Zaune Alhaji Mansur da Maman Labiba suke a tsakar gidan Malan Sani yayin da Halima take jingine da filo Rumaisa tana gefenta gwanin tausayi.
Tunda aka tafi da Malan Sani washe gari ta tashi da rashin lafiya, makwabciyarta ce ma tashigo saboda ma'aikaciyar asibiti ce tazo su gaisa dan ta saba kullum sai tashigo sun gaisa kafin ta wuce, bayan ta shigo ta isketa cikin wannan yanayin hakan yasa ta tsaya sai da ta taimaka mata tayi wanka ta had'a mata shayi sannan ta koma gida ta kira mai aikinta suka kama Halima suka nufi asibiti.
Bayan anyi mata gwaji aka gano tana da ciki har ya kusa b'arewa sakamakon tashin hankalin data shiga, hakan yasa aka bata magunguna har yamma tana can, sai da matar ta tashi daga aiki kana suka dawo tare kuma ta hanata aikin komai har sai ta warke, taso ta barta a asibiti Halima tace bata so, shiyasa suka dawo, Mai aikinta tasa ta kawo masu abinci dan tace Halima kada tayi aiki.
Cike da tausayi Alhaji Mansur yake mata ya jiki tare da kwantar mata da hankali. Hannu tasa ta goge hawayen da suka zubo mata tana fad'in wallahi Alhaji sharri akayima Malan, tunda yashigo na gane ba'a hayyacinsa yake ba, taya za'ace Malan ne zai... Hannu Maman Labiba tasa ta rufe mata baki tana fad'in ya isa haka.
Alhaji Mansur yace yanzu kam bamu da wata sheda, duk da nayi magana da Brr. Kamal kuma shima yace sunyi waya da Alhaji akan yana so yaje suyi wata magana mai muhimmanci saboda zai shigar da k'ara, amma yace Alhaji bai riga ya bashi wata sheda da zai iya tsayawa da ita ba, kawai zaije ya tsaya ma Malan Sani idan Allah yasa basu da shedar da zata kada Malan Sani komai zaizo cikin sauki, idan kuma suna da ita sai dai Allah ya bimasa hakkinsa domin kotu da sheda take amfani.
Halima tace bakomai nayi imani da k'addara, kuma ina rokon Allah yasa mani juriya akan wannan abun tashin hankalin daya samemu, insha Allahu Allah bazai bar kosu waye suka aikata haka ba.
Alhaji Mansur yace haka ake son mutum mai yarda da k'addara, inaso kuma idan komai ya lafa mutafi gaba d'aya Kano tunda Malan Sani yace shima can zai koma.
Murmushi Halima tayi tana fad'in matuk'ar aka yanke hukunci mukayi nasara to tare zamu tafi, amma idan sune sukayi nasara zan zauna anan har sai ranar da Malan ya rasu, idan ina raye zan koma Kano da zama, idan kuma nima na tafi to ga Rumaisa nan ku kular mani da ita.
Tausayin Halima ne ya kamasu, hannu yasa ya goge idonshi kafin ya mik'e yana fad'in ina so naje naga Malan Sani. Saurin kallonsa tayi tana fad'in dan Allah ka tafi damu. Alhaji Mansur yace shikenan muje.
***
Kuka kawai sukeyi Alhaji Mansur ne yake lallashin su. Bayan sunyi shiru Malan Sani yace shikenan yanzu an rufe Alhaji ba tare da nayi rakiyarsa ba? Wallahi an cutar dani, Allah ne kad'ai zai saka mani, yanzu ina Ummun Ra'eez take?.... Labarin halin da take ciki Alhaji Mansur ya bashi.
Sosai yake kuka yana fad'in Allah ya isa, Allah ka saka mani. Alhaji Mansur yace bani labarin abinda ya faru.....Komai Malan Sani ya fad'a masa har zuwansa gida ya kwanta. Hannu Alhaji Mansur yasa ya goge kwallar data zubo masa, kallon Malan Sani yayi yana fad'in wad'an nan mutanan shed'anu ne, dalilin barinka araye saboda su d'ora laifin awajenka.
Malan Sani yace bakomai Alhaji, zan d'auki kaddarata da hannu biyu, fatana Allah ya albarkaci abinda na bari. Alhaji Mansur yace insha Allahu zaka kara samun wasu zuri'ar ma.
Saurin kallon Halima yayi ita ko ta duk'ar da kanta. Tambayarta yayi wata nawa? Da hannu tayi masa nuni wata biyu. Murmushi ne ya sauka akan fuskarshi, itama Halima murmushin takeyi.
Malan Sani yace narokeki Halima da ki cire damuwa aranki saboda ki kular mana da zuri'ar mu, kinga dai halin da nake ciki, ke kad'ai zaki cigaba da kula da tarbiyar yaran mu, ki daure kisa juriya aranki dan Allah.
Jinjina kai tayi tana hawaye. Alhaji Mansur yace zanga Brr. Kamal insha Allahu zamu san abunyi. Murmushi kawai Malan Sani yayi, dan yasan Alhaji Mansur ya fad'a ne kawai dan ya kwantar masa da hankali, amma yasan dole ayanke masa hukunci. Sallama sukayi masa suka tafi yana kara kwantar ma Halima da hankali.
***
Fetur Lucky yasa ma Wayar Naseer da Kamfutar Alhaji bayan sun gama kallon abubuwan da suke ciki, wuta ya kuna nan take suka kama da wuta.
Dariya Alhaj Marusa yasa yana fad'in Brr. Barau aiki yayi kyau, saura zuwa kotu, nasan dole a yanke ma Malan Sani hukunci.
Brr. Barau yace ai mune da kotu, kuna da ni sannan muna da 'Yallab'ai, dan haka ku kwantar da hankalin ku, wani abu sai ma na zama Alkali. Dariya sukasa gaba daya.
**** ***
*Safiyar Litinin a kotu*.....
Wajen k'arfe tara na safe akayi addu'ar sadakar ukku ta Alhaji Maiwada, bayan an kammala suka nufi kotu saboda k'arfe goma za'a fara shari'a, tare da Halima suka tafi bayan ta mik'a Rumaisa makaranta.
Babbar kotu ta cika da al'umma, domin kowa yana so yaji yanda wannan shari'ar zata kasance, hatta da Mr. Kallah sai da yazo, duk da yau litinin yana da aiki a ofis amma haka yazo dan tunda Alhaji ya rasu hankalinsa ba akwance yake ba, gani yake kamar za'a ganosu idan akazo kotu, shiyasa ya tsaya yaga komai ya kammala agabanshi.
Brr. Barau yau shiri yayi na musamman, fuskarsa babu alamun far'a dan so yake ya nuna matuk'ar damuwa akan wannan shari'ar saboda kowa ya yarda dashi, koda ya iso bakin kotu be tsaya magana da kowa ba yashiga ciki, dan baya so aganshi tare da kowa ayi tunanin wani abu, shiyasa suka shirya baza suyima juna magana ba har sai sun bar kotu saboda idon mutane ga yan jarida agefe.
isowar Alkali yasa kowa ya natsu, bayan ya zauna aka shigo da Malan Sani, gaba d'aya aka bishi da kallo, kwana biyu amma ya canza, Halima kuwa duk'ewa tayi tana kuka. Malan Sani kuwa tunda yashigo yaki kallon kowa.
Bayan an natsu Alkali ya bada ikon a karanto k'ara. Tashi Magatakarda yayi yana fad'in *a yau litinin goma ga watan Mayu shekara ta dubu biyu da takwas (10/05/2008), wannan kotu zata saurari k'arar da hukumar kwastam ta shigar akan mutuwar shugabansu Alhaji Hamza Maiwada wanda ake zargin direbansa wajen aikata kisan a daren juma'a da misalin k'arfe bakwai na dare, bayan nan kuma suna zarginsa da hayyek'ema matar Ubangidansa a wannan rana inda sanadiyar haka har cikinta ya zube kuma ta had'u da lalurar tab'in hankali sakamakon dukan da yayi mata akai, yanzu haka tana kwance a asibiti*.
Risnawa yayi tare da mik'ama Alkali takardar, komawa yayi ya zauna. Duk'ar da kai Malan Sani yayi hawayen bakin ciki suna zubo masa, addu'a kawai yakeyi.
'Dago kai Alkali yayi yana fad'in ina lauyoyin da zasu gabatar da shari'ar? Tashi sukayi suna risna kai. jinjina kai Alkali yayi kafin ya basu iznin gabatar da kan su. Brr. Barau ne ya fara gabatar da kansa a matsayin wanda zai kare Alhaji, sai Brr. Kamal ya gabatar da kansa amatsayin wanda zai kare Malan Sani.
Alkali yace wanda zai fara ya fito. Komawa Brr. Kamal yayi dan ba shine zai fara ba. Matsowa Brr. Barau yayi yana fad'in idan kotu ta bani dama inaso nayima Malan Sani wasu tambayoyi. Kotu ta baka, Malan Sani ya matso gaban kotu.
*Brr. Barau*... Kotu zata so taji sunanka da kuma san'ar ka.
Sunana *Malan Sani*, kuma sana'ata shine tukin mota.
*Brr. Barau*... Malan Sani meye alak'ar ka da Alhaji Maiwada?
*Malan Sani*... Bamu da wata alak'a ta jini tsakanin mu, sai dai ina masa aikin tuki, nine direbansa tun farkon daya fara aiki a garin nan.
*Brr. Barau*... Zaku kai shekara nawa tare?
*Malan Sani*... E to gaskiya mun dad'e dashi, a kalla zamuyi shekara sama da biyar atare.
*Brr. Barau*... Idan na fahimceka kun dad'e sosai har kun zama 'yan uwan saboda sabo?
*Malan Sani*... Maganar gaskiya Alhaji ba Ubangidana bane kad'ai, ina jinsa tamkar Yayana da muka fito ciki d'aya, domin Alhaji ya gama mani komai arayuwa.
*Brr. Barau*... Malan Sani, kotu taji irin yanda ka d'auki Alhaji Maiwada, sai kuma gashi duk irin alkhairin da yayi maka hakan bai hanaka kashe shi ba kuma ka keta ma Iyalinsa haddi...
Ina da ja ya mai shari'a, ya kamata abokin aikina ya kula da maganar da yake jifar Malan Sani da ita, har yanzu ba'a tabbatar shine ya aikata kisan ba zarginsa akeyi, be kamata yarik'a masa irin wannan tambayar ba. Nagode.
*Alkali*... Brr. Barau ka kiyaye. Risnawa Brr. Barau yayi yana fad'in za'a kiyaye.
*Brr. Barau*... Malan Sani aranar juma'a da misalin k'arfe bakwai da 'yan mintuna kana ina?
*Malan Sani*... Ina tare da Alhaji a wannan lokacin muna kan hanyar mu ta zuwa gida.
*Brr. Barau*... Ko Malan Sani zai fad'ama kotu abinda ya faru a wannan lokacin da suke kan hanyar gida?
*Malan Sani*... E to muna cikin tafiya sai tayar motar mu tayi faci, muna kok'arin fita sai ga wasu mutane kamar daga sama, kafin suzo wajen mu sai Alhaji yace na tafi gidansa na tafi ta matarsa gidana saboda yana tsoron wani abu ya faru da ita, shine na tafi ashe kashe shi zasuyi.
*Brr. Barau*... Murmushi yayi yana fad'in, Malan Sani kamar yanda ka fada, kace kuna hanyar ku ta zuwa gida ne, wanda mun san cewar Alhaji Maiwada yana zaune a unguwar Apapa ne, sai gashi kun taso daga wajen aikinsa kun canza hanyar da zata sada ku da gida, ko zaka fad'a mana dalilin da yasa bakubi hanyar da kuka saba bi ba.
*Brr. Kamal*.... Ina da ja ya mai shari'a, wannan tambayar bata da alak'a da wannan shari'ar, domin kowa yana da ikon bin inda yakeso domin zuwa gida.
*Alkali*..... Korafi bai karb'u ba, dole zai amsa wannan tambayar domin tana da alak'a da wannan shari'ar. Brr. Barau kacigaba.
*Brr. Barau*.... Risnawa yayi kafin yace kotu tana sauraron ka.
*Malan Sani*... Haka ne, bayan fitowar mu daga wajen aiki sai muka had'u da wani yaro yana neman taimako, sai Alhaji yace mu d'aukeshi, bayan ya fad'a mana unguwar da zaije muka tafi, sai dai da muka isa a bakin hanya muka ajeshi saboda nasan layin beda kyau, bayan mun juya zamu koma hanyar mu ta zuwa gida shine mukayi faci har wannan abun ya faru.
*Brr. Barau*... Girgiza kai yayi yana fad'in bayan ka isa gida ya akayi ka fito ba tare da Matar Alhajin ba?
*Malan sani*.... Bayan na shiga gidan muka gaisa da Madu mai gadin gidan, anan nake fad'a masa zanshiga ciki, bayan na shiga ciki mun gaisa da Hajiya, ina kok'arin na fad'a mata abinda Alhaji yace sai kawai mukaga wasu mutane sun shigo fuskarsu a rufe, Hajiya tana kok'arin magana sai kawai wani ya kwad'a mata sanda, nan take ta fad'i sai ganin jini nayi yana fita daga k'afarta, kafin nayi wani yunku'ri suka hura mani wani abu, tun daga lokacin ban sake sanin abinda yake faruwa ba, domin kaina yayi nauyi, ina kallo suka sa hannunta a wuyana suka yakusheni da farcenta, sai suka turoni waje, bayan na fito wajen gida suka sani a mota muka tafi, suna ajeni k'ofar gidana suka tafi, iya abinda na sani kenan amma wallahi ba nine na kashe Alhaji ba, haka kuma banyima Hajiya abinda ake zargina dashi ba.
*Brr. Barau*... Malan Sani zaka iya tafiya. Ya mai shari'a inaso nayima Maigadin gidan Alhaji wasu tambayoyi. Kotu ta baka.
*Brr. Barau*... Kotu zata so taji sunan ka da aikin ka.
*Sunana Amadu wanda akafi sani da Madu*, kuma aikina shine gadi agidan Alhaji.
*Brr. Barau*... Ka kai shekara nawa agidan Alhaji kana masa aiki?
*Madu*.... Zanyi shekaru kusan sama da shidda tare dashi.
*Brr. Barau*..... Ko akwai wata matsala da kasani wadda take faruwa atsakanin Malan Sani da Alhaji a zaman su?
*Madu*... Gaskiya tun had'uwar Alhaji da Malan Sani basu tab'a samun sab'ani ba, asalima Alhaji yana kyautata masa sosai, domin hatta da karatun d'iyarsa shine ya d'auki nauyi, gidan da yake ciki ma Alhaji ne ya cika masa ya sayeshi, gaskiya ban tab'a ganin sun samu matsala ba.
*Brr. Barau*.... Aranar juma'a a wane yanayi Malan Sani yashigo gida?
*Madu*.... E to gaskiya yashigo ba'a yanayin dana saba ganinsa ba, ina zaune ya buga mani k'ofa, bayan na bud'e sai na ganshi wani iri idanuwansa sunyi ja hannunsa rik'e da wata bak'ar jaka wanda bansan meye aciki ba, sai na tambayeshi ina Alhaji sai yace mani akwai matsala bara ya fito daga ciki, ban tsaya tambayarsa ba na barshi yashiga kasancewar nasan amintaccen Alhaji ne, ina zaune sai naji kamar ihun Hajiya, amma sanin Malan Sani yana ciki sai banyi yunkurin shiga ba, ba'a dad'e ba sai naga Malan Sani ya fito jikinsa duk jini yana tafiya kamar a buge, dana tareshi ina tambayarsa sai kawai ya ture ni har sai da na faad'i, kafin na tashi ya fice, ina lek'awa sai dai kurar mota na iske babu shi, sai nayi saurin shiga ciki, Hajiya na iske a kwance cikin jini hakan yasa nayi saurin fitowa domin na sanar da mutane. Iya abinda na sani kenan.
*Brr. Barau*.... Madu mungode zaka iya tafiya. Ina so zanyima Inspector Bello tambaya idan kotu ta bani dama. Kotu ta baka dama.
*Brr. Barau*.... Kotu zata so taji sunnanka kuma kayi mata bayanin binciken da kukayi.
*Sunana Bello Kabir*, nine d'an sandan da yake kula da case d'in mutuwar Alhaji Maiwada. A ranar juma'a mun samu waya daga wasu daga cikin ma'aikatan mu da suka fito aiki cewar sun samu motar Alhaji Maiwada tare da gawarsa aciki, bamu b'ata lokaci ba mukaje wajen, bayan an d'auke gawarsa daga motar sai muka binciki motar, mun samu sirinji da kwalbar wata allura a ciki, haka muka had'a komai muka nufi asibiti da gawar domin likitoci suyi bincike akai.
Bayan munje mun kama Malan Sani sai na koma asibiti, bayanin da likita yamun akan mutuwar Alhaji yasa a jiya na koma gidan Malan Sani domin yin wani bincike, a binciken da mukayi mun samu wata bak'ar jaka b'oye a d'akinsa acan k'asan gado wacce take d'auke da muk'udan kud'i a kalla zasu kai milliyan biyar, a cikin jakar muka samu irin kwalbar allurar da muka samu a motar Alhaji. Wannan sune takardun binciken da akayi ga kuma jakar.
Cusa kai Halima tayi cikin k'afafuwanta tare da sake sakin wani irin kuka, tunda 'yan sanda suka zo jiya suka gano wannan jaka a d'akin Malan Sani take cikin tashin hankali, bata san lokacin da aka aje jakar ba, ta tabbata Malan Sani ba zai aje wannan jaka ba, kuma ita tunda aka tafi da Malan Sani bata sake shiga d'akinsa ba sai kawai jiya da aka zo bincike taga an fito da jaka ashe wannan abun ne aciki, shikenan tasan babu wanda zai fitar da Malan Sani sai Allah.
*Brr. Barau*... Mungode zaka iya tafiya. Ina so zanyima likitan da yayi binciken gawar Alhaji tambaya idan kotu ta bani dama. Kotu ta baka dama. Likita ya fito gaban kotu.
Wani abokin aikin likitan ne ya mike yana fad'in likitan yayi waya yana hanya ya taho motarsa ta samu matsala amma ya kusa k'arasowa.
Dafe kai Brr. Barau yayi, kada dai likitan bazai zo ba gashi akwai abubuwa masu muhimmanci awajensa, dole ya nemi hanyar fita yanzu ko hutu ne ya nema.
Risnawa yayi yana fad'in ya mai shari'a ina rokon wannan kotu data bada izinin hutu ko na rabin sa'a ne domin akwai abinda za'a kawo mai muhimmanci wanda ya shafi wannan shari'ar.
Alkali yace muje ga sheda ta gaba kafin likita ya k'araso. Risnawa Brr. Barau ya sakeyi yana fad'in ina neman alfarmar kotu ta bada wannan hutu saboda wani uzuri daya taso mani yanzu.
Jinjina kai Alkali yayi yana fad'in kotu zataje hutun mintuna ashirin, idan be iso ba zamu cigaba da gabatar da shari'a. Buga tebur yayi.
Girgiza kai Alhaji Mansur yayi hawaye suka zubo masa, har cikin ranshi yana zargin wannan *ALKALIN*. Tashi yayi ya fita zuciyarsa na zafi, ga tunanin Ra'eez wanda har yanzu besan Mahaifinsa ya rasu ba, tsoro yake kada wani ya fad'a masa tunda Alhaji babban mutum ne mutuwarsa bazata b'oyu ba, dole gobe idan suka koma yaje ya d'aukoshi.
Ur's.
Nabeelert Lady🖋*Wannan littafin na kud'i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shoot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k'asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub'e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.*
1⃣8⃣
A waya Brr. Barau ya kira likita, hak'uri ya bashi yace gashinan zuwa. Sosai Brr. Barau ya sake nana ta masa abinda zaice kafin ya kashe wayar.
**
Bayan an dawo hutu Alkali ya bada izinin acigaba da gabatar da shari'a, tambaya yayi idan likitan ya iso? Tashi Brr. Barau yayi yana fad'in ya iso ya mai shari'a, inaso nayi masa tambaya idan kotu ta bani dama. Kotu ta baka dama, likita ya fito gaban kotu.
*Brr. Barau*... Kotu zata so taji sunan ka da kuma bayanin binciken da kayi.
*Sunana Aliyu Sani*, nine likitan da yayi binciken gawar Alhaji Maiwada, a binciken da nayi mun samu shatin hannu wanda akayi amfani dashi wajen shak'e Alhaji kafin aka masa wannan allurar da 'yan sanda suka kawo mana wacce aka samu a motarsa, ita dai wannan allura tana da had'ari sosai, domin tana kisa a cikin lokaci kad'an, Alhaji yaci matuk'ar wahala alokacin da akayi masa allurar, domin alokacin da aka kawosa tuni ya dad'e da rasuwa, haka wuyansa ya kumbura kuma yayi ja, gaba d'aya rahoton dana rubuta yana wajen Inspector Bello na had'a masa.
*Brr. Barau*... Jinjina kai yayi yana fad'in ko allurar da aka samu a cikin jakar da take d'akinsa tayi dai-dai da wadda aka samu a motarsa?
*Likita*... Kwarai kuwa, dukkansu iri d'aya ne.
*Brr. Barau*... Mungode likita zaka iya tafiya. Ina so zanyi tambaya ta k'arshe ga likitan da yake kula da Matar Alhaji Maiwada idan kotu ta bani izini. Kotu ta baka dama.
*Brr. Barau*.. Kotu tana so taji sunan ka da kuma bayanin binciken daka gudanar akan matar Alhaji.
*Sunana Saddik Mansur*, nine likitan da nake kula da Hajiya Bilkisu matar Alhaji Maiwada, bayan da 'yan sanda suka kawo ta sai muka gano cikin da yake jikinta ya zube sakamakon fad'uwar da tayi asamanshi da k'arfi, haka kuma a rahoton da aka bada na cewar fyad'e ne yayi silar zubewar cikinta maganar gaskiya babu alamun wani fyad'e, sanadiyar bugun da akayi mata akai yasa ta faad'i saman cikin wanda ya jawo zubewarsa, sannan taji abinda ya firgita ta, sannan sakamakon bugun da akayi mata akai ya jawo ta samu tab'in hankali wanda yanzu haka tana kwance tana karb'ar taimako daga gare mu, sai bincike na k'arshe shine mun samu jini a cikin farcenta, bayan da muka auna muka gano sakamakon duk na had'a na bama 'yan sanda. Wannan shine abinda na sani.
*Brr. Barau*... Likita mungode zaka iya tafiya.
Murmushi yayi yana fad'in ya mai shari'a Malan Sani yayi nasarar kashe Alhaji Maiwada ne ta hanyar daya shirya, tun daga kisan da yayima Alhaji ya tabbatar mana cewar ya dad'e yana shirya yanda hakan zata kasance, domin a daren juma'a bayan sun taso daga wajen aiki sai Malan Sani yayi dabara ya canza masu hanyar da zata sadasu zuwa gida, yayi amfani da faci ya tsayar da motar domin ya fita ya duba, da haka ne ya shiga bayan mota da niyar d'aukar wani abu kasancewar Alhaji baya zama a baya sai gaban mota, ta baya ya shakoshi kafin ya caka masa allura a wuyansa kafin ya d'auki jakar kud'in Alhaji yayi saurin barin wajen.
Yayin da yayi kok'arin hayk'ema Matar Alhaji sunyi kokowa da ita domin an samu shatin faratan ta a wuyansa, sannan jinin jikin farcenta yayi dai-dai da jinin Malan Sani, sannan an samu hoton hannunsa a nata, ganin zata tona masa asiri sai ya buga mata abu akai, ganin ta suma ya d'auka mutuwa tayi shiyasa yayi saurin barin wajen yana tunanin ya gama da ita.
Wad'annan sune sakamakon da aka samu a wajen likita da duk wata sheda da zata tabbatar ma kotu Malan Sani shine ya aikata wad'an nan laifukan da ake zarginsa dashi. Ina rokon wannan kotu mai albarka da tayi amfani da wad'annan hujjoji domin ta yanke ma Malan Sani hukuncin da yayi dai-dai dashi. Nagode.
Gaba d'aya kotu ta d'auki kus-kus kowa da abinda yake fad'a. Brr. Kamal gaba d'aya jikinsa yayi sanyi domin yasan sun fad'i, duk wata sheda Brr. Barau ya gabatar da ita, kuma ko waye dole ya yarda da abinda aka gabatar saboda sheda ce tabbatacciya, amma dole ya tashi yayi wani abu ko dan kada aga gazawarsa.
Bubbuga tebur Alkali yayi, bayan anyi shiru Alkali yace Baristan da yake kare wanda ake k'ara ko kana da abinda zaka fad'ama kotu? Tashi Brr. Kamal yayi cike da kwarin guiwa yace ina dashi ya mai shari'a, ina so nayi ma Maigadin gidan Alhaji tambaya idan kotu ta bani dama. Kotu ta baka dama maigadi ya fito.
*Brr. Kamal*... Madu a cikin bayanin daka bayar naji kace lokacin da Malan Sani ya shigo gidan ya fad'a maka akwai matsala, sannan kace kaga idanuwansa sunyi ja, sannan kaga bak'ar jaka a wajensa, shin ko waccan jakar da aka gabatar tayi dai-dai da wadda ka gani? Sannan daya shigo kaga yanayin maye atare dashi? Sannan alokacin da kace kaji ihu meyasa bakayi saurin shiga ciki ba amatsayinka na wanda yake kula da mutanan gidan? Kace Malan Sani ya fito da jini a jikinsa, sannan ka ganshi acikin yanayi na maye, amatsayinka na maigadi ya akayi ka barshi har ya fita daga gidan ba tare da ka rik'esa ba?
*Madu*.... E to gaskiya lokacin daya shigo babu yanayin Maye a tare dashi, kawai dai baya cikin natsuwarsa, alamu sun nuna kamar yana cikin tashin hankali domin jan da idanuwansa sukayi sun nuna alamun kamar wanda yayi kuka. A lokacin da naji ihu kuma dalilin da yasa ban shigaba saboda nasan Malan Sani yana ciki, kuma nasan amintaccen gidan ne, alokacin da ya fito kuma nayi kok'arin tareshi amma sai ya ture ni, kuma tabbas da yanayin maye ya fito, sai dai kafin na tashi ya fice, saboda gaskiya jikina ne yayi sanyi saboda ganin abinda ban tab'a zato ba, hakan yasa na kasa yunkurin rikeshi da kyau. Sannan kuma wannan jakar tabbas irin tace na gani a hannunsa, kuma nasan ta Alhaji ce domin koni nasha d'aukarta idan ya fito zai fita domin nasan jakarsa ce da yake saka kamfutarsa.
*Brr. Kamal*.... Kace jakar kamfutarsa ce, kenan lokacin da Malan Sani ya shigo da ita kamfutarce aciki? sannan kace ya fito cikin yanayin maye, shin ya fito da jakar ko kuma be fito da ita ba?
*Brr. Barau*... Ina da ja ya mai shari'a, duk da Madu yace yaga Malan Sani ya shigo da jaka ta kamfutar Alhaji ai be zama dole ace kamfutar bace aciki tunda alokacin be bud'a masa ba, ya kamata abokin aikina yasan irin tambayar da zaiyima mai bada sheda. Nagode.
*Alkali*... Brr. Kamal ka gyara yanayin tambayarka. Risnawa yayi yana fad'in zan kiyaye.
*Brr. Kamal*... Madu kotu tana sauraronka shin kaga Malan Sani ya fito da wannan jakar?
*Madu*.... A gaskiya ban lura da hannunsa ba, saboda yana fitowa naga jini a jikinsa sai hankalina ya tashi hakan yasa bazan iya cewa ya fito da jaka ba. Iya kar abinda na sani kenan.
*Brr. Kamal*.. Jinjina kai yayi yana fad'in mungode zaka iya tafiya. Ina so nayima Malan Sani wasu tambayoyi idan kotu ta bani dama. Kotu ta baka dama.
*Brr. Kamal*... Malan Sani kace alokacin da aka tare ku Alhaji yace ka tafi domin kaje ka tafi da iyalinshi gidan ka, shin ko zaka fad'ama kotu abinda kuka tattauna da yasa yace kaje ka tafi da matarsa.
*Malan Sani*... Tabbas Alhaji shine yace naje na tafi da Hajiya, sannan ya bani jakar kamfutarsa yace na tafi da ita saboda mutanan da suka taremu kada su ansheta dan akwai abubuwa masu muhimmanci aciki.
Hannu Brr. Barau yasa yana gyara zaman gilashinsa jin abinda Malan Sani ya fad'a, kada fa aje allura ta tono galma, kada ace Malan Sani ya b'oye wata shedar da zata tabbatar da abinda sukayi.
*Brr. Kamal*.... Malan Sani kace akwai abubuwa masu muhimmanci acikin kamfutar Alhaji hakan yasa ya baka ka tafi da ita, shin ko zaka fad'a mana wani abu wanda ka sani idan Alhaji ya sanar da kai.
*Malan Sani*... Tabbas akwai masu neman rayuwar Alhaji, kuma hakan ya faru ne saboda sun gano yasan wani sirri nasu akan abubuwan da sukayi mashi, kuma ya shirya komai yana jiran litinin tayi domin ya shigar da k'ara saboda ya samu duk wata sheda da zata tabbatar da abinda sukayi domin shedar bidiyo ce da maganganunsu aciki, wanda suka san duk abinda yayi hakan yasa suka shirya kashe shi. Wannan dalilin ne yasa ya bani kamfutar yace na tafi da ita.
*Brr. Kamal*... Ko zaka iya fad'a mana su waye suke kokarin kashe shi?
*Malan Sani*... E to wad'an da aka turo ban san su ba, amma mutanan da suke cikin kamfutar 'yan tawagar Alhaji Marusa ne kuma shine babban su domin shine abokin takun sak'ar Alhaji.
A zabure Brr. Barau ya tashi yana fad'in ya mai sharia wannan magana da Malan Sani yake fad'a ba gaskiya bane, yariga da yasan komai na Alhaji hakan yasa zeyi amfani da wannan damar ya kare kanshi domin ya ga beda wata hanyar tsira, Malan Sani yasan duk wani sirri na Alhaji, yasan cewar sun samu sab'ani da Alhaji Marusa alokacin baya, hakan yasa zaiyi amfani da wannan damar ya sako Alhaji Marusa a cikin wannan shari'ar, ina so kotu tayi watsi da wannan gurguwar hujjar ta Malan Sani tayi duba da hujjar zahiri da aka gabatar mata domin ta yanke masa hukunci, domin Malan Sani zai b'atama kotu lokaci ne kawai, kuma idan beyi hankali ba Alhaji Marusa yana da damar neman hakkinsa akan b'ata masa suna da yake kok'arin yi. Nagode.
*Brr. Kamal*... Ya mai shari'a maganar Malan Sani tana kan hanya, babu wanda besan alak'ar da take tsakanin Alhaji Marusa da Alhaji Maiwada ba, kuma tabbas hakan zata iya kasancewa domin Alhaji Marusa yana takun sak'a da Alhaji Maiwada. Inaso wannan kotu da tayi duba da maganar Malan Sani, kada tayi saurin yanke hukunci, abashi dama domin ya tabbatar da abinda ya fad'a. Nagode ya mai shari'a.
Hayaniya ce ta cika kotun. Bubbuga tebur Alkali yayi kafin akayi shiru. Kallon Malan Sani yayi yana fad'in Malan Sani ko kana da shedar da zaka tabbatar ma kotu abinda ka fad'a gaskiya ne? Duk'ar da kai Malan Sani yayi hawaye suna zubo masa yace bani da sheda ya mai shari'a domin mutanan da suka shiga gidan Alhaji sune suka amshe kamfutar da shedar take ciki.
Ajiyar zuciya Brr. Barau ya saki jin abinda Malan Sani ya fad'a.
Girgiza kai Alkali yayi yana fad'in kowa ce kotu tana amfani ne da kwakkwarar hujja kafin ta yanke hukunci, dan haka wannan kotu baza tayi amfani da abinda ka fad'a ba amatsayin hujja. Brr. Kamal idan kana da sauran tambaya kotu tana sauraronka.
Jiki a sanyaye Brr. Kamal yace bani da ita ya mai shari'a. Komawa yayi ya zauna yana jin d'aci aranshi, tabbas yasan akwai munakisa acikin wannan shari'ar, amma saboda basu da hujja dole suyi hakuri Allah zai saka masu.
*Alkali*... Brr. Barau kana da sauran abinda zaka fad'ama kotu? Tashi yayi yana fad'in bani da sauran abun fad'a, ina so wannan kotu da tayi gaggawar yanke ma Malan Sani hukunci saboda zaluncin daya aikata. Nagode.
Rubutu Alkali yayi kafin yace kotu zataje hutu na rabin sa'a. Bubbuga tebur yayi kowa ya tashi.
Zamewa k'asa Malan Sani yayi yana sakin kuka mai tsuma zuciya. Da sauri Alhaji Mansur da su Halima sukayo wajensa.
Ur's.
Nabeelert Lady[3/10, 8:38 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud'i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shoot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k'asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub'e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.*
1⃣9⃣
Hannu Alhaji Mansur yasa ya kamo Malan Sani yana fad'in kayi hak'uri Malan Sani, Allah yana tare da kai, koda sunyi nasara akan ka yanzu wallahi baza suyi nasara akan ka ba ranar lahira, Allah yasan komai, kuma yana kallon su, shine kad'ai zai saka maka, zuciyata tana mani wani tunani akan wannan Alkalin, sai dai bana so nayi zarginsa kada Allah ya kama ni da laifi, a gaskiya daga farko yanda naga yana yawan goyon bayan Brr. Barau sai nake tunanin ko an bashi cin hanci ne, amma daga baya sai na gano ko wane Alkali hakan zaiyi, domin kotu da sheda take amfani, da yawan Alkalai suna yanke hukunci bisa hujjar da aka gabatar masu, ko da hujjar ta k'aryace matuk'ar aka aminta da ita suna amfani da ita, dan haka kayi hak'uri Allah zai saka maka.
Hannu Malan Sani yasa ya goge ido shi yana fad'in bakomai Alhaji, wallahi tun ba yau ba na sadak'as, nasan dole irin wannan hukuncin ya hau kaina, shiyasa tunda farko ban tsaya b'atama kaina lokaci wajen fad'ama Brr. Barau komai ba daya tambaye ni, ai kunga alokacin banyi maganar dalilin da yasa Alhaji ya bani kamfutarsa ba, ban kawo komai na abinda nasan sunyima Alhaji ba, saboda nasan kona kawo bani da hujjar tabbatar da hakan, saboda Brr. Kamal ne yasa na bud'e baki nayi magana, shima bana so yaga yana mani kok'ari amma naki bashi had'in kai, amma kaga yanzu da yasan babu hujja zai hak'ura, wallahi na d'auki k'addarata, fatana Allah ya bani ikon cinyeta.
Cike da tausayi Alhaji Mansur yace amin Malan Sani. Cikin kuka Halima tace nikam Malan zan tafi gida, bazan iya tsayawa a yanke maka hukunci ba, ina tsoron binda zai faru dani, bana so muyi asarar abinda yake ciki na.
Jinjina kai Malan Sani yayi yana fad'in tunda na ganki naji rashin dad'in zuwanki, kinsan baki da lafiya, kuma nasan matuk'ar aka yanke mani hukunci wani abun zai iya faruwa da ke, dan Allah ki koma gida, kinga an kusa tashin su Rumaisa idan ta koma gida zata iske babu kowa, ki kwantar mata da hankali, bana so tasan abinda yake faruwa har sai ta k'ara hankali.
Alhaji Mansur yace bara mu rakata ta tafi hakan zaifi, dama tace tana son zuwa shiyasa muka taho da ita. Malan Sani yace akwai kud'i a inda nake ajewa kiyi amfani dasu, tunda kina sana'ar cikin gida ki k'ara jari nasan Allah bazai tozarta ki ba. Kai kawai ta d'aga tayi waje da sauri.
***
Bayan kowa ya dawo Alkali yashigo, nan kowa ya natsu. Zama yayi yana gyara takardu. Kotu tayi tsit tana jiran abinda Alkali zai yanke.
*Alkali*... 'Dago kai yayi yana fad'in bayan dogon bincike da kwararan hujjoji da aka gabatar agaban wannan kotu, kotu tayi dogon nazari akansu kuma ta tabbatar da ingancin su, domin duk abinda aka gabatar mata babu wanda yake na bogi, an tabbatar cewar an samu allurar da akayima Alhaji Maiwada agidan Malan Sani, sannan an tabbatar da hoton hannun jikin wuyan Alhaji yayi dai-dai dana Malan Sani, haka zalika an tabbatar da hoton jikin hannun matar Alhaji yayi dai-dai dana Malan Sani, sannan jinin da yake jikin farcenta yayi dai-dai dana Malan Sani, bayan haka Malan Sani ya gaza kawo ma kotu wata hujja da zata tabbatar da abinda ya fad'a gaskiya ne, dan haka kotu zata yanke hukunci.
*A k'arkashin penal code sashe na 302,da 201,da 180, da 340 sashen kisa amfani da makami ko wani abu, bisa la'akari da wannan sashe na kundin tsarin mulki na k'asa penal code, wannan kotu ta yanke ma Malan Sani hukuncin d'aurin rai da rai agidan yari, sannan zai biya tarar naira dubu d'ari biyar ga Iyalan Alhaji amatsayin cin zarafinta da yayi na yunk'urin haike mata, haka zalika zai biya diyya ga Iyalan Alhaji idan suna da buk'atar hakan. Kottttt!!!!.*
Gaba d'aya mutanan kotun suka mike kowa da abinda yake fad'a, wasu suna yabama Alkali da Brr. Barau abisa kok'arin da sukayi, yayin da wasu suke ganin gaskiyar Malan Sani. Haka kowa ya fita 'yan sanda suka taso Malan Sani wanda hawayen idanshi suka k'afe ya koma yin kukan zuci.
Alhaji Mansur kasa motsi yayi daga inda yake, gaba d'aya jiyake kamar amafarki abubuwan suke faruwa. Maman Labiba kuwa kuka kawai takeyi.
Alhaji Musa ne da Alhaji Usman suka k'araso wajen Alhaji Mansur, kamoshi Alhaji Musa yayi suka fito waje. Jingina sukayi da mota Alhaji Musa yana fad'in sai hak'uri Alhaji, Allah kad'ai yasan gaskiyar wannan al'amarin, domin har cikin zuciyata na kasa yarda da abinda ya faru, na jima da sanin Malan Sani haka kawai nake jin bazai iya aikata abinda akace yayi ba.
Alhaji Usman yace wallahi kaji na rantse maka banyarda da abinda aka gabatar ma kotu ba, kawai babu yanda zamuyi ne, koda zamuje kotun da tafi wannan iya hukuncin da za'a zartar kenan, saboda ko waye aka bama wannan shedun dole ya amince dasu, mu da mukasan hakan bazai yuwu ba mu kad'ai zamu iya k'aryatawa, amma an cutar da Malan Sani, domin nasan waye Alhaji Marusa, zai iya komai akan kud'i, tunda naji sun fara takun sak'a da Alhaji Maiwada nasan ba zai barshi haka ba, domin duk wani ma'aikacin kwastam da za'a kawo nan matuk'ar mai gaskiya ne Alhaji Marusa shine yake silar barinsa garin nan, saboda aminin Mr. Kallah ne shugaban Kwastam na k'asa.
Alhaji Musa yace wallahi tunda Malan Sani ya fara bada labarin dalilin da yasa aka kashe Alhaji naji na yarda da abinda ya fad'a, ko Brr. Barau beda gaskiya, domin a lokacin naga yanda yanayinsa ya canza, sai dai kawai mu barma Allah amma sun cutar da Malan Sani.
Alhaji Usman yace kasan abinda yafi bani mamaki? Brr. Barau lauyen Alhaji Marusa ne, sai gashi ana fad'in wannan abu ya fito da wuri amatsayin wanda zai kare Alhaji Maiwada, a tunanina Brr. Kamal shine lauyen daya tsayama Alhaji a wancan karon, amma sai gashi an juya abun, tun daga lokacin nasan akwai wani abu.
Ajiyar zuciya Alhaji Mansur yayi yana fad'in duk abinda zan fad'a maku bazai canza komai ba, amma kusa aranku Brr. Barau, Mr. kallah, 'Yallab'ai da Alhaji Marusa duk a rumfa d'aya suke, nasan mutane ukku d'ayan ne ban sani ba, amma wallahi su dukansu munafukai ne, babu yanda zamuyi ne dole mu barma Allah, zanje na biya tarar da akasa ma Malan Sani, sannan amatsayina na dangin Alhaji da Matarsa mun yafe diyyar da aka fad'a, kuma insha Allahu yau zamu wuce Kano, kome kenan zamuyi waya saboda Bilkisu.
Alhaji Usman yace wannan ba matsala bane, insha Allahu zata samu kulawa kamar tana kusa da ku, su kuma ka barsu, wata rana Allah zai nuna su a lokacin da basuyi zato ba, zasuji kunya tun aduniya, ina rok'on Allah ya k'ara masu tsawon kwana ko dan su girbi abinda suka shuka. Gaba d'aya suka amsa da amin.
K'arasawa sukayi wajen Brr. Kamal, anan sukayi masa godiya. Brr. Kamal kam hak'uri yayi ta basu zuciyarsa cike da damuwa. Alhaji Mansur yace haba wallahi bakomai, mun bar ma Allah.
Kafin a tafi da Malan Sani Alhaji Mansur ya rok'esu alfarmar su bashi mintuna biyar. Matsawa sukayi daga wajen suna fad'in yayi sauri.
Dafa kafad'ar Malan Sani yayi yana fad'in kasa Allah aranka, kuma kacigaba da addu'a Allah maji roko ne, sannan yana saurin amsa addu'ar wanda aka zalunta yayi hak'uri, insha Allahu wata rana zakaga sakamakon hak'urin da kayi, kuma ina tabbatar maka zaka fita daga wajen nan, ta silar Alhaji Maiwada kashigo wajen nan, domin kana aiki a k'asanshi akayi amfani da wannan aka kulla maka wannan abun, insha Allahu jinin Alhaji shine zai kwato maka hakkin ka, da izinin Allah sai Ra'eez ya zama lauya, domin tun yanzu zan fad'a masa irin zaluncin da akayi ma mahaifinsa da kai, zai tashi da burin d'aukar fansa, ta haka ne zai dage ya cimma burinsa.
Kai Malan Sani ya jinjina yana fad'in zan so naga wannan ranar, ka dage Alhaji Ra'eez yayi karatu, kada ka barshi a k'asar nan, domin har yanzu acikin makiyan Alhaji babu wanda yasan yana da 'Dah, insha Allahu sai Ra'eez ya basu mamaki.
Ayanzu da kayi wannan maganar sai naji wani haske ya ziyarci zuciyata, kuncin da nakeji yayi sauki, inajin zan shiga gidan yari hankali kwance, kuma zan zauna ba tare da wata damuwa ba, domin bazan bari damuwa ta kamani ta kassara lafiyata ba, zan roki Allah ya ara mani rana domin naga wannan rana da kake fad'i, nagode sosai Alhaji.
Alhaji Mansur yace haka nake son ji Malan Sani, ayanzu kasa zuciyata tayi dad'i, domin damuwakar zata sa naji babu dad'i, amma ayanzu nasa burin d'aukar fansa, zan tsaya ma Ra'eez har ya kai matsayin da zai tsaya mana, kuma insh Allahu zan kula da matarka da d'iyar ka, Allah ya k'ara maka hak'uri.
Malan Sani yace amin. Haka aka tasa Malan Sani suka shiga mota mutane sai kallonshi akeyi, shi ko gaba d'aya yaji damuwarsa ta ragu sosai, haka suka bar kotu.
***
Hannu Halima tasa ta goge idonta bayan ta gama jin abinda ya faru, sannan Alhaji Mansur ya fad'a mata yanda sukayi da Malan Sani.
Murmushi tayi wanda yafi kuka ciwo tana fad'in daga yau nima zanyi yaki da damuwar da take zuciyata, dole nayi irin ta Malan matuk'ar ina so naga wannan rana, haka idan ina so na raini yaran mu dole na cire komai araina, zan toshe kunnuwana daga jin surutun mutane, zan bama kowa mamaki domin zan kasance jarumar mace wadda tafi wasu mazan, Allah ya shige mana gaba.
Alhaji Mansur yace amin Halimatu, hakika kin k'ara sanyaya mani zuciyata da kalamanki, kamar yanda kika d'auki wannan k'addarar ina tabbatar maki Allah bazai barki haka ba, zan tsaya akan al'amuran ku, duk wata matsala bana so ki b'oye mani, ki d'auke ni amatsayin Yayanki, ga Maman Labiba nan ki d'auketa amatsayin 'Yar uwarki, insha Allahu babu abinda zai gagara.
Jinjina kai Halima tayi tana masu godiya. Alhaji Mansur yace zamuje can gidan domin a kulleshi, zan aiko da duk wasu kayan abinci da suke gidan saboda idan an barsu zasu lalace, nasan hakkin Ra'eez ne da Bilkisu, kuma zan masa bayani nasan bazai hana a baku ba, ita kuma Bilkisu ga halin da take ciki, saboda haka babu wata matsala dan an baku abinci, sauran kayanta zan aikama Likita dasu saboda arika kula da tsaftar ta, idan akwai wad'an da ya kamata abayar zan fad'a masa ya aika dasu gidan marayu, haka kayan Alhaji duk zan tafi dasu, idan Ra'eez ya d'auki wanda yake so sauran za'a bada sadakarsu dan banga amfanin ajesu ba, sauran abinda yake da amfani duk zamu tafi dasu, kaya masu nauyi ne kawai zamu bari nasan babu abinda zai samesu, domin munyi magana da Alhaji Musa yace zai kawo maigadin da zai zauna agidan sai na rik'a biyanshi saboda Madu yace bazai iya zama ba.
Halima tace mungode sosai, Allah ya biyaka da alkhairinsa, kuma insha Allahu zan rik'a zuwa duba Ummun Ra'eez sai ka fad'a mani sunan asibitin.
Alhaji Mansur yace sai dai muje tare domin likitan ya ganki, dan na fad'a masa kada ya yarda da kowa, tunda gaki ke kad'aice wadda zata rik'a zuwa wajenta dan ina jin tsoron a illata ta. Maman Labiba tace wannan haka yake.
Tashi yayi yana fad'in bara muje mu fara da wuri dole ma sai gobe zamu tafi saboda mu gama komai, tunda ga mota Alhaji Musa ya bani nayi zirga-zirga da ita gara na gama, idan zamu kawo kayan abincin sai ki shirya muje can asibitin. Halima tace shikenan sai kunzo.
**
Duk wani abu mai muhimmanci na takardun Alhaji sai da suka had'asu a cikin akwati, kayansa kaf sun had'a, dama shi Alhaji Maiwada baya tara sutura, da yayi d'inki yake bayar da wasu dan baya son tara kaya.
Haka kayan Ummu duk sun had'a mata, sai kayan abinci suka had'a komai sukasa amota. Madu sai kuka yakeyi. Suna cikin had'a kaya sai sukaji sallamar Ladi.
Bayan tashigo sai tayi turus, kada dai abinda takeji gaskiya ne? Tunda ta shigo Lagos a mota take jin ana wani labari, sai dai bata gazgata ba. Ganin Madu yana kuka yasa tayi saurin matsowa tana tambayarsa.
**
Kuka kawai Ladi takeyi bayan da ta gama jin komai. Maman Labiba tace sai hak'uri Ladi, haka Allah ya tsara bamu da hanyar kaucewa. Ladi tace ikon Allah, wannan abu da me yayi kama? Da zan tafi dubu ashirin Alhaji ya bani kud'in gudummuwa Hajiya ta k'ara mani goma ashe shikenan rabuwar kenan, ya Allah kajik'an Alhaji, itama kuma Hajiya Allah ya bata lafiya, Malan Sani kuma Allah ya saka mashi.
Gaba d'aya suka amsa da amin. Ladi tace dan Allah kuje dani na gano Hajiya, shikenan yanzu dole na koma gidana amma insha Allahu bazan manta da alkhairinsu ba. Alhaji Mansur yace shikenan bara mu k'arasa sai mu tafi.
Ladi tana kuka haka ta tayasu had'a kaya, sun bata wasu kayan abincin hada wasu kayan Ummu Maman Labiba ta bata. Alhaji Mansur yace zaije ya ciri kud'i sai ya basu na sallamarsu. Haka suka rufe ko ina bayan sun zare mahad'ar wutar gidan, dama kuma wutar kati ce.
Bayan sun fito suka rufe gate d'in gidan suka tafi hada Madu, Alhaji Mansur yace idan ya dawo anjima sai ya bama Alhaji Musa mukullin gate d'in da motarsa tunda a hotel zasu kwana saboda da wuri zasu tafi.
Sai da suka aje kayan sannan suka d'auki Halima suka nufi asibiti. A mota sai jajanta ma Halima Ladi takeyi tana fad'in tunda unguwarsu babu nisa bazata yarda zumunci ba.
***
Kallon su kawai Ummu takeyi, domin tunda ta farka bata magana sai kallon mutane. Ganin su Halima da Ladi suna kuka yasa itama ta fashe da kuka. Girgiza kai Dr. Saddik yayi yana fad'in abinda takeyi kenan tunda ta farka, idan ta gama kallon mutum sai kawai ta fashe da kuka.
Alhaji Mansur yace yaushe ne za'a maidata can? Dr. Saddik yace nan da kwana biyu idan ta k'arasa warwarewa.
Alhaji Mansur yace ga Halima nan itace Matar Malan Sani, idan ba ita ba kada abar kowa yazo wajenta. Dr. Saddik yace wannan ba damuwa, zan amshi lambarta kome kenan zan rik'a mata bayani. Alhaji Mansur yace mungode likita.
Haka suka gama ganinta ba tare da tace masu komai ba suka tashi zasu tafi bayan sun aje akwatin kayanta. Har sun kai k'ofa sukaji muryarta tana fad'in Abbun Ra'eez sun kashe shi, akira mani Ra'eez kada su kashe mani shi. Saurin juyowa sukayi gaba d'aya.
Shiru tayi sai kuma ta fashe da kuka tana fad'in duk saina kashe su da wuk'ar makka. Hatta da Alhaji Mansur sai da kwalla ta cika masa ido, jiki a sanyaye suka bar d'akin. Dr. Saddik yace kada ku damu, dama fatana ta fara magana, tunda ta fara sai mugodema Allah, insha Allahu zata samu lafiya. Alhaji Mansur yace mungode sosai. Haka sukayi mashi sallama suka tafi.
**
Bayan Alhaji Mansur ya ciro kud'i yayi masu sallama mai tsok'a, godiya sukayi mashi Madu yace zai tafi. Alhaji Mansur yace wai Madu yanzu ina zakaje? Madu yace zanje na nemi wajen da zan zauna kuma.
Da sauri Halima tace idan zaka yarda ka zauna a shagon waje na gidan mu hakan zai zamar mana tsaro musamman yanzu da babu namiji agidan dan Allah.
Jinjina kai Alhaji Mansur yayi yana fad'in maganar ki gaskiyace, abinda zuciyata take tunani kenan. Dan Allah Madu ka zauna hakan zai zame masu kariya, kaga akwai Rumaisa, kuma kana da amana ka zama tamkar d'an uwa agaremu, duk da wanda ya had'amu baya raye be kamata mubar abinda ya had'a ya lalace haka ba.
Jinjina kai Madu yayi yana fad'in shikenan zan zauna sai na rik'a biyan kud'in haya. Halima tace wallahi bazamu amsa ba, kayi zamanka har mutuwa ta raba babu wani abu, dama mutanan unguwar sun saba ganinka agidan, dan ka dawo ba wani abu bane, tunda shagunan biyu ne sai ka bud'e shagon saida abubuwa a d'ayan dama Malan Sani yana so ya bada hayarsa, tunda ga yanda komai ya kasance sai kawai kayi amfani dashi saboda kada ka zauna haka, akwai band'aki a cikin d'ayan shagon sai ka d'aukeshi a d'akin ka.
Alhaji Mansur yace wannan haka yake, kuma bana so kace a'a. Madu yace shikenan nagode da wannan abu da kukayi mani, wallahi da zan iya zama agidan Alhaji da bazan bari wani ya zauna ba, kawai idan na zauna hankalina bazai kwanta ba, amma nine yafi cancanta na zauna na rik'e amanar gidan, amma duk da haka zan rik'a kula da gidan bazan bari wani abu ya sameshi ba, saboda wanda za'a ba gadin gidan abokina ne agidan Alhaji Musa yake gadi su biyu ne.
Alhaji Mansur yace bakomai Madu na fahimceka, kunyi sabo sosai da Alhaii, dama nasan bazaka iya zama agidan ba, hakan ma da zakayi yayi, dan haka zan fad'ama Alhaji Musa kaine zaka rik'a kula da gidan. Madu yace nagode.
Bayan sun aje su aka bud'ema Madu shagunan domin ya gyara, katifarsa daya d'auko da kayansa ya shigar dasu ciki kafin ya gama gyara. Ladi kuwa sallama tayi masu tana godiya kafin ta sake zagayowa saboda basu da nisa.
Kud'i Alhaji Mansur ya bama Halima masu yawa yana fad'in idan zaiyi aike zai turoma Dr. Saddik sai yarik'a bata tunda bata da account. Godiya tayi masa kafin suka fita.
A mota yake fad'ama Maman Labiba zasuje ya kama d'aki sai ya barta ta huta yana so yaje yaga Mr. Kallah yasan gobe zai koma abuja, duk da sune suka kashe Alhaji amma shine shugabansu ta hanyarsa za'a samu kud'in Alhaji su fito cikin sauki, kuma idan yaga yaje wajensa da maganar zaifi maida hankali kodan su fita daga zargi.
**
Bayan ya kama d'aki suka shiga, wanka ya farayi kafin yayi sallah yasa aka kawo masu abinci sukaci. Tashi yayi yana fad'in ta kulle zaije ya dawo. Addu'a tayi masa kafin ya nufi wajen Mr. Kallah.
Ur's.
Nabeelert Lady🖋
[3/10, 8:38 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud'i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shoot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k'asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub'e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.*
2⃣0⃣
Gaba d'aya kunya ce ta rufe Mr. Kallah, ji yake kamar Alhaji Mansur zai gano su, da kyar yasa jarumta aranshi. Canza fuska yayi zuwa kalar tausayi yace yanzu shikenan fa, har yanzu na kasa mantawa da mutuwar Alhaji Maiwada, shiyasa muka tsaya sai da aka yanke ma direbansa hukunci domin munyi zaman amana da Alhaji.
Alhaji Mansur yace an dai yanke hukunci, amma wad'an da suke da laifi ai sun san kansu dan wata shari'ar sai alahira.
K'warewa Mr. Kallah yayi da sauri ya d'auki ruwa yasha. Murmushi Alhaji Mansur yayi yana fad'in sannu. Kai Mr. Kallah ya d'aga yana fad'in yanzu meke tafe da kai? Alhaji Mansur yace akan maganar kud'in Alhaji Maiwada ne.
Jawo takarda Mr. Kallah yayi yana fad'in wannan baka da damuwa, Alhaji Maiwada na mu ne, dole mu tsaya komai nashi ya fito. Yanzu ka bani lambarka kome kenan zamuyi magana, amma ina tabbatar maka kud'inshi bazasu dad'e ba nayi maka alk'awari.
Jinjina kai Alhaji Mansur yayi yana fad'in nagode sosai, kawo wayar taka nasa maka lambartawa. Bayan ya gama saka masa yayi masa sallama, har bakin mota Mr. Kallah ya rakoshi.
Yana tafiya ya saki ajiyar zuciya. Ciki ya koma yana lalaubar lambar Alhaji Marusa. Yana d'agawa Mr. Kallah ya fad'a masa yanda sukayi da Alhaji Mansur.
Alhaji Marusa yace abokina kasan yanda zakayi komai ya fito cikin lokaci, bana son asake tada maganar Alhaji Maiwada, gara a sallamesu nasan bazai sake zuwa garin nan ba.
Mr. Kallah yace amma ina tsoron matarsa ta warke ta tona mana asiri. Alhaji Marusa yace ai babu abinda ta sani, iyaka tace Malan Sani beyi mata abinda aka fad'a ba, amma bazata k'aryata kisan da muka d'ora masa ba, idan kuma kana ganin akwai matsala itama tabi bayan mijinta kawai.
Da sauri Mr. Kallah yace haba Alhaji, wai wace irin zuciya kake da ita ne haka? Kai kisa baya maka wahala, kada kamanta rayuwaka biyu muka kashe fa, dan Allah kabar wannan maganar, shikenan bani da wata damuwa akan matarsa abarshi ahaka gobe ma zan koma abuja daga can zanje waje nayo sati biyu dan na samu natsuwa.
Dariya Alhaji Marusa yasa yana fd'in abokina kacika tsoro, nifa akan dukiyata babu abinda bazan iya ba, dan haka kadena sako mani maganar wata matsala. Mr. Kallah yace shikenan na dena. Sallama sukayi Alhaji Marusa yana ta tsokanarsa.
****
Wai Maman Naseer baza kici abincin ba, haba dan Allah, ya kike so nayi ne, ga rashin Naseer ke kuma kina so ki jefa kanki cikin damuwa.
Hannu tasa ta goge idonta tana fad'in yanzu shikenan haka zamu bar wad'an da suka kashe Naseer susha banza kenan Baffan Naseer, kana gani wanda aka kashe su a rana d'aya har an yankema makashin hukunci amma mun kasa tab'uka komai sai kace an kashe mana karan gida.
Hannunta ya kamo yana fad'in Hajiya Zainabu Abu kenan, wani lokacin mata k'aramin tunani gare ku, shi wanda aka yanke ma hukuncin kinsan irin hujjojin da aka gabatar ma kotu kuwa? To bari kiji, duk da banje kotu ba a labarai naji yanda shari'ar ta kasance, hatta da lauyen da ya tsayama Alhaji Maiwada sai da aka bashi lambar yabo domin ya gabatar da shedu kwarara wanda a kowace kotu akaje dole ta amshe su, kinga kuwa bazamu had'a kanmu da su ba.
Ni na barma Allah akan mutuwar Naseer, domin nasan zamusha wahala ne kawai idan mukace zamu nemo wad'an da suka kashe shi, domin babu wata alama da aka bari a mutuwar Naseer, ko Waye ya kashe Naseer ba k'aramin makashi ba ne, abinda nake so da ke kema ki barma Allah sai ya saka mana.
Jinjina kai tayi tana fad'in shikenan Baffan Naseer tunda ka fad'i haka, insha Allahu bazan sake d'aga maganar ba, dama su biyu Allah ya bamu koma waye ya aikata hakan zan cigaba da addu'a Allah ya tona asirinsa.
Baffa yace amin Zainabu. Murmushi tayi tana goge fuskarta. Sallamar Yayan Naseer ce tasa suka kalli k'ofar tare da amsawa. Zama yayi yana fad'in sannun ku da gida. Baffa yace yauwa sannu *RAFIK*.
Maman Naseer tace ga abincinka a kicin ka d'auko kaci ina kaje haka ne? Kallonta yayi yana fad'in Mama kinci naki ko? Baffa yace ina fa taci, yanzu nake mata magana kasan yanda tasa damuwa akan rashin gano wanda ya kashe Naseer aranta.
Maman Naseer tace baka bani amsata ba. Rafik yace naje wajen Junaidu ne nayi masa gaisuwa kinsan makarantar mu d'aya shima k'aninsa ne aka tsinci gawarsa an kashe shi da wuk'a kuma d'an makarantar su Naseer ne, shine naje nayi masa gaisuwa kinsa abokina ne abu iri d'aya muke karantawa ma.
Baffa yace ikon Allah, dama fa naji ana sanarwa a masallaci an kashe d'an makarantar su Naseer har nake cewa nazo gida naji ko Naseer yasan shi ashe nima bazan iske nawa d'an ba, ya Allah ka tona asirin ko suwa suke aikata wannan mugun abun, ace duk lokaci guda akashe mutum ukku.
Maman Naseer tace shiyasa nake damuwa da mutuwar Naseer, ina ma akwai wata sheda da mun shiga kotu. Rafik yace haba Mama mu barshi da Allah kawai, wahala zamusha idan mukace zamu shigar da k'ara domin babu sheda, Allah yajik'an Naseer ya bamu ikon jure rashinsa kawai, gashi yau har anyi sadakar ukku ma.
Baffa yace amin dai. Yaushe zaka koma makaranta? Rafik yace sai anyi kwana bakwai sannan, shima saboda mun kusa fara jarabawa ne. Baffa yace wannan karatu naku akwai wahala ko? Rafik yace da sauki Baffa, idan muka dawo sai munyi (IT) kafin mu koma.
Baffa yace lallai kace zaka fara karanto labarai. Rafik yace da saura dai, ai yanzu muka fara baza'a bamu karanta labarai ba, zamu dai je muga yanda akeyi.
Mama tace ina ruwan Rafik d'an jarida. Dariya sukayi Baffa yace zamusha tambaya dai. Rafik yace Baffa ai sai a wajen aiki ake surutu amma agida wazan ma tambaya. Baffa yace Allah dai ya taimaka ya cika maka burinka ka zama cikekken d'an jarida. Gaba d'aya suka amsa da amin.
**** ****
Washe gari tunda wuri suka bar kano cike da kewar su Alhaji Maiwada. Alhaji Mansur sai da yayi kwalla lokacin da jirginsu ya tashi saboda tunowa da amininsa kuma d'an uwansa.
***
Koda Halima ta gama abincin safe sai ta zuba ma Madu ta bama Rumaisa ta kai masa. Da fara'a Madu ya amsa gaisuwarta yana fad'in hada abinci haka, to kice mata nagode sosai.
Bayan ta koma taci abincinta Halima tace Rumaisa ki maida hankali akarantun ki kinji, kinga Babanki yace idan baki karatu zaku b'ata. Rumaisa tace Mama yaushe Baba zai dawo to? Halima tace Babanki yayi tafiya shida Abbun Ra'eez zuwa wata k'asa bazasu dawo ba sai kunyi girma.
Dariya Rumaisa tasa tana fad'in zasu kawo mana tsara ko? Halima tace sosai kuwa, ke dai ki maida hankali kiyi karatu, babu ruwanki da k'awa kiyi rayuwarki ke kad'ai domin k'awaye gori garesu, ko tashi akayi kada ki tsaya kowa kiyi tahowarki kinji.
Kai ta d'aga tana fad'in ai babu ruwana da kowa idan akayi break ma ni kad'ai nake zama naci abincina, kuma kinga Auntyn mu tace saura sati biyu muyi hutu da mun dawo zamu shiga aji biyar ai kinga mun kusa gamawa.
Halima tace sosai ma kuwa, shikenan sai atafi wata makarantar. Rumaisa tace to Mama zan tafi kada amun duka. Halima tace Allah ya ba da sa'a kiyi addu'ar fita daga gida kinji, kuma duk wanda ya tare ki yana maki tambaya akan Babanki ko kallonsa kada kiyi, kome zaice kitafi kada kitsaya duk karya sukeyi kinji. Rumaisa tace to bazan tsaya ba.
Bayan Halima ta gama karyawa sai ga Sister Hassana tashigo dan su gaisa. Zama tayi suka gaisa, bayan sun gama gaisawa tace Maman Rumaisa ashe haka abu ya kasance kuma? Duk'ar da kai Halima tayi tana kok'arin maida kwallar data taho mata.
Sister Hassana tace Allah ya kyauta gaba, dan Allah Maman Rumaisa kada kisa damuwa aranki, wallahi har cikin raina ban yarda da abinda akace Malan ya aikata ba, kinsan dama haka aikin Kwastam yake, matuk'ar zakayishi da gaskiya dole ka samu makiya musamnan masu kud'i, dan haka kicigaba dayi masa addu'a wata rana gaskiya zata fito, Allah ya baki ikon jurewa.
Halima tace amin nagode Sister Allah ya bar zumunci. Sister Hassana tace amin. Ina so duk abinda kike da buk'ata kiyi mani magana matuk'ar befi k'arfina ba zanyi maki, ina fatan kina shan maganin ki? Halima tace ina sha, sister tace yauwa, idan yashiga watan fara zuwa awo sai ki fara insha Allahu babu abinda zai gagara.
Halima tace nagode sosai. Dubu biyu Sister Hassana ta aje mata tana fad'in zan wuce sai na dawo. Halima tace nagode sister Allah ya saka da alkhairi tace amin.
Har ta juya ta dawo tana fad'in yauwa wannan mutumin da nagani a shagon k'ofar gida kamar ina ganinsa yana zuwa wajen Malan ko? Kai Halima ta d'aga mata kafin ta bata labarin yanda akayi.
Murmushi Sister Hassana tayi tana fad'in amma gaskiya ya kyauta, irin wad'annan mutanan ba'a barinsu domin suna da amana, kuma nima naji dad'in zamanshi anan domin kariya ce, a jiya har Dadyn 'yan biyu yana mani magana ko a samo maki maigadi saboda tsaro, to sai kuma daya dawo da dare yake fad'a mani yaga wani mutum a shagon gidan idan nashigo na tambayeki ashe ma na gida ne.
Halima tace wallahi kuwa. Sister Hassana tace to Allah ya k'ara tsarewa, ita kuma Allah ya bata lafiya. Halima tace amin. Sallama tayi mata ta fita.
Madu ne yayi sallama ya tsaya a zaure. Hijabi Halima ta d'auka ta lek'a. Bayan sun gaisa ya k'ara jajanta mana kafin yace dama kasuwa zaije yayo sarin kaya shine ya leko ko tana da sako.
Halima tace ina da sako kuwa, bari na rubuto maka abubuwan da za'a siyo mani, tunda zaka bud'e shago sai na canza wasu abubuwan da nake saidawa a gida.
Madu yace baza'ayi haka ba, ki rubuto mani abubuwan da kike saidawa sai asiyo maki a zubasu ashago sai na rik'a saida maki, sauran abinda baza'a aje a shago ba kuma sai ki ajeshi a cikin gida.
Murmushi Halima tayi tana fad'in nagode sosai Madu. Yace haba ai bakomai, zan samo littafi sai arik'a rubuta komai. Halima tace haba meye na wani rubutu. Madu yace ko musulunci ya yarda da rubutu ai, dan haka babu komai. Halima tace nagode sosai.
**** ****
A washe garin ranar da suka dawo Alhaji Mansur ya nufi makarantar su Ra'eez, bayan sun gama gaisawa da shugaban makarantar ya fad'a masa abinda yake faruwa. Shugaban makarantar yace Allah sarki, ashe Alhaji Maiwada yana da yaro a makarantar nan? Alhaji Mansur yace wallahi kuwa, da yake nine na ke zuwa wajensa shiyasa.
Jajanta masa yayi kafin yace yanzu jarabawa sukeyi saura sati d'aya suyi hutu, ranar juma'ar nan suke gamawa kaga yau saura kwana biyu kenan tunda yau muna laraba, me zai hana kayi hak'uri zuwa ranar juma'a sai kazo ka tafi dashi.
Alhaji Mnsur yace haka ne kuma, idan yasan Mahaifinsa ya rasu zai shiga damuwa wata kilama ya kasa rubuta jarabawar, shikenan, dama ina jin tsoron kada yasan labarin daga sama ne, amma tunda sun kusa gamawa ranar juma'ar zan dawo. Shugaban makarantar yace bakomai Allah yajikansa. Alhaji yace amin. Sallama yayi masa ya tafi.
***
A ranar juma'a yazo ya d'auki Ra'eez, duk hankalin Ra'eez ya tashi ganin anzo d'aukarsa ba'ayi butu ba, duk da Alhaji Mansur yace masa bakomai amma hankalinsa yaki kwanciya, saboda sunsha ganin ana zuwa d'aukar wasu idan iyayensu suka rasu.
Tun amota Ra'eez ya fara kuka, Alhaji Mansur sai lallashinsa yakeyi shima hawayen suna shirin zubo masa, ganin Ra'eez sai ya sake dawo masa da mutuwar sabuwa.
Haka suka isa gida ba tare daya fad'a masa komai ba. Maman Labiba ma tana ganin Ra'eez ta fashe da kuka, saurin juyawa Alhaji Mansur yayi saboda hawayen da suka zubo mashi.
Zama Ra'eez yayi yana sakin wani kukan. Ya jima ahaka kafin Alhaji Mansur yafito. Abinci yasa Maman Labiba ta kawo masa, sai dai duk yanda sukayi yaci kinci yayi.
Gyara zama Alhaji Mansur yayi ya jawo Ra'eez, cikin kwantar da hankali ya fara bashi labarin abinda ya faru......
Ra'eez yasha kuka bana wasa ba, wanda kukan da yakeyi ya sakar masa zazzafan zazzab'i lokaci guda. Gaba d'ayansu suma kukan sukeyi, jin jikinshi yayi zafi sosai yasa Alhaji Mansur ya kaishi d'akinsa, rigarsa ya cire ya kawo ruwa ya fara goge masa jikinsa.
Ya dad'e yana masa haka har sai da jikin yayi sauki, magani yasa Maman Labiba ta kawo masa, tadashi yayi yasha sannan ya kwanta, cikin lokaci kad'an bacci yayi gaba dashi.
Fitowa sukayi Maman Labiba tana fad'in irin wannan ranar nake tsoro, dole Ra'eez yashiga damuwa, domin yasan komai akan Iyayensa, Allah ne kawai zai saka masa, bawan Allah gashi dai yaro amma yana da halin manya.
Alhaji Mansur yace bazan bari sai nan da shekara biyu kafin ya gama makaranta ba, tunda yana da kok'arinsa idan sun koma makaranta aji biyar zai shiga, zanyi magana da shugaban mkarantar asa sunanshi cikin 'yan aji shidda domin ya zana jarabawa acikinsu, kinga zuwa shekara mai zuwa sune zasu gama sai kawai yaje ya fara karatunshi.
Maman Labiba tace hakan yayi dai-dai, Allah ya saka masa kok'ari da hazak'a ya kuma bashi ikon cimma wannan burin da muka d'auka. Alhaji Mansur yace amin.
**** ****
Tun daga wannan lokacin Ra'eez ya koma shiru-shiru, hatta wasan da sukeyi da Labiba tamkar abokan wasa yanzu sai dai yayi murmushi, gaba d'aya baya dariya sai ta kama dole, a islamiyarsu kuwa sosai yake maida hankali, yanda kasan an bud'e masa kwakwalwa yanzu haka yake karatu, duk abinda ya d'auka sai ya iyashi.
Kasancewar dogon hutu ne na canjin aji yasa suka dad'e agida, ana saura sati biyu su koma ya roki Alhaji Mansur akan suje Lagos yaga Ummunsa. Babu b'ata lokaci Alhaji Mansur ya amince, dama saboda kada ya tada masa hankali yasa bece suje ba. Haka suka shirya suka tafi su biyu dan ta jirgi suka bi.
**** ***
Halima tana zaune tsakar gida ita da Rumaisa suna gyara alaiyahun da zata zuba amiya, sai sauri sukeyi dan Alhaji Mansur yayi mata waya tun jiya yace zasu zo. Rumaisa sai murna take Yayanta zai zo.
Bayan ta gama komai suna zaman jiransu sai sallama sukaji, hakan yasa Rumaisa tayi saurin tashi tana murna. Amsa sallamar Halima tayi ta sako hijabi tana fad'in bismilla sannun ku da zuwa.
Shigowa sukayi Ra'eez yana goge idonshi, dan tunda suka sauka a Lagos yake kuka. Idanuwan Halima ne suka cika da kwalla ganin Ra'eez. Bayan Rumaisa tayi masu shimfid'a suka zauna.
Bayan sun gama gaisawa Halima ta kamo Ra'eez tana shafa kanshi sai hak'uri take bashi. Zama Rumaisa tayi tana fad'in Yayana kadena kuka mana, ai Mama tace da Baba da Abbu sunje unguwa sai na girma zasu dawo kaima kadena kuka kaji.
Murmushi Ra'eez ya saki hawaye suna zubo masa jin shirmen Rumaisa. Dad'i Alhaji Mansur yaji ganin Rumaisa tasa Ra'eez murmushi.
Tashi Halima tayi zata kawo masu abinci Alhaji yace Halima bar abincin nan sai anjima, yanzu ina so muje wajen Bilkisu ne, ina Madu ko baya nan ne? Halima tace yanzu ya leko yace mun zaije can gidansu Alhaji ya dawo.
Alhaji Mansur yace Allah sarki, ya zaman naku yake babu wata matsala ko? Halima tace babu komai wallahi, ai Madu ya zame mani tamkar d'an uwana, dole Alhaji yake rik'eshi, domin mutum ne mai gaskiya da amana, babu abinda bayayi mana, cefane duk bayan kwana biyu sai yayo mana, haka Rumaisa shine yake bata kud'in tara, sannan ya amshi kayan da nake sayarwa anan yasa ashago yana tara mani ribar, gaskiya babu abinda zance sai Allah yasa albarka, amma Alhaji ya tafi ya barmu da masu kula damu, Allah yajik'ansa.
Alhaji Mansur yace amin, ai gaskiya Madu mutumin kirki ne, Allah ya saka masa da alkhairi, ina Ladi fa? Halima tace jiya ma tazo nan mun wuni sai yamma ta tafi, gaskiya ta rike alkawari tana zuwa wallahi, gaskiya bana cikin damuwa sai ta rashin Malan, amma Allah ya had'ani da mutanan arziki, ga Sister Hassana da mijinta babu abinda basa mani, wancan satin ma naje naga M.....
Shiru tayi ganin Rumaisa tana wajen. Alhaji yace na gane, yana lafiya ko? Halima tace lafiya lau, dan naji dad'in ganinsa a haka, shine ma yasa hankalina ya k'ara kwanciya dan shima ya kwantar da nashi hankalin.
Alhaji Mansur yace idan kin gama muje asibitin sai muwuce wajensa, Rumaisa kije gidan Sister ki zauna zamuje mudawo kinji. Kai ta d'aga tana fad'in Yayana taho muje.
Alhaji Mansur yace asibiti za'a kaishi yanzu zamu dawo. Rumaisa tace wayyo sannu kaji, idan anyi maka allura da zafi ka fad'a mani zan rama maka.
Dariya Ra'eez yasa yana kallonta. Da mamaki Alhaji Mansur yake kallonshi ganin yayi dariya. Gyara wajen Halima tayi suka fita.
***
Kasancewar an mayar da Ummu asibitin Mahaukata yasa suka nufi can. Suna zuwa shima Dr. Saddik ya isa dan sunyi waya dashi. Bayan sun biya mai mota kud'insa suka k'arasa ciki.
Da fara'a Dr. Saddik ya tarbe su, bayan sun gama gaisawa suka shiga ciki. Ofis d'in *Dr. Najib* suka nufa. Bayan sun gama gaisawa Alhaji yayi masa godiya akan kok'arin da yakeyi. Dr. Najib yace haba bakomai wallahi, ai jikinta da sauki sai dai acigaba da addu'a.
Alhaji yace mungode fa. Dr. Saddik yace muje su gaisa ga yaronta nan. Dr. Najib yace ikon Allah, sannu kaji sai hak'uri. Kai kawai Ra'eez ya d'aga yana maida kwallar data taho masa.
Suna tura k'ofar d'akin da take Ra'eez yayi saurin shigewa, jikinsa har rawa yakeyi yana so yaga Ummunsa. Kwance take idanuwanta a rufe kamar me bacci.
K'arasawa Ra'eez yayi ya kamo hannunta hawaye suna zubo masa, a hankali ya furta Ummunah! Da sauri ta mik'e tsaye, ganin Ra'eez agabanta yasa ta kwala k'ara tana fad'in Ra'eez sun kashe shi, wallahi sun kashe shi, ka samo mani wuk'ar Makka sai na kashe su dukansu.
Tashi Ra'eez yayi yana kuka ganin yanda Ummunsa ta koma, su kansu sai da jikinsu yayi sanyi ganin yanda tsigar jikinta ta tashi sai rawa jikinta yakeyi. Hannu tasa ta rik'e kanta tana wani k'ara.
Da sauri Dr. Najib yayo kanta, kafin ya k'araso ta tafi zata faad'i, aguje ya tareta ta fad'a jikinsa a sume.
Ur's.
Nabeelert Lady🖋
[3/10, 8:39 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud'i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k'asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub'e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.*
2⃣1⃣
Sai da aka yi mata allurar bacci kafin suka samu kanta, gaba d'aya yau jikinta ya rikice zuwan Ra'eez. Bayan ta samu bacci Dr. Najib yace suje ofis.
Kallon su yayi yana fad'in ayau naga wani canji atare da ita ganin d'anta da tayi, alamu sun nuna bata mance dashi ba, kuma ina ganin idan tana ganinshi zata iya tunawa da wani abun, tunda kace karatu yakeyi mai zai hana duk hutu yarik'a zuwa yana ganinta kila ta haka zamu samu shawo kanta.
Gyara zama Alhaji Mansur yayi yana fad'in likita zuwan Ra'eez bazai yuwu ba, domin zai shiga aji shidda, kuma kaga zasu fara karatu mai zurfi ga islamiyya yanayi hakan nema yasa koda Mahaifansa suna nan baya zuwa wajensu, bayan nan kuma gaskiya waje nakeso yayi karatu, akwai wata makaranta *Queen Mary*, law school ce a Landon, tunda nasa ma raina inaso ya karanci fannin shari'a na fara duba makarantu masu kyau, hakan yasa na zab'a masa wannan makarantar, kuma bana so idan ya tafi ya rik'a dawowa, amma tunda akwai wannan lalurar zanyi kok'ari yarik'a zuwa ko so d'aya a shekara ne.
Jinjina kai Dr. Najib yayi yana fad'in kaima da naka uzurin, bakomai, tunda zai rik'a zuwa hakan ma yayi, dama bana so ace kwata-kwata bazai rik'a zuwa ba domin yin hakan zai maida mu baya.
Alhaji yace insha Allahu zai zo, Allah ya bata lafiya. Gaba d'aya suka amsa da amin. Tashi sukayi suka masa godiya. Ra'eez yace abarsa a wajenta. Alhaji Mansur yace Ra'eez kaga ciwonta yana tashi kana so tarik'a shan wahala? Kai ya grigiza yana goge hawayen idonshi.
Alhaji Mansur yace kayi hak'uri zan barka a gidan Maman ku kayi sati d'aya kaga idan zata zo ganin Ummunka sai kuzo tare kaji. Kai ya jinjina.
Murmushi Dr. Najib yayi yana fad'in gara kasa juriya azuciyarka hakan zaisa kayi karatu sosai, idan kasa damuwa aranka bazaka gama karatu da wuri kazo ka kwato maku hakkin ku ba.
Godiya sukayi masa suka tafi. Dr. Saddik yaso ya kaisu amma Alhaji Mansur yace ya barshi, baya son arik'a ganinsu tare. Haka suka wuce gidan yari wajen Malan Sani.
***
Malan Sani yasha kuka, ganin Ra'eez sai ya dawo masa da mutuwar sabuwa, shima Ra'eez d'in kuka yakeyi, duk dauriyar da Halima takeyi sai da tayi kuka, da kyar Alhaji Mansur ya basu hak'uri.
Kamo Ra'eez Malan Sani yayi yana fad'in wallahi sharri sukayi mani Ra'eez, ban kashe Alhaji ba, haka kuma ban.... Rufe masa baki Ra'eez yayi yana girgiza kai.
Zame hannunsa yayi yana fad'in Kawu kadena fad'ar haka, duk da k'arancin shekaruna nasan abinda zakayi da wanda baza kayi ba, tunda Abbah ya bani labarin abinda ya faru nasan cewar ba gaskiya bane sharri akayi maka, zanje nayi karatu insha Allahu wata rana sai ka fita daga nan, kuma sai gaskiya ta tabbata.
Gaba d'ayansu tsayawa sukayi suna kallon Ra'eez jin yanda yake sako magana mai cike da hankali da nutsuwa sai kace wani babba, alokacin gaba d'aya shekarunsa bazasu wuce 17 ba amma yana maganar masu shekaru da yawa.
Murmushi Alhaji Mansur yayi aranshi yana fad'in Allah mai iko, Allah mai shirya yanda yaso, gashi dai ya hukunta wannan abun sai kuma ya kawo Ra'eez, yasa masa natsuwa da zurfin tunani. Ya Allah ka tabbatar da ikon ka akan wannan bawan naka.
Sun dad'e a wajen Malan Sani suna fira, lokacin da zasu tafi Alhaji Mansur ya samu shugaban ma'aikatan suka gaisa, alheri yayi masa yana rok'onsa akan ya kula da Malan Sani. Murmushi yayi yana fad'in bakomai Alhaji, babu abinda zamuce da wannan k'asa tamu sai addu'a, amma wata shari'ar sai a lahira. Godiya Alhaji Mansur yayi masa suka tafi.
***
Bayan sun gama cin abinci sukayi sallah. Zama sukayi da Madu suna ta fira. Madu yake fad'a masa komai lafiya na gidan Alhaji, dan Maigadin yana kula da komai, motar Alhaji ma an rufeta da tampol, sai dai yana ganin gara a cire tayoyin a d'ageta zaifi.
Kallon Ra'eez Alhaji Mansur yayi yana fad'in Ra'eez ko dai asiyar da motar asaka maka kud'in a banki tunda nan gaba yayinta zai wuce? Kallonsa Ra'eez yayi yana fad'in Abbah idan aka barta har na girma akwai abinda zai sameta? Kai ya girgiza masa.
Ra'eez yace dan Allah Abbah abarta, ina so idan na girma na tuk'ata domin narik'a tunawa da Abbu kaji. Murmushi Alhaji Mansur yayi yana fad'in angama Ra'eez, insha Allahu baza'a sai da ta ba, kuma sai ka tuk'ata da izinin Allah, sai dai ina ganin zamu tafi da ita can kano kaga akwai gareji sai sata ciki kawai.
Murmushi Ra'eez yayi yana fad'in yauwa Abbah. Madu yace shikenan ma, nima hankalina zaifi kwanciya idan aka tafi da ita, domin za'a iya d'auketa, amma idan aka tafi da ita ya rage sai gida kawai shiko babu wanda zai d'aukeshi, shima dan kace abarshi amma da an sayar dashi hankalin kowa ya kwanta.
Alhaji Mansur yace akwai dalilin da yasa nace baza'a siyar dashi ba, wata rana Ra'eez zai zo yayi aiki agarin nan, kuma bana so ya zauna a wani waje, dan haka ka barshi babu abinda zai sameshi da izinin Allah, idan ma Maigadin ya gaji sai asamo wani. Madu yace begaji ba, shikenan ayi yanda kace.
Rumaisa ce ta shigo tana fad'in Yaya kazo muje kaga takarduna to. Murmushi yayi yana fad'in kilama duk ziro kikaci. Rumaisa tace wallahi duk na cinye, kok'ari fa gareni, kusan kullum sai an bani kyauta a aji. Ra'eez yace to muje na gani.
Dariya sukayi Alhaji yana fad'in ina ruwan Ra'eez, tunda yasan mutuwar mahaifinsa ban sake ganinsa cikin annashuwa ba sai da mukazo yaga Rumaisa, shiyasa na yanke shawarar barinsa yayi sati d'aya idan yaso sai ya taho ta jirgi, ni kuma sai na tafi da motar dan bana son na tafi dashi amota kasan hanyar Lagos. Madu yace haka ne, Allah ya tsare mana kai. Alhaji yace amin.
**** ****
Wshe gari tunda asuba Alhaji Mansur ya tafi bayan ya cika Halima da kud'i ita da Madu. Ra'eez da Rumaisa sai dad'i sukeji zai zauna yayi sati.
Sosai Halima take jin dad'in zaman Ra'eez domin koda yaushe yana koyama Rumaisa karatu, haka idan tayi ba dai-dai ba yana tsawatar mata, sai take ji ina ma abar matashi kodan Rumaisa.
Tunda sukaje asibiti basu sake komawa ba sai ana saura kwana biyu Ra'eez ya tafi, a wannan rana jikin Ummu bai tashi ba, haka Ra'eez ya wuni a wajenta dan Halima acan ta barosa, duk da ita kad'ai take shirmenta amma shi d'auka yake fira sukeyi, dan ita labarin Abbu kawai take bashi, hakan yasa shima yayita bata labarin Abbun.
Idan ka gansu sai ka d'auka mai hankali ce, gaba d'aya masu kula da ita aranar sunyi farin ciki domin kowa yasan Ra'eez yazo, duk wanda yaje sai ta fad'a masa ga Ra'eez shine zaije makka yasiyo mata wuk'ar da zata kashe wad'an da suk kashe mata Abbun Ra'eez, gaba d'aya aranar kowa sai da ya gaji da jin sunan Abbun Ra'eez.
Sai da yamma sosai Madu yazo tafiya da Ra'eez, anan fa Ummu tace bata san maganar ba, kuka da ihu tashiga yi za'a sace mata Ra'eez, haka ta rik'eshi tana kuka duk ta yakushe shi, sosai Ra'eez ya tsorata da yanayinta, duk yanda aka so akwace Ra'eez abun ya faskara domin wani irin k'arfi ne yazo mata, ta jima mutane da yawa ciwo hakan yasa dole suka kira Dr. Najib.
Koda yazo shima yasha fama, sai da yayi ta maza ya rik'eta da k'arfi akayi mata allura kafin tayi shiru, har bacci ya d'auketa hannunta yana rik'e dana Ra'eez, a hankali aka cireshi daga jikinta. Ra'eez yana waigenta har suka fita daga d'akin suka wuce gida sai kuka yakeyi.
A ranar haka ya wuni da kyar Rumaisa tasa yaci abinci. Bayan kwana biyu aka gama mashi komai na tafiya Madu ya d'aukeshi domin ya kaishi inda zai hau jirgi. Daga Rumaisa har Halima sai da sukayi kuka da zai tafi, shima kukan yakeyi da kyar suka rabu.
*** ***
Lokacin daya sauka Alhaji Mansur hada Labiba sukaje d'aukoshi, Labiba sai murna takeyi abokin firarta ya dawo. Haka suka nufi gida.
***
Lokacin da hutunsu ya k'are haka Alhaji Mansur ya had'a masu komai, d'aki yaja Ra'eez ya fad'a masa kud'in mahaifinsa sun fito, kuma ya saka masa abankin da Alhaji Maiwada ya bud'e masa ya saya masa hannun jari domin arik'a juya kud'in. Ra'eez yace Abbah bana so kace bazaka tab'a kud'ina ba, kaga a waje zanyi karatu ina so nayi karatu da kud'in Abbu domin ina so nayi amfani da guminsa nayi karatun da zan kwato masa hakkinsa.
Murmushi Alhaji Mansur yayi yace Ra'eez kenan, ko sisi baza'a tab'a maka ba, nine nayi niyar sai kayi karatu a waje kuma zakayi shi komin tsadarsa. Ra'eez yace dan Allah Abbah. Alhaji Mansur yace naji yanzu dai muje kada muyi dare, kuma bana so kasa damuwa aranka idan ba haka ba baza kaje karatun aikin lauya ba kaji. Ra'eez yace zan dage.
Haka suka fito suka yima Maman su sallama suka tafi cike da kewar gida, Labiba sai haushi takeji an canza ma Ra'eez aji yanzu saiya rigata gamawa, itama taso amayar da ita ajinsu amma Alhaji Mansur yace bazai maida ta ba dole ta hak'ura.
***
Haka rayuwa tacigaba da tafiya, wasu suna jin dad'i wasu suna cikin wahala, tuni Halima ta fawwalama Allah al'amuranta, ta rungumi k'addararta da hannu biyu, cikin ikon Allah take tafiyar da rayuwarta babu abinda ta nema ta rasa, Madu yana kokari akansu sosai, ga Sister Hassana da mijinta.
Cikinta sai girma yakeyi tana zuwa awo ba tare da wata matsala ba, damuwarta d'aya idan taje ganin Malan Sani, ganin yanda take damuwa yasa Malan Sani yace ta dena zuwa kawai tacigaba da kulawa da kanta.
Su Brr. Barau kuwa rayuwa tayi masu dad'i, domin arzik'in yanzu ya wuce na baya, sun had'a hannu da Alhaji Marusa suna shigo da kaya wad'an da suke so, domin Adebayo shine aka ba kujerar Alhaji Maiwada dama kuma alk'awari aka masa matuk'ar komai yayi dai-dai shi za'a ba yayin da aka bama Umar matsayinsa. Wannan dalilin ne yasa suke cin karen su babu babbaka dan yanzu mutane suna kuka da yanda ake amsar masu kudi.
****
Lokacin da cikin Halima ya isa haihuwa safiyar juma'a ta tashi da nakuda, alokacin Rumaisa tayi shirin zuwa makaranta sai fasawa tayi, da gudu taje ta kira Sister Hassana, haka suka d'auketa suka nufi asibiti.
Cikin ikon Allah ta haifi d'anta namiji. Bayan an gama komai suka koma gida. Bayan da ta gama gyara jikinta Ladi tayima yaro wanka, kunu ta kawo mata da d'umamen tuwo, kasa ci tayi sai kuka takeyi.
Zama Ladi tayi tana fad'in haba Halima, godiya ya kamata kiyima Allah daya sauke ki lafiya, nasan kina tunanin rashin Malan Sani, ki sani bazaiji dad'i ba idan yaji kina cikin damuwa, kinsan yanzu ba'a son kina saka damuwa aranki, ki daure kici abinci dan Allah.
Hannu tasa ta goge idonta tana fad'in shikenan Ladi nagode. Amsar kunun tayi ta fara sha tana kwalla.
Da wayar shugaban ma'aikatan gidan yari tayi magana da Malan Sani, sosai yaji dad'i haka yayi ta lallashinta kuma yace mata zai zo insha Allahu. Bayan sun gama waya shugaban ma'aikatan yace masa zai kaishi yaje yayi ma yaron hud'u ba. Sosai Malan Sani yaji dad'i yayi ta masa godiya.
Sai da dare suka je, alokacin Rumaisa ma tayi bacci. Haka yayi ma yaron hud'uba da *Abdallah*, yaso yasa sunan Alhaji Hamza amma sai ya tuna da maganar Alhaji Hamza da yake fad'a masa.. *idan Ummun Ra'eez ta haihu idan mace ce zai saka sunan mahaifiyarsa, idan kuma namiji ne zaisa sunan mahaifinsa Abdallah, saboda beyi amfani da sunansa a jikin takardunsa ba, sai yayi amfani da sunan da ake kiransa dashi a cikin 'yan uwa wato MAIWADA, hakan yasa yake son yasa sunanshi na gaskiya*. Wannan dalilin ne yasa Malan Sani ya cika ma Alhaji Maiwada burinsa. Ya dad'e yana kallonshi, wajen Rumaisa yaje yayi mata addu'a, sai da yaci abinci shida shugaban sannan suka tafi yana ta yima Madu godiya.
***
Dubu hamsin Alhaji Mansur ya aiko mata asayi rago ayi siyayyar kayan yaro. Godiya tayi masa. Haka akayi hidimar suna cike da rufin asiri tamkar Malan Sani yana nan.
****
Bayan da Ra'eez ya zana jarabawarsa suka baro su Labiba amakaranta, satinsa biyu a Kano ya taho Lagos yayi hutu kafin jarabawarsu ta fito. Sosai Rumaisa da Halima sukaji dad'in zuwanshi.
**** ****
Bayan da jarabawarsu ta fito haka aka kammala masa komai, cikin sa'a ya samu gurbin shiga makarantar koyon aikin lauya da take Landon, cike da farin ciki yaje yayi ma Ummunsa sallama, sai dariya takeyi kamar tasan abinda yake fad'a. Haka yayi ma kowa sallama ya tafi cike da fatan nasara.
*** ***
*Bayan shekaru da dama*,
Abubuwa da yawa sun faru, aciki hada kaddamar da Brr. Barau a matsayin sabon Alkali na babbar kotu bayan da tsohon Alkali ya aje aiki, sosai yayi farin ciki da wannan al'amari dan ya dad'e yana jiran wannan rana.
Mr. Kallah ma ya dawo Lagos da zama saboda ya aje aiki, gaba d'ayansu girma ya kama su, sai dai naira ta hana aga tsufansu, har zuwa wannan lokaci Alhaji Marusa yana shigo da haramtattun kaya, sai dai yanzu abun nashi na zamani yakeyi dan an samu cigaba.
Ummun Ra'eez tana kan amsar magani, zuwa yanzu jikinta da sauki sosai, sai dai bata da yawan magana, idan ka ganta tamkar mai hankali amma bata magana, a koda yaushe maganarta d'aya Abbun Ra'eez sai kuma d'anta.
Su Alhaji Mansur suna yawan kawo masu ziyara, haka wajen Malan Sani suna zuwa wajensa. Komai yana tafiya yanda ya kamata.
A yanzu haka Rumaisa an girma tana aji ukku a babbar makaranta. Sosai kyanta ya k'ara fitowa, ga natsuwa ga kok'ari, sosai take maida hankali a karatun ta. Abdallah ma yashiga fimare, sosai suke waya da Ra'eez.
Labiba kuwa tuni ta kammala makarantar ta, inda tayi karatu a FCE kano har ta kammala dan shekara ukku ne, yanzu haka ana shirin bikinta.
****
Bayan da Ra'eez ya kammala karatunsa haka ya dawo gida cike da nasara dan ya fita da first class, sosai Alhaji Mansur yaji dad'in haka.
Bayan dawowarsa yaje yaga Ummunsa kafin ya dawo kano, haka Alhaji Mansur ya nema masa (Bar school) da take abuja. Sai da akayi bikin Labiba kafin ya tafi.
Shekara d'aya yayi kafin ya kammala, bayan ya dawo yayi service shekara d'aya, alokacin Rumaisa zata jana jarabawar fita daga makaranta.
Yana kammala service d'insa ya samu aiki a babbar kotu da take kano. Kasancewar Ra'eez mai natsuwa da hazaka, cikin lokaci kad'an ya saye zuciyar mutane, dan duk abinda yasa agaba sai yaga bayansa, haka duk shari'ar da zaiyi sai yayi nasara, danshi baya amsar shari'ar da yasan babu gaskiya a cikinta, shiyasa mutane suke masa lak'abi da Mai gaskiya.
Sai da yayi shekara d'aya a kano kafin Alhaji Mansur yayi nasara aka canza ma Ra'eez wajen aiki zuwa babbar kotu da take lagos. Ranar da takardarsa ta fito sosai sukaji dad'i, haka Alhaji Mansur yayi ta masa nasiha yana bashi shawarar yanda zai tafiyar da komai musamman da yasan cewar Brr. Barau shine Alkali a kotun da Ra'eez zaiyi aiki, kuma yaja kunnansa akan ya b'oye komai nashi, dan baya so kowa yasan yana da alak'a da Alhaji Maiwada har sai komai ya kammala.
Cike da d'oki ya shirya ya tafi Lagos yana mai farin cikin zai koma kusa da abun sonshi Rumaisa, dan ya girma ne da soyayyarta, sannan zai koma kusa da Mahaifiyarsa.
Sai da sukayi kwana ukku suna gyaren tsohon gidansu dan Alhaji Mansur yace ya zauna acan, alokacin tuni an sake maigadi kusan ukku bayan wancan, haka aka gyara komai kamar alokacin aka zuba su.
A d'akin Abbunsa yace zai zauna. Haka ya shirya komai nashi. Yaso Maman Rumaisa su dawo gidan amma tace yayi zamansa tafi son ta zauna acan, duk yanda yayi haka ya hak'ura dan sai da Alhaji Mansur ya shiga maganar sannan.
*Wannan shine asalin labarin Alhaji Hamza Maiwada*
Ajiyar zuciya Kawu yayi yana goge hawayen da suka zubo masa. Ra'eez kuwa kuka yake sosai kamar k'aramin yaro. Hannunsa Kawu ya kamo yana fad'in kada ka barsu Ra'eez, sun cutar dani sama da shekaru da dama, nayi kuka har na gaji, nayi dauriya har sai da hak'urina ya kusa k'arewa, sun lalata mani rayuwa, sun b'ata mani suna, sunci mutuncin Mahaifiyarka, ta kwashe shekaru tana cikin hali na rashin lafiya.
Girgiza kai Ra'eez yayi yana fad'in kada ka damu Kawu, na girma da shirin d'aukar fansa, zan b'ullo masu ata yanda basuyi zato ba, insha Allahu sai asirin su ya tonu, sai Allah ya kawo mani hujja gamshashshiya, kamar yanda sukayi amfani da kwakkwarar hujja suka kada ka nima sai Allah ya bani wannan damar, kacigaba da tayani addu'a Kawu.
Murmushi Malan Sani yayi yana fad'in ina kan yi Ra'eez, kaine keda nasara a wannan karon, sai sunyi nadamar abinda suka aikata. Allah yayi maka albarka.
Ra'eez yace amin Kawu, zan zo na koma ka k'ara hak'uri Kawu. Malan Sani yace yanzu kam acikin farin ciki nake, fatana Allah ya barni da raina domin nasha kallo. Murmushi Ra'eez yayi yana fad'in amin. Sallama yayi masa ya tafi cike da damuwa aransa.
Ur's.
Nabeelert Lady🖋
[3/10, 8:39 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud'i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k'asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub'e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.*
2⃣2⃣
Yana kan hanyarsa ta komawa wajen aiki wayarsa tayi k'ara, yana dubawa yaga *Alkali ne*, saurin d'auka yayi, yana d'agawa ya fara tambayarsa ina yaje? Ra'eez yace na d'an fita na siyo magani ne ganinan dawowa. Kashe wayar akayi.
Tsaki Ra'eez yayi yana jin wani b'acin rai, sosai yake jin hushin Alkali Barau, tunda yasan irin muguntar da sukayi ma Abbunsa da Ummunsa ya k'ara tsanarsa. Gudun motar ya k'ara dan yayi sauri ya isa.
Inda ake aje motoci ya aje kafin ya fito, kai tsaye ofis d'in Alkali Barau yawuce, sai da ya fara kwankwasawa aka bashi zini kafin yashiga da sallama.
Kallonshi Alkali yayi yana fad'in baka jin dad'i ne? Kai Ra'eez ya d'aga yana fad'in kaina ne yake ciwo amma nasha magani yayi sauki.
Alkali yace ko dai ka tafi gida kila bacci ne. Ra'eez yace da sauki zan iya zama. Murmushi Alkali yayi yana fad'in shikenan, dama nace idan an tashi ko zaka bini gidana nasa ayi abinci da kai amatsayin ka na sabon ma'aikacina mai kwazo, ina so na gabatar da kai a wajen Iyalina.
Kau da kai Ra'eez yayi yana fad'in badamuwa nagode Allah ya kaimu atashi. Alkali yace amin, kuma naji dad'i, dan haka idan an tashi zan maka magana sai mutafi. Ra'eez yace to. Juyawa yayi ya fita.
Zaune yake a ofis suna fira shida Brr. Jabeer, sauran ma'aikatan ne suka iso suna ma Ra'eez sannu da zuwa. Da murmushi ya amsa yana basu hannu suna gaisawa.
Bayan sun gama Ra'eez ya kalli Jabeer yana fad'in gaskiya naji dad'in zuwa wannan kotun, domin mutanan cikinta suna da kirki musamman 'Yallab'ai.
Murmushi Jabeer yayi yana fad'in wai Alhaji Barau kake nufi? Ra'eez yace shi nake nufi. Murmushi Jabeer yayi yana fad'in kayi a hankali dai, domin kura ce rufe da fatar akuya.
Ra'eez yace bangane ba? Jabeer yace bakomai manta kawai. Murmushi Ra'eez yayi yana fad'in tunda nazo muka gaisa da kai sai nake jin kamar kaine kafi cancan ta nayi abota dashi a wajen nan duba da yanayin ka, sai gashi nazo kai kuma kana so ka b'oye mani wani abu, kyakkyawar alak'a ana kullata ne da kyakkyawar zuciya, amma kila ni d'in ne banyi maka da zama aboki ba.
Hannunsa Jabeer ya kamo yana fad'in wallahi ba haka bane, kasan ba'a son mutum yarik'a saurin fad'ar mugun abu ga wanda yazo waje amatsayinsa na sabon zuwa, ban sani ba kilama 'yallab'ai d'an uwanka ne haka kawai nayi sara akan gab'a.
Ra'eez yace amma na fad'a maka ba'anan nake ba, bani da kowa nan aiki ne ya kawo ni. Jinjina kai Jabeer yayi yana fad'in nima ai ban dad'e anan ba, kawai nasan labarinsa ne a wajen Kawuna, domin sunyi aiki tare dashi alokacin yana lauya, yanzu haka Kawuna yana Babbar Kotu da take garin Abuja, da tare suke anan, sai Kawu na yaje ya k'aro karatu, sukayi wani taro na k'asa da k'asa akan yanda za'a kawo cigaba akan shari'ar k'asarnan, Kawuna ya bada gudummuwa sosai, hakan yasa aka maidashi babbar camber da take abuja, kaji dalilin da yasa yabar wannan kotun domin yanzu yana saman Alhaji Barau.
Ra'eez yace lallai ashe dai gadon aikin shari'a kayi. Jabeer yace wallahi kuwa, domin acikin 'ya'yansa ma akwai lauya amma shi yana Jos acan yake aiki, a cikin dangin mu kusan mu biyar ne muke aiki a wannan fannin, da anan garin kake kila da ka san Kawuna, sunansa *Kamal S. Buzu*, alokacin da yake aiki tare da Alhaji Barau yasha wahala, domin bakinsu d'aya da manyan masu kud'i, gashi ya iya tsara magana, shiyasa duk yawancin shari'a shine yake nasara musamman ta masu kud'i, yasan yanda zai maida gaskiya ta koma k'arya, ta yanda babu wanda zai iya ganowa.
Ra'eez yace lallai kace yanzu sai ya raina kanshi tunda Kawun ka ne samansa. Jabeer yace ai yanzu yayi sauki sosai, kasan dama idan kaga mutum yana yanda yaso ba'a bashi shugabanci bane, ai tamkar ka d'auki ajiya ne ka bama b'arawo, kaga dole idan kazo amsa ya baka, shiyasa wasu suke ganin da zama da munafuki gara zama da b'arawo.
Dariya Ra'eez yayi yana fad'in wallahi Jabeer kana da abun dariya, gashi ka iya karin magana kamar wanda tsofaffi suka yaye, to ni dai ban fahimci abinda kake nufi ba.
Murmushi Jabeer yayi yana fad'in ina nufin yanzu shine shugaba, dole abinda lauyoyi suka fad'a shi zaibi, domin yanzu kotu ce take tafiyar dashi ba shine yake tafiyar da kotu ba, kasan duk abinda lauya ya fad'a dashi kotu take zama ta duba kafin ta yanke hukunci, shiyasa nace maka yanzu yayi sauki, dole yake yanke hukuncin gaskiya, shiyasa yanzu mutane suke sara masa, gani suke shid'in mai gaskiya ne, musamman koda yana lauya ba'a tab'a kamashi da laifin cin amanar aikinsa ba, shiyasa yanzu duk inda kaje zakaji ana fad'in Alkalin babbar kotu yafi kowa iya aiki, dan haka mutane suke son kawo k'ara a wannan kotu, damma ana soke wasu amaida su k'ananan kotu.
Jinjina kai Ra'eez yayi yana fad'in lallai irin wad'an nan mutanan wahalar sha'ani garesu, domin sun riga sun gama saye zuk'atan mutane, duk yanda wani yaso ya fad'i wani aibunsu mutane bazasu yarda ba har sai an gabatar masu da babbar hujja akansu.
Jabeer yace shiyasa ka zuba masu ido yafi, domin fad'a da aljani ba kyau, ko kace zakayi ma kaine a k'asa, domin zaka sa mutane su tsaneka ne kawai, shiyasa duk da nasan shid'in ba mai gaskiya bane dole na had'iye abuna nake binsa a yanda kowa yake kallonsa kafin ranar da Allah zai kamashi, wata kila a duniya wata kila kuma sai anje can.
Ra'eez yace irin wad'an nan mutanan asirinsu ya tonu aduniya yafi dad'i, domin mutanan da suka basu gaskiya zasu ga komai da idanuwansu, sannan masu aikata makamancin laifinsu zasu hankalta, idan suna da rabon shiriya sai kaga sun shiryu, amma abarsu sai anje lahira ai sun bar baya da k'ura.
Jabeer yace kai da kasan haka kenan, addu'ata d'aya Allah ya bayyana gaskiya, domin Kawuna yasha fad'a mani wata shari'a da sukayi wacce har yanzu bata wuce a zuciyar Kawu ba, saboda tare sukayi ta kuma shine yayi nasara, saboda irin hujjar daya gabatar ma kotu dole ne ta yanke hukunci, kuma Kawu yace ba hujjar gaskiya bace, sai dai shima bai da ikon k'aryatawa, domin an gabatar da ita ne amatsayin ta gaskiya, sune kad'ai suka san cewar ba ta gaskiya bace.
Ra'eez yace shari'ar waye haka? Jabeer yace an dad'e fa, shari'ar wani marigayi daya rik'e shugaban Kwastam a garin nan, kaga na manta sunansa wallahi, amma dai naji Kawu na yana fad'in har yanzu direbansa da aka k'ullama sharrin yana nan a gidan yari, kai wallahi wata shari'ar sai alahira kaji, amma mutanan da suke zaune agidan yari masu gaskiya suna da yawa.
Murmushi Ra'eez yayi yana fad'in Allah ya kyauta, mu kuma ya bamu ikon tabbatar da gaskiya, amma aikin mu yana da had'ari sosai, idan mutum yaso zai nemi lahira dashi, idan kuma yaso sai ya tara abun duniya dashi. Jabeer yace wannan haka yake, muje muyi sallah naji an fara kira.
***
Bayan da suka tashi Ra'eez yayi sallama da Jabeer, bakin motarsa ya tsaya yana jiran fitowar Alkali. Yana nan tsaye sai gashi ya fito shida Brr. Bajinta suna tafe suna magana sai dariya sukeyi.
Da wani irin kallo Ra'eez ya bishi yana jin wani zafi aranshi. K'arasowa sukayi Alkali yana fad'in Ra'eez yi hak'uri na tsayar da kai. Ra'eez yace ai bakomai.
Brr. Bajinta yace 'yallab'ai yau kana da babban bako kenan? Alkali yace wallahi kuwa, bara muje sai Allah ya kaimu. Brr. Bajinta yace Allah ya kaimu. Alkali yace Ra'eez bara na shiga gaba sai ka biyoni abaya ko.
***
Tunda suka shiga unguwar Surelere idanuwan Ra'eez suka canza kala, gaba d'aya jijiyoyin kansa suka tashi, shigowarsu unguwar sai ya tuna masa da rayuwar Iyayensa. Runtse ido yayi lokaci guda suka kawo ruwa.
Tunaninsa ya tsaya ne alokacin da yaga Alhaji Barau ya tsaya a k'ofar gidan da yake tunanin ya tab'a rayuwa acikinsa a shekarun baya, tabbas ko ba'a fad'a masa ba yasan wannan gidan Abbunsa ne daya gina da kud'insa wanda Abbu yayi masa wayau akan baya sonshi hakan yasa ya koma Apapa.
Tsayawa yayi har yaga motar Alhaji Barau ta shige ciki, tunani yayi ko dai ya tafi, dan bazai iya shiga gidan ba. Wata zuciyar ta bashi shawara daya daure yashiga, dole ya b'oye komai matuk'ar yana son gano gaskiya.
Cike da gamsuwa da shawarar da zuciyarsa ta bashi ya kutsa kan motar cikin gidan, yayin da yake kok'arin saita kanshi. Alhaji Barau ya fito yana jiran fitowar Ra'eez.
Sai da ya rufe motar kafin ya nufo wajen Alhaji Barau. Murmushi kwance a fuskarsa ya kalli Ra'eez yana fad'in bsimilla muje. Haka yabi bayansa yana kallon gefen gidan wanda Abbunsa yace b'angarensa ne zai gina idan yayi aure su zauna, tuni an gama gina wajen da alama b'angaren baki ne ko na yaransa maza. Girgiza kai Ra'eez yayi aranshi yana fad'in fenti kawai aka sake ma gidan amma komai nashi yana nan.
Tunaninsa ya dawo alokacin da Alhaji Barau yake gaisawa da mai aikin gidan. Risnawa Ra'eez yayi yana gaishe da mai aikin daya fito daga gidan.
Har ciki suka shiga bakinsa d'auke da sallama, sai dai babu kowa afalon sai TV da takeyi ita kad'ai. Kallonsa Alhaji Barau yayi yana fad'in zauna Ra'eez bara nayima mutanan gidan magana.
Zama yayi yana k'are ma gidan kallo. Da sauri yasa hannu ya goge kwallar data zubo masa, duk yanda yaso ya tsaidata kasawa yayi dole sai da suka zubo, hakan yasa yayi saurin goge su.
Motsin da yaji ne yasa shi kallon matattakalar benen, wata mata ce ya gani sun jero da Alhaji Barau sai murmushi take suna magana. Tana k'arasowa falon ta kalli Ra'eez tana fad'in lallai Alhaji yau muna da babban bako, ka kyauta daka kawo manishi, dan tunda ka bani labarin yanda ya tafiyar da shari'ar su Amina naji ya burgeni, sannu da zuwa Ra'eez.
Zamewa Ra'eez yayi yana gaisheta. Zama tayi tana amsawa. Alhaji Barau yace ai Ra'eez yana da kirki, jinsa nake tamkar d'ana. Hajiya Hauwa tace nima haka kawai naji ya kwanta mani, shiyasa nace maka naji dad'i daka kawo manashi.
Alhaji Barau yace ina *Raheenatu* take? Hajiya tace tana ciki, bara na kirata ta kawo masa abunsha. Ra'eez yace Hajiya kibarshi akoshe nake tafiya ma zanyi. Alhaji Barau yace ai ba haka mukayi da kai ba, dole kaci abinci ko kad'an ne.
Duk'ar da kai Ra'eez yayi bece komai ba. Wucewa Hajiya tayi tana fad'in ina ma za'ayi haka ai har abinci sai kaci. Bayan ta kira Raheena ta wuce kicin.
Suna zaune Raheena ta fito, tun kafin ta k'arasa shigowa falon k'amshin turarenta ya bud'e falon, a hankali Ra'eez ya d'ago kanshi domin yaga wanda yashigo da k'amshin.
Ido suka had'a da Raheena alokacin da ta fito sai kwarkwasa takeyi, wata doguwar rigace ajikinta mai kyan gaske, d'inkin yayi kyau domin tabi jikinta, kanta d'aure da d'ankwali fuskarta tasha kwalliya, sosai kayan suka matseta sai yanga takeyi tana taubar cingam ko mayafi babu.
Kicin ta wuce, ta jima kafin ta fito hannunta d'auke da faranti babba. Ra'eez kuwa tunda ya kalleta ya d'auke kai. Alhaji Barau ne ya tashi yana murmushi yace bara nashiga daga ciki ka saki jikinka kaci abinci nan ma gidan ku ne, yanzu zan fito, Raheena ki tayashi fira.
'Daga kai tayi tana murmushi. A tare da Hajiya Hauwa suka haura sama. Zama Raheena tayi tana fad'in barka da zuwa da fatan kazo lafiya? Ra'eez yace lafiya lau.
Lemu ta zuba masa ta mik'a masa tana fad'in bismillah. Amsa yayi yana fad'in nagode. Matsowa tayi kusa dashi tana fad'in naji labarin shari'ar daka gudanar gaskiya kayi kok'ari, sosai naji dad'i fa.
Ra'eez yace nagode. Shiru tayi ta tsura masa ido, tunda take arayuwarta bata tab'a ganin namiji mai kyansa ba, haka tunda Dadynta yace mata tayi kwalliya zai zo da bako take jin farin ciki, ashe wanda zai zo had'ad'd'an gaye ne, gaskiya dole ma Dady ya aura mata shi don ayanzu kad'ai jitake bazata iya rabuwa dashi ba, idan ko yaki amincewa da ita. zata iya shiga wani hali.
Gyaran murya Ra'eez yayi ganin irin kallon da take masa, da sauri ta d'auke idonta tana murmushi. Ra'eez yace zaki iya tafiya nagode. Raheena tace haba Yayana baka son na taya ka firar? Kauda kai yayi yana fad'in kaina yana mani ciwo ne.
Murmushi tayi tana fad'in bara na kawo maka magani. Kai ya girgiza yana fad'in bana shan maganin ciwon kai kawai surutu ne bana so. Tashi tayi tana fad'in nayi shiru bara na zauna acan, kallon ka ya fiye mani surutun ma.
Zama tayi a saman kujera tana binshi da kallo. Kauda kai yayi yana jan tsaki a zuciyarsa dan har itama haushinta yakeji gashi bata da kamun kai.
Fitowar Alhaji Barau ce tasa ya d'an saki fuska. Alhaji Barau yace Ra'eez har ka sha ruwan ko? Ra'eez yace nasha tafiya ma zanyi. Hajiya Hauwa da ta sauko take fad'in ga abinci fa zamuci.
Mik'ewa Ra'eez yayi yana fad'in nagode Hajiya ana jirana a gida ne. Da sauri Raheena tace kana da aure ne? Murmushi Alhaji Barau yayi yana fad'in beda aure kila dai abokinsa ne yake jiransa.
Ajiyar zuciya ta saki tana fad'in har naji dad'i Dady. Hajiya Hauwa tace Oh! ni Hauwa'u, wallahi Raheena baki da kunya. Alhaji Barau yace nagode Ra'eez, amma wata rana zaka zo muci abinci tare.
Ra'eez yace insha Allah. Sallama yayi masu sai godiya suke masa. Alhaji Barau ne ya kalli Raheena yana fad'in bazaki rakasa mota ba. Da sauri tayi gaba tana fad'in na d'auka kai zaka rakashi ai Dady. Hajiya Hauwa tace waye k'arami anan ai dole kece zaki rakashi.
Har bakin mota ta rakashi, bayan ya zauna zai rufe tayi saurin rik'e murfin, langwab'ar da kai tayi tana fad'in Yayana sai yaushe kuma? Kau da kai yayi yana fad'in nima ban sani ba.
Shagwab'e fuska tayi hada dira k'afa tace kai dan Allah Yayana! Murmushi yayi dan ta basi dariya. Kallonta yayi yana fad'in shikenan zan samu lokaci nazo. Murmushi ta saki tana fad'in nagode Allah ya kaimun kai gida lafiya.
Ra'eez yace amin nagode. Rufe masa k'ofar tayi. Sai da ya fita daga gidan kafin ta shige ciki. A mota Ra'eez sai jan tsaki yakeyi akan abinda Raheena takeyi, sai kace ba mace ba, wai nan har karatu tayi. Murmushi yayi yana shafa fuskarsa, a hankali ya furta Alhaji Barau zan bar maka tabo biyu kuwa.
***
Da tsalle tashiga gidan ta rungume Hajiya Hauwa tana dariya. Alhaji Barau yace ikon Allah lafiyar ki kuwa? Hajiya Hauwa tace da alama anyi nasara.
Alhaji Barau yace ai tunda na ganshi nayi ma Raheena sha'awarsa, domin nasan shine irin zab'inta. Hajiya Hauwa tace wallahi nima ya kwanta mani, yaro sai kace jinin larabawa, jikinsa na hutu ne, da gani kasan ya fito daga babban gida, dan ya tsumu a cikin daula.
Raheena tace wallahi Dady ina matuk'ar sonshi dan Allah ka aura mani shi zan iya shiga wani hali idan na rasashi. Saurin rufe mata baki Hajiya Hauwa tayi tana fad'in haba shalele, kima daina fad'ar haka, ke d'aya muke da ita mace, sannan kece ta gaban goshin mu, dole ma ki auresa. Sake rungumeta tayi tana fad'in nagode Momy nah.