*Alhaji Job'e Marusa* d'an asalin garin *Mayo Barwa* ne, cikekken bafullata ni ne, duk cikin zuri'arsu shi kad'ai ne yayi karatun boko, shima wani Yayan Mahaifinsa *Bukar* ne ya d'aukeshi ya koma wajensa da zama a kudu, sana'ar Yayan Mahaifinsa shine siyar da Fata, babban dila ne kuma hamshakin mai kud'i ne, be tab'a haihuwa ba hakan yasa ya d'auki Alhaji Marusa ya koma dashi gidansa.
Baffa Bukar yana da mugun son kanshi, daga matansa sai masu masa fadanci kawai yake sakar ma bakin aljihunsa, sannan mugun mutum ne, sam baya so yaga wani ya fishi, zai iya kashe rai akan abun duniya, kuma be yarda da asara ba, zamansa a kudu ya k'ara masa rashin imani, yana da babban matsafi wanda yake masa aiki, yafiso akoda yaushe ya kasance shine a sama.
Haka Alhaji Marusa ya taso duk wani bakin hali na Baffansa ya d'aukeshi, a k'asar waje yayi karatunsa acan ya kara koyo mugayen halaye, sam ibada bata dameshi ba sai yaga dama, hatta da azumi ciyarwa yakeyi wai ulcer yake da ita.
Bayan daya kafu da kanshi sai Baffansa ya basa babban jari ya fara shigo da kaya daga k'asashen waje, cikin lokaci k'ank'ani Allah ya bashi abinda yake nema, hakan yasa ya tashi ya koma Lagos da zama, gidan da yake zaune kanshi abun kallo ne, domin shine ake kira da Aljannar duniya, dan Alhaji Marusa mutum ne mai son jin dad'i.
Wani zuwa da yayi k'asar waje acan ya had'u da wani abokinsa da sukayi karatu mai suna *Herry*, bature ne, sana'arsa siyar da miyagun k'wayoyi, bayan daya samu labarin Alhaji Marusa yana kasuwancin kai kaya k'asar najeriya sai ya bashi shawarar ya fara siyar da kwayoyi zaici riba sosai.
Jin harkar k'aruwa yasa Alhaji Marusa ya amince, nan ya fara saka miyagun kwayoyi acikin kayan da yake shigo dasu, yana shigo da shaddodi, su taliya da sauran kayan masarufi, acikin kwalayen ake saka miyagun kwayoyin ta yanda za'aga kamar kayan gaskiya ne a ciki, hakan yasa da wuya a kama kayan Alhaji Marusa da laifi, musamman da yake saye manyan kwastam da k'ananan su.
Sam beda matsala da bodar Lagos shiyasa yafi son shigo da kaya tanan, matarsa d'aya da yaransa biyu yasa aka cire mata mahaifa dan baya son haihuwa, ko kauyensu baya zuwa sai dai yayi masu aike, haka baya son wani nashi yazo inda yake, danshi be yarda da jininsa ba yafi son mutanan gari, acewarsa besan su ba idan sukayi masa abu zai iya masu rashin mutunci.
Brr. Barau tun yana k'aramin lauya yake masa aiki har ya zama babba, ya kware a harkar aikinsa, domin Allah yayi masa wata baiwa, ya iya tsara zance, idan yaso maida k'arya gaskiya babu wanda zai iya gano gaskiya, hakan yasa yayi saurin d'aukaka domin lauyen manyan mutane ne.
Zuwan Alhaji Maiwada bodar Lagos yasa Alhaji Marusa ya fara sanin meye damuwa akan shigo da kaya, gashi Baffansa ya jima da rasuwa da tuni ya kai sunan Alhaji an d'aure bakinsa, ganin zai caza masa kai yasa ya had'a masa wannan sharrin.
Shi da Mr. Kallah aminan juna ne, sunfi shekara goma sha atare, kowa yasan sirrin kowa, kuma Mr. Kallah shine yake goya masa baya a duk wani abu da zaiyi.
***
*Garba Bala* shine asalin sunansa, bamaguje ne daya fito daga garin *Malumfashi* cikin kauyen *K'afur*, yayi karatun boko sosai, yana da masifar kok'ari, ya rik'e muk'amai da yawa daga baya ne ya maida sunansa *Mr. Kallah*, idan ka ganshi bazaka tab'a cewa bamaguje bane, zaka masa d'aukar cikekkan musulmi, hausa abakinsa dama gadonsa ce, domin kowa yasan yanda maguzawa suke jin hausa, rashin hasken musulunci daya rasa shine ya banbantasa da musulmai, amma acikinsu yake komai, shigarsa da mu'amalarsa duk irin na musulmai ne.
Mr. Kallah yana da son kud'i, matuk'ar zaka yaga masa zai iya tsaya maka, sai dai yana da matuk'ar wayau, domin shi mutum ne mai aiki da kwakwalwa, duk yanda zaiyi abu baya bari aganosa, shiyasa a zahiri mutane suke masa kallon mai gaskiya da amana, wannan halin nasa yaja masa k'arin matsayi sosai, wanda a yanzu haka shine shugaban kwastam na k'asa, a Abuja yake zaune da matarsa ta farko, matarsa ta biyu kuma tana Lagos, gidansa na Lagos babban gida ne, waje guda ya ware ya gina katafaren ofis, idan yazo hutu anan yake aikinsa danshi mutum ne wanda baya son zaman banza.
Duk wani mai kasuwanci matuk'ar yana shigo da miyagun kaya to yana da alak'a da Mr. Kallah, saboda yana goya masu baya yasa suke cin karensu babu babbaka, sai wanda yaso yake ma k'arin matsayi, idan kuma yaga baka binsa yanzu zai canza ka da wani. Alokacin da aka kawo sunan Alhaji Maiwada akan abashi shugaban kwastam na lagos yaso ya hana saboda yasan halinshi, amma gudun maganar mutane yasa ya amince dashi, sai gashi yazo yana caza masu kai.
Wannan shine labarin *Mr. Kallah* da *Alhaji Marusa*
***** *****
Washe gari Alhaji Maiwada ya tashi da k'arfinsa, domin yaji sauki sosai, zugin da yake ji a zuciyarsa ma yayi sauki sai damuwar da baza'a rasa ba, bayan da likita yazo ya aunashi yaga jinin ya sauka.
Zaune suke a falo bayan sun gama karyawa. Alhaji Mansur ne ya kalli Alhaji yana fad'in naji dad'i dana ganka katashi ahaka yau, dama kuma haka akeson bawa ya kasance mai tawakkali da yarda da K'addara, Alhaji nafi kowa saninka, nasan abinda zakayi da wanda baza kayi ba, kada ka damu da kallon da mutane zasuyi maka, Allah yasan baka aikata abinda akace ba, kuma shine zai saka maka akan zaluncin da akayi maka, dan haka kada kasa damuwar komai aranka, ka d'auka wannan dukiyar Allah ne ya baka kuma gashi zai amshe abunsa, dan haka kada kaji komai zamu biyasu abinda kotu tace, insha Allahu sanadiyar wannan kud'i da zaka basu sune zasu zamo silar lalacewar tasu dukiyar.
Hannu yasa a aljihu ya ciro wata takarda, bud'eta yayi yana fad'in d'azu aka aikota daga hannun kwamishna, sunzo sai suka ba Madu, iya yawan kud'in da za'a biyasu ne aka rubuta aciki, kuma wata guda suka bada idan yacika ba'a basu ba zasu amsa da kansu.
Naira miliyan saba'in yace ya kashe akayan da suka b'ace hada kud'in daya kashe na zuwansu nan. Aje takardar yayi yana dafe kai. Murmushi Alhaji Maiwada yayi yasa hannu ya d'auki takardar yana kallo. Kuka kawai Ummun Ra'eez takeyi jin makudan kud'in da zasu biya.
Gyara zama Alhaji yayi yana fad'in Alhaji Mansur zansa wannan gidan nawa akasuwa. Da sauri Alhaji Mansur ya kalleshi jin abinda ya fad'a. Jinjina kai yayi yana fad'in wallahi gidan nan ya fitar mani arai, da nasan gina gidan nan zai jawo mani irin wannan zargin bazan tab'a ginashi ba, dama na ginashi ne saboda muji dad'in rayuwa nida iyali na, sai gashi hakan ya jawo mana tashin hankali, da zan samu wanda zai bani kud'in gidan nan ayanzu wallahi bazan sake kwana aciki ba.
Girgiza kai Alhaji Mansur yayi yana fad'in baza'ayi haka ba, dama abinda suke so kenan su rabaka da wannan gidan, idan sukaga kasa shi akasuwa burinsu zai cika, dan haka bazaka siyar dashi ba, zamusan yanda za'ayi.
Murmushin takaici Alhaji Maiwada yayi yana fad'in kayi hakuri Alhaji Mansur, ina d'aukar shawarar ka, amma a wannan karon ko Alhajina ne yace kada na siyar da gidan nan bazan jishi ba, kwanciyar hankalina shine nabar gidan nan, na ciresa araina hakan zaisa na samu natsuwa.
Cikin kuka Ummun Ra'eez tace dan Allah Abban Labiba ka barsa ya siyar dashi, kasashi ya aje har aikin mu koma kano da zama wallahi bana son garin nan. Hannu Alhaji yasa ya kamo hannunta yana fad'in kada ki sake fad'ar haka Bilkisu, idan na aje aikina kamar ban yarda da k'addara bane, kuma zuciyarsu zatayi sanyi tunda sun sa na aje aikina, idan kinga na bar aikina to takardar sallama aka bani, amma matuk'ar basu bani ba to mutuwa ce zatasa nabar aikina sai kuma idan lokacin aje aikin yayi, dan haka matuk'ar kina sona ki tayani cin wannan jarabawar da Allah ya d'ora mani.
Jinjina kai tayi tana goge ido tace shikenan Abbun Ra'eez, na amince ka siyar da gidan, ina maka addu'a akan Allah yayi maka sakayya akan zaluncin da akayi maka, kuma ya baka ikon cigaba da aikin ka.
Alhaji Mansur yace amin, nima na amince da abinda kace, bakomai Allah ya shige mana gaba. Alhaji Maiwada yace amin, ka kira DPO ka sanar masa zan siyar da gidana, nasan Alhaji Marusa ne zai siyeshi kaga sai ya fad'a masa, akira dillalai suzo suyima gidan kud'i, idan na biyasu zan sayi wani gidan sai mu koma can da zama.
Kwalla Alhaji Mansur ya goge yana fad'in Allah ya saka maka. Alhaji yace amin.
**** ****
Cikin kwana biyu aka gama komai, dillalai suka yima gida kud'i akan naira miliyon d'ari biyu, tayin farko wanda Alhaji Marusa ya aiko yace ya siya, haka aka gama komai aka mik'a masa takardun gida shedu suka sheda, dama acikin kwana biyun Alhaji ya kwashe kayansa, a unguwar *APAPA* ya samu wani gida mai kyau kuma aka sayar masa akan naira miliyon tamanin, nan take ya amince.
Bayan da aka mik'a masa kud'insa agaban 'yan sanda da hukumar bincike sukaje shida Alhaji Mansur da Malan Sani suka biya Alhaji Marusa naira miliyon saba'in da biyar da ya buk'ata, bayan da aka gama cike-cike suka bar wajen.
Kud'in gidansa ya biya sauran kud'in yasa a banki. Alhaji Mansur gudummuwar milayan d'aya ya bashi amma da kyar ya amsa, haka abokinsa Alhaji Usman wanda ya tab'a kwatoma kayansa shima sai da ya bashi dubu d'ari biyar, haka mutanan da suke mutunci suka rik'a kawo masa gudummuwa.
Bayan sun maida kayansu zuwa sabon gidansu suka gyara ko ina, gida ne mai kyau, sai dai ba me bene bane, bangare biyu ne, wanda d'ayan bangaren yake kamar d'akunan maza, sai babban b'arin mai d'auke da babban falo, sai kicin mai had'e da sito, sai wani d'aki akusa da kicin mai d'auke da band'aki wanda yake amatsayin na masu aiki, daga can kuma zaka shiga wata hanya mai d'auke da d'akuna biyu dukkansu da band'aki aciki, wannan shine b'angaren matar gidan, daga gefen falo akwai d'aki wanda shine na maigida, sai wajen teburin cin abinci. Daga waje kuma akwai d'akin mai gadi sai harabar gida da wajen aje motoci sai rumfa.
Sosai Ummun Ra'eez taji dad'in gidan dan ya burgeta, haka kawai ta tsinci kanta cikin farin ciki duk damuwar da take ciki sai ta tafi. Haka suka gyara komai dama gidan besha wahala ba, Ladi tasa kayanta a d'akin ta, kayan Ra'eez kuma aka aje masa a d'akin da yake na kusa da Ummunsa.
**
Bayan kwana biyu Alhaji Mansur yayi masu sallama ya koma yana mai sake kwantar ma Alhaji Maiwada da hankali, haka ya tafi cike da tausayin abokinsa.
Malan Sani yaji dad'i da suka samu gida a wannan unguwar saboda baya so ace sun bar unguwa mai kyau sun koma marar kyau, sai gashi itama wannan d'in tana da kyau.
Tunda wannan abu ya faru Alhaji be lek'a ofis ba, yana jiran yaji halin da yake ciki, babu inda yake zuwa sai masallaci, sosai hankalinsa ya kwanta dan ya dage da addu'a hakan yasa Allah ya yaye masa damuwar da take ransa yasa masa dangana, duk yanda yake tunanin mutanen gari zasu yaya tashi sai Allah ya kwantar da abun, wanda ba haka su Alhaji Marusa suka so ba.
Suna kwance ad'aki ya samu kira daga Mr. Kallah, bayan sun gaisa ya sake jajenta masa akan abinda ya faru, anan yake fad'a masa gobe ana nemansa a can abuja. Alhaji Maiwada yace nagode kuma zan zo akan lokaci. Sallama sukayi ya kashe wayar.
Ajiyar zuciya ya sauke yana fad'in ya Allah ka zab'a mani abinda yafi alkhairi akan wannan aikin. Hannunsa Ummu ta kamo tana fad'in nemanka ake ko? Kai ya d'aga mata. Murmushi tayi tana fad'in nasan mijina mai tawakkali ne, kuma nasan zaka amshi duk abinda yazo maka da hannu biyu, dan haka kada ka damu da kiran da suke maka, idan su basa tare da kai ni da Ra'eez muna tare da kai har abada.
Murmushi ya saki wanda har hak'oransa sai da suka fito, sake matseta yayi yana fad'in nagode Uwar gidana, ina mai tabbatar maki matuk'ar suka barni akan aikina sai na zaluko gaskiya, ko bayan raina sai duniya tasan cewar bani da laifi, sai Allah ya haska su kowa ya gansu.
Ummu tace amma kayi komai a hankali kada su sake maka wani sharrin. Alhaji yace kada ki damu, wannan abun da ya faru alkhairi ne a wajena, domin ya k'ara haska mani duhun da nake ciki, ayanzu zasu gane basu da wayau, domin zanyi aiki ta k'ark'ashin k'asa. Murmushi tayi tana fad'in nasan zakayi fiye da haka.
**** ****
Cike babban d'akin taron yake da manyan mutane masu babban matsayi, bayan da aka gama tattaunawa kowa ya fad'i ra'ayinsa akan Alhaji Maiwada, wasu suna ganin ayi masa canjin wajen aiki tare da rage masa matsayi, wasu suna ganin takardar sallama ce ta dace dashi domin yaci amanar aikinsa, idan aka barshi hakan zai bama wasu dama su aikata irin abinda yayi ko fiye da haka, wasu suna ganin a bashi takardar jan kunne.
Bayan da kowa ya gama kawo tasa shawarar Mr. Kallah ya mik'e yana fad'in naji duk abinda kuka fad'a, kuma a dokar tsarin aiki idan aka kama mutum da laifi abu na farko da akeyi ana duba file d'insa, idan har ba'a tab'a samunsa da wani laifi ba to ana masa uzuri, acikin mu nan babu wanda bai san irin tsarin aiki na Alhaji Maiwada ba, tun yana k'aramin ma'aikaci ake yabon iya aikinsa, yarik'e matsayi kala-kala ba'a tab'a samunsa da karb'ar cin hanci ko so d'aya ba, har kawo warsa wannan matsayin ba'a tab'a kamasa da wani laifi daya sab'a ma doka ba, kuma wannan abu daya faru ina ganin kamar akwai lauje cikin nad'i, koma menene Allah ne yasan gaskiya, be kamata ace mun rufe ido munyi masa haka ba, idan mutum yayi ba dai-dai ba sai ajuya a kalli aikin kwarai nashi sai ayi masa hukunci dashi, dan haka ni dai a tawa shawarar ina ganin aja masa kunne a bashi dama ta biyu, kuma ya tsaya a aikinsa, kada yarik'a shiga aikin wasu, idan ya kiyaye shikenan, idan kuma aka sake kamashi sai ayi masa hukuncin daya dace.
Bayanin Mr. Kallah yayi ma mutane da dama dad'i, kuma sun gamsu da bayaninsa, nan take aka amince da shawararsa. Bayan sun gama rubutu aka rufe taro.
Alokacin Alhaji Maiwada yana zaune a inda aka tanadar ma baki dan ba dashi akayi taron ba, bayan sun fito Mr. Kallah yayi kiransa suka shiga ofis, su ukku ne a ofis d'in. Bayan ya gama karanto masa abinda suka yanke anan kowa yayi masa tashi nasihar.
Bayan sun fita ya rage su biyu Mr. Kallah ya dubeshi yana fad'in kayi hak'uri haka aikin kwastam ya gada, kafin nazo wannan matsayin nasha wahala sosai, matuk'ar kace zakayi gaskiya dole karik'a had'uwa da sharrin mutane, shawarar da zan baka ka tsaya akan aikin ka, kuma duk abinda zakayi karika tanadar kwakkwarar sheda, sannan ka rage shiga harkar Alhaji Marusa dan zai iya b'atar da kai. Alhaji Maiwada yace bakomai zan kiyaye, nagose sosai. Mr. Kallah yace bakomai.
Kud'i ya d'auko dubu d'ari biyar ya mik'a masa yana fad'in ga tawa gudummuwar. Alhaji yace kabarshi Mr. Kallah nagode. Murmushi Mr. Kallah yayi yana fad'in sunyi kad'an ko? Girgiza kai Alhaji yayi. Mr. Kallah yace to ka amsa. Amsa yayi yana masa godiya, haka sukayi sallama ya fito yana jinjina kirki irin na Mr. Kallah.
Mr. Kallah kuwa yana fita yayi murmushi, ya rasa ya akayi duk cikin ma'aikatansa yake jin nauyin Alhaji Maiwada, sosai yake masa kwarjini, duk da abinda yayi masa yayi ne dan ya k'arama kansa yarda awajen mutane amma ya rasa dalilin da yasa baya so Alhaji Marusa ya cutar dashi. Wayarsa ce tayi k'ara hakan yasa ya dawo daga tunanin da ya keyi.
**** ***
Haka Alhaji Maiwada ya koma bakin aikinsa, sosai ya canza daga yanda suka sanshi, babu ruwansa da kowa, abinda ya kamata shi yakeyi, kowa ya raba masa wajen aikinsa, kuma idan kayi aiki dole ka kawo rahoto ya duba, duk abinda ya faru sai anzo an sanar dashi, haka duk wad'an da zasu duba kaya dole su duba su da kyau, kuma dokar amsar cin hanci tana nan, sai dai ba ruwansa da kayan Alhaji Marusa, idan sunzo ma ba shine yake dubasu ba, amma duk da haka ana bincikasu yanda ya kamata, idan akwai abinda aka samu ana cirewa, shima Alhaji Marusan ya rage shigo da miyagun kwayoyi ta bodar Lagos, yace sai abun ya lafa.
Adebayo da Umar kowa yaga sun canza, domin hada sabbin motoci suka sake, sosai suke fantamawa, saboda suna cikin kud'i yasa basu damuwa da dokar ansar cin hanci ba.
A b'oye Alhaji yasa Abubakar da Moses suna bincika masa abinda yake faruwa, dan wannan abun daya faru yasa Moses yaji tausayin Alhaji, domin yasan wani abun daga cikin abinda su Adebayo sukayi, kawai yayi shiru ne saboda beda sheda, kuma yasan halin Alhaji Marusa matuk'ar ya ganoshi zai iya kashe shi, hakan yasa yaja bakinsa yayi shiru, amma yayi alk'awarin sai ya taya Alhaji sun gano gaskiya koma me zai faru, hakan yasa ya had'e da Abubakar.
Ur's.
Nabeelert Lady🖋
[3/10, 8:38 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud'i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shoot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k'asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub'e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.*
1⃣3⃣
*Bayan dogon lokaci*
Wajen wani abokinsa mai suna *Tayo* Moses yaje domin ya taimaka masa, dan wannan hanyar ita kad'ai zasubi domin su gano gaskiyar komai, dan Moses yayi alk'awarin sai ya taimaki Alhaji saboda yasan abubuwa da yawa a wajen su Adebayo kawai beda sheda a hannu ne.
Tayo gurun kamfuta ne, kuma abinda ya karanta kenan. Babu b'ata lokaci ya bama Moses abinda zaiyi amfani dashi, wasu na'urori ya bashi sai yayi masa saitin da wayarsa hada kamfutarsa ta hannu duk ya had'a masa ya nuna masa yanda zaiyi amfani dasu. Godiya Moses yayi masa ya tafi.
A ofis d'in Adebayo ya fara zuwa yasa d'aya daga cikin na'urorin da aka bashi, sai yayi kok'ari yasa a cikin motarsa, daga nan yaje wajen da ake duba kaya nan ma yasa guda d'aya, saura d'aya ta rage kuma yana so ya sata a gidan Alhaji Marusa musamman inda yaga yana ganawa da mutane, duk da yana zuwa gidanshi ada yanzu ya rasa ta yanda zaije yasa wannan na'urar, kuma duk tafi sauran muhimmanci saboda yasan a wajen Alhaji Marusa za'afi sanin komai.
Shiru yayi yana tunanin abunyi sai ga Abubakar yazo, nan yayi masa bayanin abinda yake kok'arinyi. Abubakar yace gaskiya Moses ka kyauta, tun jiya nake tunanin hanyar da zamubi mu taimaki Alhaji, ashe har ka rigani.
Moses yace abinda nakeso shine yanda zan had'a wannan abun agidan Alhaji Marusa. Shiru Abubakar yayi kafin yace akwai maigadin gidansa nasanshi, mai zai hana mu je masa da maganar kila ya amince.
Moses yace kasan halin mutane da son kud'i, kada muje muna tunanin yasa yaki sakawa yaje ya fad'ama Alaji kasan dai bazai barmu ba.
Abubakar yace kai dai muje, inaji yau ba shine keda aikin kwana ba, idan mun tashi daga nan mu biya ta wajen da yake zama insha Allahu zai amince. Moses yace shikenan.
***
Bayan da suka tashi suka nufi wajen da Maigadin Alhaji Marusa yake zama. Yana ganin Abubakar ya saki murmushi yana fad'in kaga kwastam masu gidan kud'i, murmushi Abubakar yayi yana fad'in *Malan Hassan* bazaka dena fad'a mani wannan abun ba ko, ai ma'aikatan banki sune masu gidan kud'i.
Malan Hassan yace ai dole na fad'a, kowa yasan kwastam kuna morewar ku domin kunfi masu banki 'yanci. Murmushi yayi anan suka gaishe shi. Malan Hassan yace wannan abokin aikin ka ne? Abubakar yace aikuwa dai Malan Hassan.
Zama sukayi Malan Hassan yana fad'in ina shugaban ku bawan Allah? Abubakar yace yanzu muka rabu ya wuce gida, ashe kaima kana tausaya masa? Malan Hassan yace ai dole na tausaya masa domin kowa yasan sharri akayi masa.
Moses yace Baba kaima kasan sharri akayi masa kenan? Malan Hassan yace ni ganau ne ba jiyau ba. Dariya Moses yayi yana fad'in Baba me kake nufi haka? Shima dariya yayi yana fad'in Abubakar ya fahimci abinda nake nufi ai.
Murmushi Abubakar yayi yana ma Moses bayani. Dariya Moses yayi yana fad'in Baba nima na fahimta yanzu. Abubakar yace wallahi Malan Hassan Alhaji mutumin kirki ne, kawai ya had'u da sharrin su Alhaji ne.
Gyara zama Malan Hassan yayi yana fad'in nan wajen babu tsaro ko zamuje cikin motar ku? Da sauri suka tashi domin abinda suke nema kenan.
Bayan sun zauna Moses ya kunna wayarsa saboda kada Malan Hassan yazo ya k'aryatasu idan lokacin hakan ya taso. Malan Hassan yace Abubakar Alhaji Marusa da kake gani mugun mutum ne, Allah dai yasa a k'ark'ashinsa zanci abinci shiyasa nake zaune a gidansa har yanzu, duk abinda kukaji ance Alhaji Maiwada yayi wallahi k'arya ne, abu ne wanda aka shiryashi, hatta da kayan da sukace sun b'ace ina tunanin k'arya ne, domin akwai abinda nake gani.
Abubakar yace Malan Hassan kaima baka da tabbaci kenan? Malan Hassan yace tunda ban gani da idona ba bazan ce ba, amma akwai abubuwan da nake gani agidanshi.
Mr. Kallah da kuke gani abokin Alhaji ne sosai, domin yana yawan zuwa gidansa idan yazo Lagos, sannan akwai wasu mutane biyu suma irin aikin ku sukeyi ina yawan ganinsu, d'aya bahaushe ne, d'ayan ko hausa bayaji sosai, sai wasu manyan mutane da ganinsu kasan mugaye ne, tunda nake ganinsu hankalina bai kwanta ba, babu yanda za'ayi naje naji abinda suke fad'a saboda acan wajen hutawarsa suke zama, amma tabbas sune suka k'ullama Alhaji Maiwada wannan sharrin.
Abubakar yace muma abinda muke tunani kenan, akwai abinda mukeso asa mana a wajen hutawarsa, babu wanda zaiyi mana wanan aikin idan ba kai ba Malan Hassan, shine nace muzo ko zaka taimaka mana domin Allah.
Malan Hassan yace kome kuke so zanyi maku domin nima nayi aikin lada. Na'urar Moses ya fiddo yana masa bayanin inda suke so yasa. Malan Hassan yace dan wannan ai mai sauki ne, kawai ku koya mani yanda zan sata.
Nan Moses yashiga koya masa yanda zaisa ta, bayan sun gama Malan Hassan yace gobe nine zanyi aikin kwana, kuma agoben zanje na saka kada ku damu, Allah zai taimaka mana, idan na gama zan fad'a maka Abubakar.
Sosai sukaji dad'in abinda yayi masu, kud'i Abubakar ya ciro ya mik'a masa. Malan Hassan yace haba Abubakar, dan zanyi maka aiki sai ka bani kud'i? Abubakar yace ba biyanka nayi ba kawai kyautace. Amsa Malan Hassan yayi yana fad'in nagode sosai. Sallama sukayi masa suka tafi.
***
Washe gari suka samu Alhaji a ofis sukayi masa bayanin abinda ake ciki. Shiru Alhaji yayi yana tunanin sunan Mr. Kallah da aka fad'a, girgiza kai yayi yana fad'in gaskiya ban yarda akwai sa hannun Mr. Kallah aciki ba, nasan dai abokin Alhaji Marusa ne, kila wani abun yake kaishi gidan amma bana tunanin zai iya aikata mani haka.
Moses yace Sir, kada kayi saurin yanke hukunci, mujira ai gaskiya zata nuna kanta. Jinjina kai Alhaji yayi yana fad'in nagode sosai. Abubakar yace haba Alhaji wannan ba wani abu bane, insha Allahu gaskiya zata fito.
Alhaji yace wallahi ba saboda kud'ina su dawo nakeso a gano gaskiya ba, ina so na wanke kaina awajen mutane, sannan kowa yasan abinda Alhaji Marusa yake aikatawa. Moses yace zamu kamasu ne zasuci Ubansu. Murmushi Alhaji yayi yana fad'in nagode.
A daren ranar Malan Hassan ya kira Abubakar ya fad'a masa ya gama komai. Abubakar yace nagode Malan Hassan Allah ya bamu sa'a. Yace amin.
**** ****
Haka rayuwa tacigaba da tafiya kowa yana aikinsa, duk hutu Ra'eez yana zuwa yayi sati d'aya ya koma saboda islamiya, alokacin da yazo sai da yayita tambayar dalilin da yasa suka canza gida. Ummunsa ce tayi masa dabara tace b'arayi suka matsa masu shiyasa suka tashi. Da wannan suka rufe bakinsa.
Tun bayan da Alhaji Marusa yayi ma Alhaji Maiwada wannan abun sai ya fara samun matsala a kasuwancinsa, cinikin da yakeyi sosai ya fara raguwa, ga yawan asara da yakeyi a wajen kawo masa kaya, amma da yake ya tara hakan yasa dukiyarsa bata girgiza ba, sai dai duk wacce ya fitar aka saro kaya da wuya ta dawo fiye da yanda take.
Haka su Umar da Adebayo komai ya fara lalace masu, mata da shaye-shaye ne suke cinye masu kud'i, duk yawan kud'in da suke samu basa masu afki.
Alhaji Maiwada kuwa tamkar anasa ma dukiyarsa taki, sosai yake samun bud'i, sai dai duk bud'in da yake samu sai yaji tsoron ya sayi kadara a Lagos, hakan yasa ya turama Alhaji Mansur kud'i ya saya masa gidaje a kano ya zuba masa haya, sannan ya bud'ema Ra'eez asusu a banki yana zuba masa kud'i a ciki dan baya son yarik'a tara kud'i a bankinsa dan ya tsorata da abinda ya faru.
**** ****
Dogon hutu su Ra'eez suka samu saboda sun zana jarabawa ta aji ukku zasu shiga babban aji idan sun koma, hakan yasa ya rok'i Abbunsa akan ya barshi yazo ko wata d'aya yayi tunda hutun dogo ne.
Alhaji yace Ra'eez wata d'aya yayi maka yawa, Labiba zata wuceka a islamiya da sauran 'yan ajinku, kuma kaga shirye-shiryen sauka kukeyi. Kuka Ra'eez yasa mashi yana rokonsa.
Ummu ce tasa baki tana fad'in tunda Ra'eez ya taso baka tab'a zaman sati biyu dashi ba, baka tsoron rashin mu ya tab'a karantunsa? kabarshi tunda har ya fito ya rok'a yakamata muyi masa wannan alfarmar, karatu ba wani abu bane tunda yana da kok'ari zai iske su, idan yazo nan bazai rik'a fita yawo ba sai yarik'a karatu.
Murmushi Alhaji yayi yana fad'in shikenan Uwargida na amince, nima inaso ya zauna akusa dani, rayuwar Lagos d'ince take bani tsoro shiyasa bana son yazo yayi rayuwa acikinta, nafiso sai ya kammala karatunsa yayi hankali kafin yazo muzauna.
Murmushi tayi tana fad'in nagode. Alhaji yace Ummun Ra'eez nifa ban yarda dake ba, naga kamar kin canza kwana biyu anya babu ajiyata kuwa? Dariya tasa ta rufe fuskarta. Alhaji yace wallahi bazan iya hakura ba tashi muje asibiti aduba idan ma babu komai duk zan gani.
Dariya tayi tace dan Allah ka barni bana son tashi. Mikewa yayi yana fad'in abu mai sauki bara na d'auke ki. Rik'eshi tayi tana fad'in zan fad'a maka. Zama yayi yana fad'in to inajinki. Duk'ar da kai tayi tana fad'in maganarka gaskiya ce, Ra'eez zai samu K'anwa ko K'ani.
Wani irin farin ciki ne ya lullub'e Alhaji, rungumeta yayi yana fad'in narasa bakin magana, Allah yayi maki albarka Bilkisu, tashi muje a duba aga ko wata nawa ne. Tashi tayi tana fad'in tunda kace sai anje muje.
Suna zuwa asibiti aka gano cikin watansa ukku, sosai yayi murna nan suka koma gida. Waya ya d'auka ya kira Alhaji Mansur yana masa albishir. Sosai sukayi farin ciki, anan Alhaji yake fad'ama Alhaji Mansur Ra'eez zeyi hutun wata d'aya anan idan yazo. Alhaji Mansur yace wannan yayi dai-dai, amma idan yazo yarik'a karatu bana son a wuceshi. Alhaji yace insha Allah.
**** ***
Tunda Ra'eez yazo baya zuwa ko ina, iyakar yawansa Malan Sani ya kaishi gidansa wajen Rumaisa wacce yanzu tayi wayau tana a aji ukku firamare, duk lokacin da yaje yana koya mata karatu, idan suka gama Malan Sani ya maidashi.
Sosai yake karatunsa, inda bai gane ba ya tambayi Ummunsa ko Abbunsa, zuwansa hutu suka k'ara shakuwa da Abbunsa, koda yaushe suna tare, yana dawowa ofis suke zama suyi ta fira, wasu abubuwan haka nan Alhaji yake fad'a masa duk da yasan wayonsa bazai d'aukesu ba, amma sanin natsuwar Ra'eez yasa Alhaji yake fad'a masa komai nasa.
Lokacin da hutu ya k'are haka suka had'a masa komai shida Labiba, alokacin Alhaji ya samu hutu sai suka tafi gaba d'aya kano. Sosai Maman Labiba taji dad'in zuwansu ita da Mijinta.
Satinsu biyu a Kano sannan suka koma Lagos cike da kewar juna. Haka Ummun Ra'eez ta aika ma Maman Rumaisa da tsaraba mai yawa, sannan ta aika Malan Sani yaje ya d'auko Ladi, itama ta samu tsaraba sai godiya takeyi.
**** ***
Dube-dube Malan
Hassan yakeyi a wajen daya aje na'urar da su Abubakar suka bashi amma be gani ba, mamaki ne ya kamashi ganin inda ya aje abun babu komai a wajen.
Motsin da yaji ne yasa shi saurin juyawa, Alhaji Marusa ya gani da wani mai aikinsa inyamuri. Jikin Malan Hassan ne ya fara rawa ya fara kok'arin barin wajen.
Alhaji Marusa yace Malan Hassan a iya sanina aikin ka agidan nan shine gadi, ko mai kula da tsaftar wajen nan baya aiki da dare, sai gashi kai kuma kazo wajen da dare bayan nasan bakwa zuwar mani cikin gida, ko dai wani abu ka aje kake nema? Jikin Malan Hassan yana rawa ya fara matsawa da baya.
Kallon wanda suke tare Alhaji Marusa yayi hakan yasa kawai yaje ya damko Malan Hassan, juyawa Alhaji Marusa yayi ya nufi wani b'angarenashi da yake gefe, haka mutumin ya d'auki Malan Hassan suka nufi wajen.
*** ***
Mamaki ne yayi ma Alhaji Maiwada yawa ya kasa furta komai saboda abinda idanuwansa suke gani da abinda kunnuwansa suke ji.
Zaune suke a ofis d'in Alhaji bayan an tashi daga ofis, Moses ne da Abubakar da Alhaji suke kallon abinda Moses ya tara a kamfutarsa wanda ya d'auka.
***
Abinda yafi basu mamaki d'aukar da akayi wajen da ake duba kaya, wani kwali ne aka bud'e na taliya amma ba taliyar bace aciki duka, rabin kayan miyagun kwayoyi ne aciki hada hodar ibilis. Adebayo ne yake waya da Alhaji Marusa yana fad'in kayan sunzo komai lafiya, bayan ya gama ya kalli Umar yana fad'in Alhaji Marusa yace a fitar da kayan yanzu kada abari Sir, ya dubasu tunda anci sa'a bayanan. Umar yace ai tunda Alhaji Marusa yayi ma Alhaji hankali yanzu ya sakar masa mara, kai ko mutum ya rasa katafaren gida irin wannan ai dole ya tsorata, gaskiya Alhaji Marusa bai da imani, gashi dai ya kulla masa sharri kowa ya yarda ya shashi asarar gida, kuma ya saye gidan sannan ya cabke kud'insa ga kayansa babu wanda yayi ciwon kai muma an raba damu.
Adebayo yace Yanzu wannan motar kad'ai ta rage mani acikin kud'in da aka bamu na sallama, kason Mr. Kallah dana Brr. Barau sunfi yawa gashinan har yanzu suna cin abunsu.
Umar yace baka san kason wanda yake da yawa ba, Mr. Kallah da Brr. Barau ba sune masu kaso mai yawa ba, Babban Yallab'ai nashi yafi nasu yawa ai, domin kasan shi baya wahala amma ana bashi kasonshi a duk lokacin da akayi irin wannan harkar. Adebayo yace wai Alhaji Marusa kake nufi? Umar yace bashi ba, wannan ai shine Oga kwata-kwata, babban Yallab'ai nake nufi.
Dariya Adebayo yayi yana fad'in wallayi Umar baka da kyau, har na manta dashi ai, kasan shi baya son asan dashi sai dai yaji kud'i kawai. Umar yace gaskiya muje mu samu Alhaji Marusa ya k'ara mana wani abu asusuna yayi k'asa, kaga dai yanzu bama samun cin hanci. Adebayo yace idan aka d'auki kayan kawai muje.
Hannu Alhaji Maiwada yasa yana goge zufar da ta zuba masa,
***
canza wata d'aukar Moses yayi sai ga Adebayo zaune a mota yana waya da Mr. Kallah....
Yallab'ai wallayi Alhaji Marusa ne yace a fad'a maka anjima kayansa zasu iso kuma wannan karon yace rabin kayan ba wanda ya saba kawowa bane, gashi ta bodar mu yace ashigo dasu kuma yau Sir, yana ofis gashi Abubakar ne yake da aiki yau, d'azu yakira baka d'auka ba shine yace idan na sameka na fad'a maka saboda kayan wannan karon masu tsada ne sosai kuma za'a samu riba, shine yace ka d'auke Abubakar daga wajen shida Sir, hakan ne zaisa a tafi da kayan ba tare da an duba ba.... E, yauwa, sauran ma'aikatan nasan basu da matsala. Toshikenan mun gode.
Murmushin takaici Alhaji Maiwada yayi domin ya tuna ranar da Mr. Kallah yayi masa waya akan suje Abuja shida Abubakar akwai abinda zasuyi, ashe dama wannan harkar zasuyi. Runtse ido yayi yana jin takaici da kayan suka samu wucewa, ya tabbata yanzu sun gama rabar dasu ga dilolinsu.
***
'Dayan d'aukar Moses ya kunna wadda take a gidan Alhaji Marusa. Fitowar farko Alhaji Marusa ne da Brr. Barau, Mr. Kallah sai wani babban mutum wanda ya juya baya ba'a ganin fuskarsa. Zaune suke a saman kujeru gabansu cike da kayan motsa baki.
Yanda yaga suna nutsuwa suna nuna ladabi ga wannan babban mutumin ya tabbatar masa koma waye mai babban matsayi ne.
Muryar Alhaji Marusa sukaji yana fad'in Brr. Ina kara maka godiya akan kok'arin da kayi mana a wancan karon na shari'ata da Alhaji Maiwada, wannan karon ma akwai wata shari'a nida wani abokin kasuwancina, kayansa na cinye kuma ya biyani, to nawa ne bansan ya akayi suka salwanta ba shine naji bazan iya biyansa kud'insa ba sai kawai nace ai rabin kud'in ya bani yace idan na bashi kaya zai cika mani, shine yanzu yake fad'in zai shigar da k'ara, kuma gaskiya kud'in da yawa, ina dasu kawai bana jin zan iya biyansa shiyasa nake son a juya maganar, domin jiya na bashi rabin kud'in kuma na d'auka lokacin da nake bashi.
Muryar babban mutumin sukaji yana fad'in wannan ba wani abu bane na tada hankali, nasan Brr. Barau zai iya da wannan matsalar kawai ka bar masa komai. Brr. Barau yace Yallab'ai duk abinda kace angama ai.
Mr. Kallah yace Alhaji Marusa baka da kyau akan kud'i. Alhaji Marusa yace kud'i ai dole muso su, nifa duk yawan kud'ina banki su linka so goma ba, shiyasa nake so ka d'auke mana wancan jarababben Maiwadan ko harka zata k'ara bud'ewa. Mr. Kallah yace kwantar da hankalin ka k'arshen shekarar nan zan canza masa wajen aiki, gara ya dawo kusa dani kaga hankalin mu zai kwanta. Dariya sukasa gaba d'aya.
***
Wuce wajen Moses yayi, sauran d'aukar duk bata da amfani, wucewa yayi tayi har yazo wani waje, sai kawai sukaga wani babban mutum da ganinsa mai gadin Alhaji Marusa ne, tsaye yake a wajen yana ta dube-dube yana kallon agogon hannunsa wanda suke jin k'arar harbawarsa, da alama wani abu yake nunawa, can kuma sukaji yana fad'in kemera kuma anan? Nasan dai ba Alhaji bane yasata domin da ya sanar dani, hannu sukaga yasa a wajen sai kawai sukaga hoton ya d'auke.
Hannu Moses ya tafa yana fad'in kassh! Wannan banzan ya lalata mana. Zama yayi yana cije baki. Abubakar yace bakomai mun samu abinda muke so, domin ko wannan kad'ai ya ishe mu sheda.
Ajiyar zuciya Alhaji yayi yana fad'in kwashe su duka ka had'a mani a (Flash) in tafi dasu akwai abinda nakeso nayi, dole sai ancire abubuwa marasa amfani abar masu amfani kafin mu gabatar dasu, bana so na bar maka kayi aikin kada tsautsayi yasa wani ya gani, amma idan naje dashi gida nasan acan yafi tsaro domin ni kad'ai ne zanyi aikin.
Moses yace yanzu kuwa Sir, nima bana son su zauna a wajena saboda wallayi tsoro nakeji, zan turasu duka sai na goge komai. Dariya Abubakar yayi yana fad'in kai dama ai sarkin tsoro ne.
Kallonsu Alhaji yayi yana fad'in muryar wannan babban mutumin tayi mun kama da ta wani, naso an d'auko fuskarsa domin koma waye babba ne a k'asar nan, lallai duniya babu gaskiya, amma koma waye idan aka mik'asu kotu zasu fad'esa.
Tabbas na tuna shari'ar da Alhaji Marusa yayi da abokin kasuwancinsa har akace shine yayi nasara, ashe dai shine beda gaskiya, lallai Brr. Barau mutumin banza ne, insha Allahu k'arshen su yazo.
Bayan Moses ya gama ya mik'a ma Alhaji sannan ya goge komai, haka suka fito, sallama yayi masu Malan Sani ya tuk'a suka nufi gida, a hanya Alhaji yake bashi labarin abubuwan da suka faru, sosai Malan Sani yayi mamakin abinda Alhaji ya fad'a masa, dama shi yana zargin Mr. Kallah kawai Alhaji ne ya yarda dashi. haka suka nufi gida Malan Sani yana bashi shawara akan abinda ya kamata.
**** ***
A cikin wani d'aki mai duhu aka jefa Malan Hassan, Alhaji Marusa yace ka barsa nan zuwa safiya zamu bincikesa, wannan babban al'amari ne, yanzu zanyi waya dasu Brr. Barau dole suzo asan abunyi domin ina da tabbacin Alhaji Maiwada ne ya aikosa, kuma tabbas ya kalli wannan d'aukar, idan har ya fito da ita ya gama damu, zan iya yin komai domin na kare mutuncin kai na koda ya had'a da wani ya rasa ransa ne.
Rufe k'ofar da Malan Hassan yake ciki akayi da makulli kafin Alhaji Marusa ya wuce ciki hankali atashe yana neman wayar Mr. Kallah.
Ur's.
Nabeelert Lady🖋
[3/10, 8:38 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud'i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shoot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k'asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub'e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.*
1⃣4⃣
A daren wannan rana Alhaji Maiwada bai samu bacci ba, sai da ya gyara komai ya had'ashi kamar a lokaci guda akayi komai, bayan daya gama ya b'oye wani a cikin kamfutarsa dan guda biyu yayi saboda tsaro, cire flash d'in yayi wanda shine zai kai a kotu, k'asan gadonshi ya b'oyeshi saboda washe gari juma'a yafiso sai litinin sannan yashigar da k'ara kotu dan Brr. Kamal yakeso gobe ya samu suyi maganar kafin litinin.
**
Malan Hassan kuwa gaba d'aya ya tsure, hankalinsa a tashe yake dan yasan halin Alhaji Marusa, akan dukiyarsa babu abinda bazai iya ba, haka ya zauna yana ta fargabar wayewar safiya dan yana tsoron abinda zai faru, babban tashin hankalinsa Iyalinsa, duk da d'azu yayi masu sallama amma besani ba ko zai koma garesu da rai. Haka yayi ta tunani har barci b'arawo yayi gaba dashi.
***
Kasancewar akwai band'aki a cikin d'akin hakan yasa yashiga yayi alwalar asuba, bayan yayi sallah ya zauna yana ta addu'a.
K'arar bud'e k'ofa yaji hakan yasa cikinsa ya d'auki k'ara, ga yunwa dama yanaji dan ko abincin dare beci ba. Alhaji Marusa, Brr. Barau, sai wasu majiya k'arfi guda biyu ne suka shigo d'akin.
Da sauri Malan Hassan yaja da baya yana cira ido, k'ofar suka jawo sannan Alhaji Marusa ya kunna wuta hakan yasa haske ya gauraye d'akin. Waje suka samu shida Brr. Barau suka zauna, sauran mazan kuma suna tsaye sun hard'e hannuwa akirji.
Brr. Barau ne yace yanzu kai tsoho da kai amma ka iya munafurci, da Lucky be gano abinda kayi ba shikenan a jiya kake tunanin d'auke abinda kasa kaje ka kai masu ko? Lallai tsoho ka kira mutuwar ka, dan wallahi bazamu bari ka tarwatsa tamu rayuwar ba tun lokacin mu beyi ba.
Cikin rawar murya Malan Hassan yace na roke ku kuyi mani rai, wallahi ina da iyali, basu da kowa sai ni, idan kuka kasheni zasu shiga matsala.
Alhaji Marusa yace bakasan darajarsu ba shiyasa ka jefa kanka a cikin matsala, mu da kake shirin tona mana asiri ai bamu da Iyali ko? Wallahi kaji na rantse maka ko Matata na samu da irin wannan laifin sai na kasheta, arayuwata bana had'a dukiyata da komai, kana tunanin idan aka mik'amu kotu bazan rasa komai ba? Dan haka inaso ka fad'a mani *WAYE NE*(Tsohon littafina), ya saka wannan aikin? Shiru Malan Hassan yayi jikinsa na rawa.
Brr. Barau yace Alhaji bamu da lokaci, na tabbata wannan abun da sukasa sun riga sun ganshi a can, domin had'awa akeyi, duk abinda yake faruwa anan zasu ganshi a wajensu, muyi abinda yake gaban mu domin muje garesu tun kafin su fitar dashi domin nasan yanzu suna jiran Malan Hassan ya kai masu wannan su had'a dashi.
Alhaji Marusa yace Mr. Kallah yana hanya dan munyi waya dashi, kallon Malan Hassan yayi yana fad'in bazaka fad'a ba? Jiki a sanyaye Malan Hassan yace su Abubakar ne da abokinsa Moses, sunyi ne dan su taimaki Alhaji Maiwada, dan Allah kubarni wallahi nayi maku alk'awari zan kwashe Iyalina mu koma garin mu har abada bazan sake dawowa nan ba.
Murmushi Alhaji Marusa yayi yana fad'in daga baya kenan, kallon Lucky yayi yana fad'in bana son aji labarin gawarsa. Ficewa sukayi shida Brr. Barau. Malan Hassan duk rokon da yake masu sai da suka kashe shi, nad'eshi sukayi suka d'aukeshi zuwa mota suka nufi bayan gari suka binneshi.
***
Abbun Ra'eez ka tasa abinci kana kallo ka kasa ci, kuma na tambayeka kayi mani shiru, anya babu abinda yake faruwa kuwa? Ajiyar zuciya ya saki yana fad'in Bilkisu dole na bar wannan aikin, dole mubar garin nan ina aje aikina, wallahi aikin Kwastam ya fice mani, nayi danasanin fara yinsa.
Matsowa tayi tana fad'in haba Abbun Ra'eez ya zaka fad'i haka, tun jiya dama nake ganin ka wani iri, dan Allah ka fad'a mani abinda yake faruwa kila ina da abinda zan taimaka maka dashi.
Beyi magana ba ya fara cin abincinsa, sai da yaci rabi sannan ya aje, hannunta ya kama suka nufi d'aki. Bayan sun zauna ya kalleta yana fad'in Bilkisu kicigaba da tayani addu'a domin Allah ya fara haska mani wad'an da suke bibiyata da sharri. Murmushi ta saki tana fad'in kai amma naji dad'i, meya faru? Wayarsa ce tayi k'ara hakan yasa yayi shiru ya d'auka.
Alhaji Mansur ne, bayan sun gaisa yake tambayar Alhaji k'arin bayani akan sakon daya tura masa jiya? Gyara zama Alhaji Maiwada yayi yana fad'in wallahi jiya na gama aiki naji bazan iya kwanciya batare dana fad'a maka abun farin cikin da nake ciki ba........
Labarin komai ya fad'ama Alhaji Mansur Ummu tana gefe tayi tagumi tana jin abun al'ajabi. Bayan ya gama Alhaji Mansur yace Allah mungode maka, lallai Allah shine abin godiya, abinda nakeso da kai kada ka bari wannan maganar ta fita, Malan Sani nasanshi beda matsala, sannan kayi magana da Brr. Kamal zuwa litinin zan biyo jirgi domin ayi komai ina nan, wallahi kaji na rantse bazamu yarda ba sai an bi maka hakkin ka, wannan gidan daya anshe maka sai ya maidoshi, sai a maida masa kud'insa.
Alhaji yace insha Allahu zanyi yanda kace, Allah ya kaimu litinin d'in. Alhaji yace amin. Sallama sukayi yana fad'in sai ya sake kira. Hannunshi Ummu ta kamo tana fad'in yanzu kam na goyi bayanka akan maganar aje aiki, ana kammala shari'ar nan ka aje masu aikinsu, wannan gidan ma kasayar dashi mu koma Kano da zama, Malan Sani ma nasan zai bimu kawai mutafi dasu bazamu sake waiwayar Lagos ba.
Murmushi Alhaji yayi yana fad'in insha Allahu aikina yazo k'arshe, abinda na tara ya ishe ni, Allah ya albarkaci abinda zan samu anan gaba. Ummu tace amin.
**** ****
Zaune suke su Ukku, Brr. Barau, Mr. Kallah da Alhaji Marusa, magana suke akan yanda zasu b'ulloma wannan abun. Alhaji Marusa ne yace abinda nake gani kawai mu kawar da Alhaji Maiwada. Zaro ido Mr. Kallah yayi yana fad'in kasan abinda kake fad'a kuwa? Brr. Barau yace wannan itace mafita, dole ya mutu kuma mu anshe shedar da take wajensa, hatta da wannan direban nasa bazamu bari ba saboda yasan komai.
Girgiza kai Mr. Kallah yayi yana fad'in maganar gaskiya bazan iya aikata kisan kai ba, duk son kud'ina bai kai nayi kisan kai ba, ina laifin mu saceshi tare da matarsa har sai ya kawo mana duk wata sheda da yake da ita.
Murmushi Alhaji Marusa yayi yana fad'in Mr. Kallah ka manta waye ni, to Malan Hassan ma da aka ba aikin tuni ya tsufa arami. A zabure Mr. Kallah ya mik'e yana fad'in haba Alhaji Marusa, duk da ban kasance musulmi ba nasan kisa ba abu bane mai kyau, me yayi mana? Sheda ce yake da ita kuma muna da hanyar da zamu karb'eta.
Tashi Alhaji Marusa yayi fuska a d'aure yana fad'in Mr. Kallah bana so mu fara haka da kai, kasan yanda muka dad'e da kai muna harka, bana so saboda wannan k'aramun abun mu samu matsala, kasan dai tunda muka san sirrin juna dole mucigaba da tarayya, dan haka ka amince da abinda muka fad'a.
Murmushi Mr. Kallah ya saki ya kamo hannun Alhaji Marusa yana fad'in haba abokina ai wannan abun bazai lalata tarayyar mu ta shekara da shekaru ba, ka sani nima bazanso asirin mu ya tonu ba, shikenan ayi abinda kukace.
Murmushi Alhaji Marusa ya saki yana fad'in ko kai fa abokina, wannan hanyar ita kad'ai zamubi mu rufe wannan maganar, domin Allah kad'ai yasan iya abinda suka samu akan mu.
Brr. Barau yace amma ya zamuyi dasu Abubakar da Moses? Alhaji Marusa yace zasubi wanda sukasa aikin ne. Mr. Kallah yace kisan zaiyi yawa fa, kasan yanda jini yake zai iya binmu, abinda zaifi zanyi masu canjin wajen aiki, kuma zamusa su Lucky suyi masu barazana akan abinda sukayi.
Brr. Barau yace shikenan ayi hakan na yarda da kai. Alhaji Marusa yace duk ranar da wani abu ya faru babu ruwana. Mr. Kallah yace babu abinda zai faru ma.
Wayar Brr. Barau ce tayi k'ara, yana dubawa ya kallesu yana fad'in babban 'yallab'ai ne bara naji abinda zai fad'a kunsan kiransa samu ne.
Saurin tashi yayi yana fad'in shikenan 'Yallab'ai ka kwantar da hankalin ka zanji da wannan abun, wanda ya fishi ma muna rufewa bare kuma yau ya had'o da kai, shikenan zamuzo anjima akwai wata magana da zamuyi dama.
Kashe wayar yayi ya zauna yana fad'in wata sabuwa. Alhaji Marusa yace meya faru kuma? Brr. Barau yace kunsan akwai Yaron wajen 'Yallab'ai na biyu mai suna Fawwaz ko? Kai suka jinjina.
Brr. Barau yace wallahi wani tsautsayi ne ya faru dashi, yaron yana makarantar *King's collage* ne, kunsan yaran zamani akwai wauta, tsautsayi yasa sukayi fad'a da wani abokinsa akan mace shine fa ya yankeshi da wuk'a a wuya ajali yana kusa yaron ya mutu, 'Yallab'ai yace agaban mutum biyu akayi abun yanzu haka sun wurgar da gawar a wani waje, to sauran mutum biyun manyan abokansa ne nasan bazasu tab'a tona masa asiri ba, to amma d'aya daga cikinsu yace yaga wani d'an ajinsu kamar yana d'aukarsu alokacin da akayi abun, domin yaga lokacin daya fito ya ruga, shine hankalin 'Yallab'ai ya tashi, domin idan wannan maganar ta fito zai rasa kimarsa, toshine yace naje yana nemana.
Jinjina kai Mr. Kallah yayi yana fad'in lallai wannan babbar magana ce, abinda ya sameshi ai ya same mu ne, dan haka kutashi muje yanzu sai mu gama komai kawai.
**** ***
*Naseer* ne ya fito daga gidansu hankali atashe, ya rasa wanda zai nuna ma wannan abun daya d'auka, haka Allah yayishi da tsoro gashi yaje ya gano abinda yafi k'arfinsa har ya d'auko saboda ya nuna sheda, domin yaron da aka kashe abokinsa ne suna gaisawa.
Kallon wayarsa yayi yana tunanin wanda ya kamata ya nuna ma wannan abun, ko a gidansu babu wanda yasani, shiyasa ya fito kada Mamansa ta ganoshi. Tunani yayi ko dai ya kaima Baban Fawwaz tunda babban mutum ne yasan dole ya d'auki mataki akanshi.
Jinjina kai yayi cike da gamsuwa, wayarsa yasa aljihu yana fad'in bara yayi sallah yaje ya kaimasa shima ya huta. (Allah sarki Naseer yarinta ta hana ka gane tsakanin Uba da 'Dahsai Allah🤦🏻♀) .
***
Lokacin da yaje gidansu Fawwaz Maigadin gidan ya samu, bayan sun gaisa ya fad'a masa d'an makarantar su Fawwaz ne malaminsu ya aikoshi wajen Babansu. Murmushi maigadi yayi yace aikuwa Alhajin yayi baki suna lambu suna ganawa, amma tunda sako zaka bayar kaje ka fad'a masa kada na tsaida ka bansan lokacin da zasu gama ba.
Godiya Naseer yayi masa yashiga, babu wanda ya ganshi har ya d'auki hanyar lambu, yana dab da zai isa wajensu yaji muryar Brr. Barau yana fad'in 'Yallab'ai ba ance sunan yaron daya d'auki kisan Naseer ba? Abinda zaifi anemoshi a daren yau a kashe shi kawai.
Hannu Naseer yasa ya dafe kirjinsa jin abinda aka fad'a, har ya juya zai gudu sai kuma jarumta tazo masa, wayarsa ya d'auko ya kamo wajen ya matsa kusa dasu yanda zai d'auka da kyau ya b'oye yana d'aukar su.
Mr. Kallah yace wai Brr. Barau meyasa fad'in kisa baya maka wahala ne, kace akashe Alhaji Maiwada, sannan kuma k'aramin yaro kace akashe shi Allah fa zai kama ka.
Alhaji Marusa yace Mr. Kallah yanzu idan yaron ka ne aka ce ya aikata haka zaka bari a yanke masa hukuncin kisa bayan be gama more rayuwarsa ba? Brr. Barau yace Fawwaz shekararsa 19 ya isa ya d'auki kowane hukunci, tunda aji shidda yake yanzu gab suke da gamawa domin jarabawa suke zanawa, Mr. Kallah kayi tunani mana, mu da 'Yallab'ai mun saba tonawa mu rufe domin zaman lafiyar mu, idan asirin wani ya tonu acikin mu gaba d'ayan mu ya shafa.
Jinjina kai Mr. Kallah yayi yana fad'in haka ne, yanzu ya kuke gani za'ayi? Alhaji Marusa yace ayau za'a kashe su duka, Abubakar da Moses na tura su Lucky tun d'azu ina da tabbacin sun kamasu yanzu, zanyi magana da Peter 'Yallab'ai ka tambayar mana kwatancen gidan su Naseer zaije ya d'aukoshi za'a shafe babinsa, shi kuma Alhaji Maiwada su Lucky zasu kaddamar masa anjima bayan ya taso daga wajen aiki.
Dariya Brr. Barau yasa yana fad'in shugaban kwastam ake fad'a maka, daga yau bamu da sauran tashin hankali, Alhaji zaka cigaba da tafiyar da kasuwancinka yanda kakeso, muma zamu k'ara hannun jari domin ya bunk'asa.
'Yallab'ai yace wannan haka yake, dama dole kasa rigar mutunci ka b'oye zahirin ka idan kana so ka zauna lafiya da mutane, domin yanzu mutum ake kiwo ba dabba ba, nafi son mutuncina so dubu.
Mr. Kallah yace amma akwai abokan Fawwaz da kace sun san komai, baka tunanin yanayi yasa su tona? Brr. Barau yace bazasu iya tona komai ba, kawai zanyi magana dasu akan su manta da komai, 'Yallab'ai dole a fitar da Fawwaz waje yayi karatu hakan zaisa hankalinsa ya kwanta.
Jinjina kai 'Yallab'ai yayi yana fad'in nagode sosai, kuma zanyi hakan, abinda nakeso mu k'ara rik'e sirrin junan mu, Brr. Barau kayi mani alkhairi da yawa arayuwa, abu d'aya zanyi maka wanda zan saka maka, kaine zaka zamto *ALKALIN GOBE* na babbar kotun ku. Murmushi Brr. Barau yayi yana fad'in nagode Allah ya saka, ashe zan kai wannan matsayin.
Jiki na rawa Naseer ya baro wajen, gaba d'aya zufa ta gama rufeshi, ko takan Maigadi bebi ba yayi hanyar waje, Maigadi yana tambayarsa ya bada sakon amma be saurareshi ba yayi waje da gudu.
Kai tsaye d'akinsa ya shige ya saki kuka, ya dad'e yana kuka kafin ya d'auko Flash ya jona da wayarsa, gaba d'aya abinda ya d'auka ya tura, kayan jikinsa ya canza ya b'oye Flash d'in a aljihu ya fito.
Mamansa ce ta kalleshi tana fad'in Naseer wai yau lafiyar ka kuwa? Murmushi yayi yana fad'in lafiya lau Mama. Dama zanje gidansu Mannir na amso littafina saboda muna da jarabawa da safe ranar litinin a makaranta na mantoshi a ajakarsa.
Jinjina kai tayi tana fad'in yanzu za'ayi kiran sallar magriba ka biya masallaci kayi sallah kafin ka wuce, kuma kasan yanda unguwarsu take da ka bari ma sai da safe. Naseer yace bazan dad'e ba Mama. Murmushi tayi tace shikenan kaje kayi sallah. Naseer yace to Mama yanzu zanyi. Har ya kai bakin k'ofa Mamansa ta kirashi, dawowa yayi yana fad'in gani.
Ido ta tsura masa kafin tace Naseer kamar akwai abinda kake b'oye mani ko? Saurin girgiza kai yayi yana fad'in bakomai Mama. Murmushi tayi tana fad'in shikenan ai nasan baka mani k'arya, Allah ya tsare ka gaishe da Mannir d'in.
***
Risnawa Maigadi yayi yana fad'in barkan ku da fitowa, hannu Alhaji Marusa yasa aljihu ya ciro kud'i yana fad'in ga wannan anci goro ko. Amsa yayi yana masa godiya. Har sun kai bakin k'ofa Maigadi yace 'Yallab'ai wannan yaron ya samu ganin ka kuwa? Cak suka tsaya jin abinda yace.
'Yallab'ai yace wane yaro kenan? Maigadi yace d'azu wani yaro yazo yace yana nemanka shine nace kana da baki, sai yace sako zai baka inji malaminsu, shine nace kuna lambu yaje ya sameka, to bayan wani lokaci ina zaune sai kawai naga yaron ya fito a firgice, yanayin yanda naganshi yasa na taso ina tambayarsa ya ganka, amma be tsaya saurarata ba yayi waje a guje, to da yake bansan yanda kukayi ba shiyasa na kyaleshi na zauna.
Gaba d'ayansu hankalinsu ne ya tashi jin binda Maigadi ya fad'a. Brr. Barau ne yace a ina Yaron yace maka yake? Maigadi yace ni dai yace mun d'an ajinsu Fawwaz ne. Dam... Gabansu ya sake fad'uwa.
Da sauri suka fita waje hankali tashe. Da kallon mamaki Maigadi ya bisu ganin yanda hankalinsu ya tashi.
Dafe kai 'Yallab'ai yayi yana fad'in duk yanda akayi wannan yaron turoshi akayi. Brr. Barau yace ba lallai turosa akayi ba, nafi tunanin yazo wajenka domin ya fad'a maka abinda ya faru, sai kuma yaci sa'ar sauraron abinda muke tattaunawa wanda ya tada hankalinsa ya kasa ganinka ya fita da sauri, abin tambayar anan shine, ya d'auki abinda muke tattaunawa akai ko kuwa saurara kawai yayi? Alhaji Marusa yace koma menene bazamu barshi ba, dole anemoshi kuma a amso wannan shedar daya d'auka.
Waya ya ciro yana fad'in bara nakira Lucky. Bayan ya d'auka Alhaji Marusa ya bashi umarnin su nemo Naseer a duk inda yake, su kashe shi kuma su amso wayarsa.
Peter ya kira anan yake fad'a masa ya baza yaranshi su jiran Alhaji Maiwada ya fito su k'addamar masa. Godiya yayi masu ya kashe wayar.
Fawwaz ne yazo wucewa shida abokansa, risnawa sukayi suka gayar dasu Alhaji, duk sai Fawwaz ya tsargu ganin fuskokinsu d'auke da damuwa. Dadynsa ne yayi kiransa, bayan yazo ya tambayesa unguwar su Naseer. Fad'a masa yayi, Brr. Barau yace baka da hotonsa? Fawwaz yace akwai, wayarsa ya d'auko ya nuna masu, amsa Alhaji Marusa yayi nan take ya tura awayarsa, bayan sun shiga Alhaji Marusa ya turama Lucky had'e da kwatancen unguwar.
Brr. Barau yace zamu wuce 'Yallab'ai ka kwantar da hankalinka babu abinda zai faru, anjima zan dawo domin in gana da abokan Fawwaz hada shima. Godiya yayi masu yana fad'in ab'atar da duk wata sheda. Alhaji Marusa yace wannan ba matsala bane nasan yarana.
****
Bayan an gama sallar magriba kafin Naseer ya fito yaji ana sanarwar mutuwar abokinsa wanda aka tsinci gawarsa a cikin daji saboda unguwarsu d'aya. Runtse ido Naseer yayi hawaye suka zubo masa, da sauri yazo fita sai yaji an dafashi, yana juyowa yaga wani abokinsa ne makwafcinsu.
Hannu yasa ya goge idonshi yana fad'in Saddik ya gidan? Saddik yace lafiya lau Naseer, naji wanda aka fad'a ya rasu a makarantar ku yake ko? Kai Naseer ya jinjina masa. Saddik yace Allah yajik'ansa, cike da k'osawa Naseer yace amin kafin ya fice.
Wayarsa ya d'auka ya kirawo abokinsa Mannir, yana d'auka Naseer yace Mannir kana gida? Mannir yace ina gida lafiya naji muryarka wani iri? Naseer yace akwai wata magana da nakeso na fad'a maka akan mutuwar abokin mu amma ka jirani agida yanzu zanzo. Mannir yace shikenan sai kazo.
Mota ya tare ya hau yana fad'in dan Allah Malan ofis d'in shugaban kwastam zaka kaini, jiyowa mai motar yayi yana fad'in sai dai na ajeka bakin titi domin bana son harka da kwastam. Naseer yace bakomai muje.
Tafiya suke sai mai motar yaga kamar ana binsu, kallon Naseer yayi yana fad'in nifa jikina yana bani wani abu, sai nake ganin kamar ana binka, kodai ka d'auko wasu kud'i ne? Naseer yace ba wasu kud'i kawai ka tsargu ne.
Lucky ne ya kira Alhaji Marusa ya fad'a masa sun samu yaron mma sunga kamar ya d'auki hanyar ofis d'in Kwastam. Alhaji Marusa yace kuyi a hankali kunga dai dare beyi ba sosai, bana so kuzo ba tare da kungama komai ba.
Tsayawa direban yayi yana fad'in iya nan zan tsaya sai ka k'arasa. Kud'i Naseer ya bashi yana fad'in nagode. Tafiya ya fara gabanshi yana fad'uwa, yanaso yaje ya tambaya a nuna masa shugaban Kwastam dan shine yaji su Alhaji suna maganar za'a kashe, gara yaje ya fad'a masa yasan kila shima ya samu kariya, gashi ko ganinshi bai tab'ayi ba ballantana ya ganeshi, dole sai yayi tambaya.
***
Alhaji Maiwada bayan ya gama aikinsa ya fito, sallama sukayi da Malan Bala yana fad'in gobe bazan shigo aiki ba sai litinin, a gyara ofis d'in da kyau. Malan Bala yace insha Allahu. Kud'i Alhaji ya ciro ya mik'a masa yana fad'in gashi kayi kud'in mota kayi cefane naga wata ya raba tsakiya. Godiya sosai Malan Bala yayi masa, har bakin mota ya rakoshi.
Ganin su Abubakar da Moses yasa ya tsaya, k'arasowa sukayi suna fad'in har yanzu basu samu wayar Malan Hassan ba, kuma agidanshi ance bai koma ba. Moses yace ina tunanin wani abu, ko dai sun kamashi ne suka kulle? Alhaji yace insha Allahu babu abinda zasuyi masa, gobe zamuje can gidanshi muji. Godiya saukayi tare da masu sallama yashiga mota Malan Sani yaja suka tafi.
Su Moses suna barin wajen kasancewar a motar Abubakar suke, bayan sunyi nisa yaran Peter suka tare su, nan take suka shiga motar suka bar wajen dasu bayan sun watsa masu wata hoda.
**
A hanya Alhaji yana gyara wasu aiyuka a cikin kamfutarsa yake fad'ama Malan Sani yanda sukayi da Alhaji Mansur. Malan Sani yace Alhaji ni har wannan kamfutar ma da kadena fitowa da ita kasan akwai abu mai muhimmanci aciki. Alhaji yace ai babu wanda yasan yanda ake bud'eta, kuma natura shedar a Flash saboda tsaro. Malan Sani yace hakan dai yafi.
***
Jikin Naseer ne ya fara rawa ganin kamar ana binsa, nan take tsoro ya kamashi sai ya baza da gudu yana tunanin ya koma gida kada garin neman shugaban kwastam akamashi, haka kawai ma yaje garin tambaya wani yace shine sai ya fad'a masa gaskiya a kamashi tunda duniyar babu gaskiya, gudu yake aranshi yana fad'in babu wanda zan tambaya gara naje na fara saninshi a hoto kafin naje wajensa.
***
Birki Malan Sani ya taka da sauri ganin mutum ya faad'o masa. Alhaji yace lafiya dai Malan Sani? Bud'e motar Naseer yayi ya shige sai haki yake yana fad'in dan Allah ku taimaka mani wasu ne suka biyo ni.
Alhaji yace ikon Allah! Kai ko yaro meya had'aka dasu? Naseer yace kawai 'yan iskan gari ne. Malan Sani yace ka tabbata abinda ka fad'a gaskiya ne? Naseer yace wallahi da gaske nakeyi. Alhaji yace tuk'a muje.
Malan Sani yace Alhaji... Hannu ya d'aga mashi hakan yasa yaja suka tafi. Naseer yayi masu kwatancen unguwar su Mannir, kasancewar hanyar gidansu bata da kyau Malan Sani yace sai dai mu ajeka bakin hanya dan yasan unguwar bata da kyau. Naseer yace hakan ma yayi nagode.
***
Waya Lucky yakira Alhaji Marusa yana fad'a masa yaron yashiga motar su Alhaji Maiwada. A firgice Alhaji Marusa ya mik'e yana fad'in mene? Wallahi idan kuka bari ya sha sai na kashe ku, inaso kushiga gabansu yaron yana fita ku gama dashi, shima Alhaji bazai sha ba yana barin wajen su Peter zasu k'addamar masa.
**
Malan Sani ne yace Alhaji kaji labarin wani yaro da aka kashe ko? Alhaji yace wallahi d'azu nakejin labari, kai zamanin nan ran mutum ba abakin komai yake ba. Naseer yace ai abokin mu ne makarantar mu d'aya. Alhaji yace Allah sarki, Allah yajikansa ya tona asirin wad'an da suka kashe shi. Naseer yace amin. Yana so ya fad'a masu gaskiya yana jin tsoro hakan yasa yaja bakinsa yayi shiru.
Suna zuwa bakin hanya Malan Sani ya tsaya yana fad'in kayi sauri ka wuce kasan dai wannan hanyar bata da kyau. Godiya Naseer yayi masu, jiyowa yayi yana fad'in Abba nagode. Murmushi Alhaji yayi masa yace bakomai ka kiyaye ka daina kaiwa dare a waje kaji. Kud'i ya bashi yana fad'in ga wannan kasa kati.
Godiya Naseer yayi masa, haka kawai yaji ya yarda da mutumin, sai yayi tunanin ya b'oye Flash d'in amotarsa yasan zai gani, idan ya gani zai taimaka. Hannu yasa ya zaro Flash d'in, a hankali ya turashi k'asan kujerar baya ya fita.
Kan motar Malan Sani ya juya yana fad'in wallahi shiyasa nake jin dad'i da Ra'eez baya zama agarin nan, kallifa ko isha'i ba'ayi ba amma an fara bin mutane. Alhaji yace kai dai sai addu'a, shiyasa nace maka muna gama wannan shari'ar zan aje aikina na bar garin nan. Malan Sani yace ai k'afarka k'afata Alhaji, domin bazanji dad'in zaman garin nan ba idan bakanan.
Alhaji zaiyi magana kenan sukaji motarsu tana rawa alamun taya ta samu matsala. Malan Sani yace kila kuwa mun taka k'usa, Alhaji yace tsaya mugani. Malan Sani yace gara mu tuk'ata ahaka wajen nan beda kyau kuma babu mutane. Alhaji yace Malan Sani kaci ka tsoro, dare fa beyi ba gara mu canza wata tayar zaifi.
***
Taku ukku Naseer yayi yaji an damkoshi, baki ya bud'e zeyi ihu aka rufe bakin, d'aukarshi sukayi zuwa cikin motarsu. Kasancewar motar bakin gilashi ne yasa ba'aganin na ciki.
Mari Lucky ya d'auke Naseer dashi yana fad'in mai ka fad'ama Alhaji Maiwada? Cikin firgici Naseer ya kallesu yana fad'in waye haka kuma? Lucky yace motar data ajeka yanzu ai shugaban kwastam ne aciki meya had'a ka dashi? Farin ciki ne ya kama Naseer jin ya aje shedarsa a inda ta dace, kuma ko zasu kashe shi bazai fad'a masu abinda ya aje ba.
Dukan da akayi masa yasa ya dawo daga tunanin da yakeyi. Cikin wahala yace wallahi babu abinda na fad'a masa ni bamma sanshi ba kawai ragemun hanya sukayi dama wajen shugaban kwastam zanje sai kuma tsoro ya hanani k'arasawa shine na dawo sai muka had'u suka d'aukoni.
Amsar wayarsa Lucky yayi, yana dubawa yaga abinda ya d'auka duka suna nan, waya ya kira Alhaji Marusa ya fad'a mashi, murmushi yayi yace ku gama dashi kuma ku jefar da gawarsa, banaso ku rifeta ku barta domin Iyayensa su masa sallah.
Duk magiyar da Naseer yake masu haka suka kashe shi suka ja motar zuwa inda zasu yarda shi sukayi tafiyarsu da wayarsa bayan sun cire layin sun yona rami sun rufe.
***
Cike da tsoro Alhaji yake kallon mutanan da suke tun karosu, Malan Sani yace Alhaji kana ganin abinda nake gani kuwa? Alhaji yace dama tunda su Moses sukace Malan Hassan ya b'ace jikina ya bani kamashi akayi, sun gano komai shine suka turo akashe mu. Abinda nakeso da kai Malan Sano ka fita da gudu kai ka tsira.
Malan Sani yace ka daina fad'ar haka, bazan barka anan ba. Alhaji yace dole wani ya tsira acikin mu, Bilkisu da Ra'eez basu da kowa sai ni, idan suka kasheni zasu iya zuwa su kashe ta, Ra'eez zai taso cikin maraici, inaso kaje ka fitar da ita daga gidan nan, inaso ka kula mani dasu domin rayuwata suke nema ba taka ba, idan ka tsaya zasu had'a da kai.
Kuka Malan Sani yasa yana mai rik'e da hannun Alhaji.Kamfutarsa ya miko masa yana fad'in jeka da ita, ka tabbatar ka fitar da Bilkisu, kace ta yafe mun kuma tayi hakuri da rayuwa, Allah ya albarkaci abinda zata haifa, kuma kuyi kok'arin barin garin nan kada kuzauna aciki dan Allah, ka shafa mani kan Rumaisa da Ra'eez.
Kuka kawai Malan Sani yake haka ya fita daga motar, kasancewar bata b'angaren da suke taho yake ba hakan yasa ya gangare basu ganshi ba, wani daga cikinsu ne ya hango giccensa nan ya fad'ama Peter.
Kafin su k'arasa ya kira Alhaji Marusa ya fad'a masa direban ya gudu hada jakar kamfuta a hannunsa. Alhaji yace nasan gidan Alhaii Maiwada zaije domin ya ceci matarsa, kuji da Alhajin zain tira su Lucky gidan yanzu, nasan zasu rigashi zuwa tunda da mota hannunsu shima zasu kasheshi.
Fito da Alhaji sukayi, yana rok'on su amma basu saurareshi ba, wani kyalle sukasa suka nad'e mashi wuya dashi har sai da yadena numfashi. Wurgashi cikin motar sukayi suka bar wajen.
**
Brr. Barau ne yayi kiransu Lucky ya basu umarnin kada su kashe Malan Sani su barshi sun canza shawara, kawai sujirashi agidan yazo su amso kamfutar su fito.
Ur's.
Nabeelert Lady🖋[3/10, 8:38 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud'i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shoot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k'asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub'e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.*
1⃣5⃣
Tsayawa Malan Sani yayi yana hutawa sai dube-dube yake, hawaye kawai suke zubo masa, shikenan yanzu sun kashe Alhaji, kai duniya. Hannu yasa ya ciro wayarsa, Alhaji Mansur ya kira, yana d'auka ya sake fashewa da kuka.
Hankali tashe Alhaji Mansur yake tambayarsa abinda yake faruwa. Tsagaita kukansa yayi ya fad'a masa abinda ya faru. Salati Alhaji Mansur yasa jikinsa yana rawa.
Malan Sani yace yanzu haka ina hanya inaso na k'arasa can gidansa na tafi da Hajiya. Alhaji Mansur yace kaga tana d'auke ta juna biyu, kayi yanda hankalinta bazai tashi ba dan Allah, kuma shima Alhajin insha Allahu babu abinda zasuyi masa, gobe da wuri zan iso, Allah ya tsare ku gaba d'aya.
Mota Malan Sani ya tare yana saka wayarsa aljihu. Gani yake kamar mai motar baya gudu, addu'a kawai yake Allah yasa basu yima Alhaji komai ba.
***
Ta bayan gidan suka shiga dan Alhaji Marusa yace baya so Maigadi yasan da zuwan su saboda Brr. Barau ya had'a wani shiri ta yanda zasu fita daga zargi.
Ummun Ra'eez tana zaune a falo sai gwada kiran wayar Alhaji take amma taki shiga, duk da tasan yana wuce haka bedawo ba amma kafin ya baro ofis sunyi waya yace ta dafa masa kwai guda ukku zaici abinci dasu.
Gashi Ladi bata nan taje Kauyensu ana biki sai litinin ma zata dawo. Wayar ta aje tana mai jin wani irin sanyi yana shigarta, rufe ido tayi tana karanto duk addu'ar data zo mata.
**
Madu ne ya bud'e k'ofa jin k'arar bugawa, mamaki yayi ganin Malan Sani shi kad'ai ga idanuwansa duk sun kumbura.
Shigowa Malan Sani yayi yana fad'in Madu akwai matsala fa. Madu yace matsalar me ina Alhajin? Malan Sani yace ina zuwa bara na fito. Be jira abinda zai fad'a ba yayi gaba. Zama Madu yayi yana fad'in ikon Allah, wace matsala ce kuma wannan? Taya Malan Sani zai dawo shi kad'ai kuma, ga jaka a hannunsa kamar ta kud'i, sannan idanuwanshi duk sunyi ja kamar wanda ya shawu, ko dai Alhajin ne ya aikosa? Amma da mamaki, Redionsa ya jawo yana fad'in bari ya fito muji.
Bayan Ummu ta bud'e k'ofar sai taji gabanta ya fad'i ganin Malan Sani d'auke da bak'ar jaka ta kamfutar Alhaji. Batayi magana ba ta shiga ciki tana fad'in shigo mana.
Shiga yayi ba tare daya rufe k'ofar ba. Zama Ummu tayi tana fad'in Malan Sani Abbun Ra'eez ko aiki ya rik'esa ne? Duk'ar da kai yayi hawaye suna cika masa ido yace shine ya aiko ni na d'auke ki mu tafi can gidana gobe kuma zamu wuce kano.
Zatayi magana kenan sukaji alamun motsin shigowa, dama zaman jiran Malan Sani sukeyi kuma aka ci sa'a be rufe k'ofar ba.
Saurin mik'ewa sukayi ganin manyan mutane a cikin gidan. Hannu Ummu tasa ta dafe cikinta tana fad'in Malan Sani kace mun sun kashe Alhaji kawai, gashinan kaima kuka kakeyi, meyasa zasuyi mani haka, ina gawarsa take dan Allah? Kuka Malan Sani yasa yana kallon su yace narok'e ku da girman Allah kada ku kashe ta, ku kasheni amma kubarta ita da abinda yake cikinta.
Zuciya ce ta ciyo Ummun Ra'eez ta rarumi flask d'in ruwan zafi da yake kusa da ita ta wurga ma Lucky, saurin kaucewa yayi cikin zafin nama ya kwad'a mata sandar da take hannunsa akai.
K'ara Ummu ta saki ta fad'i da k'arfi saman cikinta, nan take jini ya b'alle mata. Salati Malan Sani yasa yayi kanta da sauri, kamota yayi yana jijjigata amma babu alamun rai ajikinta, ga kanta yana fitar da jini k'asanta ma jini na fita.
Kuka yake yana fad'in baku da imani, me wannan matar tayi maku. Tsaki Lucky yayi danshi baya b'ata lokaci a aikinsa. Wata hoda ya fesama Malan Sani nan take yaji kanshi yayi nauyi, hannu yasa ya dafe kanshi yana jin yanda falon yake juya masa.
Duk'awa Lucky yayi ya kama hannun Malan Sani ya kamo na Ummun Ra'eez, Malan Sani yana kallonsa amma jikinsa ba kwari, hannun Ummun Ra'eez yasa a wuyan Malan Sani ya karceshi da faratan ta da bata yanke ba, nan take sahu ya fito harda jini.
D'aukar jakar kamfutar sukayi suka kamo Malan Sani suka fito dashi sai layi yake dan sam baya cikin hankalinsa. Turashi sukayi hanyar gate, sai da sukaga ya kama hanya yana tafiya yana layi kafin suka fice ta bayan gidan.
Saurin tasowa Madu yayi ganin Malan Sani yana tangad'i, kamoshi yayi yana fad'in lafi... Tsayawa maganar tayi ganin jini a jikinsa, zeyi magana Malan Sani ya tureshi har sai da ya faad'i yayi tafiyarsa ya fice daga gidan.
Yana fita su Lucky suna jiransa bakin k'ofa, saurin kamashi sukayi sukasa a mota suka tafi. Koda Madu ya lek'a sai kurar motar ya iske.
Mamaki ne ya kamashi, me yasamu Malan Sani haka? Me ya aikata acikin gida tunda yasan Ladi bata nan? Ga jini ajikinsa, ko dai wani abu yayima Hajiya? Ai kuma yaso yaji ihu, Saurin komawa Madu yayi, cikin gidan ya nufa jikinsa sai rawa yakeyi.
Yana shiga falo yayi mutuwar tsaye, da sauri ya fito yana gudu yayi wajen gidan yana neman taimako. Makwabcin su ya gani shida abokinsa, da sauri ya k'arasa wajensu jikinsa na kyarma.
Tsayawa sukayi ganin Madu. Makwabcinsu mai suna *Alhaji Musa* yace Madu lafiya kuwa? Kuka Madu yasa yana nuna masu cikin gidan. Mamaki ne ya kamasu sukace meya faru? Madu yace ya kasheta wallahi gata can a kwance cikin jini Alhaji.
Wanda aka kira da Alhaji yace waye ya kashe ta kuma wa aka kashe? Madu yace Hajiya ce, Malan Sani ne yashigo kuma shi kad'ai ya dawo ba tare da Alhaji ba, hannunsa d'auke da jaka kamar ta kud'i, yana shiga cikin gidan sai ihun Hajiya naji, band'au ka wani abu bane ina zaune sai gashi ya fito jikinsa duk jini, dana rik'esa saiya tureni ya fito, kafin na fito wata b'akar mota ta d'aukeshi sun bar wajen.
Abokin Alhaji yace tabbas naga bak'ar mota har nake maka magana nace mai motar can yana tukin hauka ashe da abinda suke ma sauri.
Ajiyar zuciya Alhaji yayi yana fad'in lallai duniya babu gaskiya, yanzu bazamu shiga gidan ba, bara nayi waya a turo 'yan sanda idan suka zo sai mushiga saboda tsaro.
***
Sai da suka d'auki yaron daya gano masu gidan Malan Sani sannan suka wuce unguwarsu, har k'ofar gida suka kaishi, kuma sukaci sa'a ba mutane a wajen, ajeshi sukayi suka kama gabansu.
Cikin layi Malan Sani ya k'arasa cikin gidansa yana rik'e da kanshi. Halima da Rumaisa suna zaune tsakar gida suka ga Malan Sani yashigo ko sallama babu. Da sauri Halima ta tashi tana fad'in Malan lafiya kuwa? Hannu ya d'aga mata, beyi magana ba yayi hanyar d'akinsa, bayansa tabi cike da damuwa ga jini ajikinsa duk sai hankalinta ya sake tashi. Yana shiga ya rufe k'ofar yasa mukulli, zubewa yayi saman gadonsa nan take nannauyen bacci ya d'aukeshi.
Kamo Rumaisa Halima tayi suka zauna nan take hawaye suka wanke mata fuska, gaba d'aya jikinta yayi sanyi ganin Malan Sani a cikin wani yanayi wanda betab'a shiga ciki ba.
***
Bayan 'yan sanda sun gama bincike motar asibiti ta d'auketa aka nufi asibiti da ita dan sunce ba mutuwa tayi ba. Gaba d'aya unguwar hankalinsu atashe yake saboda abinda ya faru. Madu kuwa kamar wanda aka watsama ruwan zafi, gashi yakira Alhaji wayar bata shiga.
Ana shirin rufe gidan sai ga wata motar 'yan sandan sunzo. Bayan sun shigo suka tambayi maigadin gidan. Madu ya taso yana fad'in gani nan. Tambayarsa sukayi nan ne gidan Alhaji Maiwada shugaban kwastam? Jiki a sanyaye Madu yace nan ne.
Hannu babban cikinsu ya mik'ama d'an sandan da suka samu, Alhaji Musa makwabcin su Alhaji ya matso yana tambayar lafiya? 'Dan sandan yace mun samu gawar Alhaji Maiwada ne a motarsa shine akayi mana kwatancen gidansa, yanzu haka gawarsa tana asibiti an wuce da ita domin ayi bincike, tare ma muka kaita data wani yaro da muka tsinta itama anjefar, gaba d'aya de suna asibiti kafin mu samu Iyayen yaron.
Wani irin kuka Madu yasa yana fad'in shikenan shima ya kashe shi, kai Malan Sani ina zaka kai alhakin wad'an nan mutanan? Mutum ya d'auko ka cikin talauci ya taimake ka amma kazo kayi masa butulci.
Alhaji Musa ne ya kamo Madu yana fad'in ya isa haka, tunda hukuma tashigo ciki za'ayi bincike. 'Dan Sandan yace kasan gidan Malan Sanin? Kai Madu ya d'aga yana fad'in sosai ma.
Kallon Alhaji Musa yayi yana fad'in Alhaji zamuje can gidan domin mutafi da Malan Sanin, idan akwai wani d'an uwan Alhaji Maiwada asanar masa domin dole a rufe gidan nan kafin su zo.
Alhaji Musa yace gaskiya danginsa ba anan suke ba, kuma bani da lambar kowa. Madu yace ina da lambar Alhaji Mansur a kano yake. Alhaji Musa yace kawo lambar asanar masa idan yaso sai arufe gidan ku tafi da mukullin wajen ku kafin yazo.
Bugu biyu Alhaji Mansur ya d'auka, ganin bak'uwar lamba yasa gabanshi ya sake fad'uwa. Bayan sun gaisa Alhaji Musa ya fad'a masa halin da ake ciki. Salati kawai Alhaji Mansur yakeyi jikinsa yana rawa, ya dad'e kafin yace gobe zai taho da wuri, sannan ya roki alfarmar Alhaji Musa ya kula da Ummun Ra'eez kafin yazo da matarsa. Alhaji Musa yace bakomai sai kazo.
Haka aka kulle cikin gidan Madu yace zai cigaba da zama kafin ya tafi dan shima bazai iya cigaba da zama ba. Haka ya kulle gate d'in yashiga motar 'yan sanda suka nufi gidan Malan Sani, sauran 'yan unguwa sai jimamin abinda ya faru sukeyi.
***
Har sun rufe gida taja Rumaisa d'akinta sun kwanta dan Rumaisa har tayi bacci, ita ko ta kasa baccin, tunanin halin da Malan Sani yake ciki kawai takeyi.
Jin k'arar buga gida yasa tayi saurin tashi tana lallubar fitila, hijabi tasa kafin ta nufi waje jiki a sanyaye. Tsayawa tayi tana tambayar waye? Daga waje akace 'yan sanda ne ki bud'e.
Jikinta ne ya tsananta rawa, da kyar ta iya bud'e k'ofar. Madu ta fara gani hakan yasa taji sanyi, kallonshi tayi duk idanuwanshi sunyi ja. 'Daya daga cikinsu ne yace ina maigidan ki? Halima tace yana ciki ina jin beda lafiya dan ya kule k'ofar d'akinsa kuma ya dawo cikin wani yanayi.
'Dan sandan yace muje ki nuna mana d'akin munzo tafiya dashi ne. Gabanta ne ya faad'i ta kalli Madu tana fad'in wai meye yake faruwa dan Allah? Matsawa Madu yayi gefe yana goge kwalla ya kasa magana.
Kuka Halima tasa tare da komawa ciki ta fara bubbuga d'akin Malan Sani. Shiru babu alamun motsi hakan yasan d'an sandan yace zamu b'alle k'ofar tunda bai bud'e ba.
Abun buge k'ofa suka samo haka suka bud'eta da k'arfi. Mamaki ne ya kamasu ganinshi kwance kamar gawa, da sauri Halima tayi ciki tana fad'in Malan na shiga ukku me yasame ka haka? Ciki suka shiga suna tsoron kada dai ace shima ya mutu shirin da Brr. Barau yayi ya rushe.
Komawa baya d'aya daga cikinsu yayi ya d'ebo ruwa, yana zuwa ya watsa mashi, a firgice ya tashi sai dai jikinsa babu kwari. Rungumoshi Halima tayi tana kuka tace Malan me yasame ka? Kallonta yayi idanuwansa suna rufewa amma ya kasa magana.
'Dan Sandan yace Malama ki matsa muyi aikin mu kina b'ata mana lokaci, idan kina son sanin abinda ya aikata zaki iya zuwa ofis d'in mu gobe da safe amma yanzu dashi zamu tafi.
Kuka Halima tasa tana fad'in wallahi mijina ba me laifi bane, dan Allah kada ku tafi dashi. Murmushi d'an sandan yayi yana fad'in idan baki sani ba to mijinki makashi ne, domin ya kashe uban gidansa kuma ya nemi matarsa da alfasha yanzu haka tana asibiti.
A zabure Halima tayi baya tana binsu da wani irin kallo, hannu tasa ta rik'e cikinta jin yanda ya murd'a mata, ganin halin da take ciki yasa wani daga cikin 'yan sandan yaji tausayinta, duk'awa yayi yana fad'in ki kwantar da hankalin ki, idan akayi bincike beda laifi babu abinda za'ayi masa.
Ajiyar zuciya Halima ta saki tare da sakin wani irin kuka. Tana ji tana gani suka rik'e Malan Sani dan bema iya tafiya saboda mutuwar jiki, sai kallonta yakeyi, yana so yayi magana amma ya kasa, hawaye ne suka zubo mashi, haka sukayi waje Halima tana zaune ta kasa tashi.
Jin k'arar motarsu yasa tayi saurin tashi, mararta ce ta murd'a hakan yasa ta duk'e tana cije baki, ta jima ahaka kafin ta dafa bango har ta kai k'ofa, tsayawa tayi tana kallon kurar motarsu hawaye suna wanke mata fuska. A hankali ta maida k'ofar ta rufe kafin ta koma d'aki ta fashe da kuka.
***
Wai Baffan Naseer har yanzu baka samu wayar tashi ba? Ajiyar zuciya Baffa yayi yana fad'in duk kiran da nakeyi wayarsa akashe take, gaba d'aya hankalina ya tashi domin Naseer baya kai dare awaje.
Mama tace kuma fa gidansu Mannir yace zaije a masallacin unguwar nan ma yayi sallar magriba. Baffa yace ba agida nayi sallah ba da bazan barsa yaje ba, idan ma yace dole yaje sai dai na kaishi da kaina, kinsani sarai bana son yawon dare.
Mama tace kayi hakuri gani nayi yace littafinsa zai amso. Baffa yace wai baki da lambar shi Mannir d'in? Mama tace ina da ita dan Naseer ne ma ya ajeta saboda wata rana yana kiransa da wayata.
Baffa yace bani lambar. Bugu biyu Mannir ya d'auka, bayan sun gaisa suka tambayeshi Naseer. Shiru Mannir yayi yana mamakin Naseer baya gida, yace masa zaizo da yaga shiru ya d'auka ko agida aka hanashi.... Labarin yanda sukayi da Naseer ya fad'a masu.
Jiki asanyaye suka masa godiya. Hawaye ne suka zuboma Mama tana fad'in kada dai ace saceshi akayi. Baffa yace banga ta zama ba bara na kira DPO gara mushigar da k'ara da wuri.
Suna gama waya da DPO yace yajirashi zaisa yaranshi suje su duba. Zama sukayi gaba dayansu jiki amace.
Can wajen sha biyun dare DPO yakira Baffa, yana d'auka yace masa ya tura yaranshi zasuyi bincike, amma wani yace an kai wasu gawawwaki guda biyu d'azu asibiti data babban mutum data yaro, ko zasuje su duba? A zabure Baffa ya tashi yana fad'in yanzu zan fito DPO mu had'u a asibtin. Da sauri DPO ya amsa saboda Baffa babban mutum ne akwai naira.
Tare suka tafi hada Mama sai kuka takeyi domin Naseer shine autan ta, yaranta biyu babban yana can abuja yana karatu.
***
Kuka kawai sukeyi asaman gawar Naseer, Mama tana fad'in su waye ne suka maka haka Naseer? Ya Allah ka saka ma bawanka. DPO yace Alhaji kuyi hak'uri insha Allahu zamuyi bincike, idan muka gano wad'an da suka aikata haka dole ashigar da k'ara kotu.
Jinjina kai Baffa yayai kafin suka wuce domin su amshi gawar. Likita yace zasuyi bincike dole su bari zuwa safiya tunda ba yau za'a rufeta ba. Baffa yace ayanzu zakayi binciken ka bani gawar Yarona, gara naje na kwana ina masa karatu daya kwana anan. Jikin likita yana rawa yace angama.
Ur's.
Nabeelert Lady🖋
[3/10, 8:38 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud'i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shoot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k'asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub'e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.*
1⃣6⃣
Washe gari ko da Malan Sani ya farka sai ya dawo cikin hankalinsa, tashi yayi yana dafe kanshi da yake masa ciwo, a hankali abubuwan da suka faru jiya suka fara dawo masa, tun daga shigarsa gidan Alhaji har abinda ya faru ya fito ya shiga mota har zuwanshi gida, iya nan kawai ya iya tunawa sai kuma yau daya tashi.
Da sauri ya d'aga kai yana sake kallon inda yake, mamaki abun ya bashi, yasan dai yashiga d'akinsa amma gashi a wajen 'yan sanda. Runtse ido yayi yana salati tunawa da abinda ya faru, kada dai sun kashe Ummun Ra'eez? Saurin sa hannu yayi a wuyansa, zafi yaji a wajen dan har yayi fushi saboda yakushin da sukasa Ummun Ra'eez tayi masa, a hannunsa yana jin shatin faratan ta.
Girgiza kai yashigayi hawaye suna zubo masa, tabbas yasan yashiga tsaka mai wuya Allah ne kad'ai zai iya fitar dashi, domin wannan abun daya faru yasan duk shirin su Alhaji Marusa ne. Dafe kai yayi yana kuka, ko a wane hali Halima take ciki yanzu? Jin motsi yasashi saurin d'agowa.
Wani d'an sanda ne yazo wajenshi dan yaga beyi sallah ba kuma shi zai tafi shine ya matso yaji ko yana da buk'atar yayi sallah, dan tunda aka kawoshi jiya yana zaune a ofis kawai yaji ya tausaya mashi, yanayin da aka kawoshi yasan akwai abinda ya sha ko kuma akasa mashi.
Saurin tashi Malan Sani yayi yana fad'in dan Allah inaso nayi sallah kaga har gari yayi haske sosai. Murmushi d'an sandan yayi yana fad'in ai tun d'azu naga kana bacci shiyasa ban tasheka ba, fito ga wajen sallah can.
***
Mota ce ta sauke Alhaji Mansur da Matarsa a k'ofar gidan Alhaji Maiwada saboda ta jirgi suka zo. Idanuwan Maman Labiba har sun kumbura saboda kuka, shikanshi Alhaji Mansur idanuwansa sunyi ja saboda ba k'aramin tashin hnkali yashiga ajiya ba.
Isowar Alhaji Musa ne yasa suka k'arasa cikin gidan saboda da suka zo basu shiga ba. Da sauri Madu ya taso yana masu sannu da zuwa, shima duk jikinsa a sanyaye yasha kuka.
Bayan sun gama gaisawa suka jajanta abinda ya faru, anan Alhaji Mansur yayima Alhaji Musa godiya sannan yace su wuce asibitin domin a gama komai a basu gawar Alhaji ayi masa sutura.
Alhaji Musa yace shikenan bara na d'auko mota ta sai mutafi, zansa a kawo tabarmi saboda zaman gaisuwa, Madu sai ka gyara cikin rumfar can idan suka kawo sai a shimfid'a. Kai Madu ya d'aga yana share kwallah.
***
Sosai Abubakar da Moses suka tsorata da abinda sukaji, gashi su Peter basu kyalesu haka ba sai da suka basu wahala sosai, domin a wajensu suka kwana, sun jigata sosai, haka kuma sunyi kukan mutuwar Alhaji Maiwada da Malan Hassan, Abubakar yanaji kamar laifinsa ne, da be sako Malan Hassan a cikin wannan abun ba da haka bata faru dashi ba, gashi babu halin yaje ya sanar da Iyalinsa yanzu za'a tsareshi ya nuna gawarsa kuma besan inda take ba, hakan kuma zai sashi cikin matsala,, dole ya bar abun sai dai Allah ya basu hak'uri.
Shigowar Lucky da Peter ne yasa sukayi saurin kallon su. Matsowa Lucky yayi fuska babu annuri yana fad'in kunci sa'a ba'a bamu umarnin kashe ku ba, kashedi kawai akace muyi maku, nasan zuwa yanzu jikin ku ya fad'a maku abinda muke nufi, dan haka zaku samu takardar canjin wajen aikin ku da zaran litinin tayi, matuk'ar kuka sake nuna kan ku ko kuma wani yaje neman wata sheda akan ku zamu kashe kowa naku.
Cike da tsoro Moses yace wallayi aboki bazaka sake gani na a lagos ba, tsautsayi ne yasa nayi haka, amma na goge komai bani da wata sheda kada ku kashe ni.
Abubakar yace insha Allahu bazaku sake ganina a lagos ba koda da yawo, kuma babu abinda zan fad'a, bazan barima asan nasan wani abuba, dama bani da iyali anan suna can dan haka ayau zan bar garin.
Murmushi Lucky da Peter sukayi kafin suka kwance su, hannu suka rik'e saboda tsamin da yayi masu, ga kansu da yake ciwo saboda abinda suka shak'a masu. Haka suka d'aure masu fuska suka fita da su.
***
Kuka kawai Maman Labiba takeyi alokacin da taga gawar Alhaji Maiwada, Alhaji Mansur kanshi kasa daurewa yayi, juya baya yayi ya saki wani irin kuka, Alhaji Musa ne yayi ta bashi baki.
Gaba d'aya gawar Alhaji ta canza kama, fuskarsa duk da kumbura, wuyansa yayi wani irin ja gwanin tausayi. Brr. Barau ne tare da d'an sandan da yake kula da case d'in Alhaji suka shigo.
Hannu suka bama su Alhaji suka gaisa, kallon Alhaji Mansur yayi yana fad'in sunana Brr. Barau, kuma nine lauyen da zan kula da wannan shari'ar ta Alhaji Maiwada, domin nine lauyensu na wajen aiki, bazamu tab'a bari jininsa ya zuba abanza ba, duk wanda yake dasa hannu akisanshi sai mun kamashi, to abun yazo da sauki domin an kama direbansa da ake zargin shine ya kashe shi, saboda an kamashi da laifin yima matar Alhaji fyad'e har yayi sanadiyar zubewar cikinta, yanzu haka yana kulle.
Tunda ya fara magana Alhaji Mansur ya zuba masa ido har sai da Brr. Barau ya tsargu da kallon da yake masa. Gyaran murya yayi yana fad'in kada ka damu Alhaji zanyi aiki sosai akan mutuwar Alhaji Maiwada.
Kauda kai Alhaji Mansur yayi yana jin wani irin tukukin bakin ciki, yasan komai akan Brr. Barau, domin babu abinda Alhaji Maiwada ya b'oye masa, amma kaji saboda rainin hankali wai shine zai tsayama Alhaji, gashi sun kullama Malan Sani sharrin da babu mai fitar dashi sai Allah, tabbas yasan sune suka aikata hakan, amma iya abinda ya sani a baki ya tsaya beda sheda ko kad'an a hannu, ita kuma kotu da sheda take amfani, dole yasa ido yaga yanda komai zai kasance, idan aka cutar da Malan Sani sai dai Allah ya saka masa.
Muryar Alhaji Musa yaji yana fad'in bakomai Brr, mungode sosai, gaskiya ka kyauta da zaka tsaya domin a kwatoma Iyalan Alhaji Maiwada hakkinsu, domin har yanzu ita Hajiyar bata farfad'o ba, shi kuma wannan direba ayi masa hukunci dai-dai dashi domin hakan ya zama darasi a wajen 'yan baya.
Brr. Barau yace insha Allahu babu abinda zai gagara. Alhaji Mansur yace yanzu dai muna so a bamu gawar Alhaji muje mu suturta ta. Brr. Barau yace nima abinda yasa nazo kenan saboda nasan Alhaji Maiwada beda kowa a garinnan shiyasa nazo domin an fad'ama wajen aikinsu suna jira suji lokacin jana'izar domin suzo a suturtashi.
Dan sandan yace ai duk wani bincike mungamashi, duk wani abun daya kamata anyi dan haka zakuje wajen likita ku gama dashi sai abaku gawar, sannan motarsa nasa yarana su kaita gidanshi yanzu. Jinjina kai sukayi kafin suka nufi ofis d'in likita.
Haka aka gama komai aka basu gawar Alhaji Maiwada, acikin motar asibiti aka d'aukeshi saboda babban mutum ne, a motar Alhaji Musa suka tafi.
***
Kafin wani lokaci mutuwar Alhaji Maiwada ta yad'u, manyan mutane duk sun halarci k'ofar gidansa domin ayi masa sallah, 'yan wajen aikinsu gaba d'aya sun halarci wajen, Malan Bala sai kuka yakeyi yana tuna rabuwarsu da Alhaji jiya, ko kud'in daya bashi bai gama kashe su ba amma wai ya rasu.
Kafin wani lokaci an gama shirya Alhaji, haka mak'udan mutane suka taru aka sallaceshi, kafin Alhaji Marusa ya iso har an sallame, yana zuwa sai dai ya juya domin rakiyar kai gawa. Mr. Kallah kuwa yana gida sai sun dawo zai zo masu gaisuwa, gaba d'aya hankalinsa tashe yake, tunda Alhaji Marusa ya kirashi ya fad'a masa an kashe Alhaji yake jin babu dad'i aransa, amma babu yanda ya iya dole ya bar komai aransa tunda mai faruwa ta faru.
Hatta da Abubakar sai da yazo jana'izar Alhaji, duk da baya jin dad'in jikinsa amma haka yazo saboda yana tsoron rashin zuwanshi yasa a zargeshi musamman da mutane suka san suna shiri da Alhaji.
Bayan an dawo daga binneshi aka shiga yima juna gaisuwa, sauran abokan aikinshi wad'an da ba musulmai ba haka suka fara zuwa suna gaisuwa, Mr. Kallah ma yazo gaisuwa kuma ya zauna a kusa da Alhaji Marusa anan aka cigaba da zaman gaisuwa dasu.
Cikin gida kuwa Maman Labiba itace Uwar amsar gaisuwa, matan unguwa duk sunzo suna tayata zaman makoki, abinci kuwa azahar tanayi aka fara shigo dashi kuloli, abunka da birni sai dai akawo abinci daga waje, *sab'anin wani wajen da zaka iske masu mutuwa sune suke ciyar da 'yan zaman makoki, d'an abincin da suka samu sadaka kafin a share makoki mutane sun cinye wasu hada guzirin na gida*.
***
Sai da Ummu tayi kwana d'aya da yini kafin ta farka, Hajiya Amina matar Alhaji Musa tana zaune a gefenta tayi saurin tashi ganin tana motsi, hannu Ummu tasa ta dafe kanta, da k'arfi ta saki ihu tana kiran Abbu. Saurin matsawa Hajiya Amina tayi tana rik'eta.
Shigowar wata ma'aikaciya ne yasa Hajiya Amina ta matsa domin ta bata waje, ganin yanayin da Ummu take ciki yasa ma'aikaciyar tayi saurin danna wata alama, kafin wani lokaci sai ga likitoci sun shigo.
Fita Hajiya Amina tayi cike damuwa. Haka suka shiga duba Ummu, ganin ta kasa natsuwa yasa dole sukayi mata allurar bacci kafin suka gungurata zuwa wani d'akin gwaji.
***
Alhaji Mansur ne da Alhaji Musa suka iso da sassarfa dan Hajiya Amina ta kirashi shine suka taho, Alhaji Mansur yaso ya taho da matarsa amma baya so abar gidan abud'e saboda basu san halin wasu ba.
**
Zaune suke a ofis d'in babban likita. Bayan ya gama 'yan rubuce-rubuce ya d'ago kai yana fad'in agaskiya Hajiya ta had'u da lalurar tab'in hankali sakamakon dukan da akayi mata akai da kuma abinda yashiga zuciyarta na tsorata, sannan cikin jikinta ya zube, yanzu haka munyi mata allurar bacci saboda jikinta babu kwari muna buk'atar ta samu hutu shiyasa mukayi mata allura, idan ta samu saukin ciwon jikinta dole zamu maidata asibitin mahaukata wanda nine zan mayar da ita can saboda takasance matar Alhaji Maiwada, tunda na fahimci tana d'auke da wannan lalurar nayi alk'awarin zan kula da ita.
Salati Alhaji Mansur yayi yana fad'in Allah mungode maka da wannan jarabawa taka, ya Allah ga baiwarka nan Allah kada ka mayar da Ra'eez Maraya gaba da baya, ya Allah ka bata lafiya. Gaba d'ayansu sukace amin.
Alhaji Mansur yace amma likita ina da magana, inaso idan ta samu sauki zamu maidata Kano domin zatafi samun kulawa akusa damu, kuma haka ne kawai zanyi na kyautata ma Alhaji Maiwada, domin yanzu bani da burin daya wuce na rike iyalinsa, kuma na cika masa burinsa na barin garin nan da yayi niya.
Gyara zama likita yayi yana fad'in ban tari numfashin ka ba Alhaji, dama tunda naji Alhaji Maiwada beda 'yan uwa agarin nan nake jiran wani nashi yazo domin na nemi wannan alfarmar, naroke ka da girman Allah ka barni na samu wannan ladar, Alhaji Maiwada yana da muhimmanci agaremu, ta silarsa Yayana Alhaji Usman ya samu kayansa da aka sace suka fito tun yana farkon zuwa garin nan, Yayana tunda yaji wannan labari yace shine zai d'auki nauyin kud'in jinyar Matar Alhaji, ayau da muka gano matsalar da take ciki nayi alk'awarin zan kaita wajen abokina da yake kula da masu irin wannan lalurar, kuma acan asibitin zata zauna har Allah ya bata lafiya, sannan idan tana garin nan zatafi saurin dawowa hankalinta tunda anan abun ya sameta.
Shiru Alhaji Mansur yayi dan likita ya d'aureshi, ajiyar zuciya ya saki yana fad'in shikenan likita bazan hanaka aikata aikin alkhairi ba, nasan abubuwan alkhairin da Alhaji Maiwada yayi sune suka jawo masa haka, dama ance idan kana aikin alkhairi ko bayan mutuwarka aikinka yana nan, bakomai Allah ya baka lada, kuma zamucigaba da magana ta waya ina jin halin da take ciki.
Godiya likita yayi masu, anan sukayi musayar waya Alhaji Mansur yace da anyi sadakar ukku zasu tafi, kafin lokacin yana so su gana da wancan likitan. Murmushi likita yayi yana fad'in babu damuwa.
Alhaji Musa yace 'yan sanda sunzo nan kuwa likita? Likita yace sunzo tun a washe garin ranar, sun d'auki hoton shatin hannun Hajiya na dama wanda naga jini acikin k'umbarta, sai sukasa mukayi awon jinin da yake cikin farcanta muka basu sakamakon, sai dai sunce fyad'e akayi mata amma gaskiya babu alamun haka, kila dai garin yin fyad'en ne cikin ya zube, ganin jini yasa sukace fyad'e ne, amma gaskiya babu wani fyad'e.
Girgiza kai Alhaji Mansur yayi wani takaici ya turnuk'eshi, gashi dai yasan gaskiyar wasu al'amuran amma beda halin magana. Tashi yayi yana fad'in likita mungode sai mun had'u a kotu ranar litinin dan nasan bazasu ja shari'ar ba, idan angama da wuri zamu wuce saboda ranar ne sadakar ukku. Godiya yayi masu suka fita.
Alhaji Mansur yaso Hajiya Amina tazo su koma gida itama ta huta amma Alhaji Musa yace ai babu komai baza'a bar mai jinya ita kad'ai ba. Haka suka tafi bayan sun aje masu abincin da suka zo dashi.