Bai iya magana ba sai nunata da yayi a tsayen da yake inda zufa ta shiga wanke masa fuska,
Matarsa da ta shigo da tuwon tsakin da ta yi masa mai dan banzan dadi, wato mahaifiyar Anna ta ja ta tsaya da mamakin yannayinsa,
A hankali ta karaso dan gannin me ya firgita shi haka? Me yake kallo a waya?
Kurawa Anna ido ta yi, duda dan duhun wajen dan da haske aman ba irin tau din nan ba, sannan da yannayin girmanta da ya fara kama Anna, ba zai yiwu ta bace mata ba, tun usul mai kama da ita haka mutun daya ne, wanda suka nema suka rasa, kwararo kwararo har tsayin shekaru, wanda daga karshe ta yi hakuri kamar yanda mijinta ya roka, suka ajiye a jiyu, in da ranta Allah ya bayana masu ita , sannan sukai sadaka idan ta mutu ne Allah ya nuna masu gawarta ya sa ta huta,
A hankali ta karbi wayar inda jikinta ya kwashi rawa tana kallo ta kara kurawa wayar ido, a hankali ta ce" *ALLATCHI?* ALLATCHI ke ce?
Anna ta fashe da kuka, bata san lokacin da ta karaso kusa da wayar ta karbe a hannun sarkin ba ta matso wayar sosai kusa da ita tana kallon iyayen nata,
*Hatimi* wato mahaifiyar Anna ta yi taga taga zata kife inda mijinta *Gukunni* ya tareta jikinsa da wayar a hannunsa sunna duban Anna,
Shima muryarsa na rawan ya ce" Allatchi, dama kina raye? Ina kike yanzu mu zo Allatchi? Ki dawo gare mu, muna son ki Allatchi,
Anna ta lumshe idannuwanta ta bude ta ce" ina so na ganni wajenku yanzu , sai dai ba hali ,
Mahaifiyarta ta ce" mu gamunan zuwa!
Kit suka datse kiran inda Anna ta kifa kanta cikin cinyoyinta tana kuka, iyayenta du tsufa ya fara zuwan masu danma ana cikin rayuwar dadi, duda auren wuri sukai tsakaninsu dan tun suna yan university suka yi aure,
Girman soyayar da suke mata ta tuna, ta tuna irin yanda suka rayu babu ita tsayin shekarunnan danma an san musulmi da tawakali, Ba Ba hm!
Hajia aminiyar Ayya ce ta shigo dalilin kiran da Sarki ya saka a yi mata domin itace uwar gidan sarki
Tana zuwa Suka gaisa da Sarkin Timiya,
Sarki ya nuna mata Anna a matsayin y'ar gidan amininsa da ta bata wato Gukunni
Ta sha mamakin wannan lamari, daga baya ta shiga murna,
Nan ta matso kusa da Anna ta duka inda Anna ta zauna kasa wajen cafet ta ce" ki yi hakuri da kukannan haka, muma mun san da batanki, dan a lokacin sarki bai hau sarauta ba, baima aureni ba (Sarkin Agadez dogon karatu yayi , dalilin da ya saka bai yi auren wuri ba, aka ajiye masa yar kanwarsa karama sosai domin dai sarauniyar Agadez itama ba zata wani fi su Annan ba)
Sarki dake dan nesa ya yi gyaran murya ya ce" ai mai yiwuwa sunma taso, duda na fada masa kar yayi tafiar gagawa aman fir ya kiya,
Anna ta kale shi da sauri ta ce" aa, kar su taso a mota bayan har dare yayi, dan Allah su bari mu mu tarar da su,
Sarki ya yi murmushi ya ce" mota fa, aa, ai yanada jirginsa da ya malaka wato ket privé, sannan yanada damar tashi a lokacin da ta kama dan sune hukumar.
Wani sanyi ta kara ji a ranta a yau yau kennan idan Allah ya yarje mata zata ga mahaifanta? Kai Allah da girma yake, Allah da jinkan bayi yake.
Paris
Wardugu na kowama Hotel ya fice a motar ba tare da ya cewa Agaishat ta fito ba, hasalima kule motar ya yi tana ciki ya shige hotel din
Yana zuwa dakin da ya dauka ya dauki jakarsa ya zuba abinda yake iya dauka ya goya ya dauki echarp na maza na wuya ya rike a hannunsa ya fito ya basu kys dinsu ya fice abinsa
Yana zuwa motar ya ga ta kara volume din kukanta aman yana zuwa ta yi dif tana kikifta ido,
Motar ya bude ya shiga ya ja,
Bai zame ko.ina ba sai butik,
Yana zuwa ya fada masu kaya yake so a zaba mata cikin gagawa da dan kwali,
Abinka da kasar ......, sai ya kasance suturun da ake nuno masa du daga dogon damamen wando, sai yan bintiyalan riguna, sai dogayen riguna aman masu mugun bin jiki,
Kansa ya dafe gannin lokaci na neman yi ba damar ya je wani butik din sai jirgi ya barsu, ransa ne ya kara baci wai su basu da Abaya ne?
Basu da Abaya, sai da babarsu ta mike da kyar ta zakulo cikin kayansu masu tsadar gaske wa.inda sai wane da wane suke nunawa su ko a kasar, ta cirota wata riga blue mai hasken sama ta kawo masa tana tunanin bama zai iya ba dandai idan batai masa ba ya dauki wata ne dan tsadarta
Dagata ta yi inda suka bita da kallo, doguwar riga ce itama mai rike jiki bale daga sama, aman tanada dogon hannu daya kwal, sai dan siriri tamkar na shimi da akai masa wani irin kwana aka malaka shi jikin rigar daga sama,
Sai dan kwali irin kananuwan nan sosai shima mai sharashara mai ruwan fari fari da blue blue din
Kansa ya dafe yana duban kayan, ba kudin da aka fada masa bane damuwarsa dan kudin sun kai jika dari hudu, aa, yannayin rigar ne, aman gannin ya yi rantsuwa, sai kawai ya bata umarnin ta shiga wajen saka kayan ta saka su fice,
Da sauri mai butik din ta nuna mata ta bita ta tsaya daga kofa ta saka kayan sannan ta shiga ta gyara mata sosai, ta saka dan kum ta dan cacaje mata lalausan gashin kanta ta dora mata dan kwalin ya nadu ya yi kyau a fuskarta,
Wani irin kyau kayan sukai mata sannan suka fitar da kirar jikinta inda cikarta ta bayanna ,
Waouh macen ta fada kafin su fito tana nunawa Wardugu,
Mikewa ya yi bai kaleta ba dan shi ba dan hakan ya zo siyen kayan ba ya karbi jakar takalmin ya mikawa macen sannan ya juya bayan ya cewa Agaishat idan ta saka takalmin ta dauko wa.inda ta cire din maza su tafi
Da sauri ta saka takalmin, Allah ya taimaketa bai daukar mata mai tsini ba, plat ne mai igiya dan haka ta daura igiyar ta dauki wa.inda ta cire ta fito da sauri sauri ta nufi motar
Ja yayi suka tafi, tana ji tana ganni ya tsaya kofar gidan da bada jimawa ba yake gidan mijinta ya jefa kayan da ta cire ya dawo ya shiga motar yana tafe yana waya da yaronsa har suka karasa aeroport din
Nan suka iske shi har ya karaso dan haka wardugu ya bashi ky din motar sukai salama suma suka daga sai Niger Garin taraya Niamey garin zabarmawa, garin ka zo na zo
*Niamey*
Mota na tsayawa na fice da gudu daga motar inda sai a lokacin ya bita da kallo, yanda ta kwasa a gujen har dan kwalin kanta ya sulube daga saman kan nata ga yanda jikinta ya jijiga ya jijigo ne ya saka shi kawar da kai yana astagafari dan kuwa matar da batai idar sakin mijinta ba kalonta haka ai ba kyau🤨
Dan zama ya yi yana tunanin ya shiga ne ko kawai ya yi tafiarsa?
Wata zuciyar ta fada masa Wardugu Ayya fa mahaifiyarka ce, kuma indai kere na yawo, zabo na yawo watarana an hade, dan haka ka je!
Ayya dake zaune tana kallon tv, a lokacin wajen karfe takwas da rabi na dare ne,
Sai jin kukan y'arta ta yi da ganinta ta fado da gudu ta fada jikinta ta kankameta tana rizgar kuka,
A rikice Ayya ta shiga kokarin tashi da ita tana fadin" Agaishat? Agaishat? Innalilahi wa.ina ilaihi raj.une, Agaishat ke ce? Lafia ? Ke da wa kuka zo? Me aka yi? Ina mijin naki? Ina wardugun? Ke?
A daidai lokacin Wardugu ya shigo yana tafia a hankali ya karasa saman kujerar zaman mutun guda ya zauna yana dubansu yanda ta makalkale Ayya da irin yanda Ayya ta rikice sai tambayoyi take tana duban wardugun,
Kamar daga sama ta tsinci maganarsa, koma tace kamar saukar mari, ya dan ja iska yana duban Ayya ya ce" *Ya saketa ne*,
Dif Ayya ta yi da tambayoyinta tana duban Wardugu, saki? Abinda kunnayenta suka jiyo mata kennan?
A hankali ta kankace idannuwanta tana duban Wardugu zatai magana kennan ta ji Agaishat ta ce" Ayya wai ya sake ni, Ayya ban san laifin da na yi masa ba,
Ayya ta kallo wardugu ta ce" Saki,? Aka yiwa y'ata? Shin ciwon nasa haukata shi yayi kafin a gane har na dauki y'a na bashi ? Mahaukaci ne da riga?
Wardugu ya dago yana duban Ayya da auna yannayinta, daga muryarta ya fara dauko cewa Ayya ta fara hawa, wato tana harhada dukan abinda gareta na tashin hankali wanda yayi imanin zata saki a yanzu yanzu,
Ajiyar zuciya ya saki ya ce" da hankalinsa
Ayya ta zabura ta mike tsaye, idannuwanta ta karasa kankancewa ta nuno wardugu da dan karamin yatsarta ta ce" ni? Ni zaku yiwa wulakanci? Ni zaku tozarta? Ni zaku watsawa kasa a ido? Ni zaku tonawa asiri? Ni zan dauki yarinya na baku ko wata batai ba ku sako mini bayan ba kangarariya na baku ba kuma ba hujajen buhu na baku ba? Ba nakasashiya na baku ba kuma ba neman kai nake da ita ba na dauka na baku ba? Gaskiyar Aghali, a lokacin da ya zo min bankwana nake fada masa maganar kun tafi neman aurwn yarinyata yace da ni haba Ayya, ai da ni zan ce ina so, na yi mata dukan abinda za.a yiwa yar gata na aureta a kaita gidana na kula maki da yarinya, aman yanzu kika baiwa abokin Wardugu kin tabata zai rike maki y'a?
Wardugu ya dago kansa da sauri, dan tunda ta fara maganar kansa ke sade, bai yi niya ba, bai so tanka Ayya ko daya ba, dan an bata mata tanada damar yin fada ta yi abinda take so, shine mai laifi dan shi ya uzurata , ya lalabata har ta aminta da a je a dauro auren, ya so yin shiru ta kare kansa, shi kuwa tasu shi da Mu.azam ne, Takunsu na gogagu ne, zasu goga ! Sai dai ji yayi bakinsa ya ce" Haka yace kennan?
Ayya ta ce" Ubanka yace Wardugu, nace Uban nan naka yace! Ba gashi ba ya nuna halin ba.a je ko.ina ba? Sai na yi shara.a da shi! Ba zan barku ba ku duka! Wato an baku y'ar a saukin kudi ko? Baku yi tade tadensu na buzaye ba kun samu abin a bagas ko?
Agaishat dake kallon Ayya, ta ce" Ayya, dan Allah a bashi hakuri ya mayar da ni , walahi ba zan kara yi masa koma mene yace na yi masa ba,
Ayya ta juyo da mamaki ta rike habarta ta yi tsai tana kallon Agaishat inda dakin ya dauki wani dan shiru, can ta ce" kina ji? Ki tashi, ki je dakinki ki cire mini wannan rigar ki yi mini wanka ki wanke ruwan gidan wannan banzan, ki yi sallah ki kwonta ki yi baci tun kafin na yi baja baja da ke a gidannan! Ka ji rashin sannin ciwon kai? Namijin zaki turani lalabo shi? To ko ku haka kuka a tadanku na buzaye na soke maki hakan a rayuwarki na haramta maki hakan! Walahi walahi walahi ni Ayya in dai na rike ki ko na kwana daya ne karya ne ki kuma waiwayar wani Mu.zzam koda shi daya kwal ya rage a duniya! Agaishat bace min da ganni kafin na maki marin da zai kufumta maki kunne!
Da sauri ta mike tana karkarwa ta shiga taka matatakalar benen ta haye da gudu ta nufi dakinta tana waiwayen Ayya dake tsaye sai da ta bacewa ganninta ta juyo wajen wardugu,
Takowa ta yi har gabansa ta tsaya ta ce" in sha Allah na dauki alwashin sai ta zama abin hangensa daga nesa, sai ya yi dan daman bai sakar min y'a ba, ubankuma bai isa ba bale ku (wato Marahut), wasan kuke so bugawa da ni ko? Ni zaku kawowa wargi a wannan lamarin ko? Na gode , aman ka fada masa gidana da gaishe da ni sun haramta a gare shi! Yarinyata nada gatanta, in da hakinta kuma ban yafe ba!
Shi dai Wardugu kansa na kallon kasa, shi ganima yake da sauki tunda bata kai ga kifa masa mariba, sannan a haramtawar tata banda shi, dan haka ya sada kai sai da ta kare fadanta ta juya ta haye sama ya samu wuf ya fice a gidan,
A wannan dare kwana Ayya ta yi tana fada tana kai kawo tsakannin dakinta da na Agaishat tana duba lafiarta da banka mata harara danma karta yarda ta kuma kawo mata shirmen wai a lalaba shi, yo Allah ta tuba ko ita dake tsohuwa ta wani bi namiji a yanzu bare y'arta yarinya mai jini a hanci son kowa kin wanda ya rasa? In sha Allah zata kulata ta gama idarta tsaf sai su san abin yi, fatanta Allah ya sa bata dauko ciki ba dan a yanda take cikennan kar a je sai da ya kumsa mata ciki ya saketa (wato dai du a tunaninsu wani abu ya shiga tsakannin Agaishat da Mu.azam.....)
Wardugu kuwa na shiga gidansa ya tarar da gidan shiru kamar koda yaushe,
Bai wani damu da neman gannin matarsa ba ya nufi bangarensa,
Yana shiga ya tarar da farar takarda an ajiye ya dauka ya karanta, mai aikinsa ce ta yi masa salama da fadin ba zata iya ba madame ta koreta ta mata alkawarin in dai ta zauna mata a gida zata soketa da wuka!
Murmushi yayi ya yarda takardar nan ya shiga dakin da kyau, falon ya danyi kura abinka da fararan kaya nan ya yarda jakarsa ya nufi wajen wayar dake dakin ya daga ya shiga latsa numbobi.....
Tafiar awa gudu suka yi kafin su karasa garin Agadez capital de l.aïr
Hilux din sarki ce ke jiransu da direba, suna sauka direba ya dauko su inda kamshin turaransu ya cika motar
.....................comment comment.comment
🐫🐫🐫🐫 *BAK'A CE* 🐫🐫🐫🐫
https://www.facebook.com/Idan-rana-ta-fito-writers-association-114558343535568/?referrer=whatsapp
*☀IDAN RANA TA FITO WRITER'S ASSO🌤* ____________________________________________
*Fad'akar da al'umma tare da nishad'antar da masoya shine fatanmu*😘🤝🏻😘
Na
*SAJIDA*
6️⃣0️⃣
Motar na saka hancinta cikin gidan *Hatimi* ta rike hannun mijinta gam,
Shima din a zaunen kawai yake aman du gani yake ba.a sauri an kasa karasawa,
Anna dake tsaye a falon sarki dan baki daya can ya dugunzuma su sai kallon kofa take tana kai kawo ,
Turo kofar da aka yi ne ya saka ta tasayawa cak tana kallo ,
Direban ya fara shigowa kafin *Gukunni* sai *Hatimi*,
Dan tsai suka yi kafin Hatimi ta daga kafa da sauri sauri jikinta na bari ta karasa wajen Anna da kafafuwanta suka kasa dagawa daga tsayuwar ,
Tana zuwa rungumeta a jikinta inda Gukunnima ya karaso kafafuwansa na hardewa ya hadasu su duka ya rungume,
Ido kawai ta lumshe wanda jin nauyinta ya yi yawa ya saka Hatimi sasauta rikon da tai mata tana talafeta tana faman kufce mata dan ta yi nauyi da yawa,
Da kyar suka samu suka talafota, Anna ta suma
Nan fa hankali ya tashi sai ihun a fitar da mota a tafi asibiti suke suna talafe da ita a jikinsu,
Sarki je ya karaso da ruwa da sauri aka shafa mata
Wani irin numfashi ta ja kafin take buda idannuwanta a rikice irin farkawar sumarnan da mutun ke yi.
Ganninta jikin mahaifinta , wanda yake da dan gemu kadan fari wato furfura sai girarsa da ta fara farin itama, sai hannun mahaifiyarta fa dake jimke da nata ta dan daga a hankali ta ga hannun ya dan fara yakushewa irin na tsufan nan,
Kuka ta fashe da shi tana kara shigewa jikinsu, ji take tamkar idan ta sake su zasu bace a gabanta ne, dan haka ta ririke su tana kallonsu tana kara shigewa jikinsu
Sun jima a wannan yannayi, inda yayanta ke zaune can gefe , kukan yarima jariri ne ya fargar da su inda Anna sai a lokacin ta tuna da y'ayanta,
Dan sasauta rikon ta yi masu gannin ana dan waiwayawa inda yaran nata suke zazaune suna fama mimika Yarima boy sunna jijiga shi a tsakaninsu,
Tsare su Hatimi ta yi da ido kafin a hankali ta dawo da dubanta wajen Anna,
Murya na rawa ta ce" *Allatchi?*, ina kika shiga kika barmu cikin tashin hankali da rashin nutsuwar zuciya?
Anna ta tsareta da idon itama,
Gukunni ya riko hannunta ya ce" Allatchi, kin san irin tashin hankalin da na shiga dalilin dawowa daga wajen aiki da na yi na tarar da anmanki da *Herde* tsakar gida suna kuka wai baki motarki aka ganni a kofar gida aman ke baki dawo ba kuma wayarki bata shiga? Ina kika je?
Anna ta sada idannuwanta kafin a hankali ta ce" ban san da me ya juyar da hankalina ba, wanda tunda na baiwa gida baya ban san takamaiman abinda ya faru da ni ba sai nan da kwana goma na dawo hayacina, hasalima ban san *zaman da na yi da shi na shekara da shekaru ko da aure muka yi shi ko kuwa zaman haka muka yi?* , gashi harda y'aya suma sun fara haihuwa,
Zabura Gukunni ya yi ya mike tsaye, nan da nan jikinsa ya dauki rawar bacin rai da tashin hankali, murya bace ya ce" waye? Dan gidan waye? Wanene ubansa da kuma shi din kansa? Ko wanene ina mai tabatar maki da sai dai a yi daya cikin ni da shi, sai na rufe shi rufewar da ba zai fito ba sai dai a fitar da shi!, koda ya ki fitowa yaransa zan rufe sai ya bayanar da kansa! Sai na nuna masa danyen kai koda ubanshi sarki ne!
Anna dake zaune ta dago da kanta da sauri gabanta na faduwa, muryarta na rawa ta ce" yaranshi? Ko yarana? Abanna, bai damu da yaren ba dan ya yi rayuwarsa ne ta hanyar siyar da su, wato yana karbar sadakin yarana a tafi da su shikennan , ba sai ua damu da yaranba zai damu dan an rufe su? Aa ba za.a taba mini yaranna ba dan ina son su!
Ta karashe tana mai fashewa da kuka ta ce" mun yi rayuwa cikin dajin Timiya,
*Algabitt* ya kasance dodo , kura, fitina a rayuwarmu ni da yaranna,
*Algabit?* Hatimi ta tambaya tana mai son karin bayani kan waye hakan? Dan ta manta, bata taba kawowa a ranta ba,
Anna ta dubeta da kyau ta ce" Algabitt wanda Muka kade da Mota ni da Herde daga karshe Abanna ya dauke shi aiki a gida,
Hatimima mikewar ta yi a tsorace tana fitar da idannuwanta baki daya tana kallon Anna,
Anna ta dago kanta ta shiga kora masu dukan abubuwan da kwakwaluwarta ke iya tinnawa,
Mahaifiyarta kawai mutuwar tsaye ta yi, dan abin ya mugun daketa, wai Algabitt? Yaron da ta dauka tamkar dan gida? Eh lale aikinsa baiwa fulawowi ruwa, aman tunda ta ga y'ayanta na son lamarinsa ta yarge masa shiga falonsu, a zauna da shi a sha dariya, bale da ya fada masu shi maraya ne shikennan suka kara yarda da shi duda wani lokacin mahaifin su Anna na fadin yaron nan yanada wani kallo irin na munafukai, sai ta yi daria ta jinjina hannunta tana fadin sai alkalina, kai fa ka saka na aminta da mu dauko yaronnan, sai yanzu da muka shaku da shi kai kuwa ka fara hango wani abin?
Bayan Anna ta yi shiru da labarinta Hatimi ta duka inda take zaune ta jata jikinta irin rarashi,
Gukunni kuwa sai wani irin numfashi yake fitarwa na bacin rai, bai ko kalli inda su Gaishata suke ba, dan shi kama suke masa da yaron, sai yanzu ya tina yaron, kam, lale haduwarsa da wannan bakin macijin za.a sha mamaki,
Hatimi ta dago tana share hawayenta ta ce" Gukunni, ka yi hakuri, yanzun ya dace mu yi murnar ganninta, na tabata asiri yayi mata, mu yi fatan da aure ya rayu da ita , mu rungumi jikokinmu, na san Herde sai ta fi kowa murnar yarannan , ta kwashi yayan wasuma bare na yar uwarta wace suka shaku ? Ai ni da zaka amince minma da ba zamu wani yi shara.a da wannan yaro ba, idan har ya sanar mana gaskiyar da aure ya rayu da ita? Ya sawake mata salim alim ya je, duniya ce, sannan mai duka na madakata, ya je ya yi abinda yake so idan tunaninka kai din wani shege ne a duniya toh tabasa akoy wanda ya dameka ya shanye, ba zan yi shara.a da shi ba, bai isa ba, cuta ya gama cutata , sai dai na gode Allah da tun kasa bata rufe mani idannu ba Allah ya bayanar min da ita,
Gukunni ya juya yana kallon su Agaishat , ya juya wajen su sarki dake zaune sun yi zuru suma,
Da kai Sarki ya jinjina masa irin nuni da ya yi hakuri, ya tausasa zuciyarsa,
Dan yatsansa karami ya dantsa a bakinsa kafin ya kada kai ya nufi wajen su Agaishat da suka tsurewa nufo sun da ya yi,
Yana zuwa ya duka ya dauki Yarima Boy dake kuka ya juya ya fice a falon da shi,
Murmushi Hatimi ta yi tana duban su ta ce" zai huce, ko dan dan jaririn wannan fushinsa ba zai yi tsayi ba, dan yana son yara kamar me, burinsa ya samu dan jika ,
Sarki ya sauke ajiyar zuciya, ya kuma kiran uwar gidansa domin ba a gabanta akai komai ba,
Tana zuwa ya umarceta da ta baiwa baki wajen hutawa,
Dukansu suka mike suka je bangaren sauke bakin alfarma aka basu dakunna wanda matar sarki ta nuna masu kowa dadaya, aman Anna ta kiya kan su hade suka,
Hakan kuwa aka yi dan haka sai aka shigo da sauran gadajen dan dakunnan akoy girma aka yi masu shinfidun alfarma inda suka shiga gaba dayansu,
Sai a lokacin Hatimi ta zo wajen su Agaishat dake tare waje guda ta zauna tana kallonsu,
A hankali ta ringa rungumarsu tana tausaya masu, zuka zukan yan mata ya wannan aman a cikin duhun kai, suturun jikinsuma abin tausayi wai a nan sun wanku ne? , ko.ina yar uwar tasu take ita? Shiga halin kaka naka yi har ka cire da ka mika kyauta, karshe a zo a aure shi bada izini ko saninka ba sai komai ya wakana a sanar da kai,
Kai bata tunanin akoy kotun da zata iya yi mata shari.a da Algabitt a nan gidan duniya.
*NIAMEY*
Jakar hannunsa ya yar a nan ya shige dakansa yana yatsina fuska dan kyankyamin wajen yake,
Samu ya yi ya buda wajen tufafinsa ya ciro kaya masu tsafta
Yana kokarin rufewa ta shigo dakin, yauma dai cikin kwaliyar take duda bata san da zuwansa ba,
Walyn kam akoy kama jiki, akoy kanshi, akoy iya kwaliya,
Karasa shigowa ta yi tana duban hannunsa da mamaki, wasu kayan ne ya dauka, ina zai je kuma? Shida yanzu shigowarsa har zai juya?
Da sauri ta idasa kusa da shi tana mika hannu wajen kayan ta ce" Wardugu, ina zaka je? Dan Allah yanzu fa ka dawo, daga ina kake haka wajen sati uku? Kuma ka dawo yanzu ka kuma fita?
Bai tsaya sauraronta ba ya goce kar ta karbi kayan ya rabata zai fice
Hankalinta ne ya kara tashi, ta san waye mijinta wajen harkar mu.amalarsa da matarsa(aurataya), aman yanzu har tsayin wannan lokacin bai wani nemeta ba?
Da sauri ta je ta bayansa ta rungume shi, hannunsa ta kamo ta dora saman rigarta wajen mararta ta ce" baka tambayi ajiyarka ba zaka tafi? Baka damu da cikinka dake jikina ba?
Wardugu ya janye hannunsa ya juyo yana kallonta tun daga kanta har kasa, idannuwansa ya dan bude kafin ya ce" kudin account din ki sun yi kasa ne?
Wani abu ta ji marar dadi a ranta, tabas tana yawan yi masa biyaya idan tana son kudi, aman ita yanzu bama kudin ya kawota ba, gannin baya gida ne ya fara daga mata hankali,
A hankali ta kai hannunta bayan zip dinta ta zuge shi har kasa, ta ja rigar ta cire ta shiga nufo shi tana mai kokarin jan ra.ayinsa,
Bai wani kawar da kai ba, sai da ya kureta da kallon tsaf kafin ya saki wani murmushi irin na ka raina abu ya juya ya fice a dakin ya barta nan tsaye tamkar mutun mutuni,
Ido ta kwalalo da matsanancin mamaki ta kwala wani ihu kafin tace" walahi ban yarda ba, kai ka ga haka ka tsalake? Kawai ka tare da wata yar iskar, walahi sai na bika na gani,
Wardugu na jan dankareriyar motarsa ya fice Walynma ta fito da tata ko dan kwali babu saman kanta tsabar neman fitina da jayowa kai fitina ta shiga bin bayansa a hankali inda ya ganta ta miroir tunda danja ta tsayar da shi,
Murmushi ya saki mai tsada kafin ya ciro wayarsa ya nemo lambar Basma a cikin whatsupp dinsa ya danna mata kira
Ka na rana, in sha Allah za.a samu na dare

6️⃣1️⃣
Hanya ya canza ya dauki ta gidan minister,
Kiran da ya yi mata daya kwal ta daga ya fada mata yana anguwarsu kishi ya kama shi yana muradin ruwa,
Abinka da yan gayu, dama a wanke take a lume cikin katuwar kujerar falonsu, tana jin haka ta mike da gudu ta haye sama ta feshe jikinta da turare ta ajiye wayarta ta sauko kicin ta dauki faranti fari ta dora goran ruwan Awa, ta kuma kiran saurayinta da zai zo zance cewar kar ya zo ta fita!
Dan nesa da gidan ya tsaya, domin a kofar gidan gwomnatin yaransa ne ke gadi suna baiwa gidan tsaro,
Yana nan zaune yana hangen Motar Walyn sannan ya dan dago ya hangota ta fito daga gidan nasu,
Cancandi inji ni, yarinyar fa ta gama haduwa, farin ne? Tana da shi, kyan ne? Ta gaje shi, tsarin halitar ne? Ta ninka Walyn sau biyu, yarinya Shuwa Arab, gashinta ta yi kwaliya da shi ta sake shi, taku take da dogon takalminta dan kara jan ra.ayinsa, inda ya kawar da kansa daga dubanta , wani uban tsaki ya jawa kansa, wani haushin kansa ya ji a lokacin da zuciyarsa ta raya masa wani lamari a kan wada ba zai so zuciyarsa ta falasa shi ba, zuciyarsa ce ta hasko masa gudunta na dazu da rigar dake jikinta Blue mai ruwan samaniya, zuciyarsa ta fada cewa" ta zarce misali,
Idannuwansa ya rintse daidai nan ya ji tana buga masa glas din mota,
Cire lock din ya yi dan haka ta bude ta taka ta shiga
Tana shiga ta juyo da ruwan da iya kwarkwasar da ta san tana tafia da duban samari ta yi masa salama,
Dubanta ya yi irin na tsaf din nan kafin yake karbar ruwan ya yi mata nuni da tana iya tafia,
Ido ta zaro kafi ta shagwabe fuska ta ce" haba abincin ruhina, daga zuwa sai ka kore ni?
Wardugu ya hade fuska ya ce" fitarmin a mota na ce!
Da sauri ta kama marfin motar ta dira daga motar tana kallonsa ya watsa mata wani kallon kyama ya yi ribos ya nufi hotel dan ba zai iya kwana a gidan ba ya yi masa dati,
Walyn kam kamar mahaukaciya ta tada motar tana zabga gudun sai ta kamo shi , ta yiwa yarinyar kuma kallon tsaf tana kwafa kan zata dawo gareta
Yana tsayawa da mota ya fito, ta fito da sauri ko rufe motar batai ba ta tunkaro shi
Sai dai kafin ta karaso yannayin fuskarsa ya saka ta rage saurin da take,
A haka ya shiga cikin Hotel din inda take binsa da sasarfa
Du daki daya kwana daya jika dari uku ne , ky ya karba ya juya ya je wajen accenseur ya shiga,
Tana tsaye har ta ga wajen da ya tsaya ya nuna ya dawo ta danna itama ta shiga ya daga da ita,
Yana budewa ta sako kafarta guda wajen ta ji an yi sama da ita sannan an rufe bakinta,
Wutsil wutsil take har ya shiga dakin ya direta saman kujera,
Kafarsa guda ya dora gefen kujerar yana dubanta kafin ya ce" ke, kin raina ni ko?
Fashewa ta yi da kuka , tana kuka ta ce" yanzu wardugu amanata kake ci? Budurwa ka yi? Wannan yarinyar dake yawo itace ta dauke min hankalinka har sati uku? Wardugu cikinka nake dauke da shi fa? Wardugu kai fa batube ne, ka san ko a al.adunmu ba.a yiwa mace kishiya sai ta haihu kamar uku ko hudu, yanzu Wardugu ko cikin na fari bai fito a jikina ba ka fara zuwa wajen budurwa ka yi zamanka ka manta da ni du irin kiran da na yi ta yi maka?
Sai da ta kare magangannunta ya ce" auren zobe na yi da ke?
Ni ka daina fadin maganar auren zobe, ba wani auren zobe, ai mu ba auren zobe ya kawo mana wannan ba, al.adunmu suka hana.
Adini ne? Ya fada yana kara tsareta da ido,
Walahi ba adini bane aman muna rike da su da karfin gaske, kuma ko Ayya ba zata bari ka taka su ba, ta fada tana son kauce dubansa dan ba zata iya ba,
Wardugu ya yi murmushi ya nunota da yatsarsa manuniya ya ce" Baki da kunya Walyn, Ayyata kike nufi? Wace kika raina,
Walyn ta ce " ni ban raina Ayya ba, ba zan taba iya rainata ba.
Kansa ya girgiza ya sauke kafarsa ya tsaya gabanta ya ce" kin san me? Nifa da a tsarina babu maganar na auri macen da ta furtan kalmar so , gaskiya wayewata bata barina gannin matar nan a mace, kema kin shigeni da yawa ne
Kin gane, ina son mace mai aji , wace ta san kanta,
Walyn ta mike ta ce" ai koda ni na fara cewa ina sonka kaima daga baya kace kana so na,,
Wardugu walahi in dai ina raye ba kai ba wata mace a duniya sai ni,
Wardugu ya yi murmushi yana kallon yanda take girgiza ita ga marar kunya, kansa ya kada ya shiga cire rigarsa ya ce" je ki,
Walyn ta dube shi, ta je fa?
Wardugu da ya gama balewa ya juyo yana dubanta tana dubansa ya ce" ki tafi.
Walyn ta ce" aman ka san idan na fita yanzu za.a rufeni ne ko? Dan umarninka ne,
Wardugu ya daga kafada ya ce" eh ki je,
Ido ta shiga kikiftawa tana dubansa, matsowa ta yi tana dubansa ta ce" Wardugu, shin baka san ciwona bane? Ai ko albarkacin cikinka dake jikina sai ka sasauta mini,
Wardugu ya buga wayarsa dake hannunsa da kasa ya yi taku biyu ya shaketa ya kaita jikin bangon dakin ya hadeta ya firfito mata idannuwansa baki daya ya daga murya ya ce" bayan wanda kika zubar? Ke daba baki da hankali? Kina tunanin zan aureki na sakeki sakaka kina yawo tamkar tinkiya? Du motsinki, du abubuwan da kike ina sane da ke, wada ta nuna maki hanyar zubar da cikin tana rufe, ke da kika zubar ba sai na kara kwonciya da ke ba bale ki kara daukan cikin? Walyn kauce maki nake kina biyo ni a filin rashin mutunci? Kin manta waye ni? Halaya basa sakewa sai dai a sada kai dan kunya! Ke taraki nake, bana son ki ga ranar da zan dago ki, kike ikirarin aure? Toh bari ki ji ba.a yi ba ba za.a yi ba macen da zata dora min dokar ba zan kara aure ba tunda ba dokar Allah bace,
Zan dauki yan aiki mata a gidana daga gobe tunda ke baki san ana daga maki kafa ba, yan mata zan kula na ga me zaki yi? Walyn ikirarinki ki soke ki kashe ko? Ni da ke za.a ga ainahin asalin batube, zamu gwada sokewar!
Cikata ya yi ta zube wajen tamkar mataciya tana jan numfashi ya dauki ky din motarsa da carte dinsa ya fice a dakin ya yi tafiarsa
Wakyn kam suma ta yi na dan lokaci kafin take dawowa hayacinta,
Ta jima kwonce kafin take janyo numfashi ta zabura tana zaro ido tana neman inda yake, hannayenta biyu ta dora saman kanta , ya sani? Ya san na zubda cikin? Ya sani? Wayo na shiga uku,
Da kyar ta iya rarumar ky dinta tana dingisawa ta fito ta shiga motarta ta tayar tana tafe tana labe labe har ta karasa gidansu
Wardugu kam a nan cikin mota ya kwana idonsa biyu yana duban titi, da safe bayan ya dawo daga masalaci ya shiga motarsa ya tayar, kokarin harbata titi yake ya dan yi tsai ya afka tunani:
Tun yana can aka turo masa bayanin an maidota asibiti tana zubar da jini,
Doctern da ya dubata aka turawa wardugu numbersa, nan yake shaida masa maganin zubar da ciki ta sha,
A hankali Wardugu ya binkita ya gane da wa da wa ta yi mu.amala har aka gano masa wanda ta kaita da wanda ya siyar mata,
Su duka aka rufe ita kuwa ya yi murmushi cewar zata gaje kurenta, daga lokacin ne ma ya kara daukar niyar sai ya kara aure koda zata mutu, kuma ba zai saketa ba su je zuwa tunda har shi zata zubar da cikinsa dan wani shirme nata na kar ta haihu da wuri ya kara aure? Zai kula matan ya ga wanda zai hana shi!,
Kansa ya girgiza a zaune a motarnan, yaushema aka yi aurensa da Walyn? Yarinyar da ta nuna masa zata rayu da shi komai bakin halinsa? Ta shanye wulakancinsa? Yanzu ta zame masa fitinaniya? Shi kam baya ra.ayin sakinta, da zata gyara halayenta ma zai rayu da ita a haka, aman ba zai daina kudirinsa na aure ba.
To wa zaka aura? Ya yiwa kansa tambayar nan,
Basma? , ko cikin sauran yan matan? Ko zuwa kake ka samu wata yar liman ka aura?
Murmushi ya yi gannin du sai ture shawarwarin zuciyarsa ke yi, a fili ya furta" ke ki nutsu, *wada kike hange ba zai yiwu ba, domin ko ba ransa ta taba zama tasa*
(Toh Fa)
Sai wajen karfe goma na safe Ayya ta shiga dakin Agaishat,
Zaune ta sameta tana kallon waje guda,
Ayya ta karasa ta zauna kusa da ita,
Hannunta ta kamo tana dubanta , da dukan kulawa ta ce" Agaishat, ki yi hakuri, ki yi hakuri, ki barwa Allah kin ji? Bana tunnanin saka lamarinnan a rai zai saka ki ji sanyi, ki dauka lokacin mutuwar aurenki ne ya yi ba dan wani mugun halaya ko wani abin ba, ki roki Allah ya maye maki gurbinsa da wanda ya fi zama alkhairi , ki yafe min kin ji?
Agaishat ta matsa ta dora kanta a cinyar Ayya, murya na rawa ta ce" Ayya ba abinda kikai min, na tsorata sosai da jin wai ya sake ni, Ayya na yi tir da rashin ilimina, da zan samu na je makaranta da na ji dadi, dan bana son a sake maimaita min abinda akai min Ayya, ashe zaune nake gidan mutumen da ya sake ni? Kuma ya kasa dubana ya fada min ya sake ni? Me na yi da zafi haka? Wannan lamari ya girgizani Ayya,
Ayya ta lumshe ido tana shafa kan Agaishat ta ce" in sha Allah, da aljihuna, da lokacina zasu kare a kanki har sai kin samu ilimi, fatana ki yi hakuri , ki daina damuwa,
Agaishat ta kara kwontar da kanta tana jin wasu hawaye masu dumi na gangaro mata daga gurbin idannuwanta, ba zata so ta rayu kamar mahaifiyarta ba, ka zama tamkar abin wasan namiji? Ai matayenku ba takalmanku ba aka ce, abokan rayuwarku ne, idan dadi bai hadata da miji ba, ba zata so ta yi rayuwar wulakanci da shi ba.
Paris
Yau kwana na uku kennan Mu.azam baya gannin Wardugu ba kuma ya gannin Agaishat sun zo ganninsa sai Marahutt dake nan wanda shima yace zai juya a gobe tunda jikin da sauki,
Ya tambayi khadija sai dai gargadin likita ya saka bata ce masa komai ba, daga nan ya gane kawai Wardugu ya ga sakonsa.
Marahutt dake tsaye kan lamarin Mu.azam khadija ta fada masa komai, ya ji ba dadi sosai abinda Mu.azam din yayi, aman ya yi masa uzuri da jiran jin bayaninsa ta waya dan juyawa zai yi gida
Mu.azam ya birkicewa Khadija sai da ta bashi wayarsa , nan ya yi ta gwada kiran number Wardugu aman amsar daya ce ba zai same shi ba.
Abinda ba.a so din ne dan kuwa ya fara tada hankalinsa , dan ya kasa samun nutsuwa dalilin rasa Wardugu har kansa ya fara ciwo
Hakan ya daga hankalin su Marahutt dan haka ya shirya ya juya gida, wato niger
Direct office din Wardugu ya je, nan ya same shi yana cikin aiki,
Kamar yanda ya saba hawo shi kai tsaye , yanzun ma kai tsayan ya hau shi inda ya dana vidio call ya ajiye masa ya fice a office din,
Kaĺlon junna suke ,
A hankali Mu.azam ya ce" ka yafe mini War, ka yafe mini na roke ka,
Wardugu bai bashi amsa ba sai kallonshi da yake
Mu.azam ya ce" ya kake so na rayu da macen da ka fini son ta?
Wardugu ya mike tsaye yana dubansa kafin cikin karaji ya ce" *Ni na fada maka ina son ta?* *a ina muka taba yi da kai cewar ina son ta?*
🙄🙄
🐫🐫🐫🐫 *BAK'A CE* 🐫🐫🐫🐫
https://www.facebook.com/Idan-rana-ta-fito-writers-association-114558343535568/?referrer=whatsapp
*☀IDAN RANA TA FITO WRITER'S ASSO🌤* ____________________________________________
*Fad'akar da al'umma tare da nishad'antar da masoya shine fatanmu*😘🤝🏻😘
Na
*SAJIDA*
6️⃣2️⃣
Ka kasance mai zama da mutun da zuciya daya, na yi imanin koda wani ya zo rayuwarka dan ya cutar da kai Allah zai kare ka👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻
Mu.azam ya rintse ido dan harga Allah baya son yannayin wardugu na fushi, shi walahi tsoronsa yake,
Tausasa murya ya yi ya ce" Wardugu nine fa? Ni ne Mu.azam,
Idan kaine Mu.azam sai aka yi yaya? Ko an fada maka dan kai ne Mu.azam shikennan ka san ko ni wanene? Harma ka san abinda yake raina ko me?
Mu.azam ya sauke ajiyar zuciya yana dubansa, a hankali ya ce" ka yafe mini,
Wardugu ya daki table din gabansa da hannunsa ya nuna wayar ya ce" dan ka san kana cikin halin rashin lafia ka yi min wannan gangancin?
Mu.azam baka da huja, hujarka bata da wani ma.ana, ya zaka saki yarinyar da na je na karbo amanar aurenta wajen iyayenta a gabanka wai kan wata banzar hujarka ni Wardugu ina son ta?,
Mu.azam ya yi shiru yana duban wayar,
Wardugu ya dan rage ihun bacin ran aman muryarsa a kausashe ya ce" dan kana da wace kake so ka wulakanta mini ita?
Mu.azam ya kwararo ido da mamaki,
Wardugu bai barshi ya ce wani abu ba ya ci gaba" Mu.azam ka san irin halin da na tsinci kaina na irin kukan da ta ringa gumzawa a kanka?
Bakai min adalci ba, baka rike min amana ba, kai ka isa ka yi hukunci ne? Kan zaton da kake?a abinda ka yi hasashe? Ko akoy wanda zai fito yace na taba fada masa ina son ta ?
Mu.azam ya talafe habarsa da hannunsa na dama yana yiwa Khadija alama da kar ta leko wayar, (😳),
Wardugu ya juya ya juyo ya tsare shi da jajayen idannuwansa ya ce"
Yau koda hakan ne, koda ace wai na taba soyaya da ita bama maganar ana tunanin ina sonta ba, Mu.azam aure? Aure abin wasa ne? Da ace ita ta fito maka da hanyoyin da suka girgizaka , da ace ita ta nuna maka kiyaya da idan ka saketa da hujar bata sonka ba zaka iya zama da ita ba hankalina zai dauka, aman Mu.azam ka saka mini ita ta yi ta kuka? Wanda yau kwana hudu tunda na ajiyeta ban koma ba dan ban san shin ta daina kukan rashinka ba ko bata daina ba? Ni kadai nake da alhakin sakata kuka, daga lokacin da na karbo amanarta wajen mahaifiyarta ta zama abin karewana ta gaske,
Ba zan lamunta ba, ba zan iya kawar da kaina daga du wani wanda zai sakata zubar da hawaye ba!
Yana kai karshe ya datse kiran ya zauna yana saka hannunsa cikin sumar kansa,
Marahut dake daf da kofar office din, kasancewar murya dage Wardugu ya yi magana da Mu.azam ba abinda bai ji ba,
Ido ya kurawa kofar, kafin yakr kada kai ya juya ba tare da ya shiga daukar wayarsa ba, dan ya tabata idan ya shiga a haka zasu kara hawa sama ne, dan ransa a bace, kansa ya girgiza yana adu.ar Allah ya shiryi wardugu da zuciya, kuma abu gashi zahiri sai ya take sai ya ji jiki ya lalubi mutun.
Yau kwananta daya a gidan Ayya,
Tunda ta je wajen mahaifiyarta ta kora mata bayani , uwar ta buga ta buga suka ga basu da hanyar bi da ta wuce su je wajen mahaifiyarsa dan sun tabata itace kawai ke zabga masa mari ya sada kai, ta tankwasa shi ya yi koda baya so,
Ayya ta sha mamakin ganninsu, sai dai da ta ji abinda ke tafe da su, domin mahaifiyar Walyn nunawa ta yi ta zo da gaskiya dan a gaban Ayya har marin Walyn ta yi tana fadin irin gangancin da ta yi na zubar da ciki, da kukanta daa komai take rokar Ayya ta ji kanta ta kama mata, harda fadin yayan zamani ne ka haife su baka haifi halinsu ba,
Sosai ta nuna bacin ranta na irin halayan Walyn duka Ayya na kallonta,
Ayya bata da yanda zata yi, na farko dai ita ta yi imanin idan da zuciya biyu ne Allah zai iya masu, na biyu ko ba komai ta ji dadin ashe matar dan nata ta san bata kyautawa ? Duda bata nemeta ba sai a yanzu da take gannin ta masa madaukakin laifi? Na uku gaskiya ne, yayan yanzu sunna abubuwa ne gabam kansu, ba zata so a saki yar wani ba dan an saki tata bata ji dadi ba, a gaskiya sakin da akaiwa Agaishat ta ji shi har cikin ranta, dan haka ta amince ta zauna nan gidanta na dan lokaci har ta iya da lamarin Wardugu sai ta koma dakinta,
Duda ba haka suka so ba, sun so ne ta yi kiransa a lokacin ta bashi umarni, aman sai suka hakura dan matakin da suka taka na neman galaba kar ya kubuce masu,
Dalilin da ya saka Walyn ke zaune a gidan Ayya yau kwana biyu, inda take cikin dakin da yake na Mu.azam, domin dakin Wardugu daman Agaishat ta zaune shi ,
Tana zaune a gidan ne ba tare da shiga sabgar kowa ba, idan lokacin cin abinci ya yi mai aiki zata je ta fada mata, wani lokacin ta fito a ci da ita inda tana ci tana dana waya, wani lokacin kuwa tace bata ci sai sun gama ci ta zo ta diba ta ci,
Sai abinda ke bata mamaki irin yanda yarinyar nan yar kauye da suka dauko ta zama, duka dukama wani lokaci ta dauka a gidan? Aman cikin ikon Allah yarinyar ta wanku ta zama wata big girls irin yayan yan gayun nan, komanta irin na yan gayu ne, ita tambayace cike da cikinta, ba ita bace Mu.azam ya aura? To ina Mu.azam din? Duda tana yawan zama da doguwar riga da dan kwalinta a kanta, bata wani harkar samari dan Ayya na kilaceta wai ida take, sai karatu da aka daukar mata malamar makaranta dake zuwa tana koyar da ita sau biyu a wuni dan Agaishat dai ba komai take yi ba, ita kuwa malamar apbashin koyar da agaishat din yama fi na wanda ake biyanta a makaranta , dan haka ta rike damarta take aikinta da zuciya daya inda suke bi a hankali suna karatun su,
Ba abinda ke hada su , dan walyn bata taba zuwa ta tarar da Agaishat zaune ta nuna ta san da mutun a wajen ko ta yi kata salama ba, itama Agaishat ta gwada gaisheta sau uku aman Walyn bata amsawa dan haka sai ta kama kanta, domin wani yatsina fuska Walyn take idan ta ganta, wai yar kauye ta samu waje,
Zaune suke a fali, Ayya na saman kujera baba inda Agaishat ke zaune kasa da litafi a hannunta tana bitar hada sunna tana karantawa a hankali Ayya na gyara mata wajen gyarawa,
Bayan sati biyu
Fitowa ta yi ta sha shada tana baza kamshi ta dan tsaya nesa da su Ayya kadan ta ce" Ayya, zan je wajen auren kawar tawa,
Ayya ta dago tana dubanta, ta so ta share ta tafin, sai dai fa tunanin yanzu fa a wuyanta take ya saka ta ce" bari na fadawa mijinki,
Wayarta ta saka Agaishat ta dauko mata domin wayar a kashe take wajen sati biyu kennan dan kara nunawa Wardugu tsananin fushin da take ciki,
Agaishat ta mike yau kuma da yake ta san ba wani namijin dake shigo masu iya su ne, dogon wando ne jikinta mai dan santsi sannan daga kasa da irin igiyar nan ta daure kasan da shi, bai kamata ba aman ya bi shap din jikinta, sai fara kar din riga body wace bata da kwaliyar komai jikinta, sai dan kwali karami da ta yane gaban goshinta da shi , idan ka ganta kamar irin beautiful din balck americain din nan, ga kamshin turaran wankanta mai karawa fata santsi da take bazawa du idan ta gita,
Da ido Walyn ta bita kafin take yatsina fuska, kamar tace a barshi kar a yi kiransa dan bata so, ko da wasa bata shirya tarbansa a yanzu yanzu ba, ita gaba ta kaita rashin zuwansa gidan, da farko a dari dari take daga baya ta sake abinta take lamuranta hankali kwonce , ba abinda ta nema ta rasa, dan haka ta kwontar da hankalinta ta san dai ko ba jima zai nemeta tunda bai saketa ba,
Kafinma Agaishat ta dawo da wayar karan dankareren babur din nan nasa ya isar da zuwansa gidan,
Wani irin juyawa Walyn ta yi wajen kofar gabanta na faduwa da wani irin sauti da cikinta ya bada, Wardugu ne a gidan warhaka?
Ai bata san lokacin da ta cire dogon takalmin nata ta jefar nan bayan kujerar Ayya ta yi sauri ta karasa saman cafet ta zauna ba saman kujera ba,
Ayya dake binta da kallo ta dago sukai ido hudu, wata kunya ta ji ta kamata, tunda suke bata taba zama a kasa Ayya ta zauna a sama a matsayinta na wace ta girmeta bale a je ga maganar sirikarta, zama take duwaiwanta da nata ba abinda ya shafeta aman yanzu da ta ji motsin Wardugu ta zo da gudu ta zauna a kasa,
Murmushi Ayya ta yi tana waiwayawa dan jin tafiar Agaishat wato ta dauko wayar,
Tana saukowa shi kuwa yana shigowa,
Matatakalar ba a saitin kofar shigowar take ba aman dan fitina idannuwansa suka hasko masa ita ta cikin bakin gilashin da ya saka,
Kara kicin kicin ya yi da fuska ya maido dubansa wajen Ayya wace itama ta hade fuska inda Agaishat ta juya da gudu ta koma dan saka hijab
Harga Allah bai ga Walyn ba, domin tunaninsa ba zai taba kawo masa wai Walyn na zaune a gidansu ba, sannan Walyn a kasa a zaune? Bai kawowa ransa haka ba, dan haka ya karasa kujerar dake facing din Ayya ya zauna yana kallon Fuskar Ayya, a ransa ya ayyana bata huce ba dai,
Murmushi ya yi kafin ya ce" Maman Wardugu barka da yama,
Ayya ta zabga masa harara kafin ta ce" ni zaka gaisar da gilash?
Cire gilash din ya yi wanda ya saka ta ga idannuwansa sun yi ja, ko na meye oho?
Wardugu na cirewa ya ce" ina son Ayyana 👏🏻
Ayya ta yatsina baki tana duban Walyn, hakan da ta yi ya saka shi duban inda take kallo,
Zoben hannunta na zinari ya toni ko wacece domin shi ya sayi zoben,,
Juyar da kansa ya yi tamkar bai gane wacece ba, kamarma bai ga wanda ke zaune ba,
Ayya ta girgiza kanta dan sarai ta san ya gane ko waye aman ya wani basar,
Ayya ta ce" kai, mace na karkashinka aman bata gidanka tsayin wannan lokacin baka bibiyi inda take ba? Kana da lafia kuwa Wardugu?
Wardugu ya kaleta irin kallon nan na tsai, murmushi ya yi ,
Ayya ta ce" wani ahu ta yi maka ne?
Wardugu ya girgiza kai bai yi magana ba,
Ayya ta ce" Wardugu ka min magana mana ko kurma ka zama?
Wardugu ya yi murmushi dan kuwa ko ba komai yanda ta masa magana haka ya ji dadi, dan haka ya ce" wace matata?
Ayya ta kale shi inda Walyn ta dago da sauri itama tana dubansa,
Ayya ta hade fuska ta ce" ka dauki matarka ku koma gidanku , koma me ta yi ka yi hakuri ,
Wardugu ya dago da sauri ya ce" Ayya?
Ayya ta hade fuska ta kawar da kanta ta ce" na ce ka yi hakuri.
Wardugu ya dan matso bakin kujerar,
Hannunsa mai dauke da zoben azurfa ya dago a hankali ya shafo kansa zuwa sajensa,, ya yi haka sau wajen biyu kafin yake dan dagowa ya kalli Ayya, itama shi take kallo sannan da idannuwanta ta nuna masa da ya bi umarninta,
Wani murmushi mai ciwo ya sakar mata kafin yake dan muzgutawa ya koma cikin kujerar ya zauna ,
Ayya ta dubi wajen Walyn dake zaune ta ce" ki tashi ki koma dakinki, ki kiyaye dukan abinda mahaifiyarki ta fada
Mikewa ta yi zurbat ta dan sosa kanta tana duban Ayya, aman batai masa gargadin kar ya mata wani abin ko ya daina fushin da yake da ita ba,
Sai dai ba halin ta kawo maganar domin ko a fuskar Ayyan bata ga fuska ba,
Dan haka ta samu ta raba Ayya ta fice da sauri ta shiga motarta ta nufi gidanta.
Tana fita Ayya ta maido hankalinta wajensa tana dubansa, ta sani sarai shirunnan da ya yi gwara ya yi magana, aman sai ta share, idan tana son tankwasa shi bata nuna wani tausayi ko tsoron zuciya,
Rai ta hade ta ce" an yi maka laifi mai girma, ka yi hakuri , kar ka ci gaba da nuna mata wani abin, ka kwontar da hankalinka, dukan tsanani yana tare da sauki.
Idannuwansa ya lumshe ya kai dubansa wajen matatakalar Ayya, kansa ya juyo yana duban Ayya ya ce" alfarma faya nake nema a wajenki Ayyana,
Ayya dake dubansa ta ce" wace alfarma ce?
Idan na tashi neman aure , ina so tsakanina da ke ki sanya mani albarka, ba ruwanki da maganar wani al.adu da me za.a dube ki, Ayya bafa adini bane, dan na taka ba Allah zai kama ni ba, ba kuma wani zqi hana mini ci ko sha ba, ba wanda zai hana ni shiga inda nake so, hasalima koda za.a yi da ni sai dai a yi a boye, ki toshe kunnayenki na roke ki!
Ayya ido kawai ta zuba masa, zata fi kowa murnar gannin wardugunta ya samu wani canji bangaren mata,
Ya kasance mai farin jinnin mata, suna likun masa a duk inda ya saka kafarsa, sai dai abin takaicin cikin matan nan wa.inda ya samu wani kusanci da su du sun saka ya ji dan damanma, har yanaiwa mata kallon zuma daga nesa, idan suka karaso gareka sun zama madaci,
Me ya rasa? Ya kasance namiji har namiji sai dai ya rasa macen mutunci,
Ya mace zata zubar da cikinka wai a zuwan ba zata haihu da wuri da kai ba dan tana maka tsananin son da ba zata so ka auri wata ba?
Ta iya zubar da gudan jininta, dan sunna dan tsaninin kishi ya zata dauki lamarin zaka auri wata?
Danma a haka wai tana shayinsa, du haukanta tama tsoron su hade daga ita sai shi idan ta yi masa laifi, aman lamarinta na saka Ayya a shakun jin wai wardugu zai dubi wata bare ya aureta,
Sai dai ina, ba zata shiga hakinsa ba , ba zata shiga ba, ya isa haka, harda laifinta irin yanda take tsawata masa idan ya dace ya hukuntata, ta samu damar da take sakawa ranta ita daya kwal ta ishe shi ko kowa ya rasa,
Ajiyar zuciya ta sauke tana kawar da kanta, zatai ta adu.a, aman ko wacece zai aura zata hadu da fitinar matarsa sai dai idan ita dinma wata kwaron kanta ce!
Gidan su Anna
Tunda suka sauka a gidan su Anna ba rajar banza da ba za.a yi baki ba, sun zo yi masu barkar gannin y'arsu,
Abin har mamaki yake baiwa su Gaishata, sai dai duba da irin mukami da datijantakar tsohon gidan ya tarawa kansa daraja,
Wani abu dake baiwa gaishata mamaki, shi ne irin kirarin da ake yiwa mahaifiyar Anna,
Sai dai zaman da ta yi da ita na dan lokacin nan ya saka ta gane ba wai likawa aka yi ba, ta cancanci hakan ne,
Ita bata taba gannin mace irinta ba, a duniya duda tsufan da ya kamata ko me take, ko da wa take, mijin nan nata yana gaba da komai,
Wato wani irin kulawa, wani irin cancanna, wani irin salo da take bazawa a cikin gidan ba ruwanta da jikokinta ki yayanta ko wasu sirikai, ta iya tafia da mijinta a gaban kowa, kuma cikin ikon Allah du irin zafinsa idan ya kwashi zafi ya fice zatai murmushi ne idan ya je ya dawo ta bi bayansa zai fito kamar ba shi ba,
Har wani kirari take masa namijin mazaje ja gaban Hatimi aban Herde da Allatchi,
Zaka ga yana wani kayatancen murmushi,
Ko yanzu gaba ta saka Gaishata bayan ta gama lumdarta da turare, domin ita ke kula da harkar wankan jegonta koda yaushe tana daka tana lumdeta da shan zafin daki ta dubeta ta ce" ni kishiyoyinki nawa?
Gaishata ta ce" biyu,
Yara ne suma kamarki ko sun manyanta?
Gaishata ta ce" dayar na fita, dayar kuma ta manyanta,
Hatimi ta gyada kanta ta mike ta dauko wani kindirmo da ta dada ta zuba wani ruwan itace da ta dafa da kanta ta bata ta ce" ya mu.amalarki da su? Irin zumunta?
Gaishata ta ce" a gaskiya bama fada kuma bama shiga harkar juna,
Hatimi ta ce" me yasa bakwa shiga harkar juna? Kina nufin a cikin gida daya kuke aman ba ruwan kowa da kowa? Irin rayuwar idan wani na cikin wani hali ma ba ruwan dan uwansa da shi?
Gaishata ta ce" da na je na tarar da ita bata taba nunan hanyar zumunci ko akasin hakan ba, yayanta basa zuwa inda nake, hakan ya sa nima nake rayuwana, da ya kara aurema itama da ta zo bata shiga sabgarmu,
Hatimi ta tsaya tana dubanta da mamaki, kafin take cewa" kuma ya shi yake daukan haka?
Gaishata ta ce " yakan yi jajen wani lokacin, aman wani lokacin baya nunawa,
Hatimi ta girgiza kanta ta ce" bakwa tsoron Allah? Kishin ne haka ko hauka? Ku baku yi zubde zubden hauka ba , aman kuna zama tamkar masu gaba da juna? Me hakan ke nufi?????????
Gaishata ta ce" ni ban san ya zan yi ba,
Akoy lokacin da ta haihu na je barka, ina shiga aka rufe jaririn, ni kuwa da na dawo ban koma ko zaman wuni ba,
Kuma yanzu da na haihu cikinsu ba wanda ta leko ni, har ranar sunna, sai ana gobe zamu taho na ji hayaniyarsu suna fadan dan me zai biyo mu, shi kuwa ya fada masu ba zai iya zama ba
Ajiyar zuciya ta sauke ta umarceta da ta shiga wanka, ita kuma ta fita ta je ta dauki waya suka gama waya da wanda ta saka a kawo sabin kayan daki dan canzawa gaishata idan ta tashi komawa, sannan ta je tsakar gida ta fice yan matan biyu wato su mariama suna ta dariya da aku suna magana yana maimaitawa,
Su Herde ta gani zaune suna hira, kanta ta girgiza ta ga halamar idan ba da gaske aka yi ba zasu daina tuno da suna kukannan ba,
Da kyar ta ga mijin nata da jikansa a cinyarsa dan jariri ya rungume, ga kuma sirikin suna zaune saman tabarmar leda kasan inuwar mangwaro suna hira a nitse,
Salama ta yi masu ta samu waje ta zauna,
Nan sarki ya mike dan basu waje
Hatimi ta dube shi ta ce" aa mai gida, ai ni da san samu na yi wajenka na zo,
Dawowa ya yi ya zauna yana dubanta,
Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce" ban san ta inda zan fara ba, aman zan so ka sani ba kawo min hirar gidanka ta yi ba hasalima mamaki ne ya ishe ni gannin garinku akoy network, kuma yarinyar nada kishiyoyi, sai dai ban ga suna wani kiran juna ba, duda da wuya idan basu da waya?
Ka yi hakuri, ina jin yaran nan har tsokar jikina, a yanzu da ta yi nesa da yan uwanta bata da kowa sai su sai kai a garin, rayuwa zai mata wahala idan ya kasance ba wani zumunci ko fahimtar junna tsakanin su,
Menene matsalar? Zan so a gane a yi masalaha tsakaninsu, dan kai namiji ne, ba koda yaushe zaka zauna ka yi hira da ita ba, duba da ba ita kadai keda kai ba, ga fita nema da sauransu.
Ajiyar zuciya sarki ya sauke, a nitse ya ce" an samu matsalar ne tun daga aurenta, ita ta nuna ba zata zauna da kishiya ba , ni kuwa na jima daman ina son na samu aurenta, shine na yi rantsuwar sai na rabu da ita idan ta kawo min wani abin a cikin maganar aurena,
Shi ne tace ba komai na je na auro yar gwal, ita kuwa zata zuba mana ido ta ga ta zaman lafia,
Hatimi ta jinjina kanta tana dubansa ta ce" eyah,
Ga tushen fadan,
Ka yi hakuri d'ana, aman na tabata kana nuna wani fifiko tsakanin su?
Gukunni dake dubansu ya kai dubansa wajen sarkin ya ce" aboki, shin ka kasance mai nuna wani wariya tsakanin matanka wanda har matan naka suka fahimta suka san ka fi son wani da wani tsakanin su??
Kansa ya sada ya shiga tunani kafin yake dagowa ya ce
🐫🐫🐫🐫 *BAK'A CE* 🐫🐫🐫🐫
https://www.facebook.com/Idan-rana-ta-fito-writers-association-114558343535568/?referrer=whatsapp
*☀IDAN RANA TA FITO WRITER'S ASSO🌤* ____________________________________________
*Fad'akar da al'umma tare da nishad'antar da masoya shine fatanmu*😘🤝🏻😘
Na
*SAJIDA*
6️⃣3️⃣
Ya jima kafin yake cewa" ni babu wani madaukakin bambanci da nake nunawa a tsakaninsu, abu daya dai na sani idan sako ne zuwa wajena fada du wace ya kasance dole sai na ji a lokacin da nake zaune da talakawa sai an bi ta kanta, wannan kuma dalilina shi ne, zata shigo min da nutsuwa koda kuwa sakon mai firgitarwa ne,
Abu na biyu, sababin suturuna na ajiye a wajenta, dan ita ke kilace min ta yi masu wajen da ba mai zuwa sai ni,
Sai idan zan yi bakin kunya, ita ke girkinsu dan ta iya girkin sannan takan sako mini a kwanon da ba zan ji kunya ba
Ni kam iya abubuwan da zan iya tinawa kennan, sai wa.inda a rashin sani ne,
Hatimi ta gyada kanta ta ce" wa ke saya masu kwanoni? Shin kai ne? Idan kai ne kana saya kowace iri guda?
Ka taba baiwa wata cikinsu ajiyar kayan aka bata? Ka nuna mata dalilin da zai sa zaka kwashe bata kula ba?
Sai maganar tarar da kai wajen taronka da talakawan garinka, shin watansu ta taba zuwar maka a hargitse ne? Ta tayar maka da hankali? Ka zaunar da su ka nuna masu ga yanda kake so su kasance idan zasu je wajenka basu kiyaye ba?
Ajiyar zuciya ya sauke ya ce" kwanoni ni ke sayan masu du idan na shiga birni,
Nasu na bacewa ne da wuri sai su ce wai yara ke lalatawa, kuma ba ruwansu ba zasu nemi gyarawa ba idan na yi bakon sai dai na ga wani abin tashin hankali cikin har hada min marfi ake daban da kwano,
Sannan gaskiya ban taba zaunar da su na fasa masu su kilace min suturuna ba, a ganina irin girman miji a gurin matarsa har sai na fada masu haka? Da girmansu da komai? Ita ai ba fada mata na yi ba,
Sannan a gaskiya sau biyu aka yi irin ina cikin mutane, idan abin kuka ne za.a shigo mini da gudu jiki fata fata a ja a tsaya an ci damara a gwaza kuka ana jijiga , har sai na yi rarashi da roko kafin a gwaza min abinda ke faruwa, hakan ya saka na soke tarar da ni fada ,
Murmushi ta yi ta ce " ka yi hakuri mai martaba, mace du girmanta idan ta takarkare ta tafka maka wani abin wani lokacin sai ka yi mamaki,
Kar yannayin da Gaishata ke nunawa na kimtsi ya saka ka tunanin ita kadai xe kimtsatsiya a cikin matanta ko mai tarbiya, idan fa tana haka ne dan bata fara haihuwa ba?
Yau da gobe ai sai Allah, dole rayuwar yau da kulun sai ana tarowa ana gargadi, ana uzuri, ana nuna hanya, ana nuna bacin rai a abu kafin ka ga dan daidai,
Kar ka yi mamaki idan nace da kai dan daidai, domin daidai fa sai Allah, ita mace a karkace take, wata barazana ke tsoratar da ita , wata sai an nuna mata jan wuya, wata yar a bi a laluma ce, aman du miji a gidansa kafin ya zama laushi sai ya zama tauri,
Nufina a nan shi ne, kai mai mata uku reras a jere, dole sai ka cire maganar so a ranka ka kamanta adalci
Kar ka ga kamar sun nuna basu damu ba, sun damu fiye da tunaninka, kuma shirunsu halaka ne a wajenka a lahira, don kuwa idan a nan ka fi karfinsu na zasu iya yi maka komai ba a lahira fa? Kuma ba zasu taba jituwa da wada ka fifita a kansu ba,
Dole ka kwatanta zaunar da su lokaci zuwa lokaci, kanai masu nasiha, wace ta taka dokarka ko wacece ka hukuntata daidai tsarin adinni, idan ka ga lamarin zuwa wajenka sun kasa daidaitawa ka soke zuwan , koda wani irin abin ne a yi hakurin zuwanka,
Numfasawa ta yi ta dubi mijinta da ya mike da jariri a hannunsa dan ya fara dan kuka ta maido dubanta wajensa ta ce " ka yi hakuri, ina barar ka duba shawarwarina,
Murmushi ya yi yana gyada kai, shi fa wly du abubuwan sun shige masa ba wai dan bai sani ba , aa , sai irin yanda cikuluftun shara.ar mutanen garinma kadai ta ishe shi, gashi ita din irin yanda ta kasance mai masa biyaya daga bayan nan, hakan ya saka du ya watsar da wani ya zasu ji ko me suke tunani da hukuncinsa yake yanke abinsa , tabas yanzu ya yarda da laifinsa a irin zaman doya da man jan da ake a gidansa, .
Bayan wata uku
Taro ne na jama.a, datijai ne , bakake da fararan buzaye an cika kofar gidan yau asabar wajen karfe shida na yama,
Sojoji makil suna zazaune kan fafaran kujerun da aka jejera du yawanci da kayansu na aiki domin wasu daga aikin suke wasu kiwa zasu hau suka biyo wajen karbar sadakin abokin nasu,
Can kusan kofar gidan kuwa sun dukufa wakilan ango da amarya ana zantawa kafin ake miko jimgin kudin sadakin da ya baiwa jama.a da yawa mamaki, ba.a taba ji ba, yau aka fara, sadakin farar buzuwa haka?
Domin ana miko kudin mahaifin amaryar ya juyo wajen Wardugu da jimkin kudin a hannunsa , dan dukawa ya yi kusan kunnensa ya yi masa magana, inda Wardugu ya shiga gyada kai yana jinjinna girman datijon a ransa,
Kudi na mamaki har million goma ne suka zo da su a matsayin sadakin wannan zukekiyar yarinya sai dai mahaifinta ya katse masu hanzari ta hanyar irgar jika hamsin ya cire ya mika masu sauran kafin yake fadin" Allah ya saka masu Albarka, wannan ya isa sadakin *Alhinayett*, kaya ka yi mata abinda ka ga dama aman iya sadakin y'ayana kennan,
Du wajen sun yi mamaki inda suke bin datijon da kallo kafin a shiga shaidar an karbi sadaki,
Uzurinsu na bukatar a yi auren da wuri suka kawo inda mahaifin Alhinayett ya nuna in sha Allah ba damuwa dan haka a nan ya yanke ranar aure wata guda danma ya aan ba zasu rasa dan shirshiryensu na mata ba da me zai yi jira? Shi daman baya so a saka auren yaro ya jima yana yawo da sadakin wani a kansa, kayan daki kuwa in sha Allah ba zasu gagara ba domin mahaifin Alhinayett ba wani hamshakin mai kudi bane, yana nema alhamdulilah yana samu sosai.
A wannan lokacin aka karbi sadakin mai neman auren Alhinayett wato colonel Aba gana bisa sadaki jika Hamsin , inda aka saka aure nan da Wata guda.
Wardugu ne tsaye kan lamarin nan, ba wani washe baki yake yana babaga dariya ba, aman du wanda ya sanshi idan ya ga fuskarsa zai gane yana cikin farin ciki,
Bai samu ya dan zauna ba sai da mutane suka watse , inda mahaifin Alhinayett da yan uwansa sukai ta saka masa albarka kafin yake shiga motarsa ya nufi gidan da suke yana mitar wai dan za.a kawowa mutun sadaki sai ya bar gida?
Kamar yanda ya yi tunani hakan ne,
Alhinayett bata da wasu kawaye, sai abokanannan aiki wa.inda bata fada masu ba tace sai aure zasu ji,
Tsakar gida suka shinfida tabarma gidan kanwar matar Abansu ce mai suna Fatima zahra suka je,
Gefe sun jika zobo sun saka masa kankara suna yi suna kurba,
Gefe guda kuwa nama ne suka yanyanka suka tsitsira a tsinke Agaishat ta yi garwashi suka dora gashi saman abin gashin auntyn nasu ,
Redio ne kanwarta mai suna Sajida wato jida ta kuna sai shayin da ta dora masu wanda yake dahuwa a yar tukunyar shayi,
Su takwas ne, su uku nr zaune saman tabarmar inda Alhinayet ta sha lafaya fara kar , Sajida ta saka doguwar riga blue wace kadan ta fi gwuiwarta , Agaishat ma lafaya ta dora kan doguwar rigarta wace itama bata kai har kasa ba sannan ta dan kama jikinta ta yi mata kyau mai ruwan ja, suna zuwa suka cire lafayar suka shiga shagalinsu suna dan taba rawar buzaye domin sun saka guitar ne a redion yana tashi,
Gefe kuwa yan matan ne wa.inda kanun Alhinayett ne suma suna ta raharsu suna casunsu dan kowa murna yake domin Alhinayett ba ruwanta da wani bambaci tsakaninsu, tana taimakawa kowa da abinda Allah ya hore mata, ba ruwanta da kai kararsu, idan abin ta fada maka gaskiya ya kama zata dubeka ta fada maka sai dai idan ka gama fushin ku dawo ku shirya,
Jida wato sajida ce ta dubeta a lokacin da take ziga shayi ta ce" Aunty, wai ke ina kawayenki ne?
Agaishat dake juya naman dake saman abin gashi ta juyo itama da yaren buzanci ta ce" ba gamu ba?
Alhinayett ta girgiza kanta tana duban message din Aba tana murmushi,
Jida ta ajiye zugar shayin ta nufin Wajen Agaishat ta dan duka irin yanda Agaishat din ta yi , ta saka hannunta tana gyarawa Agaishat gashinta dake zubo mata yana faman hanata aikin da take kafin take cewa" mu? Mu fa kika ce? Ko ban san shekarunki ba na san aunty ta fi ki sosai, kawa fa kamar ana nufin kamar ni da Leila, da Nana, da Mariam, aman kin san da aunty Alhinayett bata da kawa sai aboki?
Agaishat dake jin dadin hira da yar budurwar buzuwar ta bada hankalinta kanta tana ji tamkar kanwarta da ta rasu , a hankali ta daga kai tana hangen yan matan, take yan uwanta da mahaifiyarta suka fado mata a rai, ko ina suka shiga? Wardugu ya je kauye a lokacin sarkima bai dawo ba wai sun shiga birni wajen dangin Anna, gashi ya ce zai koma aman har yau bai samu ya koma ba dan aiki ya sha kansa,
Hankalinta ta maido wajen jida da ta hi zaman yan bori gabanta ta ce" sai ki fada waye abokin nata?
Jida ta yatsina fuska tana girgiza kai irin abu ya bata takaicin nan ta ce" ko kin ji ana fadin wani Wardugu?
Agaishat ta zaro ido bata bata amsa ba,
Jida ta ci gaba da fadin" bana zaki kasa sannin General Wardugu ba, wannan gabjejen katon mai ruwan samudawa, yana nan dogon nan fari aman fuska uwa kashin safe takwaf ba annuri, ni du zaman da nake rayuwana zan ce saurayinta ne, domin dai kin ga Abanmu tsauri ne da shi baya barinmu kula maza in ba wa.inda zamu aura ba, aman abin mamaki wai shi abokinta ne,
Ai ni kalonsu kawai nake, har a school ina fadawa kawayena ai yayata soyaya take da General Wardugu du wace ta taba ni zamu rufeta,
Wai kawai yanzu wai ace wani Aba? Hm na yi mamaki
Agaishat ta yi murmushin da ya bayanar da wutsiryarta ta mike dan dauko abin fifita wutar dan garwashin ya yi sanyi sai dai me? Ganinsa ta yi tsaye daga bakin kofar shigowa gidan, ya harde hannunsa saman kirjinsa, idannuwansa sanye da gilashi, aman yannayin fuskarsa kamar ita yake kallo,
Gabanta ne ta ji ya fadi, tunda suka dawo daga Paris bai fi sau a kirga ba suka hadu, ya yi tafia kan aikinsa, da ya dawoma baya wani yawan zuwa gidan sai jifa jifa sai matarsa dake dan lekowa a tsatsaye ta fice abinta,
Kallo daya ta yi masa kafin take juyar da kanta ta nufi wajen Alhinayett ta fada mata cewar Wardugu ne, ita kuwa ta dauki lafayarta ta nada a iya kugunta ta juya neman abin hura wutar,
Alhinayett ce ta sanyo shi gidan, inda yan matan du suka shiga watsewa a hankali dan kowace ta san shi farin sanni basa son abinda zai hada su da shi, ya rage daga Alhinayett dake zaune facing dinsa, sai Agaishat da Jida dake dan nesa da su suna aikinsu na dafa shayi da Barbecue.
Gilashinsa ya cire yana duban Alhinayett kafin ya sakar mata murmushi ya ce" inyeh amarya,
Alhinayett ta turo baki ta ce" kafa ce ba zakana tsokana na ba.
Murmushi ya sakar mata ya ce" ai ba tsokana bane ,
Alhinayett ta ce" War, wai dan Allah da gaske an karbi kudin?
Wardugu ya kanance idonsa guda ya ce" ke baki da kunya ko? Da ba.a karba ba ya zaki yi?
Kafadunta ta daga ta ce" ba sai in ci gaba da zama a gidan ba, kai kuma in ci gaba da damunka ba, 🤷🏻♀️
Ya miko hannunsa zai lalace hancinta yana murmushi dan wani nishadi yake ji Aminiyarsa kanwarsa zata yi aure kwana kusa kennan jiddah ta kwala ihu ta shiga bura tana kokarin dage lafayar Agaishat
Agaishat din kuwa ta rintse ido ta kasa motsi inda take tsugune
Da sauri Alhinayett ta nufe su tana tambayar lafia?
Jida ta nuna mata cinyar Agaishat ta ce" ina ziga shayi ne ashe ta kawo hannunta ni kuwa na juyo shine ya zubun mata a nan,
Alhinayett ta aniya janye lafayar bayan ta dungure kan Jidda tana fadan ke komai zaki yi ba zaki yi shi hankali kwonce ba sai da katsamniya tamkar wata saniya?
Agaishat kam zufa ce ta ji a goshinta inda idonta ke rintse, dan Walahi bata ji zuwan abin ba sai zubarsa ta ji saman cinyarta , gashi ya gama tafasa kennan ga zafin shayi, ji take gaba dayama kamar kafar ce ta tsoma cikin ruwan zafi
Wardugu dake zaune bai san lokacin da ya rintse ido ba jin abinda ya faru, kokowa ya shiga yi da zuciyarsa da tunaninsa kan kar ya mike, kar ya je, kar ya je, ga kururuwar kanwar Alhinayett din nan dake kara caza masa kwakwaluwa, a hankali ya lalubi hanki yana kokari goge fuskarsa da bai san me zai goge ba wayarsa ta shiga kuka,
Lalubar wayar ya yi da sauri ya daga kiran baima tsaya gannin waye ba,
Walyn dake tuka mota ta ce " Wardugu, gamu mun fito daga gidan su Alhinayett din an ce wai ba can take ba, ina ne gidan da take mu je?
Wardugu ya shiga yi mata kwatancen gidan kafin yake datse kiran ya tsurawa yatsotsin Agaishat ido domin Alhinayett ta kawota wajen tabarmar ta zaunar da ita da kyar ta samu ta bude wajen ta saka a kawo mata ruwan gishiri ta shiga tofa mata adu.a,
A hankali idannuwansa lumshe yake kallon yatsutsan kafar nata, dogayen yatsutsan kafa gareta, wa.inda suka kawatu da faratuna masu dan tsayi farare kar kar aman can samansu da dan jan lale, kafarta ta dama na dauke da dan karamin yatsa irin shidanin nan, sai yan kananun gashi dake saman kowace yatsa luflufluf da su,
Tsikar jikinsa ne ya ji ta tashi a hankali yake kokarin kawar da kansa sai dai ruwan gushirin da Alhinayett ta zuba mata ya saka ta jimke hannun Alhinayett da hannunta guda sannan ta kawo dayan hannun wajen kafar nata mai shidanin ta damki kafar ta cije lebenta kafin take kifa kan nata saman kirjin Alhinayett ta shiga sauke ajiyar zuciya,
Zabura ya yi ya karbe kofin ruwan giahirin kafin ya zabgawa Jida wata uwar hararar da ta sakata juyawa sumui sumui ta bar wajen ta koma wajen gashinsu a ranta tana ayanna kumurci!
Tsayuwa ya yi a kansu wanda ya saka Alhinayett dagowa tana dubansa,
Murmushi ta saki kafin ta girgiza kai a ranta tana ayanna zan ga gudun ruwanka gide, in sha Allah yar buzuwa ba zata bika ba kamar yanda sauran yan matanka ke binka, da yardar Allah zaka kawo kanka ne,
A hankali ya duka ya ci fuaka ya kai hannunsa ya daga wajen da ta kone din,
Wajen ba wani tashi ya yi ba aman ya yi duhu alamun jini ya kwonta,
A rayuwarsa ya ga ciwon da ya fi wannan girma, shi kansa a jikinsa ya ji mugun ciwon da ya fi wannan dan har harbinsa an taba yi,
Maganar zubuwar ruwan zafi kuwa idannuwansa sun ga abinda da za.a maimaita a yanzu ba zai iya fayacewa ba,
Sai dai abin mamaki wannan dan ciwo da ta ji ya ji hankalinsa ya yi mugun tashi, bai san lokacin da bakinsa ya buda ya dubi Alhinayett kan wada ya ji haushin tunda ya shigo gaisuwa daya kwal ta yi masa bata wani zo inda yake ba ta kara gaishe shi ba, ya ji bakinsa na fadin" mu kaita asibiti alhi
Alhinayett ta dube shi da mamaki, zata bashi amsa wayarsa ta kara daukan kuka,
Mikewa ya yi ya daga yana cusa hannunsa cikin sumar kansa ya amsa kiran,
Eh kawai yace kafin yake datse kiran ya juyo da dubansa wajensu inda ya sauko da gilas dinsa ya rufe jajayen idannuwansa wa.ina a yanzu ne suka dauki jan, labarin zuciyarsa ne ke isarwa gare su
Fitowa suka yi daga motar, ita da aminiyarta yar gidan gwomna matar minister,
Kowace ka duba sai ka kara duba domin tun daga suturun jikinsu zuwa kalar fatarsu da irin adon fuskarsu da takalman kafafuwansu da jakunkunnan hanayensu da irin kanshin da suke bazawa zaka gane manya ne ,
Fuska Walyn ta yatsina tana duban kawarta kafin suke bushewa da daria,
Kawar ta ce" wai ke da yarinyar yar gidan talakawa dangin talakawa ce har haka? Ke da Alhinayett din basu da komai a gari har kike tada hankalinki kar a je budurwar Oga ce?
Walyn ta yatsina fuska kafin take bushewa da daria ta ce" ba zaki gane ba, na rasa wani irin abu ne tsakaninsu, aman yau mu shiga mu keta mata rashin mutunci yar gidan taki zama!
Tafawa suka yi suka nufi yar kofar gidan da niyar shiga su shikawa Alhinayett rashin mutunci da ikirarin ta rasa wardugu sai dai yaransa (han)😬
Wayo azumi na matsowa, ni kam kamar nace da ku da sai mun hade in da ranmu bayan azumi🙁

6️⃣4️⃣
Zaune yake cikin talakawansa ana shari.a kan wani datijo da ya karbi kudin auren yarinyar wajensa sai da aure ya zo yace ai sai an linka kudin idan ba haka ba ba zai bayar ba,
Wannan rigimar suke ciki tunda safe inda ya umarci a je a kawo masa shedun da aka karbi kudin auren a gabansu ,
Daga inda yake zaune yana iya jiyo kukan Sultan, yaron wajen Gaishata , yaron akoy rigima, baya baci kuka ne da shi sosai wanda duda da yarinya mai tayata raino aman baiwar Allah sai ramewa take dan bata son tsotsa da kuma rigimar,
Gaban goshinsa ya dan dafe yana mai jin tausayinta a ransa, shi kam Allah ya jarabe shi da son yarinyar nan a ransa, hakan ya sa komai nata ke shigarsa ba tare da ya shirya ba.
Hangen Asadeek da rakumansa suke tun daga nesa abinka da waje a bude hayam ba a kasan rumfa suke ba, har ya matso kusa da su inda suka ga ai mutun ne saman rakumin,
Mikewa dogaran suka yi suna tsayar da shi tare da tambayarsa abinda ke tafe da shi
Asadeek baban dan kasuwa ne a garin Timiyar, ya kasance makiwaci, yana kiwon rakumansa yana shiga sahara da su, a kadan idan ya yi tafia sai ya kwashe wata shida sai dai abin mamaki wannan tafiar duka duka kwanansa uku da tafia abinka da karamin gari an san kowa an san me wane ke ciki, dan haka suka shiga mamakin ganninsa a irin wannan lokacin gashi kuma dauke da mutun
Asadeek ya janyo akalar Rakuminsa ya matso kusa da su,
Kamawa suka yi aka sauke mutumen dake saman rakumin, ba rawani a kansa wanda da sauri aka shiga neman rawani dan a nada masa domin buzu ba rawani tamkar tsirara yake jin kansa , tozarci ne a gare shi, ko alwallah zai yi yana yawan yi bayan idon mutane dan kar a ganshi ba rawani,
Da sauri suka luluba masa rawani , kafin suke maida hankalinsu kan Asadeek dake gurfane gaban sarkinsa ,
Duda da yawan cikinsu sun gane ko waye a wajen, aman basu nuna ganewar tasu ba gannin sarkin bai wani gane shi ba domin ya kyankyadare ya fita a hayacinsa tun ba.a je ko.ina ba,
Asadeek ya ce" Allah ja zamani, na je wajen rijiya dibarwa rakuma ruwa na ganshi kwonce gefen rijiyar a sume, da alama ruwan ya je dina sai dai karfinsa ya kare hakan ya sa ya fadi wajen ga zafin rana ga kishirwa ga iska ga idan yama ta yi sanyin sahara ya jigata ban san adadin kwanakin da ya dauka a haka ba ni dai na yi iya yina ya farfado inda ya hada wuta ya tatsi sabon nono na dan tafasa na bashi , hakan ne ya saka ya dan dawo hayacinsa aman gashinnan baya magana sai dai bina da ido da yake sai zazabin dake ta hawa yana sauka a jikinsa,
Da tausayi Sarki ke amsawa inda ya dubi mutumen da ya yakune tsofo sak ya ce" bawan Allah daga ina? Tafia ta riskeka yankin sahara? Kai din dan ina ne?
Da mamaki dogarai ke dan kara sada kansu dan sun gane sarki bai fa gane ko waye ba, sai dogari mai maimaici da ya daga murya ya maimaita maganar sarki,
A hankali ya dago kansa inda gaba daya jikinsa ke bari ya dubi sarki, wanda hakan da ya yi ya saka sarki zabura ya mike tsaye yana dubansa,
Hannunsa ya nuna ya ce" Algabiit? Daman kai ne? Daman kana yankin timiya ko dawowa ka yi?
Algabiit dake zaro idannuwa murya irin ta wanda ya sha wahala ya dago hannunsa zai nuna sarki da yatsarsa wani yaron dogarin ya saka mafici ya buge hannun yana fadin" hatara dai tsofo kar a nunawa mai garin timiya yatsa, kimtsa zamanka da lafazinka ga sarkin timiya
Sarki ya juyo ya yi masa wani kallo mai nuni da bai ji dadin duke hannun da aka yi ba, hakan ya sa suka kwashi masa kirari da ban hakuri,
Algabiit ya dan ja baya yana dubansu , baki na rawa ya ce" ina ka kai mini ita? Da yarana? Masu neman aurensu sun zo bakwa nan sun baza nemana kan idan ban biya ba sai dai su tafi da ni? Ina zasu kai ni? Me zasu yi mini? Ka fada mani inda suke ta bani yarana in basu ko zasu shafa mani lafia!
Sarki ya girgiza kansa yana dubansa, wato dai bai nutsu ba, alamun gajiyawar ba har cikin zuci ba,? Baya tunanin zai iya dogon bayanin fahimtar junna da wannan bawan Allah, arziki daya ya ci na haihuwar matarsa da ya yi, dan haka ya ce"
Baka da labarin ta dawo hayacinta? Tana garin Niamey gidan Kugunni ka je can ka dauko su,
Wata zabura ya yi yana dafe kirjinsa, yana duban sarki ya ce" Gukunni? Shikennan ka tona mani asiri, ka wulakanta ni, sai ka sakar mani y'ata, idan baka sakar mani y'ata ba sai na zame maka fitina a rayuwa da mulkin da kake takama da kwonciyar hankalin gidanka!
Dogarai du suka mike inda sarkin bulala ya zabura ya mike bulalar hannunsa ta shiga wulgawa tana karawa,
Sarki ya lumshe idannuwansa kafin yake budewa,
Fuska hade ya bada umarnin a shiga da Algabitt dakin sirri!
Jansa aka yi yana ihun a sake shi , aman ina ba zai iya kwatar kansa ba aka nufi dakin sirrin sarki da shi, wanda bai san wani dakin sirri a gidan ba sai yau, su kuwa suna zuwa tamkar wani kayan wanki suka jefar da shi suka fito abinsu suna baza rigunnansu, inda sarki ya ci gaba da shara.arsa kafin yake gamawa su tashi salar isha.i,
Bayan salar ne da ya shiga gida bai fito ba domin ya hada tarin gagawa na matarsa da sirikinsa da shi din kansa wanda zasu wakanar a dakin sirrinsa dake daf da shiga cikin gidan matansa. Wannan kennan
Niamey
Kanta na rawa , dan malolon mayafinta a hannunta ta afka gidan inda kawarta ke biye da ita,
Sai dai me? Kafin take idasa shiga ba da salama ba ta hango keyarsa don ya baiwa kofar shigowar baya ne,
Bata taba sannin ta iya gagawa irin wannan ba, domin a lokaci kankani har ta ja mayafinta ta rufa a kanta sai jansa take dan ya dan sauka hakannanma, ta shiga gyara daurin dankwalinta, sannan ta dan waiwayo dan fadawa kawarta Wardugu ne , sai dai da mamakinta ta fice tuni a gidan, wato ta yi baya, kennan ta gane ko waye,
Nutsuwa ta gayato karfi da yaji kafin take watsawa yayan buzayen harara ta kakaro murmushi ta yi salama tana karasawa gurin su, don zuwa lokacin Wardugun dai ne ke tsaye kikam cikin zafin ranar garin ya tsurawa wajen da randa take kamar hankalinsa na wajen shinkuwa idannuwansa kawai suke wajen,
Su Alhinayett kuwa suna zaune a tabarma inda Agaishat ta ja ta rufe wajen da ya bude ya ganni ta dauki wayarta dake ta ruri ta daga,
Ayya ce ke kiranta dan haka ta amsa murya sanyaye inda Ayya ta shiga tambayarta lafia? Dan muryarta ta yi mata kama da wace ta yi kuka,
Ajiyar zucia ta sauke ta ce" lafia kalau Ayanna,
Ayya ta ce" Madame Rukaya ce ta zo karbar excercice din da ta baki , ni kam ko kin yi? Kina dokin zuwa sadakin nan tun jiya?
Agaishat ta kwabe fuska ta ce" Ayya, na yi , yana cikin dakina kusan gado, Ayya ni fa ke zaki zo daukana ni dai
Ta karashe tana kyakyabe fuska irin na batatun yaran nan,
Ayya ta ce" kar na ji an min kuka, meye a su zuwa dauko ki? Da kin gama ki yi kirana zan zo na dauko ki yar autana,
Murmushi ta saki kafin su kashe wayar,
Alhinayett da ta gama amsa barkan Walyn ta dan zunguri Agaishat ta cuni mata baki ta ce" mai baci kawai,
Agaishat ta yi mata gwalo kafin take kokarin mikewa dan tunda ta juyo ta lura da uban hararar da ta samu daga wajen matar banban yaya,
Wardugu dake zaune shima saman kujerar kwal dake wajen a ransa ya ayyana ina kuma zata je?
Ta cikin gilashin yake kallon yanda da ta mike sai da ta daga hannayenta biyu ta harhada gashin kanta ta saka dan ribom dinta fari ta daure shi, sannan ta juya masu baya ta kwonce laylfayarta da kyar ta dan kakabeta a jikinta sannan ta samu ta nada kayanta har kanta,
Juyawa ta yi ta shiga dingisa kafarta ta koma wajen gashin naman dai inda Jidan dai take,
Kuma tana zuwa suka shiga kokowar sai ta karbe cokalin juyawar tana fadin ita ba dafa shayi bane aikinta,
Ina ba zai yiwu ba,
Shi ne abinda ya fada a fili, kafin yake mikeqa ya hade fuska ya ce" Ke, dawo ki zauna,
Tunda ya ce ke din, du ke din dake wajen ta dawo da hankalinta wajensa dan kar a je ita ke din yake nufi, domin ke dai lakanin suna ne da ake cewa mace halita wato Ke,
Inda hankalinsa ya fi kaiwa du suka kuma mayar da dubansa, wace qkiwa kallon itama ta ji uwa ta tsunduma a guje dan tsoron ihun da ya yi da kuma du kallon da suka yo mata,
Ajiye cokalin ta yi, zuwa lokacin du sun kawar da dubansu banda Walyn, Wardugu da Alhinayett,
Walyn mutuwar zaune ne ta yi, bata gane komai ba, aman irin ihun da ya yi kan ta zo ta zauna ya sakata itama tsura mata ido, a hankali ta maida dubanta kansa, ita din dai ya tsare da kallo har sai da ta karaso ta zauna kafin yake daukan babar wayarsa ya shiga dadanawa,
Zama ta yi tamkar mai kallon tv, don ta yi juyi ya fi a kirga tsakanin yannayin mijinta da shirun da wajen da ya yi, da yar hirar da su Alhinayett din ke yi fa yaren buzanci inda Alhinayett ta rage murya wajen fadin" ke da kika ji ciwo me ya kai ki tashi?
Agaishat ta ce" wannan har wani ciwo ne Alhinayett? Wajen da ko tashi bai yi Allah ya yi masa tsawa? Ina dan dingisawan nan ne dan zaman da na yi kafafuwana a tankwashe sun min tsami,
Alhinayett ta ce" Eyah, ai shi Wardugu bai gane ba,
Warsugu da suke zancen da yaren buzanci shima da yaren nasu ya ce" kar ki saki ki tashi, ki zauna ya huce, kin ji na fada maki,
Agaishat ta dube shi, yanda ya yi magana da yarenta abin sai ya mugun birgeta, murmushi ta saki kafin ta kawar da kanta ta tuna ashe fa yana jin Buzanci, Allah ya taimaketa ba wani abu ta fada ba da ya ji,
Alhinayett ta kai dubanta wajen yan matan gannin sun fitar da kayan zuba abincin sannan sun fara zuba shayin sai dai du suna tsoron zuwa wajen dan Wardugu da ya hade rai,
Walyn ta hadiye wani abu a zuciyarya kafin take kokarin cicibawa ta mike tana duban Wardugu ta ce" mu tafi Wardugu dare na yi kar dare ya yi,
Dubanta ya yi da kulawa, ko dan mutanen dake wajen baya saurin gwasaleta gaban mutane, dan haka ya dubeta da kyau kafin ya ce" ke da motarki daban tawa daban, kuma ba ke kadai bace? Ki je kawai gani nan zuwa,
Tsam ta yi tana bin yan matan da kallo, yanzu a cikin wannan zuga zugan yan matan zata tafi ta bar mijinta?
Sai dai ta makaro tunda ta mike idan tace zata zauna ko wani abin za.a samu matsala, dan haka ta yi masa murmushi ta juya ta fice ba tare da tace da su sai an jima ko su ci kansu ba, sai Alhinayett ce tace da ita ta gode,
Bata bata amsa ba ta fice tana ta tunani ta tarar da kawarta na shating da waya inda ta gyara zamanta ta tura masa sako kamar haka" namijin duniya , jarumin jarumai, na hangoka, ka kara sacen zuciya Warduguna, ina son ka koda kuwa kai baka so na,
Hango Walyn da ta yi ya saka ta yi gagawar gogewa ta fita a whatsupp din baki daya ta daidaita kanta daga tafia yabon mijin aminiyar nata da ta afka, ita fa ta fice da class din Walyn aman saboda ta samu shiga wajen Wardugu ya saka take yawo da ita a gari,
Motar ta bude ta shiga ta rufe da karfi kafin take juya dubanta wajen kofar shigan,
Dankwalin kan nata ta tuje ta yi tsai tana tunani kafin ta dubi kawar tata ta ce" kina tunanin Warduguna zai iya kula *Bakar Mace?*
Ido ta zaro ta ce" Bak'a kuma?
Walyn ta gyada kai tana dubanta,
Shewa ta yi kafin ta juya idannuwanta ta ce" ke, kina zaune da mijin naki baki san waye shi ba? Wardugu? Mutumen da a jarida ake bayannin kasashen da ya taka? Kin san kasashen da ya je mata tamkar su suka halici kansu? Ke dan ki zama mai sa.a a cikin mata shi ne zaki yi tunanin wai Wardugu zai dubi wata bak'ar mace? Me aka yi aka yi *Bak'a*? , me zai tayar da hankalinsa ya ja ra.ayinsa a bak'a ko yar gidan uban waye? Ke a bakar mace ina jin dadi? Bare harka? Me zai duba? Bakaken yan biyun ko bakin ogan?
Daria suka kwashe da ita suka tafa kafin walyn take sauke ajiyar zuciya, aman a zuciyarta ta yi waje ta ajiye irin shiga zuciyar da *Bak'ar* yarinyar ta yi a wajen uwar mijinta da mijin nata kansa, zata so sannin asalin yarinyar duda ta ga a inda aka daukota aman bata san meye dalilin daukotan ba!
Ba wardugu ya bar gidan ba sai wajen magariba, ba komai ba kuwa ya hana shi tafia sai dan kar ta tashi ta shiga wani aikin, yana zaune ya hade rai tamkar hadarin gabas komai sai dai a kawo mata rabonta har sai da ya tashi tafia ya saka ta yi kiran Ayyanta a gabansa kafin ya fice ya bar gidan,
Alhinayett kam tunda ya fada mata aure nan da wata guda jikinta ya yi sanyi, bai ce da ita komai ba sai dai ya dubeta ya yi mata murmushi , ita kuwa du tsoro ne ya gama kasheta a zaunen da take, abin ya zo mata da gagawa, ita tsoronta Allah tsoronta auren soja!
Dare ne ya tsala, a lokacin da bayi ke hutawa shi kam juyi yake saman makeken bed dinsa,
A bukace yake da ainahin matarsa, sai dai ya jima rabonsa da ya wani kai mata kansa, idan ta zo halas idan bata zo ba sai dai ya yi ta juyi abinsa har safiya ta yi,
Kamar daga sama ya fara jiyo kamshinta,
Lamo ya yi bai nuna zalama ba har ta karaso gareshi,
Jikinsa ta shige ta shiga kokarin sarafa shi,
Ya jima kafin yake bata amsa inda sai da suka hau sama ya mike dan saka abinda ya tsiro mata da shi tun bayan dawowarta gida, ya daina yarda ya zuba mata wani abinda ya fito daga jikinsa, danma tsaro yakan aiki da abinda zai tare masa tana jintana gani,
Mikewa ta yi tana dubansa jiki sanyaye ta ce" Wardugu, me yasa kake haka ne? Danme kake anfani da irin wannan abin bayan da matarka ta sunna kake tarawa?
Dubanta ya yi tsaf kafi yake turata baya ta fada saman bed din,
Kafin ya bi bayanta ya ce" kamar yanda kika kawo kanki a yau, haka zan yi yanda na ga yana gyara ni, ko ba komai hankalina kwonce ba sau ya rikide ya fara zama gudan jinina a markade shi ba kafin mai rikewa ta zo !
🤦♀ ba zan iya fadin sunnaye gatsai ba😭