Haka walyn ta yi gum da bakinta, domin ita dai bata iya rarashin miji wai dan ta yi masa laifi komai girmansa kuwa,
Wannan laifinma da ta tafka masa, ta bi ta hanyar da baya iya ja an maidota, da baya kulata ta kuma bi ta hanyar da koke koke an yi masa tsawa, hakan ya sa ya dawo kulatan aman da nashi takun, domin idan zai yi aurataya da ita sau dubu sai ya saka roba , yana gamawa yake tashi ya bar mata dakin koda nasa ne, baya irin na da ya rungumeta a jikinsa,
Karara nisa ya shiga tsakanin su, wanda du macen arziki ta lira da irin nisan nan tsakaninta da mijinta toh fa hankalinta zai tashi ta shiga neman hanyar sulhu da gyaran abinda ya hadasa haka, aman ina, ta ci gaba ne da bibiyar dukan motsinsa, tana kaiwa du wata mu.amalarsa da mace izgili, ta ci gaba da yawon bukukuwanta, ta ci gaba da kawance da kawayen banzan da basu zauna suka baiwa cikinsu bama bale su yi tunanin gyaran aure wai har a je ga biyayar miji,
Ita dai ta fito a ganta, mawaki ya waketa, ta koma gida gida ta tarar da miji ya leleta, (Anya kuwa? Abin da kamar wuya gurguwa da auren nesa),
Haka ya gama ya sauka ya fito daga dakin da tawul a kugunsa ya nufi bayin falonsa,
Juyawa ta yi saman bed din abinta tana mai jin wani iri a jikinta dan zafi, ta jima sosai kafin take mikewa ta fito dan tafia dakinta, nan ta gansa zaune saman cafet ya lumshe idannuwansa,
Tsai ta yi ta tsura masa ido,
Tunda suka yi aure ya kasance cikin tsaf tsaf, ko dan sun raba bangare suna haduwa lokaci zuwa lokaci ne? Ba zata ce ga ranar da ta ganshi da kazanta ko ta tarar sumar kai ce ko saje bale jiki,
Yana da kula da adininsa, baya wasa da sallah da ibadun da yake a bayanne da wa.inda yake yi a boye,
Yana da fitina, rigima, tashin hankali aman fa idan an shiga hanyarsa, tabas bashi da saurin hadiye wulakanci ko.na waye, aman yana da kawar da kai, abinsa ba zai hada ka da shi ba, uwa uba mijinta tsarare ne, Allah ya yi halita mai nitsa zuciya , ko a cikin kawaye idan aka tashi maganar dogon yaro ga fari ga farin jini ga yayan banki sai an fara ajiye masa gaisuwarsa kafin a hangi wani dan tafe yake da zamaninsa, sai dai kash zuciyar nan tasa na tayar mata da hankalinta, zata so ya zama yanda take son ya zama, da ta yi ihun ta more miji,
Kafa ta saka ta fice a falon , bata wani damu da irin zamansa, da dalilin zaman ba, ita dai abinda ta saka a ranta zatana zuwa ta kawo masa kanta, ya samu nitsuwar da ba zai dubi wata y'a da wannan muradin ba, sauran zata ji da su , dan ita dai ba aikin fari take ba na baki ba, tana kwashe salarry kafin a yiwa ma.aikatan gwanati biya, tana shiga babar mota tana zuba zinaria ta saka shada, damuwarta Wardugunta, zako ta ci uwar uban du wata mai rawar kan da zata rabar mata miji!
Basa zama a kwanakin nan,
Shirye shirye suke tun karfinsu,
Ba wai wani yawon kaiwa yan mata cati ko wani gayace gayace ba, aa siyaya ne suke a hankali na abubuwan da zata bukata a gidan miji inda matar mahaifin Alhinayett ke saka su a hanya da zuciya daya tana mai basu kyawawan shawarwari,
Ayya kam ta hakura da jajen ita gaskiya a bar fitar mata da y'a gannin fitar da y'ar nata na kawo ci gaba ta hanyar kara iya mu.amala da mutane kala daban daban da take gani a wajen siyaya ne, a saloon, da wajen gyaran jikin da Alhinayett ta biya suke zuwa tare a yi masu dan kuwa itama tsale ta yi ta dire kan tana so ,
Sukan tsalake kwana biyu basu fita ba, idan aka ce zasu fita kuwa Ayya kanta har mamakin itin tsararen shirin da y'ar tata ta koya,
Ta iya saka kaya masu saka jiki a nutsuwa, ta fi nacewa atampopi dinkunnan dogayen rigunnan zamani masu tsari irin na yayan yan gayu ba masu fitar da tsiraici ba,
Wani sa.in takan zurmuka hijab dinta a saman shigarta mai kyau da birgewa, wani sa.in kuwa sai ta yafa dan gyalenta ,
Idan ka ganta ba zaka taba kawowa ta taba aure ba, hakan ya saka du fitarsu sai ta samu mai tayawa dan ba karya dorinar kyau ne da ita ga dorinar ado, kaya saka su kawai take su yi mata das ba ciko ba acuci ko daya.
Alhinayett na lure da irin kokarin da mahaifinta ke yi, dan haka ta kwatanta zuwar masa da shawarar tana da yan kudadenta a banki, idan ya amince ra kawo ya kara ya yi mata gadon, sai dai ya yi murmushi ya ce" Alhinayett, ke dai Allah ya yi maki albarka irin dawainiyar da kike da mu baki daya, aman ba zan amshi kwandalarki ba, zan yi kamar yanda na yiwa kannun ki, ki je kudaden ki ki kara abubuwan nan naku na zamani na gayu ,
Haka ta mike ta yi godiya ta fito, itafa tausaya masa take domin nauyi ne ba kadan ba a kansa, gashi da y'aya mata masu cikuluftun yau a sayi kaza gobe a sayi kaza, gashi dangi na kauye du a kansa suke, ta so ya karba ko ba komai zai rage wasu abubuwan aman ya kiya gashi aure har sauran sati biyu,
Zuwa ta yi dakinta ta tsala wanka ta saka abayarta baka sannan ta daura nikaf a fuskarta ta fito ta yiwa yan gidan salama kan zata je wajen gyaran jiki da karbo dinki da kai wasu dinkunnan, wai a nan du irin tarin suturun da take saya ne , lefe an ce sai gobe za.a kawo,
Tuki take hankalinta kwonce a yar karamar motarta ta nufi gidan su Wardugu dan dauko kawalin nata wace take kanwa a wajenta kuma kawar shawara dan a duniya nitsuwa da hakuri Agaishat ya saka ta aminta da ita,
Tana tsayawa ta bude ta fito sai jin karan shigowar messages ta yi a wayarta rututu,
Dakatawa ta yi ta bude pos dinta ta ciro wayar inda ta maida hankalinta wajen tagar Agaishat tana hangen ko zata ganta ta nuna mata ta zo fa,
Tana buda wayar ta shiga, wata sabuwar number ce ta Niger, dan haka ta shiga cikin messages din,
Hotunnan ne , hotunnan gadaje, kujeru, table din tv, na tsakar daki, na cin abinci, show glass, kowane da katon tambarin katon butik din da ake siyar da su, irin kayan wajen nan ne,
Murmushi ta yi tana fita a wajen ta ayanna a ranta yo wannan ko gidanmu za.a siyar ba zai kai kudaden wadinnan kayan ba, ni me ya kai ni?
Murnushi ta yi ta shiga gidan,
Ai kuwa ta shirya cikin wata doguwar rigar atampa A yi mata dinkin mai dogon hannu aman a bude sosai dan kuwa du hannun ya cinye sauran atampar,
Ta yi daurin dan kwalinta da irin carto din nan baki, ta dan fitar da yalwatacen gashin kanta daga kasan dan kwalin,
Kunnenta dauke da yan kunayen azurfa mararsa nauyi da fadi sai dai tsayi,
Hannunta dauke da dan zobe karami na azurfar shima,
Fuskarta ba wata kwaliya sai dan kwalin da ta saka sai lebenta na kasa da ta shafawa dan jan baki kalar ja aman ta murje shi ya kasance kadan ne ya fito a jikinta,
Kamshi take bazawa ta dora kafarta ta dama saman ta hagu tana dan kadawa ta cuno baki wai Ayya ce ke fadan bata son saka takalma masu dan tsayi ita kulun sai plat kamar wata tsohuwa wanda ko ita Ayyan na saka mai tsayinta idan ta yi ra.ayi, dan haka ta karbe katon hijab din da ta dauko da takalmin ta koma ta dauko mata wani mayafi fari kal mai shara shara da takalma masu dan tudu farare da pos fara kar mai igiya yar doguwa ta dawo tana fadan sai kace wata datijuwa ta wani kinsima hijab kulun kulun? Ke da nake so kema na wanke ki abina na maki aure mai sunnan aure?
Alhinayett ta yi dariya tana kallon yanda ta daura takalman a kafarta tana cuno baki ta dauki pos din ta saka wayarta a ciki kafin take juyawa wajen Ayya ta sakar mata murmushi ta ce" Ayyana, ni ba zan yi auren ba, na hakura da auren, kin ga ba kin mini auren ba aman na dawo maki? Kawai mu yi zamanmu ,
Ayya ta gala mata harara ta kawar da kai irin ta shakan nan bama zata bata amsa ba, dan haka sukai mata salama ta bi su da adu.a suka fice a motar Alhinayett din.
Tafe suke suna dan hira inda wakar guitar ke tashi kadan kadan a motar suna bin mawakin Buzun mai sunna Bombino bisa wakarsa ta *Arakkham nah*,
Wayarta ce ta dauki kara dan haka ta samu waje ta dan tsaya,
Tana dagawa ta ji yana cikin kayaniya dan haka bai tsaya sun yi wata doguwar gaisuwa ba ya isar mata da sakon inda zata tardo shi yanzu yanzu ,
Da to ta amsa ta datse kiran tana duban Agaishat ta ce" Wardugu ne, yace mu tarda shi shagon nan na siyar da kaya yanzu ko lafia?
Agaishat ta tsura mata ido bata ce da ita komai ba har ta tada motar ta dauki hanya, Agaishat kam na so tace da ita dan Allah ta ajiyeta ta je ta dawo sai dai ta san bama zata saurare ta ba , dab gaja ta tsurawa hanya ido,
Ita ba komai ke rikitata ba sai irin yanda gabanta ke faduwa idan ta hadu da shi, ko dan ya cika fada ne? Wani lokacin yana da saukin kai, aman yawancin lokutan ya cika fada da daure fuska, ita kuma tsoron hakan take.,
Sun jima suna tafia kafin ta tsaya kofar tankamemen shagon kayan dakin,
Baki da hanci Agaishat ta saki tana duban wajen da suka tsaya,
Alhinayett ce ta fara fita a motar ,
Gannin Agaishat bata fito ba ta leka dan gannin abinda ya hanata fitowa,
Agaishat kamar an mintsineta ta juyo wajen Alhinayett ta ce" ke gala, ko dai mun bace da wajen ne? Na ji kin ce yana gudan siyar da gadaje , ke kuwa na ga kin kawo mu wannan waje dake shige da manyan ma.aikata?
Alhinayett ta bushe da dariya ta ce" Agaishat yanzu wannan ne ma.aikatar? Ba na ce da ke ba idan har kin ga waje ki ringa karantawa kar ki yarda ki nuna wani kauyanci ba?
Agaishat ta shafe gaban goshinta ta ce" hm, ke dai bari, yo ni ta karantawana nake? Wajen gadaje kayan katako an saka su a wannan waje an kilace? Lale du abu idan ya kasance yana da daraja zaka ga an kilace shi,
Alhinayett ta zagaya ta bude mata motar tana fadin malama fito kar ya kagauta ya yi mana abinda ba shi ba, mu je mu fito mu yi tafiarmu
Tana fitowa ta gimtse dariar da take yi ta kama kanta ta bi bayan Alhinayett,
Sai da suka je wajen wani madubi da mutun da tsaye ya saka dan injin caje mutun din nan ya caje su kafin suke shiga cikin boutik din,
Gaskiya ne, idan har ba kai din dan gayun bane, toh fa ka san wajen, in ba haka ba kana shiga kana iya faduwa fan kallo,
Wannan shi ake kira murmushin amarya, kukan iyaye kennan,
Tafdi, haduwa, karshen haduwa, tsari, kaya ne na manya,
Saman luntsumemiyar kujera suka hango shi zaune da mai wajen baki daya,
Yau kam shada ce jikinsa mai ruwan maroon , an yi masa tazarce kawai, ba.ai mata adon komai jikinta ba sai kace karamar shada, abinka da an wanku an jiku sai ta yi bada wani samfari a jikin nasa, ga wata hula da ya kafa yar daidai da kan nasa da ra kuma hau da kayan jikinsa,
Kai wardugu mai kyau ne,
Hira suke da mutumen, da alama ba yau ya fara zuwa wajen ba, koma sun san juna ,
Yau baki dayansa annuri yake fitarwa, inda suka tsinci muryar Elhajin na fadin" Oga, ai sai ka fada min gaskiya kawai zaka gwangwaje ne, kai zaka dauki amarya haka? Gaskiya Oga kana ja,
Wardugu ya yi murmushi yana girgiza kai, daidai sun karaso ya ce" aminiyata ke aure ba ni ba, Alhinayett fada masa ko ya bani lafia,
Yana ganninsu ya juya wajen yaronsa ya ce" kai Idrissa, zo kakabe kujerun nan maza, ai ko yanzu aka ciro su a leda sai an goge domin hajiyoyin ne da kansu,
Alhinayett kawai ta yi murmushi tana duban wajen da za.a goge masu wai, wajen sai daukan ido yake a hakama, aman dan da mai ajin suke tare sai suka caje inda suke har aka zo aka goge masu wajen zaman suka zauna,
Gaishe shi suka yi,
Wardugu ya amsa da lfy, kamar yanda ya saba amsa gaisuwa a datse,
Duban Alhinayett ya yi, a kasan ransa kuwa ya ji kamar ya shige su da fada, wai ita ba zata daina yawo da yarinyar nan ba? Ba zata barta a gida ta yi zamanta ba? Han,
Katon albom aka kawo masu aka ajiye,
Dubanta ta kai itama wajen Wardugun da yannayin tambaya,
Wardugu ya ce" ki bude ki zabi wa.inda sukai maki
Kallon kur take masa bata kawar da fuskarta ba dan neman karin bayani ,
Mai shagon ne ya ce" hajia, ai idanma a nan basu yi maki ba sai na yi kira su turo mana sababi ki zaba cikin sati zaki ga kayanki,
Sai da ya gama magana tana dubansa kafin ta maido dubanta wajen Wardugu,
Fuska ya hade ya kawar da kansa,
Ajiye litafin ta yi ta katsa kusa da shi,
Murya ta rage ta ce" Wardugu, me kake nufi?
Wardugu ya ce" ban gane me nake nufi ba? Kayan daki zaki zaba Alhinayett mana, kin san minti nawa na yi a wajen nan ? Ina da taro fa ,
Alhinayett ta juyo da kallonta wajen Agaishat, gani ta yi ita kawai ta tsurawa wata agogo ido mai ruwan dawisu sai kyali take ta hadu karshe,
Dubanta ta maido wajensa, hannayenta ta hade waje guda ta ce" Warsugu, kennan zagin nawa da ake cewar na makale maka wai kawance dan dai na tsotsi abin hannunka ne zai tabata? Wardugu, kayan dakin ka rasa a inda zaka siya min sai a wannan tsadaden shagon da idan ba isa ka yi ba zaka saka kafarka bama koda dan kalo ne? Wardugu Abanna me zai ce? Wardugu wahalar ta isa haka, dan Allah ka rufa mani asiri ka bar maganar kayan nan ,
Wardugu ya zaro ido da mamaki, murya a kausashe ya ce" ni zaki rainawa wayo Alhinayett? Ni zaki fadawa irin magangannun nan? Ni?
Da sauri Agaishat ta juyo da dubanta wajensu, mikewa ta yi tsaye domin ta ga ya nuna Alhinayett da yatsa alamun ransa ya mugun baci,
Muryarsa ta kuma ji ya ce" walahi yau da wata ce ta mani irin haka sai na dauke mata hakora kafin ta karasa maganar, an gaya maki ni sakarai ne mai daukan jita jitan mutane? Ko qn gaya maki idan ban yi magana da Aban ba zan yi gaban kaina? Malama da na kiraye ki ki zaba dan na san halayenku mata da shegen tsare tsare ana iya zabar maki ki ce basu yi maki ba! Ki zaba ku bace min da gani kuma idan na kara gannin wacen ba hijab sai na kade ku!
Hawaye ne ke zubar mata a idannuwanta, wasu na korar wasu, rayuwa kennan, ita ta taba tunanin zata hau irin wannan gadon? Wajen Agaishat dake tsaye tana kikifta ido ta dawo da sauri ta dauki litafin ta mika mata ta ce" zabar min,
Agaishat ta dubeta ta canza harshe zuwa yaran buzanci ta ce" me kuma mukai masa da zai kade mu? Yaushe ne zai kade mun? Kuma muna cikin motar za.a iya kade mu daman? Kin ga Ayya amanata ta baki idan kika bari ya kade ni ke da ita ne.
Alhinayett ta ce" Agaishat kin manta yana jin yarenki ne?
Da sauri ta zaro ido, ran harga Allah ita ta manta da yana jin yarenta, dubanta ta waiga wajensa ta ga yana danna waya, da alama bai jita ba, dan haka ta sauke ajiyar zuciya ta ja Alhinayett suka kara matsawa tana duban har yanzu ta ki yin shiru,
Hannu ta dago tana dubanta ta ce" to wai kukan fa?
Alhinayett dake shasheka ta ce " Agaishat, wai na zabi kaya fa yace?
Agaishat ta ce" to menene?
Alhinayett ta ce" Agaishat, ba zaki gane ba,
A wajen nan kayan masu tsada ne na yayan gata, sun fi karfina, ni wa? Yar wa?
Agaishat ta yatsina bakinta wanda du idan ta yi sai dimple dinta ya loma, ta karbi litafin ta shiga dudubawa,
Hankalinta kwonce ta kallo tana ta santi a ranta, a fili ta ce" kin ga ni na rikice, karbi ki zaba,
Alhinayett ta karba ta ja hannun Agaishat har gaban Wardugu dake dan zantawa da Elhaj, duda ransa a bace aman yana amsa shi,
Suna zuwa Alhinayett ta ce" War?
Wardugu ya dubeta bai bata amsa ba,
Ta ce" ka yi hakuri, na tuba👏🏻,
Idannuwansa ya dan lumshe ya bude a kansu,
Alhinayett ta turo Agaishat gabansa, irin sosai ta matso kusa da shi domin turota ta yi da biyu, ta ce" Agaishat, ki taya ni godiya wajensa, bani da bakin gode masa ki kama mani,
Agaishat ta zaro ido ta juyo da dubanta wajen Alhinayett , kafin take juyawa kusa da shi,
Kamshin turaransa ne ya saka ta fara jin wani irin dadi a ranta,
Wardugu dake kallon kasa kasa ya shiga wani yannayi na jinta gashi gata,
Agaishat ta shiga kame kame tana dan shafa gaban goshinta,
Dago idannuwansa ya yi ya zuba mata saman fuskarta, yanda take shafa fuskar tana dan waige , tana kuma kallon wajen da yake abin sai ya saka shi nishadi, irin ta daburce ne? Ai kuwa sai ya saki murmushin da ya nuna fararan hakoransa,
Yan wushiryarta ne suka bayana na sama wajen hakoranta biyu da suka dan yi kasa kamar na zoma sai dai basu fito sosai ba sun bada wani kala mai birgewa da tsari ne, suka bayanna, ta lumshe manyan idannuwanta ta bude ta ce" Mun Gode, Allah ya kara arziki, Allah ya kare ka a duk inda kake, ya baka kaima masu yi maka domin Shi👏🏻,
Bai iya amsata domin yakan zama wawa a duk lokacin da suka samu kusanci irin haka, shi ya sa ya daina yawan zuwa gidan Ayya, domin a gidan Ayya wani lokacin yana tarar da ita tana zuba tabara shi kuwa uwa wawa sai ya saki baki da ido yana rakata da kallo yana sakin murmushi 🤦♀🤦♀🤦♀🤦♀🤦♀
Paris
Alhamdulilah, jiki ya yi kyau, a hankali har ya fara dan fita daga gidansa yana gannin gari ya koma,
Khadija dake fama da shi ta fara kosawa kan maganar aurensu aman abin mamaki ya nace aa, ba yanzu ba, shi ba zai iya auren da ba Wardugu ba, shi sai wardugu ya aminta zai iya auren ko wace mace!
Takan ji takaici da gannin bai san darajarta ba, sai ta nuna ta yi fushi , sai ta kasa ta dawo ko dan ya ci abinci dan idan bata nan baya ci!
Kamar yau yana zaune yana kallon fulawowin tsakar gidansa,
Iska mai dadi na busa shi ya.....
🐫🐫🐫🐫 *BAK'A CE* 🐫🐫🐫🐫
https://www.facebook.com/Idan-rana-ta-fito-writers-association-114558343535568/?referrer=whatsapp
*☀IDAN RANA TA FITO WRITER'S ASSO🌤* ____________________________________________
*Fad'akar da al'umma tare da nishad'antar da masoya shine fatanmu*😘🤝🏻😘
Na
*SAJIDA*
6️⃣6️⃣
Kai jama.a ni dai wollah Azumi🙄🙄🙄🙄
Iska mai dadi na busa shi yana mika hannunsa a kai a kao yana dan tsigo fulawar ya sinsina hat sai ta yi laushi sai ya zubar ya kuma tsinko wata,
Tsaye take bayansa tana dubansa, ta dan dauki lokaci kafin ta juya ta shige gidansa ta dauki wayarsa ta dana masa kira,
Ya jima, kai harma ta cire rai da zao daga domin ta kira ta kara bai daga ba , da kyar dai ya daga bai yi magana ba sai dan hayaniyar muryar Alhinayett bakinta ya kasa rufuwa dan murnar abin alkhairin da ta samu na aurenta,
Salama ta yi a hankali na wajen uku kafin yake amsawa shima,
Ajiyar zuciya ta sauke ta ce" Wardugu Khadija ce,
Wardugu ya ce" na gane,
Khadija ta yi tsam ta ce" Wardugu kun san gaba ta fi kwana uku salar mutunma ba.a karba?
Wardugu ya ce" eh na sani,
Khadija ta cire wayar da mamaki a kunenta, kafin take maidawa ta ce" kun sani aman kuke yi?
Wardugu ya ce" ke din wa ya baki damar kirana ki min tambaya irin haka? Ni mace ne da zan tsaya gaba da wani?
Khadija ta sauke ajiyar zuciya ta ce" Dan Allah ka yi hakuri, baya jin maganar kowa idan ba taka ba,
Me saurayin naki ya yi maki? Ya tambayeta kai tsaye,
Wata kunya ce ta kamata, kennan ya san halin da take ciki ko me? Ai tunda ya sani bara kawai ta fito a mutun, ta ce" Wardugu, ya ki maganar aurenmu, yana irgawa Agaishat ta fita a ida, wai shi sai ka yafe masa, dan Allah ka yi wani abu, idanma hada mu za.a yi a yi auren ni da ita in dai zaka yafe masa dan Allah ka yi,
Idannuwansa ya rintse, ya jima kafin ya bude ya furzar da wata iska ya ce" haka yake tunani ko tunanin ki ne?
Khadija ta ce" neman mafita nake,
Warsugu ya girgiza kai yana murmushi ya ce" ki iya da shi kin ji?
Kit ya datse kiran,
Juyawa ya yi wajen da suke, ta daura mayafin a kugunta ta yi tsaye gaban katon madubin dake jikin bed din da Alhinayett ta zama tana juyi suna daria wai ga yanda Alhinayett zatana yi a dakinta ita daya gaban madubi,
Dubansa ya kai wajen Elhaj ya ga yana tsaye shima yana dariar domin tana abin ne gwanin sha.awa,
Ji ya yi ransa ya baci da hakan, dan haka ya karasa wajensu ya ja ya tsaya ya gala mata hararar da ta sakata tsayawa bata shirya ba,
Hankalinsa ya mayar wajen elhajin ya ce" Elhaj sun gama ne?
Elhaj ya ce" sauran su kayan kyale kyalen falon Elhajinmu
Wardugu ya ce" ai su je kawai, sauran a duba tsarin kayanta a hada mata wa.inda zasu yi kyau,
Elhaj ya amsa da an gama ya juya wajen yaransa ya shiga basu umarnin yanda za.a shirya kayan a loda maza a kai adres din Alhinayett wasu cikinsu kuwa ya saka su karasa hada abubuwan da ba.a hada ba,
Alhinayett ta karasa kusan wardugu ta tsaya daf da shi, irin idan tana sin yi masa maganar siri ta ce" War, Mu kam mun yi kasuwa a nan fa,
Wardugu dake dubanta daman ya san magana take da shi, dan haka ya yi mata duban bai fahimta ba,
Alhinayett ta ce" Elhajin nan yana ciki fa,
Wardugu ya gimtse fuska yana dubanta dan ta fara gajiyar da shi sai wana masa magana take, ya ce" cikin ina wai?
Alhinayett ta ce" yaja son Agaishat mana,
Wani irin dago da idannuwansa ya yi ya sauke a kan fuskar Alhinayett dake murmushi tana dubansa irin ta yi da biyu dan ta ga reaction dinsa, aman da yake ya fita iya duniyanci sai ya yatsina fuska ya watsa hannayensa yana mai tausar zuciyarsa ya ce" shi zai iya jimawa da ita ko? Dan kam na gaji da yi mata aure ana sakota ,
Ido Alhinayett ta zari tana rufe bakinta da mamakin Wardugu, ta ce" Wardugu har sau nawa ta yi auren? Ai ko abokin ka da ya sake ta bai ganta a haske ba, sannan bai san ciwonta ba, na tabata du wanda ya dauki Agaishan ayya a yanzu zai yi mata rikon gold ne
Ido ya kankance yana dubanta ya ce" meye zai saka a yi mata rikon hakan? Yarintar? Ko kanantar? Kin san me ke rikita maza kuwa? Mace ginaniya, wace idan ta motsa zata motsa da shi ba yar jaririya ba, shima Elhajin Mubarack din nan nake yi masa duban baban yaro ashe dai yaro ne,
Ido ta kara zarowa tana dubansa yanda ya gama magangannun ya gimtse fuska yana kuma kallonta kafin yake juyawa ya ce" ta yafa mayafin nan a saman kanta,
Tafiya ya yi Alhinayet na kallonsa baki sake, murmushi ta saki kafin take girgiza kanta , ta yiwa Agaishat dake kara kallon kaya magana suka kara gaba,
Ko a wajen gyaran jiki yau da aka fara jika jikin Alhinayett da turare haka ta kara kudin wajen Agaishat itama aka shiga yi mata sak irin gyaran amare,
Tsume tsumen nan da ake basu kansa tana shanye abinta kai tsaye inda Alhinayett ke yi mata kallon ta san ko na meye tunda ta taba aure, hakan ya sa itama ta kama abin da karfi karfi gannin wace ta taba aure batai masa da wasa ita kuwa Agaishat na sha ne dan dadi yake yi mata, ,
Sosai suka wuni cikin farin cikin da Wardugu ya saka su, suna dawowa suka tarar d Ayya a wajen hutunta tana zaune da jarida a hannunta,
Gannin su ya saka ta ajiye jaridar hannunta tana dubansu da yalwatacen murmushi a fuskarta dan yau an yi masu dilka sai sheki suke,
Suna zuwa Alhinayett ta karasa kusa da Agaishat kadan ta duka har kasa kanta na kallon kasa ta ce" Ayya, ina rokon Allah subahanahu wata.ala ya kara rufa maki asiri ke da kika yi silar zuwan Wardugu duniya da mahaifinsa da dukan wani wanda ya shafe shi, ya Allah ya yi maku sakaya da gidan Aljana, Allah ya rabaku da kunyar duniya da ta kiyama, Allah ya.....sai ta yi shiru sanafiyar hawayen dake zubar mata ,
Ayya ta dafe kanta ta ce" ya salam, Ke Alhinayett tashi tashi maza goge hawayen ki, menene haka? Haka Mahaifin ki da da maman ki basu dade da fita a gidannan ba, ke idan bai yi maki haka ba , ni da kaina sai na ga bakinsa irin yanda kuke tare da zuciya daya? Maza daina wani kuka ba yayanki bane?
Alhinayett ta shiga share hawayenta tana duban Ayya,
Ayya ta sauke ajiyar zuciya tana duban Agaishat da ta yi narai narai ta ce" kin ci abinci kuwa?
Agaishat ta daga kanta,
Alhinayett ta dungureta ta ce" ta sha solani dai, bata ci abinci ba,
Ayya ta dafe kai, ta ce" kin ga, frij cike yake da kalolin solani tunda na fadawa Wardugu ta mayar da solani abincinta ya kasance kafin ta gama da ta frij an kawo wasu an cika a frij, du wajen yarar gidannan ki ka duba zaki ga ledojinsu na yawo a ciki, tsorona ya saka mata ciwon ciki gata ba shan maganin zafi ba sai ina tsaye,
Ayya ta karasa tana dafe kanta,
Agaishat ta zauna gefen kujerar da take zaune ta dora kanta saman jikin Ayya ta dora hannunta wajen jaridar da ta ke karantawa ta ce" Ayya, wai mai siyar da kayan gadajen nan ya ce yana so na,
Ayya ta zaro ido tana dagata daga kwonciyar da ta yi kamar mage ta ce" ke kuwa ki ka ce da shi me?
Agaishat ta dubi Alhinayett ta ce" ni kalon sa na yi, kafin nake dan motsa bakina, na kada kaina sai kuma na yi gaba na bude motar Alhinayett na zauna na sada kaina, kin ga ban nuna zumudi ba, ban kuma yi masa rashin kunya ba, ko Alhin
Ayya ta yi murmushi tana duban Alhinayett ta ce" Alhinayett zauna mana,
Alhinayett ta zauna sosai, dan ta lura yau Ayya na yi da ita, ta sake mata fiye da kulun, dubanta ta kai wajen Agaishat ta ce" auta, dauko min faro,
Agaishat ta mike ta nufi ciki
Ayya ta dubi Alhinayett ta ce" Alhinayett, ki yafe ni kan wasu abubuwan da nake nuna maki kin ji? Kin san rayuwa, yau ko Wardugu na dan cikina dole na saka ido a mu.amalarsa da kowa bale mata, gashi a zamanin ku ake kawance mace da namiji, har ga Allah na sha saka shi gaba da fadan ya aure ki sai yace da ni kawarshi ce ba zancen soyaya tsakanin ku, hakan ke saka ni a halin tsoro , idan kika yi duba da tsakanin mace da namiji akoy shedan,
Alhinayett ta gyada kanta tana duban kasa ,
Ayya ta ce " tun yaushe mahaifiyar ki ta rasu?
Alhinayett ta dago da kanta tana duban Ayya, ya aka yi ta ji? Sai dai bata da amsa ta san tunda ta yi mata tambayar toh tana da labarin yanzu, dan haka ta ce" rasuwar mamana , wani soja ne ya kadeta, kuma sojan mahaifinsa ne baban mutun hakan ya saka suka rufe akama ki bin maganar,
Mafarin haduwana da Wardugu kennan, ba wancen labarin ba, domin na je na kai masa kukana, na fada masa komai hakan ya sa ya yi bincike, cikin ikon Allah ya tarbi abin da karfinsa inda ya samu baban Alkalin nan datijo mai sunna *Gukunni* ya zama lauyana a lokacin baban lauya ne da ake shayi , nan ya shige gaba suka hada karfi da karfe cikin ikon Allah suka kada shari.ar , dalilin da ya saka mahaifina ya cirewa Wardugu shamaki da cikin gidan mu, dalilin da ya saka na samu sa.ar zama abokiyar Wardugu, har ake mamakin irin kusancin mu da irin yanda muke hira da Wardugu, kuma duda haka sau biyu yana yi min dukan da ba zan taba mantawa ba , dayan kan karatuna da na so na yi wasa da shi, ya yi magana ya yi magana na kiya har Abana ya bashi damar ya yi maganina, a ranar sai da na kwana asibiti, na biyun da na fara samari masu hatsari, irin yaran nan yayan masu kudi dake hurewa yara kunne, suka so su saka ni a uku a lokacin yana Spain, ya yi min nasiha, ya gwada min ilar abin du na kasa fahimta sai da ya dakar min fata na suma sau biyu , tun daga shi na yi byby da samarinma baki daya sai yanzu Allah ya yi,
Ayya ta girgiza kai tana dubanta kafin ta yi murmushi, ta ce" daga yau ku daina zuwa gyaran jikin, in sha Allah zan karasa maki a gida,
Godiya Alhinayett ta yi ta yiwa Ayya har ta dakatar da ita,
Ayya ta hangi Agaishat tafe da faro ta ce" kin san menene, ina son Agaishat tamkar yar da na haifa a cikina Alhinayett, na yi sake aurenta da na tashi na baiwa yara haka , har ina tuhumar kaina da ni na haifa zan ko yi haka? Ina jin haushin kaina,
Alhinayett ta ce" Ayya, ba maganar sake, abinda Allah ya tsara sai ya kasance a kan bawansa, aure kuma ai lokaci ne , idan ya yi ko a halin yaya sai an yi shi idan kuwa lokacin mutuwarsa ya yo komai so sai an rabu, Agaishat na girmama girmanki a zuci da fili, bata taba nuna laifinki kan komai ba, koda ta san ta yi laifi takan yi murmushi ne tace Ayyana zata min fada, kuma ta je ta kasa barci, kin ga kuwa karara shakuwa ta iyaye ta bayana a lamarin,
Ayya zata yi magana ta karaso dan haka ta yi shiru, ko ba komai bata so ta san irin girman son da take mata dan karta sangarce mata, Agaishat duka duka bata fi 21 ba, har yanzu yarinya ce
Wardugu ne zaune da waya a hannunsa yana amsa kiran Elhaj Mubarack,
Elhaj Mubarak ya ce" Elhaj, nafa ga iri a wajenka,
Wardugu da ya dago zancen , ya gane inda ya nufa sarai, ya san me yake son fada masa , dan haka sai ya dantse lebensa na kasa yana sauraronsa,
Elhaj Mubarack ya ce" zan so a bani na kai gidana, wannan Hajia ce , sai Elhaj Mubarack,
Wardugu ya lumshe idannuwansa, bai san lokacin da ya ce" wai menene a tare da ita dake saka mutane bibiyarta ne?????????
Elhaj Mubarack ya yi wata dariya ta manya yana lumewa cikin kujerar falonsa inda matarsa ke gefe zaune tana zuba abinci tana jin abinda yake fada ya ce"..........
🐫🐫🐫🐫 *BAK'A CE* 🐫🐫🐫🐫
https://www.facebook.com/Idan-rana-ta-fito-writers-association-114558343535568/?referrer=whatsapp
*☀IDAN RANA TA FITO WRITER'S ASSO🌤* ____________________________________________
*Fad'akar da al'umma tare da nishad'antar da masoya shine fatanmu*😘🤝🏻😘
Na
*SAJIDA*
6️⃣7️⃣
Sai da ya gama murmushi ya shafa gemunsa ya kara kafin ya ce " Elhaj, ai fure ce, zan so na yi mata yayafi,
Wardugu ya rintse idannuwansa, kansa ya kawar kafin yake ajiye wayar ba tare da ya kasheta ba,
Jikinsa ya matsa ya jinginar da jikin kujerar da yake kai, idannuwansa ya lumshe yana mai jin wani tukukin tashin hankali na taso masa daga zuciyarsa yana yin sama,
Idannuwansa ya rintse irin ruf din nan ya shiga kokowa da zuciyarsa, aman ina ya kasa ba zai iya ba!
Mikewa ya yi rai bace ya dauki kys din sa ya fito yana gannin garin ya yi duhu sosai ,
Motarsa ya shiga ya bale da gudun gaske ya yiwa gidan Ayya tsinke,
Yana karasawa ya fice a motar kys dinsa a hannunsa ya nufi falo dan ya tabata irin wannan lokacin suna zaman falo ne
Yelemin kuwa, suna zaune Ayya na yi mata dankwashi ita kuwa tana zuba shagwabarta ,
Jikinta doguwar riga ce har kasa sai dai irin yadin nan ne mai likewa a jikin mutun ko ya ka motsa zaku motsa tare ne kuma komai rashin kabrin jikin ka zayana nuna motsin halitar jikinka, tana da irin rigunnan da yawa dan yannayin zafi Ayya ta kwaso mata a lokacin da akai mata aure.
Da katon takalminsa ya shigo falon domin bai riga ya cire takalmin da kayan dake jikinsa ba ya samu kiran Elhaj Mubarack,
Haka ya takawa Ayya capet din falonta, abinda ta tsana a rayuwa , dan haka da mamaki take dubansa dan shi ne mutun na farko da zai fadi bata son a shigo mata daki da takalmi, hasalima shi din ma ya tsani hakan a rayuwarsa,
Takim takim yaa tunkaro su inda suka dago su duka suna binsa da kallo har ya karaso gaban table din kwalbar dake gabansu mai dauke da ruwa da jus
Yana zuwa ya zuba kys din hannunsa da garaje saman table din hakan ya saka suka bada wani kara tamkar zasu fasa table din,
Hannunsa na hagu ya doro saman table din, da na dama kuwa ya dago yatsansa na kusa da baba ya nunata ya ce" ke , daga yau, daga rana mai kamar ta yau, na soke du wani shige da ficen ki a shigar da ba nikaf, hijab dogo da safa, idan kuwa ba haka ba sai na babala ki Agaishat!
Ya karashe yana mai daga muryar da ya saka ta mike tsaye da sauri ,
Mikewar da ta yi ya ainahin girgiza jikinta da karfi domin irin mikewar tsoracen nan ce,
Ido ya zaro ya ce" ba ga irinta ba! Ba ga irinta ba! A ce yarinya baki da kimtsi sai tsale tsale da guje guje da juye juye a gaban ko wani karamin dan iska? Ke ko kunya bakya ji zaki fito da wani mayafi mai kama da rariya ki wani zo kina juyi gaban madubi? Ke ke......
Da haushi haushi ya nufeta da niyar gaura mata mari domin a tsaye da take baki ta turo tana kikifta masa ido, wanda hakan ya kara hautsina masa lisafi
Ayya da ta yi mutuwar zaune cike da mamaki, da kuma darsuwar vakon zargi a kan tilon dan nata game da yar amanarta ta yi sauri cewa" walahi ka dakar min y'a sai ran ubanka ya baci Wardugu!
Ja ya yi ya tsaya, a hankali ya juyo wajen Ayya ya ga ta mike tsaye, kansa ya sada ya karaso kusa da ita a hankali kafin ya ce" Ayya, ya zaki sakawa yarinya ido tana fita da mayafi dan Allah?
Ayya ta ce" Wardugu, auren wani ke kan yarinyata ko bakon abu ne fita da mayafi a matar aure ma bare wace bata da aure? Ba wani shigar tsiraici take yi ta fita ba, aman idan ka saka mata irin dokar nan ba zan dauka ba !
Wardugu ya dago jajayen idannuwansa ya ce" Ayya, sai ta fita da dan mayafi zata samu miji ne? Wani irin miji take nema a rayuwarta ne? Shin ba karatu kika ce tana yi ba? Dan Allah du yanda za.a dagawa mutun hankali an sani? Yaya kuke so na yi ne?
Ayya ta kwalalo idannuwanta kafin ta tafa hannayenta ta ce" Warsugu wani laifi muka yi maka ne?
Wardugu ya yi shiru ya tsurawa cafet din falon ido, can ya fago idannuwansa ya sauke saman fuskar Agaishat dake tsaye tana dubansa, idannuwan su ne suka sarke da juna, kallon second 5 , idannuwan Wardugu jajaye jir da su tamkar gauta, sai dai da wasu yan kwala da ba zata iya kiransu da kwallah ba sai dai tace da su na bacin rai, wani irin kallo mai nauyi, mai tafe da sakwonni, mai dauke da ma.anoni ne ya zuba mata a cikin maraitatun idannuwanta da ta yi tsai ta jefe shi da kallo mai tura sakon *Ka ji tausayi na*,
A hankali ta lumshe idannuwanta ta ji wani irin sulbi a cikin idannuwan nata sannan suka fara rawa sanadiyar irin dokawar da zuciyarta ke yi du idan ta yi arba da shi,
A hankali ya taka ya nufe ta, wanda du takunsa ke barazana da tunanin kwakwaluwarta har ya kasance tunanin ya tsaya cak, ba wani sauran abinda ke aiki a cikin kwakwaluwar nata sai tarin kwalar da ta cika gurbin idannuwanta a hankali ta shiga zubowa,
Kure mata waje ya yi, ya shaki kamshin turarenta,
Idannuwansa ya lumshe ya kai hannunsa ya riko nata , riko na ya riko hannun kanwarsa, riko na ya kamo hannun kanwar sa dan ya jadada kashedinsa a gareta,
Sai dai laushin su ya saka shi dago da hannun da kyau ya bude idannuwansa ya tsura masu ido,
Ajiyar zuciya ya sauke kafin yake daga dan yatsarsa ya ce" ki bi dokana ki tsira, idan ki ka kiya zaki saka mu a uku ne, dan zan farauce ki a duniya ne, zan yi maki farautar kwai ne, Agaishat ki rufa mana asiri ki bamu lokaci, ki rufawa Ayyanki asiri kar ta yi zaman jinya !
Yana gama fada ya juya ya dauki kys dinsa ya juya yana tafe yana hada hanya ya fice a fallon,
Kuka Agaishat ta fashe da shi wanda ya farfado Ayya daga uwar sumar mamakin abinda ya faru da raka Wardugu da ido da ta yi,
Da sauri ta nufi wajen Agaishat ta kamota ta ce" ke Agaishat, menene? Tsoro kike ji ko? Kar ki ji wani tsoronsa in sha Allah ina tare da ke ba abinda zai yi maki!
Agashat ta rike hannun Ayya da kyau , da kyar ta bude bakinta ta ce" Ayya zuciyata ke bugawa, Ayya jikina rawa yake min, Ayya wayo zuciyata gabana ke faduwa du idan na ga yaya Wardugu, Ayya ciwon zuciya ne nake ko????
Shiru Ayya ta yi itama gaban nata ya fadi, kai ina! Aa ba su ba, menene haka? Me ke shirin faruwa ne?
Wardugu na komawa gidansa bangaren Walyn ya nufa,
Kai tsaye ya ritsata zaune tana kallon film a nollywood hankali kwonce,
Hannunsa ya saka ya mikar da ita, a hankali ya jata jikinsa ,
Idannuwansa lumshe ya lalubo lebenta jajir ya kai masu lalausan harshensa ya shiga kissing dinta passionately,
Fama take a kai fage, domin itafa ta fi gane can duda takan jigata aman gani take wani sakwanin wasani bata lokaci ne dan haka ta yi kokarin juya wasan zuwa ga fage mai rikitarwa, hakan ya saka ta yi gagawar cire yar rigar dake jikinta wace ta bayanar da yan berayen halitun jikinta,
Hannunta ya ja yana so ta yi tafia a gabansa duda ya kashe hasken fitilar dakin, dan damemen gajeran wandon dake jikinta yake so ta motsa ta bashi ma.ana, so yake ta bashi spectacle, yana so idannuwansa su juye kamar yanda a dazu suka juye daga kallon abinda bai zama halalinsa ba,
Saman kujerar ya zauna yana dubanta gannin faman ta baje take, wato ita dai kulun ta baje shi ta iya,
Kansa ya shafa yana dubanta, farar mace jajir, yar suwaiwai mafarkin dubunai, me ke damunsa? Ga hargitsinsa a gabansa ba wani ba, ga cakula kwakwaluwarsa a gabansa ba wani ba,
Hannayensa ya daga duka biyu ya dora saman kansa kafin a fili ya ce" kai kai, ina ba zai yiwu ba, wace wanina ya shiga? Gidan da aminina ya malaka? Wace irin kunya nake son kwasarwa kaina haka?
Walyn dake jiransa ta dube shi da kyau ta ce" Wardugu?
Wardugu ya bude idannuwansa yana dubanta, bai taba sakar mata nauyinsa mai suna nauyi ba, yakan shigar da gaban motarsa ne dan gannin gidan motar ba zai iya da shi ba, wai ko dai tausaya mata ne da yake yake sakata daukan raini tana sauke masa? zata iya da shi ne? Kai yau bara ya sakar mata nauyinsa , ko dai dan yana rage sauran nauyin nasa nema take tunanin karfin su daya?
Abinka da shawarar keta mai samun mazauni, nan da nan ya ji wani karfi na kara shigarsa, karfi irin na namijin saurayin zaki,
Mikewa ya yi ya nufeta da irin bukatarta ya..........
(Rashin kunyar ta isa haka woolah😢)
Dama kyawawa ne, suka kara da wanka, hakan ya saka yan matan suka wani fito fas da su, Mariama da Zainaba sun wani haska suna taku irin na manyan yara,
Abu daya ke kawo masu cikas a zamansu a birni shi ne rashin iya french, su kuwa yan mata da samarin garin Niamey sun dauki yaren French tamkar yaren haihuwarsu, karkadaf idan ka yi wasa zaka bace a hira da su, wato sun lakance shi ne ya saka har ruwa ruwa suke da harshe da gagawar magana tamkar jikokin macron (😕),
Kakarsu tana cikin koya masu wanka na yayan gayu da suka jiku a cikin gayu,
An koya masu mota, su ke zuwa alimentation siyayar kayan kicin da na frij, suna koyan su cake da sauransu,
Anna ta murje, ta murje ta faso, Anna bata magana daya biyu ba tare da ta jefa turanci wato inglish a ciki ba domin makarantar da ta yi ana koya masu yaran ne duka biyu a tare,
Rayuwarta na da ya dawo, ta dawo cikakiyar yar birni mai wayayen kai da iya tafiar da rayuwarta a nitse ba da hayaniya ba,
Takan shiga damuwar rashin labarin Agaishat, sai dai hankalinta na kwonciya idan ta tuna ai ta bada aurenta tana dakin mijinta kuma ko ba dade ko ba jima zata neme su fatanta dai Allah ya sa tana cikin rayuwa mai nagarta a gidanta,
Sai maganar Algabitt da suke jiran bilowarsa dan abinda ya tsaye masu a rai ya sakar masu y'a !
Timiya,
Sarki ya kada , ya raya, yana so ta janye maganarta aman fir ta rikice masa kan walahi ita magana daya ce tana so a fitar mata da hakinta a matsayinta na yar gari wace take da inci a kan wanda ya cuta mata,
Ya so su yi lamarin a sirri aman ta kiya ita kawai a yi masu shari.a da Algabitt dake rufe a matsayin mai dauke da laifi mai girma a gidan sarki,
Garin ba wanda bai san halin da ake ciki ba dan haka kananun magangannu ke yawo cewar za.a ga idan sarki zai hukunta sirikinsa bisa laifin da ya yi, idannuwa dai a kansa wanda hakan ya saka dole ya fitar da shari.ar fada,
Komai na son sirri, abinda ya yi ta nanatawa Gaishata dake kukan wannan lamari,
Gigirigin kennan ranar fadin gaskiya,
Tare wajen yake dankam, cike da jama.a, an taru an cika an yi makil abinka da kauye kowa ya zo ya ga kwaf,
Sarki zaune ya hakimce da rawaninsa na turkudi, gefe da gefensa du dogarai ne da yaran gidan sarki,
Sarkin bulala tsaye yana dan kadata lokaci zuwa lokaci,
Gefe guda matan sarki ne laye cikin shiga ta alfarma kowace na isa da kanta a matsayin na matar mai garin timiya,
Gaishatama zaune take ta sha turkudinta mai kala biyu blue da maroon an yi mata dinkin zamani ta rufa da katon mayafi hannayenta dauke da warwarayen zinari , ba yara a wajen domin ko yayansu a gida a aka bar su ,
Dayan gefen kuwa Algabiittt ne ke zaune shima yana ta kale kale alamomin rashin gaskiya sun bayana a tare da shi,
Gayaran murya sarki ya yi kafin ya ce" kamar yanda Timiya yake karamin gari mai dauke da sarki ni Ibrahim Asadeek, timiya ta kasance garin da talakanta ke da inci, muna zakulo du wanda ke tayar da zaune tsaye mu hukunta shi bisa tsarin adini,
Dogarai sai amsa shi suke kafin ya ci gaba da fadin" a yau , mun zauna a wannan waje dan tuhumar Malan agabitt kan manyan laifuka da muke tuhumarsa da su wa.inda matar da yake zaune da ita ta shigar da karar tun kafin ta bar gari , yanzu da bata nan bisa madadinta ga y'arta wato gimbiya gaishata , muna masu umartar Algabiit da ya bayana mana haduwarsa da mahaifiyar yayansa, dalilin da ya saka ya yi rayuwar wulakanci da ita....
Shiru ya yi yana kifta ido ya ki yin magana,
Ajiyar zuciya Sarki ya sauke kafin ya ce" idan har mai laifin ya yi gardama, kadarorinsa na gida da gonarsa da ake yi masa noma za.a karbe sannan ya fuskanci hukunci mai tsanani,
Ido ya zaro yana duban Sarki, shi bashi da damuwar wai mutanen wajen su ji abinda ya aikata, shi damuwarsa hangen daya daga cikin wa.inda suka bashi kudaden su Mariama da ya yi, ya tabata idan sarki ya kore ahi daga Timiya ya kade, dan haka ya gyara rawanin kansa ya shiga bada labari kamar yanda Anna ta bada har zuwa ranar da zai tafi da ita inda ya ce" a ranar safiya na yi na koma wajen bokana, wanda yake anguwar Talagué pays ba, ina zuwa na karbo abubuwan da na bashi ajiya domin ni ke kai masa abubuwa shima yana neman kudi da ni, inda ya dora ni a hanyar da zan hadu da yar masu kudi,
Maganin cire ne, wanda hasalij kirana daga garin haihuwana wato tanut dan ina yawan ciren yayansu,
Dakatar da shi aka yi ta hanyar tambayar menene cire?
Dago da kansa ya yi ya ce" Cire, wani asiri ne da fulanin daji ke yi , wanda na gada wajen kakana na wajen mahaifiyata dan shi filo ne, cire asiri ne da idan aka yiwa mace take bin namiji , bata da wani ra.ayi nata sai nashi,
Na hada da cire da asirin da bokan ya samo wajen wani bokansa dan dogon dutsi cewar idan na aikata idona idonta an kare zata bi ni ne du inda zan je, kuma ko me zan mata ba zata iya barina ba dan zatana jin tsoron zuciyata da bacin raina , sai dai kar na yarda ni da bakina na ambata mata sunnan garin su , ko sunnanta na asali, ko na yan uwanta, in dai ba ni na fada ba koma wa zai fada sai dai ya shiga tunani kamar ta san abin aman ta watsar daga baya dan zai tayar mata da hankali sosai
Na ci sa.a na cireta, muka fice a gidan daidai salar azahar muka dauki hanya da kudaden jakarta inda na yi wurgi da wayarta muka dauki yawon duniya,
Masalatai sun fi a kirga na je dan a aura mana aure, aman sai su ce koda bamu da kowa a duniya sai sun yi magana daga su sai ita, daya na amince sun fara maganar na ga sai wani tambayoyi yake yana faman tona asirina na bige shi da sadanta na dauketa muka kara shiga yawon duniya kafin daga baya na yada zango a nan,
Zufa ce ta shiga karyowa Gaishata, sarki kansa ji ya yi lumfashi na neman gagararsa,
Gaishat bata san lokacin da ta ce" kana nufin ba.a daura aurenka da matarka tsawon zaman da ka yi da ita harda hayayafa ba?????
To fa

6️⃣8️⃣
Asalamu alaikum
*Allah ya kawo mu wata mai albarka, banban wata mai tare da lada ,wata mai cinye zunubi, RAMADAN, ALLAH KA KARAWA ANNABI DARAJA TARE DA WASILA DA FARILLAH A ALJANAR FIRDAUS Allah ka jikan magabatan mu, ka sa sun huta, idan tamu ta zo ka sa mu cika da imani ka sa mu tarda alkhairi 👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻 Ya Allah, muna rokon ka, ka shirye mu, ka inta mu, ya ubangiji ka yafe mana zunubanmu, Allah ka hane mu saba maka,Ya Allah ka dora mu a hanyar bautarka, ka karbi ibadunmu, Ya Allah ka sa mu bayansa lafia ka maimaita mana, ni sajida ina mai yi mana fatan Alkhairi da fatan Allah ya kai.mu rai da lafia bayan sallah*
Algabitt ya dago da dubansa ya sauke kan Gaishata dake wani irin numfarfashi gabanta na faduwa tana duban mahaifin nata,
Algabitt ya kauda kansa yana bin mutanen dake zaune daya bayan daya da ido,
Kansa ya girgiza kafin ya kai dubansa wajen sarki ya ya buda bakinsa zai yi magana sarki ya mike tsaye ya ce" ya isa, kar ka fadi komai,
Muryar uwar gidansa ne ta ce " sarkina, talakawa na zaune suna jiran hukunci,
Amaryarsa ce ta gyara zama ta saki murmushi ta ce" sarkina, muna masu neman alfarmar a yi hukunci yanda aka saba yiwa sauran talakawa,
Gaishata dake bin su da kallo su duka biyu ta maido dubanta wajen Sarki da ya tsurawa matan nasa ido cike da takaici,
Gaishata ta share hawayenta ta sada kanta kasa,
Sarki ya koma ya zauna yana duban dogarai dake muzurai , sun so su tsawatarwa da matan sarki sai dai gannin matan sarkin ne tsoro ya hana su su yi masu magana domin ba wanda yake da hurumin yin magana idan sarki da kansa na shari.a duda kauye ne, idan baya nan akoy mai wakiltarsa ,
Hade rai ya yi ya ce" du wanda ya kara buda baki ya yi magana a wajen nan zai karbi hukunci komai kusancinsa da Sarki!
Idan Dogarai suka ga abin tsawatarwa basu tsawatarba zasu fuskanci fuahina!
Ji kake suna fadin" tuba muke sarkin talakawa,
Sarki ya maida hankalinsa wajen Algabittt ya ce" tabas ka kasance mutun mai son kansa, ka yi rayuwa bisa umarnin zuciyarka, tabas munada muradin jin bukatar wace aka fi cuta duda ta bada amanar yarta ta wakilce ta, dan haka zamu iya sauraron zuwanta ko maganarta a waya,
Magana yake hankalinsa ba a kwonce ba domin tunda Gaishata ta sada kanta bata dago ba,
Mikewa ya yi ya danna kira kan number Gukunni ,
Bayani ya kora masa na komai cikin nutsuwa , yana gamawa Gukunni ya tarda matarsa da y'arsa, cikin hikima ta manya ya zayane masu komai wanda ya saka Anna fashewa da wani irin kuka har tana dukewa tana dafe cikinta da dukan hannayenta,
Mahaifiyarta dake kuka itama tana duban jikokin nata da suka dora hannayensu saman kansu sun kasa magana tsabar shiga firgici da tashin hankalin jin wai su din ashema ga ta hanyar da aka same su duniya ta kawar da kanta wajen mijinta dake zaune sai zufa yake ta rintse idannuwanta zafafan hawaye suka zubo mata ta bude murya ta ce" na haifi Allacthi ta hanya mai kyau wace Allah ya nufe ni,
Ban bi kowa ba, haka mahaifinta ya kasance mai kiyaye wannan lamari,
Wannan kadara ce mai girma wace ta girmi tunanina,
Tabas na zama wawa a wannan lamari,
Shin wa zan kaiwa kuka a nan gidan duniya?
Yau du abinda za.a yiwa wannan bawa in dai ba dawo da shekaru baya za.a yi ba a dawowa da y'ata martabarta bana tunanin zan ji zuciyata wasai,
Yau ko yikuwa na cakawa wannan mutun ban goge komai ba,
Idan rufe shi aka yi ma ba.a dawo baya ba,
Wai wai wai ni Herde wai rayuwa Hamdulilah, Allah na gode maka,
Gukunni, dan Allah ka yi kiran wannan yaron ka fada masa ni nace dan Allah ya saki wannan mutumin da ba zan so maimaita sunansa ba,
Ya bar shi, *wata shari.ar sai a lahira*,
Tana fada tana ta share hawayenta ne tana kula da irin yanda Anna ta dafe zuciya tana gumurzun kuka,
Wajenta ta nufa dan ta lura Gukunni sauraronta kawai yake,
Kama Anna ta yi ta kwontar da ita ta dubi Mariama,
Hade fuska ta yi danma kar su daga mata hankali ta ce" ke maza je ki yi kiran docter Aliyu, maza ya zo ina jiransa,
Maida dubanta ta yi wajen Gukunni ta ce" ba zai ga bayan farin cikin gidanna ba, ba zan yarda wani katon gardin dan kauye saka baki a rayuwar da ta doso ni mai tsananin haske,
Zan so na ga jarumtar ka a wannan lamari Gukunni? Zan so na ga dauriyarka, ka kama mani kar na rasa y'ata, sannan ka fadawa Ibrahim Asadeek cewa idan ya ga zama da Gaishata wani damuwa ne, ya dawo min da ita da yaronta,
Gukunni dake zaune yana dubansu ya mike ya fice a gidan ,
Zuwa ya yi aeroport neman jirgin da zai kai shi agadez domin mai tuka nasa jirgin yana hutu ba zai so takura shi ba,
Sai dai ina ba jirgin agadez kwata kwata a ranar, dan haka da kansa ya tuka mota zuwa gidan yaron nasa soja kuma matukin jirgi ya je masa ya fada masa bukatarsa inda ya baiwa matarsa hakuri cewar idan har sun kwana hali ne ya kama babu niyar hakan!
Abinka da manya masu garin, haka suka zarce inda ya yi kira ya nemi alfarmar zai tashi da jirgi tafiar gagawa abinda ya shafi familynsa domin koda kana da jirginka ba kyau tashi lokacin da ka yi niya sai an baka izini
Basu wani sauka a Agadez ba, tafia suka yi mai dan tsayi sai garin timiya inda ya yi ta shawagi dan samu wajen sauka wajen da ba rere da kuma duwatsu, sannan wajen da idan zai tashi zai samu dan hanyar tafia kafin ya cira,
Da kyar dai , da kyar ya samu wajen da ya nuna masa zai iya sauka, inda yara tuni suka fito baki bude sunna kallon wannan abu mai kara mai ficewa can sama yau yana yin kasa kasa cikin gari, hakan ya saka wasu firgita da tsoron fadowa zai yi ya kashe su,
Inda wannan lamari ya ja hankalin mutanen fada da suka ki watsewa du suka dugunzuma zuwa gannin abinda ke faruwa kuma,
Dole sarki ne zai je gaba , dan haka ya mike ya kai dubansa wajen Gaishata dake yanda take ya juya da sauri ya tafi dan duba lamarin kauyensa inda yake tafe yana ayyana dole ya ajiye sarauta , shi kam ya kai wajen da ya ji takaicin kasancewarsa sarki,
Suna samun tsayawa Gukunni ya mike ya fito domin ya bude masa kofa inda shi kuwa ya zauna ciki yana gyare gyare da duba idan komai lafia dokin wajen ba wajen saukar jirgi bane
Ido Sarki ya kwalalo gannin Gukunni,
Mutane kuwa kallon mutun da baki haka a cikin jirgi suke, daman bakima na shiga?
Wajen sarkin ya nufa inda Algabitt ya kusan zubewa kusa da dogarin dake tsare da shi,
Ai kuwa juyawa ya yi da jiyar baiwa wandonsa iska sai dai an tare ko.ina,
Hayaniyar a sake shi ta ja hankalin Gukunni waje sa, dan haka ya saki hannun sarki da suka gaisa ya nufi wajensa yana dubansa da kyau
Yana zuwa ya tsaya gabansa inda Algabity ya zama wani cirit a gabansa,
Gukunni ya girgiza kansa, a fili ya ce" wai a gaban halita irinka kana haka ina ga ka je gaban wanda ya halice ka? Tabas ba sauran abinda zan yi shari.a a nan,
Yana gama fada ya koma wajen sarki ya ja hannunsa gefe,
Cikin nutsuwa ya ce" ina gaishata ne?
Sarki ya sada kansa kafin ya ce" tana cikin wani hali, ba yanda ban yi da ita kan a yi shari.arnan a sirince aman ta kada kai ita sai an yita a fada, hakan ya hadasa mata tashin hankali,
Kansa ya girgiza idannuwansa da sukai ja ya ce" ka san me? Shi du abinda Allah ya hanna, ma.aiki ya kawo mana mu yi aiki da shi,
Shi tsananta bincike ba kyau,
Yanzu wa gari ya waya?
Sarki ya kada kai yana duban gefe da yannayin damuwa,
Gukunni ya ce" zan so ka bani ita mu je gida, idan har kana ra.ayin hakan, zan so ta je ta huta, zamu so mu hada su su duka mu yi magana da su, zan so su saurari gargadi da nasiha ta zaman da zasu yi na rayuwa,
Tanas duniya ta ci gaba aman banda wajen mata,
Wannan bakin fentin na iya hana su sukuni cikin mata yan uwansu,
Zan so ka yi min wannan alfarma,
Sarki ya gyada kansa ya ce" tabas mata suna girma aman suna cin kasa, a yanzu haka har na so soke maganar abokan zaman nata suka takalota,
Dan haka yin hakanma ba laifi bane, nima ina kan duba wani lamari na nan , zan yi shawara da tsofafi magabata in sha Allah, a taya mu da adu.a Allah ya sa abinda za.a shiga alkhairi ne
Gukunni ya amsa shi cike da farin cikin zai bashi Gaishatar da zuciya guda,
Juyawa suka yi dan shiga ciki Gukunni ya ce" ita dai dayar har yanzu ba labarinta ko?
Sarki ya ce" aa, da wasika da wanda take hannunsa ya kawo, bara na dauko wasikar ni ai na sha.afa abubuwa sun shige mini,
Juyawa ya yi cikin gidansa inda Gukunni ya karasa wajen Gaishata ya duka,
Hannunsa ya saka ya dago habarta, kir idannuwanta abude suke sannan a soye,
Sauke idannuwanta da ta yi saman fuskar kakanta ta ji bakinta ya bude, murya na rawa ta rike hannunsa ta ce" ashe mu shagu ne ba aure Algabitt ya rayu da mu? Ya zamu yi rayuwa a cikin wannan lamari? Ya zan rayu cikin kishiyoyi da kauye a haka?
Ya kanuna da basu samu miji ba zasu samu a irin wannan rayuwa ta yanzu? Idan Agaishana ta ji haka, ya zata dauka? Ya mijin dake aurenta zai dauka?
Gukunni ya lumshe idannuwansa ya mike ya samu ya dagata ya dubi mai aikinta ya yi mata umarnin maza a dauko sultan,
Bai bata amsa ba sai jan hannunta da ya yi suka nufi wajen jirgi inda ha baki bude aka raka su da kallo , da yawan mutanen da fadin ko dai Uban Agaisha ne? Wato Bak'A?
Nan ya tsaya jira har sarki ya fito suka kara gaisawa ya bashi takardar da Wardugu ya kawo dauke da wasikar da bai karanta ba,
Juyawa ya yi ya basu waje shi da matarsa su yi salama kafin suke dagawa,
Wajen yama tuni sun dawo garin niamey inda mai tuka shi ya ja su har gidan su,
Suna zuwa ya saka ta fice shi kuwa yana rike da Sultan dake dan wasansa na jarirai ,
Ajiyar zuciya ya sauke ya daga idannuwansa sama yana kallon sararin samaniya,
Takardar nan ya bude ya duba,
Number waya ne kawai tsararu masu bin juna sai sunnan da ya zirawa ido da mamakin gannin sunnan , shin sunna ne ya zo daya haka ko kuwa shi din ne?
Wato jan gwarzon nan, yaro mai hazaka, yaron da yake ji fa shi dan aiki na yawan hada su, yaron da idan yana kallon abubuwan da ya yi a duniya har wani tsam yake ji da jin wani yannayi na shauki da jinjina masa da gannin girmansa tamkar wani datijo, yaro karami mai watsa taron yan daba, wato *WARDUGU BATUBE DAN MARAHUT*
MA.ASALAM
🐫🐫🐫 *BAK'A CE*

7️⃣0️⃣
Barkan mu da sallah jama.a,
*KUTKALE*
*Aure yakin mata ne*
*Kamarta bata da niyar cutarwa*
Kar ku bari a baku labari.....
Mikewa ta yi tsaye, nan doguwar rigar da ta saka wace ta bi jikinta ta sauka kasa ta kara ainahin fitar da surar jikinta da wani tsararen kyau mai fizga,
Lafayar ta dauko da niyar sakawa sai dai me, tana dubawa da kyau ta ga ai wannan ta ranar dinern da aka shirya ce,
Juyowa ta yi wajen Alhinayet dake zaune cikin shigar turkudi riga da zani sannan ta yaye kanta da shi ta fiti fit Buzuwarta ta ce" Alhi, dan Allah ki saka a kaini gida na dauko Lafayata, wannan ta gobe ce na dauko ashe,
Alhinayet ta ce " Ohk ki je wajen Salisu motar a hannunsa dan tun jiya colonel ya hana na kuma fita da ita ,
Agaishat ta amsa inda ta dauki Abayarta ja mai adon baki baki a jiki mai mabalai ta saka sannan ta yane kanta da mayafin abayar,
Kai Agaishat fa ta gama haduwa, dogon hancin nan nata ya zo har kusan bakinta mai dan girma kadan, gashin girarta kuwa ta caje shi ta daidaita shi ya yi tsaf da shi ya bada kala, tsarin fuskarta kyauta ce daga Allah, gashi kuma ya hadu da nutsuwar yannayi,
Cikin nutsuwa take takawa har ta samu fitowa inda ta hange shi domin an saka fitilu ko.ina,
Tana zuwa da muradinta ya mike ya tafi wajen motar suka shiga ya jata sai gidan Ayya, wato mahaifiyar ogansu,
Suna shiga gidan Agaishat ta ga motoci har shida,
Biyar din kalarsu daya, sannan ga sojoji tsatsaye du sun hade fuska tamkar an zage su,
Tsayar da ita aka yi sai da aka cajeta dan kuwa ogansu na ciki ko wa bai isa ya shiga kansa tsaye ba,
Ji ta yi kafafuwanta na rawa, dan ba alamar sasauci a fuskokin su, dan haka a hankali ta samu ta raba ta haye inda ta fura kofar falon ta shiga da salama murya a dan dage kadan dan mutanen dake ciki su ji ta,
Salamar ce ta katse, a daidai lokacin da idannuwanta sukai mata arba da su,
Da Farko dai Wardugu ne da kakin soja sai dai botiraan rigar a bale inda rigar shi ta ciki fara kar ta samu damar bayana kanta da pecto dinsa,
Kafarsa daya kan daya ya dora, yana danna waya aman salamarta ya saka shi dago kansa da sauri tare da bugawar zuciyar da ta saka shi lumshe dara daran idannuwansa,
Gefe kuwa mijinta ne, uhum ba mijinta ba, tsohon mijinta, wato Mu.azam, docter Mu.azam ne zaune sanye da costume bakake da cravate dinsa ya daure cif da shi, duda kansa a aske kwal aman bai hanna bayanar kyansa ba,
Sai Ayya dake zaune cikin lafayarta , daga kasa kuwa Khadija ce ta duka da alama neman gafara take,
Idannuwanta ta lumshe, ta kara,lumshewa, dukan wata jarumta da take tunanin tana da ne take gayatowa , sai dai ina, gaba daya jikinta ne ya kwashi rawa wanda hakan ya yi sanadiyar sakin dankareriyar samsung dinta kasa inda ta bada Pats screen ya mutu🤦♀,
Dubanta ta kai wajen wayar , ta yi azamar dukawa dan dauka, sai dai gaba daya ta shiga raruma tana saki, ta kasa daukan!
Dan haka ta mike ta tsalaka wayar ta juya da gudu gudu ta shiga hawan bene dan neman dakinta tana kokarin dane wani katoton kuka dake taso mata da karfin tsiya,
Ayya ce ta mike da sauri, inda ta ga gilmawarsa kawai, da karfinsa yake taka matatakalar yana nufar inda take inda idannuwansa suka rufe hankalinsa ya tashi,
Ayya ta ce" Wardugu,
Ina baya jinta, shima adu.a yake, fata yake na Allah ya sa ba kukan abinda yake tunani take yi ba,
Dakinta ya tura ya shiga,
Idannuwansa kyam saman kanta inda ya ga ta cire abayar jikinta sauran doguwar rigar nan ta cire dan kwali ta yar , ta kifa kanta saman abin bed, kuka take har tana jijiga,
Innalilahi wa.ina ilaihi raj.une, shi ne abinda ya iya furtawa kafin yake karasawa inda take,
Hannayensa ya saka wajen kafadunta ya dagota tsaye gaba dayanta,
Kokarin bude jikakun idannuwanta take , sannan zufa ta jike gashinta daga gaba tamkar ta watsa ruwa, fuskar nata ta jike jagab tana hakin kuka,
Bai bari ta karasa bude idannuwan nata ba ya janyota gaba dayanta cikin ni.imtacen jikinsa, wani irin riko ya yi mata gaba dayanta tamkar sabon babyn da baya so a kwace masa,
Kamshinsa, da wani irin bugawar da zuciyarsa ke yi wada tana iya ji a irin rikon da ya yi mata, da kuma bakon lamarin wai ita Agaishat kwonce a kirjin Wardugu, namiji daya ya daya, Wardugu zaki, wardugu guguwa lahaula wala kuwata, wani juuu ta ji wata juwa na neman debarta ita dake kwonce luf a saman kirjinsa, kukan ta nema ta rasa, hasalima mantawa ta yi ta yanda ake rera wakar kukan, sai wani ajiyar zuciya da take zaukewa mai dumin gaske saman kirjinsa dake bude,
Hannunsa dake rawa ya dago a hankali ya dora saman gashin kanta dake malale saman gadon bayanta ya dora ya dan ja hannunsa kasa sannan ya maido sama,
Tsayar da hannun ya yi yana kokarin bude idannuwansa da ya rufe ruf,
Muryarsa na rawan da bai taba yi ba, hannunsa na rawa ya ce" menene? Mu.azam ne?
Shiru ta yi bata iya bashi amsa ba, hasalima kokowa take da numfashinta domin yana buda baki maganarsa na watso mata kanshin turaran baki da yake anfani da shi mai kanshin banana
A hankali ya dora hancinsa saman goshinta, hakan ya baiwa bakinsa damar zuwa wajen jikakun idannuwanta,
Ji ta yi ya damki hannunta na dama da dan karfi kadan, sannan ya ce" *Son shi ki ke yi ko?*, *KUKAN SON TSOHON MIJINKI KI KE?*
masha Allah, Alhamdulilah, barkan mu da sallah yan uwa. ALLAH ya karba mana .....Amen
*TALLAH TALLAH TALLAH*,
*KUTKALE*
*PRISON KUTKALE*
Kwonce take inda aka gama jibgarta dan ta yiwa Eliz gardama, wani bacin wahala me ya kwasheta inda kamar daga sama ta ji ana lalubarta,,
Hannu ne, kokarin kai hannun ake cikin dadaudan sqet dinta wanda ko karamin wando babu a ciki, wato dai malan shigo...........
Domin karin bayani ka tumtubi +22791466605
Labaru masu zuwa in sha Allah
*AURE....YAKIN MATA NE*
*KAMARTA BATA DA NIYAR CUTARWA*
DAGA ALKALAMIN *SAJIDA* YAR MUTAN NIGER MARUBUCIYAR
*DUK KARYAR KADA*,
*YAR MAHAUKACIYA*
*DAGA TAFIA DAUKAR SOJA*
*BANI DA ZABI*
*NEMAN NA KAINA*
*BAK'A......*
Fan's barka da sallahna🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔😢😢🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔😢🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔😢🤔😢😢😢😢😢😢😢😢
🐫🐫🐫🐫 *BAK'A CE* 🐫🐫🐫🐫
https://www.facebook.com/Idan-rana-ta-fito-writers-association-114558343535568/?referrer=whatsapp
*☀IDAN RANA TA FITO WRITER'S ASSO🌤* ____________________________________________
*Fad'akar da al'umma tare da nishad'antar da masoya shine fatanmu*😘🤝🏻😘
Na
*SAJIDA*
6️⃣8️⃣
Asalamu alaikum
*Allah ya kawo mu wata mai albarka, banban wata mai tare da lada ,wata mai cinye zunubi, RAMADAN, ALLAH KA KARAWA ANNABI DARAJA TARE DA WASILA DA FARILLAH A ALJANAR FIRDAUS Allah ka jikan magabatan mu, ka sa sun huta, idan tamu ta zo ka sa mu cika da imani ka sa mu tarda alkhairi 👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻 Ya Allah, muna rokon ka, ka shirye mu, ka inta mu, ya ubangiji ka yafe mana zunubanmu, Allah ka hane mu saba maka,Ya Allah ka dora mu a hanyar bautarka, ka karbi ibadunmu, Ya Allah ka sa mu bayansa lafia ka maimaita mana, ni sajida ina mai yi mana fatan Alkhairi da fatan Allah ya kai.mu rai da lafia bayan sallah*
Algabitt ya dago da dubansa ya sauke kan Gaishata dake wani irin numfarfashi gabanta na faduwa tana duban mahaifin nata,
Algabitt ya kauda kansa yana bin mutanen dake zaune daya bayan daya da ido,
Kansa ya girgiza kafin ya kai dubansa wajen sarki ya ya buda bakinsa zai yi magana sarki ya mike tsaye ya ce" ya isa, kar ka fadi komai,
Muryar uwar gidansa ne ta ce " sarkina, talakawa na zaune suna jiran hukunci,
Amaryarsa ce ta gyara zama ta saki murmushi ta ce" sarkina, muna masu neman alfarmar a yi hukunci yanda aka saba yiwa sauran talakawa,
Gaishata dake bin su da kallo su duka biyu ta maido dubanta wajen Sarki da ya tsurawa matan nasa ido cike da takaici,
Gaishata ta share hawayenta ta sada kanta kasa,
Sarki ya koma ya zauna yana duban dogarai dake muzurai , sun so su tsawatarwa da matan sarki sai dai gannin matan sarkin ne tsoro ya hana su su yi masu magana domin ba wanda yake da hurumin yin magana idan sarki da kansa na shari.a duda kauye ne, idan baya nan akoy mai wakiltarsa ,
Hade rai ya yi ya ce" du wanda ya kara buda baki ya yi magana a wajen nan zai karbi hukunci komai kusancinsa da Sarki!
Idan Dogarai suka ga abin tsawatarwa basu tsawatarba zasu fuskanci fuahina!
Ji kake suna fadin" tuba muke sarkin talakawa,
Sarki ya maida hankalinsa wajen Algabittt ya ce" tabas ka kasance mutun mai son kansa, ka yi rayuwa bisa umarnin zuciyarka, tabas munada muradin jin bukatar wace aka fi cuta duda ta bada amanar yarta ta wakilce ta, dan haka zamu iya sauraron zuwanta ko maganarta a waya,
Magana yake hankalinsa ba a kwonce ba domin tunda Gaishata ta sada kanta bata dago ba,
Mikewa ya yi ya danna kira kan number Gukunni ,
Bayani ya kora masa na komai cikin nutsuwa , yana gamawa Gukunni ya tarda matarsa da y'arsa, cikin hikima ta manya ya zayane masu komai wanda ya saka Anna fashewa da wani irin kuka har tana dukewa tana dafe cikinta da dukan hannayenta,
Mahaifiyarta dake kuka itama tana duban jikokin nata da suka dora hannayensu saman kansu sun kasa magana tsabar shiga firgici da tashin hankalin jin wai su din ashema ga ta hanyar da aka same su duniya ta kawar da kanta wajen mijinta dake zaune sai zufa yake ta rintse idannuwanta zafafan hawaye suka zubo mata ta bude murya ta ce" na haifi Allacthi ta hanya mai kyau wace Allah ya nufe ni,
Ban bi kowa ba, haka mahaifinta ya kasance mai kiyaye wannan lamari,
Wannan kadara ce mai girma wace ta girmi tunanina,
Tabas na zama wawa a wannan lamari,
Shin wa zan kaiwa kuka a nan gidan duniya?
Yau du abinda za.a yiwa wannan bawa in dai ba dawo da shekaru baya za.a yi ba a dawowa da y'ata martabarta bana tunanin zan ji zuciyata wasai,
Yau ko yikuwa na cakawa wannan mutun ban goge komai ba,
Idan rufe shi aka yi ma ba.a dawo baya ba,
Wai wai wai ni Herde wai rayuwa Hamdulilah, Allah na gode maka,
Gukunni, dan Allah ka yi kiran wannan yaron ka fada masa ni nace dan Allah ya saki wannan mutumin da ba zan so maimaita sunansa ba,
Ya bar shi, *wata shari.ar sai a lahira*,
Tana fada tana ta share hawayenta ne tana kula da irin yanda Anna ta dafe zuciya tana gumurzun kuka,
Wajenta ta nufa dan ta lura Gukunni sauraronta kawai yake,
Kama Anna ta yi ta kwontar da ita ta dubi Mariama,
Hade fuska ta yi danma kar su daga mata hankali ta ce" ke maza je ki yi kiran docter Aliyu, maza ya zo ina jiransa,
Maida dubanta ta yi wajen Gukunni ta ce" ba zai ga bayan farin cikin gidanna ba, ba zan yarda wani katon gardin dan kauye saka baki a rayuwar da ta doso ni mai tsananin haske,
Zan so na ga jarumtar ka a wannan lamari Gukunni? Zan so na ga dauriyarka, ka kama mani kar na rasa y'ata, sannan ka fadawa Ibrahim Asadeek cewa idan ya ga zama da Gaishata wani damuwa ne, ya dawo min da ita da yaronta,
Gukunni dake zaune yana dubansu ya mike ya fice a gidan ,
Zuwa ya yi aeroport neman jirgin da zai kai shi agadez domin mai tuka nasa jirgin yana hutu ba zai so takura shi ba,
Sai dai ina ba jirgin agadez kwata kwata a ranar, dan haka da kansa ya tuka mota zuwa gidan yaron nasa soja kuma matukin jirgi ya je masa ya fada masa bukatarsa inda ya baiwa matarsa hakuri cewar idan har sun kwana hali ne ya kama babu niyar hakan!
Abinka da manya masu garin, haka suka zarce inda ya yi kira ya nemi alfarmar zai tashi da jirgi tafiar gagawa abinda ya shafi familynsa domin koda kana da jirginka ba kyau tashi lokacin da ka yi niya sai an baka izini
Basu wani sauka a Agadez ba, tafia suka yi mai dan tsayi sai garin timiya inda ya yi ta shawagi dan samu wajen sauka wajen da ba rere da kuma duwatsu, sannan wajen da idan zai tashi zai samu dan hanyar tafia kafin ya cira,
Da kyar dai , da kyar ya samu wajen da ya nuna masa zai iya sauka, inda yara tuni suka fito baki bude sunna kallon wannan abu mai kara mai ficewa can sama yau yana yin kasa kasa cikin gari, hakan ya saka wasu firgita da tsoron fadowa zai yi ya kashe su,
Inda wannan lamari ya ja hankalin mutanen fada da suka ki watsewa du suka dugunzuma zuwa gannin abinda ke faruwa kuma,
Dole sarki ne zai je gaba , dan haka ya mike ya kai dubansa wajen Gaishata dake yanda take ya juya da sauri ya tafi dan duba lamarin kauyensa inda yake tafe yana ayyana dole ya ajiye sarauta , shi kam ya kai wajen da ya ji takaicin kasancewarsa sarki,
Suna samun tsayawa Gukunni ya mike ya fito domin ya bude masa kofa inda shi kuwa ya zauna ciki yana gyare gyare da duba idan komai lafia dokin wajen ba wajen saukar jirgi bane
Ido Sarki ya kwalalo gannin Gukunni,
Mutane kuwa kallon mutun da baki haka a cikin jirgi suke, daman bakima na shiga?
Wajen sarkin ya nufa inda Algabitt ya kusan zubewa kusa da dogarin dake tsare da shi,
Ai kuwa juyawa ya yi da jiyar baiwa wandonsa iska sai dai an tare ko.ina,
Hayaniyar a sake shi ta ja hankalin Gukunni waje sa, dan haka ya saki hannun sarki da suka gaisa ya nufi wajensa yana dubansa da kyau
Yana zuwa ya tsaya gabansa inda Algabity ya zama wani cirit a gabansa,
Gukunni ya girgiza kansa, a fili ya ce" wai a gaban halita irinka kana haka ina ga ka je gaban wanda ya halice ka? Tabas ba sauran abinda zan yi shari.a a nan,
Yana gama fada ya koma wajen sarki ya ja hannunsa gefe,
Cikin nutsuwa ya ce" ina gaishata ne?
Sarki ya sada kansa kafin ya ce" tana cikin wani hali, ba yanda ban yi da ita kan a yi shari.arnan a sirince aman ta kada kai ita sai an yita a fada, hakan ya hadasa mata tashin hankali,
Kansa ya girgiza idannuwansa da sukai ja ya ce" ka san me? Shi du abinda Allah ya hanna, ma.aiki ya kawo mana mu yi aiki da shi,
Shi tsananta bincike ba kyau,
Yanzu wa gari ya waya?
Sarki ya kada kai yana duban gefe da yannayin damuwa,
Gukunni ya ce" zan so ka bani ita mu je gida, idan har kana ra.ayin hakan, zan so ta je ta huta, zamu so mu hada su su duka mu yi magana da su, zan so su saurari gargadi da nasiha ta zaman da zasu yi na rayuwa,
Tanas duniya ta ci gaba aman banda wajen mata,
Wannan bakin fentin na iya hana su sukuni cikin mata yan uwansu,
Zan so ka yi min wannan alfarma,
Sarki ya gyada kansa ya ce" tabas mata suna girma aman suna cin kasa, a yanzu haka har na so soke maganar abokan zaman nata suka takalota,
Dan haka yin hakanma ba laifi bane, nima ina kan duba wani lamari na nan , zan yi shawara da tsofafi magabata in sha Allah, a taya mu da adu.a Allah ya sa abinda za.a shiga alkhairi ne
Gukunni ya amsa shi cike da farin cikin zai bashi Gaishatar da zuciya guda,
Juyawa suka yi dan shiga ciki Gukunni ya ce" ita dai dayar har yanzu ba labarinta ko?
Sarki ya ce" aa, da wasika da wanda take hannunsa ya kawo, bara na dauko wasikar ni ai na sha.afa abubuwa sun shige mini,
Juyawa ya yi cikin gidansa inda Gukunni ya karasa wajen Gaishata ya duka,
Hannunsa ya saka ya dago habarta, kir idannuwanta abude suke sannan a soye,
Sauke idannuwanta da ta yi saman fuskar kakanta ta ji bakinta ya bude, murya na rawa ta rike hannunsa ta ce" ashe mu shagu ne ba aure Algabitt ya rayu da mu? Ya zamu yi rayuwa a cikin wannan lamari? Ya zan rayu cikin kishiyoyi da kauye a haka?
Ya kanuna da basu samu miji ba zasu samu a irin wannan rayuwa ta yanzu? Idan Agaishana ta ji haka, ya zata dauka? Ya mijin dake aurenta zai dauka?
Gukunni ya lumshe idannuwansa ya mike ya samu ya dagata ya dubi mai aikinta ya yi mata umarnin maza a dauko sultan,
Bai bata amsa ba sai jan hannunta da ya yi suka nufi wajen jirgi inda ha baki bude aka raka su da kallo , da yawan mutanen da fadin ko dai Uban Agaisha ne? Wato Bak'A?
Nan ya tsaya jira har sarki ya fito suka kara gaisawa ya bashi takardar da Wardugu ya kawo dauke da wasikar da bai karanta ba,
Juyawa ya yi ya basu waje shi da matarsa su yi salama kafin suke dagawa,
Wajen yama tuni sun dawo garin niamey inda mai tuka shi ya ja su har gidan su,
Suna zuwa ya saka ta fice shi kuwa yana rike da Sultan dake dan wasansa na jarirai ,
Ajiyar zuciya ya sauke ya daga idannuwansa sama yana kallon sararin samaniya,
Takardar nan ya bude ya duba,
Number waya ne kawai tsararu masu bin juna sai sunnan da ya zirawa ido da mamakin gannin sunnan , shin sunna ne ya zo daya haka ko kuwa shi din ne?
Wato jan gwarzon nan, yaro mai hazaka, yaron da yake ji fa shi dan aiki na yawan hada su, yaron da idan yana kallon abubuwan da ya yi a duniya har wani tsam yake ji da jin wani yannayi na shauki da jinjina masa da gannin girmansa tamkar wani datijo, yaro karami mai watsa taron yan daba, wato *WARDUGU BATUBE DAN MARAHUT*
MA.ASALAM
🐫🐫🐫🐫 *BAK'A CE* 🐫🐫🐫🐫
https://www.facebook.com/Idan-rana-ta-fito-writers-association-114558343535568/?referrer=whatsapp
*☀IDAN RANA TA FITO WRITER'S ASSO🌤* ____________________________________________
*Fad'akar da al'umma tare da nishad'antar da masoya shine fatanmu*😘🤝🏻😘
Na
*SAJIDA*
7️⃣1️⃣
*KUTKALE* (prison)
*AURE YAKIN MATA NE*
*KAMARTA, BATA DA NIYAR CUTARWA*
daga alkalamin yar mutan Niger in sha Allah,
........kar ku bari a baku labari...............
Wannan karron ma bata iya bashi amsa ba, ina ba zata iya budar bakinta ba, wani irin nauyi bakinta ya yi mata, sannan wani haushi take ji, *SO?* yo ita ba Mu.azam ba, ko waninsa bata tunanin zata kuma aminta ta so dan gudun idan ya wulakanta ta ta afka damuwa, dan haka sai ta dan motsa hannunta da ta fara jin zafin irin rikon da ya yi masa sannan ta bude idannuwanta a hankali ta dan janye goshinta daga wajen hancinsa sannan ta dago da dubanta a nitse ta sauke saman fuskarsa,
Kallon kasan ido yake yiwa du wani motsinta, hakan ya sa ya dan sasauta kusancin da ya saka a tsakanin su kafin yake bude idannuwansa gaba daya ya zuba cikin nata da kallon da ta tsare shi da shi,
Da sauri ta sada nata idon, domin idon Wardugu ya kada yay jajir, tsoro ne ya shiga dirar mata duda irin magangannun da ta fadawa kanta na ba zata kuma bari tana irin tsoron nan ko a gaban waye ba,
A hankali ta dan ja baya ta zauna saman bed din , ta sada kanta kasa,
Wani irin abu take ji, wata faduwar gaba da take ji da wani sanyi sanyi, sai uwa uba wani irin dadi da take ji na kulawa da damuwarta da Wardugu ya yi a daidai wannan lokacin,
Bayansa ta dago ta tsurawa ido , dogon namiji, namiji ingarma,
Hannunsa da ya dafe goshinsa ta kalla , wato damatsunan hannun , da sauri ta sada kanta domin sai da gabanta ya fadi, a zuciyarta take ayana shi wannan wani irin jiki ne da shi haka?
Wardugu kam kokarin saita kansa yake, gabba daya ransa ne yake ji a jagule, hankalinsa du a tashe dalilin kukan nan, shi kukan yake son sani na menene? Kuka? Ta zubar da hawayenta haka kawai? Bata san girman darajar hawaten ba? Sai ya waka ne? Ya ilahi,
Juyowa ya yi yana dubanta kafin yake daga kafarsa a hankali ya dangana shima da bakin bed din,
A dan tsorace ta dago dan gannin ya zauna kuma, kar ta ja ya daketa a banza kafin a amsheta wannan ai har ya sumar da ita, haba dole su suma idan yana dukansu yo wannan hannu haka?
Bana son yawan magana da tambayar mutun yana kyaleni. Wardugu ya fada hankali kwonce.
Dagowa ta yi inda bakinta ya shiga dan rawa rawa kafin ta ce" ina cike da tunani ne....
Wardugu ya tsura mata ido yana mai jin zuciyarsa na dokawa, a hankali ya ce" *Tunaninsa?*
Agaishat ta sauke ajiyar zuciya ta yatsina fuskarta , tunananinsa? Kanta ta girgiza ta ce" aa, ina yawan tunanin a yan kwanakin da na yi da shi, menene girman laifin da nayi masa da har ya kai shi mayar da ni karamar bazawara? Wani kure ne wannan na tafka masa da ya saka shi ahiga jikina sannan ya sake ni?
Da sauri Wardugu ya dago da idannuwansa ya sauke kanta, *SHIGA JIKINA* kalma mai ma.ana biyu, innalilahi wa.ina ilaihi raj.une, ji ya yi kansa ya fara juya masa, duda yana da wani tunanin da wuya ta yi irin furucin nan a gabansa, aman wani lamarin ya rinjaye shi,
Innalilahi kawai yake maimaitawa domin ya jima da daina jin me take fada da idannuwansa ruf a rufe suke,
Da kyar ya iya mikewa ya shiga dan takawa a hankali , bai ce da ita ufan ba ya bude kofar nata ya fice a dakin yana mai dan dafe kansa,
Maganarsa ya tsinta inda yake cewa" Ayya, a facebook ne na ga sanarwar auren Alhinayett, abinda ya sa muka zo kennan, dan girman Allah Ayya ki duba maganata , ki zauna ki nazarceta, zaki ga iya gaskiyata kennan, Ayya ba zan yi maki karya ba, ba zan iya wannan gangancin ba👏🏻
Bai iya tsayawa a falon ba ya zarce zai fita, nan ya taka wayarta dake yade hakan ya saka ya duka ya dauka idannuwansa na kara rikidewa da tsabar masifa a cikinsu,
Da kallon tsoro, da kuma mamaki Ayya ta raka shi, kafin take juyowa da sauri wajen Mu.azam tana mai tarababin abinda ya fada kan Wardugu, ya salam! Shi ne abinda ta iya furtawa, sai kuma abubuwa suka shiga dawo mata daki daki,
Tana kallo Mu.azam ya mike ya bi bayan Wardugu, tana son tsayar da shi aman tunanin lamarin ya saka harshenta yin nauyi,
Da sauri ya karasa inda yake tsaye ya mika hannu ya taba kafadarsa,
Da sauri Wardugu ya juyo jin an taba shi,
Wani irin kakausan kallo ya jefawa Mu.azam , kallo mai nunin zan iya kasaraka, kafin ya furzar da wata iska ya maida dubansa wajen yarensa da suke tare hakan ya saka suka matsa suka basu wuri domin sun biyo Mu.azam ne kar ya karasa wajen ogansu
Kansa ya dafe , muryarsa a dan dage sannan cike da tashin hankali ya ce" dan me sai ita? Me yasa zaka ringa kokarin sakata kuka? Ka san ya na jure wanda ta yi ta yi min a lokacin da ka wulakanta ta? Ya zaka biyo mini ita nan ka kara sakata kuka?
*Ka CUCE NI*, me yasa Mu.azam? Me ya sa? Me na yi maka ka huce a kanta? Ya aka yi ka min haka? *Ban cancanci haka ba*, wayo wayo wayo Allahna.......! WARDUGU ya karashe yana mai dukan hanayensa a kansa da karfinsa,
Mu.azam ya dan ja baya, ransa bace da yannayin nan ya ce" danme ba zaka fuskanci lamarin ba? *Agaishat* *KADARA* ce! Nauyin baki, tsoro! Zai saka ka yin aikin dana sani, domin idan ni na kawar da kai ga tarin ni.imarta wani ba zai iya ba!
Wardugu ya harzuka ya cakumi wuyan rigarsa cikin karaji ya ce" ni zaka fadawa maganar banza maganar ni.imarta? Ni kake nufi ina tsoron mace ko me? Na taba fada maka wata magana a kanta ne?
Mu.azam da ya rike hannunsa da kyar yana so ya sakar masa wuya aman ya kasa suka ji muryar Ayya tana tafa hannu,
Hankalinta tashe ta karaso wajen su ta saka hannunta bibiyu ta kama jan hannun wardugu da iya karfinta,
Da kyar ya cika hannun kafin rai bace ta nuna masa hanyar fita ta ce" jeka gidanka! Tafi ka bani waje!
Rigar kakinsa ya ja ya cire baki daya ya yi masa sauran ta cikin kawai , ya juya ya nufi wajen motocin dake parke du sun yi cirko cirko suna sauraron fadan cike da taoron su shiga abin ya juye kansu,
Zuwansa ya saka aka bude masa ya shige suka tayar suka dauki hanya,
Kansa kawai ya jinginar ya lumshe idannuwansa kafin ya shiga hasasota a idannuwansa, ya Rab shi ne abinda ya iya furtawa ya kule bakinsa yana saurare har suka karasa gidansa ,
Ficewa ya yi ba tare da yace da su su ci kansu ba ya shige part dinsa ,
Walyn ce kwonce saman doguwar kujerar dakin daya kwalin kwal wace aka canza kayan dakin da kallolin aka saka masu ruwan zeba da dan ratsin fali aka saka kujerar zoguwa ta yi kwana ita daya mai wani irin zubi irin kujerun gidan sarakai, gannin idoma zai nuna maka da an kashe kudi a kanta, domin da ka kaleta zaka ga tamkar tana gayatarka ne zama samanta
Ido ya tsura mata ta saamu baci abinta, hankalinta kwonce abinta, ta sha yar karamar rigarta ta baci baka mai shara shara ta daure gashin kanta waje guda ta yi shar da ita ,
Da ita ya yi tafia ta wajen sati biyu,
Zagaye kujerar ya yi ya nufi dakinsa na baci yana faman neman bayi ya watsa ruwa mai sanyi ko zai ji zuciyarsa ta rage nauyi,
Bayan ya fito a wanka wayarsa ya tarar tana ringin,
Wajenta ya nufa ya dauka ya amsa kiran Alhinayett ce, sauraronta ya yi ta gama maganar kafin yace" kin ga ki raba ni Alhinayett, idan ni ina uban gidansa a wajen aiki ke uban gidanki ne a rayuwar aure, kar ki yarda ki ringa fada min laifinsa domin idan ina yawan yi masa magana tsanarki zai yi, ke wai ke din ba mace bane ba? Dole sai kin masa katsalandan a abubuwan da ya tsara maku na rayuwa? Haka kawai yara kananu kuna saka mutane yawan magana da tashin hankali? Ohk yanzu da kika kirani kika fada mani so kike in kiraye shi in tirsasa masa saka turkudi a ranar da za.a yi masa murnar aurensa na sojoji ni babansa ko? Kawai dan kina buzuwa shikenan zaki sako shi a gaba dan wulakanci ranar sojoji ki saka shi ya nada rawani kamar sarkin wani gari ko wani tsohon baruma? Yaki ba zai saka ba, nace ba zai saka ba!
Ya karashe da dan karaji,
Alhinayett da ta rafka tagumi tana tarababi da fadin ikon Allah wa ya tabo shi a ranta, ta zaro ido ta ce" Toh, ikon Allah
Wardugu ya ce" ni ne toh din ko? Ni ne toh din?
Ai kuwa kitt ta kashe kiran tana zazaro ido ta kai dubanta wajen matar abansu ta saki wani murmushi mai kama da ba.a dace ba,
Haka ya bi wayar da kallo kafin ya yi kwafa ya ajiye wayar
Har zai karasa kusan bed ya kai dubansa kan wayarta samsung da ta farfashe,
Juyowa ya yi ransa a jagule ya jujuya wayar,
Abin cire sim ya dauka a gaban sif dinsa ya ciro sim din wayar kwaya daya na airtel ya bude wayarsa iPhone 11 ya saka layin a ciki ya kunna wayar ya ajiye nan kafin ya zarce wajen bed din ya kwonta ya lumshe idannuwansa,
Kansa yake ji na sara masa sosai, dan haka ya yi adu.ar baci da fatan Allah ya sa ya samu bacin ya lumshe idannuwansa bayan ya kashe fitilar dakin
Ayya kam sosai abin ya daketa, ta yi mamaki, sannan ta tausaya masa, anya kuwa? Anya ta taba gannin abinda ya yiwa irin wannan son da idannuwansa ke rufewa idan tana waje ? Jikinsa fuskarsa, da act dinsa baki daya ke nuna kariya ga abin? Ita kam ta shiga wani yannayi, ta yaya? Yaushema ya yi aure?
Gannin damuwa na neman hadasa mata ciwon kai ya saka bayan su Mu.azam sun tafi hotel domin wannan karon a hotel suka sauka ta haye sama wajen Agaishat, nan ta tarar da ita ta yi baci hannunta dafe da goshinta,
A hankali ta zauna gefenta ta sauke mata hannun dan kar ya sage sannan ta tofa mata adu.o.in tsari ta ja mata rigarta ta rufe mata inda ya bude a jikinta ta mike ta tafi ta ja mata kofa tana tausaya mata , ko me ya dawo da ita daga wajen sabgar auren?
Tanaa shiga dakinta ba kwonciya ta yi ba, alwallah ta daura ta raba dare saman salaya tna mai neman zabin Allah da kawar da du wata fitina............
Wannan kennan
Ranar daurin Aure
Tun karfe biyar Ayya ta tayar da Agaishat ta barta ta kimtsa inda itama ta koma dakinta ta karasa shiryawa,
Wanka ne ta darza sosai domin bakonta ya zo mata tsakiyar dare,
Tana fitowa ta saka auduga da pant, sannan ta zauna a yar kujerar turaren wutarta ta yi turare mai sanyayan kamshi sosai har gashin kanta,
Tana gamawa ta mike ta mayar da komai wajensa sannan ta daura tawul a jikinta ta zauna gaban coiffeuse dinta,
Cikin nutsuwa take kimtsa kanta, hodar ruwa mai duhu duhu irin fatar jikinta ta dan shafa yar madaidaiciya wace ta kara haska mata fuskarta da wani sirri,
Nan ta samu ta kara bin gashin girarta ta gyara shi tsaf,
Jan baki ta dauka ta dan shafa kadan kalar pink domin koda Agaishat nada duhun fata lebenta kalar pink ne na kasan na saman ne mai duhu hakan ya saka na kasan kawI take sakawa jan bakin hakan sai ya bada kala.
Tana kokarin zirara kwali a idannuwanta ta ji dirar motoci,
A hankali ta mike ta leka ta windows,
Ya Allah, shi ne abinda ta iya furtawa ta saki labulen ta koma wajen gyaran kanta ,
Su Wardugu ne, motoci ne laye farare kar, du sun sha shada ruwan Baka, color din ya wani irin fito da shi, ya kafa hular da......
Tunaninta ne ya katse lokacin da Ayya ta turo dakin,
Hannunta dauke da wani Lafayar ta karaso ,
Ayya ta ce" tashi ki saka kayanki su Wardugu sun zo daukarmu
Mikewa ta yi ta karbi lafayar mai mahaukacin kyau da wani tsare tsare mai ruwan turkudin ta je ta ciro yar doguwar riga mai gajeran hannu fara kar a kayanta ta dawo ta saka rigar ba wani bars a ciki,
Ayya ta mike da Lafayar ta shiga nada mata cikin nutsuwa har ta gama tana dubanta,
Hancinta ta ja ta ce"ki karanta lahaula wala kuwata illa billah ki shafa a jikinki da li.ilafi, masha Allah kin yi kyau Yata,
Agaishat ta saki murmushin jin dadi ta ce" Ayana na gode😊,
Ayya kam binta take da kallo inda Agaishat ta juya ta dauki takalmi da yar jaka wace ta ado ce kawai domin ko wayar babu batama san inda ta yarda wayar ba,
Nan ta shafa humura da turaren feshe na hamata sosai ta shashafa sannan ta karasa kusan Ayya tana duban irin yanda Ayya ke kallonta
Fitar dakin ta kashe da Ac suka rankaya kasa ,
Tun daga sama gabanta ya buga, domin Walyn ce hakimce ta hade cikin shadar baka itama ta yi wani irin kyau tamkar sarauniyar mekka,
An zuba zinari an coge da dogon takalmi da jaka , tana danna watsetsiyar iPhone dinta tana sakin dan murmushi da alama chating take kuma yana birgeta,
Da sauri ta kawar da kanta daga dubanta domin ta dago ta watsa mata kallon da ta rasa na kyama ne ko na raini ne take mata a kulun idan sun hadu?,
A hankali ta dube shi kanta a kasa ta ce" ina kwana Ya Wardugu,
Amsawa ya yi da "Lafiya,
Kawai, aman kuma kyam kallonta yake, lafayar ta yi mata kyau da yawa, gashi dan jaraba harda gayar yan daurin aure yake yawo maza masu farauta kuwa!
Fuskarsa ya gimtse ya mike ya fice gaba kafin du suke biyo bayansa,
Ja ya yi ya dan tsaya inda Walyn ta zarce wajen motar da suka shigo shi da ita, da dan mayafinta sai isa take bazawa ta shige motar ta hakimce abinta,
Ayya ce ta karaso kusa da shi, nan ya samu damar kara dubanta murya kasa kasa da yaren tubanci ya ce" yanzu Ayya fisabililahi a haka zata je wajen daurin auren? Gidan bikin da ya tara shegun masu jar fatan nan?
Ayya ta zaro ido tana dubansa kafin ta tafa hannayenta ta ce"""""
Barka da safiya
🐫🐫🐫🐫 *BAK'A CE* 🐫🐫🐫🐫
Na
*SAJIDA*
7️⃣2️⃣
*KUTKALE* (PRISON)
*AURE YAKIN MATA NE*
*KAMARTA, BATA DA NIYAR CUTARWA*
daga ALKALAMIN yar mutan niger *SAJIDA* in sha Allah,
.............kar ku bari a baku labari.........................
Ayya ta tafa hannayenta ta ce" ni ban ga aibun shigar yarinyata ba,!
Gaba ta yi taki tsayawa maganar ta yi tsayima inda Wardugu da mamaki ya dan rike habarsa yana girmama irin son da Ayya ke yiwa yarinyarnan , dan kuwa idan ba a kanta ba , bai ga abinda zai fada ba Ayya ta musa masa,
Kansa ya kada yana hangen inda aka bude masu, motar dake gaban tasa nan suka shige bayan su duka,
Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya hanzarta ya tafi wajen tasa da Walyn ya shiga shima,
Tafia suke inda Walyn ta narke masa kan kudin jakarta sun mata kadan shi kuwa ba tsayawa zai yi bank ta ciri kudi ba,
Yana dubanta da kulawa ya ce" menene marar dadin da ya hada ki da Agaishat ne da bakya amsa salamarta?
Tsai ta yi da shagwabarta ta dan tsura masa ido kafin ta dan hade yannayin farin cikinta ta ce" Wacece haka?
Wardugu ya juyo da kansa saman fuskarta da kyau, wacece? Taf, shi ya ayanna a ransa kafin yake gimtse fuska dan kar ta yi kokarin kawo masa raini da safiyar nan,
Walyn ta hadiye tashin balagar fitsararta ta ce" to aman Heart ka ga ai kai kadai ta gaisar, bayan kuma ni na girmeta, kuma ni ta tarar a zaune ko? Haka take min yarinyar ban san me take jin kanta da shi ba idan ta ganni ba zata girmamani yanda ya dace ba sai dai a wani dake ta min magana, ni shi yasa bana shiga sabgarta ko daya !
Wardugu kam tunda ya kawar da kansa bai kara ce da ita komai ba, shiru ya yi inda ya kai dubansa kan Wayarsa da sim din Agaishat ke ciki,
Wannan number tun jiya take kira da tura messages, messages sakarkarun messages, messages masu ban haushi,
A hankali ya bude wanda ya shigo yanzu ya karanta kamar haka " haba targui, tau ashak din naki ne ya motsa tun jiya an ki a kula ni? Ni kam zan yi maza na kawo kudin gaisuwa gida a san da zamana ko za.a yi maganarmu, bafa na son wasa da zuciya Targui,
Murmushi ya saki wanda ba zaka gane manufarsa ba kafin yake ajiye wayar yana kallon sun karaso sun parke ana jira daga gare shi,
Duban Walyn ya yi , da yatsarsa ya yi mata nuni da ta tsaya kar ta fita, sannan ya fita a kotar
Yana fita du suka nufo wajensa suka shiga kakare shi daga maroka da masu son su gaisa kai harma da masu harin rayuwarsa, su kam a shirye suke, tabas shadoji ne a jikinsu aman kasan rigarsu ba wanda bashida bindiga yar karama wace a koni lokaci suna iya cirota idan bukatar hakan ta tashi,
Tsayuwa ya yi ya kali gabas da yama, kudu da arewa, can ya yafito kanin Alhinayett dan saurayi sannan ya yi masu nuni da su barshi ya karaso,
Musabaha suka yi kafin ya ce" ina so a bude hanya a shiga da mahaifiyata,
Ai kuwa da sauri ya matsa dan zuwa ya bude hanyar sannan a bude kofar shiga da motar,
Wajen motar ya karasa wajen direba ya bude ya masa umarnin fita,
Yana fita shi kuwa ya msye gurbin direban sannan ya tayar da motar a hankali ya fitar da ita daga layin motocin ya shiga tukata cikin nutsuwa har cikin gidan su Alhinayett inda sojoji masu kaki dake wajen du suka kame masa wasu kuwa suka rufe motar dan bata tsaro har ya dangana da wajen da zasu fito sannan ya fita ya zagaya ya budewa Ayya gefen da take,
Jakar hannunta ya karba ya kamo hannunta na dama ya taimaka mata ta fito cikin nutsuwa sannan ya kai dubansa kan Agaishat dake ta son ta bude gefenta ya ki buduwa bata san sai da kys din hannunsa kowani bangare na motar ke iya buduwa ba,
Hannunsa ya mika mata fari kal fafada da shi inda ya dan leka dan ta gane nufinsa,
Hannun ta bi da kallo, kafin take dago nata dake rawa rawa a hankali ta dora saman nasa ta yunkura ta sako kafarta daya mai dauke da takalmi mai dan matsakaicin tsayi kafa ciki na fata aman an yi masa adon fari kar, zamo kafar da ta yi ya saka lafayar ta dan dage har kaurinta a waje,
Ita dai bata san ya aka yi ba, sai gani ta yi ya saki hannunta ya saka hannayensa biyu ya ja lafayar ta sauka ta rufe wajen da ya fito, sannan ya dago da fuskarsa suka hada ido cikin ido ,
Idannuwansa ya wani irin lumshewa a hankali, ya rage masu girma sosai , hakan ya sa samansu suka kumburo kamar mai jin baci kafin yake saka hannunsa ya ja rufar kan ta rufe gashin kanta da kyau domin kadan ya dan fito da siririn yan kunayenta masu tsayi da suka kara kawata kwaliyar,
Karasa fitar da ita daga motar ya yi ta hanyar kara kamo hannun nata,
Rawa rawa kafafuwanta ke yi, hakan ya sa ya bi cinyoyinta da kallo, dan kuwa lafayar dake jikinta bai hana cinyarta kadawa ba sakamakon rawar da kafafuwanta ke yi, dubansa ne ya kai kan yarensa, ya ga suraj kyam na kallonta, wani uban harara ya zabga masa wanda ya saka shi juyawa gaba dayansa lokaci guda,
Ayya ya ga bata wajen, wato ta shigewarta wajen matan , dan haka ya kara kusanta kusancin dake tsakaninsu ya rage murya ya ce" ki daina haka mana, ki daina rawa rawar nan, domin ba iya kafarki da cinyarki ke motsi ba😔,
Agaishat kam da ido take binsa tamkar ta ga sabuwar halita, inanta ke motsi? Ya Allah, da sauri ta kara jan mayafinta ta gyara rufar lafayarta kafin ta mika hannu ta dauki jakar Ayyarta da ya ajiye nan dan gyara mata lafaya ta hada da tata kanta na duban kasa ta shiga neman ta inda zata raba ta bar wajen domin gaba daya idannuwanta basa nuna mata hanyar bi , du ya cika wajen,
Tsayuwa ta yi gabansa hakan ya bata damar tsayuwa daidai kirjinsa domin ya fita tsayi, ajiyar zuciya ta sauke a lokacin da ta dago da fuskarta ta dube shi ido cikin ido, gabanta ne ya kara faduwa , wasu hawaye take ji suna kokarin zubo mata domin ji take sam jikinta tamkar ba laka, da kyar ta iya shagwabe fuskarta kamar koda yaushe idan zata yi magana ta ce" zan je wajen Alhinayett,
Wardugu ya yi murmushin da bai yi niya ba ya dan kauce ta raba gefensa ta shiga tafia mutanen na kadawa tamkar wace ke yi da gangan ,
Idannuwansa ya kara lunshewa sannan ya juya da kafarsa suka rankaya da jama.arsa suka koma waje,
A jikinsa yake jin Walyn na binsa da kallo, , niyarsa yana fitowa ya je itama ya sanyota, sai dai ya tarar wajen angwaye sun karaso an fara haramar daurin aure gashi kuma shi ke zama kusa da mahaifin Alhinayett din,
Hakan ya sa ya bada kys din motar ya bada umarnin a sanyota domin sosau waje ya dauki harama,
Captain Ashiru ne ya karasa wajen motar ya bude ya sanar mata abinda Wardugu ya ce,
Idannuwanta da sukai ja na bacin rai da tashin hankali kawai ta iya budewa ta watsa masa kafin ta mika hannunta ta ciro kys din motar ta fito ta shiga gidan gaba ta tayar da motar ta fita da ita ta yi tafiarta
Bata zame ko.ina ba sai gidan aminiyarta, tana shiga hankali tashe ta je ta zauna saman kujera,
Dubanta take tana tambayarta lafia?
Walyn ta ce" menene tsakaninsa da ita? Wacece ita?
..................gidan biki.............
Shagali kawai ake, biki irin na buzaye, guitar ake ta kadawa inda du suka hakimce suna dan shiga rawa da dadaya maza da mata ana cashewa cikin nutsuwa , sai ruwan kudin da ake zuba masa domin fitacen mawakin nan ne Bombino.,
Maza kuwa tunda aka gama daurin aure suka tatara suka daga sai compagni baba inda suka je suka wuni.suna gashin shanun da suka yanka sai dai udan lokacin sallah ya yi a tashi a gabatar ga masu yi , a ci gaba da gashi , wasu na buga coss, wasu na game din buil, wasu na zukar shishar su, abin dai ya kankama domin kowa da gayarsa ne, haka Mu.azam ya saje da su dan kuwa ba wani abinda Wardugu ke nuna masa na bacib rai a gaban mutane normal yake amsa shi idan hakan ta kama har yama ta yi suka watse kowa ya nufi gida dan a shirya daukan amarya,
An kai amarya gidanta, yan matan amarya sun sha adonsu ba.a kama hannun yaro, an sha shagali a tsare a tafiye irin ta sojoji, tsari irin na sojoji,
Daga nan aka kwashe yan matan amaryar kowace aka shiga maida su gida, Agaishat ta zo shiga motar gugun yan matan wani soja da kaki yace da ita General yace a mayar da ita gida,
Tsai ta yi da dan alamar tsoro tana dubansa dan bai nuna mata shaidar hakan ba, sai da mijin Alhinayett ya fito da waya a kunensa yana amsawa ya karaso inda suke tsaye ya ce" in sha Allah sire,
Yana kashewa ya dubeta ya fada mata General ya sa a mayar da ita gida,
Wajen motar ta karasa ta shiga ya jata suka dauki hanyar gidan Ayya ba um ba umum tsakaninsu dan tukinsa kawai yake duda tarin tambayar dake cin ransa,
Ranar diner............
*Chaina*
Garin da aka kawo Anna dan neman lafia tun daga lokacin da suka kaita asibiti docter ya tabatar masu da ta samu shanyewar barin jiki sanadiyar hawan jinninta da ya mugun tashi wanda take da shi da jimawa yanzu ya yi karfin da ya kaita haka, damuwa, faduwar gaba, fargaba, tashin hankali, da rike damuwa a cikin rai suka taru sukai mata ruf daya suka kwontar da Anna,
Likitan da ya dubata, shi ne ainahin wanda suka yi karatu da shi, wanda suka hadu lokacin da ta kawo fatimata jinyar yoyon fitsari, amininta, cike da mamakin itace haka? Ina ta shiga ya yi masu maganar su fita da ita, domin akoy halin hakan alhamdulilah sannan tana da bukatar nesa da kasar ko zata kwontar da hankalinta ta karbi magani yanda ya dace.
Toh Alhamdulilah za.a ce domin dai yanzu wajen sati uku kennan tana daukan magani da massage, da kulawar famillynta dake zagaye da ita, tana yakar kanta dan gannin bata saka su a damuwa ba, tana raha duda kasan zuciyarta na cike da kawar Agaisharta,
Sai abinda ke bata haushi irin yanda *Aminullah* damun mutane da kira da nacin ya take!
Zan iya cewa du wani mai tsoro a kusa ba zai iya shiga wajen ba,
Domin kuwa a yau ranar sojoji sun fito sun nuna su din su ne,
Kaki suka saka mai ruwan tsanwa da fari, baki dayansu,
Kowa ya karbe shi da tsarin halitarsa,
Sai hulunansu , sai wukake farare kar masu lankwasa,
......laye suke su....
Wayo hannuna😕😕😕😕😕😕😕😕
Hey readers more comment plz🙄🙄🙄🙄
🐫🐫🐫🐫 *BAK'A CE* 🐫🐫🐫🐫
Na
*SAJIDA*
7️⃣3️⃣
*KUTKALE* (PRISON)
*AURE YAKIN MATA NE*
*KAMARTA, BATA DA NIYAR CUTARWA*
daga alkalamin yar mutan niger *SAJIDA* in sha Allah,
........kar ku bari a baku labari.....
Laye suke tun daga bakin hall din har ciki suna jiran karasowar amarya da ango, inda mutane ke zauzaune gefe da gefe wato hagu da dama bisan kujerun karfe farare kar da aka dan daudaura masu wani dan kyale pink da fari a jikinsu sai yan table table a gabansu ,
Can gaba kuwa kujeru shida ne masu shige da kujerun falo na alfarma wa.inda aka tanada domin zaman ango da amarya da aminin ango da matarsa da kuma general da matarsa
Guitar kuwa sai tashi yake inda mutanen da suka riga suka zo suka nuna takardar gayatarsu aka barsu suka shiga suke dan rausaya daga zaune abinsu domin an hana kowa shiga rawa tukunnan
Kannen amarya da sukai anko da kawayensu cikin shadarsu bugagiya sai meko take kowace ka kala sai ka kara kala don sun hadu ba wani kwaramniya sun fito ba ta yarwa,
Haka akai motarsu hudu, sai motar amarya wace ke tare da Agaishat ,
Ta sha dinkinta da ta zaba, yau kam bata lulube gashin kanta ba daurin dan kwalin da akai mata daga gaba aka fitar da shi sosai sannan daga tsakiya daure shin da aka yi da dan karamin ribom sai aka fitar da shi gaba dayansa, hakan ya sa ya malalu a bayanta, ga rigar kanta yau mai wuyan Bateau ce wato irin wuyan nan na zamani mai tsayawa a kafada , sai yar siriryar sarka mai wani dan dutsi kwaya daya tal fari kar da yan kunayensa, sai farin takalmi da farar pos mai kyalkyali mai forme din heart, gashin idonta ta saka masa maskara hakan ya sa ya kara tsatsayawa ya kara yin duhu sosai, lebenta ta shafa masa jan baki ja mai dan haske kadan ba dayawa hakan ya kara fitar da kwaliyar tata dan daidai masha Allah wace ko a cikin duhu zaka iya gannin hasken fuskarta komin karancin hasken waje kuwa,
Kusa take da amarya wace ta sha nadin Lafaya fara kar aka zuba mata sarkar gold dinta da awarwaraye sai takalmi mai dan tudu itama mai ruwa sarkar wato zeba zeba hannunta bata rike da komai dan zai zame mata kaya,
Su biyu ne kawai a cikin katuwar motar da irinta kwaya biyu ce , dayar basu san ko su waye a ciki ba, aman baki daya motocin bakake ne wuluk har madubansu baka gannin na ciki ko daga gaba inda direba daya rak ke jan su cikin ayarin motocin,
A lokacin da suka karaso nan yan matan suka shiga fitowa inda Kanwar Alhinayet ta kara jadada masu tsarin shigar, dan kuwa sai amarya da ango sun fara shiga gaba, sannan General da matarsa, sannan aminin ango da matarsa, sai su kawayen amarya kowace da dan bouquet dinta na flower dan karami sai ta layu da soja daya wa.inda suke cikin yan tafiar makusanta da ango ne sosai manyan mutane ne suma daga colonel sai captain su shida ne wato harda Agaishat nada daya su bi bayan Amaryar da angon a haka su ratsa ta tsakiyar sojojin dake tsaye suka hada kawunnan wukaken nan na hannayensu sukai masu runfa da su, gldaga can gefe kuwa da yan yara biyu yayan buzaye dake watsa wani kyalkyali kyalkyali ga du wanda ya zo shigewa,
Wayarta dake jakar Agaishat ce ta shiga kuka a hankali da kidan celine dion i love u,
Cirota Agaishat ta yi ta mika mata , nan ta daga ta kara a kunnenta tana hangen motar dake kama da tasu mutanen ciki basu fito ba aman ta hangi angon nata ya fito ya karasa wajen motar,
Kallon Agaishat ta yi dake son a bude mata ta je wajen su sajida ta riko hannunta kafin take amsa shi da ohk in sha Allah,
Tana kashewa ta dubi Agaishat ta ce" Agaishana, dan Allah kar ki layu da kowani namiji kin ji? Ki zo mu shiga tare da ke mu saka Colonel tsakiya (wato mijinta)
Agaishat ta zaro ido da mamaki ta ce" wani irin ku saka shi tsakiya ba wani tsari sai kace mai.mata biyu? Allah ya sawaka yo dan me ba zan layu fa wani ba sai kace matar wani?
Alhinayett ta zaro ido ta hada hannayenta ta ce" ki rufa mini asiri dan Allah kar ki yi haka, walahi idan kika yi ina tsoron wajen nan ya hargitse 👏🏻
Agaishat ta yi mata wani kallon mamaki, da tarin tambayar me take nufi? Sai fai kafin take aika mata da tambayar aka bude motar,
Colonel ne, cikin shigarsa ta kakin shima, ya hade ya gama haduwa, hannunsa ya mikowa Alhinayett nan ta saka nata ta sauko,
Idannuwan Agaishat ne suka sauka kansa, shine a cikin motar ashe, ta madubi take hangensu, shi da matarsa, ta sha doguwar riga baka mai shegen kyau, ko dan ta san ita din fara ce take son saka bakin kaya? Sai dan gyale baki da ta dan yane kanta ta yi irin daurin larabawa da shi ya zagaye kyakyawar fuskarta, sai tanfatsetsiyar jaka baka mai adon fari fari wace ke cike da yayan banki domin yau ranar ta kara kankarowa kanta mutunci ne .
Kanta ta kauda cikin jin zuciyarta wani iri, a hankali ta kara kai dubanta wajensa, kaki ne jikinsa irin na kowa, sai hular kansa da ta dan banbanta, sai bakin takalmi dake walwalwal ko daga nesa ka hanga ka san zai yi kudi,
Fuskarsa a hade take yana duban yanda ake laya mutanen dan shiga wajen diner da yake fatan a yi a gama lafia,
Bai ga adonta ba, bai san a ya ta zo wajennan ba, yana fatan bata yi dinki irin na yan matannan ba , domin doguwar riga ce du suka yi sai dai an yi mata fant har saman kaubri, so yake ta fito a motar aman har yanzu shiru .... shi ne damuwar Wardugu!
Kallonta ta kawar daga dubansa ta mayar kan Alhinayett dake tsaye tana jiranta,
Murmushi ta yi ta saki kafarta ta fito a motar ta tsaya gabansu,
Innalilahi wa.ina ilaihi raj.une, shi ne abinda Wardugu ya fada a file kafin ya kawar da kansa daga dubanta ya maida wajen gugun mazan wajen,
Ido hudu suka yi da Mu.azam dake tsaye tare da Khadija da kuma daya daga cikin Kanwar Alhinayet tanai masu magiyar su zo su bi layin masu shiga da amarya aman fir ya kiya kan shi da ba soja ba ya zai bi lafi ya bata masu tsari
Kawar da kansa wardugu ya yi ya maida inda suke tsaye, nan ya yi ido hudu da mijin Alhinayett dake masa magana da fuska aman bai gane me yake nufi ba,
A hankali ya maida dubansa wajenta, dinkin shadar doguwar rigar da akai mata da sket , an saba lesh da shada ne cikin juna, leshen kuwa mai manyan tiloli ne, sannan du inda aka saka shi mai yawa ake sakawa, ga tsagun da akai gefe da gefe har saman ciki duda sket din ya hau har saman cikin aman du yanda ta yi wani juyi sai rigar ta dage dan kuwa an rage mata nauyi sosai tana daguwa du yanda aka so ta dagun,
Rintse idannuwansa ya yi lokacin da ta juya tana dafe kanta da alama fafatawa suke kan maganar ba zata jera da wani gardi ba bisa umarninsa, juyawar da ta yi, kamar da gangan ta hargitsa bayin Allah dake biye da ita ba dare ba rana wa.inda Allah ya halitata da su dan ta ringa zaman kawai (🤣), sai da sukai sama sukai kasa hakan ya saka shi jin kansa ya sara sakamakon tunanin ko ba shi kadai ya ga hakan ba?
Juyowa ta yi tana duban mijin Alhinsyett ta ce" dan me ni kadai za.a hana cikin mu duka? Wani abin na yi? Ni a maida ni wajen Ayyana dan kuwa ba zan zo dan taron ba ace ni ba zan shiga ba
Ta karashe tana yin takwaf takwaf da fuskarta tamkar zata fashe masu da kuka,
Alhinayett ta matso ta kama hannunta zata yi magana kennan sai ga Farid, cikin shigar shada gizner ta sha aiki simple ruwan sararin samaniya ya dan dora wani mayafi fari kar a kansa abin rawaninsa ne sai ya yi yafe da shi, dogon buzu fari, bashi da jiki ko kadan ,
Ya jima a wajen tun kafin motar amarya ta karaso yana ts nemanta,
Gaban Alhinayet ne ya fadi ta yi saurin kara damkar hannun Agaishat tana dan waiwayen Wardugu ta ga kyam a tsaye yake su kawai yake kallo,
Da dan karfi ta janyo Agaishat da ta ga Farid ta sakar masa dan murmushi tana kokarin gaisawa da shi Alhinayet ta janyota,
Alhinayett ta hade fuska sosai ta ce" ki rufa mana asiri, ki rufawa kanki asiri Agaishat,
Kar ki tabo abinda ya fi karfinmu,
Kina wasa da lamarin da ba zaki iya tara ba,
Kar ki kula kowani namiji a wajen nan, idan ba haka ba ina mai tabatar maki zaki janyo rigimar da zamu kwana muna tserere a wajen nan a yau!
Ido ta zaro da yannayin tsoron yanda Alhinayett ke magana, ga mijinta shima sai waige waige yake yannayinsa na nuna bashi da nutsuwa,
Bata kara tsurewa ba sai da ya matso ya ce" Alhi, idan ta ki amincewa mu juya gida mu duka a fasa dinern,
Agaishat ta ce" wai me ke faruwa? Meye aka yi?
Mijin Alhinayett ya dubeta da kyau ya dan karancin yannayin firgicin da ta shiga , dan haka ya ce" wajen ne da hatsari, shi yasa ake kare lafiarki domin ba.a san me dauke da hatsarin ba,
Ai kuwa nan da nan ta shiga kifta ido ta rike hannun Alhinayett ta shiga waiwaye, ganninsa ta yi kyam a tsaye, ba zata iya fadin yannayinsa ba domin dare ne koda kuwa wajen ya kawatu da hasken fitila dare dare ne,
A yanzu muradinta ta kasance kusa da Ya Wardugu, snce waje da hatsari? Dubanta ta maida wajen shigar, an layu su kawai ake jira,
Sai ta maida wajen Farid ta ga yana tsaye da wayarsa a hannunsa, ita yake kallo, hakan ya saka da hannunta ta masa nuni da ya biyo bayansu,
Juyawa suka yi suka je gaban layin inda Wardugu ya cira kafarsa da Walyn da hannunta ke cikin nasa ta gama wayar da take amsawa suka bi bayansu,
Da farko tsakiya suka saka mijin Alhinayett, daga baya ta bar wajen ta koma bayan su Alhinayett ya kasance su Wardugu da Alhinayett sun sakata tsakiya,
Yau Wardugunma bata iya gaisarwa ba, dan a dan rikice take , fama take su yi su shige, aman ganninta kusa da shi sai ta ji ta samu nutsuwa, ko ba komai ta san idan wani abin ya nufota da yardar Allah zai tare mata, kai ba ita ba, du wanda ke wajen bashi da dar!
A hankali suke takawa, salon kidan ya canza, daga can gefe aka harba bindigar toka ta yi kara sannan aka saki kidan harbin bindiga wanda ya saka du jiki ya kwashi wani tsam,
Idannuwansa a kanta, du wani motsi nata , sannan hankalinsa du a tashe yake, sai dai a fuskarsa ba zaka taba fahimtar hakan ba domin ya hade fuskar tamau ba wani fara.a, hakama yaran nasa ba wani mai isashen sakewa dan kuwa kasancewa a wajen party ba zai hana ya ci ubanka ba idan ta kama!
Yanda tsarin yake sai amarya da angonta sun zauna kafin kowani namiji da ya jero da mace ya rakata har wajen zamanta gefen hagu sannan ya koma gefen dama domin rawar guitar, (sai wanda ya san yanda ake yi zai fahimata🤪🤪🤪🤪🤪),
Amarya da ango na zama suka fara juyawa dan kai yan matan wajen zamansu,
Dan tsai ta yi a lokacin da ta fahimci yanda wajen zaman yake, haka ta juya jiki sabule zata je wajen zaman yan matan ta zauna ita daya,
Bai fi taku biyu da ta yi ba ta ji hannunta cikin nasa, ba zata iya rasa sannin hannunsa bane domin ta gama karantar yanda hannunta ke zama daram cikin nasa,, ta yannayin da jikinta ke nuna mata du idan ya yi irin wannan lamari ya saka ko dubansa bata yi ba ta karantawa zuciyarya shi din ne, a hankali ya kara kusanta kusancinsa da ita ya shiga bin takunta ba tare da ya kaleta ko ya ce da ita ufan ba har suka sauka suka nufi wajen zama,
Suna karasawa ya tsaya wajen kujerar da kanwar Alhinayett ke zaune, wace take facing dinsa ,
Kallonta kawai ya yi da idannuwansa ta mike a wajen ta koma wata inda ya kali yannayin kujerar kafin da hannunsa na hagu ya yi mata nuni da ta zauna,
Cikin nutsuwa ta dago idannuwanta da sukai mata nauyi , nan ta ga ikon Allah ashe du yawancin hankalin mutanen wajen na kansu, tun daga kan sojojin har yan matan wajen, uwa uba Farid da ta gani zaune shima ya yi zuru yana kallonsu,
Da sauri ta zauna tana dan zaro idannuwanta inda ya dan yi tsai , kafin ya rage tsayinsa wajen kunnenta ya ce" Na haramta maki motsawa a nan har sai an tashi!
Du mai kallon su, zai yi tunanin maganar soyaya ake a wajen nan, zai yi tunanin an gama mutuwa a son juna ne, bai damu da kallon da ake binsa da shi ba, hasalima sai da ya dan kara tsayawa ya mike da kyau ya bi kowa da kallo hakan ya sa mutane suke kawar da dubansu daga kansa kafin yake nufar kujerarsa,
Walyn, Walyn, walyn, wani kakausan kallo take binsa da shi har ya gama du abinda yake ya dawo ya zauna a wajensa wato kusa da ita,
Bata dubi tarin mutanen wajen ba, bata yi la.akari da wajen ba bale ta ari kissa irin tamu ta mata ba, yana zama ta shiga magana kamar haka" Wardugu, wannan wani irin mulakanci ne? Meye hadinka da kaskantaciyar yarinyar da muka dauko daga kasurgumin jeji dan cireta daga kangin talauci? Meye daraja a bakar mace har da zaka dauki hannunka mai daraja ka rike nata? Wardugu menene tsakaninka da tsohuwar bazawarar da amininka ya aura ya saki dan ba zai iya zama da ita ba? Wardugu wacece ita a wajenka? Wardugu!
Ta karashe tana mai dan daga murya da wawatsa hannayenta wanda duka na kusa da su na jin abubuwan da take fada da irin dibar albarkar da take tafkawa inda na nesa da su ke hangen Walyn na yuwa Wardugu fada , domin kuwa geste dinta kamar uwa na yiwa yaronta fada ce, irin zazafan fadan nan ma kuwa,
Dubansa ya dago ya dora saman kanta, hauka? Shirme? Aa Raini! Kai tsaye, ido cikin ido, ba wani gargadar murya, ba wani kawar da fuska, ko tausasa harshe Wardugu ya ce" kina son ki san ko wacece ita? Ita din *ORRONUR* dina ce.......
Dankari,
Kaka kara kaka
Ku samo ma.anar ORRonur sai na baku wani page😕
Walyn? Walyn! Wardugu!
Agaishat
More comment bilahi🙄🙄🙄🙄🙄