Bata kai ga magana ba dogarai ke sanar da shigowar sarki falon sirikan nasa , daman da baba tsoho ma shi ke fasara tsakaninsu domin ba komai yake ganewa ba shi kuwa sarki ya zauna da tubawa
Tunda ya shigo Anna ta sada kanta dan kunyar siriki, shima du a wani takure yake inda Gaishat ke binsa da kallo tana tambayar kanta me ya kawo shi ko bakinsa ne?
Gyaran murya ya yi ya ce" Anna, ina fatan kin san baba tsoho, wanda Agaishat ke zuwa wajensa babanta kennan
Daga inda yake ya daga murya da irin abin haushi haushi ya ce" ya zata manta kwartanta uban yarta? Ai ni dama na san dubunki sai ta cika munafuka, yau dai ga zance zai bude
Da wani irin yannayi Wardugu ya kai dubansa daga inda ake maganar, wa ke magana ta rashin da.a haka? Shine abinda yake tambayar kansa din wardugu na jin yaren buzanci kai bama buzanci kadai ba wardugu irin mutanen nan ne masu kwakwaluwar kwashe yaren da ba nasu ba, yana jin yaruruka da dama, hakan ya bashi damar jin abinda ake fada harma wanda Algabiit ke aikowa daga daka
Sarki ya girgiza kansa kawai, ya san wanene Algabiit farin sani, kuma fa ya san harma gudumuwarsa wajen Algabiit ya tsula tsiya a garin aman ba komai zai dauki mataki ne tun kafin ya saka a tarwatsa su baki daya
Anna da ta kasa hada ido da shi ta gyada kanta, ya zata kasa gane mutun mai daraja a idannuwanta? Wannan mutumin ko dan tsufansa a girmama shi aman Algabiit ke aiko masa da zagi haka? Ta yi imanin ba ita ba ko Algabiit din baba tsoho ya haife shi
Bak'a kuwa tunda ta kyala ido ta ga baba tsoho ta samu ta rakube jikinsa tana dan jefo masa tambayoyi a hankali da alamun tsegumi
Hannunsa ya saka ya dungure mata kanta yana murmushi, a ransa ya ayyana idan kika tafi,....nishadina, murmushina, zai tafi da ke
Sarki ya ci gaba da fadin" wadinnan mutanen da kike ganni, wannan baiwar Allahm mahaifiyar wannan bawan Allahn ce, sannan ta taso tun daga garin da kuka kai Fatimata rashin lafia ta zo Agadez daga nan sun dauki hanya sun zo garin nan dan neman baba sofo da ya baiwa dan nata maganin huka tun yana yaro bisa alkawarin idan an samu lafia sai ta bashi abinda ya samu
Toh Sai aka tashe su Allah bai yi sun kara haduwa ba, tun daga lokacin take nemansa domin mutun ce mai son cika alkawari abin na tsaye a ranta sai yau Allah ya yi
Dan numfasawa ya yi, ya ci gaba" kin ga, ba a niger ba, ko a kasar waje masu fada a ji ne,
Sun zowa Baba sofo da alkhairi na mamaki sai dai abin mamaki baba ya ce sam shi yanzu ba ta abin duniya yake ba, ya yafe sai dai damuwarsa *AGAISHAT CE*
Anna ta dago da sauri ta ce " AGAISHAT?
Sarki ya ce" kwarai kuwa, Baba ya nemi alfarmar......................................................gaba daya sarki ya kwashe yanda suka yi baba da su Wardugu ya fadawa Anna dake zaune kanta na kallon kasa sauran yayanta na zagaye da ita Bak'a kuwa na jikin Baba sofo
Da sauri Bak'a ta dago ta kai dubanta wajen Anna da Sarki, ta maida dubanta wajen baba Sofo,
Baba Tsoho ya yi gyaran murya ya ce" shakuwa, da tunani ya hana ni sakun nutsuwa Annar Agaishat, na sani bani da ikon zartar da hukunci kanta domin ban haifeta ba sannan ni ba wani shakikikin dan uwa ba
A duniya adu.ata biyu ce, Allah ya sa in gama da duniya lafia Aljanna ta zamo makomata , fatan Allah ya nuna min ta zama mutun mai cikaken inci, ta samu nutsuwar zuciya , ta samu zama itama mutun,
Anna Agaishat ta yaya hakan zai faru? A timiya mu duka bamu fi kirgo da yatsu ba, nan da kike ganina har limamin garinnnan na nemi alfarmar ya aure man ita mana aman ya nuna aa ba zai iya ba
Almajirina ma ya kiye min,
Gashi yau da gobe sai Allah, Agaishat girma take, mu kuwa gajiyawa muke kara yi,
Idan ta fito daga nan ina ta fada? Me ta ci? Ya ta yi ta samu Allah ne masanin gaibu, ni kam a matsayina da wanda take zuwa wajensa sannan ta daukeni tamkar uba nakan yi mata nasiha, nakan tsoratar da ita, nakan nuna mata karara rayuwa da abinda Allah ya bani ikon sani
Annar yara , Ba zan tirsasa maki ba, ba zan saka ki daukan abinda zaki yi ta nisawa zuciya bata da tabas, aman ina so ki yi tunanin gaba da bayan lamarin, in da hali ki dauki Agaishat ki baiwa wannan mata riko da zuciya daya, ki yi kyakyawan zato, ki saka a ranki alkhairi ne sannan ki bi da adu.a, na yi imanin koda mugaye ne Allah zai saka mata kaunar yarinyar shari ya juye wa khairi
Wardugu ya yatsina fuska ya dubi Ayya dake zaune tana kallon su, da yaren tubanci ya ce" Ayya, yarinyar nan fa wannan mahaifiyarta ce , kuma ina jin shegiya ce shi ya sa wancen yake zazaginta haka! Ayya me ya sa suke faman rabuwa da yarinyar? Ayya
Wardugu ya isheka haka , Ayya ta fada tana zaro masa idannuwanta, murya a kausashe ta ce" baka lura da abinda ke faruwa ne?
Ba zato ba tsamani muryar Anna, cikin yaren Tubanci ta ce" ba shegiya bace, wannan da ka gani ya shige daki ya labe shine ubanta, yana kyamatarta ne dan ta zo duniya *BAK'AR FATA*
Da mamaki du suke kallonta,
Ayya ta taso ta karasa kusa da ita, hannunta ta kamo tana kallonta ta ce" batuba ce ke?????
Anna ta lumshe idannuwanta sai ga hawaye sharsharshar ta dan jijiga hannun Ayya ta ce" ban sani ba, ban san ko mecece ni ba,
Damko hannun Ayya ta yi da dan karfi ta saka idannuwanta cikin nata ta ce" ban san ko dan ina jin yarenki ba? Sai kawai nake ji zan iya sadaukar da y'ata wa ke, zaki rike mini yarinya da gaskiya?
Ayya ta ji gabanta ya dan fadi, matar na tare da wani banban lamari, Ayyan ta jijiga hannayenta itama tana kallonta ta ce" mudin raina
Algabiit dake ciki sai zaro ido yake, ya shiga ukunsa, ya aka yi Anna bata manta yaren nan ba? Aman abinda ya yi mata *Harta sunnanta ta manta*! Domin kafin ya lulo timiya da ita sai da ya tabata ta iya yarensa, ta iya saka kaya irin nasu, ta iya yan dabi.unsu, shigewa ya yi ciki ya zauna jikinsa na dan rawa rawa
Anna ta lumshe idannuwanta, ta ce" thank you,
Wardugu dake tsaye ya kalo su , Inglish kuma? Inglish ta yi?
Hai san ya karasa shigowa dakin da kyau ba sai da ya karasa, inda shigowarsa ya saka du yan matan suka tsaya kallonsa da mamaki, Bak'a kuwa ta lafe da tsoro jikin baba tsoho jikinta du yayi wani sanyi tana son fahimtar maganar tafiya da wa wai ake? Ina ai ita ba inda zata, ba zata bi wasu mutanen da bata sani ba bata taba gani ba ta je a kasheta, ya zata iya tafia ta bar yan uwanta da annarta da baba Sofo? Wa zai ringa kawo masa ruwa? Wa zai ringa saya masa gogo yana gurza masa a karfen gurje goro? Wa zai ringa koya mata karatu? Wa zai ringa ce mata itama mutun ce dan tana baka Haka Allah yake son ganninta ?
Wardugu yana karasowa ya dan duka yana kallon Anna ya ce" di u speak Inglish?
Anna ta dago ta kale shi, ta amsa masa da kanta, a ranta tana nanata inglish? Wani yare ne shi kuwa? Ba irin wanda suke yi da matar bane kennan?
Wardugu da mamaki ya ce" ya aka yi kika iya inglish? A ina kika koya? Wa ya koya maki? Daga wani gari kika zo?
Anna da kanta ya fara sarawa ta dafe kanta da sauri , muryarta ya fara rawa rawa ta ce" i...i...i don't know ! Ta fashe da kuka tana rungume hannayenta da sauri Gaishat ta karasa tana rungumo Annarsu itama tana kukan za.a kuma raba su da yar uwarsu? Domin ta sani ne , a yanda anna ke jin zafin irin abubuwan da ake yiwa Agaishat , a yanda aba ya tasota a gaba da man bleating kan sai ta shafa ya yi kudinta itama , anna na neman koma waye ta bashi aurenta ta tafi ta huta, ta gwamace ta tafi ta auri koma waye da aba ya yi kudinta itama kar a je ta fada irin rayuwar da fatimata ta fada ko ma wace ta fi ta
Sai da Anna ta yi kuka mai isarta, suba bata hakuri kafin take share hawayenta ta yafito Bak'a sake kukan yan uwanta da mamanta na kuka
A hankali ta taso ta nufo Anna
Tunda ta taso suka sauke idannuwansu kanta
Wardugu ya tsura mata ido, a ransa ya ayyana " Eh lale baka ce, tana da baki sosai da kuma kazanta, a rayuwar kauye dole su tsangwameta domin gari ne mai bambace bambance
Kawar da kansa ya yi, jikinsa ya yi sanyi da lamarin uwar yarinyar, tabas akoy bamban al.amari a tatare da ita, da farko ya so ya cakula abin, ya kasance an watse su yi tafiarsu ba tare da Ayya ta kwaso masu wani jangom din ba, sai dai ina yanda matar ta yi yarensa tar tar tamkar nata, sannan ta shiga turanci tamkar yarenta shima, kuma ta furta bata san bama sunnan yaririkan da ta yi, harma ta shiga wani yannayi dan za.a takurata da tambayoyi ya saka shi yin sanyi, a hankali ya furta" sai na san su waye ku!
Anna ta kamo hannunta ta zaunar da ita daf da daf, ta dago fuskarta, abinda bata taba yi ba irin kusancin nan da yar tata, tana so ta yi tana mugun tsoro da kunya
Murya a raunane ta ce" Agaishat, Ina son ki
Da sauri Agaishat ta kara kallonta,
Anna ta sakar mata murmushi ta ce" sosai, ina son ki, kuma ina so ki samu canjin rayuwa, bana so ki kare a haka bana so ki kare a ciki duhun rayuwa
Gaishat ta ce" Anna, Anna
Anna ta kallota ta ce" menen Gaishat? Kar na raba ku da yar uwarku?
Na san muna cikin jimamin mutuwa, muna cikin rudu, aman ku kun fi kowa sannin rayuwar da muke , mutanen nan na tafia in dai ba da ita ba na yi imanin ba zai barta ba tunda ya saka wannan lamarin a ransa sai ya aikata
Da wa zai hadata? Ina zata fada? Mai yiwuwa idan aka tsilira da ita wani wajen koda ta so guduwa ishrwa ta kasheta a hanya,
Agaishat ta fashe da kuka jikinta ya kwashi rawa ta ce" Anna aa, aa Anna, kar ki bada ni haka Anna, ku kadai na sani Anna, kar ki raba ni da ku, kar ki yi mini haka Anna, ki barni ina ganninki har in mutu, ki barni ina gannin baba Sofona ina kai masa ruwa yana kiya mini karatu, ni ba ruwana Aba ya yi ta dukan nawa ba komi Anna in dai ina ganninki ina gannin yan uwanna ina gannin Baba Sofo ya isheni Anna, kar ki rabani da abinda nakeda a duniya wato ku........
To jama.a ya zama kwashe ne? ............m
🐫🐫🐫 *BAK'A CE*🐫🐫🐫
Na *SAJIDA*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________
1⃣7⃣
Anna zuciyarta ta yi mugun karyewa
Hawaye yana shatatar mata muryarta na rawa ta ce " Agaishat, ki yi hakuri ki bi su, ba mugaye bane
Agaishat ta buda idannuwanta da kyau ta ce" kina da tabacin ba mugaye bane? Kina da tabacin su din mutanen kirki ne??
Jikin Annan ya yi sanyi ta sada kanta
Gaishat dake hawaye itama ta matso ta dafa hannun Agaishat ta ce" Agaishat....
Anna ta dago ta ce" bani da tabacin halayensu, ba zan ce su din mutanen kirki bane kuma ba zan fadi akasin hakan ba
Agaishat, ni da na haike ki, ni da na yi rainon cikinki, na haife ki , tunda kika ji na ce ki je, toh ki je din kawai....ba zaki fahimci girman maganana ba sai ranar da Allah ya nuna maki kin haihu, soyayar dake tsakanina da ke na iya cewa ki je to ki yarda da na yi imani na barwa Allah komai ne, a nan kike ko a wani wajen dama shi ya halice ki, ko wace rayuwa zaki fuskanta shi ya kadaro maki, ni ban isa na hana ko na saka ba sai dai na yi ta kai kukana wajensa ina neman jin sanyi daga wajensa
Agaishat ta rintse idannuwanta, ita bama bin nasu ba, wannan mutumen da suke tare wanda yake tsaye tunda suka zo wanda fuskarsa bata ga saki ko tausayi a tatare da ita ba, shi take tsoro, in dai mugaye ne ta san shine mai yanka mutanen domin wannan da gani shine bamban mugun
Algabiit dake daka sai sintiri yake, haka zata tafi? Ba.a bashi komai na kudin tafia da ita ba? Koda ba yarsa bace ai shi yake ciyar da ita tunda aka haifeta, ya isa a yi shawara da shi sannan a biya shi! Sai dai yana ganin yanda wardugu ya diro daga motar nan ya nufosu, tun a lokacin ya fara sakin fitsari domin shi yama yi tunanin an zo kashe shi ne, ba zai fita gaban wannan mutumin mai kwarjini ya yi wani abin ba, aman ta yarda ta bada Bak'a haka zata gane bata da wayo!
Bak'a na ji tana ganni, tana gurzan kuka mahaifanta da rai ba babu ba, ba aure ba ba dangi ba aka fitar da ita tana waiwayen Anna da ta koma da sauri ta shige bayi ta rufe ta shiga rizgar kuka, aka shiga da ita cikin motar da bata taba gani da idannuwanta bama bale ta shiga,
Tana ji tana ganni matar nan ta shiga ta riko hannunta tana dan murzawa Alamar rarashi
Tana kallon baba Sofo har aka sako shi motar shima kafin da kyar sai da Wardugu ya yiwa Walyn tsawa ta shiga motar wai karni take ji na bak'a, ya shiga suka tayar tana ji tana ganni aka bar anguwarsu gidansu yara sai bin bayan motar suke suna ihun murna sun ga mota manya sai daga hannu suke har sai ta bace da ganninsu aka je kofat baba sofo aka tsaya suka sauke shi
Agaishat ta kara rikicewa gannin da gaske sun bar baba Sofo wanda ya tsaya yana daga mata hannu idannuwansa sun kara kodewa alamun kuka yake na zuci sai dai ya fi farin cikin hakan da zamanta a garin
Haka suka dauki hanya ba tare da sun huta ba ko sun sha ruwan garin ba suka dibi hanyar komawa garin Agadez
Kukan take tana fadin"" Anna, Sofo, Anna, sofo
Walyn ta ja tsaki ta ciro ecouteurs dinta ta saka a kune, Wardugu dake gaba ya rufe idannuwansa a tunaninsa zata gaji ta yi shiru ne aman ina sai kara boda Agaishat ke yi Ayya na tausarta tana bata hakuri da tubanci bata san ta dan iya hausa ba ita kuwa bata iya buzanci ba
Juyowa ya yi, da yaren buzanci ya ce" Ke ki rufe mini baki a nan tun kafin na saukeki na yi maki dukan tsiya, shiiit bakin nan naki ya mini shiru ko na ciro maki shi a hannunki
Wa ya ga hadiya, Agaishat hadiye kukanta ta yi, tana zaro ido tana kallonsu daya bayan daya tana sauke ajiyar zuciya,
Ayya tana magana tana yi mata nuni da ta yi hakuri ta yi shiru ta daina kuka
A hankali Agaishat ke ajiyar zuciya sannan ta damke hannun Ayya wace ke rike da nata itama, tana kallonta, a nan ita kadai ta dan hangi laushi a tare da ita
Tafiya suke suna ratsa sahara har suka baro suka debi titi,
Agasihat ko dis ba baci a tare da ita sai kallon titin da take , tsoro fal ranta haka idannuwanta suka nuna, mamaki take dama Shukoki na gudu? Domin yanda motar ke gudu sai take gannin suma shukokin gudu suke tun karfinsu
Walyn dake takure tana sakin numfashi sama sama ta shiga yinkurin amai tana kakari
Ayya ta kai dubanta wajenta da mamaki, lale walyn bata da mutunci, yanzu du irin yanda ta fafeshe su da turare tana jan tsaki kuma ta kai amai zata yi dan warin Yarinyar da suka dauko
Ta girgiza kai kawai ko ci kanki bata ce da ita ba
Wardugu dake zaune a ransa ya ayanna Walyn bata son zaman lafia, in dai Ayya ce ta isheki ba abinda ya dame ni!
Ba su su karasa cikin gari ba sai can wajen karfe goma na dare
Abinka da agadez ma ba wani banban gari sosai bane sai ya kasance shiru garin sai yan mata da samari wasu na tafe a kafa wasu a mota wasu a mashin suna dan yawansu na yau da kulun wasu sun nufi gidan rawa, wasu sun tafi gidan cin abinci, wasu suna yawatawa dan shan iskan gari kuma suna hirarsu
Idan ta juya can sai ta juyo nan, kallo take irin na kauyawa sosai jikinta kuwa har zuwa wannan lokacin bata saki ba, sai dai ta rakube jikin Ayya wace take kara rike hannunta dan ta saki jikinta
Direct gidan Sarki aka kai su Ayya, har ciki suka shiga da motar suka sauke su Ayya Walyn sai sauke ajiyar zuciya take ta rabu da alkakai
Har sun juya motar Wardugu ya ce" tsaya
Sojan ya ja ya tsaya ,
Wardugu ya juyo wajen Walyn ya ce" sauka ki kwana wajen Ayya
Walyn ta dago da sauri daga kakabe kakaben jikinta ta zaro ido ta ce" me me ka ce?
Wardugu ya tsareta da wani kallo na kar ki raina min wayo
Walyn ta ce" aman Wardugu , wani irin na sauka na kwana a wajen Ayya bayan ga mijina wajenka na sauka kayana a wajenka komaina na tare da kai? Yama zaka raba ni da kai ka hada ni shakar iska daya da wannan mumunar yarinyar mai siffar aljannu
Yatsina fuska ya yi, a ransa ya ce wai siffar aljannu, ko a ina ta san aljannun ita? A fili kuwa ya ce" Haka na yi ra.ayi
Walyn ta ce" Wardugu kar ka yi min haka, me na maka? Kar ka yi min irin horon nan!
Wardugu ya kalli sojan nan ya ce" sauka mu je
Sojan dai bai ce komai ba ya bude ta fita da bindigarsa yana kallon ikon Allah
Wardugu ma ya fito ya rufe ya tafi wajen sojan ya fara tafiya, sojan ya waiwaya ya ga a yanda suka ajiye motar a bakin hanya, bayan wannan matarsa a ciki, sannan tsakanin fadar da hotel din sojojin akoy tazara, kuma idan mutun ya tunkaro wajen haka kai tsaye daga bakin karfe goma na dare ordre da aka baiwa sojojin shine harbi ba ji ba gani in dai ba a mota ko wani abinda yake malakinsu ba wanda da ya tunkaro wajen akoy adadin odar da aka ce su yi dan shaida su ne wada kowace safiya ake canzawa
Shi dai biye yake da shi da sauri yana hadawa da fan gudugudu suna tafiya har suka fita daga gidan suka dauki hanya (🤔 sisi kika ce zaki iya da wardugu ko?🤣)
Walyn wani ihu ta saki a daidai lokacin da ta fahimci wardugu bara mata ya yi motar gaba daya ya tafi a kafa da ya je da ita, Wardugu ita yake wulakantawa? Toh ita kuwa ba zata shiga wajen wannan uwar tasa da wannan yarinyar mai karnin jini ba! Sai dai ta kwana a motar!
Haka ta takure a motar nan ta ki kunna hasken waya dan a gaskiya tsoro take ta kunna waya wani abin ya lura da mutun tun bama dare da ya tsala maguna suka fara kukan jarirai ba,
Kawata, tsakaninki da Allah ke haka rayuwarki wata irin mace ce bahaguma? Yanzu yarinyar nan da kika kwaso kin san asalinta ne?
Ayya ta yi murmushi tana kallon kawarta aminiyarta matar sarki, ta ce" mamanta ta iya tubanci
Anna matar sarki ta dafe kai ta ce" dan ta iya tubanci sai me? Dan ta iya yarenki shikennan sai ki wani kwaso yarta? Kin ce a gidansu kuka daukota
Ayya ta ce" ki gane kawata, lamarin mahaifiyar yarinyar da yarinyar ne akoy sarkakiya, wai kawai dan kalar fatarta shikenan take fuskantar tsangwama, ita kuwa uwar sai kawai ki ji tana yare kuma wai tace itama bata san sunnan yaren ba, kuma ni na yi haka ne dan cika alkawarin bawan Allahnan, baki ga yanda ya tsufa ba aman haka yake nisa lamarinta,
Anna matar sarki ta dafe kanta da hannunta dake cike da zobunnan zinari ta kalota ta ce" ai idan kin lura yanzu wannan matsakar ta zama ruwan dare, a kauye suna kin bakar fata tare da jahilci a birni suna kiyaye bakar mace dan dogon buri irin nasu sannan suna hakan ne da dabara, kina ganni daidaiya zaki ga a yanzu mutun ya tashi ya dauko bakar mace, sai ki ji suna fadin Allah ya basu farar mace koda maya ce, banza idan ta cinye su fa?
Ayya ta dora kafarta daya saman daya tana ajiye tufar da ta gutsura ta ce" ba ko.ina ba, ban ki maganarki ba aman nima nace maki ba ko.ina ba,
Du macen da kika ga ana yi mata duban marar kyau ko anai mata wani gani gani ina mai tabatar maki ita ta saki kanta,
Mace du muninta idan ta iya wanka ta iya kula da jikinta ta iya kwaliya daidai da yannayinta sai ta kara da adu.a kawai
Sannan ita bakar mace da kike ganni baiwa ne da ita, bakar mace tana da kwarjini, bakar mace nada juriya a kowani fani, bakar mace na da kyau mai fuzga, idan bakar mace ta sakar maki tsararen murmushi zaki hangi haske ne a tatare da ita, ke kawata zaki sha mamakin yar amanata in sha Allah
Anna matar sarki ta yi murmushi tana jujuya kanta ta ce" oho dai, kina kare bakar fata dan kina da ita bayan taki mai kyau ce, na rantse maki ko ni na samu taki ina so domin bakinki mai kyau ne, ba gashi ba Wardugu ya samu dan bakinki da farin mahaifinsa sai ya samu kalar fatar nan ta yan ethiopia baki ga yanda fatarsu take ba? To aman wannan yarinyar kina ganni da akace wanka ta saka kuka aman kika biye mata wai kika rakata ta yi baci a haka? Anya kuwa zaki iya wani gyarata?
Ayya ta ce " ki saka ido kawai.....
Sojan nan tafiya dai yake aman ba karamin gajiya ke tatare da shi ba, sai ya ga Wardugu daga kafa kawai yake yana jefawa yana kara kutsawa cikin duhun garin suna ta sauki su karasa hotel din
Ba su su karasa ba sai kusan sha biyu na dare,
Suna karasawa Wardugu ya saka kai kai tsaye ya nufi shiga wajen da idan ka shigo harbi ne zai salamo maka ....................
Kadan ne ku yi maneji😍😍😍😍
🐫🐫🐫 *BAK'A CE*🐫🐫🐫
Na *SAJIDA*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________
1⃣8️⃣
*Godiya ta tabata ga Allah sarkin sarauta ubangijin talikai, godiya mai dumbin yawa gareku da adu.a Allah ya saka da alkhairi ya biya ....*
*Khadijat tawa ta grup BAK'A CE* wannan page din naki ne
Ja sojan ya yi ya tsaya bai san lokacin da ya ce " Oga, zone interdite ce fa
Wardugu ya juyo yana kallonsa, ya yi murmushi ya ce " tsoro kake ka mutu sergent?
Kansa ya dan shafa yana kallo Wardugu,
wardugu ya kara cewa" mutuwa fa ko kana kan gadonka sai ta daukeka sergent ba gwara mu tunkareta ba?
Kara kwalalo idannuwansa ya yi yana kallon wardugu
Wardugu ya matso ya dafa kafadarsa ya yi murmushi ya ce" mu je ......
Haka suka kutsa gaban Sergen din nan tamkar ya bale ya fado dan tsoro,
Sai dai ga mamakinsa sai ya ga sun kama wata yar raga a nan Wardugu ya bude ya shige
Shima shiga ya yi yana ta waige waige yana biye da wardugu nan ya hango ashe har sun shiga balbalin hotel din sun fice hatsarin
Wara wawar ajiyar zuciya ya sauke yana biye da wardugu
Wardugu ya rage sauri ya dan rage sautin muryarsa ya ce" nima bana so na yi mutuwar bindiga fa Sergen, ina so na mutu cikin nutsuwa kai da zabi gareni in mutu ina sallah kuma ranar juma.a,
Aman kawai yau ranar asabar gatsai gatsai sai mu tarbi mutuwa? Da juma.a ne ma,
Ya dan yi murmushi ya yi gaba ya barshi nan tsaye yana murmushin shima, kai ogansa idan ya yi wani abin tamkar ba shi ba, wai shifa a nan wasa ya yi masa da rai🤔
Tun fa wuri ta farka daga bacin da ya saceta, sai dai ta ki motsawa tun a jiya da aka sauketa saman gado ta yi baci ta kasa ta sauko kasa ta kwonta saman farin tls din ta rufa da mayafinta na turkudi tana kallon yanda pankar sama ke juyawa har baci ya dauke, a yanzuma ta farka tun da wuri tana son tashi sai dai tsoro take hakan ya sa ta yi kuri da abin mamaki a fuskarta tana kallon pankar nan, mamaki take menene? Ya aka yi bai daina gudu haka ba? A gaban idannuwanta aka kunna , tunda ya dauki gudu bata ga ya tsaya ba, ita tsoroma take ya yo kasa kasa ya kasheta
Ayya ce ta bude dakin ta shigo da salama a bakinta
Firgigit Bak'a ta tashi ta zauna jikinta jikin garu tana bin Ayya da kallo
Ayya ta yi tsam itama tana karantarta, a kasa ta kwana du sanyin nan na kasa, sannan da alama bata yi sallah ba
Dukawa ta yi kusa da ita tana kallon yanda take jan mayafinta tana lulubawa a jikinta,
Murya a sake ta ce" kin yi sallah?
Da ido kawai Agaishat ke bin Ayya domin bata san me take fada da yaren tubanci ba
Ayya ta yi dabara ta kamo hannun Agaishat ta mikar da ita ta jata suka nufi bayi
Suna shiga Ayya ta dauki butar karfen dake wajen ta kunna ruwa mai dumi dumi ta cika mata ta nuna mata wajen da zata iya dukawa domin ta san ba wani gane lamarin wc zarai ba tukunnan dai, ta yi mata nuni da ta yi dagara ta yi alwallah ta yi sallah , ta yi mata nuni da har rana ta fito
Da kai Agaishat ta amsata tana kallo sai da ta fita ta duka ta yi fitsari nan inda aka nuna mata ta wanke jikinta ta mike ta yi alwallah tana jin dadin yanda ruwan keda dumidumi
Tana gamawa ta fito ta ga salaya aman ba kowa a wajen dan haka ta hau ta tayar da sallah ta yi abinta cikin nutsuwa kamar yanda Baba tsofo ya koya mata
Tana gamawa ta zauna ta hade kanta da gwuiwarta tana zubar da hawaye, tunani take ya Anna ta tashi? Ya yan uwanta? Ya baba sofo? Wa zai kai masa ruwa? Wa zai gurza masa goro? . .....
Buda kofar aka yi aka kuma shigowa ,
Wannan karon matar sarki ce da wata baiwa buzuwa da kuma Ayya
Ayya ta kali matar sarkin ta ce" so nake a fada mata ina so ta yi wanka ta shirya mu tafi garinmu domin Wardugu yace jirgin karfe daya zamu bi
Matar sarki ta yi murmushi har yanzu tana mamakin daukarwa kai irin na aminiyarta, ita da ko hausar juna basu iya ba
Ta kali baiwar nan cikin isa da dakewa ta fada mata abinda zata fadawa Agaishat wace tunda matar sarkin ta fara fadi take kallonta daga zaunen da take tana fahimtar yarenta
Kafin ma baiwar ta fadi Agaishat ta kallo Ayya, a hargitse ta ce" ina zamu tafi kuma? Kar ki kaini wani wajen kin ji? Ki barni a nan ma
Tana fada ne tana dan nufo su Ayya dake tsaye
Baiwar ta yi saurin tareta , da yaren buzanci ta ce" ki tsaya nan, kin san ina ne kike a nan? Kina garin agadez, a garin agadezma kina masautar agadez, a masarautar agadez ma gaki gaban matar sarki uwar gida sarautar mata,
Ki koma baya ki cika umarninta
Rakubewa Agaishat ta yi tana kallonsu, ta shiga ukunta, ya zata yi? Matar sarki kuma? Ko sarkin garinsu talaka bai isa ya yiwa matarsa ko yayansa wargi ba bale na garin Agadez
Kanta a sade ta ce" zan yi wankan
Ayya dake tsaye ta karaso kisanta tana kamo kafadunta ta kallo aminiyarta ta ce" me ta ce mata? Sai nake gannin kamar ta tsorata? Kar ta tsorata min yarinya fa kar ta rikitata
Anna dariya ma kawai yannayin Bak'a ke bata, ta fadawa Ayya abinda aka yi
Ayya ta dafe kanta ta zabgawa matar nan harara ta ce" ku tafi abinku tunda dai ba zaku tausasa ba, idan ita sarauniyarta ce ke ni ai aminiyata ce, bana son irin yanda kike nunawa kan yarinyar nan, kina manta mutun ce itama ?
Anna ta yatsina fuskarta ta ce" kin ga bara na je na ga in an kawo kayan da kika ce kina so, gaskiya ki yi hakuri ba zan iya wannan faman ba
Ayya na kallo Anna ta juya baiwarta ta bi bayanta suka tafi
Zaunar da Bak'a ta yi gefen gado wace ta takure waje guda, ta juya ta fauko wayarta ta zauna ta danna kira
Ana dagawa ta ce" kana ina?
Amsawa ya yi da" gani gefen aghali muna ratauna wata magana
To ka bari ka zo yanzu yanzu nan bangaren da aka saukeni ina ciki ina jiranka
Da toh ya amsa ya mike yana cewa Aghali ina zuwa
🐫🐫🐫 *BAK'A CE*🐫🐫🐫
Na *SAJIDA*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________
1⃣9️⃣
Shiga ya yi ya zarce dakin Ayya ya tarar bata nan sai ya fito ya shiga dayan dakin, daman falo ne mai daki biyu,
Yana shiga ya tarar da ita tsaye , Bak'a kuwa zaune inda ta ajiyeta
Karasawa ya yi yana tambayar lafia?
Ta amsa shi cikin kulawa ta tambayeshi kwannan iyalinshi
Ya yi murmushi dan ya san Walyn bata zo nan ba kennan wajen matar sarki ta je?
Ayya ta ce" Wardugu, zo ka yi mana fasara da y'ata ka ji? Ina son yi mata magana yanda zata fahimta aman ban lamunce maka ka rikita min ita ba ka ji?
Da mamaki yake kallonta, daman shine dalilin kiran nasa? Kai? Yanzu Ayya ya zata yi idan baya nan toh?
Kai kawai ya dan girgiza ya karasa inda Agaishat ta kara rakubewa jikinta ya fara rawa ta nuna alamar tsoronsa take ji
Ayya ta ce" Wardugu ka yi wani abin mana, ka ga tsoronka take ji, bana so dan Allah
Wardugu ya sauke ajiyar zuciya ya kali Ayya ya kara kallonta, uwa uwa hummm
Karasawa ya yi ya dan rage tsayinsa yana kallon yarinyar, kokari ya yi ya saisaita maganarsa ya ce" me ke damun ki?
Kallonsa take ita kuwa, irin kallon nan na kana jiran gannin me za.ai maka
Wardugu ya dan rontse idannuwansa ya bude ya ce" kin ga, mu fa ba mayu bame, ba mugaye bane kamar yanda kike tunani, mamanki tace mu zo da ke, idan kika kwontar da hankalinki kika nutsu sai ina kai ki kina gaishe da mamanki, kinga dai yanda kuka yi da ita ko so kike a mayar da ke ne??
Tsam ta yi tana kallonsa bata bashi amsa ba
Ayya ta matso ta ce" me kake ce mata?
Wardugu ya kali Ayya ya ce" ba komai
Ayya ta ce" to ka ce mata ta tashi ta shiga ta yi wanka , ko na yi mata da kaina ma
Ido Warsugu ya zaro, sai kuma ya basar, ya kaleta sosai ya ce" kin ce Sofo na koya maki karatu ko?
Kai Agaishat ta shiga daga mai
Ya ce" yawa, kuma sofo ya fada maki tsafta na cikin adini? Sai mai tsafta zai shiga aljannah fa
Agaishat ta kara gyada masa kai,
Ya fara jin haushin gyadegyadan kan nan, aman Ayya na wajen ta kasa ta tsare, ya tausasa murya ya ce" toh ki tashi ki shiga bayi, Ayya ta nuna maki kayan wanka ki yi wanka sosai kin ji?
Kai ta kuma gyada masa ta mike tana kallon Ayya, tunda ta ji yace za yana kaita wajen Annarta zata gwada yi masu biyaya ......
Ayya da jin dadi ta rakata bayin ta kuna mata ruwa masu dumi sosai ta bata sabulu da soso sababi, ta bude bruch da maclean ta mika mata ta yi mata nuni da yanda zata yi ,
Har ta juya ta dawo tana nunawa ta ce" ki cuta jikinki lungu lungu sannan ki wanke tafin kafafuwanki kin ji
Kai Agaishat ke gyadawa har Ayya ta gama ta fice
A hankali ta tube kayan jikinta, ta yi tsaye gaban ruwan tana kallon yanda yake zuba
Da tsoro tsoro ta tara hannunta ta janye, ta kuma tara ta janye hardai ta yarda da ruwa ne ke zubowa kuma ba zai konata ba
A hankaki ta shiga tana bismillah a ranta ta yi tsaye ruwan ya shiga kwararun mata a jikinta tun daga kanta dake da kitso kwaya daya tal har jikinta
Sai da ya gama dukanta ta dauki sabulun ta shiga gogawa a jikin soson tana jin yanda kamshinsa ke tashi tana jin dadin kamshin
A hankali ta shiga cuda fuskarta da soson nan ta cudeta da kyau ta darwaye kafin ta shiga wanke wuyanta sosai da bayan kunnayenta da cikin kunnen ta gangaro hamatarta kamar yanda Ayya ta nuna mata ta daga ta kama dirza ta yi kasa ta wanke jikinta sosai ta bi ruwan nan ya shiga darwaye mata kumfar da har ta zama baka dan tsabar datin dake jikinta, tana kallo ruwan na bin yar magudadar ruwa yana tafiya
Ta koma ta darwaye soson ta kara yin yanda ta yi , ta shiga saba sabulun a tufkeken gashinta na buzuwar usul ruwan nan na dareaye mata,
Abinka da tufkeken gashi wani wajen ya wanku sama sama aman cikin kam da datinsa daskare, haka Agaishat ta yi ta wanka tana sakewa tana jin kanta wani sakayau tana kara balbaluwa a cikin ruwan nan tana jin dadinsa abinka da ba sabanba ta wanke tafin kafafuwanta da abinda Ayya ta nuna mata nanma ta ga dati sai fita yake , har yatsarta ta saka ta debo datin tana kallo da gaske dati ne ta wanke da sabulu tana daga kanta sama ruwan na shiga idannuwanta yana kara ratsa gashinta da jelar ta sako tana yawo du idan ta juya kan
Fitowa ta yi ta dauki kayanta wa.inda sai a lokacin ta ji suna wani irin bugawa da ta rabu da datin jikinta, har ta shiga tunanin ko ta wanke? Sai wani abin yace mata idan kika wanke ki saka me kuma? Mayar da kayan ta yi ta fito ba tare da ta kashe panpan ba domin bata iya ba
Ayya dake zaune tana jiranta domin Wardugu ya tafi abinsa , ta mike tana fadin" eyah Agaishat ki cire kayan nan mana
Agaishat ta yi kasakai tana kallonta
Ayya ta dafe kai ta ce" wani yare kika iya
Agaishat kin iya frencais? Angalais? Ko hausa?
Agaishat dake kallon Ayya ta ce" Ayya, hausa kadan kadan
Ayya cikin itama dan yaren hausar nata ta ce" ouf , mun samu na gaisuwa, ki fida kayan nan ki canza wasu kin ji
Agaishat ta gyada kanta tana kallon wa.inda Ayya ta nuna mata, sannan ta juyo dan gannin a gaban Ayyan zata saka sai ta ga Ayya ta nufi kofa abinta
Ajiyar zuciya ta sauke ta tube kayan ta dauko wa.inda aka ajiye mata
Tsayawa ta yi tana kallon doguwar rigar abaya baka wace bata san ina ne gabanta ko bayanta ba sai dogon wando wanda ta daga tana ta jujuyawa irin na maza ta ayanna a ranta sai dai ba irin na mazan garinmu ba domin wandunnansu tamkar buhu........
Da daurin kirjinta tana tsayen nan Ayya ta dawo ta ga bata saka kayan ba
Nufota ta yi ta ce" aa ya baki saka ba?
Agaishat ta mika mata ta ce" Anna ban iya ba
Ayya ta yi murmushi ta shiga nuna mata ta juya ta saka wandon da kyar domin ya yiwa jikinta kadan duda fadinsa da yanda kuma yake jayuwa,
Ta dora rigar ta kule yar igiyar dake ciki
Ayya ta juyo tana kallonta, ba laifi kayan sun amsheta sai dai sam wankan nan bai yiwa ayya ba , gani take bata wanku ba da saura duda yanda du wani jirwayi na turkudi da fari fat din nan ya fita
Mai ta miko mata ta shafa , ta miko mata turare ta tayata shafawa
Agaishat bata san tana sakin murmushi ba sai da ta waiga wajen madubi
A hankali ta taka ta karasa, hannunta ta mika ta taba madubin tana kallon kanta, a hankali ta juyo wajen Ayya ta ce" na gode Anna
Ayya ta karaso da dan kalabin rigar ta kama kanta da bai karasa bushewa ba ta saka mata ribom ta daure mata sannan ta nada mata dan kwalin ya zagaye fuskarta
Kwali ta dauko ta nuna mata da ta shafa , Agaishat ta ce bata iya ba , hakan ya sa Ayya ta saka mata idonta ya fara ruwa ruwa abin rashin sabo Ayya tace ta jure karta murje ta kuwa juren
Abin maskara ta dauka ta fitar da shi ta saka wani mouchoir (kyale) ta goge bakin jikin tas tas, ta dauki jagira mai ruwan baka ta gogoga a jikin abin ta samu ta caje girar bak'a, girar ta kwonta tsaf a inda ya kamata ba kamar da farko yanda take wawatse ba
Ayya ta juyata wajen madubin ta ce" Agaishat, Tsafta, kwaliya, ya zama wajibi ga macen da ta san ciwon kanta, ki rike wanka , ki kasance mai tsafta kin ji??
Kai Agaishat ta daga tana kallon kanta da mamaki, tamkar ba ita ba, ta sawaya hancinta ya wani tafi zuwat, wai a nan Ayya bata gamsu da wankan ba jira take dai su karasa Niamey ta dauki lamarin a hannunta..........
Karfe sha biyu da minti arbadin suka fito daga masarauta suka nufi aeroport, ita dai Ayya bata san yanda wardugu ya yi ya samawa Agaishat waje ba bata tambaye shi ba
Sauran minti biyar suka karasa, suna zaune Ayya na kallonsa yanda ransa ke bace, bata ga Walyn ba bata tambayi inda take ba domin ba wani shiga lamarin juna suke ba, bata san zuwanta ba sai da ta ganta daga ina kwana wani abin bai kara shiga tsakaninsu ba sannan dan yanzu bata ganta ba itama ba zata wani tambayi inda take ba , Allah ya basu zaman lafia ita da mijinta ba abinda ya shafeta da zamansu haka kuma ba zata shiga dan wani gyara ba!
Ba.a jima ba suka mike domin an fara kiraye kirayen sunnaye,
Ita dai agaishat tunda aka haliceta bata taba gannin jirgin bama bale wai har ta shigeshi
Ta dai bi bayan Ayya da ta kama hannunta ta shiga nuna mata yanda zata taka matatakalar ta hau suka hau tare tana kara rike Ayya da kyau dan kar ta fadi har suka shiga
Kallon tsarin cikin jirgin take a ranta ta ayanna ba irin na mota ba ,
Nan Ayya ta tsaya sai da Wardugu ya shige kusan madubin domin sam ya hannata zama a nan in dai tafiar jirgi zata yi, ita dai sai dai ta yi murmushi kawai irin yanda yaron nata ke sonta ke kokarin kareta har mamakinsa take ,
Yana shiga sai ta saka Agaishat ta shige tsakiya , shi kam bai yi magana ba domin ransa a kololuwar bace yake, wai Walyn ta bi jirgin damagaran gobe ta bi na niamey ta karasa, shi zata nunawa zuciya ko? Han......
Ayya ma ta zauna ta ja ceinture ta sakawa Agaishat sannan itama ta saka bayan ta kashe babar wayarta ta android
Ba.a jima ba aka shiga fadin a daura ceinture a kashe waya da yarurukanmu na niger da kuma french da inglish duka , bayan an gama jirgin ya fara tafiya wace suuuuuuuuuuuuuuuuuuuuuuuuuu ne saman doguwar hanyarsa har ya zo wajen hatsarin wato tashi da saukar jirgi ba,
Cikin adu.a a bakin Ayya
Nan fa ake yinta domin abin tashin jirgin nan, kun san ko wanda ya saba sai ya ji cikinsa ya yi kasa bale wanda shigarsa ce ta fari kuma sha.af Ayya ta sha.afa da fada mata abinda kan iya zuwa sannan tace da ita tashi zasu yi sama, ita kuwa a kauye baba sofo ya taba gaya mata akoy harda wani abin mai tashi sama a birni sunnansa jirgi ,
Ai gaba daya ta shiga jijiga ta damki cinyar wardugu dake gefenta na dama ta damko ta ayya ta bude baki ta........
🤣🤣🤣🤣 ku taro su kauyawa a birni🤣😂😂😂😂😂
🐫🐫🐫 *BAK'A CE*🐫🐫🐫
Na *SAJIDA*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________
2️⃣0️⃣
Ido Wardugu ya zaro, ya kai kallonsa kan hannunta wanda ke dauke da dogayen akaifu domin ba wani cire su take son yi ba sai baba sofo ya sakata gaba take yanke akaifunta sai tace nai ai susa take da su,
Wardugu bai gama tantance meye haka ba ya ji wani irin ihun da ya yi barazanar tarwatsa masa dodon kunne,
A tare suka juyo wajenta shi da Ayya ......
Ayya cikin yannayin tashin hankali da yaren tubanci ta ce " Wardugu Wardugu tsoro ne take ji na manta ban fada mata ba, kuma ban riketa ba , mai yiwuwa bata taba ganninsa bama bale ta shiga;
Bak'a da jikinta ke bari gaba daya ta kwalallo idannuwanta, daurin dan kwalin nata ya kunce , hawaye tuni sun kama zarya, ihu kawai take tana ambatan innalilahi wa.ina ilaihi raj.une!
Mutanen dake kusa da su harma wa.inda ke dan nesa da su ne hankalinsu ya fara tashi du aka fara jiyowa wajen su Ayyar da ayyar tambaya da alamun tsoron a fuskokin su....
Daga can kofar masu kula da passenger wata mata mai kulawa da bukatun passenger ta fito da sauri da dan sket dinta, ta sha kwaliya, tana dan sauri tana fadin kowa ya zauna kowa ya kwontar da hankalinsa ba komai bane , sannan tana nufo wajen su wardugu;
Hannunsa ya daga na dama ya shafa sumarsa, a kasan zuciyarsa ayannawa yake wannan wani irin tashin hankali ne? Shi Wardugu da girmansa da irin yanda duniya ta san shi, shine za.a yiwa taro da yar kauyen nan! Merde! merde! merde!
Juyowa ya yi wajenta, hannunsa na hagu dake kusa da ita ya saka ya janyota jikinsa, ya sakata a jikinsa da hannun nasa ya karkata fuskarta gefen hannunsa na dama , ya saka hannun nasa na damar ya yiwa bakin nata mai ihu wata damka ...ai kuwa shiru kake ji ba ihu ba di kira da salamcewa sai dan mutsu mutsu wanda shima da ya kara riketa sai laf tamkar ta lafe ne a jikinsa. (WARDUGU kan keta)
Tambaya matar nan take lafia ? Me ke faruwa??
Wardugu gannin bakuwa ce yar amerika, sai ya ciro carte dinsa da hannun hagu dinsa ya nuna mata mai shaidar ko shi waye, sannan da lebensa ya yi mata nuni da mahaukaciya ce kar ta wani damu........🤔
Ai kuwa ta shiga bada hakuri da iya yi, ta juya ta koma.
Ayya sai faman ya cika yarinya take aman ya tsareta da ido ya ki yin maganama;
Nauyin da ya ji ta yi ne ya saka shi sasauta rikon, ba.a wani dauki lokaci ba Agaishat ta yi baci sai kace wata baby, bacin tsoro da tashin hankali, bacin wahala, gashi daman daren jiya ba wani bacin kirki ta yi ba dan tsoro da zulumi, sai ajiyar zuciya take saukewa du ta goge hawayenta a jikin rigar wardugu.
A hankali wardugu yake kokarin kwontar da ita jikin kujerarta, Ayya ta zabga masa harara ta jinginar da Agaishat a jikinta tana kara tabata dan tabatarwa in ba suma ta yi ba.
Murmushi Wardugu ya yiwa mahaifiyarsa na alamun bada hakuri kafin ya jingina yana duba agogon hannunsa domin tafiar idan Allah ya yarda ba wata mai tsayi bace a jirgi tsakannin Agadez da Niamey.
Allah ya sauke su lafia, Wardugu da kansa ya tuka motar da ya je da ita ya ajiye aeroport ,
Bai zame ko.ina ba sai gidan Ayya.
Suna zuwa Ayya ta yi hamdallah ta kamo Hannun Bak'a wace ke kallo da baki da hanci da ido gaba daya
Fitar da ita ta yi ta ce" mu tafi yar gidan Ayyarta
A hankali ta fito itama kamar yanda Ayya ta koya mata ta bi bayan Ayya tana waiwayen Wardugu da ya fitar da kafarsa guda waje yana ta faman yamutsa gashin kansa, wayarsa ya ciro yar karama ya dannawa abokinsa kira wato docter DOCTER MU.AZAM
Yana dagawa ya ce" Ranka ya dade oga *Wardugu Marahut*
Wardugu ya ja tsaki ya ce" Mu.azam ni za ka yiwa rashin mutunci? Yaushe ka fara karya?
Mu.azam ya yi shiru, ......tamkarma ya kashe kiran.
Wardugu ya duba ya ga kiran na tafia, ya kara karawa a kunnensa ya ce" kai!
Mu.azam ya sauke ajiyar zuciya ya ce" abokina, ka yi hakuri ka ji? Jikina ne ya tashi aman yau nake fita asibiti in sha Allah da na huta sai na kamo hanya.
Wardugu da ya gama jin abinda ya fada, cikin mutuwar jikin da bai san ko na meye ba ya ce" me ke damun ka ne harda kwonciya hopital? (HOSPITAL)
Mu.azam dake kallon karin ruwan da aka saka masa ya lumshe idannuwansa, jiki a mace ya ce" idan Allah ya kawo ni zan fada maka koma menene,
Wardugu ya sauke ajiyar zuciya, bai bashi amsa ba ya katse kiran ya rufo motar ya tayar dan ya samu ya karasa gidansa ya huta
..........................
TIMIYA
Rana ce, karfe biyu na rana ne, aman da dan lulumi kamar yanda garin ya saba,
A kasan innuwa suke zaune su uku suna yamutsa garin kwakwi da mai da yaji da manda (gishiri),
Fatimata ce mai kwadawar, Ayya na yiwa maryama susa a kanta
Mariama ce ta dago ta ce" Fatimata kar ki hade yajin nan duka ki ware min a robar nan kuma kar ki zuba mai iya shi din sai mandan ya isa kin ji?
Fatimata ta amsata da kai, Ayya dake mata susa kuwa a ranta take tambayar kanta Mariama ko ta daina cin yaji ne? Kai ina Mariama da yaji ai akoy amana.
Fatimata na gama warewa, Maryama ta mike ta dauki dankwalinta ta daura, ta dauki robar ta nufi wajen tulun Anna kwaya biyu dake cike da ruwa ta dauki guda ta dora saman kanta ta kama hanyar fita,
Kallonta suke da mamaki, Fatimata ta ce" Mariama ina zaki tafi kuma? Ki bari mu ci mana.
Mariama ta juyo ta ce" ki ware min nawa, zan je wajen Sofon nan na Agaishat na dubo shi ne,
Murmushin da Anna ta jima bata yi ba ta saki, sanyi ta ji a ranta daman tana ta tunaninsa halin da yake ciki mutumen kirki
Mariama oga kennan, Mariama ba daukan raina,
Bata zame ko.ina ba sai majalisar mahaifinta,
Tana zuwa ta mika masa hannu ba alamar wasa ta ce" kudi nake so Aba,
Bakinsa ya yatsina, Mariama fa ta fara isarsa da wannan ya bata ya batan, tunda ya karbi kudin aurenta take tatikarsa, idan ya nuna ba zai bada ba kuwa a ji su,
Rai bace ya saka hannunsa a aljihun rigarsa ya ciro dala dari ya mika mata a ransa yana adu.ar Allah ya sa ta karba kar ta ce ta yi mata kadan!
Karba ta yi ta maida tulunta da robar saman kanta ta juya ta nufi gidan mai goro....
Nan ta sayi goro har na dala Ashirin, ta sayi man zafi na ciwon jiki ta sayi yar tsintsiya, dauka ta yi ta nufi runfar baba Sofo.
Tana zuwa ta yi salama har sau biyu kafin take jiyo muryarsa can kasa yana amsawa;
Shiga ta yi tana wara idannuwanta dan ganni da kyau domin ta biyo rana idannuwan nata duhu suke ganni.
Yana kwonce fuskarsa na dubinta, ya takure ya kara yamutsewa da cazbaharsa yana ja kuwa,
Bata yi masa magana ba ta karasa inda ta ga tulun ta jawo ta fitar da shi ta wanke shi tas ta juye ruwan nan na cikin tulun Anna,
Ledojin da suka shihigo da kararuwa ta tatare ta fitar kafin take juyowa ta shiga share bukar inda baba sofo ya samu ya zauna yana binta da kallo da mamaki a kasan zuciyarsa; wannan ai yayar Agaishat ce, mai fadan nan, ikon Allah kawai yake fadi a kasan zuciyarsa.
Tana gamawa ta dauko robar abincin ta debo ruwa ta dawo ta darwaye hannunta ta zauna, ruwan nan ta kara yayafawa garin dan ya kara yin laushi sosai, tana yi bata ko kallonsa dan ta yi imanin ya tsareta da ido ne,............
Sai da ta kai bakinta ta ji idan mutun yace tsotsama zai yi tsaf zai tsotse abinsa ta dago da dubanta a hankali ta kai wajen baba Sofon dake kallonta ta ce"""
🐫🐫🐫 *BAK'A CE*🐫🐫🐫
Na *SAJIDA*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________
2️⃣1⃣
Ta ce" ga abinci, ina magurjinka?
Hannunsa dake dan rawa ya saka ya fitar da magurjin ya mika mata yana kallonta dai,
Mikewa ta yi ta wanko magurjin da goron, sannan ta dauko wata yar roba mai marfi da ta amso wajen mai siyar da goro ta kara darwayeta itama, ta dawo ta zauna ta saka yar farar leda a kasan abin gurzawar ta shiga gurza goron nan manya har uku;
Robar ya saka hannunsa ya janyo, bismillah ya yi har zai fara ci maganar Bak'a ta dawo masa inda take cewa < ka ringa wanke hannunka Sofo, ka ga jiki na iya daukan dati mai yawa banda ciki ka ji sofona? >
Dubansa ya kai wajen Mariama, a hankali ya ce" Mariama?
Dagowa ta yi tana dubansa bata amsa ba,
Baba tsoho ya ce" ina kwana,
Mariama ta kifta idannuwanta ba wani dar ta ce" Lafia, still tana kallonsa
Murmushi ya yi ya yi mata nuni da kofin ruwan dake hannunta sannan ya nuna mata hannayensa.
Tasowa ta yi ta karasa, dukawa ta yi ta kamo hannun nasa ta wanke masa da kanta sannan ta kuma ciko kofin ta ajiye masa ta koma ta ci gaba da gurza goron ba tare da ta furta masa kalma daya ba.
A hankali baba ya fara cin garin nan, yana ci yana dan kallon yannayin Mariama, Mariama ikon Allah, Mariama mai albarka,
A hankali ya ce" nima ina jin rashinta sosai,
Mariama ta dago kanta ta zuba masa ido, murya a cinkushe ta ce" dan me ka rabata da danginta?
Sai da baba Tsoho ya hadiye wanda yake dan tsotsa a hankali ya dan kurbi ruwa ya ce" dan ta rayu cikin nutsuwa, ta samu inci kafin ta yi kaura zuwa lahira
Mariama ta ce" a wajen danginta, a kusa da mahaifiyarta ta fi samun inci Sofo!
Idannuwansa ya dan lumshe kafin yake budewa ya ce" ta yaya? Ta hanyar ta kare rayuwarta a bakin titi? Ita ko arzikin mazan zamanin ta kasa samu idan sun shigo gari da gari dan jar fatar yayanmu ne da gashi da kyau! Ba ruwansu da tarbiya, usuli , da halaya! Burinsu shine au samu iri mai kyau ....bayan su kansu idan suka kalli kansu a madubi zasu gane cewa a da ba haka Allah ya halice su ba, kwonci tashi kuma fatarsu sai ta dawo irin tawa idan Allah ya nufa masu tsayin rai ne,
Su da ka hadata da su din kana da tabacin a inda zasu kaita ba.a kyamar bakar fata? Mariama ta maido masa da amsa du a hargitse da yannayin bacin rai tamkar a lokacin ne za.a tafi da Bak'a,
Baba tsofo ya ce" birni da kike ji ana fadi, wata duniya ce a cikib duniyarmu mai cike da abubuwan al.ajabi,
A birni mutane basu da lokacin dan kina da fata baka ko dan kina da muni ya kasance du idan kin zo waje za.ana kwagirar ki ko a hantare ki! Sannan birnu cike take da mutanen da kwakwaluwarki ba zata iya hasaso maki ba, idan wani ya tsana wani zai so.......Mariama, ku yi hakuri.
Kanta ta mayar ta ci gaba da aikinta, tana gamawa ta ware masa wanda zai ci a lokacin sannan ta zuba masa sauran ta kai kusa da dardumarsa ta ajiye masa ta ajiye tsintsiyar a gefe, ta fitar da sauran canjin kudin ta ajiye saman dardumar ta dauki robar Anna da tulunta ta juya,
Har ta fita ta dawo ta duka kusa da shi kanta a kasa da yaren buzancinta ta ce" ta kasance abokiyar fadana, wace idan na tashi itace kanwata ita nake cin zali, takan kwaso kayana ta wanke min, idan dare ya yi can tsakiyar dare in na je juyawa sai in jita nanake da jikina, sai in rungumeta sosai a jikina ita da marigayiya, sai gashi lokaci guda a cikin kwana goma na rasa su! su duka biyu, ita wace ta rasu ina binta da adu.a baba wace kuwa take raye inai mata adu.a sannan zan yi iya yina dan gannin na kyautatawa wa.inda take so take kyautatawa, haushinku nake ji ku duka har Annar!
Tana gama fada ta mike ta yi gaba abinta .
Baba sofo ya yi murmushi har cikin ransa ya ji dadin haka, ashe dai Mariama na tare da ikon allah, Mariama kennan Allah ya sa ranar da zaki hadu da yar uwarki ki bini da adu.a koda na mutu.
NIAMEY
Doguwar riga fara kar ce a jikinta mai siririn hannu aman tsayinta har kasa, irin mai laushin nan ce bata da kwaliya ko das ta tafi ne ta bi tsarin halitar jikinta,
Kamshi take bazawa du inda ta gota sai fai fuskarta ta cabe da hawaye tana biye da shi,
Murya a raunane ta ce" WARDUGU, nice ya dace na yi fushi irin yanda ka wulakantani, ka banzatar da ni a cikin duhu a garin da ba nawa ba , a garin da na je dominka, ka fice ka barni, sannan da safe da ka dawo ko ka kali motar da ka bar ni a ciki, ka yi tafiarka wajen mamanka ni kuwa ko oho! Shine dan na tafi zaka dauki zafi da ni haka?
Wardugu da ya gama saka mabalin rigarsa ya juyo ya kare mata kallo, a ransa ya ayyana '''''rainin hankali kennan, ta dawo daga tafiarta wace ta isa da kanta , shine aka sha karamar riga aka sha wankan turare aka zo ni ga maye ga mai jira aka kawo min na karbe ko?
Murmushi ya sakar mata kafin yake binta da wani mugun kallo irin na rainin nan, ya dauki yar karamar wayarsa ya bar ta chating din nan ya dauki ky din mota domin garin da hadari hadari baya son ruwa ya foke shi yau, ya fice ba tare da ya furta mata ci kanki ba;
Da kallo ta bi shi kafin take zama bakin bed din tana shafe idannuwanta, bakinta ta zumburo a fili ta furta" zaka sauko ne, haka kawai ka wani hada ni shakar numfashin wannan uwar taka harda wata karin malatin? Naki din wardugu! Na ki na shirya da mamanka duda baka tambaye ni ba na san hakan kake so sai dai ni a gaskiya ba zan iya jure mulkinta ba sai kaceatar wani sarki dan tana uwar General! ........hum
Wardugu bai zame ko.ina ba sai aeroport, yana zuwa ya ajiye motarsa ya shige ta wajen sojojin dake tsaron kofar bayan sun sara masa ya shige ciki ya haye wajen tarban baki
Bai kai ga karasawa ba ya ji muryarsa ya ce" mek (men),
Juyowa ya yi, arba ya yi da amininsa, abokinsa, Mu.azam zaune saman kujera, gilas a idannuwansa ya saka costume kafarsa sanye da takalmi sau ciki baki sai sheki take.....sai dai abinda bai masa ba irin yanda ya rame
Yana kallonsa har ya karaso inda Mu.azam ya mike tsaye yana murmushi ya bude hannayensa irin ya zo ya rungume shi ,
Ido Wardugu ya zaro ya nuno shi da yatsa ya ce" kai ko?
Mu.azam ya saki dariya yana kara kure Wardugu da kallon yaushe rabo ya mika masa hannu ya ce" Asalamu alaika amini
Wardugu ya karbi musabaharsa yana mai furta" amen wa.alaika salam amini,
Murmushi suka yi kafin suke gaisuwar larabawa,
Wardugu ya yatsina fuska ya ce" kai dai ka cika naci, gaisuwar nan ta wani runguma ba wani sonta nake ba aman sai ka wani damki mutun kato da kai!
Mu.azam ya bushe da dariya yana biye da shi inda soja guda ya karbi jakar Mu.azam dake hannun wardugu ya shiga ja har wajen mota ya bude ya saka masu ya juya bakin aikinsa,
Wardugu ke jan motar yana dan kallon Mu.azam jifa jifa, a kasan zuciyarsa yana tare da damuwa na abubuwan da ya gani a tatare da Mu.azam wannan zuwan, ya rage magana, ya rage fara.a, ga dan cazbi a hannunsa yana dan dadanawa, ga rama da ya tafka ta mamaki sai dai fatarsa ta gyaru ta yi fresh aman ba alamun yana jin dadin rayuwa.....
Haka har suka karasa gidan Ayya wada rabonsa da gidan kwana hudu kennan tunda ya kawo su bai samu aiki ya barshi ya zo ba , aman ita Ayyar ta ue har wajen aikin ta amshi carte dinsa ta banki wai zasu je shopping ita da sabuwar yarta, ya yi murmushi da ya tuna irin kudin da suka kaso, Ayyarsa uwarsa Ayya manya.......
Zaune Ayya take saman kujera tana kallon yanda Agaishat ke dan turo baki tana kallon Ayyar da yannayin abin tausayi,
Daga ita dai gajeran wando da yar rigar da Ayya ta yi mata jan ido kafin ta yarda ta zauna da su dan ta shafa mata gomage a jikinta da fuskarta tamkar amarya, gefe hijab dinta ne baki dan kar kalar abin madarar ya bata hijab din Ayya ta dauko ko dan idan an yi baki, wani irin kulawa Ayya take baiwa Agaishat (Bak'a), kudi ta kashe na mamaki wajen siyen mayuka masu gyara fata ba canza kalar fata ba, sannan ta shiga kasuwa da kanta tare da Agaishat tana nununa mata abubuwa nasu na tubawa na gyaran jiki ta kwaso itacen magarya ta kwaso kayan gyaran jiki suka dawo gida, wata irin shakuwa ce ta shiga tsakannin Ayya da Agaishat, domin Ayya wayayiyar mace ce ta yo anfani da irin yanda ta waye ta ja Agaishat a jiki tun tana tsoro tana baya baya har ya zamana sun shaku tana dora kanta saman cinyar Ayya ta yi baci ba tare da wani dar ba.
Yauma sun tashi da niyar yin gyaran jikin ne, Ayya ta dadaure mata gashinta da abin nan na saloon wanda idan an wanke kai ake sakawa a dadaure gashi da shi dan ya nanade ya bushe, ta kwaba abin gyaran jikin nan ta samu ta shafa mata ta yi mata hayakin mai mugun zafi wanda fuska kawai ake fitarwa, tana gamawa ta sakata ta yi wanka ta shafa mata na madarar nan suka zauna a fali sunna kallo aman ta hanata magana dan kar na fuskar ya saka fuskar ta yakune........
Mai gadi ne ya fara shigowa da jaka, Wardugu na biye da shi sai Mu.azam wa.inda shigowarsu ne ya ankarar da Ayya ta warci hijab din Agaishat ta ......
🐫🐫🐫 *BAK'A CE*🐫🐫🐫
Na *SAJIDA*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________
2️⃣2️⃣
Da sauri Ayya ta samu ta rufa mata hijab din inda Bak'a ta yi mutuwar zaune a ranta tana ayana Ayya wayo daman sai da na fada maki Ayya ...........
Karasowa suka yi, Mu.azan na kallon inda aka rufe da hijab yana son sannin ko waye,
Wardugu kuwa kallo daya ya yiwa wajen ya kawar da kai a ransa fadi yake" me Ayya ke son yiwa fatar nan da ta rine?
Da murna Ayya take kwalawa mai aikinta kira da ta zo ta dauke akwatin Mu.azam sannan ta kawo masa tarba,
Ayya ta tarbo shi tana murna ta kamo shi ta zaunar da shi sai murmushi take tana kallonsa ta ce" yarona, yaushe gamo?
Mu.azam dake jin wata nutsuwa na saukar masa ya dube duba irin na mahaifiya, a hankali ya duka kasa ya ce" Ayyana ina yini
Ayya ta kuma kamo shi ta tayar da shi tana kallonsa, yannayinta ya fara canzawa ta kai hannunta wajen wuyansa ta ce" me ke damunka? Ya haka ka rame har haka? Ko dai ka je ka sakawa kanka ayuka ba hutu ne??
Dariya ya saki yana kallon Ayya , kafin yake maida dubansa wajen Wardugu ya ce" freind Ayyana har yanzu akoy yannayin nan?
Wardugu ya yi dan murmushi yana kallon su,
Ayya ta yatsina fuska ta ce" ba wani nan, yanzu tashi ka je ka yi wanka ka fito zan fara yi maka dura ne tunda abin haka ne!
Yana dariya ya mike ya kalli Wardugu ya ce" mu je ko?
Wardugu ya gala masa harara ya ce" a matsayin matarka ko dan jagorarka?
Mu.azam ya yi murmusho yana ji a cikin ransa ya yi missing din abokinsa da mahaifiyar abokin nasa,
Juyawa ya yi ya nufi dakin da ake sauke shi wanda yake a matsayin nasa,
Ayya ce ta dubi wardugu, da idannuwanta ta yi masa nuni da ya tashi mana shima baya gannin mutun?
Wardugu ya daga kafadu ya ki tashin yama mayar da dubansa wajen tv inda ya dauki commande ya canza tasha ya kai Canal plus sport ya shiga kallon ball.
Ji take ta fara gumi , ga kuma ta kage a yannayin zaman nata, ba.a jima ba Mu.azam ya dawo daga wankan da ya tafi ya zu suka kara kasancewa mutun biyu maza kennan,
Ayya ta tashi da yannayin jin haushi ta dunguri kan Wardugu ta ce" ta yi maka kyau!
Wajen Agaishat ta karaso ta kamata ta mike kafarta ta yi mata tsami sosai, ta samu ta saka mata hijab din ta ce" je ki yi wanka Agaishat ki sauko mu ci abinci .
Da toh ta amsa ta bi ta bayan kujerun ba tare da ta gaisar da su Wardugu ba,
Mu.azam da ayar tambaya ya kallo Ayya, bai yi nauyin baki ba ya ce" Ayya ina kika samo wannan?
Ayya ta karasa kusa da su sosai ta zuba jus ta mika masa shima kamar yanda ta mikawa Wardugu ta ce" Me ke damunka tukunnan yarona??
Mu.azam ya shiga dan sosa bayan keyarsa, ya kallo wajen Wardugu, ya kuma kalli Ayya.
Haka kawai wardugu ya ji gabansa ya fadi, shima kure shi da kallon yake kafin ya ajiye yar wayar dake hannun nasa ya zuba masa ido,
Murmushin dai ya kara yi masu, ya ce" na yi rashin lafia ne Ayya, kuma yanzu alhamdulilah na samu sauki,
Ayya ta sauke ajiyar zuciya tana kallonsa ta ce" na tsorata da yannayinka, ka wani rame, ba komai haka ne idan jiki ya tabu sai a hankali aman yanzu ka zo kennan sai na ga yarona ya koma yanda yake da koma ya fi haka kafin ka bar gidannan,
Wardugu dake kallonsa ya shafa kansa shima kwata kwata bai yarda da maganar Mu.azam ba! Kai haba a irin yanda suka san juna Mu.azam ba zai layance masa ba
Mikewa ya yi ya nufi kofa da wayarsa a hannu inda suka bi shi da kallo,
Mu.azam ya ce" Ayya ya tafi fa kennan??
Ayya ta daga kafadunta ta dan yatsina fuska ta ce " ya gaishe su!
Mu.azam ya yi dariya yana kallonta, a ransa kuwa dadi yake ji yannayin, kai yana jin dadin zama da su, Wardugu rikitace, mahaifiyarsa ta iya zama da shi, ta kai ta kawo ne idan tama da bukatar ganninsa a wayarsa ya yi mata activen localization, du inda yake idan ta shiga nema za.a nuna mata kawai sai dai ya ganta kuma sam baya gigin kashewa doka ce!
Suna tsaka da tataunawa mai aikin Ayya ta shinfida ledar cin abinci ta kawo abincin ta ajiye, ta kawo kayan zubawa da na sha, ta kawo su jus na gida da Ayya ke yin abinta da kanta ta saka a frij du ta ajiye, Ayya ta umarci Mu.azam da ya sauko bara ta dubo yarta.....
Wardugu ya dawo, bayansa *ALHINAYET* kawarsa ce ke biye da shi,
Salama ta yi ta shigo dakin inda Ayya ta tsaya ta saki baki tana kallon Wardugu da Alhinayet din,
Alhinayett na zuwa ta shiga gaisar da Ayya cikin yannayin ladabi da mutunta mutun,
Ayya ta dan kebe baki, ta amsata ta juya dan dubo Bak'a
Mu.azam dake zaune ta juyo ta dafe habarta ta ce" su likitoci ne a garin namu???
Mu.azam ya sakar mata murmushi ya ce" lauya, lauya, lauya mai kunce mai laifi , zamani lauya iko, lauya mai saka kato ya duka,
Kai ta dafe ta ce" wace ni, rufani ka sayani, ai ba dan an san ni aminiyar *Aboki* bace da an fige ni a Niger!
Mu.azam ya ce" kai ai rigimama ta san waye *Oga*
Wardugu ya girgiza kai yana zama ya ce" *ALHIN* ki zauna mu hau wannan abubuwan kafin ku ci gaba da kirar da kuka koya!
Alhinayettt ta je kusa da Wardugu ta zauna tana fadin" General ka duba lamarin nan je ten conjure................(plz)
Wardugu ya kaleta zai yi magana sai ga Ayya ta dawo da Agaishat,
Doguwar riga simple irin ta zaman gida ce Ayya ta bata, bayan ta saka ayya ta bata Dan kwalin rigar nufin ta yane kanta sai dai suka hau rigima kan aa dan Allah ta bata hijab,
Gannin sai su bata lokaci ne ya saka Ayyar bata hijab ta zumbula suka sauko,
Sai a lokacin Agaishat ta duka ta ce" ina yinin ku,
Alhinayettt da Mu.azam ne suka amsa inda Wardugu ya kebe bakinsa bai wani amsa ba aman yana yi mata kallon tsaf, a ransa yake ayyana black, but ko a baki *BUZU MAI KYAU NE* 😂😂😂😂🤪😜😜😜😜😜😜😜😜😜🤪🤪🤪 na fada a zo a dake ni🧐🧐🧐🧐🧐🧐🧐🧐🧐🧐🧐🧐🧐
May be 23......zuwa dare in sha allah, idan comment ya birge ni😄😁😆😅😂🤣
🐫🐫🐫 *BAK'A CE*🐫🐫🐫
Na *SAJIDA*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________
2️⃣3️⃣
Waje Ayya ta samu ta zauna , nan Agaishat ta je kusa da ita sosai itama ta zauna ya kasance an saka baban plateau din a tsakiya,
Ayya ce ta bude inda abincin yake, tuwon tsaki ne da miyar kubewa wace aka yita da naman shanu ta sha dadawa da kayan miya 😋..ga kuma man shanu na kirki a gefe,
Sai su fruits da aka hi masu yanka mai kyau aka sasaka cikin plat plat, sai jus da ruwa,
A hankali Ayya ta dauko abincin, Agaishat ta dauko abin zubawa,
Cikin wannan banban plateau din Ayya ta zuba abincin ta daidaita miyar, ka.ida ne in dai ka zo gidan Ayya daidai cin abinci bata raba assiete, sai dai a hadu a ci a abu guda .......
Bayan ta zuba ta kare Agaishat ta kawo abin wanoe hannu da kuma cokula a wata yar roba,
Gaba dayansu cokulan suka dauka banda Agaishat da Ayya , hannayensu suka wanke ....
Ayya ce ta fara saka hannunta, sai Wardugu, sai Mu.azam, sai Alhinayettt, sannan Agaishat dake karamar cikinsu, hakane gidan Ayya baba ke fara saka hannu cikin kwanon cin abinci sannan yaro ke rike kwanon dan kar ya ringa yawo, ba.a magana idan ana cin abinci, ba.a dane danen waya, ba.a wani kale kale sai an gama, sannan bata yarda ana tsaka da cin abinci ana shan ruwa ko jus, sai an gama ake sha, sannan ana cin abinci daidai ne ba.a matsawa ciki a yi mugun koshi, lamarin gidan Ayya sai yayanta (🤣),
Abincin nan ake ci cikin nutsuwa, Alhinayettt ta kure Agaishat da kallo, sam batai mata kama da tubawa ba, sannan ba bahausa bace ko daya duda hijabin dake kanta gaban goshinta lufluf yake kwonce da gashi, girartama wani irin gazar gazar da ita, du bakinta lebenta haske ne da shi tas tas, ga girar ido ga manyan idannu, wannan cikin biyu daya ce ko bakar balaraba ko bakar buzuwa!
Alhinayettt dai ba wani yawan zuwa gidan Ayya ba take ba, sukan hadunsu ne da wardugu a wani wajen, yanzuma zuwa ta yi da rigimarsu ta kansu wace ta zo su yi kan irin yanda ake cece ku ce a gari na matarsama idan ta cika dare kwanan cel take bare wani banza!
Alhinayettt kwata kwata ta manta zancen ba.a magana idan ana cin abinci gidan Ayya dan haka ta kali Agaishat da kyau, haka kawai ta yi niyar yi mata magana da buzanci dan ta gaskata zatonta,
*ABZIN?* , ta fada tana kallon agaishat,
Agaishat da ta hadiye abinci ta kaleta itama, itama ta so ta ayanna hakan cewa wannan buzuwa ce, gannin yannayinta sai dai bata fadi ba dan ba wajen fadin bane,
Ai kuwa Agaishat ta washe baki itama da yaren buzancin ta maida mata cewa" eh , ke fa??
Alhinayettt zata maida mata maganar Wardugu ya tsimki hannunta na dama dake kusa da shi, sannan ya zabgawa Agaishat wata muguwar harara wace ta sakata sada kanta hannunta na rawa rawa,
Ayya yatsina fuska ta yi bata yi magana ba,
Sai da aka gama mai aiki ta shiga kwashewa, Agaishat na tayata kaiwa komai wajensa ta dawo ta zauna kasa kusa da kafar Ayya,
Wardugu ne ke kallon wayar Alhinayet tana nuna masa hotunnan birthday dinta da ta yi baya nan yana dan murmushi kasa kasa ya ce" Alhinayettt , ina tunanin kin girma ashe dai na daina tunanin nan?
Alhinayettt ta yi dariya ta dora hannunta saman nasa ta ce" na baka ka sha? (Irin su taba zata bashi wani labarin)
Ai kuwa Wardugu ya dan cafke hannunta yana sauraronta, inda ya bata hankalinsa suna ta hirar su,
Ayya ce ta dan ja tsaki, ta girgiza kai tana kallon Mu.azam ta ce" kana ji? Zamani ya zo mana da abubuwan mamaki, sai ka ga mace na tafawa da namiji, tana raba jikinta da nasa wai a zuwan mutunci kawarsa, !
Mu.azam ya zaro ido yana kallon Ayya, a fili kuwa ya furta" Lah, yana dafe bakinsa,
Wardugu da ya gama jin komai ya saki murmushi yana kallon Ayya, ya ce" Ayya, qna abota mace da namiji, abota sak ba wani soyaya ba kuwa,
Ayya ta juyo bangaren su a takaice , daman jira take wani abin ya hada su ta ce" wardugu ba abota ba dai yayan awaki! Nace yayan awaki, Ke yanzu Alhinayettt kike ko wa? Aman ke marainiya ce ko? Ina nufin mahaifiyarki ta rasu?
Alhinayettt dake kallon Ayya a dan tsorace ta ce" Aa Ayya,
Ayya ta dafe habarta ta ce" Toh abin mamaki, aman ita baku rainata kamar yanda kuka rainani ba ko? Ina nufin Wardugu baya zuwa gidan ku a matsayin aboki sai saurayi?
A tare suka kalli juna Alhinayettt da Wardugu, suka maida dubansu wajen Ayya,
Ayya ta ce" to in ba haka ba, ya za.a yi ni ina mahaifiyarki , kato ya ringa zuwa wajenki a matsayin aboki kuma na zuba ido yarinya kin kai kin kawo min a gida?
Wardugu ya shiga gyada kai yana kallon mahaifiyarsa, ta jima tana son aikata wannan aika aikar wa zumuncinsa da Alhinayettt, yau dai ta yi hankalinta sai ya kwonta kuma ko?
Ayya kamar zugata ake sai magangannunta take son ranta karshe ta ce" to ni ba tsohuwar banza bace, in sonta kake ka fito a mutun ka fada ku daina boyewa Allah kadai ya san tsakanin ku! Dan haka tun wuri a fasa daukana a wata marar ilimi ana ce min wai kawa! Aa abokiyar tagwaitakarka ce Wardugu!
Wardugu kallon Ayya kawai yake, inda Alhinayettt ta dan sada kanta kasa, a ranta ayannawa take ita bata ga laifin zumunci da suke da Wardugu ba, walahi da soyaya suke da ba haka ba, kwata kwata ba wani zance wai shi soyaya tsakaninsu, haka kawai Allah ya hada jininsu suke mutunci, Wardugu bashi da shamaki a gidan su, hakama saurayinta wanda zasu yi aure suna mutunci da Wardugu, aman haka ne itama kakarta ta sakawa zumuncinsu ido har sun mayar da ita tamkar mahaukaciya domin idan sun ga zata fice sai su shiga magana kasa kasa da yaren french ai kuwa ta kama zage zage tana fadin ita za.a munafinta? Toh gashi itama maman Wardugu kallon masu soyaya take masu bayan ita koda bindiga ba zata iya soyaya da wardugu ba domin ta san waye shi, Wardugu dan yana son ki ba zai hana ya yi maki dukan mutuwa ba, dan yana son ki baki fi hukunci a wajensa a gaban koma waye ba, hum soyayama da wardugu ai tashin hankali ce, ita mai ya kaita? Ta fi son namiji marar rigima mai bata damar ta yi rayuwarta cikin aminci........
Wardugu dake kallon Ayya tar, ya maida dubansa wajen Mu.azam ya ga sai gumtse dariya yake,
Kansa ya girgiza ya maido dubansa wajen Ayya, da hannunsa na dama ya daga ya sara mata, sannan ya yi mata nuni da ta ci wasanfa , ta more abinta,
Hannunsa na hagu ya mikawa Alhinayettt ta mike itama ya ja hannunta tana waiwaye tana so ta yi hira da agaishat aman ya jata kiiii sukai waje
Kusan motarta suka tsaya,
Alhinayettt bata bi ta kan fadan Ayya ba, bata nuna damuwarta ko a fuska ba, ta ce" Wardugu, rigingimunka sun isheni haka, ya isheka malan!
Wardugu ya shiga gyada kai yana kallonta bai bata amsa ba,
Ta ci gaba da maga domin ta san ba amsar zai bata ba, ta ce" ta ya zaka saka Walyn kwana a cel? Wardugu ina jin zafi idan na ji ana fadin baka da sasauci, baka wasa, baka sulhu, Wardugu matarka ce fa? Ya kake so mutane su fasaraka??
Wardugu ya tsura mata ido kawai,
Ta ci gaba murya a sanyaye" ka daina Wardugu, ina so idan na zo waje na tarda ana fadin alkhairi a kanka, ina so idan ana maganarka ta kasance ana yabonka Wardugu, ka ringa sasauci freind,
Wardugu ya yi mata dan murmushi ya miko hannunsa ya dungure mata kanta bai ce mata komai ba,
Alhinayettt ta ce" Wardugu ina kula samu buzuwa??
Wardugu ya yatsina fuska ya ce" hum, Ayya ce ta daukota wai ta yi y'a,
Alhinayettt ta ce" yarinyar ce ta birge ni, irin yanda tana buzuwa , bakar buzuwa aman bata bata bakinta ta hanyar shafe shafe ba, ina son mutun haka walahi.....
Wardugu ya daga kafada ya ce" daga kauye, can cikin kauyen kauye fa ta fito, inama ta ga man bale ta shafa? Allah dai ya sa idan ta dan waye ta zama dan kauye ya fi na birni shegantaka....
Alhinayettt ta ce " sai dai idan ba tare da Ayya take ba, Ayya ce zata wani bari haka ya faru? Yarinyar ce innocente, dan Allah ka hada ni da ita mu zama kawaye,
Wardugu ya waro ido, a fili ya furta" kawaye? Ki kirani aboki kuma ki yi kawance da wannan? Aa!
Alhinayettt ta yi murmushi tana kai masa dan dukan wasa ta ce" ina son ta zama kanwata ne Wardugu, ina son na kara nuna mata shafe shafe karma ta saka kanta, sannan na kara wayar da ita......
Kafadunsa ya daga irin ita ta gano, kafin yake bude mata motar ya yi mata nuno da ta shiga
Dariya ta yi ta shiga , ta kunna wato dai ta ishe shi da magana ko?
Hannu ta daga masa, ya yi mata nuni da sai ya zo , ta tayar da dankareriyar motarta ta kama hanyar makarantar kannenta dan ta dauko su ta mayar da su gida
Komawa Wardugu ya yi, yana shiga ya tarar da su sai labari suke suna dariya abinsu, Mu.azam kuwa ya kasance du motsi sai ya kali Agaishat dake zaune tana kallon Tv kuri, ita har yanzu mamaki take mutane a cikin wannan allon suna ta magangannu suna komai abinsu, har bayan take lekawa wai ko zata gansu ta nan ta sha yiwa Ayya tambayar kuma yanzu idan suka fito fa? Yanzunma Ayya ta kuna mata wakokin dandali, kalo take tana ta sakin murmushi kumatunta na lotsawa dimple har biyu a fuskarta, wani wajen sai ta rufe fuska idan namiji ya fara rawa, sosai take dan gane hausar da suke tana kara koya ta nan, shi kuwa abin na birge shi, sannan ya yiwa Ayya tambayar wacece ita? Da french, ayyarma ta shiga kora masa bayanin komai.....ya sha mamaki, ya ji wani lamari a tare da yarinyar, yana son inganta rayuwarta......
Wannan kennan.
Wardugu na zuwa ya ce" tashi mu je,
Mu.azam ya mike ya bi bayansa suka nufi dakin Mu.azam din , Ayya ta yatsina fuska a ranta ta ayanna mai yiwuwa ya yi fushi🤣.
Suna shiga Wardugu ya ce" c'est bon, maintenant tu me dit la verité sur ce qui t'arrive ( ya isa, yanzu sai ka fada min abinda ke damunka!)
Mu.azam ya tsare shi da kallo, a hankali ya zauna saman kujera yana kallon Wardugu,
Wardugu ya karaso ya zauna shima, ya ce" ka san dai kana iya yiwa kowa karya banda ni! So ka fada min tun kafin na hasala Mu.azam, wata irin cuta ce wannan wanda baka taba yi a gabana ba ta zugeka haka? Me ya samu kasan gashinka ? Kana tunanin ban lura ba? To gashinan kasan gashinka a aske! Sai ka janyo sauran ka rufe, du ka zama wani iri? Ka duba fa ka gani wandon vest ne a jikinka ka dauko riga rose (pink) ka saka sai kace mace? Hannunka ba agogo, yannayinka na nuna kama tare da damuwar da ta fi karfin furucinka, ina hawa aiki karfe goma na dare, ka fada mani na juya!
Mu.azan da wata irin murya ya ce" Cancer du cerveau ke damuna..... (cancer ta kai)
Wani irin tsam Wardugu ya yi, ya kaste maganarsa a lokacin da bai shirya ba,
Zurbat ya mike yana duban Mu.azam, hannayensa duka biyu ya saka ya dafe kansa, baya baya yake ja ya......
🐫🐫🐫 *BAK'A CE*🐫🐫🐫
Na *SAJIDA*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________
2️⃣4️⃣
Wani irin tsam Wardugu ya yi ya katse maganarsa a lokacin da bai shirya ba,
Zurbat ya mike, duban Mu.azam yake da wani irin kallo, hannayensa duka biyu ya kai saman kansa ya shiga yamutsa gashin kansa , baya baya ya shiga yi da kafafuwansa, bai fi taku hudu ba ya tsaya ya juya ya juyo, hanunsa ya jimke ya daki dayan da shi,
A hargitse ya dawo wajen Mu.azam, so yake ya zauna aman ya kasa...... murya a cinkushe ya ce" yaushe, yaushe? Yaushe ka sani? Ya aka yi ka sani?????
Mu.azam ya mike yana dan sakar masa murmushi yana kokarin ganin ya saka shi ya dan nutsu aman ya kasa kama shi, dan haka ya tsaya yana kallonsa ya ce" Wardugu, har na kai wajen da gashina baya zama fa, ya jima a jikina ciwon ....nima ina gannin alamu a matsayina na likita sai dai ina turewa na ki maida hankali, ya kai ni sai na suma na yi awani a sume, na daina shiga tiyata ba yau ba, ina zuwa asibiti ne dan kar imanina ya yi rauni, ina zuwa ne dan haduwa da wa.inda suka fi ni damuwa, ina yi mana adu.a a tare, Wardugu idan na jima a gabannan na kara shekara hudu a duniya,...
"C'est faut!,(KARYA NE!) Wardugu ya fada tun karfi yana nuno Mu.azam da yatsarsa,
Taku ya yi wajensa ya ce" idan kai ka fada, idanma wani sakaran likitan ya fada na fada karya kuke, karya ne Mu.azam, ku baku isa ku fadi abinda Allah ya boye ba, ba wani mahalukin da ya san ranar mutuwarsa , mutuwa bata shawara, bata fadi sai an ganta, mutuwa na zuwarwa bawa a lokacin da bai sani ba, sannan a lokacin da bai shirya ba domin a kulun bawa baya cikin shirinta,
Wardugu ya yi shiru, gaba daya ji yake jikinsa ba karfi, a hankali ya kai kasa ya zauna nan kasa, waje guda ya tsurawa ido kafin ya ci gaba da fadin" sannan Allah kadai ya san gawar fari, ba wai dan wane bashi da lafia wane lafiarsa kalau za.a ce sai marar lafiar nan ya rigayi mai lafia rasuwa,
Mu.azam da ya karaso , a hanakli ya duka ya dora hannayensa saman na Wardugu, murya a raunane ya ce" ban taba tunanin wani abin zai girgizaka haka ba Wardugu, menene a ciki? Ko dan abin ya shafeka ne baka so ka ji? Wardugu ka yi hakuri, ka daina tayar da hankalinka kan maganar nan, nima na fada maka ne dan na ji sanyi sannan na samu wanda ya san ciwona, Wardugu ka....
Bai tsamaci lamarin ba, sai jinsa ya yi jikin Wardugu, Wardugu da dan ya tsokane shi yake ce masa sai sun yi gaisiwar larabawa, yau gashi da kansa ya rungume shi,
Murya a cunkushe wardugu ya ce" bana so bana so.....
Kasa karasawa ya yi kuma ya saki Mu.azam ya mike ya fice da wani irin sauri .......
A hankali Mu.azam ya hade kansa da gwuiwarsa, , tabas mutuwa Aya ce, duk mai rai mamaci ne, tabas ba karamar ni.ima bane da Allah ya boyewa bayi ranar mutuwarsu, shi gashi, hasashe ne aka yi, likitoci sukai a kansa, rayuwar turai da za.a fada maka komai kwaro kwaro ne, sun kiyasta lokacin da suke gani zai kai a raye a doron kasa sun fada masa, wai basu fada masa rana da lokaci bama aman gashi du ya firgice ya fice a hayacinsa,
Idannuwansa ya lumshe yana jin saukar zazafan hawayensa, zuciyarsa ce ta ci gaba da fada masa" ka zo kasar nan je dan ka kara ninninka ibadunka, ka kara yawaita sadaka da aikata abubuwan alkhairi, ka zo kasar nan ne dan ka samu ka raya sunnar ma.aiki idan Allah ya nufeka, mutuwa kowa yi zai yi Mu.azam, ka daina karaya ka yi hakuri har Allah ya yi ikonsa a kanka,
Wayarsa ce ta dauki kuka ya kai dubansa wajen wayar ya mike daga tsugunnin nan ya daukota ya daga,
Docter me ka yi kennan? Na zo wajen aiki na tarar da takardar barin aikin ka? Saboda ni kake son yin nesa da aikinka ko saboda na fada maka ka yi hakuri a yi maka aikin nan? ......
Kansa ya shafa yana sauraronta, masoyiyarsa wace ke nuna masa kauna, tana son Mu.azam tamkar nama daya na cikin miya, tana son kasancewa da shi, labarin rashin lafiarsa ya gigitata har itama ta kwonta, nan ne ta yi ta fadi tashi har ta gano ana iya yi masa aiki a cire wajen, aman aikin ne keda hatsari sosai, yana iya samun tabuwar tunaninsa, ko ya kasance ya shiga coma wace shigekan daga ita ba zai tashi ba, ko idan Allah ya aminta ya yi jinya sumul ya samu sauki aman shi ya kara kai da kasa ba zai harda a wani buda kansa ba a dawo kuna ba wani succes,
MU.azam ya ce" Aisha,
Aisha ta ce" ka dawo na roke ka, ka dawo tun kafin lokacin a iya yi maka aiki ya shige,
Ki yi hakuri ki daina kirana Aisha, Mu.azam ya fada da sanyin murya, ya ci gaba da fadin" nawa kuka yiwa aikin? Nawa suka fita? Karshe dai du yawanci daga dakin aikin za.a fitar da su basu san inda kansu yake ba, zasu dawo kulun a jone da inji yana taimaka masu wajen numfashi, da na.urori masu basu abinci, da masu jan fitsari da masu karban kashin su, zasu dauki lokaci a wannan yannayin har ya kasance ko a cire masu na.urorin ko dare daya su tsaya sun daina aiki, su basu dauki kadara suka yi ta ibada suna shinfida a makwoncinsu na gaskiya ba, su basu san a inda suke tsakannin duniya da lahira ba, Aisha, Allah ya dora mani, ba zan kai labari ba! Ki yi hakuri......
Yana gama fadar haka ya katse kiran,
Docter Aisha dake kai kawo tsakannin dakinta da falonta ta dafe kai ta fashe da kuka, yar balaraba kyakyawa da ita, a fili ta furta" innalilahi wa.ina ilaihi raj.une, Mu.azam, in sha Allah zaka warke, sai mun rayu da kai Mu.azam.......
(😔😔😔😔😔😔)
Bayan sati uku
Ayya ce zaune tana nunawa Agaishat yanda ake gyara lale ja domin tana son kunsa mata ne,
Bayan ta tankade shi lukui ta kawo mahanabiya ta zuba masa sannan ta zuba dan madaidaicin ruwa ta kwabe shi sosai ya yi shar da shi ta zuba dan ruwa gefe ta ajiye tana kallon Agaishat ta ce" yi ki wanke kafar mana Agaishat, kin ga yayanki Mu.azam ya ce zaku fita ku zaga gari , ni kuwa na fi so idan mun gama kunshin nan sai ku tafi....
Agaishat ta yi sauri ta shiga darwaye kafar nata ta cire ta dauke ruwan ta kai ta zubar ta dawo ta dauki abin goge kafar ta gogoge ruwan kafin take zama ta tankwashe kafafiwanta Ayya ta shiga daura mata iskwace tana fadin"ki lura dan gobe ki daura abinki kin ji Yar Ayya,
Agaishat ta gyada kai tana murmushi, a kowani lokaci a kowani yannayi ta tsinci kanta tunda ta sauke kafarta a gidan Ayya sai iyayenta da yan uwanta da baba sofo sun fado a ranta, bale yanzu Wardugu kansa da yake yawan hararata a farkp ya daina, shi dai baya shiga lamarinta aman baya hana wani shiga, Alhinayettt ma tana lekowa wani sa.in idan Wardugu na gidan su sha hira da yaren buzanci domin tana jin dadin jin yaren raurau ana hira da ita ba wani kyama, sosai Alhinayettt ke dan gwada mata wasu abubuwan, da hikima take nuna mata wasu yan al.adun yan birni sannan Mu.azam na mugumugun sakata a jiki, yana sakar mata fuska fiye da tunanin mai karatu, idan ta kali kayayakinta, suturun da suke malakinta a yanzu, sai ta ji hawaye na neman zubo mata, tunaninta me yan uwanta suke sakawa a yanzu? Wani hali suke ciki? Jiya i yau ne ki Baba ya canza halayensa?
Sai dai takan bi su da adu.a kawai, itace kadai abinda take iya yi masu a yanzu, kuma tanaiwa iyayen rikonta adu.ar gamawa da duniya lafia, ba.a wani sakata makarantar boko ba domin shekarunta sun tafi shekara goma sha takwas har ta kusa cike sha tara, aman a gida Ayya na koya mata abinda ya sawaka sai karatun islamiya da ta kara zurfafawa sosai tana kara neman ilimin adininta.
Ayya na gama daura mata kunshin ta mike tana leka windows, mamaki take irin yanda yanzu wardugu ya ajiye kafarsa a gidan, duda ta san amininsa na nan dole za yana yawan zuwa aman abin na bata mamaki, bai jima da fita ba fa aman har ya dawo, sannan yanzu basa fada da mu.azam akasin da da sai ta shiga tsakani ko ta gindaya masa doka kan Mu.azam din kafin yake barinsa ya huta, yanzu kuwa bini bini ya shigo ya haye wajen Mu.azam su yi ta hirar da ita bata san ko ta meye ba, yanzun ma tsaye suke su uku, da yar jajar nan Alhinayettt sai hira suke suna dariya,
Rufe windows din ta yi ta juya ta fice ta bar Agaishat na zaune tana jira ya bushe ta wanke kamar yanda Ayya ta fada
Bayan kunshin Agaishat ya bushe, ta mike ta saka takalminta silifas ta yi bayi,
Wanke kunshin ta yi, jan kunshi yayi jajajir, ga mamakinta ya fito sosai a fatarta har ya haska mata fatar kafar da hanayen,
Da sha.awa take kallon kunshin ya yi kyau a idannuwanta,
Ta dauki lokaci a bayi domin sai da rmta yi wanka ta fito ta je bakin madubi tana goge gaban goshinta inda ruwa ya taba kannanuwan kitson da Ayya ta dage akai mata wa.inda sai warwarewa suke dan kansu ,
Turarukanta ta zauna ta shafa na madara masu sanyin kanshi, ta shafa mai kadan a jikinta,
Kwali ta dauka tana adu.a domin har yanzu ta kasa sabawa da saka shi da dadi sai ta yi ta fama, bayan ta saka ta caje girarta, ta dauki wani jan baki mai ruwan lebe wanda Ayya ta fada mata kadan za tana shafawa a lebenta na kasa,
Hakan kuwa ta yi ta shafa kadan kafin take tsurawa madubin ido, tunda ta zo garin nan ka.ida ne a wuni sai Ayya ta tsareta yin wanka sau biyu wataran har sau uku, idan kuwa ta yi wanka dole ne ta zauna ta kula da du wata gaba ta jikinta, tun tana kallon haka a wani iri har ya kasance idan bata yin ba itama bata jin dadi, sannan ta yarda da mutun sai da gyara, wannan mugun bakin da take gani a jikinta a ruwan wanka ta ga yana sauka daga jikinta, tsabar rashin wanka na kirki ne da kuma karin bakin turkidi(tufafin buzaye), yanzu fatarta ta kasance bak'a mai haske, irin bakin nan mai kyau mai birgewa, ga gyara yana kara samu yau da kulun, har santsi santsi take ji fatar tata ta fara yi mata,
Mikewa ta yi dai ta shiga fitar da riga da siket din da Ayya ta rataya jikin abin turaren wuta tun da safe kan su zata saka,
Wani ni.imtacen kanshi suke na turaren tubawa,
A hankali ta saka slipe (pant) dinta, an ta kasa saka breziyar domin har yanzu bata iya aiki da ita ba, kai ita bata ma sonta ne ,
Kayan nan ta saka sket da riga, sun amsheta sun mata cicif a jikinta dinkin zamani ,
Tsaye take tana kallon lufayar da Ayya ta bata, ta nuna mata ta koya mata daurawa sai dai bata iya ba har yanzu (daura lufaya sai a slow),
Gashin kanta kawai ta sakawa ribom ta saka yar bakar hular da Ayya ta hada mata da kayan ta luluba Lufayar ta fice da takalman a hannayenta dan Ayya ta nada mata da kanta,
Alhinayettt karfe nawa ne zaki je wajen auren? ,
Agaishat ta tsinci muryar Wardugu da bata da siri tana tambayar Alhinayettt dake zaune tsakiyarsu Ayya kuwa na wajen table din diner tana gyara shirin da mai aikinta ta yi mata domin bai mata ba!
A hankali ta sauko, ta karaso tana hangen yanda Mu.azan ke sakar mata murmushi,
Karasawa ta yi sosai kafin take gaisar da su a jimila ta hanyar fadin" Ina kwanan ku,
Alhinayett ta amsata tana yaba kunshinta da harshen buzanci wanda Wardugu ya ji me take fada ya yatsina fuskarsa yana girgiza kai.
Mu.azam ya kai dubansa wajen agogo ya maido wajenta ya ce" Agaishana, yanzu ne safiya, duba karanto min karfe nawa ne? Na ga ko kin gane yanda na koya maki,
Ai kuwa ta juya wajen agogo ta shiga nunawa da hannayenta tana irgawa tana faman fada masa lokacin Ayya ta karaso ta kama hannunta ta ce" a bar y'a na gama shiryata, ita da bata yi safiyar zuwa wajen namiji ba ai ba lale ne ta gane safiya ce ko rana ko yama ! Ayya ta karasa tana murguda baki irin na tsofafin nan masu rigima ta kai dubanta kan Alhinayettt, wato dai da Alhinayettt ake,
Wardugu ya mike ya karasa wajen Ayya, ya kasance sun saka Ayya a tsakiya shi da Agaishat wace hannunta ke cikin na Ayya tana so ta warware mata Lufayar nan ta nada mata,
Sosai ya so rage muryarsa, sosai ya yo yaki da muryarsa ya ce" kin ce baki tsufa ba? Da yaren tubanci,
Juyowa ta yi ta murguda masa baki ta ce" eh da saurana,
Wani tsadaden murmushi ya sakar mata yana dan juya kansa, ya kamo dayan hannun nata cikin nasa ya ce" kin san du duniya ba a yi ba ba kuma za.a yi ba macen da zan so kamar mahaifiyata ko?
Ta kawar da kanta bata bashi amsa ba, ya ce" in dai kina irin abin nan sai in fara tunanin na bani Ayyana ta fara tsufa,
Hannunta ta warce ta dungure kansa kamar yanda takan yi idan ya hasalata ta ce" ni ba wani tsufa ko rashin tsufa bane, ina jin haushin irin yanda kuka dauki al.adar yahudawa kuka mayar naku, tun da safe take gidan nan
Wardugu ya ce" Mu.azam ya gayace mu baki daya mu raka shi ya ga gari,
Ayya ta yi tsam tana kallon sa, Mu.azam ya gayace ku?
Wardugu ya gyada mata kai,
Hannunta ta kai wajen wuyansa ta taba wai ta ji da zafi,
Kalau ta ji wuyansa, ta saki ta dafe habarta da mamaki, ta ce" yaushe mage da bera suka fara shan innuwa daya har shawararsu ta fara zama daya? Me ke damunku? Shirin naku kuma ya fara bani tsoro,
Wardugu ya saki hannun nata yana murmushi ya karasa ya ce" ku fice mu je ta fito idan an gama shiryata, kai yama zaka hada mana fita da karamar yarinya? Yanzu fa dole ka saka mutun ya rike bakinsa gaban yara!
Mu.azam dake biye da shi yana dariya Alhinayettt kuwa da naci ta zauna sai da Ayya ta nadawa Agaishat ta saka takalminta plat, suka kamo hanya Agaishat ta mugun yi mata kyau a idannuwanta, sai ta fito kamar wata chocolate color din balaraba, ta hade ta yi wani sihirtacen kyau
Haka suka karaso suka bude bayan suma suka shiga, ita dai Agaishat kanta a kasa, irin kalon da mu.azam ke jifanta da shi ke bata kunya, sai ta rasa me ya sa yake irin kallon nan,?
Alhinayettt ta mika hannu ta dauko wayar Wardugu ta dawo ta shiga nunawa Agaishat hotuna suna dariya,
Wardugu ya ce" ina muka nufa oga?
Mu.azam ya ce" ka kai mu Bienvenu a Wardugu place,
Wardugu ya taka wani wawan birki, ya kalo shi ya ce" wasa kake?
Mu.azam ya ce " aa can nake son zuwa, yana mai hade rai shima ya mayar da dubansa gefen titi (BIENVENU a Wardugu place, waje ne da mahifin Wardugu ya buda da sunnansa tun suna tare suna ganewa juna kafin abinda ya hada su ya hada su su bar shi da mumunar rantsuwa a tsakani, an ce yanzu matarsa da ya aura take kula da wajen wai ita Aisata ,......mugun tsama ne tsakanin wannan family masu matukar kaunar junansu a da, kuma har yanzu da daya kwal da ya malaka dai Warsugun ne..........).....
🐫🐫🐫 *BAK'A CE*🐫🐫🐫
Na *SAJIDA*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________
2️⃣5️⃣
Wardugu da ya mayar da dubansa gefen titi ya kai hannunsa yana shafa kansa a hankali, tabas Mu.azam yana tako shi kwanakin nan, in sha Allah shi kuwa zai yi iya yinsa dan gannin ya faranta masa...
Motar ya tayar ya dauki hanya, tafiya ce suka yi mai dan tsayi kafin suke karasowa wajen,
Daga mu.azam har Alhinayettt sun yi mamakin yanda ya yarda ya zo wajen,
Mu.azam ya ji wani girman Wardugu ya karu a idannuwansa , kaunar aminin nasa ya linku a zuciyarsa, adu.a ya yi masa da fatan alkhairi ...
Sai dai me, suna shiga da motar suka fara hango wasu abubuwa,
Yan mata ne da muguwar shiga, shiga ta kananun kaya sosai, da samari suna kai kawo suna dan badalar su,
Gaba dayansu kalon wajen suke da mamaki, Wardugu ya jinjina kansa a ransa ya ayanna, *Abinda ka zabarwa kanka kennan Uban Wardugu!*
Mu.azam ya yi tsam ya ce" Wardugu , ko mu juya dai? Domin wajen shi har ya fara bashi tsoro irin yanda ake shiga ana fita ana wasu abubuwan,
Wardugu ya juyo bangarensa, ya saki dan murmushi ya ce" ai mun zo sai kun shiga,
Ya bude ya fice bayan ya dauki hularsa casquette dan baya so kowa ya gane ko waye shi,
Jiki a sanyaye suke bin bayansa har ya karbi tikect din su hudu wanda zai basu damar leka ko.ina sannan su ci abinda ransu ke so, du tiket daya jika talatin ne, a wajen ba abinda babu, a da da aka bude shi an bude shi ne dan yara da iyayensu ranar weekend kawai ake bude shi, sannan ka.ida ne sai ka zo da mahaifiyarka ko da mahaifinka zaka shiga, ba.a barin budurwa da saurayinta shiga domin wajen an kawata shi da su piscine, su kayan lilo na zamani wajen game, wajen hutawa, da wajen cin abinci,
Aman a yanzu sai ta canza zani tunda ta karbi wajen da nufin zata kula masa da shi ta canza komai banda sunnan wajen, domin dalilin sunnan da ta bari doka ke tsalake su, Wardugunma bashi da labari , a yanzu wajen ba.a barin yaron da bai kai 18 shiga ba, sai gaga gagan yan duniya, sannan ba abinda ba.a yi a ciki, kan masu bushe bushen su, sai masu aikata zina a fili (wa.iyazubillah) shi kansa mahaifin wardugun bai san takamaimain abinda ake aikatawa a wajen ba, hasalima baya zama tunda abinnan ya faru da iyalansa ya ji niger din ta fice masa a rai, dan haka yake yawonsa yana kasuwancinsa a duniya, idan ya zo niger ba dan ya jima bane, koda an kawo masa korafi bai wani dubawa dan kuwa baya so ya baiwa yan tsunguri tsoma damar kawo masa korafin gidansa,
Jikin Agaishat haka yake rawa, gannin irin abinda baba sofo ke fada mata cewar ba kyau yawo jiki a bayane haka sannan ba kyau aikata zina, Ayya ma ta yi mata fadan ko a tv ta ga sun saka mace na namiji na rungumar juna ta canza tashar ba kyau aikata zina sannan ba kyau kallon tsiraicin wani banban zunubi ne ,
Wajen cin abinci Wardugu ya zame da su, domin daga nan du wani abin hange zai hango shi.
Suna zuwa suka zauna a tsararun kujerun wajen, kamshi sai tashi yake, yayan sangartatu , yayan masu hannu da shuni, da kuma masu hannun da shuni, yayan talakawan da suka zabi rayuwar hutu da zama a inda Allah ya ajiye su, sai bushasha ake ana tafiyar da lamarin cikin tsarin yan gayu.....
Menu ne aka kawo masu aka aajiye masu, nan Wardugu da kansa ke a dan duke dan kar wani ya gane shi ya dauki menu dinya kare fuskarsa da ita,
Alhinayet da gabanta ke faduwa na yannayinsa, jikinsa ya nuna ya hau, yannayinsa ya nuna ransa a bace yake,
Ta kali Mu.azan da ya rapka tagumi bai taba Menu din ba ta kuma mayar da dubanta wajen Agaishat ta ga du a firgice take sai sada kanta take bata son kallon mutanen wajen , abin bako ne a gareta,
Hannunta ta kama ta ce" Agaishat, tashi mu je,
Ai kuwa tamkar jira take ta mike ta bi bayan Alhinayettt suka fito daga dakin cin abincin suka zauna a wata farar kujera inda suka baiwa wannan lamari baya.
A hankali yake karanta menu din, harda porc, da giya kala daban daban, sannan abinda ya fi daukan hankalinsa wani abu da aka zana fari shi kuwa aka rubuta masa kudi , shi idan dai ka dauke shi dole sai ka biya, kudi masu yawa haka,
Kiran serveuse din mai dan bingilin sket ya yi da hannunsa,
Tana zuwa tana wani irin juyi fa tafia ta karaso ,
Ta saman gilas dinsa ya kare mata kallo, kafin yake mika mata menu din ya nuna mata abinda yake so,
Kallonsa take dan gane idan har dan hannun ne? Ko kuwa? Domin sunna taka tsantsan sosai bisa umarnin hajiarsu, dan ta fada masu au kula fa, kar su yarda wani mai bakin cikinta ya yi masu rami su afka, domin abin nan hoda ce, hoda ta shaye shaye,
Jikin wardugu wando ne wanda ya dan dara gwuiwarsa, sai bakar riga wace bata da zanen komai a jikinta, sai hular baka itama wace bata nuna ko ta meye ba ya dorata saman gashin kansa wanda yake da dan tsayi kadan ba dayawa irin na samarin nan dai na zamani, yannayinsa ta karewa kallo, girkeken namiji, bai yi mata kama da police ba, in ba police ba kuwa wa zai zo masu leken asiri? A tunaninta, dan haka sai ta ce" oga, ka kawo carte din ka ko kach zaka biya?
Wardugu dake zaune a aljihunsa ba kudi, sai dai a mota, carte dinsa kuwa idan ya bada za.a iya gane ko waye shi tun kafin ta karasa wajen,
Yana tunanin mafita Mu.azam ya mita tasa carte din ta bank,
Karba ta yi ta karanta sunnan,
Kallonsa take shima, a take ta ayannawa ranta yan hannu ne, wani lokacin likitoci na zuwa siyen abinnan su dai basu san ko me suke da shi ga,
Juyawa ta yi ta tafi dan kawowa ,
Wardugu ya hade jimkaken hannunsa da wanda yake bude ya shiga murza su a tare,
Sannan yana kara bin wajen da mutanen wajen da kallo,
Table sun kai biyar da ya hango suna fan dukawa su ja wani abin da yake kyautata zaton hodar maye ne a saman plat dan karami mai ruwan zaiba mai shegen kyau kafin su dago su dora daga inda suka tsaya,
Abin mamaki harda yan mata, kananun yan mata wanda a cikinsu sai ya yi rantsuwar akoy wace bata kai 18old din ba!
Wajen a da kafin ya dawo haka yake etablissement privé, wanda etat gwomnati ta san da zamansa ta bada amanar a bude shi, bisa takardun fa aka gabatar a da an gabatar ne kan irin wancen tsarin na wajen hutun yara da iyayensu ranar da ba.a karatu, aman a yanzu ta sauya zani wanda shi dai da hannunsa bai saka hannun a bude haka da shi ba,
Kansa ya girgiza, yau ko uban wa ya daure masu zasu ci ubansu!
Dubansa ya kai waje, nan ya hangi su Alhinayet suna fan taba hira da Agaishat,
Idannuwansa ya tsaida kan Agaishat wanda bai ma san ya yi hakan ba, kallon me yake mata? Sho kansa bai sani ba ko yannayinta ne ya fi yiwa idannuwansa dadin kallo?
Yana tsaka da kallon nan nata aka gabatar masa da harakar gabansa harda abin ja,
Ajiye carte din ta yi ta juya,
Wardugu ya dago hannunsa ya shiga dubawa da kyau, lale kwarai ita ce, ta ina? Ta ya aka yi take shigowa kasar? A ina take samu? Ita ke oder ko mijinta ya canza yake samo mata? Wa yake basu? Ta wace hanya ake bi a kawo har nan? Ina polisawan dake bincike a bakin titi ba dare ba rana?, ina tsaron da yake takamar ya baza a sauran garuruwa ma bale a garin da yake ciki?, ya aka yi ya yi sake haka har wannan lamarin ya cin masa da ransa da lafiarsa?
Yana tsaka da tunanin ne sai gata ta shigo,
Mace har mace, farar buzuwa mai shegen kyau, ta sha wasu mahaukatan sket da riga kanta ko dan kwali babu, ra sha wani dogon takalmi mai tsini, tana tare da wani balarabe ya sha jalabiyarsa hannunsa rike da makulin mota ,
Wani na biye da su da jaka baka suka shige tana dan dadagawa mutanen da sukai sabo hannu,
A hankali Wardugu ya mikowa Mu.azam ky din motar da suka zo da ita,
Murya a bace ya ce" ka tashi ka dauki yarwn can ku koma gida, minti talatin na baku ku shige gida da abin hawan nan, ko ku je gidan su Alhinayet dan ya fi kusa da wajen nan, domin idan kame ya ritsa da ku sai kun kwana a cel!
Ido Mu.azan ya zaro, kame a karfe uku na yama? Gashi ranar asabar ne ranar da mutane da yawa kan fita dan shakatawa, aman me ya sa zai yi kame har cikin gari bayan a cikin nan ne ake badalar?
Yar karamar wayarsa ya dauka ya dana kira,
Daga dayab bangaren aka daga ana mai fadin' Chef👮🏻♂️ (Sir),
Wardugu ya ce" ina so yanzu ka yi kira wajen Gn na Gendaremeri, sannan ka hado min mahaukatana, ina son motoci masu yawa su cika gari, ina son mahaukatam su karaso nan Wardugu place, kana jina da kyau, polisai su kama du wani wanda ya yi masu shige da suspect, ba zancen takardunka ko wani abin yau kamun yannayin mutun nake so a yi! Na fitar maka da iyaye mata wa.inda suka bayar da kwakwaran hujar daga inda suke, sai wa.inda suka kai yarensu wani wajen, bayan su a kama a cike mani cel!
Da a vos ordre ya amsa yana katse kiran ya mike ya shiga aikatawa ba jira,
Mu.azam mikewa ya yi da sauri ya fice ya tisa su a gaba da adu.ar Allah ya kai su inda zasu je lafia kar abin nan ya ritsa da su , duda motar Wardugu ne, da lambar shaida shi ne, ba zai hana a bincike su ba domin matarsa ta saka ya dora dokar ko motarsa a ringa bincikawa a gari! .........