_*Sun tanadarwa da mata kayan gyaran jiki masu kyau da inganci magungunansu babu almundahana a ciki mutukar kika fara amfani da ingantattun magungunan company manzil alwafir to ba zaki daina ba saboda ingancin magungunansu ko wace matsala kike fama da ita mutukar ta shafi zamantakewar auranki manzil alwafir zasu share miki hawaye da akwai gruops na mussaman da suka bude domin taimakon mata masu fama da matsaltsalo a gidan auransu idan kanki na cikin duhu mutukar kinyi rijistar dasu to kukanki ya 'kare idan kina bukatar kiyi rijistar sai kiyi magana.*_
*******Humm! Rayuwa kenan Naja'atu 'yar gata kuma 'yar gaban goshin Abbah Abbas ita ce kasance a wulakance a lalace a hannun Bash! shi yaci mutuncinta mahaifiyarsa da 'Yar uwarsa suci mutuncinta su wulakanta su takata yanda ransu yake so, gabadaya munira ta sanja mata tsakaninsu kallon banxa ne da baqar magana, sosai take cikin mawuyacin hali da takura wayarta kuwa dama tuntuni ya 'kwace dan ranar da zai kwace wayar tana jin mahaifiyarsa na zugashi a kan ya kwace wayar domin wai barin wayar a hannunta a kwai matsala kada taje ta tona masa asiri a gari.......Aikuwa a ranar ya kar'be wayarsa ya barta cikin halin bakin ciki da damuwa kasancewar wayar na d'ebe mata kewa sosai haka dai cigaba da ta kasance cikin damuwa gami da nemawa kanta mafita domin tana ganin Bash da mahaifiyarsa da 'Yar uwarsa rayuwarta kawai suke nema to idan ba hakaba me tayi musu da zafi da zasu dinga a zabtar da ita! abinci sun daina bata mai kyau wani sa'in ma yini take da yunwa a gidan sai taji tana shirin mutuwa tukkuna za taje ta tsaga billeta tace tana bukatar abinci to nan ma sai anja mata rai za'a sa mai aiki ta kawo mata shima ba wanda zai gamsar da ita ba, hakanan take hakuri ta kar'ba taje taci ta kwanta, sannan komai dare Bash ya dawo daga yawonsa haka zai afka mata yayi ta sasakarta tana ihun wahala saboda gabadaya rashin gamshashshen abinci mai gina jiki yasa ni'imar ta ta dauke kullum a bushe take qamas! haka bash yake gwada mata rashin imani yayi ta jajjagarta yana kokarin kaita lahira.......Aikuwa kafin kice kwabo ta lalace ta zama tamkar zautacciya kusan kullum cikin firgici take daga ta kwanta bacci za tayi ta muguwayen mafarkai marasa dadi! rashin abinci da rashin kwanciyar hankali da kulawa ya mayar da Naja'atu shuru shuru kullum tana dakinta a zaune ko a kwance yanzu ta daina wasa da ibadah lokacin sallah nayi za tayi ta d'aga hannunta sama tana rokon Allah ya kawo mata mafita.
Ranar Lahadi Mommy da Munira tun safe suka fita gidan sai ya kasance shuru kadaici da damuwa ya isheta sai ta shirya tsaf ta fito cikin hijabi ta fito harbar gidan tana kalle kalle so take ta samu ta fita daga gidan taje ta nemi gidan mmn sajida ko zata taimaketa da shawarwari tunda dai mmn sajida tasan labarin rayuwarta to watakila akwai irin taimakon da za tayi mata.
Maigadin gidan ne taga ya bude gate mota ta shigo gabanta ya yanke ya fad'i dan a tunaninta ko Bash ne har tana mamakin abinda ya dawo dashi kuma! sai taga bashi bane mahaifinsa ne ya fito daga motar yana sanye da 'kananun kaya shart da jins da farin gilashi a idonsa, dama bata ta'ba ganinsa ba sai a hoto kallo daya tayi masa ta sunkuyar da kanta tana jin faduwar gaba! wani irin kallo Alhaji Aminu yake mata, da sauri ta tsuguna har kasa tana gaisheshi.
Yana wani murmushi irin na shegun 'yan duniya ya amsa yana shafa gemunsa ta mike tana kokarin komawa gurinsu....Yace."Doghtar zo muje akwai muhimiyar maganar da nake so nayi dake." A sanyaye ta kalleshi tana mamakin maganarsa wace irin magana zaiyi da ita, cikin zuciyarta tace ko dai ya samu labarin bakar wahalar da muta nan gidan suke baki zai rarrasheki! A jiyar zuciya ta sauke tabi bayansa cikin gidan tana jin faduwar gaba kad'an.
Kasa nutsuwa tayi a palon sanin da tayi cewar babu kowa hatta da mai aiki bata zauna ba itama ta tafi sabgoginta tunda tasan da cewar masu gidan basa nan tayi tafiyar ta sai da yamma zata dawo tayi aikace aikacenta.
Tana zaune a inda take taji muryarsa yana kiranta daga cikin dakinsa...Ta amsa da sauri ta mike ta nufi dakin....Gabanta ne yayi wani irin faduwa ganinsa daga shi sai gajeran wando a tsaye a bakin kofar dakin...Da sauri ta juya zata fita kawai taji ya ri'ki hannunta ya janyota ta fad'o jikinsa! taji yana kici kicin kulle kofar...."Innalillahi wa'ina ilahi raji'un! Abinda ta ambata kenan tayi kukan kura ta bangaje shi da mugun gudu ta fita daga dakin tana gyaran hijabinta daya tattare! A sukwane ta fito a harabar gidan tana rarrabawa idonta sai haki! take tana waige waige! can ta nufi bakin gate gabanta na dukan uku uku! tana kokarin bude karamar kofa maigadi ya fito daga dakinsa ai kafin ma ya karaso ta bude ta fice daga gidan....maigadi daya fuskanci cewa itace sai ya mayar da kofar ya rufe ya koma ya zauna hankalinsa kwance dan baiyi tunanin guduwa tayi ba...
Hanya ta kama ta dingi tafiya tanayi tana goge hawaye gami da nanata kalmar innalilihi wa'ina ilaihi raji'un! jama'a wane irin gida Allah ya kaita Ashe shima maigidan d'an busuru ne? wai shin to da yake kokarin kulleta a dakinsa me yake shirin yi mata.
Tsayin wata uku da tayi a gidan bata ta'ba ganinsa ba saboda washe garin daurin su yayi tafiya, a tunaninta dawowarsa kenan! amma saboda tsabar shi mara mutunci ne zai haike mata a matsayinta na matar d'ansa! Babu shakka rayuwarta na cikin gagarimin had'ari! dole ne ta nemawa kanta mafita tun kafin wata mummunar qaddara ta afka mata.
Taci bakar wuya kafin ta kai kanta gidan mmn sajida, lokacin ma da taje bata nan ta tafi kasuwa cefena, sai ta samu rumfar kwanon da jama'a ke zama ta zauna tana wani irin nishi mai wahalar gaske........Duk wanda zai wuce sai ya kalleta kai wasu ma har tsayawa suke suyi mata magana, ganin haka yasa tayi shahadar shiga gidan mmn ladi! tana shiga soron gidan ta soma jin muryar mmn ladi sai zage zage takeyi! kafin tayi wani yunkuri taga mutum ya fito yana gyara kwalar rigarsa sai zabga tsaki yake, da yake Saleh ba a cikin hayyacinsa yake ba bai ma ganta ba yasa kai ya fita daga gidan....Naja'atu tayi kasaqe tana jiyo mmn ladi na fad'in "Shege tsinanne wallahi na daina yarda kana yi min hawan qawara kullum sai kazo kana cikani da dad'in baki da daddare ka haye kaina kayi ta suburbudata amma washe gari idan na tambayi kudin cefane kace baka dashi to wallahi na daina yarda da kai tunda abun ya zama rashin mutunci to kwanan auran ma siyarwa zanyi idan kana bukata sai ka biya kudin zan barka kayi aikin banza kawai."!!
Naja'atu gabanta ya tsananta fad'uwa shin wane irin zaman aure mmn ladi takeyi da mijinta? idan akwai matsala su rabu ai babu dole mai zai sanya kullum su dinga tsinewa junansu....Gidan ta shiga da sallama a bakinta, mmn ladi na huci! tace" Ke kuma daga ina? dama baki tafi garinku ba."? a sanyaye tace"Na tafi qaddara ta sake dawo dani."
Mmn ladi taja tsaki mai qarfi tace"Ke! kowa da kika gani yana da matsala dan Allah kada kice zaki fad'a min matsalarki ki rabu dani naji da matsalar da ta dameni.
Zama tayi kan tabarma tace"Mmn ladi dan Allah zauna mu fuskanci juna." Mmmn ladi tayi mata wani irin kallo kafin ta zauna tana kallonta tace me kike shirin fad'a min ne."?
Murya na rawa tace"Mmn ladi dan Allah ki dinga sawa zuciyarki ruwan sanyi kafin na shigo gidan nan duk naji irin xage zagen kikeyi dan Allah ki daina babu kyau zagin miji da tsiyatashi ko banza kun haihu da juna idan ya lalace zaki fi kowa jin ciwo saboda yayan da kuka haifa tare.
Mmn ladi ta sauke gwaron numfashi kafin tace"Wallahi naja'atu mutumin nan bashi da mutunci tunda ya aureni yake bani wuya, gabadaya baya sauke hakkina da yake kansa kin dai zauna kwana biyu kinga irin rayuwar da nakeyi abinci ma da kyar yake bani! da farko na dauka babu ce sai da nayi bunkice na gane cewar yana samun kudi kawai yana bakin cikin ya kawo gida sai dai yaje ya lalatar a waje da daddare kuma ya isheni da jaraba shiyasa na yanke shawara kan cewa duk ranar da ya nemi yayi wani abu dani sai ya biya ni dan ni ba shashar mace bace.'' Naja'atu shuru tayi tana nazarin maganar matar tace"Mmn ladi ki daina wannan maganar dan Allah musulunci bai hallata hakan ba, ki amince da mijinki a duk lokacin daya bukace ki mutukar ba a cikin tsarki kike ba, sannan dan Allah ki daina kama mijinki da kokawa kuna dambe a gaban yara kinga karfin ku ba daya bane kuma kina da 'ya mace watarana abinda kika aikatawa akan babanta itama shi zata aikatawa mijinta, kuma idan ban manta ba kwanaki naji mmn sajida na yi miki nasiha kan cewar ki dinga hakuri da kad'an! idan ba zaki iya ba to ki kama sa'ana shi kuma ki kyaleshi da halinsa mutukar yana zalintarki sai ubangiji ya saka miki wannan tashin hankalin da kikeyi da masifa ba shine zai kawo miki kwanciyar hankali ba.
Mmn ladi jikinta yayi sanyi jin nasihar da naja'atu tayi mata tace"Shikkenan na'ajatu zanyi kokarin ganin na dauki shawararki amma wallahi abin ne da ciwo ace dari biyu shine kudin cefanan gida ki duba kiga yanda rayuwar nan ta koma komai yayi tsanani!! kuma yanzu da kike maganar na kama sana'a ina naga jarin da zanyi sana'ar dashi." ? Ajiyar zuciya ta sauke tace"Insha Allahu ni idan na samu yanda nake so zan baki jari ki dinga sana'a domin ki rufawa kanki asiri amma dan Allah ki daina wannan mummunar d'abiar da kikeyi a gidan auranki." Allah sarki Naja'atu rayuwa ta koya mata hankali wai yau itace takeyi wa wata nasiha...Mmn Ladi tace"To nagode sosai Naja'atu Allah ya saka da alkairi." Naja'atu na kokarin yin magana mmn Sajida ta shigo gidan ganin naja'atu yasa ta tsaya tana mamaki! murmushi mai ciwo naja'atu tayi tace"kinyi mamakin ganina ko."? Mmn sajida tace"Wallahi kuwa ai na dauka kin tafi." Naja'atu a sanyaye tace"Na tafi mummunar qaddara ce ta sake dawo dani.'' Mmn sajida ta rike bakinta had'e da fadin wace irin mummar qaddara kuma."? Mmn Ladi tace"Nima mamakin maganar nake dama yanzu nake shirin tambayarta sai gashi kin shigo."
Mmn sajida ta zauna kusa da ita tace"Ni wallahi jikina yayi sanyi da jin wannan maganar naja'atu wace irin qaddara ce ta dawo dake garin jos."?
Zafafan hawaye ne suka shigo zubowa daga idonta tana kuka mai tsuma zuciya ta shiga basu labarin abinda yake faruwa, tun daga farkon al'amarin harkarshe bata 'boye musu komai ba sai da ta fad'a musu.
Maman Ladi ta rike baki cikin mamaki gami da al'ajabi tace Ikon Allah "Yanzu Naja'atu dama ashe kece matar da Bash ya aura? mu dai mun samu labarin cewar yayi aure ya auri yar kano kuma bazawara har a gari a kan dinga surutu da yawa mutane na cewa dama sai da yaje inda ba'asan halinsa ba ya nemi aure dan gabad'aya mu nan mun sanshi kuma mun san mummunar sana'arsa ta 419 (damfara) gami da sace sace a manya gurare uwa uba Harkar luwadi da yake yi........Gaskiya duk wanda yake da hankali ya kuma san waye bash to ba zai dauki 'yarsa ya aura masa ba dan a zahirin gaskiya bash ba mutumin arziki bane kuma ba mutumin da zakayi fatan ka had'a zuria dashi bane! sai kuma maganar mahaifinsa da kikace ya kulleki a daki yana neman lalata dake gaskiya nayi mamaki sosai dan a sanin da jamaar gari sukayi masa mutumin kirki ne! to amma babu mamaki Ubangiji ne yayi nufin tona masa asiri watakila ya dad'e yana lalata da 'ya'yan mutane sai yanxu asirinsa ya tuno gaskiya duniyar nan a bar tsoroce wallahi naja'atu na tausaya miki da tun farko kinzo ki fad'a min halin da ake ciki wallahi da bazan barki ki auri Bash ba(Allah sarki mmn sajida a lokacin da idanun naja'atu suka rufe kome zaki fada mata a kan auranta da bash ba zata dauka ba) Mmn Ladi tace"Ni wallahi abin ne ma yake bani mamaki na rasa abinda zance Allah dai yasa baki da ciki dan shine babbar matsalar a yanzu.
Naja'atu na goge hawaye tace"Bana tsammanin inada ciki mmn ladi ni tunani na yanda zanyi na ku'buta daga hannun wad'annan mugwayen mutanan."
Mmn Sajida tace"Gaskiya zamanki a tare dasu bai taso ba yana da kyau ki nemawa kanki mafita kije gida ki shedawa iyayenki halin da ake ciki."
"Mmn sajida ina jin kunyar tunkarar iyayena da wata magana wallahi mahaifiyata tayi min gargadi kancewar kada na sake nazo gida da wata matsala tunda dai ni naji na gani da auran bash to naje na zauna nayi hakuri.....Mmn Sajida tace" To ai wannan matsalar babbace dole su san da ita idan baso suke ki shiga cikin masifa ba." Shuru tayi tana kuka gami da tunanin yanda za tayi.
Naja'atu haka ta wuni a gidan mmn sajida suna ta bata sharwarin yanda za tayi da zata tafi mmn sajida ta bata dari biyar hade da soyayyan nama mai uban yawa, har bakin titi suka rakota ta shiga napep su kuma suka juya suna sake tattauna maganar...
Cikin fargaba ta shiga gidan tayi sauri ya shiga gurinsu ta rufe da key sabida har yanzu tsoro takeji kada 'katon kwarton gidan yasan ta dawo yazo ya afka mata.....Da yake taci abinci ta koshi a gidan mmn sajida bata damu ba sai tayi kwanciyarta tana ta istigifari a cikin zuciyarta.
*ANGO*
'bangaran Abbah Abbas kuma al'amura suna ta tafiya cikin tsari da kwanciyar hankali maganar auransa da Zainab ta kammala iyayensa da duk wani makusancinsa yasan da maganar, Halisa ta shiga cikin tsantsar tashin hankali da damuwa jin cewa mijin nata zai auri yarinya mafi karancin shekarun Naja'atu sai duk ta raina kanta kullum tana kwance a daki tana nadamar rayuwa........Duk abinda ake bukata ango yayi Abbah Abbas yayi wa yarinyar sannan itama halisan yayi mata dadai gwargwado duk domin ya kwantar mata da hankalinta....Gidanshi dake 'Danbare yasa aka sake qawata shi da abubuwan morewa rayuwa da jin dadi! dama bangare uku ne nashi guda na amarya daya na uwargida daya.........Kafin zuwan ranar daurin auren da kansa yaje har gidan Limamin yaga yarinyar masha Allah ya yaba sosai da ita Zainab mai matsaikacin tsayi da 'yar qiba amma ba mai muni ba, kuma masha Allah tana da kyau daidai gwargwado dan ba za'a sata a layin munana ba, sai dai yanda yarinyar ta kar'be shi tana nuna masa iyayi da rashin ta ido abin ya bashi mamaki mutuka ya lura da yarinyar na sonsa sosai mussaman yanda take yawan kiran wayarsa a kai a kai da sassafe zata kirashi ta gaisheshi idan rana tayi zata kirashi ta tambayeshi yanayin kasuwa, idan dare yayi kafin ya kwanta sai ta kirasa tayi masa sai da safe! Sai al'amarin ya dinga bashi mamaki mutuka yana mamakin wayo da dubarar yarinyar babu shakka ko cikin mata uku ya ajiyeta zata iya zama dasu saboda tana da wayo da kuma iya mu'amula ba irin Naja'atunsa sarkin rigima da koke koke ba....Yanzu dai komai ya kammala an kuma tsayar da ranar da za'a daura aure juma'a mai zuwa bayan an gabatar da sallar juma'a.
******
Naja'atu daina shiga sashen su mommy tayi har sai da ta tabbatar da cewar maigidan ya gama hutunsa ya tafi sannan ta cigaba da shiga nan ma idan ta shiga da sun gaisa bata dadewa take fitowa! Munira kuwa dama dawowar mahaifin nasu ne yasa ta tsahirta da abinda take, yana tafiya kuwa ta cigaba da yawace yawacenta sai taje gidan Muktar tayi sati daya ko biyu acan ba tare da damuwar mahaifiyarta ba..........
bash da abokanan sana'arsa sunyi nasarar shiga wani babban bank sunyi gagarimar sata ta maqudan kudade, dama duk sanda suka bushi iska haka suke shirya irin wannan ta'addacin saboda sun tanadi matakan kare karansu kome zasuje suyi a guri babu wanda zai gansu sai bayan sunyi sun gama ma'aikatan gurin zasu fahimci akwai matsala haka zasuyi ta binkice daga inda matsalar ta afku idan sun kasa ganowa sai su hakura......To yau dai Allah ya nuna musu ikonsa idan sunayin abu suna ganin babu wanda yake ganinsu to shi yana ganinsu kuma yau yayi nufin tona musu asiri bayan sun fito daga bank din sun shiga motocinsu lokacin CCTVCAMERA ta tona musu asiri dan wani irin qara ta dinga yi tana nuna akwai babbar matsalar dake faruwa, kafin kace kwabo ma'aikata da jamian tsaro kowa ya ankara sun fito hankali a tashe nan suka hangi motacin su Bash na kokarin fita daga bank din, a guje! jama'an tsaro suka shiga mota suka bi bayansu da harbi! abunka da dare gari yayi shuru sai karar harbi ne ke tashi.....Su bash sun tsorata mutuka dan rana bata ta'ba kwace musu irin yau ba, sai kawai kowa ya shiga kokarin tserar da kansa...Bash tunda ya samu ya sunkuci wata jaka wacce take sha'ke! da kudi yayo fit ya fito daga motar ya nausa cikin daji ya dingi gudu shima yana sakin harbi da bundigarsa....Sauran su ganin matakin da bash ya dauka dama shine garkuwarsu tunda shine kadai yake da bindaga, sai kawai suka bude mota suka fito da gudu suna kokarin arcewa! Cikin ikon Allah Allah ya bawa jami'an tsaro sa'a suka rufar musu, da harbi a take suka fad'i a gurin suna wani irin ihu! da rirrike kafafunsu.
Bash kuwa yana samun nasarar shiga gida sai ya sauke ajiyar zuciya ya sake rike jakar kudin dake hannunsa da kyau, yana wata iriyar tafiya ya nufi bangaransa, maigadi dai binsa da kallo yake dan yanda ya shigo gidan a guje kuma a gigice ya nuna masa cewar akwai babbar matsalar dake faruwa.
Naja'atu na tsaka da bacci ta dinga jin motsi da buge buge a firgice ta mike zaune tana kokarin kunna hasken dakin, Shi ta gani yana ta aikin zazzage kudi yana shiryawa cikin wata akwati mai fadi! A tsorace tace"Bash wannan kudin fa."?....."Shiiiii."! Yayi mata hade da dora yatsansa a saman le'bansa! Naja'atu tayi shuru tana kallonsa gabanta sai buguwa yake babu shakka Bash sata yaje yayo a wani gurin....Tana zaune tana kallonsa ya gama shirya kudin tsaf-tsaf taga ya mike ya bude gurin kayansa ya dauko wasu bakake yasa a jikinsa ya sunkufe kansa da bakar hula ya saka face mark a fuskarsa hankalinta ya tashi miyau ya qafe a bakinta lokacin da taga yazo ya tsaya a kusa da ita sai da ta kusa sakin fitsari! jajayan idanunsa kawai take kallo, taji yace."Naja'atu yau karshen zama dake yazo na sakeki saki uku! inaso ki cireni daga rayuwarki ki manta kinsan Bashir a rayuwarki, burina ya cika na samu kudaden da zasu isheni na qetara qasar waje naje naci karena babu babbaka saboda haka wannan itace magana ta dake ta karshe."! Yana gama maganarsa ya sunkuci! akwatin kudinsa ya kama hanyar fita......Cikin wani irin masifaffan yanayi na tashin hankali da razani ta d'aga hannunta hade da kiran sunansa *"BASH!!"* Juyowa yayi ya kalleta yayi wani irin murmushi kafin ya daga mata yatsun hannunsa biyu ya bude kofar dakin ya fita da gaggawa!
"Innalilihi wa" ina ilaihi raji'un." Kalmar da ta iya furtawa kenan ta kwanta a gurin tana wani irin kuka na tsantsar tashin hankali gami da nadamar rayuwar da Bash ya jefa kansa a ciki.......Haka ta kasance har asubah! lokacin da take yunkurin mikewa domin daura alwala a lokacin ne kuma ta dinga jin kukan motar jama'an tsoro a cikin gidan....A furgice ta mike tsaye ta nemi zaninta ta daura kan rigar baccinta ta zura hijabinta ta fara kokarin fita, tana fitowa palo suka shigo su kusan bakwai ko wanne hannunsa da bindiga suka shiga rarraba idanunsu a palon!! Hannu tasa ta rufe bakinta jikinta na wani irin karkarwa! Babban cikinsu yace."Ina Bash yake shi kadai muke nema kada ki firgita." Saboda tsananin firgicin da take ciki kasa magana tayi ta zube a gurin tana sake qumshe bakinta ji takeyi tamkar ana ragargaza mata gwiwowinta.....Tsawa! mai qarfi ya buga mata ya d'ora mata tsinin bindiga a goshinta yace."Zaki fada mana inda mijinki yake ko sai na sakar miki bullet."! Allah sarki Naja'atu fitsari ne ya kwace mata a gurin, cikin wata iriyar magana tace"Ya had'a kayansa ya fice daga gidan tun misalin biyu da rabi ya shigo naga yana hada kudi a kwati da nayi magana yace nayi shuru bayan ya gama ya tsaya a kaina tare da fad'a min hukuncin da ya yanke a kaina ya sake ni saki uku."
Bakin bindigar ya cire daga kanta yace."Tashi muje kiyi mana jagora cikin gidan inda iyayensa suke. Ta mike da sauri suka tasa ta a gaba har dakin Mommy wacce take ta sharar baccinta.....Jin tsinin bindiga a saman goshinta yasa ta tashi a firgice tana zazzare ido! ganin jamian tsaro yasa gabanta ya yanke ya fadi! ta kalli naja'atu a tsorace tace"Me yake faruwa ne? naja'atu yanzu sai dai kika tonawa mijinki asiri."?
Jin wannan magana da tayi yasa babban cikinsu yace."Ina Bash."? Ta kalleshi cike da fargaba tace me yayi muku kuke nemansa wallahi matarsa sharri tayi masa."
Lafiyayyan mari ya kwada mata ya kalli na gefansa hade da umartarsa daya daura mata ankwa! Mommy ta dinga kuka tana musu magiyar su kyaleta da fadin duk zargin da suke akan yaronta ba gaskiya bane.....Yace."Tunda mun samu labari daga bakin maigadi cewa uban yaron baya gari to ke zamu kama mu daure a madadinsa duk inda yake idan yaji labarin kina hannunmu zai bayyana kansa dama mun dade muna bunkice a kansa alhamdullhi yau Allah ya bayyana mana shi." Mommy kuka kawai takeyi tana basu hakuri sunki kulata suka angiza keyarta
Naja'atu kasa motsi tayi jikinta sai rawa yake tana kallo suka sata a cikin motarsu tana kuka tana kiran sunanta tare da fadin ta taimaka mata, hakika ranar taji tausayin matar sosai da sosai! babu shakka son zuciyarsu shine ya janyo musu shiga wannan masifar su haifi d'a a cikinsu amma su dinga turashi yana sata ai dama hausawa nacewa duk tsuntsun daya ja ruwa shi ruwan kan doka, tabbas da haihuwar d'a irin Bash to gwara Allah ya barka babu haihuwa domin hakan shi zai fi maka alkairi a rayuwarka....A sanyaye ta juya domin zuwa taje ta had'a kayanta.
*😀Yau akwai Celaberation Vip madadi ga pege din da kuke ta jira ya iso😍 Sai dai kuma akwai sauran qalubale anya kuwa mutumin naku zai mayar da Naja'atu dakinta kuwa? duba da cewar Allah yayi masa sauyi na Alkairi ina ganin da qyar idan zai waiwayi naja'atu da maganar kome amma dai bari mu gani😢*
*Littafin na kudi ne....*
Koda zaki ganshi a groups na sata ne idan kina da bukatar biyan kudin karatu ga yanda abin yake Vip group #600 normal #300 accont numbar...0542382124...Binta umar gtbank...Idan katin waya zaki tura kiyi min mgn ta whasap da wannan number
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
57
Wata qaramar akwati mai tayoyi ta samu a dakin, ta kwashe masa tarkacen kayansa da suke ciki a guruguje ta shirya 'yan kayanta da basu kala biyar ba ta rufe da sauri ta gyara hijabinta ta dauki akwatin ta kama hanyar fita daga dakin.....Tana fitowa harabar gidan taga dandazon jama'a harda 'Yan jarida sun cika gidan suna tayi wa maigadi tambayoyi, tsorata tayi dan gabadaya bata so a watsa hotonta a duniya jama'a su ganta su sheda ta a matsayin matar d'an ta'addah! Tana kokarin ratsesu ta fita daga gidan wani dan jarida yasha gabanta yana yi mata magana tare da kara mata wayarsa a daidai bakinta, rufe fuskarta tayi da hijabinta muryarta na rawa tace"Dan Allah ka matsa ka bani guri na fita ni ban san a binda ke faruwa ba....Dan jaridar yace."Hajiya a matsayinki na matar Bash wanda ake zarginsa da aikata munanan ayyuka wanda suka sa'ba dokar qasa da kuma dokokin musulunci muna bukatar jin ta bakin ki dangane da wannan al'amarin da ya faru." Jin muryar d'an uwansu yana tambayar Naja'atun yasa da sauri sukayi mata caaaa! a kanta kowa na miqa abin daukar rahotonsa a bakinta.......Tana kakkare fuskarta da hijabin ta tace"Na fad'a maka nima ban san komai ba akan wannan al'amarin kuma ka daina dangantani da Bash domin yanzu ba mijina bane."! Tana maganar suna daukar hotonta had'e da daukar muryarta........" Duk da haka hajia ba zaki rasa ta cewa ba a kan wannan abun tunda dai a kan idonki komai ya faru." Da sauri ta dauki akwatinta ta fice daga gidan, kamar mayu suka bi bayanta har wajen gidan suna daukar hotonta...sai da ta qule tukkuna suka koma cikin gidan tare da titsiye maigadi da tambayoyinsu kamar yanda suka saba.
Dari biyar din da Mmn sajida ta bata kwanakin baya da ita tayi kudin mota mai Napep ya ajiye ta har kofar gidan, ta bashi kudinsa da sauri ta shiga gidan tana jan akwatin hannunta.
Mmn Sajida na yanka salak kawai ta ganta ta shigo a firgice!! Mmn Sajida ta ajiye wukar hannunta da sauri ta miqe ta rike ta tana dudduba jikinta had'e da godewa Allah!
Naja'atu rungume ta tayi ta dinga wani irin kuka na tsantsar tausayin kanta...mmn sajida kasa daurewa tayi sai ta shiga tayata kukan tana rarrashinta da kalamai masu sanyi, har sai da ta samu tayi shuru hankalinta ya dawo jikinta tukkuna tace" Naja'atu naji dadin ganinki wallahi dama tun dazu nida mmn ladi muke zancen ki dukkaninmu mun shiga damuwa sakamakon jin abinda ya faru da mijinki mun samu labari cewar jami'an tsaro sun kama mahaifiyarsa saboda basu samu nasarar kama shi ba sai muke ta fargaba ko sun hada dake sun daure, mun dade da mmn ladi muna tattauna maganar kafin ta shiga gidanta.
Naja'atu na goge hawayen da suka kasa tsayawa tace"Mmn Sajida tunda nake banta'ba shiga masifa irin ta jiya da yau ba! Allah ne kawai ya nufa ina da sauran kwana a gaba da tuni sai dai kuji mummunan labari 'Yan sanda sun harbeni." Mmn Sajida ta rike ha'ba! cike da tu'ajibin al'amarin tace"Haka kawai baki ji ba baki gani ba su harbe ki sai kace kece kika turashi yaje yayi sata ai naji dadi da suka kama uwar tasa tunda dama sune suke daure masa gindi nasan yanzu ai duk inda labari yake yajewa Alhaji Aminun shima nasan sai sun daureshi kuma insha Allahu asirinsu sai ya tuno."
Ajiyar zuciya ta sauke tana girgiza kanta tace"Mmn Sajida na tabbata jami'an tsaron nan da basu tarar da mahaifiyarsa a gidan ba to ni zasu kama a madadinsa kinga kuwa dole na shiga tashin hankali wallahi har yanzu ban dawo daidai ba."Mmn sajida na kokarin yin magana Mmn Ladi ta shigo gidan, ganin Naja'atu a zaune yasa ta sauke ajiyar zuciya tana godewa Allah ta zauna suna sake jajanta al'amarin a nan ne Naja'atu ta tabbatar musu da saki ukun da Bash yayi mata.
Mmn Ladi ta dinga tsine masa tana fad'in " Allah ya rabaki da masifa Naja'atu fatan mu anan shine Allah yasa baki da ciki shikkenan kin rabu da alaqaqai gabad'aya." Naja'atu tace"Ni sai maganar ciki kike kina fad'ar min da gaba na fad'a miki tun zuwan da nayi kwanakin baya bani da ciki dan Allah ki daina wannan maganar." Mmn ladi tace"To shikkenan na daina tunda bakya so Allah ya kiyaye gaba." gabadayansu suka amsa da "ameeen Ya Allah."
To labarin al'amarin dake faruwa a garin Jos ya zagaya sauran jahohi ta hanyar kafafan sadarwa, kowa sai fad'ar albarkacin bakinsa yake...To Abbah Abbas ma dai a labaran karfe hudu na tashar freedom redio ya saurara lokacin ma yana kasuwa...... Al'amarin ya firgitashi jin mai gabatar da labaran na fadin sunan Alhaji Aminu dan jarida yana sake jajjadawa cewar a cikin masu laifin harda d'ansa mai suna Bashir wanda dubunsa ta cika a ranar dama kuma tsohon mai laifine wanda ake nemansa ruwa a jallo......Yana tsaka da mamakin al'amarin yaji sun sako muryarta lokacin da takewa d'an jaridar nan bayani kan ya kyaleta da tambaya ita bata san komai ba......Wani irin gumi ne ya shiga tsatstsafo masa a saman goshinsa Yasa hankici ya goge yana cigaba da sauraran muryar mai labaran....Sai da a ka gama labaran tsaf! ya samu damar ajiye wayar ya shiga mamakin al'amarin ya jima sosai cikin alhini da tunanin wace irin rayuwa yarinyar take ciki kafin ya sauke ajiyar zuciya daga bisani yayi furucin alkairi akan abunda ya faru tare dayiwa wad'anda ake tuhuma da laifin adduar shiriya, da fatan Allah yasa 'karshen masifar kenan....Ammafa jin muryar Naja'atu cikin tashin hankali ya tsaya masa a zuciya yana so yayiwa abokinsa magana idan sun tashi daga kasuwa yana tunanin wani abu, zai dai saurara ya gani ko shi abokin nasa zai fara tuntun'barsa da maganar yasan tabbas ya samu labarin abinda ke faruwa da 'Yar uwar tasa....
Bayan kwana uku al'amura sunyi sauqi Naja'atu ta samu nutsuwa gidan Mmn Sajida sosai take kulawa da ita gami da bata ingantaccen abinci mai kyau tana ci ta koshi, sannan idan sun ke'be tayi ta rarrashinta gami da nuna mata ta kwantar da hankalinta ta dauka abunda ya faru da ita qaddara ce bayan nan kuma ta shirya fuskantar iyayenta da maganar domin su san halin da ake ciki...Duk sanda Mmn Sajida tayi mata wannan maganar takan shiga damuwa sosai da sosai, itafa yanzu gabad'aya kunyar had'a ido take da kowa dan idan ta koma gida bata san da wane ido zata kalli mutane dashi ba, auran data qallafa ranta a kansa gashi anyi mata amma wata uku da kwanaki ya wargaje anyi mata saki mafi muni irin wanda Allah baya so, to ta yaya ma zata iya yi musu bayanin yanda al'amuran suka kasance, kullum da wannan tunanin take kwana da kuma shi take tashi.
Yau dai Mmn Sajida kafin ta fita gurin sana'arta tace"Lallai dole sai ta kira wayar wani mafi kusa da ita ta fad'a masa ga halin da take ciki dan zaman da takeyi bashi da amfani iyayenta basu san halin da take ciki ba.
Gudun 'bacin ran Mmn Sajidan yasa ta kar'bi wayar tata ta sanya numbar aunty maryam a kai, gabanta na dukan uku uku ta shiga kiran number
Aunty maryam na gidan Alhaji suna ta shirye shiryen daurin aure kasancewar washe garin ranar daurin auren Abokin mijinta shiyasa ta yini gidan Alhaji suna ta aikace aikacen walimar da angwaye zasuyi bayan daurin aure.......Duk da bata sheda numbar ba hakan bai hanata dagawa ba tayi sallama a nutse tare da fad'in "Da wa nake magana."
Naja'atu tayi wani qwal-qwal! hawaye na kokarin sauko mata sai dai ta daure murya na rawa tace"Anty maryam kina magana da Naja'atu."
Cike da farin ciki Aunty maryam tace"Naja'atu idonki kenan? ashe kina nan kin ya damu kwana biyu me ya samu wayarki ne sai ayi ta kira bata shiga."
Murya na rawa tace"Lalacewa tayi." Tace"Ayya! shiyasa mana to ina fatan dai kina lafiya ya maigidanki."? Tace"Lafiya anty ya nake jin hayaniya a kusa dake."
aunty maryam tace"Ina gidan Alhaji wallahi muna aiki Gobe bayan sakkowa daga sallar juma'a Abbah Abbas zai daura aure." Aunty Maryam bata fad'i maganar da wata manufa ba tsakaninta da Allah ta fadi maganar ba dan ta cuzgunawa naja'atu ba tunda ita a ganinta ai babu wata alaqa a tsakaninsu da zai sanya taji zafi dan zaiyi aure.
Ita kuwa Naja'atu ji tayi tamkar Naja'atu maryam din ta fad'a mata ranar mutuwarta wani irin zazzafan gumi ya shiga yanko mata....Zazzafan kishi! ya turnuqeta! murya na rawa tace"Aunty maryam wace magana naji kina yi waye zaiyi aure ban fahimce ki ba."?
Aunty maryam ta fuskanci sauyin yanayi a tattare da Naja'atun sai ta sassauta murya tace"Abbah Abbas nake nufi nace dake gobe zai daura aure insha Allahu."
Kuka ta fashe dashi murya na rawa tace."Aunty maryam da bakinki kike fad'a min wannan maganar shin kin san halin masifar da nake ciki kuwa."? Aunty maryam tayi kasaqe da waya a kunnanta jikinta yayi sanyi jin irin kukan da Naja'atun takeyi, tace"Kiyi shuru dan Allah kiyi min bayanin abinda ke faruwa."
Kai tsaye tace"Aunty Maryam Bash! Yayi min saki uku yau kwana uku da suka wuce."....."Innalilihi wa'ina ilahi raji'un! kalmar da aunty maryam ta furta kanan wacce tayi dadai da zuwan hajia gurin tana tambayar ta abinda yake faruwa take furta wannan kalmar.........
*Littafin na kudi ne...!*
Koda zaki ganshi a gruopa na sata ne idan kina bukatar biyar kudinn karatu ga yanda abin yake...
Vip gruop#600 normal group#300 account.. 0542382124...Binta umar gtbank...Idan katin waya zaki tura kiyi min mgn ta whasap da wannan number.
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
Barkamu da Juma'a My Fans💞 Ina rokon Allah ya sadamu da alkairan dake cikinta 👏🏻
58 Hajia Abu ta qaraso inda aunty Maryam take hankali a tashe take tambayarta abinda ke faruwa. Aunty Maryam jiki a sanyaye tace"Naja'atu bari zan kira ki anjima."Sai kawai ta kashe wayar tana kallon hajian bakinta sai rawa yake yi tsabar fargaba da tashin hankali ya hanata magana, ita ma Hajian jin ta ambaci sunan Naja'atu sai gabanta ya tsananta faduwa ta zauna kusa da ita tare da dafa kafadarta tace"Maryam me yake faruwa da Naja'atu? jikina yana bani akwai mumman abinda ke faruwa da rayuwarta."Aunty Maryam tayi qasa da kanta tana tunanin yanda zata fad'a mata maganar....Aure wata uku kacal har anyi angama kuma saki har uku dan tsabar wulakanci a ganinta ko wane irin laifi naja'atu tayi bai cancani a wulakantata irin haka ba(Hausawa nacewa ciwon 'ya mace na 'ya mace ne) hakika aunty maryam ta tausayawa Naja'atu sosai yarinya da quruciyar ta da komai maza sai katantawa suke da ita, koda yake na farko itace taqi to amma wannan a tunaninta ba daga gurinta bane kawai ta had'u da sharrin d'a namiji....Sai da ta dan samu nutsuwa tukkuna ta d'ago kanta cikin tararrabi da alhini tace"Hajia al'amarin ne babu dadin ji wallahi shiyasa kikaga duk jikina yayi sanyi Naja'atu ce ta kira ni take tabbatar min da cewar wai mijinta ya saketa saki har uku kwana uku da suka wuce."
Hajia tayi salati tana sanar da Ubangiji tace "A kan me? me tayi masa yayi mata wannan wulakancin saki Uku!!? innalillahi wa'ina ilaihi raji'un! Ai kafin kice kwabo palon ya cika da jama'ar da suke waje mafi akasari 'yan uwan Alhaji ne da hajian sai kuma Yaya Ramlatu! dukkanisu suka dinga tambayar ba'asin abinda yake faruwa, Aunty Maryam da hajia sukayi shuru domin sirrinta al'amarin, irin wannan maganar ba mai dadin fada bace shiyasa sukayi shuru.....Yaya Ramlatu tayi murmushi tana girgiza kanta tace" Hajia meye abun 'boye magana nifa dama nasan sai haka ta faru shuru kawai nayi muku ban sanar miki da halin da ake ciki ba, kwana uku da suka wuce na samu labarin abinda ya faru da mijin data aura ashe d'an fashi ne 'barawo d'an shaye-shaye d'an Luwadi ne manemin mata! ke mutumin daj mugun mai laifi ne jam'ian tsaro sun jima suna nemansa sai a ranar dubunsu ta cika shida abokanan harkarsa sun shiga wani bank sunyi sata sun fito asirinsu ya tuno yanzu dai 'yan sanda sun samu nasarar kama abokan harkar tasa shi kuma ya tsere amma sun damqe mahaifiyarsa jiya na sake samun labarin cewar sunje har inda mahaifinsa yake sun damqe shi, yanzu dai sun baza binkice sosai dan gano inda yake shima su damqe shi! ai wallahi naso harda ita shegiyar suka damqe dama ai duk tsuntsun daya ja ruwa shi ruwa kan doka! makwadaita kawai gashi nan sun dauki 'yarsu saboda tsabar kwadayi sun aurawa 'barawo."
Palon yayi tsit! kowa yana mamaki da salati a cikin zuciyarsa! Yaya Ramlatu ta cigaba tsinewa Baba malam dashi da zuriarsa tana kwashe musu albarka! Hajia da taga abun nata na nema ya wuce gona da iri sai ta tsawatar mata Yaya Ramlatu ta fita daga palon tana cigaba da surutai....Hajia ta sallami kowa tace kowa ya koma ya cigaba da aikinsa.
Shuru palon yayi bayan fitar jama'ar hajia ta kalli anty maryam dake zaune da waya a hannu tace"Sake kiran number data kira ki da ita.'' Aunty Maryam ta duba numbar da sauri ta shiga kira... swich up wayar a kashe take! tayi ta kira ana ce mata a kashe take, cike da mamaki tace"Yanzu fa mukayi waya amma duba suna cewa a kashe wayar take."
A sanyaye hajia tace"To watakila babu chaji a wayar anjima kadan kafin ki tafi sai ki sake gwadawa mugani." Aunty maryam tace"To shikkenan.
Naja'atu bayan gama wayarsu da aunty maryam kwanciya kawai tayi tana kukan bakin ciki! gami da nadama da dana sani! Hakika tasan duk abinda ya faru da ita itace ta janyowa kanta, gashi yanzu tazo tana dana sani wanda hausawa ke cewa qeya ce! da tasan auran Bash ba zai tsinana mata komai ba data hakura ta zauna a dakin mijinta data san Bash amanarta zai ci to da babu abinda zai sanyata ta fujirewa auran *MADADI* da iyayenta sukayi mata, hakika da tasan Bash ba mutumin kwarai bane to da babu abinda zai saka ta za'be shi a matsayin abokin rayuwarta...Data san ! data san! Data san! (babu wanda yasan gaibu sai Allah kuma komai ya faru da rayuwarki qaddara ce amma kuma akwai son zuciya da qin jin maganar magabata mafi akasari iyaye zasu za'bawa d'ansu abunda yake alkairi ga rayuwarsu sai su kuma 'Ya'yan fujire su nuna ga abinda suke so, hausawa nacewa abinda babba ya hango yaro ko ya hau bishiyar rimi ba zai hango ba)
Mmn Sajida data gaji da rarrashinta sai kawai ta fita gurin sana'arta ta qyaleta dan al'amarin Naja'atun tana gani kamar yafi karfinta......Mmn Sajida da wayarta ta fita tana so ta bayar a kai mata chaji kasancewar kwana biyu wutar unguwar ta lalace sai ta ajiyeta a kusa da ita ta cigaba da hada hada da jama'a! kawai wani d'an bana bakwai yazo siyan abinci ya dauketa yasa a aljihu a gurguje ya cinye abincinsa ya bar gurun.....Sim card din ya cire ya yar ya qara gaba abinsa.
Sai bayan jama'a sun tsagaita ta qwalawa Walid kira ya fito daga cikin gidan Mmn Ladi yana amsawa, ta laluba kusa da ita zata dauki wayar taji wayam! tashi tayi tana zazzage jikinta tana dubawa babu waya babu dalilinta, ta dudduba bata ganta ba sai tace"Shiga cikin gida ka tambayi Naja'atu ko wayar ta nan watakila dama ban fito da ita ba.
Yaron ya shiga gidan da sauri ita kuma ta cigaba da abinda take....Minti biyar Walid ya fito yace."Mama wai tace baki wayar a cikin gidan ba da ita kika fito kika ce zaki bada chaji ."
Mmn Sajida tace"Shikkenan sun sace yau kuma tsautsayin a kan wayata ya afka ai shikkenan Allah ya mayar min da alkairi." Mutanan dake tsaye a kanta suka shiga jajanta mata, tace"Wallahi ni layina ma nake ji." Da sauri daya yace''Bani numbar na kira muji." Da sauri ta shiga fada masa yasa a wayarsa a take aka ce masa wayar a kashe take, ya dinga kiran yana sake bude hands free domin taji! Girgiza kanta tayi tace"qyale kawai ai duk wanda ya dauka dama ba zai barta a kunne ba yaje yayi min guzirin kiyama zai biyani a inda bashi dashi." Mutumin yace."Kinyi magana hajia Allah ya mayar miki da alkairi shi kuma daya dauka Allah ya tona asirinsa.
Amma yana da kyau kije ayi miki swapping d'in layin naki saboda jama'arki." Tace"Habu sai na samu lokaci zanje kana ganin dai irin sana'a ta bani da lokacin kaina amma insha Allahu na samu lokaci zanje ayi min.
Naja'atu taji takaicin sace wayar da akayi, haka sukayi ta maganar kafin su hakura, Mmn Sajida ta cigaba da sabgoginta kamar ma 'batan wayar bai dameta ba ita kuwa Naja'atu damuwa ta shiga sosai ta dinga tunanin hanyar da za tabi domin ganin ta taimaki kanta da kanta.
Aunty Maryam dai haka ta gaji da kiran waya ta hakura domun har ta zo tafiya wayar bata shiga ba, Hajiyar tace ta bari kawai tunda taqi shiga....Gabadaya da ita da hajiyan a sanyaye suka rabu da juna
Tun a mota take so tayi wa mijin nata maganar tana jin tsoro dan akwai sanda ta ta'ba yi masa maganar yarinyar ya nuna mata koda wasa kada ta kuskura ta sakeyi mata maganarta, ya nuna mata cewar shi babu ruwansa da yarinyar, a lokacin har sa'bani suka samu sabida hakan, ya daina mata magana tsayin kwana uku, al'amarin ya dinga bata mamaki! mutum da 'yar uwarsa ina laifinta dan ta nuna kulawarta a kanta zai dinga gaba da ita, sai itama ta fusata ta dauke masa wuta! kwana uku dan karan kansa ya sakko ya nemi shiri da ita to tun daga ranar bata sake yi masa maganar yarinyar ba...Sai yanzu da take ganin dole ta fad'a masa abinda ke faruwa tunda dai yarinyar babu wanda ta fara nema da maganar sai ita to tilas ta fad'a masa koda kuwa zai dauki gaba da ita kamar wancan karon....Ta kalleshi a nutse tace"Wai kasan abinda yake faruwa da Naja'atu kuwa.? Abbah Magaji na driving yace."Maryam ashe ban hanaki yi min maganar yarinyar nan ba."? Tace" Kamar yaya? wannan wai wace irin magana kakeyi Naja'atu fa kanwarka ce uwa daya uba daya duk abinda zanyi a kanta saboda kai zanyi amma sai ka dinga nuna wani abu daban.
Yace."To bana so na fad'a miki babu ruwana da yarinyar nan, kada ki sake ki tunzura min zuciyata duk abinda ya faru da ita itace ta janyowa kanta." Murmushin takaici tayi tace"Au! ashe kasan abinda yake faruwa tsayin kwana uku kayi shuru da bakin ka ko."? Yace." Na sani asirin mijinta ya tuno wanda nasan dama komai daran dadewa dole sai haka ta faru dashi wannan yaron mugun mai laifi ne ni ganau ne ba jiyau ba shiyasa lokacin auran naqi saka kaina a ciki saboda nasan karshe ba zaiyi kyau ba."
Tace"To dai yanzu duk wata magana ta qare tashin ma maganar bacin rai ne dan Allah kayi hakuri ka yafe mata kuma ku duba halin da take ciki! Dazu ta kirani a waya tana kuka take sheda min cewar ya saketa saki uku! Tsabar tashin hankalin dana shiga a lokacin yasa na kasa tambayarta inda take, na kashe wayar, to kuma dana sake kira sai wayar taqi shiga nida hajia mun shiga damuwa sosai da sosai A nan ne nima nasan abinda ke faruwa a bakin Ramaltu.....Yace."Maryam ki rabu da yarinyar nan dan Allah! ai tasan hanyar gida, tunda ya saketa to zaman me takeyi sai ta tattaro ta dawo gida. Buqatarta ta biya."
Maryam shuru kawai tayi tana jimanta al'amarin Eh wannan itace shawara mai kyau tunda babu aure a tsakaninta da Bash din to zaman da takeyi a gidan bai da amfani ta tattaro ta dawo gida ta nemi gafarar iyayenta.
Washe garin ranar haka kowa ya wayi gari cikin alhini da damuwar abinda ya faru da Naja'atu, dan Hajia kasa barin maganar tayi a ranta a daran ta samu alhaji ta sheda masa halin da ake ciki....Alhaji Sama'aila ya shiga tashin hankali gami da damuwar abinda ya faru da rayuwar Naja'atu, mutumin kasa bacci yayi a daran saboda alhini da asubah kuwa suna fitowa daga massalaci ya samu malam suka ke'be guri daya, kafin ya sheda masa abunda ke da akwai sai da yayi masa nasiha sosai sannan ya sheda masa rayuwar da Naja'atu take ciki....Baba malam ya jima kansa a kasa yana kiran sunan Allah kafin ya d'ago kansa ya kalli Alhaji a nutse yace."Allah yasa haka shi yafi alkairi a rayuwata, hakika na jima banji abinda ya tayar min da hankali irin wannan ba ashe dama yaron nan dashi da mahaifinsa ba mutanan arziki bane suka zo suka yaudaremu muka dauki amanar yarinya muka basu, to babu komai ai tunda da alkairi muka nufe su suka nufe mu da sharri ina rokon Allah yasa haka shi yafi alkairi." Alhaji yace."Wannan adduar itace abinda ya kamata sabida haka yanzu na yanke shawara cewa bayan anyi daurin auran nan hankali ya kwanta gobe da wuri zan sa direba ya dauki Hajia Rabi tunda ita tasan gidan taje ta dauko yarinyar ina ganin wannan shine abinda yafi kamata muyi.
Baba malam yace."To hakan yayi Alhaji nagode kwarai da gaske ina rokan Allah ya dubi gabanka da bayanka halinka nagari ya bika a duk inda kake." Alhaji Sama'ila ya mika masa hannu tare da fad'in "Babu komai malam Naja'atu tamkar 'yar cikina haka na dauketa dole ne na tsaya a cikin al'amuranta inayi mana fatan alkairi gabad'ayan mu."
*ANGO*
A shirya ya fito daga dakinsa yana sanye da wata dakakkiyar geznar milk color babbar riga da 'yar ciki da wani irin sirfani mai kyau a wuyan babbar rigar! Kasancewar shadda mai haske ce yasa yayi amfani da baqar hula had'e da bakin takalmi sau ciki agogon dake daure a hannunsa na dama shima baki ne, kai hatta da links din da yayi amfani dasu masu duhu ne! Wani irin kamshin turare yake mai dadi irin na manyan mutane! Kallo guda nayi masa na tabbatar da cewar ya amsa sunansa na ango sai dai kuma yanayin rashin walwala dake fuskarsa yasa na gane cewar akwai abinda ke damunsa.
Koda ya fito bai tunkari ko ina ba sai dakin Halisa...Tana zaune kasan kafet abin duniya ya taru yayi mata yawa, ga tarin magunguna nan a gabanta Halisa har yanzu taqi lafiya daga an toshe waccar matsalar sai wata ta bayyana yanzu wasu irin qananun kuraje ne suka feso mata a gabanta da matsematsin cinyarta kullum cikin susa take duk ta kwailaye fatar jikinta! Wannan dalilin yasa Abbah Abbas baya yarda wata mu'amula ta aure ta shiga tsakaninsa da ita ko toilet dinta baya shiga yayi wani uziri saboda a gabansa Dr Sa'adatu ta tabbatar masa da cewar Halisa na dauke da mugun sanyi wanda yayi masifar cin karfinta, wannan dalilin yasa ya janye jikinsa sosai da ita sai dai kuma duk wani abu da take bukata yana yi mata kuma yana tsaye kan duk wani maganin da Dr zata bada umarnin siya komai tsadarsa kuwa zai fitar da kudi ya siya sannan kuma ya jajurce a kan ta tayi amfani da maganin a kan ka'ida
Ganininta a firgice a lalace! yasa jikinsa ya d'anyi sanyi, Halisa sarkin kwalliya da gayu itace ta koma wata iriya tamkar mara hankali! Tausayinsa yaji saboda yasan duk irin halin da ta jefa kanta a kansa ne wannan dalilin yasa ya sassauta fuskarsa ya shiga dakin ya zauna gefan gado yana kiran sunanta.
Ta dago tana kallonsa wasu lafiyayyun hawaye suka wanke mata fuska! In da saboda ya saba da ganin wannan hawayen nata
Gyaran murya yayi a nutse yace."Ina fatan kinsha maganin naki a kan ka'ida."? Hanci ta shaqa! wasu hawayen na sake shararo mata, Yace."Kiyi hakuri wannan koke koke bashi ne mafita ba a gurinki addua ce mafita ki roki Allah ya yaye miki sai dai kuma ba zan gaji da fada miki cewar kece kika siya da kudinki dan haka dole kiyi hakuri ki 'kar'ba! ni nayi miki al'kawari insha Allah daga dubu daya zuwa miliyan daya zan iya fitarwa a kan lafiyarki saboda haka ki kwantar da hankalinki! ki cigaba da rokan Allah ya baki lafiya ."( Lallai Abbah Abbas ka cika dan halak) Halisa hannu tasa ta goge hawayen fuskarta tace"Abbahn mufida nagode sosai dan Allah kada ka juya min baya." Murmushi yayi yace"Halisa nasan fa duk wannan masifar da kika shiga saboda da ni ne to akan me zan sake ki ko na juya miki baya ni ba haka nake ba, zaki cigaba da zama a matsayin matata har karshen rayuwarki."
Hanci taja ta sunkuyar da kanta a qasa tare da fadin "Nagode Abban Mufida." Mikewa yayi yana duba agogon hannunsa yace."Ni zan tafi gurin daurin aure." Ta kalleshi le'banta na rawa tace"To Allah ya sanya alkairi."
Amin yace a takaice ya juya da niyar fita daga dakin.....Kallo ta bishi dashi hawaye wani na bin wani lallai babu shakka abunda yafi karfinka dole ka saka masa ido...Yau mijinta da take bala'in so zai daura aure da dalleliyar budurwa tabd'ijam! ashe da ranta za taga wannan ranar.
*To Alhamdullhi*
An daura aure lafiya 'Bangaran Amarya suna cikin tsantsar farin ciki tare da taya 'yarsu 'yar uwarsu Zainab dace da samun miji nagari.....Yayin da kuma 'Bangaran ango dashi kansa angon suke cikin damuwa da tararrabi al'amarin da yake damunsu, ha'ki'ka! Yanda suka nuna damuwarsu a kan al'amarin Naja'atu zaka fahimci cewar suna tsananin qaunarta gami kuma da tausaya mata, wannan dalilin ne ma ya sanya bayan hankula sun kwanta suka ke'be kansu gabad'aya harshi angon suna tattaunawa dangane da abunda ya faru, a nan ne Alhaji ya sake sanar musu da shawarar da ya yanke na tura Hajia Rabi taje ta daukota ...Gabad'ayansu sun amince da hukuncin da Alhajin ya yanke.
Cikin gidan Alhaji ma hakane ya kasance Baba Talatu da Hajiya aunty Maryam su kad'ai ne suka san abinda ke zuciyarsu kawai dai sun sake ne suna hidima da jama'ar da suka tara......Ita kuwa Yaya Ramlatu ta manta da wata Halisa yanzu ta amarya take, ta tara mutane a gefe guda sai hira suke suna shewa babu abinda ya dameta, burinta kawai a kawo amarya taga wace iri ce idan irin wacce za'a had'u da ita a rufawa kai asiri ce to za tayi kokarin riketa hannu biyu! Zata kuma yi kokarin ta d'orata a kan hanyar data d'ora Halisa a kai......Kwana biyu da Halisa ta daina daukar shawararta duk a dame take ga rashin kudi da yake damunta! a lokacin da suke tare da Halisa kudi basa yanke mata dan sosai Halisa take sato mata kudin mijinta ta bata, to cikin kwanakin duk a takure take, dan tayi tayi da Halisan akan tazo su sake komawa gidan Boka Halisa taqi amincewa shine take jin haushinta ta daina zuwa dubata! so take amarya tazo su had'a kai su muzgunawa Halisan.
*ANGO DA AMARYA*
Abbah Abbas kasa Ta'bukawa amarya komai yayi saboda rashin nutsuwa da kwanciyar hankalin da yake ciki, hakanan yana ji yana gani ya sanyawa dalleliyar amaryasa ido bayan sun gabatar da sallar ma'aurata sai kawai ya umarceta da taje ta kwanta! Zainab ta mike a nutse taje ta kwanta tana mamakin rashin walwalar angon nata, duk da bata da shekaru da yawa amma tana da wayo kuma tasan yanda ango ke rawar jiki a kan amaryarsa idan bata manta ba akwai wata kawarta mai suna Mariya da akayiwa aure ta dinga basu labarin irin rawar jikin da angonta ya dinga yi mata a daran amarcinsu.......Kuma itama ba saurayi bane zaiyi Abbah Abbas d'in! Dan har da sukaje gidan suka dinga sha'awar irin rayuwar da 'kawarsu mariya takeyi da sugar dady d'inta! lokacin itama taji tana sha'awar auran manyan mutane saboda taga yanda mijin Mariya ke kula da ita yanda ya kamata! To sai gashi burinta ya cika angon nata sai wani salalaf-salalaf! yake yi kamar wani mara laka a jikinsa sam baya wani nuna gand'okin sa a kanta......Haka tayi bacci cike da takaici da bakin ciki...Da asubah ta gane a dakin ya kwana dan ganin wayoyinsa a kan bed kusa da ita...Alamu sun nuna mata cewar ya tafi.massalaci. Sai ta mike ta nufi toilet, tayi wanka da alwala ta fito ta shirya jikinta tsaf tsaf! ta hau kan dadduma ta gabatar da sallar! Sai da tayi addua sosai kana ta mike ta nufi mirror dinta dake shaqe da kayan kwalliya, Zainab ta zauna ta tsantsara kwalliya mai kyau da burgewa har dasu gashin ido sosai tayi kyau ta fito amarya sak! Zama tayi kan bed tana jiran shigowarsa....Koda ya shigo dakin kasa dauke idonsa yayi daga kanta..Yaushe rabon da yaga irin wannan kwalliya tun kafin Halisa ta kwanta ciwo, dama itace ke yi masa irinta Naja'atu dama can wannan kwaliye kwaliyen bai dameta ba! Shi kuma gashi yana san gayu! Zainab sarkin dubara da wayo ko a fuska bata nuna masa jin haushin abinda yayi mata jiya ba ta tsuguna har a qasa ta gaidashi, ya amsa yana mirmushi mai kyau da ma'ana, kanta ya dafa a nutse yace."Allah yayi miki albarka! Ta amsa da ameen tana fari da idonta! saurin dauke kansa yayi yace"Tashi muje ku gaisa da Halisa da yaran ki ko." Murmushi tayi a nutse tace"To Habibi." Mikewa tayi ta yafa mayafi a jikinta sai murmushi take tana sunkuyar da kanta! Ya kama hannunta ya ri'ke a cikin nasa suka fita daga dakin.....Kai tsaye 'bangaran Halisa suka nufa.......
*Littafin na kudi ne...!*
Koda zaki ganshi a groups na sata ne idan kina bukatar ki biya kudin karatu ga yanda abin yake....Vip group #600 normal gruop#300.. accont number.. 0542382124...Binta Umar gtbnk...Idan katin waya zaki tura kiyi min mgn ta whasap da wannan number
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
*******59 Baba Larai kad'ai suka samu a palon tana aikace akaice kamar ko da yaushe suka gaisa a mutunce ya tambayeta kwanan yara tace"Sun tashi lafiya kalau." Zainab ta dan risina cike da ladabi ta gaisheta, Baba Larai ta amsa cikin farin ciki tana jin dadin girmamata da yarinyar tayi lallai babu shakka duk inda ta fito gidan mutunci ne....Zainab din ya dan kalla yace."Ki zauna bari na shiga gurin 'Yar uwar taki." Tace"To tare da samun guri ta zauna kan kujera, Baba Larai ta juya domin cigaba da aikinta tana murmushi Lallai Allah ya musanyawa da Alhaji zankad'ed'iyar mata sarkin ado da kwalliya dama hausawa nacewa wani hanin ga Allah baiwa ne......Su saddiqa ne suka fito daga dakinsu ita da Mufida suna sanye da Atampa iri daya shi kuma Mussadiq yana sanye da shadda blue color tsaf tsaf dasu suna gudanar da komai nasu cikin tsari da tarbiya dan sosai baba larai take tsaye a kansu da kula da tarbiyarsu.
A nutse suka gaishe da Zainab suna mata kallon rashin sani, ita kuwa Zainab sai murmushi take tana jan hannun Mussadiq har sai da ta samu nasarar zaunar dashi a kusa da ita tana masa magana, Baba Larai ta kalli Saddiqa tana murmushi tace"Naga sai kallon rashin sani kuke mata itace sabuwar aunty ku Amaryar Abbanku."
Saddiqa da Mufida suka shiga dariya suna 'boye fuska, Baba Larai tasa dariya tana fad'in "Au! kunyarta kukeji? To amarya ga 'ya'yanki nan wai kunyarki sukeji."
Zainab na dariyar farin ciki tace"Haba dai meye najin kunyata ni mamanku ce ku saki jikinku dani kome kuke so kiyi min magana zanyi muku."
Mussadiq na murmushi yace."Aunty ya sunanki."? Tace."Sunana Zainab." Yayi qasa da kansa yana murmushi tare da fad'in "Aunynmu munji dadin kasancewa dake muna miki fatan alkairi.'' Cike da nishadi ta amsa da ameen tare da dan rungumeshi a jikinta, aikuwa a kan idon Abbah lokacin da yake fitowa daga dakin Halisa tana biye a bayansa....Ganin yaransa na murmushi ga Mussadiq rungume a jikin Zainab sai yaji wani farin ciki a cikin zuciyarsa yarinyar ta sake samun matsayi a zuciyarsa....Halisa ta danji dama dama dan tayi wanka tayi kwalliya daidai gwargwado amma ganin amarya zainab sai da ya sanya ta shiga cikin halin damuwa, daurewa kawai tayi ta zauna tana dan kauda kanta daga kan yarinyar....(Kishin nan fa dole sai anyi) Itama Zainab din kafin ta gaida Halisan sai da ta dan jima tukkuna tace" Aunt Ina kwana fatan kin tashi lafiya ya jiki kuma."? Cikin dauriya tace"Lafiya lau jiki da sauki nagode sosai." Shuru tayi da bakinta tana jin wani irin bakin kishi na taso mata a ganinta ai tunda ya samu wannan 'yar yarinyar magana ta qare tafi kowa sanin halin mijinta gurin son matan tsiya watakila ma tun daran jiya ya gama da yarinyar, sai taji hawaye na kokarin zubo mata...Ta riga ta tashi daga aiki a gurinsa tunda tsoron ma rike hannunta yake sabida kada ya dauki cuta(Kaico da wannan rayuwa da kika jefa kanki).....Abbah Abbas na qayataccen murmushi yake kallon Zainab yace."Ina fata kun gaisa sosai da yaran naki."
Yarinyar ta wani wulkita ido tana gyara bakinta cikin wata iriyar magana tace"Wallahi mun gaisa dasu sosai kuma naji da dadi dana samesu masu tarbiya da girmama na gaba dasu a gaskiya Habibi family d'inka sun burgeni sosai ina rokan Allah ya albarkace ni da samun zuria da kai." Palon yayi tsit! Sakamakon maganar da Zainab take yi! Baba Larai da Halisa kasa 'boye mamakinsu sukayi sai da suka kalli yarinyar suna jimanta bud'ewar idonta kamar ba 'yar malamai ba😀 gata 'karamar yarinya amma sai firirita take gami da zaro zance ko kunyarsu ba taji." Shi kuwa lafiyayyan murmushi ne a kwance a fuskarsa yace"Naji dadi kwarai da adduarki zainab Allah ya tabbatar mana da alkairi." Ta amsa da amin tare da gyara zamanta a kan kujera
Halisa ta daure zuciyarta sosai ta kalleshi a hankali tace"Abbah Mufida ina ganin zan koma na kwanta jikina bana jin dadinsa." Yace."Okey kafin ki kwanta ki tabbatar kinyi braek ki kuma tabbatar da kinsha maganinki." Mikewa Tayi a hankali tare da fad'in."Insha Allah ." Zainab ta kalleta babu yabo babu fallasa tace"To aunty Allah ya sawaqe." Ciki ciki ta amsa ta bar gurin, Abbah ya kalli Baba larai a nutse yace."Komai ya kammala."? Tace"Eh Alhaji." Mi'kewa yayi ya kalli Zainab din da yaran yace."Ku tashi muje mu karya." Suka mike a nutse suka bi bayansa gurin cin abincin.
To a takaice dai Abbah Abbas bai tunkari amaryarsa da wata magana ba har sai da tayi uku a gidansa tukkuna ya tunkareta da wata bukata! sai kace wacce take jiran zuwansa ta kar'be shi hannu biyu, shi kuma ya shiga gwada mata soyayyarsa mai wahalar samu! Zainab itama ta dinga nuna masa fitinarta sai dai da akazo fad'an qarshe ne ta gane bata da wayo! dan ba wai tausayinta ya tsaya yi ba aiki yayi sosai ya zage a kanta ya bata kashi duk tarin sha'awar da ya tara ta tsayin wattanin da suka gabata ranar sai daya samu cikakkiyar gamusuwar da yake bukata da yarinyar...Zainab taji maza! ai lokaci guda ta shiga hankalinta ta daina rawar kai kullum a tsorace take da angon nata dan tun ranar daya mayar da ita cikakkiyar mace ya daina d'aga mata k'afa kullum sai ya biya bukatarsa har kwanaki bakwai d'inta suka qare, ta dinga murna tana godewa Allah zata sarara."
******
'Bangaran Naja'atu kuwa abun babu dad'in ji dan tun ranar data samu labarin auran Abbah Abbas taqi lafiya ciwon kai ciwon kirji da dai sauran ciwoka! Gashi sai 'boyewa Mmn Sajida take taqi ta bari ta gane bata da lafiya, to itama Mmn Sajidan da yake 'yar sabga ce bata fahimci komai ba sai dai sa'i da lokaci idan ta kalli Naja'atun takance" Naja'atu duk kin rame kinyi haske dan Allah ki cire damuwa da fargaba daga ranki! wallahi nasan iyayenki nacan hankalinsu a tashe sakamakon rashin ganinki ke kuma sabida wata manufa taki kin'ki kije garesu, duk fa abinda ya faru da rayuwarki qaddarace iyayenki musulmai ne zasu kar'bi qaddarar da Allah ya dora miki ba zasu guje ki ba."
Duk sanda Mmn Sajida tayi mata wannan maganar ba ta cewa komai sai da tayi murmushi tayi shuru da bakinta.
Mmn Sajida haushi yasa ta tattarata ta qyaleta da taurin kanta.
To kamar yanda suka yanke shawara kancewa Hajia Rabi zata je garin jos domin dauko Naja'atu hakane ya kasance Direba ya dauketa da wurwuri suka nufi garin........Sai dai tun kafin direban yayi parking din motar suka hango gate din gidan garqame da 'katon kwado! Ga unguwar shuru babu wanda zasu tambaya...Hajia Rabi ba tayi qasa a gwiwa ba ta dauko wayarta ta kira mijinta domin sanar dashi halin da ake ciki...Alhaji Ya shiga mamaki mutuka yace."Lallai su samu wani a unguwa wanda zasu tambayi domin yayi musu qarayin bayani .......Direba ya fito ya tsaya jikin mota yana kallon yanayin unguwar...Cikin ikon Allah wani bawan Allah yazo wucewa sai ya tsayar dashi da sauri ya miqa masa hannu suka gaisa yace."Malam dan Allah ko kana da labarin mutanan nan gidan nan." Ya fada yana nuna masa gidan
Mutumin ya jima yana kallonsa kafin yace."Amma ba a garin nan kake ba ko."? Da sauri yace."Eh kwarai kuwa." Mutumin ya girgiza kansa gami da fara bashi labarin abinda ya faru da mutanan gidan ya rufe maganarsa da fad'in 'Wannan gidan da kake gani yanzu yana hannun bank dan haka tun wuri ku bar gurun nan tun kafin jama'a su ankara daku." Da
Haruna Direba ya mika masa hannu yana masa godiya ya bude mota ya shiga...Ya kunna da sauri suka fita daga layin gidan....Sai da suka hau titi sosai san Ya sanar da Hajia Rabi abinda mutumin ya fad'a masa... A sanyaye tace"Wannan al'amari baiyi dadi ba ko kadan ko yanzu ina Naja'atu take? Kira ne ya shigo wayar ta ta dauka da sauri dan ganin wanda ya kira.
Alhaji yace."Ina fata kun samu cikakken bayanin inda Naja'atu take, a sanyaye ta shiga fad'a masa maganar da mutumin nan ya fad'a dangane da gidan Aminu Dan jaridan....Alhaji yayi shuru yana tunanin inda zasu samu Naja'atun a cikin garin Jos.
*ANA WATA GA WATA*
Wani masifaffan amai ne ya tashe ta daga baccin da takeyi na safe! A guje ta dafe kirjinta ta nufi bakin rariya ta dinga kwararawa tana wani irin kakari tare da dafe kirjinta............Ta kai minti goma tsugune a gurin kafin ta dan samu sassauci ta dauraye bakinta tare da mikewa tana dafa bango(garu) ta ciko buta da ruwa tazo ta wanke gurin data 'bata, tana tangadi ta koma daki ta zauna tana mayar da numfashi...............Bayan Mintina ashirin tana zaune a takure zazzabi na neman rufeta ta sake jin wani aman ya sake yunkuro mata da masifar qarfi! da sauri ta mike ta nufi bakin rariya ta tsuguna tana yi tana hawaye! tun tana amayo abinci har sai da ta dawo amayo ruwa shima ruwan ya daina fitowa sai miyau da majina ne kadai ke fita, kuka takeyi tana kiran sunan Allah ta samu gefan rariyar (kwata) ta kwanta tana wani irin nishi tare da janyo numfashi da kyar! Naja'atu haka ta yini kwance a bakin rariya daga taji yunkurin amai sai tayi ta kakari amma babu abinda zai fito sai miyau mai dacin gaske.....Haka Mmn Sajida ta dawo daga cefane ta sameta lokacin ma ta galabaita sosai dan jikinta yayi laushi duk ya saki....Hankali a tashe Mmn Sajida ta shiga gidan Mmn Ladi suka fito tare, a daidaita sahu suka samo suka kamata dakyar suka sata a ciki suka zazzauna a gefanta domin ri'keta asibitin kudi Mmn Sajida tace su nufa dan ganin yanda Naja'atun ta galabaita yasa ta yanke wannan shawarar tana jin tsoron kada yarinyar mutane ta mutu a hannunta a tuhumeta shiyasa take gani ko nawa ne zata iya kashewa domin samun lafiyarta.
Gwajin farko Dr ya tabbatar musu da cewar tana da ciki dan kimanin sati tara! Wata biyu da sati daya! Mmn Sajida Da Mmn Ladi suka shiga cikin mamaki mai tsanani Ciki ciki! lallai Allah ya had'a Naja'atu da babbar qaddara........
*Littafin na kudi ne...!*
Koda zaki ganshi a groups na sata ne idan kina bukatar ki biya kudin karatu ga yanda abin yake....Vip group #600 normal group #300 accont....0542382124...Binta umar gtbank...Idan katin waya zaki tura sai kiyi min mgn ta wahsap da wannan number
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
*MANZIR _ALWAFIR ABUJA🌴🌴*
_*Sun tanadarwa da mata kayan gyaran jiki masu kyau da inganci magungunansu babu almundahana a ciki mutukar kika fara amfani da ingantattun magungunan company manzil alwafir to ba zaki daina ba saboda ingancin magungunansu ko wace matsala kike fama da ita mutukar ta shafi zamantakewar auranki manzil alwafir zasu share miki hawaye da akwai gruops na mussaman da suka bude domin taimakon mata masu fama da matsaltsalo a gidan auransu idan kanki na cikin duhu mutukar kinyi rijistar dasu to kukanki ya 'kare idan kina bukatar kiyi rijistar sai kiyi magana.*_
*****60 Mmn Ladi tace"Dama fa ni wallahi sai da jikina ya bani cewar haka zata iya kasancewa kawai dai dan yarinyar ta nuna bata san maganar ne yasa nayi shuru amma da tun farko ta dauki maganata da muhimanci munje asibiti sun dubata sosai a lokacin da sai mu san yanda zamuyi da cikin tunda baiyi kwari ba amma yanzu ciki har ya shiga wata na uku ai akwai matsala idan akace za'ayi wani yunkuri a kansa, gaskiya na tausayawa yarinyar domin haihuwa da irin su Bash matsala ne da da yanda za'ayi kawai a zubar da cikin nan wallahi.
A sanyaye Mmn Sajida tace"Nima dai jikina yayi sanyi wallahi amma bari ta tashi daga bacci muji hukuncin data yanke." Ajiyar zuciyarta da shashshekar kukanta sukaji.
da sauri suka kalli gadon da take kwance! Ta bude idonta a hankali hawaye wani na bin wani ta kalli Mmn Sajida murya na rawa tace"Ciki ne dani ko."? A sanyaye Mmn Sajida ta daga mata kai
Rintse idonta tayi hawaye suka cigaba da zubowa'' Innalilihi wa'ina ilaihi raji'un."! Ta furta wannan kalmar tare da sake bude idonta tana kokarin mikewa zaune.....Mmn Ladi dake kusa da ita ta taimaka mata ta zauna tana goge hawayen fuskarta amma kamar bata gogewa wasu ne suke zubowa.
"Allah na kar'bi wannan kyautar da kayi min ba zan sake yunkurin sa'ba maka ba Ubangiji Allah ka ingata abinda ke cikina Allah kasa ya zama cikon addinin musulunci." Wannan maganar ta fad'a tana me tsurawa rufin dakin ido.
Mmn Ladi tace"Bamu gane me kike nufi ba Naja'atu yanzu sabida baki da hankali sai ki yarda ki haifi cikin nan to wane labari mai dadi zaki bawa d'an da kika haifa idan ya girma? ai kwanciyar hankalinki da samun nutsuwar ki kawai ki zubar dashi shine yafi alkairi a tattare dake."
Girgiza kanta ta dinga yi tana kallonsu tana kuka kokarin tsayar da ruwan hawayen dake gudana a fuskarta, tace"Bazan 'kara aikata kuskuran da nayi a baya ba Mmn Ladi koda ace wannan cikin ta hanyar banza na sameshi ba zan zubar dashi ba sai na haifeshi domin ban san munufar ubangiji a kansa ba. Wallahi mutukar kinga ban haifi cikin nan ba to Allah ne bai nufa domin ni yanzu abinda zai kusantani da ubangiji nake so ba abinda zai nesanta ni dashi ba, a baya nayi kuskure wanda har yanzu nake cikin nadamarsa, to bana fatan na sake aikata wani kuskuran da Allah zai yi fushi dani ya tuhume ni a ranar lahira kawai ku dai taya ni da addua kan Allah ya rabani dashi lafiya.
Wannan kalaman nata sune suka kashe musu jiki Mmn Sajida tace"To shikkenan Naja'atu zamu cigaba da taya ki addua kan Allah ya saukeki lafiya ya kuma kawo miki mafita a rayuwarki, ammafa yana da kyau ki koma ga iyayenki domin zaman da kike a tare damu bashi da wani amfani na fad'a miki duk inda iyayenki suke suna can hankalinsu a tashe suna neman inda kike me zai sanya ki dinga jin tsoro da tunanin wani abu daban."
Ajiyar zuciya ta sauke tace"Mmn Sajida ko dai kin gaji da zama dani ne? ko kin gaji da ciyar dani abincinki shiyasa kike wannan maganar."? Mmn Sajida ta shiga girgiza kanta tana murmushi mai ciwo tace"Gaskiya Naja'atu ban ta'ba tsammanin jin wannan maganar daga gurinki ba Haba dan Allah meye makwanci meye kuma abinci da har kike tunanin saboda su nake cewa kije ga iyayenki! To idan tunanin da kike kenan ki daina Mmn Sajida ba haka take ba duk wani abu da nake miki inayi miki ne tsakani da Allah bada wata manufa ba."
Naja'atu qasa tayi da kanta tana nadamar maganar data fad'awa Mmn Sajida dan sai bayan ta fad'i maganar ne ta gane kamar bata kyauta ba, tasan halin Mmn Sajida macace mai karamci da mutuncin itace zata fad'awa wani hakan
Likita ne ya shigo dakin hannunsa rike da wata farar takarda! Ya mikawa Mmn Sajida da fadin duk wasu bayanai na jikin takardar nan idan kun duba zaku gani." Mmn Sajida da Mmn Ladi basa jin turanci sosai shiyasa basu fahimci rubutun da likita yayi a jikinta takardar ba.
Naja'atu ta kar'bi takardar tana dubawa, gabanta ne ya fad'i ganin kudin gadon data kwanta yini guda dubo goma sai kudin magungunanta dubu bakwai da dari biyar....qasa tayi da kanta tana jin nauyin fad'a musu abinda ke rubuce a takardar....To a Ina Mmn Sajida taga dubu goma sha bakwai yanzu gabad'aya Jarin abincin siyar wa ta baifi na dubu ashirin ba dashi take ci take sha ita da 'yayanta yanxu idan ta sanadiyar ta ta ruguza mata sana'arta me zata ce.? jikinta ne yayi sanyi sosai ta tsirawa takardar ido tana tunanin yanda za'ayi.
Mmn Sajida tace"Naja'atu me Dr din ya ruboto." A dan sanyaye tace"Mmn Sajida me yasa kuka kawo ni pravite hospital baku kaini na gomnati ba."?
Mmn Sajida tace"Naja'atu tsorata nayi da yanayin yanda ganki shiyasa na yanke shawarar kawo ki asibitin kudi domin ayi gaggawar dubaki sanin da nayi cewar idan na gomnati mukaje kafin ma mu samu kati babban aiki ne sannan idan mukaje gurin ganin likita nan ma sai mun 'bata lokaci shiyasa kawai na yanke wannan shawarar."
Wasu hawaye masu zafi suka sauko a kumatunta gaskiya ta tabbatar da cewar Mmn Sajida masoyiyarta ce har ta mutu ba zata ta'ba mantawa da karamcinta ba.
Shuru dakin yayi Mmn Sajida jikinta yayi sanyi itama tana jin tsoro da fargabar abinda ka iya zuwa ya dawo...Tace"Nawa ne kudin gadon dana maganin insha Allahu ba zai gagara ba."
Ta kalleta tana girgiza kanta tace"Dubu goma sha bakwai da dari biyar." Mmn Ladi ta ri'ke bakinta cike da mamaki tace"Dubu goma sha bakwai harda wata dari biyar a kai! Tabdijam! ko awa hud'u ba kiyi a kwance ba har kinci wannan kudin."
Naja'atu tace"Ba kudin gado bane kadai harda na magani." Mmn Ladi tace"Duk da haka dai wallahi da tsada haba abin yayi yawa dubu goma sha bakwai fa ba kad'an bane gaskiya asibitin nan suna da tsada ta'bdijam."! Mmn Sajida tace"Duk mu bar maganar dan Allah ko nawa suka rubuta ai hakkinsu ne tunda dai mu muka zo neman taimako kuma sun taimaka mana a lokacin da muke bukata bai kamata mu tsaya surutu ba, Yanzu ni abinda ke hannuna gabad'aya dubu bakwai ne dama na ajiyesu saboda wata matsalar, amma yanzu zan koma gida zan dauki buhun shinkafar dana siyo shekaran jiya zan kaiwa maigari mai kanti ya siya nasan idan na siyar za'a had'a kudin
Girgiza kanta ta shiga yi tace"Kin san Allah Mmn Sajida ba zaki ruguza sana'arki kaina ba! Ban amince ki siyar da shinkafar ki ba." Mmn Sajida tace"To ya kike so ayi? Kin san dai babu wanda zanje gurinsa da bukatar ya bani aron kudi ya bani kai tsaye mutane yanzu kwata kwata basa bada bashin kudin.
Naja'atu shuru tayi tana tunanin yanda za tayi gaskiya ba zata bari Mmn Sajida ta rusa sana'arta a kanta ba tunani ta shiga yi ko ta kira Abbah Magaji a waya ta fad'a masa halin da take ciki! Girgiza kanta tayi, gaskiya ba zata iya kiransa a waya ta fad'a masa cewa ya taimaka mata da kudin magani ba saboda tasan halin masifarsa, kuma bata manta cin fuskar da tayi masa ba tana jin kunya sosai.....'Daya bangare na zuciyarta yace mata kawai ki kira wayar Abbah Abbas zai taimaka miki tunda dama shi mai tausayi ne zai iya turo da kudi a biya asibiti kudinsu...Ajiyar zuciya ta sauke tana tunanin kamar wannan shawarar data yanke itace shawarar data dace dan gaskiya ba zata amince da shawarar Mmn Sajida ba.....Suna tsaka da tunanin mafita likita ya sake shigowa ya kalli Mmn Sajida da fad'in "Hajiya ku muke saurara dan tuni mun sallameku ku biya asibiti hakkinsa.
Murya na rawa Mmn Sajida tace" Dr kayi hakuri yanzu zan je gida insha Allahu kafin goma na dare zan kawo maka kudin."
Dr yace"Ni tara tana yi na tashi daga aiki wani ne zai maye gurbina kuma kuka kwana to kud'inku ya qaru zaku biya dubu ashirin da bakwai da dari biyar." Mmn Ladi ta zare ido tana kallonsa! Ita kuwa Mmn Sajida mi'kewa tayi da sauri tana fad'in "Insha Allahu yanzu zan dawo." Dr ya kalli agogon hannunsa da fad'in "Okey idan kika wuce tara baki dawo ba to ba zaki sameni ba." Yana gama maganarsa ya juya da niyyar fita.
"Dr." Muryarta ta katse musu hanzari daga shi har Mmn Sajidan da take kokarin bin yansa domun tafiya.....Duk suka juyo suna kallonta, tace"Idan babu damuwa ina bukatar ka bani aron wayarka zan kira mahaifina da ita insha Allah za'a tura maka kudinka."
Dr yayi kasaqe! yana kallonta kafin ya d'an d'age kafad'arsa ya dauko wayarsa dake gaban aljihun rigarsa ta likitoci ya karasa har bakin gadon da take zaune ya miqa mata....Ta kar'ba a sanyaye, tana dubawa dama kafin ya bata wayar sai da ya cire mata sucurity da yake kai.....Tana tararrabi da fargaba ta sanya numbar Abbah Abbas din a wayar ta shiga gurin kira gabanta na wani irin fad'uwa ta shiga kiran wayar.....Daf da zata katse aka d'aga! ta sauke wata zazzafar ajiyar zuciya tana jiran taji muryarsa sai kawai taji murya mace mai tafe da iyayi da feleqe! tana fad'in "Waye yake magana."? Gabanta ya dinga dukan uku uku! wacece wannan? Take tambayar kanta, tasan muryar Halisa kuma tasan muryar Saddiqa Mussadiq Mufida! muryar wannan me maganar ce bata tantance ba, Zuciyarta tayi saurin fad'a mata cewar amaryarsa ce! ji tayi idanunta na neman rufewa! tsabar fargaba! Tayi gum! da bakinta takasa magantuwa tana jin muryar Zainab sai magana takeyi amma uffan ta kasa cewa....Zainab tace" To ikon Allah waye wannan anata magana yana ji yayi shuru tsaki taja ta kashe wayar......Naja'atu ta shiga rarraba idonta a dakin gumi! na tsatstsafo mata! Dr yace."Ke nake saurare naji kamar an d'aga wayar ana magana kuma baki ce komai ba.
Da sauri ta dawo hankalinta tace"Yi hakuri Dr bari na sake kiran wayar bana ji sosai shiyasa na kasa magana." Okey kawai yace ya zuba mata ido yana kallonta tamkar zai lasheta.......Zainab hannunta r'ike da wayar ta kama hanyar fita palo inda Abbah Abbas din ke zaune yana hutawa.. tana daf da karasawa inda yake wani kiran ya sake shigowa, a maimakon ta kai masa wayar sai kawai ta d'aga tare da kara wayar a kunnanta da fad'in "Waye yake magana." Naja'atu ta daure da kyar tace."Nice."? Zainab jin miryar mace yasa gabanta faduwa tace"Kece wa."? Abbah Abbas yayi saurin juyowa yana kallonta jin yanda tayi maganar cikin izzah! da gadara!
'Bangaran Naja'atu kuwa ji tayi tamkar yarinyar ta soka mata wuqa a kirjinta jin yanda take wani daka mata tsawa kamar uwarta! har ta hasala! sai kuma ta sassauta zuciyarta tace."Naja'atu." Zainab tayi shuru tana mamaki! Naja'atu Naja'atu? tasan sunan rad'au! a bakin yaran gidan kuma ta samu cikakken bayani a bakinsu da sauran jama'ar gari tunda dama hausawa nacewa ko haqa rami kayi ka bunne abu to wata rana sai ya fito an ganshi, duk labarin Naja'atu tasan shi daga farko har'karshe sai dai duk yanda take zungurar maigidan kan maganar koda wasa bai ta'ba bata wani labarin da ya dangace shi dashi da Naja'atun ba........"Oh! nagane to wa kike nema."?
Naja'atu murmushin takaici tayi Kai tsaye tace"Ina neman mijinki ne idan yana kusa ki basa wayar zanyi magana dashi." Zainab tace"Okey kada ki damu." Sai kitt! ta kashe wayar ta nufi inda yake tana wata karairaya ga wani tsadaddan murmushi a fuskarta, zama tayi a kusa dashi tasa hannu a fuskarsa tana shafa gemunsa tare da wasa da karan hancinsa tace"Masoyinta sannu da hutawa." Kafad'arta ya r'ike hankinsa na kan wayarsa dake hannunta ya kar'ba yana fad'in "Waye ya kira ne."? Tace" Wata ce aka samu akasi ta kira number ka." Abbah Abbas bai gamsu da maganarta ba ya 'kurawa number ido, wayarsa babba ce sosai shiyasa daga ko wane gari ko wace qasa aka kirashi sai ta nuna masa, ganin number daga garin jos ne yasa ya d'an shiga mamaki! Sai kawai ya tsinci kansa da kiran wayar...Lokacin Dr har ya kar'bi wayarsa zai fita kiran ya shigo, da sauri ya dawo da baya ya miqa mata wayar.....Rai a 'bace! ta daga wayar ta kara a kunnanta tace"Ke! dallah malama! ki bawa mai wayar abarsa mana wai ke amarya sai hauka kikewa mutane mtssw! ki bawa mai waya wayarsa zanyi magana dashi."
Muryarta ta dinga dukan kunnansa yayi shuru yana sauraranta har sai da ta gama hayaniyar sannan yayi gyaran murya a nutse ya kira sunanta. *"Naja'atu!!!*
Wani irin yarrr! taji tun daga saman kanta har i zuwa tafin 'kafarta a sanyaye tace"Na'am Abbah Ina wuni."? Ajiyar zuciya ya sauke da fad'in "Lafiya lau ya kike ya maigidanki." ? Ya nuna kamar bai san abinda ke faruwa ba.
Kuka tasa masa tace"Abbah bani da lafiya gani a kwance a gadon asibiti likita na bukatar kudi bani dashi bani da wanda zai biya min shine na kira ka ko zaka taimaka min kamar yanda Allah yake taimaka maka." Jin maganar rashin lafiya yasa ya mayar da abin serious yace."Baki da lafiya Baki da wanda zai biya miki kudin magani ina mijinki yake."? Tana kuka tace"Ya sake ni ai."? Shuru yayi dama abinda yake so kenan yaji daga gareta...Yace."Yanzu kina ina."? Cikin shashshekar kuka tace"Ina tare da wata mata mai kirki tana taimakona." Girgiza kansa yayi yace"To Allah ya sawwaqe! Bani Likitan zamuyi magana dashi." Tayi saurin miqawa Dr din wayar........Tana jinsu suna magana da Dr din yana tambayarsa abinda ke damunta Dr yayi masa cikakken bayani sannan ya fad'a masa kudin da ake buqata....Yace Yanzu ya tura masa account number nasa zai sa masa kudin...Sallama sukayi da juna Dr ya kallesu a nutse yace."To alhmdullhi zaku iya tafiya yanzu." Mmn Sajida da Mmn Ladi sukace "To mungode." Da sauri Dr ya fita daga dakin su kuma suka shiga shirye shiryen tafiya gida......
*_Allah yasa cikin ya zube Aunty Binta ci kuma!!! 🤦🏻♀️ dan Allah kada ta haihu da Bash Aunty Binta wannan pege d'in ya bani haushi😀......Wato kuna so rabo ya kashe ni ko? 🧐 To Yanda Allah ya saukar da ikonsa a kan Naja'atu nima 'yar kallo da addua ce........Alhamdullhi saqona na cikin littafin nan ya soma isa, ha'kika wani baya ta'ba haihuwar d'an wani Allah ya qaddarta akwai rabo mai zafi a tsakanin Bash da Naja'atu shiyasa suka rabu da Abbah Abbas cikin 'kan'kani lokaci ta auri Bash shima suka rabu cin 'kan'kanin lokaci bayan ya saukar da ikonsa a kansu, babu wani wanda yasan gaibu sai Allah👌🏻*
*Littafin na kudi ne....!*
Koda zaki ganshi a groups na sata ne idan kina bukatar ki biya kudin karatu ga yanda abin yake Vip group #600 normal group #300 account....0542382124....Binta umar gtbank.....Idan katin waya zaki tura kiyi min mgn ta whasap da wannan number.
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
****61 Abbah Abbas shuru yayi da wayar a hannunsa yana tunanin maganar da dr ya fad'a masa, Naja'atu na dauke da cikin wannan lalataccen yaron! hakika wannan al'amarin ya tsaya masa a rai mutuka, ba wai yana kishi ne da faruwar hakan ba yasan Allah ba yanda baya tsara al'amarinsa, yarinyar kawai yake tausayawa had'uwar jininsu da yaron da duniya tasan mutumin banza ne, koda yake Ubangiji kan saukar da shiriya akan bayinsa a lokacin da yaso, wannan dalilin ya sanya yaji zuciyarsa tayi sanyi sai kawai yayi addua a kam Allah ya shiryi Bash din ita kuma Naja'atun Allah ya sauketa lafiya ya sanya rabuwar auranta da Bash din shine alkairi......Zainab kuwa kunya ce ta isheta tana jin tsoron kada ya tuhumeta a kan me yasa tayi masa karya bayan ta gane Naja'atu ce ta kira wayarsa, sai taga gabad'aya ma hankalinsa da tunaninsa bayan kanta yana can wani tunani na daban.
Sai goma shaura na dare suka isa gida, Mmn Ladi kai tsaye gidanta ta wuce saboda tasan mijinta ya dawo kuma bata fad'a masa zata fita ba tunda bata da waya, yanzu babu laifi sun shirya sun daina fada sosai duk a sakamakon nasihar da Naja'atu tayi mata......Mmn Sajida ganin mutane sun cika rumfar kwanon siyar da abincinta yasa ta sallamesu da fadin yau babu abinci sai gobe idan Allah ya nufa......Dantalle ya nufo inda suke ya sha shaddarsa 'yar rini hannunsa rike da mukkulin lifan d'insa, yana washe baki yace."Mmn Sajida dama wannan qanwar taki tana nan."? Mmn Sajida tace"Eh tana nan Dantalle ya gida ya iyali."? Ya amsa idanunsa a tsaye a kan Naja'atu." Yace." 'Yan mata ya kike ya gari ya jin dadi."? Naja'atu duk da halin ciwon da take ciki sai da ya bata dariya, wai shi dole sai ya burgeta ta lura mutumin yana so ya wuce gona da iri....Tace"Lafiya lau jin dadi na gurinku."' Dantalle dadi ya isheshi ya kalli Mmn Sajida yace yau babu abinci naga alamar ma kamar daga unguwa kuka dawo ko."? Mmn sajida tace wallahi kuwa munje wani guri ne." Yace."To bbu laifi bari naje na dawo kada ku rufe gida da wuri." Mmn Sajida tace"To shikkenan." Ya juya da sauri ya nufi inda lifan dinsa yake.....Su kuma suka shiga gidan Mmn Sajida na fad'in "Wahalalle kawai ya fito ya bar iyalinsa yana biye biyen gidajen abinci gabad'aya Dantalle baiyi ba wallahi." Naja'atu murmushi tayi tace."Ni kam gani nayi ma kamar sonki yake." Mmn Sajida na kokarin bude dakinta tace"Ai ko maza sun kare a duniya ba zan auri dantalle ba Gwara nayi ta zama a haka."
Walid da Sajida tuntuni sunyi bacci da yake Walid nada wayo shine yayi musu shimfida ya daura musu net suka kwanta, ita kuma Mmn Sajida kicin ta nufa da sauri da yake tana da karamin gas sai ta fara kokarin d'ora ruwa ta dafa musu indomee sai kawai sukaji sallamar Dantalle daga waje....Mmn Sajida tace"Naja'atu gashi can ya dawo ko zaki 'kokarta kije kiji dame yazo.'' Naja'atu tace"Rabani da wannan guy Mmn Sajida ki daure dai kije kada yace an masa wulakanci." Mmn Sajida ta dauki mayafinta ta fita....Minti biyar sai gata ta shigo hannunta rike da manya manyan ledoji Dantalle yaje ya kashe musu kudi gurin siyayyar kayan ciye ciye gami da kayan masarufi." Sosai Naja'atu ta dinga mamakin siyayyar tafi ta dubu biyar haka kawai bai ka gidansa ba yazo yana bawa duniya kai Allah ya shiryi mazan dakewa iyalinsu mugunta suna bayarwa a waje....Mmn Sajida tace"Kadan kika gani in dai Dantalle ne kuma wannan hidimar da yake yi da biyu yake wallahi ko shakka bana yi saboda dake yake yi.
Naja'atu ta shiga girgiza kanta tana mamakin al'amarin wasu mazan........To Sai da suka zo kwanciya Mmn Sajida take tambayarta dazu da wa tayi a waya a asibiti...Naja'atu kai tsaye tace mahaifinta ne anan Mmn Sajida tace na fada miki dama suma iyayen naki suna can hankalinsu a tashe dan Allah kiyi hakuri ki koma garesu ko kya samu nutsuwar zuciyarki idan kina zaune a gurina lalattatun maza irinsu Dantalle zasuyi ta kawo miki farmaki." Tace"Mmn Sajida insha Allah zan tafi gida amma sai jikina ya warware tukkuna." Mmn Sajida tace to Ubangiji Allah ya baki lafiya mai amfani kuma ya rabaki da abinda ke cikin ki lafiya."
Bayan wata biyu cikin Naja'atu yayi wata hudu da 'yan kwanaki....A lokacin ne Allah ya azurta Zainab da samun nata cikin, murna a gurinta tamkar me! shima Abbah Abbas din sosai ya nuna farin cikinsa a kan karuwar daya samu, ya shiga lalla'bata gami da nuna mata so da kulawa, yarinyar ta samu sake sosai sai abinda take so takeyi a gidan......Halisa ta sake shiga cikin wani irin hali na tashin hankali da damuwa dan duk irin kokarin sauke hakkinta da maigidan yake yi gani take kamar baya adalci a tsakaninsu tana gani tamkar yafi fifita Zainab din a kanta lokaci guda tayi wata iriyar rama mara kyawun gani.....Zainab mai wayo gami da so ta siye zuciyar mijinta ai tuni ta janye yaran sun koma bangaranta yanzu komai nasu na gurinta haka take kulawa dasu gami da sanyasu farin ciki, tuni yaran suka manta da wata Naja'atu saboda sun samu wacce ta maye musu gurbinta sai dai sa'i da lokaci Mussadiq yana tunawa da ita.......Ranar wata Alhamis da yamma Yaya Ramlatu ta dira a gidan, kai tsaye bangaran Halisa ta nufa, ta zauna suna gaisawa! Halisa tace"Yaya Ramlatu sai yau aka tuna dani."? Ta'be bakinta tayi tace"Halisa kenan ai lamarin ki ne yake bani haushi wallahi dubeki dan Allah duk kin lalace yarinya qarama tazo ta kwace miki miji da gida da yara kin kyaleta ba zaki dauki mataki ba."
Halisa tayi shuru tana nazarin maganar Tace"Yaya kenan ni yanzu ba tashin hankali ne a gabana ba ingantuwar lafiyata kawai nake bukata.'' Ramaltu ta ta'be bakinta tace" ai shikkenan tunda kin mayar da kanki sususu!! ni kinga tafiyata." Sai kawai ta miqe ta kama hanya ta futa.
Tana fitowa ta durfafi bangaran Zainab, lokacin suna zaune ita da yara a palo suna kallo suna wasa da dariya! Kawai sai ganin mace tayi ta shigo mata babu sallama......Yaran duk sukayi tsuru-tsuru murya na rawa suka shiga gaisheta! Ramlatu ta samu guri ta zauna tana muzurai sai bin palon da kallo take tana watsawa Zainab kallon banza.....Zainab dama a ciki take da matar domin ta tsani d'abiar da take mata kamar ba babba ba sai ta dinga shigo mata babu sallama...sai kawai ta dauke kanta taqi kallonta ballantana ma ta gaisheta.
Yaya Ramlatu ta fusata! sosai ! tace"Ke baki san matsayina bane da ba zaki gaisheni ki bani girma ba."? Wani irin kallo Zainab tayi mata tace"Nasan matsayin ki mana kina so nayi miki sujjada ne."?
Ya Ramlatu tace"Ko baki yi min sujjada ba ai sai ki mutuntani a matsayina na yayar mijinki." Zainab ta ta'be bakinta tare da dauke kanta....Wannan abun da tayi ya fusata Yaya Ramlatu mutuka, sai kawai ta shiga zaginta tana fad'in "Ita bata daukar raini wallahi idan tace rashin kunya za tayi mata sai taci mutuncinta.
Zainab tace"Kinga dan Allah ki tashi ki fice min a gida ni ban gayyatoki ba haka kawai kizo kina min masifa me nayi miki kike zagin iyayena to bari kiji ni ba Naja'atu da kuka raina bace nasan daraja da mutuncin iyayena." Ya Ramlatu ta miqe ta iska inda take tana zaginta hade da dungure mata kai tace."Za kici ubanki zanyi maganin.....Kafin ta qarasa yarinyar ta miqe a fusace! ta wanke ta da mari! Tace"Wallahi ba zanji kunyar cin mutuncinki ba mutukar zaki ta'ba martabar iyayena.
Yaya Ramltu ta dafe kumatunta jikinta na wani irin tsuma mamaki da al'ajabi kamar ya kasheta 'yar qaramar yarinya da bata wuce jikarta ba itace ta mareta! Sai kawai ta rufe ta da duka ta ko'ina! Zainab ta dinga ihu! tana kokarin kwatar kanta Ramlatu ta haye kanta sai jibga take.....A kid'ime! Saddiqa taje ta fad'awa Halisa halin da ake ciki sai gata sun shigo ita da Baba Larai! gabadayansu sun firgita da ganin duk da Ramlatu takewa Zainab! da kyar suka janyeta sai haki take tana fad'in "Tunda take a duniya babu wanda ya ta'ba marinta sai yarinyar na saboda haka sai ta dauki tsatstsauran mataki a kanta...Baba Larai ta bude bakinta za tayi magana ta buga mata tsawa da fadin tayi mata shuru bata son munuafurci. Yafan mayafinta ta gyara ta dauki jakarta ta kama hanyar fita sai zage zage take...
Halisa ma juyawa tayi ta nufi gurinta uffan ba tace ba dama itama haushin zainab din take ji shiyasa taji dadin dukan da Ramlatu tayi mata
Baba Larai ta taimaka mata ta tashi zaune tana kuka kamar ranta zai fita Baba larai ta rarrasheta gami da yi mata nasiha akan ta zauna lafiya sannan ta fita daga sabgar Ramlatu tunda ba mutunci ne da ita ba, Zainab jinta kawai takeyi saboda haka tana fita ta dauki wayarta ta kira mijinta tana wani irin kuka ta shiga zayyane masa abinda ke faruwa tace tana kwance ta kasa tashi cikinta sai ciwo yake.....Wannan al'amarin ya daga masa hankali sosai ashe Ramlatu ba zata kyaleshi ya huta ba! Dama yana jin haushin abinda tayi masa a kan Halisa kawai ya kyaleta ne, to yanzu kuma shine taje har gidansa ta daki matarsa da 'karamin ciki a jikinta wannan karan zai dauki mataki a kanta....Kasuwar ya bari ya nufi gidan, ya dauki Zainab sukaje asibiti aka dubata sosai komai lafiya ya dawo da ita gida tare da tarin siye siyen da yayi mata a hanya, yarinyar sai narkewa take tana kuka gami da riqe cikinta ya dinga rarrashinta yana bata hakuri da kyar ta barshi ya koma kasuwa............Koda ya tashi daga kasuwa, wani jami'in 'Dan sanda yaje ya dauko a motarsa suka nufi gidan Ramlatu dake tudun wuzurci...Tana zaune a tsakar gida tana gyara kayan miya, yaro ya shigo yace."Wai Ramlatu tazo su gaisa da dan uwanta yana waje. duk a tunaninta Alhassan ne saboda sa'i da lokaci yakan kawo mata ziyara, ta yafa mayafi ta fita, sai ganin Abbas tayi da dan sanda! jikinta a sanyaye take kallonsa yayi bala'in shan kunu tare da umartar d'ansandan ya daure mata hannu! Kuka ta fashe dashi taje "Abbas ni zaka tozarta a kan matarka."? Ko kallonta baiyi ba ya sake Umartar dansandan da maganar, Yaya Ramlatu ta juyo da sauri zata shiga gidanta shi kuma police din nan ya kama hannunta ta baya yasa mata takunkumi! Yara suka cika a gurin Sakina kishiyarta ta fito tana tambayar ba'asi! Abbah kuwa yana ganin an soma taruwa a gurin ya shiga mota ya sauke glass din motarsa mai duhu yana hango artabun da police din keyi da ita taqi sai turjewa take tana kuka da fad'in " Dan uwana ne fa matarsa ce tasa yazo yaci mutuncina wallahi banyi laifin komai ba." Jama'a sai kace kace ake a gurin ya cika sosai....Abbah Abbas Yana kokarin jan motarsa ya bar gurun Salim yayi parking din motarsa ganin abinda ke faruwa yasa hankalinsa ya tashi har ya nufi inda mahaifiyarsa take Abbah ya dan sauke glass din motar ya kirashi...Da sauri ya karaso gurin yana risinawa! Abbah yace."Ina fatan ka kammala ayyukan dana sanya ka kafin barowa ta kasuwa."? Yace."Eh Kawu na had'a komai kamar yanda kace!." Yace."Okey jeka ce da wancan D'an sandan nace ya kwance mata abinda ya daura mata a hannu." Salim yace."Kawu wai meke faruwa ne."? Yana kokarin kunna motarsa domin barin gurin yace kaje ka tambayeta zata fada maka." Kawai yaja motarsa da sauri ya bar gurin ba tare da mutane sun farga dashi ba
Yaya Ramlatu ta muzanta mutu'ka kafin police din ya kwance mata hannunta ya qara gaba abunsa ita kuwa yara ne suka kewayeta suna surutai a kanta gami da qananun maganganu! Salim jikinsa a sanyaye yaja hannunta tana wani irin kuka na tsantsar kunya da takaicin tozarcin da dan uwanta yayi mata cikin unguwa a kan titi tunda gidan nata a kan titi yake shiyasa jamaa yara da manya suka cika gurin cikin gidan suka shiga ita da Salim rayukansu a mugun 'bace.....'Karya da gaskiya Ramlatu ta shiga fad'awa 'Danta tana kuka da fad'in ''Yana da kyau ya dauki mataki kan irin tozarcin da Dan uwan nata yayi mata, Salim ya fusata sosai bai ta'ba jin tsanar Kawun nasa ba sai ranar ko lokacin da ya auri naja'atu bai ji haushinsa ba kamar yanzu yace."Kiyi hakuri Mama nagane abinda yasa mutumin nan yake miki wulakanci saboda Allah ya fifitashi a kanku yana da kudi yana da iko shiyasa duk wulakancinsa yake qarewa a kanki to insha Allah sai nayi miki maganinsa sai kinji mummunan labari wallahi sai na daukar miki fansar tozarcin da yayi miki a unguwa." Ramlatu jin furucin da yaron nata yayi yasa ta tsagaita da kukan da take tana qara tunzura masa zuciya a kan yabi ta qarqashin qasa ya tagayyara Dan uwan nata
'Bangaran Naja'atu sai dai godiyar Allah dan wannan cikin na jikinta da alama lafiyyye ne ya hanata sakat! kullum cikin ciye ciye kwadayi iri iri idan ba taci kaza mai kuli kuli ba ji take tamkar zata mutu! al'amarin ya dinga bawa Mmn Sajida tsoro wannan wane irin d'an gayun ciki ne, duk kokarinta sai da ta gaza domin yau da gobe kayan Allah ne kuma tana jin tsoron saka Dantalle cikin harkar sabida kada ya nemi ya fanshe hidimarsa ta rasa bakin magana.....Kawai sai ta shirya da sassafe tayi mata sallama tace zata je wani guri! Asibiti ta nufa, cikin ikon Allah kuwa ta hadu da Dr shima shigowarsa kenan, suka gaisa a mutunce kafin ta tambayeshi bukatar da ta kawo ta, Dr yace to Allah yasa bangoge numbar ba bari na duba dai." Tace"To Allah yasa dai baka goge ba.
Ya jima yana dube dube a wayar tasa kafin yace."Alhamdullhi kinga number nan. Ajiyar zuciya ta sauke tace to dan Allah rubuta min a takarda bani da waya wallahi." Biro ya ciro a gaban aljihunsa ya bude wallet dinsa ya dan yagi jikin wata takarda ya rubuta mata number a gurguje ya mika mata ya wuce cikin asibitin....Tana murna ta fita daga cikin asibitin ta danyi tafiya kadan ta samu masu communication tace"Dan Allah zanyi waya ta minti biyar ko goma nawa zan biya.''? Guy yace."Kawo naira dari." Ta bashi kudin had'e da miqa masa number yasa a wayar tana fara ringing ya miqa mata gurin ta bari ta samu inda babu mutane......Abbah Abbas na kokarin shiga toilet domin yin wanka yaji kira a shigo wayarsa dawowa yayi ya dauki wayar yana duba number, ganin sabuwar number daga Jos yasa yayi saurin dagawa tare da yin sallama....Mmn Sajida ta gaishi a nutse ya amsa yana tambayarta wacece ita, tace"Alhaji ni sunana Safiyya ina zaune a jos nice kuma wacce Naja'atu take zaune a gurinta dama na kira kane domin na fad'a maka halin da take ciki! Alhaji Naja'atu tana cikin halin taimako ga cikinta kullum sai qara girma yake a matsayinku na iyayenta yana da kyau kuyi hakuri ku gafarceta akan sa'ba muku da tayi ku dubi halin da take ciki kuzo ku dauketa dan nayi nayi da ita akan ta dawo gareku ta'ki! wannan dalilin yasa nace bari na kira ku a waya na fad'a muku halin da take ciki sabida bana so har lokacin haihuwarta yazo bata gaban iyayenta"........Ajiyar zuciya ya sauke bayan ya gama jin bayaninta yace."Sannu da kokari Safiyya Allah ya baki ladan taimakon da kikayi akan yarinyar nan kuma naji dadi sosai da kikayi tunanin sanar damu halin da ake ciki Allah ya saka miki da alkairi mungode sosai Insha Allah cikin satin nan zan turo da mota a dauketa watakila ma ni da kaina zanzo Okey dik dai yanda tayi wu zaki bani cikakken address din inda kuke." Tace"To shikkenan Alhaji insha Allah yanzu zan turo maka text za kaga address d'in idan ma baka gane ba kana shigowa unguwar sai ka tambayi Mmn Sajida mai abincin siyarwa insha Allah za'a nuna maka." Yace."To masha Allah mungode kwarai." Sallama sukayi da juna Mmn Sajida tayi saurin tura masa text din ta mikawa mai wayar, ya duba balance da sauri yace sai kin ciko talatin kin qara minti uku akai." Hamsin ta mika masa ya dauka ya bata sanjinta tayi saurin tarar Napep ta shiga domin komawa gida.
Shi kuwa Abbah Abbas bayan gama wayarsu da Mmn Sajida sai ya yanke shawara kancewa idan ya isa kasuwa zai samu abokinsa ya sheda masa fa halin da ake ciki yana ganin kamar alhakin komai yana kansu tunda yarinyar dai tuntuni ta bar hannunsa to kafin ya zartar da wani hukunci dole sai magabanta ta sun sani. Da wannan shawarar ya mi'ke ya nufi bandaki domin yayi wanka ya fita harkokinsa....
62******Yau tsawon kwana uku kenan da Abbah Abbas ya sanar da abokinsa halin da ake ciki dangane da maganar dauko Naja'atu dake can garin Jos, ya jima yana ta sauraran yaji ta bakinsa a kan a'lamarin Amma Abbah Magaji Yaja bakinsa yayi shuru yaqi cewa komai ballantana ya bada goyon bayan ayi tafiyar........Shi kuma a lokacin gabad'aya hankalinsa ya kasa kwanciya a tsakanin kwanaki ukun kullum da yarinyar yake kwana yake tashi a cikin ranshi...........Shi kansa ya kanyi mamaki akan mai yasa yarinyar da cikin dake jikinta suka tsaya masa a zuciyarsa?
To Yau daya isa kasuwar ko zama bai bari yayi ba ya nufi rumfar abokin nashi.........Koda Abbah Magaji ya ganshi sai da yasha jinin jikinsa gaisawa sukayi a tsanake Abbah Abbas yace."Wai ya ake ciki ne dangane da maganar da nayi maka kwanaki uku da suka wuce ina ta sauraron naji ta bakinka har yau baka ce komai ba.''
Abbah Magaji yace."Dan Allah Alhaji Abbas ka cire kanka daga sabgar yarinyar nan wai shin meye ma na damun kanka a kanta yarinyar nan fa kai ta tozarta amma ka kasa dauke kanka daka kanta, bana so aje inda take a yanzu a rabu da ita duniya ta cigaba da koya mata hankali idan taji uwar bari da kafafunta zata dawo gida.
Abbah Abbas ya girgiza kansa yana kallon abokin nasa yace."Ban tsammaci jin wannan maganar daka bakinka ba wallahi! wato kana so Ubangiji yayi fushi damu akan rashin yarda da qaddara ko? to inaso ka sani Naja'atu bata isa ta tsarawa kanta rayuwar da take so tayi a duniya ba, komai ya faru da ita dama a rubuce yake daga Allah! Naja'atu ni tayiwa laifi kuma wallahi tuntuni na yafe mata babu wani 'kulli a zuciyata dangane da ita.....Sannan naji kana maganar damuwa, dole na damu da yarinyar tunda ni yanzu a matsayin uba nake a gurinta, bayan haka kuma dole dani da kai da duk wani wanda ya shafeta ya damu da ita ya kula da ita saboda juna biyun da take dauke dashi, ina ganin akan wannan ma Ubangiji na iya tuhumar mu."
Abbah Magaji yace." To tunda abun ya kasance haka kai kana iya zuwa ka daukota ko ka tura a daukota ni kam ina da uziri kai ko bani da uziri babu inda zanje wallahi."
Abbah Abbas ya fusata sosai yace."Ashe haka kake da ri'ko! ? wai shin me yarinyar nan tayi maka me zafi da kake 'kinta haka gaskiya ka bani mamaki."!
Abbah Magaji na murmushi yana kallon abokin nasa dake huci! yace."Laifin da tayi min bai isa yasa na yanke mata irin wannan hukuncin ba, kai tayi wa laifi ni kuma na ara na yafa amma naga kamar kana so ka watsa min 'kasa a ido."
Abbah Abbas ya mi'ke yana jan tsaki! da fad'in "Idan kai baka yafe mata ba ni da tayiwa laifin na yafe mata kuma na fasa turawa a daukota da kaina zanje wallahi dana san wasa za kayi min da hankali da ban sanar maka da maganar ba sai dai kawai ka budi ido kaga yarinyar a gabanka." Yana kar'e maganarsa ya buge rigarsa ya kama hanyar futa.
Abbah Magaji ya bishi da kallon Mamaki! to irin wannan fusata da abokinsa yayi anya kuwa ba so yake ya mayar da yarinyar gidansa ba? Girgiza kansa ya shiga yi yana mamakin al'amarin.
Yana tsaye a tsakiyar katuwar rumfar kasuwarsa yana magana da yaran dake qarqashinsa, Salim ya shigo gurun.......Abbah Abbas sallamarsu yayi da fad'in kowa ya koma gurin zamansa.......ya kalli Salim fuskarsa babu walwala yace "Zan tafi jos bayan azuhur insha Allah komai dare zan dawo ka cigaba da kula kamar yanda ka saba." Salim yace."Insha Allah zan kula amma Kawu ina da maganar da nake so muyi da kai.
Abbah ya tsaya tare da fadin "Wace irin magana ce." Salim yace dangane da abinda ya faru tsakaninka da Yayarka ina nufin mahaifiyata.''
Abbah Abbas ya sake tsuke fuskarsa yace."Okey ta turoka ne kayi min rashin kunya." Girgixa kansa yayi yace."Wallahi ba ita bace nine kawai naga dacewar nayi magana kan hukuncin daka yanke gaskiya Kawu ba zan boye maka ba raina ya baci sosai ba kayi binkice ba ka yanke hukunci cikin 'bacin rai! Ashe ita aunty Zainab dince ta fara marin ta shine ita kuma ta kasa hakuri ta doketa."
Abbah shuru yayi yana nazarin maganar, yace kai waye ya fada maka Zainab ta mari mahaifiyarka."? Yace."Aunty Halisa da sauran yaran gidan sune suka tabbatar min da maganar....Abbah ya shiga mamaki mutuka ashe Zainab bata da kunya tunda har zata iya futar da hannu ta mari yayarsa gaskiya al'amarin ya bashi mamaki sosai komai zai dauki mataki a kanta...............amma sai yace"Ni a ganina duk laifin na mahaifiyarka ne a matsayinta na babba mai ya kaita zuwa gidan yara! ko shakka bana yi ita ta tunzura zuciyar yarinyar har ta kai ga ta mareta."
Salim takaici da bakin ciki kamar ya kasheshi ya girgiza kansa tare da fadin"To Allah ya sawwaqe." Abbah yace."Abinda za'ace kenan amma al'amarin mata sai su.
To kamar yanda ya fad'awa Salim cewar bayan yayi sallar a zuhur zai dauki hanya hakane ya kasance Abbah Abbas yayi sallama da yaran rumfarsa ya sake jaddadawa Salim ya kula sosai kana ya shiga motarsa ya dauki hanya ba tare da yayiwa abokinsa sallama ba dan har yanzu bai daina jin 'bacin rai dangane da abin da ya faru a tsakaninsu
*Sharrin zuciya gami da kyashi da hassada!*
Salim bayan fitar Kawun nasa murmushi yayi yana bin katafariyar rumfar dake ciki da kayan maqudan kudi da kallo! girgiza kansa yayi ya nufi wani qaramin daki dake cikin gurin yasa key ya bude a nutse ya shiga ya rufo kofa!....Wata drowar naga ya bud'e kudad'e ne bandir bandir anan suke shiryawa kafin motar banki tazo ta dauka.....Yasa hannu ya dinga dauko dauri dauri! sai da ya d'auki dauri talatin ya mayar da drowar ya rufe, ya samu wata 'bakar leda mai girma da 'kwari! ya loda kudin a ciki ya daure bakin ledar tamau! mikewa yayi ya fito daga dakin ya mayar dashi ya rufe.....Yana jiran dare yayi ya aiwatar da abinda ya tsara!
A 'ka'idar kasuwar kafin magariba kowa ya tashi idan kaga mutum bai rufe rumfarsa ba to yana da baki sun ri'keshi ko kuma yana wani muhimin abu....Kowa ya tashi sai d'ai-d'ai dan har masu gadi sun iso domin fara aikinsu, Salim sai da yaga duhu ya shigo tukkuna ya fito daga cikin wannan dakin hannunsa rike da ledar kudin daya loda....Lokacin sauran yaran Abbahn sun tafi sai mutum daya, shima da yaga ledar hannun Salim din bai damu ba saboda ya saba ganin irinta wani sa'in Abbah ya kan sanya shi ya rage kudi ya kai masa banki shiyasa koda Abdulhamid yaga wannan ledar kudin bai damu ba...Tare suka rufe rumfar sannan sukayi sallama kowa ya nufi inda motarsa take....Salim yasa ledar kudin a bayan mota yayi saurin zama a mazauninsa ya figi motar yana d'agawa masu gadi hannu.................'Karfe takwas da rabi na dare Abbah ya sauka a garin jos a daidai lokacin ne kuma al'amarin ya bayyana wata gagarimar wuta mai tafe da ba'kin hayaki ta dinga tashi a cikin katafariyar rumfar Abbah Abbas dake cikin kasuwar........Tashin hankali kenan! Hankalin masu gadi ya tashi mutuka suka doshi katon gate din daya rufe rumfar suna kokawar ya za'ayi su bude!
Kafin kice kwabo labari ya bazu a gari, tuni masu rumfuna a wajan gurin suka bazamo domin duba dokiyoyinsu...Salim yazo gurin hankalinsa a tashe yana ihu! kamar gaske ya durfafi gate din rumfar da yayi wani irin ja saboda wutar dake cinsa, ihu! yake da wai sai yaje ya bud'e! a take aka rirri'keshi Abbah Magaji da Abbah Alhassan suka janyeshi su kaishi can gefe guda suka ajiye! Kasuwar ta cika da 'yan a gaji kowa na iya bakin kokarinsa....a takaice dai sai da wuta taci ta cinye komai na cikin rumfar kasuwar Abbah sannan suka samu nasarar tunkarar gate din suka bud'e, nan ma sai da mutane uku suka fad'i suka suma! sakamakon shaqar hayakin da sukayi.........Ganin haka yasa jama'a da dama suka tsorata sai kowa yaja da baya haya'ki ba'kikkirinn ya dinga fitowa daga cikin rumfar..
Gidan Mmn Sajida baiyi wa Abbah wahala ba,dan da kansa yaje gidan bayan yayi tambaya a farkon layin wani matashin saurayi ya kwatanta masa, da yake akwai wutar nepa yasa hankulan Mutanan dake gurin ya dauke gurin kallon motar Abbah dake kokarin samun gurin yin parking.
"Alhamdullhi ya furta a fili a nutse ya bud'e murfin motar ya fito, karaf! idanunsa ya sauka kan Naja'atu dake zaune kusa da Mmn Sajida da Plate din abinci a hannunta tana ci, ga wasu zaratan samari a tsaye a kansu da alama abinci zasu siya.
Ya dinga jin wani tsantsar bacin rai da takaici na kokarin fasa masa zuciyarsa, mutum ne shi mai tsananin kishi mussaman a kan abinda yake so, yaushe Naja'atu ta lalace haka? har take zama a kan hanya gaban maza tana cin abinci kamar tunkiya, gaskiya bai ji dadin wannan al'amari ba....Taku d'aya yayi da niyyar isa gurin sai kira ya shigo wayarsa, a nutse ya fito da ita yana dubawa ganin abokinsa ne yasa yaki dagawa, ya cigaba da tafiyarsa yana jin wani kiran na shigowa, dubawa yayi sai yaga Salim ne, sai ya kara wayar a kunnansa tare da yin sallama..........." Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un."!! Wannan kalmar daya ambata itace ta dauki hankulan jama'ar dake gurin, Naja'atu ta miqe zumbur!! tana kallonsa tana so ta tabbatar da shi ne ko ba shi bane!! Jin muryarsa rad'au! na fad'in "Ina fatan wutar ba taci kowa ba." Salim yace babu wanda taci amma mutum uku sun suma sannan komai dake cikin rumfar ya kone harda kudin da muka shiryasu a cikin drowar.
Yace."Salim daina maganar kudi da sauran wasu abubuwa wannan duk a duniya na samesu nasan tunda me nema ne ni Allah zai mayar min da gurbin abinda na rasa babban farin ciki na shine wutar bata ci wani ba,nagode Allah da yasa wutar ta tsaya iya kan dukiya bata ta'ba wani ba.
Salim jikinsa ne yayi sanyi baiso yaji haka daga gurinsa ba ya dauka zai gigice koma sitiyarin mota ya k'wace daga hannunsa yayi hatsari! sai kawai yaji shi yana godewa Allah.A sanyaye yace."To kawu Allah ya mayar maka da alkairi sai ka dawo kenan.? Yace."Insha Allah gani a inda Naja'atu take kuma komai dare zan dauko hanya tare da ita." Salim cikin zuciyarsa cewa yayi Allah yasa gurin hanyarka ta dawowa kayi accident kowa ya huta, a zahiri sai yace."To Allah ya kawo ku lafiya Kawu." Abbah Abbas ya amsa da amin kafin ya kashe wayarsa.....Yana kallon gabansa yaga Naja'atu a durkushe kasan k'afafunsa tana shashshekar kukan da yayi mugun d'aga masa hankalinsa, damuwarsa a yanzu ganinta da yayi a tsakiyar maza tsakiyar hanya gaban mai abinci ba wai damuwarsa wutar data cinye masa dukiya ba babban damuwarsa wannan hawayen da take zubarwa..........