Da gudu Raheena tayi d'akin ta tana mai cike da farin ciki, da kyar tayi sallolinta abinci ma a d'aki taci ta kosa dare yayi sosai ta kira Ra'eez dan ta amshi lambarsa a wajen Dadynta.
**
Ra'eez bayan ya kammala abubuwan da yakeyi ya kakkab'e gadonsa ya kwanta, rungume filo yayi yana jin kewar Iyayensa, tun dawowarsa gidan da aka gyara komai ya koma d'akin Abbunsa da zama, domin yana matuk'ar son gadon Abbunsa, babu abinda aka canza hatta da filo da katifar duk sune na kusan shekaru takwas, zanin gadon kawai ya canza shima na Ummunsa ya d'auko yasa, duk lokacin daya kwanta a gadon yana mai jin dad'i, sai yake jin kamar yana tare da Abbunsa ne.
K'arar wayarsa ce ta dawo dashi daga tunanin da yakeyi, d'auka yayi yana bin wayar da kallo har ta tsinke, dan besan lambar da ya gani ba, sake kira akayi amma be d'auka ba, sai da aka kira sau ukku kafin ya d'auka.
Shiru yayi ba tare da yayi magana ba. Mak'e murya Raheena tayi cikin shagwab'a tana fad'in haba Yayana sai da na kira sau ukku sannan zaka d'auka.
Murmushi Ra'eez yayi dan ya fahimci mai magana. Raheena tace koda yake laifina ne da ban baka lambata d'azu ba, amma kuma ya kamata ace ka d'auka tun akira na biyu.
Gyara kwanciya yayi yana fad'in kin kira waya sai surutu kikeyi baki fad'i sunanki ba. Cikin shagwab'a tace kai Yayana nasan dai ai ka d'auki muryata? Ra'eez yace ai ni ko wata mukayi da mutum ba lallai bane na rik'e muryarsa ba.
Murmushi tayi tana fad'in Raheena ce fa. Ra'eez yace Raheena? Wace Raheena fa? Yanzu kam kukan shagwab'a tasa hada birgima asaman gado, duk yana jiyota sai ma murmushi da yayi.
Gyaran murya yayi yana fad'in Malama zan kwanta naga alamar bakida abun cewa. Cikin sauri tafe Raheena da kazo gidan mu d'azu a Surelere fa.
Tab'e baki yayi yana fad'in Allah sarki ashe kece? Nasan dai ban baki lambata ba shiyasa nayi mamaki. Raheena tace awajen Dady na amsa ai. Ra'eez yace to yayi kyau ya 'yan gidan ki gaishe mani da su.
'Dif ya kashe waya yana sakin murmushin mugunta. Raheena kuwa saurin cire wayar tayi tana binta da kallo, sake kira tayi amma a kashe. Wurgar da ita gefe tayi tana mai jin haushi, amma bakomai zata jure komai matuk'ar zai amince da ita, tasan ma yana da saukin kai zai amince da ita. Bargo ta jawo tana murmushi.
***
Washe gari wayar Raheena ce ta tashesa abacci, dan bayan yayi sallar asuba ya kunna wayar ya kwanta bacci ya d'aukeshi. Saurin tashi yayi yana kallon yanda gari yayi haske sosai, wayar ya kalla yaga lambar jiya ce dan beyi saving ba.
Hannu yasa ya d'auka akaro na biyu da ta sake k'ara. Gaishesa tayi tana fad'in Yayana ko bacci kakeyi ne? Murza ido yayi yana fad'in wallahi kuwa gashi har na kusa makara, gaskiya nagode maki.
Dad'i ne ya kamata ta sake kank'ame wayar tana fad'in naji dad'i kuma zan rik'a tada ka a koda yaushe dan bana so ka makara. Murmushi yayi yace nagode, bara nashiga wanka.
Da sauri tace da ina kusa dana had'a maka ruwan. Ra'eez yace hakan ma nagode. Kashe wayar yayi ya nufi band'aki.
Raheena kuwa fad'awa tayi saman gado tana murmushi, saurin tashi tayi ta jawo hijabinta domin tayi sallah, dan alokaci zatayi sallar asuba, ahakan ma saboda suyi waya da Ra'eez yasa ta tashi wajen k'arfe takwas, dan Raheena akwai sallah a makare, wani lokacin sai ta kai k'arfe tara batayi sallar asuba ba.
Tashi tayi tana fad'in dole nasa alarm ko dan narik'a tashinsa sallar asuba, da haka zan saye zuciyarsa, idan na tashesa nima zan daure nayi sallar sai na koma bacci kafin alarm d'in 7:30 yayi na sake tadasa yayi wanka. Murmushi tayi tana kabbara sallah.
***
Komai beci ba ya rufe gidan ya nufi gidan su Rumaisa dan ya saba saiya fara duba su kafin yawuce wajen aiki.
A tsakar gida ya iske su suna karyawa koko da kosai, Rumaisa kuma tana had'awa da shayi dan bata shan koko. Da sallama yashiga. Amsawa sukayi Mama tana fad'in yanzu nake fad'in Rumaisa ta kawo mani wayata na kiraka naga shiru baka shigo ba.
Zama yayi yana fad'in wallahi yau makara nayi Allah yaso ma Raheena ta tashe ni da... Kwarewar da Rumaisa tayi ne yasashi yin shiru yana kallonta.
Mama tace kiyi ahankali mana Rumaisa. Shayin ta d'auka tasha tana goge hawayen da suka taho mata wanda babu wanda ya gani sai Ra'eez.
Murmushi yayi dan ya fahimci dalilin kwarewarta. Juyawa yayi yana gaishe da Mama. Bayan sun gama gaiswa Rumaisa ta gaishe sa. Harara ya buga mata yana fad'in shine ko ki tashe ni ko? Duk'ar da kai tayi fuskarta a d'aure.
Mama tace Rumaisa kawo masa kofi ya karya kafin yawuce. Ra'eez yace Mama na kusa makara gara dai na tafi kawai. 'Daure fuska Mama tayi tana fad'in tashi ki kawo masa kofin.
Murmushi yayi dan yasan halin Mama bata son ya fita beci komai ba. Tashi Mama tayi ta koma ciki ta barsu a waje. Zuba masa tayi ta mik'a masa kular kosan.
Amsa yayi yana kallon yanda tayi kicin-kicin da fuska kamar zatayi kuka. Murmushi yayi yana girgiza kai yace K'anwata waya tab'a mani ke kuma? Zama tayi tana kok'arin maida hawayen idonta.
Kosan ya kai baki yana kallonta sai juya kosan hannunta takeyi. Murmushi yayi yana fad'in ke shayi zaki sha ni kuma kin had'ani da koko saboda son kai ko? Kauda kai tayi bata ce komai ba.
Ra'eez yace wai bazaki kulani ba ne yau? Turo baki tayi tana fad'in kaje Raheena ta baka. Dariya yayi yana fad'in lallai sunan yayi maki dad'i, daga fad'ar suna so d'aya shikenan har kin haddace, ko kina so na had'aku kawance ne? Tab'e baki tayi tana fad'in Allah ya kyauta.
Girgiza kai yayi yana fad'in kada ki sake kiranta da Raheena domin Yayarki ce. A zabure Rumaisa ta tashi tana dira k'afa tayi d'akinta.
Dariya yayi sosai yana girgiza kai, abincinsa yacigaba da ci aranshi yana jin wani sanyi yana ratsa masa zuciya ganin yanda Rumaisar sa take nuna kishinta akansa, yana matuk'ar sonta amma har yanzu ya kasa fad'a mata, yana jira ta kammala karatun ta kafin ya fad'a mata amma a yanzu baya jin zai iya jiranta, domin yana buk'atar mai kula dashi, dole ma ya fito mata da abinda yake zuciyarsa shekaru da yawa.
Bayan ya kammala yayi ma Mama sallama. Fitowa tayi tana masa addu'a, kud'i ya aje yana fad'in Mama yau sakwara nake son ci. Mama tace badamuwa za'ayi maka, kun gaisa da Madu ko? Ra'eez yace lokacin dana shigo yana band'aki sai dai idan na fita yanzu.
Mama tace to Allah ya tsare ya baka sa'a a duk abinda kasa gaba, Allah ya kareka daga sharrin masu sharri. Murmushi yayi cikin jin dad'i yace amin Mama.
Mama tace ina Rumaisar fa? Ra'eez yace tana d'aki kila wani abun takeyi. Mama tace to sai ka dawo. Fita yayi yana waiwayen d'akin Rumaisa. Sai da suka gaisa da Madu ya bashi kud'i yana ta masa addu'a kafin ya tafi.
Asibiti ya fara biyawa ya duba Ummunsa kafin yawuce wajen aiki, koda yaje ya iske har Alhaji Barau yazo, kai ya jinjina yana fad'in lallai yau na makara da yawa. Ciki yawuce yana gaisawa da mutanan da suke waje.
Lokacin daya shiga ofis d'in Alhaji Barau tare da bako ya iskeshi, risnawa yayi ya gaishe su. Alhaji Barau yace Ra'eez ko dai bakayi bacci jiya da dare bane? Murmushi yayi yana fad'in wallahi makara ce kawai nayi.
Alhaji Barau yace Mr. Kallah kaga sabon lauyen da nake fad'a maka. Da sauri Ra'eez ya kalli wanda aka kira da Mr. Kallah, domin duka sunayen wad'an da suka zalunci Abbunsa babu wanda bai rik'e ba.
Murmushi Mr. Kallah yayi yana fad'in lallai ankawo maka cigaba a ofis d'inka, domin samun lauyoyi masu hazak'a yana k'arama waje kima, sannu Ra'eez kacigaba da dagewa kaji.
Kai Ra'eez ya d'aga. Alhaji Barau yace ga wani file nan kaje ka dubashi yanzu aka kawoshi, bana son ka wahalar da kanka domin ba wata babbar shari'a bace kasan wasu mutanan basu da kwakkwarar sheda kawai saboda sun maida kotu wajen wasa komai su kawo k'ara.
Ra'eez yace zan duba. Kai Alhaji Barau ya jinjina yana fad'in zaka iya tafiya. Sallama yayi masu ya fita. Mr. Kallah yace gaskiya natsuwar Yaron nan tayi mani sosai, daga ganinsa d'an manyan mutane ne.
Alhaji Barau yace shiyasa nake son had'ashi da Yarinyar waje na. Mr. Kallah yace wai Raheena kake magana? Alhaji Barau yace ita fa, ai kasan ita kad'aice mace sauran maza ne.
Mr. Kallah yace lallai kayi tunani, kaga nan gaba ko zaka aje aiki zaka iya d'orashi a matsayin ka, kaga shikenan bamu da sauran damuwa kotu ta zama tamu. Alhaji Barau yace kamar kashiga zuciyata. Dariya sukasa suna kashewa.
**
K'arfe d'aya dai-dai wayar Ra'eez tayi k'ara, yana dubawa yaga sunan daya sama Rumaisa a saman wayar ( *Cutie*) . Murmushi yayi kafin ya katse kiran, dan baya d'aukar mata waya sai dai ya kashe ya kira.
Da kallo Jabeer ya bishi ganin yanda yake sakin murmushi. Wayar yasa a kunne yana jiran ta d'auka. Tana d'agawa suka gaisa, shiru tayi ta kasa magana. Ra'eez yace an gama fushin dani ne? Rumaisa tace dama lokacin sallah ne yayi.
Sosai ya saki murmushi dan ya gano manufarta. Rumaisa tace katashi kayi sallah to. Jinjina kai yayi kamar tana gabansa yace yanzu kuwa rankiyadad'e, nagode da wannan kulawa, kinga yau kin riga Rah.... Katse wayar tayi dan bata son ya k'arasa fad'ar sunanta.
Dariya yayi yana kallon wayar. Dafashi Jabeer yayi yana fad'in Mr. Love idan ka gama muje kada atayar. Girgiza kai yayi yana fad'in waya fad'a maka soyayya nakeyi K'anwata ce fa.
Jabeer yace naga alama, tashi mutafi to. Dariya Ra'eez yayi yana fad'in da gaske fa nakeyi. Jabeer yace kaji kama kai, kaji nace wani abu ne? Muje kada atayar. Sosa kai Ra'eez yayi suka fita.
Kasancewar a ofis ya bar wayar suna shigowa ya iske wayarsa tana k'ara, kafin ya d'aga ta katse. Hannu Jabeer yasa ya d'auke wayar yana fad'in yanzu kuma waye ya kira? Ido ya zaro yana fad'in missed call takwas fa.
Hannu Ra'eez ya kai zai amshe wayarsa yana murmushi. Jabeer yace sai dai kuma lambar babu suna amma duk mutum d'aya ne. Ra'eez zaiyi magana wayar ta sake k'ara.
D'auka Jabeer yayi yasata a speaker, harararsa Ra'eez yayi yana amsar wayar, kafin ya cire a speaker Raheena tace Allah yasa ba laifi nayima Yayan nawa ba, tun d'azu nake kira amma shiru har kasa hankalina ya tashi fa.
Saurin cireta yayi yasa a kunne yana kallon Jabeer da yake masa dariya. Zama yayi yana fad'in Raheena ce? Shagwab'e fuska tayi tana fad'in yanzun ma bakayi saving lambar tawa ba? Murmushi yayi yana fad'in ayi hak'uri mantawa nayi.
Raheena tace nayi ai baka laifi a wajena, ina fatan dai kaci abinci? Ra'eez yace sallah ya kamata ki fara tambaya ko dai bakiyi ba kema? Rufe baki tayi dan itama batayi sallar ba bare ta tambayi wani, wayancewa tayi tana fad'in ai nasan baka wasa da sallah shiyasa ban tambaya ba, amma nayi tawa.
Ra'eez yace to kin kyauta dan bana son mutum mai wasa da sallah. Raheena tace insha Allahu bazan sake wasa da sallah ba tunda baka so. Ra'eez yace da naji dad'i kuwa.
Murmushi tayi tana fad'in bazan sake ba, yanzu dai kaci abinci? Ra'eez yace banci ba. Raheena tace gaskiya bazanji dad'i ba ace har yanzu baka ci abinci ba, bani minti talatin yanzu zan kawo maka.
Ra'eez yace nasa Mama tamun sakwara kibarshi nagode. Raheena tace kai Yayana dan Allah ka barni nazo. Ra'eez yace kibarshi nagode. Shagwab'e fuska tayi tana fad'in to kamun alk'awari zakazo anjima kaji.
Ra'eez yace zan duba nagani. Raheena tace nagode, ka kular mun da kanka. Ra'eez yace nagode. Kashe wayar yayi yana murmushi.
Zama Jabeer yayi yana kallonshi hada tagumi. Gira Ra'eez ya d'aga mashi yana fad'in ya dai? Jabeer yace lallai kai d'in azimun ne.
Gyara zama Ra'eez yayi yana fad'in kacika sa ido wallahi. Jabeer yace naji amma a bani amsa ta. Ra'eez yace kasa ido kacigaba da kallo kawai. Jabeer yace bazaka fad'a ba kenan? Ra'eez yace ka bari idan na tashi zuwa sai muje tare. Jabeer yace yanzu naji batu. Dariya sukayi suka cigaba da aiki.
Suna tashi Ra'eez yace ma Jabeer dole sutafi tare suci abinci a wajen Mama, Jabeer yace shikenan daga can sai mu wuce ko? Ra'eez yace shikenan amma sai munyi magriba. Jabeer yace sai dai mu fara biyawa gidan mu kada Ummana taga na dad'e sai mu wuce. Ra'eez yace shikenan muje.
***
Bayan sun biya gidansu Jabeer suka wuce gidan su Rumaisa. Tunda Jabeer yaga yanda Rumaisa take sunne kai ya gano abinda yake tsakanin su, musamnan da yaji Ra'eez yana fad'in ta sako hijabi su biyu ne. Shiru kawai yayi yana dariyarsa.
Ra'eez yace kai fa d'ansa ido ne. Jabeer yace me kaji nace kuma? Kwafa Ra'eez yayi ya jawo kwano suka fara cin abinci. Mama tace lallai Jabeer ka ciri tuta, da alama hankalin Ra'eez ya kwanta da kai, ban tab'a ganin Ra'eez da aboki ba sai yau.
Murmushi yayi yana fad'in nima nace masa nayi shiyasa ya amince dani Mama. Murmushi tayi tana fad'in gaskiya naji dad'in had'uwar ku, Allah yasa hakan ya zama alkhairi, sai ku kula da aikin ku kunsan yanda yake da had'ari. Gaba d'aya suka amsa da insha Allah.
Bayan sun gama suka tashi. Mama tace tafiya zakuyi ne? Jabeer yace zan rakashi wajen... Take masa k'afa Ra'eez yayi hakan yasa yayi shiru. Kallonshi Rumaisa ta tsaya yi. Ra'eez yace yanzu zan dawo Mama.
Wayarsa ce tayi k'ara, yana d'agawa yace gamu nan zuwa, kashewa yayi yana fad'in muje. Kallon Rumaisa Jabeer yayi yaga yanda ta had'e fuska, fita sukayi tana mai binsu da kallo cike da bakin ciki.
Ur's.
Nabeelert Lady🖋
[3/10, 8:39 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud'i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k'asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub'e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.*
2⃣4⃣
Tsaye suke a jikin mota acikin harabar gidan su Raheena, tunda suka shigo anguwar fuskar Ra'eez ta canza, haka kawai yake jin wani d'aci a zuciyarsa, a hanya sai wasa da dariya suke da Jabeer amma suna shigowa anguwar yanayinsa ya canza.
Jabeer ya d'auka wani abunne shiyasa yayi shiru, amma a yanzu da suke tsaye suna jiran fitowar Raheena sai yaga abun yayi yawa, domin yana zolayarsa akan ya fad'a masa tsakanin Rumaisa da Raheena wacece yake so aciki amma sai yaga Ra'eez bai san yanayi ba dan hankalinsa yana wajen kallon gidan, musamman ginin da yake can bayan gidan.
Hannu Jabeer yasa ya tab'o Ra'eez, da sauri ya juyo jin an dafashi. Ido Jabeer ya tsura mashi ganin yanda idanuwansa sukayi ja. Duk'ar da kai Ra'eez yayi yana kok'arin b'oye b'acin ransa.
Jabeer yace Ra'eez lafiyar ka kuwa? Murmushin yake Ra'eez yayi yana fad'in lafiya lau me kagani? Jabeer yace tun shigowar mu anguwar nan naga yanayin ka ya canza, tsayuwar mu anan kuma sai naga abun ya k'aru, gashi kana kallon wani waje har idanuwanka sunyi ja, da alama akwai abinda ya sosa maka zuciya ko? Murmushi Ra'eez yayi yana fad'in bakomai kawai kai ne kaga haka.
Jabeer yace bazaka fad'a mani ba ne kawai, amma har fa magana nake maka hankalin ka yana wani waje har sai da na tab'oka kafin kasan ina magana.
Ra'eez yace babu komai kawai ina tunanin dalilin da yasa Raheena take son nazo bayan nasan babu komai atsakanin mu, duka jiya muka fara ganin juna kuma.
Jabeer yace kaima kasan soyayya ce kad'ai zatasa ta nemeka, nifa tun wayarku ta d'azu na fahimci komai, sai dai kaine ban gane maka ba, a gida ga Rumaisa sannan kuma anan ga Raheena, ban sani ba ko auren gata zakayi.
Ra'eez yace meye kuma auren gata? Jabeer yace auren mata biyu a lokaci guda mana, idan ba gata ba taya zaka had'a mata biyu kana soyayya dasu alokaci guda kuma dukansu wajen kunya ne babu wacce zaka iya ajewa.
Murmushi kawai Ra'eez yayi bece komai ba. Jabeer yace duk da bansan komai a labarin ka ba amma na fahimci kana da alak'a mai k'arfi dasu Rumaisa, kaga kuwa bazaka iya yaudararta ba, ga 'Yallab'ai kuma, kaga kana aiki a k'ark'ashin sa bazaka iya yaudarar d'iyarsa ba.
Ra'eez yace haka ne, domin Rumaisa ruhin jikina ce, da soyayyarta na girma, domin soyayyarta ta samo asali tun lokacin da naji sunanta, bayan da muka fara gaisawa awaya sai ta k'ara shiga zuciyata, aranar dana fara ganinta duk da muna yara amma najita a jinin jikina, daga lokacin da na mallaki hankalin kaina sai na fahimci ta zama b'argon jikina, in tak'aice maka mutuwace kad'ai zata iya rabani da Rumaisa.
Baki Jabeer ya rik'e yana kallon Ra'eez wanda yake zuba bayani har wani lumshe ido yake yayin da hannunsa yake saman kirjinsa yana nuni dashi. Dariya yayi yana fad'in ita kuma Raheena fa? Ra'eez zaiyi magana yaji k'amshin Raheena ya dakar masa hanci.
Shiru yayi yana kok'arin d'ago kanshi. Cike da yanga Raheena take taku kamar bata son taka k'asa, kayan jikinta kamar zatayi nishi su yage saboda yanda suka matse ta, k'aramin gyale ta yafa a saman kanta ko d'ankwalin kayan bata sa ba, sai gashin data k'ara data bazo a bayanta.
Kallo d'aya yayi mata ya d'auke kanshi cike da takaici, badan akwai abinda yake sak'awa aranshi ba da babu abinda zaisa yazo wajen wannan abar.
Fuskarta d'auke da murmushi ta k'araso wajensu tana fad'in sannun ku da zuwa wallahi banyi zaton zaka zo ba. Fuska a had'e Ra'eez yace sallama ya kamata ki farayi ba wannan maganar ba.
Saurin dafe bakinta tayi ta juya tana fad'in kayi hak'uri na manta ne amma bazan sake ba. Seda ta koma da baya kafin ta dawo bakinta d'auke da sallama.
Gaba d'aynsu suka amsa Jabeer yana fad'in sannu da shanyamu Raheena. Murmushi tayi tana fad'in kuyi hak'uri bansan kun taho ba ne kuma shirina dad'ewa gareshi kusan awata d'aya ina shiryawa.
Ra'eez yace idan kika cigaba da haka bazaki sake ganin mu a wajenki ba, domin mu bama jiran da yawuce minti biyu. Hannuwa ta had'e tana fad'in ayi hak'uri, daga yau bazan sake ba, tunda dai baka son jira nima bazan sake dad'ewa ina shiri ba koda baka nan zanyi kok'arin koyon sauri matuk'ar hakan zai saka farin ciki.
Murmushin gefen baki Ra'eez yayi ya kauda kai. Jabeer ne yace Hajiya Raheena ina wuni. Murmushi tayi tana fad'in la.... Kallon da Ra'eez yayi mata yasa tayi saurin yin shiru.
Ra'eez yace lallai ma, abokin nawa zai gaisheki ki amsa, bayan kinsan daga sallama gaisuwa itace tafi dacewa. Hannu tasa ta d'an bigi kanta tana fad'in dan Allah kuyi hak'uri wallahi ban saba da hakan bane amma zanyi kok'arin gyarawa tunda abinda kake so kenan. Ina wunin ku? Jabeer yace lafiya lau.
Raheena tace mushiga ciki bana fira awaje akwai wajen zaman baki acan. Ra'eez yace bana fira a cikin falo nafi son waje saboda nafi buk'atar iskan waje.
Murmushi ta saki tana fad'in duk yanda kace, ga kujeru acan muje kuzauna to. Jinjina kai Ra'eez yayi yana fad'in muje.
Bayan sun zauna mai aiki ta iso da kayan motsa baki a faranti, har k'asa ta duk'a tana gaishe su, bayan sun amsa ta fara kok'arin zuba masu lemu.
Da sauri Ra'eez yace kibarshi kije kawai. Raheena tace haba ka barta mana aikinta ne fa. Kallonta Ra'eez yayi beyi magana ba. Raheena tace shikenan jeki.
Kallon Jabeer tayi tana fad'in gashi bansan sunan ka ba. Jabeer yace zakiji a bakin abokina ai. Kallon Ra'eez tayi tana fad'in Yayana kusha ko ruwa ne mana wane zan zuba maku? Ra'eez yace da ace kece kika had'a komai da kanki kuma kika d'auko daga gida kika kawo har nan shine zan sha, amma ni bana cin abinda masu aiki suka had'a.
Shagwab'e fuska tayi tana fad'in kayi hak'uri daga yau nice zan rik'a maka hidima, duk da bana shiga kicin amma zan fara akan ka.
Tab'e baki Ra'eez yayi yana fad'in amma kin bani kunya, yanzu kamar ki ace bata shiga kicin idan kikayi aure waye zai rik'a maki aikin kuma? Rausayar da kai tayi tana fad'in ai na iya dafa indomie.
Ra'eez yace Jabeer kaji fa. Dariya Jabeer yasa yana fad'in aikin kenan, ai yanzu duk wata mace data fito daga gidan hutu indomie kad'ai zaka sameta ta iya girkawa, wasu ma ko ruwan zafi basu iya d'orawa ba, shiyasa ka ganni nan bazan iya auren macen data fito daga gidan masu kud'i ba.
Raheena tace kai Jabeer kada ka tunzura Yayana mana, wallahi daga yau zan fara koyon komai matuk'ar zaisa shi farin ciki ni kuma zanyi koda zan cutu ne.
Murmushi Jabeer yayi yace lallai Ra'eez ana ji da kai, sai dai kace mani Raheena K'anwar kace amma gashi naji wata maganar kamar... Harara Ra'eez ya sakar masa hakan yasa yayi shiru yana dariya.
Raheena tace e Yayana ne amma wanda za'a iya aura, Jabeer ina so ka tayani neman soyayyar abokin ka, tunda Allah yasa na fara jin sunanshi a wajen Dady naji soyayyarsa a zuciyata, aranar dana fara d'ora idanuwana akansa sai naji komai ya kwance mani, maganar gaskiya bazan b'oye maka ba inama abokin ka soyayya mai zafi, wallahi bana ji zan iya rayuwa babushi.
Tashi Jabeer yayi yana fad'in lallai wannan maganar babbace, Raheena sai nace Allah ya bada sa'a, amma sai kin dage dan abokina mai zafi ne. Wucewa yayi yana kallon Ra'eez yana dariyar shakiyanci, yana mamakin Raheena yanda take fad'ar magana kamar itace saurayin sam babu aji, gata dai 'yar gayu amma tana kwafsawa.
Ko kallonsa Ra'eez beyi ba amma yasan dariya yake masa. Wayarsa ce tayi k'ara alamun sako yashigo hakan yasa ya maida hankalinsa yana dubawa.
Rumaisa ce, murmushi yayi kafin ya bud'e *Yayana gaskiya ka dawo gida akwai d'orin da zakamun kuma yanzu nake so kamun.* murmushi yayi ya maida wayar a aljihunsa.
Yana d'ago kai suka had'a ido da Raheena da ta langwab'ar da kai tana masa wani irin kallo, saurin d'auke kansa yayi aranshi yana fad'in wannan yarinyar bata da kunya wallahi.
Saurin tashi yayi yana fad'in zamu tafi. Da sauri ta mik'e tana fad'in haba My D, shikenan bazaka tsaya muyi fira ba daga zuwa zaka tafi ko amsata baka bani ba fa.
Kallonta Ra'eez yayi yana fad'in idan kika gyara halayenki da bana so alokacin zan fad'a maki abinda na yanke wanda nasan kece zai taimaka.
Murmushi tayi tana fad'in kasa naji dad'i sosai, kuma daga yau zan fara gyara duk abinda baka so, nan da wata d'aya zan zama macen da ta iya girki sosai.
Ra'eez yace zangani ai. Jerowa sukayi zuwa wajen motarsu sai labari take basa kamar zata shige jikinsa, shi kuwa hankalinsa yana wajen Rumaisa ya kosa ya koma.
Itace ta bud'e masa k'ofa tana fad'in Jabeer nagode sosai, idan ka sake dawowa girki na zakaci. Jabeer yace lallai naga alamar da wuri zaki d'auki darasin abokina.
Murmushi tayi tana duk'ar da kanta cikin motar tace My D, kayi tuki a hankali bana so ka wahala, idan kun isa zankira naji yanda ka isa kaji. Kai ya d'aga yana d'aukar mukullin motar.
Tana tsaye har suka fita. Ajiyar zuciya ta saki tana jin wani dad'i na ratsa ta, sam batayi tunanin Ra'eez zaiyi saurin amincewa da buk'atar ta ba, shiyasa zata dage domin ta gyara komai matuk'ar hakan zaisa ta sameshi.
Juyawa tayi da niyar kiran mai aiki tazo ta kwashe kayan sai kuma ta tuna abinda Ra'eez yace. Murmushi tayi ta juya zuwa wajen kayan ta fara had'asu tayi cikin gida.
Tana shiga Momynta ta fara tambayarta an dace? Kai ta d'aga tana fad'in sosai ma, bara na kai kayan nazo. Tana fitowa tazo ta rungume Momy tana fad'in ai na fad'a maki Ra'eez bazaiki amincewa dani ba, ko awancan ranar baki ga yanda yake bina da wani kallo ba, gaskiya Momy Ra'eez ya had'u.
Momy tace amma naji dad'i sosai, kinga nan da wani lokaci sai mu fara shirin biki, lallai zanyi bikin da ba'a tab'ayinsa adangi ba, duniya sai ta sheda bikin ki Raheena, bari Alhaji yazo tun yanzu zamu fara shirya yanda komai zai kasance, ke dole duniya tasan za'ayi bikin ki.
Dariya Raheena tasa tana fad'in nagode Momy na, dole na koma group d'in mu dana fita na kawayena, domin ina son su san irin mijin da zan aura kuma inaso na tara mutane da yawa domin kowa ta samu abun fad'a.
Momy tace haka nake so 'Diyata. Mai aiki ce tashigo bakinta d'auki da sallama. Da sauri Raheena ta amsa tana fad'in Lawisa ya akayi? Ba Lawisa ba har Momy tayi mamakin abinda Raheena tayi, domin tsakaninta da masu aikin gidan kyara ce, kome zakayi mata baka burgeta, haka kuma bata tab'a kiran sunan ka sai dai tayi amfani da kalmar Ke, ko Kai, sai gashi yau itace hada amsa sallama da kiran suna.
Duk'ar da kai Lawisa tayi tana fad'in dama abinda za'a dafa maki da dare nazo tambaya. Tashi Raheena tayi tana murmushi tace ai yau tare zamu shiga kicin d'in nima daga yau zan rik'a tayaki girki domin ina son na kware sosai.
Murmushi Momy tayi tana fad'in Raheena anya? Tashi tsaye tayi tana fad'in Lawisa muje, kallon Momy tayi tana fad'in Momy nasan bazaki so kiyima 'Diyarki aure taje gidan miji bata iya komai ba.
Kai Momy ta jinjina tana fad'in wannan haka yake d'iyar albarka, amma naji dad'in wannan tunanin naki, ko kuma nace nagode ma Ra'eez domin nasan wannan sabon canjin daga garesa ne. Dariya Raheena tasa tayi kicin tana fad'in kai Momy.
****
Tunda suka tafi Jabeer yake damun Ra'eez da tambaya akan yanda zaiyi da Raheena. Murmushi Ra'eez yayi yana fad'in yanda kowane namiji yakeyi da 'yan matansa nima haka zanyi da ita. Jabeer yace amma dai kai bakayi kama da mayaudara ba.
Ra'eez yace ka sani ko zan fara daga yau. Dukansa Jabeer yayi yana fad'in dan Allah muyi maganar gaskiya. Ra'eez yace amma dai a gabanka kaji tace tana sona ko? Kaga kuwa bazaka kirani da mayaudari ba, bata tsaya tayi binciken akwai wacce nake so ba ko babu kawai kanta ta sani, kaga kuwa idan taga na auri wata bazata zargeni ba.
Jabeer yace duk da haka, ya kamata ka fad'a mata akwai wacce kake so idan zata iya rayuwa da kai ahaka shikenan, idan kuma bazata iya ba kaga sai ta hakura.
Ra'eez yace bazan iyaba, ka sani ma wai ko ina sonta. Dariya Jabeer yasa yana fad'in ai har mata hud'u ma zaka iya aure, to Allah ya bada sa'a, amma wallahi duk ranar da aka rutsa ka kada ka nemeni. Ra'eez yace insha Allahu.
Sai da ya fara aje Jabeer gida kana yawuce gidansu Rumaisa, tana jin k'arar motarsa tayi saurin shigewa d'aki ta gyara fuskarta hada fesa turare.
Muryarsa tajiyo a tsakar gida shida Mama, kwala mata kira Mama tayi tana fad'in ki d'auko littafin ga Yayan naki nan yazo. Ciki ta shige ta barshi a saman tabarma.
Kai ak'asa Rumaisa ta fito, bakinta d'auke da sallama ta k'araso wajenshi. Tunda ta fito yaji k'amshin turarenta, dama shine yake shiya mata saboda yana matuk'ar son k'amshinsa saboda na mata ne.
Idanuwa ya tsura mata ganin yanda tayi kwalliya kamar mai shirin fita wani waje hada shafa janbaki ita da bata sonshi. Amsa mata sallamar yayi yana sakin murmushi.
Tana zama ta gaisheshi. Amsawa yayi yana fad'in Rumaisa ko dai bako zakiyi ne? Saurin kallonsa tayi tana zaro ido. Murmushi ya saki yana kallonta yanda ta zaro idanuwanta masu matuk'ar burgesa.
Maida kanta k'asa tayi tana wasa da hannunta tace ni babu wani bakon da zanyi, waye ma yake zuwa wajena. Ra'eez yace to wannan kwalliya wa akayi mawa? Rufe fuska tayi tana fad'in haka kawai naji ina buk'atar nayi.
Ra'eez yace Uhmm! Ke dai ki fad'i gaskiya. Rumaisa tace da gaske mana, yauwa wai Yaya ina kukaje? Ra'eez yace naje fira ne. Saurin kallonsa tayi idanuwanta tuni suka canza, a hankali ta mik'e tana shirin komawa d'aki.
Da sauri ya tashi yana fad'in ina zaki ba'ayi k'arin ba? Murya na rawa tace na iya ai. Ra'eez yace dawo ki zauna. Kasa dawowa tayi kawai tashige d'aki da gudu saboda kukan da taji ya taho mata, ashe dama ita kad'ai take haukanta, ta d'auka kulawar da yake bata soyayyace ashe ba haka bane a zuciyarsa, lallai ta cutar da kanta data bari ta girma da soyayyarsa a ranta.
Ra'eez kuwa jiyayi jikinsa yayi sanyi, tabbas yasan Rumaisa tana sonshi, meyasa zai fad'a mata haka? Kada garin neman ruwa kwad'o yayi masa k'afa. Lek'awa yayi wajen Mama yayi mata sallama.
A mota ya zauna yana tunanin abunyi. Kasa daurewa yayi kawai ya jawo wayarsa ya fara rubuta sako.... *Haba pretty na taya zaki tafi kibar Yayanki bayan kinsan ke kad'ai yake gani yaji dad'i, ina da kamar ki ina zan iya zuwa fira, wasa nake maki fa, Rumaisa ina matuk'ar sonki bazan iya had'a kowa da ke ba, kece rayuwata, da sonki na girma bana jin zan iya rayuwa babu ke, na dad'e ina son na fad'a maki wannan maganar amma ina tsoron kada ki kasa amincewa dani, ina sonki Rumaisa, kuma kisa aranki kece Uwar 'Ya'Yana da yardar Allah, ina so ki maido mani da amsa idan ba haka ba bazan iya bacci ba.*
Ya mai-maita sakon daya rubuta yafi so biyar kafin ya tura fuskarsa d'auke da murmushi, yana turawa yayi saurin barin k'ofar gidan.
Rumaisa da Mama take tama fad'a akan k'uncin da ta sameta tanayi taji k'arar wayarta, amma saboda Mama tana wajen sai ta share taki dubawa. Mama tace idan kin gama k'uncin ki fito ki kai Abdallah yayi fitsari ya kwanta tunda bazaki fad'a mani abinda yake damunki ba, bansan lokacin da kika fara b'oye mani abu ba Rumaisa.
Tashi Rumaisa tayi tana turo baki tace bakomai fa Mama Yaya ne yace dole sai na bashi hadda gobe ko mu b'ata. Murmushi Mama tayi tana fad'in ai gara ku b'ata tunda kina son wasa da karatu.
Bayan ta kwantar da Abdallah taje tayi shirin kwanciya ranta a dagule, saman gadonta ta kwanta sai tsaki takeyi, wayarta ta jawo domin ta kunna karatu ko zataji sauki sai taci karo da sakon Ra'eez.
Da sauri ta bud'e, tana fara karantawa tayi saurin tashi zaune tana mutstsike ido, bata san lokacin da murmushi ya bayyana a fuskarta ba, filo ta jawo tana sakin dariya. Ta karanta sakon daya turo yafi akirga.
Kwanciya tayi tana fad'in ashe ma yana sona shine yake ja mani aji, nima bazan maida amsar ba sai gobe nima sai naja aji. Kwanciya tayi da anjima sai ta jawo wayar ta sake karanta abinda ya rubuta.
Can dai ta kasa daurewa, tashi tayi domin ta maida masa amsa... *Yayana nagode da soyayyarka agare ni, insha Allahu zaka sameni amatsayin Uwa tagari a wajen 'Ya'yan mu, amma dan Allah kadena mani wasa da wata mace zuciyata bazata iya d'auka ba. Kayi bacci lafiya nagode.*
Tana turawa tayi saurin kashe wayar gaba d'aya tana murmushi.
***
Ra'eez daya kasa bacci yana rokon Allah yasa ta amince dashi, k'arar wayarsa yaji alamun shigowar sako, jiki na rawa ya jawota yana fatan Allah yasa yayi farin gani.
Ur's.
Nabeelert Lady🖋
[3/10, 8:39 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud'i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k'asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub'e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.*
2⃣5⃣
Ra'eez besan lokacin daya tashi zaune ba, filo ya jawo ya rungume yana sakin murmushi, ya dad'e yana jiran irin wannan ranar domin shima yashiga sahun masoya amma sai yau Allah yasa zai shiga.
Komawa yayi ya kwanta yana kok'arin kiran Rumaisa, sai dai kiran farko yaji wayar akashe. Murmushi yayi yana fad'in sarkin kunya, dama nasan bazan sameki ba.
Lumshe ido yayi yana tunanin ya kamata ya sama mata gurbin shiga makaranta kafin ayi bikinsu. Saurin girgiza kai yayi yana fad'in bana son ta fara karatu garin nan saboda ba lallai zaman mu ya d'ore anan ba, daga ranar da aka gano gaskiya dole zasu koma kano, gara ma ya bari bayan anyi biki a hankali sai tayi karatun ta.
Cike da gamsuwa ya jinjina kai. Shiru yayi yana tunanin Raheena. Murmushi yayi yana fad'in kiyi hakuri Mahaifinki ne ya jaza maki, amma dole su d'and'ana illar yaudara da zalunci, koba komai nima zakici moriyata.
Haka ya kwanta cike da tunanin masoyiyarsa har bacci ya d'aukesa.
*** ***
Kiran wayar Raheena ne ya tashesa a bacci da ya makara, saurin tashi yayi ya d'auka. Murmushi Raheena tayi tana fad'in lokacin sallah yayi. Ra'eez yace amma nagode maki, badan ke ba da na makara, amma nasan kema bakya tashi sallar asuba ya akayi har kika tashe ni? Raheena tace wallahi ada ne bana tashi sai da safe nake sallah, amma tun daga ranar da kace kaji dad'i dana tasheka kuma kana son mai sallah da wuri yasa nake tashi, saboda kai har alarm nasa wallahi.
Murmushi Ra'eez yayi yana fad'in Allah yasa ki dawwama a haka, kuma ina so ki rik'a yin komai saboda Allah ba danni ba, hakan zai sa abun ya bi maki jiki ko dani ko bani kicigaba.
Raheena tace insha Allahu. Ra'eez yace nagode bara naje masallaci. Raheena tace ka sani cikin addu'ar ka. Murmushi yayi yana fad'in insha Allah. Sauka yayi ya nufi band'aki yana murmushi yayin da k'asan zuciyarsa ya fara tausayin Raheena danshi mutum ne mai tausayi.
***
Bayan ya kammala shirinsa na fita aiki ya tsaya yana duba wayarsa, yasan bayan ya fito wanka Jabeer ya kirasa, bayan sun gama waya ya ajeta saman gado yacigaba da shiri.
Kugu ya rik'e yana mamakin ina ta shige? K'aranta ya faraji alamun ana kiransa, dubawa ya farayi har ya gano daga k'ark'ashin gado k'aran yake fitowa. Murmushi yayi yana fad'in ashe kina nan.
Hannu yasa ta k'asan gadon sai dai tayi ciki hakan yasa ya tashi ya fara d'aga katifar, sai da yasa k'afarsa ya tokare katifar kafin ya duk'a ya d'auko wayar.
Bayan ya d'auko wayar har ya d'ago ya koma yana duba jikin gadon ganin kamar wata durowa a jiki, mamaki ne ya kamashi yana tunanin dama anama gado durowa? Murmushi yayi yana fad'in mutanan Da akwai dabara. Hannu ya kai zai bud'e wayarsa tayi k'ara, yana dubawa yaga Mama ce, saurin sakin katifar yayi ya tsinke kiran kafin ya kirata.
Tana d'agawa ta fara tambayarsa lafiya be fito ba har yanzu? Ra'eez yace na shirya wayata na tsaya nema amma gani nan. Kashe wayar tayi. Juyawa yayi yana kallon gadon kafin ya d'auki jakarsa da mukulli yayi waje yana tunanin abinda yake cikin durowar.
Yana tuki ya kira Alhaji Mansur, bayan sun gama gaisawa yake tambayarsa jikin Ummunsa? Ra'eez yace kamar koda yaushe Abba, kwana biyu banje ba saboda wani aiki da nakeyi amma yau daga ofis zan je na ganta.
Alhaji Mansur yace baka kyauta ba gaskiya, kasan dai yanda take jin dad'i idan kaje shine zaka kwana biyu ba tare daka lek'a ba. Ra'eez yace ayi hakuri Abbah zanje yau.
Alhaji Mansur yace shikenan, yasu Mamar taku da Rumaisa fa? Ra'eez yace duk suna lafiya ina hanyar zuwa gidan ma. Alhaji Mansur yace ina Kawun ka fa? Ra'eez yace duk yau zan lek'a insha Allahu.
Alhaji Mansur yace idan kaje wajensa ka had'amu ina so mugaisa, kaima idan ka samu lokaci akwai maganar da zamuyi, ina fatan kana kula a wajen aikin ka ko? Ra'eez yace sosai ma Abbah.
Alhaji Mansur yace haka ake so, da fatan kana kula da yanayin Alkalin ku? Ra'eez yace Abbah shekaran jiya har gidansa ya gayyace ni cin abinci wai yana sona, ashe d'iyarsa yake so ya had'amu, sai da mukaje gidan na samu ashe tsohon gidan Abbu ne.
Alhaji Mansur yace ka kula fa, duk yanda zai jaka jikinsa kada ka saki jiki dashi har ya gano wani abu daga gareka, bana so kowa yasan kana da alak'a da Mahaifinka, nasan waye Brr. Barau, yana da matuk'ar wayau, dan haka ka kula sosai.
Ra'eez yace insha Allahu. Alhaji Mansur yace ina fatan ba son yarinyar tasa kake ba ko? Zaro ido Ra'eez yayi yana fad'in haba dai Abbah, ai ko d'aura mani ita akayi na kwanceta na gudu.
Murmushi Alhaji Mansur yayi yana fad'in ai dole na tambaya kasan ita zuciya ba ruwanta da kiyayyar wasu. Ra'eez yace babu komai a zuciyata Abbah, ni yanzu ma ta Rumaisa nake dan jiya na fad'a mata abinda yake raina.
Murmushi Alhaji Mansur yayi yana fad'in ja'iri, ai na d'auka zaka cigaba da b'oyewa ne, ko jiya Ummanku tamun maganar nace ta barka idan ka gaji da ajiyar abunka zaka furta ne, ashema har ka shigar da kan ka.
Shafa kai Ra'eez yayi yana fad'in wallahi kuwa Abbah. Alhaji Mansur yace haka akeso, Allah ya tabbatar da alkhairi. Kasa amsawa Ra'eez yayi yana fad'in ina Labiba? Alhaji Mansur yace jiya ma tazo gida da yaranta.
Ra'eez yace zan kirata. Alhaji Mansur yace bara na barka gashi ma ka kusa makara, ka gaishe dasu Maman ta ku. Ra'eez yace nagode agaishe da Ummah.
****
Koda yaje gidan su Rumaisa bai isketa a tsakar gida ba, tana jinsa tayi saurin shiga band'aki. Bayan sun gaisa da Mama ta kawo masa abinci.
Yana ci suna fira yana fad'a mata Abbah yana gaisheta. Mama tace Allah sarki ko jiya munyi waya da Umman ka ai. Ra'eez yace anjima idan na taso zan biya wajen Kawu da Ummu.
Mama tace wallahi nima ina son naje na ganshi, Abdallah yana yawan tambayarsa. Ra'eez yace kushirya idan na dawo sai na biyo mutafi gaba d'aya, amma sai dai Abdallah ya hakura da islamiya tunda dawuri zan dawo.
Mama tace shikenan. Rumaisa ta kwalama kira amma taji shiru. Tsaki tayi tana fad'in bansan me kike a band'aki ba idan ki kashiga kamar wacce zata canza fata.
Ra'eez yace Mama kibarta tayi wankanta atsanake. Rik'e baki Mama tayi tana fad'in goya mata baya zakayi? Dama saboda kai nake kiranta tazo ku gaisa.
Tashi yayi yana murmushi yace zamu gaisa a waya ai, idan Abdallah ya dawo agaishe mani dashi sai na dawo.
Mama tace to Allah ya bada sa'a ya kare ka daga sharrin mahassada. Ra'eez yace amin. Kud'i ya aje mata yayi waje da sauri dan yasan halinta. Tana tambayarsa abinda zaici amma yayi waje.
Madu ne ya taso yana fad'in Ra'eez har ka fito? Ra'eez yace nafito Baba Madu ya kasuwar? Madu yace gatanan Alhamdulillahi sai godiya. Kud'i Ra'eez ya ciro ya mik'a masa yana fad'in ga wannan, anjima idan na dawo ka shirya zamu kaima Kawu da Ummu ziyara.
Madu yace gaskiya daka kyauta, angode sosai Allah yayi albarka sai ka dawo. Ra'eez yace amin na tafi.
Yana shiga mota ya latso wayar Rumaisa, bugu biyu ta d'auka bakinta d'auke da sallama. Lumshe ido yayi yana amsawa tare da fad'in kin gama gudun? Murmushi tayi mai sauti ta fara gaishe shi.
Ra'eez yace bana cin mike, wallahi idan kina mani rowar ganin ki zakisa na rik'a kula wasu. Da sauri Rumaisa tace kayi hak'uri to. Ra'eez yace bazanyi ba, aikinsan bazan iya aikin kirki ba idan ban ganki ba ko.
Saurin tashi tayi tayo waje tana bashi hak'uri, kamar ance ya d'aga idonshi sai ganinta yayi a k'ofar gida ta langwab'ar da kai tana kallonshi hannunta rik'e da waya tana murmushi.
Da sauri ya kashe wayar ya fito. Yana zuwa tayi saurin duk'ar da kanta k'asa tana sake gaisheshi. Tsura mata ido yayi yana fad'in ashe dai ana tsoron kishiya? Turo baki tayi tana fad'in ni bana tsoro.
Dariya yayi yana fad'in gashi daga fad'in magana kin fito, ai dama nasan ba wani abinda kikeyi aband'aki saboda kada Mama ta kira ki kawo mani abinci yasa kika shige band'aki, to daga yau bazan sake cin abinci ba matuk'ar ba kece kika kawo mani ba.
Kallonshi tayi tana fad'in shikenan bazan sake ba. Murmushi yayi yana fad'in yauwa Pretty na, ina fatan dai jiya kinyi bacci mai dad'i? Kai ta d'aga a hankali tace sosai ma.
Ajiyar zuciya ya saki yana fad'in bara na tafi aiki na kusa makara, idan na dawo zamuje wajen Kawu da Ummu. Murmushi ta saki tana fad'in sai ka dawo ka kular.... Shiru tayi tana sunne kai.
Murmushi yayi mai sauti yana fad'in zan kular maki da kaina sosai. Da sauri tashige ciki tana murmushi. Girgiza kai yayi ya juya zuwa mota ya tafi.
Da Mama taci karo a tsakar gida. Saurin duk'ar da kai tayi kamar marar gaskiya. Murmushi Mama tayi tana fad'in zaku k'araci gulmar ku dai. Turo baki Rumaisa tayi tace kai Mama me nayi kuma? Mama tace ina zan sani, idan tayi wari dai naji.
Dariya Rumaisa tayi tashige ciki. Murmushi Mama tayi tana fad'in Allah ka tabbatar da alkhairi. Idanuwanta ne suka ciko da kwalla tana fad'in Allah ka kawo mana k'arshen wannan masifa da muke ciki, Allah ka fiddo bawanka haka nan, ka bama Hajiya lafiya kuma ka tona asirin munafukai.
**** ****
Zaune suke a ofis suna ta aiki Ra'eez yana kok'arin had'a aikin da Alhaji Barau ya bashi akan wani case wanda za'ayi da Yaron abokin kasuwancinsu, Alhaji Marusa shine yayi mashi jagora domin yasan matuk'ar akazo kotun su case d'in zai mutu cikin ruwan sanyi.
Bayan da aka kawo ma Alhaji Barau sai yace Ra'eez zai bamawa. Alhaji Marusa yace abama Brr. Bajinta domin shine namu, shine yasan yanda muke tafiyar da komai, bana so azo a samu matsala.
Murmushi Alhaji Barau yayi yana fad'in ina da dalilin da yasa na bama Ra'eez, domin idan muka bama Brr. Bajinta aikin su wad'an can zasu iya d'aukar Ra'eez ya tsaya masu, na tsora ta da yaron domin yana da wata baiwa, koni da nayi gogayya alokacin ina Barrister bazan nuna masa komai ba, kaga dan ya goga da Brr. Bajinta tuni zai kadashi, wannan dalilin ne yasa na bashi case d'in, domin zamu bashi shedar bogi kuma kaga dole da ita zaiyi amfani, nasan zasu iya d'aukar Brr. Bajinta domin sun san yana kada mutane, kaga shikuma sai yaki zaluko kwararen hujjoji, kaga kuma kotu da kwararen shedu take aiki, shikenan case ya mutu.
Tafi Alhaji Marusa yayi yana fad'in Alhaji Barau har yanzu kana nan yanda na sanka, shiyasa akoda yaushe hankalina yake kwance, domin nasan kowace katob'ara nayi ina da mai tsaya mani.
Alhaji Barau yace ai baku da matsala, wani abun ma sai ya zama surikina. Dariya sukasa, Alhaji Marusa yace amma duk da haka Brr. Bajinta ya tarbi wad'an da suka kawo k'arar yace zai tsaya masu kada suje su bama wani lauyan. Alhaji Barau yace kaima ka kawo shawara, shikenan hakan za'ayi. Dariya suka sake sawa da haka suka bar zancen akan a bama Ra'eez case d'in, sai gashi kuma an bashi.
Shiru Ra'eez yayi yana kallon takardun da masinjan Alhaji Barau ya kawo masa. Sake dubasu yayi yana mamakin irin wannan abu, gashi dai an bashi takardar case, ina ruwanshi da aiko masa da shedu kuma? Ai wannan aikinsa ne yaje ya nemo komai da kanshi, kuma yana so ma ya gana da yaron da zai tsaya mawa.
Tsaki yayi yana fad'in bazan biye tasu ba, dole na gano lauyen da zai tsaya ma d'ayan b'angaren domin nasan irin shirin da zanyi, tunda yaga haka ajikinsa yasan abinda aka bashi babu gaskiya aciki, shi kuma yayi alk'awarin bazaiyi aikin rashin gaskiya ba.
Jabeer ne ya dafashi yana fad'in Ra'eez lafiya kuwa? Ajiyar zuciya yayi yana fad'in wallahi nashiga tunanin wani rainin hankali da akeso amun ne. Jabeer yace akan mefa? Takardar Ra'eez ya mik'a masa yana fad'in wani k'arfin hali nake gani yanzu, sai kace wanda yake aikin gata, ace ina lauya amma sheduma sai an nemo mani kawai zuwa zanyi na gabatar dasu.
Dariya Jabeer yayi yana fad'in da sannu dai zaka fara gano halin mutumin. Tsaki Ra'eez yayi yana fad'in ko kasan wanda zamu kara dashi? Jabeer yace yawuce Brr. Bajinta.
Saurin kallonshi Ra'eez yayi cike da alamun tambaya. Jabeer yace nasan dole hakan ne zata kasance, domin farkon zuwana da nayi wani case nayi nasara anyi mani irin haka, sai dai alokacin ban gama gogewa da kowa ba sai nayi yanda suka ce, kuma nida Brr. Bajinta muka kara, abun ya bani mamaki ganin yanda yake ma wanda yake karewa wata irin tambaya, sai ka kad'auka shine yake kare wanda nake karewa, gashi dai abinciken da suka bani nasan akwai alamun tambaya, bangama shan mamaki ba sai da shari'ar tazo k'arshe, ina ji ina gani aka yanke ma wanda Brr. Bajinta yake karewa hukunci, mutane sunyi mamakin yanda sabon zuwa kamata ya iya kada kwararren lauya, kuma a shari'ar da mukayi ya fini baki amma duk da haka nine nayi nasara.
Jinjina kai Ra'eez yayi yana sakin murmushi ta gefen baki, kallon Jabeer yayi yana had'a takardu yace ka barni dasu, zanyi wasa dasu, za'aga yanda ake shari'a a wajena domin bazan bari su sani aikata kuskure irin nasu ba.
Jabeer yace sai kayi da gaske kam. Ra'eez yace dole inaso na had'u da yaron domin bazan shiga shari'a da abinda suka bani ba. Jabeer yace kayi dai-dai, tashi muje sallah.
*** ***
Bayan sun tashi daga aiki kowa ya fito ya nufi motarshi, wani dattijo suka gani zaune a gefe ya buga tagumi ya lula tunani, har sun wuceshi sun kai wajen motarsu sukaji alamun motsi.
Dattijon suka gani yayo wajensu da d'an sassarfa. Tsayawa sukayi suna kallonshi. Bayan ya k'araso ya matsa kusa da Ra'eez fuskarsa d'auke da damuwa. Ra'eez ne ya fara gaisheshi yana fad'in lafiya dai Baba? Wanda aka kira da Baba yace ba lafiya ba Yaro.
Gyara tsayuwa Ra'eez yayi yana fad'in mecece damuwar ka Baba? Hannu Dattijon yasa ya goge kwallar data zubo masa yana fad'in nazo wajen nan dasa ran ganinka domin nasan zaka iya kwato mana hakkin mu, tun ranar dana fara kallon shari'ar ka da akayi ta farko na yaba da kwazon ka, duk da ban tab'a tunanin zan samu kaina a kotu na kawo k'ara ba amma tun a wancan lokacin nake aiyana koda shari'a zata had'oni a kotu tabbas kaine wanda zan nema, sai gashi lokaci yazo shari'a ta kawoni kotun ku, an zalunceni anci mutuncin Auta ta, nazo neman lauya sai na samu ance kaine wanda zai kare Yaron daya lalata rayuwar 'Yata, abun ya bani mamaki alokacin da Brr. Bajinta ya tarbeni kamar dama ni yake jira, kuma anan take yace shine zai tsaya mani, tunda ya fad'i haka jikina ya kasa amincewa dashi, domin nasan shi lauyan manyan mutane ne, narasa inda zansa raina hakan yasa nace dole sai na ganka naji da gaske kaine zaka tsayama wannan Yaron ko kuwa.
Ajiyar zuciya Ra'eez yayi cike da tausayin wannan Dattijo, tabbas su Brr. Bajinta sun shirya wani abu, tun daga jin bayanin Baba yasan akwai alamun tambaya.
Kallon Dattijon yayi yana fad'in Baba kayi hak'uri, insha Allahu kaine zakayi nasara, tabbas nine wanda 'Yallab'ai ya bama damar kare wanda kake k'ara, amma ina mai tabbatar maka kaine zakayi nasara.
Dattijo yace ta yaya Yaro? Nasan irin basirar ka baza'a iya kada ka ba, yanzu kam inaji na hak'ura da wannan shari'ar, cuta ce an cuci Auta ta, zan koma gida muyi hakuri da K'addarar da Allah ya aiko mana, shi kuma mun barsa da Allah, zai biyamu alokacin da beda kowa.
Jabeer ne yayi saurin fad'in Baba kada kace haka, tunda abokina yace kaine zakayi nasara to kasa aranka zakayi d'in, bazamu bari a danne maku hakkin ku ba, ka yarda damu.
Jinjina kai Dattijon yayi yana fad'in shikenan, na amince da ku, Allah ya bamu sa'a. Ra'eez yace amin Baba, yanzu kashiga mota ina so naje naga Autar taka dan bana so kowa ya gammu tare, kuma kada ka fad'ama kowa munyi magana da kai kawai kayi abinda Brr. Bajinta yace maka. Dattijo yace nagode sosai. Mota suka shiga Ra'eez yana fad'in na makara ma akwai inda zamuje, amma daga can sai na d'auko su Mama mu wuce kawai. Shima Jabeer yashiga tashi motar ya bisu abaya.
Ur's.
Nabeelert Lady🖋*Wannan littafin na kud'i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k'asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub'e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.*
2⃣6⃣
Idanuwan Ra'eez ne suka ciko da kwalla tun daga lokacin da yayi ido biyu da Yarinyar Baba wacce bazata wuce shekara 16 ba amma an lalata mata rayuwa. Hannu yasa ya goge idonshi yana kallon Mahaifiyar Yarinyar yana fad'in Mama kuyi hakuri, insha Allahu zakuyi nasara, duk da ba nine zan tsaya maku ba kusa aranku ku nake ma aiki.
Goge idonta tayi tana fad'in na yarda da abinda kace, mungode da wannan taimako. Ra'eez yace bakomai, ya sunanta ne? *Habiba* sunanta, ita kad'ai gare mu mace dama su ukku ne, biyu maza sai ita, babban cikinsu ya rasu yanzu su biyu ne, muna murnar ta kammala babbar makaranta Malan yana cewa za'a sama mata wata makarantar tunda burinta ne ta karanci aikin lafiya sai gashi an lalata mata rayuwa, duk da bamu da k'arfi mun yanke shawarar tsaya mata tayi ilimi domin ta cika burinta, hatta da Yayanda iya karsa babbar makarantar sakandire, ganin bamu da hali yasa bece zai wuce ba haka ya fara sana'a, sai gashi yanzu Allah ya d'aukakashi, ganin haka yace dole Habiba tayi karatu zai tsaya mata, amma yanzu an cutar da ita.
Ra'eez yace insha Allahu sai burinta ya cika. Habiba ina so kisa jarumta aranki, kada kiyi kallon an ruguza maki rayuwa ki hakura da karatun ki, da izinin Allah sai kin d'aukaka, kisa aranki zakiyi karatu, domin shi kad'ai zakiyi kijawoma kanki daraja a wajen kowa, idan kika zama wata babu wanda zaifi karfin ki, amma idan kika sare ma rayuwa haka zakiyi ta cikin kunci, saboda ko aure zakiyi babu wanda zai d'auke ki da daraja, amma idan da ilimin ki zakiga yanda za'a daraja ki.
Kai Habiba ta jinjina tana share hawayen idonta. Jabeer yace duk yanda za'a maki tambaya a kotu kada ki bari a saki fad'in abinda ba shikenan ba, ki tsaya akan gaskiyar ki kuma kada kiji tsoro, koda Brr. Bajinta ya zo yace ki fad'i abinda zai tsara maki kada kice bazaki amince ba, ki bari sai anje kotu sai ki canza abinda ya fad'a ki fad'i abinda kika sani.
Baba yace mungode sosai Allah ya saka maku da alkhairi. Gaba d'aya sukace amin. Amsar lambar wayar Baba Ra'eez yayi yasa masa tashi yana fad'in zamu rik'a magana a waya kafin litinin ashiga kotun.
Baba yace nagode sosai. Tashi sukayi Baba ya rakosu sai godiya yake masu. Bayan ya koma gida Ra'eez yace wallahi duniya babu gaskiya, ka duba fa acikin shedun da Alhaji ya bani hada rahoton likitan daya duba Habiba, saboda shima d'an rashawa ne har ya canza abinda ya gani, amma ka barni dashi dole zai zo kotu zamuji komai, nima zan caza masa kai.
Jabeer yace ai duniya babu gaskiya, da likita, da 'Yan sanda da Lauyoyi dama ana samun azzalumai, domin kowa kud'i yake so, shiyasa duk inda suke kansu a had'e yake. Ra'eez yace Allah ya kyauta, bara na wuce sai gobe ko.
Jabeer yace gobe juma'a bazan fito da wuri ba. Ra'eez yace kaji d'an gayu, dan Allah kazo da wuri bazanji dad'i ba idan bakanan. Dariya Jabeer yayi yana fad'in shikenan Allah ya kaimu.
Wayar Ra'eez ce tayi k'ara, yana dubawa yaga Raheena ce, d'agawa yayi. Sallamarta yaji tana mai kwantar da murya, yana amsawa ta fara gaisheshi. Murmushi yayi ya amsa aranshi yana fad'in lallai su Raheena an fara canzawa.
Daga can Raheena tace kira nayi naji yanda ka tashi daga aiki. Ra'eez yace lafiya lau gani zan tafi gida ma. 'Dan zaro ido tayi tana fad'in biyar fa ta kusa amma baka koma gida ba? Ra'eez yace naje wani waje ne yanzu zan tafi.
Murmushi tayi tana fad'in bara na barka idan kaje mayi waya, ina fatan dai kaci abinci? Ra'eez yace idan naje zanci dai. Raheena tace shikenan kaci dani, amma yaushe zaka zo? Tab'e baki yayi yana fad'in wani aiki zanyi kuma yana buk'atar natsuwa, bazan samu hutu ba har sai na kammalashi.
Raheena tace shikenan amma dan Allah ka rik'a kirana hakan zai mun dad'i naga kiranka awayata. Ra'eez yace shikenan. Sallama sukayi ya kashe wayar.
Har zaisa aljihu wayar ta sake k'ara. Murmushi ya saki yana mai tsinke kiran domin ya kira. Sakin baki Jabeer yayi yana kallonshi.
Pretty na kinga na dad'e ko? Murmushi tayi tana fad'in damuwata rashin cin abincin ka gashi yamma tayi. Ra'eez yace ni kuma damuwata na wuni banji muryaki ba kuma banga fuskarki ba, amma gani nan yanzu zanzo amun kwalliya mai kyau, da nazo na ganki naci abinci sai mu tafi.
Murmushi tayi tana fad'in sai kazo, kayi tuk'i a hankali. Ra'eez yace angama Pretty na, ki kula da kanki. Dariya Jabeer yasa yana fad'in dama haka kake? Ra'eez yace namafi haka, ka zauna nan ayi babu kai, wallahi abokina soyayya dad'i gareta, gaskiya an barka abaya.
Jabeer yace abinda bangane ba shine, yaushe ka fara soyayyar? Ra'eez yace lokacin kana bacci. Dariya Jabeer yasa yana fad'in Allah da gaske nake, nasan dai kace mun kana son Rumaisa kuma nasan baka fad'a mata ba, amma kuma gashi kuna waya kamar wad'an da suka dad'e suna soyayya.
Ra'eez yace kasan duk soyayyar da aka tara, aka jik'ata ta tsimu ba'a sanin lokacin da ake fara ta, idan kuma aka fara ba'a mata bakunta, to haka tamu take, ajiya muka bayyanata gashi kuma har tabi mana jiki.
Jinjina kai Jabeer yayi yana fad'in lallai kam, soyayya tayi kam, sai nace Allah ya bada sa'a, ga Raheena kuma a gefe. Ra'eez yace ba ruwanka kasa ido kawai kayi kallo.
Jabeer yace hada jiki ma duk zansa, ina jiran ranar da zansha kallon da kyau. Ra'eez yace E naji. Murmushi Jabeer yayi yana fad'in soyayya ko wahala. Ra'eez yace ga wanda bai samu ba ko. Tab'e baki Jabeer yayi yana fad'in kaga Malan sai da safe. Ra'eez yace ai gara katafi ka tsareni da surutu Pretty na jirana.
Murmushi Jabeer yayi yana fad'in agaishe da Pretty to. Ra'eez yace wannan sunan ya fita abakin ka wallahi. Baki Jabeer ya kama yana fad'in yanzu kuwa. Dariya sukasa sukayi sallama kowa ya nufi gida.
****
Ganin yanda Rumaisa tayi kwalliya sai gyare-gyare takeyi yasa Mama ta koma d'aki tana mata dariya dan tasan Ra'eez yakusa dawowa. Abincinsa ta shirya a falo ta koma d'aki wajen Mama.
Zama tayi tana satar kallon Mamar. Murmushi Mama tayi tacigaba da linke kaya. Kallonta Rumaisa tayi tana fad'in wai Mama naji kinyi shiru sai murmushi kikeyi. Mama tace kuka kike son inyi? Turo baki Rumaisa tayi tana fad'in amma ai ba haka kikeyi ba.
Mama tace ya kike so nayi bayan kina ta shiri da alama bak'o zakiyi ban sani ba. Rufe fuska Rumaisa tayi tana murmushi tace ba wani bakon da zanyi kawai fa abincin Yaya ne na aje masa yace sauri yakeyi kada mu makara.
Mama tace naga alama ai, wannan kwalliyar ta zuwa unguwar ce ko? Tashi Rumaisa tayi tana kwalama Abdallah kira. Dariya Mama tayi tana fad'in kwayi ku gama.
Da gudu Abdallah ya shigo hannunsa d'auke da leda yana fad'in Aunty Yaya ya dawo kinga ya siyo mun kayan dad'i. Amshe ledar tayi tana fad'in kawo insha. Abdallah yace kai Aunty yace fa taki tana mota zai baki.
Rumaisa tace ya akayi ka sani? Abdallah yace daya bani nace masa ina taki shine yace ai taki ta dabance tana mota. Murmushi Rumaisa tayi ta d'auki alewa d'aya.
Muryar Ra'eez taji yana fad'in banda kwad'ai dai. Murmushi tayi tashige falo. Da sallama ya k'arasa shigowa. Mama ce ta fito tana amsawa. Har k'asa ya duk'a yana gaisheta.
Amsawa tayi tana masa sannu da aiki. Ra'eez yace kunjini shiru wallahi wani aiki aka bani ranar litinin ma zamu shiga kotu wata shari'a.
Mama tace aifa shari'a bata k'arewa, to Allah ya tabbatar da alkhairi kuma ya baka sa'a. Ra'eez yace amin. Hannun Abdallah taja tana fad'in kashiga kaci abincin mutafi ko. Sosa kai yayi ya kasa tashi. Murmushi tayi ta wuce d'aki, cike da kunya ya shiga falo. Rumaisa tana jin Mama ta shiga d'aki ta fito da sauri.
Tsayawa tayi a bakin k'ofa tana wasa da hannunta. Ido ya tsura mata yana murmushi, takowa tayi tashigo bakinta d'auke da sallama. Amsawa yayi yana fad'in bazaki dena wannan kunyar ba ko? Saurin zama tayi tana masa sannu da zuwa.
Ra'eez yace yunwa nakeji fa. Saurin bud'e abinci tayi ta fara zuba masa. Kallonta yake yana jin sanyi, sosai tayi masa kyau, tasa bak'ar jallabiya ta yane kanta da pink d'in mayafi fuskarta tasha kwalliya mai sauki.
Mik'a masa abincin tayi tana shirin tashi. Kallonta yayi yana fad'in ina zaki? Kanta ak'asa tace abinci zan barka kaci. Murmushi yayi yana fad'in aiko bazanci ba.
Zama tayi tana murmushi tace to kaci. Cokali ya d'auka yana fad'in damma bance ki bani ba. Saurin cusa kanta tayi a cinyoyinta tana murmushi. Murmushi shima yayi ya fara cin abinci yana mata fira.
Bayan ya gama ta kwashe kayan suka fito. Rufe gidan sukayi Madu na jiransu. Shida Ra'eez ne a gaba su kuma suka shiga baya. Suna tafiya Ra'eez yace wai Mama ina Aunty Hassana kullum ina so na tambayeki ita? Mama tace Allah sarki Sister Hassana sarkin kirki, ai sun dad'e da tashi, tunda aka canzama mijinta wajen aiki itama ta nemi canjin wajen aikinta suka tafi suna Abuja.
Ra'eez yace lallai kunyi nisa sai dai waya. Mama tace tana kirana muna gaisawa kuwa ai tana da kirki har cewa tayi zata zo ta d'auki Rumaisa taje mata hutu can.
A zabure Ra'eez yace ba dai Abuja ba wallahi, waye zai kaita haka kawai mayun garin nan su sa mata ido. Dariyar da Madu yayi ce ta ankarar dashi abinda yayi. Hannu yasa yana sosa kai.
Rumaisa kuwa duk'ewa tayi tana murmushi. Mama tace ni kuwa har na amince mata k'arshen wata zata zo su tafi. Kicin-kicin yayi da fuska yana kallon Rumaisa ta madubin motar, be sake magana ba kawai yayi shiru.
Murmushi Mama tayi tana kallonshi. Madu yace ai Halima baza'ayi haka ba, Ra'eez shine babba kuma shine namiji, dole sai ya amince zata je ko Ra'eez? Fuska a d'aure yace bazan amince ba ma, dan hadda zata fara babu inda zataje hutu.
Dariya Mama tayi, yanda yayi maganar kasan haushi ne yake cinsa. Madu yace angama Alhaji Ra'eez nima ban amince ba. Mama tace ai shikenan tunda kun fini k'arfi. Murmushi Ra'eez yayi yana shafa gefen fuskarshi.
Wajen Kawu suka fara zuwa dan kada magriba tayi. Zaune suke a cikin d'akin da ake ganawa da masu laifi. Bayan sun gama gaisawa da ma'aikacin wajen wanda dama sun saba da Ra'eez, shine ya aika akira Malan Sani.
Kallon Ra'eez yayi yana fad'in ya aiki kuma? Ra'eez yace aiki muntashi sai gobe kuma. Yace to Allah ya taimaka, bara na baku waje ku gaisa. Godiya Ra'eez yayi masa ya fita.
Tunda Malan Sani ya tunkaro wajen idanuwan Mama suka cika da kwallah, da gudu Abdallah yaje ya taroshi, duk ya tsufa saboda wahala, sai dai har yanzu jikinsa akwai jarumta, dan yasa dakiya aranshi hakan yasa zuciyarsa bata raunana ba bare ta shafi lafiyarsa.
Yana zuwa Ra'eez ya tashi yana gyara masa wajen da zai zauna. Zama yayi murmushi d'auke a fuskarshi. Hannu ya mik'ama Madu suka gaisa yana tambayarsa rayuwa.
Har k'asa Ra'eez da Rumaisa suka duk'a suka gaishe da Malan Sani. Kamosu yayi yana murmushi yace lafiya lau ina fatan ana kula da karatu Rumaisa? Kai ta jinjina tana b'oye hawayen da suka taho mata.
Kallon Mama yayi ganin ta kasa magana sai share hawaye. Wani abu ya had'iye yana fad'in Halima kuka dai, shiyasa fa bana so kina zuwa domin kina raunana mani zuciya, bayan kin tafi kuma ina jinyar zuciyata, ina tsoron kada hakan ya fara tab'a lafiyata, idan bazaki rik'a dakewa ba gara ki zauna agida sai murik'a gaisawa ta waya.
Hannu tasa ta goge idonta tana fad'in na dena, gaishesa ta farayi. Murmushi yayi yana fad'in lafiya lau ya gidan? Bazan tambayi komai ba domin nasan ina da masu kula da ku, sannan idanuwana sun ga abinda nake son gani, kuma naji dad'i a zuciyata.
Ra'eez yace Kawu Abbah yace idan nazo zaku gaisa bara na kirashi. Malan Sani yace Allah sarki ya iyalan nashi? Ra'eez yace lafiya lau. Waya ya d'auka ya kira Abbah.
Bayan sun gaisa ya mik'ama Malan Sani. Gaisawa sukayi yana tambayarsa rayuwa. Malan Sani yace lafiya lau Alhaji, ai rayuwar gidan yari tabi jikina, nasa araina nan d'in Muhallina ne, domin ina son naga ranar da Allah zai kawo mani k'arshen zama acikinta, ina son nayi wata rayuwar hakan yasa nasa juriya araina dan gudun damuwa ta kassarani.
Alhaji Mansur yace wannan haka yake, kuma naji dad'i sosai, dama abinda nake son na fad'a maka kenan, domin acikin satin nan bani da tunani sai na yanda zamu maido da shari'ar ku baya, domin kwanakin baya na had'u da tsohon ma'aikacin Alhaji Abubakar, dan yanzu a Kano yake aiki shima ya zama babba, Allah ne yasa zamu had'u har labari ya kawo muka zo maganar Alhaji Maiwada, ya tabbatar mani a yanzu baya tsoron kowa, kuma duk lokacin da muke buk'atar taimakonsa ashirye yake, abokinsa da aka canza ma wajen aiki Moses shi ya mutu a had'arin mota, amma yace shi zai zo ya bada sheda.
Jinjina kai Malan Sani yayi yana fad'in wallahi nima kwanan nan mafarkin da nake yawanyi kenan, wai an sake shari'a kuma munyi nasara, ina nan ina fad'ama Allah nasan kuma zai shige mana gaba, ko ban fita a nan ba matuk'ar asirin azzalumancen zai tonu burina ya gama cika.
Alhaji Mansur yace zaka fita, matuk'ar asirin su ya tonu dole a wanke ka, dan haka kacigaba da daurewa komai zai zo k'arshe. Malan Sani yace insha Allah. Sallama sukayi ya kashe wayar.
Sai da yaci abincin da suka kawo masa suna ta fira, bayan ya gama Ra'eez ya bashi ledar da suka kawo masa mai d'auke da kayan bukata, kud'i ya bashi yana fad'in zamuje wajen Ummu.
Godiya Malan Sani yayi masa yana fad'in agaisheta. Tashi sukayi kowa jikinsa a sanyaye, duk dauriya irin ta Malan Sani sai da kwalla ta cika masa ido, azuwansu sai yaji damuwarsa ta yaye, yanaji kamar a gida suke zaune, amma yanzu da zasu tafi sai yaji duk babu dad'i.
Mama kuwa saurin fita tayi tana kuka, bayanta Rumaisa tabi itama kukan takeyi, kama Abdallah Madu yayi sukayi hanyar fita shima jikinsa a sanyaye. Kallon Malan Sani Abdallah yayi yana fad'in Baba sai yaushe zakazo gidan mu? Saurin juya baya Malan Sani yayi hawayen da yake b'oyewa suka zubo masa, yana jin muryar Abdallah amma ya kasa magana, ganin haka yasa Madu yayi saurin jansa sukayi waje.
Hannu Ra'eez yasa ya goge idonshi kafin ya dafa Malan Sani yana fad'in Kawu zamu tafi sai mun sake dawowa. Ajiyar zuciya ya saki yana fad'in Ra'eez kada ka sake kawo su, idan zaka zo kazo kai kad'ai dan Allah.
Jinjina kai Ra'eez yayi yana fad'in insha Allah. Tare suka fito suka k'arasa wajen ma'aikacin. Kallonsu yayi cike da tausayi yana fad'in zaku koma? Ra'eez yace magriba ta kusa, mungode sosai.
Hannu yasa ya ciro kud'i ya mik'a masa yana sake masa godiya. Amsa yayi yana fad'i ai babu komai nima nagode. Sallama yayi masu Malan Sani ya d'auki kayanshi ko juyowa beyi ba yayi gaba yana kuka.
A mota gaba d'ayansu shiru sukayi kowa yana jimami, Abdallah kanshi da yake yaro shiru yayi ya kwanta jikin Rumaisa yana goge mata fuskarta, har suka isa asibiti babu mai magana.
Sai da Ra'eez yayi ma Dr. Sadeek waya, dan yanzu ya zama babba baya aiki a asibiti sai dai sune masu kula da wajen, hakan yasa ya damk'a Ummu a hannun babban likitan da yake wajen duk da idan yashigo yana kawo mata ziyara.
Bayan sun gama wayar suka fito suka nufi d'akin da Ummu take. A zaune suka isketa tana sanye da hijabi ta kurama tv ido wadda ake shirin addu'ar safe da marece, wata dattijuwa ce zaune a gefe da alama itace take kula da ita.
Idan kaga Ummu sai ka d'auka mai hankali ce, domin komai fess a jikinta, fuskarta ta nuna alamun manyanta kad'an saboda tana samun kulawa ga cima mai kyau sai fatar ta tayi kyau sosai, sam yanzu bata komai sai dai wani lokacin idan ta fara kuka tana kiran Abbun Ra'eez sai ta kai wani lokaci ta nayi, wani lokacin dole sai anyi mata allurar bacci kafin suke samun saukinta.
Wani lokacin kuma sai tayi sati bata nuna alamun hauka ba, magana ma batayi sai dai mai kula da ita ta rik'a kula da abinda take so tayi mata, dan yanzu kam ta zama shiru-shiru, idanuwanta duk sun canza kala sun rage girma saboda kuka.
Da sallama suka shiga d'akin, matar da take zaune tayi saurin amsawa ta mik'e tana masu sannu da zuwa. Har suka shigo Ummu bata kalli inda suke ba, yanda kasan bata cikin d'akin dan yau 'yan miskilancin take.
Bayan sun gaisa da matar ta basu waje tayi waje. Ido Ra'eez ya tsura ma Ummu kwalla tana cikowa a idonshi, kusa da ita ya matsa yana mai kamo hannunta.
Shiru tayi bata kulashi ba. Zama yayi ya jawota hawaye suna gangarowa a fuskarshi. Mama dasu Rumaisa duk sai sukaji wani sabon kuka, a hankali Ra'eez yace Ummu kiyi hak'uri aiki ne yamun yawa shiyasa banzo ba amma bazan sake ba.
Tamkar bada ita yayi magana ba haka ta kyaleshi idanuwanta suna kan Tv tamkar mai fahimtar abinda akeyi. Matsowa Mama tayi ta kamo Ra'eez tana fad'in kayi shiru mu bata lokaci zatayi magana idan ka tursasata kanta zai iya d'aukar zafi.
Zama sukayi kowa da abinda yake tunani, Ra'eez kam yana rik'e da hannun Ummu yaki sakinta. Can yayi saurin kallonta yana fad'in Ummu jiya fa nayi mafarkin Abbu ina kwance a kan gadonshi har... Zumbur tayi tana kallonshi, kamoshi tayi tana fad'in Abbun ka? Nima jiya yazo mun anan ma ya kwana, hannu tasa tana buga gadon da take zaune.
Murmushi sukayi dukansu, Ra'eez yace Ummu meyasa baki tsaidashi har nazo ba? Dariya tayi tana tafa hannu tace ai yau idan yazo igiya zansa na d'aureshi, jiya nace ya zauna tare dani shine yamun wayau ya gudu, amma ka barshi yau sai na d'aureshi kaga bazai sake barina ba ko.
Murmushi Ra'eez yayi ya gyara zama tare da d'ora kanshi saman cinyarta yana fad'in sosai ma Ummu, zan kawo maki igiya ki d'aure manashi kullum murik'a ganinshi.
Nan fa Ummu ta saki jiki da Ra'eez sukayi ta firar Abbu, haka ya biye mata yana taya ta shirme duk dan suyi labari, Mama da Madu kuka kawai sukeyi a b'oye ganin yanda Uwa da 'Danta suke fira ta marasa hankali.
Cikin firar sai dai Ra'eez yasa hannu ya goge hawayen da suke zubo masa saboda firar tana sakashi shiga cikin yanayi, ita ko Ummu dariya kawai takeyi suna firar Abbu.
Da haka Mama ta zuba mata abinci, amsa Ra'eez yayi suna fira yana bata abaki, itama haka tarik'a bashi, duk da akoshe yake haka yake amsa yanaci yana hawaye.
Bayan sun gama tacigaba da bashi labarin shirmenta. Har akayi sallah suka fita shida Madu da kyar ma ta yarda suka tafi. Bayan sun dawo ta jawo Ra'eez tana fad'in kaima yau anan zaka kwana idan Abbunka yazo sai muyi fira muci abinci gaba d'aya.
Murmushi Ra'eez yayi ya haye saman gadon yana fad'in tabbas anan zan kwana Ummu muga Abbu atare. Wayarsa ce tayi k'ara, yana dubawa yaga Alhaji Barau ne, tsaki yayi kafin ya d'auka.
Bayan sun gaisa ya fad'a masa idan anyi sallar isha'i yana nemansa muhummiyar magana ce. Ra'eez yace shikenan sai nazo, kashe wayar yayi yana tsaki.
Mama ce ta tambayeshi wanda ya kira? 'Bata fuska yayi yana fad'in Alhaji Barau ne wai yana... K'arar da Ummu tasa ne yasashi saurin yin shiru. Kular abincin da take kusa da ita tayi wurgi da ita tana fad'in sai na kashe shi, wallahi sai na kashe shi, Abbunka baya sonshi, ya takura ma Abbunka.
Saurin tashi Ra'eez yayi yana kok'arin rik'eta amma ya kasa, da sauri Madu ya fita domin kiran ma'aikatan, kafin suzo duk ta hargitse wajen tana ihu, hannun Ra'eez kuwa duk taji masa ciwo.
Allura akayi mata cikin mintuna biyu bacci ya d'auketa. Zama Ra'eez yayi tare da sakin wani irin kuka mai cin rai. Kamoshi Madu yayi yana lallashinsa.
Tashi Mama tayi tana fad'in mutafi tunda ta samu bacci, Ra'eez kada ka sake yin maganar wad'an nan azzaluman agabanta, nima mantawa nayi har na tambayeka.
Kai ya d'aga ya tashi yana mai sake kallon Ummunsa, sosai ya k'ara jin kiyayyar su Alhaji Barau. Haka yayi ma ma'aikatan alkhairi da wannan matar kafin suka tafi, a waya ya fad'ama Dr. Saddek halin da take ciki.
Dr.. Sadeek yace insha Allahu Ummunka ta kusa samun sauki, tunda har take jin haushin mutanan da take zargi tabbas alamun sauki sun fara bayyana, gobe zan shiga dan a d'auki hoton kwakwalwarta.
Godiya Ra'eez yayi mashi ya kashe wayar. Mama tace idan ka ajemu sai kaje kaji kiran da yake maka. Ra'eez yace bazanje ba sai dai mu had'u a ofis gobe. Mama tace a'a, idan bakaje ba zaiyi tunanin wani abu.
A fusace Ra'eez yace wallahi bazanje ba, saboda sunanshi kad'ai komai na Ummu ya hargitse, muna firar mu daga jin sunanshi komai ya tsaya, idan naje wallahi zan iya yin wani abu da zaisa na b'ata masa.
Jinjina kai Mama tayi tace shikenan ka fad'a masa wani uzuri to. Kai ya d'aga yana goge idonshi.
Bayan ya ajesu Mama tace yashigo yaci abincin dare. Ra'eez yace akoshe nake ai munci a asibiti gida zan tafi kaina yana mun ciwo. Mama tace idan kaje kasha magani, kuma bana so kasa wata damuwa aranka wani ciwon ya shige ka. Kai ya d'aga yana masu sai da safe.
Har yashiga mota Rumaisa ta fito, jiki a sanyaye ta k'arasa bakin motar. Idanuwa ya tsura mata ganin yanda take kuka. Fitowa yayi ya hard'e hannuwansa a kirji yana kallonta.
Kasa magana tayi sai kawai ta juya, da sauri ya kamo hannunta ya maidota baya, sakinta yayi kafin yace ta goge fuskarta.
Hannu tasa tana goge fuskarta wasu hawayen suna zubowa. Murmushin k'arfin hali yayi yana fad'in kina so na kasa bacci ne? Kai ta girgiza.
Ra'eez yace to bana son kukan ki, idan naje gida zan kiraki kimun fira mai dad'i da zata sakani bacci kinji? Kai ta d'aga tana murmushi.
Ra'eez yace da kyau Pretty nah, yanzu kishiga gida sai na kiraki, kuma kici abinci kinji? Kai tazo d'agawa yayi saurin fad'in magana zaki mun Malama.
Dariya tasa tana rufe fuskarta. Shima murmushi yayi yana jin sauki a zuciyarsa. Kallon shi tayi tana fad'in kayi tuki a hankali Yaya. Murmushi yayi yashige mota yana fad'in zanyi amma sai kince kina sona idan ba haka ba a 180 zanje gida.
Zaro ido tayi tana fad'in kai Yaya. Gira ya d'aga mata yana fad'in sosai kuwa. Murmushi tayi tace to ka rufe idonka zan fad'a. Ra'eez yace Allah beyini makaho ba kuma bazan rufe ba, idan bazaki fad'a mun ba zanje na saurari na wasu Mat... I love you!
Kafin ya kallota sai kurar gudunta ya iske tayi cikin gida. Besan lokacin daya saki wata dariya ba. Baki ya rik'e yana fad'in lallai ma Pretty, anya itace ma tayi maganar? Lumshe ido yayi yana mai-maita abinda ta fad'a.
Rufe motar yayi ya nufi gida, shi kad'ai sai murmushi yake saki, a hankali ya furta lallai soyayya tana da dad'i, kuma tana taimako sosai, kafin minti goma zuciyata zafi take ina cikin damuwa, amma cikin mintuna biyar na samu canji. Allah nagode maka da ka saka soyayya a zukatan mu.
K'aran wayarsa ce ta katse mashi abinda yakeyi, saurin d'auka yayi yana fad'in Abbah ina hanyar gida dana k'arasa zan kira ka. Abbah yace shikenan amma ka kirani fa. Kashe wayar yayi.
K'ara gudun motar yayi dan yasan tunda Abbah yace zeyi magana dashi to ba k'aramun abu bane, yaso ma tun d'azu ya kirashi a ofis to yasan Abbah baya son magana a waje shiyasa bai kirashi ba.
Ur's.
Nabeelert Lady🖋[3/10, 8:39 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud'i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k'asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub'e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.*
2⃣7⃣
Cikin sauri ya kammala abubuwan da ya saba kafin ya kwanta, kallon agogo yayi yaga k'arfe 8:30, wayarsa ya jawo yayi kiran Abbah kirjinsa yana bugawa, tun lokacin da yaji yana son magana dashi yake jin fad'uwar gaba.
Bayan sun gaisa Alhaji Mansur yace Ra'eez ya Ummun taka da jiki? Ra'eez yace da sauki sosai Abbah, sai dai sunan Alhaji Barau da Mama ta ambata agabanta ya jefata cikin tashin hankali har sai da akayi mata allurar bacci kafin aka samu kanta.
Jinjina kai Abbah yayi yana fad'in da alamu sauki ya fara zuwa. Ra'eez yace haka Dr. Saddek ma ya fad'a, yace zai shigo asibitin gobe domin suyi mata awo.
Abbah yace to Allah yasa muji alkhairi. Ra'eez yace amin Abbah. Gyaran murya Abbah yayi yana fad'in Ra'eez ya kamata a birkito da abinda ya faru shekaru 11 da suka wuce.
Ajiyar zuciya Ra'eez ya saki jin abinda Abbah ya fad'a. Ya naji kayi shiru Ra'eez? Abbah ya fad'a jiki a sanyaye. Murmushin yake Ra'eez yayi yana fad'in bakomai Abbah, kawai maganar ce naji tazo mun daga sama.
Abbah yace ya kamata kasa wannan maganar aranka, ka tuna akowane lokaci zamu iya maidota domin bazamu tab'a barin jinin Alhaji ya tafi abanza ba, idan kaga haka ta faru to bamu da cikakkar hujjar da zamu gabatar ma kotu.
Ra'eez yace nima wannan abun yana damuna Abbah, wani lokacin ina ganin kamar bamu da shedar da zamu iya mik'a su Alhaji Barau kotu, duk wata hujja sune suke da ita, koda kotun duniya zamu kaisu sune zasuyi nasara akan mu.
Abbah yace kada kayi saurin sarewa Ra'eez, mai gaskiya Allah baya tab'ar dashi, ko alhakin Malan Sani ya isa yasa a wannan karon muyi nasara, domin zalunci baya d'orewa.
Jinjina kai Ra'eez yayi yana fad'in insha Allahu muna kammala shari'ar da zamuyi ranar litinin zan fara shirya yanda tamu zata kasance, zanje na lalubo kundin shari'ar su Abbu domin na fara dubashi.
Abbah yace haka nake son ji Ra'eez, ai fad'uwar gaba asarar namiji, kasa aranka zamuyi nasara. Murmushi Ra'eez yayi yana fad'in insha Allahu Abbah.
Abbah yace sai kuma maganar waccan motar da take ajiye a gareji, badan kace kana sonta ba da ansayar da ita da ayita ajiyarta bata komai.
Ra'eez yace dan Allah Abbah abarta, inaso idan nazo Kano na kaita ayi mata seti dan ita nake son nacigaba da hawa. Murmushi Abbah yayi yana fad'in haba Ra'eez, ai zamaninta yawuce, idan aka ga kana hawanta sai arik'a maka kallon matsolo.
Dariya Ra'eez yasa yana fad'in Allah Abbah sai na hauta kona 'yan watanni ne, tun lokacin da Abbu ya siyeta nake cewa idan na girma zai koya mani ita, kuma yace zai ajeta har na girma a cikinta zai fara koya mani mota, kaga tunda ban fara koyo acikinta ba ai gara na hauta.
Abbah yace wannan haka yake, bakomai duk lokacin da kazo sai ka kaita a dubata, amma maganar shari'ar da zakuyi ina fatan babu wata matsala? Ra'eez yace akwai Abbah, amma insha Allahu komai zaizo da sauki, idan muka kammala zan baka labari. Abbah yace shikenan Allah ya bada sa'a. Ra'eez yace amin. Sallama yayi mashi ya kashe wayar.
Kwanciya yayi yana kallon saman d'akin, tunanin ta yanda zai nemo kundin shari'arsu Abbu kawai yakeyi, dole ya k'ulla alak'a da ma'aikacin d'akin ajiyar kundi.
K'arar wayarsa ce ta maido dashi daga tunanin da yakeyi. Raheena ya gani, d'an tsaki yayi kafin ya d'auki wayar.
Sallama tayi masa, bayan ya amsa ta gaishe shi tana tambayarsa gajiyar aiki. Ra'eez yace lafiya lau. Raheena tace d'azu Dady yake fad'amun zaka zo ina ta murna sai kuma yace wai wani uzuri ya hana ka zuwa duk banji dad'i ba ko abinci kasa ci nayi, ta fad'a cike da shagwab'a.
Murmushi yayi jin abinda ta fad'a. Raheena tace Allah baka san irin son da nake maka bane, saboda kai duk wasu abubuwa da nakeyi marasa kyau na dena, yanzu tsakanina da masu mana aiki sai alkhairi da girmamawa, abinci kuwa tuni na fara iyawa duk saboda kai.
Ra'eez yace haka akeso ai, kinga har abada bazaki tab'a mantawa dani ba, domin ta sila ta kin samu rayuwa mai kyau.
Murmushi tayi tana fad'in sosai kuwa, kaga nima zan zamo Uwa ta gari, zan kula da yaran mu wad'an da zamu haifa. Dariya Ra'eez yasa wacce besan da zuwanta ba.
Raheena tace kadena dariya nasan auren mu bazai ja lokaci ba, dan Momy da Dady duk sun san da maganar, kai kawai nake jira ka amince dani kuma nasan zaka amince tunda gashi kana kula ni.
Zeyi magana kiran Rumaisa yashigo wayarsa, dafe kai yayi aranshi yana fad'in ga sarkin kishi nan, amma bari ya gwada ta, sharewa yayi suka cigaba da magana.
Rumaisa kuwa ganin call waiting yasa taji ranta ya b'aci, sake gwadawa tayi amma yana waya, haka tayi ta kiranshi kusan mintuna ashirin begama wayar ba, haushi ne ya isheta tayi wurgi da wayar ta kwanta.
Hankalin Ra'eez gaba d'aya yana wajen Rumaisa, duk da yayi hakan ne dan ya tsokaneta amma sai yaji babu dad'i. Raheena kuwa sai zuba masa surutu takeyi, ganin yanda yake amsawa yasa tace Dear da alamu bacci kakeji.
Ra'eez yace gaskiya kam. Raheena tace shikenan bara na barka bana so na takura maka, ina fatan zakayi bacci mai dad'i. Ra'eez yace sosai kuwa. Raheena tace Dear bazaka ce naci abinci ba? Ya kamata ka lallasheni ko abu marar nauyi ne naci.
Murmushi Ra'eez yayi yana fad'in to kisha tea da biscuit kafin ki kwanta. Murmushi ta saki tana fad'in yanzu kuwa my one. Sallama yayi mata ya kashe wayar.
Latso lambar Rumaisa yayi, har ta gama k'ara ba'a d'auka ba. Murmushi yayi ya sake kira amma bata d'aga ba. Sai da ya kira so biyar bata d'aga ba. Sako ya tura mata kafin ya aje wayar yana murmushi.
Rumaisa tana kwance ta gama jin wayarta na k'ara amma taki d'agawa wai tayi fushi. Jin alamun sako yasa tayi saurin jawo wayar.
*Tunda baki son jin muryata bara na nemo wadda zata taya ni fira kafin nayi bacci.*
Saurin tashi tayi tana kok'arin kiranshi. Murmushi ya saki a lokacin da yaga kiranta. Kashewa yayi kafin ya kirata.
Tana d'agawa ta fara masa rigima. Dariya yasa yana fad'in ashe dai ana sona? Turo baki tayi tana fad'in Allah Yaya wata rana zakasa zuciyata ta buga.
Ido ya zaro kamar tana ganinsa yace rufa mun asiri, idan zuciyarki ta buga nayi rayuwa da wa kuma? Da wacce kuke waya ka share ni mana.
Dariya yayi yana fad'in nikam naji dad'i domin an nuna ana kishina yau. Rumaisa tace Yaya... Kinga ni bana son wannan Yayan, ga sunaye nan masu dad'i kinemo kisa mun.
Murmushi tayi mai sauti tana fad'in ai bansan su ba. Ra'eez yace shikenan zancigaba da sauraran wacce take kirana da sunaye masu dad'i. Da sauri Rumaisa tace kayi hak'uri *Deel*.
Saurin kallon wayar yayi yana sakin murmushi, zeyi magana ta kashe wayar. Kwanciya tayi ta rufe fuskarta tana murmushi.
Sake kira yayi amma yaji akashe. Murmushi ya saki yana rungume filo, juyi yayi yana jin wani irin sanyi aranshi, tabbas soyayyar Rumaisa tayi nisa aranshi, baya jin zai iya rayuwa ba tare da ita ba, fatanshi a kammala wannan shari'ar ayi maganar aurensu. Haka yayi ta tunani har bacci ya d'aukeshi.
***
A gurguje ya shirya, koda yaje gidansu Rumaisa da kyar yasha tea ya tafi ko had'uwa da Rumaisa basuyi ba dan tunda safe Alhaji Barau yayi masa waya akan maganar jiya hakan yasa yake ta sauri.
***
Zaune yake a ofis d'in Alhaji Barau, mamaki yake ganin yau yashigo da wuri ko dan yau juma'a yasa yazo? Bayan sun gama gaisawa Alhaji Barau yace ai tun jiya naso kazo dan dai kace kana da uzuri.
Dama akan maganar wannan shari'ar ce da aka baka, maganar gaskiya Ra'eez wannan yaron da zaka kare Yaron abokin kasuwancin mu ne, babban aminin Alhaji Marusa ne, kasan yanda talakwa suke idan suna jin haushin mutum, wannan yarinya 'yan unguwarsu ma sun bata shedar bata da hali mai kyau, amma koma menene ina so ka duba shedun da aka baka da kyau, bana so ashiga kotu a samu matsala, domin wannan kotun kowa yasan yanda take da adalci bazan so ace a wannan karon dana zab'eka ace an samu matsala.
Gyara zama Ra'eez yayi yana fad'in insha Allahu Alhaji bazan kasance mai samar da rashin adalci a kotun ka ba, kamar yanda kowa yasan wannan kotu da adalci ina mai tabbatar maka zan tsaya tsayin daka domin a tabbatar da gaskiya a wannan shari'a.
Murmushi Alhaji Barau yayi yana fad'in nasan bazaka bani kunya ba, nagode sosai, zaka iya tafiya. Tashi yayi, har ya kai bakin kofa yaji muryar Alhaji Barau yana fad'in Raheena tace na gaishe ka.
Murmushi kawai Ra'eez yayi ya d'aga kai kafin ya fice. 'Yar dariya ya saki jin wani rashin kai a wajen Alhaji Barau, wai Uba ne yake bada irin wannan sakon. Tsaki kawai yayi yawuce. Kallon mutumin da suka taho tare da Brr. Bajinta yayi, kauda kai yayi yawuce dan ya gane Mr. Kallah tun wancan zuwan da suka had'u.
Bayan sun gaisa da Alhaji Barau Mr. Kallah ya kalli Brr. Bajinta yana fad'in d'an bamu waje zamuyi magana. Gimtse fuska Brr. Bajinta yayi dan beji dad'in abinda yayi masa ba.
Kallonshi Alhaji Barau yayi yana fad'in kaje kawai. Kai ya jinjina kafin ya fice fuska a d'aure.
Gyara zama Mr. Kallah yayi yana fad'in ka ganni da sammako ko? Murmushi Alhaji Barau yayi yana fad'in mamakin da nakeyi kenan, gashi baka kira kace zaka zo ba.
Mr. Kallah yace wani abu ne ya bani haushi siyasa na taso dan nasan baka da masaniyar abun. Alhaji Barau yace menene kuma ya faru? Mr. Kallah yace mutumin ka mana Alhaji Marusa.
Cire glass Alhaji Barau yayi yana fad'in wani abun yayi ko? Tab'e baki Mr. Kallah yayi yana fad'in ai nasha fad'a maka Alhaji Marusa beda gwani, tunda ya iya yakice 'yan uwansa nasan cewar kowama zai iya yakicewa.
Alhaji Barau yace dan Allah ka bani labari duk kasa kaina ya fara caji. Gyara zama Mr. Kllah yayi yana fad'in ajiya cikin dare ina duba Email d'ina sai ga sako yashigo mani daga *Mark* yana fad'a mani maganar da Alhaji Marusa yayi masa akan wannan kasuwancin da mukace zamu bud'e na shigo da manyan kayan zamani da Mark ya gano mana, kasan harkar akwai k'aruwa sosai, dan matuk'ar muka dace mun gama zama masu kud'i a duniya, kai ina tabbatar maka wannan aikin dole ka ajeshi dan zaman garin nan ma began mu ba.
Jinjina kai Alhaji Barau yayi yana fad'in ina jinka.
Mr. Kallah yace ashe Alhaji Marusa ya zagaye ya fad'ama Mark shi kad'ai zai sayi kayan saboda shine ya dad'e a harkar kasuwaci daga baya ya jawo mu, ya kyale mu zai yaga mana wani abu idan komai yayi dai-dai, to ahaka suka tsaya, kasan Mark beda munafurci, shine ya turo mani da sako jiya cikin dare yake fad'a mani yayi mamaki da abinda Alhaji Marusa ya fad'a saboda yasan yanda muka aminta da juna, shi kuma baya iya munafurci dan baya so yaga ta silarshi ya raba abokai, hakan yasa ya fad'a mani domin muje mu sasanta kan mu.
Dariya Alhaji Barau yasa yana buga tebur. Mr. Kallah yace indai Alhaji Marusa ne kuka ma sai ya saka. Tashi Alhaji Barau yayi yana fad'in wallahi k'aryarsa tasha karya, idan yana tak'ama da jinin fulani ajikinsa zan nuna masa irin namu cin duduniyar, ka barni dashi, cikin ruwan sanyi zan nuna masa rashin wayonsa.
Zama yayi yana fad'in kai baka tab'a tunanin dalilin da yasa na rabashi da gidanshi na Surelere ba? Duk da gidan ya kasance da zalunci aka amshe shi amma dai ya biya kud'in gidan, domin nasan da Iyalan Alhaji Maiwada suna nan har abada bazasu manta da wannan gidan ba.
Tun lokacin da wannan gidan ya zama mallakinsa na kudira araina sai na rabashi dashi, hakan yasa cikin ruwan sanyi da muka fara gabatar da kasuwanci atare lokacin da muka samu kaya masu kyau bayan an raba ya nuna yana son wasu daga cikin nawa na barmasa babu ja, da wannan na yaudareshi har ya siyar mani da gidan akan kud'i kalilan gashi yanzu ina rayuwata aciki nida iyalina hankali kwance.
Dariya Mr. Kallah yasa yana fad'in baka da kyau Alhaji Barau, ai tun alokacin na cika da mamakin yanda akayi ya siyar maka da gidan a wannan kud'i, ashe dai ka nuna masa kafishi sanin kan duniya.
Alhaji Barau yace ai karatun lauya ba k'arya bane, cud'anya da mutanen da nayi betashi abanza ba tunda gashi yayi mani amfani. Jinjina kai Mr. Kallah yayi yana fad'in a wannan karon ma baza muyi sanya ba, bana so abotar mu ta tab'u amma kada ka bari yasan munsan komai.
Alhaji Barau yace sa ido kayi kallo kai dai. Dariya sukasa suka cigaba da tattaunawa.
****
Bayan sun fita sallah Ra'eez be jira Jabeer ba ya sulale yaje ya dubo Ummunsa, sosai yaji dad'in ganinta dan jikinta da sauki, sai dai be samu ganin Dr. Saddek ba saboda yana sauri, hakan yasa yawuce.
Lokacin daya koma duk yanda Jabeer yaso yaji inda yaje be fada masa ba yace kawai Mama ce tayi masa kiran gaggawa hakan yasa ya yarda.
Bayan sun tashi daga aiki Ra'eez yace Jabeer ya masa rakiya zuwa gidan su Yaron da zai tsaya mawa. Jabeer yace kamar kasan abinda yake raina kenan, gara muje domin kaji ta bakinsa. Ra'eez yace haka ne, sai dai bana so kowa yasan naje wajenshi.
Jabeer yace muje akwai abinda zan fad'a masa wanda zai hanashi fad'ama kowa. Mota suka shiga suka tafi.
Ur's.
Nabeelert Lady🖋
[3/10, 8:39 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud'i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k'asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub'e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.*
2⃣8⃣
Sun dad'e a tsaye jikin mota suna jiran su samu wanda yasan Yaron da suka zo wajenshi. Kallon Jabeer Ra'eez yayi yana fad'in kaga na manta sunan yaron da Baba ya fad'a mana rannan.
Jabeer yace anya ya fad'a mana sunansa kuwa? Gaskiya bana jin ya fad'i sunanshi. Waya Ra'eez ya ciro yana fad'in bara na tambayeshi gara musan sunanshi bana so asan wajenshi muka zo.
Bugu d'aya Baba ya d'auka, bayan sun gaisa Ra'eez ya tambayeshi sunan Yaron? Bab yace sunanshi *Sameer* gidansu shine na biyu akan layinsu yana nan mai bakin gate.
Ra'eez yace shikenan sai munyi waya. Kashewa yayi yana kallon gidan da suke fuskanta. Jabeer yace meye sunansa? Sameer! Ra'eez ya fad'a yana mayar da wayarsa aljihu.
Wani matashi ne yazo wucewa, da sauri Ra'eez yayi masa sallama, bayan sun gaisa yake tambayarsa ko yasan Sameer da yake wancan gidan? Murmushi Matashin yayi yana fad'in *B-Boys* zaka ce.
Jinjina kai Ra'eez yayi yana fad'in shi nake nufi. Matashin yace yanzu zaka ganshi ya dawo dan lokacin zuwanshi bitch yayi. Jabeer yace lallai babban yaro ne. Matashin yace idan B-Boys ne ai beda wasa akwai son harka da jin dad'i.
Ra'eez yace mungode. Sallama yayi masu yawuce. Jabeer yace da ka sallameshi taya zamu iya ganeshi bayan bamu tab'a ganinshi ba? Murmushi Ra'eez yayi yana fad'in sa ido kawai kayi kallo, mu k'arasa k'ofar gidansu zamufi saurin cimmasa.
Basu dad'e a wajen ba sai ga wata rantsatstsiyar mota mai bakin glass ta shigo layin, tun kafin ya iso sauti yake tashi, ganin mutane a bakin gate kuma Matasa ya hana Sameer yin horn, amma a k'aidarsa yana doso gidansu yake horn, kafin ya iso an bud'e gate sai dai kawai ya shige.
Sautin motar ya rage kafin yaja burki ya sauke glass d'in motar. Hannu yasa ya cire bakin glass da yake idonshi yana bin su Ra'eez da kallo, ko ba'a fad'a masa ba yasan wad'an nan matasan masu ji da kansu ne, domin su duka kyawawa ne, shigar jikinsu abun kallo ce domin dogayen kaya sukasa kasancewar yau juma'a.
Saurin matsawa Ra'eez yayi fuskarshi d'auke da murmushi ya mik'a mashi hannu yana fad'in barka da zuwa Sameer. Jiki a sanyaye Sameer ya bashi hannu suka gaisa.
Ra'eez yace idan bazaka damu ba inaso ka juya kan motarka zuwa inda tamu take akwai maganar da nake so muyi. Kallon rashin fahimta Sameer yayi masa.
Murmushi Ra'eez yayi yana fad'in kada ka damu, sunana Brr. Ra'eez, nine wanda zan kareka a kotu ranar litinin. Jinjina kai Sameer yayi yana fad'in am sorry ban ganeka ba, muje.
Zaune suke a cikin motar Sameer sun zuge glass ta yanda baza'a gansu ba. Kallon Sameer Ra'eez yayi yana fad'in duk da an bani duk wata sheda dazan kareka nafi son nazo wajenka naji da bakin ka hakan zaisa nasan yanda zanyi na kare ka da kyau.
Jiki a sanyaye Sameer ya kalli Ra'eez yana fad'in wallahi Halima sharri take mun fa. Ra'eez yace kasanta kenan? Girgiza kai yayi da sauri yana fad'in haka naji wasu suna kiranta anan nasan sunanta.
Jabeer yace anan unguwar take ne? Sameer yace nifa bansan gidan su ba, kawai tana sona nayi mata wulakanci shine tace sai tasa an d'aure ni, bayan kwana biyu har na manta sai ga mahaifinta yazo wai nayima d'iyarsa fyad'e, ni mema zanyi da wannan k'azamar nida nake harka da.... Saurin had'iye abinda zai fad'a yayi.
Ra'eez yace dama kana harka da wasu matan ne? Saurin girgiza kai yayi yana fad'in nifa ko lafiyar kirki banda ita hakan ne ma yasa banyi aure ba amma har k'anina yayi aure.
Ra'eez yace ashsha, to Allah ya kyauta, shikenan zamu wuce, amma bana so kowa yasan nazo wajen ka idan ba haka ba shirin mu zai rushe.
Jabeer yace kana fad'ama Mahaifinka lauyen ka yazo shikenan hankalinsa zai tashi zaiyi tunanin ka fad'i wata magana. Cike da gamsuwa Sameer yace babu wanda zan fad'amawa dan Allah kada ka bari a rufe ni.
Ra'eez yace kada ka damu kotun mu wajen adalci ne. Jinjina kai Sameer yayi yana fad'in nagode. Sallama sukayi suka fita zuwa motarsu.
Kallon Ra'eez Jabeer yayi yana fad'in meka fahimta agame dashi? Beda gaskiya kawai, Ra'eez ya fad'a. Dariya Jabeer yayi yana fad'in kaifa lauyensa ne ya zaka fad'i haka? Murmushi Ra'eez yayi yana fad'in su lauya manya, ai kasan Allah baza suyi nasara ba. Jabeer yace sai ka kula fa, bana so su Alhaji Barau su san cewar da gangan ka kadasu. Ra'eez yace kai dai kasa ido zakasha kallo, cikin week end d'in nan zan gama komai.
Jabeer yace Allah ya bada sa'a. Hannu Ra'eez ya bashi yana fad'in sai litinin ko? Jabeer yace haba dai, bazaka shigo ba? Ra'eez yace sai dai wani satin, dan wannan satin bazan fita ba inaso na shiryama wannan shari'ar. Jabeer yace shikenan, nima zan kwanta na huta sai munyi waya.
Sallama sukayi kowa ya nufi motarsa zuwa gida.
****
Wai Raheena har yanzu Ra'eez bece komai ba? Kallon Momy tayi tana fad'in yace mana, uhm! Wallahi Momy D, ya iya soyayya, bakiga yanda yake sona ba, damma suna da shari'a ranar litinin da wannan week end d'in tare zamu yishi anan gidan.
Murmushi Momy tayi tana fad'in amma naji dad'i sosai, shiyasa jiya nayi magana da Dadynki akan shirin bikin ki, waje nake so muje a had'o komai.
Rungume Momy tayi tana fad'in gaskiya naji dad'i, bakiga yanda k'awayena suke santinshi ba, rannan dana d'ora wani hotonshi dana had'a da nawa bakiga yanda mukayi kyau ba kamar atare muka d'auka, wasu sai cewa suke nayi dace.
Momy tace zauna nan su rufe ki da dad'in baki wata ta kwace maki shi. Zaro ido tayi tana fad'in haba dai Momy, ai Ra'eez nawa ne ni kad'ai, idan ban sameshi ba Allah kad'ai yasan halin da.... Saurin rufe mata baki tayi tana fad'in ko da zan rasa komai sai kin aureshi, dan haka ki kwantar da hankalin ki, kisa aranki anyi auren ku, dan yanda na fara fad'ama k'awayena an kusa aurenki bazan bari naji kunya ba.
Murmushi Raheena tayi tana fad'in ina sonki Momy na. Mai aikinsu ce ta shigo da sallama. Bayan sun amsa ta kalli Raheena tana fad'in Aunty lokacin shiga kicin yayi.
Saurin tashi Raheena tayi tana fad'in amma nagode, muje kada mu makara. Dariya Momy tayi tana fad'in Allah nagode maka, gaskiya naji dad'in zuwan Ra'eez rayuwarki Raheena, ta silarsa gashi kin canza, sallah akan lokaci, ga girmama masu aiki sannan abinci ma kin iya, ai dole ma na dage ki auri Ra'eez.
*** ***
Cikin kwana biyu Ra'eez ya kammala abubuwan da yakeyi, ko Ummunsa da kyar yake zuwa ya duba ta saboda beda lokaci, sunyi magana da Dr. Saddek yace sai litinin zasuyi mata awon akwai wani likita da suke jira zaizo.
Gidan su Rumaisa ma so d'aya yake zuwa da rana yaci abinci, yafiso ya kammala komai ta yanda zai shiga kotu da kwarin guiwa, hatta da wayoyinsa baya d'auka sai idan kiran me muhimmanci ne.
***
Safiyar litinin da wuri ya kammala shirinsa, haka ya nufi gidan su Rumaisa, bayan sun gaisa yace zai wuce. Mama tace abinci fa? Ra'eez yace Mama yayi safiya da yawa idan muka kammala zanci.
Girgiza kai tayi tana fad'in zauna kasha ko shayi ne. Haka ya zauna Rumaisa ta kawo masa. Zama tayi tana kallonshi harya kammala. Murmushi yayi yana fad'in kimun addu'a Allah ya bani sa'a kinji.
Kai ta d'aga tana fad'in inayi maka ai, kuma nasan zakayi nasara. Ra'eez yace nagode, da mun kammala zan maido maki da lokacin ki dana ara. Murmushi tayi ta mik'e.
Addu'a sosai Mama tayi masa kafin yawuce wajen aiki.
Ofis d'insa ya fara wucewa kafin lokacin shiga kotun yayi.
K'arfe goma babbar kotu tacika da mutane suna jiran isowar Alkali. Bayan daya shigo kowa ya samu waje ya zauna ana jiran afara.
Bayan ya zauna ya umarci magatakarda daya karanto shari'a. Tashi yayi ya fara karantowa.
*A yau litinin goma ga watan oktoba shekara ta dubu biyu da sha tara wannan kotu mai albarka zata saurari k'arar da Malan Haruna ya shigar ta Sameer Aliyu Jabb'ama, wanda yake zarginsa da yima d'iyarsa 'yar shekara sha shidda fyad'e.* Risnawa yayi ya mik'a takardar.
Bayan da Alkali ya gama dubawa yace lauyoyin da zasu gabatar da shari'a fa? Tashi sukayi, fitowa Brr. Bajinta yayi yana fad'in sunana Brr. Bajinta, nine wanda yake kare wad'anda suke k'ara.
Sunana Brr. Ra'eez, nine nake kare wanda ake k'ara. Jinjina kai Alkali yayi yana fad'in lauyen da zai fara bismilla.
Fitowa Brr. Bajinta yayi yana fad'in ya mai shari'a inaso zanyima Sameer wasu tambayoyi idan kotu ta bani dama? Koti ta baka dama, Sameer ya fito gaban kotu.
Brr. Bajinta... Kotu zataso taji sunanka.
Sunana Sameer Aliyu Jabb'ama.
Brr. Bajinta... Malan Aliyu kaji abinda ake tuhumarka dashi, shin ko da gaske ne ka aikata abinda ake zarginka dashi?
Sameer... Ban aikata abinda ake zargina dashi ba gaskiya.
Brr. Bajinta... Kana nufin baka san Halima ba?
Sameer... Tabbas ni bansanta ba idan ba ranar da tazo wajena wai tana sona ba, ni kuma tamun yarinta nayi soyayya da ita sai nace ta tafi ta bani waje, nan fa ta fara mani rashin kunya wai idan tana son abu dole ta sameshi kuma zanga abinda zatayi mani, shine fa kawai naji anzo ana fad'in wai nayi mata fyad'e.
Brr. Bajinta... Kana nufin dai baka tab'a kaita gidanku ba?
Sameer... Aini banda lafiyar da zan iya kwanciya da mace ma, hakan yasa ko aure banyi ba.
Brr. Bajinta... Ko kana da shedar da zaka nuna ma kotu cewar baka da lafiyar kusantar mace?
Sameer... Kwarai ina da sheda tana wajen likita na.
Brr. Bajinta... Shikenan iya kar abinda ka sani kenan akan wannan abun da ake zargin ka?
Sameer.... Iyakar abinda na sani kenan.
Brr. Bajinta... Zaka iya tafiya, inaso nayi ma likitan Sameer tambaya idan kotu ta bani dama? Kotu ta baka dama.
Brr. Bajinta.... Kotu zata so taji sunanka da aikin ka.
Sunana Dr. Sa'eed Jafar, nine likitan da yake kula da lafiyar Sameer kusan shekaru ukku kenan.
Brr. Bajinta.... Likita wace irin rashin lafiya Sameer yake da ita da har yake zuwa wajen ka?
Dr. Sa'eed.... E to, a shekarun baya sunzo wajena shida Mahaifinsa kasancewar nine likitan gidansu, alokacin Mahaifinsa yake sheda mani wai Sameer har lokacin baya kula mata, daya bincikeshi sai yace masa shi kawai baya sha'awar mace, shine sukazo wajena, alokacin ne na gano Sameer beda lafiyar da zai iya kusantar mace, hakan yasa na d'orashi akan magani, wannan shine sakamakon binciken da akayi masa, ga magungunan da yake sha.
Brr. Bajinta... Shikenan zaka iya tafiya. Ina so nayima Dr. Kaseem tambaya. Kotu ta baka dama.
Brr. Bajinta.. Kotu zataso taji sunan ka da aikin ka.
Sunana Dr. Kaseem Nuhu, nine likitan daya duba Halima alokacin da Iyayenta suka kaita asibiti.
Brr. Bajinta... Dr. Kaseem alokacin da aka kai Halima asibiti a wane hali take?
Dr. Kaseem.... E to, gaskiya ba wani cikin damuwa sosai aka kaita ba, asalima da k'afafuwanta taje, bayan da Mahaifinta yayi mani bayanin fyad'e akayi mata sai muka shiga da ita d'aki domin mu dubata, to abinda na gani yasa nayi mamaki da akace wai fyad'e ne, domin babu alamun wani ciwo ajikinta, da ganin yanayinta kamar ta saba mu'amula da maza haka, sai kawai na rubuta mata magungunan ciwon jiki na kwantar ma da Mahaifinta da hankali dan gaskiya besan halin da d'iyarsa take ciki ba, na fad'a masa anyi mata d'inki kawai zata kwanta na kwana biyu.
Brr. Bajinta... Idan na fahimceka Halima ba fyad'e akayi mata ba kenan?
K'arya ne ya mai shari'a, wallahi 'Diyata bata tab'a aikata masha'a ba, wannan likitan k'arya yakeyi, domin shine ya dubata sai dai idan siyeshi akayi kuma.....
Bubbuga tebur Alkali yayi hakan yasa Malan Haruna ya koma ya zauna hawaye suna bin fuskarshi, kallon Brr. Barau kawai yakeyi zuciyarsa na masa zafi, yanda yake tafiyar da aikinsa kamar shine yake kare mai laifi.
Kallonshi Alkali yayi yana fad'in kada ka sake magana akotu dan nan ba kasuwa bace, idan kana da magana kajira abaka dama, Brr. Bajinta zaka iya cigaba.
Risnawa yayi yana fad'in Dr. Kaseem zaka iya tafiya mun gode. Ina so nayima Halima tambaya idan kotu ta bani dama? Kotu ta baka dama.
Jiki a sanyaye Halima ta fita gaban kotu, da kyar take iya d'aga k'afarta, kanta ak'asa hawaye ne kawai suke sauka ajikinta.
Brr. Bajinta.. Meye cikekken sunan ki?
Sunana Halima Haruna.
Brr. Barau... Shin ko kinsan wancan? ya nuna Sameer.
Kai Halima ta d'aga.
Brr. Bajinta... Baki zaki bud'e kiyi magana.
Halima na sanshi.
Brr. Bajinta... Meye alak'ar ku dashi?
Halima... Babu wata alak'a tsakanina dashi, abinda na sani duk lokacin da zanje islamiya yana tare ni da maganganun banza ni kuma bana kulashi, wata rana nayi latti nazo wucewa kawai naga yasha gabana, zanyi magana kawai ya shafa mani wani kyalle a fuskata, daga nan ban sake sanin abinda yake faruwa ba sai bud'e ido nayi na ganni kwance a d'akinsa cikin jini, kuka nasa shine yace ko nayi shiru koya k'aramun, cikin tashin hankali na kama bakina, sani yayi na tashi yace na fice kuma kada na bari kowa yasan daga d'akinsa nake, nasan dai na fita daga gidansu na kama hanyar gida, kafin na kai gida bansan abinda ya faru ba sai dai na bud'e ido a gadon asibiti.
Brr. Bajinta... Halima kuma kin tabbata Sameer ne kika gani? Kai ta d'aga tana fad'in wallahi shine.
Brr. Bajinta... Shikenan zaki iya tafiya. Ya mai shari'a iya tambayoyin da nake dasu kenan, ina fatan wannan kotu zatayi duba da shedun da aka gabatar domin a kwatar ma me hakki hakkinsa. Nagode.
Wasu daga cikin kotun dariya suka farayi k'asa-k'asa dan ganin wata bahaguwar shari'a, domin yanda Brr. Bajinta yayi tamkar ba shine yake kare Halima ba.
Ra'eez kuwa yana zaune ya nutsu ya gama had'a duk wasu bayanai da aka gabatar ma kotu.
Bayan kowa yayi shiru Alkali yace lauyen da yake kare wanda ake k'ara bismilla.
Ra'eez... Ya mai shari'a ina so nayima Dr. Sa'eed tambaya idan kotu ta bani dama. Kotu ta baka dama.
Ra'eez... Likita naji bayanin daka bayar yanzu a kotu akan rashin lafiyar Sameer, shin dama har namiji ya girma baya iya gane beda lafiya ne?
Dr. Sa'eed..... Yana ganewa mana, ai tun lokacin da namiji ya isa balaga zai iya fahimtar yanayin da yake ciki.
Ra'eez... Amma naji kace shekaru ukku da suka wuce aka gano Sameer beda lafiya wanda nasan Sameer zai kai shekaru talatin da hud'u ko da biyar ma, shin kana nufin tun alokacin baya besan cewar beda lafiya ba? Kada fa maganarka ta jawo masa bakin jini yazo ya rasa matar aure nan gaba.
Dr. Sa'eed... E to, kasan ba kowane yake maida hankali akan lafiyarsa ba, wasu kuma zaka samu haka suke Mata basa gabansu koda suna da lafiya.
Ra'eez.... Mungode likita zaka iya tafiya. Ya mai shari'a ina so nayima Dr. Kaseem tambaya idan kotu ta bani dama. Kotu ta baka dama.
Ra'eez... Dr. Kaseem kace lokacin da aka kawo Halima wajenka da k'afarta ta tako ko?
Dr. Kaseem... Kwarai kuwa da k'afarta ta tako.
Ra'eez.... Kenan lokacin da aka kawota kaine ka amsheta?
Dr. Kaseem... Saurin d'ago kai yayi yana kifta idanuwa. Ra'eez yace tambayarka nakeyi. E to ba nine na amsheta ba amma nine na dubata.
Ra'eez... Ai ba cewa nayi kaine ka dubata ba, tambayar ka nake kaine ka amsheta?
Dr. Kaseem... Ba nine na amsheta ba.
Ra'eez... To ya akayi ka gane da k'afarta tazo?
Dr. Kaseem... Yanayinta ya nuna bata cikin wahala ai.
Ra'eez.... Murmushi yayi yana fad'in amma ai ka kwantar da ita har na kwana biyu kafin ka basu sallama.
Dr. Kaseem... Kasan idan marar lafiya ya nuna sauki ajikinsa hakan yake bamu damar sallamarsa, to ita ta nuna rashin kwari a jikinta hakan yasa dole na kwantar da ita.
Ra'eez..... Alokacin da aka kawo ta asibiti jikinta duk jini, gashi kai kuma kace babu alamun fyad'e ajikinta saboda ba shine na farko ba, ko zaka fad'a mana jinin na meye?
Dr. Kaseem... E to, da yake akwai ciwo a jikin hannunta ina ji jinin ciwon ne.
Ra'eez... Shikenan zaka iya tafiya. Ina so nayima sister Asabe tambaya idan kotu ta bani dama. Kotu ta baka dama.
Hannu Brr. Bajinta yasa yana gyara wuyan rigarshi, dama yasan Ra'eez bazai tab'a goyon rashin gaskiya ba, gashinan anyi gudun gara an fad'a gidan zago.
Haka sauran mutanan kotun duk kansu ya d'aure, gashi dai sunji kowa da lauyenshi amma kuma abun ya juye.
Ra'eez... Kotu zata so taji sunanki da aikin ki.
Sunana Asabe Habu, kuma ni ma'akaciyace a asibitin Dr. Kaseem wanda ya kasance na kud'i ne.
Ra'eez.... Shin ko zaki fad'ama kotu abinda ya faru alokacin da aka kawo Halima asibitin ku?
Asabe.... E muna zaune gab da magriba sai ga Mahaifinta ya shigo da ita a hannunsa a rud'e, alokacin ma ko motsi batayi ga jikinta duk jini harya b'ata rigar Mahaifinta, yana kuka ya rok'emu akan mu taimaka masa, alokacin ni d'aya ce nan na nuna masu gado ya kwantar da ita, turata nayi zuwa d'aki domin bata taimakon gaggawa, gaskiya abinda na gani ya tada hankalina, sai dai kafin na fara dubata sai ga Dr. Kaseem ya shigo sai yace mun na tafi zai k'arasa dubata, naso na tsaya na taimaka masa sai yace kawai na tafi, hakan yasa na tafi.
Ra'eez.... Jinjina kai yayi yana fad'in kamar meye kika gani ya tashi hankalin ki?
Asabe... Yanda aka ci mutuncinta yasa hankalina ya tashi, domin ko waye ya aikata mata haka to da k'arfi ya shigeta.
Ra'eez... Mungode zaki iya tafiya. Ina so nayima Sameer tambaya idan kotu ta bani dama. Kotu ta baka dama.
Ra'eez... Malan Sameer, kace Halima tace sai tayi maka rashin kirki ko? To dama can kuna takun sak'a ne da ita?
Sameer..... Gaskiya ko magana bamayi domin bansanta ba, nasan dai ta k'ofar gidan mu take bi idan zataje makaranta, saboda tana ganina yasa tazo tace mun tana sona ni kuma nayi mata wulak'anci shine tace zan gani.
Ra'eez.... Sameer ko kasan wannan zoben?
Sameer... Hankali tashe Sameer yake kallon zoben hannun Ra'eez, tabbas tun bayan rabuwarsu da Halima ya nemeshi ya rasa ashe yana jikinta. Wata irin zufa ce ta fara keto masa, kwalla ne suka cika masa ido, kasa magana yayi sai dai ya duk'ar da kai.
Ra'eez... Murmushi yayi yana fad'in wannan zoben Malan Haruna ya sameshi ne a jikin gashin Halima alokacin da yake kok'arin kaita asibiti, hakan yasa ya cireshi ya aje, gashi kuma a wannan hoton naka naga irin zoben a hannunka, wata kila ko kama ce kawai.
Hawaye ne suka fara zubo ma Sameer, a yanzu kam ya sare domin yasan dole a ganoshi, gara kawai yayi kundunbale ya fad'i gaskiya kamar yanda Ra'eez ya kirashi ya fad'a masa ya gano gaskiya shine ya aikata laifi, idan ya tona kanshi shi zai tsaya masa ayi masa hukunci mai sauki.
Ajiyar zuciya ya saki yana sake kallon hoton hannun Ra'eez, ya rasa a in da ma ya samu hoton.
Ra'eez... Juyowa yayi yana fad'in ya mai shari'a da alama wannan zoben da Malan Haruna ya bayar bana Sameer bane tunda gashi ya kasa amsawa, ze iya yuwuwa kawai kama ce, domin za'a iya samun irinshi a waje da yawa, kamar yanda Dr. Sa'eed ya sheda ma kotu Sameer beda lafiyar da zai iya hayk'ema mace ina so wannan kotu tayi duba da wannan magana tashi domin ta.....
Nine na aikata laifin ya mai shari'a, Sameer ya fad'a da k'arfi cikin muryar kuka. Da sauri kowa ya kalleshi. Murmushi Ra'eez ya saki kafin yayi saurin canza fuska ya juyo.
Gaba d'aya wajen ya hargitse da surutu, Brr. Bajinta kuwa kamar wanda aka dasa haka yake kallon Ra'eez, lallai ya tabbatar yafi k'arfin tunanin Alhaji Barau ba shi bama, wannan rainin hankalin yayi yawa, bayan ya gama fito da gaskiya kuma ya koma yana kok'arin kare Sameer.
Bubbuga tebur Alkali yayi jiki a sanyaye, gaba d'aya Ra'eez ya kwance masa notin kanshi, daurewa yayi ya tattaro jarumta yasa aranshi.
Mahaifin Sameer ne ya tashi yana fad'in k'arya ne wallahi, kowa ya sheda Yarona beda lafiya, ina rokon wannan kotu da ta d'aga wannan shari'ar domin aje ayi binciken kwakwalwar Sameer dan wannan maganar da yayi tayi kama da ta masu tab'in hankali.
Da hankalina Dady! Sameer ya fad'a yana kuka, kallon Alkali yayi yana fad'in zan fad'i gaskiya ya mai shari'a.
Jinjina kai Alkali yayi kafin yasa akayi shiru. Komawa Ra'eez yayi ya zauna. Sake kallon Sameer Alkali yayi kafin yace muna sauraron ka.....