Kamar yanda nace maku mu ukku ne abokai a kings college, tun farkon had'uwar mu muka kulla abota, duk wanda yazo makarantar atare ya sammu, domin kusan arana d'aya mukaje, hakan yasa wasu suke tunanin 'yan uwa ne mu.
Duk cikin mu Fawwaz ya fimu wayewa, domin Mahaifinshi yafi namu kud'i, sannan gatan da ake masa ba'ayi mana, sai Sufwan, shima d'an gata ne, a cikin mu ni kad'ai ne nake shakkar Mahaifiyata, duk da Abban mu yana mana gata kuma baya hana mu abinda muke so, amma gaskiya Mamy tana kula da mu sosai.
A hankali muka zama manya amakarantar, ajin mu d'aya da Naseer, ganin yana da kok'ari yasa muke kulashi, munso mu jawoshi cikin mu amma yaki amincewa domin yanayin mu da nashi ba d'aya bane, abokinsa d'aya Munnir. Ganin yaki bamu had'in kai yasa muka kyaleshi amma duk da haka muna gaisawa.
Zuwan mu aji shidda Fawwaz ya k'ara zama tantiri, wani abun ma muna tsawatar masa amma duk da haka sai abinda yaga dama, akwai wata yarinya *Minal* aji biyar take alokacin, Fawwaz yana matuk'ar sonta, sai dai ita bashi take so ba, wani d'an ajin mu take so *Farouk*, Fawwaz ya dad'e yana jama Farouk kunne akan ya rabu da Minal amma yayi banza dashi, saboda shima akwai zuciya.
Ganin abun ya fara koma masu fad'a yasa muka fara bama Fawwaz hakuri akan ya rabu da ita ya nemi wata, amma yace bazai hakura ba.
Wata rana da yamma zamu tafi gida yaga Minal da Farouk suna zaune suna shan lemu, takawa yayi har inda suke, yana zuwa ya kwashe Farouk da mari, cikin zafin nama Farouk ya rama, yana marinsa Minal ta k'ara masa hada juye masa lemu a jiki.
Saurin rik'e Fawwaz mukayi gudun kada abun yayi tsamari, duk yanda yaso mu sakeshi kiyawa mukayi, haka muka turashi mota naja muka tafi gida.
Washe gari koda mukazo makaranta muna zaune sai dai mukaga Fawwaz yana murmushi yana sakin kwafa, da muka tambayeshi lafiya yace bakomai.
Aranar mun tsaya lesson har yamma, bayan mun tashi mukaga Fawwaz ya mik'e ya fita da sauri, juyawar da mukayi sai mukaga ashe Farouk ne ya fita zuwa bayan aji da alama band'aki zaije, har mun zauna sai kuma muka tashi muka bi bayansu.
Kafin mu k'arasa muka hangosu suna fad'a, kasancewar wajen babu mutane yasa babu wanda yagansu, da sauri muka nufesu, sai dai kafin mu isa Fawwaz ya zaro wuk'a ya yankar masa wuya nan take ya zube.
Cike da firgici muka isa tare da rik'e Fawwaz, muna dubawa mukaga Farouk baya numfashi, cike da tashin hankali na fige wuk'ar naje na sata cikin wani k'aton rami da ake kona bola, dawowa nayi mukaja Fawwaz muka wuce, sai dai alokacin naga Naseer ya juya baya da gudu ya bar wajen yana kok'arin maida wayarsa aljihu, tabbas ko ba'a fad'a ba nasan ya d'auki abinda ya faru.
Sai alokacin shima hankalinsa ya tashi. Kuka yasa yana fad'in shima kashe shi za'ayi, lallashinsa muka farayi muna fad'in bazamu bari kowa yasan shine ya kashe shi ba, saboda muna son junan mu.
Kai tsaye gidansu muka nufa, wajen Dadynshi mukaje, bayan daya gama jin abinda ya faru na d'auka zai shiga tashin hankali ko kuma yayi ma Fawwaz fad'a amma sai naga cikin ko in kula ya kamo kafad'ar Fawwaz yana shafa kanshi yana fad'in Auta ka kwantar da hankalin ka, meye zaka tashi hankalin ka dan d'an wannan abun, ka d'auka kwananshi ne ya k'are, dan haka ba kaine ka kashe shi ba tsautsayi ne ya kai wuk'ar hannunka wuyanshi, amma babu mai kashe wani sai Allah, dan haka ka kwantar da hankalin ka kacigaba da hidimar ka tamkar yau aka haife ka, bana so ka nuna damuwa, ina fatan babu wanda ya ganku? Suka amsa mashi da babu. Saurin kallonshi nayi nace masa naga wani abokin mu Naseer ina tunanin ya d'auki abinda ya faru kuma ya gani da idonshi dan naganshi yana maida waya aljihu.
Jinjina kai yayi yana fad'in nine Alkalin babbar kotu, kome na fad'a ya zauna, ko case d'in yaron baza'a kaishi kotu ba bare aje afara bincike, zakuce na fad'a maku babu wanda zai tada maganar kawai gawar yaron za'a d'auka a rufe Iyayenshi suyi hakuri, dan haka kuje kawai, shima waccan yaron zansan yanda zanyi dashi.
Kud'i ya bamu masu yawa yana fad'in kuje kusayi wani abu. Anan take Fawwaz ya warware, ni kuwa jikina ne yayi sanyi sosai, ba dan ina son Fawwaz ba babu abinda zai hana na rabu dashi, amma amintakar mu daban take. Haka na wuce gida jiki a sanyaye, aranar da zazzab'i na kwana.
Washe gari haka mukaje makaranta abun mamaki babu wanda yaje da sunan bincike, sai nake jin labarin wai an tsinci gawar Farouk a bayan gari an yankashi, koda na tambaya a ina nayi tunanin za'ace a makaranta amma babu wanda yace haka, abun ya bani mamaki, nan Fawwaz yake rad'a mana ai Dadynshi ne yayi komai, muna tafiya yayi magana da shugaban makarantar akaje inda gawar take aka fita da ita ba tare da kowa ya sani ba, wannan dalilin ne yasa babu wanda yasan a cikin makarantar aka kashe shi, sai dai aka buga ajarida amma Iyayenshi basu tada maganar ba saboda basu san wanda zasu tuhuma ba.
A ranar mun dawo daga yawo mukazo gidansu Fawwaz kawai muka iske Dadyn Fawwaz yayi bak'i, anan aka kiramu, Brr. Barau shine wanda ya tambaye mu kwatancen gidan su Naseer tare da hotonshi, bayan mun bashi ya sake ja mana kunne akan kada mu fadama kowa, nan muka jaddada masu babu wanda zamu fad'amawa.
Kafin mu wuce naji yana waya da wasu yana fad'a masu kada su bar Naseer, su amso abinda ya d'auka kuma su kashe shi. A lokacin nashiga firgici jin za'a kashe Naseer, tun daga lokacin naji Fawwaz ya fice mun arai, nayi danasanin tarayyar mu, haka na wuce gida.
Washe gari sai labarin mutuwar Naseer naji, tun daga lokacin zuciyata ta tsinke, haka kuma tarayyata da Fawwaz tayi baya, Allah yaso zamu fara jarabawa babu sauran zama amakaranta, hakan yasa ban cika shiga cikinsu ba, bayan mun kammala jarabawa aka fitar da Fawwaz waje, tun daga nan muka rabu sai dai waya.
Shigata makaranta a hankali halayyata ta canza, a hankali na rika shiga damuwa saboda abubuwan da suka faru sun kasa barin zuciyata, shiyasa har yanzu ban mance abinda ya faru ba, duk da an d'auki shekaru na kasa manta koda kalma d'aya ce, wani lokacin inajin kamar ina da laifi, domin nayi tarayya wajen b'oye mai laifi, kuma nine silar tona Naseer, domin nine na fad'a ya gammu.
Abinda ya faru da Yaya Sameer da kammala komai har zuwanshi wajena ya fad'a mun Fawwaz ya dawo da abinda yakeso nayi yasa hankalina ya sake tashi, kuma nayi alk'awarin a wannan karon zan tsaya na bada kowace irin sheda ake buk'ata domin a tabbatar da gaskiya, duk abinda ya faru yana nan a zuciyata be goge ba, dan haka ashirye nake domin bada sheda.
Jinjina kai Ra'eez yayi yana fad'in tabbas wannan 'Yallab'ai d'in da muke nema ina kyautata zaton tsohon Alkali ne wato mahaifin Fawwaz, domin alokacin da sukaje gidansu Fawwaz su ukku sun had'u, kunga kenan shine na hud'unsu.
Rafeek yace babu tantama shine na cikon hud'unsu, kuma dole zamu tabbatar da abinda zai tona asirinsu, ayanzu mu kad'ai ne mukasan gaskiya, kuma mu dukan mu babu wanda yake da tsinken da zai iya rik'ewa a matsayin hujja, kotu bata amfani da hujjar baki, ko shari'ar muka dawo da ita baya sune zasu sake nasara domin sune masu hujja mai kwari, dan haka ba yanzu zamu tado da maganar ba.
Jabeer yace wannan haka yake, gobe zan samu Kawu da maganar abinda yace zakuji, Yaya dole mu fara bincike a b'oye, sai mun had'a komai kafin mu fara aiki.
Ra'eez yace ina ganin shari'ar su Naseer zamu fara, itace zata tono waccan shari'ar. Rafeek yace haka ne, domin muna da d'an wani abu akan shari'ar Naseer, duk da itama ba mai kwari bace, domin d'ayan abokinsu ya mutu, ko yana nan su biyu bazasu bada sheda ba, ko sun bada baza tayi amfani ba saboda abaki take, kunga anan ma sai mun zurfafa bincike.
Jabeer yace Adnan kana da hoton ku alokacin kuna makaranta? Adnan yace ina da su sosai ma. Jabeer yace Fawwaz bazai iya k'aryata abotar ku ba, kana da labarin shugaban makarantar ku? Adnan yace e amma yanzu baya makarantar ya aje aiki, sai dai nasan gidanshi dan d'anshi abokina ne.
Rafeek yace turk'ashi, yanzu ya za'ayi musamu ganawa dashi bana so abokin ka yayi tunanin kayi masa rashin mutunci idan yaji kana dasa hannu wajen saka Babanshi cikin masu laifi.
Adnan yace a wannan gab'ar babu batun abotaka, tunda har na amince zan tsaya a yanke ma babban aminina na da hukunci babu wanda zan iya rufa ma asiri, domin shi Nabeel jami'a mukayi dashi, shikuwa Fawwaz akwai shakuwa atsakanin mu, dan haka ku bani lokaci insha Allahu Nabeel zai bamu goyon baya, duk da Babanshi ya aikata laifi amma dole a hukuntashi.
Rafeek yace mungode sosai, kuma zamu tafiyar da komai yanda ya kamata, idan komai ya kammala zasu san gata mukayi masu domin sun huta amsar hukunci a lahira.
Tashi Adnan yayi yana fad'in zan wuce gida dare yayi. Rafeek yace muje na aje ka zamuyi waya. Hannu ya bama su Jabeer suna ta masa godiya. Rafeek yace zuwa gobe zan fara binciken mutanan da sukayi tarayya a waccan shari'ar.
Jabeer yace nima a goben zan samu Kawu da maganar. Ra'eez yace Allah ya kaimu, nima gobe zan koma aiki. Tashi sukayi suka rakasu kafin suka dawo.
Bayan sun kwanta wayar Ra'eez tayi k'ara, yana dubawa yaga Raheena ce, duba agogo yayi yaga har sha biyu tayi, tsaki yaja yana fad'in bana son rashin hankali wallahi.
Murmushi Jabeer yayi yana fad'in bacci ta kasayi shiyasa ta kira ka. Kashe wayar yayi gaba d'aya yana fad'in sai tayi da wani kuma.
Jabeer yace Ra'eez na Raheena, wallahi kuna bani dariya, tun farko na fad'a maka ka rabu da ita gashinan tana baka ciwon kai. Tsaki Ra'eez yayi yana fad'in daga ita har Iyayen ta basu da kai, sufa a haukansu jiran yan gidan mu suke suje neman aure, har kayan d'aki fa sun siyo.
Gyara kwanciya Jabeer yayi yana fad'in ka bari da Allah? Ra'eez yace wallahi kuwa, ba na fad'a maka zasuje Dubai ba a week end d'in da naje Kano ba.
Jabeer yace haka ne. Ra'eez yace wallahi jiya take fad'a mun wai kayan suna hanya, nifa na fara tausaya mata ma. Jabeer yace da nace maka ina tausayinta meka fad'a mun? Nifa aganina bekamata kayi ramuwar gayya akanta ba, duk da an zalunceka amma bata da laifi, idan mukayi haka kamar Allah zai kama mu ko kuma ya hana mu samun wani abun da muke so.
Ajiyar zuciya Ra'eez ya saki yana fad'in b'acin rai ne yaso ya jefani cikin damuwa, tabbas Raheena bata cancanci nayi mata haka ba, amma insha Allahu a yanzu zan fad'a mata tayi hakuri kawai.
Jabeer yace baza'ayi haka ba, Raheena tana maka so mai yawa, idan ka fito fili ka fad'a mata abinda yake ranka zata iya fad'awa wani hali, ina ganin abi komai a hankali.
Ra'eez yace shikenan nasan abinda zan rubuta mata. Wayarsa ya jawo ya kunna ya fara rubutu. Jabeer da yake gefenshi yace kafin ka tura ka bani na gani. Ra'eez yace sa ido. Jabeer yace gaskiya dai. Murmushi Ra'eez yayi yana fad'in bara na gama to.
Mik'a masa wayar yayi yana fad'in bance kamun gyara ba. Amsa yayi yana fad'in sai dai idan baka kwafsaba, dan na lura da kai haushin Mahaifinta yasa ka tsani kowa.
Jinjina kai yayi yana fad'in ba laifi kayi amfani da kalamai masu ma'ana, sai muce Allah yasa mata dangana. Ra'eez yace amin.
Shuru sukayi gaba d'ayansu bayan sun tura sakon. Jabeer! Ra'eez ya kirashi a hankali, be amsa ba sai juyowa da yayi yana fuskantarshi.
Mai zai hana ka nemi auren Ra... Kada ma ka k'arasa, Jabeer ya fad'a. Murmushi Ra'eez yayi yana fad'in wallahi tausayinta nakeji.
To kayi ta biyu da ita mana. Jabeer yace yana harararshi. Dariya Ra'eez yayi yana fad'in haba abokina, yanzu da bakin ka kake fad'in nayima Pretty kishiya.
Jabeer yace ai naji kana wani kilibibin kana tausayin ta, idan har bazaka iya aurenta ba damme zaka lak'aba mani ita? Ra'eez yace saboda naga babu soyayyar kowa a zuciyar ka.
Tsaki Jabeer yayi yana fad'in to kama dena wannan maganar, babu abinda zanyi da ita, na fad'a maka bazan iya soyayya da wacce ta mutu akan wani ba, wanin ma kai, haka kawai idan na aureta data ganka sai tsohon tsumin soyayyarka ya tasar mata.
Dariya Ra'eez yasa yana fad'in kawai kace kishi kake malan, bakomai Allah zai bata wani. Jabeer yace hakan ma yafi, amma kada ka janye mata lokaci guda kamar yanda ka rubuta kaga baka fito fili kace mata baka sonta ba. Ra'eez yace kada ka damu.
*** ***
*Raheena ina so ki tsaida hankalin ki wajen karanta abinda na rubuta maki, bana so kiyi mani wata fassara, dalilin rubuta maki wannan sakon saboda naga kunyi nisa akan abinda zuciyar ku take tunani shiyasa naga ya dace nayi maki magana dan kada ku zurfafa, a tunanin ku ayi bikin ki nan da wani lokaci, domin naji kina fad'ar kunje siyayyar kayan d'aki, idan baki manta ba na fad'a maki ki jirani zanyi tunani akan soyayyar ki, kuma har yanzu ban gama yanke hukunci akai ba, domin ko Iyayena banyi maganar dasu ba, kuma ni gaskiya ba yanzu zanyi aure ba dan akwai abubuwa masu muhimmanci akaina, kuma bazan tab'a yin aure ba har sai na kammala su, shiyasa nace zan fad'a maki gaskiya dan naga kamar kina son yin aure da wuri, ina fatan zaki fahimce ni dan bana son a takura mani dan ban shirya aure yanzu ba, dan haka kudena maganar yin aure ayanzu. Nagode.*
Ta maimaita sakon yafi a kirga, zufa kawai take zubo mata, wasu zafafan hawaye ne suka zubo mata, hannu tasa ta goge tana fad'in me D yake nufi da wannan sakon? Gashi dai bece mani baya sona ba, *Dama can kuma be tab'a fad'a maki kalmar so ba.* wata zuciyar ta kwab'eta.
Gyara zama tayi tana zurfafa cikin tunani, tabbas sunyi gaggawa wajen aminta da maganar aurenta dashi, amma tunda yace akwai abinda yake gabansa zata mashi uzuri, kuma bazata fad'ama kowa wannan maganar ba, sai dai zata nuna masu abar maganar aurenta zuwa wani lokaci, idan ya kammala komai tasan zai dawo gareta.
Murmushi ta saki tana fad'in zan jiraka, bazan tab'a bari naji kunya a wajen k'awaye na ba, bara naje muyi magana da Momy.
Ur's.
Nabeelert Lady🖋
[3/10, 8:40 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud'i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k'asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub'e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.*
3⃣6️⃣
Ban gane abar maganar auren ki sai zuwa gaba ba? Matsowa tayi tana fad'in Momy Ra'eez yace beyi magana da Iyayenshi ba saboda akwai wani aiki mai muhimmanci da yakeso ya kammala kuma baya so maganar aurenshi tasa yaki maida hankali akan aikin, kinga babban biki ne za'ayi dole yana buk'atar natsuwa, nima bana so ace za'ayi bikin mu kuma yana wani aikin sai kiga bikin beyi dad'i ba, kuma tunda yace aiki ne mai muhimmanci nasan ba k'aramun abu bane, kinsan kuma yanayin aikinsu dole yana buk'atar natsuwa da zurfafa tunani, shiyasa yace a bari harya kammala aikinsa kafin yazo ayi magana.
Murmushi Momy ta saki tana fad'in yanzu naji batu, ai na d'auka ko wata matsala kuka samu, haba dan wannan ai bakomai, kaya ne an riga ansiyo su, idan ma baki son su zuwa lokacin auren za'a iya siyar dasu aje asiyo maki wasu dan bancika son amfani da tsofaffin yayi ba.
Murmushi Raheena tayi tana fad'in yanzu Momy zaku iya sake mani wasu kayan? Momy tace to me zamuyi da kud'in? Ke d'aya muke da ita shiyasa muke so muyi maki abinda ko d'iyar shugaban k'asa iya abinda za'a mata kenan, dan haka idan har aikin ya jashi dogon lokaci dole asiyar da kayan idan lokacin bikin yayi asiyo maki wasu.
Raheena tace nagode Momy, sai kiyi ma Dady bayani. Babu wani bayani da za'a mun domin naji komai. Alhaji Barau ya fad'a yana sakkowa daga bene. Murmushi Momy tayi tana fad'in ashe har ka gama shiryawa? Zama yayi yana fad'in tunda kin gudu wajen d'iyar ki dole na shirya ni d'aya.
Tashi Raheena tayi tana fad'in Dady ayi hak'uri bazata sake ba. Dariya sukasa gaba d'aya. Alhaji Barau yace bakomai naji duk abinda kuka fad'a, tunda dai yana sonta ai babu damuwa, ni dama ban matsa sai Raheena tayi aure da wuri ba dan nima bangaji da ita ba, dan haka zamu jirashi ya kammala abinda yakeyi.
Momy tace kila ma kaine ka bashi aiki mai wahala ko? Alhaji Barau yace babu ruwana, kila dai a wani wajen zaiyi aiki amma ni bana bashi aiki mai wahala. Momy tace to Allah ya nuna mana lokacin. Yace amin.
**** ***
Bayan sun tashi daga aiki Jabeer yace zaije wajen Kawu akan maganar su. Ra'eez yace bakomai zan wuce wajen Kawu daga can na biya wajen Ummu. Jabeer yace ka gaishe su mu had'e gidan Mama. Ra'eez yace ka gaishe dasu Mamy.
****
Hannu Kawun Jabeer yasa a hankali ya zare glass d'in idonshi, ido ya kurama Jabeer jin abinda yazo dashi. Kauda kai yayi yana jinjina kai.
Shiru Jabeer yayi yana addu'ar Allah yasa Kawun ya amince ya taimaka masu. Gyaran murya Kawu yayi yana fad'in Allah mai iko, lallai duniya da girma take, wai akace d'an hakkin daka raina wata rana zai iya tsone maka ido.
Kallon Jabeer yayi yana fad'in wai kana nufin tare kuke aiki da Yaron marigayi Alhaji Maiwada? Jabeer yace kwarai kuwa Kawu, yanzu haka shine babban gwarzo a kotun mu.
Kawu yace naga alama daga labarin shari'ar da kace yayi, wannan shine ikon Allah, ashe dama irin wannan ranar zata zo? Ashe jinin Alhaji Maiwada ba zai zuba abanza ba? Ashe Malan Sani zai samu adalci? Ashe wad'an can azzaluman zasu fuskanci hukunci dai-dai dasu? Lallai Jabeer ka zo da magana mai matuk'ar amfani, ayanzu ne zanyi ramuwar abinda na gazayi ashekarun baya, ayanzu ne zan nuna masu Brr. Barau bakomai ne kud'i yake badawa ba, tabbas anzo wajen, dan haka kaje ka fad'ama Ra'eez, da Rafeek ina son ganin su ko zuwa dare ne.
Cike da farin ciki Jabeer yace angama Kawu. Kawu yace bana son wannan maganar ta fita, shiyasa daka fara fad'a mani nace maka muzo mota, inaso komai ya tafi yanda ya kamata, insha Allahu zan shirya yanda komai zai kasance, sai Alhaji Barau yaji kunyar da bai tab'a jinta ba, sai ya gwammace k'asa ta tsage ya shige ya huta, kaje ka fad'a masu.
Godiya Jabeer yayi ma Kawu ya tashi ya tafi cike da farin ciki, tun alokacin yayi masu waya ya fad'a masu sakon Kawu, sosai sukayi murna.
****
Rafeek ne ya fito daga ofishin 'yan sanda tare da wani d'an sanda, har bakin motarshi suka k'arasa. Hannu Rafeek ya bashi yana fad'in nagode *Usman* Allah ya bar zumunci.
Murmushi wanda aka kira da Usman yayi yana fad'in haba babu komai, ai wannan taimakon juna ne, duk da baka fad'a mani dalilin da yasa kake neman Alhaji Bello Kabeer ba.
Rafeek yace bakomai fa, akwai wani yaro da yake son shiga aikin d'an sanda shine nace masa zan taimaka masa, to da nayi bincike sai na gano a ofis d'in ku yayi aiki harya kai babban matsayin Kwamishina na 'yan sanda ayanzu, shine nace zan fara zuwa wajen ka na fara jin labarinshi kafin nasan ta yanda zanje mashi.
Usman yace indai zaka bud'e masa bakin aljihu baka da matsala dan 'Yallab'ai akwai son naira. Rafeek yace babu damuwa tunda dai kayi mani kwatancen gidanshi insha Allahu zan sameshi Allah yasa mudace.
Usman yace amin. Sallama sukayi yashiga mota. Tafiya yake yana tunanin ta yanda zai fara b'ulloma Alhaji Bello Kabir, amma tunda ya ganoshi zai shirya masu fira ta haka zai san yanda yayi ya tab'o mashi maganar wannan shari'ar.
Agogo ya duba sai yaga lokaci ya tafi, yaso ya biya asibitin da Dr. Aliyu Sani yayi aiki yaji ko yana wajen har yanzu ko kuma ya k'ara matsayi, ajiyar zuciya ya saki, dole ya bari sai gobe saboda neman da Kawu yake masu.
***
Daga wajen Ummunsa gidan Mama ya wuce, acan ya iske Jabeer suna ta fira da Mama. Bayan sun gaisa suka wuce masallaci, bayan sun idar da sallah suka zauna Rumaisa ta kawo masu abinci.
Kallon Jabeer yayi yana fad'in nifa jinake akoshe nake duk na k'osa muje wajen Kawu, ina son naji ana bani labarin Abbuna. Murmushi Jabeer yayi cike da tausayin Ra'eez.
Wayar Rafeek ce tashigo, yana d'auka ya fad'a mashi suna gidan Mama. Rafeek yace dama yanzu na fito bara na k'araso mugaisa da Mama. Ra'eez yace shikenan sai kazo.
Jabeer yace gaskiya Yaya yana da kirki. Ra'eez yace shiyasa nace maka tunda muka had'u naji ya kwanta mani, kasan bana saurin yarda da mutane amma akanshi naji na yarda dashi.
Jabeer yace wai jiya inaso na tambayeka ka d'auki bayanin Adnan kuwa? Dafe kai Ra'eez yayi yana fad'in wallahi na manta, kuma kasan nace maka daga yanzu duk wata sheda da zamu samu sai mun rik'a d'aukarta gudun yaudarar mutane.
Jabeer yace Allah yasa kada ya yaudare mu, duk da naga alamun gaskiya atare dashi amma kasan halin yau, zuciya bata da k'ashi babu ta yanda bazata iya canzawa ba, sai dai muyi fatan Allah yasa ya cika alk'awarinsa.
Ra'eez yace amin, amma da ya gama damu idan ya kasa zuwa ya bada shedar abinda ya sani. Jabeer yace kaga sai mu kiyaye. Wayar Ra'eez ce tayi k'ara, saurin tashi yayi ya fita yana fad'in Yaya ne.
Sosai Mama taji dad'in bayanin da Rafeek yayi masu akan gano Alhaji Bello Kabir wanda yake inspector a lokacin da akayi shari'ar su Malan Sani, godiya tashiga yimasa tana saka masa albarka.
Rafeek yace haba Mama babu komai, insha Allahu wannan karon mune da nasara. Mama tace Allah yasa. Abinci tasa akawo masa yace daga gida yake, kallonsu Jabeer yayi yace muje kada Kawu yajira mu. Sallama sukayi ma Mama suka fita.
**** ***
Ido Kawu ya tsurama Ra'eez, tabbas ga kamanninsa da Mahaifinsa a fuskarshi, amma sai wanda ya san Alhaji Maiwada zai iya sheda hakan, kuma sai ka k'arema Ra'eez kallo zaka gano kamannin su, lallai Alhaji Barau be yima Ra'eez kallon tsab ba da tuni ya gano kamannin Mahaifinsa.
Gyara zama yayi yana fad'in sannu kaji Ra'eez, tabbas kai d'in Kainuwa ne dashen Allah, domin Allah yasan dalilin da yasa ya bar su Alhaji Barau har yanzu araye, haka kuma ya barka kaida Malan Sani da Ummunka araye, domin ya tsara yanda ikonsa zai kasance, hakika Mahaifinka yayi mutuwar cutarwa, domin wad'an da suka kashe shi basu da imani ko kad'an, amma ayanzu zasu gane kuren su.
Kayi hak'uri na kasa tsayama Mahaifinka, duk da alokacin nasan su Alhaji Barau suna da sa hannu a kisanshi amma bani da ikon magana saboda bani da hujjar da zan nuna, ita kuma kotu hujja take so, amma ayanzu dana ganka sai naji gashi can mun cinye shari'ar, da izinin Allah zamu samo hujjar da zata ruguzasu gaba d'aya.
Hannu Ra'eez yasa ya goge hawayen da suka zubo mashi, duk'ar da kai yayi yana fad'in babu komai Kawu, Allah ya rubuta dole sai hakan ta kasance, ko ka bada hujjar baza tayi tasiri ba alokacin tunda Allah ya tsara haka, amma ayanzu zamu samota Kawu.
Jinjina kai yayi yana fad'in dole amaido da shari'ar baya, domin ita shari'a bata tsufa, koda ta kai shekaru hamsin za'a iya maidota, kuma awannan kotu za'a gabatar da ita, dan haka zan shirya yanda komai zai kasance, koda Alkali Barau yace bazai amshi shari'ar ba za'ayi masa magana kuma dole ya amsheta.
Rafeek yace mungode Kawu, kuma zamu k'arasa nemo sauran mutanan da suka tsaya a waccan shari'ar matuk'ar suna raye. Kawu yace gashi kusa mani lambar ku, daga yau inaso ku kasance ashirye, domin zaku fara aiki mai had'ari, dan mutanan da zaku kara dasu azzalumai ne, zasu iya komai saboda rufin asirin su.
Bayan sun saka mashi lambar sukayi masa sallama suna ta godiya suka tafi. A can suka rabu da Rafeek yayi gida suma suka wuce gida saboda dare yayi.
***
Ina jinka Lucky. Gyara tsayuwa Lucky yayi hannunshi nad'e a kirji yana fad'in 'Yallab'ai gobe ne za'a kawo kayan Alhaji Marusan, kuma nasa yarana su ankare baza'a samu matsala ba.
Ruwa Alhaji Barau yasha yana fad'in Lucky na sanka da son kud'i, bana so ka fad'ama Alhaji Marusa komai dan nasan zakayi tunanin zai iya k'ara maka kud'i idan ka fad'a masa, mu ba kud'in bane suka dame mu, yaudara da cin amanar da yayi mana muke so mu nuna masa iyakarsa, kasan dai daga ni har Mr. Kallah bamu da zalamar kud'i, wannan aikin idan har ka yishi yanda ya kamata kana da kaso mai tsoka, kaga dai yanzu ka manyanta, aiki da yawa sai dai kasa yaranka suyi, dan haka ina so wannan ya zama sirri, kamar yanda nace ku kwace kayan kuma ku kashe masu d'aukar kayan zakaga abinda zan saka maka dashi.
Murmushi Lucky yayi yana fad'in Alhaji baka da matsala, wannan harka mun dad'e muna yinta daku, kuma ka dena tunanin zan koma wajen Alhaji Marusa domin shi d'in ba mai alk'awari bane, kanshi kawai ya sani, kafin ku shi muka sani ni da abokina Peter, amma saboda cin amana da son kud'i irin na Alhaji Marusa daga abokina yayi masa kuskure d'aya yasa aka kashe shi, har yanzu ina da haushin wannan abun, dan haka zanyi maku aiki koda bazaku biya ni ba, domin nasan Alhaji Marusa ya zuba makudan kud'i a wannan harkar, matuk'ar ya rasa wad'an nan kayan zai shiga tashin hankali, sannan hukuncina na farko da zanyi mashi nasa babban yarona yaje cikin dare ya kona mani babban store d'inshi.
Dariya Alhaji Barau yasa yana fad'in Mr. Kallah kaji mutumin ka ko? Mr. Kallah yace lallai Lucky ka d'ebo da zafi, ayi masa hakuri yaji da wannan asarar ma. Alhaji Barau yace aifa kai har yanzu bazaka canza hali ba, kada kamanta amanar mu yaci, tare muke kashewa mu rufe amma yau saboda harkar k'aruwa tazo shine yaci amanar mu, dan haka ka bari shima anuna masa iyakarsa, ganin yana da kud'i yasa yake abinda yaga dama, idan ya fara shin-shino karayar arziki kaga dole ya dawo k'asan mu.
Mr. Kallah yace shikenan yanda kace babban Alkali. Dariya sukasa Alhaji Barau yace zaka iya tafiya Lucky sai munji daga gareka. Lucky yace nagode Alhaji.
Yana fita Mr. Kallah yace yanzu kai ka yarda dashi? Alhaji Barau yace shiyasa ai na zab'eshi saboda nasan yana da haushin Alhaji Marusa akan kisan abokinsa, kaga kuwa bazai tab'a komawa bayanshi ba.
Mr. Kallah yace zaiji idan cin amana tana da dad'i, kuma zamu nuna mashi munshiga tashin hankali. Alhaji Barau yace da masu ilimi fa yake tare wad'an da suka goga da mutane, duka nawa iliminshi yake, meya sani a harkar duniya, kabarshi zamu nuna mashi muma munyi asara. Mr. Kallah yace Alhaji Barau a kiyaye ka. Dariya sukasa.
**** ***
Wai Adnan kayi shiru bayan kuma akwai magana abakin ka. Murmushi Adnan yayi yana fad'in bakomai kawai wani abu na gani d'azu daya tada mani wani tsohon ciwo da yake zuciyata shekaru masu yawa da suka wuce.
Nabeel yace lallai agaisheka, taya zan iya aje abu araina har na wasu shekaru masu yawa, kaganni nan ko b'ata mani rai akayi baya wuce kwana biyu yawuce, amma kuma bansan wane irin ciwo bane aranka, kasan wani ciwon sai mutum ya mutu dashi be manta ba.
Adnan yace d'azu muka had'u da Yayan wani abokin mu da aka kashe lokacin muna aji shidda a secondary, rabona dashi tunda mukaje masu gaisuwa, saboda yasan nine babban abokinsa yasa da muka had'u d'azu muka zauna muna ta fira hada firar abokina mukayi bakaji yanda jikina ya mutu ba, gaba d'aya sai mutuwar ta dawo mani sabuwa musamman da naga yana kuka, kuma yake fad'a mani har yanzu Mahaifiyarsu bata warke ba akan ciwon daya sameta alokacin da aka kawo mata gawar d'anta, wannan abun shine ya tada mani hankali sosai.
Nabeel yace Allah sarki, amma basu shigar da k'ara ba ne? Adnan yace basu shigar ba. Nabeel yace da sun sani sun shigar da k'ara, kasan wani lokacin idan aka kashe maka naka matuk'ar an yanke ma wanda yayi kisan hukunci kana jin sauki a zuciyarka domin ka rage wani abun.
Adnan yace taya zasu shigar da k'ara bayan an juyar da abun, kasan fa ita shari'a sai da shedu take amfani, domin kisan a makarantar mu akayi ta amma sai aka gano gawar abokina a wajen gari, alokacin ma Abban ka ne shugaban makarantar.
Nabeel yace a kings college ko? Adnan yace nan fa. Nabeel yace tabbas acan Abbah yayi aiki ashe kayi karatu ak'asanshi? Adnan yace sosai kuwa, ai Abbanka beda wasa, nayi mamaki alokacin da aka kashe Farouk da aka fita da gawarsa kuma be tsananta bincike ba. Nabeel yace dan Allah bani labarin abinda ya faru.
Adnan yace abinda na sani ance a makaranta aka kashe shi, domin akwai wanda yaga lokacin da akayi kisan kuma har d'auka yayi, sai dai kuma daga baya aka samu gawarsa a wajen gari sannan yaron daya d'auki shedar shima aka kashe shi, kuma shedar ta b'ace, mamakin da nayi duk zafin Abbanka da iya aikinsa amma beyi komai ba, daga baya kuma nayi tunanin kila besan a makaranta aka kashe shi ba.
Girgiza kai Nabeel yayi yana fad'in duk da haka Adnan ya kamata ace anyi bincike koda da gaske ba'a makarantar aka kashe shi ba amatsayin Abbah na shugaban makaranta ya kamata ace yayi ruwa da tsaki wajen nemawa Farouk hakkinsa.
Murmushi Adnan yayi yana fad'in Nabeel kenan, kaida kayi wannan tunanin zaka fad'i haka, ka rabu da duniya idan akace akwai azzaluman shuwagabanni, talaka beda ikon aiwatar da komai matuk'ar ta had'oshi da mai kud'i, ko d'azu Yayan Farouk ya fad'a mani da zai samu sheda koya take saiya maido da shari'ar Farouk kotu, sai anyi bincike koda wanda ya kashe shi baya duniya.
Jinjina kai Nabeel yayi yana fad'in amma Abbah bazai iya taimakawa ba? Adnan yace a wajen me kenan? Gyara zama Nabeel yayi yana fad'in dole yasan duk wasu masu gadi da sukayi aiki dashi a waccan shekarar, ina zargin kamar an had'a baki da masu gadi wajen fitar da gawar Farouk, kaga idan aka tabbatar da haka dole za'a gano wanda yasa suka aikata haka, daga nan kuma zai kai agano wanda yayi kisan, danni ina tunanin kamar a cikin yaran makarantar ne aka samu wani ya kashe shi, kaga makarantar yaran masu kud'i ce dole asan yanda za'a rufe maganar.
Adnan yace abu ne me wuya Abbanka ya saurari wannan maganar, domin shekarun da yawa, idan aka tado mashi da maganar zaiga kamar anaso asashi wani babban aiki ne, tunda ya jima da aje aiki kaga abu ne mai wuya ya koma binciken abinda ya faru abaya.
Nabeel yace wallahi duk naji jikina yayi sanyi, kasanni Adnan bana son zalunci, haka Allah yayi ni, matukar naga anyi zalunci bana kyalewa, shiyasa a secondary d'in mu nine Ameer dan gaskiya bana goyon bayan zalunci, shiyasa fa ban zab'i makarantar ku ba dan bana son irin makarantun yaran masu kud'i, dan haka ka barni da Abbah zanyi magana dashi cikin sanyi, kuma zamuyi nasara.
Adnan yace Nabeel sai kayi ahankali kaga Mahaifinka ne. Nabeel yace koda shine ya aikata laifin bazanji kunyar tonashi ba, domin Allah ya hana zalunci.
Ajiyar zuciya Adnan yayi cike da farin ciki, yana masa godiya. Shiru Nabeel yayi can ya kalli Adnan yana fad'in akwai abinda ka b'oye mani Adnan.
Saurin kallonshi Adnan yayi yana fad'in kamar mefa? Murmushi Nabeel yayi yana fad'in wasa nake, kome kenan zamuyi magana. Adnan yace nagode sosai abokina. Nabeel yace bakomai.
Sallama yayi mashi ya rakoshi. Sai da ya tafi kafin ya nufi d'akin Mahaifinshi cike da fatan dacewa dan yasan yanzu yana kallon news.
****
Sai da Adnan ya tsaya wata super market yayi siyayya kafin ya fito zai wuce gida. Adnan Abdurrazak Matawalle! Saurin juyowa yayi jin ankirashi da cikekken sunanshi.
Gabanshi ne ya faad'i ganin wanda yake gabanshi. Matsowa Fawwaz yayi yana ware hannu ya rungume Adnan yana dariya. Jiki a sanyaye Adnan ya rungumeshi zuciyarsa tana tsinkewa.
Kallonshi Fawwaz yayi yana dariya yace shegen kaya, kaganka kuwa? Lallai na yarda ka zama Baba. Murmushi Adnan yayi yana fad'in Fawwaz dama da gaske ka dawo, Yaya Sameer yake fad'a mani shine ko kaneme ni.
Fawwaz yace taya zanki nemanka kawai abubuwa ne sukayi mani yawa, yanzu haka sauri nake zamuje wani party na abokin mu.
Adnan yace lallai dole bazaka nemeni ba saboda kazama d'an gayu ga sababbin abokai kayi. Fawwaz yace No ba haka bane, kasan yanzu kai ka girma, kana da Iyali bekamata narik'a sako ka cikin mu ba, gashi gaba d'aya ma naga kacanza daga yanda nasanka, duk da tun kafin mu rabu naga sabon canji daga gare ka.
Murmushi Adnan yayi yana fad'in dole nake canzawa, domin mun aikata babban laifin da har mu mutu yana bin mu, naga kamar kai kamanta, duk da ba nine na aikata laifin ba kullum cikin nadama nake da istigfari, amma kai gashinan kana morewar ka yanzu ma party zakaje.
Canza fuska Fawwaz yayi yana fad'in bangane ka aikata laifi ba? Adnan yace ka aikata dai, mu kam ai taimaka maka kawai mukayi nida marigayi.
Ja da baya Fawwaz yayi yana k'ank'ance idanu yana kallon Adnan. Murmushi Adnan yayi yana fad'in kada ka damu kawai na tuna maka ne saboda inaso ka fara neman yafiyar Allah, amma tabbas har yanzu ina kallon lokacin da ka yanki Farouk da wuk'a.
Sosai Fawwaz ya canza fuska tamkar wanda be tab'a dariya ba, jijiyoyin kanshi suka tashi idanuwanshi sukayi ja, hannu yasa aljihu ya ciro kwalin sigari, abaki yasa kafin ya bata wuta, sai da yayi mata kyakkyawar zuk'a ya fesar kafin ya kalli Adnan yana fad'in ban d'auka zaka iya tuna wannan abun ba, kamar yanda kasa ma bakin ka kwad'o a wancan karon to inaso kacigaba da zama ahaka, bazan d'auki wannan maganar ba, idan kuma ka san zaka rik'a mani ita to ka d'auka bamu tab'a sanin juna ba.
Jinjina kai Adnan yayi yana murmushi yace haba abokina, kada ka manta da amintakar mu, ada ma banyi magana ba bare yanzu, kawai shawara na baka tunda baka so baza'a sake ba.
Murmushi Fawwaz yayi yana fad'in nasanka ai bazaka iya tona asiri na ba, nagode ka gaishe da Yaranka. Adnan yace zasuji tunda babu kara. Fawwaz yace zan wuce.
Mota Adnan ya shige ranshi fess, koba komai ya tado mashi da abinda yawuce, idan yana da hankali maganar bazata bar zuciyarshi ba.
Fawaaz har ya shiga mota ya d'auki hanyar wajen Partyn yayi saurin canza hanya, tsaki yayi yana zuk'ar sigari ranshi ab'ace, gaba d'aya Adnan ya b'ata masa shirinshi, ya tuno masa abinda ya dad'e da mantawa.
Wayarsa ce tayi k'ara, yana dubawa yaga abokinsa ne, d'auka yayi yana fad'in Guy bazan samu zuwa ba gida zanje kaina yana ciwo. Shiru yayi kafin ya kashe wayar, gudun motar ya k'ara zuwa gida.
Ur's.
Nabeelert Lady🖋
[3/10, 8:40 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud'i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k'asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub'e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.*
3⃣7️⃣
Fawwaz lafiyar ka kuwa? Kauda kai yayi yana fad'in Ammi normal. Zama tayi tana fad'in kace mun zakaje wajen Party amma kuma kadawo kana b'ata fuska ko partyn beyi maka ba? Ammi kawai b'ata mun rai akayi shiyasa.
Murmushi tayi tana fad'in Fawwaz nasha fad'a maka ka girma, yakamata karage wannan shirmen da kakeyi, zuwa yanzu yaci ace ka aje Iya.... Ammi dan Allah kada ki k'arasa, duka me nayi a duniyar da zan cutar da kaina ta hanyar aure har da tara wasu Iyali can, kina ganin Dady sai da ya more rayuwarsa kafin yayi aure, bayan aurensa ma sai da kuka dad'e kafin ya yarda kika haihu gashinan yanzu kowa yaganki bazaiyi tunanin kin haifeni ba, da ace kin haihu da yawa ko kinyi aure da wuri da yanzu kila hak'oranki sun fara fita.
Duka ta kaimashi yayi saurin kaucewa yana dariya. Dadynshi da yake jinsu ya shigo yana fad'in kada ki dokar mani yaro kinsan tunda ya taso besan me ake kira zafin duka ba.
Ammi tace ai duk kaine ka sangartashi, ba damar yaro yayi laifi a tab'ashi sai ka fara fad'a, idan bam manta ba har rabuwa mun tab'ayi akan zan dokeshi.
Dady yace sa'a kikaci baki kai ga dukansa ba shiyasa hukuncin ya tsaya a haka kikaje gida kikayo kwana biyu, da ace kin dokesa kila sai nayi babban hukunci.
Tab'e baki tayi tana fad'in dad'ina da gobe saurin zuwa, shima gashinan ya girma damma ka hanashi aure ai da yanzu shima ya fara jin yanda naji akan Yara.
Zama Dady yayi yana fad'in My Son wai kana son aure yanzu? Saurin girgiza kai yayi yana fad'in bana so Dady, gara abari na k'ara girma.
Ammi tace lallai kam zamu mutu bamuga auren ka ba. Dady yace aikuwa da ran mu zaiyi aure, kana ji na, kada ka damu da ita ka kwantar da hankalin ka babu me takura maka akan aure, duk lokacin daka shirya sai kayi abunka.
Gyara zama Fawwaz yayi yana fad'in Yawwa Dady d'azu daka aike ni gidan Abbah Barau na ga wata yarinya d'iyarsa ce? Dady yace Raheena kenan, itama waje tayi karatu lafiya? Ya mutsa fuska yayi yana fad'in ko gaishe ni batayi ba tana zaune a wajen lambu duk da taji shigowar mota kuma taji masu aiki suna gaishe ni.
Ammi tace dan me zata gaishe ka bayan ba kusa kuke ba, ina ma ruwanka da ita dan batayi maka magana ba? Kika sani ko Yaron nawa ya k'yasa. Dady ya fad'a.
Murmushi Ammi tayi tana fad'in to wannan dai anyi mata miji dan Hajiya Binta ta fad'a mani sunje Dubai siyo kayan aurenta kila ma bikin bazai wuce wata d'aya ba.
Kallonta Fawwaz yayi yana fad'in d'an bani lambarta mugaisa to. Harara Ammi ta banka masa tana fad'in bana son sakarci, meye zaka amshi wayarta bayan kaji aure zatayi.
Dady yace bana son haka fa, da Raheena da Fawwaz duk d'aya ne a wajena, domin Alhaji Barau na hannun dama ta ne, kuma Fawwaz kamar Yaya yake agareta, ko kinji yace maki yana sonta? Girgiza kai Ammi tayi tana fad'in kasan halin zuciya.
Dady yace to ki bashi suyi zumunci, yace maki ba aure zeyi yanzu ba damme zakisa zargi akanshi. Murmushi Ammi tayi tace ayi hak'uri baza'a sake ba.
Kamo hannun Fawwaz Dady yayi yana fad'in akwai abinda yake damunka dan nasan baka saba dawowa kamar haka ba. Yamutsa fuska Fawwaz yayi yana fad'in Dad babu komai kawai gajiya nayi zan kwanta.
Tashi Dadyn yayi yana fad'in shikenan ka kwanta, Ammi muje kada mu hanasa bacci. Tashi tayi tana fad'in Allah ya tashemu lafiya. Fawwaz yace amin.
Kwanciya yayi sai dai daya juya maganganun Adnan ne suke dawo masa, tsaki yayi yana fad'in wallahi Adnan ka b'atamun rai, banda jahilci taya zaka tado abinda yawuce shekaru kusan sha biyu, gashi nan nima abun ya dawo mani.
Tashi yayi ya d'auko wata kwalba a cikin durowarsa, bud'ewa yayi ya shanye abinda yake ciki duka, wurgar da ita yayi ya haye gado yana jin jikinsa yana saki, a hankali idanuwansa suka fara rufewa tamkar wanda ake yawo dashi asama, da haka bacci yayi gaba dashi.
****
Washe gari har wajen k'arfe goma be fito ba, Dady ne ya kalli Ammi yana fad'in wai yau lafiyar Fawwaz kuwa, nasan baya tashi da wuri amma kuma yana fita motsa jiki idan ya gama ya sake kwanciya yau banji motsinshi ba? Ammi tace nima abinda nake tunani kenan. Dady yace muje mu dubashi.
Da mamaki Dady yake kallon kwalbar da take hannunshi, kallon Ammi yayi yana fad'in dama Fawwaz yana shan syrup ne? Ammi tace wallahi nima sai yau na gani.
Girgiza kai Dady yayi yana fad'in wannan syrup d'in mai k'arfin ne, shiyasa be tashi ba har yanzu, da alama kuma be had'ashi da komai ba haka kawai ya sha dan banga robar lemu ba.
Hannu Ammi tasa ta fara tadashi, girgizashi tayi kafin ya farka a firgice yana kiran sunan Farouk. Da mamaki suka bishi da kallo. Zama Dady yayi yana fad'in Fawwaz waye kuma Farouk? Hannu yasa ya dafe kanshi yana goge zufar datake goshinsa.
Sake tambayarsa yayi kafin ya kallesu yana fad'in bakowa. Ammi tace banyarda ba, taya zaka farka da sunan mutum abakin ka da alamu mafarkinsa kayi, kuma da tunaninshi ka kwanta.
'Bata fuska yayi yana kokarin sauka yace Ammi nace bakowa wani abokina ne. Dady yace shikenan tashi kaje kayi wanka kayi sallah kazo ina da magana da kai.
**** ****
Wai Nabeel lafiya kake kuwa? Jiya da dare ina kallo kazo ka zauna kayi shiru kamar da magana abakin ka, na tambayeka kace bakomai ka tafi, yauma gashi kazo mun gaisa kuma kazauna kamar zaka fad'i wata magana amma kayi shiru.
Gyara zama Nabeel yayi yana fad'in Abbah dama wata tambaya zanyi maka to jiya naga hankalin ka yana wajen kallon news shiyasa na tafi.
Kofin shayin Abbah ya aje yana fad'in ina jinka. Duk'ar da kai Nabeel yayi yana fad'in d'azu ne da ana gyara wancan tsohon d'akin na kaya shine naga wata tsohuwar jarida, har na barta sai kuma naga sunan makarantar da kayi aiki a jiki ga hoton wani yaro a kwance da kayan makarantar jikinsa duk jini, hakan ne yaja hankalina na karanta shafin, kuma hada hotonka na gani a kasan shafin a matsayin ka na shugaban makarantar, to shine labarin yaja hankalina nakeso naji yanda abun ya faru.
Saurin zare glass d'in idonshi yayi yana kallon Nabeel, ido Nabeel ya d'ago yana karantar mahaifinsa. Kayi hak'uri Abbah idan maganar ta b'ata maka rai.
Ajiyar zuciya Abbah yayi yana fad'in waye ya baka wannan labarin? Nabeel yace a jarida na gani. Jinjina kai Abbah yayi yana fad'in dama ba'a kone duk wasu jaridun d'akin ba? To yaushe ma aka fiddo da kayan d'akin tunda nasan babu abinda za'ayi a d'akin, ko dai kaine kaje kayi mani bincike? Saurin girgiza kai Nabeel yayi yana fad'in da gaske gyaran d'akin nasa ayi, gashi can ma suna k'arasawa.
Ina jaridar take? Abbah ya fad'a jiki a sanyaye. Hannu Nabeel yasa a aljihu ya cirota ya mik'a masa. Shiru Abbah yayi yana kallon hoton Farouk da yake kwance cikin jini ga wuyansa da shatin wuka.
Wasu hawaye ne suka taho masa, da sauri ya maida glass d'inshi ya aje jaridar. Kallon Nabeel yayi cikin dakiya yana fad'in wannan ai tsohon abu ne, kanaga tun 2008 fa, ni harna manta da abun ma, muma haka muka samu labari dan abun ya faru ne bayan an tashi daga makaranta.
Nabeel yace to Abbah bakuyi bincike ba? Girgiza kai yayi yana fad'in duk abinda ya faru bayan makaranta to bamu da hakki akansa, sannan kuma abun ba'a makaranta ya faru ba, kaga bamu da ikon yin wani abu, kayan makarantar da suke jikinsa ne yasa kaga ansa hotona saboda 'Dalibina ne, da ace Iyayenshi sun nuna zasu shigar da k'ara da amatsayin mu na shuwagabannin makarantar Yaron mun taimaka wajen ganin a kwato masa hakkinsa, amma koda mukaje gaisuwa Mahaifin Yaron yace abar maganar.
Amma Abbah.... Kaga Nabeel bana son yawan tambaya, kana son jin abinda ya faru kuma na fad'a maka, bansan ta yanda aka kashe shi ba tunda ba'a makaranta ya mutu ba, dan haka bana so ka tado mani da abinda yawuce shekaru da yawa, ka maida hankali wajen aikin ka zaifi maka. Tashi kaje, kuma bana so naji ka sake tada maganar dan nasanka da son kwato ma mutane hakkinsu, shiyasa ma ka zab'i kayi aiki a hukumar kwato ma d'an Adam hakkinsa.
Jiki a sanyaye Nabeel ya fice, kai tsaye wajen masu gyaran d'akin ya nufa, yana zuwa ya iske har sun gama sun rufe d'akin an kwashe dattin. Zama yayi yana murmushi, dama yasan za'a iya samun tsohuwar jarida a wannan d'akin, shiyasa tunda Adnan ya fad'a masa an buga labarin ajarida a daren jiya yayi tunanin yazo ya bincika dan yasan Abbanshi akwai aje tsofaffin kaya, hakan yasa yau tunda safe yashiga d'akin, cikin ikon Allah yaga jaridar, shiyasa yasa masu aiki su gyara d'akin gudun kada ya kaima Abbah jaridar yace da niya ya bincikota.
Ajiyar zuciya yayi yana tuna yanayin da yaga Abbansa aciki, tabbas akwai wani b'oyayyan lamari, akwai abinda Abbansa ya sani yake b'oyewa, haka ma Adnan ba gaskiyar labarin ya bashi ba. Dole yasan gaskiyar labarin kodan ya taimaki Abbansa kada mutuwa ta riskeshi da hakkin wasu.
Waya ya ciro ya kira Adnan, bayan sun gaisa yace mashi yana so su had'u anjima. Adnan yace shikenan. Kashe wayar yayi ya koma cikin gida.
**** ***
Hello Alhaji Marusa lafiya kuwa naji kamar kana cikin damuwa? Alhaji Barau ya fad'a cikin tashin hankali. Alhaji Marusa yace nima tambayar da zan maka kenan najika cikin tashin hankali, yanzu nake shirin kiranka sai gashi ka kirani.
Narke murya Alhaji Barau yayi yana fad'in store d'in kayana akazo cikin dare aka yashe ni, komai basu bar mani ba, da asuba Mr. Kallah yamun waya babban shagonshi na garinsu cikin dare ya kama da wuta ko tsinke ba'a fitar ba, shine nace bara na kiraka na fad'a maka halin da muke ciki.
Hawaye ne suka zubo ma Alhaji Marusa yana fad'in naku me sauki ne, tun jiya na kira ku amma wayar ku bata shiga, wallahi jiya banyi bacci ba, gaba d'aya tashin hankali yamun yawa ko abinci na kasaci, shikenan talauci ya fara mani sallama Alhaji Barau.
Mekake fad'a ne haka Alhaji Marusa? Sun takaita ni Alhaji Barau, kayan da nayi oda jiya an d'auko mani su cikin dare aka tare masu motar aka kwace sannan aka kashe su, kaya ne masu tsadar gaske, na saka dukiyata mai yawa wajen d'aukosu, sannan babbar ma'ajiyata itama yau da asuba akamun waya ta kone kurmus, shikenan nashiga ukku.
Murmushin gefen baki Alhaji Barau yayi kafin ya canza fuska yana fad'in yaushe ka bada odar kaya Alhaji Marusa? Ai na d'auka mun yanke shawarar had'a guiwa mu d'auko wasu kaya gaba d'aya, tun daga lokacin kuma babu wanda ya sake shigo da kaya amma gashi kace an kawo maka kaya jiya? Daburcewa Alhaji Marusa yayi yana fad'in ba su bane, wad'annan wasu ne daban abokin harkallarmu yamun tayinsu shine na tura masa kud'i, dan Allah kazo inaji dole muje asibiti dan numfashina baya tafiya dai-dai.
Alhaji Barau yace shikenan kazauna kada ka tashi gani nan. Godiya yayi masa ya kashe wayar. Wata irin dariya Alhaji Barau yasa yana fad'in damu kake magana, Allah yasa ma kasheka mu huta. Jakarsa ya d'auka ya saukko.
A falo ya iske su Momy, kallonta yayi yana fad'in direba zaizo ya amsar mani kayan kari sauri nake Alhaji Marusa beda lafiya. Momy tace ikon Allah, meya sameshi kuma? Alhaji Barau yace idan na dawo zakiji amma dai bala'i ne ya afka masa.
Momy tace to Allah ya kyauta, ince dai babu komai naka a cikin bala'in? Murmushi yayi yana fad'in babu. Kai ta jinjina tana fad'in to mun gode Allah, sai ka dawo.
Yana fita direbanshi yazo ya amshi jakar hannunsa ya bud'e masa mota yashiga suka bar gidan. A hanya aka kirashi da wata lamba, yana d'auka aka fad'a masa babban 'Dan Alhaji Marusa ne. Alhaji Barau yace naji dai, lafiya ko? Daga can aka fad'a masa Alhaji Marusa ne ya fad'i an wuce dashi asibiti. Cike da jimami yace gashinan zuwa.Murmushi yayi ya kalli direba yana fad'a masa su wuce asibitin su. Mr. Kallah ya kira ya fad'a masa yace gashinan zuwa.
**** ***
Fawwaz meya had'a ka da wannan maganin mai k'arfi haka? Kauda kai yayi yana fad'in Dady mura nakeyi shine nasha. Ammi tace murar ce tasa ka shanye kwalba d'aya? Saurin kallonta yayi yana fad'in Ammi wace irin kwalba d'aya kuma, ya dad'e fa iya yanda akace asha nake sha kawai jiya ne ya k'are.
To meya saka dogon bacci haka? Dady yace isa haka Ammi tunda yace ba duka yasha ba abar maganar. Tab'e baki tayi tana fad'in kaje kaci abincin ka. Dady yace sa akawo masa nan.
Tashi tayi tana fad'in wallahi Alhaji kana shagwab'ar da yaron nan, ya girma amma ka hanashi ya fahimci haka. Dady yace e naji bakomai. Murmushi Fawwaz yayi yana fad'in Dady da Ammi nah.
**** ****
Abbah ina kwana ya gidan? Lafiya lau jiki yayi sauki ai. Alhaji Mansur yace to madalla, sai ka k'ara kula, bana so kana saka damuwa aranka, sai jiya Maman ku take fad'a mani baka da lafiya.
Ra'eez yace ai na warke Abbah. Alhaji Mansur yace ta fad'a mani kokarin da kukeyi kai da abokan ka, kayi masu godiya, insha Allahu komai ya kusa zuwa k'arshe.
Ra'eez ya fad'a masa yanda sukayi da Kawun Jabeer. Alhaji Mansur yace Allah sarki Brr. Kamal, kaga kuwa na rasa lambarshi ka turo mani sai muyi magana dashi, Abubakar ma zan kirashi na fad'a masa shari'ar ta kusa zuwa dan ya shirya.
Ra'eez yace yanzu zan turo maka. Alhaji Mansur yace maganar motarka ban manta ba, wannan satin zai dawo zai zo ya dubata. Ra'eez yace to Abbah nagode, agaishe dasu Umma.
**** ***
Yes, shigo. *Malan Dauda* lafiya dai,,? Risnawa yayi yana fad'in 'Yallab'ai kana da bako. Bako kuma, waye ne? E to ya nuna mani katinshi ma'aikacin gidan babban redion ne.
Shikenan kace yashigo. Da sallama Rafeek yashigo ofis d'in Kwamishna, amsawa yayi yana nuna mashi wajen zama. Hannu Kwamishna ya mik'a masa suka gaisa. Murmushi yayi yana fad'in lallai yau muna da manyan baki.
Murmushi Rafeek yayi yana fad'in 'Yallab'ai barka da aiki. Kwamishna yace yauwa kaima sannun ka da aiki, ai kune masu aiki domin kuna nishad'antar damu da labaruka masu gamsarwa, musamman kai, dan ina kallon labaranka.
Ruwan da masinjan ya aje ya d'auka yasha yana fad'in ai abun ba sauki 'Yallab'ai. Kwamishna yace to Allah yasa mudace. Rafeek yace amin.
Wato dama nazo ne ina so naroki alfarmar fira da kai agidan redion mu idan babu damuwa. Murmushi Kwamishna yayi yana fad'in haba babu damuwar komai, ai gidan redion ku babba ne, kunsan abinda kukeyi shiyasa nake matuk'ar son sauraren abinda ya fito daga can, babu komai yaushe ne lokacin firar? Rafeek yace 'Yallab'ai kaine zaka sa mana lokaci ai.
Murmushi Kwamishna yayi yana fad'in ko gobe ma yayi. Rafeek yace to mungode Allah ya k'ara girma. Kwamishna yace amin. Kati Rafeek ya mik'a masa shima ya bashi nashi. Godiya yayi masa ya baro ofis d'in cike da farin ciki, kai tsaye asibitin da akayi masa kwatance mallakin Dr. Aliyu Sani ya nufa.
Kwamishna kuwa farin ciki ne ya rufeshi jin za'ayi fira dashi a babban gidan redio, yasan tunda suka gayyaceshi sun yaba da aikinsa shiyasa suke son fira dashi, yasan kilama ya samu lambar yabo idan aka ga karramawar da 'yan gidan redion zasuyi mashi.
**** ****
Adnan maganar daka fad'a mani gaskiya ce kuwa? Kallon Nabeel Adnan yayi yana fad'in baka yarda dani bane? Girgiza kai yayi yana fad'in na yarda da kai, sai dai acikin labarin daka bani baka fad'a mani gaskiyar yanda abun ya faru ba, da alama kasan komai tunda makarantar kuce, kuma Yaron ajinku d'aya, kawai dai kana b'oye mani ne saboda kana jin kunyar ka tona asirin mahaifina.
Adnan yace ya kake fad'in haka, waye ya fad'a maka Abbanka yana da hannu acikin abinda ya faru? Idan beda hannu ka fad'a mani waye yake bayanshi to? Ajiyar zuciya Adnan ya saki yana fad'in wai Nabeel lafiya kake kuwa, yanda ka d'auki wannan abun kamar wani naka ne haka ta faru dashi.
Murmushi Nabeel yayi yana fad'in kada kamanta aikina ne, Allah ya bani ilimin sanin yanayin da mutum yake ciki, gashi kuma ina aiki a k'arkashin masu kare hakkin d'an Adam (Human right), tun daka fad'a mani wannan labarin nasan dole Abbah yana da alak'a dashi, kaima kana neman wani abu ne shiyasa kazo mani da maganar, domin bani da had'i da labarinka amma gashi kazo mani dashi, shekarar mu nawa tare baka tab'a bani wannan labarin ba sai jiya. Uhmm Adnan ko baka fad'a mani ba dole Abbah yana da masaniya akan wannan abun, kuma ka sani idan baka fad'a mani ba zanje nayi bincike da kaina, domin tunda ka bani labarin nan ya tab'a zuciyata, kuma naji ina da sha'awar taimakawa.
Jinjina kai Adnan yayi yana fad'in kayi hak'uri zan baka labari, abun ne babu dad'in ji dan bansan yanda zaka kalleshi ba tunda ya shafi ahalin ka, amma tunda kace na fad'a maka zan fad'a maka, sai dai ina rokon ka koda kaji labarin idan har bazaka taimaka ba saboda Mahaifinka dan Allah kada ka fad'ama kowa.
Nabeel yace wallahi koda Abbah ne ya kashe Farouk sai na tabbatar da gaskiya, dan haka ina jinka....
Ur's.
Nabeelert Lady🖋
[3/10, 8:40 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud'i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k'asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub'e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.*
3⃣8️⃣
Hannu Nabeel yasa yana share hawayen da suka jik'a masa fuska na tausayin labarin da Adnan ya gama bashi, Adnan ma kukan yakeyi, jiyake kamar ayanzu abun ya faru.
Girgiza kai Nabeel yayi yana fad'in na sani dama Abbana yana da masaniya akan wannan abun, tun d'azu da mukayi magana naga halin da yashiga hankalina bai kwanta ba, hakan yasa nace ka fad'a mani gaskiya.
Adnan yace wallahi Nabeel tunda Yaya Sameer yazo mani da maganar hankali na yake tashe, duk da abaya ina d'an tuna abun amma ba kamar da Yaya yazo mani da maganar ba, tun daga ranar komai ya canza mani, wallahi jiya har mafarkin Naseer da Farouk nayi, shiyasa na kudirta araina ko zan rasa raina sai na bayar da sheda akan shari'ar da za'a gabatar, gaba d'aya laifin mu ne, da ace mun fad'i gaskiya duk haka bazata faru ba.
Nabeel yace dole a tabbatar da wannan gaskiyar, koda ace dasa hannun Abbah akayi kisan wallahi sai an tona komai, sai kuma Allah yasa babushi aciki, laifinsa d'aya daya taimaka ma masu laifi wajen b'oye gaskiya, nasan shima dole ayi masa hukunci.
Jinjina kai Adnan yayi yana fad'in nagode Nabeel, hakika kai d'in abokine nagari, na d'auka zansha wahala kafin ka bani had'in kai sai gashi kaima zaka bada taka gudummuwar, tabbas ka dace da yanayin aikin ka, Allah ya saka maka da mafificin alkhairi.
Nabeel yace amin, sai dai kuma banso kayima Fawwaz wannan maganar ba, domin nasan duk inda yake maganar tana masa yawo akai, duk lokacin da yaji an shigar da k'ara kaine zaka fad'o masa arai, zai iya yin duk abinda zeyi wajen ganin bakaje kotu ba.
Adnan yace ka barshi Allah ya fishi, gara da nayi masa maganar na tabbata bazai sake kwanciyar hankali ba. Nabeel yace haka ne, Allah ya bamu ikon tabbatar da gaskiya. Adnan yace amin. Sallama yayi mashi yawuce cike da farin ciki.
**** ****
Tsaye Rafeek yake a bakin k'ofar asibitin Dr. Aliyu Sani sai kallon agogo yakeyi, wani ma'aikacin wajen ne yazo wucewa, da sauri Rafeek ya k'arasa yayi masa sallama.
Murmushi mutumin yayi yana amsawa dan ya gane Rafeek saboda ba b'oyayye bane kasancewarsa ma'aikacin gidan babbar redio.
Hannu Rafeek ya bashi suka gaisa. Mutumin yace yau muna da babban bako, shine kuma kake tsaye a waje Malan Rafeek. Murmushi Rafeek yayi yana fad'in ai ban dad'e da zuwa ba dama ina jiran naga wani ne.
Mutumin yace barka da zuwa ni sunana *Dr. Sageer Isah*, kai kam nasan naka domin sananne ne a wajen kowa. Murmushi Rafeek yayi yana fad'in nagode sosai Dr. Sageer.
Shiru yayi kafin yace dan Allah Dr. Aliyu fa? Dr. Sageer yace aikuwa yau zaishigo dan yau ranar zuwansa ne, kasan Dr. Ba kasafai yake shigowa ba akwai wasu aiyukan da suke gabansa, amma yau munyi waya yace zaishigo, sai dai ban sani ba ko da wuri zai shigo.
Jinjina kai Rafeek yayi yana fad'in ina jin labarinsa gaskiya babban likita ne, gashi har ya bud'e asibitinshi, ga na gwamnati da yake aiki, ga sauran wajaje da yaje gudanar da aiyukansa, hakan yasa nakeso mu d'an gana dashi.
Murmushi Dr. Sageer yayi yana fad'in ai Dr. Ba sauki, mutum ne mai matuk'ar son kud'i, shiyasa gaba d'aya rayuwarsa beda lokacin kanshi, duk wani abu indai zai kawo kud'i to Dr. yana gaba wajen nemoshi, shiyasa asibitin nan muke da abubuwa da yawa, ba dai muje waje muyi wani abu ba sai dai ma azo wajen mu ayi.
Rafeek yace Allah sarki, gaskiya yasan kanshi, ai duniyar sai da neman kud'i. Dr. Sageer yace muje daga ciki ka jirashi ai bazamu bar babban bako a waje ba. Rafeek yace shikenan muje, amma idan naga bezo ba zan tafi saboda na baro aiki.
****
Ra'eez Yaya fa yace mu fara shirya yanda za'a shigar da k'arar su Naseer, dan sunyi waya da Adnan ya fad'a masa an samu Nabeel zai taimaka, tunda ba'a gano Iyayen Farouk ba gara ashigar da shari'ar Naseer hakan ne zai tono ta Farouk.
Ajiyar zuciya Ra'eez yayi yana fad'in nima so nake zuwa litinin afara shari'ar dan bana so murasa damar da muke da ita. Jabeer yace sai dai Yaya yace beyi magana da Baffansa ba, yafiso sai anshigar da k'arar kafin yayi masu magana.
Ra'eez yace ina tsoron kada suce basu amince ba. Jabeer yace zasu amince, domin babu wanda zaiji labarinka be tausaya maka ba, kuma ta shari'ar su ce za'a tado taka.
Ra'eez yace Allah yasa. Jabeer yace amin, wai ina mutuniyar? Tsaki Ra'eez yayi yana fad'in ko jiya tamun waya muka gaisa. Jabeer yace baiwar Allah. Tashi Ra'eez yayi yana fad'in muje ni kada ka fara kawo mani maganar wata Raheena. Dariya Jabeer yayi yana fad'in daga fad'in gaskiya.
**** ***
Dr. Sageer ya aiki ina fatan komai yana tafiya dai-dai? Jinjina kai Dr. Sageer yayi yana fad'in aiki lafiya lau babu matsalar komai, sai dai kana da babban bako.
Glass ya cire yana fad'in bako kuma? Ai babu wada yace mun zai zo. Dr. Sageer yace wannan ma'aikacin babban gidan redion ne *Rafeek Sambo Jarmai*.
Jinjina kai yayi yana fad'in meya kawo d'an jarida waje na kuma? Dr. Sageer yace yanda kake cigaba 'Yallab'ai ai dole 'yan jarida surika son ganinka, shima d'azu ya gama yabonka.
Murmushi Dr. Aliyu yayi yana fad'in ka shigo dashi to. Dr. Sageer yace yanzu kuwa.
Bayan Rafeek yashigo suka gaisa sai Dr. Sageer ya basu waje. Dr. Aliyu yace yau kaine da kan ka? Rafeek yace wallahi kuwa, jiya nashiga babban asibiti wajen wani abokina shine ake maganar irin kwazonka shine nace ni kuma zanzo naga asibitinka kuma mugaisa.
Murmushi Dr. Aliyu yayi yana fad'in amma nagode, ai mutum baya zama gwarzo dole saiya jajirce, kafin na kawo wannan matsayin nasha gwagwarmaya sosai, da haka dai ina hak'uri har Allah ya d'aga ni.
Rafeek yace wannan haka yake, ai kamar babban Alkali ne Alhaji Barau, duk wanda yasanshi yasan yanda yake da jajircewa awajen aiki, saboda kok'arinsa sai da sunanshi yayi fice a gidan redion mu, sannan ga tsohon Alkali, su duka biyun mutane suna alfahari dasu.
Gyara zama Dr. Aliyu yayi yana fad'in Allah sarki Brr. Barau, ai mutumina ne sosai, yanzu ma aiki ne yamun yawa shiyasa muka rage gaisawa, ai ta silarsu na samu alkhairi sosai, zan iya cewa ta silarsu na kai wannan matsayin da nake ayanzu, domin sun taka rawar gani arayuwata.
Jinjina kai Rafeek yayi yana fad'in da alama kayi masu abinda sukaji dad'i hakan yasa suka tsaya maka. Dr. Aliyu yace sosai kuwa, domin nine na fara taimaka mashi ya kai wannan matsayin da yake kai kafin shima yasa tsohon Alkali da wasu manya suka dafa mani, tabbas nine na fara taimaka masu.
Rafeek yace idan haka ne kaine ka tsaya masu ba sune suka tsaya maka ba, domin duk wanda zai maka wani taimako har kaci nasara arayuwa to baka da kamarsa, duk da bansan abinda kayi masu ba amma nasan amatsayinka na babban likita nasan ka cece rayuwar wani daga cikinsu.
Girgiza kai Dr. Aliyu yayi yana fad'in ko d'aya, kawai nayi masu.... Gyaran murya yayi yana fad'in haka ne, kasan mu likitoci akwai mu da taimako, idan kuma mutum yasan alkhairi to baya mantawa damu, wannan shine abinda ya had'ani dasu har muke abota.
Rafeek yace gaskiya kai d'in na daban ne, gashi dai kaine mai taimakon amma duk da haka kana ganin sune suka taimaka maka, Allah ne zai iya biyanka.
Murmushi Dr. Aliyu ya saki yana fad'in maganar ka gaskiya ce Rafeek, ya kamata ace har yanzu suna bani girma, sai dai kuma nine nake nemansu ba sune suke nemana ba, akwai Alhaji Marusa da Mr. Kallah duk mutane na ne.
Rafeek yace saboda ka gama masu amfani shiyasa suka kyale ka, kasan suna hud'd'a da mutane da yawa dole surik'a samun masu yi masu alfarma da yawa shiyasa bazasu rik'a neman wad'an da suka taimakesu ba.
Murmushi Dr. Aliyu yayi yana fad'in aiko be kamata ace sun manta dani ba musamman shi Brr. Barau, domin na bada gudummuwa wajen hayewarsa wannan kujera, gaskiya ka sosa mani inda yake mani kaikayi ma, maganar ka gaskiya ce, bekamata ace nine nake binsu ba domin nine nayi masu rana.
Murmushi Rafeek yayi ya mik'e yana fad'in 'Yallab'ai zan koma, dama nace zanzo mugaisa ne. Hannu Dr. Aliyu ya bashi yana fad'in nagode Rafeek, ga katina sai murik'a gaisawa ko.
Rafeek yace nike da godiya. Sallama yayi mashi ya fice ya barshi yana juyi a kujera cike da tunani. Murmushi ya saki yana fad'in Allah yayi maka albarka Rafeek, ka sosa mani inda yake mani kaikayi, ga babban Lab can zan fara ginawa dama ina tunanin gininshi bara nayi amfani da wannan damar, Allah ma yaso banyi sub'utar baki ba dana fad'a masa tsohon sirrin mu.
Waya ya ciro ya fara neman Alhaji Barau. Bugu biyu ya d'auka, bayan sun gaisa Alhaji Barau yace babban likita kwana da yawa, ka ganni nan nazo asibiti an kawo Alhaji Marusa.
Dr. Aliyu yace kunki dai dawowa asibitina duk da kunsan nima ina da kayan aiki. Alhaji Barau yace ba haka bane, kasan asibitin mu hada turawa kai kuma naka babu wasu kwararrun likitoci, kasan ni kuma bana son wasa da rayuwa shiyasa na rik'e asibitin Dr. James.
Jinjina kai Dr. yayi yana fad'in idan da amana ai ruwa bazaici gwani ba. Alhaji Barau yace me kake nufi? Gyara zama Dr. yayi yana fad'in manta kawai, dama wasu 'yan kud'i nake so zan fara gina parmanent side na Lab d'ina kuma babu kud'i masu yawa a hannuna shine nace bara na maka magana.
Shiru Alhaji Barau yayi kafin yace haba likita, taya zaka zo mani da maganar kud'i da rana tsaka haka. Murmushi Dr yayi yana fad'in ko bashi ne ai zan samu ko? Alhaji Barau yace amma kaji nace ankawo Alhaji Marusa asibiti ko? Kuma ni yanzu banida kud'in da zan iya baka aro dan bikin d'iyata za'ayi, wai Likita meyasa kake son tambayata kud'i ne.
Dr yace yanzu dan nace ka bani bashi shikenan ya zama laifi, haba Alhaji kada ka mance da alkhairin da nayi maka fa, ko shekaru dubu za'ayi bekamata kamance da abinda nayi maku ba, domin nayi maku babbar rana kaima kasani, kuma har yanzu da bazata kake rawa.
Tsaki Alhaji Barau yayi yana fad'in ni bangane abinda kake magana akai ba danni bani da lokacin tunawa da rayuwar baya, koma menene bani da kud'i sai dai kajira Alhaji Marusa ya warke, ka gaishe da iyalin ka sai anjima.
Kallon wayar yayi jin an katse. Murmushi yayi yana fad'in maganar ka gaskiya ce Rafeek, dama nayi haka ne dan na gwadasu, lallai Brr. Barau ya cika butulu, amma bakomai indai nine bazan sake nemanshi ba, nagode Allah nima ina da kud'i, ko ba komai naci daga jikinsu da kud'in su ma nayi wannan ginin.
*** ***
Wai *Marwan* meya faru ne? Wanda aka kira da Marwan ya yamutsa fuska yana fad'in nima bansani ba, nazo zan amshi wasu kud'i ina shiga falon kawai na ganshi ya mik'e daga zaunan da yake, kafin na shiga kawai naga ya zube k'asa, gashi can dai ana dubashi.
Alhaji Barau yace shima Alhaji Marusa sai da nace mashi ya zauna nazo amma ya tashi, ba'a son idan tashin hankali ya same ka ka tashi. Marwan yace kamar ya ban gane ba? Labarin abinda ya faru ya fad'a masa.
Yamutse fuska yayi yana fad'in amma ai babu abinda zai tab'a dukiyarshi dan ya rasa d'an wannan abun dan nasan Dad yana da mak'udan kud'i, meye nashi nashiga damuwa gashinan zai jama kanshi, da kyar idan bai samu mutuwar b'arin jiki ba, yanzu ko kula dashi ai aiki ne, sai dai ya biya kud'i a fiddashi waje yayi jinyarsa acan danni cikin satin nan zan koma India.
Ido Alhaji Barau ya tsura ma Marwan har ya gama maganarshi. Ajiyar zuciya ya saki yana fad'in yanzu ina K'anin naka? Marwan yace kasan baya son zaman k'asar nan, dama kuma Dad baya son muna zuwa gida, Mom kuma taje Dubai sai jibi zata dawo.
Alhaji Barau yace to Allah ya kyauta, sai ka tsaida tafiyarka ka kula dashi kafin asan abunyi. Waro ido yayi yana mik'ewa, kallon agogo yayi yana fad'in yanzu ni ina da wajen zuwa, dama kai na tsaya jira da naji kace kana hanya, zanje kafin anjima na dawo.
Bai jira amsar Alhaji Barau ba yayi gaba. Baki Alhaji Barau ya saki yana kallon Marwan, a hankali yake fad'in Allah nagode maka da baka bani namiji ba, tabbas yanzu Alhaji Marusa zaiyi nadamar rashin kula da yaranshi da yayi, koba komai ita tarbiya wani abu ce, saboda baka son takura ka tura yara waje sai dai ka aika masu kud'i, lallai Alhaji Marusa taka tazo k'arshe, nima ba zama zanyi ba ina da aikinyi.
Fitowar likita yasa yayi saurin binshi zuwa ofis. Bayan sun gaisa yake fad'a masa sanadiyar fad'uwar da yayi ya samu mutuwar b'arin jiki, dole abashi gado saboda za'a fara masa gashi, anci sa'a ma akwai sauran kud'inshi da yawa a asusun asibitin da ya zuba ana juyawa saboda rashin lafiyarshi data iyalinshi, dan haka yanzu kulawa kawai zasu bashi, sannan jininsa ya hau dole ya samu hutu.
Alhaji Barau yace lallai tashi ta sameshi, tunda akwai kud'i ai damuwar da sauki, yanzu acigaba da bashi kulawa zamu rik'a waya. Likita yace ba komai zamu kula dashi. Sallama yayi mashi ya fita.
**** ***
Wai Rafeek lafiya kwana biyu ka canza ba kamar yanda kake ba? Murmushi yayi yana fad'in lafiya lau Baffa kawai wani aiki ne ya tasoni gaba shine yasa bana zama.
Gyara zama Baffa yayi yana fad'in bana so kana matsama kanka, nasha fad'a maka aikin ku yana da had'ari, shiyasa kaji ina yawan tambayarka dan bana so kajefa kanka cikin damuwa kazo kaja mana, dan Allah Rafeek kada kajawo mana abinda zamu rasaka kamar yanda muka rasa d'an uwanka, kome zakayi arayuwa yana da kyau karika sanar mana domin addu'ar mu agareka kariya ce.
Jinjina kai Rafeek yayi yana fad'in Baffa banyi niyar sanar da ku komai ba har sai na kammala abinda nakeyi, amma wannan maganar da kayi tasa jikina yayi sanyi, tabbas akwai abinda nake shirinyi, kuma ina da niyar sanar daku nan gaba kad'an, amma dole yanzu na fad'a maku.
Dama shari'ar marigayi Naseer ce nakeso zan dawo da ita domin abi masa hakkin sa sabo.... Dakata Rafeek! Ummansu ta fad'a cikin karaji, da sauri ya d'ago kai yana kallonta.
Hawaye ne suka gangaro a fuskarta tacigaba da fad'in ban amince maka ka tado wannan maganar ba, abinda yawuce shekara da shekaru meye amfanin tadoshi, wato acan baya k'arfin ka be kawo ba shiyasa da mukace abarshi ka hak'ura, yanzu kuma kana ganin kayi kwari ka isa tsayawa da k'afafuwanka shine zaka tado mana da tashin hankalin da muka manta dashi, wallahi Rafeek ka fita a idona, zan sab'a maka akan wannan maganar, babu wanda ya isa ya maido da wannan maganar baya, domin nasan ruhin Naseer yana can cikin salama.
Matsowa Rafeek yayi yana had'a hannu, magiya zai fara mata ta daka masa tsawa dole tasa yayi shiru. Girgiza kai Baffa yayi yana fad'in shiyasa jikina be bani ba kaji nayi maka wannan tambayar, yanzu Rafeek so kake kaima mu rasaka kamar yanda muka rasa Naseer? Allah ya fimu sanin wad'an da suka aikata masa haka ka barsu dashi zeyi maganinsu, idan ma ka shigar da k'ara inaso kaje ka soketa, domin babu wanda zai sani shiga kotu, ko kai babu inda zakaje.
Hawaye ne suka zuboma Rafeek, kai yashiga girgizawa yana fad'in dan Allah Baffa ku saurare ni, wallahi ba saboda Naseer zanyi wannan abun ba, inaso a tabbatar da gaskiya shiyasa na fara sako maganarshi amma.... Tashi kabar gidan nan Rafeek, kuma kada ka sake shigowa matuk'ar da wannan maganar zaka zo. Umma ta fad'a cikin dakiya.
Kallon Baffa yayi yana hawaye. Kai ya jinjina masa hakan yasa ya fice yana share hawayen idonshi, yanzu ya zeyi dasu Ra'eez, duk wani sa ransu akanshi ne, sai da komai yazo k'arshe za'a hanashi.
Wayarsa ce tayi k'ara, yana dubawa yaga Ra'eez, saurin seta kanshi yayi kafin ya d'auka. Bayan sun gaisa Ra'eez yace Yaya mun gama rubuta k'arar da za'a shigar, zan kawo maka kagani zuwa gobe juma'a sai ashigar da ita zuwa litinin ashiga kotu.
Runtse ido yayi cikin k'arfin hali yace Ra'eez kai da Jabeer ina so anjima kuzo inaso muje wajen su Baffa ne. Ra'eez yace Yaya kamar akwai matsala ko? Murmushi yayi yana fad'in bakomai kawai kuzo. Jiki a sanyaye Ra'eez yace Allah ya kaimu.
Kashe wayar yayi yana goge hawayen idonshi, dole ya sako su Ra'eez a wannan maganar idan ba haka ba Umma bazata tab'a amincewa ayi shari'ar ba, shi kuma yana so kowa yasan cewar ba Abbun Ra'eez kad'ai suka kashe ba, yafiso kowa yasan yanda suka aikata mugayen abubuwa. Motarshi ya nufa ya bar gidan.
Ur's.
Nabeelert Lady🖋
[3/10, 8:40 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud'i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k'asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub'e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.*
3⃣9⃣
Guiwa biyu Ra'eez yasa a k'asa ya had'e hannuwansa biyu yayin da hawaye suke ambaliya a idonshi, matsawa kusa da Baffa yayi bayan daya gama basu labarinshi, cikin kuka mai tab'a zuciya da raunanniyar murya yake fad'in Baffa na roke ku da girman Allah ku bar Yaya ya tayani wannan yakin, zuciyata tana da rauni, Allah shine yasan hakan shiyasa ya had'ani da Yaya tare da Jabeer, tabbas Yaya jigo ne agareni, shid'in tsani ne wanda zai taimaka mani zuwa ga kai matakin da nake fatan kaiwa da dad'ewa, matuk'ar kuka janyeshi acikin wannan shari'ar nasan zuciyata zata raunana, duk wani sa rai da nake dashi zan rasa shi, na amince a janye shari'ar Naseer amma dan Allah ku bar Yaya ya tayani kwatoma Ummu na hakkinta ko hakan zai zamo silar samun lafiyarta.
Shiru yayi yana wani irin kuka mai ban tausayi. Gaba d'aya falon shiru yayi babu wanda baya kuka, duk dauriya irin ta Baffa sai da ya zubar da kwalla.
Umma ce tayi saurin kamo hannun Ra'eez tana share masa hawaye yayin da nata suke zubowa. Girgiza kai tayi tana fad'in ban tab'a jin labarin daya tab'a zuciyata irin naka ba, ya isa kadena kuka, daga yau ka zama 'Dah na, haka zalika ga Baffansu nan ya zam mahaifinka. Kallon Rafeek tayi tana fad'in na amince maka ka tayashi tabbatar da gaskiya, shari'ar Naseer kuma baza'a fasata ba, kushigar da k'aran aranar litinin za'ayita.
Tabbas ayanzu bazan yafema kaina ba idan naki amincewa ayi wannan shari'ar, dan haka na amince maka. Runtse ido Rafeek yayi hawayen farin ciki suna zubo masa.
Murmushi Jabeer ya saki yana rungume Rafeek. Hannu Baffa yasa yana goge idonshi yace tabbas duniya babu gaskiya, ashe dama wad'an nan azzaluman sune sukayi silar mutuwar Mahaifinka? Tabbas nasan mahaifinka mutum ne mai gaskiya, duk da bani da alak'a dashi amma zuwanshi ya samar mana kwanciyar hankali, duk wasu masu shigo da haramtattun kaya sai da yayi maganin su, lallai barin irin su Alhaji Barau a duniya babbar illa ne, dan haka nima na amince a tabbar da wannan shari'a.
Gaba d'ayansu farin ciki ya rufeso haka suka shiga yi masu godiya. Umma tace babu komai Allah yayi maku albarka, kuma yayi maku jagora akan wannan aiki da zaku fara, insha Allahu sai naga yanda k'arshen azzalumai zai kasance.
Bayan sun fito Rafeek ya kallesu yana fad'in yanzu kam hankalina ya kawanta, shiyasa dama nace kuzo nasan zuwan ku ne kad'ai zaisa su Baffa su amince dani, dan haka Ra'eez akai wannan takardar kotu, nasan kana da basira ina so kasan yanda zakayi magana.
Ra'eez yace insha Allahu. Sallama sukayi mashi suka wuce cike da farin ciki. Kai tsaye gidan su Jabeer suka wuce, acan suka ci abinci, sai da suka zauna suka huta kafin suka wuce gidan su Rumaisa.
*** ****
*Liberty Radio*
'Yallab'ai barka da zuwa. Kwamishna yace yauwa sannu Rafeek, amun afuwa aiki yamun yawa shiyasa ban samu zuwa da wuri ba hakan yasa na kira ka nace sai da dare zan samu shigowa.
Murmushi Rafeek yayi yana fad'in har na cire ran zaka zo, dama aikin dare nakeyi yau shiyasa tunda nashigo da safe naga baka zo ba kawai na fita sai kuma ga kiranka.
Gyara zama yayi yana fad'in ai bana son karya alk'awari, shiyasa nace maka sai zuwa dare nasan lokacin na samu saukin aikin. Rafeek yace barka da zuwa, ruwa ya aje masa tare da zubawa.
Amsa yayi yana fad'in nagode. Bayan ya shanye ya kalli Rafeek yana fad'in sai mu fara kada na samu wani kiran. Murmushi Rafeek yayi ya tashi yana fad'in bismilla dama kafin kazo mun shirya komai.
'Yallab'ai gidan redion mu yana maka barka da zuwa.
Murmushi Kwamishna yayi yana fad'in yauwa barka dai.
Rafeek.. Jama masu sauraron mu barkan mu da sake had'uwa a wannan gidan redion namu mai albarka, ayau muna da babban bako wanda ya kawo mana ziyara kuma zamuyi fira dashi, mai sauraro idan kana biye damu zakuji sunan bakon namu da kuma yanda firar tamu zata kasance, kubiyomu a cikin shirin namu.
To 'Yallab'ai mutane zasu so suji cikekken sunan ka da kuma irin matakin da kake ayanzu saboda kowa ya sheda ka.
E to, ni dai sunana Bello Kabir, kuma nine kwamishnan 'yan sanda a garin lagos.
'Yallab'ai nasan kafin ka kawo wannan matsayin kasha gwagwarmaya har zuwa lokacin da Allah ya kawo ka wannan matsayin, ko zaka fad'ama masu sauraron mu irin gwagwarmayar daka sha?
Kwarai kuwa nasha gwagwarmaya kafin nazo wannan matsayi, kuma dama kowa yasani kafin aji dad'i dole sai ansha wuya, kamar yanda kowa ya sani aikin 'Dansanda aiki ne na jihadi, aiki ne wanda dole sai ka bada k'arfin ka, dukiyar ka da kuma lokacin ka, duk wani d'an sanda yana fuskantar kalubale arayuwarsa, wasu ma suna rasa rayukansu akan wannan aikin, kamar yanda na bada misali da dukiya, tabbas akwai wani abun idan yazo maka dole sai kayi amfani da dukiyar ka kafin kaci nasara akanshi, haka ma lokaci, duk wani d'an sanda beda lokacin kanshi matuk'ar yasa aranshi k'asarshi yakema aiki, wani lokacin koda kana hutu zaka iya samun kira daga sama kuma dole kaje, shiyasa nace maka aikin d'an sanda aiki ne na sadaukarwa, d'an sanda beda lokacin kanshi sai lokacin al'umma domin su yake ma aiki, hakki ne ya rataya akanshi dole ne ya bama kowa tsaro, to da haka dai mukayi ta fafatawa da dad'i ba dad'i har Allah ya kawo ni wannan matsayi.
Jinjina kai Rafeek yayi yana fad'in gaskiya dole na sara maka, tabbas aikin d'an sanda babban aiki ne, yakamata mutane su k'ara jinjina ma 'yan sanda kuma su k'ara basu muhimmanci domin suna da muhimmanci arayuwar mu baki d'aya.
Kwamishna yace nagode, amma ina ganin mutane kad'an ne suke fahimtar muhimmancin mu, domin kuwa masu zagin mu sunfi yawa.
Murmushi Rafeek yayi yana fad'in tabbas nasan akwai masu zagin 'yan sanda da yawa, sai dai kuma wasu suke b'ata wasu, da yawa mutane suna ma 'yan sanda kallon masu cin hanci da rashawa, wannan bakin fentin har yanzu yaki goguwa a wajensu, kuma wasu ne suka jawo wannan abun, duk yanda kuke aiki matuk'ar ana samun masu k'arb'ar cin hanci to al'umma bazata tab'a ganin muhimmancin ku ba, shiyasa ake son arik'a kamanta gaskiya.
Kwamishna yace wannan shine babban abinda muke yaki dashi, amma har yanzu an kasa dainawa, saboda mutane suna d'aukar cin hanci shine abinda zai rik'esu.
Murmushi Rafeek yayi yana fad'in 'Yallab'ai a matsayin ka na wanda yayi shekaru yana aikin d'an sanda, nasan dole akwai wani babban kalubalen daka fuskanta wanda bazaka iya mantawa dashi ba, ko zaka fad'ama masu sauraron mu irin kalubalen daka fuskanta?
Kwarai kuwa akwai kalubale da yawa dana fuskanta, kowa yasan idan kana irin aikin mu akwai kalubale sosai akan mu, kuma nasha wahala sosai, amma juriya da jajircewa irin tawa yasa na kawo wannan matsayin.
Jinjina kai Rafeek yayi yana fad'in duk da lokaci ya fara hararar mu amma zanso ka fad'ama masu sauraron mu a shekarun baya lokacin kana aiki a k'aramin ma'aikaci wane case ne yafi baka wahala kuma ya baka tsoro.
E to, gaskiya nayi cases da yawa wad'an da bazan iya tunawa da wasu ba, amma ina ganin akwai wani case da na tab'ayi wanda yayi matuk'ar bani wahala da tsoro, idan ban manta ba yau kusan shekaru goma kenan, case ne wanda yake a cukurkud'e hakan yasa nasha wahala kafin na kammala lashi, zan iya cewa a wannan case d'in bayan kammalashi har k'arin matsayi na samu.
To 'Yallab'ai tambayata ta k'arshe a wannan shirin ko zaka fad'a mana dalilin zuwanka wannan matakin?
Gyara zama yayi kafin ya d'auki ruwa yasha yana gyara glass d'in idonshi. Kofin ya aje yana fad'in E to, gaskiya wannan matsayi dana zo zan iya cewa dalilin taimako ne yasa nazoshi, nasan kuma mutanan da suka taimaka mani nazo wannan matsayin har yanzu suna alfahari dani, bazan iya fad'arsu ba domin ba'a son ka fad'i wanda yayi maka alkhairi tunda dan Allah yayi, amma gaskiya har in mutu bazan iya mantawa dasu ba.
Murmushi Rafeek yayi yana fad'in 'Yallab'ai kayi mana halin ku na 'yan sanda, domin baka fito fili ka fad'a mana silar zuwanka wannan matsayin ba.
Murmushi Kwamishna yayi yana fad'in wannan kuma sirri ne. Dariya sukasa gaba d'aya. Rafeek yace daga k'arshe wata shawara zaka bama sauran 'yan sanda.
E to inaso nayi amfani da wannan damar na k'ara bama sauran yan sanda shawara akan surike gaskiya, dan duk wanda ya rike gaskiya baya tab'ewa, kuma su sani wannan aikin da sukeyi a ciki zasu nemi duniyarsu da lahirar su, Allah yasa mudace amin.
Juyowa Rafeek yayi yana fad'in to masu sauraron mu anan muka kawo k'arshen wannan shiri na fira da mukayi da Kwamishnan 'Yan sanda, sai muce mungode Allah yasa aje gida lafiya.
Kwamishna yace madallah nima nagode, masu saurare ina maku fatan Alkhairi.
****
Bayan da Rafeek ya koma gida duk da dare yayi sai da ya tace shirin da ya gabatar ya adanashi dan yasan zeyi masa amfani kafin ya kwanta.
**** ****
Alhaji ya jikin Alhaji Marusan? Jiki da sauki za'ace, amma fa yana can yana jin jiki. Momy tace bawan Allah, gaskiya asara bata da dad'i dole yashiga wannan halin, amma ai zaku taimaka masa da wani abun ko zai rage asara ko? Murmushi yayi yana fad'in Hajiya Binta kenan, baki san waye Alhaji Marusa ba, shine fa silar arzikin mu, taya kike tunanin dukiyarsa zata girgiza dan kawai yayi wannan 'yar asarar, kawai shegen son kud'i gareshi shiyasa yashiga wannan halin, amma babu abinda zamu taimaka masa dashi sai kulawa.
Jinjina kai tayi tana fad'in to Allah ya kyauta ya kuma tsayar akanshi. Yace amin. Kallonta yayi yana fad'in wai Ra'eez yana zuwa gidan nan kuwa? Girgiza kai tayi tana fad'in rabonsa da gidan nan tunda yazo sukayi sallama da zamuje Dubai, amma tace aiki ne yayi masa yawa shiyasa.
Murmushi yayi yana fad'in wallahi na kosa naga Raheena a gidan miji nima ko na samu jika. Momy tace lokacin zai zo, ai anyi mewuyar tunda ta samu mijin aure, Allah dai ya bashi ikon kammala wannan aikin lafiya. Alhaji Barau yace amin ya Allah. 🤣
**** ****
Wajen k'arfe goma na safe Ra'eez ya kwankwasa k'ofar ofis d'in Alhaji Barau dan yaga lokacin da yazo, amsa mashi yayi tare da bashi izini hakan yasa ya tura k'ofar bakinsa d'auke da sallama.
Amsawa yayi yana fad'in wai Ra'eez kaine shine ka tsaya kwankwasawa? Gaisheshi yayi yana fad'in wallahi kuwa. Kujera ya nuna masa yana tambayarsa k'arfin jiki.
Ra'eez yace jiki yayi sauki babu abinda yake damuna yanzu. Alhaji Barau yace nima asibiti na biya shiyasa ban shigo da wuri ba, abokina Alhaji Marusa ne beda lafiya wata asara ce ta sameshi tunda yaji hankalinsa ya tashi ya zube shikenan sai ya samu shanyewar b'arin jiki.
A zabure Ra'eez ya kalleshi yana fad'in Alhaji Marusan? Ido ya tsura mashi kafin ya furta kasanshi ne? Duk'ar da kai Ra'eez yayi yana fad'in a wajenka nasanshi shiyasa naji tausayinsa.
Murmushi ya saki yana fad'in ai da sauki tunda likita yace jininsa ya sauka saboda har yanzu basu bari ya farka ba, sunfi so sai ya samu hutu zuciyarsa ta natsu sannan, a wajenshi ma na d'an jima saboda babu kowa a gunshi, kasan yaran zamani, akwai babban d'anshi amma saboda be damu dashi ba ko kuma ince shi Alhajin be jawosu ajikinshi suka saba ba shiyasa basu damu dashi ba, ga matarsa taje Dubai sai gobe zata dawo.
Ra'eez yace Allah ya kyauta. Alhaji Barau yace amin. Kallonshi yayi yana fad'in kamar akwai magana a bakin ka ko? Jinjina kai Ra'eez yayi yana fad'in dama jiya bayan mun tashi daga aiki wani yazo ya shigar da k'ara, to case d'in kisa ne, kuma nine suka d'auka amatsayin wanda zai tsaya masu, shine nazo inji ko an kawo maka takardar?
Gyara zama Alhaji Barau yayi yana fad'in yanzu na shigo gaskiya ban iske takardar komai ba, kila dai ko zuwa anjima, amma case d'in waye? Ra'eez yace e to, gaskiya tsohon case ne, dan abun ya dad'e za'ayi kusan shekaru sha biyu da faruwar abun, to alokacin basu da shedar da zasu gabatar ma kotu shiyasa sukayi hak'uri, amma ayanzu sun samu duk wata sheda shiyasa suke so ayi shari'ar.
Tsaki Alhaji Barau yayi yana fad'in kaji wani shirme, ko sababbin cases nawa muke dasu duk basu ishemu ba sai an koma shekarun baya an d'auko mana wata tsohuwar shari'a saboda kawai an maida kotu wajen wasan yara, yanzu haka ko anyi shari'ar bance shedarsu zata wadatar ba, saboda na tabbata da wuya a samu wanda yayi kisan araye, idan ko an sameshi to wasu shedun basa nan, gaskiya banji dad'i daka amshi wannan case d'in ba, kawai ka turasu k'aramar kotu.
Gyara zama Ra'eez yayi yana fad'in Alhaji a taimaka masu, kasan kowa yana alfahari da wannan kotun, ba kowa bane kuma yake jawo mata farin jini sai kai, yau idan babu kai a wajennan nasan ba kowa ne zaiso ya kawo shari'arsa nan ba, domin kaine hasken da yake haske kotun, duk wasu mutane da suke zarya nan saboda kai suke zuwa, idan sukaji kayi fatali da case d'insu zaka sare masu sa ran da suke dashi, domin idan basu samu adalci a wajen ka ba sun san babu inda zasuje a amshe su.
Murmushi Alhaji Barau yayi yana gyara zaman glass d'inshi yace wannan haka yake, nagode daka tunatar dani, shiyasa nake jin dad'in kasancewar ka akusa dani, domin wani lokacin nakan so na kwafsa amma sai ka maidoni hanya, gaskiya Ra'eez kai d'in na daban ne, shikenan kashirya tsaya masu zuwa litinin za'a fara shari'ar, kuma insha Allahu zan sama masu adalci kodan ta silarka.
Turo k'ofar ofis d'in akayi had'e da sallama, amsawa sukayi kafin ya shigo. Alhaji Barau yace Malan Jamilu yau ka makara ko? Wanda aka kira da Malan Jamilu yace wallahi iyalina ne basuji dad'i ba sai da mukaje asibiti amma da sauki.
Alhaji Barau yace Allah ya basu lafiya, ai bazaka zauna ba dama yau juma'a sa hannu kawai ka tafi. Mik'a masa takarda yayi yana fad'in jiya aka kawota lokacin ka tafi shiyasa na ajeta, takardar... Katseshi yayi yana fad'in Ra'eez yayi mani bayani, amsa yayi yana fad'in zaka iya tafiya.
Godiya yayi mashi Ra'eez ya gaishe shi yana masa ya mai jiki. Kud'i Alhaji Barau ya bashi yana fad'in ga wannan ka siya mata magani. Godiya yayi mashi ya fita yana mamakin yau Alhaji Barau yayi masa kyauta. (Niko nace agaban suriki ai dole yayi gwaninta😉)
Tashi Ra'eez yayi yana fad'in zan koma nagode Alhaji. Murmushi yayi yana fad'in babu damuwa Allah ya bada sa'a, idan kana da wata matsala kazo ka fad'a mani, domin bazan bari ka fad'i ba. Godiya yayi masa ya fice.
****
Dariya sosai Jabeer yayi jin yanda Ra'eez yayi da Alhaji Barau. Tsaki Ra'eez yayi yana fad'in wallahi wannan mutumin beda kunya, amma ka kyaleshi na kusa koya masa yanda akejin kunya.
Jabeer yace gashi kuwa hada maka addu'ar neman sa'a besan akanshi zata k'are ba. Ra'eez yace ai d'azu munyi waya da Yaya yace ayau zai sanar da shari'ar dan yana so tayi mutane.
Jabeer yace kasan kuwa duk wanda yaji za'ayi shari'ar shekaru da yawa dole yazo yaji yanda zata kaya, ni kaina ina so litinin tayi kawai naji yanda za'a fafata.
Ra'eez yace wallahi ni kaina nakosa akammala komai kona samu natsuwa, gaba d'aya bani da lokacin kaina, Pretty hak'uri kawai take dani damma muna d'an waya.
Jabeer yace ai komai ya kusa zuwa k'arshe da izinin Allah. Waya Ra'eez ya d'auka yana fad'in bara naji muryarta ko naji kwarin yin aikin dan gaskiya yau dole na tsaya fira.
Murmushi Jabeer yayi ya mik'e yana fad'in nayi nan kada naji kayan haushi. Ra'eez yace idan kaji haushi gobe na ganka da budurwa. Jabeer yace kai dai kasa ido Allah ya kusa kawota.
Maganar da yaji yasa ya maida hankalinsa ga wayar. Jabeer kuwa ficewa yayi yana masu dariya. Bayan ta gaishe shi yace Prettyna ki k'ara hakuri kinji, ni kaina ina kewar ki da yawa.
Murmushi tayi tana fad'in haba bakomai, ai wannan aikin da kakeyi mu kake mawa, dan haka ina nan ina jiranka kuma ina maka addu'a nasan zakayi nasara. Ra'eez yace nagode sosai ina so yau kimun kwalliya kamar zakije party dan yau fira zamuyi.
Murmushi tayi tace shikenan yanda kace, sai kazo. Ra'eez yace me zan taho maki dashi? Duk abinda yayi maka ta fad'a cike da farin ciki dan tayi kewarsa, kwana biyu koya zo baya dad'ewa shima da Mama kawai suke gaisawa.
Ra'eez yace shikenan sai nazo ki gaishe da Abdallah da Mama. Zasuji ta fad'a. Kiss yayi mata yana fad'in miss u, da sauri ta kashe wayar. Dariya yayi yana fad'in zan kamaki ne.
**** ***
Tsaki Fawwaz yaja a karo na ba adadi, zaune yake a cikin lambun gidansu, yau kwana biyu kenan ya kasa samun nutsuwa, tunda Adnan yayi masa maganar Farouk shikenan hankalinsa yaki kwanciya, duk yanda yaso ya cire abun aranshi ya kasa, gashi baya so ya fad'ama Dad d'insa hankalinshi ya tashi, gara kawai yayi shiru ya magance matsalar da kanshi.
Kashe sigarin daya gama sha yayi yana kurb'ar giyar da ya zuba a kofi, a 'yan kwanakin nan ko wajen abokansa baya zuwa saboda damuwa, shaye-shayenshi ya k'aru ko zai samu sauki amma abanza.
Waya ya d'auka ya kira babban abokinsa, yana d'agawa yace *Milo* mu had'u a gidan shakatawa ta akwai maganar da zamuyi, amma kazo kai d'aya. Shikenan sai kazo
Ur's.
Nabeelert Lady🖋
[3/10, 8:40 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud'i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k'asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub'e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.*
4⃣0⃣
What? Dude kasan abinda kake fad'a kuwa? Kai Fawwaz ya jinjina yana zuk'ar sigari. Gyara zama Milo yayi yana fad'in lallai kai babba ne Dude, haba shiyasa baka da tsoro ashe tuni tsoron ya bar zuciyar ka, ai duk mutumin da zai iya aikata kisan kai bana tunanin yana da tsoro a ranshi, ka ganni nan ko fad'a bana so saboda nasan yanda halin maza yake akwai bak'ar zuciya, da an fara fad'a yanzu zakaji an yanki wani ko an fitar masa da jini, wannan dalilin ne yasa bana son zama a club.
Tsaki Fawwaz yayi yana fad'in kada ka bani kunya mana Milo, ina tunanin na kawo kuka gidan mutuwa sai kazo mani da wannan banzar maganar.
Gaskiya na fad'a maka ai, Milo ya fad'a yana kunna sigari. Ajiyar zuciya Fawwaz yayi yana fad'in wallahi tsoro nakeji kada Adnan ya tona abinda ya faru.
Murmushi Milo yayi yana fad'in haba kada ka bani kunya, kada kamanta Dadyn ka shine tsohon Alkalin babbar kotu, duk da ya aje aiki har yanzu yana fad'a kuma anaji, sannan kace abun ya faru tun kuna secondary banga dalilin da zaisa ka damu kan ka ba, shima Adnan d'in cewa yayi kawai ya tuna maka ne bawai zai tona asiri yake nufi ba, kaga idan har zaka saka damuwa aranka ina tabbatar maka kaine zaka tona kan ka, kawai ka share kacigaba da chilling.
Dariya Fawwaz yasa yana fad'in shiyasa nake sonka abokina, amma wallahi kwana biyu bana baccin kirki. Hannu Milo yasa aljihu yana fad'in ina zuwa, ai nine mai bada maganin bacci, ina tabbatar maka daga yau ka dena rashin bacci.
Mik'a masa yayi yana fad'in kaga wannan kwayar ita ake kira da 'yar hutu, nima wani abokina ne ya bani ita d'an gidan Alhaji Marusa.
Fawwaz yace ba dai Marwan ba? Shifa, ai kasan Gayen yasan ta kan kayan hutu, shiyasa fa kaga muna d'asawa dashi dan baya harka da kayan Nija dan basu da inganci, jiya mukayi waya dashi yake fad'a mani ranar monday zai koma india kasan baya son zama a Nija.
Amsa Fawwaz yayi yana fad'in ai gaskiya Marwan babba ne, shiyasa nima banso su Dad sukace na dawo ba, acan hankalin mu kwance sai abinda mutum yaga damaryi.
Milo yace tashi muje Beb d'ina tana jirana d'azu tazo mani week end. Fawwaz yace ai kai kaji dad'inka tunda an ware maka gidanka, ni kuwa basa bari na kwana a wani waje duk da an mallaka mani gida.
Tashi Milo yayi yana fad'in ba sai karik'a wuni anan ba wayasan abinda kakeyi, iyaka sai lokacin bacci yayi ka koma. Fawwaz yace ka kawo shawara haka za'ayi, nagode abokina.
**** ****
Wai Marwan ba magana nake maka ba. Baki ya turo yana fad'in wai meyasa kike son takura mani Mom, ko dan kinga ina zuwa ganin ku, shi *Khalil* da baya zuwa ai bakiyi masa haka.
Hannunshi ta kamo tana fad'in yi hakuri ba takura maka nakeyi ba, naji kace mun Alhaji beda lafiya kuma kana maganar zaka tafi bayan kasan yanzu ne Alhaji yake da buk'atar ka tunda kaga halin da yake ciki, ni dai mace ce bazan iya jinyarsa ba, gashi ba wani d'an uwa gareshi ba da an kirashi, dole kaine babba kai zaka tsaya ka kula dashi.
Saurin kallonta yayi yana fad'in wallahi Mom bazai yuwu ba, shikenan abubuwan da nake dasu acan sai na hakura dasu, Dad fa yana da kud'i, idan kana da kud'i babu abinda zai gagareka, shi kanshi likitan yace zasu kula dashi tunda akwai kud'inshi da yawa a account d'insu, dan haka ni bazan iya jinya ba.
Kai ta jinjina tana fad'in shikenan dena fushin, tunda akwai kud'in za'a samu masu kula dashi, nima ba zama zanje inyi ba saboda kasuwancina, amma zan rik'a lek'awa, kaga yanzu asara ta sameshi idan ban tsaya na kula da tawa dukiyar ba sai nima nabi sahunsa dan shi tsufa ya taho masa ga mutuwar b'arin jiki ai kaga beda sauran amfanuwa matuk'ar be warke ba, yanzu haka kayan dana saro suna hanya jiransu ma nakeyi kafin na lek'a asibitin tunda kace allurar bacci sukayi masa.
Tashi yayi yana fad'in zan fita ni. Kallonshi tayi tana fad'in amma Marwan akwatin da naga ka d'auko a d'akin Alhaji na meye? Fuska ya d'aure yana fad'in amma ai ina da gadonshi ko? Kai ta d'aga, kauda kai yayi yana fad'in amfani zanyi dasu to.
Be jira amsarta ba yayi waje. Murmushi tayi tana fad'in Marwan manya, da Alhajin yana nan zai baka wad'an da sukafi haka ma. Wayarta ce tayi k'ara hakan yasa tayi saurin d'auka ganin wanda ya kira.
A zabure ta mik'e tana fad'in ban gane ba, ka bincinka jirgin da akace ya nutse kuwa? Shiru tayi tana sauraronshi. Salati tasa hawaye suka fara wanke mata fuska, hakuri ya bata ya kashe wayar.
Zaman 'yan bori tayi tana kwara ihu, da sauri masu aikin gidan suka fito jin Hajiya na ihu. Kuka suka isketa tanayi kamar k'aramar yarinya, nan suka shiga bata hakuri amma kamar izata sukeyi.
**** ****
Ido kawai Alhaji Marusa ya tsura ma Matarsa da take zaune a gefenshi tana share hawaye, Alhaji Barau da Mr. Kallah sai hakuri suke bata jin asarar data sameta.
Alhaji Barau yace Hajiya hakuri zakiyi, kinga yanayin da yake ciki be kamata arik'a tada masa hankali ba, addu'a zakiyi Allah ya maido maki da wasu kud'in. Goge idonta tayi tana fad'in dole nayi kuka, wannan bala'i kamar wad'anda aka sama hannu, so akeyi asirin mu ya tonu.
Mr. Kallah yace Hajiya sai hakuri, yanzu Alhaji kulawa yake buk'ata dole ki daure ki kula dashi hakan zaisa ya samu k'arfin jikinshi tunda likita yace abun beyi yawa ba za'a iya shawo kan matsalar dan yanzu haka zasu fara mashi gashi kinga idan kina kwantar masa da hankali zaifi saurin warkewa.
Alhaji Barau yace to Allah ya kyauta, Mr. Kallah muje ko. Tashi sukayi suna fad'in Alhaji Allah ya k'ara sauki. Kai ya jinjina masu yana binsu da kallo har suka fita.
Zaune suke a mota suna kwasar dariya. Mr. Kallah yace gaskiya na tausaya masu, ga Hajiya itama asara ta sameta, gashi a kwance ko magana baya iyawa, gaskiya da munsan haka zata faru dashi da bamu aikata masa haka ba.
Alhaji Barau yace bamuda laifi, son kud'inshi ne ya jawo masa haka, ita kuma Hajiya kila zakkace aka fitar mata, itama son kud'in gareta ai, kasan kuwa yanda take cin kud'in Alhaji ita da 'Ya'Yanta, ga satar da suke masa, ai alhakinsa ne ya kamata.
Mr. Kallah yace duk da haka ya kamata mu tausaya mashi a fitar dashi waje sai kaga cikin kwana ukku ya tashi amma zafin zeyi masa yawa, gaskiya ko bazaka taimaka ba ni zansa afitar dashi. Ganin yanda Mr. Kallah ya dage yasa Alhaji Barau ya amince.
Fita sukayi zuwa ofis d'in likita, anan suka masa bayani, nan take ya kira wani abokinsa a America, babu b'ata lokaci suka gama komai, inda za'a tafi dashi gobe saboda litinin a fara masa magani.
Sallama sukayi masa suka wuce domin nema masa Visa, dole da Mr. Kallah zasu tafi tunda Marwan yace bazeyi jinya ba. Kasancewarsu manya nan take suka samu jirgin safe na gobe, haka suka rabu.
**** ****
Washe gari tunda safe jirginsu ya d'aga, Hajiya taso ta bisu dan bata jin dad'in zaman gidan, wayar data samu daga Yaronta zai zo yasa ta fasa binsu asalima taji dad'in tafiyar tunda zata sake wannan karon a gida zasuyi sha'aninsu ba sai taje gidanta da suka saba had'uwa ba tunda Marwan ma yau ya tafi.
**** ***
Duk wani shirin shiga kotu sun kammalashi, duk inda kaje zakaji ana maganar shari'ar da za'ayi gobe, mutane da yawa suna son suje suji wace irin shari'ace haka bayan shekaru masu yawa kuma za'a maidota baya.
Wajen k'arfe sha biyu su Alhaji Mansur da Matarsa suka sauka lagos, Ra'eez da Jabeer suka d'aukosu, kai tsaye gidan Mama suka kaisu inda Alhaji Mansur zai zauna a gidan Ra'eez.
Sosai Mama tayi farin ciki da zuwan su, Rumaisa ta kawo masu abincin da zob'o. Zama sukayi aka gama gaisawa kafin suka ci abinci, haka suka cigaba da tattaunawa.
Da yamma Alhaji Mansur da su Ra'eez suka nufi wajen Kawu tare dasu Jabeer. Sosai Kawu yayi farin cikin ganinsu. Haka suka zauna suna ta fira. Alhaji Mansur yace sunyi waya da Abubakar yace da zaran za'a fara gabatar da shari'ar su Malan Sani zai zo.
Murmushi Kawu yayi yana fad'in wallahi jinake kamar mafarki, bani da abun roko daya wuce Allah ya nuna mani ranar da zan fita daga wajen nan, ranar da zanga lokacin da za'a tona asirin munafukai.
Ra'eez yace ai Alhaji Marusa da Mr. Kallah suna America. Alhaji Mansur yace akan ciwon Alhaji Marusan ne? Ra'eez yace wallahi kuwa, nima d'azu Alhaji Barau yake fad'a mani.
Alhaji Mansur yace ina rokon Allah ya bashi lafiya domin ya amshi hukuncinsa, bakomai nasan bazasu dad'e ba tunda kace jikin da sauki, kafin a kammala wannan shari'ar zasu dawo da izinin Allah.
Wayar Ra'eez ce tayi k'ara, yana dubawa yaga Dr. Saddek ne, d'agawa yayi, bayan sun gaisa Dr,
yace masa yazo yana son ganinshi. Ra'eez yace gani nan zuwa.
Kashe wayar yayi yana fad'a masu abinda Dr, yace. Alhaji Mansur yace ai sai kutashi muje kila wani abunne. Kawu yace aduba mani Hajiyar.
**** ***
Zaune suke a ofis d'in Dr. Saddek, bayan sun gama gaisawa Dr, yace dama akan maganar shari'ar da naji za'a gabatar gobe ne, tunda har shari'ar zata kai zuwa gano abinda ya shafi abinda yayi silar jefa Hajiya wannan halin ina ganin zaku tafi da ita, ina so na gwada wani abu ko Allah zaisa a dace, shiyasa nace bara nakira ka.
Alhaji Mansur yace likita kana ganin babu matsala atafi da ita? Bana so fa Alhaji Barau ya gano wani abu, sannan kada aje garin gyara ayi b'arna, kana gani kwanaki daga fad'in sunanshi yanda tayi, inaga ace ta ganshi kuma ta san shine Brr. Barau d'in.
Likita yace Alhaji jikina yana bani wani abu shiyasa kaji nace aje da ita, kasanfa da yawa irin wannan haukan yana warkewa ne ta silar faruwar wani abu, musamman idan mutum yaga abinda ya tsaya masa arai, ina rokon ka amince aje da ita, idan Allah besa zata warke ba shikenan sai adawo da ita.
Hawaye ne suka zubo ma Ra'eez, kallon likitan yayi yana fad'in koda ace Ummu bazata warke ba ana kammala wannan shari'ar zan tafi da ita, tunda dai haukarta bata duka bace ni zan cigaba da zama da ita ahaka.
Dafashi Alhaji Mansur yayi yana fad'in insha Allahu Ummunka zata warke, bakomai likita zamuyi yanda kace, amma akwai maganin da zaka bata ko? Kai likita ya jinjina yana fad'in zan bata magani, kuma nima zan halarci wajen tare da wasu daga cikin ma'aikatan mu, kuma zamu kula babu abinda zai faru.
Godiya sukayi masa. Sallama sukayi mashi akan gobe zasu taho da ita, sai dai bazasu bari kowa ya gane daga asibiti suka fito ba. Alhaji Mansur yace shikenan mungode, akwai Maman Rumaisa da Hajiya sai su kula da ita goben.
**** ****
Zaune suke su biyar sai Alhaji Mansur na shida a gidan Ra'eez. Rafeek ne ya kalli Adnan yana fad'in ina fatan ka shirya ma shiga kotu gobe? Jinjina kai Adnan yayi yana fad'in sosai kuwa, domin a wannan karon bazan bari a sake aikata zalunci ba.
Rafeek yace Nabeel fa? Nabeel yace ashirye nake Yaya, domin nashirya duk yanda zan shawo kan Abbana, dalilin da yasa banyi masa maganar ba bana so yaje masu Alhaji Barau da maganar shiyasa nace sai yau da dare zanje na rokesa akan ya fad'i gaskiya.
Ra'eez yace lallai da ka kwafsa, ai gara da baka fad'a masa ba, kabarshi idan yaje zaiji komai da kunnansa, abinda nakeso kawai kayi kok'arin sashi yazo kotun domin nasan za'a buk'aci ganinsa.
Nabeel yace shikenan dana koma gida zansan yanda zan fad'a masa. Rafeek yace insha Allahu babu abinda zai gagara, domin kowa yasan yanda komai ya kasance, shikuwa Fawwaz ku barshi Alkali da kanshi zai bada umarnin a kawoshi.
Alhaji Mansur yace ni narasa ma bakin magana, agaskiya nayi farin ciki da wannan had'in kan naku, domin taimako ne zakuyi kuma Allah ne kad'ai zai iya biyanku, dan haka idan kowa ya samu dama kafin ya kwanta yayi nafila ta neman nasara, sai kuga Allah ya taimake mu, Allah yayi mana jagora. Gaba d'aya suka amsa da amin.
**** ****
Abbah ka kalli labaran jiya na Liberty radio kuwa? Abbah yace labaran da yawa ai, wanne a ciki? Gyara zama Nabeel yayi yana fad'in aikuwa agari naji ana ta maganar shari'ar da akace za'ayi gobe a babbar kotu kuma tsohuwar shari'a ce, naji mutane suna fad'in zasuje suyi kallo.
Abbah yace wai wace irin shari'ace haka bayan shekaru kuma za'a maidota? Nabeel yace gaskiya ban sani ba, amma koma menene nasan babbar shari'arce tunda gashi an maido ta.
Abbah yace aikuwa nima zanje kodan naji wace shari'ace haka, kasan ina son zuwa saurarar shari'a. Murmushi Nabeel yayi yana fad'in nima nace zanje ai. Abbah yace dama ku ai ba'a barin ku abaya. Murmushi Nabeel yayi yana fad'in ai bana son naga anyi zalunci Abbah. Abbah yace to Allah ya bama masu gaskiya sa'a. Nabeel yace amin.
***** *****
*Safiyar litinin a Kotu*
Cike babbar kotu take da mutane, yayin da su Mama da Maman Labiba, Rumaisa sai Ummun Ra'eez da matar da take kula da ita suke zaune a cikin kotun, saboda dawuri sukazo dan kada su rasa wajen zama, sannan basa son sai an shiga su shiga gudun kada Ummu tayi wani abun, duk da jikinta amace yake tun maganin data sha.
A hankali mutane suka shige ciki kowa ya zauna ana jiran zuwan Alkali. Shigowar Alkali yasa kowa ya mik'e, bayan ya zauna kowa ya zauna.
Shiru kotun tayi ana jiran a fara. Bayan ya kammala abinda yake Magatakarda ya tashi domin ya karanto shari'ar da za'a gabatar.
*A yau litinin biyar ga watan december shekera ta dubu biyu da shatara wannan kotu zata saurari k'arar da Iyalan Alhaji Sambo Jarmai suka shigar akan kissan gillan da akayima 'Dansu a shekarar dubu biyu da takwas, wanda aka tsinci gawarsa a ranar juma'a da misalin k'arfe tara da rabi na dare, suna rokon wannan kotu mai albarka data kwato masu hakkinsu.*
Mika takardar yayi ya koma ya zauna. Gyara zama Alkali yayi yana fad'in ina lauyoyin da zasu fabatar da shari'ar? Tashi Ra'eez yayi yana fad'in ya mai shari'a nine lauyen da zai k'are wad'anda suke k'ara.
Jinjina kai Alkali yayi yana fad'in zaka iya farawa.
Fitowa Ra'eez yayi yana fad'in Iyalan Alhaji Sambo Jarmai sun shigar da wannan k'ara ne saboda suna da yakinin a wannan kotun ne kad'ai za'a iya kwato masu hakkin su, duk da wannan case ya dad'e amma dalilin rashin kwakkwarar sheda yasa basu shigar da k'ara ba, haka zalika basu shigar da k'ara a ofishin 'yan sanda ba, sai dai kuma alokacin da abun ya faru akwai shedar sa hannu ta 'yansanda a wancan lokacin, wannan shine rahoton da muka samu a ofishin 'yan sandan da suka kula dashi a wancan lokacin.
Amsar takardar Magatakarda yayi ya mik'a ma Alkali. Ra'eez yace a shekarun baya an tsinci gawar Naseer Sambo Jarmai a wajen gari da misalin k'arfe tara da rabi na dare, kuma 'yan sanda ne suka d'auki gawarshi suka mik'ata asibiti, a lokacin inspector Musa shine wanda ya kula da wannan gawa harya d'auketa zuwa asibiti inda ya mik'a case d'in ga abokin aikinsa Inspector Bello Kabir wato Kwamishnan 'yan sanda na yanzu, inaso kotu ta bani dama na kira Alhaji Musa domin muji bayani daga bakinsa. Kotu tana buk'atar Alhaji Musa.
Ra'eez.... Kotu zata so taji sunanka da kuma aikin ka.
Sunana Alhaji Musa Adam, nayi aikin d'ansanda a shekarun baya, amma ayanzu na aje aiki tun shekaru biyar da suka wuce, ayanzu haka ina kasuwanci ne.
Ra'eez... Alhaji Musa ko zaka iya tuna abinda ya faru a shekarar dubu biyu da takwas akan gawar da kuka tsinta ta Naseer Sambo Jarmai? Muna so kayima kotu cikekken bayani.
Alhaji Musa.... Kwarai kuwa zan iya tuna wannan case d'in, domin bashi kad'ai muka samu a wannan dare ba, kuma wannan lokacin yana d'aya daga cikin abinda bazan iya mantawa ba, domin a wannan shekarar a wannan kotun anyi zazzafar shari'a, wanda d'aya daga cikin gawar da muka tsinta had'e data Naseer ce akayi shari'a akanta, sai dai ita ta Naseer Iyayenshi basu buk'aci yin shari'a ba, saboda babu wata sheda da muka samu a lokacin da muka tsinceshi.
A wannan dare na juma'a mun samu waya cewar an samu gawar tsohon shugaban kwastam wato Alhaji Maiwada, bayan da 'Yallab'ai Bello ya tura mu wajen, da muka d'auko gawarsa mun taho muka sake samun labarin gawar da wasu suka gani, haka muka wuce muka d'auko gawar Naseer, kai tsaye asibiti muka nufa dasu, daga can kuma case d'in ya koma hannun Ogana wato 'Yallab'ai Bello Kabir, iya abinda na sani kenan akan gawar Naseer, sai rahoton dana baka wanda nine na rubutashi da hannuna.
Ra'eez... Mungode Alhaji Musa zaka iya tafiya. Ya mai shari'a wannan shine d'an sandan daya d'auki gawar Naseer, ga rahoton mutuwarsa nan, sai dai a binciken da mukayi mungano Naseer yana aji shidda ne a makarantar Kings college a wancan lokacin, kafin mutuwarsa akwai abinda ya faru a makarantar su wanda akan idonshi abun ya faru, yayi kok'arin ya tabbatar da gaskiya sai dai silar wannan abun ya jawo mashi mutuwar wulakanci.
A binciken da mukayi akwai abokinshi *Fawwaz Muhammad Sanda* wanda shima d'alibi ne a makarantarsu, bincike ya nuna mana akwai rigima da akayi tsakanin Fawwaz da d'an ajinsu mai suna Farouk, wanda Adnan da Sufwan duk sun san da wannan rigima domin su ukku suke tare abokai ne sosai, kuma bincike ya nuna cewar bayan rigimar Farouk da Fawwaz a ranar aka tsinci gawar Farouk a wajen gari, komenene ya faru alokacin Fawwaz ne zai fad'a mana saboda yasan Naseer, ina neman alfarmar wannan kotu data bada umarnin a kawo Fawwaz Muhammad Sanda domin muji komai daga bakinsa. Nagode.
Tashin hankali wanda ba'a samasa rana. Gaba d'aya zufa ce ta lullube Alkali da Abban Nabeel, da wani zaije kusa da Alhaji Barau zaiji yanda zuciyarsa take bugawa, jarumta ya tattaro ya kalli Ra'eez, cikin k'arfin hali yace an d'age wannan shari'ar zuwa gobe, kafin nan kotu tana umartar akawo mata Fawwaz Muhammad Sanda zuwa gobe. Kotttt!!!
Gaba d'aya kotun ta d'auki hayaniya, Abban Nabeel kuwa kasa tashi yayi daga inda yake, gaba d'aya hankalinsa ya tashi, abinda ya guda shekarun baya gashi zai faru, Allah ya sani tun bayan daya aikata wannan laifin yayi nadama, bayan da Nabeel yazo masa da maganar kuma be sake samun kwanciyar hankali ba, haka kawai yake jin kamar wani abu zai faru ashe kuwa lokacin jin kunyarsu ne yazo.
Cira ido kawai Ummu takeyi saboda gaba d'aya hayaniyar tayi mata yawa, jin kanta tayi yana sara mata. Wasu mutane da suke bayansu taji suna fad'in.... Ai wannan shari'ar da akayi ta shugaban kwastam Alhaji Maiwada a wancan lokacin Brr. Barau ne yayita, gashi kuma yanzu shine Alkali, amma kuma Fawwaz da ake magana ai d'an gidan tsohon Alkali ne, lallai wannan shari'ar akwai lauje cikin nad'i, ga mutuwar Farouk ana magana kuma duk 'yan makaranta d'aya ne, tabbas za'ayi tone-tone a yanda na fuskanci wannan shari'ar babban al'mari ne.
Zumbur sukaga Ummu ta mik'e, saurin tashi Mama tayi tana kok'arin kamota amma ina tuni Ummu ta zube k'asa yayin da kanta ya bugu da kujera.
Da sauri ma'aikatan da sukazo tare sukayo kanta, hankali tashe Ra'eez ya nufo wajenta, sai dai kafin ya iso Alhaji Mansur yayi saurin rik'eshi yana girgiza mashi kai, dole ya tsaya. Jabeer ne ya jashi sukayi waje.
Haka hankalin mutane yayo kanta, sai dai kafin a taru tuni anyi waje da ita ansata mota sun wuce. Da sauri su Alhaji Mansur sukabi bayansu shida Rafeek.