Kusan ta mance da abdulyasar gaba daya,don a qalla an kusa sati da wani yammaci akace ana sallama da ita,tayi mamaki sosai don a yanzu tasan bata da appointment da wani kan zaizo nemanta,har ta aika yaron tace masa yaje yace bata nan hajja ta tsaidashi,tace
"kace masa tana zuwa" fuska tadan bata tana duban hajja
"Nifa wallahi hajja ban san waye ba,da kin barshi kawai ya tafi"
"A'ah,ai baza'ayi haka ba,idan kuma shine mijin auren fa kika koreshi?" Saita dan buga qafa kadan tana turo baki,sannan ta miqe ta nufi daki.
Ganin doguwar riga ce a jikinta mai dogon hannu,kuma budadde ne dinkin babu ta inda ya kama jikinta saita sanya qaramin mayafi tayi rolling dashi sannan ta fito.
Yana jikin katangar gidan a jingine tayi sallama,da murmushi a fuskarsa ya dago yana amsawa,sai a sannan ta gane waye,saita dan sake masa fuska kadan suka gaisawa.
"Hala baki gane waye ba" dan qaramin murmushi tayi
"Na gane mana,sunanka ne kawai ban sani ba"
"Nima haka,ai anmin rowar suna,har muka rabu banji sunan malamar ba,shi yasa yanzu nayo tattaki nazo naji daga bakinta....nidai sunana abdulyasar......" Daga nan yayi mata bayanin kansa,itama bataqi ba ta gaya mishi sunanta,sannan ya gabatar mata da abinda ya kawoshi,ya kuma dora da cewa
"Ni da gaske nazo,kuma da gaske nake,ina fatan babu wani a gabana,kuma babu wanda ya rigani?" Murmushi kawai tayi ba tare data bashi amsa ba,dai dai sanda motar haidar ta danno layin,ta kuma qaraso gaban gidan,yayi horn mai gadi ya bude masa ya shige,da alama yau ya dawo yazo hutune kamar yadda yakanyi kusan duk qarshen wata.
Tasan halin ya haidar din duk da bata ga alamun ya ganta ba,amma gudun faruwar wani abu yasa tayi masa sallama ta shige gida,bayan ya nace ya amshi lambarta.
Kafin ta qarasa sassansu wayarta dake hannunta tayi tsuwwa,hindatu ce ke kiranta,saita dakata da tafiyar ta tsaya amsa wayar
"Ya akayi ne qawa?"
"Lafiya wallahi.....ya gida yasu daddy?"
"Lafiya lau,duka na barosu a gida bama tare"
"Ina kika tafi kuma?" Zahran ta tuhumeta tana dan tsuke gira
"Ba wani waje bane me nisa,lagos ne,ana bikin wata qawata....so akwai wani event da za'ayi a nan din" gyara tsaiwa tayi
"Amma fisabilillahi hindu biki a kasa yinsa a garinsu amarya har sai an dauki wani event din an kaishi wani gari me nisa haka?"
"Wanne nisa tafiyar jirgi?,yan mintuna marasa yawa anje"
"A ina kuka sauka kenan?"
"Guest house mana,muna da wanda muka sani ne?" Dogon tsaki zahran taja
"Kunnen qashinki shi zai sa mu raba gari dake hindu,tunda bakya yarda da abinda nake gaya miki" dariya ta saki
"Ko kin raba gari dani ni bazan raba dake ba.....karki damu,idan akwai wani abu ba dai dai ba daddy ko mommy xasu yi magana,ni kiranki nayi ma na gaya miki....gobe fa za'a je strike din nan,kuma sai baba ta gani sunce" bata rai zahra tayi
"Wato a duniya shi dalibin nigeria bazai taba gama karatu ta dadin rai farinciki ko walwala ba?.....ai shikenan,sun yiwa kansu,muma mayi azuminmu a dadi,Allah yasa sai an sallace za'a koma" dariya hindatu ta saki
"Wallahi nima haka nace,kinsan hali dai,idan ina azumi ba kanta,bana ganewa kwata kwata" saita kauda wannan zancan ta dauko na farko
"Yanzu yaushe xaki dawo?"
"Gobe in sha Allah...."
"Kin tabbata?"
"Da gaske nake....jibi ma zanzo har gida ki tabbatar da kanki,saka ranki a inuwa" daga haka zahran ta katse wayar,Allah ya sani tana qaunar hindatun,kuma tana da halaye masu kyau na kirki da son jama'a,amma rayuwarta ita a wajenta da iyayenta ba komai bane saboda tsabar wayewa,dukkansu bata zarginsu da aikata alfasha da maza,amma saidai yanayin yadda suke gudanar da rayuwarsu wayewarsu tayi yawa,irin wayewar da dole zata iya janyo maka zargi ga idanun al'umma,kuma yana daga cikin cikar kamalar mutum ya guji dukkan wani abu da zai jefa zarginsa a zuciyar al'umma,da wannan tunanin ta isa sassan hajjan,saita tadda haidar dofane a hannun kujera yana latsa waya,jikinsa wata fara qal din shirt ce ta maza mai V neck short sleeve,sai wandon kaki dake jikinsa,da wani farin qal din booth da yakai masa har qauri,hajja na zaune daga gefansa,da alama wata maganar takeyi dashi,shi kuma yana sauraronta,yayi wani irin kwarjini musamman yau daya bar iya wandon ma kawai a jikinsa,hakanan fatarsa tayi fresh tamkar babu abinda ke damunsa,saidai kuma fuskarnan tana nan kamar kowanne lokaci babu rahama ko digon dariya tattare da ita,sai gashinsa daketa glowing wanda ya qara masa kyau da cikar mazantaka.
Kansa ya daga ya jefeta da wani irin kallo,murya a dake yace
"Ke....zonan" da baya ta dawo ta zauna jikin hajja kamar zata shige cikinta,ya cira kai da lumsassun idanunsa dake cike da kwarjini yace yana duban hajja
"Ya akayi ta fita da wannan shigar?,waye kuma a waje data tsaya dashi?" Duban zahra hajja tayi sannan ta dubeshi
"Me ya samu shigar tata?,sannan idan saurayi yayi sallama da budurwa dama binsu ake a tsaya tare dasu ko kuwa?" Sai daya lumshe idanunsaya budesu sannan yace
"Amma hajja kinfi kowa sanin tsarina a kansu tun sauran na gidan nan ko game da saka qananun mayafai ko?,sannan haka sama taka ba'asan mutum ba yazo ya kirata ta kada wadannan zoqala zoqalan qafafun nata ta fita?".
Wayyo....ji zahra tayi kamar ya kwada mata mari,tunda take ba wanda ya taba aibanta surarta saishi,tasha ji a bakin maza daban daban yadda suke koda halittarta duk da ita ba burgeta hakan yake ba,ba kuma damuwa tayi dasu ba,shine yau shi don wulaqanci zai jefeta da wannan kalmar?.
Hajja kam baki ta kama sannan ta saki tana ruqo hannun zahran
"Karka sake gayawa jikata haka,a ciki ni banga abun laifi ba,indai ba daga bracck aka bata kama rai ba zaka zo ka juyeshi a nan ahto" qaramar ajiyar zuciya ya sauke
"Ke tashi ki bamu waje" ya fada cikin sigar bada umarni,saita miqe da hanzari,ta murguda baki bayan ta juya musu baya cikin ranta tana mita.
Sai da yaga shigewarta sannan ya dubi hajja dai
"Hajja....yarinyar nan,haka kawai kuka kaita universty,ke baki ganin sauyin dabi'u tattare da ita?" Hannu ta daga masa
"Haidar....haidar...me yasa haka ne?,ni babu wani abu da zahrata ta sauya dashi,kada na sake jin wani abu makamancin haka daga bakinka" wayarsa ya mayar aljihun unifoarm din sojojin dake jikinsa,sannan ya miqe a nutse
"Ina kuma zaka muna magana?" Cikin i don't care manner yace
"Akwai kaya da nakeso a fito dasu kafin na shiga ciki,don bazan samu fitowa da wuri ba....idan na fito ma tattauna" daga haka ya soma takawa da wata irin tafiya mai cike da qasaita da nuna qarfi da ginuwar gangar jiki yabar falon.
Sai a sannan zahra dake labe ta fito da hanzari muryarta na rawa kamar zata sake kuka tace
"Kinji ko hajja....kinji sharrin da yakeson yimin,ni ba'ace komai a kanshi ba saboda zaman bariki ba saini don ina makaranta"
"Kinga dagani....na gaji da wannan iskancin naku keda zaki,yara kamar mayu?,kamar masu ganin hanjin juna?,to wallahi idan bakuyi wasa ba aure zan saka iyayenku su daura muku naga qaryar iskanci" wani irin tsalle zahra dake zaune a jikin hajja ga buga kamar wadda aka dorawa kunama a jiki,ita kanta hajjan saida tayi sak cikin tsoron tana duban zahra dake fadin
"A'uzu billahi minash shaidanir rajim,hajja....wacce irin masifa kike ambata da yammacin juma'ar nan?" Ta fada idanunta duka a waje,tafin hannu kawai hajja ta saka tana rufe bakinta dashi tana fadin
"La'ilaha ilallahu,muhammadurrasulullahi,sallallahu alaihi wa sallam inna wuro?,kamar wadda tace miki tsohuwarki ta mutu?,wannan zancen ne masifa?,anya zahra?" Ganin yadda bacin ranta ya bayyana yasa ta sassauta nata,ta qarasa wajen hajjan ta zauna tana narke murya
"Kiyi haquri hajja,ba haka nake nufi ba,don Allah ki haquri,amma.in sha Allah na daina shiga huruminsa,dama ni ba shiga nake ba,shine haka nan ba gaira ba dalili ya matsantamin"
"Kema ai bajin magana kike ba,ko don kinga ina baki kariya?"kamar zatayi kuka tace
"kiyi haquri dai don Allah abar zancan,na daina in sha Allahu" shuru tayi kamar ba zatayi magana ba,sai kuma ta sake ajiyar zuciya
"Ai shikenan....Allah ya kyauta" jin haka don kada ta sake jan wata maganar saita miqe kawai tayi dakinta,a ranta tana juya zancan
"Itama.hajjan nan wani lokacin wlh tuburarriya ce,haka kawai da yammacin ranar juma'a,dai dai sanda ake amsa addu'a ki fadi wannan mummunan kalamin kisa 'yan amin su amsa?" Ita daya ta qaraci mitarta cikin daki harta haqura.
Da magariba zata gurin me gadi amsowa hajja goro da me gadi yace tazo ta amsa taga qofar gidan nasu cike da jama'a,kusan hakan ba sabon abu bane wajensu,duk randa aliyyu ya sauka a garin gidansun baya rabo da mutane,duk da cewa ko baya nan din ba'a rasa mabuqata jifa jifa masu neman taimako,amma kuma cikarsu bata kaiwa yadda take a yanzun.
A yanzun ma rabon kayan abincin azumi da alama yasa akeyi,don ga kwalayen kayan abinci nan kala kala da qananun buhun shinkafa,tabe baki tayi sanda taji wani yana zabga addu'a da koda layin duk da baya wajen,don baya zama a inda ake rabon,saidai ya wakilta ma'aikatan gidan
"Uban tausayi uban talakawan unguwar nan dama gundumar nan gaba daya,zuciyarka fara tas take hakama ayyukanka,ubangiji yasa kafi haka,ya qara arziqi da daukaka"
"Green snake....under green grass kenan" ta fada qasa qasa tana sake tabe baki,tana tsaye tana kallon yadda suke layi suna karba cikin farinciki,don mai gadin shima yana can,sai daya hangota sannan ya iso yana cewa
"Kiyi haquri uwar masu gida,banga zuwanki ba,saqon hajiya hajja ko?,ina can muna rabon aikin alkhairin haidar.....wannan yaro ya dace,ubangiji ya kareshi yasa yafi haka,yana faranta ran talakawa" ya fada yana cusa kanshi dan dakinsa,ya dauko saqon ya miqa.mata ta karba ta juya,tana sake jiyo kalaman yabo daga bakin mutane.
Ta sani cewa wani lokaci akan zo ma su hajja godiya kan wani abu da aliyyun yayi cikin unguwar,saidai su amsa don babu wanda yasan ma yayi din,kusan haka dabi'arsa take idan zaiyi wani abun alkhairin,itakam tana dauka kawai shashanci ne irin na mutane,don bataga alamu a yadda aliyyun yake da baqar zuciya,zai iya wani abun arziqin da zai farantawa wani rai ba.
*************
Kamar da wasa kuwa wata washegarin ta gama wankewa hajja qananun kayanta ta fito ta falo,tana tsaye gaban tv taji kamar muryar hindatu tana magana,da alama yaran gidansu ne da yau gaba dayan 'yan mazan da matasan abba babba ya raba musu gyaran flowers da farfajiyar gidan,tunda an yiwa wanda yake musu wannan hidimar rasuwa,ya tafi qauye.
Aje remote din tayi tana tafa hannu cikin mamaki da jin dadi
"Na zaci zancanki ne kawai fa da kika ce zaki zo" itama tana murmushin tace
"Kin taba ganin na saba alaqawari" kai ta girgiza tace
"Ina sara miki ta wannan sashen ai".
Sai data gabatar mata da ruwa da lemo sannan ta yiwa hajja magana ta fito suka gaisa,ba wannan bane zuwanta gidan na farko ba,ta taba zuwa sau daya,wannan ne na biyu,hindatun ta jima sosai suna hira,don a nan taci abincin rana ma,sannan ta kira jannah batula nadiya da farida suka hada kira na bai daya suka sha hira har zuwa sanda akayi sallar la'asar,ta shiga nan bandakin zahra din ta daura alwala.
Tana saman abun sallar zata tayar kenan ta waiwayo ta dubi zahra
"Yauma fa na sake ganin yayankunnan,ya hakimce saman kujera qafa daya saman daya yana karatun jarida,duka yaran kowa cikin hankalinsa yake aikinsa ba hayaniya da alama shike gadinsu,bakiga yadda tsare gidan da yayi yayi masa kyau ba"hindatu ta fada,kallonta zahra tayi
"Wanne fa?,ya musty ko ya shamsu?"
"A'ah fa....sojan nan....wallahi nikam idanuna basu taba ganin namijin da yamin kwarjini,ya kuma burgeni,na kuma ji na shirya aurensa ba irinsa....don Allah qawata ki shigemin gaba mana" ta fada cikin karyar da murya.
Tsaki zahra taja
"Don girman Allah ki tada sallarki ya fiye miki arziqi,wannan maganar taki ki nema abokin yinta amma ba zahra'u ba" saita sanya filo saman katifarta ta kwanta rub da ciki,hindatun dai bata haqura ba tace
"Saboda me kika ce haka?"
"Ki barni don Allah hindatu" da taga ta matsa da maganar,da zancan saita gaya mata dalili sai tace
"Ba ya haidar ba?,ai nan ne gidansu,kuma yana cikin gidan,kina iya gwada sa'arki,kije ki gabatar masa da kanki mana qawata"
"Au haka kika ce?,zakiga aiki kuwa da cikawa"ta fada tana kabbara sallarta
"Da dai yafi" itama ta amsa mata tana gyara kwanciyarta.
Tare suka fito don mata rakiya,zuwa sannan sun gama gyaran sai ganyayyakin da suke hadawa,ya mustapha na nuna musu inda zasu zuba za'azo a kwashe daga wajen kwashe shara.
Har yanzun haidar din na zaune inda yake,saidai wannan karon maimakon jarida wani littafine a hannunsa yana dubawa,mai kalar kakin soja,tabo zahra hindatu tayi,saita matsar da hannunta ba tare data dubi zahran ko inda haidar din yake ba,don ta fuskanci abinda take nufi,sai tayi gaba hindatun na biye da ita.
Bata ankara ba taji hindatun na gaida haidar cikin wani salo,saidai bai amsa ba sai data sake magana karo na biyu sannan ya amsa ciki ciki da qyar kamar wanda aka tilasta.
Suna qarasa ficewa qofar gidan zahra ta kwashe da dariya
"Wai me hakan?" Hindatu ta tambaye ta tana dubanta
"Ai gwara da kika ga halinshi da idanunki,idan da gaya miki nayi ba lallai ki yarda ba" tsaki hindatu taja
"To sai me?,ni wallahi burgeni ma ya sakeyi"
"Au Allah?"
"Qwarai kuwa"
"To Allah ya taimaka" zahra ta fada tana dariya harta raka hindatun bakin 'yar qaramar motar da aka siya mata ta tasheta tabar layin,ita kuma ta koma ciki.
23/10/2021, 08:40 - 馃憤馃徎馃憤馃徎: 14
*OUM DUFAIL!!*
_GIDAN ADO 茦AWA DA KECE RAINI_馃拕馃拝馃徑
_OUM DUFAIL ta tanadar muku dukkan nau'in kayayyakin gyaran fata gashi dama jiki gaba daya ZAHIRINKI DA BA茒ININKI samfurin MAIDA TSOHUWA YARINYA_
*kayayyakinmu sune kamar haka*
FACE AND BODY SCRUB=2500(300ml)
Face and body mango butter=3k (250ml)
Face cream= 1800
Corretor oil/vitamin C oil=2k
Fairness skin lotion= 2500
Hot chocolate skin lotion 2500
Serum (for Nuckles )2k
Nuckles cream (stubborn)3500
Mix fruits Arabian black =soap 1800
Mix fruit glycerine soap =1900
Beetroot=1900
Coconut, milk,egg..face soap=1200
Lavender mix fruit soap =1800
Body wash =1500
cleanser=1600
Hair spray =700
Hair oil =1500
Hair relaxer =700
Hair butter 1700
Shampoo =1500
Breast=oil 2k powder 2k
Strech marks cream= 2k
Beetroot pink lips =700
Baby care soap glycerine=1k
Baby care butter =1500
Shea butter baby soap =700
Tsumin tula =2200
Tsumin zinariya =1200
Sliming tea =1500
Amarya set =25k
Liquid Arabian black soap =1900
Cleansing water =1500
*Ku dubamu a handle namu na Facebook da Instagram*
Ummu Dufail
*ko ta number wayarmu kamar haka*
07067943479
*_muna turawa kowacce jaha dake fadin nigeria da yardar Allah_*
*_INGANCI DA RAHUSA SHINE TAKENMU_*馃馃従馃馃従馃馃従
_____________________________
Za'a iya cewa abdulyasar ya samu shiga wajen zahra saboda halayen daya nuna,wadanda suka sanya tun tana dari dari dashi harta saki jikinta,saidai shi kansa yadan dauki lokaci kafin ya samu ta sake dashi,saboda tana ganin kamar za'a koma 'yar gidan jiya ne,saidai yadda yake kaffa kaffa da ita,da yadda yake nuna tsananin kishinsa a kanta,da kuma yanda yake yawan jan hankalinta kan rayuwa kamewa da kula da mutuncin kai yasa ya sake samun fada a wajenta.
Sau tari idan yaga wata halayya ta wasu yammatan yakan qalubalancesu,don hatta su hindatu sai daya so ya rabata dasu,saidai data zauna tayi masa bayani da kuma alfanun zamansu tare ta yadda zata ci gaba da nusashshesu yasa ya fahimta ya kuma haqura.
Ta nata fannin sosai take qoqari wajen ganin ta kyautata masa shima,saboda yadda ya damu da dukkan lamuranta,ta lura mutum ne maison cima mai dadi,saidai ba kowacce iri ba,hakan ya sanya duk sanda zaizo wajenta girki na musamman take masa,koda bazaizo bama,sau tari idan akwai kudi hannunta zata kirashi ranar taji abinda yafi sha'awar ci,shi zata dafa masa ya aiko a karba masa,ko yazo da kansa,yawanci yafison cimar gargajiya,kamar dambu,danwake,alala,wainar fulawa da sauransu wani lokaci harda dan malele,to koda su din zata masa,zata kashe kudi sosai ta qawata masa su,misali alala,na 'gwangwani baifi uku ba,zata zuba masa qwai wadatacce,hakanan wainar fulawa zata cika mata qwai,harka dinga jin kamar wainar qwai qwai,fulawa fulawa,kirkinsa da yadda ya samu fada wajen hajja saboda dabi'unsa yasa koda batayi niyyar yi ba hajja da kanta zatace tayi masa,da kudinta kuma,takance
"Abudulyassar akwai kirki akwai hankali,ai babu abinda ba za'a yiwa yaron nan ba,yana da nutsuwa da sanin ya kamata,ni ba abinda yake burgeni irin yadda yake tsaronki,kamar yadda yayanku haidar yakeyi".
Hatta fita siyan katin waya idan yaji tayi ranar babu zaman lafiya,ya dinga fushi kenan da ita,bare kuma ya kira sama da sau biyu yaji busy,alamun tana waya kenan,ya dinga mita da qorafi da binbini,tun bata saba ba har halayyarsa ta zama ba baquwa bace wajenta,abokai da na kusa da ita kance
"ki gode Allah,mai yiwuwa sauyi alkhairi ubangiji zai miki,shi yasa dama ya kore dukka wadancan ya kawo miki wannan".
Na biyu tana jin dadin aduk sanda tayi girkin ya tafi dashi gida yake cewa mama(mahaifiyarsa)taji dadinsa,harma wani lokaci yakan kirata ya bata maman su gaisa ta kuma yi mata godiya
(A baya nasa abdulyasar dan kaduna ne,afwan zamu canza mu barshi a dan kano ne saboda wasu dalilai da anan gaba zan fadesu).
Bata mantawa akwai wani lokaci da wasu 'yammata suka zo suka wucesu,sosai sunyiwa fuskarsu bleeching wanda koda yaro qarami yana kallonsu zai gane,tasan halinsa,don haka tayi sha'awar tsokanarsa
"Nima man nan xan fara shafawa fa.....dama duk cikinmu da muka tashi na fisu duhun fata,kaga nima saina fito washar abuna" fuska ya tamke sosai yana dubanta
"Zahra'u,kice min kawai lokacin rabuwarmu ne yayi" idanu ta fiddo tana boye dariyarta
"Kamar yaya?"
"Eh mana....,ai daga randa naga kalar fatarki ta canza,ko naga qibarki tafi yadda kike a yanzu,hakan na tabbatar min kina amfani da wasu magunguna kenan,todaga ranar bana jin alaqarmu zata ci gaba da wanzuwa" dariyarta ta sake,tana sake jinjinawa tsantseni irin na abdul yassar din,da kuma yadda yake kiyaye doka da qa'ida,da qoqarinsa na azata bisa turba kowanne lokaci
"Ka kwantar da hankalinka,nima duka irin wadan nan ababen basa birgeni sam,saboda dukka alqawari ne da shaidan yayi kan saiya batar da 'yan adam,ya sanyasu sun aikata hakan,Allah ya bamu labarin hakan cikin suratun nisa'i wato surar mata kenan,saboda ubangiji yasani cewa mu mukafi kowa saurin dulmiya daga kaidin shaidan,suratun nisa'i,aya ta dari da sha tara.
"Allahu akhbar"ya fada yana lumshe ido
"Shi yasa kowanne lokaci nake godewa Allah da ya bani ke,na dade daji a jikina tun sanda na soma ganinki nayi matar aure,kuma irin macen da kowanne namiji zaiyi burin mallaka" kafin ya sake cewa wani abu wayarsa ta dauki tsuwwa,ya ciro ya duba
"Eh ina wajenta....ok to" ya fada yana murmushi,ya maida wayar aljihunsa
"Auwal ne"
"Ayyah....dama kwana biyu baiyo rakiya ba"
"Wallahi....wasu 'yan sabgogi ne suka sanyashi gaba,kinsan mu talakawa saida nema" murmushi kawai tayi sukaci gaba da hira,auwal abokinsa ne sosai,wanda yawancin lokutta yana daukoshi suna zuwa tare.
Ba'a rufa minti ashirin ba auwal ya iso saman babur dinsa lifan
"Na fatima zahra,bada kanka a sare kaje gida kace ya fadi" ya fada yana dariya kana ya bashi hannu suka cafke,kana ya maida dubansa ga zahra
"Dama ai nasani,bazai wuce nan din ba....gaskiya fatima kin dace da masoyi na gaske,kowa yasan abdulyasar yasan ki,ba wanda baida labarinki,ya dagawa kowacce mace red card saboda ke,wai don Allah meye sirrin?" Murmushi tayi tana cewa
"Um um auwal banda ziga,irin wannan koda abokinka haka?,kada fa naga ba haka ba" dukka hannayensa ya daga sama
"A'ah....aini bana shakka....bana shakka kan maganata,ke kike shakka saboda bakiga yadda ya damu dake ba ya kuma damu da zancanki ba....amma lokaci yana nan zuwa da zaki yarda"
"To Allah ya nuna mana". Baifi minti goma suka qara ba auwal din ya daukeshi suka wuce.
Cikin haka watan azumi ya sake kamawa,shima yazo musu a sanda ASUU suke halin nasu,don haka wannan karon ma a gida sukeyin azumin.
Rana ta farko misalin qarfe biyu na rana,bayan zahran ta idar da sallar azahar,kusan tana idar da sallar azahar take fara girke girken shan ruwa ita da baba gaje,wanda ita baba gaje da haidar suke shan ruwa a nan,sai kuma su abba babba da duk ranar satin qarshe suma suke shan ruwa tare da mahaifiyarsu,ma'ana duk bayan kwana bakwai,to tare dasu ranar za'ayi girki,to yanzun ma da haidar din bai dawo gida ba iya su ukune girkin,amma hajjan takam fidda sadakar abincin mutum uku haka zuwa maqota ko biyr wadatacce da zai isheshi mutu yaci harma ya rage,bayan wanda akanyi a raba sadaka,ta nade abun sallarta ta fito falo,dai dai sanda taji hajjan na cewa gaje
"Tunda haidar bai dawo ba,lokaci lokaci a dinga saka sanwa da yaron nan abdulyasar" murmushi baba gaje tayi
"Hajja kina ji dai da yaron nan"
"To gaje....ai duk wanda zaiso naka ya gama maka komai"
"Gaskiya ne....wannan haka yake" ta amsa tana komawa zuwa kitchen,zahra kuma ta qaraso wajen hajjan
"Hajja,da kawai an qyaleshi,tunda kusa da gida yake,inda ace nesa ne shine"
"Kijimin 'ya da rashin son alkhairi,to banda ma lalacewa ta zamani,mu a yadda muka tashi mukaga iyayenmu da kakanninmu nayi,koda wucewa mutum yazo yi ya dan zauna ya huta a qofar gidansu yana da kwano ranar a cikin gidan,ko kwana nawa zaiyi a wajen,bare kuma surukin gida guda" jin zata mata tarere saita barta,tabi bayan baba gaje zuwa kitchen.
Sosai abdulyassar kuwa yake nuna yabawa da dawainiyar abincin,a haka har aka sallace azumin gaba daya,saidai ita abinda yake bata mamaki,duk da ba damuwa tayi da komai nasa ba,abdulyasar din ba gwanin kyauta bane,amma da sukayi maganar da salma sai tace
"Kada ki damu,wani haka yake,saikin shiga gidansa sannan zaki gane ba rowa bace,gwaji ne" da wannan ta share zancan.
Biyu ga salla gidansu ya cika da baqi,jikoki da yaran da aka aurar,cikinsu harda su salma yasira yusra hafsat,sai manyan yayyensu da suka dan jima da aure,anty alawiyya anty fiddausi da anty nusaiba,wadanda kowaccensu daga me yara hudu saimai biyar,dukkansu qannen ya haidar ne,anty nusaiba ce kawai ta bashi shekara daya da wata uku,mama tayi kwainika a tsakaninsu(gwarne inji wasu hausawan ko?馃槀),hakan ya sanya koda ka gansu ma ba zaka zaci ta girmeshi ba,duka saiya zama yayan kowa.
Itakam zahra ranta a bace yake,don gaba daya dinkunanta babu wanda telor dinta yayi mata,saboda rainin wayo ma data matsa sai yaran shagon sukace ya tafi ittikafi lagos,badon takai zuciyarta nesa ba a ranar su kansu yaran da sun sha ruwan zagi,Allah yasa tana da wasu kala hudu da maman hindatu ta dinka musu iri daya da hindatu ,dasu ta dinga amfani,amma ana ya gobe 'yan gidan nasu suzo,saboda wani dan qaramin taro suke ranar kowa zaizo,ta daga hankalinta,saboda akwai kayan da takeso sakawa a ciki,don haka ta shirya da safe da wuri ta iske hajja a falo.
Ita da haidar ne zaune,sai umaima 'yar abban tsakiya da nuratu dake gefe gaban tv suna goge kayansu,da alama suma su zasu saka yau ko goben da kowa zai hallara
"Ummm.....kaga 'yammatan gidan nan,wadan nan kayan na yaushe ne?" Da ido umaima ta mata nuni da sashen da haidar din ke zaune,don ita bata lura dashi ba,daga kai tayi ta dubi wajen,magana suke da hajja,hannunsa riqe da kudade,yayin da hajjan ke riqe da wata takarda wadda kamar list din sunayen mutane ne a jiki,ta kuma tabbatar da hakan sanda hajjan ke fadin sunayen yana irgo kudin yana miqa mata tana ninkesu,da alama su za'a baiwa kenan,saita yatsina fuska ta dawo da dubanta kan yaran,wato kowa indai da haidar a wajen baida sukuni?,for god sake zai dami kowa ne ahaan....
"Waye zai rakani amso dinki?" Duk sai sukayi matsa gefe
"Anya ko yaya zahra zaki samu dan rakiya yau,wallahi ya musty ne yace kowa ya shirya zai kaimu shoprite mu zabi abinda mukeso,daga nan mu wuce minjibir park" ta fada qasa qasa don kada haidar din yaji saita kama baki
"Yau ni ake qin rakawa?....to ai gobe ma rana ce" suna 'yar dariya suke cewa
"Ki haquri yaa zahra...Allah yace duk wanda yaje wani gun bazai jirashi ba" batace komai ba ta qarasa wajen hajja,a sannan har haidar din ya miqe,hannunsa empty,da alama ya rabar da kudinne gaba daya.
Fuskarta ba walwala ta gaidashi harda dan rusunawa kadan saboda idanun hajja,don ta fuskanci tun dag wancan lokacin ta sanya musu idanu,shi yasa take iya bakin qoqarinta na nuna mata cewa ta daina din kamar yadda tace,ya amsa a dake kamar yadda dabi'arsa take,bata damu ba ta dubi hajja
"Hajja...zanje na karbo dinkin nan,na samu guda daya"
"To...ba matsala....amma haidar ya saukemin ke,naga fita zakayi ko?" Tayi maganar tana dubanshi,ya amsa da eh ba tare daya daga kanshi daga matsa wayar da yakeyi ba
"Yauwa,ka sauketa da Allah,inaso ta dawo da wuri ta kitsemin kan nan nawa" ta fada masa sanda yake takawa yana barin falon,wani irin sak zahran tayi,ta buda baki zatayi magana yadda hajja ke kallonta yasa ta wayance
"Hajja santsin gashinki fa yasa kitso bai zama fa"
"Hakanan za'amin,bana son zama da tsefaffan kai"
Kai ta gyada kawai sannan tabi bayansa itama ta fice,hajja ta samu waje ta zauna,cikin ranta tana raya cewa yawan samun kusancinsu kamar haka me yiwuwa *SABANIN ALKIBLA* da rashin fahimtar dake tsakaninsu zai ragu ko yaya.
Sanda ta iskeshi a ma'ajiyar motoci har ya kunna motar,ta bude gidan baya ta zauna,a nutse ya waiwayo ya mata wani kallo daya sanyata tilas ta fito daga bayan ta dawo gaba,don ga fahimci manufar kallon nasa sarai.
Luff tayi cikin motar,wani irin qamshi mai taushi da sanyawa zukata nutsuwa ke tashi cikin motar,ga sanyin ac daya karade motar,shi kansa wani qamshi yake busowa kamar an zuba iskar wani abu,yayin da wani slow music ke tashi qasa qasa yadda bazai takura me sauraro ba.
Basuyi nisa ba wayarshi ta kama ringing,cikin wani sauti mai dadi,wayar ya janyo ya kara a kunnensa da hannu daya,yayin da daya hannun yaci gaba da tuqi dashi
"Ya akayi?" Ya fada da sauti mara amo
"Ok....ba damuwa....ganinan" ya fada yana aje wayar ba tare daya damu da kasheta ba,sannan ya sanya signal ya fada wani titin.
Da sauri zahra ta dubeshi,don ba titin da zatayi ba kenan,kwata kwata sun kauce hanya
"Ya haidar b....." Hannunsa ya daga mata alamun ta dakata ba tare daya waiwayo ya dubeta,a hankali ya gangara gefan titin,sannan yace
"Sauka" still idanunsa na kallon gaban motar,da mamaki ta kalleshi,ta kalli titin da suke kai,indai tace anan zata samu abun hawa zataci wahala koda kuwa ace ba bikin sallah ake ba,saboda titin ya baude sosai da hanyarta,saita kau da kanta daga duban data masa,shuru ya ratsa motar na sakan goma,sannan ya tasheta yaci gaba da tafiyarsa hankali kwance.
Basuyi nisa ba suka tsaya qofar wani gini,wanda baiyi kama da gida ba,yafi kama da qawatacciyar ma'aikata,parking yayi da kyau,sannan ya buda murfin motar yayi ficewarsa,ta bishi da kallo har aka bude masa qofar ya shiga.
Ajiyar zuciya ta saki ranta na baci sanda ta kalli agogon hannunta taga ta kwashi minti talatin zaune a motar babu shi babu dalilinsa,Saita fara neman abinda zata rage zaman kadaicin dashi,tunda ta baro wayarta a gida,a tunanin yanzu yanzu zataje ta dawo.
Aljihun gabar motarsa ta bude,duk da zuciyarta na gargadarta da aikata hakan,tana budewa wani dan qaramin littafi mai adon zaiba ya fado,yana da 蓷an nauyi kadan,saita daukeshi daga qasa,har zata maida sai taji ya dauki hankalinta,don haka ta tsaya ta bude.
Shafin farko ne kawai ke dauke da wasu kyawawan rubutu,wanda ajiki akayi magana mara tsaho kamar haka
_Abune mai matuqar ciwo ne a rayuwa rashin masoyi ko kuma wanda yake qaunarka,zaka yita tunawa cewa yayi maka nisa,kullum idan rana ta fito ta fadi ya maka nisan da babu masaniyar ranar da zaka taddoshi,sannu a hankali saika soma manta yanayin murya dariya ko murmushinsa,kome yawan damuwarka ba zata taba dawo maka da shi ba,amma sai zuciyarka ta kasa gasgata hakan,kayita hasashe da fatan zai dawo gareka_
Yaa zahra ce ta fado mata a rai,tasan tabbas kalamanta ne,da ita yake,hakanan sai taji jikinta yayi sanyi,kalamai ne marasa yawa amma masu ratsa zuciya,saita samu kanta da sake maimaita rubutun.
Tana tsaka da maimaita rubutun taji tsaiwar mutum a kanta saitin window din da take,aliyyu ne tsaye,harde da hannayensa a qirji yana dubanta,kwarjininsa da tsoro yasa ta diririce,ta soma qoqarin maida littafin inda yake,sai taga kawai ya miqo mata hannu,ba musu ta sanya masa littafin a hannun nasa a sanyaye,sai kuma taga ya bude murfin sit dinta,da idanu ya mata alamun ta fito,a sanyaye ta fito cike da tsoron me zai mata,tana tsaye ya zagaya ya shiga nashi sit din,ya sanya hannu ya rufe daya murfin bayan ya rufe nasa,sannan ya kunna motar yaja yana barin wajen,zahran ta bishi da kallon mamaki har sai daya fice daga layin.
Ginin daya fito daga ciki tabi da kallo,haushi da takaici na cikata,koma me ya mata hajjan ce ta jawo mata,inda ta qyaleta ina ruwan biri da gada?,ta hau napep asirinta a rufe ya kaita ya dawo da ita,yanzu gashi nan ya jawo mata bankada tana zaman zamanta,haka ta dinga takawa da qafafunta har ta isa titi,saidai acan ma sai data dan sha wuya kafin ta samu abun hawa,kasancewar garin kano kan cika ya tumbatsa da baqi a duk yayin da ake shagulgulan bikin sallah,hakan yakan sabbaba cinkoso da rashin samun abun hawa akan kari.
Ranta a bace ta isa shagon,abinda yadan sanyaya mata raima taje ta taras ya gama mata duka dinkunan,tana amsa tayo gida,saidai batayi niyyar gayawa hajja ba sam bare tace wani abu da zai sake dagula mata lissafi.
*********** **** ********
*_BANKA茒A_*
_abun 蓳oye!_
A hankali take takowa daga cikin gidan zuwa qofar gida sanye da doguwar riga marron mai sulbi,duk da ba kwalliya tayi ba amma tayi mata kyau sosai,hakanan jikinta na fidda wani qamshi mai aji da tsayawa a rai.
Abdulrashid ke kiranta,wanda tasan da zuwansa dama,tunda jiyo yazo harta zuba mishi bincin salla da sukeyi,wanda a tsarin gidan kwana uku akeyi ana abincin sallah,ran salla washegari da wata washegarin,ya shaida mata gobe zaiyi tafiya,an kirashi wani aiki me muhimmanci,amma kafin ya wuce zai biyo suyi sallama.
A tsaye ta sameshi ya bata baya,goye da jakar matafiya,ya waiwayo fuskarsa fadade da fara'a yana amsa sallamarta
"Wai har ka gama shirin?" Agogonsa ya duba
"Wallahi,ni suke ma jira abokan tafiyar fa,bazan iya tafiya bane saina zo na ganki".
Murmushi tayi,sosai takejin dadin yadda yake bata kulawa
"To ai gani" ta amsa masa tana murmushi,kafin ya bata amsa wayarsa ta sake tsuwwa,ya cirota daga aljihunsa ya daga
"Ok....gani,ganinan ai nace" maida wayar yayi yana cewa
"Fatima,tafiya zanyi saina dawo,banajin zan wuce sati daya kacal"
"To Allah ya tsare hanya....am na manta,bari na shiga na dauko ma saqo minti daya" tuni ya soma tattakawa
"Jirana ake fatima afwan....amma da mun dauki hanya zan kiraki in sha Allah,daga nan har zuwa 12 na dare ki jirani" kai ta gyada
"To shikenan,Allah ya tsare hanya,ya dawo daku lafiya"
"Amin na gode" ya fada yana takawa da sassarfa,ita kuma ta juya zuwa cikin gida.....
Masu karatu
*AL茦IBLARSU!*馃毝馃従鈥嶁檧锔忦煔娥煆锯€嶁檧锔忦煔娥煆锯€嶁檧锔忦煔娥煆锯€嶁檧锔忦煔娥煆锯€嶁檧锔忦煔娥煆锯€嶁檧锔忦煔娥煆锯€嶁檧锔忦煔娥煆锯€嶁檧锔忦煔娥煆锯€嶁檧锔忦煔娥煆锯€嶁檧锔忦煔娥煆锯€嶁檧锔�
23/10/2021, 08:40 - 馃憤馃徎馃憤馃徎: 15
*_ina 'yan uwa musulmai masu kishin addinin islama???_*
*_maza ku matso ga wani aikin lada ya samu_*
*_茒anku kuma dan uwanku kuma qaninku wato ABDURRAHMAN,yaro mai hazaqa gami da kwadayin haddace littafin Allah mai tsarki,ya bude YOUTUBE CHANNEL nashi na qashin kansa,ku tallafa masa ta hanyar shiga wannan shudin rubutun ku danna masa subscribe,ba abunda xai rageku dashi saima samun dimbin lada dalilin KARFAFA MASA GWIWA,MUN GODE 馃檹馃徑馃檹馃徑馃檹馃徑_*
馃憞馃徑馃憞馃徑馃憞馃徑馃憞馃徑馃憞馃徑馃憞馃徑馃憞馃徑馃憞馃徑馃憞馃徑
https://youtu.be/WWIGq5Jbtb0
Tana komawa cikin gida shirin kwanciya tayi saboda a gajiye take yau din,duk da tana son zuwa susha hira da hafsat wadda tazo dazun,zata kuma kwana har uku,saboda me gidan nata wata tafiya ta kamashi,da qyar kuwa ya haidar ya barta saida yaji daga bakin mijin nata,sun yiyyi baqi yau din sosai,bata zauna ba hakan yasa ta gaji da yawa.
Sai data kwanta sannan ta kira hafsat tace karta jirata,tayi kwanciyarta gobe da sassafe zata shigo ta tasheta
"Ba komai wuron hajja,Allah ya kaimu"
"Aha" tace tana datse kiran.
Tana sane da maganar da sukayi da abdulyassar din kan ta jirashi zai kirata,tasan kuma tsaf bacci zai iya daukarta,don haka sai kawai taja laptop dinta 'yar qarama da abban gwammaja ya siya mata ta kunna,ta zabo daya daga cikin fina finan ciki ta kunna ta soma kalla.
Tun tana cijewa tana kallon har idanunta sukayi nauyi,batasan sadda bacci ya dauketa ba.
Sanda ta farka da sauri ta jawo waya tana dubawa,a zatonta zata samu miscal din abdulyasar din,babu miscal babu kuma saqo,ta kalli agogo,sha biyu na dare har da rabi,kenan ya saba lokacin da yace zaiyi kiran nata?,hakanan sai taji idanunta ya bushe,baccin yayi nasa guri,saita miqe ta shiga bandaki ta daura alwala,ta dawo ta tada salla.
Ta kusa kaiwa qarfe biyu saura na dare tana zaune saman abun sallahn,har bacci ya sake dibanta taji qarar wayartata,saita miqa hannu ta dauko wayar,idanunta ya sauka kan agogon qarfe biyu da rabi na dare,ga mamakinta lawal ne abokin abdulyassar yake kiran,sosai hakan ya bata mamaki,wata mummunar faduwar gaba ta ziyarceta har batasan sanda ta daga wayar ba.
Muryar lawal dince ta bayyana cikin tsantsar tashin hankali yake fadin
"Zahra....abdul ya mutu,abdul ya rasu,qarfe sha biyu na dare yayi hatsari a hanyarsa ta tafiya,Allah yayi masa cikawa a take" dif wuta ta dauke mata,saita daina jin abinda lawal din yake fada,sai wata qara dake ratsa kunnenta kamar an buga qarfe da qarfe,ita dai batasan mintinan data shafe a haka ba,batasan kuma sanda lawal ya katse nashi kiran ba,batasan yadda akai ta kai kanta dakin hajja ba,sai ganinta tayi ta fada saman hajjan tana wani irin numfashi.
A matuqar firgice hajjan ta miqe ta zauna,don dama bata jima da gama sallar dare ba ta koma ta kwanta
"Zahra'u....zahra'u!....mene ne?,innalillahi wa inna ilaihi raji'un,yi kuka....kiyi kuka zahra'u,barshi ya fito" ta fada taba danne mata qirji,ganin yadda yake sama da qasa numfashinta kuma na wahalar shaqa,cikin ikon Allah ta fusgo numfashin da qarfi sai kuma ta saki wani qaqqarfan kuka ta fada jikin hajja gaba daya ta qanqameta
"Innalillahi" hajja keta maimaitawa,cikin ikon Allah itama zahran saita kama,tsayin wasu mintuna masu tsaho sannan ta iya magana cikin sheshsheqar kuka
"Hajja.....abudul....yassar ya.....mutu,yayi hatsari baya.....n nyabar wajena,ya rasu hajja!" Ta qarashe cikin gunjin kuka.
Sosai hankalin hajjan ya tashi,ta sake qara qarfin salatinta tana kuma maimatawa,wannan dare ya zamewa zahra dare mai tsaho duhu da kuma qunci,haka suka zauna ita kuka hajja lallashi,kafin gari yakai ga wayewa tuni idanunta suka suntuma suka kumbure,qwayar idanunta dukka sun shige ciki.
Suna idar da sallar asuba hajjan ta daga waya ta kira abba yusuf,saboda abba babba baya gari,cikin lokaci qanqani ya iso,bayan su gaisa ta shaida masa zancan rasuwar
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" shima ya dinga maimaitawa
"Yanzu abinda za'ayi....inaga idan gari ya sake shaaa,ka bawa mustapha ko shamsu muqulli sukaita gidansu yaron,don hankalinta bazai taba kwanciya ba,ba zata zauna ba,in yaso idan ya dawo daga kaitan zuwa lokacin mu mun kintsa saiya miqa mu,idan mukaje saimu duka mu dawo tare,ku kuma ko zuwa yamma haka zuwa dare kwa leqa ku yiwa iyayensa maza ta'aziyya"
"To shikenan,Allah yayi masa rahama,yasa ya huta".
Da qyar hajja ta sanyata tayi wanka,ta shirya cikin doguwar riga da hijabi,duk wanda ya ganta saiya tausaya mata,saboda yadda gaba daya fuskarta ta sauya saboda kuka,ga wani irin ciwon kai daya saukar mata lokaci daya,har dan zazzabi zazzabi takeji.
Kafin su tafi saiga hafsat ta fito itama a shirye,hajja zatayi qorafin ta koma tace da ita
"Ba za'a barta ta tafi daga ita saisu umaima yara ba,na kirashi na gaya masa mutuwar,nace zan rakata yace babu damuwa"
"Khalas....shikenan" hajja ta fada sanda hafsat din ta shige motar,shamsu ya tayar da motar suka fice.
Ko a cikin motar ma dai kukan take yaqi tsaya mata,ta dora kanta saman kafadar hafsat tana shashsheqa
"Kiyi haquri zahra ki masa addu'a,a yanzu ita yafi buqata"
"Shikenan hafsa...shima ya tafi ya barni,hafsat nice mutum ta qarshe da yazo wajenta,nice mutum ta qarshe daya kira da wayarsa,ashe da yazo bankwana yazo yimin?,ashe ya tafi kenan?" Sosai ta karyarwa da hafsat zuciya,haka taci gaba da lallashinta har suka isa qofar gidan su abdulyasar da taimakon kwatance da lawal ya dinga musu.
Babu kowa qofar gidan sai daidaikin mutane,da alama an tafi kaishi makwancinsa na gaskiya,hafsat din ita ta riqe zahra har zuwa cikin gidan.
Cike gidan yake da mutane,wasu kuka wasu tagumi,hafsat ce mai qarfin halin gaidasu,sannan ta tambayi inda hajiyan abdulyassar din take,aka nuna musu wani falo dake cike da jama'a suka nufi can.
Kana kallonta zaka gane mamansa ce saboda suna kama,tana zaune saman kujera,sanye da ash din hijabi da carbi a hannunta tana ja.
Gabanta suka samu suka isa,zahran ta zube a gabanta hafsa ta zauna gefanta,hafsat ce ta fara yi mata ta'a ziyya sannan zahra cikin shaqewar murya,daga bisani hafsa tace
"Zahra ce hajiya" hafsan ta zaci zataga wani alamu na nuna kulawa ko sanayyar sanin sunan,babu wani alamu na ta gane abinda hafsan ke fada,tadai ce
"Allah sarki,mun gode Allah ya bada lada".
Zaman shuru ne yaci gaba da wanzuwa a falon,zahra na cikin hijabinta tana kuka,ganin yadda falon ke sake cika yasa hafsan ta sama musu wajen zama daga waje,abinda ta lura dashi har suka tashi hajiyan ma bata lura da tashin nasu ba,zataso tambayar zahran cewa anya sunsanta kuwa?,to amma yanayin da a yanzu take ciki ba lokaci bane na mata wannan tambayar ba.
Awa kusan guda kenan da zamansu a wajen zahra ga dubi hafsa
"Hafsa qishirwa nakeji,bazan kuma iya shan komaj cikin gidan nan ba"
"To muje waje mana mu samu wani shop ko lemo kisha" kai ta kada
"Ruwanma ya wadatar" ta fada tana miqewa da qyar
"Wash kaina" ta fada sanda ta miqe din
"Lafiya?" Hafsa ta tambayeta,saita dan ya mutsa fuska
"Mtsweww,kaina ke ciwo"
"Dole ai,wannan kukan da kikayi ai ba kadan bane"da haka suka taka zuwa wajen gidan.
A yanzun layin a dinke yake da jama'a,da alama har sun dawo kenan,haka yasa sabuwar qwalla suka zirarowa zahra,yanzu haka abdul nacan kwance,nacan kwance qasan qasa,babu kowa saishi kadai,babu kowa sai halayyarsa da ayyukansa.
"Zahra duka shagunan layin nan a rufe suke" taji hafsat na fada,kai ta gyada tana share hawayen fuskarta
"Eh na gani,amma layin nan kamar layin gidansu rabi'ah ishaq ko?,da kika tana rakoni?"
"Eh tabbas,aiga gidan nasu can ma qarshen layi"
"Yauwa,mu qarasa nasha ruwan a can kawai"
"Ok" hafsat ta fada,kai tsaye suka miqe zuwa gaba,wanda gidan ke jerin gidajen dake jikin gidansi abdulyasar din,tsakaninsu da gidansu abdulyasar din gida biyar ne kacal.
Da sallama suka shiga gidan,wata mace dake duqe bakin fanfo tana wanki ta daga kai tana amsa musu sallamar
"Ku qaraso mana" ta fada tana dagowa daga duqen da tayi.
Gaidata sukayi sannan suka shaida mata su din qawayen rabi'ah ne
"Ayyah,kuma gashi bata dade ta fita ba wallahi"murmushin qarfin hali zahra tayi
"Babu komai,dama ruwa muka shigo zamu sha_ta qarashe maganar ta duqawa kamar wadda zatayi ruku'u saboda yadda kanta keci gaba da sara mata
"To babu damuwa,bari A kawo muku" saita yi gaba daga can qarshen tsakar gidan,ta bude wani fridge dan qarami dake qasan rumfa tana cewa
"Hala daga gidan rasuwar gidan su abdul kuke?" Hafsat ce ta amsa mata
"Eh wallahi" cikin nuna jimami da alhini ta sake cewa sanda take ciro ruwan
"Ai mun tashi da tashin hankali yau,mutuwar matashi yaro,babban abun tausayin ma,yau satinsa biyu cif da kai kudin aure....." Kalma mafi girma da muni data daki zuciya da kunnuwan zahra,kalmar da taji kamar a wani mugun mafarki aka furtata,kafin ta dawo hayyacinta sautin muryar hafsat cike da zallar mamaki ta furta
"Sati biyu da kai kudin aurensa?"amsa musu tayi sanda take rufe fridge din tana dawowa zuwa garesu
"Wallahi Allah,bari kawai....daxun yarinyar da ya kaiwa kudin tazo,abun gwanin ban tausayi,bakiga kukan da take ba,tana faduwa ana dagata,dukkanmu sai data sanyamu qwalla,sai data sake saka hajiyarsa kuka sosai,qarshe kasa zama tayi sai gida aka maidata,kinga keyholder din kai kudin akan window na ma,ni ko amfani da ita bankai ga yi ba" qarashen maganar yazo dai dai da zamewar zahra daga durquson da tayi zuwa zama dabas a qasa
"La haula wala quwwata illa billah" kawai zahran ke fada cikin zuciyarta,bakinta zuwa maqogaronta ya sake bushewa raqayau kamar bata taba kurbar maqwarwa daya ta ruwa ba tunda Allah ya halicceta,tana jin sanda matar ke miqo ruwan amma saita kasa amsa,maimakon karba ma saita miqe tsaye kawai ta nufi qofa,bataga wani sauran amfanin zamanta ba kuma,tana jiyo hafsa na mata godiya gami da sallama.
Tuni ta miqi hanya ba tare dako waiwaye ba,ita kanta hafsat din sai cimmata tayi a hanyar
"Zahra....da kin tsaya ya shamsu ya dawo ya maidamu" kaita girgixa idanunta na sauka kan gungun abokan abdulyasar dake zaune qasan wata rumfa,can ta hango auwal a tsakiyarsu,wani abu ya caki zuciyarta,tsanar auwal din ta kamata,tabbas babu shakka yasan komai,yasan duk abinda ke wakana tunda amininsa ne,dashi aka hada baki,dashi aka rufeta
"Muje kawai hafsa,ma hadu a hanya" a yanayin data ga ta shiga,tasan cewa koda bayani tayi mata babu lallai ta fahinta,don haka taci gaba da binta a baya suna tafe zafin rana na dukansu.
Basuyi nisa ba suka soma jin hirar wasu mata biyu a bayansu
"Kai mutuwa....mutuwa masu gari,babu ruwanta da babba ko yaro,tsoho ko tsohuwa kawai dauka take"
"Hmmm....kedai Allah yasa mu dace,mutuwa ma irin wannan ta abdul ai tafi ratsa jiki da daga hankali,mutuwar saurayi?,sati biyu kacal da kai kudin aure ashe ba za'ayi auren ba,babu ma abu mafi tausayi irin yarinyar daya kaiwa kudin,kamar zata shide wallahi abun tausayi"
"Ai da tausayi,Allah yasa mu cika da imani".
Cak zahran da hafsan duka suka tsaya,a sace zahra ya waiwaya ta dubesu,dukkansu babu wanda tasan fuskarsa a cikinsu,suna tsaye sukazo suka giftasu,da alama ma basu ankara da tsaiwarsu ba,sukayi gaba suna ci gaba da hirarsu.
A zafafe zahra ta soma takawa tana koma zuwa layin da suka baro,hafsa ta cafki hannunta
"Ina zaki?"
"Zanyi magana da auwal" daga haka ta zame hannunta ta koma.
Suna nan inda ta barsu,harda qarin wasu abokan nashi wadanda yakanje dasu lokaci zuwa lokaci,dukkansu tasan fuskarsu sunsan fuskarta.
Auwal din ne ya soma ganinta,saiya miqe,kafin ya tarbota harta iso wajen,cikin tsananin nuna jimami yace
"Sannu zahra....ashe kin iso,ya mukaji da wannan abu daya samemu?" Dukka sauran abokan sai suka soma yunqurin yi mata gaisuwa,a qalla sunkusa su biyar,hankalinta ta maida kan auwal
"Zuwa nayi na maka godiya kan zalunci da munafuntata da kukayi,na gode sosai,ubangiji ya saka da alkhairi" cikin yanayi na rudewa ya soma magana
"Munafuntata kamar ya?" Tana ji a ranta baqincikin da datake ji ba zata iya rufeshi ba
"Da kun gayamin kai da abdulyassar ban dace dashi ba,da kun gayamin yakai kudin aure...dana fahinceku na kuma rabu dashi ta sauqi bawai ta irin wannan hanyar ba".
Sai auwal din ya dora hannu saman ka yana cewa
"Kai innalillahi,Allah ya tsinewa munafuki.....wai mutum ma na qarqashin qasa,ko awanni biyu bai cika ba amma ba zasu bar gawarshi ta huta ba....to duk wanda ma ya gaya miki qarya yake,kawai 'yan hada husuma ne wadanda basaso a zauna lafiya,masu zuwa lahira da qoqon dambu....ko ba haka bane mansir?" Ya fada yana maida dubansa ga daya abokin nasa wanda daga auwal din sai shi a wadanda abdulyassar din yafi zuwa dasu
"Haka yake....hakane auwal"
"Baya ga key holder din dana gani!" Ta fada a zafafe
"Au....wannan fa friends ne suka hada suna tsokanarsa saboda yadda sukaga ya tsani yarinyar....just for fun akayishi,shine mutane suka sauya zancan?"
"Dakata!" Ta fada da sauri tana daga masa hannu ganin yanason raina mata hankali
"Dukkan abinda bawa ya shuka shi zai girba,kaje....na barku da Allah" da haka ta juya ta soma barin wajen,tana ji abokan nasa na qwala mata kira hankali tashe,saidai babu wanda ta waiwaya ta kalla bare ta koma,saima ta tsaida musu napep ta haye hafsat tabi bayanta.
Wani yawu mai tauri take hadewa cikin motar,gaba daya ji take zuciyarta ta bushe ta qeqashe,lamarin maza ya fice mata fit a ka,me yasa ne basu da *AL茦IBLA?* me yasa kowanne da kalar zaluncinsa ga 'ya mace?,saboda muna da rauni?,saboda ba zamu iya aurar da kanmu ba saidai a auremu?,me yasa mazan zamanin nan suka zama fitina ga rayuwar 'ya'ya mata?,me yasa duk wani bala'i,shiga ha'ula'i da tashin hankalin mace mafi akasari kan 蓷a namiji ne?,baki auren ba baki huta ba,kinyi auren baki huta ba,sai yaushe diya mace zata hutama ranta?,ba a iya kanta ba,akan mata 'yan uwanta da yawa taga irin hakan,me yasa suka maidashi kamar anko ko gasa,sun maidashi abun kwalliya,YAUDARA!....shin basa tunani ne?,basa tunanin cewa suna wataran iyayen wasu ne?,basa tsoro da fargabar kada abinda sukayi a fanshe kan diyoyinsu wadanda basuji ba basu gani ba?,inda ta godewa Allah....babu wanda ta saidawa mutuncinta,babu wanda yayi nasarar tarwatsa mutuncinta,yau inda acw ta aikata hakan ta tabbatar nadama da dana sanin da take ciki ta zarta ta yanzu,sai Allah yasa bata watsar da tarbiyyarta ba,bata bari rudi da zaqin soyayya ya jata ta aikata babban kuskure mai tarwatsa rayuwa ba,kuskuren da bashi gyaruwa har abada, yanzu kam takai qarshe.....takai maqura,enought is enough....ta dauki iya abinda zata iya dauka,ya isa haka!,ya isa!......
Ire iren wadan nan tunane tunane su ta dinga yi har suka qaraso gida,wanda ko tsaiwa a biya mai napep din kudinsa batayi ba,batasan ya suka qarke da hafsat ba.
A falo ta tadda hajja tana karyawa,bata bi ta kanta ba ta wuce dakinta da wani irin sassarfa,gaban mudubi ta tsaya,ta cire hijabi ta kuma cire doguwar rigar jikinta,daga ita sai vest da under wear,kanta take qarewa kallo lungu da saqo,sai a sannan kukan ya qwace mata,da gudunsa kuwa kukan yazo,kukan da zaka tabbatar da cewa yana fita ne daga tsakiyar zuciya,yana kuma tafe da wani irin qunci da baqinciki
"Me na rasa?,meye bani dashi?,meye illata!,ku gayamin!" Ta fada a fili hawaye na gudu tana kuma tambayar kanta da kanta.
Ji tayi an rungumeta,hajjanta ce
"Me haka zahra'u?,ki nutsu mana,kita maimaita Allahumma ajirni fi musibaty,wa akhlifni kairan min ha" da muryar kuka ta kama addu'ar tana ta maimaitawa har ta soma samun nutsuwa,don haka hajjan ta zaunar da ita gefan gadon tana shafa bayanta kadan kadan tana tayata nanata addu'ar.
*_wajen daya kamata a tsaya mu fafata kan wanda yafi iya yaudara cikin samarin nan uku yayi,da kuma matakin daya kamata budurwa ta dauka idan ta samu kanta cikin irin wannan situation din,idan kuna da buqata ku sanar min domin bude grp musamman saboda haka,karku manta,dama munce akwai fafatawa da tattaunawa kan mai zafi kan kowanne littafi,ma'assalam_*
23/10/2021, 08:41 - 馃憤馃徎馃憤馃徎: 16
*KIJI TSORON ALLAH鈽濔煆锯槤馃従鈽濔煆锯槤馃従,kada ki dauka ko kiyi amfani da kayan da ba naki bane,ba kuma mallakinki bane!*
A hankali aka turo qofar dakin,hafsat ce jiki a matuqar sanyaye,idanunta kan zahran,zuwa sannan kukan da takeyi ya ragu sai ajiyar zuciya
"Zahra.....sawwama nason magana dake,tana falo"
"Sawwama?" Ta tambaya tana kallon hafsat
"Eh sawwama ta layin shago tara" ta ganeta,duk da babu alaqa tsakaninsu,saidai gaisuwar mutuci saboda babu tazara sosai tsakanin unguwanninsu
"Lafiya?" Zahran ta tambayi hafsan tana kallon yadda yanayin fuskarta ta sauya fiye da dazu
"Daga gaisuwar gidansu abdulyassar take" shuru tayi yana juya maganar,to meye ya faru?,saita miqe kawai kai tsaye ta fice zuwa falon.
Kallo daya ta yiwa sawwaman tasan cewa lallai tasha kuka itama ba na wasa ba,gaba daya idanunta sun tasa har lebunanta,zahran ta qarasa a hankali ta zauna gefan sawwaman
"Ashe kema kinsan abdulyasar?" Kai ta iya jinjinawa kawai ba tare da tace komai ba,saboda wano ciwo dake taso mata a qirji
"Ashe bani kadai bace?....bani kadai ya yiwa haka ba?" Maganar da taja hankalin zahra kenan da ta daga kai ta dubi sawwaman,kallon da take mata yake nuna tana da buqatar qarin bayani
"Abdul yayimin alqawarin aure....infact ma yau sati daya da tura magabatansa gidanmu,amma abun mamaki sai nakejin yau sati biyu dakai kudinsa wajen wata walida....baya ga haka ashe kema...." Hannu ta dagawa sawwama murmushin takaici na fita daga fuskar zahran,a take wasu kalamai da abdul din yake yawan gaya mata suka dinga dawo mata aka tar kamar a sannan yake furta mata su
"Duk duniya akwai wata bayan ke?,duk duniya akwai wata diya mace data isa ta rabani dake?,me kike fargaba a kaina?,akwai wata mace data isa na bata lokacina akanta na tafi zance wajenta idan bake ba.....zahra duk kyan mace....duk ajinta....duk gayunta saidai tabi bayanki"
"Duk abinda kika fada haka ne....hakane sawwama" kuka sawwaman ta fashe dashi,wanda da alama zallar baqinciki da bacin rai yake cin zuciyarta
"Abdul ya cuceni,ya zalunceni...abdul..." Da sauri hajja data fito tace
"Kiy shuru karki sake cewa komai,kuyi haquri ku masa addu'ar Allah ya yafe masa kuskuren daya tafka" miqewa zahra tayi ta koma daki don ba zata iya ci gaba da tattauna wannan maganar ba,hajja da hafsat sune suka sallami sawwama.
A ranar ko kusa ko alama bacci bai gitta ta ba bare ya samu nasarar daukarta ba,duk juyin da zatayin abdul din take tunawa,kalamansa da salon yadda yaso sabuleta daga rayuwarta ta wata siga mai masifar ciwo,shima so yayi yayi mata irin yadda nasir da nuraddeen sukayi mata?,so yayi ya karya mata zuciya?,yayi gutsi gutsi da ita?,don ta tabbatar a yadda ta bawa soyayyar abdulyasar amanna da Allah ya barshi da ransa hakan ya faru babu tantama zata iya rasa lafiyar zuciya,saita goge hawayenta ta miqe ta zauna tana gayawa kanta,wala'alla Allah ne ya sota da rahama ya daukeshi,ubangiji baiyi zataga wannan baqinciki da bacin ran da tashin hankalin ba,amma lallai ta yanke tsammani,hakanan ta debe haso daga dukkan lamarin maza,abun ba qarami bane,sha'aninsu ya wuce tunaninta.
Kwanyarta tana iya tuna mata sanda abdulyasar din yake musanyan waya da ita,ya aje mata wayarsa yacw ta bashi tata aga wanda yafi gaskiya a cikinsu,aga wanda saurayi ko budurwa zasu kira,ashe a sannan wala'alla sabon layi kenan yake sakawa?,ko layin da ba'a sanshi dashi ba?.
Sannan tana iya tuna sanda yakan rufeta da masifa cikin zallar kishi,yana cin alwashin duk randa yaga wani ya kulata ko ta tsaya dashi,ba shakka saiya masa diban karen mahaukaciya ya sadashi da qasa ya take wuyansa,kome zai faru indai a kanta ne saidai ya faru,tana iya tuna sanda yake tsaidata ya rakata makaranta ko wani guri da kansa,tana iya tuna sanda fafur ya hanata shiga kasuwa,ashe duk bogi ce?,qarya ce?,ashe bayan ita hadda sawwama wadda yakai magabatansa?,anya ko magabatan gaske ne bana haya bane?,anya kuwa bana bogi bane?,saboda babu iyayen arziqin da zasuje maka maganar aure wannan satin,wani satin kuma suje maka gidan su wata da saninsu,to bayan ita da sawwama mata nawa ya yaudara?,wannan Allah ne kawai masani.
Cikin daren ta yiwa kanta da kanta fada,ta gayawa kanta cewa da batasan abdulyasar ba,kafinshi kuma wasu sun yaudareta,ta kuma ci gaba da rayuwarta ba tare da komai ya sameta koya sauya ba,hakanan a yanzun ma zataci gaba da rayuwa babu shi,zata dora daga inda ta tsaya,ba zata bari damuwar wanda baisan da damuwarta ta dameta ba,damuwar wanda baya doron duniyar ma gaba daya,kai koda yana raye.....dukkan namijin da zai miki haka bai cancanci ki damu kanki saboda shi ba,saboda ya nunawa duniya cewa u r a zero behind decimal point,baki da wani amfani a tare dashi,keda babu duka daya,don me zaki damu da irin wadan nan?,me yasa irin wannan namijin zaki dora damuwarki a kanshi?,a daren,a kuma sannan ta yiwa kanta alaqawarin cire dukkan damuwar wani abun banza namijin daya yaudareta,ta kuma dasawa kanta takunkumin tserewa soyayya da kuma nisantarta bakin iyawarta,har sai taga abinda ya turewa buzu nadi,ko kuma abinda alqalamin qaddararta ya rubuta ya tabbata.
Sosai hajja tayi mamaki washegari da taga sakewa a tare da zahran,wanda sam batayi tsammamin ganin hakan tattare da ita ba,bata tanka mata ba sai taci gaba da biye mata,can qasan ranta tausayin zahran yana ratsata,duk inda ta gifta sai ta bita da kallo,haqiqa ta hadu da jarrabawa mai tsauri da wahala,amma kullum fatanta ya zama nasara ce a rayuwarta.
A irin hakan zahran ta lura da kallon da hajjan ke mata,ta fahimceta sarai,amma sai tayi murmushi
"Wai ya kiketa kallona tsohuwa?,kodai na miki kyau ne?" Kai hajjan ta gyada sannan tace
"Ina miki fata da addu'ar wannan ya zama karonki na qarshe da zaki sake fuskantar qalubale irin wannan kaf rayuwarki" saita rausayar dakai kawai,cikin zuciyarta tana amsa da amin.
Wannan karon ma umminta kasa jurewa tayi sai data titsiyeta
"Innawuro.....ki gayamin gaskiya idan akwai wani abu a qasa...."
"Wallahi ummi bansan komai ba,bansan meke faruwa ba" shuru ummin ta danyi na wasu mintina,sannan a sanyaye tace
"Kin tabbatar ba saida musu mutuncinki kike ba?" Sosai maganar tayi ma ummin kanta nauyi da zahran,saidai ya zamana dole ta yiwa zahran wannan tambayar,saboda uwa bai kamata a muhallin irin wannan da kike bincike da qwaqwwafi ba ki dinga boye wasu maganganun,wai don kawai kunya da nauyinsu,kan zahran a qasa tana fitar da qwalla tace
"Allah ya tsareni ummi,ubangiji ya tsare miki ni,kuma har abada bana fatan ya bani ikon ko damar da zata sanya nayi fatali da tarbiyyar da kuka gine ni a kanta,wallahi wallahi koda tunanin aikata hakan bai taba zuwa kaina ba bare na aikata ummi,ki yarda da 'yarki" nannauyar ajiyar zuciya ta sauke
"Na yarda dake.....ba kuma wai ina zarginki bane,amma ya zama dole nayi aikina na uwa na bincika da kyau,na tabbatar addu'ar da kullum ba dare ba rana da nake miki keda 'yar uwarki dama sauran dukkan yaran dake gidan nan ba zata fadi qasa banza ba,na yarda jarabtace kamar yadda take rubuce a rayuwar kowanne musulmi.....kici gaba da addu'a,kada dimuwa ko zafin jarrabawa yasa ki kasa cin ribar haqurinki....karbi wannan" ta fada taba miqa mata wata doguwar takarda,addu'o'ine a rubuce a cikinta,addu'o'i ingantattu masu ma'ana,wanda suke dauke da kalmomi masu girma da tsarki gami da kambama ubangiji,wadanda su kadai sun isa sanya nutsuwa a zuciyar bawa da samun biyan buqata daga wajen ubangijin talikai.
Godiya ta yiwa ummin sannan ta baro sashen,tun a ranar sata soma addu'o'in ta dinga jin sukuni da nutsuwa yana ratsata,ta sake jin zuciyarta wasai kuma fes,haqiqa ubangiji yayi gaskiya da yace ku saurara,da ambaton Allah kawai zukata suke samun nutsuwa,lallai babu abinda yakai ambaton ubangiji sanya nutsuwa a zuciyar mai damuwa.
Cikin satin ta hada kayanta ta koma bakin karatunta,tunda komai ya daidaita an koma makaranta,ta kuma fuskanci karatunta da kyau,ta watsar da duk wani damuwa da hayaniyar soyayya,babu wani da namiji da take tsaiwa ta kalla sau biyu ma bare ta saurari kalaman bakinsa,duk ta musu kudin goro gaba dayansu.
*_BAYAN WANI LOKACI_*
Zaune take cikin dakin kwanan dalibai wanda ya zama mallakinsu ita da hindatu batula da jannah,yayin da nadiya da farida suke daki daya daura da nasu suda wasu mutum biyun,to amma idan baka sani ba zaka zaci dukkansu daki guda suke,saboda kusan komai a nan dakinsu zahran sukeyi,hatta da abinci daya sukeyi,duk da basi fiya ma girma abinci ba,saidai suyo takeaway,idan kaga girkakken abinci to aikin zahra ne,sau tari sukan mata qorafin tana walahar da kanta da wani girki,ta bari kawai suyo takeaway suci,takan ce
"Ni ban saba bafa,abincin da zaka girka da kanka yafi albarka,sannan kayan anincin da nazo dasu daga gida saina jibgesu su lalace?,ko kuma na maidasu gida idan an tambayeni nace qawaye suna siya min ina ci?" To su dinma idan ta dafa kowa dafifi yake wajen ci,saboda ita din ba baya bace wajen iya girki.
Kamar yau dinma dakin nasu cike yake da hayaniyar 'yammata,kasancewar suna cikin ranakun qarshen mako ne,kuma wannan karon kusan dukkaninsu basuje gida weekend ba,ita zahra saboda CA da zasu fara,kuma a satin zasuyi kusan gudan hudu,shi yasa taga gwara ta zauna waje guda tayi karatu sosai.
Yau dinma ita ta dafa musu abincin,kowa yaci ya qoshi,da suka kammala saita taja takardunta da system dinta saman gadonta ta barsu nan tsakar dakin kan carfet din da suka malale dakin dashi
"Yar allazi boko" taji su suna tsokanarta,bata kulasu ba sai murmushi kawai datayi taci gaba da karatunta,batason ta tsaya tankasu su dauke mata hankalinta,suma sukanyi karatun,amma saidai baiko kai nata ba,sukance sun gaji basu iyawa,da sun taba iya yadda zasu iya suke ajewa su shiga sabgarsu.
Yanzun ma hira suke masu charting nayi,harda qawayen su batula daga wani dakin,ana tsaka da haka taji mardiyya qawae farida ta luqa ashar
"Ferry....zoki gani....maza maza zo kiga" da sauri farida ta aje tata wayar ta matso kusa da mardiyya,saita zare glass din fuskarta,da qarfi ta furta
"What.....muhsin ne fa,wata fa naga ya dora yana furta kalaman soyayya a qasan pic dinta,kan bala'i" saita fada tana dauko wayarta da sauri tana duba wajen status dinta
"Zo kiga,ni bai nuna ajerin nawa status din ba,babu status dinsa" dariya wata rabi'ah dake zaune kusa dasu tayi,ta tashi ta zauna tana cewa
"Wai baku gane meke faruwa bane,ai na taba gaya miki farida tun kwanaki kika qi yarda,kinzo kina wani jin kin isa kinkai,wai waye ya gaya miki ma cewa a yanzu ana cika baki kan namiji?,ai wannan lokacin ya wuce,lokacin cika baki da alfahari,da basu amanna dari bisa dari.....everybody listen to me" ta fada tana gyara zamanta sosai a tsakiyarsu tare da miqe qafafunta,hakanan maganar da rabi'ah din ta soma fada ta dauki hankalin zahra,bata sauke littafin hannunta ba amma hankalinta na kanta
"Luggar mazan yanzu.....zasu iya yin budurwa dari ko dubu ta watsapp....kuma zasu iya dora hotonta a status...amma kuma,duk sanda zasu dora hoton daya,tofa zasu cire dukkan sauran su sanyasu a jerin wadanda a ranar ba zasuga status dinsu ba,ba zasu ciresu ba har sai hoton yayi disappering,ko kuma ranar naki pic din zasu saka,saisu cilla waccar cikin inda suka ciroki ke kuma a fito dake,donki gani,kiji dadi,ki kuma qara amanna dasu...so dukka abun bugene,duk ta yadda suka biyo miki ki bi musu ta haka,kada ku saurara kunji....kuyita musu yadda suke muku kawai,dakun samu na dauka ku dauka ku watsar dasu" ta qarasa fada tana sheqewa da dariya.
Maganar status din ta baiwa zahra mamaki,wato kullum sabon salo suke fiddawa?,saidai fatan samun shiriya,amma kuma zancan gogayya da samari barkatai sam shawarar batayi mata ba,saita tabe bakinta kawai taci gaba da karatunta,gefe guda hayaniyarsu tana cika mata kunne,da Allah ya taimaketa zuwa wani lokaci suka fara raguwa da kadan kadan,har dakin ya rage daga ita sai hindatu wadda ta haye gado ta kwanta zata dan rage bacci a cewarta kafin ta tashi tayi karatu.
Turo qofar dakin da aka sakeyi da qarfi yasa zahra dagowa tana fatan ba sune suka sake dawowa ba,basu din bane yanzun jannah ce,sanye da straight gown da hill shoes,sai qaramar hand bag da qaramin mayafi data nade wuyanta dashi,kusan shigarta kenan wanda kusan kullum sai sunyi rigima da zahra akan haka.
Yau din fuskarta sam babu alamun walwala,gefan gadonta ta samu ta zube tana zare mayafin kanta cikin masifa take magana
"Ni hisham zaiwa haka?,ni zaiwa wannan akuyancin?" Hindatu dake kwance bacci ya fara dibarta ta daga kai tana dubanta
"Ke kuma meya hadaki da hisham din naki yau?" Iska ta furzar daga bakinta sannan ta zame 'yar hular dake kanta ta sabule takalminta ta zauna sosai saman gadon tana harde hannayenta
"Yau ni hisham zai fito qarara yacemin nayi haquri da maganar aurenmu....shi matarsa ta gida ta isheshi" sosai hindatun ta tashi ta zauna
"Hisham din da kansa da bakinsa?" Kai ta jinjina cikin tsananin jin zafi
"Shi din fa....shi yasa ya kasa zuwa ya gaida dad,ko mami ma danace yaje cewa yayi wasu shirye shirye yakeson ya kammala tukunna...."dauke kanta hindatu tayi zuwa sashen da zahra ke zaune
"Kinji fa zahra?" Saita ture littafinta gefe
"Naji" ta fada tana saukowa daga saman gadonta,ta daura dankwali sannan ta fita zuwa toilet,mintina kadan ta dawo ta samesu suna tattaunawa,ta koma bakin gadonta ta zauna sannan ta dubi jannah.
"A inda kullum muke fada dake kenan fadan gaskiya....ita kuma gaskiya daci gareta,hakanan fure take bata 'ya'ya,ita kuma rayuwa duk abinda ka shuka shi zaka girba,ba zaka taba shuka qaya ba kace inibi kakeson cira,jannah.....na dade ina miki nuni da waye hisham,illa da dafin dake tattare dashi,hisham yayi amfani da son da kike masa yayi fooling naki,ya kuma yi amfani da damarsa a kanki,a yanzu ya gaji dake ne shi yasa ya fito miki ta wannan hanyar kai tsaye,don ya ajjiyeki ya kuma lalubi wata mai tsautsayin me qaramin tunanin....kiyi haquri da harsh word da nake amfani dasu a kanki,kawai ni duk inda gaskiya irin wannan tazo gittawa ta gabana saina fadeta,abinda yasa na kira dame qaramin tunani shine....babu ta yadda wanda yakeson ya aureki ki zame masa uwar yaransa kuma mace ta gari abar alfahari ya daukeki cikin motarsa yana yawo dake,ya daukeki ba cikin gidanku ba,ba gaban iyayenki ba,ku hadu a wani waje ya saki gaban mota kuna yawo,yaje ya killace 'yarsa,yaje ya killace matarsa,yaje ya killace mamarsa....amma kefa?,saboda baki da wani daraja,baki da wani matsayi da za'a baki,shi yasa bai dauki hakan a bakin komai ba,daga sanda wanda yace miki yana son aurenki yazo miki da magana kan matarsa qazama ce,matarsa bata iya soyayya ba,matarsa yar qauye ce,kece kika iya komai,matarsa ta gaza ta kowanne fanni,amma kuma ko yaushe yana nanuqe dake,yana fasa miki kai,ta wani sashen kuma a dabarance yana qoqarin ku dinga hulda ta hada jiki romance da kissess amma kuma ko sau daya bai taba tunanin kiyi aure ba,ke koda ya taba tunanin hakan ko furtawa toba shakka na yaudara ne,daga sannan kuma kin samu babbar matsala,a haka da kike yawo dashi janna,cikin irin wannan shigar da wannan rayuwar kike tunanin zaya daukeki yakai gidansa a matsayin matar aure?,me zaya killace?,me zai burgeshi har yakai ga aikata hakan?,bakayi haka bama da sautayi a wannan zamanin ya kuka qarke dashi bare ace kinyi?,ni na isheki manuniya da ishara,kafin kice hisham ya yaudareki ya kamata ki fara cewa kin yaudari kanki,idan maganata ta miki zafi jannah kiyi haquri"sosai taga yadda jikinta yayi masifar sanyi,saita kasa cewa komai,sai dogon nazari da tunani data fada,bama ita kadai ba har hindatu dake kwance.
********** ******** ********
*_茦ADDARA....ta riga fata_*
Cikin sati sunyi CA sa yawa kamar yadda ta zata tun wancan satin,to satin gaba ma kusan akwai sauran tarin karatuttuka,hakan ya sanya kowacce ta sake haqura da zuwa gida weekend,saidai kuma sun shirya zuwa daya daga cikin masaukan baqi hotel don su huta a can a cewarsu.
Sanda suke shirya tafiyar zahra na zaune tana jinsu bata tanka ba,tadai yanke idan sun tafin gida zata wuce ko kwana guda ne ta rage ta dawo.
Saida suka gama hayaniyar yadda zasu gudanar da ranakun qarshen makon sannan suka soma raguwa sannan hindatu ta iso kusa da zahra ta zauna
"Amini....ko sau daya baki taba karar binmu bafa" kallonta tayi
"Ko sha'awa wajen banayi,me zai kaini nikam,kuma ina mamakin yadda kuka maida wajen kamar ba'a bakin komai ba zuwanshi" dariya sosai hindatu tayi
"Kinga,mufa mutanenmu ne suka yiwa wajen mummunan fassara,amma a qa'ida wajene da iyali ma suke iya zuwa su kama daki suyi dukka iya kwanakin da sukeso,su huta daga hayaniyar gida data jama'a,ni kusan duk qarshen wata bazan manta ba kafin nakai haka,sannan abubuwa basu yiwa daddy yawa ba muna zuwa muyi kwana biyu haka ko uku,ba wani abu bane me muni,saidai idan mutum dama da mummunar niyyarsa yaje,don Allah kizo muje wannan karon,sau daya dai tak" kai zahran ta girgiza
"Naji bayananki,amma am sorry bazan iya zuwa ba hindatu saikun dawo" ranta ta bata da alamun bataji dadi ba
"Shikenan....tunda baki yarda dani ba,komai kika fadamin ina qoqarin yi dabi,bana tsallakewa shawararki saboda nina aminta dake....na gode,dama sunatamin dariyar cewa ni kadai na damu dake,yau na gasgata hakan" saita sauka daga gefan gadon ta koma nata tana hada kayan da zasu je dasu.
Ganin yadda harta gama hada kayan bata kalleta ba dakin shuru yasa taji duk babu dadi,ba kaifi hindatun tana daukar duka shawarin zahran da qoqarin ganin tayi abinda zahran keso,da gaske taji haushinta kenan sosai,har ta isa bakin qofa zata fita zahran ta kira sunanta
"Haushi kikaji kenan?" Kafada ta daga
"Saboda me?,bayan baki yarda dani ba?,akanme zan takuraki kiyi abinda baki niyya ba" kaita kada tana murmushi
"Zanje....shikenan ko?" Cikin murna ta dawo
"Na gode sosai....ina mai tabbatar miki zakiji dadin tafiyar da zamuyi,gobe da kanki zaki ce muje" murmushi kawai tayi ba tare da tace komai ba.
23/10/2021, 08:41 - 馃憤馃徎馃憤馃徎: 17
*KIJI TSORON ALLAH 鈽濔煆锯槤馃従鈽濔煆�,karki taba kayan da ba naki ba ba kuma mallakinki bane*
茦arfe hudu na yammacin ranar suka dunguma su shidda cikin motar gidansu hindatun suka tafi.
茒aya daga cikin tsadaddu kuma qawatattun hotel sukayi masauki,suka kama daki guda babba wanda zai ishesu a wadace,itakam tana zaune daga gefe tana kallonsu yadda suka sake tamkar suna cikin gida ko cikin makaranta,ita kam har cikin ranta bata jin wani walwala ko karsashi ko kuma wani jin dadin zuwa wajen,sai take ji acikin zuciyarta duka wani irin babu dadi,sai takejin kamar ta aikata wani mummunan abu mara kyau,haka kawai takejin babu dadi har qasan ranta,har sai da farida ta ankara da haka
"Ki sake mana haba zahra,mu kadai ne fa a dakin,babu wanda yake shigo mana ko ya isa ya shigo" murmushi kawai ta musu,sai tabi lafiyar lafiyayyen gadon dake dakin tayi kwanciyarta akai,don kafin su fito tasha karatu sosai,tana son ta huta kafin ta sake dora wani,don ta taho da dukka litattafanta,har suna tsokanarta cewa ba hutawa zataje yi ba kenan,tunda ba zata bar qwaqwalwarta ta huta ba.
Suna ta hayaniya da walwalarsu har zuwa sanda akayi knocking qofar aka kawo musu abincin dare,kowa ya fara diban nasa duk da cewa akwai sauran lokaci kafin ma ayi sallar magariba din,hindatu ce ta dubi zahran
"Zahra....ga abinci,ki sauko kowa nacin nasa" kaita kada tana hamma
"Kai a'ah,sai an idar da sallah" daga haka ta sake gyara kwanciyarta,tun tana jin hirarrakinsu sama sama har ta fara daina jiyosu,babu jimawa kuwa bacci mai nauyi ya debeta.
Sanda ta farka hindatu ce kawai tayi saura a dakin,tana niyyar saukowa daga gadon tana duba agogo,qarfe bakwai da ashirin na dare,inda Allah ya taimaketa tana hutun sallah
"Duka ina suka shiga?" Ta jefawa hindatun tambayar wadda ke tsaye gaban madubi tana gyara sumarta da mayukan gyaran kai
"Duk sun fice,amma sun kusa dawowa"
"Fita kuma?,nan duka bai ishesu yawo ba?" Ta sake tambayar hindatun
"Nan kusa da inda muke nefa,aka bude wani sabon wajen cin abinci daxun,to na wani abokin farida ne,shine ya gayyacesu" baki kawai ta tabe,ba shakka duk inda wayewa tayi yawa matsala ce,su a wajensun wannan normal ne,ba wani abu bane,amma a asalin tarbiyyar malam bahaushe wannan din mummunar illa ce,saita miqe ta shiga toilet ta canza pad ta kuma daura alwala ta dawo ta zauna bakin gadon tana karanto azkar dinta na maraice da bata samu damar karantowa ba,tana yi tana duban hindatu daketa shiri da alama fita zatayi,batace mata komai ba har sai data ga ta daga waya tayi magana na 'yan mintuna ta aje,ta dauki mayafinta tana yafawa
"Ina kuma zaki kema?" Waiwaya tayi tana duban zahran
"Waya zamuje siya nida mudassir a glass show,minti talatin ta isa munje mun dawo" sosai zahran ta hade fuska
"Yanzu kina ganin kamata ce ki fita da saurayi takwas saura na dare siyan waya?,cikin motarsa daga ke saishi?"
"Babu komai qawata kada ki damu,ko a gida dana sanarwa mommy muke tafiya" maganar ta ratsata,batasan illar boko xallah ba sai yanxu,gaba daya duk wani abu daya kamata a kalleshi amatsayin abun qyama suba hakan bane a wajensu saboda rashin tasirin ilimin addini,saita miqe ta isa inda hindatun ke tsaye.
"Hindatu,a koda yaushe inason ki dinga tuna cewa kina rayuwa ne a qasar hausa,ina son ki dinga tuna cewa qa'ida da kwaikwayo kan tafarkin addini shine gaba da komai,na miki uzurin rashin tashi kan irin nawa bigiren,wala'alla har a zuciyarki ba komai bane hakan,amma idan baki sani ba bari na gaya miki illar.....akwai babbar illa a wajen 'ya mace ko ince ganganci wajen shiga motar wani da namiji,nasha maimaita miki wannan maganar....abinda yasa na nace mata shine,shiga motar da namiji ki yadda ya tuqaki shine mafarin komai,shine sila da dalili na faruwar komai,komai zai iya faruwa,idan nace komai ciki harda rasa budurcinki gaba daya....." Idanu hindatun ta qwalalo
"Ki yarda dani qawa.....wallahi ban taba zina ba,ban taba bada kaina ba" murmushi zahra tayi ta dafa kafadarta
"Haba hindatu....ta yaya zan miki wannan mummunan qazafin,amma idan kin kubuta daga zargina sauran mutane fa,kin isa ki wanke kanki?,akwai abubuwan da zaka dinga aikatawa da zasu iya ja maka mummunan zargi da zato daga mutane,zargi mai wuyar wanke kai,irin wannan rayuwar,ku kunsan bakwa wani mummunan aikin,amma shaidar da mutane zasu muku itace ku bana gari bane,idan kin shiga motarsa komai bai faru ba zaki iya kubuta daga riqe miki hannu da zaiyi?,zaki iya kare kanki daga yunqurin miki kiss ko runguma?,idan yaso cutar dake kin isa ki bawa kanki kariya?,sannan kome ya miki baki da hujja,laifinki ne,ke kika kai kanki hindatu" sosai jikinta yayi sanyi,ta daga kai tana duban zahran
"Gaskiya kika gayamin qawata,na kuma fahimta maganarki,sannan na gode miki qwarai da gaske,ban dauki hakan a wata babbar tawaya ba sai da kika nusashsheni,in sha Allah irin hakan ba zata sake faruwa ba" ta qarashe maganar tana cire mayafinta,sannan ta dauki wayarta ta tura masa tex ta koma ta zauna.
Daya daga cikin halayen hindatun da suke burge zahra kenan,sauqin kai da kuma saurin daukan shawara.
Tana zama saiga sauran suna shigowa,kafin kace me sun sake hautsina dakin
"Kai....kai jama'a,ku bakwa gajiya dan Allah da hayaniya?" Inji zahra da suka hana kunnuwanta sakat,dariya suka saka gaba daya jannah tace
"Kamar yadda baki gajiya da karatu ba" saita saki murmushi kawai tana gyada kai,tasan me hali dai bazai fasa halinsa ba.
***** ***** ****** *****
Washegari a daki dukka suka yini a tare,saidai da yammaci lis suka shirya dukkansu domin zuwa siyayyan kayayyakin amfani da kuma kallon wani sabon hausa film da za'a haska a film house cinema dake ado bayero mall.
Fir tace ba zata bisu ba,hakanan idan suka jima basu dawo ba saidai suzo suga ta tafi,basu ji dadi ba,saboda sunce ba jimawa zasuyi ba,hakanan bai kyautu su barta ita kadai ba,amma tace sam itadai sai sun dawo,hasalima akwai sauran karatunta da bata qarashe ba,haka suka shirya suke fice a motar jannah.
Karatunta taci gaba dayi,lokaci lokaci tana kallon tv dake aiki,saidai ba'a jima ba taji zaman ya gundireta,shuru hakanan babu kowa ba motsin kowa,don haka ta aje littafin tana duba agogo,dab ake da kiran sallar magariba,koda ta fita bata da matsala,tunda tana fashin sallah,don haka ta dauki mayafin doguwar rigarta ta yane kanta,sannan ta zira plate din takalminta daya dace da kayan jikinta,ta buda dakin ta fito.
A sama suke,saidai akwai qawatacciya kuma doguwar baranda ta bayan dakunan wadda zaka iya hangen farfajiyar hotel din idan ka tsaya ta jikinta,hakanan wanda yake qasa shima zai iya ganinka idan kaso,anan din ta tsaya,tana kallon yadda mutane ke kai kawo cikin hotel din kowa na sabgar gabansa,wanda yawanci duk wanda zai shigo ko ya fita cikin mota yake,da kadan da kadan take kallon wajen tana kuma karantar wasu abubuwa masu tarin yawa.
A qalla ta shafe kusan minti ashirin tsaye a haka har duhu yadan fara yi sannan taji tsaiwar ta soma isarta,saita janye idanunta da niyyar juyawa tabar wajen,saidai caraf idanun nata suka fada kansa.
Matashin saurayine fari sol,ma'abocin tsaho hakanan baida jiki,mai yalwar baqar sumar kai da kuma qasumba,sanyw da qananun kaya yana kuma tsaye jikin motarsa idanunsa fes bisa kanta,tsaki taja mai qarfi data lura da irin kallon qurilla da yake mata,ranta yana quna,tana fadi a ranta,wama yasan adadin lokacin da ya shafe yana kallonta bata sani ba.
Koda ta koma daki bandaki ta shiga ta sauya audugar jikinta,sannan ta dawo ta fesawa hannuwanta da jikinta turare ta koma kan karatunta,tanayi tana duba lokaci,saidai har yanzu babu su hindatun babu alamarsu,ranta ya soma baci,ta soma jin haushin kanta kan me yasa ta biyosu?,bayan gaba daya tsarin rayuwarsu ma ba daya bane?,yanzu meye amfanin zamanta a nan?,saita dauki wayarta ta soma kira.
Saidai duk wadda ta kira din tana shiga tana kuma ringing amma ba'a dagawa,babu kuma amsa,haka ta qaraci kiransu gaba dayansu babu wanda ya daga,zuwa sannan tara da rabi na dare agogo ke nuna mata,ga yunwa tana ji,duk da sun gaya mata taje tayi order din abinci a reception idan tana da buqata kowanne iri ne,to batason fita shi yasa bata karbo ba,ga wayar dakinsun daxu ta samu matsala bare ta kira daga daki a kawo mata,zuwa yanzu kuma yunwa takeji bata wasa ba,hakan yasa ya zame mata tilas ta fita ta karbo din kenan,saita sake tashi ta gyara yafenta ta kuma fito daga dakin.
Cikin tuqi mai cike da nutsuwa ya sako kai farfajiyar hotel din,hannunsa daya yana tuqin dashi,yayin da daya hannun yake amsa wayar cikin nuna girmamawa ga ubangidansa da gazo gani cikin hotel din,wanda ganawa ce ta sirri da zasuyi dashi gabanin taron qasa sa za'a gabatar na dukka ma'aikatan tsaro na qasa,kama daga sojojin sama dana qasa dana ruwa gaba daya,yanzun yana amsar direction ne na daki da inda zai ganshi,har ya qaraso wurin ajiyar motoci sannan ya ida wayar yana mai cewa
"Yes sir!" Sannan ya sauke wayar daga kunnenshi ya kasheta gaba daya,ya janyo aljihun motar ya zurata,sannan ya zauna na wasu mintuna yana karantar yanayin wajen a matsayinsa na qwararren jami'in tsaro,sai daya tabbatar komai na wajen yayi masa sannan ya bude murfin motar ya fito.
Duk wanda ya kalleshi saiya kuma,duk da cewa babu wata alama da zata nuna maka yanayin aikinsa,amma shigar da yayi da wasu shegun qananun kaya masu kyau da aji sun amsheshi,takawa yake zuwa reception cikin wata tafiya me cike da kuzari mazantaka da kuma karsashi,hannunsa daya riqe da key din motarsa,daya hannun kuma wata 'yar mitsitsiyar waya ce da yake iya rumtseta a tafin hannunsa guda daya.
Yana magana da daya daga cikin receptionist din sanda ta qarasa saukowa,a nutse itama ta tsaya saitin daya ma'aikacin wajen tana gaya masa abinda ya sauko da ita.
Cak ya tsaya da maganar da yakeyi,a hankali ya juya kanshi zuwa sashen da yakejin muryar na fitowa,daidai sanda itama qamshin turaren da take tsammanin ta sanshi,a kuma cikin gidansu ya soma shiga hancinta,har kuma yaja hankalinta zuwa ga kallon gefanta.
Ido hudu sukayi,cikin matuqar tsoro da razani taja baya tana kallon cikin idanunsa,yayin da shima ya kafeta da idanun yana mata wani kallo daya sanya taji kamar an maida qafafunta sama ne kanta kuma a qasa,tashin hankali da gigita suka bayyana tun daga zuciyarta zuwa saman fuskarta.
*_kuyi manage don Allah,yau nayi busy_*
23/10/2021, 08:41 - 馃憤馃徎馃憤馃徎: 18
_*YERWA INCENSE & MORE**_
_(The scents with diff essence for YOU& your HOME)_
_(MASARAUTAR KAMSHI)_
_Ina masu neman kayayyakin kamshi yan nahiyar ketaran chadi da Senegal? Kai harma da ingataccen had鈥檌 yan bornu? To ku matso domin nesa tazo kusa..._
_YERWA INCENSE & MORE: Sun zo muku da kayayyakin turaruka kamar haka:_
_Khumra kowacce Iri._
_Turarukan Wuta_
_Mopping khumrah_
_Washing khumrah_
_Bathing khumrah_
_body mist_
_kullaccam_
_scented hair cream/spray_
_wardrobe balls_
_carpet spray_
_air-fresheners_
_scented pebbles_
_body sprays_
_oil perfumes_
_Perfumes_
_kabbasa_
_burners_
_coal igniter_
_tong_
_kasko_
_kujerar tsugunno_
_english coal_
_dilke&halwa set_
_scented body mist_
_kai dama sauran kayayyakin da bamu ambata ba, YERWA INCENSE AND MORE, Na tura kayayyakin su ko鈥檌na a fadin Nigeria da ketare. Domin tuntubar su. Suna instagram: _@yerwaincense_and_more. Ko _Facebook site:YERWA _COLLECTIONs. Ko a duba su ta number su: ___08095215215/09044191709! _
_suna bada kayan su kan sari ko sayi dai-鈥榙ai_
_______________________________
Da wani irin zafi ya soma takawa inda take tsayen,tamkar ma ya manta da cewa gap din dake tsakaninsu ba wani me yawa bane,itama sai tayi yunqurin ja da baya,wanda hakan yasa yakai mata cafka da zafinsa,ya samu nasarar riqe singalalin hannunta,abinda ya sake rudata kenan ta sake daburcewa,tsoro ya kuma cikata,yayin daya bude baki cikin wata tsawa
"Me ya kawoki nan!" Ya fada da dakakkiyar murya mai qarfin amo da sauti,irin ta sojan daya saba karba da bada umarni a fagen daga.
Yadda dai daikun mutane suka juyo suna kallonsu ya ankarar dashi,saiya sake mata hannun nata da sauri,fuskarsa na gauraye da wani irin bacin rai,ya zare muqullim motar daya maida aljihunsa ya cilla mata,ya kuwa sauka saman qafafunta,duk da taji zafin amma ba shine a gabanta ba,tashin hankalin dake a gaba take hararowa,tasan cewa abinda zai biyo baha din ba dan qarami bane,ta kuma fahimta me yake nufi,don haka ga duqa ta dauki key din ta fara takawa tana ficewa daga wajen kamar kazar da qwai ya fashewa a ciki.
Sai data fice sannan yabi bayanta ba tare daya tsaya amsar number dakin da yake nema din ba,tana gaba yana bayanta amma ba zaka zaci tare suke ba har ta isa bakin motar,daidai lokacin matashin da tun dazun yake dawafi cikin hotel din yana nemanta tare da burin sake ganinta ya hangeta,don haka da sauri sauri ya sauko a nufosu idanunshi a kansu,yana ganin sanda haidar ya fisge muqullin ya buda motar ta shiga baya ta zauna.
Sai daya tabbatar ta shiga sannan ya sanyawa motar lock,duk da ya dage dukkan gilasan motar bakan baisa yayi tunanin kunna mata ac koya rage wani glass din ba don iska ta shigo mata.
Yana zare key din yaji an dafe hannunsa,ya daga kai a nutse don ganin waye
"Me haka kake?,zaka kama yarinya ka rufe cikin mota saboda me?" Wani banzan kallo haidar din ya kafeshi dashi,cikin ransa yana tambayar kansa da kansa shi din waye?,sosai ransa ke tafasa baiso ya huce masa laifin da bashi ya aikata ba,amma kuma yanajin wani sabon bacin ran na taso masa dangane da rainin hankalin da yakeson zuwar masa dashi,shi waye nata da zai qalubalanceshi kan hakan?,ya santa ne?,shi ya kawota?,ko tare suka zo?.
Zare key din yayi ba tare daya sake bi ta kansa koya dubeshi ba,ya juya ya soma takawa zaibar wajen saurayin ya mara masa baya yana ci gaba da cewa
"Malam ka budeta nace tun kafin ka gano kuskurenka.....bakasan waye ni ba ko?" Ya fada cikin zafi dason nuna nashi qarfin qwanjin.
Wani irin juyowa haidar din yayi a zafafe har hana take masa rabin qafa da ingarman takalminsa
"Idan kaci gaba da bina kana min wannan 蓳a蓳atun sai na saka kayi nadama kai da banzan matsayinka,kuma zaka gane kuskuren aikatamin hakan kafin ni na gane nawa kuskuren,stay awa frm me tun ban rugurguza kwanyarka" tabbas ya hangi wani strong abu cikin idanunsa,ya kuma hangi yadda yake furta maganar bilhaqqi,ya kuma tabbatar ba'a banza yake magana kan yarinyar with confidence haka ba,amma a amtsayin da mahaifinsa keda shi a nigeria yafi qarfin wani da baisan ma ko waye ba ya gaya masa magana irin haka ya qyale ba,don haka zai jira yaga yadda za'ayi ya fita daga hotel din ya kulle 'yar mutane cikin mota
"Zan gani ta yadda zaka fita daga wannan ginin" ya furta sanda haidar ke komawa zuwa ciki,sai daya sake bi ta reception aka gaya masa dakin sannan ya wuce.
A nutse ya bude dakin da sallama a bakinsa,mutumin wanda a qalla ya kusa shekara hamsin da biyar ya amsa mishi,yana zaune saman kujera riqe da jarida yana dubawa,koda ba'a gaya maka ba shima kasan cewa soja ne,irin wanda ya jima cikin harkar bautawa qasa da bawa rayukan al'umma tsaro.
Fuskarsa dauke murmushi dake nuna kulawa da qauna yace
"Barka da zuwa aliyyu" qyam ya tsaya ya sara mishi kamar yadda sojoji keyi don nuna girmamawa ga manyansu,ya karba gaisuwar yana nuna mishi wajen zama.
Da kansa ya tashi ya nufi fridge na dakin ya daukowa zaki abun sha,yana mitar
"Bansan ina haisam ya shiga ba....almost one hour daga zaiyi waya" ya qarashe maganar yana miqa haidar drinks din,wanda ya miqe yasa hannnu ya amsa yana cewa
"Thank you sir"
"U r welcome" ya amsa mishi yana murmushi,suka zauna a tare.
Saida Aliyyun ya soma shan lemon sannan suka soma maganar daya sanya ya kirashin,general hamza adamu gusau kenan,mutum mai kirki qwarai da tausayin na qasa dashi,kusan shi ya zama kamar role model na aliyyu,saboda yadda yake da hazaqa da gaskiya riqon amana da aiki tuquru,yana son aliyyu sosai,hakanan yana mu'amalantarsa kamar dan cikinsa,saboda yadda Aliyyun keda jajircewa sadaukantaka gaskiya riqon amana da rashin tsoro,duk wani abu na ci gaba yakanyi qoqarin kawo aliyyun ya sakashi agaba,tun matsayinsa baikai wajen bama,hakan ya sanya cikin qaramin lokaci ya dinga samun qarin girma har zuwa matsayin da aliyyun yake kai a yanzun,yana samun kulawa da horaswa ta musamman daga wajen general hamza din,hakan yasa Aliyyun ya zama gagara badau,kuma qwararren soja daya iya aikinsa ya kuma san me yakeyi,dalili kenan da yasa su kansu sukeji dashi,domin kamar sun horeshi ne yazo ya kuma fisu qwarewa da sanin dabarun aiki kala daban daban,don haka ko ame akace akwai haidar din a ciki basa haufi.
Sunyi nisa da tattaunawar da sukeyi akayi kncoking,general ya bada umarni sannan aka turo aka shigo.
Daga kai aliyyu yayi daga duba wani map da daddy ya bashi kamar yadda yake kiransa yana amsa sallamar,idanunsa ya sauka kan saurayin,sun gane juna fes,sai kowanne ya daure fuskarsa,aliyyun yaci gaba da duba map din saurayin kuma ya qaraso ciki lokacin da daddy hamza ke cewa
"Daga ina haka?,kusan awanni biyu?" Shafo kansa yayi yana cewa
"Am sorry dad....wani abune ya tsaidani,but am back ai" kai ya jinjina yana nuna masa haidar
"Da daya yarona nan,Aliyyu mas'ood dabo" da sauri ya cira kai yana duban aliyyun,saboda koda fuskarshi boyayya ce to sunansa sananne ne a kunnuwa mutane ciki harda shi,bare ya jima yana jin sunan a bakin baban nasa,da kuma yadda yake ji da haidar din
"Ku gaisa mana haisam" yayi maganar yana maida kallonsa ga aliyyun,wanda ya aje takardar hannunsa saboda girmamawa ga daddyn ya miqe tsaye,yayin da haisam din shima ya tako inda aliyyun yake ya miqa masa hannu,shima miqa masa yayi sukayi musabaha,murya can qasa haisam din yace
"Nice to meet you!" Kai kawai haidar din ya kada masa yana zame hannunsa daga na haisam din ya koma ya zauna.
"Ka ganshi nan,yaqi aikin soja,yafison kasuwanci" inji daddy yana nuna haisam da baki,fuskar aliyyu ce kawai tadan motsa alamun murmushi yayi,sam hankalinsa shi bai wajen,Ya qagauta ma su gama maganar da zasuyin yabar wajen.
Sai daya qara kusan wata awa dayan sannan general ya sallameshi,ya miqe ya sara mishi ya qame sannan yamiqa masa hannu sukayi musabaha,ya dubi haisam
"Ka raka dan uwanka haisam zuwa mota,kwayi musayar lambobin waya ko?"general ya fada bayan sun gama sallama da aliyyu
"Ok daddy"ya fada yana miqewa,ya gyara zaman shirt din jikinsa yana bin bayan aliyyu.
Yadan masa rata amma ya dage ya cimmasa,ya tsaya daga gefan kadarsa,saidai duk da tsahonsa ashe aliyyun ya zartashi a tsaho,duk da yayi masa kallon nashi tsahon yafi nasa,ashe cika da murjewar jiki da haidar din ya fishi yasa yayi tunanin ya zarta tsahonsa
"Yaronmu kake ashe?,sai kabi a hankali ko?" Haisam ya fada yana duban haidar ta gefan ido.
Cak haidar din ya tsaya,ya zube hannayensa cikin aljihun wandonsa yana dan fidda wani murmushi na gefan baki,tsahon sakan biyar sannan ya waiwayo sosai yana duban haisam din,sai daya nuna hanyar da suka baro da hannu sannan yace
"Wancan da muka baro....girmansa nada yawa a dunun haidar....banda haka daka fahimci cewa ko jimina ta saka kanta a tabo...ba za'a kira kaza ba,amma duk da hakan zan gaya maka wani abu guda daya wataqila yayi maka amfani.....yaro tashi ka nemi suna....karka raba kanka da kowa,zaifi maka kyau da cikakken alfahari ka shaidawa duniya kai tsaye cewa kaine wane wane kamar yadda kullum nake alfahari da cewa nine Aliyyu mas'ud dabo....bawai ka cewa duniya kaine 蓷an general hamza tahir ba" saiya murza yatsunsa saman fuskar haisam sannan ya qara da cewa
"Ka kiyayi shiga gonar haidar ta irin wannan sigar.....i repeat my self....ka kiyayi shiga gonar haidar" daga haka ya juya yaci gaba da tafiya ya barshi nan a tsaye.
Maganganun haidar din sun masa ciwo sosai,yana son ya nuna masa nasu qarfin ikon amma abu daya ke masa shamaki,yarinyar daya sanya cikin mota ya kulle,wanda tunda ya ganta yaji nan duniya ya samu matar aure,baisan alaqar dake tsakaninsu da ita ba,yana tsoron kada yaje ya bata rawarshi da tsalle,don dai yasan tabbas ba shakka baya ga macen bariki,babu wanda zaiwa macen da bai isa da ita haka ba ta bishi ta kuma yi biyayya,amma koma meye zaibi a sannu ya bincika,saboda haka ya nufi tashi.motar da sassarfa ya bude ya shiga,yayi ready yana jiran yaga tashin motar aliyyun don ya mara masa baya.
Duk da rashin mashiga da mafitar iska cikin motar amma a cure take waje daya,duk da gumin daya gama jiqeta saboda tsabar tunanin data fada yasa sam batajin jiqewar,tunanin mafita da makomarta take,harta hango kanta a gabansu abba tsakiyarsu suna tuhumarta meya kaita hotel,da wanne baki zata kare kanta?,wanne irin wawanci da dolanci haka ta aikata?,me yasa?,me yasa?,haka take tuhumar kanta,hankalinta a wani matuqar tashe.
Sanda taji yana bude qofar sai da hantar cikinta ta kada,wani matsanancin tsoronsa da bata taba jin irinsa ba ya rufar mata,tana nan a yadda take har zuwa sanda ya bude motar ya shiga,ya maidata ya rufe sannan ya tada ita ba tare da yace mata kanzil ba,abinda bata taba tsammata ba,tana jiran taji hukunci ko wata magana daga bakinsa amma saidai tunda suka fara tafiya har suka isa gidan babu abinda yace da ita.
"Fita!" Ya fada cikin daka tsawa data sanyata kama murfin motar ta fito da hanzari,cikin gudu gudu sauri sauri tayi sassan hajja,saidai tana gab da shiga sukayi karo da anty uwani,taja da baya da sauri,haka itama anty uwanin,mace guda daya tilo da halayyarta kan zahran ta bayyana,tana matuqar adawa da yadda hajjan kewa zahran,kulawa qauna da soyayya da take nuna mata,ko dama can macace mai fada,masifaffiya ce ita din,ita 'yace ga qanwar hajjan,tayi aure tana da yara hudu,uku maza sai mace guda daya autarta suwaiba,wanda itama ta dauki son duniya ta dorawa suwaiban,ji take sosai da ita,mijin nata ya rasu,koda kuma bayan rasuwar tasa bata sake wani auren ba.
"Me haka ke kuma kamar wadda aka biyo?" Ta fada cikin masifa tana qare mata kallo
"Ina kwana yakumbo" ta fada kamar yadda suka saba gaya mata,ko amsarta bata tsaya ji ba ta qara wuta zuwa ciki,sai anty uwanin ta bita da kallo ta kuma fara masifa
"Eyeee....ni zaki gaisar a haka?,lallai yarinyar nan iskancinki kullum qara gaba yake,koda yake kina da daurn gindi ne shibyasa,amma zamu hadu dake bari naje na dawo" ta fada tana buga cinya gami da yin gaba.
Sam bata kula da umminta dake falon hajjan ba sai data isa gaban hajja,saboda abune baqo a wajenta,ba kasafai ta saba ganinta din ba
"Lafiya?" Hajjan ta jefa mata tambayar tana duban qwayar idanunta,saboda yadda ta ganta kamar a birkice,yayin da ummin tata itama hankalinta gaba daya yake kan zahran a fakaice,don a zahiri ba zaka ce hankalin nata yana kanta ba.
Ko kafin tace komai haidar yayi sallama,a nutse yake takowa zuwa cikin falon,yana qoqarin rage zafi da radadi da yake ji daga cikin qirjinsa zuwa maqoshinsa,kallo daya ummin ta yiwa fuskarsa tasan ba lafiya ba,don idanunsa nakan hajjan da zahran,hakan ya sanya ta miqe don basu waje,duk da can qasan zuciyarta hakanan ya cika da zulumi da fargaba,sai taji batason tafiya,amma saita tanqwara zuciyarta ta duqa ta dauki carbinta ta fice ba tare da sun ankara bama.
Tana barin cikin falon taji ta kasa sake daga qafarta,abinda bata taba yiba kaf tsahon rayuwarta ta tsaya sauraren zancan wasu koda kuwa ya shafeta,amma a yau din sai taji tabbas tana son jin me ya faru?,wanda jikinta ya bata kan zahra ne,don ba haka ta saba zuwa gida weekend ba.
"Kai zaki.....lafiya?" Hajja ta jefa masa tambayar ganin yadda idanunsa suka sauya launi,ya kafeta da ido ya kuma kasa cewa komai
"Gata nan hajja,a hotel na daukota" idanu hajjan ta zaro sosai,hannunta dafe a qirjinta
"Kai haidar,banason shirmen banza da wofi,kasan kuwa me kake fada?,otel fa kace!" Kai kawai ya jinjina mata alamun tabbatarwa
"Kai!,haidar.....na gaya maka banason sakarci ko?,ka gayan gaskiya" wannan karon sai yaqi tanka mata,illa lumshe idanunsa da yayi kawai bai sake furta komai ba,sai hajjan ta waiwaya inda zahra ke tsaye,tana jin kamar zata saki fitsari
"Innawuro....abinda ya fadi gaskiya ne?"kamar ta dora mata dala da gauron dutse haka taji
"Eh hajja....amma...." Salatin hajjan shi ya katse sauran magana da bayanin da tayi niyyar yi mata,yayin da umminta dake tsaye daga can bakin qofa ta soma maimaita
"Hasbunallahu wa ni'imal wakil,Allahumma ajirni fi musibaty,wa'akhlifni khairan min ha" daga haka ta ja qafafunta da take jin sun mata nauyi ta soma barin wajen cikin matsanancin tashin hankali,wani hazo hazo take gani a idanunta,a haka takai kanta bangarenta cikin mawuyacin hali.
"Zahra'u....hotel fa zahra'u,hotel aka ce fa?" Ta fada tana duban zahra wadda takejin inama ana iya maida hannun agogo baya ta maida ta goge dukkan wani kuskure data aikata nabin su hindatun da tayi
"Hajja....ki tsaya na miki bayani,wallahi ba abinda kuke zato bane,ba abinda kuke tunani bane....na rantse d...."
"Rufemin baki....zahra'u ai yau ni kika kunyata,ni kika baiwa kunya wallahi,oh ni fadimatu" hajjan ta fada cikin matsancin firgici tsoro da kuma tashin hankali
"Matsa daga kusa dani,tashi ki ban waje nace" karon farko da hajjan ta taba korarta daga inda take tunda suke a rayuwarsu,hakan yasa taji wani sabon tashun hankalin ya rufto mata,saita kasa jurewa ta kwasa da gudu tayi daki.
Shikam haidar na tsaye,sai a sannan ya bude idanun nasa,ya juya ya soma takawa zaya bar falon
"Haidar....zo nan" hajjan tayi kiran sunansa tana qoqarin binne tashin hankalinta,baice komai ba ya dawo ya tsaya daura da ita,ta masa kallo na tsaf,ta karanci yadda ranshi yake masifar bace
"Bana son naji maganar nan a bakin kowa haidar....banaso" idanunsa ya bude sosai yana kallon hajjan,kamar ba zaya tanka sai kuma ya bude bakinsa
"Me yasa zakice haka hajja?,sai yaushe xaki daina bata kariya kan dukkan laifin data aikata koda kuwa muninsa yakai wannan?,wannan kariyar ita ta zame mata rigar da take iya shiga ta buya a ciki,taci gaba da aikata abinda ranta yaso a sanda taso ba tare data samu wata tirjiye ko kuma shamaki da zai hanata kaiwa ga ci gaba da aikata mara kyau ba....don Allah hajja wannan karon....ki cire soyayya ko qauna,ki kuma kauda kai,ki bari ayi hukuncin dashi yafi dacewa"
"Haidara" hajjan ta sake kiransa karo na biyu
"Nasan zahra'u ciki da bai,na santa sanin dako mahaifiyarta bata sani ba,ni ina ji a jikina,ina jin cewa zuwanta ko ganinta a wajen baya nufin ta aikata ko tana aikata wani mummunan abu ne,kuma nasan bayanin da taketa qoqarin yimin kenan,saidai naqi bata dama da wuri tayi bayanin,har sai rashin bata damar ya zama wani hukunci mai zaman kansa a gareta,nayi imanin jinina bazai taba aikata wata mummunan alfasha har kamar haka ba,addu'a ba qarya bace" shuru yayi ransa yana baci,yana ganin hajjan tana bata kariya ne kawai saboda kada ta fuskanci hukunci,wanda hakan ya jima yana bata masa rai,shin ita hajja bata ganin sauyi qarara tattare da yarinyar ne?,har sai yaushe sannan zata ankara su yiwa tufkar hanci?,duk wasu doka da qa'idoji na gidan hajjan da karan kanta tasha karyasu indai akan yarinyar ne,wannan shine dalilin da yasa sam yarinyar bai hada idanuwa da ita,saboda yana da yaqinin duk sanda ta masa wani abu mai kama da sangarta ko rashin kunya zai iya 蓳a蓳蓳alata ya zubar.
Saiya juya kawai yaci gaba da takawar,hajjan nada wani irin girma da qima a idanunsa,amma yana jin sam hukuncin bai kwanta masa a rai ba,saidai kodon saboda girmanta da matsayinta bazai iya tsayawa yayi ja'inja da ita ba,a haka ya fice ba tare daya sake cewa komai ba.
************
Kwana uku da dawowartata amma sam hajja taqi tsaiwa ta saurareta ko taji bayaninta,wanda hakan yayi mugun daga mata hankali,don hajjan itace last chance dinta,tana da yaqinin koda kowa yaqi saurarenta,koda kowa yaqi yarda da ita zata samu dukkan wadan nan abubuwa daga wajen hajjan tata.
Cikin kwana ukun ta rame ta fada saboda fargaba,sai a rana ta ukun hajjan ta tsaya da qyar ta saurari bayaninta,ta yarda da ita ta kuma gamsu,saidai tasha fada da masifa daga wajen hajjan irin wadda bata taba yi mata irinsa ba,duka bai damu zahra ba,tunda ta samu abinda takeso,sai data gama fadanta tsaf ta miqe sannan tace cikin dari dari da tsoron amsar da zata bata
"To hajja makaranta,anata CA bana nan" wani kallo mai kama da harara tayi mata
"Saiki jira kiji abinda yayanku zaice,don shurun da yayi kan zancan bazan sake tilastashi kan makomar makarantarki ba"
"Sai kace shine uban kowa cikin gidan nan?,koshi ya haifi kowa?" Abinda zahra keson fada kenan,amma tasan fadin hakan shi zai sake dagula komai,bata ma isa tace din ba,haka taja bakinta tasa masa zip ta zuge ta zubawa sarautar Allah ido,cike da fargaba kada ta rasa abubuwa masu muhimmanci acan makaranta.
Har hajjan takai bakin qofa ta waiwayo
"Waye haisam?" Tambayar data daurema zahra kai
"Haisam kuma?" Zahran itama ta maimaita sunan ta sigar tambaya wa hajjan
"Eh shi" nazari kadan zahra ta fada,tafi kowa sanin cewa ta jima da yiwa kanta shamaki da duk wani da namiji bare tace ko yana da alaqa ne da rayuwarta,don haka ta girgiza kai
"Bansanshi ba hajja" kai ta jinjina
"Bari yayankun ya dawo" bin hajjan kawai tayi da kallo saboda ta kulle mata kai,waye haisam din?,kuma meya hadinsa da yaa haidar?,data kasa canka saita tattara tunanin duka ta watsar,koma waye kuma koma.meye matsalarsu ce,itakam ta jima sa cire sabga ko sha'anin maza daga tsarin rayuwarta,hakanan ta dade da ciresu daga cikin jerin matsalolinta da zasu dameta.
Tun randa ta dawo a daren hindatu ta nemeta basu ganta ba,washegari tazo gidan,ta gaya mata lafiya lau,kada ta damu karsu nemeta,zata nemeta da kanta.
Tunda hajjan ta fita take kwance tana saqa tana warwara kan yadda lamarin zai warware mata cikin sauqi ba tare da wata matsalar ga sake sawo kai ba,tunda tana fatan wannan ta mutu,a haka har bacci yayi nasarar yin awon gaba da ita.
*_ABINDA KA SHUKA_*
A nutse take tafiya kan hanyarta zuwa gida,tun daga nesa take hango mutum biyu,daya a tsugunne daya a tsaye bisa saman kansa,haka taci gaba da tahowa tana matsar inda suke harta qaraso dab dasu,sai a sannan taga fuskokin mutum biyun sosai.
Na tsugunnen abdulyassar ne,na tsayen kuma auwal ne,sam babu alamu na walwala ko farinciki kan fuskar abdulyassar din,face ma uban gumi da yake hadawa,fuskarshi amurtuke sosai.
Kai ta dauke zata gotasu taji an riqe hijabinta,saita juyo da sauri,auwal ne,ya soma magana cikin zallar damuwa kamar zaiyi kuka
"Haba zahra....yanzu kina ganin abdulyassar haka zaki wuceshi ba zaki kulashi ba?,don Allah ki dawo ki tambayeshi me yake damunsa?,wallahi kinga munyi munyi ni da hajiyarsa ya gaya mana abinda yake damunsa yaqi cewa komai tun daxu,babu yadda bamuyi dashi ba,munyi munyi ma ya tashi daga nan amma yaqi" hijabinta ta fincike daga hannun auwal din tayi gaba abinta,tana jin auwal din na kiranta,tana kuma hangen yadda abdulyasar din yaci gaba da zama awajen.......
(Exactly haka yarinyar tayi mafarkinsa kwana biyar da rasuwarshin,na manta ban kawoshi tun a sannan ba saboda ajizanci na mantuwa).
Firgigit ta farka daga baccin daya dauketa din,ambaton sunan Allah ta shiga yi tana tunawa daya bayan daya dukkan abinda ya faru cikin mafarkin,a yanayin da taga abdulyasar din yana cikin damuwa babu ko shakka,saita miqe ta soma cire kayan jikinta ta shiga bandaki tayi wanka ta fito ta shirya,har a sannan mafarkin na maqale cikin ranta,saboda haka koda ta fito falo ta zuba abinci tana ci hajja ta soma baiwa labari.
"Zai iya yiwuwa haqqinku ke tambayarsa,ki yafe masa idan kinsan a baya baki yafe masa ba" baki zahran ta tabe
"Ni na yafe masa mana hajja,yaji da haqqin sauran da bansan adadinsu ba,da marasa zuciyar tausayi da zasu kasa mancewa bare su yafe masa".
Tana kammalawa tace bari taje wajen umminta,don tunda tazo bata je wajenta din ba,saidai yanayin yaddata amsheta,da yadda ta amsa gaisuwarta ta ya daga mata hankali ya bata mamaki,ta kuma shiga wasu wasin anya kuwa ba wani abu taji kan case din daya dawo da ita gida ba?,tunda haidar din mutuminta ne,to amma ita kanta tun ranar bata sake ganin haidar din ba,asalima kamar taji suna waya da hajja na masa fatan alkhairi kamar ma tafiya yayi wani waje,wannan abun saiya sake sanyata a rudanin data fita,ko sansa ta koma sassan hajjan saita kasa sukuni.