Sautin kuka ne ke tashi a cikin d'akin, daga jin
mai yin kukan har cikin ranta takeyin shi, wanda
zan iya cewa koma dai menene, ta dad'e a haka,
don kuwa idanunta sunyi jajir sannan fuskarta
ma tayi ja saboda farar mace dama idan tayi
kuka fuskarta ta kanyi ja.
A hankali aka turo k'ofar d'akin aka shigo, daga
bakin k'ofa yaja ya tsaya yana k'are ma matar
tasa kallo a lokaci guda kuma yana girgiza
kansa cike da takaici. Sai da yaja numfashi ya
had'iye 6acin ransa sannan ya soma takowa a
hankali har yazo daidai bakin gadon da matar
tasa ke kwance tana kukan fitar rai.
A hankali ya dafa ta had'e da kiran sunanta cikin
wata irin sigar rarrashi.
"Hajiya Bilki."
Bata d'ago ba amma ta dakatar da kukan da
takeyi hakan ya nuna cewa taji kiran mijin nata.
A hankali ya soma magana.
"Haba Hajiya Bilki, dama ace bazaki iya d'aukar
kaddara ba? Har ki zauna kina kuka saboda
Allah ya jarabe mu? Haba Bilki! Kin bani mamaki
wallahi."
Shi d'inma k'arfin hali kawai yakeyi amma
zuciyarsa ta raunana!
Tashi tayi zaune gami da share hawayen
fuskarta tana fuskantar mijin nata da har yanzu
yake tsaye bai zauna ba. Sannan itama ta soma
magana cikin 6acin rai.
"Don Allah Alhaji ka barni, na gaji da wa'azain
nikam gaskiya hak'uri na ya k'are haba! Ta yaya
za'ayi ace mun shekara akalla sha biyu da aure
amma duk shekara sai nayi 6ari? Meyake faruwa
ne? Ka duba fa ka gani kaf danginka bak'ina
suke gani gaba d'aya sun tsane ni sun sa min
ido! Abin ya fi d'aga min hankali sai jiya da
muka je sunan gidan Hajiya Karima bakaga
yadda ake nuna ni ba! Gaba d'aya na zame
musu tamkar wata mujiya haba!"
Ta k'arashe tana cigaba da kuka. Alhaji ya
runtse idonsa yana mai jin rad'ad'i a cikin
zuciyarsa, tabbas yasan haka maganar take sai
dai kuma yasan basufi k'arfin Allah ya jarabe su
da rashin haihuwa ba, shi ya d'auki hakan a
matsayin kaddara. Don haka sai ya nutsu ya
fara magana.
"Hajiya Bilki a kullum bazan gaji da fad'a miki ba
Allah ubangijinmu mai baiwa ne sannan mai
hikima ne, kar ki manta ke d'in baiwarsa ce
sannan duk yadda yaga dama yayi dake haka
zaiyi dake, Allah yayi miki baiwa da yawa ba
dole sai kin samu haihuwa
zakiji dad'in rayuwarki ba, ki gode masa da ya
baki kyau, arzik'i ya wadata ki
da lafiya, sannan uwa uba ya barki da ranki, har
akwai abinda yafi wannan jin dad'i a rayuwa?"
Gwauron numfashi ya saki tare da zama a kusa
da ita yana kallon cikin k'wayar idonta sannan
ya cigaba da magana.
"Haihuwa ta Allah ce, idan yaga dama zai baki
idan kuwa bai ga dama ba duk dabararki bazai
baki ba, duk yanayin da kika tsinci kanki kamata
yayi, ki d'aga hannunki sama ki gode masa
sannan ki rok'e sa gafara da rahama.
Wad'annan maganganun nasha fad'a miki su ba
tun yau ba amma naga kamar ta iske suke bi.
Wallahi ki nutsu kar garin garajenki kije kiyi
sa6o, kina jina?"
Ta d'aga kanta a hankali yayin da ta sa
yatsanta ta share hawayenta. Yayi murmushi irin
nasu na manya yace.
"Bilki duk ba wannan kizo ki bani abinci yunwa
nakeji."
Ta6e baki tayi tace
"Kayi hak'uri na manta ban girka ba."
Yayi murmushi yace
"Bilki kenan ya za'ayi mijinki ya fita aiki tun
safe amma ya dawo gidansa abincin ci ya
gagare shi?"
Tace
"Haba Alhaji! Yau sati na d'aya fa dayin 6ari ya
kamata ka barni na huta mana."
Inda sabo ya saba da halin Bilki amma da yake
Allah ya zuba masa hak'uri sai kawai yayi
murmushi yace
"Haka ne Allah ya baki lafiya."
"Amin" kawai tace yayinda ta koma ta kwanta
gami da bashi baya. Tashi yayi ya fice daga
d'akin yana mai jinjina hali irin na Bilki.
D'akinsa ya fad'a kai tsaye yayi wanka yana
fitowa ya zumbula jallabiya fara ya fito ya nufi
kitchen, fura da nono ya had'a mai yawa ya
dawo parlor ya zauna had'e da kunna T.V yana
kallon tashar Aljazeera. Sai da ya gama shan
furar tas sannan ya koma ya kwanta tare da
lumshe idanu a lokaci guda kuma ya fad'a kogin
tunani a haka har bacci ya sace sa.
Awarsa biyu daidai ya farka ya duba agogon da
ke mak'ale a bangon hannunsa, k'arfe 4:19pm,
zumbur ya mik'e yaje yayi alwala yayi sallah,
bayan ya kammala kansa tsaye ya wuce d'akin
Bilki tana kwance kan gado tana latsa waya,
kiranta yayi a hankali.
"Bilki." Tana taunar chewing gum sai da yayi
k'ara k'as sannan ta d'ago ta kalleshi tace
"Na'am." Ajiyar zuciya ya sauke ya fara magana
fusakarsa ba annuri ko kad'an.
"Yanzu kina ganin bacci ya kwashe ni amma har
lokacin sallah ya wuce ki kasa tashi na inyi
sallah?"
Tace
"Kayi hak'uri na manta ne."
Girgiza kansa yayi yace
"Allah ya kyauta, zan fita daga can zan wuce na
gaida Goggo (mahaifiyarsa) sai na dawo."
Ko kallonsa batayi ba tace
"To sai ka dawo, daga nan ka siyo man nama
mana."
Fita yayi daga d'akin yaje ya sake yin wanka ya
shirya cikin farin yadi kalar kunun kanwa marar
nauyi ya fice daga gidan.
Sai da akayi sallar magriba sannan ya wuce
gidan Goggo dake cikin Layout a garin Katsina,
yana shiga ya fad'a d'akinta kamar yadda ya
saba bayan sun gaisa tasa aka kawo masa
tuwon masara miyar kuka da man shanu ya ci
ya k'oshi ya kora da fura. Nan suka d'an ta6a
fira kamar kullum sannan ta soko masa zancen
da kullum baya son shi.
"Ya maganar aure Hamza?"
Yayi dum ya kasa cewa uffan, tabbas shima
yana son k'ara auren sai dai kuma yana gudun
tashin hankalin Bilki, don haka bai ce komai ba
kansa dai na k'asa.
AUREN FANSA 02
✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐๐น๐น๐น⭐๐น๐น๐น⭐
๐น⭐✨⭐๐น⭐✨⭐๐น
๐น✨⭐✨⭐✨⭐✨๐น
✨๐น✨⭐๐⭐✨๐น✨
⭐✨๐น✨⭐✨๐น✨⭐
✨⭐✨๐น✨๐น✨⭐✨
⭐✨⭐✨๐น✨⭐✨๐
๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น
AUREN FANSA!!!
๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น
๐นNa๐น
๐นMARYAM S BELLO๐น
(MSB)
๐๐นPure Moment Of Life Writers๐๐น
Dedicated to Ummi Aisha and Zeebee๐
๐น02 ๐น
"Daman nasan bazaka amsa ni ba Hamza, kuma
ni har ga Allah bazan maka dole ba. Sai dai kana
buk'atar kaje kayi tunani sosai akan maganar,
idan kana da ra'ayin aure to zaka iya yi, idan
kuma bakada shi babu damuwa."
Shiru yayi yana nazari, yana son faranta ma
mahaifiyarsa rai sannan bayason tashin hankalin
Bilki, don haka sai ya k'ak'alo murmushin dole
yace.
"Goggo zan je inyi shawara da Bilki kome kenan
zan zo na sanar dake."
Murmushi tayi tace
"Allah ya nuna mana."
Yace "Amin."
Bai bar gidan ba sai wurin tara ta wuce na dare,
gida ya wuce kai tsaye. Yana shiga ya wuce
d'akinsa yayi wanka ya sanya kayan bacci ya
fito parlor.
Bilki na zaune tana latsa waya tana kallon wani
American series, jin alamun shigowa yasa ta
kalleshi lokaci guda kuma tace
"Har ka dawo?"
Yace
"Na dawo." A lokacin da yake zama kan kujera
yana gyara zaman glass d'in idonsa. Matsowa
tayi kusa dashi tare da kwantawa bisa k'irjinsa.
Dukansu kowa yayi shiru kafin Bilki ta katse
shirun nasu
"Hamza, wai ya maganar mu ne?"
Yace
"Wace magana kenan?"
Ta zum6uro baki tace
"Ba dai har ka manta ba?"
Yayi shiru tabbas yasan maganarta bata wuce
tana son kud'i.
Tayi murmushi tana mai kashe murya had'e da
shagwa6a tace
"Kace zaka bani kud'i naje Dubai mana saro
kaya."
Shiru yayi gami da sauke nannauyan numfashi
yace
"Bilki kenan, ay mun gama wannan maganar tun
rannan kuma nace zan baki, sai dai ba dole sai
kinje ba yanzu ay inace sautu ake badawa kuma
bama haka ba, ina k'awarki da ke yawan zuwa
basai ki bata ba ta kawo maki."
Ba haka taso amma ya zama dole ta lalla6a shi
don haka sai tace
"Duk d'aya ay kuma bakomai sai na bata d'in
nawa zaka bani?"
Yace
"Zan baki dubu 100 ki fara da ita daga baya sai
na k'ara maki."
Da sauri ta tashi zaune
"Dubu d'ari kuma? Ni gaskiya ta mani kad'an."
A fusace ya tashi tsaye yace
"Toh idan har bakiso gaba d'aya a barshi mana,
ya zan baki ki raina? Gskiya ki chanza halinki."
Daga haka ya tashi ya shigewarsa d'aki yayi
kwanciyarsa maganar auren da basuyi ba kenan
don ya fusata.
Washe gari ta kama Monday, kamar kullum ya
tashi ya shirya kasancewar aikin banki yake
yasa tun asuba idan ya tashi baya komawa
bacci.
K'arfe bakwai daidai ya kimtsa ya fito daman
baya jiran breakfast don Bilki bayi takeyi ba, a
hanzarce yake komai tashinta yayi daga bacci ya
ce mata zai tafi aiki, juyi d'aya tayi tashi tace
masa "Toh" sannan ta ja bargo ta rufe har
kanta. Girgiza kansa yayi ya shiga motarsa ya
harba titi.
Wani shop ya tsaya ya sayi bread da yoghurt sai
lemo sai kuma kayan tea da biscuit don na office
d'insa sun k'are, daman ya kan aje saboda ko
yaji yunwa sai yaci kawai.
A haka ya isa office d'insa ya soma aikinsa
kamar kullum. Haka ya wuni yana juya maganar
Goggo a ransa yanata sak'e sak'e, haka dai
yake sukuku dashi har lokacin sallah sannan ya
tashi ya fice tare da sauran abokanan aikinsa
musulmai.
Kamar kullum yau ma sai kusan k'arfe 6 ya diro
gida, gajiya kam ya gaji ba kad'an ba ga yunwa
data addabe shi ga uwa uba ana zafi agarin.
Yana shiga gida ya ci karo da Bilki a bakin k'ofa
taci ado tayi kwalliya na fitar hankali ga gidan
sai k'amshi ke tashi. Taro sa tayi bakin k'ofa
tana mai aika masa da sak'koni ta ko wane
fanni, a hankali ya ture ta yace
"Kinga Bilki na gaji bari naje na fara watsa ruwa
kafin lokacin sallah yayi."
Murmushi tayi ta sake sa sannan ta koma parlor
ta zauna tana binsa ta kallo har ya shige
d'akinsa.
Sai da ya kimtsa ya fito sannan ya wuce kitchen
don neman abinda zaici. Tana kallonsa ya fito
da cup d'in tea da biscuit a hannunsa ya zauna
kan dinning yaci. Sai da ya kammala tazo ta
zauna a kusa dashi tana yatsina baki tana wani
yanga da kwarkwasa. Can kuma tace
"Alhaji."
Bai kalle ta ba yace
"Na'am."
Tace
"Alhaji daman k'awata zatayi bikin k'anwarta
shine nake so ka bani kud'i na bata guddumawa
ta..."
Da sauri yace
"Haba Bilki daga dawowata zaki tare ni da
zancen wasu kud'i ay sai ki bari na huta dai
ko?"
Murmushi tayi tace
"Haba Alhaji duk bai kai ga tashin hankali ba ka
huta sai muyi magana."
Bai k'ara magana ba illa tashi da yayi ya fita
don yaga lokacin sallar magriba ta gabato.
***
"Mummy!" Yaro d'an kimanin shekara goma ya
rugo da gudu, Maman tasa na zaune kan wata
irin makekiyar kujera tana duba magazine da
glass d'in karatu a idanunta. A hankali ta d'aga
ido ta kalli yaron da ke ta gudu kafin kuma ya
haye bisa cinyar ta yana mai hugging d'inta.
Itama hugging d'insa tayi tana kallonsa cike da
so tace.
"Lafiya ka shigo da gudu haka FARUK?"
Yaron da ta kira da Faruk yana mai tsananin
murmushi kafin ya rufe baki wani babban mutum
dogo fari ya shigo yana sanye da kayan
hausawa harda babbar riga, sai da yazo daidai
bakin k'ofar da zata sadasa da parlon yaja ya
tsaya yana murmushi, sannan kuma yace.
"Ay Faruk ya d'auko grade mai kyau, sannan ya
lashe baki gaba d'aya wato overall as always."
Dukansu suka d'aga ido suka kalli mutumin dake
tsaye ya hard'e hannayensa biyu yana
murmushi.
Matar da aka kira da Mummy ta rungume Faruk
sosai a jikinta tace
"That's my boy, haka nake so Allah ya k'ara
maka basira, toh saura na Islamiyya, idan har
kayi k'ok'ari shima akwai kyautar dana tanadar
maka ta mussaman."
Cike da jin dad'i Faruk yace
"Allah Mummy?"
Tace
"Kayi ka gani I promise."
Mutumin dake tsaye ya tako ya shigo parlon,
kusa da kujerar dasu Faruk ke zaune ma'ana
doguwar kujera, sai da ya cire babbar rigarsa
sannan ya zauna yana shafa kan Faruk yace.
"My boy aje a cire uniform ayi wanka ko sai
kazo muci abinci."
Faruk yace
"Ok Daddy."
Sannan ya tashi da gudu ya shige d'akinsa.
Matar da ke zaune kusa dashi mai suna Reemah
wadda na k'are ma kallo kyakkyawar gaske ce
fara mai yalwar gashi don kuwa har gaban
goshinta ya fito. Bana tantama ta had'a iri da
larabawa. Kamo hannun mutumin tayi mai suna
Adam tace
"Muje ka watsa ruwa kaci abinci ko?"
Murmushi yayi yana jin son matarsa na k'ara
fizgarsa sannan yace
"Muje sahibata."
Murmushi tayi sannan suka mik'e a tare suka
nufi kan bene inda hannunsu na mak'ale da na
juna...
AUREN FANSA 03
✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐๐น๐น๐น⭐๐น๐น๐น⭐
๐น⭐✨⭐๐น⭐✨⭐๐น
๐น✨⭐✨⭐✨⭐✨๐น
✨๐น✨⭐๐⭐✨๐น✨
⭐✨๐น✨⭐✨๐น✨⭐
✨⭐✨๐น✨๐น✨⭐✨
⭐✨⭐✨๐น✨⭐✨๐
๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น
AUREN FANSA!!!
๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น
๐นNa๐น
๐นMARYAM S BELLO๐น
(MSB)
๐๐นPure Moment Of Life Writers๐๐น
Dedicated to my darling Maman Ihsan (SAFNA)
much love darl๐๐❣️
๐น03 ๐น
***
Daddare sai da Bilki ta k'ara tada masa da
maganar wasu kud'in inda a ranar sai da ya yi
6ata mata rai fiye da tunaninta sannan ya nuna
mata ta cika son kud'i, duk dai abubuwan da ya
dad'e dasu a ransa shekara da shekaru sai da
ya amayar mata dashi, sum sum ta tashi ta
koma cikin d'aki tsabar borin kunya.
Jingina yayi da kujerar parlon tare da lumshe
idanu don ya samu nutsuwa sai dai bai kai ga
yin hakan ba wayarsa ta fara ruri, kallon screen
d'in wayar yayi yaga sunan da ya bayyana wato
My sister, murmushi ya saki na tsananin farin
ciki a lokaci guda kuma damuwarsa ta 6ace 6at,
d'auka yayi gami da yin sallama, d'ayan
6angaren aka amsa sannan tace.
"Ya Hamza! Da fatan an wuni lafiya?"
Sai da yayi murmushi sannan yace
"Lafiya lau Amina ya gida?"
"Alhamdulillah, ya Anty Bilki?"
"Tana nan lafiya ya zafi kuma?"
"Lafiya lau ya Hamza, da fatan komai lafiya?"
Yace
"Alhamdulillah ya jiki kuma?"
Ta d'an yi murmushi kad'an sannan tace
"Alhamdulillah gashi nan muna ta fama."
Dariya yayi yace
"To Allah ya raba lafiya."
Tace
"Amin."
Sannan ta kuma cewa
"Ya Hamza akan maganar mu dai ce yasa na
kira ka, kaga yanzu cikina ya shiga watan
haihuwa kuma nasha fad'a maka idan na haifi
babyn nan na baka shi ka rik'a..."
"Amina! Insha Allah ke zaki rik'a babynki sai dai
ki dinga kawo min shi hutu."
Tayi murmushi mai bayyana hak'ora sannan tace
"Ya Hamza na kenan, yaya na na kaina, nidai
kayi min alk'awarin rik'a abinda zan haifa koda
bayan raina ne, shine kad'ai burina a halin
yanzu."
Haka kawai sai yaji gabansa ya fad'i cikin firgici
yace
"Kinga Amina, nasha fad'a maki mutuwa lokaci
ne kuma insha Allah zaki ga abinda zaki haifa
har ma ki shayar da shi ki daina fad'in
maganganu haka ba dad'in ji."
Tayi dariya
"Ya Hamza mutuwa fa na kan kowa sanin gaibu
sai Allah nidai alk'awari na zaka rik'e min kaji?"
Nannauyan numfashi ya saki sannan ya d'ora
"Naji shikenan are you happy now?"
"Yeey! Allah ya bar mana kai ya Hamza,
nagode!"
Dariya yakeyi sosai itama tana taya sa, sanann
ya kawar da wancan zancen ta hanyar jefo mata
tambaya
"Ya kingama rubuta list d'in abubuwan da kike
buk'ata?"
Tace
"Eh na gama ya Hamza yana hannun Goggo na
bata."
Yace
"Ok zan kar6a insha Allah sai na ga abinda za'a
siya."
Tace
"Toh ya Hamza Allah ya k'ara bud'i."
Sai da suka d'an ta6a fira kad'an sannan sukayi
sallama ko wane yana mai farin cikin ganawa da
d'an uwanshi.
Amina k'anwar Hamza ce uwa d'aya uba d'aya,
bayan nan kuma su kad'ai ne Goggo ta haifa
bayan Amina sai haihuwar ta tsaya, tunda ta
haifi Hamza sai bayan shekara kusan bakwai
sannan ta haifi Amina, kasancewar su biyu ne
kacal yasa suka shak'u da juna sosai Hamza na
son Amina kuma yanaji da ita, kullum suna
mak'ale da juna tun suna yara har kawo yanzu
da aure ya rarraba su kuma, amma kusan kullum
sai sunyi waya.
Amina tasha ci ma Bilki mutunci akan halayanta
da take nuna ma Hamza saboda bazata iya jure
ganin d'an uwanta cikin bak'in ciki da k'unci ba.
Mijinta ya rasu tun tana da ciki wata biyar Allah
ya amshi ransa, ga bashi da uwa bashida uba
haka ma shi kad'ai ne mahaifiayarsa ta haifa,
bayan rasuwar tasa ta zauna nan gidanta da ke
cikin garin Katsina a G.R.A.
Wannan kenan!
***
BAYAN 'YAN KWANAKI
Yau weekend ne Hamza baya zuwa aiki don
haka yana gida yana hutawa, bayan ya gama
waya da Amina kamar kullum Bilki ta shigo cikin
shirin fita unguwa ta sha ado sosai tana ta zuba
k'amshi. A hankali yake binta da kallo kafin
kuma ya sauke su kan shigar da tayi. Sanye take
da wata silky doguwar riga mai dogon hannu
kalar brown an mata aikin duwatsu ba laifi rigar
ta kamata sai ta yafa gyalen kayan. Haka ma
takalminta mai tsini ne kalar kayanta da jaka
kalar kayan. Har tazo ta zauna bai bar kallonta
ba cike da mamaki, Bilki tace.
"Hamza zan fita."
Ya kalleta da mamaki yace
"Ina zakije?"
Ta had'e rai
"Gidan Hajiya Laila."
Shima ya had'e rai
"Ba inda zakije."
Ta mik'e zumbur!
"Me kace?"
Yayi banza da ita, ta rik'e k'ugu tana sassarfa
masifa
"Hamza! Gaskiya ka takura min haka kawai!
Kuma ay dah ba haka kake ba wannan
k'anwarta taka duk ta zuge ka."
Tashi yayi a fusace yana nuna ta da yatsa
"Kar ki k'ara saka Amina a cikin zancen mu
saboda babu ruwanta, kina ji na?"
"Ahayye nanaye, an ta6o masa rabin rai, to an
fad'a Amina ce ke zuge ka kayi abinda zakayi."
Bai san lokacin da ya d'auke ta da mari ba yace
"Kisani ni mijinki ne, kuma nafi k'arfin ki
wulak'anta ni, sannan wallahi kika k'ara fad'in
magana makamancin wannan a bakin aurenki!"
Ta zaro idanu waje
"Iyye! Kan mage ya waye, lallai Hamza yanzu
kayi baki, amma tunda ka mare ni don na fad'i
gaskiya shikenan kaje Allah zai saka min."
Yace
"Nidai na fad'a miki ki iya bakinki, kuma fita
bazakiyi ba ay inace dai sai na bada izini ko? To
mugani idan kin isa!"
Har ya tafi ya dawo yace yana mata mugun
kallo.
"Magana ta k'arshe ina so ki sani aure zan k'ara
na gaji da zama da mace irinki wadda batasan
inda duniyar ta dosa ba, na aure ki don ina
tsananin sonki amma kisani dole zan k'ara
aure."
A fusace ta cakumo masa wuyan riga kamar
kura taga nama.
"Aure Hamza! Baka isa kayi min kishiya ba, ni
kad'ai ce babu k'ari!"
Yayi dariya gami da cire mata hannu daga rik'on
da tayi masa sannan yace
"Kin isa ne ki hana? Ay baki isa ba aure kamar
anyi ne an gama."
Yana gama fad'in haka yayi shigewarsa d'aki ko
kallonta baiyi ba. Yana jin ihuta tana fad'in
"Wallahi babu wacce ta isa ta shigo min gida ta
zauna lafiya, wallahi koma wacece sai na kashe
ta!!!"
AUREN FANSA 04
✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐๐น๐น๐น⭐๐น๐น๐น⭐
๐น⭐✨⭐๐น⭐✨⭐๐น
๐น✨⭐✨⭐✨⭐✨๐น
✨๐น✨⭐๐⭐✨๐น✨
⭐✨๐น✨⭐✨๐น✨⭐
✨⭐✨๐น✨๐น✨⭐✨
⭐✨⭐✨๐น✨⭐✨๐
๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น
AUREN FANSA!!!
๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น
๐นNa๐น
๐นMARYAM S BELLO๐น
(MSB)
๐๐นPure Moment Of Life Writers๐๐น
Dedicated to my Zarah Surbajo and Sadnaf๐❤️๐
๐น04 ๐น
Zuciyarsa har wani zafi take masa, kwanciya
yayi kan gadonsa yana mai maida numfashi
sama sama, meyasa Bilki bazata ta6a chanza
halayenta ba? Yasani tun kafin suyi aure yake
fama da iri iren halayenta na nuni da maita akan
kud'i, sam bata gajiya da tambayarsa kud'i, ko
lokacin auren su Goggo taso ta hana don sam
tarbiyyar Bilki bata yi mata ba, batada kamun
kai ga shegen yawo, sai dai a lokacin yadda
yake tsananin sonta baijin zai iya hak'ura da ita,
a haka yayi ta lalla6a Goggo har ta amince akayi
auren. Gashi sam bai iya mata fad'a idan tayi
masa laifi sannan bai iya hanata kud'i idan ta
tambayesa ya rasa dalilin da yasa haka. So da
yawa idan ta tambayesa sai yaji kamar kar ya
bata amma sam sai ya kasa haka yayi ta
rayuwa da ita tana cutarsa ba tare da ya ankara
ba. Gashi da anyi abu ta iya kukan k'arya kuma
nan da nan sai zuciyarsa ta karaya yaji yana
tausayinta, a haka ta gano lagonsa abu kad'an
zata sa masa kuka.
Ajiyar zuciya ya saki tare da gyara kwanciya
yanzu yasan mafita d'aya ce ya k'ara aure k'ila
hakan zai sa ya gane banbancin zama da Bilkin,
wata k'ila ma wadda zai aura batada halayen
Bilki ya yarda ya amince zai k'ara auren, tashi
yayi da niyyar shiryawa yaje ya sanar da Goggo
ya shirya ko yau za'a iya d'aura masu aure,
wayarsa ta fara ruri. Goggo ya gani a saman
screen d'in wayar haka kawai gabansa sai da ya
fad'i. A sanyaye ya d'auka gami da yin sallama,
da sauri Goggo tace
"Hamza kana ina yanzu?"
Yace
"Inagida Goggo, lafiya dai ko?"
Tace
"Babu lafiya Hamza, maza maza ka taho asibiti
k'anwarka na nan na nak'uda, kuma ta kafe
tak'i shiga d'akin haihuwar wai sai ka zo, kuma
ga haihuwar tazo kar ta haihu a gaban d'aki
Hamza, kayi sauri don Allah."
A rud'e yace
"Gani nan yanzu wace asibiti ce?"
Tace
"Alheri clinic kayi sauri."
"To." Kawai yace ya fito da gudu daga d'akin,
takalmansa ma daban daban yasa tsabar rud'u
ga gabansa sai fad'uwa yakeyi. Haka dai ya
daure ya figi mota ya fice da sauri, duk da
asibitin batada nisa daga gidansa amma gani
yake bazai isa da sauri ba. Cikin k'ank'anin
lokaci Hamza ya iso Alheri clinic da gudu ya
shiga ciki yana tambayar suna ina. Koda yaje
hanashi shiga akayi sai da ya kira Goggo yace
gashi nan sun hana shi shigowa. Da k'yar ta
rok'esu suka barshi ya shigo.
Yana shiga ya iske Amina sai faman nak'uda
takeyi mai zafi tana kiran sunan Hamza tana
kuka. Da sauri ya isa gareta tana ganinsa ta
k'ara sautin kuka tana fad'in
"Ya Hamza na gode da kazo, wata magana zan
fad'a maka."
Jikinsa yayi sanyi yace
"Koma meye ay sai ki bari ki haihu tukunna..."
"Ya Hamza bazaka gane ba bazan iya bari sai
na haihu ba, amma don Allah ka tsaya ka
saurareni!"
Ta fad'a cikin muryar tsawa, tashi yayi ya fara
safa da marwa idanunsa sun kad'a sunyi ja,
yasan tatsunniyar gizo bata wuce ta k'ok'i,
tabbas yasan maganar da ta saba fad'a masa
yau ma ita d'in ce zata fad'a masa. Don haka
sai yace
"Ko meye zaki fad'a na riga na sani, don haka ki
tashi a shiga dake d'akin kar ki haihu a nan."
Duk'awa tayi tare da fasa wata irin giggitaciyar
k'ara wadda bama Hamza ba har Goggo da
malaman asibitin sai da suka rud'e, fad'i take
"Bazan shiga ciki ba ya Hamza sai kayi min
alk'awari na k'arshe."
Da sauri ya kalleta
"Haba Amina! Meyasa kin faye kafiya ne? Ba
mun gama maganar nan tun tuni ba? Meyasa
kike tado zancen kuma, ki bari ki haihu zamuyi
magana."
Girgiza kanta tayi tana hawaye
"Kayya ya Hamza, don Allah kayi min alk'awarin
kawai."
Goggo ce ta sa baki tace
"Hamza kasan zafin haihuwa, kawai kayi mata
alk'awarin a shiga da ita."
Da k'yar ya iya bud'e bakinsa yace
"Na maki alk'awari Amina, Allah ya sauke ki
lafiya."
Duk da zafin nak'udar da Amina keyi ba hanata
yin mumushi ba, sannan tace
"Nagode ya Hamza nagode!"
Juya mata baya yayi don bazai iya jure ganin
Amina cikin wannan halin ba, a haka aka shiga
da Amina rik'e da hannun Goggo wadda aka
samu aka raba su da k'yar."
Goggo kuka takeyi sosai ji take kamar Amina
bazata fito ba idan ta shiga. Hamza ya zo ya
dinga rarrashinta har ya samu tayi shiru.
Minti kusan talatin ana abu d'aya Amina ta kasa
haihuwa, har an fara shawarar ayi mata CS don
da k'yar idan zata iya haihuwa da kanta. Har
sun fara shawarar a sanar da 'yan uwanta Allah
cikin ikonshi ta haihu. Su Hamza suna jin kukan
jariri suka fara murna suna hamdala.
Jim kad'an wata sister ta fito da jariri tana zuwa
su Goggo suka yo kanta, Goggo ce ta fara cewa
"Alhamdulillah! Ta haihu lafiya."
Hamza kuwa hannu yasa ya kar6i babyn yana
kallo kafin kuma ya kalli nurse d'in yana
murmushi sosai. Nurse d'in ce tace
"Ta haifi mace."
"Alhamdulillah!!" Shine kawai abinda suke cewa.
Kafin kuma Goggo tace
"Ina ita Aminar? Ba'a gama kimtsa ta ba mu
shiga?"
Nurse d'in ce tace
"Sai dai kuyi hak'uri..."
"Me kike nufi da kalamanki?" Cewar Hamza a
d'an rud'e, Goggo ma ta rud'e tace
"Bamu gane abinda kike cewa ba."
Nurse d'in tace
"Abinda nake nufi shine kuyi hak'uri Allah ya
amshi kayanshi, ma'ana Amina ta koma ga
mahaliccinmu."
Saura kad'an Hamza ya saki d'iyar sai da nurse
d'in tayi saurin amsar ta, Goggo kuwa in banda
salati ba abinda takeyi kafufuwanta kasa
d'aukarta sukayi ta zauna da sauri.
Hamza zaman k'asa yayi dirshen yana salati
kafin kuma ya fashe da kuka kamar k'aramin
yaro.
"Daman Amina tafiya zakiyi da gaske? Tasha
fad'a min mutuwa zatayi na kasa yarda." Haka
yayi ta sambatu kamar zautacce a yayinda
Goggo ke kuka rungume da babyn.
Sai da aka fiddo da gawar Amina lullu6e cikin
farin zanin gado bisa gado mai taya a lokacin
kuma suka gasgata ta mutu d'in. Wurin ya kuma
rud'ewa inda Hamza ya rugo ya rugume gadon
yana magana da gawar Amina. Goggo na tsaye
tana kuka tana tausayin Hamza, da k'yar aka
6am6are shi daga jikin gadon aka sanya ta cikin
doguwar ambulance.
Hamza na tuk'i yana kuka har baya ganin
gabanshi, ga kukan baby dake k'ara rud'a shi.
Can gidan Goggo dake cikin G.R.A suka nufa.
Suna isa aka shiga da gawar a cikin gida.
Bayan anyi ma Amina wanka an mata sutura sai
kuma aka d'auketa za'a kaita makwancinta na
k'arshe, gidanta na gaskiya! Hamza na ji na gani
ya saka Amina cikin kabarinta, Masha Allah
Amina tayi mutane don kuwa har tutse akeyi
wurin sakata a makwancinta.
Bayan an gama kuma suka juyo gida inda su
Hamza suka cigaba da kar6ar gaisuwa.
Itama Bilki kullum sai tazo amma bata ta6a dafo
komai ba a matsayin abincin sadaka ba hasali
ma sai tayi kwalliyarta take zuwa bata nuna
wata damuwa ba.
A haka aka yi sadakar uku ana zaman makoki,
inda Hamza ya dangana yana amsar gaisuwar
kowa saidai fa baya magana sai dai yayi shiru
ya k'ura ma wuri d'aya ido kamar yana tunani.
Ko kuma idan akayi masa gaisuwa sai ya dad'e
yana kallon mutum kafin kuma ya amsa
gaisuwar.
Shikenan Amina ta tafi, mutuwa mai yankar
k'auna mai raba tsakani, saidai Allah baya barin
wani don wani yaji dad'i. Allah kasa mu dace,
Allah kayi mana kyakkyawan k'arshe Amin
thumma Amin.
AUREN FANSA 05
✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐๐น๐น๐น⭐๐น๐น๐น⭐
๐น⭐✨⭐๐น⭐✨⭐๐น
๐น✨⭐✨⭐✨⭐✨๐น
✨๐น✨⭐๐⭐✨๐น✨
⭐✨๐น✨⭐✨๐น✨⭐
✨⭐✨๐น✨๐น✨⭐✨
⭐✨⭐✨๐น✨⭐✨๐
๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น
AUREN FANSA!!!
๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น
๐นNa๐น
๐นMARYAM S BELLO๐น
(MSB)
๐๐นPure Moment Of Life Writers๐๐น
Dedicated to mairo๐ aka Maryam Gafai I heart
you sis❤️ and my sisi Ammin SS ๐๐๐
๐น05 ๐น
BAYAN KWANA BIYU
Ranar suna yarinya taci sunan mamanta
marigayiya Amina, daman bawani taron sunan
da akayi wane taro ma ana zaman makoki?
Amina duk da tana jaririya Allah ya zuba mata
hak'uri ga bata kuka sosai sai dai idan taji
yunwa ko wani abin na damunta. Kammaninta
sak na mahaifiyarta ta d'ebo hartta gashinta irin
nata ne lub lub, hasken ne kawai bata d'ebo ba
sa6anin marigayiya da take fara tas kamar
yayanta Hamza amma Amina babyn ita ba fara
bace tas, sai dai tana da kyau duk da batada
hasken ana ganin kyawunta. Idan ta bud'e ido ta
kalli mutum zaka gansu manya ne farare tas!
Baya 'yan kwanaki a lokacin Amina ta kwana 20
cif a duniya Goggo ta kira Hamza da Bilki
gidanta akan cewa tana son magana dasu.
Bayan sun iso suka gaisa Goggo ta d'auko
Amina dake kwance kan gado tana bacci, ta
mik'a ma Hamza ita tana murmushi tace
"Hamza kamar yadda kasani marigayiya ta baka
amanar rik'on Amina kuma ka d'auki alk'awarin
haka, don haka yau na damk'a maka Amina a
matsayin d'iyarka halak malak, da fatan zaka
rik'e ta bisa amana."
Sai kuma ta juyo ta kalli Bilki tace
"Bilkisu ga amanar Amina nan ki rik'e ta amana
saboda kar ki manta marainiya ce gaba da baya
idan har kika ci zalinta Allah zai mata sakayya."
Hamza yace
"Insha Allah Goggo kar ki damu ina k'auanar
Amina kamar 'yar dana haifa haka nake jinta a
raina. Insha Allah zamu rik'e ta amana, Allah ya
taya mu rik'o."
Goggo tace
"Amin, daga cikin dukiyar da mahaifinta ya bar
mata a ciki ake siya mata su pampers da su
madara, sai kayan sawa da sauran abinda ba'a
rasa ba, amma ba kasafai nake amfanin da
kud'in ba sai idan ba kud'i hannuna, amma
tunda yanzu zata dawo hannunku da zama
sheyasa zan damk'a maka kud'inta a hannunka
ka adana mata ko ka juya mata su duk yadda
kaga ya dace."
Jiki a sanyaye Hamza yace
"Insha Allah Goggo."
Daga haka Goggo ta tashi ta had'o kayan Amina
tas sannan ta kira mai gadinta ya saka cikin
mota.
Sai da suka ci abincin rana sannan suka koma
gida, inda ko a mota Bilki ce ta rik'e Amina
sannan ga mamakin Hamza bata nuna komai ba
har rungume ta tayi tana fad'a ma Hamza d'iyar
ta shiga ranta sosai. Ba k'aramin sanyaya mishi
zuciya hakan yayi ba, duk wata fargaba dake
ransa ta kau yadda yaga Bilki na tarairayar
Amina kamar 'yar cikinta.
Bayan sun koma gida da daddare Bilki ta had'a
ruwan zafi tayi ma Amina wanka tas sannan ta
shirya ta cikin kayan baccinta wato overall pink
wadda tayi mata kyau, gashin babyn ya wani yi
irin pam d'innan sannan duk da haka a nannad'e
yake gwanin kyau.
Bayan ta gama ta had'a mata madararta ta bata
tasha ta k'oshi, sannan ta rirrigata ta tayi bacci,
duk akan idon Hamza wanda yake mata kallon
mamaki, abinda baiyi zato ba yau gashi Bilki
nayi.
Bayan ta rirriga Amina tayi bacci zuwa tayi kusa
da Hamza tana rok'on gafarar abubuwan da ta
masa, bai gasgata ba sai da ya ga Bilki na kuka
sosai tana rok'onsa, take ya yarda ta yi nadama
don haka sai ya yafe mata suka shirya.
Haka cikin dare da Amina tayi kuka Bilki zata
tashi ta bata madara har ta koma bacci, gashi
sam bata kukan dare yunwa kad'ai ke tashinta
da kuma an bata madara zata koma shikenan
kuma sai asuba.
Da safe ma haka tayi mata wanka tas ta bata
madararta, koda wasa Hamza bai yi tunanin
za'a samu wata matsala ba daga wurin Bilkin
ba.
Don haka sai ya saki jikinsa ya manta da
maganar k'arin aure.
Duk sadda Hamza ke gida to Amina na
hannunsa yana mata wasa, yana ce mata
"Meenah!" Ya bata madara, ya chanza mata
pampers, ya mata tsarki, sannan ya rirriga ta
har sai tayi bacci.
A haka har sunan ya bita don Hamza Meenah
yake ce mata idan yana mata wasa.
Watan Meenah biyar amma ta zama wata irin
k'atuwa tayi nauyi sosai, da k'yar ake d'aga ta,
ga bata wasa da abinci komai ci takeyi, sai
dad'a kyau takeyi kullum.
Hamza na matuk'ar nuna mata kulawa kullum
yana manne da ita especially weekends ranar da
ba aiki, baya zuwa ko ina zai zauna gida yana
kula da Meenah. Sannan komai yana siya mata
daidai gwargwado bai ta6a nuna gazawarsa ba,
tsaye yake kai da fata wajen ganin Meenah ta
taso cikin ingatacciyar rayuwa.
Watan Meenah bakwai daidai Bilki ta samu ciki,
Allah cikin ikonshi cikin baya bata wahala, murna
had'e da godiya ga Allah suka yi ba adadi.
Zo kuga zakwad'i da rawar kai wurin Bilki. Tun
cikin bai tasa ba ta fara siyayyar kaya kamar
hauka a 6oye, tasan Hamza zai bata kud'i idan
lokacin yayi amma tsabar son abin duniya yasa
bata iya hak'uri. Ko kuma ta d'auka idan ya aje
da yake bai ta6a tunanin tana masa sata ba
sheyasa bai farga ba, sai dai idan yaga kamar
kud'in ba daidai suke ba yayi ta tunanin yadda
akayi ya kashe su.
***
Faruk ne kwance bisa gadonsa na alfarma yayi
ruf da ciki yana game cikin system d'insa. Sai
yanzu na k'are ma d'akin nasa kallo, color d'in
d'akin dark da light blue ne, hartta gadonsa blue
ne da bed-sheet d'in da ke shimfid'e a sama.
Carpet d'in da ke shimfid'e a d'akin blue ne.
Gefe guda kuma study table ne shima blue, sai
cikin wata k'atuwar box kayan wasansa ne
wanda mafi yawa nafi hango jirgin wasa kala
kala, hartta kan gadonsa jirgin wasa ne yakai
biyar gefensa, d'aya kuma a hannunsa, a raina
nace to shi kuma son jirgi yake?
Mummy ce tsaye bakin k'ofa tana kallonsa kafin
kuma ta k'araso tare da zama a kusa dashi ta
dafa shi.
Juyowa yayi yana kallonta kafin yace.
"Mummy na."
Murmushi tayi tana shafa gashin kansa sannan
tace
"Faruk ya naga kana game? Ba nace kazo ka
koyi hardarka ba, ba gobe zaka bayar ba a
islamiyya?"
Murmushi yayi yace
"Nayi Mummy."
Tace
"Anya Faruk?"
Yace
"Allah yanzu na gama."
Tace
"Ok zo muje muyi dinner Daddy da Anisah (auta
'yar shekara uku) suna jiranmu."
"Ok." Yace a yayinda ya d'auki jirginsa ya bi
bayan Mummy....
MSB๐
AUREN FANSA 06
✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐๐น๐น๐น⭐๐น๐น๐น⭐
๐น⭐✨⭐๐น⭐✨⭐๐น
๐น✨⭐✨⭐✨⭐✨๐น
✨๐น✨⭐๐⭐✨๐น✨
⭐✨๐น✨⭐✨๐น✨⭐
✨⭐✨๐น✨๐น✨⭐✨
⭐✨⭐✨๐น✨⭐✨๐
๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น
AUREN FANSA!!!
๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น
๐นNa๐น
๐นMARYAM S BELLO๐น
(MSB)
๐๐นPure Moment Of Life Writers๐๐น
๐น06 ๐น
Kan dinning suka nufa inda Daddy da Anisah ke
zaune suna labari harda dariya, zama sukayi
itada Faruk
da Daddy ke musu fira a yayinda Mummy ta
zuba ma kowa abincinsa. Wurin kuma yayi tsit
sai k'arar spoon ake ji. Anisah ce ta katse shirun
ta hanyar jefo ma Daddy tambaya.
"Daddy idan na girma me zan zama?"
Daddy dake shirin kai loma a bakinsa ya dakata
yana kallon Anisah kafin kuma yace
"Anisah kenan, duk abinda kike so shi zaki zama
ay."
Anisah tayi dariya
"Ni banason na zama komai nafiso na shiga
aljanna."
Kowa a wurin sai da ya maida hankalinsa gareta
kafin kuma Mummy tace
"Insha Allah zamu shiga aljanna kinji ko?"
Mummy tace
"Abban Faruk ya batun baka manager d'in ko
sun fasa?"
Daddy yayi murmushi
"Ba fasawa sukayi ba Reemah, sai sun duba
cancanta kafin su bada, idan na dace a bani
manager zasu bani, idan kuma wani ya dace a
ba za'a bashi."
Tayi murmushi
"Haka ne kuma, nidai fatana Allah ya baka sa'a
a dukkan lamuranka"
Yaji dad'in addu'ar matarsa ba kad'an ba,
abinda ke k'ara masa sonta kenan kullum cikin
yi masa addu'a takeyi yana murmushi yace
"Amin ya Allah Reemah."
"Ka fidda ranar da zamu tafi Disney world d'in
kuwa?"
Reemah tace bayan ta had'iye abincin dake
bakinta. Daddy ya sha cup d'in Apple juice kafin
yace
"Eh zuwa upper week dai insha Allah lokacin su
Faruk sun gama exams a islamiyya."
"Yeeyy! Mummy Disney world zamuje da gaske?"
Mummy tayi murmushi tace
"Eh Mamana ko bazaki ba?"
Anisah ta zum6ura baki
"O'o ni zanje."
Faruk yace
"Kalle ta to baza'a dake ba."
Anisha ta sa kuka
"Daddy wai baza'a je dani ba?"
Daddy yayi murmushi
"Ya isa yace bazaki ba, ay kece head d'in tafiyar
gaba d'aya zamu iya barinsa amma ke bazamu
iya barinki ba."
Gwalo ta ma Faruk tana share hawayenta. Faruk
yasa dariya. Anisah tasa kuka.
"Mummy kinga Ya Faruk na min dariya ko?"
Mummy ta harari Faruk
"Zaka fara ko Baba na? Meyasa kakeson ganin
kukan k'anwarka ne?"
Yayi dariya
"Aww dariya ma kakeyi Faruk? Bazaka bata
hak'uri ba?''
Ya buga k'afa.
"Wannan 'yar yarinyar zan ba hak'uri? Tab
bazan bada ba."
Daddy yace
"Just say sorry Faruk, you know she won't stop
crying unless you apologize."
Mummy tace
"Oya Faruk now!"
"Ok sorry!"
Take ta bar kukan inda kuma ta cigaba da cin
abincinta kafin kuma ta kalli Daddy
"Daddy zansha ice cream."
Mummy tace
"Me nace miki akan zak'i?"
Anisah ta turo baki
"O'o ni zansha."
Mummy zata k'ara magana Daddy ya d'aga
mata hannu
"Ba ruwanki Reemah, zan siya mata ice cream."
Anisah tashi tayi da gudu ta wuce parlor tana
tsallen dad'i.
Daddy yayi dariya Mummy na taya shi tace
"Anisah kenan, badai rigima ba."
Daddy yayi dariya
"Lokacinta ne, kema kinyi naki ay."
Mummy tace
"Daddy Faruk fa na wurin."
Yayi dariya
"To sai me? Sai na fad'i abubuwan da kikayi ay"
Da sauri ta tashi tana fad'in
"Haba Daddy!"
Yayi dariya
"Kina tantama ne? Bari kiga..."
Kafin ya k'arasa tayi sama da sauri tana dariya.
Daddy ya tashi ya bi bayanta
"Guduwa kikayi Reemah!"
Faruk tsayawa kallonsu yayi yana dariya cikin
ransa yace
"Allah ka k'ara had'a kanmu what a lovely
family!"
***
Meenah na zaune kan carpet tana wasa da abin
wasanta haka kawai kuma sai tasa kuka, Bilki
dake zaune saman kujera tana shan rake tana
kallon wani movie da take so kukan Meenah ya
cika mata kunne. Tsawa ta daka mata
"Ke da Allah kiyi mana shiru yarinya sai shegen
kuka haba!"
Abinka ga yaro wannan tsawa da aka daka mata
ita ta firgita ta yasa ta k'ara fashewa da wani
irin kuka. Haushi ya cika Bilki yasa ta tashi tayi
shigewarta d'aki ta bar Meenah nan na ta faman
kuka kamar zata shid'e. Meenah tayi kuka
baiwar Allah har ta gaji. Nan ta kwanta k'asa
tayi ta ajiyar zuciya har baccin wahala ya
kwashe ta a nan.
Bilki na kwance a d'aki ta jiyo k'arar shigowar
motar Alhaji. Da sauri ta fito tazo ta d'auki
Meenah dake a k'asa ta rungume ta tare da
zama kan kujera tana rirriga ta.
Haka Hamza ya shigo ya same ta, da murmushi
a saman fuskarsa ya k'araso. Yana zama Bilki
ta kalle shi
"Sannu da zuwa Alhaji."
Yana murmushi yace
"Yauwa sannu da aiki Bilki, Meenah bacci akeyi?"
Tayi murmushi
"Eh wallahi yanzu ta gama rigima sai na rirrriga
ta tayi bacci."
Yayi murmushi
"Meenah kenan, ay batada rigima ma k'ila dai
baccin takeji daman."
Tayi yak'e
"Sosai ma ay Meenah baiwar Allah ce batada
rigima."
Yace
"Hakane Allah ya raya mana ita."
Tace
"Amin."
Yace
"Bari naje na watsa ruwa na gaji."
Tace
"Ok sai ka fito."
Tana ganin shigewarsa ta kalli Meenah taja
dogon tsaki, sannan taje ta kwantar da ita a
d'akin Meenah d'in kan gado.
Bayan Alhaji ya gama wanka suna zaune kan
dinning suna cin abinci ya kalli Bilki yace
"Bilki a gaskiya ba abinda zance miki sai dai
nace Allah ya saka da alkhairi akan aikin ladar
da kikeyi. Allah ya baki lada."
Ta kalli Alhaji tace
"Haba Alhaji meye na godiya ay yi wa kaine,
kuma ma Meenah kamar d'iyar dana haifa haka
na d'auke ta. Idan har kana min godiya sai naji
kamar baka d'auke ta a matsayin 'yar cikina
ba."
Yayi murmushin jin dad'i
"Wallahi ko kusa ba haka bane, kawai dai na
yaba da k'ok'arinki."
Tayi dariya
"Allah sarki. Uhm uhm Alhaji dama madararta da
pampers sun k'are shine nace ya kamata a bad
a siyo mata wasu."
Yace
"Wannan ba damuwa zan baki isashen kud'i ki
siyo mata wanda zai dad'e, naga kamar tafison
madarar ma akan abinci."
Tace
"Hakane."
Bayan sun gama ya d'auko kud'i har dubu goma
ya bata. Amsa tayi tace
"Shikenan zanje na siyo mata.
Yace
"Toh ko ki bari idan na fita na siyo mata mana."
Da sauri tace
"Kai haba kai ina kake da lokaci? Ni da nake
gida kullum ka bari zan siyo mata."
Yayi murmushi
"Toh shikenan."
***
Watan haihuwar Bilki ya kama. Kullum sai ta
tambaye shi kud'in siyayya bai ta6a hana ta ba
saboda har ga Allah ya d'auka Bilki ta shiryu.
Wata rana nak'uda ta kama Bilki gadan gadan,
Hamza ya kaita asibiti, suna zuwa ba'a jima ba
ta haifi 'ya mace. Kyakkyawa fara tas mai
k'oshin lafiya.
Haka aka cigaba da zaman barka inda komai
Hamza yayi mata daidai gwargwado komai yana
tafiya daidai.
Ranar suna yarinya taci sunan kakarta ta wurin
Hamza wato Fatima. Haka aka gama taron suna
aka watse lafiya kowa ya koma gidansa....
AUREN FANSA 08
✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐๐น๐น๐น⭐๐น๐น๐น⭐
๐น⭐✨⭐๐น⭐✨⭐๐น
๐น✨⭐✨⭐✨⭐✨๐น
✨๐น✨⭐๐⭐✨๐น✨
⭐✨๐น✨⭐✨๐น✨⭐
✨⭐✨๐น✨๐น✨⭐✨
⭐✨⭐✨๐น✨⭐✨๐
๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น
AUREN FANSA!!!
๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น
๐นNa๐น
๐นMARYAM S BELLO๐น
(MSB)
๐๐นPure Moment Of Life Writers๐๐น
Another page for my Ummi Aisha thanks for all
the support and care one love dear๐Allah ya k'ara
basira Amin๐น
๐น08 ๐น
Laila ce ta cigaba da magana.
"Ko dai har yanzu baki fahimta ba ne?"
Ajiyar zuciya Bilki tayi, sannan tace
"A gaskiya Laila ban iyawa, kisa fa kika ce? Don
ina son dukiya sai akace na kashe su, gaskiya
mu chanza shawara dai."
Laila tayi kwafa.
"To sai akace mu zamu bisu mu aikata
k'udirinmu? Ko kusa ba haka nake nufi ba,
abinda nake nufi a nan shine..."
Nan naga ta rad'a mata wata magana daga
k'arshe dukkansu suka kwashe da dariya.
Bilki tana dariya tace
"Shegiyar gari, lallai Laila sai dai a barki amma
ke shu'uma ce wallahi."
Hajiya Laila ta k'yalk'yale da dariya sosai
sannan tace
"Kema haka."
Bilki ta tashi tana gyara zaman d'ankwalinta
tana kallon Laila tace
"Kamar naji kuman Zarah bari na dubo ta."
Laila tace
"Yi sauri kuwa nima naji."
Jim kad'an sai ga Bilki ta shigo da Zarah a
hannunta da alama yanzu Zaran ta tashi daga
bacci, tana zuwa Laila ta mik'a hannu ta fara
mata wasa, can sai ga Meenah ta fito da alama
bacci ta tashi don kuwa kanta buzu buzu yake,
saboda yanayin gashinta mai cika kuma ga
tsawo sheyasa ko ya ta kwanta sai yayi buzu
buzu. Zuwa tayi kusa da Bilki tana murza idanu.
Su kuwa sai faman ta6e baki sukeyi. Meenah
tace
"Maama wunwa."
Laila ta ta6e baki tace
"Uban me tace?"
Bilki tace
"Ohon mata, ke tafi can ki bamu wuri."
Abinka ga yaro da ba ganewa tayi ba, sai ma ta
matso kusa da Bilki ta jingina da ita. Da sauri
Bilkin ta hankad'e ta gefe ta fad'i k'asa tim!
"Wannan yarinya anyi mayya! Mts." Cewar Laila
had'e da jan tsaki.
Bilki ta jawo hannunta da k'arfi, Meenah ta
fashe da kuka.
Kitchen suka nufa ta had'a mata tea a cup tana
tsaki sannan ta dire mata k'asa.
"Oya zauna kisha yarinya bata aje komai ba sai
ci? Haba!" Nan ta zauna ta shanye tas sannan
ta fito daga kitchen d'in.
Tana gama fad'an haka ta fice taje ta had'o ma
Zarah cereal ta koma parlor, Laila ke bata har ta
kammala sannan aka bata ruwa.
A tare suka girka abincin rana inda Laila tayi ma
Zarah wanka, sannan suka dafa fried rice da
papered chicken sai had'ad'en salad. Wuraren
uku da kwata Laila tayi sallama da Bilki ta tafi
gida.
Sai wurin biyar saura sannan Bilki tayi ma
Meenah wanka ta bata abincin rana.
Kamar kullum bayan Alhaji ya dawo gida yayi
wanka yaci abinci, suka zauna palor suna 'yar
fira kafin a kira sallar magrib. Kasancewar
Meenah batasan dawowar Baban nata ba, tana
can d'aki tana wasa. Sai data fito, aiko tana
ganin shi ta rugo da d'an gudunta ta zo kusa da
shi tana fad'in
"Dada!"
Cike da jin dad'i Alhaji yace
"D'iyar Dada ashe ana ciki, zo nan."
Tana zuwa ya d'auke ta ya zaunar kan cinyarsa
yana mata surutu tana dariya. Can kuma sai
tace
"Dada kaga Maama ta bije ni d'azu."
Ya ware idanu
"Me kikayi wa Maama ta bige ki?"
Tayi shiru tana kallonsa can tace
"Bakomai."
Bilki ta taso tana dariya tace
"Kai yaro ma dai daban ne, d'azu ne fa na shiga
wanka nazo na iske ta tana zubar da madara,
shine fa nace mata kar ta k'ara. Alhaji yayi
dariya
"Ah ah Meenah a daina 6arna ba kyau kinji ko?
Idan Maama tace a daina a daina kinji?"
Ta gyad'a kai. Sai kuma yace
"Bilki ya naga Meenah ta rame ne ko bata son
cin abinci?"
Tayi dariya tace
"Ay Alhaji inda kasan yadda nake da fama da
yarinyar nan akan taci abinci ko? Sai kayi
mamaki sam batason ci na rasa dalili."
Yace
"To kuma ya baki sanar dani ba? Muka sani ko
wani abin ke damunta? Kinsan yaro tunda ba
fad'a zatayi ba."
Tace
"To k'ila dai."
Ya juyo da dubansa ga Meenah
"Haba Meenan Dada, meyasa baki cin abinci?"
Nan ma shiru. Yayi murmushi
"Zaki sha ice cream?"
Nan take da washe baki tana murna. Shima yaji
dad'i yace
"Yauwa to bari idan na fita yanzu kafin na dawo
gida zan siyo maki harda biscuit ma."
Saukar da ita yayi daga cinyarsa yace
"Bilki bari na wuce masallaci lokacin sallah yayi
sai na dawo."
Tace
"A dawo lafiya."
Sai da ya fita ta bishi da harara dashi da
Meenah dake tsaye a tsorace gaban Bilki.
Tana huci tace
"Gaskiya abinnan ya fara isa ta, sai wani nan
nan yake da yarinyar nan amma naga ba
ruwanshi ma da Zarah, lallai Alhaji ka haifi d'iya
a cikinka amma ka nuna son d'iyar wata? To da
sake mts."
Daga nan ta shige d'aki, Meenah na tsaye tana
zare idanu.
Haka kuwa akayi Alhaji da zai dawo sai da ya
tsaya ya siya ma Meenah ice cream da biscuit
sai ya k'aro mata kayan lashe lashe na yara.
Zarah kuwa wani d'an abin wasa ne na yara ya
siya mata tunda yasan bata isa shan wad'annan
kayan ba.
Yana dawowa Meenah ta tare shi tana murna,
ya bata ice cream d'inta nan ta zauna ta shanye
tas sannan ya bata biscuit d'inta ta tafi d'aki.
Abin wasan yara ya bama Zarah dake hannunsa
yana mata wasa. Ita kuwa sai dariya takeyi.
Bilki na zaune kusa dasu tana wasa da Zarah.
Can Alhaji yace
"Ina Meenah tayi ne?"
Tayi tsaki a ranta tace
"Yanzu ta tafi d'aki ay ta ga k'wad'ayi kuma
tunda bazata ci abinci ba."
Tashi yayi yana fad'in
"Ina zuwa."
Ta6e baki tayi tana mai jin haushin Meenah.
Yana shiga d'aki ya ishe Meenah kwance k'asa
da biscuit a hannunta bacci ya kwashe ta.
Murmushi yayi ya d'auko ta ya d'ora ta kan
gado, ya gyara mata kwanciya sannan ya kashe
fitilar ya fito.
Koda ya fito Bilki bata nuna komai ba, Zarah ta
k'ar6a tayi d'aki da ita don yi mata wanka.
BAYAN KWANA BIYU
Bilki ta fito wanka da safe kiran Laila ya shigo,
tana d'auka Laila tafara magana
"Kash Hajiya Bilki yanzu naji labarin iyalen Alhaji
Adam sun koma Abuja gaba d'aya."
Da sauri Bilki tace
"Haba dai? To yanzu ya kenan?"
"Bansani ba nima, plan d'inmu ya rushe don
gidansa na Abuja akwai tsaro sosai, ko ina sojoji
ne a gidan."
Bilki tace
"Gaskiya akwai had'ari mu ce zamuyi wani motsi
yanzu. Amma ki bari tukunna a sake shawara."
"To shikenan." Laila tace tare da katse kiran.
Nan tayi ta sak'a da warwara ta rasa mafita.
***
Haka rayuwar ta cigaba da gudana har akayi
shekara d'aya amma har yau sun rasa wata
mafita.
A lokacin kuma Meenah ta shekara biyu harda
rabi Alhaji ya fara shirye shiryen saka ta
makaranta da kuma islamiyya. Don ya fuskanci
zata iya da wuri don a yadda ya fahimce ta, ta
iya saurin d'aukar abu da kuma maganarta ta
fito ga surutu ba abinda bata fad'i.
Sheyasa ma yanzu Bilki ta rage takura mata don
muddin Alhaji ya dawo zata kwashe komai ta
fad'a masa. Tana gudun kar tun baya tunanin
komai har ya fara zarginta...