan na gama baza bayani wajen Abbana da wannan Umar ɗin. Kenan dolene na sake satowa. (Idan bai ƙonaba ko?) zuciyarta ta ayyana mata. Karan farko da matsanancin tsoro ya risketa. Da sauri ta fita a ɗakin zuwa can cikin gidan. Gidan shiru alamar masu gidan babu wanda ya tashi kasancewar weekend ne. Kitchen ta nufa. Tako iske Blessing kawai tana haɗa breakfast kamar yanda tayi hasashe.
Ko gaisuwar Blessing ɗin bata amsaba taja hannunta suka shige cikin store. Sai da ta leƙa ta tabbatar da babu kowa sannan ta tura ƙofar store ɗin ta rufe ta juyo ga Blessing da jikinta harya fara rawa. “Please ki nutsu, ba wani abu bane tambaya zan miki, ina fatan kuma zaki bani amsa kamar yanda kike bama Omar... Oh sorry Richard”.
Cike da tsoro Blessing zata fara rantse-rantse Aymah ta tsaidata......
“Karki wahal da kanki wajen mani rantsuwa nasan komai daga wajensa. Inason nasan zuwan Richard nawa gidan nan?”.
Da tsoro sosai a fuskar Blessing tace, kusan bakwai”.
“Dama can anan yake sauka kenan tunkan aurena da Yoohan kokuwa a yanzune yake sauka anan?”.
“Eh dama yana sauka gaskiya, amma sai Oga yana ƙasar”.
Jimm Nu'aymah tayi alamar tunani, sai kuma tace, “Mikike tunanin yana zuwa yi nan gidan?”.
Cike da tsoro sosai Blessing ta buɗe ƙofar kaɗan ta leƙa, hakan yasa Yoohan daya biyo Aymah yake a laɓe saurin komawa ya lafe a bango. sai da ta sake tabbatar da babu kowa sannan ta dubi Aymah murya can ƙasa sosai. “Na yarda dake sosai Aunty na, dan tun a zuwanki gidan nan na fahimci ke mutuniyar kirkice wlhy. dan haka zan sanar miki komai duk da nima ba komai ɗin na saniba”.
“Okay ina saurarenki”.
“Tun bayan wucewarku Austria nakeji wasu maganganu masu gidan nayi a kanki. Dan akwai randama na taɓajin an bada kwangilar kasheki ta hanyar likitan da zasu miki aiki. To sai dai kwanan mutuwarki bai rigada yazoba dan ke ƴar baiwane. Sai akazo baki mutuba. Su boss sunje dubaki, bandai san miya faruba bayan dawowarsu Uncle Richard naga ya nacema zuwa gidannan. Sanan yakan sani na masa wasu abubuwa akan boss ko madam ɗin gidan nan. Sannan ko baya gida zai kirani yaji mi akayi ko mi ya faru. Badai komai nake fahimtaba gaskiya, tunda banida hurumin yin komai. Sai dai matsalar dana fuskanta shine randa su papa suka shiga sashenku ita da Solomon da Madam. Sun miki bincike a ɗaki sai dai basu sami komaiba suka fita. Bayan hakan Uncle John yazo ƙasarnan yaga yanda akai miki da ɗaki shine ya zane Gebrail a tunaninsa shine ya shigar miki. A zahiri papa baicema Uncle John komaiba akan dukan Gebrail. Amma bayan barinsa gidannan ba ƙaramin rikici akayiba tsakaninsa da maman madam dama madam ɗin. Shima kuma papan naji yana wasu maganganu tsakaninsa da Brothers ɗin nan nasa wanda ban ganema kansuba sam. Wanann rikicin ne ya saka su Maman Destiny barin gidan nan. Dan sun nuna goyon bayan Uncle Yoohan fiye da Gebrail. Shine yasa akai rikici duk suka wuce. Bayan nan kuma sai Uncle john ɗin da yazo last time madam ɗin gidan nan ta shigar masa ɗ.........”
Da sauri Yoohan dake a laɓe ya rin tse idanunsa tare da shiga kiran sunan Nu'aymah tamkar ya shigo nemantane. Rikicewa sosai Blessing tayi, amma Aymah ko'a jikinta saima ɓata fuska tayi ta buɗe ƙofar bayan ta ɗebo noodles guda biyu.
“Oh Sweet boo ganinanfa a store. Nazo amsar noodles ne a wajen Blessing shine take nunamin inda take”.
Cike da mamaki yake jinjina wayonta. Amma shima sai ya waske yana mai dafe kansa da faɗin, “Kinsa duk na ruɗe na fito ban gankiba a gaba ɗaya sashen”.
“I am sorry Hubby”.
“Silly girl yana iya dake. Yanzu yaya za'ai da Noodles ɗin?”.
“Zan dafa ne anan”. Ta faɗa saboda son ya barta ta ƙarasa jin zance a wajen Blessing.
Fahimtar hakan da yayine ya sakashi hayewa saman kitchen cabinet ɗin yana cewa, “Okay dafa to mu wuce. Dan kinsan akwaima fa inda zamuji ga lokaci nata ƙurewa, Omar ma jiranmu yakeyi tuni. Koma kibama Blessing ɗin ta dafa miki muje ki shirya data gama sai kici kawai”.
Duk da Aymah bataso hakan ba sai ta amince kawai. Dan ita bama cin noodles ɗin zatayiba sam. Blessing ta ƙwalama kira. Sai gata ta fito da sauri hannunta ɗauke da abinda zata dafa da rana irin dai shi ta tsaya ɗebowa. Sai dai kallo ɗaya Yoohan ya mata ya fahimci tsoron dake tattare da ita.
Bata dahuwar noodles ɗin tayi suka fice. Gaba ɗaya hankali Nu'aymah akan Blessing yake. Amma Yoohan yay mata tsayuwar sojan badakkare aka komai tare sukayi. Koda suka fito Blessing ta kawo noodles ɗin catai ta ƙoshi. Sai Yoohan ɗinne yaci tare da Omar. Dama yasan baci zataiba ai. Dan tunda ta samu cikin nan tabar cin indomie sam.
Koda suka gama ficewa sukai a gidan batare da sunbi takan kowa ba. garama mama debora sun haɗu da ita a falo tana shan shayi. Tako hanasu fita saida akaima Aymah addu'oi ita da cikinta. Dan tace ita yanzu ta daina yarda da madam Chioma a gidan sam😂🤣.
Ita dai Aymah yanzu tsohuwar birgeta takeyi. Dan har suka bar gidan batabar murmushi ba akan abinda ya faru.
Tafiyarsu ta ɗanyi nisa Omar ya fahimci ana binsu a baya. Shima Yoohan ya gani amma baice komaiba. Dan babu abinda zuciyarsa ke masa sai tariyar zancen Aymah da Blessing. Tunaninsa wane abu ne Aymah ke zargin an shigar mata ɗaki akansa ana nema? Sannan kuma ashe papa ne da madam Chioma suka shigar masa ɗakin mata hardama Solomon?. wane bincike Umar keyi akan iyayen nasa? Mi Aymah ta shiga yi ɗakin papa a wancan karon daya dage kareta a wajensu amma hardayin ƙaryar taga wanda ya shiga ɗakin ashe itace? Miyasa mahaifinsa yasa a kashe masa mata? Dolene yasan waɗanan tambayoyi a lokacin ƙanƙani insha ALLAHU.
Da wnanan tunani da yakene yasa har Omar ya gudama masu binsu shi baisan yaya akaiba. Sai ganinsu kawai yayi a station ɗin su Jay.
Aymah dai har suka shiga tana maibin wajen da kallo tare da jami'an tsaro. Ko ɗar batajiba duk da ta fahimci wajene bana wasan yaraba. Yau saɓanin ranar Office ɗin Jay aka kaisu direct, acan suka sami Dawood da Little bee da bily. Sai Afrah da adalilin zuwan Aymah Jay yasa akazo da ita. Dan ita karatun lauyanci takeyi batabi ayarin su little bee ba.
Duk da a hoto sukasan juna ita da Aymah hakan bai hanasu gane junaba. Suka rungume juna kuwa cike da ɗoki dan sunyi sabo sosai ta chart da waya. Daga haka Aymah ta gaida little bee dake zaune tanata danne danne a Computer alamar miskilawan na kusa. Dan duk ihun dasu Aymah sukeyi ko kallo basu ishetaba, aikinta takeyi hankali kwance. Gaisuwarma a haka ta amsata. Sai daga baya ta ɗago ta kalli Nu'aymah sannan suka gaisa dasu Yoohan.
Nu'aymah dai bata sake bi takantaba itama ta juya ta gaida Dawood da Miemaa data amsa mata da fara'a da kulawa, dan itama ta taimaka mata ta zauna a kujera. Daga haka ta gaida Jay da a kallonsa sai da gabanta ya faɗi. Duk da ba tsananin kamanni suke da Yoohan ba dolene kaga yanayin gittawar jini tattare a tsakaninsu. Duk da ba mutum bane shi mai yawan wasa saida ya tsokaneta kaɗan. Har hakan ya bama su Yoohan mamaki. Dan su dai ba taɓa ganin dariyarsa sukaiba tunda suke mu'amula da shi.
Sai da aka lafa da gaishe-gaiahe Jay ya fara magana.
“So ba shirita ne ya taramu ananba. Inason ku bani hankulanku nan gaba ɗaya. Da farko dai kece bakisan dalilin zamanmu ananba duk da mijinki ya tabbatar mana ta hanyarki yasan wasu abubuwan. Sai ko Afrah da sanin nata baida muhimmanci daga tushe duk da itama da taimakonta ne muka samu bayanan sirri game da gidanku. So yanzu little zata miki sabon bayani, ke kuma Afrah jeki waje ki jiramu”.
Sosai Afrah ta ɓata fuska kamar zatayi kuka. Cikin magiya tace, “Abie Please ka barni dan ALLAH, wlhy nima zan taimaka muku da wani abun kaimafa ka sani. Duk da ba aikin nan nakeba so nawa ina muku aiki ta ƙarƙashin ƙasa”.
Fuska ya haɗe zai mata magana Aymah da duk kwarjininsa ya cika mata idanu tace, “Abie dan ALLAH, indai hakan ba laifi bane ka barmin Aunty zanfi samun ƙwarin gwiwa nima”.
Kasa cewa komai Jay yayi, ya kai dubansa ga little. Da wani style na ƙwarewar aiki taima mahaifin nasu alamar roƙon yabar Afrah ɗin. Dan itama tana hasashen tasirin zamanta a wajen.
Ɗauke kansa kawai yayi ya maida ga Yoohan dake ta kallonsa kamar ya samu television. Sai kuma ya ɗauke ya sake maidawa ga little bee alamar ya bata damar yima Aymah bayani.
Tsaf ta gama yima Nu'aymah bayanin komai. Dan haka taketa duban Yoohan da Umar cike da mamaki. Da damuwa a harshenta tace, “Amma Yah Yoohan baka gudun Abbana kar yaga ba'a ƙyauta masaba. Sam baya son laifin jama'ar gidan nan namu, shiyyasa yake ƙoƙarin maida laifukansu kuskure dan gudun lalacewar zuminci”.
“Zeeynab inhar muka cigaba da bama Uncle goyan baya akan hakan tabbas sai an salwantar da ran ɗaya daga cikinsu ko ke ko Muhammad a wannan gidan naku. Dan ni nasan mina ganarma idona a Austria da wasu maban-banta wajaje dangane da ke”.
Bata iya tace komaiba dan tasan gaskiya Yoohan ya faɗa. Bandama ALLAH yasa tanada sauran kwana a duniya ai da tun tana jinjira an aikata barzahu ɗin. Sannan shima Muhammad ɗin ai ansha gwada rayuwarsa a mabanbanta lokuta Abba na ɓoyewane kawai........
Cikin katse mata tunani Jay yace, “Karki damu akan Sheikh, ni zan masa bayanin dazai gamsu akan hakan. Yanzu zamu tafine kai tsaye akan abinda ya taramu anan tunda kin gama jin bayanan farko. Dan dama munsa mijinki ya dawo dake ƙasarnan ne dan zamu ɗanaki a gidanku ne matsayin tarko. Dawood minene bayani akan binciken wayar matar nan da aka sakeyi?”. Ya ƙare maganar da maida hankalinsa ga Dawood.
Takardun gabansa ya ɗauka ya fara bayani. “Sir bayanan sununa tabbas ana amfani da wayarta batare data saniba. Kamar maganar yin waya da mai aiki da aka turoma matar Yoohan anan Abuja, sam ba Rabi bace ke waya da Uwaliya. Mun tabbatar da hakane ta hanyar binciken ainahin muryar da aka samu a voice recording ɗin nan. Haɗine ta hanyar makirci babba na masu ilimin sani akan na'ura mai ƙwaƙwalwa. Suna amfani da wani app... Ne da aka saka cikin wayar matar, dama kowacce waya idan ta sake sai suke sarrafa wayar tata daga wajensu batare da ita ta saniba, suna barin mata bayanan abinda sukai da tasu wayar, dan ko an tashi bincke ita za'a zarga kai tsaye. Hakan yana nufin kenan tun fil azal da aka kawota gidan dama akwai manufa a ciki, kokuma daga baya aka fara amfni da ita. Waɗanan sune tatattun bayanai akan ainahin contact dake a wayar Rabi wanda suke aiki da saninta. Waɗanan kuma sune ainahin waɗanda ake amfani da ita ta wayar batare data saniba. Kuma insha ALLAHU zasu taimaka mana mu zaƙulo kosu wanene masu aikata hakan kamar yanda Abdurrahman Sameer Saifudden ya bamu tabbaci, dan shine yay wannan bincike gaba ɗaya tun daga ƙasar india. Ya kuma tabbatar mana idan ana buƙatarsa zai iya zuwa koshi ko abokan aikinsa yan uwan tagwaicinsa kenan”.
Cikin jinjina kai Jay ya amshi takardun yana duban little bee. “Bilkisu! Minene bayanan wajenki akan zaman Afrah gidan?”.
Juyowa Little bee tayi da kujerar da take a kai tana fuskantarsu. Yoohan ta sake kallo kamar yanda dama tuni shi take kallon a sace bisa ƙyaƙyƙyawan nazari datakeyi akansa tun farkon fara ganinta da shi.
“Sir! Bayanan dake anan sun nuna wasu sunaye da Afrah ta rubuta akan zarginta, saboda wasu al'amura da suke aiwatarwa a gidan na marasa gaskiya. Akwai Rabi. Mai aikinsu, a yanzu tana a hannunmu. Sai Mai aikin sashen Addah, sai ita kanta Addah da tafi kowa kusanci da Umm a gidan. Sai Nasir wanda asali shi bama ɗan gidan bane yana zuwane lokaci-lokaci. da wasu sunaye a jerin ɗaliban Uncle Soorajidden ɗin. Ta tattara waɗan nan sunayen ne bisa dalilai mabanbanta da suka faru akan idonta da kuma yanda labarin yazo garemu. Zamu iya jin bayani daga bakinta gata nan idan da buƙatar hakan”.
A yanzu kam bily ce tai wani gutun murmushi tana kallon Jay. Cike da nuna ƙwarewar aiki tace, “Boss niko kaga a duk jerin sunayen nan mutum uku kawai naba ayar tambaya. Sauran kuma inaji a jikina basa zaune a cikin gidan. Abinda yasa nai wannan maganar shine duk lokacin da za'a cutar da ita Nu'aymah akan yine lokacin wani taro a gidan. Hakan na nufin akwai mazauna gidan dake zaune a waje cikin tafiyar. Amma ƙasurgumin azzalumin yana nan cikin gidan tare da su ko akasin haka.
Murmushi Jay yayi a karo na farko. Ya sauke numfashi da ɗan buga pen ɗinsa akan takardar gabansa. “Tabbas komai zai iya kasancewa. Dan suma sauran ai hasahe mukeyi, tunda ga Rabi a hashe muka samota kuma sai gashi babu laifinta”.
“Hakane kuma boss. suspect ɗinmu na gaba sune, Nasir, Ameer, Hamisu, Kubrah, Abdallah. Da iyayen su Abdallah n”.
Da sauri Aymah tace, “momy!” cikin zaro idanu. sai kuma ta shiga girgiza kanta da sauri-sauri tana cigaba da faɗin, “Bazai kasance hakaba Momy. Uncles ɗina suna matuƙar son Abbana. Hakama Yah Abdallah na matuƙar sona. Bazasu cutar damu ba sai dai idan Nasir ne”.
“Relax Nu'aymah. Muma bamun tabbatar bane hashene kawai. Dan dolene mu alaƙanta laifin nan da mafiya kusanci da iyayenki dake kanki, shiyyasa zamuyi amfani da wannan lokacin da mukasan duk ahalinki zasu taru a gida saboda bikin aure da saukar yaran gidan marayunku mu ɗana musu ke a matsayin tarko wajen damƙesu batare da sun fargaba.....”
Yoohan ya katse Bily da cewar, “Humm tabbas Momy bana tantama akan hakan. Musamman akan Abdallah. Dan ta dalilinsa na sakama sauran ayar tambaya. Abdallah yayi fushi yabar Nigeria saboda ba'a aura masa itaba. Amma kuma a bayan fage yana a cikin ƙasar, dan yana yawan shigowa akai-akai. Sannan kuma yana bibiyar al'amarinta dani kaina. Dalilina na biyu a kansa shine wani business da yakeyi a ɓoye batare da sanin iyayen nasaba. Dalili na uku akwai harƙalla akan aurensa da yara biyu na gidan da aka aura masa dalilin sace Zeeynab da akai ranar wancan auren nasu. Ya saki yaran batare da ɗaya ta tare ba. Wadda ta tare ɗin bincikena ya tabbatar min da tasha wahalar zama da shi. Zargi na uku. Akan hotona da aka kai gidansu ni da ita. A yanda labarin yazo kakarsu bata bari su Abdallah sunga hotunanba a waccan ranar, amma daga baya sai hotunan suka zo hannun Abdallah harya kaisu office ɗina. Hakan na nufin bayan na hannunsu akwai wasu kenan dama a wajensu komi? Zargi na biyar, Abdallah yafi kowa ɗaukar zafi akan hotunan a gidan, duk da kuwa nasan Uncle da Umm sai sunfi kowa jin raɗaɗi da zafin hakan game da tilon ƴarsu. Amma sai ya nuna zaƙewa akan hakan harda kawomin abokinsa wai yay Arresting ɗina. Zargi na ƙarshe, miyasa a duk lokacin da akai tunanin ƙulla aurensu sai wani dalili ya ruguza shi?......”
“Please Yah Yoohan ya isa haka mana. Miyasa dukanin zarge-zargenka zai ƙare akan Yah Abdallah? Kana kishi da shi ba shike nufin komai ka yaya ka aza a kansaba”.
Sosai zantukan Aymah suka zafi zuciyar Yoohan, dan gani yake matar tasa tana goyen bayan tsohon saurayin natane kawai. Sai dai kuma uffan baice akan hakanba, yama ɗauke kansa daga gareta kawai.
Karan farko little bee ta saki murmushi tana kallonsu. Sai kuma ta taɓe baki da faɗin, “Wannan faɗane da ya shafeku a gidanku Mrs and Mr”.
Hararta Yoohan yayi, dan dama tunba yauba yana jin haushin yanda take zaman yimasa kallon ƙurilla a fakaice. Yana nuna bai gani bane kawai saboda kunyar iyayenta.
“A'a bar hararata malami, ni yanzu saina sassafa ka a gaban sahibar taka babu ruwana”.
“Ashe kuwa mijinki ma zai sassafu a hannuna tare da wannan miskilar fuskar taki mai ƙinyima mutane dariya”.
Harara itama little ta zuba masa tana tsuke fuska. “Oh kace dama kullum cikin takaicina kake bana maka murmushi, to ƙwalelen kare da hantar kura”.
Baki Yoohan ɗin ya taɓe da ɗauke kansa gefe yana cije lip. Dan saiya saita yarinyarnan akan layi kafin a gama case ɗin nan. shi babu ruwansa da wani ƴar-sandancin ta ehe. (Kuji ƙarfin hali irin na Yoohan. Da alama mafa little bee ɗin zata bashi shekara ɗaya a duniya, amma wai yarinya😂lol)
Babu wanda drama ɗintasu baisa dariyaba. Sai Jay da Bily basu dara ɗinba a fili sai a zuciya. Sundaita kallonsu cike da nazarin suɓutar harsunan nasu.
Kai jay ya girgiza kawai yana katse little dake son ƙara magana. “Kunga ku aje wannan shirmen naku sai kun fita can sai kuyi, idan kunso ku sassafa kawunan naku munada likita a kusa da zai duba ku. Yanzu dai Yoohan dole a yau ɗin nan Nu'aymah ta wuce kano. Dan aikin nan banason ya shige satin nan bamu kammalashi ba. Maganar Abdallah kuwa na tabbatar jin Nu'aymah na Nigeria zaizo shima koda a ɓoyen daya saba ne. Yanzu zan baza jami'ai da zasu fara bibiyar lamarin motsin kowa na gidan idan ya fito. Shima Nasir ina buƙatar a jawomin hankalinsa yazo kano. Babu sanya a aikinmu, duk wanda mukaci karo da rashin gaskiyarsa zamu kamasane mu tuhumesa kamar Rabi. Za kuma mu maida Rabi itama dan wayarta zata taimaka mana sosai wajen zaƙulo abubuwa”.
Cike da gamsuwa kowa ya amsa masa. Duk da kuwa Yoohan dai da alama baiso yin nisa da matarsaba. Amma ya fahimci hakan zai taimakesa gameda ƙudirin papa kuma a kanta. duk da kuwa a kanon ma wasu kurayen zata tarar. amma gara can akwai jami'ai masu sanya ido a lamarinta.
________★
Koda su Aymah suka dawo gida bata ga Blessing ba. Hakama Madam Chioma da papa da alama basa gidan ma. Yara kawai suka tarar da Mama debora. Joy ta wuce makaranta, Miracle kuwa mama debora ke basu labarin wai ta haɗa kayanta ta koma gida.
Ko a jikin Yoohan. Aymah kuwa yar dariyar shaƙiyanci tayi abinta ta wuce sama cike da tunanin ina Blessing ta shiga. Ɗakinta ta nufa direct, ta fara zame kayanta zuciyarta taf damuwa akan maganar hoton nan. Agogonta data cire ne ya faɗi ƙasa. ta ɗan matsa baya tana dubawa ta tillesa da ƙafa yay ƙarƙashin gado. Abin ya bata haushi, dan harta barsa akan yayta zama sai kuma taji tanason ɗakko kayanta dan Yoohan ya batashi matsayin ƙyauta a ranar da suka cika shekara ɗaya da aure. Fita tai ta ɗakko mopping stick dan Yoohan bai shigoba har yanzu yanacan tare da mama debora. Durƙusawa tai gaban gadon batare da damuwa da cikin dake gabantaba saboda wauta. Ta kunna fitilar wayarta ta haska. Da ƙyar ta iya hango agogon ta saka mopping stick ɗinnan ta turosa a hankali. Sai da yazo dab da ita ta fahimci harda wani abu take jawowa. Hannu ta miƙa danta jawosu duka ta kasa. Dole ta sake zungurowa da iccen mofa ɗin sannan suka fito. Jikinta har rawa yake wajen fara ɗaukar envelope ɗin ta buɗe. Tai wani irin waro ido na al'ajabi da mamaki. Batama san sanda ta ƙwaƙume hoton a ƙirjiba saboda murna. Jin an taɓa ƙofar za'a buɗe tai saurin sakin hoton ƙasa, kafin Yoohan daya shigo ya ƙaraso ta tura hoton ciki yanda bazai ganiba.
Duk da ta masa alamun rashin gaskiya sai bai nuna yama fahimcetaba. Yay baya da fiɗin, “Oh ashe kina nan, bara na watsa ruwa saiki shirya kema zuwa biyar na yamma zamu wuce kano. Amma mi kikeyi ma a durƙushe anan? Bayan kinsan bake kaɗai bace?”.
Miƙewa tai tana nuna masa agogon data ɗakko. “Kaga abinda na yadda nan na ɗakko”.
“Ki kulafa, dan na fahimci har yanzu wautanki na nan”.
Baki ta kumbura da iska batare datace masa komaiba. Shima sai ya juya abinsa ya fice kawai ya barta batare daya sake maganaba. Sai dai bai rufe ƙofaba. Da wannan damar ya samu zarafin laɓewa kozaiga mitakeyi. Aiko tana ganin ya fita ta sake duƙawa ta ɗakko hoton tana ambaton ‘Alhmdllh ya ALLAH. Da banga hoton nanba da bazan taɓa yafema duk wanda ya ɗaukesaba. Dolene nasan wacece wannan mai kama da mijina ɗin insha ALLAHU’.
Dukkan maganganun Aymah a cikin kunnen Yoohan ne. Hakan yasa zancen tsaya masa a rai tare da son jin ganin hoton nan shima. Yayi kamar zai dawo sai kuma ya fasa. Akan idonsa ta maida hoton a Wadrobe. Tafiya yay ɗakinsa tunda yaga inda ta ajiye. Sai dai kamar tasan yana kallonta. Yana barin wajen ta ɗauke hoton ta sakashi a ƴar jikkar data haɗa kayan tafiya kano wai dan kar wani ya sake shigo ya sace mata. Tana shiga wanka Yoohan ya dawo duba hoton. Sai dai kuma komai kama da shi bai ganima. sai ma kamashi da Aymah taso yi ALLAH dai ya taimakesa ya gudu.
Haka suka kammala shirin wucewa kano mamakin atsabibancin Aymah na damun Yoohan, shi ganima yake ta gansa shiyyasa ta canjama hoton waje.
Itako Aymah ranta fal baƙin cikin rashin ganin Blessing da Yoohan yasa tabar gidan har sai sun wuce dan bayason ta sanamar Nu'aymah abinda ya faru tsakaninsa da Momynsa.
*_KANO TA DABO_*
Ƙarfe bakwai dai-dai jirgin su Aymah ya sauka a kano. Batare da sanin kowa daga ahalintaba har su baba malam. Sai da Yoohan yasa suka fara biyawa sukai shopping na tsarabar da zata kaimusu sannan suka wuce gidan.
Ganin Aymah da Yoohan ya saka mai gadi buɗe musu gate mai taxi ya shiga har ciki. Nu'aymah zata fita da kwakwazo Yoohan ya riƙota yana girgiza mata kai. “Please kibi a hankali, a ganinama ba gara ki shige babu wanda ya san da zuwanki ba da safe sai kiyi musu surprise”.
Baki ta ɗan tura gaba. Sai kuma tai saurin sakin dariya da cewa, “Yes Yah Yoohan kayi gaskiya kuma”.
Murmushi yay mata da bata sumba a gefen kumatu. Daga haka suka fito a motar. Gidan shiru kowa yana a sashensa, hakan yasa Yoohan taya maigadi kaima Aymah kayanta bakin ƙofa. Sannan ya turata ciki ya sulale ya koma taxi ɗin suka fice. Dan hotel yake son guduwa kafin baba malam su fito massallaci su ritsashi.
Umm na zaune a bedroom tana karatu da jiran lokacin sallar isha'i sai ji kawai tai an rungumeta. A firgice ta juyo dan harga ALLAH ta tsorata. Ta waro idanu sabida mamakin ganin wadda batayi zatoba.
“Nu'aymah wai kece da gaske?”.
Kukan murnar ganin Umm ɗinta ta saki tana faɗin, “Nice Ummna, I miss you so much”.
Rungumeta Umm tayi da ƙyau a jikinta itama ƙwalla na cika mata idanu. Kai ɗa dabanne gaskiya. Sanin ba ita kaɗai bace yasa Umm tadata daga durƙuson da tayi a ƙasa ta zaunar da ita a bakin gado. Gaba ɗaya Aymah sai kuma taji kunyar Umm ta mamayeta, sai ta duƙar da kai ƙasa tana ƙara lulluɓe cikinta da gyale. Dariya abin ya bama Umm sosai. Sai dai bataiba. Saima tambayarta tai ina mijin nata?.
Kan Aymah a ƙasa tace waje ta barsa ita dai suna kwaso kaya shi da maigadi. Jin haka yasa Umm fita ta leƙa. Sai dai babu Yoohan babu dalilinsa sai maigadi kawai dake shigo da kayan ɗan barandar falonsu. Shine ke sanar mata Yoohan ɗin ya juya tare da mai taxi akan da safe zai dawo insha ALLAH.
Kai kawai Umm ta girgiza ta koma ciki, inda ta iske Aymah ta fito daga toilet da alama fitsari tayo. Cike da kulawa tace, “Kinji mijin naki ya tafi wai zai dawo da safe. Dama kunyi dashi hakan?”.
“A'a wlhy Umm, ni kawai yace na shigo zaije massallaci ne”. Tai maganar cikin ɓata fuska. Murmushi kawai Umm tayi ita dai, tace, “To kiyi wanka kawai sai na samo miki abinda zakici ke tunda shi ya gudu. Cike da kunyar Umm ɗin data aro ta yafama kanta ta amsa da to. Daga haka ta koma toilet ɗin danyin wanka.
Babu wanda Umm ta sanarma da zuwan Nu'aymah a gidan sai hajjo. Sai ko Muhammad daya dawo massalaci ya ganta a bazata. Baba malam ma sai da ya sallami ɗalibansa ya shigo yaci karo da ita a falo zaune ita da Hajjo da Umm da Muhammad dake liƙe da ita.
Tuni Nu'aymah ta manta da kunya, ta miƙe da sassarfa ta nufi Abbanta dake kallonta cike da kewa da so da ƙaunarta. Gabanta tai niyyar durƙusawa ya riƙota yana faɗin, “A'a mamana keda ke fama da kanki. Irin wannan zuwa haka na bazata”.
Hannunta yaja ya maida a kujera sannan shima ya zauna. Kanta a ƙasa ta shiga gaisheshi cike da kewa. Shiko yana amsawa da kulawa. Abakin Umm yaji cewar Yoohan ya gudu. Dariya kawai yayi dan ya fahimci kunya Yoohan ɗin keji da alama.
Haka sukayi murnarsu su huɗu kawai. Ganin dare ya farayi Hajjo taje sashenta danta kwanta. Aymah kuwa a ɗakin Umm zata kwana tare da Umm ɗinta data bar baba malam shi kaɗai.
Aiko maimakon barci sai suka buɗe sabon babin hira ita da Umm ɗin, sai da suka kusan kai asuba sannan barcin ya kwashi Aymah, daga nan itama Umm tayi.
__________★
Washe gari kam a bazata kowa yaga Nu'aymah a gidan. Kafin kace mi sun rikice da murna da hayaniya. Tun Aymah na ƙunshe-ƙunshen ciki harta saki jikinta ta shige cikin ƴan uwanta anashan shafta. Zuwa tashin hantsi kuwa sai ga Hajarah tazo gidan, dan ita dama tasan da zuwan nata. Rungume juna sukai cike da farin ciki. Yanda suka nuna ɗin har mamaki ya bama kowa. Dan gaba ɗaya salon shaƙuwar Adawiya da Nu'aymah ne ya koma kan Hajarah a yanzu.
A ranar da yamma suma ƴan Abuja suka iso. Ganin Nu'aymah kuma ya matuƙar basu mamaki dansu da suke Abujan ko a labari basusan da zuwan nataba. Har Momy ma sai da ta kasa haƙuri tai complain ɗin cewar Yoohan bai ƙyautaba. Suna matsayin iyayen Nu'aymah amma yazo da ita har Abuja bai fara kaita canba sai dai suzo su ganta anan tsulum.
Daga karshe dai Yoohan ɗinne da yazo gidan ya kare kansa akan wannan tuhuma. Dan Aymah bata iya cewa komaiba tunda itama tunanin zuwa can ɗin baizo mataba. Zumuɗinta kawai azo kano.
Ya bama su baba malam haƙuri akan rashin tsayawarsa jiya. Acewarsa aikin gaggawa ne ya samesa shiyyasa bai tsayaba. Duk sun masa uziri akan haka. Sannan suka ɗora da godiya akan hidimarsa ga gidan marayunsu daketa ƙara nunkuwa a koda yaushe. Akan bikin nanma kawai da za'ai ba ƙaramin hidima yayiba.
Washe gari baƙi suka fara cika gidan, ƴan katsina, ƴan lagos da sauransu, kowa kuwa yana sake yaba yanda Aymah ta ƙara girma da canjawa a cikin shekara ɗaya kacal. Gashi daga gani ansan ta samu lafiya yanzu. Sai dai fatan ALLAH ya sa ta sauka lafiya kuma.
Da yamma sukaje can orphanage akai walima, anan ta haɗu da sauran yayunta su Kubrah. Tayi mamakin ganin yanda Aunty Kubrah ɗin dukta lalace. Harta kasa haƙuri ta tambayi aunty Hajarah.
Cike da damuwa Hajarah tace, “Humm Aymah ke dai ALLAH ya ƙyauta, zaman natane babu daɗi daga ita har mijin da kishiyar. Kwanaki ai kusan watanta biyu a Lagos wajen Abbah Musbahu. Sunyi faɗa ya daketa shine taje can”.
Kasa magana aymah tayi saboda damuwa. Kodai babu komai Kubrah ƴar uwartace duk da a yauma ta nuna har yanzu ba sonta takeba.
Duk wannan hidima da akeyi kuwa su Aymah zagaye suke da yaran Jay ta ko ina. Motsin kowa akan idonsu yake faruwa. Tun daga orphanage har cikin gidansu.
Washe gari juma'a aka ɗaura auren amare ashirin da takwas maza da mata. Kowa ya kalli su baba malam yasan suna cikin farin ciki. Sai dai ai fatan ALLAH ya basu ladan hidimarsu ga marayun ALLAH babu gajiyawa.
An miƙa amare ɗakunansu, daga haka baƙi suka fara raguwa sai na jiki kawai aka bari. Kamar yanda Jay ya samu tattaunawa da baba malam a ranar ɗaurin aure a yau suka yanke hukunci bisa shirinsu. Duk da kuwa da ƙyar baba malam ɗin ya yarda da buƙatar Yoohan, Jay, Omar ɗin. Dan basu ɓoye masa komaiba game da shirin nasu gudun kar a samu matsala.
Tun a yammacin ranar baba malam ya fara takalar Umm da batun mallakama Nu'aymah wasu kaddarorinsa dan yasan lallai mai musu laɓe na tare da su saboda tuna Nu'aymah tazo garin ya fahimci mai laɓen ya ƙara ƙaimi wajen yimusu. Ta riga tasan shirinsu, itama sai ta biye masa. Sai dai zancen bai tsahoba suka barshi akan zasu ƙarasa da safe dan lokaci baba malam nada uziri..........✍
ZAFAFA BIYAR 2021
Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
(Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗
Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗
Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗
Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋
Duka akan farashi mai rahusar gaske.
Kamar haka👇🏻💃🏻
Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇
ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇
0903 234 5899
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇
09033181070
💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍
ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
[7/6, 9:38 AM] +234 913 412 2711: *_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.
No. 73
.............A yau kam su Nu'aymah da duk wanda yasan da wannan shirin sun tashi a shirye tsaf bisa yaƙinin tarkon da suka ɗana ya ɗanu. Kasancewar sanyi da akeyi duk sauran jama'ar gidan da ƴan biki suna can a sassan gidan a maƙale, duk da madai ƴan bikin da suka rage duk na jikine babu bare. Babu kowa a tsakar gidan sai yaran Jay dake ɓoɓɓoye.
Yau kam Jay ya shiga har falon baba malam tare da lauyan malam mahaifin su baba malam a zuwan zasu tattauna akan kaddaririn baba malam ɗin. Acan kuma ta waje little bee ce da wasu jami'a a harabar gidan a mabanbanta wajaje duk da Jay yasan akwai camaras ɗin da Afrah ta saka masa a wancan zaman. Yafi buƙatar gani ga ido ga kowa kafin ya bankaɗa sirrikan dake a cctv ɗin. An kira Aymah da Yoohan falon, sai su Abban Abdallah da hajjo data san komai itama. Sai Omar da yazo matsayin lauyan Nu'aymah shima.
Bayan buɗe taro da addu'a baba malam ya fara da nasiha a garesu duk dai a cikin salon tarkonsu, dan a zahiri fa babu wani maganar mallakama Nu'aymah kaddarorinsa da yakeyi. Shirine kawai irin nasu Jay.
A gefe kuwa idanun su Yoohan gaba ɗaya na'a Windows ɗin falon a kaikaice. Baba malam kuwa na cikin nasiha sai ga abinda suke jira ya bayyana. Kallon juna sukai shi da Jay dasu Yoohan sukayi murmushi. Daga haka ya cigaba da bayaninsa hankali kwance.
Acan waje kuwa su Little bee na mammaƙale a maɓoyarsu sai ga mutum sanye cikin dogon hijjab har ƙasa da niƙab ya fito daga tacan bayan gidan yanda babu mai iya fahimtar daga ainahin sashen da aka fito. Basu da tabbacin mace ce ko namiji, dan komai an rufe ba'a gani.
A yanda mai laɓe ke tafiya da dabaru zaka san cewar lallai an ƙware, sannan aikine da akeyi tunba yanzuba. Cikin salon iya aiki Little bee taima abokan aikinta wani salo da yatsun hannunsa suka bada ɗass!! Sau ɗaya. A take duk suka ƙara shiryawa dan suma dai suna biye da mai laɓe akan idanunsu.
Sai da suka tabbatar mai laɓe ya isa dai-dai sashen Malam marigayi alamar dai ɗan gidanne, tunda har ansan a ina su baba malam zasuyu taron nasu aiko sai wanda yasan gidan. Kamar yanda mai laɓe ya saba a koda yaushe ya isa jikin Window. Wani siririn abu ya saƙa a tsakanin glasess ɗin Window ɗin da alama na ɗaukar magana ne. Dan yana gama turashi ya kai hannu ya taɓa kunnensa alamar tabbatar da daidaitar komai. Ƙaramin tsaki akaja jin Nasihar da baba malam ya fara dan ba ita ake buƙataba a yanzu. Jin baba malam zai fara jawabinsa mai laɓe ya ƙara nutsuwa da maida hankalinsa ga window ɗin domin saurare..
Da wannan damar su Little bee sukasamu isowa wajen cike da ƙwarewar aiki suka toshe gaba da baya na ɗan siririn lungun bayan ɗakin malam marigayi. Ƙarar saƙon daya shigo wayar Little bee daga Jay ne ya fargar da mai laɓe ya juyo da sauri. Sai kawai ganinsa yayi zagaye da mutanen da baisan ta ina suka ɓullo ba.
Tashin hankali ba'a saka maka rana. Wannan shine ɓoyayyar kalma a zuciya da bakin mai laɓe duk da bai fito ya furta manaba a zahiri. Dan kuwa dai gabas da yamma kudu da arewa babu wajen guduwa. Katanga a bangon gabas. Ginin sashen malam a bangon yamma. Little bee da jami'ai uku a bangon kudu duk sun nunasa/ta da bindiga. Dawood da jami'ai uku shima a bangon arewa duk sun nunata/sa da bindiga nanma.
Wannan itace kwana casa'in da tara ta barawo ɗaya tak ta mai kaya. Little bee ta ciwo wayarta da hannu ɗaya a aljihu ɗayan kuma riƙe da bindigar data nuna mai laɓe. Kiran Jay tayi a waya. Yana ɗagawa tace, “Sir! Aikinmu ya kammala zaku iya fitowa”.
“Woow!” Jay ya faɗa yana miƙewa idonsa akan su baba Malam. Takawa yay jikin windown da yake hango inuwoyinsu ya zuge gilas ɗin tare da net. Abinda mai laɓe ya saƙala ya faɗo. duƙawa yay ya ɗauka yana jujjuya shi a hannunsa kafin ya kalli su baba malam da suma duk shi suke kallo.
“Malam zama ya ƙare ai, suspect ɗinmu yazo hannu zamu iya zagayawa”.
Harga ALLAH sai da gaban baba malam da Umm ya faɗi. Hakama Aymah duk sai taji tsoro kuma. Su Abba Musbahu da basusan mi akeyiba suka shiga kallonsu da tuhuma. Ko a jikin Yoohan da Umar. Dan sunema farkon ficewa a falon.
Baba malam dake kallon su Abban Abdallah yace, “Kuyi haƙuri wannan itace kawai mafita a garemu gudun kar wataran a kai ga rasa rai bisa makircin da bamusan wake ƙullasa ba”. Daga haka yay gaba ya barsu da kallon kallo ma juna sai dai ganin kowa ya fice suma sukabi bayansu jiki a sabule.
Ganin duk sun iso Little bee ta dakama mai laɓe tsawa da faɗin, “Cire Niƙaf”. Ko motsi ba'ayiba. Sai dai yanayin tsayuwar ya tabbatar da koma wanene a tsorace yake kuma cikin ƙololuwar tashin hankali da firgici.
“Inada cikaken dama nayin harbi, hakan na nufin bullet ɗin zasu iya fita a cikin bindigarnan zuwa jikinki/jikinka a koda yaushe. Zan irga iku kawai bisa lasisin dama a gareki ko a gareka. *_Ɗaya! Biyu! Uku!!”_* ta fita daga bakin Little bee tare da bullet ɗinta zuwa ƙafar mai laɓe da ko motsi baiyiba balle ya nuna kota nuna zata cire nikab din da aka bada umarni.
A take ƙarar muryar mace ta karaɗe gidan saboda azaba shigar bullet. Ƙasa ta durƙushe jiki na rawa. Da wannan damar Little bee ta ƙarasa gareta tasa hannu ta fisge niƙab ɗin ta jefar gefe. Baba malam da Umm da sauri suka kauda kawunansu gefe da tsananin fargabar tsoron ganin koma wanene. Sai da Nu'aymah ta furta,
“Illalillahi wa'inna ilaihirraji'un Addah!! Kece dama?!!!”.
Sannan su Umm suka juyo a firgice. A take wajen gaba ɗaya ya ɗauki salati. Dan duk jama'ar gidan kururuwar ihun Addah da Little bee ta harba dama duk ya fito dasu a hautsine.
Cikin girgiza kai hawaye na sakkoma Umm a guje tace, “Inaa bazai yuwuba. Addah ki sanar musu ba abinda suke zargi bane ya kawoki nan. Dan ALLAH ki tabbatar musu domin bamu kariya kema kika zo nan. Ki tabbatar musu bake bace kike laɓen nan dama can dan ALLAH, kicemin yau kika farayi......”
“Bata da bakin baki waɗan nan amsoshin domin wanke kanta Umm-Muhammad. Domin kuwa duk saɓaninsu da baki eson ji daga bakinta sune gaskiyar amsoshin naki da ma kowa dake anan wajen”.
Bily dake kusa da Jay tsaye ta bama Umm amsa kanta tsaye.
“Karkice dani haka Maman Awwab. Dan ALLAH karkice haka. Wannanfa Fauza ce, wadda muka tashi tare tun ƙuruciya tamkar uwa ɗaya uba ɗaya ta haifomu. Ban taɓa ɓoye mata sirrinaba, itama bata taɓa ɓoyemin nata ba. Tare muke raba farin ciki, sannan mu raba kuka tare idan ya samemu.....”
Murmushi Bily tayi da takawa a hankali zuwa gaban Addah daketa faman magowar azabar ƙafarta dake zubda jini. Ta nunata tana mai kallon Umm ɗin, “Tabbas a zahiri haka take a gareki Umm-Muhammad. Amma a baɗini itace babbar maƙiyyarku. Idan kuna buƙatar tabbatarwa mu a shirye muke wajen nuna shaidar gani da ido a gareku dan duk mun tanajesu dama”. Ta ƙare maganar tana duban su baba malam da alamu ya nuna tamkar duk sunyi sumar tsaye ne har yaran Addah da duk suma suna a wajen.
Daga haka Jay ya bama Yoohan da Omar damar cire bullet ɗin jikin Addah. Cike da ɗacin murya Yoohan ya dubi Jay ɗin idanunsa jazur. “Uncle ka gafarceni, hannuna bazai taɓa iya aikata jinƙai ga maci amana ba”. Daga haka ya kama hannun Nu'aymah da jikinta ke karkarwa suka bar wajen.
Murmushi kawai Jay yayi. Baba malam zaiyi magana Jay yace, “Karka takura masa Malam. Umar Please ka cire mata sai mu wuce da ita. Malam sai ku samemu a statlon ɗinmu nan kano mu ƙarasa maganar”.
Da sauri baba malam yace, “A'a Jawaad ina neman alfarma komi zai faru muyisa anan cikin gidan domin rufin asirinmu, wannan itace alfarmar da zan nema a gareku”.
Ɗan jimm Jay yayi, sai kuma ya kaɗa kansa alamar karɓawar alfarmar baba malam ɗin.
Badan Umar yaso ba ya amince zai cire. Dan haka aka ɗakko Adda daga lungun zuwa sashen Malam. Gaba ɗaya yaran sa'an su Muhammad zuwa kansu Adawiya ba'a barsu sun shigaba. Duk da kuka da Adawiya keyi iyakar ƙarfinta wanda babu wanda yasan dalilinsa. Su Hajarah da sauran yayunta na ma'auri duk suna gidajensu basusan abinda akeyiba. Sai malam ƙarami kawai da sauran ƙannensu. Shiko gaba ɗaya da alama ma jinsa da ganinsa sun gushe dan bai iya motsawa a lungunba har kowa ya fice. Hakama Abba Mustapha saida Hajjo ta kama hannunsa da kanta saboda tsabar firgici.
★★★
Bayan azabar cire bullet da Addah ta gama sha Omar yay mata allurar rage raɗaɗi. Umm dake kuka har yanzu ta sake duban Addah. “Fauza dan ALLAH ina roƙonki a karo na ƙarshe ki ƙaryata tuhumar da ake miki. Ki tabbatar musu da kawai yau ƙaddara ta kawoki amma ba ke bace. Har abada bana fatan kunnuwana da zuciyata suji saɓanin tunaninsu a kanki Fauza.......”
Shiru Addah batai ko motsiba, kanta a ƙasa kuma taƙi kallon kowa. Gyaran murya Jawaad yayi da gyara zama. “Hajiya karki wahal damu anan, dan alfarma ki ke ci, badan darajar malam ba da zamu wuce dake station ne ki mana bayani ta duk hanyar da mukaso bi da ke. Kar kiyi tunanin ɓoye mana komai dan a tafin hanunmu kike, duk wanda ke cikin labarinki sai da na gurfanar da shi a gabana kafin ki ganni anan, na zaɓi bin komai mataki-mataki ne saboda sauƙaƙa firgici a zuciyar waɗanda kikema cin dunduniya. Nasan kinsan Hamisu ai gashi a gabanki tsaye”.
Da sauri Addah ta ɗago ta kalli inda Jay ke nuna mata. Kallon ido cikin ido sukaima juna kuwa ita da Hamisu. ya ko zuba mata mummunan kallo. Da sauri maida kallonta ga Jay. Kai shima ya jinjina mata fuska a ɗaure. “Bayan Hamisu akwai ƴarki Kubrah ko, sannan akwai......”
Da sauri ta ɗaga masa hannu, sai kuma ta fara tari, gefen ɗan kwalinta tasa ta tare bakinta sai ga jini na zuba. Babu wanda bai mata kallon tsoro da firgici ba a falon. Ta goge mabinta saboda tsagaitawar tarin sannan ta kalli kowa dake falon tana Murmushi mai ciwo a karon farko. Ta kalli ƙafarta dake naɗe da bandage hawaye na ziraro mata. Dan har yanzu tanajin raɗaɗin azabar shigar bullet a karon farko na rayuwarta. Kallon baba malam tayi ta sake sakin murmushi sannan ta maida akan Umm dake a gabanta zaune.
“Ko babu ƙarfin iko hukuma dama lokaci yayi da Firdausi! Zata san wacece Fauza a gareta. Dan tun bayan auren Nu'aymah wannan ranar dama nakewa zaman jiran tazo a gareni, dan nasan tana cikin ranakun da ko naso koban soba sai sun riskeni a duniya ko a lahira, musamman daya kasance gajerun kwanaki suka ragemin a duniya. Wannan Fauzar dake gabanku ba Fauza bace ta shekarun baya mai lafiya, hatsabibiya, mai aiki da zuciya kawai bada tunaniba, mai son kanta, mai aiki da huɗubar shaiɗan. Wannan Fauzar maƙasƙanciyace a gabanku yanzu, mai rauni, mai ɗauke da ciwon zuciya da ciwon kansar jini (blood cancer), wadda likita ya tabbatarma watanni kaɗanne suka rage mata a duniya. Wannan Fauzar mai dana sani ce da nadama da yin kaico akan ayyukan data tafka batare daku kun saniba saboda iya SARAN ƁOYE”.
Tarine ya kuma sarƙeta da kuka. Nanma tanayi jini na fita, saida ta tsagaita sannan ta sake dubansu. “Da wahala shara'ar alƙalin duniya ta iya dacewa da laifukan Fauza, shara'ar UBANGIJI datafi cancanta dani ta fara bayyana a gareni tun daga randa likitanci suka sanarmin sakamakon abinda nakeji a jikina. Amma lallai halina dolene yaje kunnunwan mai saurare ko zai zama izina ga masu irin halin suji tsoron ALLAH su canja kafin lokaci ya ƙure musu”.
“Firdausi! Da gaske ni Addah na soki so na gaskiya a zamanin ƙuruciyarmu. Duk da ko a wancan lokacin duk randa kika samu abinda ni nafi cancanta da samunsa inajin zafinki a raina. Musamman idan nai la'akari dana fiki komai a rayuwa. Ni ƴar gatace ko a gidanmu, duk wani jin daɗi da yaro kan tashi ya samu daga iyaye na samesa. Mahaifina yafi naki komai a rayuwa. Hakama mahaifiyata tafi taki. Hasalima da yawan lokuta ƴan gidanku kunaci ne daga alfarmar iyayena. Sai dai kash duk da wannan gatan namu da tarin alfarma kin fini basirar karatu, bama ke kaɗaiba duk ƴan gidanku ALLAH ya basu wannan baiwar, gashi duk kun fimu ƙyau, sannan da wahala ku zauna da mutane basu soku ba. Dan yayyenki ma sunsha ciwo nasarorin dake sa yayuna jin zafinsu, sai dai mahaifiyarmu kan ƙwaɓemu akan hakan. Nasararki a kaina bata taɓa kaini ga ƙololuwar jin zafinkiba sai a randa Sheikh Soorajidden yazo har gidanmu akan neman aurenki”.
Ta share hawaye masu zafi dake gangaro mata har yanzu sannan ta cigaba da faɗin,
“Hakan ta faru dalilin soyayyarsa da taimin shigar sauri cikin zuciya tun a ranar kammala karatunmu. Idan baki mantaba tun a wajen bakina bai hutaba da zance a kansa har kika nuna ƙosawarki akan hakan. Mun dawo gida zuciyata na ɗunbin begensa, sai dai a randa na buɗi ido na gansa a gidanmu sai labari ya canja salo. Ke! ke! ke!! Firdausi! kin sake yanke igiyar nasarata kamar yanda kika saba a koda yaushe”.
Tai maganar da matsanancin kukan da har ya hanata kasa cigaba da magana sai da tai tari mai tsaho. Falon kansa yayi tsit ko motsi kowa ya kasa saboda shock. Da ƙyar ta tsagaita kukanta da tarin sannan ta cigaba.
“Naji zafinki a wannan ranar zafin da idan aka bani makami zan iya halakaki. Nayi kuka harna rasa hawayen zubarwa. Amma daga ƙarshe sai nayi haƙuri bisa ga shawara da nasihar da babbar yayarmu ta min, a lokacin sai naji na haƙura na barmiki, duk da dai son nasa na nan maƙale a raina. A haka aka kammala komai na maganar aurenku ni bani da wani tsayayyen saryima. Har lokacin biki yayi mukasha bikinku. ALLAH ya sani ban taɓa cin karo da rana mai ciwo da raɗaɗi ba irin ranar aurenku. Dan aranar na gama yanke hukuncin dolene na shigo gidanki matsayin kishiyarki. Amma sai kash. Ƙaddara ta riga fata, dan kuwa haɗuwata da Mustapha sai ta kasance almakashin daya datse wannan zaren a karo na biyu. Ya nuna yana sona, amma ban amsa masaba a ranar, shi kuma ya zata kunyace ta sani ƙin amsawar, dan haka yay amfani da wannan damar yayma rayuwata kutse ta bayan gidan adalilin neman aurena da Sooraj yaje yayima ƙaninsa a gidanmu tamkar yanda yayima kainsa. Babana kuma babu wani tsayawa ja'in-ja ya bashi. Na sake shiga ruɗani a karo na biyu, amma sai yayata dai ta sake ɗorani akan mizanin hankali da nasiha kamar wancan karon. Ta kuma tabbatarmin Mustapha shine mijina dama ba Sooraj ba, tanada yaƙinin kuma shine zai zama mafi alkairi a gareni insha ALLAHU. A wannan karonma taci nasara. Dan duk da babu son Mustapha a raina na aminta zan auresa kodan darajar jini da suka haɗa da Sooraj, sannan a fuska ma suna kammani da juna”.
Ta share hawayenta tana murmushi da kallon Umm.
“Firdausi! Shigowata gidan nan shine ya sake canzama zuciyata salo a kanki. Dan tun a yanayin taron aurena da Mustapha na fahimci a wannan gaɓarma kin sake min tsere. Ban sake tabbatarwa ba sai da na tabbata ɗaya daga cin wannan ahalin. Zamantakewar ki da Sooraj tana ɗaya daga abinda ya dagula min tunani. A zahiri mutane ɗauka suke tsoron Sooraj kikeyi, amma wanda zai ganku a sashenku kaɗaine zai goge wannan tunanin a ransa saboda soyayya da tattalin da kike samu daga garesa. Sannan kasancewarsa babban ɗa a gidannan duk wata daraja ta matar gida kin kwashe a sama da tamu. Wannan yasa ita kanta Momyn Abdallah kejin zafinki ganin anan kikazo kika sameta. Abinda ya ɗan sakamin sassauci a kanki lokacin haihuwa dana rigaki yi kuma namiji, har takai sai da na jera huɗu sannan kika samu ciki. Maganar gaskiya bazan ɓoye mikiba naji matuƙar jin kishi akan samun cikinki duk da kuwa inada ƴaƴa har huɗu a lokacin. Dan idan ina ƙaunar mutuwata to ina ƙaunar buɗar ido naganki da wani cigaba daya ɗara nawa a rayuwa, dan na tsani cikin nan naki tun yana ɗan tayinsa. Duk da ban taɓa tunanin cutar dake ba adalilin cikin nan zuciyata ta fara rayamin hakan, dan kullum huɗuba takemin na ɓarar da cikin kawai kowa ya huta. Sai dai ina shirin aikata hakan a gareki Sooraj ya ɗaukeki kuka wuce saudia, nayi baƙin ciki nayi takaici irin wanda bazai misaltuba. Gashi baku dawoba sai gab da zaki haihu. Koda kuka dawo ban fasa aiwatar da ƙudirina akan cikinki ba, sai dai babu wata makamar yin hakan dana samu har ALLAH ya saukeki lafiya a wani dare. Hankalina ya tashi ganin kema da namiji kika fara, zuciyata ta sake bushewa da kangarewa akan na kashesa kawai tun yana jaririn.........”
Cikin ɗacin murya Baba malam ya katse Addah da cewar, “Fauza kenan kece kika kashe mana yaro?”.
Kuka Addah ta sake fashewa da shi kanta a ƙasa ta kasa kallonsu. Ga tari ya kuma sarƙeta har jini na fita guda-guda yanzun.
Ko batace komaiba sun fahimci shirunta na nufin haka ɗinne. A take gaba ɗaya falon suka ɗauki salati. Umm kam ido kawai ta tsurama Addah hawayenma sun tsaya cak. Hakama baba malam kallon ƙasa kawai yake ya gaza koda motsi. Abba Mustapha zai miƙe Hajjo ta hanashi, dan har yanzu ai ba'azo inda take buƙatar ba.
Jay ne ya katse shirun nata da faɗin, “Ke muke saurare”. Yay maganar yana kallon agogon hannunsa.
Da ƙyar Addah ta tsagaita kukanta ta cigaba da faɗin, “Na shaƙa masa maganine, irin wanda naso shaƙama Nu'aymah aka samu akasi Rabi mai aikinki ta kusa rutsani, dan a lokacin kin tafi wanka Nu'aymah kin barta ta dinga leƙata a ɗaki, ni kuma saina aiketa domin aiwatar da ƙudirina, sai akai rashin sa'a kafin na shaƙama yarinyar maganin Rabi ta shigo, motsin nufowarta bedroom. Wannan shine dalilin tsoratata na saketa a ƙasa kanta ya bugu. A take ta suma, ni kuma nai saurin ɓoyewa dan kar rabi ta ganni gakuma kema naji yanda kika rikice a toilet kina ƙoƙarin fitowa. Sai da ta fita da gudu tana ihun kiranki saboda rikicewar da tayi ni kuma na samu na fita a sashen, daga baya na shigo cikin matan gidan muka shiga jajen yaya akai a tare. Kowa yama zata Nu'aymah ta rasu, sai dai hajjo ta matsa a kira likita. Zuwansane ya tabbatar mana da suma tayi, ba haka nasoba, amma lokacin da aka dawo da ita daga asibiti da tabbacin sanadin faɗuwar tata ta samu ciwo a ƙwaƙwalwa sai naji daɗi a raina saboda bushewar zuciya da huɗubar sheɗan”.
“Likita ya fara ɓusa zargin yaddota akai daga gado, kema kuma Firdausi kin tabbatarma kowa kina toilet kinji motsin shigowar mutum bedroom ɗinki, sai dai kin zata Rabi ce, sannan kuma kinji sanda yarinyar ta faɗi ƙasa ta bugu. hakan yasa aka tuhumi Rabi, amma kuma saita rantse da iya gaskiyarta ba ita bace dan nama aiketane ta dawo,, tana shigowa taji ƙarar Nu'aymah datai sau ɗaya kafin ta suma. Maigadi ne ya sake wanke Rabi a wajen kowa. Haka kawai na tsargi kaina akan karfa asirina ya tonu, dalilin da yasani saurin ɗaukar mataki kenan na saka malamin da ya bani abinda zan shaƙama yarinyar rufemin bakin kowa a gidan nan akama bar wani hasashe-hasashen son sanin yaya akai Nu'aymah ta faɗo a gadon?. Ban sake yunƙurin cutar da yarinyarba, dan a ganina ciwon data kamu da shi ya isa kai rayuwarta ƙarshe. Sai dai na saka an daɗe bakin mahaifarki yanda bazaki sake haihuwa ba. ALLAH kuwa ya amincemin baki sake samun ciki ba sai bayan haihuwar Nu'aymah da kusan shekaru biyar, hankalina ya sake tashi na nufi malamina. Saina iske ALLAH ya masa rasuwa. Lallai nayi gamo da tashin hankali na haƙiƙa a wannan lokacin, dan zan iya cemuku daga wannan lokacin ban sake samun malamin da yaymin aikin da yaci a kanku ba.......”
“Mtsoww!! Malami ko boka dai”. Abban Abdallah ya faɗa a fusasce.
Wani irin kallo Addah tai masa, sai kuma ta kwashe da dariya ta ɗauke kanta kawai. Hakan da tayi kuwa yaba kowa mamaki. Amma sai babu wanda yayi magana. Har shima Abban Abdallah ɗin bai sake cewa komaiba.
Addah ta cigaba da faɗin, “Tunda na fahimci aikin malami ya daina tasiri sai na koma laɓe da son zubar da cikinki, to ALLAH ya tabbatar Muhammad sai ya shaƙi iskar duniya sai gashi kin haihu lafiya duk da ba haka nasoba. ta wannan hanyar laɓe ne nakejin duk wani abinda ya shafeku, dan duk da amintarmu firdausi ke mutumce mai zurfin ciki. Nakan faɗa miki sirrikana kai tsaye ko kema zaki warwaremin naki babu shamaki. Amma sai da na fara muku laɓe na fahimci kina bala'i-bala'in rainan hankali. Dan babu wani sirrinki mai muhimmanci da kike sanarmin sai ƙananu kawai. Hakan yasa nima na ɗauki ɗammarar bi dake ta yanda kikazo min”.
Ta kai dubanta ga Abban Abdallah. Wanda a take mood ɗinsa ya canja ya wani zazzaro mata idanu kamar zai haɗiyeta da su. Murmushi tayi da ɗauke kanta ta cigaba da faɗin, “A dalilin son halaka Muhammad na haɗu da babban makirin daya ƙara faɗaɗa ƙwaƙwalwata akan ƙiyayyarki da zuri'arki. Dan ta sanadinsa ne wasan ya canja salo daga soyayyar Sooraj zuwa wani abun daban. Ba kowa nake nufiba sai Lurwan ga shinan”. Tai maganar tana nuna Abban Abdallah da tun fara maganar tata ya zabura zai miƙe a fusace amma Hajjo ta riƙoshi cikin fushi.
Babu wanda bai zaro ido ba a jama'ar falon. Abban Abdallah ya sake zabura yana ƙoƙarin ƙwace hanunsa daga hajjo. “K baƙar annamimiya, makira, azzaluma. dan ubanki sharrin naki da makirci yazo kainane kenan komai?”.
Dariya sosai Addah tayi tana kallonsa, tace, “Lurwanu ai ka fini iya makirci, dan kaine malamina a wannan fanin kuwa. Da farko ta hanyar malami kawai nake samun nasara akan Firdausi, amma haɗuwata da kai ya sani hutawa daga zuwa wajen kowanne irin malami, dan kai kafi malamin hatsabibanci ma. Yau ranace mai kama da ranar hissabi, yanda nasan cewar ayyukanmu bazasu ɓoyu ba a wannan rana dake jiranmu to ina tabbatar maka yau ɗin nanma tun a duniya zan fara fallasasu dan kowa ya yaji. Dan wlhy yanda duniya tasan waceceni a yau, ƴaƴana sukaji shukar danayi, mijina yaji, dolene kaima uwarka da yayanka da matarka da ƴaƴanka da sauran ƴan uwanka susan kai wanene a cikinsu”.
Sake zabura yay kanta kuwa da ƙarfin tuwo ya fisge hannunsa a cikin na hajjo, amma sai Dawood yay azamar shan gabansa da bindiga. “Ka kama girmanka, inba hakaba zan maka irin tabon dake a ƙafarta kaima. Ka nutsu ka riƙe sauran mutuncinka”.
Jikin Abban Abdallah rawa yakeyi sosai, dan bai taɓa kawowa a ransa tone-tonen Addah zai iso kansaba musamman da yasan irin gargaɗin da yay mata kafin ya yarda su fara aiki tare, da kuma kalaman datai amfani dasu a yau wajen shimfiɗa labarinta. Yayi zaton zata rufa asirinsa ne.
A hankali baba malam ya yunƙura ya miƙe hawaye na sakko masa akan fuska. Yasa babbar rigarsa ya share sannan ya dubi jama'ar falon. “Inaga dan ALLAH mubar maganarnan gaba ɗaya, wannan tone-tonen a ganina sam bashi da amfani. Sun aikata abinsu a ɓoye sai mu barsu kawai da nauyinsu suje can su ƙarta. Bana buƙatar jin abinda Rudwan ya aikata ku barni haka, n.......”
“Dolene kuwa kaji ɗan malam, dan haka koma ka zauna”. Hajjo tai maganar cike da bada umarni. Baya iya ƙetare maganar mahaifiyarsa. dan haka ya koma jagwab ya zauna yana mai dafe kansa da hannaye biyu saboda jirin dake kwasarsa.
Addah tai murmushi mai ciwo da cigaba da faɗin, “Lurwanu shiya canja tunanina daga fushin rasa masoyi zuwa na mallakar dukiya, dan huɗubarsace ta fahimtar dani cewa ina dukan taiki ne kawai ina barin jaki, haukana kawai nake akan nafi Firdausi ƴaƴa nafita nasara yanzun. sai dai ashe dukiyar da mijinta ya mallaka a cikin ƴan uwansa ta ninka wadda nawa mijin ke da shi sau fiye da bakwai. Kaso biyu na dukiyar gidan nan mallakarsace, kaso ɗaya ne na mazajenmu da Hajjo. Gaba ɗaya komai ya susuce min a lokacin nama nema rasa makamar tunani da hankalina. Amma sai ya dinga kwantarmin da hankali ta hanyar nunamin inhar zan taimakesa muyi aiki tare to lallai dukiyar baba malam zata koma ƙarƙashin ikonmu ne. Nace masa ta yaya kenan?. Ya bani tabbacin ta hanyar Abdallah. Tunda akwai shaƙuwa sosai tsakanin Nu'aymah da Abdallah hakan na nufin nangaba kaɗan soyayya zata iya bayyana a tsakani duk da ƙuruciyarsu. Dan bazaiyi wasaba wajen ɗora Abdallah akan matakin daya kamata game da Nu'aymah. Ɗari bisa ɗari na yarda da hakan a wancan lokacin. Saboda a yanda ya faɗaɗa min bayanansa na fahimci inba ta wannan hanyarba babu ta inda zamu mallaki wannan dukiyar. Wannan shine sanadin dunƙulewarmu waje guda ni da Lurwan muka fara aiki tare. Amma wlhy kullum hankalinmu cikin ƙara tashi yake gameda haɓaka da dukiyar Sooraj keyi abun tamkar roƙo. Shima kuma sake ɗaukaka yakeyi fiye da sauran ƴan uwansa akan ilimi da soyayyar mutane. Wanda ɗaukakar tasa itama tana ɗaya daga cikin abinda ke ƙara ɗora Lurwan ga son cutar da shi. Haka muka cigaba da tafiya munama Sooraj *SARAN ƁOYE* da iyalinsa harma da duk wanda tsautsayi ya sakko a tarkonmu. Dan kuwa dai Rabi na ɗaya daga cikinsu. Mun sakata tana mana wasu ayyukan akan dole wasu ko bama tasan muna amfani da ita munayiba musamman ta wayarta. Akwana a tashi mun cigaba da tafiya wataran muyi nasara akan aikinmu wataran su tsallake tarkonmu. A haka maganar soyayyar Abdallah da Nu'aymah ta fito, har takai Nasir yayi zuciya yabar gidan nan dan shima yana sonta. Da gaske Abdallah tsananin son Nu'aymah yakeyi, kamar yanda itama sonsa takeyi saboda tsananin shaƙuwar dake a tsakaninsu, amma a hankali muka fara canja tunanin Abdallah muna kwaɗaita masa dukiyar Sooraj. Tun yaron nan baya fahimtar mi muke nufi yana bijire mana harya hau kan hanya saboda ɗaukesa da iyayensa sukayi zuwa wajensu. Dan mun fahimci zamansa da Firdausi ne ke mana illa komin masa huɗuba itake wargaza mana komai ta hanyar ƙaunar da take nuna masa ta gaskiya. Gaba ɗaya mun tattara shirinmu ne akan auren Nu'aymah da Abdallah, shiyyasa duk likitan da aka samo da tabbacin zai mata aiki akan matsalarta sai munbi duk hanyar da zamubi wajan daƙile hakan saboda wani likita ya tabbatar mana da wahala ai mata aikin nan ta tashi, mukuma burinmu muyi amfani da wannan damar sai bayan aurenta da Abdallah aimata aikin ta sheƙa mu samu abinda muke buƙata, dan inhar muka gama da yarinyar kauda ƙaninta abune mai sauƙi a garemu. Har ALLAH yasa burinmu ya cika aka tsaida ranar auren Abdallah da Nu'aymah. Sai dai Abdallah baisan da shirinmu akan bayan aurensa da Nu'aymah so muke ta mutu ba. Wannan daga ni sai mahaifinsa ne muke shirinmu. Amma kash tarihi sai ya nema maimaita kansa tsakanin Adawiya da Nu'aymah tamkar ni da Firdausi. Dan kuwa dai Adawiya soyayyar Abdallah ce tai mata shigar sauri, tanata ɓoyewa har takai ta gagara hakan lokacin data tabbatar zai kubuce mata. Na jima da fahimtar tana sonsa amma sai na ɗauka kawai ƙuruciyace, sai da aka tsaida rana na fahimci yarinyata da gaske takeyi. Shine fa na samu Abban Abdallah da zancen kozamu samu mafita. Kai tsaye ya nunamin hakan bamai yuwuwa bane. Na harzuƙa matuƙa, dan ina buƙatar farin cikin ƴaƴana, dan haka nace to kuwa sai dai kowa ya rasa. Da dai ya fahimci zan lalata komai bayan nasara dake tunkaromu sai ya lallasheni akan to na fahimcesa mana, mu bari ayi auren Nu'aymah da Abdallah. bayan komai ya faru Aymah ta mutu wajen aiki duk yanda zaiyi zaiyi a aurama Abdallah Adawiya. Na zauna nayi nazari sosai kafin na yarda da tsarinsa, dan nima a nawa hangen dukiyar da zamu mallaka ɗin idan Abdallah ya auri Adawiya zata sake dawowa wajenane tunda jikokina sune zasu zama magadan Abdallah, daga haka muka cigaba da shirye-shiryen biki, sai dai kash ana gobe matakin cikar burinmu zai tabbata aka sace Nu'aymah. Ina mai tabbatar muku munfi iyayenta shiga tashin hankali a wannan lokacin, duk da ni ɗaura auren Adawiya da Abdallah ya ɗan min daɗin da har tashin hankalina ya sassautu. Amma bayyana muku kalar ruɗanin da Lurwan ya shiga a wannan ranar ba'a magana. Dan har sai da muka samu matsala kanmu ya rabu, ni haushina ƙiyayyar da Abdaallah ya nuna akan yarinyata, shi kuma Lurwan takaicinsa suɓucewar damarmu. Daga baya dai muka dai-daita muka tafi shirya filan b. Iya bincike kuma munyi mun rasa gano yaya akai? ta wace hanya hakan ta faru? Sannan wanene ya aikata mana hakan? Da gaske mun fara zargin asirinmu ne ya tonu, sai dai har ƙura ta lafa bamuga wani alamar hakanba sai hankalinmu yaɗan kwanta”.
Karan farko Hajjo tai murmushi mai ciwo. Amma batace komaiba.
Addah ta cigaba da faɗin. “Mun sake son ƙulla auren Abdallah da Nu'aymah a karo na biyu. Sai kuma ga Naser ya dawo wai shima da soyayyar ta. Da alama kuma tayi shirin amsarsa. Sannan hajjo da Ananah sun goya masa baya a wannan karon. Shi kansa Sooraj mun fahimci so yake ya bama Naser ɗin. Dan yanda suke takun saƙa da Abdallah baisa wani ya taɓa nuna goyon bayan Abdallah ba. Muna tsaka da neman mafita Abdallah ya saki Adawiya da Yusrah. Wannan saki shine ya kawo saɓani mai girma a tsakaninmu. Dan nikam dai na tabbatar musu sai Abdallah ya maida Adawiya zan cigaba da basu goyon bayan cigaba da aiki tare. Amma sai Abdallah ya tubure, ƙarshema ya gudu ya bar gidan saboda takurawar da mukai masa ni da Abbansa. Sai dai ya tabbatar mana shifa da gaske yanason Nu'aymah ya kuma gaji da biye mana. Hankalinmu duk ya tashi, dan tabbas da gaske munga soyayyar yarinyar a cikin idanunsa. Mun kuma tabbatar da ya daina mana biyayya kenan”.
“Ana tsaka da wannan rikicine ciwon da nake yawan ji ya takura mani, batare da sanin kowaba Mustapha ya kaini asibiti, a gwaje-gwajensu aka tabbatar mana da ina ɗauke da ciwon kansar jini, ga kuma ciwon zuciya daya ci jikina sosai shima, wanda na tabbatar yanada alaƙa da hana kaina zaman lafiya danai akan ƙadarar da ban isa canjataba tunda rubutacciyace daga littafin Firdausi da Sooraj. Lallai jikina yayi sanyi, duk wani kaushina ya sulale, adadin watanni da likitanci sukai ƙiyasin bazan zartaba ya ruguza dukkan burikana da zalamata. A karan farko zuciyata ta kwaɗaitu da son yin ƙyautatawa ga Firdausi koda sau ɗaya ne a rayuwata”. Kuka yaci ƙarfinta da tari. Yanzu kam gaba ɗaya ta cire ɗan-kwalin ta tare jinin dake fita da tarin, sai da ta tsagaita da ƙyar sannan ta cigaba da faɗin,
“Na roƙi Mustapha ya rufe zancen ciwona harga ƴaƴana saboda banason ɗagama kowa hankali, da farko bai aminceba, amma da naita lallaɓasa da hujjoji sai ya fahimta. Son kuɓutar Nu'aymah daga tarkon Lurwan ya sakani sakebin hanyar wani malami aka sakar mata jini. Ni da kaina na zuba garin magani a zoɓo na kai sashensu saboda a gabana Firdausi tasa Rabi ta dafama Sooraj zoɓi shima. sai nayi amfani da wannan damar kawai, ni na kwaɗaitama Rabi kaima Nu'aymah zoɓon ɗaki lokacin dana shigo sashen da nufin neman cucumber. Sai na aiketa ta faɗoma Firdausi zan ɗauki cucumber ɗin. Tana fita na zuba maganin. Ina laɓe ta bayan kitchen lokacin da Rabi ta tafi kaima Nu'aymah zoɓo sai ma suka gamu a falo. Inajin Nu'aymah tace bazatasha zoɓon ba na shiga damuwa. Inata ƙulla yaya zanyi kuma sai ga Rabi ta dawo kitchen ɗin ta ɗaura shayi. Dabarar bugar glass ɗin Windown nayi, Rabi ta kalla wajen ta ɗauke kai. Na sakeyi har sau biyu, shine ta leƙo, bataga komaiba da alama, shine na sake bugarsa. Shine fa tai tsaki ta fito domin dubawa. Nikuma nai amfani da wannan damar na shigo na zuba maganin na fita ta falo. Inda na wuce Aymah na kallo, sai hankalinta bai kau kainaba harna fice da sauri. Na bada awa guda sannan na sake dawowa na laɓe jikin window ɗinta, banbar wajenba harta fara ciwon ciki wanda na tabbatar magani ya fara aiki. Nabar wajen cike da farin ciki. Kafinma na isa sashena ihunta ya karaɗe gidan. Malam ya tabbatar min dama kowanne irin bincike likitoci zasuyi ciki kawai zasuyita gani ya zube a jikinta, hakanne kuma ya faru. Da wannan damar zancen ciki na sakeyin amfani na tursasa Hamisu bisa tsoratarwar zan kashe mahaifiyarsa ya kawo hotunan da ni na ɗauki Yoohan da Nu'aymah su ba shiba, ba kuma Kubrah ba kamar yanda nasan Nu'aymah zatai zargi. Nayi amfani da Hamisu ne saboda kusancinsa dana sani da Sooraj sosai, na kuma san Sooraj ya yarda dashi. Duk da Sooraj da Firdausi sun bani tausayi sosai a wannan halin na danne zuciyata na cigaba da aikata shirina dan nasan shine kawai zai kuɓutar da Nu'aymah daga sharrin Lurwan akan kwaɗayin dukiyar mahaifinta...............✍
Turƙashi😭🚶🏻
ZAFAFA BIYAR 2021
Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
(Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗
Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗
Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗
Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋
Duka akan farashi mai rahusar gaske.
Kamar haka👇🏻💃🏻
Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇
ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇
0903 234 5899
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇
09033181070
💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍
ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
[7/6, 9:39 AM] +234 913 412 2711: *_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.
No. 74
............“Dabarata ta jingina ciki ga Nu'aymah, da kawo hotonta ita da Yoohan shine burina Sooraj yay fushi yace sai Yoohan ya auri Nu'aymah. Ta hakanne kawai aurenta da Abdallah ko Naseer zai gagara. Duk da bana zargin Nasir da komai, amma inhar shi Nu'aymah zata aura tsugunne bata ƙareba kenan. Amma indai ta auri Yoohan inada yaƙinin zai bata kariya. Saboda alwashinsa na ranar da aka kirashi akan wannan batun ya birgeni. Ko bayan babu raina ina fatan ya zama garkuwa ga ahalin Firdausi. Sannan Nu'aymah ma zata samu lafiya ta dalilinsa tunda shine likitan da dama aka basu Number sa muka sace ni da Lurwan. Alhmdllh naci nasara, dan kuwa da bakinsa ya furta son auren Nu'aymah, duk da Sooraj bai bashi goyon bayaba a lokacin saboda jin nauyin ƴan uwansa akan su Abdallah na tabbatar yanason bashi. Lurwan ya shiga ruɗanin ganin zai rasa dama ta biyu, hakan ne ya sakashi sake dawowa gareni mu haɗa kai a wannan karonma. Ya kuma bani haƙuri da tabbacin zaisa Abdallah ya maida aurensa da Adawiya da zarar anyi aurensa da Nu'aymah. Na nuna masa na amince dan na samu a gama maganar auren Nu'aymah da Yahya cikin kwanciyar hankali. Daga haka na cigaba da gayama ALLAH dan agareshi kawai nake hangen samuwar nasarar kubutar da Nu'aymah daga tarkon Lurwan. Hidimar aurar da ƴaƴa kawai nake a zahiri, a baɗini kuwa ba wannan bane a gabana sam, shiyyasa na samu Firdausi da shawarar duk yanda zatayi tayi kar Sooraj ya bama Abdallah ko Nasir Nu'aymah, gara a auramata Yahya bisa wasu dalilan dana lissafa mata a lokacin waɗanda Alhmdllh sunyi tasiri a gareta. Sai da ina shirin fitowane naga Sooraj tsaye bayanmu alamar yaji komai da muka tattauna kenan. Hakan yamun dadi, dan insha ALLAHU koba komai inada yaƙinin samun nasara”.
Ta share hakawayenta ga murmushi a fuskarta. Cigaba tai da faɗin,
Jin tabbatuwar ɗaura auren Nu'aymah da Yahya shine nasarata ta farko da kobayan nabar duniya inason ƴaƴana su tuna suyi farin cikin aikin alkairi dana taɓa ƙullawa a rayuwata ta zaman gidan nan. Ko murnanr aurar da ƴaƴana guda biyu a ranar banyi murnarsa da tsananin farin ciki ba kamar yanda nayi na Nu'aymah. Amma a baɗini nabar wannan nasarar tawa. A zahiri kuwa na shiga jerin masu shiga ƙololuwar tashin hankali kamar su Abdallah da Lurwan da rayuwarsu ke a gigice. Dan wlhy aranar da aka ɗaura wannan auren kaɗan ya hana zuciyar Lurwan bugawa a gidan nan. Ya kuma sake ɗaukar alwashi kala-kala akan koma ta halin ƙaƙa saiya samu cikar burinsa. Wannan furici nasane ya sakani saka ƙanwata bin ƴan tawagar kai amarya. Sai da na tabbatar Nu'aymah ta shiga ɗakin mijinta lafiya ta hanyar ji daga gareta sannan hankalina ya kwanta. Duk da na tausayama yarinyar inda ƙaddara ta jefata. Amma sai nai mata fatan samun kariyar UBANGIJI da nasarar canjasu dalilin shigowar tata cikinsu. Daga haka na cigaba da ɓoyayyar jiyyar da mijinane kawai yasan inayi da duƙufa neman gafarar UBANGIJINA ko zan samu sassaucin raguwar zunubaina. Abinda yasa nabiku Austria ganin Nu'aymah saboda kozan samu na nema gafarartane. Ban saniba ko kafin ta dawo ƙasar ni na rasa raina. Ta ɗayan gefen kuma inason sakama Lurwan idone. dan a yanzu na daina sanin komai daga shirinsa saboda ya fahimci bana tare dasu a yanzu. Ko amincewa da zaman Adawiya da nai gidansa tanamin aikin sakamasa idone. Dan duk wani motsinsa itace ke kirana tana sanarmin batare da ita kanta tasan aiki takeminba dan ban fito fili na sanar mata manufataba”.
Wannan shine labarina, shine ƙaddarata, shine kuma son zuciyar SARAN ƁOYE dana aikata muku Firdausi, nasan bazaki taɓa yafeminba ke da zuri'arki, shiyyasama bazan matsaba wajen neman yafiyarku. Kai koma ke kin yafemin ALLAH bazai yafemin ba, dan nasan na cutar daku iya matuƙar gaya ta hanyar SARAN ƁOYE. na aminta ku kaini kowace irin kotu a yankemin hukuncin daya dace dani kafin naje na fuskanci babbar shari'ata ga babban alƙali”.
Ta ƙare maganar da fara tari mai tdanani. Sosai yanda take tarin guda gudan jini na faɗowa ya tada hankalin kowa a falon. Umm ta matsa gareta ta riƙeta sosai jikinta tana kuka. Da ƙyar aka samu tarin ya lafa. Duk da Yoohan najin zafinta har yanzu, dan shi baiji wani tausayin taba, duk da ƙoƙarin ƙulla aurensa da tai da Nu'aymah a ƙarshen ɓarnakun data tafka, amma sai ya bada shawarar a kwantar da ita zata samu sassauci daga yawan tarin. Da shawararsa akai amfani wajen kawo ƙaramar katifa aka kwantar da ita ɗin. Aiko sai tarin ya lafa sosai.
Murmushi tayi tana kallonsa, murya na rawa tace, “Nagode Yahya, ALLAH ya azurtaku da ƴaƴa nagari da zasuji ƙanku, ALLAH ya sauki Nu'aymah lafiya naga gudan jininku kafin nabar duniya”.
Uffan baiceba, baima nuna yaji mita faɗaba, amma jama'ar falon sun amsa mata da amin, duk da wasuma irin zuciyar Yoohan garesu basuji tausayin nataba.
Abban Abdallah da keji kamar ya tashi ya ƙarasa rayuwarta saboda zuciya data kumesa ya yunƙura zaiyi magana Hajjo ta dakatar da shi ta shanyar ɗaga masa hannu. Dole kuwa ya koma ya zauna yana zare idanu.
Tai gyaran murya sannan ta gyara ƙafarta mai ciwo da dubansu ɗaya bayan ɗaya ta fara faɗin, “Karma ka wahal da kanka wajen ƙaryata abinda duk Fauza ta faɗa Lurwanu. Idan bakai tunanin ana kallonku ba yau zan sanar maka cewar na jima da fahimtar kai da ita su wanene a cikinmu. Na barkune saboda na muku talalar zuwan wannan ranar. Na jima ina zargin akwai wani abu a zuciyar Lurwanu game da ɗan uwansa, dan yasha kawomin sukarsa akan miyasa kaza da kaza dole sai da umarnin ɗan malam akeyi a gidan nan?, sai dai ina nuna masa ɓacin rai. Amma ban sake tabbatarwa ba sai bayan tsaida ranar auren Abdullahi da Zainabu. Da kunnena naji dukkan abinda kuka tattauna akan soyayyar da Adawiya kema Abdullahi, tare da shirinku na bayan mutuwar Zainabu zai aureta. Hankalina ya tashi, dan zan iya cewa wannan shi e sanadin girmama samuwar hawan jini na ma. Na riƙe komai a raina na kasa faɗa har ƴar uwata tazo diba ni (Ananah) banso faɗa mataba. amma na fahimci dolene na samu shawara daga wani kafin lokaci ya ƙure. Dan wannan abune mai matuƙar sarƙaƙiya. haka na samu lokaci a wani dare mukai maganar. Itama hankalinta yayi ƙololuwar tashi dajin wnanan zance. Itace ta kawo shawarar ai tunda SARAN ƁOYE kukeyi muma yakamata mubi ta ZAGON ƘASA mu kamaku a hannu dumu-dumu. Itace ta kawo shawarar sace Zainabu ranar daren aurenta, dan hakanne kawai zai wargaza auren cikin sauƙi. A cikin shirinmu Ameer ya shigo rayuwar Zainabu matsayin abokin Abdullahi. Ameer kuwa abokin Naser ne, dan Naser shine mukaba aikin a hannunsa. Nice da kaina na shiga na haɗo kayan Zainabu a ɗakinta, na kuma jajjefa wasu ta taga. Ina cikin yi Yusrah ta shigo ɗakin da alama banɗaki zata shiga. Na tabbatar taga mutum, sai dai ban saniba kota gane waye ko bata ganeba. Abdullahi yaso lalata mana shiri a ranar saboda jan ra'ayin Zainabu da yay tayi akan suyi hira. Sai dai kuma ta dalilin Adawiya hirar batai tsaho ba. Naser ya samu damar ɗauke Zainabu ya kaita wani gida. Bamu dawo da itaba sai bayan sati biyu. Daga haka muka cigaba da bibiyar duk wani taku naku. Hatta da sace Number likitan da zaima Zainabu aiki naji a raina wani a cikinkune ya saceta, sai dai banida hujja shiyyasa nai shiru. Ina kan sani na amince da aurama Abdallah Adawiya saboda ɗana tarkon farko a gareku, inason kuma tabbatar da hannun Abdallah akan shirinku, kokuwa kuna amfani da shi ne kawai batare dashi kansa ya sani ba?. Na kuma hana Yusrah tarewa dan dama bazan yarda ta tare ɗinba. Tafiya da Zainabu Umrah yanada nasaba da son sake tabbatar da komai. Na kuma tabbatar ɗin. Waya da aka ɗagama Khadijah na hana Abdullahi zuwa Nigeria duk a cikin shirinmu ne. Munsa Nasiru ya dawo rayuwar Zainabu ne daman dan ya sake wargaza magar auren da Abdallah keta naci da son sake ganin ya ƙullu tsakaninsa da ita. Da kuma sanin da nai duk cikin shirinkune”..
“Maman Aaida data zama ƙawar Adawiya a saudia duk a cikin shirinmune itama. Mune muka sakata samun kusanci da Adawiya da ɗorata mataki-matakin kasancewa da Abdallah, a tunaninmu ko zaku dawo hayyacinku ku yarda da ƙaddara. Amma sai kuka sake tura kanku a cikin ramuka. A tarayyar maman Aaida da Adawiya ne ya bamu damar sake fahimtar bada sanin Abdallah kuke wani abunba. Dan ba komai kuke sanar masa akan shirinku ba, sannan lallai da gaske yana son Zainabu duk da ya raba hankalinsa biyu akan soyayyarta da dukiyar mahaifinta da kuka ƙwaɗaita masa a rai. Ta kuma hakane muka fahimci banzar sana'a da Abdallah yake ƙoƙarin jefa kansa a ciki. Amma Alhmdllh munyi ƙoƙarin maidosa hanya ta dalilin mijin maman Aaida ɗin, wanda ta hannunsa mukejin duk wani motsin Abdallah a yanzu haka. Maganar cikin Zainabu shine ya hautsina min tunani, saboda batare kukai aikinba yasa ban fahimci komaiba a ciki ba, duk da ina zargin kuɗinne duk da haka. Koda na tabbatar Zainabu takai mutuncinta gidan aure wannan ruɗanin na maganar ciki bai barniba sai yanzu da Fauza ta warware komai akan samuwar ciki da fitarsa. Na kai Uwaliya aiki Abuja ne dama dan Lurwanu yay yunƙurin yin amfani da ita kamar yanda Nasiru ya gano mana hanyar da sukebi wajen aamfani da Rabi itama. Na tabbatar alwashin da yahya ya ɗauka akan gano ko wanene bazai tashi a banzaba. Bakuma zai samu sauƙin ganowarba sai da wani a tsakani. Shiyyasa na tura Uwaliya ta fara sauka gidan Lurwanu ta kwana biyu sannan aka kaita wajen Zainabu. Ita kanta batasan amfani zamuyi da itaba, na ɓoyene saboda fahimtar idanunta a buɗe suke dasan kuɗu itama. Ko nawa Lurwanu ya bata lallai zata amince tai masa aikin daya buƙata akan Zainabu. Ankoyi sa'a shirinmu ya tafi dai-dai saboda Nasiru ma mutumne mai ƙwaƙwalwa da hikima. Hatta da yawan shigowa Najeriya da Abdallah ke yawan yi suna ganawa da Lurwanu duk mun sani dan duk inda yasa ƙafa Nasiru na biye da shi batare da yasani ba. Kai hatta binmu da Abdallah yayi ƙasar da akaima Zainabu aiki nasani. Dan ko a randa Yahya ya gansu suna magana shi da Lurwanu nima na gansu, sanin da nayi babu ta hanyar da zasu iya cutar da Zainabu saboda tsaron da take samu a wajen yasa na watsar da al'amarinsu. A yanzu haka mijin maman Aaida shine ya taso mana ƙeyar Abdallah zuwa Najeriya harya halarci wannan bikin duk da yazone a makare”.
Ta ƙare maganar da nuna inda Abdallah ke zaune kansa a duƙe tamkar munafuki. Harga ALLAH da yawan mutanen dake falonma sai yanzu sukasan da zamansa a falon. Hajjo ta sake gyara zamanta tana duban kowa.
“Nasan wasu zasuce miyasa duk nasan wannan amma na ɓoye matsayina na mahaifiya ga waɗan nan yara su duka?. Amsarku itace duk da ni mahaifiyace a garesu fitowa da lamarin kai tsaye dasa sabuwar fitinace da zatafi wadda muke ciki girmama. Dan inhar da tun a wancan lokacin na fiddo komai zasu kare kansu akan ba haka bane, su jefa zuciyarmu a ruɗani mu duka kokuma su canja salo, ko komai ya ɓaci duniya tasan halin da muke a ciki maƙiyanmu dake a waje su sami ƙofar yin kutse cikin wannan zuri'a su ƙarasa ɓarar da sauran abinda ya rage daga garemu. Ƙyaƙyƙyawar rayuwar da aka gina tsahon shekaru zata wargatse ta lalace kowa ya fita a hayyacinsa. Idan hakan ta kasance banci riba ba. Sannan wahalar da malam ya sha akan son gina zuri'arsa baici riba ba kenan shima. Dukansu ni na haifesu, tun a ƙuruciya nasan halin kowannensu. Dama can Lurwanu hatsabibine tun yana ƙanƙaninsa, a cikin ƴan uwan nan nasa babu wanda baisha wahalarsaba. Kaifin addu'a ne kawai ya ladabtar da shi, sai kuma kawaici da iya zama da su da ɗan uwansu yayi. Na yarda inhar ka samu ƙyaƙyƙyawar tushiya a cikin yabanyarka da izinin ALLAH zaka azurta da ƙyaƙyƙyawar albarka. Kasancewar ɗan malam ɗa nagari, mai haƙuri da kawaici, mai juriya da riƙe girmansa matsayin babba ga ƴan uwansa shine ya taimaki wannan zuri'a da kaiwa haka batare da mutanen waje sunyi tunanin samun ɓarakar shigowa cikinmu su wargazamuba. ALLAH yayima ɗan malam baiwa da ƙyautar abubuwa da yawa. Ilimi, hankali, dattako, dukiya, sanin ya kamata, nasaba. Sai dai hakan ba yana nufin zai more rayuwarsa ɗari bisa ɗari ba tunda ya haɗa komai. Shiyyasa ALLAH ya jarabcesa da atsabibancin Lurwanu dana matar ɗan uwansa Mustapha. Suka dinga wajiga rayuwarsa saboda UBANGIJI ya gwada ƙarfin imaninsa. Koni da nake mahaifiya a garesa inajin sha'awar koyi da halayensa na haƙuri da juriya duk da zuciyarsa na ƙonuwa shi da matarsa da ƴaƴansu. Wannan kawaicin da uziri shine ya kaimu ga matakin nasarar da a yau gashi su da sukecin dunduniyar sane a gabanmu suna faɗin tsiyatakun da suka aikata da bakinsu, miyafi wannan nasarar daɗi ga bawa kuwa?”.
Abban Adawiya ya share hawaye da fadin, “Babu inna, wlhy babu makamancin wannan nasara kuwa, dan hakan yana nuna mana duk mai haƙuri da tsayawa akan gaskiya, da adalci gana ƙasa da shi, ma'abocin bautar UBANGIJI, ALLAH bazai taɓa taɓar da shi ba, ALLAH bazai taɓa ƙasƙantar da shi ba. ALLAH bazai taɓa wulaƙanta rayuwarsa a hannun azzalumai ba. Ni shaidane akan hakan, dan Lurwan yaso jan ra'ayina sosai akan lamarin Yaya, kullum zancensa shine Yaya cutarmu yake a ɓoye. wai tayayama za'ai ace a raba mana gado tare, amma yazo ya fimu komai. Yafi kowa kaso mai tsoka a duka kamfanonin mu. Ga wasu harkoki da yakeyi kuma a gefe masu bala'in bashi kuɗi. Sannan kuma wai ai muduka munada ilimin addini amma tayaya za'ace kowa yafi sonsa da ƙaunarsa dajin maganarsa. Hatta mahaifiyarmu sai abinda Yaya yace takeyi a gidannan. Acewarsa wai Yaya ya asirce kowane kawai amma yake fakewa da malanta. Da farko na fara bin ra'ayinsa. Sai dai ba'ai nisaba ALLAH ya soni da rahamarsa ya fargar dani, danni dai ban taɓa ganin wani abu saɓanin ƙyautatawa ga yaya ba. Da kuɗinsa na gado ya tsaya mana mukai karatu duk da kuwa muma muna dasu. Da kuɗinsa na gado ya dinga mana hidimar rayuwa tamkar mahaifi. Idan mukai kuka shima sai kaga ƙwalla a idanunsa. Idan mukai ciwo shima sai kaga raɗaɗin a fuskarsa. Idan mukai dariya sai kuga tashi fuskar faɗaɗe da murmushi mai tsada. Shine ya nuna mana hanyar tashi mu nema na kanmu, dan shine ya fara shan wahalar kafa dukkan kasuwancin da ayanzu sune suke riƙe da duk wani motsinmu. Shine ya tsaya akanmu mukai karatu tuƙuri bayan ya tattare martabar mahaifinmu ya riƙe mana bai bada ƙofar da zamuyi sakacin da zata kufce mana ba. To miyasa son zuciya zaisa zamuyi sakaci ya sargafe tunaninmu?. Hakan yasani janye jikina daga wannan mummunar a ƙidar naita istigifari akan zargin da aka sakani nai masa babu gaira babu dalili. Ashe ya koma sun ƙulle da matata suna cutama yaya da zuri'arsa da basujiba basu ganiba. Minene laifin waɗan nan ƙananun yaran da basuma gama sanin rayuwarba balle daɗinta. Basai nace komaiba, dan Fauza azabarma da kike ciki ta isheki. kai ko Lurwanu ka jira naka sakamakon kaima, dan duk wanda yaci zalin gwani rabbi zai saka masa da alkairi a duniya ko a lahira”.
Abba Musbahu yace, “Tabbas haka zancenka yake Yaya Mustapha. Dan koni ma yaso jan ra'ayina. Sai dai fa ka sanni ni, a zuwan farko na shata masa layi duk da kasancewar sa yayana. Shine dalilin da yasa zama waje ɗaya a Lagos ya nema gagararmu sai da yabi ya lallaɓa yaya malam ta ƙarƙashin ƙasa aka maidasa Abuja aka buɗe masa company wanda ALLAH kaɗai yasan irin ɓarnar da yake a cikinsa shi da abokan aikin nasa. Domin a duk lissafin ƙarshen shekara idan mukayi sai mun tsamo yawan cuwa-cuwa da akai da kuɗaɗen company. Shi Yaya cayake daga ma'aikatanne. Niko nasan Yaya Rudwan ne dama wlhy. Nayi shiarune kawai dan ina fatan Yaya Malam ya kamashi da hannunsa dumu-dumu. To ashe aikin nasama ba anan ya tsayaba duk bala'in da ake kunnama Yaya malam da ƴan ƴaƴansa biyu da suka rage yanada hannu aciki. Wlhy ko alhakin ƙananun yaran nan bazai barku ku zauna lafiya ba balle kuma haƙƙin yaya malam da Umm-Muhammad da a kullum burinsu su ƙyautata rayuwar ƴaƴanmu a gidan nan. Kaɗanma kuka fara gani yanzu kuma”.
Momyn Abdallah daketa kuka tun ɗazun tace, “Lallaikam yanzu suka fara gani Musbahu. Wannan wace irin cin amanace haka? Wane kalar son zuciya ce?. Ba yaya kaɗai kuka cutarba ai, muma kammu iyalanku kun cutar damu, kun shiga haƙƙinmu. Wace irin ni'ima ce ALLAH bai baku ba a rayuwa amma ku gaza gode masa har sai kun ɗaura ɗammarar shiga haƙƙin wani. Alhalin dukiyar da kukema zarin ma kunfi mai ita amfana da ita ku da iyalanku. Wai miyasa ɗan adam ɗin da ALLAH yayma ni'ima shike fin tsaurin idon rashin gode masa? ALLAH ya baku ilimi alhalin ga wasu can jahilai ko yanda zasu bauta masa basu saniba. Ya baku lafiya, ga wasu can a gadon asibiti kwance basu da kuɗin neman lafiyar. Ya baku muhallin zama. Ga wasu can suna raɓe-raɓe basu da ko kangon da zasu raɓa. Ya muku sutura. Ga wasu can tufafin da zasusa su rufe tsiraicinsu bai wadacesu ba. Ya baku mutunci da daraja a idon duniya, bayan akwai dubunku da suka fiku shekaru a ƙasƙance. Ya baku dukiyar da bama kuda iyalanku ba, waɗanda suka raɓu da ku zaku iya ciyar da mutum sama da ɗari a kowanne yini. Ga wasu can iyalansuma basa iya wadatawa. Ya azurtaku da ƴaƴa maza da mata, ga wasu can suna nema da miliyoyin kuɗaɗe basu samu ba. Ya azurtaku da iyaye na gari, bayan ga wasu can iyayen nasu a gidajen baɗala. Duk waɗan nan ni'imon kuka gagara godema ALLAH a kansu, to mikuke jira UBANGIJI ya muku kafin ku gode masan? Mi kuke nema kukuwa a duniya bayan duk waɗan nan tarin ni'imomin da yay muku. Bafa kunfi waɗanda basu da shi bane, ba kuma tsoronku yasa aka baku ba. Ba kuma ƙoƙarin ibadar kuce tasa aka baku ba. Kai jama'a kaicon hannu mai butilcin amsa ga mai bashi. Kaicon zuciya mai baƙin cikin cigaban mai ƙyautata mata, Kaiconku Rudwan, tabbas bazan yafe muku ɗoramin yaro akan mummunar aƙida da kukayiba........”
Kuka ya sarƙeta ta kasa cigaba da magana. Shi dai Abban Abdallah ya kasa koda ƙwaƙwaran motsi, kansa duƙe a ƙasa ya gagara kallon kowa. hakan yasa babu wanda zai iya cewa ga a yanayin da yake.
Baba malam ma dai kansa a ƙasa yake duƙe. Babu mai shaida yanayinsa. Umm kam ganin al'amarin take tamkar a mafarki zuwa anjima zata farka. Zuciyarta ta kasa gaskata komai akan Abban Abdallah da Fauza. Mutanen da sukafi kowa kusanci da su a gidan. Kai jama'a duniya ina zaki kaimu?.....
Jin kowa bai ƙara cewa komai ba yasa Jay yin gyaran murya. Kusan duk kallonsa sukayi. Ya furzar da numfashi na takaici da faɗin, “To inaga idan kun gama da su zamu kaisu station mu haɗa bayanansu sai mu miƙasu kotu su amshi hukunci kamar yanda shari'a ta tanadar”.
Tari Addah ta fara kaɗan-kaɗan, hakanne ya saka baba malam ɗagowa ya kalleta ya maida dubansa ga Jay. “Muhammad Jawaad mubar zancen zuwa kotu kaji. Ita wannan kuma miya rage mata a duniyarma gaba ɗaya. Ai wannan izayar da take ciki kawai ta isheta izina. Sai dai mu taimaketa mu miƙata asibiti kawai....”
Murmushi Jay yayi yana jinjina kai. “Duk da haka malam ai ya kamata su fuskanci shari'a kodan hakan ya zama ilimi ga ƴan baya masu sha'awar sake aikatawa. Duk da tana cikin halin ciwo bashi ke nuna zata mutu ba, mutuwa ta ALLAH ce, takanzo a sanda taso ga wanda taso. Dan haka zamuje asibitin taga likita amma bisa ƙarƙashin kulawar hukuma. Shi ko zamu wuce da shi station”. Ya ƙare maganar yana nuna inda Abban Abdallah yake zaune.
Baba malam zai sake magana Hajjo ta katsesa da cewar, “Ɗan malam hakan shine dai-dai kuma ya kamata. Kaga idanma da mai sha'awar aikatawa a nan gaba sai ya bada himma”.
Tarin Addah daya ƙara ƙarfine ya sakasu duk maida hankalinsu gareta. Da wannan damar Abban Abdallah ya samu ya sulale a hankali yabar sashen. Sauran jami'an dake a waje basusan yaya aka ƙareba shiyyasa basu hana Abban Abdallah bi ta gabansuba ya wuce sashensa yaje ya haɗa duk wasu abubuwa nasa masu muhimmanci ya zuba a ƙaramar jikka ya fito. A gaban jami'an ya shiga motarsa maigadi ya buɗe masa gate ya fita batare da shima yasan mike faruwa ba.
Daga ciki ma babu wanda ya farga da rashinsa sai bayan an fito da Addah daketa faman zuba aman jini aka saka a mota domin kaita asibiti. Suna wucewa su Jay suka koma kan Abban Abdallah sai yace ku ɗaukeni inda kuka ajiye. A take suka hau cigiyarsa a lungu da saƙo na gidan, sai daga baya sukeji daga bakin maigadi cewar ya fita a mota tun kusan mintuna talatin da suka shuɗe.
A razane Jay yace, “What?!!, shine kuka barsa saboda baku da hankali?!”. Yay maganar wa yaransa. Duk rawa jikinsu ya kamayi suka hau rantse-rantse su basusan mai laifi bane. Ai kota kansu Jay baibiba ya shiga motarsa shi da Bily da Little. Suma duk suka shiga a wacce sukazo. sai da suka tambayi maigadi motar daya fita a ciki da lambarta sannan suka fice a guje.
Wayar Jabeer Jay ya kira, yana ɗagawa ya ce, “Jabeer inason a baza zami'ai a kowacce hanyar fita garin kano domin tsaidamin mota mai Number..... Ruwan toka”.
Jabeer na amsa masa ya yanke kiran, C.P ya kira shima dan ya taimakesu.
__________★★
A gidan su Nu'aymah kam musalta muku halin da suke ciki ɓata lokacine. Dan motocin su Jay na fita a gidan Umm ta yanke jiki ta faɗi. Hakama Malam ƙarami shiɗe musu yayi. Ga kukan da su Adawiya keyi ya taru ya ƙara ɗaga musu hankali. Baba malam kansa dauriya kawai yakeyi dan gaba ɗaya jinsa yake kamar kansa zai tarwatse dan ciwo. Gashi su Yoohan sun wuce da Addah asibiti. Hakan yasa dole aka kwashi su Umm ma zuwa asibitin.
Ɓangaren Abban Abdallah kam tunda ya fito anguwarsu kai tsaye hanyar Katsina ya ɗauka, shi kansa baisan mi yake shirin aikatawaba. Ceton kansa ko gudun kunya? Ko tsoro?. Gudu ya ke na hauka babu wasa a cikinsa. Musamman daya kasance ta gefe-gefen gari yake tafiyar, dan bai yarda yabi ta cikin gariba sam. Yana fara ɗaukar hanyar Ktn bayan ya gota Dawanau kaɗan ko mintuna goma baiyiba ya ga motar ƴan sanda na binsa a baya. A take ya ƙara ƙarfin gudun motar tamkar ya manta da kasancewarsa Dattijo. Abu kamar a film suka fara rere tsakaninsa da jami'ai.
ALLAH sarki rayuwa, duk iyawarka baka isa zarce ƙaddarar UBANGIJI ba. Dan kuwa dai wannan ƴar tsere na Abban Abdallah da ƴan sanda sunansa gudu akan igiyar ƙaddara. Dan kuwa bisa tsautsayi sukau taho mu gama da wata mota dake nufo cikin kano. A take waccan tayi gefen titi, shiko ta Abban Abdallah sai ta kife ta fara wuntsil-wuntsil daga titi ya gangara cikin gona. Tun suna jin yanda yake neman ɗaukin UBANGIJI har sukaji tsit, motar kuma ta bugi bishiyar dalbejiya ta tsaya cak.
Cikin sauri ƴan sandan da dama tuni sun fito a mota suka nufi motar domin bashi taimako. Da ƙyar kuwa akayi kama-kamar ɗaga motar aka zarosa a ciki. Gaba ɗaya jikinsa yayi face-face da jini har ba'a iya gane inane ya bugu koma yanada rai ko ya mutu. Kasancewar sun kira sun sanar sai ogansu ya basu umarnin maza su ɗakkosa su dawo cikin kano asibiti. Bisa wannan umarnin ya sakasu ɗakkosa suka juyo a guje.
Kai tsaye babban asibiti suka nufa, cikin amincin ALLAH kuma akai sa'a can aka kai Addah da su Umm suma. Su baba Malam na tsaka da tashin hankalin abinda ya faru sabon labari akan haɗarin Abban Abdallah yazo musu. A take na gida dana asibitin suka sake harmutsewa.
A yanda Yoohan yaga al'amarin ya kasance sai da yaji nadamar shigewa gaba wajen wannan bankaɗe-bankaɗe. Sai gashi da idanunsa ya ga baba malam na rusar kuka. Nu'aymah kam ai sai allurar barci ya danna mata saboda yanda ta birkice kamar dai ƙwaƙwalwar ta bata gama dawowa dai-dai ba.
Lallai wannan ranace da waɗaɗan nan ahali bazasu taɓa mantawa da itaba a jerin tarihinsu. Sauƙinsu ma har yanzu ainahin labarin bai fita kunnuwan jama'ar gariba. Sai dai kawai ana maganar Sheikh Rudwan Hashim jibiya yayi Accident a hanyarsa ta zuwa Ktn yanzu babu jimawa. A take mutane suka shiga jera masa addu'ar ALLAH ya tashi kafaɗa, musamman ma mabiyansa.
Zan iya ce muku yanda wannan ahali sukaga yinin wannan rana haka sukaga dare. Duk da kuwa Alhmdllh zuwa dare an tabbatar da Abban Abdallah bai rasuba. Ya dai samu karaya a kafaɗunsa duka biyu da kafafu. Sai manyan raunika da sukai masa kaca-kaca da jiki. Itako Addah barci suka sakata yi. Umm ma Alhmdllh ta farfaɗo ita da malam ƙarami. Hakama Nu'aymah ta farka.
Sai kusan tara na dare suka bar asibitin, ba kuma a barsu sunga Abban Abdallah ba dai. Yoohan da kansa ya fiddo Nu'aymah da ga ɗakin office ɗinsa daya sakata barci. Ananah ta taimaka mata suka ƙarasa shiga mota. Baba malam yaso su Yoohan su bisu can gidan su kwana amma suka bashi haƙuri akan zasu zauna anan asibitin ne. Badan yaso ba ya barsu.
Yoohan na ganin motocinsu sun gama wucewa ya sauke ajiyar zuciya mai kauri, A ɗaya daga kujerun dake a waje ya zauna hannayensa duka dafe da kansa. Sai yanzu komai ke dawo masa a ƙwaƙwalwa tamkar almara. Dan ɗazun su Addah na bayani ne little na fassara musu shi da Umar, duk da shi yana ɗan jin hausarma kaɗan-kaɗan yanzun.
Kusa da shi Umar yazo ya zauna shima yana sauke nasa ajiyar zuciyar. Yoohan bai motsaba balle ya kallesa. Shima sai bai damuba ya fara magana a hankali. “Haka mafi yawancin mutanen da suka samu ɗaukaka suke. Sai kaga na nesa da su na matuƙar sonsu da begen kasancewa da su. Amma waɗanda ke tare da su mafi yawancinsu ba son gaskiya suke musu ba. Ƙaso ɗaya bisa uku a ciki zaka samu suna musu ƙauna ta tsakani da ALLAH. Kaso biyun kuwa sai kaga suna raɓe da sune bisa wannan ɗaukakar da ALLAH yay musu. A zahiri kuwa su zugasu da nunama duniya babu kamarsu, a baɗini sune masu musu SARAN ƁOYE. lallai waɗanan mutanen masu zagon ƙasa suna ɗaya daga cikin jarabawar masu mafi yawan ɗaukaka”.
Ajiyar zuciya Yoohan ya sake saukewa. Ya ɗago ya dubi Umar a karon farko, idanunsa sunyi jajur. Ga barci ga yunwa ga gajiya. Shi kansa Umar ɗin a galabaice ya ke. “Zancenka haka yake Umar, bazan ɓoye makaba al'amarin mutanen nan ya sake saka tsoro a zuciyata gaba ɗaya, nasake jin tsoron halin mutum da ayyukansa. Wannan wane irin bushewar zuciya ne haka? Su da ya kamata su zauna suyita godema ALLAH bisa ni'imar da yay musu ta rayuwa, su dinga ibada sai suka zama masu butulcewa ta hanyar cutar da wanda shi ya kusan ƙare tasa rayuwarne a ƙyautata tasu da ta ƴaƴansu. Umar wai miyasa ɗan adam keda manta alkairi da yawan butulci ne?. Miyasa ɗan adam yafi yarda da biyayya wa huɗubar shaiɗan akan dokar ALLAH ne?. Miyasa ɗan adam yafi yarda ya zama mai samu bamai sadaukarwa ba? Miyasa mafi yawan mutane sunfi sha'awar cutar da wanda suka ƙyautata musu amma sunajin tsoron mai munanasu?. Ko addu'a mutum zaiyi, sai kaji yace ALLAH ka tsareni daga sharrin masu sharri. To miyasa bama addu'ar ALLAH ya karemu da aikata sharri ga masu ƙyautata mana ne?”.
“Wannan shine halin ɗan adam ɗin da ake faɗa Dude, munada son kanmu, duk kuma mutum mai son kasa zakaga shine kullum a cikin wahalar nema da faɗuwa. Dan bazai taɓa doguwar nasara ba. Daya samu take kufece masa. Amma saboda bushewar zuciya gobe ma sai ya koma sake neman sa'a. Kowane addini akwai na banza akwai na gari. Irin waɗan nan mutanen suke ja ana zagin addinin islama bayan shi kuma addinine mai koyar da ƙyawawan ɗabi'u. Ko shekara banyi da shiga musilinci ba, amma wlhy Yoohan na fahimci babu wani addini dake gogayya da shi akan koyar da ƙyaƙyƙyawar rayuwa. Komai musilinci ya haɗa. Amma ka duba su da keda ilimin sani a tsahon shekaru sunfi zaɓar su saɓama ALLAH bisa son zukatansu”.
Sosai zukatansu Yoohan suka ƙara rauni da wannan al'amari. Imani da tsoron ALLAH ya sake shigarsu a zuciya da ɓargo. Suma kansu dai a wannan dare sunyi barci ne kawai badan jin daɗi ba.
*_WASHE GARI_*
Washe gari aka bama su baba malam damar shiga su duba Abban Abdallah. A lallai duniya abin tsoro. Bawa daina cikama rayuwa baki kai ba komai bane. Duk damar da kaga ka samu a rayuwa da ga rahamar ALLAH ne. Amma wlhy idan yaso ko ƙyaftawar ido baka isa gittawa ba. A jiya iyanzu shine zaune tare da ƴan uwa da iyalansa. Amma yau gashi babu ko ƙyan gani a fuska saboda tsabar jigata da rayuwarsa tayi. Ita kanta Addah jikin nata babu daɗi.
Duk wanda ya shiga duba Abban Abdallah sai kaga ya fito da kuka. Hakan yasa dama Yoohan bai bar Nu'aymah a wajenba. Suna zuwa ma ya jata wai tazo suje wajen awo. Bata fahimci wayo yake mataba ta bishi. Sai ya kaita office yasa aka kawo mata abinci. Duk da tace masa ta ƙoshi, dan basu fitoba sai da Umm ta bata abinci ya dage sai taci. Dole taci kaɗan dan ya barta. Sauran kuma ta bashi dan ta fahimci shima yana buƙatar a tsaresa yaci abincin.
Zuwa ranar dai dukan ahalin gidan sunsan halin da ake ciki, ƴaƴan Addah dake aure da ƙannen Abdallah ma duk sunzo. Ansha sabon kuka dai kam yau ma. Daga ƙarshe baba malam dake ta ƙoƙarin danne tasa damuwar yay musu nasiha da nuna musu muhimmancin ƙaddara. Ya tabbatar musu da cewar hakan jarabawane. Dan bazai yuwu dama a rayuwa a rayuwa babu jarabawa ba. Ya hana kowa kakkausan lafazi akan su Addah, dan kuwa shi a take ranar ya tabbatarma da kowa cewar ya yafe musu. Sai su cigaba da musu addu'ar ALLAH ya basu lafiya kawai.
Baba malam ya ƙara kima a idanun iyalan Addah da Abban Abdallah. Musamman ma Abdallah da har ran yakejin tsanar mahaifinsa da Addah. Sunso su gurɓata masa tunani ALLAH ya hana hakan. Dan bayan Addah ta ɓale a cikinsu Abbansa sake zaunar da shi yay ya ɗora masa sabon karatu akan maido da Nu'aymah rayuwarsa koda ta ƙarfin tuwo ne. Wannan shine dalilin da yasa dinga bibiyar rayuwarta. Ko a randa ya bisu shopping mail ɗin nan da nufin kidnapping Nu'aymah ya je. Sai akai rashin sa'a Yoohan ya gansa tun lokacin da suke faɗansu da Aymah harta faɗa a jikinsa. Dai-dai lokacin da yake cemata ta tara musu mutane idonsa ya sauka akan Abdallah ɗin. Har suka shiga mail ɗin kuma yana sane da shi. Sannan yana akan sani yabar Aymah a wajen ita kaɗai dan yaga mi Abdallah zaiyi?.
Lokacin da Nu'aymah taji ƙamshinsa da gittawar mutum Abdallah ne, yana gab da isa gareta Yoohan ya jasa baya da ƙarfi ya toshe masa baki suka koma ta bayansu. Cikin fushi Abdallah ya hakaɗe Yoohan ɗin yana faɗin. “Kai shasha minene haka?”.
Murmushi Yoohan yayi sannan ya haɗe fuska. Cikin ƙanƙance ido ya nuna Abdallah da faɗin, “Idan ka bari gangancinka ya ɗora zuciyarka bisa dokin shiga gona ta. Na rantse da ALLAH Abdallah sai na dawwamar da rayuwarka a dana sani. Na fika hatsabibanci fiye da yanda kake tsammani. Dan haka ka kama kanka kafin na ajiye mutuncin ahalinka da nake gani gefe na ɓata rayuwarka. Karka zata bansan wanene kai ba da ubanka. Ka kiyayeni kona fallasaku duniya ta sanku da aiyyukanku akan ahalinku”.
Yana gama faɗa yabar wajen, shine yaje yaja Aymah suka wuce wajan biyan kuɗi.
Tabbas kalaman Yoohan sun girgiza Abdallah. Hakan yasa ya janye daga bibiyar Nu'aymah. Dan dama can shi mutum ne da a rayuwa bai son yawan matsawa kansa, sannan baison fitina sam. Wannan halayyar tasa tasa lokacin yana yaro ake ganinsa matsoraci a cikin yara ƴan uwansa. Dan da gaske tabbas yanada tsoron faɗa a rayuwarsa. Dai-dai da film ɗin faɗa Abdallah baya zaman kallonsa sam saboda baya ra'ayin fitina, daya zama saurayune ma dai ya fara canjawa. har zuciyar tasa tai tauri saboda zuciyar gidansu ta gado.
Ƙin faɗama Abbansa zancen yayi. Amma yayi ƙudirin janye jikinsa daga bibiyar Nu'aymah. Daga bakin Abbansa yaji samuwar Uwaliya, dan a randa aka kawota a ranar Abbansa ya tattauna da ita tun a office kafinma a kaita gidansa. Uwaliya akwai son kuɗi. jin maƙudan ƙuɗin da Abban Abdallah ya tabbatar mata zata samu akan kaso masa auren Nu'aymah da kawo musu dukkan bayanai a kanta yasa ta amince zatayi. A ranar ya bata rabin kuɗin, sauran kuwa sai aiki ya kammala.
Tasha murna a ranar, ta kuma tabbatar da lallai ta shigo Abuja da ƙafar dama. Yo ko Yoohan ɗin sukace ta bibiya akan waɗanan kudin ai ta halakashi kuwa.
Wannan shine dalilin da yasa ta fara musu aiki. Sai dai abinda bata saniba suna amfani da wayar Rabi da muryartane idan suka kirata.
Lokacin da aka wuce da Nu'aymah Austria da gaske Abdallah yaje dubatane saboda son da yake mata. Sai dai baiso Yoohan da su baba malam su gansa. Shine yaso su fara haɗuwa da Abbansa. koda suka haɗun Abban ya dinga masa faɗan da har zancen Nu'aymah ya shigo ciki saboda Addah da tazo taga Abdallah ta zata cutar da Aymah zasuyi. Anna ne Yoohan yaji da Hajjo sukaji, abinda kuma basu saniba shine baba malam ma ya gansu, ya kuma jisu. amma sai bai taɓa nunawa ko da Umm ba balle su..........✍
[7/6, 9:39 AM] +234 913 412 2711: *_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.
No. 75
.............Su Jay dai sun wuce abuja, amma duk da su Addah na a asibiti suna a ƙarƙashin kulawar hukuma ne. Bayan wucewar su Jay shi ma Omar da Yoohan suka wuce da yamma. Ya bar Nu'aymah anan kano saboda Umm bata da lafiya. Har yanzu ta kasa fida daga ruɗanin data shiga. Ga jininta yaƙi sauka yanda ya kamata. Ita kanta hajjo jininta ya hau sosai. Sai dai ita Alhmdllh bai kai na Umm da komai yazo mata a yanda bata zata ba. Bama Umm kaɗai ba hatta da ƴan uwan Umm dana Addar wannan al'amari yay masifar rikita tunaninsu da basu tsoro. Anatama Addah ALLAH wadarai da wannan hali nata. Su Hajarah kam sunyi kuka har sun rasa hawayen zubarwa. Musamman Kubrah da dama ba daɗin zaman gidan mijin take jiba. Fitinar yau daban ta gobe daban.
Yanda gidan dai yay wani iri daga shigowa zaga fahimci akwai matsala. Baba malam salla kawai ke fiddashi. Da an idar yake dawowa gida. Komansa ya tsaya cak. Dan duk da daurewar da yakeyi a bala'in gigice ya ke da al'amarin. Bai taɓa ƙawowa a ransa cikin ƴan uwansa za'a samu mai wannan tunaninba akan dukiya dauɗar duniya. Yayi kuka bana wasaba a ɓoye, har ji yake gaba ɗaya ƙasar ta fita masa a arai.