Allah ya sauke su lafia, du kuwa da irin yanda Agaishat ta jigata domin har amai ta yi a lokacin fa jirgi zai tashi da irin yar jijigar nan da yake kafin ya mike da tafia, sannan a lokacin saukarsa wannan kasan da abubuwan ciki ke yi suka saka shima ta yi tamakar ta sume,
Mu.azam na kule da ita , tausayinta yake ji, khadija ce ke kiran yan matan nan na jirgi da ta ga zata shiga wani yannayi , su ke zuwa su bata kulawa har jirgin ya sauka,
Agaishat dai na mamakin irin halin shariyar da Mu.azam ke nuna mata idan suna tare da Khadija, tun bata gane komai ba har ta gane sai dai bata nuna ko a fuska ba,
Ko wajen sauka shi ne gabansu su kuwa suna biye da shi a baya inda Agaishat ta zama ta karshe
Kanta ne ta ji yana juya mata lokacin da ta ganta cikin tankamemen aeroport din *Paris*
A hankali ta sada kanta dan ta lura du idan ta daga kan ta ga irin tsaruwar garin ne hankalinta ke tashi,
Fitowa suka yi inda manyan motocin taxi ke laye, da yawa an yi kiransu je, daidaiku ne suka zo wajen dan radin kansu
Wajen motar suka nufa , nan Mu.azam ya juyo gannin Khadija bata biyo su ba,
Budewa Agaishat ya yi ta shiga ta zauna inda Direban ya saka akwatinta bayan motar,
Wajen Khadija ya nufa yana son sai ya karanci fuskarya aman ta ki bashi dama,
Yana zuwa hannayenta ya kama yana dubanta ya ce" ba zaki biyo mu ba?
Murmushi ta sakar masa ta girgiza kai ta ce" ku je da matarka, nima zan dauki wata taxi din, zan leko ka, ka kular min da kanka nan da kwana hudu zaka dawo asibiti ka kwana biyu bisa kulawar docters kafin a shiga aiki da kai,
Murmushi ya sakar mata ya lakace hancinta ya saki hannayenta ya juya ya nufi motar inda sai a lokacin Agaishat ta kawar da fuskarta gefen madubin motar
Satar kallonta ya yi, sai a lokacin ya ji wani nauyinta, rabonsa da ya yi wani maganar nutsuwa da ita tun da Khadija ta sauka a gidan Ayya,
Kwarai Ayya ta yi masa mutunci ta nuna komai ba komai ba ta hanyar kawar da kanta ta kuma karbi bakuwarsa duda tsanar akidar kawance tsakanin mace da namiji da ta yi kuwa, sannan koda suka tashi tafia ta yi masa gargadi nasiha kamar yanda iyayensa zasu yi masa, sai dai kuma ta nanata ya rike amanar baiwar Allah,
Gabansa ne ya ji ya fadi, amanar Agaishat ya karbo fa, amana ya karba, anya kuwa haka amana ta ce?
A hankali ya mika hannunsa na hagu ya dora saman cinyarta , wanda ke nuni da yana son kara kusancinsa da ita,
Agaishat ta juyo ta dora tsararun irannuwanta saman hannunsa, daga nan bata kai dubanta sama ba ko dan kar idannuwansu su shaku da juna, sai ta kawar da kanta ta mayar bakin titi tana kallon hanya da mamakin irin tsarin garin da irin shigar mutanen garin
Bai dauke hannunsa ba, bai kuma yi mata magana ba har suka karaso kofar wani gida
Daga kofa raga ne na karfe baki, haka ya ja jakar tana biye da shi tamkar kazar da kwai ya fashewa a ciki har ya saka cod din kofar gidan nasa suka shiga,
Fulawowi ne a gidan, ba wani tankamemen gida bane , dan madaidaici ne tsarare,
Matatakalar suka hau suka shiga ainahin falon gidan,
Plat ne, ba bene, dakuna kwaya biyu ne sai katon bayi da kicin mai girma da tsari da wajen buga game, kujeru farare kar ne a falon sai dan table fari, tv tankamemiya jikin bango sai wajen da ake kuna wuta dan dakin ya dau zafi , sai ac biyu a iya falon
Kofar ya mayar ya rufe ya saki akwatin nata nan,
A hankali ya juyo yana takowa inda take tsaye kanta na kallon kasa,
Yana isowa ya kama hannayenta yana yi kata kallon kurullah,
Jin ya jima bai yi magana ba ta dago a hankali ta sauke tsumamun idannuwanta cikin nasa,
Fuskarsa ya shagwabe ya jata zuwa saman kujera mai zaman mutun biyu ya zaunar da ita,
Kusa da ita sosai ya zauna yana so sai ta kara yi masa kallon da ta yi masa aman du yanda ya so ta kiya,
Muryarsa ya kimtsa ya ce" kin daina so naπ, me ya sa kika daina so na?
A hankali ta juyo da dubanta wajensa, kurawa fuskarsa ido ta yi, a ranta ta ayyana, ai bamu kai ga gane menene so din ba aka daura auren mu, a fili kuwa sai ta kifta idannuwanta da suka fara cika da kwallah,
Murmushi ya yi ya ce" ki yi hakuri Agaishana, kar ki yi fushi da ni, na san kina da tarin tambayoyi aman ki yi hakuri ki bar su a wajenki har sai lokacin yin su ya yi , ki sani ina son ki ba zan daina son ki ba, ina gannin girmanki ina daraja ki a rayuwana, ban aure ki dan cutarwa ba,
Wani sanyi ta fara ji a ranta , nan da nan ta ji ta fara manta shaku da rudannin da ta shiga dalilin nesanta kansa da ya yi da ita kwanakin nan, (kar ku ga laifinta, baki daya a duhu take),
Dan murmushi ta sakar masa aman batai magana ba,
Mikar da ita ya yi ya ja hannunta suka nufi daki............π
*Timiya*
Wasa wasa sai da Anna ta wuni ta kai tsakiyar dare wajen karfe biyun dare ta wani irin kwala karan da ya firgita yayanta dake zagaye da ita ta aniya amsa kira tamkar ana kiranta , fadi take" *Na.am, Na.am, Na.am?*,
Kuftaya ta shiga yi da dukan mai kokarin riketa, idannuwanta rufe suke ruf tana ihun amsa kiran da basu san mai kiranta ba,
Digarin da Sarki ya bari ya kula da lafiar Gaishata dake ta faman nakuda tare da Jakadiya har zuwa lokacin bata haihu ba gashi da ta dora masa kuka sai da aka sakata cikin kurakura aka kawota gidan Annar, haka suka wuni har gashi rabin kwana zar suna fama ne ya shigo da sauri jin hayaniya,
Fitikar kwan da ya kunna ce ya kara masu haske a dakin da ta wajensu , subahanallah shine abinda yake ambata gannin irin yanda suka kasa tareta ga kuma Gaishata sai murkashi take tana kuka gashi kusa da ita suke jakadiya sai tarewa take kar a fado mata,
Gannin ana iya fado mata a samu matsala ya saka shi saurin shiga dakin ya je suka hadu su uku suka kai Anna kasa inda Jakadiya ta shiga fadin ya taho ya taho,
Da sauri Dogari ya mike ya kama Anna da ta fara dan yi lakwas ya cicibeta su kai waje domin ya gane Gimbiyar sarkinsa zata haihu ne,
Nishin Gaishata da nishin Anna du tare ne, cikin ikon Allah Gashata ta haihu lafia ta sako yaronta har Jakadiya ta yanke cibi ta dauke uwar da ta fado ta nade a zanin Gaishata bayan ta dora mata yaron saman cikinta ta aniya kimtsata tana ta murna,
A galabaice Gaishata dake lumshe ido tana budewa na ni.imar nakuda π€£ ta kallo jakadiya, murya a disashe ta ce" Annata?
Jakadiya ta ce" Allah ya ja da zamaninki kar ki damu in sha Allah da sauki, ai dogarin nan dan gidan cheik Ne, baban almajiri ne gayacan sunai mata adu.a,
Sosai suka dukufa suna yiwa Anna du adu.o.in da suka iya inda shi kuwa dogari ya dauro Alwallah ya zo shima da ruwa a kwanon kwano ya zauna ya shiga karanto mata manyan adu.o.in karya sihiri, na rukuya kai harma da na tsari duka yana tofeta da shi kuma yana tofawa a cikin ruwan,
Mikawa Mariama ya yi ta shafa mata gaba daya jikinta suka ci gaba da adu.o.in ,
Wasa wasa sai da garin Allah ya waye domin kuwa sai da aka kirayi salar asuba Anna ta ja wata irin ajiyar zuciya ta yi wata irin mika kafin take zabura ta ce" *Ayya, Ayyana, wani abu zai rufe min ido, wani abu Ayya* (kar ku manta tubawa ke kiran Mama da Ayya, wace Ayya xce haka? Shin Anna ta dawo hayacinta?))))
Kadan ne
*☀IDAN RANA TA FITO WRITER'S ASSOπ€*
____________________________________________
*Fad'akar da al'umma tare da nishad'antar da masoya shine fatanmu*ππ€π»π
π«π«π«π« *BAK'A CE* π«π«π«π«
Na
*SAJIDA*
5️⃣0️⃣

https://www.facebook.com/Idan-rana-ta-fito-writers-association-114558343535568/?referrer=whatsapp
*☀IDAN RANA TA FITO WRITER'S ASSOπ€* ____________________________________________
*Fad'akar da al'umma tare da nishad'antar da masoya shine fatanmu*ππ€π»π
Na
*SAJIDA*
5️⃣1️⃣
Da kyar suka samu kunnayenta suka jiyo magangannunsu, domin du magangannun nan da take sun firgice basu san me take fada ba da yaren Tubanci take magana,
Shiru ta yi ta shiga bude idannuwanta a hankali numfashinta na sama da kasa da sauri sauri ta kankame hannayenta a jikin kirjinta tana mai bin mutanen wajen da kallo,
A hankali numfashinta ke daidaita rayuwar da ta yi a wannan kauye ke dawo mata daki daki,
Da sauri ta tsurawa y'ayan da suke malakinta ido, kafin ta kai dubanta wajen Gaishata dake rabe jikin garu tana duban mahaifiyar tata , domin da Jakadiya zata tafi kaiwa Sarki albishir bayan an yi kiran sallah ta umarceta da ta kamata su fito wajen yan uwanta, nan ta luluba mata katon bargon nan baki mai ciyayi ta fitar da ita dan kuwa har zuwa lokacin batai wanka ba, yo yaronma ba wani kulashi ta yi ba hankalinta na kan mahaifiyarta,
A hankali Anna ke girgiza kanta kafin ta furta" innalilahi wa.ina ilaihi raj.une,
Hannayenta ta dago tana bi da kallo wa.inda turkudi ya rike su da duhu aman ana ganni za.a gane fatarta ta fara nuna alamar gajiya irin ta zama datijuwa,
Tana tsakar haka sai ga ison Sarki na son shigowa,
Da sauri dogari ya tatare abin tatarewa ya karbi tabarma a hannun Mariama ya shinfida dan nesa da su kafin yake zuwa ya dage buhun dake a matsayin makarin shiga cikin gidan,
Shigowa Sarki ya yi bayan ya tsayar da yan rakiyarsa ya karasa cikin gidan yana mai salama ,
A hankali suke amsa masa,
Dubansa ya kai wajen Gaishata dake rabe itama ta dago kanta ta dube shi ta sada kanta,
A hankali ya kai duban nasa wajen Minata dake rike da jariri ta lulube shi a cikin jikinta,
Ajiyar zuciya ya sauke ya duka yana gaisar da Anna,
Kanta kawai ta iya daga masa bata bashi amsa ba,
Zama ya yi ya ce" Anna ya jiki? Da yaren buzanci
Anna ta dago manyan idannuwanta ta sauke kansa, idannuwan kawai ta lumshe a zuwan amsawa,
Shiru ne ya biyo baya tana duban yaren, bakinta cike da magana,
Can ta ce" ina Yake?
Mariama dake son ta mike daga irin zaman da ta yi ta matsa kusa da ita sosai ta ce" ANNA tun jiya ta fita bai dawo ba, Anna ki tashi ki wanke jikinki , ko sallah baki yi ba fa,
Anna jin maganat sallah ta samu ta ciciba inda Mariama ta kamata suka nufi dan zagayen dake bayi ,
Mariama ce ta kai mata ruwa a butar karfensu kafin take zuwa ta shiga kiciniyar dora ruwan zafi , inda Sarki ya karbi yaron ya dan matsa kusa da Gaishata yana rarashinta dan ta sake ,
Ta jima tana fama da ruwa , da omo blue din da ta bata wanda shi ne sabulun wankan, ta jima kafin ta sakawa fatarta shi, ta samu da kyar ta dan rage datin jikinta ta fito ta daura alwallah ta raba su ta shige daki ta tayar da sallah,
Ta jima tana salolinta dan kuwa baki daya sai da ta rama su, tana gama tahiyar karshe ta zauna zaman adu.a , nan ta fashe da kuka mai shiga zuciya tana jijiga gaba dayanta,
Hankali tashe suka shigo dakin gaba dayansu inda Mariama ta bude takar dakin dan haske ya kara shigowa,
Zuwa ta yi itama ba wani jira ta shige jikin Anna tana kuka ta ce" Haba Anna, haba Anna, menene ne? Me ya yi maki haka? A rayuwa mun ga tashin hankali kala daban daban , baki taba tankawa ba, aman jiya karar faduwarki kawai muka ji, shin me ya miki kika suma haka? Anna ki yi hakuri, ki dawo hayacinki domin ke ce nutsuwarmuππ»,
Anna ta sasauta kukanta, tausayin y'ayan nata ya shiga zuciyarta,
Kanta a rufen nan ta vikin yaren tubanci ta ce" Amma ay yini zundu yigustiya, ayyinira unga ci? Dudonur? Tani ayyinira baranniri, abbanur dudonur ( fasara: wannan mutumen ya cuce ni, ina iyayena? Ina yar uwata? Ku taimaka ku kaini wajen mamata, da babana, da yayata.)
Mariama ta juyo wajen sarki hankali tashe ta ce" ka ji yaren da take, tun da ta farka wannan yaren ne take yi, mu bamu san me take cewa ba, Anna ki taimake mu, shin kin manta yarenmu ne?
A hankali Sarkin ya karasa shigowa ya duka dan nesa da ita ua tausasa murya sannan ya sada kai irin girmama siriki da yaren tubancin ya ce" Halasss de wonnuy? Ammanuma ngalla cuku? Tussu ko ka yogodi taha tani tudaqanur cussu qunu. (FASARA: ki kwontar da hankalin ki, ni ban fahimci komai a magangannun nan ba, waye ya cuce ki? Sannan ki taimaka ki fada min da buzanci ko zan gane da kyau.)
Ajiyar zuciya ta sauke kafin take gyara zamanta tana dubansu ta ce" Sunana *ALLATCHI* yar gidan *GUKUNNI* kannin sarki Mahamat na *Ngimi*,
Sunnan mahaifiyata *Hatimi*, sunnan yayata *Herde*
Shiru ta yi tana duban yanda yayanta da sirikinta ke binta da wani kallon mamaki, ta yi murmushi ta ce" mahaifiyata fara ce kar kar tamkar ka taba jikinta jini ya fito, inda mahaifina ya kasance baki sidik , bakinsa har shuni yake domin bakin batube ne na usil, yayata ta yi bakin mahaifina duda ta kasance mace bakin nata bai kai can can ba inda ni kuwa na yi hasken mahaifiyata,
Da zaku tuna yannayin *Agaishana* fatar jikinta, kamanun fuskarta na mahaifiyata ne ba zan taba manta kamanun mamana ba, sai fatar ta yo ta abanna duda nata nada haske sosai kan na mahaifina, aman wannan yannayin shiru, tsayuwa kan kafafuwanta du kuwa da irin halin da take ciki du tana satar yannayin Abanna,
Sarki ya tafka tagumi cike da mamakin dake neman zauta shi yana duban Anna, da saurin maganar da ba maganarsa ba tsabar firgita ya ce" kina nufin ke din Jinnin Honorable *GUKUNNI CE?*
Anna ta lumshe idannuwanta ta ce" ni yarsa ce ta biyu, wanda a sanina daga haihuwata aka juyar da mahaifar mamana dan rashin lafiar da take fama da ita daga bakin da ta samu ciki har haihuwa, ban san bayanna ko Abana ya kara aure ba . Mu biyu kawai iyayenmu suka malaka a sanina,
Sarki ya ce" na san honorable *GUKUNNI*, alkalin garin Niamey banban alkalin dake yanke hukunci masu laifi? Shi dai kike nufi?
Anna ta dago dubanta ta gyada ba tare da ta amsa ba, wani irin nauyin baki ta bude ido da shi may be haka take da.
Da mamaki sarki ya ce" aman aman ya aka yi kika tsinci kanki a nan?
Anna ta rintse idannuwanta ta ce" watarana mun fito daga saloon ni da yayata, muna cikin tuki muka bige wani saurayi mai rawani
A rikice muka tsaya nan yayata da ta fara aiki ta nunawa police din da ya zaburo wajen dan duba abinda ke faruwa da kuma kama mai laifi takardarta ta shaidar ita din likita ce mai zaman kanta ga kuma sunnan mahaifin mu dan haka aka hanzarta aka kama shi muka nufi likita a rikice sai kuka nake dan a rayuwa na kasance mai shegen tausayi da shigewa mutanen da ban sani ba du kuwa da irin gargadin mahaifiyata kan na ringa kiyayewa dan ba kowa ya zama na kirki mai zuciya sanyaya ba,
Mun kula da wannan mutun har ya samu lafia, iyayen mu sun ziyarce shi har asibiti bisa uzura masu da kuka da na yi ,
Bayan an salame shi ne ya duka yana kukan dan Allah mu taimake shi mu bashi aiki ya shigo garinnan bashi da kowa, daman zuwa ya yi neman kudi dan ya ciyar da iyayensa
Haka na nace du kuwa da irin ma.aikatan gidanmu, na kara kai da kas cewar mu dauke shi, buzu ne sai ya koya min buzanci ,
Gannin hankalina ya ki kwonciya Abana ya dauke shi aiki a matsayin mai baiwa fulawowin gidan ruwa,
Mun shaku da wannan bawan Allah domin ya kasance mai barkwonci da bayar da dariya , ni kuwa du inda za.a bani dariya ina wajen, sannan ni ba kawaye ba, gashi a lokacin yayata tana zuwa aiki, ni kuwa makaranta dan wajen shekara goma ne tsakanina da ita,
Sunnan wannan Bawan Allah *Algabittt*, Algabiitt buzu , Saurayi kyakyawa, Algabiitt mai kyan dan maciji,
Ni dai abinda zan iya shaidawa wata rana na fito daga zance da wani dan ajinmu wanda ya nuna yana so na dan nima ina karantar fannin likita ne a lokacin, na dawo zan shige na ga Algabittt tsaye da wani abu a hannunsa jikinsa na rawa sannan da ya saka wani irin turare mai karfi da wani irin abu mai juyar da kwakwaluwa, daga nan na manta wacece ni, na kasance Jelar Algabiitttttt, !
Mahaifina, mahaifiata sunna raye? Ina suke? A ina ka san su?
Anna ta jefo masa tambayoyi tana mikewa tsaye, dan ta lashi takobin yau ko wace wace, sai fa ta danganta da danginta ko a kafa ne!
*Paris*,
Sunna shiga dakin ya ajiye mata akwatin nata kusan dirowa, tsayuwa ya yi yana dubanta ya ce" Agaishana, bara na samo mana abinda zamu ci , ki yi wanka ga bayi can, idan kin gama ki yi sallah.
Da kanta ta amsa masa inda ya fice ya barta nan tsaye,
A hankali ta taka gaban katon madubin dakin ta yi tsaye tana duban kanta,
A nitse ta yi adu.a ta cire kayanta ta bude akwatinta ta dauki hijab dogo mai ruwan milk color ta saka bayan ta daura tawul mai tsayi a kasa,
Bayin ta bude ta shiga , a gidan Ayya du ta san yanda ake anfani da su domin du irin na gidan Ayyar ne, dan haka cikin nutsuwa ta sala wankanta da ruwa masu dumi kafin take karawa da masu sanyi a kasan shower ta gama ta dauro alwallah ta mayar da kayanta ta fito,
Salaya ta dauka wace ta ganni ajiye nan ta shinfida,
Wata doguwar rigar ta canza ta kabarta sallah,
Bayan ta gama sallarta ta zauna ta yi adu.a mai tsayi ga iyayenta, iyayen rikonta, da mijinta da al.umar musulmi da kanta,
Agogon dakin ta daga kanta tana kallo, a kadan ya yi awa biyu da fita,
Ajiyar zuciya ta sauke, da ba dan can daman ta saba da zaman kadaici da kuma rayuwar daji ba da ta tsorata da zama a daki irin wannan ita daya,
Mikewa ta yi ta ninke salayar nata ta gyara hijab din jikinta bayan ta fesa turare mai sanyin kanshi wanda fitarsu da Wardugu da Alhinayeet wardugu ya kwaso mata su,
Ji ta yi ta kasa nutsuwa da jin shirunsa, dan haka ta mike a hankali ta bude kofar dakin nata da ba kara gare shi ba ta fito,
Abinda idonta ya ganni ne ya tayar mata da hankali,
Mu.azam ne zaune saman kujera, Khadija na gefensa da kaya irin sakakun nan na baci ta yane kanta da farin dan kwali tana bashi abinci cikin cokali tana fadin" sai fa ka kara haka kake son baci? Ka san ba zan yarda ba fa!
Tsaye ta yi ta harde hannayenta ta tsayar da dubanta kan su,
Khadija ce ta fara ganninta wanda ya saka ta mike da sauri cikin yannayi na jin kunya, ya salam shi ne ta furta a kasan zuciyarta, ita fa har ga Allah ta sha.afa da mai mata yake yanzu, irin yanda a da take tsare shi sai ya ci abinci yanzu hakan ma iya taba zuciyar matarsa,
Kanta ta dan sosa ta sakarwa Agaishat murmushi ta ajiye spoon din ta juya kanta na kallon kasa ta bar dakin dan wani irin shakar Agaishat din ta ji na lokaci guda da tsoron hada ido da ita...........
Shima kansa ya sada kasa ya kasa dago da kan,
A nitse ta karaso wajen da yake zaune ta duka ta dauki plat guda ta saka spoon din da ba.a yi anfani da shi ba ta debi abincin da ta san zai isheta ta ce" yunwa ya fito da ni, bara ka ga na yi na ciπ,
Shatata ya yi yana kallonta har ta shige dakinta,
Agaishat na shiga ta ajiye abincin dan nesa da wajen da ta yi sallah ta cire hijabinta ta zauna ta tankwashe kafafuwanta ta dauko wayar da Wardugu ya saka mata a hannunta da kuma wayar da Ayya ta saya mata ta ajiye gefenta ta yi bismillah zata fara cin abincin
Tsai ta yi ta tsurawa abincin ido, a fili ta ce" *Me ya sa ban ji wani abu wai shi kishi kamar yanda alhinayett ta fada min wai idan kana son mutun kana masa makahin kishi?* , shi din kishin kansa waye shi? Ya ake jinsa? Ta ce min idan na ga mijina da wata zan ji hankalina ya tashi, wasu na kuka wasu kuwa na nuna bacin ransu karara,
Ko dai bani da zuciya ne a jiki na?
Arrrakham
π«π«π«π« *BAK'A CE* π«π«π«π«
https://www.facebook.com/Idan-rana-ta-fito-writers-association-114558343535568/?referrer=whatsapp
*☀IDAN RANA TA FITO WRITER'S ASSOπ€* ____________________________________________
*Fad'akar da al'umma tare da nishad'antar da masoya shine fatanmu*ππ€π»π
Na
*SAJIDA*
5️⃣2️⃣
Kafadunta ta daga tana mai baiwa kanta amsa" ai kawance ne, ba ga Alhinayett da Wardugu ba? Shi ya sa ban damu ba, kuma a hankali ai zan so shi, idan na so shin mai yiwuwa na kamun da kishin nasa?
Murmushi ta yi kafin take kuma wata bismillar ta shiga cin abincinta a nitse domin a gaskiya yunwa take ji , ita kuwa ko a daji ta saba du tashin hankalin da take ciki in dai ta samu sanwa bata raga mata , tana ci ta yi nak sai ta dora daga inda ta tsaya.
Tunda ta dauki abincin nan ya bi bayanta da kallo har ta kurewa ganninsa,
Hannayensa duka biyu ya dora a habarsa yana shafawa yana kai kawo, mamaki shi ne ya baibaye shi, ya mace zata tarar da mijinta zaune da wata a irin wannan lokacin a irin shigar Khadija duda ba wani shiga ne na kadaici ba, a irin kusancin zamansu, sannan tana ciyar da shi abinci ta juya ba tare da tace da shi ci kanka ba? Me hakan ke nufi? Ina , ina, wannan ba maganar dan ta fito a kauyen nan bata san so bane, su yan kauyen basa so ne? Su basu da zuciya ne? Su basa kishi ne? Bata nuna komai ba, shi bai ga wani yannayi na bacin rai a irin halin da ta tarar da shi da watanta ba, wani irin sanyi jikinsa ya yi harma ya katse masa hanzarinsa a kanta inda ya yi ta kai kawo ya kasa shiga dakinta dan kunyarta yake ji ya kuma kasa shiga ainahin dakinsa, har dare ya raba masa.
Su Walyn basu zo gida ba sai da ta yi kwana shida a gidansu, domin da likita ya salameta ta daure fuskar a fice gidansu da ita,
Mahaifiyarta ta bi umarninta suka je gidan su inda take samun kyakyawar kulawa daga iyayen nata tamkar su hadiye ta, dan du motsi za.a je ne a dauko kudi a banki sai dai Wardugu ya ji alert a wayarsa wace layin bankin ke ciki, yakan yi murmushi ya ci gaba da shagulgulan gabansa,
Wanka ta yi yau ta dandasa kwaliya da lifayar da ta sa mamanta ta sayo mata,
Sosai ta sha kwaliya ga kitso kananu ta yarfa a kanta ta hade karshe tana fitar da dadadan kanshi,
Yar jakar hannu ta dauka ta karbi kys din mamanta inda ta rakota bakin motar sunna bankwaba yau ta yi niyar komawa gidanta,
Zama ta yi wajen direba ta mikowa mamanta hannunta ba tare da ta yi magana ba,
Maman nata ta yatsina fuska ta mika mata carte din Wardugu ta banki ba dan ranta ya so ba ta juya ta tafi bayan ta kara jadada mata ta kiyaye hayewa Wardugu sannan in ta je ta san irin zaman da zata yi da shi!
Haka ta kamo hanyar gidan da ta bari tsawon kwana shida. (WALYN shagali)
Aiki mai tsanani ne ya rike shi yauma kamar jiya, an yankewa mutane hukucin zaman gidan yari wa.inda aka kama hannayensu dumu dumu cikin harkar shigo da miyagun kwaya da abubuwan maye wanda alkali mai girma mai shari.a *GUKUNNI* ya tsaya tsayin daka ba mai kudin ba talakan sai da ya binciko abinda ke kasan kasa kafin ya tafka gudumarsa mai nauyi ya zayano irin adadin lokacin da du mai laifi zai yi a gidan yari, ba damar daukaka kara domin babar kotu ta niger ce ta yanke hukunci,
Wannan lamari ya saka Wardugu kansa ya dau zafi domin sunna ta kai kawon canzawa masu laifin waje, ga tsare tsaren kara tsaro da aka baza a cikin gari, ga mutanen dake damunsa da magiyar ya fitar da y'ayansu su kuwa da sun san bashi da damar hakan, ga niyar zuwansa Paris a yau da dare dan a gobe karfe bakwai na safe za.a shiga aiki da amininsa dan uwansa, aikin dake tatare da hatsari, du wani masoyinsa yana cikin zulumin lamarin domin a daidai wannan lokacin Ayya ta san komai, .........
Bai gama saita abinda zai saita ba sai bayan magariba wanda a lokacin bai fi masa sauran awa hudu jirgi ya tashi da shi zuwa Paris ba.
Da gagawa ya fito ya shiga bayan motar da bodyguard ya bude masa, nan direba ya shiga ya ja shi( sabon tsarin da ya fitar , yakan yarda direba ya ja shi yanzu, wanda a da kuwa sam baya yarda), ya nufi gidan Ayya da shi,
Baiwar Allah tana zaune a tsakar gida , hasken fitulu sun garwaye gidan tana dan kada kafafuwanta da jarida a hannunta ta saka gilas na ganni a idannuwanta, shi kawai take jira
Wardugu na zuwa ta bayan kujerar ya rungume Ayya yana mai dora kansa saman kafadarta yana rintse idannuwansa,
A hankali ta dan tapng din hannunsa ta ce" Me ke damun ka?
Wardugu ya sauke ajiyar zuciya yana kokarin sakin Ayya ya dawo facing dinta ya ce" zan je na tafi Ayya,
Ayya ta girgiza kai gannin ya basar da tambayar da ta yi masa,
Hannunsa ta kamo ta rike ta ce" idan ka je ka zama jarumi , kar ka saki ambaton Allah ko me zai faru, ka kasance mai hakuri gaban abinda ya fi karfin ka, ka taimake ni ka kular min da yar amanata, ban so ka hana ni tafia ba, dan ban san ya zata tsinci kanta a ciki ba, yarinya ce, yarinya ce karama,
Wardugu ya lumshe idannuwansa kafin yake budewa a hankali yana duban Ayya, hannayenta duka ya hade ya dora a kirjinsa kafin yake sada kansa, a kadan ya kai minti biyar a wannan yannayin, wanda Ayya ta dora habarta saman yalwatacen sumar kansa utama ta lumshe idannuwan nata,
Shi ya fara motsawa a hankali yana duban mahaifiyar tasa, murmushi ya sakar mata mai tsari kafin yake cewa" adu.arki muke bara ya Anmiππ»,
Allah ya kare ka, ya bashi lafia, ya kare min yarinta....Ayya ta fada tana shafa gefen fuskarsa
Murmushi ya saki yana amsawa saman lebensa kafin yake mikewa su jero da Ayya har wajen motar ya bude ya shiga,
Tukashi ake aman yana kara gannin girman soyayar dake tsakannin Ayya da yarinyar nan,
Murmushi ya yi ya muzkuta ya dauki wayarsa ya dannawa Khadija kira,
A lokacin Khadija na zaune saman salaya tana jan carbi, Agaishat na saman doguwar kujera mai zaman mutun guda ta lumshe idannuwanta da irin carbin nan wanda ake makalawa jikin yatsa tana danawa a hankali a hankali,
Mu.azam kuwa na baci wanda na allurar bacin da ake yawan yi masa ne dan ya samu cikaken hutu tunda aka kawo shi asibitin,
Ba wani magana tsakanin su aman suna mutunta juna....
A nitse ta daga wayar Wardugu, wanda a kwana biyun nan yakan kirata sau hudu du kuwa da irin yanda aiki ya sha kansa,
Tana dagawa kamar yanda ya saba , salama ya yi mata sai kuma ya ja bakinsa ya yi gum,
Murmushi ta yi , kai halayan abokin Mu.azam na bata mamaki, wannan da mace aka yi gaskiya za.a sha yanga,
Khadija ta mike a hankali ta fita dan kar ta yi wani dan motsinma da zai iya tayar da shi ta ce" Alhamdulilah general, jikinsa na karbar magungunnan yanda ya kamata kuma yana supporter, yanzu haka ya samu baci
Ajiyar zuciya Wardugu ya sauke kafin ya ce" Agaishat?
Khadija ta shafa gaban goshinta ta ce" gatannan zaune,
Ta ci abinci? Ya fada
Wayar ta ciro a kunnenta ta kuma duban sunnan, idannuwanta ta bude da kyau, tana mai jefawa kanta tambayar" wannan damuwa haka? Dan tana yar uwarsa ko dan tana matar abokinsa? Kamar wata baby kulun ya yi kira zai tambaya ta ci abinci? Idan bata ci ba zai kashe ne da an jima ya kuma kira har sai ta shaida masa da ta ci, kuma ita ba cewa yake ta bata wayar ba, koma ba wannan ba ai Ayya na kiran Agaishat din a waya, tana da waya, baya kiranta ya tambayeta sai dai wani?
Amsa ta bashi kan ta ci, kafin yake cewa" Merci (thanx) ya katse kiran
Wayar ta bi da kallo, daga inda take tsaye ta hango Agaishat na dan motsa kafa kennan dai idannuwanta biyu,
Ajiyar zuciya ta sauke ta samu waje nan ta zauna
*Kwana uku da suka shige kafin a kai Mu.azam asibiti*
A wannan kwanakin tsakannin Agaishat da Mu.azam an samu shakuwa, shakuwa irin ta zama waje guda, shakuwa irin ta sosai din nan domin Khadija ta daina shigowa gidan sai dai shi yakan fita a kai a kai ya leka wajenta dan makotan juna ne sai dai Agaishat ta hango shi ta windows
Ya nunawa Agaishat kulawa, sukan zauna su yi hira, harma su buga gem din da ya koya nata,
Ya koya mata cacakar waya ta iya shiga ta yi abinda take so,
Ya shaku da ita sosai , sai dai da magariba ta yi zai yi mata salama ne ya rakata dakinta ya fito, shima ya je dakinsa,
Bai taba hada shinfida da ita ba, kai ko kissing din hannunta bai taba ba bale ya zarce gona da iri, yana dai bata kulawar da ya saka Agaishat ta shaku da shi, har in bata ga wulginsa ba takan shiga yannayin damuwa har sai ta ganshi sun yi hira hankalinta ke kwonciya,
Ba zaka ga yanda halitar Agaishat ta kara kawatuwa ba sai ta saka wando dogo ko gajere , damame ko sakake irin shigar bacin nan da take, nan zaka ga mace a tsaye komai ya ji sai hamdala, Agaishat irin matan nan ne da sun san su waye su sai a slow, dan kuwa zasu iya anfani da halitar da Allah ya kawata su da shi dan firgita dubu su take dubu,
Zama waje daya, cin dadi, kwonciya baci tsala wanda sai sallah kawai da suka kasance ayyukanta na yanzu ya saka ta dauki yannayi na babar yarinya, daidai da murmushinta takan dan murmusa ne ta basar, koyon danna waya ya saka ta iya zama a karkace saman kujera, takan dan karkace kadan ta shiga danna wayarta tana gem na princess tana sakin dan murmushinta mai kawata fuskarta,
Mayukanta da Ayya ta siya mata dan kara gyara fatarta bata sanya da su, tana murzawa ne a duk lokacin da ta yi wanka ko alwallah, jikin Agaishat ya zama fresh ta kara haskawa sai santsi da fatarta ta kara,
Wannan fannin kam alhamdulilah ko ita tana gannin sauyi bale mai kallonta, hakan ya sa Khadija ke kara sarewa, bata iya zama na lokaci mai tsayi a tare da Agaishat, kamshin da take bazawama na turaran tubawa ya isa ya rikita maka tunani,
Tunda ta zo abu daya ya saka ta kuka, a ranar da ana gobe za.a shiga asibiti da mijinta, Mu.azam ya kasa zuwa ya fada mata ainahin abinda ke faruwa da shi, sai da macen da yake kira da aminiya ta yi masa jagora har cikin dakin barcinta, ta samu waje ta zauna ainahin wajen da Agaishat ke zama dan lumde jikinta da humura,
Ta wani kada kai kafin ta shiga zayanno mata rashin lafiar mijinta, ta fada mata cutar cancer ce aman za.a shiga aiki da shi, ta karashe tana mai sakin gungurmen kukan da ya karasa dode kunnuwan Agaishat da ta rasa ina ta dosa, me hakan ke nufi, ta kai dubanta wajen Mu.azam da ya mike jiki a mace ya karasa wajen Khadija ya shiga rarashinta da nuna mata ba ta yi masa allawarin ba zata yi kuka ba? A wannan rana Agaishat ta yi masu kallon tsaf, a wannan rana ta ji idannuwanta na rufewa, hankalinta na tashi, a hankali ta kwonta saman bed din dakinta ta rintse ido, bata san fitar Khadija ba sai jin hannunsa ta yi saman fuskarta yana share mata hawayen da suka shiga zubo mata wa.inda batama san suna yi ba, a wannan lokacin ta buda idannuwanta da sukai mata nauyi ta sauke su saman fuskarsa, ta shiga rudani tsakannin abu hudu
Na farko, rashin lafiar mutumen da yake mijinta, wanda akai mata kira da cancer, ba.a fada mata aimahin menene cancern ba, ba.a yi mata bayani sala sala ba sai fada mata da aka yi cewar yana dauke da kansa wace za.a yi masa aiki nan da kwana uku, za.a shiga da shi asibiti a gobe gobe, wato mijinta na fama da babar cuta ne ko me?
Na biyu: irin yanda mijinta ne ke dauke da cutar, ita bata sani ba, sai da aminiyarsa ta sani, sannan aminiyarsa ce ta zo ta fada mata, du kuwa da irin kusancin dake tsakanin mata da miji?
Na uku" irin yanda aminiyar mijinta ke kauce mata, irin yanda ta hango halin shiga uku kan rashin lafiar amininta, irin yanda ya zabura ya nufeta ya dora kanta saman kirjinsa a gaban ita da take ainahin matarsa ta sunna wada ba zata nuna ranar da ya yi mata haka ba, ya rarashi aminiyarsa harma ya yi mata rakiya
Na hudu: sai a lokacin komai ya shiga dawi mata daki daki, ta kasance a dukan lamarin mu.azam tana zuwa ta biyu ne, wato Khadija ce fa fari!
Da wannan kallon cikin idon da ta yi masa na tsayin lokaci inda ya dora hannunsa na dama yana gyara mata dogon gashinta da ya bazu kan bed dinta kafin a hankali ya ce" ki yafe mini,
A haka ya ja mata bargo ya lulubeta ya kashe mata fitilar dakin ya fita da nufin ya barta ta yi baci ko me?
A haka ta hangi ficewarsa wajen ainahin aminiyarsa , Aminiyarsa, aminiyarsa!
Abinda ya faru da Agaishat da Mu.azam da khadija kennan kafin a kawo Mu.azam asibiti bisa kulawar likitoci sa Agaishat da Khadija aka shiga saka masa magungunna ta hanyar karin ruwa da nanauyan magugunnan baci dan ya samu isashen hutu.....
Wannan kennan
Wardugu na karasawa gidansa ya fita ya nufi sashensa,
Yana budewa ya shiga da sabon cerrure din da ya canza ,
Yana shiga ya ga sabuwar mai aikin da ya dauka, wace a da babu namiji a yan aikin bangarensa bisa umarnin walyn, aman a yanzu ya dauka ta gyara falon ta saka turaren ruwa mai kanshi ta ajiye abinci,
Ya san tana can bangaren da ya saka aka kaita wanda ke nesa da wajensa sosai dan haka ya zarce dakinsa
Sauri sauri ya yi wanka ya dauki jakarsa irin ta sojoji ya saka kananun kayansa na bukata da maclean da bros, da complet daya ,
Kananun kaya ya saka a jikinsa bakin dogon wando da bakar riga kafin yake dora costume (veste) saman rigar ya caje gashinsa ya gyara sosai ya fesa turare mai kanshi,
Jakar ya dauka da passport dinsa sai cart dinsa ta can wace a bankin can ya yita,
Fitowa ya yi yana duba dakin bai bar komai a jone ba?
Nan ya ga hajia Walyn tsaye, ta sha kwaliya mai kyau da birgewa tana masa murmushi ,
Kallo daya ya yi mata kafin ya kawar da fuskarsa ya juya ,
Yannayin hade fuskar da ya yi ya saka bata iya tankasa ba, tsoro ya hanata tambayarsa inda zai je duda ta sani ne fita ne zai yi ya dawo dan haka sai ta nemi waje ta mike tana jiran dawowarsa ta lalabe shi ya manta fushin da yake su shirya (to ka ji)!
Bai dauki mota ba, bai kuma bi ta kan kowa ba ya fice a kafarsa yana mai duba agogo
Taxi ya tsayar ya shiga ya fada masa aeroport,
Timiya
π«π«π«π« *BAK'A CE* π«π«π«π«
https://www.facebook.com/Idan-rana-ta-fito-writers-association-114558343535568/?referrer=whatsapp
*☀IDAN RANA TA FITO WRITER'S ASSOπ€* ____________________________________________
*Fad'akar da al'umma tare da nishad'antar da masoya shine fatanmu*ππ€π»π
Na
*SAJIDA*
5️⃣3️⃣
Timiya
A wannan ranar da kyar aka samu Anna ta koma ta zauna , shima sai da y'ayata suka rikice da koke koken dan girman Allah ta zauna a zana sunnan jaririn nan da aka samu sai su tafi, dan Gaishata ta kara kai da kasa yan uwanta da mahaifiyarta ba zasu tafi su duka su barta ba, kar a je su ki dawowa,
Gannin haka shima sarkin hankalinsa ya tashi dan haka harda shi a yan magiyar ta zauna a yi suna sai ya yi masu rakiya wajen wanda yake da alaka da gidan , wato sarkin agadez, shima rakia ya yi masa wani lokaci da suka je banban birnin, suna ganewa junna,
Haka dai Anna ta yarda ba dan hankalinta ya kwonta ba, sai dan tinawa da ta yi y'ayanta, idan ta tafi wajen wa zasu rabu su ji sanyi? Dama gashi ya fara tado maganar mutanen da suka kawo kudin aurensu sun waiwayo zasu zo a daura aure,
Wani murmushi ta yi mai ma.anoni da dama kafin take fita ta juye zuwan zafin dake tafasa Mariama ta kama suka kai bayi ta fito fuska a dan hade ta zanawa sirikin nata du abin bukata na wankan jego kan a yi gagawa a kawo kafin ruwan ya huce, (abinda da bata iya ko tsayuwa gata ga shi, Annar yanzu ba ruwanta ba wani shaka ko tsoro),
Da sauri ya amsa ya fita a gidan, inda Anna ta tube jaririn sai hada rai take na yannayin tsaftar gidan , du hankalinta da nutsuwarta ba a waje daya suke ba, sai ma da aka tashi neman turare abinka da batuba, kaf gidan Mariama ce kawai mai turare , itama irin na duran nan ne mai karfin tsiya, dan haka dole su Mariaman suka karbi makulin dakin Gaishata suka nufi gidan sarki dan ita tana da dan turaran wuta da na ruwa dan idan sarki ya je cikin birni yana bada kudi wajen mai dakin sarkin agadez q harhada masu tsumamun turaruka da sauran su,....
Wannan kennan
*Paris*
Jirgi na sauke shi ya kunna abin localisat@ din wayarsa ya shiga carte cikin iphone dinsa ya danna localisation din wayar Mu.azam, domin a kunne take kuma ya tabata nasama ba a kashe ba,
Taxi na ajiye shi kofar asibitin ya je wajen shiga ya nuna takardar shaidar waye shi, ya bada cikenken kwatancen wajen wanda ya zo da ranar da aka kawo shi da komai kafin ake barinsa shiga dan an rigaya an hana shiga, suma da suke tare da shi dan Khadija na ma.aikaciyar wajen ita da Mu.azam din,
Yana shiga ya fitar da wayar ya shiga bin kwatancen da ta dora masa saman screen dinsa har ya iso dakin da yake kwonce,
Da yake akoy katon madubin da ana tsayawa a ga marar lafia ta nan, sai Wardugu ya tsaya ya harde hannayensa ya zuba masu ido,
Khadija na nanade saman salaya carbinta ya fadi da alama tana ja baci ya kwasheta,
Agaishat na zaunen dai saman kujera kuma lokaci zuwa lokaci takan dan motsa kafarta idannuwanta a rufe har yanzu kamar mai baci, da dogon hijabinta mai ruwan jini,
Sai Mu.azam dake sheme saman gadon mararsa lafia, an aske kansa kwalkwal har kyali yake , wanda shi ya saka aka aske masa da kansa tun kafin a shiga aikinma, yana ajiye numfashi a hankali,
Idannuwansa ya rintse ya karasa wajen doguwar kujerar silbar da ya ganni a wajen ya zauna ya daga kansa sama yana jan carbin hannunsa ya tsurawa fitilar dakin ido
Yanda Wardugu ya ga rana haka ya ga dare, wajen karfe biyu ya ji motsi a dakin nasu wanda ya kyautata zaton alwalla aka dauro dan an jima ana dan motsi kafin ya ji shiru, a hankali ya leka nan ya ga Agaishat ce ta kai sujada kanta kasa tana adu.a, kawar da kansa ya yi da sauri ya koma ya zauna ya ci gaba da jan carbinsa, har karfe biyar ta yi
Ba kiran sallah zasu ji ba dan haka da agogo suke aiki , da lokaci ya yi zasu mike su yi sallah ne,
Zuwa ya yi ya samu ya dauro alwallah ya dawo,
Tapis ya dauka cikin jakarsa ya kebance kansa dan likitoci sun fara dan kai kawo ya tayar da sallarsa,
Ya jima yana rokom Allah ya sa a yi aikin nan lafia, yana gamawa ya mike dan shida ta gota ya dauki jakarsa ya dan kwonkwasa dakin
Agaishat dake kusa da kofar ta mike ta bude ,
Gabanta ne ta ji ya wani tsintsinke ya fadi a lokaci guda,
Kanta ta daga kafin take iya kallon fuskarsa, wanda shima ya dan duko da kansa ya sauke idannuwansa kan fuskarta,
Ba zaka iya karantar yannayin fa yake ciki ba, fuskarsa ba yabo ba falasa,
Shigowa ya yi ya mayar da kofar ya rufe,
Fuskarta da idannuwanta sun kumbura, hakan na nuni da ta yi kuka,
Kawar da dubansa ya yi daga kanta ya mayar kan Khadiha da ta mike itama tana dubansa,
Fuskarta itama ta bumbura ta yi jajajir,
Bai amsa gaisuwar da suke masa ba sai zarxewa da ya yi wajen Mu.azam,
Kujerar dake kusa da gadonsa ya ja a hankali ya zauna yana kallonsa, karfe bakwai saura yan mintuna Mu.azam ya farka,
Farkawarma ba can bace, ya fan buda idannuwansa da sukai masa wani irin nauyi ne,
A hankali ya ga Wardugu dake zaune ya rike hannunsa na dama,
Allah ya bashi ikon yin murmushi yana duban Wardugu,
Magana yake a hankai wanda Wardugu ya kunnayensa aman bai ji komai ba dan haka ya nuna masa da ya yi shiru,
Da idannuwansa ya nuna ya yi shirun inda ya lumshe idannuwan sai ga hawaye sun fito daga cikin idannuwan nasa,
Docter Ce ta shigo da farar riga irin ta likitoci tare da nurse da uku da gadon tura marar lafia
Wani irin mikewa Khadija ta yi ta zuba masu ido inda docter ta girgiza mata kai, haka ne daman idan kana son gannin rikicewa sai idan ciwo ya taba likita, yakan fice a hayacinsa ya zama wani kala, yakan rude komai kankantar ciwo bale mai tsanani,
Hakan ce ta faru da khadija, domin a lokaci daya ta rikice ana nuna mata kar ta yi gabansa aman ina bata san lokacin da ta dora hannayenta duka biyu saman kanta ta fashe da kuka , da sauri Wardugu ya juyo ya cire gilas din idannuwansa domin har ya mana dan baya so a san halin da yake ciki,,
Da sauri Docter ta kama hannunta suka fice inda wasu likitocin maza biyu suka shiga kokarin daukansa suka dora saman dayan bed din
A hankali Wardugu ya saka hannunsa cikin sumar kansa ya shiga yamutsawa inda gaba daya jijiyoyin jikinsa suka mike tsabar yana cikin tashin hankali
Agaishat dake tsaye sai zarar ido take gannin yanda Khadija ta fashe da kuka aka fita da ita, da yanda aka dauki Mu.azam ranga ranga aka dora saman wani gado, du fuskokin likitocin a hade irin sun ci kalar serius din nan sai ta rikice,
Tana ta zaro ido tana kallon yanda suka saka masa oxygen suka gyarashi da kyau saman gadon ,
Sai bayan sun gama gyara shi wani likita ya zo da takarda a hannunsa cikin file , da yaren faransanci ya ce" Chef, (sire), docter Khadija tace Nan zan samu Wardugu?
Wardugu dake tsaye shima yana kallon yanda aka yiwa amininsa, nan zuciyarsa ta kara tsorata da girman ikon ubangiji, kaga mutun yanzu yanzu ka zama tamkar gawa ko gawar,
Da kai ya amsa masa cewa shi ne, dan haka likitan ya mika masa wata takarda kafin yake kara masa bayani kamar haka" Docter Mu.azam ya bar maganar cewa idan za.a shiga aikinsa a baka wannan takarda ka saka hannu, takardar na nufin idan Har Allah bai yi ya fito kalau ba kai za.a ba gawarsa ba likita zata birne shi ba,
Wani irin sarawa kan Wardugu ya yi, Wardugu dai soja ne, sojan ma baba, wanda ya shiga gwagwarmaya da manyan yan ta.ada, wanda ya kwana cikin rami, wanda ya shiga hatsari kala daban daban na rayuwar yau da kulun, yau gashi gaban ikon mai duka, yana ji yana gani ya karbi biro ya saka hannun idan amininsa ya mutu a dakin tiyata a bashi gawarsa,
Yana saka hannun suka karba suka juya da Mu.azam dake sheme tamkar gawa,
A hankali wardugu ya kai wajen garu ya silale dan baki daya kafafuwansa rawa suke masa,
Agaishat da ta bi su da kallo sun fice mata da miji ta juyo da sauri wajen Wardugu ta karasa ta duka daidai inda yake yana kallon waje guda , murya a rikice ta ce" Ina zasu kai shi? Ina zasu kai min shi? Ina zasu kai min mijina? Ya mutu ne? Me ya sa suka tafi da shi? Wayyo Allahna, Wayo Allahna ,
Ta fada tana karasa zubewa kasan ta fashe da wani irin kukan da ya jima yana cin zuciyarta,
Wardugu dake kallonta ya lumshe idannuwansa kafin yake budewa,
Hannunsa dake rawa ya mika ya janyo hannunta kusa da shi sosai,
Murya can kasan makoshi ya ce" ba mutuwa ya yi ba Agaishat, aikin ne aka shiga da shi, ki daina kukan nan na tuba ki rufa min asiri ki yi shiruππ»,
Maimakun ta yi shirun sai kara kukanta da ta yi tana ta rike hannunsa tana kiran ya kaita wajensa, ya kaita ta ganshi, kar ya mutu ya barta, tana son sa!
Ido kawai ya lumshe ya yi shiru ya damke hannun nata, bai kuma yi mata magana ba sai sauraron sambatunta da yake tamkar ta zauce ,
Wasa wasa awa daya, awa biyu awa uku, awa hudu, awa biyar, awa shida ba.a fitar da Mu.azam ba, daga dakin sun canza waje ya fi a kirga inda karshe suka dangana dan nesa da dakin tiyatar kusa da Khadija dake zaune tana wani irin numfashi tamkar mai athsma, da kyar aka barsu suka tsaya nan din sai da aka kusan kwasar rashin mutunci da Wardugu kafin masu tsaron asibitin su bar shi,
Agaishat zaune take jikinta hade da garu itama tana rawar sanyi, zazabi ne jikinta inda Wardugu ya kasa zaune ya kasa tsaye sai kai kawo yake hankalinsa ba a kololuwar tashe.
Suna haka baban likitan asibitin ya fara fitowa, nasara ne mai sunna,Roger , shi ya jagoranci aikin inda likitoci kamarsa biyar suka taya shi,
Khadija ce ta fara mikewa ta nufe shi jikinta na rawa baki daya,
Daidai nan wasu uku suka fito suma suka tsaya kusan docter Roger,
Tambaya ya yi cewar" ina Wardugu?
Wardugu da ya tsaya yana hangensu ya ji gabansa ya fadi, a hankali ya shiga takowa inda wata zazafar zufa ke karyo masa, du takunsa guda daidai da mutuwar tunaninsa yake har ya karaso kusa da likitocin,
Likitan ya dago kansa cikin wani yannayi ya ce""".......
π³
π«π«π«π« *BAK'A CE* π«π«π«π«
https://www.facebook.com/Idan-rana-ta-fito-writers-association-114558343535568/?referrer=whatsapp
*☀IDAN RANA TA FITO WRITER'S ASSOπ€* ____________________________________________
*Fad'akar da al'umma tare da nishad'antar da masoya shine fatanmu*ππ€π»π
Na
*SAJIDA*
5️⃣4️⃣
Likitan ya dago kansa cikin wani yannayi ya dubi Wardugu kafin ya dubi Khadija, ya ce" mun fito aiki, za.a fitar da shi a saka shi dakin observation na sati biyu, komai nasa zai dawo hannunmu na tsayin wannan lokacin, cinsa , tsaftarsa, komansa, tsakaninku da shi sai dai ku ringa hango shi ta jikin madubin dake makale da dakin, ni kadai zan iya shiga in daidaita komai in fito, za.a baku takardar magani da kuma irin abincin da za.a ringa saka masa ta mesa ta hancinsa, fatan ka fahimta idan baka gane wani abin ba sai ka tambaye ni ko ka tambayi matar tasa *Docter Khadija* ai ta san komai itama zata kara maku haske,
A hankali ya karkata dubansa wajen Khadija inda Docter Rogger ya raba ya fice, sauran docters din suka shiga bata hannu sunai mata murnar an samu nasarar aikin ciki sai fatan ya farka daga dogon barcin da aka luluka shi wanda farkawar shi ne zai shaida aiki ya yi ko bai yi ba wanda a kala zai iya kai sati biyun idan komai ya je daidai ko sama da haka abinda ba.a fata , sannan aka bata abinda aka cire a cikin kan , du suna yi suna nuna itace matarsa suna tayata murna wardugu na tsaye a wajen kuma da yarwn French ne ba abinda baya ji
Dubanta dai kawai yake uwa ya samu tv, ita kuwa ta ki yarda su hada ido da shi ko su samu zama daga ita sai shi,
Tana gannin likitocin samu tafi ta dan dubo shi a yannayin daburce ta ce" zan zan je na karbo takardun,
Bai bata amsa ba har ta bacewa ganninsa tana sauri tamkar zata fadi,
Juyawa ya yi yana kallon Agaishat da itama tunda suka nufi wajen likitocin take kallon su, bata san abinda ake ciki ba, bata iya yaren su ba, sai ta zama bakon Tv, dan dukan idannuwanta ta bude tana bin kowa da kallo ko zata fahimci wani abin,
Yana nan tsaye yana hangenta yana tunanin me zai ce mata Khadija ta dawo ,
Kanta take dan sosawa irin na mai laifi wand Wardugu ya gama karantarta watsi ne ya yi da lamarin da baya son shiga abinda bai shafe shi ba,
Rakardun ta mika masa ta shiga masa bayani kamar haka" kasancewarsa ma.aikacin asibitin nan wanda suka dauka da kansu yake karkashinsu zai biya rabin kudin aikin wanda ya kama millions 3 da dari takwas, sai riko gado kulawa shima tabin kudin ne ya kama jika dari bakwai namu na cefa,
Sai takardun magungunna da za.a ringa karbo masa a nan cikin pharmacy na asibitin shima yanzu zan je na karbo takardar da zata bamu damar biyan rabin kudadan magungunnan du zamuna karbowa ,
Sai da ta gama yi masa bayannin du yana karbar takardun kafin take miko masa carte din Mu.azam da kuma tata ta banki ta ce" ga carte din mu na banki, ga takarda mai dauke da code din mu wato reference din mu, idan aka hada na mu biyun na tabata kudin zasu isa har a salame mu,
Da yake du bayannan nan da take idannuwanta basa kallonsa dan mugun kwarjini yake mata sai da ta ji bai karbi takardar da carte din ba ta dago da dubanta a hankali ta dube shi,
Fuskarsa ya yatsina ya juya ya barta nan tsaye da takardar da kuma carte din, aman ya karbi baki daya na asibiti da za.a biya, na magungunnan,
Tana nan tsaye tana kallon sa ya fice ya tafi infa Agaishat ta bishi da kallo,
Kanta ta daga sama ta lumshe idannuwanta, a yau ta ji wani irin takaicin da bata ji ba na rashin karatun zamani da basu samu ba, ta zama tamkar kurma marar wayo a cikin mutane, bata gane yaren su , sun zame mata sababin mutane sun zame mata sabin halitu, gashi wanda ya kawota kasar take zaune dominsa kansa ake bayani aman bata san komai ba, yau kam ta yarda da maganar Ayya inda take ce mata" Agaishat, ban ki maganar baba tsofo fannin karatun zamani ba, aman ina son ki sani a rayuwa komai yana da anfani, karatun adini, karatun bokon ne , neman sani kan abubuwa ne, shi dan adam ana so ya zama mai yawan bincike kan lamarin zaman yau da gobe, neman ilimi ba laifi bane, jahilci baban ciwo ne wanda bashi da magani, idan aka ce jahilci kuwa ba ana nufin mutun jahili ba, ana nufin abinda baka sani ba yake a cikin duhu gareka .
Idannuwanta ta dan bude gannin Khadija ta koma wajenta na da ta zauna, bata ko nemi zuwa wajen da Agaishat take ba bare ta kwatanta mata wani abin,
Tabas hasashen Agaishat ya gama tabata a kan Khadijar da mijinta,
Dan ka fito daga birni, baka yi karatun boko ba, ba ana nufin kai din wawa sakarai bane, kana hankalce da komai, hasalima ka fi wasu yan birnin lura da gane lamura a kallo kawai bama sai an fada maka ba,
Ji ta yi an shiga hakkinta da yawa, ji ta yi ba.a mata adalci ba, zuciyarta ke ingizata da ta mike ta tarar da khadijan ta fada mata ta gane soyaya suke da mijinta, aman tana so ta fada mata halin da yake ciki, ko ba komai a tunaninta kusancinta da shi zai fi da kowa duba da itace matarsa, wada ya dace ta zama sirinsa, aman sai ya kasance itace wace bata san komai game da shi ba, wata zuciyar ta ce" ki ce da ita me? Wato ke mai hayagaga ko? To dan ya mayar da ke baya cikin komai nasa sai me? Me kika sani , ina kika sani, me zaki iya yi masa a cikin lamarin? Ke ko a kauye kin zama koma baya cikin y'ayan Ba bale a birni, birni mai abin mamaki, birni mai mota mai jirgi mai kalolin fata? Birni mai madafi a daki? Birni mai tv mai abin allo? Ke kama kanki a hakama ya isa, ki saka ido ki yi adu.a, ki godewa Allah hakama ai ci gaba ne!
Idannuwanta ta yiwa wal wal wal irin ta harari kantan nan, ta dafe gaban goshinta da hannunta na hagu sannan ta dafe daidai zuciyarta da hannunta na dama, ji take zuciyarta na doka mata da sauri, takan shiga irin yannayin nan idan tana cikin yannayi na tsoro,
Ya kai minti talatin da fita kafin yake dawowa shi da wasu mutane biyu , dayan ya girmanta dayan kuwa shima saurayi ne mai jini a jika,
Su duka hannayensu da wasu manyan takardu masu dauke da tambarin asibitin wa.inda a cikinsu ne aka zuba magungunnan da take a way,
Karba ya ringa yi yana ajiyewa kusa da khadija ba tare da ya yi mata magana ba,
Sai da ya gama ajiye komai ya dawo wajensu suka yi magana ,
Khadija dai na kallon su inda Agaishat ta kawar da dubanta daga bangaren kowa kawai ta sada kanta tana mai dana carbinta,
Sara masa suka yi kafin su yi musabaha , kys din motar saurayin ya mikawa Wardugu yana mai nuni da takardun motar da komai a ciki kafin su juya, ashe yaransa ne dake zaune a kasar da sunnan Niger.
Kys din ya saka a aljihun wandonsa, ya dawo wajen Khadija dake kallonsa tana sarawa girmansa harma ya fi yanda Mu.azam ke fada mata, lale Wardugu ya nema kuma ya samu, rikeken hamshaki ne da baya nunawa ko yinkaho sai dai ka dube shi kawai ka gane nitsatsen hamshaki ne,
Takardun shaidar ya biya komai ya mika mata, a gajarce a kuma dunkule ya ce" an gama da wannan , sai na gaba.
Take a way din ya duka ya dauki takarda biyu ya bar mata guda ya juya ya nufi wajen Agaishat,
Yana zuwa Ya tsaya ya ce" mu je,
Maganarsa kawai ta ji saman kanta, dan haka ta dago da sauri, sai ganninsa ta yi saman kanta fuskarnan a hade,
Mu je? Mu je ina? An salame mu ne? To ina Mu.azam din?
Tambayoyin da ta yi ta jerawan kanta kennan ,
Gannin bafa mai amsa mata gareta ba sai ta mike tana leken Khadija dake kallon su , tana so ta yi mata magana aman Wardugu ya tsare wajen dama gidan baki daya, dan haka ta juya sumui sumui ta fara fita a wajen kafin yake daga kafa ya shiga gabanta
Sai da suka fito harabar asibitin wajen motocin dake parke ya ciro ky din ya danna dan command din dan gannin wacece motar?
Motar da ta yi kara dan amsa kiran da akai mata ya tsurawa ido yana dan shafa gefen fuskarsa, aman lale comandan Munkaila ya raina masa wayo, wannan motar ta samari wanda suma idan zasu shan iska suke hawa ne ya bashi? Gaske da ya tambayeshi marque dinta ya ki fadi ,
Kansa ya girgiza, shi ba shiba yake ji, yarinyar nan zata iya zama cikinta? Bata da sama , gaba daya saman a bude yake gashi garin ana yannayi na sanyi ,
Zuwa ya yi ya bude ya shiga inda ya waiwayo gannin Agaishat bata biyo bayansa ba,
Da ido ya yi mata nuni me take jira? Dan haka ta karaso tana kallon inda zata bude ta shiga, ita bata taba gannin kalar mitar bama dan ba wani yawo aka kaita ba, yar fitar da suka yi daga gida zuwa asibiti kuwa hankalinta a tashe batama kalli garin ba bale ta san me ke zuwa da zowa,
Bude mata ya yi daga ciki ta shiga ta zauna tana gyara hijabinta da kyau,
Tayar da motar ya yi ya dauki hanyar gidan Mu.azam dan ya san gidan kuma bai ji yace da shi ya kaura daga nan ba,
Ita dai kanta a kasa dan ji take iska ta yi mata yawa, aman da ta sada kan sai ta ji sauki sauki,
Tuki wardugu yake yana tunanin abubuwa da yawa da ya ganni kan zuwansa zuwa yanzu,
Ko yanzu sai da ya koma wajen docter Rogger ya nuna masa komai tsarin a tsanake ya kwatanta masa inda za.a mayar da shi da kuma bashi takardar da ko a wani lokaci ya zo zai iya shiga kansa tsaye
Yana tunanin nan har ya karaso kofar gidan nasu,
Fita ya yi itama ta fito tana biye da shi ya dana ya bude suka shiga,
Ita dai kallonsa take har ya je ya daga wani katon peau na flower ya dauko ky ya zo ya bude mata,
Tsaye ya yi har ta zo ta shiga, sai kuma ya mika mata take a way din guda wato rabonta ya juya da niyar tafia,
Agaishat ta yi kundunbala da tsoronta da komai ta ce" shi fa?
Birki ya ja, a hankali ya dan juyo yana mai cire gilas din da ya mayar ya yi mata kallo daya jal,
Mayar da gilas din ya yi ya saka ya juya bai bata amsa ba ya fice a gidan,
Abincin ta saki nan ta juya da sauri ta karasa wajen kujera ta zauna kasa ta hada kanta da gwuiwarta ta fashe da kuka, da yaren buzance take fadin" wayo Annata, wayo baba sofona, wayo Ayyata ku zo ku dauke ni, bana so, bana son auren, shi auren haka yake? Wayo zuciyana ciwo yake,
Bata ji motsi ba, sai karan ajiye kys da ta ji dan haka ta dago a tsorace
Shi ta ganni da abincin nata ,
Bai ce da ita komai ba ya je ya dauko plat da spoon ya darwaye ya zo ya bude ya fitar da abincin ya bude ya juye cikin plat din,
Zuwa ya yi inda take zaune shima ya zauna ya ajiye mata abincin kusa da ita, sai da ya yi da gaske kafin ya iya fadin" ki yi hakuri, an masa aikin kuma in sha Allah zai warke ya dawo gida,
To ka kai ni wajen shi Wardugu , Agaishat ta fada tana hade hannayenta,
Wannan karron kam ba kallo daya ya yi mata ba, tsai ya yi da idannuwansa kan fuskarta,
Hannunsa ya sa ya shafa goshinsa da kyau kafin ya ce" ki yi hakuri zai dawo kin ji?
Da kai ta amsa shi , ya nuna mata abincin,
Dauka ta yi ta shiga ci a hankali tamkar tana cin magani,
Wardugu ya yi ajiyar zuciya har ta gama ya mike ya ce da ita" zo ki rufe ba.a barin gida a bude kin ji? Idan kin rufe ki samu ki yi wanka ki huta zan dawo na kai ki ki ga Mu.azam,
Da to ta amsa shi da alamar murna, dan kam so take ta ganshi, ta yi missing dinsa fiye da tunanin mai karatu a dan lokacin da bata ganshi ba, sabo tirken wawa, Agaishat kam ta kamu da son mijinta, tana son abinta,
Haka Wardugu ya fice a gidan Agaishat ta rufe ta cire hijabinta ta nufi dakinta,
Tana shiga ta je wajen gadonta ta dauke matasan kan dake ajiye ta yaye abin shinfidar ,
Nan takarda ta fado wace in ba zata manta ba tun lokacin da Mu.azam ya raka Khadija ya dawo a lokacin da ya janyo abin rufa zai rufawa Agaishat ya saka mata kasan matashinta wanda ya san ta ganni , bayan ya saka din ne ya dubeta ya furta kalmar "Ki yafe min",
Gannin takardar ta fado ne ta je ta dauke duda ba wata baba bace ta kai wajen shafe shafenta ta ajiye tana fadin" bawan Allah ya mance *Takardarsa* ko ajiya ne ya bani? Bara na kara kilaceta,
Dan haka ta dauke daga nan ta kai cikin akwatinta ta saka ta dawo ta canza zannin gadon ta canza na jikin pilow din ta kwashe wa.infa ta cirw ta yi bayi dan wankewa, dan kuwa sam bata wani kai kaya wajen tara kayan dati, ita ke wanke abinta da kanta.
*Takarda kuma?*
Yawan comment samun wani page eheππππ
π«π«π«π« *BAK'A CE* π«π«π«π«
https://www.facebook.com/Idan-rana-ta-fito-writers-association-114558343535568/?referrer=whatsapp
*☀IDAN RANA TA FITO WRITER'S ASSOπ€* ____________________________________________
*Fad'akar da al'umma tare da nishad'antar da masoya shine fatanmu*ππ€π»π
Na
*SAJIDA*
5️⃣5️⃣
Wardugu na fita hotel din da aka kama masa ya nufa,
Yana zuwa ya fiya ya baiwa mai gyara mota ky ya yi gaba ba tare da ya dau komai ba,
Mai gyara motar nan ya gama gyarawa ya ciro komai a motar ya mikawa masu shigar da kaya hotel din,
Sai fa aka yi scaning din jakar kafin a dora saman abin turawa a nufi guichet, nan suka fada masa dakin da Wardugu ya sauka ya tafi kai masa
Daidai wannan lokacin Wardugu na zaune ya lumshe idannuwansa saman kujerar dakin hotel din fara kar ,
Mikewa ya yi ya bude ya karbi jakar , nan wanda ya haudo masa kayan ya mika masa wani album mai dauke da hotunnan yan mata kala daban daban , na kasashe daban daban ciki harda hausa girls, cikin shiga na tsiraici suna tala , idan mutun na so zai zabi wace ta yi masa da farashinta da numberta ya danna kira ta amsa kiransa (π)
Jefar da album din ya yi ya nufi bayi bayan ya danna kira katon butik din hotel din ya yi order kaya da siz dinsa da coler
Wanka ya yi kamar zai canza fata dan rabonsa da yi tun jiya da dare,
Ya dauro alwallah dan gabatar da sallar magarib
A nitse ya kamala komai ya saka kayan da aka kawo masa kannanun kaya ne masu tsari na manyan mutane, kalar baki ne dai sai chemise din ta ciki fara kar da cravate .
Agogo ya daura a tsintsiyar hannunsa ya fesa turare ya dauki katuwar wayarsa dan sai a lokacinma ya kula da waya,
Ayya ya fara kira , wada kamar jira take ta daga, tun kafin su gaisa ta jejefo masa tambayoyi,
Murmushi ya yi ya kora mata bayani cikin girmamawa da shagwaba irin na dan shagwaba a wajen mamansa,
Murmushi ta saki jin Alhamdulilah, ta yi adu.ar Allah ya tashe shi lafia, ta ce" ya yarinyata? Ta warware? Ta kara jiki? Ta yi kyau? Tana da wani abu ne? Hankalinta kwonce? Tana samun kulawa ne?
Tsai ya yi ya ciro wayar daga kunnensa ya tsurawa sunnan ido, Ayya, Ayya, kai ya girgiza ya mayar a kunnensa ya ce" idan na hadu da ita sai na baki ita Ayya ku yi maganar ko?
Ayya ta ce" kai wardugu bana son wulakanci , an gaya maka bama waya ne? Muna waya da ita aman kulun sai tace wai lafiarta kalau komai kalau, aman yanzu kai da ka je ba sai ka fada mani ba? Tana da wani abu ne?
Wardugu ya ce" wai menene wani Abu kuma?
Ayya ta ce" kai, baka san wani abu ba? Ina nufin an samu karuwa ne?
Kansa ya dafe , shi fa bai san me take nufi ba, dan haka ya ce" Ayya zan yi kiran ki , zan je wajen Mu.azam din,
Bai jira amsarta ba ya kashe kiran yana sauke ajiyar zuciya, toh shi yaushe zai tsaya kallon ta yi kyau ko wani abin? Shi inama ruwansa da kurewa matar mutane kalloπ.
Kira a whatsupp masu yawa inda yarinyar nan wato *BASMA* kiranta ya fi a kirga, ga na Walyn da messages dayawa, ga na abokan aiki da mutanen arziki,
Wa.inda ya dace ya maidawa ya shiga ya maidawa, wa.inda ba lale sai a lokacin zai maida masu ba kuwa ya bari sai ya zauna ya jefa wayar a aljihu ya fice
Garin dare ne aman kamar rana, haske ne ko.ina, wasu a lokacinma suke dawowa daga gudun motsa jiki, wasu na yawon kafa da iyalansu, kowa dai na sha.aninsa ba wanda ke kula da sabgar wani,
Yana tuki har ya karaso gidan Mu.azam
Agaishat ta sala wankanta ta saka wata doguwar rigar sai dai bata kai har kasa ba da dogon wando a kasan rigar ya rike kafarta tam dan rif ne da shi daga can kasa wajen idon kafa,
Tana zaune a falo suna vidio Call da Ayyanta, sosai Ayya ke yi mata hira dan sakata nishadi inda ta maida hankalinta har tana murmusawa sosai tana tambayar ayya abin tambaya tana bata amsa daidai labarinsu
A haka karaurawar dakin ta shaida da mutun wato ana son shigowa,
Mikewa ta yi tana warware dan kwalin dake daure a kanta ta yana shi a fuskarta ta je ta danna wajen budewa dakin ya bude,
Kallo daya ya yi mata ya ce " mu je,
Da wani dan gudu gudu ta juya da wayar tana fadin" Ayya, ya Wardugu ne zamu tafi wajen Mu.azan din,
Da sauri ya juyar da kansa daga kanta, irin fizgar jikinta da ta yi bai kai idannuwansa da gangan ba sai akasi da aka samu yana tsaye a wajen,
Astagafari ya shiga ja yana zabgawa idannuwansa fada, fitama ya yi a gidan ya je wajen motar ya zauna yana jiranta har ta fito da lulubeben hijab dinta mai ruwan blue da takalmi plat blue sai carbinta, ko wayar bata dauko ba ta barta a gida,
Suna zuwa suka tarar da Khadija tsaye wajen da ake hangen Mu.azam din, ta jinginar da kanta jikin madubin , tana kallon wajen wanda basu san adadin lokacin da ta dauka a haka ba, basuma san ko ta je gida ta dawo ba, su dai sun tarar da ita,
Jin motsinsu ya fargar da ita zuwansu, juyowa ta yi gare su ta sakar masu murmushi kafin murya a sanyaye ta ce" sannun ku da zuwa,
Agaishat ta karasa inda take tsaye ta ce" ina yini, ya mai jiki?
Khadija ta waiwaya eajen madubin ta waiwayo ta sauke ajiyar zuciya ta ce" Alhamdulilah,
Wardugu kam bai amsa ba ya zarce wajen madubin ta tsaya yana kallon yanda aka dadaura masa na.urori da mai taimakawa lumfashinsa, da mai aiki jikin bugun zuciyarsa, da wada in ya motsa zata yi kara, da karin ruwan dake jone , da ledar fitsari a ajiye gefe wace idan ta cika ake tsiyayewa, da fo kasan bed din,
A hankali Agaishat ta karaso inda yake tsaye itama itama ta tsaya ta kai dubanta inda yake kallo,
Idannuwanta ta zaro tana duban Mu.azan da tsoro karara a fuskarta, ai kuwa me zata yi in ba kuka ba? Ta aniya fashe masu da kuka tana nuna yanda Mu.azam yake kwonce,
Hankali tashe Wardugu ya dubeta, nan da nan ya turbune fuska tamkar bai san wata halita daria ba, rai bace ya ce" la ferme tu veut? (Chut up nah?!) ,
Ki rufe min bakin ki !
Ba wani da ihu ya yi maganar ba, sai dai a kausashe ya yita wanda dole ka yi shiru ko baka shirya ba,
Tsorata ta kara yi ta shiga ja da baya baya ,
Khadija bata taba jin Matar Mu.azam ta bata tausayi sai yau ba, dan haka ta rike hannunta ta baya ta jata suka fice a wajen,
Kuka Agaishat take tana shasheka inda du ta tsorata da komai,
A hankali Khadija ta zaunar da ita a balbalin wajen kusa da fulawowi,
Da tsinkakiyar hausarta take son rarashin Agaishat dan haka ta ce" ki yi hakuri, zai samu lafia, ki bar kuka kin ji?
Agaishat dake dubanta zuru bata iya amsara ba, dan haka Khadija ta jimke hannayenta , da kanta ta yi mata alamar ta kwontar da hankalinta sannan da dayan hannun ta yi mata nuni da sama cewar Allah na nan,
Ajiyar zuciya ta sauke ta sada kanta,
Wardugu ne ya karaso wajen ,
Ganninsa ya saka khadija ta mike ta yi masu salama ta koma ciki,
Wardugu ya zauna yana lura da yanda Agaishat ke dan ja baya, tsorata take son yi da shi baki daya dan haka ya zauna yana facing dinta,
A hankali ya ce" menene na kukan? Bakya so ki rasa mijin ki? Bakya so ya mutu?
Agaishat ta dube shi da sauri, bata san lokacin da ta ce" Wardugu,,
Sai kuma ta sada kanta kasa, a hankali ta ce" bana so ya mutu, *ina son sa*,
Shiru ne ya biyo baya,
Jin shirun ya yi yawa ya saka ta dago a hankali, dan ta ji kunyar fadin gatsai gatsai tana son mijinta, sai dai itafa iya gaskiyarta kennan, duda da alama shi hankalinsa rabe yake gida biyu, zata zauna da shi, to meye ma fan ya so watanta? Ai ba ita kadai ce mace ba, dan haka ita ba wani zata ja ba, yo irin rayuwar da ta gani a gidansu da Ba ke sheka abinda ya ga dama Anna ta bi shi ita mema akai mata? Ba zata zama mai raki da rashin godiyar Allah ba,
Wardugu dake zaune tamkar mutun mutuni gannij zata dube shi ya saka shi mikewa da sauri ya yi gaba,
Da sauri saurin itama ta bi shi dan ta fara karantar halayensa , yakan yi magana da ido, ko da jikinsa.
*Timiya*
Gari mai gawo, Timiya garin sarki ne,
Yau aka zana sunnan Gimbiyar garin Timiya, sarauniyar birnin zuciyar sarki wato Gaishata,
Taron sunnan da ya tara mutanensa na arziki, garin ya dauki jama.a ya cika makil inda aka soke amale biyar aka yanka aka shiga gashi da wasu wasu aka kai wajen madafa inda mata ke tone alkabut da gurasa na kasan kasa suka aza miya,
Cuwa cuwa ake wanda sai ka leka bangaren Amaryar jego zata ci karo da mamaki,
Wato amarya ce hakimce cikin shiga ta alfarma sabon turkudi mai fari da maroon, ta sha sarkar zinari da amarwaraye, hakama yan uwanta sai kai kawo suke sunna tarbar baki inda dakinta ya sha sababin kayan daki da gado sabo dal irin na yan birni ga inji ya bada wuta panka na sheko masu sanyi, jariri a lulube a wajen tsohuwa mai kulawa da mai jego,
Kadan kadan zaka ga Mariama ko Fatimata sun duko wajen bakinta ta fada masu abin tambaya ko na shawara, cike da aji su fice su nufi gidan da sarki ya maido su kafin a gama zanen sunna su daga wajen Anna dake zaune cikin runfar kara mai sanyi saman tabarmar leda ta sha jan kunshi a kafafuwanta da hannayenta, ta nada lifaya ja, idannuwanta dauke da kwali shar, sai zobuna da awarwaraye na zinari da ta saka itama uwar mai jego ta kuwa hakimce abinta , su zo su fadi maganar yarta ta fari ta kuwa mike idan na mikewa ne ta yi iya yinta dan gannin ta daidaita komai, idan sako ne ta tura daga inda rake cike da aji da sannin abinda take yi a je a yo a zo har yama ta yi aka shigo da kyautar kayan jariri da na uwarsa daga mai girma sarkin garin timiya....
Mai karatu zai yi tambayar ina ta samu kudade haka na sayen zinari?
*Ba* na ajiyar kudadansa idan ya samu a cikin gidansa, kuma Anna itace kadai ta san ma.adannin kudin aman koda yinwa zata kashe su ba zata iya tabawa ba dan tsabar tsoron ransa ya bace,
Bayan warwaren kulin da ya kula mata, ya kasance su har yanzu basu da labarin inda yake dan haka ta je da kanta ta kwaso baki daya kudaden da suka rage wanda bai masu mugun kashewa ba ta zo ta samu sarki a lokacin da suna ya matso ta bashi ta zana masa bukatarta baki daya yayanta harda Agaishat wace kudin aurenta ne danma sun tafi da sadakinta, ta saka a yo masu sarkar zinari da awarwaraye, ta saka a kawo masu turaren wuta na arziki da na feshe na ruwa masu kanshi, ta saka a kawowa yan matan kayan kwaliya da lale na hausa da sauransu, ta saka a yo masu siyayar kayan jiki ba wasu masu yawa ba aman masu kyau da tsada da ma.ana, nan ta kawo maganar kayan dakin Gaishata inda sarki ya nuna a bari yana da niyar canza masu su duka matan nasa, duda haka ta nemi alfarma ta kara wasu abubuwan irin zannin shinfida na gado, kayan jere na zamani, karshe dai kudin da suka rage a hannunta basu fi million daya ba inda Mariama ta kawo mata ta wajen Ba da ya basu ta hada ta rike a wajenta da niyar zasu rike saboda hanya.
Bayan zanen suna da kwana biyu,
Zaune suke suna kallon yanda Anna ke gyara miya , suna yi suna hirarsu a nitse ba wani hayaniya ko rawar kai,
Gashi gidan ya bade da sanyayan kanshin turaran wuta
Dogari ne ya yi salama daga kofa,
Mariama ta leka nan yake shaida mata sakon sarki na yana son magana da Sirikarsa
Kimtsawa Anna ta yi, ta saka hijab sai baza kanshi take ta nufi gidan sarki
Tana zuwa ta karasa bangaren y'arta ba wani dari dari ko labe labe irin na da,
Sun jima suna hira tsakanin Anna da gaishata kafin sarki yake karasowa,
Kan maganar tafiarsu ne, Sarki ya shaida masu in sha Allah zasu je agadez a jibi, su gana da sarkin agadez sai ya sada su da *Gukunnin*
Amsawa Anna ta yi , sannan suka kara daidaita maganar inda dole dai da Gaishata za.a tafi dan ta kafe , yanzu kuwa Anna ta zama mai son y'ayanta, tausayinsu na mamaye zuciyarta, takan yi tir da wannan rayuwa, sai kuma ta godewa Allah da ya dawo da ita hanyacinta tun yanzu.
*After 2 weeks*
Paris
π«π«π«π« *BAK'A CE* π«π«π«π«
https://www.facebook.com/Idan-rana-ta-fito-writers-association-114558343535568/?referrer=whatsapp
*☀IDAN RANA TA FITO WRITER'S ASSOπ€* ____________________________________________
*Fad'akar da al'umma tare da nishad'antar da masoya shine fatanmu*ππ€π»π
Na
*SAJIDA*
5️⃣6️⃣
Barka da juma.a
A kwanakin nan 14 da aka yi ,duka kaf Wardugu na nan , ba.inda ya je, yana tsaye kan lamarin amininsa, du wani abinda za.a fitar da kudi komai nauyinsu yakan karba ya je ya dawo da abinda aka bukata,
Ya kasance du idan lokacin cin abinci ya yi zai fita ya shigo masu kowa da nasa ci uku a yini,
Yakan yi jim idan ya ga sun yi jigum jigum ya ce da su" zai tashi, ku mu yi masa adu.a
Wannan abubuwan ya saka Khadija ta mugun zube kasa, wato ta ga ita ba komai bace a wajen son kyautatawa Mu.azam, wani irin girman wardugu da kwarjini, da kunyarsa suka karu a wajenta,
Ya kasance a yanzu ta yarda ba ita ta fi kowa son Mu.azam ba, sannan ta dan ja baya in dai Agaishat na wajen takan rage yawan leka wajen da Mu.azam din yake ma, sai dai idan bata nan kuma zata je ta tsurawa wajen ido,
Agaishat kanta da ya kasance kulun da sasafe zai zo ya dauketa su je asibiti, idan abinci zai je siya sai ta fadi wanda take iya ci, idan rana ta yi ya mayar da ita gida kuma sai bayan magariba ya daukota, duda ba wani hira ke hada su ba, sai kusancinsu ya karu, shakuwa ta shiga tsakaninsu, wanda hakan ba karamin illah ne ga dayansu ba,
Idan ya kawo abinci bata ci ba kuwa zai kama dago kansa jefi jefi yana duban abincin ya dubeta ya kawar da kansa, idan har ya ga lokacin cin abincin zai shige bata ci ba zai mike daga inda yake ya zo ya bude ya ajiye mata ba tare da yace da ita kala ba ya koma mazauninsa,
Kudi sun ji jiki, wai danma wasu abubuwan rabi yake biya albarkacin yana ma.aikacin asibitin, sannan likitocin nan tsaye suke kansa, baban likitan kansa ke kula da komai na Mu.azam har zuwa wannan rana inda suke tsaye a kofar su duka suna hangen likitoci uku dake tsaye kansa,
Tunda safe ya dace ya motsa, aman shiru ba alamu,
Wannan zuwansu na hudu ne wanda ya kama karfe shida daidai aman shiru Mu.azam bai motsa ba,
Zuciyoyi sun karaya, hankali ya tashi, a tsaye suke cir da kafafuwansa inda cikinsu ba wanda ya saka komai a bakinsa bale ya kai cikinsa, kai da azumi ma Wardugu ya tashi, su kuwa ba wace ta kula da wani cikinta ,
Agaishat hankalinta a karshen tashi yake, dan sala sala khadija ta kwatanta mata komai a jiya da yama, dan Gaskiyarta ta fadawa khadijar cewa ita ba karatun boko ta yi ba, bata san komai game da abinda ke faruwa ba,
Khadija ta yi mamaki ainun, daman wanda bai yi karatun boko yana iya zama wayis haka? Ita bata ga wani kauyanci a tare da Agaishat ba, ko aman da ta yi ta kelayawa a jirgi ta yi tunnanin ko irin mutanen nan ne da basa son tafiar jirgi ko mota yanzu sa kama amai, du kai kawon nan da ake a tunaninta ta gane komai idan likita ya fito ya yi bayani da french a tunaninta ta iya ta san me aka ce,
Kwarai ta ji ba dadi, ta yi tunanin da itace fa? Hakan ya sa ta zauna ta yi iya yinta da kwatance da cicirarar hausarta ta fada mata komai a nitse wanda sai da ta yi data sannin fada mata dan sai a lokacin Agaishat ta birkice fiye da da ta ringa irgen lokaci tana fadin ya taimaka ya buda ido, ita a barya ta je ta tashe shi,
Wannan karon wardugu bai iya wani tsawata mata ba, shima zuciyarsa a hautsine take
Jikinta duka rawa yake, a hankali ta kai hannunta wajen Khadija dake tsaye tamkar ba jini a jikinta ta damie hannunta ko zata ji sasaucin tsoron da take ciki,
Khadijarma ta rike hannun nata gamgam suna gannin yanda likitocin ke ta aune aune suna magana suna rubutu a takarda,
A yannayin da suka fito, dole ne hankali ya tashi,
Wannan karon kam ba wani boye boye suka tsaya gaban Wardugu, Khadija, da Agaishat suka yi masu bayannin bai farka ba kuma basu san dalili ba,
Sun auna basu ga abinda ya tare mashi farkawar ba,
Suna fadi ne fuskarsu cike da alhini,
Khadija ta kwala kara ta ce" non, non impossible non (no, no imposible no!),
Wardugu dai na duban likitan dake bayani, ya ci gaba fa fadin" cikin wasiyarsa ya bar maganar, in dai bai farka ba, kar a ci gaba da rayashi da inji, a cire masa injin dake taimakawa lumfashinsa a bar shi ya tafi, lokacinshi je ya yi ba yanda za.a yi, dan haka ku saka ranar da za.a cire masa na.urar dake bashi lumfashi,
Wayo ba za.a cire ba, wayo na shiga uku, Mu.azam kar ka yi kin haka, Wardugu ba za.a cire masa ba, in dai kuka cire mashi kun kashe ni nima walahi ko kwana daya ba zan kara ba sai dai ku kaimu mu biyu, khadija ke fada tana girgiza Wardugu kan kar ya saka hannu a wannan decision din,
Agaishat ta matso da sauri ta kama dayan hannun Khadija itama tana kuka a rikice da yaren buzanci ta ce" ya mutu ne? Ya mutu? Khadija Mijina ya mutu? Innalilahi wa.ina ilaihi raj.une ,
Ta cika hannun khadija ta damki na Wardugu fake tsaye yana dubansu zuru tamkar bai san yaren kowace cikinsu ba, tamkar wanda ya rayu cikin jeji shi kadai, sun zame masa sababin halita a gabansa,
Agaishat ta rike shi da kyau ya dago hannunsa ta dora gefen fuskarta ta girgiza hannun da kyar ta ce" Wardugu, ya mutu? Mutuwa ya yi? Wardugu ya mutu ne?
Wardugu ya janye hannayensa a jikin nasu ya juya da wani irin sauri ya fice a wajen baki daya,
Khadija ta zube kasa tana kuka inda likitocin abokannan aikinta ke rarashinta, Agaishat ta karasa jikin madubin ta jinginna kanta ta hadiye kukan a ranta ta shiga zabga masa adu.a tana tofawa tana duban ba.a rufe shi ba,
Wata likitar ta zo wajenta itama ta shiga rarashinta tana dafa kafadarta da yaren frency inda Agaishat dubanta kawai take aman bata san me take fada ba, ita dai zuciyarta ta cunkushe kukan ya tsaya cak, adu.a take ta yi kan Allah ya sa ba mutuwa ya yi ba!
Wardugu na fita ya je ya tsaya bakin titi ya tsurawa hanya ido,
Ba komai idannuwansa ke ganni ba sai zaman da suka yi da Mu.azam, abubuwa da dama wanda yawancinsu irin girman hakurinsa da zama da Wardugun ne, da wanda in ya juye wani sa.in sai an nemo Mu.azam din,
Ina son na rayu War, ina son na rayu na haihu nima na ga yarana sun girma, sai dai ban san ba ko zan samu haka?
Magangannun suka fadowa Wardugu a rai,
Idannuwansa ya rintse suka kara rikidewa sukai wani ja mai duhu!
Wani lokaci sun je kauye mai sunna Matamai nan yankin damagaran kusa da nigeria ya ga yanda garin keda ni.ima, tsarin rayuwar garin ta mugun birge shi inda ya nace sai da suka kara kwanaki kan wa.inda sukai niyar yi,
Suna lambu ne cikin garin sansayar iska na kada su yace" ka san Wani abu Wardugu?, duda an ce mutun idan ya mutu halayensa ke binsa, khairin ko sharin gwargwadon aikinsa gwargwadon kabarinsa, aman zan so na mutu a garinnan ni.imar garin ta yi min ,
Wardugu ya daki kafadarsa ya ce" sai kace wani saudiya? Kai fa haka kake motsi kadan mutuwa motsi kadan mutuwa, du inda ta zo fatan shine a cika da imani,
Ji yake jikinsa na yi masa nauyi, zuciyarsa ta cinkushe,
Wayarsa ke kuka kamar ta fasa aljihun wandonsa ta fito aman kunnayensa basa ji,
A fili ya ce" ya zaka bar wasiyoyinnan a kaina Mu.azam? Wa ya fada maka ni inada karfin zuciyar da zan iya saka hannu a takardar da zata bada damar a cire maka damar shakar numfashi ka tafi na dindindin? Wa ya fada maka cewar ni inada karfin da zan iya daukan gawarka na kaita inda zan kaita? Kai wama ya fada maka cewar ni din zan jure gannin an rufa maka dara? Innalilahi wa.ina ilaihi raj.une,!
Wayarsa ya lalubo jikinsa na wani irin kadawa , zafi kuwa ya dume masa jiki baki daya ya danna numbobin da bai yi tunanin idan an daga zai samu mutumen ba,
Da asalamu alaikum aka amsa wayar,
Wardugu ya ce" Mu.azam ne yace wai na saka hannu a takardar cire masa oxygene,
Shiru ya yi , inda hankalinsa ya tashi, murya a dan rikice ya ce" kana ina? Kuna ina?
Wardugu ya amsa da " muna paris, muna ma.aikatar Mu.azam, Mu.azam ya ki tashi!
Mikewa ya yi daga zaunen da yake , da hannunsa ya yiwa abokinsa alama da ya tafi ya fice ya nufi aeroport dan gannin ko zai samu jirgin da zai sada shi da Paris a yau yau, inda hali a yanzu????
π
Wa Wardugu ya yi kira,?
MU.azam ya tafi kennan?
Agaishat, Khafija, Warduguππ»ππ’πππππ
π«π«π«π« *BAK'A CE* π«π«π«π«
https://www.facebook.com/Idan-rana-ta-fito-writers-association-114558343535568/?referrer=whatsapp
*☀IDAN RANA TA FITO WRITER'S ASSOπ€* ____________________________________________
*Fad'akar da al'umma tare da nishad'antar da masoya shine fatanmu*ππ€π»π
Na
*SAJIDA*
5️⃣7️⃣
Tafia ta manya ce ya yi, in ba dan manyan ba daga shi sai suturar jikinsa sai cart dinsa ta banki, da ita ya ciri tiket, ya zauna yan mintuna inda jirgi ya daga da su, da ita ya ciri kudi ya yi shatar taxi ta kai shi asibiti
A kofar asibitin aka hana shi shiga, domin dare ya ratsa har wajen karfe biyun dare,
Ba yanda bai yi ba, da kwatance da komai aman masu tsaron kofar suka kiya dan su basu sanshi ba, gashi mushulmi, su kam aa yama bar masu kofar asibiti
Gashi bai san numbersa na garin ba,
Waje ya samu dan nesa da asibitin ya shiga kai kawo, dare ne ba damar ya sayi wata wayar du an rufe, gashi ba wata takarda ya zo da ita ba ko tiket ciran kudi muraran ya yi masa sun san shi a yanda yake da yawo kasashe ya shige abinsa idan ya so ya san yanda zai yi,
Kansa ya shafa a lokacin da ya tuno da whatsupp, duda ya san abune mai wuya wai ya duba whatsupp , aman sai ya shiga ya aniya kiran number Wardugu baya dagawa,
Ya yi masa kira ya fi a kirga, dan haka ya nemi guri ya zauna hankali kwonce dan waje ne mai tsaro, kuma da garaje ba za.a kama mutun ba duda suna da tsarguwa da musulmi suna tsoron yan jihad,
Daga nesa yake hangen tafiyarsa, da kyar yake daga kafarsa,
Ido ya tsura masa, daga ina yake?
Wani tausayinsa ne ya lulube shi, dan kuwa Wardugu in dai hankalinsa a tashe toh baya zama, zai yi ta yawo ne a kafa, idan wani abin fada ne ya hada shi da wani toh a hanyar yawon nan nasa kan mai tsautsayi zai kare ne,
Aman yanzu yana hangensa a wani yannayi na rashin karfi, har ya karaso inda yake zaune,
Dama Wardugu na hangensa, tun zuwansa har artabun da suka sha da masu tsaron asibitin da kiran da ya yi ta faman yi,
Yana zuwa tsaye ya yi gabansa yana dubansa,
A nitse ya mike shima yana dubansa,
Hannu ya mika masa da nufin su yi musabaha,
Wardugu ya miko masa nasa hannun shima, nan ya ji wani irin zafi hannun nasa,
Hankali tashe ya ce" aman Wardugu me kake yi haka? Yau ka fara yin rashi ne ko yau ka fara shiga tashin hankali mai tsanani? Ka tina wannan lamari gaban wanda baka da ikon motsi, jan numfashi sai ya umarta ne, kaima lokacinka na nan tafe, dan kulu nafsin za.ikatul maut,
Ba wanda ya isa, ba wanda zai iya, ba wanda zai yi in ba shi ba, kar ka manta ya rasa iyayensa a lokacin da yake saurayi, ya karba da hannu bibiyu ya rayu a cikin duniyarnan mai cike da rudani,
Idan Allah ya karbe mana shi a yau sai mu yi masa biyaya , mutuwa ta zama rigar kowa, mutuwa mai yankan kauna ne, mutuwa ba ruwanta da baba ko yaro, itace mai dauke uwa a lokacin da ta sako dan jariri, itace mai dauke jariri daga hannun mahaifiyarsa ta mika shi a kaishi wajen wanda ya fita son sa, mutuwa mai raba miji da mata, ta raba abokai, ita ba inda bata ratsawa da lokaci ya yi ya dauka ta yi gaba abinta, a halin arziki ko talauci, birni ko kauye,
Ka yiwa amininka gata mafi girma wato adu.a da kyakyawan sutura,
Wardugu ya zube kasa nan wajen kasa zaune,
Bakinsa na rawa dan ciro magana , da kyar ya iya samu bakin ya bude masa ya ce" ya ya ya bar wasiyun da sukai min tsauri da yawa, *MARAHUT* na tsinci kaina a halin da bana iya aiwatar da komai, karfin ikon Allah dole na karba, na kasa kuka, na kasa saka hannun, ana min ikirarin ni jarumi ne? Na gwada jarumta ta hanyar sadaukar masa da abinda nake so a nan gidan duniya aman yau an wayi gari na kasa daukan jarumtar saka hannu a bakar takardar da za.a cire masa abin numfashi,
Marahut ya zauna shima kusa da shi ya daga kansa sama ya ce" kalu *INNALILAHI WA INA ILAIHI RAJ.UNE*, innalilahi wa.ina ilaihi raj.une, innalilahi wa.ina ilaihi raj.une.......
Haka Murahut ya yi ta maimaita masa har shima ya karba sukai ta yi , sukai ta yi , sukai ta yi,
Can Wardugu ya shiga ajiye zuciya, a hankali ya dora kansa saman kafadar Murahuttt,
Murahutt ya yi shiru na dan Lokaci kafin ya ce" ka san cirewar ko shi ne samun rahama a gare shi? Idan ka yi duba da musulunci ya zo mana da idan mutun ya rasu a yi gagawar yi masa sutura?
Shin wace hikima ce a boye a nan? Allah baya abu kawai,
Idanfa an jima da zare ransa kune ke gannin yana numfashi? Idanda gawar ce kwonce kuke kallo?
Wardugu ya rintse idannuwansa da karfi ya ce" mai yiwuwa kuma likacin ya buda idannuwan nasa ne basu yi ba?
Kennan dai ba zaka hakura ba ? Marahut ya tambaye shi,
Wardugu ya ce" bani da karfi, ban isa na ja ba,
Marahut ya gyada kai, sukai shiru su duka
Can Marahut ya ce" ina Agaishat?
Wardugu ya dago da sauri ya dubi Marahut, shi sai yanzu suka fado masa a ransa, mikewa ya yi zurbat ya yi gaba da sauri inda Marahut ya bishi da kallo, bai yi wani gigin binsa ba dan tuni ya yi nisa a tafiar sai ido da ya zuba masa har aka barshi ya shiga asibitin,
Yana shiga ya zarce wajen da ya tabata suna nan wato wajen dakin Mu.azam,
Bayin Allah sun dunkule waje guda sun rufa da hijabin Agaishat sai sauke ajiyar zuciya suke su duka,
Tausayinsu ya kara karyar masa da zuciya, tun ranar da Khadija ta je gidansa ya gama gane ba wai kawance ne kawai ya hada su da Mu.azam ba, duda ya ga irin yanda Agaishatma ke son Mu.azam din, aman yayi imanin da wuya in ta kai khadijar dan kuwa Khadija ta jima a soyayarsa, wa.innan bayin Allahn biyu su ne marayu kan rasuwar Mu.azam, shi kuwa ya rasa amini, aboki, dan uwan shawara, dan uwa na jini
A hankali ya raba su ya nufi wajen hangen Mu.azam din,
Ja ya yi ya tsaya ya tsura masa ido, irin kallon nan na kurullah,
Idannuwansa ya lumshe yana kada kai, dan kuwa idonsa nuna masa yake ya motsa yatsarsa manuniya,
Da yake kafafuwansa rufe suke da bargo ba.a gannin motsinsu, sai da ya kara motsa yatsar nan, a hankali fatar idonsa ta dan fara rawa, bugawar zuciyarsa ya fara karuwa kan na da da ya yi kasa sosai ya yi nisa,
A hankali bugawar zuciyar ke dan karuwa wanda ya saka injin dake sasarkafe jikinsa suka kwashi kuka,
Zabura Wardugu ya yi ya kara kurawa Mu.azam ido,
Tun karfinsa ya ce" MU.AZAM, MU.AZAM, MU.AZAM!
Ba.a jin komai daga ciki, sai su Agaishat ne suka mike a firgice, daidai nan likita ya shigo da gudu ana biye da shi ana taya shi daura rigar aikinsa da safar hannu da na rufe hanci,
Wata na tura abinda ke dauke da kayan aiki,
Ai kuwa sai gasu suna ta bilowa da gudu gudu , nanfa aka shiga kokowar fitar da su Wardugu daga nan din ma ,
Da kyar aka fitar da su waje inda du suka haukace sai tambaya suke jefo masa wai ya farka ne ? Farkawa ya yi ne?
Wardugu kam bai iya amsawa ba sai kai kawo yake yana kama sunnayen Allah a zuciyarsa , baya so ya amsa masu dan bazai so ya basu espoir kuma abin ya kasance ba haka ba,
A kadan sun dauki minti arba.in, lokaci lokaci zaka ga wani ya fito da gudu ya nufi can wajen dakin kayan aiki ya dawo da wani abin da gudu ya shige, koda sun tarye shi baya bada amsa har suka hakura suka dawo bin mutane da kallo. ( ya Allah ka jikan mama da gafara, wannan ciwo da ya kaita Allah ka sa bakin wahalarta kennan alfarmar annabi muhamadu sallalahu alaihi wa salam)
Ba su su gama kimtsa komai ba sai da aka dauki wajen awa da minti talatin kafin kake gannin sun fara fitowa suna tafia makwoncinsu,
Su kam sun zama tamkar mararsa wayo,
Can sai ga docter Rogger da Elizabeth sun fito,
Murmushi kwonce saman fuskarsu,
Hannu suka shiga mikawa su Wardugu, harda Agaishat dake binsu da kallo aman ta kasa karbar hannun ko daya dan ta kagauta ta ji halin da yake ciki
Wani murmushi ne Wardugu ya saki, wanda gaba daya hakoransa suka bayana,
Da sauri ya juya ya nufi bayi dan dauro alwallah, domin lokacin nafilfilu bai shige ba, tabas zai raya wannan dare wajen godewa Allah,
Khadija ta rungume Agaishat tana murna ga hawaye na malala a idannuwanta ta ce " Agaishat, ya farka, kuma ya yi kyakyawan farkawa, dan ya gane su su duka, yanzu an ce a barshi ya huta zuwa safe mu shiga mu ganshi, Agaishat *Mu.azam dinmu ya farka*
Agaishat ta saki murmushi itama ta ce" Alhamdulilah, Allah mun gode maka, Allah ka bashi lafia mai anfani
Da amen take amsawa,
A haka Wardugu ya fito da tapis a hannunsa ya saci kallonsu kadan ya sauke ajiyar zuciya ya fice a asibitin,
Inda ya barshi nan ya same shi,
Goron ruwa ya mika masa bai masa magana ba ya samu waje ya shinfida dardumar ya tayar da sallah,
A sujadarsa ta karshe, Wardugu ya jima yanaiwa Allah kirari, ya gode masa bila adadin,
Bai tashi daga saman salayarsa ba sai da rana ta fara fitowa, dadaykun mutanen da suke fitowa motsa jiki na safe har sun fara tsayawa daga nesa suna kallon su Wardugu suna mamakin musulmai ne suna masu sallah a wuri,
Bai wani damu ba sai da ya gama jan carbinsa ya shafa fatiyarsa , ya kai dubansa wajen Mahaifinsa,
Fuska ya hade ya yi kicin kicin da fuska ya ce" ya farka a jiya,
Marahutt ya ce" na gane tun jiyan a yannayinka,
Wardugu ya dan tabe baki ya mike ya dauke abin salayar ya kai dubansa wajen asibitin ya ga an bude an fara shiga, dubansa ya kai wajen Marahutt ,
Kafin ya yi magana Marahut ya ce" na san hanya
Kansa ya juyar ya ajiye salayar nan kusa da mahaifin nasa ya juya yana neman taxi dan ba zai koma ciki daukan mota ba gaskiya.
Hotel ya je ya saka kaya masu sauki ya shiga fakin gymnastic ya motsa jikinsa sosai ,
Dawowa ya yi ya yi wanka da ruwa masu sanyi karara ya fito ya saka kaya ya fesa turare ya dauki kys ya bude dakin ya sauka , nan ya karbi kayan da ya yi order ya shige taxi din dan ya mayar da shi asibiti
Yana zuwa ya shige ,
Nan ya gansu zaune Marahutt na kusa da su suna hira jifa jifa inda Agaishat ta bada hankalinta suna hira dan sosai yake sake mata gashi yana kiranta da yarsa, hakan ya saka take son datijon da gannin girmansa
Wardugu na shigowa idannuwansu suka sarke ita da shi,
Wata harara ya sakar mata kafin ya dauke kansa,
Kamar yanda ya saba ya mikawa kowa nasa harda Marahutt,
Karban dai yan matan suka yi aman ba wada ta kai niyar ci,
Bai takurawa kowa ba, ya dai bude ya dan tataba nasa dan a jiya da azumi ya wuni banda bakin ruwa ba abinda ya sha,
Wajen karfe tara likita ta zo da kayan pensement, shiga ta yi ta yi masa ta fito,
Wajen karfe goma docter Rogger ya zo ya shiga ya bashi abincin da ya dace ya ci,
Bayan ya fito ne ya ce" da bibiyu zaku shiga, kuma kar ku yi masa hayaniya da yawa, kar ku saka shi magana, kar ku nuna yannayin damuwa a fuskarku a gabansa,
Zamu kara rike shi na dan lokaci har mu kare yi masa pensement sai mu sake shi, Docter khadija ki zo ki karbi takardunsa baki daya ki kawowa Wardugu,
Musabaha sukai da Wardugu kafin Khadija ta bi bayansa tana faman ta yi ta dawo ta shiga,
Wardugu ne yad dawo daga rakiyar doctern ya nufi dakin da niyar shiga
Marahut ya ce" Wardugu, ka shiga da matarsa mana?
Ja ya yi ya tsaya , a hankali ya waiwayo, da hannunsa ya yi mata nuni da ta shiga,
Da sauri ta mike ta tafi ta kama kofar a hankali ta tura ta shiga inda wardugu ke biye da ita a bayanta,
Tunda suka shigo ya tsura masu ido gabansa ya fadi, kunyarsu ya jo ta lulube shi, wato dai a duniya bashi da gatan da ya fi Wardugu da ahalinsa, ya san yanzu zai ji haushinsa a yanzu, aman ya tabata daga baya idan ya ji dalilinsa, zai fi kowa murnar hakan
Murmushi ne shinfide a fuskarsu har suka karasa kusa da bed din da yake kwonce,
A hankali Wardugu ya karasa kusa da shi ya dan rage tsayinsa,
Hannunsa ya kama ya damke musabaha da nuna farin ciki,
Agaishat dake tsaye ta zagaya dayan gefen ta taho kamar zata kwonto gefensa,
Ido ya zaro yana dubanta, hannunsa ya dago yana son tsayar da ita,
Ja ta yi ta tsaya tana sakar masa murmushi,
Tsoro ne ya kama shi, me hakan ke nufi? Jikinsa ne zata hau?
A hankali ya kai dubansa wajen Wardugu, duda yana halin rashin lafia, duda ya tabata A wannan lokacin wardugun na cikin farin ciki, aman abin ya daure masa kai,
Murya ciki ciki ya samu a hankali ya ce " War, bababaka ga message dina ba?
Wardugu ya ce" sakon wasiyoyin har a wayar ka turo min ko? Allah ya shirye ka.
Mu.azam kam kasa cewa komai ya yi, ya sakar masu murmushi shima, a haka har suka gama ganninsa sukai masa salama da fadin sai kuma shigar gobe dan sau daya tak zasuna leka shi,
Nan suka wuni a ranarma, sai a wannan ranar da zasu tafi Khadija ta bi su, rabonta da gidanta tun fitar da Mu.azam da aka yi,
Suna zuwa ya sauke su ya yi tafiarsa masaukinsa
Bayan gama al.adunsa na yau da kulun ya mike saman bed hankali kwonce ya shiga wayarsa,
Whatsupp ya fara shiga, nan ya nutsu ya yi ta yiwa mutane response kan message dinsu, harda su voice,
Yau kam Basma ta ja ra.ayinsa, dan ya ga dan kokari harda su voice,
Shiga ya yi ya kunna voice din nata yana saurara,
Kansa ya girgiza yana murmushi kafin a fili ya ce" Mata kennan,
Fita ya yi ya shiga wajen message dan daukan number da sergent ya turo masa na mutumen da zai canzawa su Mu.azam gida, dan angiwar batai masa ba,
Nan ya ga message din Mu.azam har guda tara,
Shiga yayi yana fadin" shi kennan tun ina Niger ya tura min wasiyoyi dan ya kashe ni lokacina bai kai ba ko?
Murmushi ya yi yana mai jin nishadin da ya kwana biyu bai ji ba tunda aka yiwa Mu.azam aiki,
Message din ya fara karantawa kamar haka
*Na yi shigar wuri, sauri sauri nake na dandanna zakin aure kafin na tafi*
*Ni mai laifi ne, ban san ya zaka dauki lamarin ba*
*Kar kai hukunci cikin fushi, kamar yanda na jima ina neman shawara da bin lamarin a hankali , ban aikata ba sai da na yi zurfin binkice da neman zabin Allah*
*An ce abinda ka ji hankalinka ya fi karkata ya fi kwonciya idan ka kasance ka barwa Allah zabi ta hanyar yin stihra, Wardugu a kulun na kwonta da barwa allah zabi na farka wannan dai shi ne zabin*
*ban rainata ba, hasalima na sota fiye da tunaninka, sai dai a lokacin ban gani ba, sai da muka dawo na fahimta*
*Wardugu, gagawa na yi, na yi gagawa, na yi mugun gagawa, ka yafe min*
*ni wani sadaukarwa na tabai maka? Ka mini da yawa wardugu ciki harda kudin karasa karatuna, ka mini dayawa*
*Wardugu, na bata a rubuce, shaida, zan kuma turo maka.....Ni Muhammad Mu.azam na sawakewa matata Agaishat aurena dake kanta, wato na tsinke igiya daya cikin uku, ba dan ta min laifi ko wani abin ba, zamanna da ita ne ya kare*
Daga nan Wardugu ya tsaya a bin messages din Mu.azam wanda sauranma na ban baki ne,
Wayar ya saki ya mike tsaye cir daga kwoncen da yake,
Gabansa ne ke wani irin dokawa , hankalinsa ya tashi,
Wani irin ihun bakin ciki ne ya saki wanda da a lokacin Mu.azam na a gabansa ba abinda zai hana ya shake shi har sai ya shaka masa kanshin mutuwa,
Daga shi sai singiletin nan ya fito rai a mugun bace hankali a tashe ya karbi kys dinsa ya fitar da motar a garaje ya.......
Comment comment
π«π«π«π« *BAK'A CE* π«π«π«π«
https://www.facebook.com/Idan-rana-ta-fito-writers-association-114558343535568/?referrer=whatsapp
*☀IDAN RANA TA FITO WRITER'S ASSOπ€* ____________________________________________
*Fad'akar da al'umma tare da nishad'antar da masoya shine fatanmu*ππ€π»π
Na
*SAJIDA*
5️⃣8️⃣
Tuki yake na garari, ba bin doka , ba tsare iyakar gudu da mota a cikin garin paris, wanda hakan ya saka motar police bin bayansa tana mai nunin ya tsaya aman fir ya ki ya tsaya,
Bai zame ko.ina ba sau gidan Mu.azam,
Yana fitowa daga motar police din ta fito da sauri tana mai nuno shi da bindiga da fadin ya tsaya ko ta harbe shi,
Hakan ya janyo hankalin daidaikun mutanen dake anguwar, wasu na dan lekowa ta takarsu, wasu na fitowa dan ganninnko barawo ne aka biyo har anguwarsu? Ciki kuwa Harda Khadija da ta ji haya hayar ta yi yawa,
Rai bace ya ja ya tsaya ya juyo yana mai saka hannunsa cikin aljihunsa na wandon dake jikinsa hakan ya saka ta kwala karan ya tsaya kar ya kara wani motsi a yanda yake!
Tsayawa wardugu ya yi, dan ya san in ya kara motsin a hakan hukuncin harbi ya hau kansa,
Da gudu ta karasa tana fadin ya daga hannayensa sama,
Kansa ya girgiza da yaren french ya bude baki rai bace ya ce" sunana General Wardugu Marahutt, ki barni na ciro maki shaidar hakan, kar ki saka min hannu a aljihu!
Ya karasa yana mai kuwa a kanta,
Da sauri ta ja ta tsaya daga niyar caje aljihun nasa ta dan ja baya still dai bata sauke bindigar ba, ta shishiryawa ko ta ware ko ta walare,
Ciro mata baje dinsa ya yi ya mika mata a dake,
Da sauri ta karba ta karanta, ta ga hoton sama da komai,
Da sauri ta sara masa, domin karatun da wardugu yayi na bashi power a kasashen wajema ba a iya niger kadai ba, dan haka ta bashi hakuri tana mai fada masa ta biyo shi ne daman dan ya taka dokar fice ka.idar gudu a cikin gari
Karba ya yi ya juyo inda itama ta shiga magana da wayar hannunta tana fadin shikennan kar a turo mata kowa General Wardugu Marahut ne na Niger .
Ko kallon Khadija dake masa magana bai yi ba ya shiga gidan ya karasa ya shiga danna karaurawar dakin ba tare da ya bari ta numfasa ba ya ci gaba da dannawa,
Dirowa ta yi daga bed, kayan baci masu santsi sakaku ne a jikinta dogon wando da riga har gwuiwa, kanta ta kunce shi ya bazu a gadon bayanta sai turaran ruwa da ta shafa a jikinta ta kwonta ta huta bacin da bata yi ba wannan karan haka ya firgitata,
A firgice ba tare da ta tuna da wani rufe kanta ba ta fito da gudu gudu ta zo ta bude dakin
Bata shirya ba, bata san zata ji ba, kai batama san wai hakan zai faru ba sai jin saukar wani fitinanen, gigitacen hautsinanan mari da ta yi imanin da bata yi fitsari kafin ta yi shirin kwonciya ba da ta sake shi ba wani ja.
Jinta da ganninta ne suka dauke na wani dan lokaci kafin take samu su dawo, a tsorace ta shiga ja da baya jikinta ya kwashi bari tana dubansa ba tare da ta yi masa magana ba, Khadijama a tsorace take biye da bayansa tana mai dora hannu a kai da fadin" Wardugu?
Wardugu da har jikinsa ke rawa shima na bacin rai ya ce" ashe ya sake ki kike zaune a gidansa? Wannan wani irin natacen so kike masa da har zai sake ki , ki ci gaba da zama a gidansa kina shan ruwan gidansa? Tir tir tir da wannan zuciyar Agaishat sai yaushe zaki fadi cewar ya sake ki? Ko jira kike ya dawo ki lalabe shi ki bashi hakuri ya mayar da ke? Tambayarki nake kike kallona tamkar kin samu sabuwar halita?
Bakinta na rawa tana kankame jikinta dan har lokacin marin na ratsata, sannan wani mahaukacin tsoronsa ne ya diro mata wanda bata taba ji ba, a yanda ya zo bata taba ganninsa daga shi sai yar rigarnan ba, ga abin bacin rai gaba daya wani yannayi nasa dake boye sai ya bayanna, kirar jikinsa, jijiyoyin jikinsa, gashin kansa ba a nitse ba aman a waje guda sama saman ne ya tatashi,
Bakinta na bari ta ce" ban ban gane me kake nufi ba Ya Wardugu, ban gane me kake cewa ba, wa aka saka? Me me
La ferme Agaishat, (churup Agaishat) ki min shiru kar ki fada min karya a nan, bai baki takardar saki ba? Ko don son da kike masa zaki ki gwadawa ne? Na tashi na je gidanku mahaifiyarki ta damkan amana gashi ba.a je ko.ina ba har na ci? Ina takardar da ya baki tun kafin na karya ki gida biyu!?
Zubewa ta yi kan gwuiwoyinta ta hade hannayenta inda tuni kuka ya kece mata, tana kukan ta ce" sai nake jin kana nufin kamar mijina ya sake ni? Ya sake ni? Me na masa? Yaushema aka yi auren da har ya mayar da ni karamar bazawara? Wani umarninsa na taka? Sannan ni dake zaune a gidansa ban san da ya sake ni ba? Har aka tafi da shi asibiti *yana shigowa har dakina*,
Ido Wardugu ya rintse tare da shiga wani tashin hankalin, yana shiga dakinta? (Kalma mai fasara biyu),
Katseta ya yi ta hanyar fadin" bai baki takarda fara ba?
Kai take girgiza cikin yannayin firgici kafin ta tsaya tsak,
Mikewa ta yi da gudu ta fada dakinta ta bude akwatinta ta ciro takardar da ta adanawa Mu.azam wace a iya sanninta da shi ita kadai ce takardar da ta taba wani hada su,
Jiki na bari, tana jin kamar ta kifa ta karaso ta mikawa Wardugu takardar inda ya bude ya karanta,
Tsaf takardar saki ce Mu.azan ya dankarawa yarinyar da suka dauka suka wanke suka bashi, a cikin kasar da bata san kowa ba sai shi, a lokacin da ta shaku da shi, sai wata yar takardar a hade da dayar inda ya rubuta" Agaishat, ki yafe min, ina son ki ba dan bana sonki ba, sai dai hakan da na yi shi ban yi kai tsaye ba. *Ina son ki*,
Dubansa ya kawo kan Agaishat dake tsaye tana jiran karin bayani daga nesa kadan da shi , sai khadija dake kukan gannin rashin dacewar abinda Mu.azam yayi duda kuwa da hakan na iya mata dadi da a lokacin da bata san su waye Wardugu a rayuwar Mu.azam ba, aman a yanzu da ta ga waye Wardugu, ta kuma ga irin halacinsa sai ta ji ta shiga wani yannayi na rashin jin dadin abinda abin kaunarta ya aikata, duba da irin yanda ran Wardugun ya baci sai hankalinta ya kara tashi,
Murya dake ya ce" fice mu tafi,
Ido ta zaro tana dubansa kafin ta shiga yarfe hannu, murya na rawa ta ce" ina son sa, ina son mijina, ka hashi hakuri ya maidani dakina, ba zan kuma yin abinda na yi ya sakenin ba, ba zan yi ba, Wardugu daga aure sai a sake ni? Me Anna zata ce? Me baba sofo zai ce? Ya zasu yarda da wannan abin? Wardugu ina son sa,
Wardugu ya dan saki hanya ya nuna mata hanya fuskarnan a hade tamkar ya shaketa haka yake ji, dan rashin sannin ciwon kai wai a bashi hakuri,
Da sauri ta ratsashi ta fice tana waiwayen Khadija dake son ta baiwa Wardugu hakuri aman tana tsoro,
Itama murya na rawa ta ce" Wardugu toh bari na dauko mata hijabinta fan Allah, kafin na je na same shi asibitin,
Ja ya yi ya tsaya, juyowa ya yi yana dubanta kafin ya ce" *Tana da gata fa, itama yar dangi ce, ko bata da kowa a duniya tana da ni, idan kin je asibiti wajen masoyinki! Ki fada masa na gode! Na juya nigeria zan dawo gannin jikinsa in sha Allah, zancen hijab ki bar shi, wannan suturar ta jikintama zan dawo da ita, na haramta mata du wani abinda zai fito daga hannunsa komai kankantarsa! Mu.azam da Ni Wardugu yake magana!*
Haka ya tafi ya bar Khadija tsaye cikin tashin hankali ya shiga motar ya jata a tsoyace yana tukin irin na dazu inda Agaishat ta hade kanta da gwuiwarta ta afka duniyar tashin hankalin da ya fi na kulun, wai ita Agaishat har namiji ya nuna mata hali tun ba.a je ko.ina ba? Ita Agaishat, itace aka dankarawa sakin da ba laifi? Ita agaishat itace zaune a gidan kato da sakinsa a kanta tana wadaga tamkar gidan ubanta? A yau ta karasa yin tir da rashin ilimi, a yau ta ji duniyar ta fice mata a rai, a yanzu da aka ce ya saketa ta ji wani kaunarsa ita kuwa, ta shiga tsaka mai wuya ga Wardugu yaki koda kallonta bale ya nuna mata wani yannayi na tausayawa, ya tafi a bacin ran irin wulakancin da Mu.azam ya yi masa da tunanin yanda zasu kwashe da Ayya,
.........bai koma hotel ba sai da ya je ya samu takardar komawa Niger ta mutun biyu kafin ya juya Hotel da ita!
Timiya
Tafiar su Anna tafia ce mai nawa, domin dai ana fitowa daga cikin Timiya saman rakumi ne, gashi Anna sai da ta dauko baba tsofo du kuwa da irin yanda ya kiya aman fir itama ta kiya sai da shi ya saka aka yi dabara aka dora shi amale tun yana tsugune , maza hudu suka tatare har amalen ya mike kafin suma sauran su hau nasu su kama hanya,
Tafia ce mai tsayi idan ba.a gagawa, tafiar sahara ga tarin yan rakia da guzurinsu, dan jariri kuwa a nade a cikin tufafi mai laushi a jikin Anna rata yi masa goyon gaba,
Ana tafiar ne ana tsayawa a baiwa baba Tsofo abinci da ruwa hakan ya sa suka wuni cir kafin su shigo gari
Dogarai ne suka juya dabrakuman inda su kuwa suka dauki motar sarki daya kwal mai baya bude suka nufi garin Agadez
Ba su su shiga garin ba sai da isha ta yi, suna zuwa direct gidan sarkin suka je
Bayan an sauko daga salar isha.in ya kara ganawa da sarki, wanda ya bukaci gannin Anna,
Anna na shiga Sarki ya mike yana dubanta, kamar gatanan a fili ta mahaifiyarta, mace mai mutunci da mutunta mutane,
Ba bata lokaci ya hada vidio call da aminin nasa,
Dagawa ya yi yana mai saka gilashinsa na karin gani yana fadin" Sarkin agadez da kansa
Sarki ya amsa yana murmushi mai kayatarwa kafin ya hasko masa Anna dake tsaye
A zabure ya mike tsaye yana mai......