"""Karfe 3;00pm na yammah motarsu ta saka kanta cikin kayataccen barikin na sojoji,wanda bariki ne,wanda ke kula da barikokin kaduna,kano,katsina zamfara da Sokoto Shine babban bariki na North a west wato *1 DIVISION NIGERIA ARMY KADUNA*...
Agaban wasu manyan gidaje daga chan yammah daga cikin barikin suka faka motarsu gidajene jere kamar estate saboda yawansu kuma dukkansu iri dayane komai da komai nasu illah nombobi ne kadai ya rabasu kowani gida dan madaidaicin flat ne mai kyau da tsari dauke da babban Falo da 3 bedroom kowanne da tiolet aciki sai babban kichen dake wajen falo,sai wajen Dining,daga waje Componud kowanne akwai parking space da dan Fili na motsa jiki ko Buga ball,tsakanin kowani apartment akwai dan tazara kadan bada yawa ba,kowani soja an makala masa sunansa da Nombarsa acikin babban kofar part dinshi,ina daga kai naga an saka da manyan baki cikin wani dan anani *CAPTAIN A.A TAMBARI BUZU* naga ansa kenan wannan gidan mallakinsa ne.
Suna gama Parking Tsirarrun Sojojin dake wayo aharabar wajen da hanzari suka kariso suna rige rigen bude musu mota,lokaci daya suna kame musu ko kallonsu Aliyu baiyi ba,jabir ne,ya daga musu hannu bayan ya nuna musu bayan motar inda kayansu yake,da hanzari suka bude suka kwashi jakukkunansu da hannu Aliyu ya nuna su,kawai sai naga sun rabu biyu,wasu sun nufi Apartment din Aliyu,wasu kuma Sun nufi apartment din dake kusa dana Aliyu dauke da jakar Jabir alamun nan ne barayinsa,Aliyu bayansu yabi duka hannuwansa cikin aljuhun wondonsa yana wata tafiyan takama bayanshi jabir yabi jin alamun tafiya yasa Aliyu ya waigo yana bin Jabir da wani Suprise look,shiko jabir gyara tsayuwa yayi yana fadin"Muje ko.."Akaikaice Aliyu yanuna shi da hannu yana fadin"to go where? dallah mallam kama gabanka,nan din gidanka ne.."? Wata dariya jabir yayi yana fadin"Nifa taimakonka zanyi,naga baka da lafiya,kana cikin damuwa kana bukatar wani akusa dakai..."Rike baki Aliyu yayi yana kallon jabir kafin yadan ware idonsa yana fadin"Don mai garinku nina fadamaka ina cikin damuwa? comon mallam kakama gabanki,yasin karka shigomin gida Ngd da Taimakon..",yafada yana Wucesa da sauri yar dariya jabir yayi kafin ya juya yana fadin"Kai kasani ga damuwa Aranka,ammh tsinannan iskancinka yasa kana wani basarwa chan ta matse maka gara kawai.."
"Aliyu bai waigo ba,yace"Ta matse maka dai azariyan wandonka banza Dan saka ido kawai.."Yafada daidai lokacin daya dauko dan makulli daga aljihun wandonsa ya zura akofar yana bude kofar falon,Sojan dake biye dashi daga bakin kofa ya tsaidashi ya karbi jakarsa saramai, yayi ammh Aliyu ko daga kai baiyi ba,sai ma shigewa ciki dayayi ya banko kofa,Sojan bai damu,domin duk wani Soja dake barikin yasan miskilancin Aliyu gadanga,shiyasa babu wanda ma ya damu dashi...
Yana Shiga falon bai tsaya ba,ya isa ga bedroom din,jefa jakarsa yayi kan gadon daya mamaye dakin yayi,kafin yafara tube takalmin kafansa,zuwa duka kayan jikinsa,boxers kadai yabari ya fada bedroom din,bai dade ba ya fito kugunsa daure da wani karamin Towel,yana Fitowa wayarsa tafara neman agaji ta wutsiyar ido ya hango mai kira *Swt Ni"ima* yagani wani dogon tsaki yaja yanajin wani daci aransa,wayar bata gama Ringing ba,ya yanke kiran bayan ya shiga ya sakata cikin blacklist,dama kawarta tun safe ya sakata,saboda bayason Takura sam,Shi yanzuma duk Abunda zai Tunamai da wata Ni"ima ma haushi kamasa yake,Da karamin Towel din ya fice zuwa wajen compound din Flask din da goggo tabasu da kulan Fanken ya duba bai gani ba,Rike kugu yayi yana hangen Apartment din Jabir saboda yasan shi ya dauka,kai gayen nan Dan mtsala ne yanzu yajamai sai ya dafa indomie Tunda bazai sake fita ba,ya dade tsaye yana Tunanin wulakancin dazaima gayen chan kafin yakoma ciki,wani guntun wando ya sanya 3quater ko riga bai dashi Ya fada katon kichen din Gas ya kunna ya dora wata karamar Tukunya,ya zuba Ruwa,lokaci daya yabude wani drower ya dauko indomie cherry guda biyu ya farka ya saka,bai fita daga kichen din ba,saima jawo wani Stool da yayi ya zauna yana ajiyar zuciya kamar wanda yayi wani auki,yunwa yakeji bai wani tsaya indomie ta tsotseba,ya sauketa da ruwa ruwa ya juyeta cikin Filet ya bude fridge ya dauko lemon cway ya fito,bisa daya daga cikin kujerun falon ya yada zangon yana daukan Remot bayan ya kunnah Talabijin din,kallon falon yake,yana ganin yadda yayi kura,karamin tsaki yaja aransa yana fadin"yasin ba sharan da zanyi am tired.."Yafada kamar wanda akasashi Dole,hakanan ya shiga Tura indomie har ya kusa cinyewa kafin ya ture filet din ya mike,ya karishe shanye Cway din,bedroom yakoma ya fada bisa gado,yana damke hannusa bisa kirji bayan ya kulle idanunsa,yashiga Tunanin Abunda ya faru daga jiya zuwa shekaranjiya,yana ta mamakin kansa,Ahaka barci ya kwashesa...
***********
_Gombe_
Tun karfe 4:00Am na Asuba Azeema ke tashi sakamakon tasan yau monday Sunada mkranta,kuma matukar bata tsaya tagama duka aiyukanta ba inna bazata taba barinta tatafi mkrantanba,sai ta kammallah komai koda zataje amakare ne,Shiyasa take tashi da wuri tagama duk Abunda takeyi kafin lokaci ya kuremata Tunda Azeeza dama yar gatace bata changal agidan,sai dai taci ta kwanta da Rashin kunya kadai ta iya.
Kafin 7:49am ta kammallah duk Abunda zatayi tayi wanka ta sanya Riga da wando da hijabi kalan Uniform din mkrantan,Madafi takoma ta dibe Tuwonta tazo tazauna tanaci,Lokaci bayan lokaci tana kallon Azeeza take kwance tana jin shesshekan datake alamar kuka takeyi,Gum Azeema tayi Domin tun dazu take mata mgana tatashi tayi sallar tayi Shirin mkranta ammh Azeeza tamata banza,ganin bazata iya barinta haka ba yasa bayan tagama cin Dumamen Tuwonta tamaida kwanon madafi tazo ta wanke hannu takoma dakin tana fadin"Azeeza keko wani irin barci ne,haka takwas fa takusa ammh baki tashi ba,ni harna Shirya zan Wuce mkranta.."Azafafe Azeeza ta tadago kanta daga kwance idanunta sunyi jawur Fuskarta ta kumbura Saboda kuka tace"Wai miye Ruwanki da Rayuwatace Adda Azeema? kin takuramin kin isheni,baza"ayi sallar ba,in kike da aljannar inna tashi shiga ki tare ni karna samu shiga.."Tafada tana mata wani banzan kallo,Azeema baya taja tana daukan jakarta wacce ta kasance ta hannu ne tana fadin"Allah ya baki hakuri...",Tafada cikin sanyin murya kafin ta dumfari kofar Fita,karaf inna Ramatu ta dago labulen dakin tana fadin"Kai Ni wannan bala"in ya isheni wlh,ke dai in da diyar wani Shehi ne,da anga kinibibi,to sai kuma kikayi dace ke diyar mallam lawal ne mai Saida kayan gwari,ina Ruwanki da yata,bakiga bata da lafiya bq ne,in tatashi Uwarki zatayi miki.."Tafada tana zabgamata harara,dukar dakai Azeema tayi kafin tadan Rankwafa tana fadin"Ina kwana inna..."Ko kallonta inna batayi ba,saima karisawa datayi cikin dakin tana fadin"Azeeza tashi,ya jikin ki? take fada tana tarairayota jikinta,Ko kallonsu Azeema batayi ba,ta fice kofar dakin inna ta tsaya tana sallama,mallam lawal dake ciki ya amsa bayan yabata izinin Shigowa,Shiga tayi bayan tacire sandal dinta mallam lawal dake kan gadon mai Rumfa ya sauko daidai lokacin da Azeema ta duka tana fadin"Ina kwana baba.."Ya amsa yana fadin"Lafiya lau diyar albarka,har anyi Shirin mkrantar..? ta amsa da cewa "Eh baba.."aljihunsa ya laluba ya fito da Naira hamsin ya mikamata yana fadin"Kin mkara ki hau mashi ko Keken napep,saura ko ruwa kyasha amkranta.."Noke hannu tayi tana mikewa tace"a"a Baba kabarshi Ban mkraba yanzu zan isa insha Allahu,ruwa kuma akwai fa famfo baba Amkrantar.."Tafada tana juya,Sunanta yakira ta waigo tana amswa mikata yayi yana fadin"Karbi diyar albarka bansanki da gaddama ba.."Hannu ta sanya zata karba taji an warje kudin bayan an Dunguremata kai,Inna Ramatu ne tsaye take kallonsu tana hararansu kan tace"ehe sannu mai diya,ammh yanzu kagama cemin baka da kudi,ammh dayake kan wannan banzar yarinyar ne,ai ka ciro ka bata,kuma dakake kokarin bata kudin ka manta kayi Auren jari da ita,Inashi mijin nata da bai bata ba.."Tafada cikin gatsine,Kallonta mallam lawal yayi yana fadin"Wai ke Ramatu meke damunki ne,koda tana da miji ni ba Mahaifinta bane,bata da hakki akaina ne? "Harzukomai tayi Tana fadin"Bata da hakkin akanka,don yanzu ba"a karkashin ikonka take ba,Azeeza ce ke karkashinka yanzu sonkai ne yamaka yawa shiyaasa baka ganin haka,uhm ayi mugani indai mune muna zaune zamu gani,kowa yana gudun hada zuru"a da bara gurbi ammh kai ka Rumguma yaron da"akace Rikakken Dan"iskane bai da aiki sai tara karuwai Achan kaduna.."Salati mallam ya saka yana fadin"Ramatu ina kika samu wannan lbrin kuma,oh ni lawal,yanzu baki Tsoron Allah yayi miki hisabi akan kazafin dakikayi masa.."Babu kazafi illah gaskiya in ba iskanci ba,ubansa yakeyi achan sai yadau lokaci bai zo gida ba,..."Azeema batagama ji ba,ta fice tana kwallah ko waiwaye batayi ba,ta fice daga gidan zuciyarta na kuna,Hanyarta ta dumfara kawai tana tafe tana lissafin zuci,Kamar ta biya gidan Baba ade Ammh kuma sai taga ta mkra sai tace bari sai ta dawo ta biya,Duk saurinta sai da Seniors suka tsaida ta tayi piciking kafin ta isa ajinsu duk wanda yaga Fuskarta sai ya Fahimci tana cikin damuwa kawai boyewa takeyi.
#Comment,share,vote....#
#Janafty...#
*ALIYU GADANGA..!*
_(The Story of Young Soldier man)_
*Wattpad:Janafnancy12*
_Mallakar:Janafty💖_
*DEDICATED TO MY MOMMAH...HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*
_Special gift to my Real Dota RAHMA😘Ladingo yar mutan Niger_
*Intelligent Writers Association*✏
_*A big congratulation to u my Sisi of life AISHA ALTO..4Completing ur Special,Amarzing,Fantactis,Adorable and Educated Novel...GIRMAN KAI(Rawanin Tsiya) d Whole book is dedicated to me,JANAFTY...kai am out of Contol fa,don wannnan babbar kyautace wanda bazan taba mantawa da ita ba,Ina mika miki Hannun Jinjina 👍Sisinah domin kin baje dukkan basiranki da Fikiranki wajen Tsara wannan Novel din,hakika kin Fadarkar damu bayan Tarin nishadi da masu karatu sukayi, kin kuma samu nasaran isar da sakonki cikin Hanya mai Sauki,ke Tadambance awajena,Hakika salonki na burgeni kuma yana Tafiya dani,ina rokon Allah yabaki ladan Fadakardamu dakikayi bayan ya duba kuran kuran dakikayi ya yafemiki Duniya da lahira..Kaunarki Araina bata da iyaka..Bazan gaji da fada ba,bakuma zanji kunyan maimaitawa ba Nagode sosai bisa karamcinki gareni My Sisi of life gabadaya shafin na yau mallakinki ne,na baki shi halak malak..Kisani ki kara sani AISHA ALTO KINA BURGENI*_😘
*NOT EDITED*💥
*Chapter 9*
"""Sati uku kenan da Tafiyar Aliyu gadanga ammh baizo gida ba,sai dai waya da sukeyi Shida goggo,ammh ba kullum ba saboda Tunda ya koma yazama yana keeping kansa busy baya zama sosai,akwai wasu bataliyan Sojoji da yake koyama Training bai samun lokacin kansa ma,balle na Tunani,ya tattara komai ya watsar da zarar Tunanin Abunda ya faru ya fadomai zaiyi Saurin Kaudashi ko Afuska baya nuna alama,hatta jabir duk nacinsa,da son gulmansa,sai da ya hakura,shiko Haisam yadai kirasa awaya sun yimagana,kuma duk Akan yayi hakuri da Abunda Allah ya kaddara maine,to ya zaiyi?ai baya da tacewa shikam Tunda haka Allah yayi dashi.
Ni"ima kuwa sai da ta shafe Sati a asibiti kafin asallameta tadawo gida,Jikin nata da sauki ammh kullum kwana take kuka saboda Rashin Aliyu atare da ita,Maminta ne da kawarta muneera suke kokarin kwantar mata hankali,ammh ina bata ji bata gani,game da Captain dinta zata iya komai,kawai tana kokarin nuna komai ya wuce ne saboda damuwar Maminta da Abbanta da kuma kawarta muneera,ammh taci alwashin bazata bari captain dinta ya subuce mata ba,zataje koda chan kadunan taasan in ya ganta bazai iya kauda ido akanta ba,dole zai tsausayamata su dawo su kara Shirya Auren nasu akaro na biyu,duk da ta san zata Fuskanci kalubale,har zuwa lokacin Ni"ima bata San cewa Captain dinta yayi Aure ba,shiyasa take ganin shawo kanshi mai sauki ne.
Bangaren Azeema kuwa babu Abunda ya chanza na dangane da Rayuwarta,inna da Azeeza sungama yawo da mganar a anguwa suna fadin Babanta yaga kwadayi ya auramata mara asali,kuma dan" iska,har a mkrantansu saida Azeeza taje da lbrin sai ya zamana Azeema tazama Abun nune da zunde duk sai taji duniyar tayimata kunci da zafi,ko kawayenta na anguwa haka suke kallonta suna fadin kwadayi zai kasheta ita da ubanta,Azeeza na fadn mganganun banza akanta ana mata dariya,mussaman in suka hadu a bohol taje debo Ruwa da kuka take dawowa,wajen Babanta kadai take samun sauki,sai ko wajen Baba Ade kakarta sai wajen uwa gareta goggo wanda tagama guje gujenta ta hakura taje gidan goggon wacce takamata ta Rumgumeta tana mata tsiya,ita goggo ta fadamata cewa ita ba"a Suruka take kallonta ba,a mtsayin Ya take kallonta saboda haka itama Tadauketa amtsayin uwace wacce ta haifi Aliyu da Azeema,dole Azeema ta saki jikinta duk da Nauyin da Goggo ke mata bata da yadda zatayi saboda goggo babu ruwanta hira take da ita kamar ba matar Danta ba,Tuni Azeema ta saki jikinta suka cigaba da yadda suke da goggon kamar da,agidan take Wuni sai yammah take komawa wannan bakin gida,Inna ko babu Abunda ta fasa na muzgunama Azeema sai ma Abunda yayi gaba,yanzu Azeeza Abunta yayi kamari ko mgana Azeema tayi mata tsab zata saka hannu ta shareta da mari bata da bakinn mgana don sai inna ta kusa kasheta lokacinta baiyi ba,shiyasa ko Baba bata bari yaji saboda duk hukuncin dayayima Azeeza akanta inna zata saukeshi shiyasa take hakuri tasha kukanta ta sharbe hawayenta bata da mai lallashinta,duk ta rame ta kanjame kamar ba ita ba,tayi baki,ga wasu kananan kuraje sun Fito mata in ka kalleta bazakayi Tunanin yarinyace yar shekara 20 ba,sai kayi zaton ta haurama talatin30 baya saboda wahalar rayuwa don ma goggo na tsaye kanta,Abun ne ya ishi goggo dole ta matsama Aliyu yazo gida tana son ganinshi don tanaso ya tsamo Azeema daga wannan kangin bautar datake ciki Tunda dai yanzu Shike da iko da ita,kuma tasan duk iskancin inna Ramatu tana shakar captain din.
*************
Sai da Aliyu gadanga ya shafe sati Shida baizo gida ba satin ma sai da ya biya gidan kawu bala suka gaisa da Ummah kawu ma bayanan ya tafi Abuja Haisam ma bayanan yana kano wajen aiki,Shiyasa bai dade ba daganan ya kamo hanyar Gombe zuciyarsa duk babu dadi saboda yaasan kiran gaggon bai Wuce mganar sokuwar yarinyarnan ba,wanda gabadaya baya son Tuna komai,Shidai burinsa da Addu"asa bai Wuce Allah ya bayyana mishi Asalin mahaifinsa ba ko zuciyarsa zata daina wannan Nauyin data dade tana fama dashi.
Da misalin karfe 2:30pm ya Iso kofar gidan nasu cikin lafiyayyayiyar motarsa din nan 4matic,kofar gidan ya faka motar,bai shiga da ita garejin ba nan ya barta ya bude booth ya shiga jiidan Tsaraban da yayima goggo yara na Jida suna shiga dashi cikin gidan goggo,wacce ke tsakar gida tana jin Radion ta taga Shigowar yara ko bata tambaya ba,Tunda taji dirin mota ranta ya bata gadanga ne,jikinta na Rawa ta mike har zaninta na neman Faduwa ta nufi hanyar waje Sukaci karo da gadanga ya taho jikinsa sanye da Riga da wando Rigar fara ce ammh wandon Nevy blue ce,sai takalmansa rufaffu ne, kansa babu hula gashinsa yasha gyara yana kyalli,Rumgumosa Goggo tayi tana fadin"Oyoyo gadanga..Sannu da zuwa Gadanga kusar yaki,ga soja mazan fama Ah..Soja na Azeema..."Goggo take fada tana Rumgume da Aliyun..
Dariya yake yana Rike da goggon yake fadin"Oyoyo goggo ta....Nayi kewarki sosai mamata.."Dunguremasa kai tayi tana fadin"bakayi kewata ba gadanga Tunda sai da nayi ta magiya kafin ka dawo.."Tafada tana Amsan jakar kayansa dake hannunsa,dariya yayi kafin ya saka hannu ya zagayo da hannunsa kan kafadanta kamar wasu kawaye suka jera zuwa cikin gida yana fadin"Haba goggo..Kefa kika haifi gadanga..Kinfi kowa saninshi ko zan manta da kowa wlh banda Uwar Ali gadanga.."Yafada yana wani lamgwabemata nishadi ya kashe goggo tana dariya,ahaka suka karisa daki,tana mai maraba,saboda murna ma goggo bata bashi Ruwa ba,saida tagama kawomai abinci kafin ta tuna,dariya ya dinga mata yana jin dadin zama da goggo sosai haka suka zauna sukaci abinci tare suna hira da dariya in ka kallesu bazakace mahaifiyarsa bace sai ka dauka Kaninta ne saboda yadda take yar daidai da ita.
Azeema data dawo daga kai nikan Alalan da inna ta Aiketa tunda tadawo mkranta ta bata nikan ko Uniform bata cire ba,tatafi kai nikn,,gashi ta tarar da layi sai da tadade bata dawo ba,tana ta sauri ta iso kofar gidan goggo gabanta ne ya fadi dataci karo da Motar yaya captain bakinta har rawa yake tana karkarwa,tana leken gidan ta yi Saurin Wucewa jikinta na rawa saboda tsoro,koda da takaima Inna nikan sai da ta mareta tace ta dade ta tsaya iskancinta bata dawo da Wuri ba,ita duk wannan bai dameta ba,duk fargaban Dawowar yaya captain ya dameta ammh ta godema Allah dayasa taga motarsa da sai ta shiga su hadu da juna,rike baki tayi tana Tuna karonsu dashi,kayan mkranta kawai ta cire tazo ta hau sharan gida,wanke wanke ta hada,ta duba rijiya babu wani Ruwan kirki,tunda rijiyar taja baya sosai babu Ruwa shiyasa take wahalam Aiki yanzu Tunda ga debo Ruwa ya karu,karamin hijabinta ta sanya Domin Riga da sikat ne ajikinta kayan ma sun mata kadan domin sun matseta,rashin wadatattcen kayan ne,yasa take sakasu har yanzu,botikai uku ta diba ta fice zuwa bohol din dake gaban gidan goggo da kadan,sai da ta leka ta tabbatar da kofar gidan goggon babu kowa kana ta fito ta wuce tana waigo koda taje wajen layi yayi yawa sosai,dayake anfara mtsalan Ruwa,idonta ne yakawo Ruwa data tuna da Abunda inna tace,tace in tawuce minti goma bata dawo ba,sai na lahira ya fita jin dadi,jikinta na Rawa ta shiga rokon yan matan dake wajen su bata da diba ko botiki daya ne,kallonta sukayi shekeke kafin su sheke da dadariya suna fadin",Ahhyyyye...Sannu isassa...Kije sojan da kwadayi yakaiki aurensa yazo ya kwatan miki,an dai ji kunya mutum yazama matar aure,ammh kullum ko karen layi bai kaishi Arha ba.."Kallonsu Azeema takeyi hawaye na zubomata domin dukkansu kannen bayanta ne,kawayen Azeeza ne,batace komai ba,sai takoma gefe tana sharan hawaye tana jiran layi ya kawo kanta ta diba.
Inna Ramatu taga Azeema ta dade bata dawo ba ga kullin Alala zai kumbura bata dawo ba,Ranta ya baci ta kwalama Azeeza kira,wacce ke daki tana kwance tana hutawa,tana kuma saka yarda zata zama mallakin Captain taji kiran innar,tana fitowa inna tace"Taje wajen bohol ta kirawomata Azeema tace in bazata kawo mata Ruwan bane ta sani.."Tura baki Azeeza tahauyi don ita ta tsani aike,Dakyar ta shiga daki ta sawo hijabinta ta fice afusace,Bagazan bagazan take tafiya Ranta bace Shikuma yana kokarin Fitowa daga motarsa ya bude gareji zai sakata yaga Wucewar Azeeza kamar wata jaka,baima ganeta ba,yadda yaga ta wucene ya bita da kallo,don shi ya zatama inna Ramatun ce,tsaki yaja kafin ya Rufo motar yana kokarin komawa cikin gida kamar an ce ya daga kai sai ya hangi Azeezar tsaye gaban Azeema domin Tazaran kadan ne da gidan goggon,yana hange bohol din da duk Abunda yake faruwa.
Tana zuwa batayi watawata ba ta ture Azeema datayi nisa cikin Tunani, sai da takusa faduwa tayi Saurin dafa bango,dagowa Azeema tayi tana fadin"Haba Azeeza baki da hankali ne,kikamin wannan bangazan..",Wani kallo Azeezar ta wurgamata kan tace"Anyi miki Din,ba inna ta aikeki ba,tun dazu kinzo kin tsaya kina bin Mutane da kallo,kamar wata sakarya.."Tafada da alamar raini,gabadaya wajen suka kecemata da dariya,Azeema ta karisa wajen kawayenta suka tafa suna dariya suna nuna Azeema dake hawaye,wani saurayi ne,dan kasan layinsu ne,sunansu sulaiman Ya tsawatar musu ammh sai suka buge damai Rashin kunya,Yana ganin haka dama layi yazo kanshi botikin daya diba ya mikama Azeemar yana fadin"Karbi ki Tafi dashi gida,ni zan jira sai na kara diba.."Azeema da hawaye ya cikamata ido ta kalleshi tana fadin'Nagode.."Tafada Hawaye suna kwararomata,Daukan Ruwan tayi ta juye adaya botikin nata ta Cicciba zata dora akanta,sai ta kaasa sai Sulaimam din yasa hannu ya taimakamata ya dora mata ammh duk da haka sai da Ruwan ya jikata,har hijabin jikinta ya lafe bisa jikinta,albarkatun kirjinta duk sun bayyana waje,hawaye na zuba ajikinta ta dago tana fadin"Nagode sosai.."mirmishi yayi mata bai ce komai ba,tazo zata wuce su Azeeza suka kwashe da dariya suna nunata sai ta zargu tafara hardewa ganin haka yasa Azeeza tahowa gabanta batai wata wata ba ta sanya hannu ta tura Azeema baya ji kake chambal...!Azeema ta fadi cikin katuwar kwatamin kwatan dake wajen botikin Ruwan ya watse bisa jikinta itakuma tayi tsamo tsamo cikim kwata,gabadaya wajen ya dau ihu,Shiko sulaiman baki ya rike cike da mamaki ganin tsabar mugunta wajen Azeeza.
Takaichi Tare da bakinciki sukayima Azeema dirar makiya tana zaune cikin kwata take bin Azeeza da kallo Tana zubar hawaye,itako Azeza banda nunata tana dariya ba Abunda takeyi tana fadin"Tabdijam lallema Adda Azeema kina nufin Ruwan botikin wannan kazamin zaki kaima na gida,wlh da sake kima sake Tunani.."Tafada tana Wurgama sulaiman din wani kallo dama ta tsaneshi saboda sam ko a anguwar baya daukan Raini baya sakarmata Fuska sam.
Yanajin Abunda tace ya nufeta yana fadin"Lalle yarinyar nan baki da kunya yanzu zan koya miki hankali..."Ya fada yana karisowa,kusa da ita baiyi wata wata ba ya daga hannu zai mareta sai yaji ance daga baya cikin wata kakkausan murya..'Hey Leave her...'"Sukaji an fada daga bayansu gabadayansu suka waiga suna kallon mai mgana.
Dukkansu sai da suka Razana hadda Azeema dake zaune cikin kwata tana kuka,yana Tsaye hannayensa gabadaya ya zuba su cikin Aljihun wandonsa,Fuskarasa Murtuke babu Annuri ko kadan har wani ja tayi saboda bacin rai,Azeza da kawayenta yake bi da wani wulakantattacen kallo,wanda Tuni suka Tsorace kamar su saki Fitsari awando ganin yadda yake kallonsu Jiyoyin kansa na mikewa saboda bacin rai,Kallonsa ya maida kan Azeema dake zaune cikin kwata tana kuka Jikinta duk ya baci ga Shi hijabinta duk ya manne mata ajiki,baisan dalili ba,sai yaji wani mugun Haushi ya tokaresa kamar ya bita cikin kwatan ya ci ubanta Tunda ta zama solobiyo,Sulaiman kuwa yana ganin captain ya koma gefe yana dariyan mugunta domin yasan daga yanayin kallon dayake musu yau din nan sai sun gane basu da wayau..
Taku yafarayi zuwa garesu yana wani kame idonsa guda daya na salon mugunta,Tuni suka tsorata suka fara ja da baya,Azeema ko jikinta na rawa ta mike saboda atunaninta wajenta zaizo ya fara ta kanta sai ta ga yayi Pointing dinsu Azeeza yana fadin1,2,3,4,5,6....All af u come here...',Yafada cikin gadara,Ai da wani tsoro suka fara kallon junansu tsawa ya daka musu yana fadin"don't Force me to Mention my Statement..All of u will be in Tourble i swear..",Yafada yana wani buga kafansa akasa,wanda saida Mutanen wajen suka Razana.
_Wowow...Ran Maza fa ya baci..Su Azeeza kun Shiga Tarama ba Uku ba,do da Alamu Fushin sojan zai sauka bisa kanku,kilama Harda horan Sojoji zai baku😂Wayyo,Allah ya kwaceku maganinku kenan,Fans ya kuka gani kuna goyan bayan Captain yaci kaniyar su Azeeza?..Cike Tagging dinki da kayatattacen Sharhi ta hakan ne kadai zan gane kuna biye dani_
*Comment,share and vote...*
*#Janafty...#*
*ALIYU GADANGA..!*
_(The Story of Young Soldier man)_
*Wattpad:Janafnancy12*
_Mallakar:Janafty💖_
*DEDICATED TO MY MOMMAH...HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*
_Special gift to my Real Dota RAHMA😘Ladingo yar mutan Niger_
*Intelligent Writers Association*✏
*Chapter 10*
""Jikinsu na rawa suka fara takowa zuwa gabansa,kowacce tanaji kamar ta saki Fitsari awando saboda tsoro da Razana,Kafin su kariso ya sunkuya akasa ya sanya hannu ya dauko wata sanda baya yakoma daga chan wajen inda ya faka motarsa ya shiga jan Dogon layi,yana gama ja,cikin wani Fusata yazo ya wucesu kamar kiftawa da bismillah ya isa chan nesa da bohol din ma nan yaja wani dogon layi,Ko kallonsu bai yi ba,daga chan bangaren ya nunasu da hannu yana fadin"Ku yan iska ko? marasa mutumci,dama kune marasa tarbiyan anguwan ko? ok To iskancinku yazo karshe daga yau oya all of u ku fara frog jump daga inda layin chan yafara zuwa inda ya kare,kuma 50 zakuyi each zuwa da dawowa to be counting one ne..."Yafada cikin gadara da isa.
Gabadayansu suka kalli juna ganin zasu batamai lokaci yasa ya fara taku zuwa garesa ai da gudu suka isa ga layin kowacce ta duka tafara,daga nesa yace"duk wacce batayi da kyau ba,ko ta gama sai ta sake so is better da ki zage kiyi yadda nace..."Yafada yana harde hannuwansa akirji Sulaiman dake gefe yana kunshe dariya yace"Yallabai zanyi musu couting.",Da kai ya amsamai yana cije lebe kafin yace"ka sa ido akansu..Duk wacce bata yi dakyau ba juz ka waremin ita yau zasu ci ubansu ne..",Yar dariya Sulaiman yayi yana fadin"Baka da mtsala yallabai,ya fada yana kallonsu yana fadin"Toh maza kuyi da jiki...one,two...three,wlh kika bari aka barki abaya zan tsayar dake.."Yafada yana dariya jin haka yasa suka zage sai yi suke kafin kace kwabo sun Fita hayyacinsu ko goma basuyi ba,ammh haka suke kuka da majina,Tuni layin ya cika da mutane anata dariya wasu kuma na murnan Abunda ke faruwa don daman kowa yasansu Azeeza alayin basu da kunya ko kadan,wasu sai fadi suke gwara hakan,kila daga yanzu sayi hankali.
Azeema na gefe tana barin jiki Tana kallonsu Azeeza yadda suke kuka harda majina,Dasun bude baki zasu yi mgana sai captain yace +anoder 50 din,dole sukayi Shuru da bakinsu domin Wannan wahala tayi kama da wahalan gidan yari ne,Shiko yana gefe ya harde hannuwa bisa kirji yana kallonsu yana dan murmusawa,Da kallo yabi Azeema yadda tayi wani kalan Tsausayi nufota yayi sai ta hau ja da baya,tana ganin ya kariso sai ta duka ta kama kunni tana fadin"Don Allah kayi hakuri nima zanyi..Zanyi.."Take fada tana kokarin Fara tsallan kwado tsawa ya dakamata yana fadin"Stand..."mikewa tayi jikinta na bari,Tsaki yaja kafin ya juya yana fadin"Ina abubuwan dakika zo dasu diban Ruwa.."Bakinta na rawa ta nunamai botikan guda biyu,don dayan kam ya fashe,bai kara kallonta ba ya isa garesu,da hanzari ya isa ga bohol din yasa hannu ya ture layin dake kai ya aza botikinta Yasa dayan laullausan hannunsa yafara buga bohol din,Jikin Azeema na rawa take binshi da kallo yana zubamata ruwa bai dauke hannunsa ba,sai da ya cika duka botikan guda biyu,da hannu biyu ya daukesu atare,ya nufota cike da mamaki mutane ke binsa da kallo yanayin komai cikin Jarumta da takama,sai da yazo gabda da ita kafin yace"Wuce muje bush girl kawai..."Yafada yana huci jikinta na rawa ta mika hannu tana fadin"ba..Bari na dauka.."Wani dirty look ya watsamata kafin yace"Leave dis place now..."Yafada a tsawace,da hanzari tashiga gaba tana bin su Azeeza da kallo wadanda sukayi chanza kammanin saboda wahala ga Sulaiman Shiko ba mutumci da gayyah sai yace basuyi daidai ba,sunyi yafi ashirin ammh yace biyar ne,mai kyau sauran sai sun sake,Bayanta yake bi dauke da ruwa,Ransa na masa kuna banda An raina masa wayau wai wanna ce matar da"aka Aura masa,kullum gantali alayi kamar wata karya,Saboda cin mutumci harda Debo Ruwa saboda Rainin wayau,Kallonta yake tana tafiya wani takaici ya makarosa ji yake kamar ya shakota ya kifkifamata mari saboda haushi,Suna zuwa kofar gidansu taja ta tsaya tana so ta kalleshi ammh tsoro yahanata,Kanta na kasa tace'Don..Allah ka..kayi hakuri ka..."Bata gama Rufe baki taga ya wuceta ya shige gidan dauke da Ruwan baki ta rike tana bin bayansa da kallo,kafin jikinta asanyaye tabi bayansa.
Inna Ramatu na zaune bisa kujeran Tsugunno atsakar gida tanata bala"i ita kadai ba Azeemar babu Azeezar ba wanda ya dawo,kawai sai ganin tayi Tsulum Mutum ya shigo gidan bai dire ko"ina ba sai agabanta ya ijiyemata botikan Ruwa ta dago ta kallonsa cike da mamaki,kafin ta mike tana zare,ido lokacin idonta ya sauka kan Azeema data shigo ta rabe gefe tana hawaye,Cikin wani masifa inna Ramatu ke fadin"Kai mallam lafiyanka kuwa zaka shigo gidan matan Aure babu Neman izini.."Tafada tana binsa da harara,domin ta ganeshi yaron nan ne mara kunya,don tanajin Haushin Rashin gaishetan da bayayi.
Ko kallonta baiyi ba,saima juyawa dayayi zai Fice yana kallon Azeema data rabe gefe tana zuban kwallah,kallonta yayi dakyau lokaci daya dayaji Tsausayinta ya tsirgamai saboda koda yaushe cikin kuka take kuma duk ganin da zai mata cikin wahala ne,Ransa ne yayi zafi Shiyasa ya waiga yana fadin"plz Inna kada Akara aikan Azeema zuwa dibo Ruwa infact duk wani aike adaina aikenta,Cuz yanzu ba da bane,tana da hukunci da Nauyin igiya uku akanta,in don wanda zai dinga debo miki Ruwa ne babu mtsala zan neman miki ammh plz and plz kada in kara ganin Azeema awaje matukar ba mkranta zata ba..."Yafada idonsa kyam a na inna Ramatu wacce ta Rike baki saboda mamaki.
Inna Ramatu hannunta abaki Tana fadin"Eh lalle sannu Lawali..Toh baza"a daina aikenta ba din,amtsayinka nawane zaka zo kana bani Umarni..."dan mirmishi yayi kafin ya tako zuwa gabanta yace"Inna kin taba zuwa bariki don Allah..."Yafada yana sosa sajensa bayan ya kafamata ido,Ganin haka yasa inna ta fara ja da baya tana kifkifta ido,Daure Fuska yayi kafin yace"Toh matukar baki bi Umarni na ba,zan sa azo asace min ke,sai kin kwana kin wuni acikin Firiza mai maida jikin dan Adam kankara,kafin na hadaki da sojoji su huce Haushi akanki..Maza ki amsa min da Toh..."yafada yana Buga hannunsa bisa cinyarsa sai da tayi kara,ai inna Ramatu bakinta na Rawa take fadin"Toh..Toh angama yallabai.."Take fada tana Dafe bakinta jikinta ba inda bai Rawa saboda jin ya ambaci xai saka asaceta tasan tsab zai iya don ba mutumci ne dashi ba..
Ganin yadda take Rawan jiki yasa dariya yakusa subucema Azeema tayi Saurin dafe bakinta,Aliyu ya bita da kallo kafin yadan murmusa yana kallon Inna Ramatu"Ahankali ya Furta "Good..."Yafada yana juyawa bai ko kalli barayin da Azeema take ba ya fice daga gidan cikin Takunsa na Takama da Jarumta,Yana ficewa Inna Ramatu ta hau leka kofar waje tana fadin"Baza abi ba din.."Tafada tana zare ido,dariyan Da Azeema take boyewa sai da ta Fito,kallonta Inna tayi tana fadin"Zan ci ubanki shegiya mai Farar kafa,wlh in yasa aka sace ni daga ke har Lusarin ubanki in nadawo bazaku ji da dadi ba.."Tafada kafin buguzun buguzun takoma daki tana borin kunya,ammh jikinta tsab da tsoron Captain..
Shiko yana fitowa ya nufi wajensu Azeema yaga yadda sukayi saboda wuya,yana zuwa yace su dakata kowacce ta mike,ai fa nan fa daya gabadayansu gwiwa tayi sanyi basa iya mikewa saboda yadda sukaji Jiki,tsawa ya daka musu suka tsaya kan kafafunsu suna rawan jiki,Kallonsu yayi yana dan mirmishi kafin yace"Gud job..Kun gaji gashi kunyi zufa,so kowacce taje ta cika botiki daya kafin in Tuna wani pushiment zaku yi next.."Kallonsa sukayi suna hawaye,Itako Azeeza duk azaban data ke ciki kallonsa take cike da so da kauna,yadda ya tsaya sai taji kamar taje ta Rumgumeshi,har wani lumshe ido takeyi tana lasan baki tsawan daya kara daka musu ne ya fargar da ita,gabadayansu suka je,kowacce taje ta cika botiki daya,na mutanen dake wajen suna gamawa yace kowacce ta dauko akanta tazo nan,haka suka dauko suka zo,suna zuwa yace"Kowacce ta kalli yar"uwanta..,Bayan sun kallah yace"Kowacce ta juye Ruwan jikin nakusa da ita..."Kwalalo ido sukayi suna binsa da kallo,tsawa ya daka musu yana fadin"in na kirga uku bakuyi Abunda nace ba,zan sauya ra"ayi daga wanka Ruwa zuwa na kasa kuma wlh zanyi Abunda nace.."Yafada kai tsaye,ah bai gama Rufe baki sukayi ma kansu wanka da Ruwa,kallonsu yayi yaga kowacce tayi tsamo tsamo kamar wasu zakaru Dariya ta kamasa,ammh sai ya matse da kallo ya bisu kafin yace"Yauwa kun warware gajiya by now kowacce tasaka gwiwanta akasa ammh kuma ta juya ta kalli hanyar gidansu.."yafada yana mirmishin mugunta,Zubewa sukayi kowacce na kuka harda majina,domin ji suke tamkar gangar jikinsu bazai iya Daukansu ba.
Wucewa yayi yafara tafiya kafin yace"Kowacce tafara jan gwiwa har zuwa gidansu,wlh tallahi duk wacce tatashi na ganta ko na kamata,yau sai ta zagaye anguwan nan tana jan gwiwa,toh tun kuna son kanku da Arziki kuyi yadda nace,dis one na small one,duk Randa kuka karama matata Rashin kunya zanyi Doubling din hukunci danayi muku yau,so be carefull.."Yafada yana wucewa kafin yace"1,2,3...Start..."Da hanzari kowacce ta fara suna jan gwiwa suna kuka wiwa,Inda Allah ya taimakesu duk yan wajajen nan,gidajensu babu nisa sosai,nan kowacce ta nufi gida da jan gwiwa tana kuka harda majina,Shiko Aliyu gida ya shige ko ajikinsa,shiko Sulaimam bai Tafi ba sai da akaci aka sude sai dariya yake Ransa fes anyi maganin marasa kunya.
Sai ga inna Ramatu da kanta ta fito tana hada Kulin Alalan tanayi tanama Azeema Allah ya isa,sai ga Azeeza ta shigo da jan gwiwa tana kuka Fuskarta ta hade da majina da kuka,ga jikinta ajike da Ruwa da hanxari tayi Wurgi da ludayin hannunta tana fadin"Na shiga Tara ni Ramatu Azeeza gamo kikayi kokuwa karo kikayi keda mai akori kura,yayi miki wannan damejin da jiki..."Tafada tana karisawa gareta tana riko Azeeza,gocewa Azeeza tayi ta zauna dirshan Tana kuka gwiwanta duk sun sale saboda janta datayi akaasa,Kafafunta kuwa ciwo suke matw kuka take tana hadawa da ihu tana fadin"Wayyo inna wlh kafata zafi takemin kuguna,ya rike ban iya mikewa saboda azaba.."Tafada hawaye suna zubomata,Azeema dake lekensu ta window ta kece dadariya tana kama bakin ganin yadda Fuskar Azeeza ta dawo kamar wacce akayi wasan kura da ita,kallonta inna tayi tana fadin"ke wai tsaya Hatsari kikayi ne komiye..?"Azeeza na kuka tace"Wani hatsari inna,ba yaya captain bane saboda naje kiran Azeema tazo in jiki ba,sai ta dauko Ruwa tazo zata wuce shine santsi ya kwasheta tafada kwata,shine shine fa,yazo ya hadamu nida su lantana,yasakamu tsallon gwado bayan mungama yasa mukama junanmu wanka,duk hakan bai ishesa ba,sai da yasamu kowannenmu yaja gwiwansa zuwa gida..",Takarishe tana yaye zanin jikinta gwiwanta ya bayyana Duk ya sabe,baya inna Ramatu taja tana salallami take fadin""Kutmar ubanchan,yanzu Shi yayi muku hakan?gyada kai Azeeza tayi tana fyace majina,Haba Inna ta rike tana fadin"Lalle ya cika mara mutumci ai sai ki tashi ki gasa jikin ki,kiyi hakuri.."da mamaki Azeeza ke kallonta kafin tace"Inyi hakuri fa kikace inna,nazata zaki Ramamin kan Adda Azeema tunda akanta ne yayi mana haka.."baya inna taja tana fadin"Wa ni? Rufamin Asiri nima bai dade da fita daga gidan nan ba,yamin kashedi sosai kan Azeema yace duk Randa na saba umarninsa,sai ya saka ansace,na kwana afiriza mai maida jikin mutum kankara,kafin ya hadani da sojoji suyi wasan kura akaina,.."Tafada tana waigen kofa,zaro ido Azeeza tayi tana fadin"da gaske inna..."Gyada mata kai tayi tana fadin"Wlh kinga kuwa ko saceni yayi babanki bazai damu baTunda yafi son Wanchan sakaryan Akanmu.."Shuru Azeeza tayi batama inna mgana ba,Tunaninta yatafi kan Tunano Fuskar Abun kaunarta,Inna da hanzari taje ta hura wuta ta saka Ruwan zafi kafin tazo ta ciccibi Azeemar zuwa kofar dakinta inda ta Shimfida mata tabarma,Azeezar sai wash wash take saboda azaba ammh kuma ko Ranta batajin Haushin Captain ba,saima tsanar Azeema daya kara cika zuciyarta ta kudiri niyar ko ta halin kaka sai ta mallaki muradin Ranta.
Inna Ramatu ita tagasa Ma Azeza jiki tana gasata tana kukan zafi bayan tagama ta shafe mata jiki da Man zafi,hakama Sauran kawayenta,kowa yaji Captain ne,ko ya taso da zafi sai yakoma don ba"a ma Soja wargi,Ballema kowa yasan waye captain kaf,anguwan nan Ansan baya da wasa yaci kaniyarka bawani abu bane awajenka,Azeema ko cikin dakinsu tana kashin dariya domin Ranar tayau ta mata dadi,kota tafito Diban Ruwa tayi wanka daga Azeezar har Inna ba wanda ya Tankata haka ta shige bayi tana dariya,wani Farinciki na Fizganta bata san dalili ba,ammh ko Fuskar captain Tatuna sai taji wani Sanyi ya Shiga Ranta,ita kadai ta Furta. *YAYA CAPTAIN NAGODE*
_______________
Ranar da Aliyu ya taho Gombe Aranar Ni"ima ta dira akaduna,Taji matukar takaichi da Bakinciki lokacin da captain jabir ke fadamata Cewa Aliyu ya taho gida,kuma bayajin zai dawo cikin satin nan,sai sati na sama,Kuka wurjajan Ni"ima takema Jabir kan yabata nombar wayar da zata samu Aliyu,dariya jabir yayi mata yana fadin"Bayajin cewa Aliyu ya chanza layi buh Abu daya yasani cewa ya kulleki ne,da zata tafi yace"Shawara mai kyau karta kuskura taje gombe wajen Aliyu in ma zata dawo ne tabari ya dawo kaduna yayimata alqawarin fadamata,taji dadi sosai Kafin tatafi sai da sukayi exchanging din Phone number,Direbanta ne yakawota Domin karya tayima mami wai zata raka Muneera biki sai yammah zata dawo Shiyasa har ta dawo gida mami batasan ina taje ba.
*************
Bayan kwanaki da Faruwan Abun,Azeema tasamu sauki sosai ta bangaren inna da Azeezar ita kanta bamai Shiga harkanta,ko aiki bamai sakata,Ammh dayake Azeemar ta riga ta saba shiyasa bata iya zama,duk Abunda tasan aikinta ne tun safe zata tashi tayi Mganar aikenta kuwa ba"a kara yi ba tun Ranar da Captain yayi mgana in ka ganta waje toh Mkranta zata ko Allo,itako da Azeeza ko mgana bata mata,in tayimata ma bata karba mata shiyasa tafita harkanta,Dayake bata zuwa mkranta tana jinyan kanta saboda kugu ya rike😂,Shikanshi mallam lawal yayi mamakin ganin chanji agidan,bai dai yi mgana bane,sai yaji dadi Aransa yana fatan ya sa Ramatun ta gyara halinta ne,itako Inna Ramatu mganar saceta a kaita barikin shine ke dagamata hankali,shiyasa ko taso yin wani Abu takejin Jikinta yayi sanyi,toh tafaa sani tsab Aliyu zai iya don ba mutumci ne da shi ba.
Goggo batasan wainar da"ake toyaba ,don yanzu bata cika ganin Azeemar ba,saboda dawowar captain sai dai da safe in zata mkranta kan yatashi take shigowa su gaisa da goggon ta wuce agurguje,Shiko Captain haryanzu goggo batamai mganar data kirasa akai ba,Shikuma bai mata mgana ba,yana jiran yaji mezatacemai,Shima yana Tunanin Dauke Azeemar daga wanchan Rayuwa zuwa wata rayuwar mai inganci.
**************
Yanasanya mota kenan Cikin garejin yana Sauri yasamu jam"in sallar isha"i yaji maganganu daga kofar gida,koda ya fito dayake akwai wuta,kuma haske ya wadata kofar gidan,Kallonsu yayi suna tsaye Azeeza takalli Azeema tace"Gaskiya Adda Azeema kidaina sakamin ido,ina Ruwanki dani,wato ke kinyi Aure,kina bakin ciki ni kar na tsaya na nemi nawa mijin,da anyi mgana sai kice,Baba yahana,don Allah kibarni naji dadin rayuwata.."tafada tana saka hannu ta ture Azeema dake tsaye sai da ta fadi,tsautsayi yasata tafadi ta gefen hannunta sai da yayi kara,dan Ihu Azeema tayi tana dafe hannun saboda azaba,Hawaye na shatata bisa kuncinta
Kallonsu yake cike da mamaki,kamar ya basar ya wuce,sai kuma ya tsaya yana kallon Azeezar harta kariso kusa dashi bata lura dashi ba,sai da taji ya dakamata tsawa yana fadim'"U Stupit,Come here.."Yana fada yana gyara tsayuwarsa,ba Azeeza da"aka dakama tsawa ba,hatta Azeema dake gefe saida ta razana,jikin Azeeza na rawa ta kariso tana kallonsa kafin tace"Gani.. YAYA CAPTAIN.."Ko kallonta baiyi ba,sai ya juya kan Azeema yana fadi cikin tsawa.."Au ke bazaki zo ba,jira kike na kiraki ko?i swear in kika bari nazo na sameki sai kin zagaye anguwanan kina tsallen kwado,wawiya kawai.."Yafada yana hararanta,ai Tun kafin ya rufe baki,ta kariso gabanshi jikinta na kyarma,hawaye na zubomata,Azeeza kuwa kuramai ido tayi tanajin wani dadi kamar ta rumgumeshi,hartana wani lumshe ido saboda yadda Shaukin ke Fuzgarta
Kallon Azeema yayi kafin yace"In kika bari hawayen ki ya zuba akasa,wlh sai kin duka kin lasheshi tas.."yafada ba alamar wasa atare dashi,Azeema da hanzari,ta hadiye kukan nata,tana share hawayenta,tsawa ya dakamusu yana fadin"Daga ina kuke Don ubanku yanzu dadddaren nan?.."Azeema bakinta na rawa tace",Da..daga Mkrantar Allo.."Sauke idonsa yayi kan Azeeza wacce tayi zurfin cikin Tunani,kuramata ido yayi yana ayyana girman Rashin kunyar yarinya,kara tamke fuska yayi kafin yace yana kallon Azeema"Waye ya girmi wani acikinku..? Da rinannun idanunta ta dago ta kalli Azeeza,wacce take wani mirmishi,Daka musu tsawa yayi yana fadin"Wai bada ku nake,mgana ba,ok so kuke yanzu jikinku yagayamuku inaga."Yafada yana kokarim zare belt,da hanzari Azeema tace"Nice,na girmeta..."Wani banzan kallo yayi mata kan yace"oh kece babba ammh kina zaune,yar kanwarki na miki Raini,harda tureki,kekuma dayake sakaryace mara wayau,har kina mata kuka ko"?yafada yana sakarmata ido
Jikinta na rawa kuka na neman kwacemata tafara ja baya,"Tsaki yaja yana fadin"bantaba ganin sokuwar yarinya irinki ba.."yafada yana maida hankalinsa kan Azeeza,Yaga yadda ta saki baki da hanci tana kallonshi nan da nan ranshi ya baci bai yi wata wata ya saka hannu ya shareta da mari lokaci daya ya sanya kafa yayi ball da ita,Azeeza dataji saukan mari abazata dakuma yadda ya hambareta tayi gefe tana fashewa da kuka"Nunata yayi da yatsa yana fadin"Shhiii..In kikayi Min kuka wlh Sai nayi miki bulala dari,don kaniyarki sa'arkice dazaki dinga dagamata murya,harkina dukanta, wato Abunda yafaru Ranar bai Tsorata ki ba ko?wlh na kara ganin kin mata rashin kunya,sai na saki cikin kankara kin kwana biyu,Try me an See.,Bacemin daga gani,tunkafin nafara kwallo,dake bush girl mai kama da monkey.."Da gudu Azeeza tamike ta shige gida tana kurukuruwan ihu,kallonsa ya dawo kan Azeema dake gefe tana sharan hawaye,Wani kulilin takaichi ya tokareshi,yanzu wai wannan wawiyar itace matarshi,gaskiya goggo bata kyautamai ba
Wucewa yayi yana fadin"Kema bita,kafin na chanza mind dina,inyi kasa kasa dake,kuma Nakara ganin kina mata kuka,sai na prison ya fiki jindadi,ko mganar banza ta fadamiki slap her,beat her,yadda zata kiyaye ki,kinji ko bakiji ba..
Da wani Rawan jiki dana baki tace"Na..naji...'" Better.."yace yana wucewa massllacin cikin sassarfa,da hanzari Azeema tafada gidan Goggo don tasan tana Shiga gidansu to tabbas sai Inna Ramatu Tarama ma Azeeza dukan da yaya Captain yayi mata,duk da yanzu tana shakkar yimata wani Abun saboda shi.
*Am Srry For d late update Na mantane ban hidi muku ba,Zaku dinga samu update din Ali gadanga duk bayan kwana daya ne,cuz am busy wlh Abubuwa sunman yawa Akwana dayan ma,karfin hali nakeyi..Masu comment da sharhi duk nagani kuma ngd sosai Am srry bansamu maida Reply ba,saboda wasu abubuwa dasuka shamin kai buh duk nagani kuma ina godiya Allah ya bar Zumunci Amin..*
*#Comment share,and vote...#*
*#Intelligent writer's asso...#*
*#Janafty....#*
*ALIYU GADANGA..!*
_(The Story of Young Soldier man)_
*Wattpad:Janafnancy12*
_Mallakar:Janafty💖_
*DEDICATED TO MY MOMMAH...HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*
_Special gift to my Real Dota RAHMA😘Ladingo yar mutan Niger_
*Intelligent Writers Association*✏
*NOT EDITED*💥
*Chapter 11*
"""Goggo na cikin kichen taji Sallaman Azeema,da hanzari ta fito tana fadin"Ah Azeema,kice kamar daga sama da daddaren nan? Tafada tana kallonta,Sunkuyar dakai Azeema tayi tana kokarin dukawa ta gaida goggon saurin Rikota tayi tana fadin"A"a tashi kada muyi haka dake,bama wannan ba,miye naga kina wani zare ido,gabadaya kamar atsorace kike,gayamin badai wani lalatattace bane ya biyoki yanzu na fita naci ubanshi,kokuma na hadashi da gadanga wlh yaci uwarshi yanzu nan fadamin waye ya biyoki naga kin Shigo a Tsorace"Dan waro ido Azeema tayi kafin tace"Ba kowa bane fa inna Dama yaya captain ya daki Azeeza saboda tamin Rashin kunya,shine na shigo nan kada na koma gida inna ta huce akaina.."Galala Goggo ta kalleta kan tace"Ai yamin daidai wlh,kema dai Azeema wlh ki kamma jikinki,in dai kina wannan sokanci wlh bazaku Shirya da gadanga ba,shi mutum ne dabayason wargi balle shashanci yo in ma kinaso sace zuciyarsa ne,na baki satan amsa ki zama mace Tukunnah bayan kinkam jikin ki Atoh.."Tafada tana Riko hannunta,Baki Azeema takama tana yar dariya,Mangare mata kai goggo tayi tana fadin"Au dariya na baki ko?yo ai gaskiya ne,ammh wani lokacin in kina wani Abun sai ki dinga Tunamin da Mahaifiyarki Fatima,wlh Azeema yadda kike da hakuri da kawaichi to Fatima ta fiki.."Tafada cikin sanyi,nan da nan idon Azeema ya ciko da hawaye,dafa kanta goggo tayi tana fadin"Karki damu Azeema wlh Tamkar Aliyu haka nake kallonki da izinin lahi sai kin zama Abun alfahari,da kin Tuna da mahaifiyarki karkiyimata kuka kiyi mata addu"a da Fatan tana kyakyawan mtsayi kinji ko? dakai Azeema ta amsa tana share,kwallah hijabin jikinta goggo ta ciremata bayan ta amshi al"qur'anin tana fadin"Maza shiga shiga ciki ki dauro alwala kizo muyi sallah sai muci abinci yanzu na gamashi da zafinsa,ai ni nagodema ja"irin nan gadanga daya bugemin Mara kunyar yarinyarnan gashi sanadin haka yata tazo wajena,duk da yanzu wasan buya ake dani Tunda Megida yadawo.."Tafada tana kyabe baki,Tura baki Azeema tayi tana fadin"kai goggo ba ina zuwa ba,kuma ni yaushe nace haka.."Goggo tayi yar dariya tana fadin"Au hakane fa,to naji baki ce ba,maza shiga kiyo ki fito an kusa sallame salla daga masallaci.."Tafada tana Ficewa daga Falon,itako Azeema dan mirmishi tayi kafin tafada bedroom din na inna wanda in ka gansa ko na wata amarya albarka saboda yadda yasha wani ubansu royal bed mai kyau da tsari gashi yana malale da capet mai kyau da tsari,da makeken wardrope dinta sai madubinta dake shake da kayan shafa na mata,wanda goggo banda kwalli bata shafa komai,ammh kullum taramata Ali gadanga yake,Tunda kawu ya daukemata Nauyin komai.
Tare sukayi jam"i da goggo suna gamawa goggo ta zubomusu abinci Shinkafa da miya sai slat datayi musu goggo fa,ba baya ba,akwai iya girki sosai kamar ka tsinke hannu,nan suka zauna Dole tasa Azeema sakin jiki don goggo dai kun santa dole ma mutum ya saki jiki da ita,da farko Azeemar kin ci tayi,aiko goggo tayimata barazana da zata kira Aliyu yanzu yazo yayimata dure,kila taci jin haka yasa taba goggo hakuri ta hau cin abinci dama yunwa takeji sosai domin tun karin safe rabonta da Abinci,Ammh tanayi tana waige da sauraran waje kada Yaya captain yazo ya Ritsata.
Itako Azeeza tana shiga gida da ihu Ta iske mallam lawal atsakar gida shida Inna Ramatu,jin ta shigo da ihu yasa Inna mikewa tana fadin"Ke lafiyanki kuwa keda wane.."gabansu Azeeza ta zube tana fadin"Inna wlh In baki dauki mataki kan Adda Azeema ba,ni zan dauka dakaina.."Tafada tana hawaye,wanda bana zafin marin da yaya captain yayimata bane,a"a takaichi yadda taga kamar yana tsausayin Azeemar ne,wanda ita ba burinta kenan ba,burinta kafin yafara son Azeemar ita ta riga ta mallake zuciyarsa Allah barshi ya dankarama Azeemar sakinta ta kara gaba.
Inna tace"Toh me tayi miki ne,nifa bangane ba? Kyabe Fuska Azeeza tayi tana fadin"Ba ba kawai mundawo daga Mkranta bane zamu bi ta kofar gidansu yaya captain Tunda Adda Azeema ta ganshi shikenan ta nufi wajensa,bansan metacemai ba,naga dai Tana ta nunoni,ban ankara ba yazo kusa dani kawai ya mareni,kuma ya saka kafa yayi Shuru dani.."Tafada tana kara barkewa da kuka kamar gaske
Kutmar ubanchan.."Inna tafada Tana rike kugu kafin ta waiga tana fadin"Ammh dai kaji Abunda tsinanniyar yarka tayi ko? ammh naga kayi Shuru bakace komai ba"Ko kallonta baiyi ba yace"Nidai ban Tsinema yata ba,sai dai in ke kika Tsinema taki,mganar kuma da makaryaciyar yarki ta fada ba gaskiya bane,na tabbata Azeema bazata kulla miki sharri har Aliyu ya dakeki ba,sai dai in rashin kunya kikamai ya hukuntaki.."Yana gama fadar haka ya mike yana kakkabe rigarsa yake dakama Azeexa tsawa yana fadin"Tashi kiba mutane waje,matukar baki zama mutum ba,har abada ni dake bazamu Shirya ba.."Yafada yana Shigewa daki.
Da kallo inna ta bishi kan takoma ta zauna tana fadin"Eh na yarda tabbas Watarana Azeema zata kashemun aure,toh kan ta kashemun ni zan mata dukan mutuwa dasai ta gwammace kida da karatu,wlh tallahi sai dai duk Abunda zai Faru ya faru..",Tafada tana huci,ganin haka yaasa Azeeza tashiga zigata na taci uban Azeemar in tadawo itako inna huci kawai take kamar wata macen zakanya.
Shiko gadanga yana idar sallah yadawo gidan,yana shigowa yaji muryan goggo tana hira cikin hiran natane yaji ta ambaci Azeema jin haka yasa yayi burki zuwa dakinsa cuz bayasan ya mtsama yarinya Tunda ya lura tsoransa takeyi,bai cika cin abinci mai nauyi ba da daddare,shiyasa goggo bata damu da nemansa ba,balle ta kaimai Abinci,har wajen goma Azeema na gidan sai lokacin tace zata koma gida goggo tayi tayi ta tsaya ta kwana ammh taki dole ta kyaleta ammh aranta tana addu"ar Allah ya hadata da gadanga ya warfatota tadawo akwai illai tana Fitowa tsakar gida cikin sanda Ya hangota dama yaji karan bude kofa,Fitowa yayi yana kallonta tana tafiya ahankali Gyara tsayuwa yayi sai da takusa isa ga kofar gidan daya kulle Tun dazu kan yace"Ke...",yafada cikin sanyi,Cak ta tsaya jikinta na rawa jin muryansa kafin ta waigo Arazane kallonta yayi kafin yace"Ina zaki.."?Bakinta na rawa tace,"Gi...gida...Za..zani.."harara ya zabgamata kafin yace"dallah wuce kibama mutane wajen gidan wa zaki Da daddrenan.."Yafada yana kokarin komawa daki,kin tafiya tayi ganin haka yasa ya dakamata tsaawa yana fadin"Au zaki wuce ko sai nazo na tattaka ki anan wajen ne.."Jin haka yaasa tayi dakin goggo da gudu tana rawan jiki,gyada kai kawai yayi ya rufe kofa ya koma ciki,tana shigowa daki taga goggo na mata dariya tana fadin"Allah yamaka albarka gadanga..."Take fada tana ma Azeema dariya,Azeema tayi nakwa nakwa da Fuskar kamar zatayi kuka da sauri goggo ta rikota tana fadin"Yi hakuri kema Allah miki albarka Azeemata muje mu kwanta kinji.."Tajata zuwa kan makeken gadon nata ta kwantar da ita,tana shafa kanta tace"Toh kwanta kiji gobe da safen zan rakaki har gidan kinji ko? gyada mata kai Azeema tayi tana dan mirmishi Aranta tanajin son goggo na ratsata saboda yadda take kula da ita.
Shiko mallam lawal koda dare ya tsala Azeema bata dawo ba,haka inna ramatu tazo kansa tanata jaraba wai Azeema bata dawo ba,tatafi gantali kuma wai nan matar aurece,hartana cewa bataga amfanin wannan Auren ba,shisshigi ba kwarjini,sai Tusa kai suke ana gwasalesu,shidai yana jinta kanzil baicemata ba,saboda yana da tabbacin Azeema na gidan goggo kuma yasan darene yayi Suwaibar tahanata dawowa,juyamata baya yayi dole datagaji ta hakura tayi Shuru Tunda bai Tankata ba.
**************
Da Asuba bayan Aliyu yadawo daga sallar Asuba ya shiga wajen goggo yana fadamata yasamu kiran gaggawa daga bariki General ne ke nemansa da kansa,sabods haka zai zo yakoma ammh yafadamata bazai dadeba wannan karan zai dawo,fatan alheri tayimai kafin Surabu agurguje yagama Shirin saboda sauri ko karyawa baiyi ba,ya dauki hanyar kaduna,har yatafi Azeema bata sani ba,don bayan ta idar da sallar asuba takoma ta kwanta Shikenan sai barci ya kwasheta bata farkaba sai wajen Takwas saura,nan ta farka tana salati ta mike ta fito falo nan ta tarar da goggo na sharan capet din dake falon,saurin karisawa tayi ta karba tana Fadin"Haba goggo gani cikin gida saiki hau shara da kanki.."Sakarmata tsintsiyan tayi tana fadin"Na kyaleki kiyi barcinki ne,nima Fitan gadanga ne yasa nafara sharan.."Da kallo Azeema tabi goggo dashi sai ta samu kanta ta tambayan "Ina yaje Goggo..? Goggo tace"Eh ya koma kaduna wai yaasamu kiran gaggawa,yanzu bai dade da tafiya ba.."Shuru Azeema tayi taciga ba da sharanta bayan ta gama tayi mooping din dakunan duka,tana gamawa goggo tasa ta shiga wanka bayan Ta fito suka karya,lokacin har goma ta wuce,tarasa mkranta yau sai dai gobe in Allah yakaimu,Bayan sungama komai Goggo tasa hijabi ta rufo gidan suka nufi gidansu Azeema.
Inna na madafi taji sallamar goggo Fitowa tayi tana binsu da wani kallo daga ita har azeemar"Karkace kai goggo tayi tana fadin"Mun tashi lafiya Ramatu.."Dakyar Inna ta amsa da cewa!Lafiya..'daga haka tajuya takoma ciki goggo bata damu ba tace"Ga Azeema jiya wajena ta kwana dare yayi na hanata dawowa,ina mallam din yana ciKi.."? Mallam lawal daya fito daga bayi yace"Ina nan Suwaiba ina makewayi ne,naji shigowarki sannu da zuwa.."Goggo ta amsa "Da yauwa mallam,dama Azeema na rako jiya tayi dare sai ta kwana wajena.."Dan dariya Mallam yayi kafin yace"Toh inbanda Abinki suwaiba ai Azeema takuce gabadaya koma komawata tayi wajenki gabadaya ai babu matsala.."Gyada kai goggo tayi kafin tace"Hakane..."Azeema ce ta duka tana gaida Mallam lawal ya karba yana tambayanta yatakwana,ta amsa da lafiya kalau,tashi tayi ta shiga dakinsu nan ta iske Azeeza tatafi mkranta tayi mamaki sosai saboda sam Azeeza bata son mkranta,goggo ko daganan tayima mallam lawal sallama takoma gida,inna ko ko tak batace ba,kamar mai ciwon baki har mallam lawal ya Shirya ya fice batacema Azeema komai ba,kawai tana kallonta ne tana Tunanin yadda zata chanzamata kammani cikin hanya mafi sauki,sai kawai ta yanke shawaran tayi bakan sai ankwana biyu sai ta dauki matakin da zata dauka.
________________
*Masauratar Garin Agadez*
""Wai babana meke damunka ne,kaki bari Asaka malamai cikin wannan laluran taka,suzo kayi musu bayanin yadda kake gani amafarki kila in andace su gane me hakan ke nufi ammh sam kaki kuma GIMBIYA RAZEENAH Tafadamin baka bar mafarkan ba yanzu ma kamar yafi nada.."Takarishe cikin nuna Abun ya dameta.
Jin Abunda Ummah mai babban daki tafadane da sunan data ambata yasa dagowa yana zabgama gimbiya Razeenah harara,itako ta kauda kai ko ajikinta,yana zaune kusa da kafafunta itakuma tana zaune kan wata kujera mai kyau da tsari irin na gidan Saurata su duka biyun suna sanyene da alkaybbu masu kyau da tsari,Kasan kuma wani capet ne daya malale dakin kowani lungu kuma dauke da Tuntu irin na gidan Sarauta,agabansu kuma shake da wani kayatattacen Faranti dauke da kayan Ruwa ma"ana Fruit.
Kallonta yayi yana Fadin"Kibamu waje zanyi mgana wa Ummata.."Yafada kai tsaye mikewa tayi kafin tace",Afito lafiya Ranka ya dade..",Ta fada tana gyara zaman alkyabban jikinta kafin ta fice,yana binta da harara lokaci daya ya dawo da kallonsa kan Ummah kafin yace"Don Allah Ummah kedaina daukan mganganun yaran chan akaina,ni basan ciwon kaina bane? kokuwa Sinfini sanin mezanyi ne,kuma mganar mafarki ko na malamai don Allah Ummah kibar mganar nan,bafa Abunda yagagari Allah koma miye insha Allahu inaji ajikina yakusa bayyana.."Yafada yana jinjinamata kai,Rausayar dakai tayi xatayi mgana yayi Saurin cewa"Don Allah kibar mganar nan Ummah,kuma kidaina basu Fuska in suka kawo miki ita,duk wacce acikinsu nake takuramawa in tana barci to ki fadamusu kada wacce takara bina Sashena don ba gayyatarsu nayi ba,bankuma ce Dole azo ba Atoh.."Yafada da alamar ya fara hasala
Jinjina kai Ummah mai babban Daki tayi kafin tace"To ai Shikenan duk basai takai ga haka ba,Allah ya bayyanamana koma miye.."Da Amin ya amsa kafin ya mike yana fadin"Zani Fada Ummah yau sarkin garin Dossso zai kawomin ziyara zamu tattauna wata mgana ne nidashi.."gyada kai Ummah tayi kafin tace"Toh Allah ya taimake ka Allah tsone idon makiya akanka babana.."Da Amin yayi ta karbawa Kafin ya fice daga makeken falo,yana Fitowa dogarai na kofar Shigowa suka yimasa rumfa suna masa barka da Fitowa,basu barshi kowa ya gansa ba, suka Rufesa da riganansu har ya shige fada ya zauna,kafin afara gabatar da Abubuwan mulki kamar yadda aka saba akowacce safiya.
....................................
_Gombe_
Bayan Sati daya da Faruwan Abunda ya faru,Yau din takama Asabar ne,Tun safe Azeema tatashi da wanki danata dana babanta sai na inna Ramatu,wannan karon kam bata dauko na Azeeza ba,domin har aranta ta gane Raini ne kawai ke karuwa matukar tana cigaba da bautama Azeeza,Sai da tagama wankin Tas tana shanya Azeeza da tashinta kenan daga barci ta fito tana mutsika ido ko sallah batayi ba,taga Azeema tacika igiyoyi da shanya ammh kaf babu kayanta daki takoma taduba ma"adanar kayanta taga ko kala daya Azeemar bata dauka ba,Afusace ta fito daga dakin tana fadin"Wai ke Adda Azeema kwanan nan mekike Nufi dani ne.."?tafada bayan ta tsayamata agaba kerere,kuma duka hannuwanta takama kugu dasu,ko kallonta Azeema batayi ba,saima tacigaba da shanyarta,Ganin haka yasa Azeeza ta fusata Tanufi kayan da Azeemar ke shanyawa duk ta rikito dasu kasa kuma tasa kafa tataka tana fadin"Kinajina ina miki mgana kina min banza,yanzu ai ina fatan kin jini ko,sai na kara fatali da sauran ne.."Tafda tana wani mata banzan kallo,Azeema dake bin kafan Azeeza da kallo daga sama har kasa taga yadda tayimata da kaya,Ranta in yayi Dubu ya baci ashe haka Azeeza ta rainata bata sani ba,bata gama mamaki ba Azeeza ta sanya kafa tayi Fatali da sauran kayan dake botiki daya rage bata shanya ba,Tana fadin"An kara zubarwa sai ki..."Ji kake Tas!Tas!Azeema tadake tsaye ta zabgama Azeema marika masu lafiya dama da Hauni,wanda saida Azeezan Ta wuntsila bakinta ya fashe da hanci Dago kanta tayi bakinta bude tana kallon yadda Azeema ke huci saboda bacin rai cikin kakkusan murya tace"Ni sa"arki ce Azeeza,ashekarun haihuwa nawa na baki? kodon kinga ina kyaleki bana tanka miki to ba tsoro bane wlh gudun mgana ne,ammh Tunda nagane baki da mutumci ballatana kunya yanzu mukafara dani dake acikin gidan nan.."Tafada kafin taDuka tana kwashe kayanta Ranta bace kamar tayi kwallah.
Mallam lawal dake kofar daki Tun dazu yace"Kinyi min Daidai diyar albaarka,Hukuncin yayimata kadan dakin hadamata harda dukane kila tashiga hankalinta mara Tunani kawai.."Yafada Ransa na kuna,inna Ramatu dake bayi tana Allah Allah ta fito itako Azeeza jin zafin mari yasa ta shiga kurma ihu kamar wacce ake yankawa,Ai da gudun bala"i inna Ta fito daga bayi tana tambayan lafiya,daga Azeema har mallam lawal ko kallonta ba wanda yayi sai ta isa ga Azeeza tana fadin"Ke dallah bar kuka gayamin me sukayi miki don naasan daga Uban har yar bamai kaunarki acikinsu.."Wage baki Azeeza tayi tana fadin"Inna Adda Azeema ce ta kifkifamin mari,wai don nazo ina mata mgana kan naga bata hada da kayana ta wanke ba,shine baba yace wai tayi daidai ta takaramin da duka.."Dafe kirji inna Ramatu tayi Tana fadin'Kutumar ubanchan lalle tayi kuskure,ko ni dana haifeki bantaba saka hannu na mareki ba,balle ita,in ita bata hada miki da duka ba,ni yanzu zan hadamata shegiyar yarinya dama ina da cikinta yau zan Famsheshi.."Tafada tana Nufar Azeema wacce ke tsaye tana kallon innar,mallam Lawal yana fadim"A"a Ramatu karma ki fara,kada ki soma,Allah kika tabata zan bata miki Rai.."ina ko jinshi batayi tana zuwa ta kifama Azeema mari tana fadin"Don ubanki jakarkice ita,da zaki mareta zaki ci uwarki yanzu nan don wlh sai nayi miki dukan mutuwa gaba ko sunan Azeeza kika ji kya kiyayeta.."Bata tsaya Sauraran Azeema dake fadin"Inna ki tsaya kiji metamin wlh Azeeza ce bata da gaskiya kada ki dakeni.."Take fada kuka na tahomata,ammh inna bata saurareta ba,ta jawo wani tsohon igiyan Gugansu ta shiga laftama Azeema wacce ta durkushe tana kuka,Mallam lawal yayi Saurin isa kusa da Ramatu yana kokarin amsan igiyan ammh taki bashi da gayyah ma,take zabgamai azuwan bata sani bane,Azeeza na gefe ta share hawayenta ta mike tsaye hannuwanta sarke bisa kirjinta tana kallo tana mirmishin jin dadi.
Goggo dake tsakar gida tana Taran Ruwa afamfo daidai gatangar gidansu Azeema takejin kuka da maganganu harda Muryan mallam lawal yana fadin"Kibari nace Ramatu,kibari ko.."Yake fada,da hanzari goggo ta ture botikin hannunta ta shige daki da Sauri ta dauko hijabinta da wayarta ko Rufe gidan batayi ba,ta fito da Sauri ta fada gidansu Azeema daidai lokacin da Inna Ramatu tawani bangaje mallam lawal yayi taga zai fadi Allah ya taimakeshi ya dafe duka hannuwansa akaasa,Itako inna harda hannu take hadama Azeema,Goggo data Shigo ta ruga da gudu tana fadin"innalillahi..Ramatu mezan gani haka?me Azeemar tayi miki kike mata wannan dukan.."?Tafada tana Ture Ramatun Ta Rumgume Azeema wacce Fuskarta tayi jajir,jikinta duk ya fashe saboda duka,baya inna Ramatu taja tana Huci da sauke gajiya tace"Malama babu Ruwanki,kifice ki bani waje,wlh in ban bar Azeema kwance ba bancika Sunana Ramatu ba.."Goggo ta dago kanta idonta yayi ja tace"Aikuwa bazaki cika sunanki Ramatu ba..."Tafada cikin Fushi kafin ta Fito da wayarta ta shiga latsawa A speaker Ta bude wayar saboda tana son Suji ansam kuwarshi.
Captain Aliyu yana bakin aiki lokacin da kiran goggo ya shigomai wasu bataliyane agabansa yana koya musu Training da dubarin yaki,kiran nata ya katseshi lokacin yana sanye ne da kakinsa,Ya fito a Captain dinsa sak,dakatawa yayu yakoma da baya ya Dauki kiran yana fadin"Goggo.."Muryan ta narawa tace"Gadanga ga matarka Azeema nan Ramatu takamata da duka,na mata mgana tabari tace bazata bari ba,Tace indai batama Azeema dukan mutuwa ba bata cika sunanta Ramatu,inason ka nuna mata ikonka,kanuna mata bata isa ba,indai ni Suwaiba ni na haifeka.."Tafada cikin daga murya.
Aliyu da Tunda goggo ta fara mgana jijiyoyin kansa suka mike Tuni idanunsa suka chanza launi,dunkule hannunsa yayi yanajin yadda muryan Goggo ke rawa batare da wani Tunani ba yace"Don Allah goggo ki bani dama..", goggo ta karba da cewa"Na baka dama gadanga..Nabaka kowacce dama Tunda dai batasan mutumci ba.."Cije lebe yayi kafin yace'Ngd goggo..Yanzu Ki dauki Azeema ki Tafi da ita in Baba na nan ki fadamai *AZEEMA TA TARE ADAKIN MIJINTA..* yafada cikin tattausawa,Dariya goggo tayi kafin tace"Angama gadanga Allah yayi maka albarka..."Daga haka suka yanke kiran,Goggo ta dago tana kallon inna Ramatu da jikinta ke rawa sai yanzu ta Tuna da kashedin Captain.
Kallonta goggo tayi kafin tace"Kinga ikon namu ko,Uhmm wannan somin Tabi ne,kijira hukunci gadanga.."Daga haka Ta riko Azeeza,mallam lawal daya mike yana haki yace"Jeki da ita Suwaiba..Azeematu Allah ya albarkacin Aurenki Duniya da lahira..',yafada wasu hawaye na ziraromai saboda takaichi,Azeema na kallon babanta na kuka,sai itama takara fashewa da kuka,ammh cikin Ranta tana amsawa Da Amin,inna Ramatu baki ta rike tana fadin"ikon Allah sai kallo,Abun rabo ne budurwa da jika,wannan wani irin Aure ne,..."Tafada tana bin bayansu goggo da kallo har suka fice daga gidan.
Azeeza dake gefe tazama mutum mutum har su goggo suka fice,kenan yanzu Azeema zata tare adakin captain a mtsayin mata,duk tana zaune batayi wani Abu ba,ina?bazai taba yuyu ba,wlh Captain nata ne ita kadai indai bata sameshi ba,sai dai kowa ya raasa,zata iya yin kisa akansa koda kisan takama na yar"uwantane Azeema,Idonta gabadaya ya soye hawaye sun kafe saboda bakinciki,juyawa kawai tayi takoma daki ko inna dake kiranta banza ta mata don alokacin ma innar haushi take bata kamar ta makureta ta mutu kowa ya huta,in da bata daki Azeema ba babu yarda za"ayi goggo tazo har takira yaya captain yace Azeema tatare adakinta ba,Duk inna taja,Ran Azeeza tafasa kawai yake saboda kishi da hassada,Shedan sai huramata wuta yake azuciya Tare da kara tusamata tsanar Azeema Aranta,kanta ta buga agaru tana fadin" *BAZAN KYALEKI BA...WLH TALLAHI SAI NA AMSHI ABUNDA YAKE MALLAKI NA NE,KODA ZA"A ZUBDA JINI NE...*"Tafada jini na biyi goshinta kafin tafada bisa gado tana fashewa da kuka.
*Tabdijam...Hmmm...Salon yanzu ya fara zuciyar Azeeza fa ta bushe babu imani ko kadan,ga Azeema zata tare agidan mijinta ga Goggo tabama Gadanga damar daukan kowani mataki..Akwai wasa sosai agaba juz keep following zan warwaremuku zare da abawa*
*Comment,share,and vote..*
*Janafty...*
*Intelligent writers asso....*
*ALIYU GADANGA..!*
_(The Story of Young Soldier man)_
*Wattpad:Janafnancy12*
_Mallakar:Janafty💖_
*DEDICATED TO MY MOMMAH...HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*
_Special gift to my Real Dota RAHMA😘Ladingo yar mutan Niger_
*Intelligent Writers Association*✏
*Srry 4d late update...Bohot bohot love Habibaties...*
*Chapter 12*
_Kaduna_
"""Yau din Takama weeked ne,Lahadin karshen mako ne,kowani soja dake barikin manya da kanana suna gidajensu domin Hutawa hakane ta faru da Captain Aliyu,Shima din Tunda ya dawo sallar asuba yakoma bai iya tashi ba saboda gajiya da barci.
Cikin barci yakejin kiran waya da karan Door bell atare,Wayar nasa tana kan Side Drower din gadon nasa ne,hannu kawai ya mika ya dauko wayar da niyyar kasheta sunan Jabir daya gani ne,yasashi ya daga kiran yana fadin",Hey Dude wht wrong kakemin irin wannan kiran..? ya fada Muryansa da alamun barci daga chan bangaren Jabir ya amsa da fadin"Dallah mallah ka watsake daga wannan barcin Gani akofar Apartment dinka.."Aliyu najin haka ya datse kiran yana tsaki yasan halin Jabir kamar maye da takura,mirginawa yayi gefe ya cigaba da barcinsa ammh sai me karan Door bell din fa bai tsaya ba,har filo yasa ya Toshe kansa ammh duk abanza,Mikewa yayi ya duro daga kan gadon,sanye yake da wani 3quater din wando babu ko Riga ajikinsa ya fito daga bedroom din yana bata rai isa yayi isa ga kofar ya bude jabir dake Tsaye hannu harde akirji Ya bayyana Kare kofar Aliyu yayi yana rollin din idonsa kafin yace"Ya? lafiya mallam kazo kahanani barci sai famam bugamin kofa kake sai kace naci bashinka ban biya ba.."?ya fada yana ballamasa harara.
Yar dariya Jabir yayi kafin yace"Ba laifina bane Captain,banbin ka bashi ammh akwai mai binka.."Yafada yana shafa sajen Fuskarsa,Shekeke Aliyu ya kallesa kafin yace"Toh waye..? Jabir yayi Saurin matsawa baya sai ga Ni"ima ta bayyana tana sanye da Doguwar riga Baka kirar Armani,tayane kanta da bakin mayafi,kafarta sanye da wani black halfcover,mai kyau da tsari,sai wata karamar jaka,da wayarta dake hannunta,Sake baki Aliyu yayi yana bin Ni"ima da kallo daga sama har kasa,itako Tunda ya fito take kallonsa gabadaya wani soyayyarshi data binne lungu da sako Ya tasomata lokaci daya hawaye suka cikamata ido saboda tsausayin kanta.
Rausayar dakai Jabir yayi kafin yace"Toh na fita ko? Kai mallam ka bata hanya Ta shiga ciki takanas daga gombe take saboda kai,ko bakomai ka girmama bakonka.."Jabir na fadin haka ya wuce ya barsu nan,Ni'ima dake tsaye batayi gaba batayi baya ba,kallonsa kawai take hawaye suka gangaromata baki na Rawa ta Furta.."Soja..Nah...",Tafada cikin muryan kuka kafin tatafi da gudu ta fada jikinsa sai kuma ta saki kukan lokaci daya,Ajiyar zuciya Captain ya sauke kafin yayi baya bayan ya sanya kafa ya Rufe kofar takoma Tarufe kanta,hannu ya sanya yana buga bayan Ni"ima lallashi itako Fadi take"Why my Captain? why..? .meyasa zaka barni alokacin danake tsananin bukatarka da burin na sameka? wlh koda da darana daya bantaba samun kwanciyar hankali da barci mai dadi ba Tunda na Rasaka don Allah Sojana kada ka sake gujemin wlh bazan iya Rayuwa baka ba,nasha wahala kafin na sameka...",Tafada tana kara kamkameshi,tanasakin wani marayan kuka.
Bambareta yayi daga jikinsa ya isa da ita kan daya daga cikin kujerun Falon ya zaunar da ita,Kichen Ya nufa yaje ya daukomata Ruwa da wani karaminn kofi ya Tsiyayamata mikamata yayi yana kallon kwanyan Idonta,Amsa tayi kafin ta sanya hannu ta share hawayenta,dan kurba tayi kadan kafin ta mikamai,kan Center table din dake Falon ya ijiye kofin kafin ya koma kujeran dake kallon nata ya zauna bayan Ya Dora kafa daya kan Daya yana Fuskarta dago da kanta tayi Tana kallonsa Shiko Remot ya dauka yana sarrafa talabijin din dake Falon.
"Soja...Nah...."Tafada cikin Rawan murya Dagowa yayi zata kara mgana yayi Saurin dagamata hannu yana fadin",Kinga nifa bani zakizo kina ma kuka ba,babanki zaki tasa kikatayima Kuka domin shi yasaka alkamashi ya datse halakan dake tsakani na dake..."Ya fada idonsa akanta Raurau tayi da ido kafin tace", i know buh..."Dagamata hannu yayi kafin ya mike yana fadin",Ki Adana kalamanki Ni"ima domin basu da muhalli awajena,Ba shakka ada na soki,na kuma so muyi,zama na har abada dake,sai dai kash Tun Ranar da mahaifinki ya watsamin kasa a ido naji kin Fita Raina,ko koda ace banyi Aure ba bazan Taba iya Aurenki ba,..."Yafada kai tsaye
Azabure ta mike hannunta dafe bisa kirji tace",Kana nufin kayi Aure ne my Captain..? Takowa yayi zuwa gabanta kafin ya sanya duka hanuwansa cikin aljihun wandonsa yana fadin"Kwarai ma kuwa ai wajen da mahaifinki yace bazai bani Aurenki ba saboda Bani da uba awajen wani Uban ya wanke yarsa ya bani,kinga ko iya karamci da hallacin yayimin,kuma koda ma ba"ayi haka ba,ni Aliyu bani da burin zama da mace Fiye da daya..So Abunda nakeson fadamiki gwara Tun Wuri kiyi Facing Realiaty Ki cireni Aranki don bazaki taba samuna ba,shawara ta karshe don Allah kada ki kara zuwa gida,ina da mutumci a idon jama"a bana Fatan ki Fusatani har na zubda wannan mutumci...',Daga haka ya juya zai Shige bedroom dinsa har ya kusa shiga ya waigo yana fadin"Armmm..In kin Fita plz close d door...",Yana fadin haka ya Shige bedroom ya banko kofa Ransa bace,kawai daurewa yake shiyasa bai Mazgeta ba,ammh azahirin gaskiya haushinta yake daga ita har Dan sandan Ubanta.
Ni"ima ko Durkushewa tayi ta fashe da kuka,kamar zata Shide,Rike kanta tayi tana girgizawa tadade tana durkushe kafin tatashi ta fice daga gidan,Direba ya kawota Jabir na gaban gidansa yana jugging ya hangi Fitowar Ni",ima Tana kuka Dan mirmshi yayi kafin yace"i know haka zai Faru dama gaskiyan nake so ki sani asauka lafiya..,"Yafada yana dan Dariya,mota ta Shige ta Umarci Direba ya taka mota suje don yadda take jin zuciyarta kamar zata Fashe saboda kunci.
_________________
_Gombe_
Yau kimanin Sati daya kenan da komawar Azeema gidan goggo,Duk wani jin dadi da Kulawa goggo na bata,domin koda ta daukota daga gidansu Kai tsaye shashen Aliyu ta budemata tace mata nan ne dakinki Azeema,ki zauna kijira mijinki har ya dawo..Toh ya Azeema zatayi bata da yadda zatayi sai bin Umarni,Goggo da kanta ta zage suka gyara shashen suka tsabtaceshi,Washegari kuwa Goggo da kanta tadauki Azeema sukaitai kasuwa tayimata siyayyah kaya da Atamfofi da Dogayen Riguna harda masu sikat,sai kayan kwalliya da takamla duk wani Abun gayu dai na mata ta siyamata domin goggo kudi har bata sanin ina zata kaisu,in kawu yazo ya bata,hakama Aliyu,kullum Tarasu take saboda babu Abunda take siya komai na more Rayuwa sun siyamata shi ta mallakeshi,harta ta wajen gyaran kai Sai da goggo takai Azeema aka gyaramata kai aka wankeshi sosai,Ita kanta Azeema tayi Farinciki da Shigarta sabuwar rayuwa,haka Baba Ade tazo tayitama Goggo godiya harda kwallah saboda murnan chanjin Rayuwa da Azeema ta samu kamar yadda Mallam lawal Shima dauke Azeema daga gidan Yafi komai yimai Dadi.
Goggo batai kasa agwiwa ba,harta girki tazage tana koyama Azeema dawasu kissa,da dubarun yadda zaka jawo hankalin Namiji gareta,kullum bata lbrai take,tare da kawomata kissa kala kala na yadda kishi mai tsafta ya gudana agidan Annabin Rahama Muhammed Sallallahu alaihi wasallam,Tare da kissosin matan sahabbai,ba shakka Azeema na dauka shawarwarin goggo sosai don tana jin dadin xama da ita,Cikin Sati daya Azeema ta chanza kamar ba ita ba, Tuni wa"innan kuraje suka kama kansu dama wahalace ta kawosu,Tayi dan yi kiba taciko uwa uba ga chanjin abinci dana Sutura,Kullum a Sashen gadanga take kwana,ammh adayan bedroom din dake kusa danashi,wanda yake akulle Tana Tunanin makullin dakin yana hannun mai Shi ne,Watarana adakin zasu wuni da goggo watarana kuma A shashen goggo,Tunda Abun ya faru Azeema bata taka gidansu ba,kai ko Fita in ba kasuwar da sukaje da goggo ba,bata taka ko"ina ba,Babanta Kadai suke haduwa dashi in ya fito da safe zai Tafi kasuwa don yanzu yakoma cikin kasuwa da sana"arsa Ssnadin gadanga don shi ya siyamai shago ya koma chan,yanzu hankali mallam lawal akwance yake,Domin Ramatu dai bata da wanda zatayi Fitina dashi Azeema ce kuma ta barmata gidan,daga ita sai yarta suci wainarsu babu babbaka.
Azeeza kuwa Duk iya tsawon kwanakin bata taba Sarara ma kanta da Tunanin mafita ba,tabuga ta buga ammh tagagara samun wata hanyar da zata cima nasara Adaren lahadi zuciyarta tagama yanke shawaran data ke ganin tabbas ita tafi dacewa kafin tafara zartar da komai,so take ta Fara lalata Auren Azeema Tukunnah ta yadda babu wanda zai zargeta da aikata hakan.
*Monday*
Monday Tushen Aiki ko bature na tsoron zuwanki,Yau Su goggo su dan makara tashi,kuma yau din ne Azeema zata koma mkranta,koda ta Shirya har 7:30am ta wuce Shiyasa kawai ta dauki jakarta tana cema goggo ta wuce,fada goggo tafara yi tana fadin ya zata tafi bata karya ba,maza ta tsaya ko Ruwan Shayi ta sha,Tura baki Azeema keyi tana fadin"Allah goggo na makara.."Fifitamata shayin goggo keyi Tanafadin"To sai me,yanzu zaki isa ni zan Rakaki har mkrantan in Tsoron duka kikeyi bamai tabaki kina matar soja..'Yar dariya Azeema tayi kafin tayi mgana Sukaji sallama suka karba atare,Daga labulen dakin akayi Azeeza ta bayyana itama jikinta sanye da kayan mkranta ga jakarta ahannu,daga Azeema har goggo da kallon mamaki suka bita,itako sunkuyar dakai tayi kafin tasaka gwiwowinta akasa Tana fadin"Don Allah Adda Azeema kiyi hakuri ki yafemin Duk Abunda nayi miki,wlh Sharrin shedan ne,Ke yar"uwatace danafi so fiye da komai Arayuwata duk inna ce,take zugani ina miki Rashin kunya,ammh bada son Raina bane,ammh yanzu na Tuba,wlh bazan kara jin zugan inna ba,don Allah kiyafemin...",Tafada tana fashewa da kuka,Kallon Goggo Azeema tayi itakuma ta gyada mata kai,da hanzari ta isa ga Azeeza ta dagota ta Rumgumeta tana fadin"Shiiii..Kidaina kuka Azeeza na yafemiki dama bantaba rikeki Araina ba,Na yadda shedan ne yakeso ya raba tsakaninmu..Bakomai Allah yayafemana gabadaya.."Lamo Azeeza tayi tana wani dan mirmishi kafin ta dago tana fadin"Duk inna..."Shiiii...Kiyu Shuru hakanan ma,karki manta inna fa mahaifiyarkice fata kawai zakimata Allah yasa ta gane itama.."
Azeeza wajen Goggo Ta nufa itama ta duka tana rokonta dagota goggo tayi tana fadin"Dukkanku ya"yana ne,babu wanda na ware acikinku,Allah ya hada kanku.."Suka amsa da Amin nan fa su Azeeza aka share kafa akayi kari mai lafiya kafin goggo ta rakasu zuwa bakin Titi su hau Daidaita Dari biyar Goggo taba Azeema tace suyi kudin Abun haawa zuwa da dawowa sauran kuma suyi kudin Tara dashi,murna sosai sukayi suna ta mata godiya har suka kulema ganinta tana Faman daga musu hannu,acikin keken napep din ma sai Hira Azeeza kema Azeema itako dayake bata da yawan mgana mirmishi kawai take mata sai ko eh ko A"a..Azeeza bata damu ba,dama komai sai Abun Ahankali juyawa tayi tana kallon gefen Hanya kafin tayi wani bazawarin mirmishi tace" Dis is juz d begining..Yanzu wasan ya fara Adda Azeema kinyi kuskure babba wajen yarda dani ganinan zuwa cikin Rayuwarki domin na wargazata...",Tafada tana cije baki har saida Taji zafi alebenta.
*Comment,share,and vote...*
*Janafty...,*
*ALIYU GADANGA..!*
_(The Story of Young Soldier man)_
*Wattpad:Janafnancy12*
_Mallakar:Janafty💖_
*DEDICATED TO MY MOMMAH...HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*
_Special gift to my Real Dota RAHMA😘Ladingo yar mutan Niger_
*Intelligent Writers Association*✏
*I dash d whole page for u my Rival..👭...HUWAILATU😂😜popular Name MISS ZERK..ga page dinki nan,karki wani damu Ana tare,dama aie Abun Uwargida na Amarsu ne.....*😂😂
*Chapter 13*
---------------------Rayuwa Tana ta gudu kamar yadda muke cinye Lokaciinmu da kwanakinmu Aduniya,suke gangara suna Neman karewa,masu imani ne da masu tunawa da zasu mutu kadai suke Shiga Tashin hankali in suka Tuna hakan,ammh akasin haka ko ajikinsu To hakan ce Tafaru da Azeeza Domin koda da wayewar gari, bata taba Nadamar ko jin Abunda take Shirin Aikatawa baida kyau ba,ko taji zuciyarta ba dadi in Tayi Tuni da Cewa Azeema yar"uwanta ce.
Duk wata hanya da Azeeza zatabi ta Shigema Azeema da goggo tayi,yanzu sun bata dukkan Amanna,gidan take Wuni,sai dare take komawa gida,tare suke komai da Azeema kamar wasu yan biyu,inna Ramatu kamar ta dora hannu aka ta kurma ihu,Saboda sabbin halin Azeeza tafito dashi shiko Mallam lawal Abun yayi Mai dadi don Azeeza tazo ta rokeshi gafara kuma ya yafemata Yana ta sakamata albarka,Inna Ramatu Abun ya Daure mata kai sosai kuma tayi tambayan Duniyan nan Azeeza tayi mata banza bata mata wani bayani ba,kuma bata yarda ta fadamata Abun da ke Ranta ba ko alama daga ita sai Allah kadai suka san Abunda ta binne Aranta.
Duk Zuwan da Azeeza take gidan goggo bata taba katarin,ganin Azeema Shashen na yaya captain ba,wanda Abunda take ta jira kenan,kullum sai dai su Tare dakin goggo susha hiransu,yau dai kam Tayi sa"a domin tana Rafka sallama atsakar gidan Azeema ta daga labulen Shashen gadanga tana fadin"Azeeza Shigo nan.."Tafada kai tsaye tana mata mirmishi Ran Azeeza yayi sanyi jikinta na Rawa ta nufi Dakin Tana washe baki,bude mata kofar Azeema tayi tana fadin"Yau goggo barci ke cinta,Har na dawo,bata sani ba shiyasa na Shigo nan don kar na dameta.."Dariyan yake Azeeza tayi tana fadin,"eh gaskiya ne..."Tafada tana bin makeken falon da kallo,wanda yaji lafiyayyun Royal chair,idonta wurgawa kawai yake tana karema Falon kallo,Azeema ce ta Kalleta tace"Zauna Azeeza bari na kawo miki Ruwa kinci Abinci? tatambayeta girgizamata kai Azeeza tayi ta kasa mgana saboda wani hoton gadanga data gani bisa wani tebur din glass,dake chan jikin bango,kyam tayi ma hoton tana kallo,itako Azeema bata lura ba kichen Ta nufa tana Fadin"Bari na dafa miki indomie..Nima ita nagama ci yanzu.."ko jinta Azeeza batayi ba hankalinta yatafi ga hoton Yaya captain,A hoton yana sanye da wasu fararen kayan hatta cambos dinsa fari ne, safa ma haka,acikin wani fili ne akayi hoton kamar dai asansanin horarwa ce,yayi tsalle yana dariya aka dauki hoton,Azeeza saboda shauki batasan sadda ta karisa kusa da hoton ba ta saka hannu ta dauki Frem din tana kallo,hannunta ta sanya tana shafa hoton sai ga Azeema ta fito tana fadin"Yanzu zata nuna na zuba miki,yunwa ba dadi..'Tafada tana karisawa kusa da ita.
Saurin waskewa Azeeza tayi tana fadin"kinga hoton danazo kallo Adda Azeema Allah yaya captain yayi kyau sosai ahoton nan.."Mirmishi Azeema tayi kafin ta amshi hoton tana fadin"Gaskiya yayi kyau kam.."Tafada itama tana kallon hoton kafin ta ijiyeshi inda yake,Talabijin din dake dakin ta kunna tana fadin"Muyi kallo Azeeza mu rage zaman Shuru.."Yake Azeeza tayi kafin tataho ta zauna tana satar kallon bedrooms din dake jere Shuru ya biyo baya Azeema ita hankalinta na wajen kallo yayinda Azeeza ke saka yadda zata fara dakan Ruwan Cikin Azeemar batare data sani ba.
Zuwa chan wata dabara ya taso mata sai tayi Farat tace"Adda Azeema nace ba..",Dagowa Azeema tayi kafin tace"mekike son Fadane Azeeza..? Yar dariya Azeeza tayi kafin tace"Wai nace yaushe yaya captain zai dawo ne..? Kai tsaye Azeema tace"Wlh bansani ba Azeeza..",Wani sanyi ya Shiga zuciyar Azeeza murna ya cikata sai ta barsa,lokaci daya ta bata rai Tana fadin"Toh meyasa Adda? bakwa waya ne.."?Jin Abunda Azeeza tacene ya sata Dagota kanta tama Azeeza kuri da ido,sai taji kunyan cewa basa waya..Cikin in ina tace"Eh..Armm..Munayi mana..'Tafada kafin tayi zaraf ta mike tana fadin"Bari na dubo miki,kila yanzu Ta isa yi.."Tafada kafin ta fada kichen,Tana Shiga Azeeza ta buga kafa tana fadin"yes...Komai na tafiya kan Tsari.."Take fada tana dariya Sai ga Azeema ta fito dauke da filet wanda ta zubo indomie aciki sai Lemon cway data daukomata ta kawomata nan Azeeza Ta share kafa ta warba tana ma Azeema hira wanda Rabin hira duk na dakan Ruwan cikinta ne,itako Azeema bata ma iya maida mata amsa sai dai tayi mirmishi ko ta gyada kai,wai Azeeza harda tambayanta ya lbrin Ni"ima Saboda mamaki sai da Ta bude baki tana kallonta,harda cemata wai ta mike tsaye don tagane yaya captain haryanzu yana Son Ni"imar,Rike baki Azeema tayi tana auna kankantar shekarun Azeeza ammh tana mganar manya,sai kuma mganar data Fada ta tsaya mata arai...Sam bataji dadin Jin Abunda Azeezar ta fada akan Yaya captain yana Son Ni"ima haryanzu ba, Batasan dalili ba,sai taji duk zuciyarta babu dadi..Lura da haka da Azeeza tayi sai tayimata sallama takoma gida ammh Ranta Fes Domin tayi hakane ta tusama Azeema tsanar yaya captain koma tana Sonshi ta cire Tunda zuciyarsa na ga wata..Kuma taga alamun Nasara kodaga yadda Azeema tachanza Tun lokacin dataji mganar...
________________
Ta Sauka daga keken napep kenan Tabashi kudinshi Ta nufo kofar gidan Kamar a Mafarki taga wani kamar gadanga zaune bisa bayan motarshi Jabir na tsaye agefe,dukkansu suna sanye da Riga da wando,wandon blue ne sai Rigar Farace kafafunsu sanye cikin booth,Kowannensu hannushi dauke da wani ubansu agogon Fata na kamfanin Rado,Fuskarsu cike da Annuri,Hannayensu dauke da gorunan Ruwa suna kurba,Da hanzari Goggo ta karisa Gadanga ne ya fara hangota da hanzari ya diro daga motar yana cema Jabir"Ga goggo chan ta dawo.."Yafada yana karisawa gareta,Maida kallonsa Jabir yayi inda goggo ke tahowa tana ta washe baki,dariya yayi yabi bayan Gadanga..
Suna karisowa goggo Ta Rumgume gadanga tana fadin"Oyoyo gadanga..Kai ammh kai ja"irin yaro ne ka iya zuwan da Annabi ya hana..Au tare ma kuke da jabiru kai marabanku da bakin sassafe.."Ta fada tana Sakin Gadanga takamo hannu jabir wanda ya duka yana gaisheta Fuskarsa Gadanga ba walwala yace"Wai goggo daga ina kikene da wannan Farar safiyan..",? Bata Fuska tayi kafin tace"ya'yana na Raka mkranta sun makara suna Tsoron duka,shine naje mkranta na fadamusu basu da hankali ne,matar auren zasu daka,kuma ma matar Auren matar soja,Aliyu gadanga.."Tafada kai tsaye ko ajikinta galala Gadanga yake kallonta kafin yace"Wasu ya"yan naki..? asakarce goggo ta kalleshi don ta gane tambayan Rainin wayau yayi mata,kauda kai tayi kafin tace"Matarka Azeema da kanwarta Azeeza ko ba ya"yana bane..? tafada tana zubamai ido,Bata Fuska gadanga yayi kamar zaiyi kuka,Tsaki goggo taja kafin tace"Ohon maka kabar wani tabe Fuska kamar kaga kashi,ni wlh al"amarinka wani lokaci na ban mamaki,bansan wakake tabema Fuska ba,mganata ko ni din kaina..? dariya ta kwacema Jabir yace"kai goggo ya"za'ayi ya tabe miki Fuska,kila mganar ne bataimai dadi ba..'Yafada yana kallon gadanga Ta wutsiyar ido wanda yayi gaba yana fadin",Don Allah goggo kibar wannan mganar juz open d door.."Harara Ta zabgamai kafin tace"Alqur"an Sai ka fasasara mai kace daga karshe,kasan dai na hanaka juyamin yare ko"Ta fada a fusace,dariya ta kullema Jabir ciki yace"Goggo cewa fa yayi ki bude kofar.."Dariya goggo tayi kafin tace"oh yanzu nagane,nima fa da inajin Turancin nan miyar kuka ne suka danneshi wlh,ammh da in na Fara Turanceku harshi gadanga sai na kureshi.."Ta fada tana bude kofar gidan wanda ta samai kwado sanda zata Fita,Dariya takama Aliyu,sai dai ya share Shiko Jabir harda kaiwa kaasa saboda dariya,Aliyu ne ma ya kwashi jakukkunansu ya Shiga dasu Kafin yakoma ya Shigar da mota gareji,Shiko Jabir yana chan wajen goggo yana janta da hira suna dariya datace zata dora musu girki cewa sukayi akoshe suke..Komawa goggo tayi ta zauna Aranta tana fadin"Dama banyi niyyah ba,kwaci kaniyarku don Ni ina da Sauran dan wake na najiya wanda Azeema tayimana.."tafada Aranta tana mirmishin mugunta,tunda ta lura daga gadanga har abokin nasa yan Air ne,komai sai sun Tsara suke aiwatarwa.
Shiko Aliyu yana Shiga Sashensa Abunda ya bashi mamaki abude ya gani bai kawo komai Aransa ba,sai ya ce kila goggoce ta bude don tagyaramai ammh sai mai ko"ina tas sai tashin kamshi,ga remot kan kujera ga Talabijin akunne,bai gama mamaki ba sai da ya leka kichen yaga komai net..Ga kuloli nan da alamu ba"a dade da wankesu ba,baki ya rike yana Tunani ko goggo ta dawo shashenshi da kwana ne,don ya san zata aika,Da hanzari ya fice zuwa dakin goggo suna tsaka da hira da jabir ya Fado yana Fadin"goggo chan Shashen kika koma da zama kuma? akarkace goggo ta kalleshi kafin tace"me..?meka gani hala.."yace"alamun mutum na Rayuwa awajen..'tsaki goggo taja kan tace"ji wata tambayar banza,dama da mutum mana,ka manta ka ijiye mata...Toh Azeema ce ke zaune aciki..'Tafada kai tsaye tana Hararanaa,Tsaye yayi yana zare ido,don shifa ya manta da wata Azeema balle har ya Tuna da Abunda ya faru dafe kai yayi kafin yace"Toh goggo miye laifin barayinki,naga dai kema kina da dakuna.."goggo tace"Eh na saukan baki ba,ammh ba wajen ijiye matar gadanga ba,.."Tafada tana kallonsa,yanajin Abunda goggo tace yafice saboda yasan halin goggo ta kan wannan mganar sai ta maida Abun ya zama babba,yana Fita jabir ke tambayan goggo dama Azeema tatarene,nan fa goggo ta gyara zama ta kwashe From A to z bata rage komai ba.mamaki yakama jabir don ko kadan Aliyu bai Fadamai ba Fatan Alheri yayi musu da Fatan zama lafiya.
Shiko Aliyu saboda bacin Rai waje yakoma ya zauna akofar gida yana latsa latsen waya saboda Haushi,yasan Halin goggo tsaf zatamai tas agaban Jabir shikuma ya samu Abun Tsokanarshi,shiyasa ya fice daga gidan ko Ransa zaiyi sanyi,yafi awa biyu har aka kira sallar azahar yatafi massllaci yayi achan suka hadu da jabir suka dawo Tare nan kofar gidan sukaci burki Aliyu Daure Fuska yayi saboda ya riga yaasan Goggo ta fadamai komai Saboda bakin goggo fa Sikat ne yariga ya santa Sarai Shiyaasa yasha kunu kallonsa jabir yayi kafin yace"Kai Dude ashe Azeema tatare,Toh yanzu ina zan Dinga sauka Tunda yanzu kayi iyali.."Kai Tsaye Aliyu yacemai"Nima Tunanin danakeyi kenan,gwara na saman maka wani waje don bazan iya hadaka shashe daya da iyalaina ba.."kallonsa Jabir yayi kafin yace"Kan ubanchan,yo meye Nufinka bunsuru ka maidani..Toh kona ina akuyanci bazan bi iyalinka ba.."Ko kallonsa Aliyu bai yi ba yace"Kaji dashi dai."Jabir yace"Muji dashi dai,Wai Dude ya mganar zuwa wajen yarinyar nan kafa san don ita nazo garin nan.."wani kallo Aliyu ya watsamai kafin yace"Dama ni kake jira na rakaka..? gyada mai kai yayi dan mirmishi Aliyu yayi kafin yace"U are not Serious,Tunkan dare yayi maka mallam kanemi mai rakaka,Ban da kana ajawo gaja harwata budurwace zaku hadu awaya kafara Dating dinta kuma wai harda zuwa zaka wajenta,toh bada niba Allah kiyaye hanya.."Yafada yana buga kafadanshi.
hararansa Jabir yayi kafin yace"Toh ina Ruwan mutum..Karkaje kar Allah yasa ka rakani nima ba bako bane a gombe,mganar budurwata kuma ka iya bakinka don daga yanayin muryata nagane cewa babbyn Ta hadu wLh.."Dariya Aliyu ya fashe dashi kafin yace"Allah mazaje.Toh anjuma ka Shirya muje sai na ganta."Riko kafadansa yayi kafin yace"Da gaske Dude.."gyadamai kai yayi Alamar da gaske ne,Hannu jabir ya bashi suka kashe kafin yace"Tanque Dude...,"Bakomai yima kaine ai.."gadanga yafada Saurin mikewa Jabir yayi yana Fadin"bari na kirata nabata Suprise kasan bata san na Shigo gombe Ba.."Kallonsa kawai Aliyu yayi kafin yace"yakamata mr love.."ya fada yana bin Jabir din da kallo yadda ya wani rabe gefe yana rage murya girgiza kai kawai Aliyu yayi yana tsausayawama Jabir don ya shiga tsaka mai wuya kafara soyayyah da wacce baka taba gani ba.
Yana nan zaune yana latsa wayarsa yaji karan mashin agabansa,kamar zai Share sai kuma yaji ya kasa yana dagowa yayi mugun gani Azeema ce da Azeeza sukayi 2parking kuma Azeema ce a tsakiya ga Azeeza nada jiki duk ta cinye wajen Shiyasa aka matse Azeema ajikin mai mashin,kutumar ubanchan Galala Aliyu yayi yana kallon yadda kirjin Azeema ya manne da bayan mai mashin,Azeeza data Fara sauka ta gefen ido ta kallon Aliyu tana ganin yadda kacokan hankalinsa yana ga bin Azeema da wani kallo,Addu"a take aranta Allah yasa yazo ya mareta,domin Tun asaman layi Azeema taso su sauka Azeeza ta hana kamar ta sani suna shaho kwanar layin tahangi jabir,kafin ta hangi yaya captain da gayyah takara matse Azeema ta kara hadewa damai mashin kuma taki yarda asaukesu ko"ina sai kofar gidan goggo,itako Azeema bata lura da Abunda ke Faruwa ba ta dirko daga kan mashin tana laluban jakarta zata dauko kudi,daga bayanta taji ance"kai..."gabadayansu suka waiga har mai mashin din,yana tsaye ya harde hannuwansa bisa kirji da hannu ya nuna mai mashin din kafin yace"kai..Come here,karka bari nazo domin Abun bazai yi kyau ba.."
galala mai mashin din ke kallon Aliyu kafn yace",Kai mallam dawo Natsuwarka domin ni bakaga nayi kama da lusarin Namiji ba,anki azo din zokayi Abunda zakayi don uwarka..."Jin Abunda yacene ya kusa saka Azeema Fitsari awando,saboda tsoro baya taja kafin tace"Armmm...Yayan mune fa mallam..,"Tafada bakinta na Rawa shiko Aliyu mamaki ya daskaran dashi,saboda jin kai tsaye wani banza ya zaganmai uwa Takowa ya farayi yana kallon mai mashin din yana wani cije baki,ganin haka yasa Azeeza Saurin Rumgume Azeema tana fadin"wayyo Adda Azeema kibama yaya captain hakuri,sai da nace mudaina hawa mashin ammh kullum sai kice sa mun hau ai ga irinta nan.."Wani banzan kallo Aliyu yabi Azeema dashi ashe bata da hankali bai sani ba,duk duniya babu Abunda ya tsana irin yaga mace ta hau mashin koda ita kadai,wato ita saboda taceewa su biyu suke hawa saboda wulakanci ko,yau zai koyamata hankali,shikuma mai mashin din daga yau bazai kara Dauka wata mace ba sai dai ko in matarshi ce.
Itako Azeema mamakin Azeeza ne ya cikata,ita yaushe take cewa su hau mashin sau biyu fa suka taba hawa,yau din ma babu abun hawa ne,wannan din ma dakyar suka samu Shiyasa suka hau su biyu,ammh ji Abunda take fada,bata samu zarafin mgana saboda yadda gadanga ke hararanta yana jifanta wani dirty look,itako Azeeza bayan Azeema takoma tana leke Farinciki Duk ya cikata burinta daya yanzu Shine Ya kifkifama Azeemar mari.
*Comment share,vote...*
*Janafty...*
*ALIYU GADANGA..!*
_(The Story of Young Soldier man)_
*Wattpad:Janafnancy12*
_Mallakar:Janafty💖_
*DEDICATED TO MY MOMMAH...HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*
_Special gift to my Real Dota RAHMA😘Ladingo yar mutan Niger_
*Intelligent Writers Association*✏
*I Dedicated dis page to u guyzs KHADIJA CANDY NOVELS..(mama)❤,BENEFICIAL WRITERS💕,JANAF NOVELLA 💖1and2,ALIYU GADANGA FANS 1,2,3 and REAL LADINGO FANS😘 Tanque all For u Hot comments Sakallahu Filjannah HABIBATIES*😍
*Chapter 14*
Yana karisawa kusa da mai mashin din ya dunkule hannu ya tokare mai hanci da baki lokaci daya yasaka hannu ya matsemai baki,jinin daya Fito daga bakinsa da hancinsa sai da ya sashi ya hadiye kafin ya sakeshi,baya yayi kamar zai Fadi saboda yadda yaji kansa yayi Aliyu yasaka hannu ya taroshi yana fadin"mekace ne dazu? dan maimaitamin banji dakyau ba..."Yafada yana kallonsa,mai mashin daya sha wuya yakalli Fuskar gadanga zuwa hannunsa yaga yadda Naman jikinsa ke jida saboda Fushi ai bakinsa na Rawa yace"ban..bance komai ba yallabai.."Wani killer smile Aliyu yayi kafin yace,"Next time kakara dauko mace daya ma,ba biyu ba zaka ga yadda zanyi dakai.."mai mashin yace"Bama zan kara dauka ba yallabai wlh maza kawai zan koma dauka.."good.."inji Aliyu kafin yajuya yana Fadin"oya Sauka daga kan mashin dinka ka dauketa bisa kanka karka sauke har saika bar layin nan.."Sororo mai mashin yayi Tsawa ya dakamai ai da gudun hanzari ya daga mashin din da hannu bibbiyu ya wuce yana waige Jabir dake gefe yana waya Tikar dariya kawai yake,yana ba budurwan Nasa lbrin Abunda ke faruwa,su ko su Azeema Tuni suka Shige gidan goggo suna Rawan jiki,Da goggo ta tambayesu Azeema kasa mgana Tayi Azeeza ce ta maida bayani Yadda akayi Dariya goggo tayi tana fadin"Banda Abun gadanga miye na Sauke Fushin kan mai mashin,.."Abun yaba Azeeza mamaki yadda lbrin yaba goggo Nishadi,suna cikin maida mganar ne sai gadanga ya shigo yana Shigowa kai tsaye Azeema ya nufa sai da yazo gabanta kafin yace"Ke..."Dago kanta tayi kafin tayi Saurin sadda kai,Nunata yayi dayatsa yana fadin"ke babban banza ce ashe bansani ba,..To dis one wil be d last time dazanganki bisa mashin din wani kato,daga yau ki dinga hawan Keken Napep tunda na lura sakarcin naki gaba yake ba baya ba.."Yafada kafin ya juya,Galala goggo tayi tana kallonsa itako Azeeza kamar ta kurma ihu saboda murna baki goggo ta rike kafin tace"toh wayace maka Azeema na hawa mashin,Toh na tabbata rashin Abun hawa ne,bata da zabi ammh Azeema bata hawa mashi yo Allah na tuba inamatake zuwa balle ta dinga hawa mashin..."Cak ya tsaya kafin ya waigo yana kallon Azeema yadda take kuka hawayenta na diga Tsausayinta ya kamashi maida kallonsa yayi kan Azeeza nan da nan Tayi wiki wiki da ido tsuramata ido yayi yana nazarinta,itako Tuni jikinta yahau mazari Abunka ga mara gaskiya,takowa yayi zuwa gabanta yana karemata kallo kafin yace"Ke..."Dago kanta tayi tana wani kifta ido matse goshi yayi kafin yace"Ni sa"an wasanki ne.. ? Shuru tayi tana Raba ido tsawa ya dakamata kafin yace"Nace ni sa"an wasanki ne..? da sauri Azeeza ta girgiza kai tana ja da baya,Wani tsawan ya dakamata kafin yace"Oya get out..Wannan yarinya wlh idonta na kama dana mayu,"Yafada yana kallon goggo ai da hanzari Azeeza ta fice ko waigo dariya takama goggo sai da dara gimtse Fuska Aliyu yayi kafin yace"Wai don Allah goggo meyasa kika sakarma wannan yarinyar Fuska ne,nifa banyarda da ita ba sam,idonta namin kama da na munafukai ne wlh.."Rausayar dakai Goggo tayi kafin tace"Toh mai gani hanji kai kowa bai maka ba,toh ko dole ka sota Tunda kana Auren yayarta.."baiyi mgana ba kawai ya fice cike da takaichin yadda goggo takasa Fahimtarsa sai yana ji ajkinsa tamkar yarinyar Tafi Azeema iya Duniyanci da wayau bayaso wani Abu yafaru agaba...
Goggo ita tayita lallashin Azeema har tayi Shuru ammh takasa daina jin Haushin kanta da mamakin Azeeza,itako Azeeza kwana tayi takaichi da bakinciki domin yaya captain yazo ya Rusata mata komai ammh ba komai yanzu tasaka kafa babu gudu babu ja da baya,bayan mangariba Jabir ya shirya Shida gadanga suka wuce Gra domin haduwa da budurwan ta jabir wacce suka hadu ta waya,ba laifi yarinyar tana da hankali da kunya babanta dan kasuwa ne,yarinyace bazata wuce sa"an Azeemar ba itama SS2 take a babban sakandiri Abun na jabir yaba Aliyu mamaki yadda yaga yana wani Rawan kafa agaban yarinya saboda Haushi mota yakoma yana game awaya Don yaga lalacewar na Jabir yayi yawa.
..
Sai pas ten suka dawo,koda suka dawo Goggo da diyarta tuni sun dade da kulle shashensu Sun kwanta suma basu bi ta kansu ba Aliyu ya kargame kofar gida suka fada shashenshi domin kwanciya,Abunda yabama Aliyu mamaki Jabir suna shirin kwanciya ya dasa waya da yarinyarnan kamar wani namamajo Ko gajiya basuyi Haushi yakama Aliyu ya fice daga dakin ya Shiga dayan bedroom din ya kwanta,nan yaga kayan Azeema da kayan kwalliyarta wadanda goggo ta siyamata,tsayawa yayi yana kallon kayan yana wani Tunanin yama Rasa ta ina xai Fara Taimakama rayuwar yarinyar don ya lura tana bukatar wani akusa da ita,Bata da sakewa ko kadan,bata da sani kan komai,shibaima san meke damunta ba,kullum kai asunkuye ko kuma ka ganta tana kuka,ada yana tsausayama kansa na Rashin cikakken Asali ammh yanzu yafi tsausayama Azeema Domin ita tana da uban ammh maraici da rayuwar Rashin yanci ya dabaibaye Rayuwarta uwa uba bata taso tare da kowa ba,Shiyasa wautarta tayi yawa,kwana yayi yana Tunanin mafita da yadda zai bulloma al"amarin.
***************
Washegari da Safe da wuri Azeema ta Shirya domin wucewa mkranta Bayan ta karya ta zauna tai zuru tana jiran ko Azeeza zata biyo mata su Tafi ammh Shuru goggo na lura da ita bata dai mata mgana bane ta tsayane taga iya Gudun Ruwanta zata fasa zuwa mkrantan ne saboda Azeeza bata biyomata ba ko yaya ne? Tana nan zaune Aliyu yayi sallama ya Shigo dakin goggo jallabiya Mai Ruwan Tokace ajikinsa,Tanajin sallamasa tayu zumbur ta mike tana mazurai Sau daya ya kalleta yakauda kai kusa da goggo ya isa yazauna ya gaisheta amsawa yayi yana Riko hannunta Da hanzari Azeema ta duka tana gaisheshi a dakile ya amsa kafin ya kalleta yace"Goggo metake jira bata tafi mkranta ba 7:30 fa ya wuce.."Kallonta goggo tayi kafin tace"Yauwa gwanda da Allah ya kawo ka gatanan,tambayeta nima Tundazu naga ta Shirya ammh ta nemi waje ta zauna bansan metake jira ba.."Sunkuyar dakai Azeema tayi Aliyu zai yi mgana kenan Jabir ya Shigo dakin Shima yana Sanye da jallabiya baka yana ganin Azeema ya washe baki yana Fadin"Ah ZEEMA kin tashi lafiya.."Dan Rankwafawa tayi tana gaisheshi Ansawa yayi cikin sakin Fuska yana fadin"Lafiya lau Zeema ya mkranta hop dai ana maida hankali.."Gyada kai tayi cikin kunya Gadanga dake zaune yayi Wuf ya mike yana fadin"Ke muje.."fuska ba walwala kallonsa jabir yayi kafin yace,"Toh miye nawani cewa kuje naganeka bakin ciki kake don ta dan Rankwafa dazata gaidani ko? hararansa Aliyu yayi kafin yace"Eh.."Adakile Akarkace Jabir ke kallonsa kafin yace"Dalili..? ko kallonsa Aliyu bai yi ba yabi bayan Azeema data fice da Sauri har zai Fice ta waigo yana fadin"kaji dan Rainin wayau ni dana rakaka zence jiya Budurwanka tama gaisheni ne,kunata rawan kafa ko Tunawa dani ai bakayi ba.."Yafada yana dariyan keta kafin ya fice Baki Jabir yakama lokaci daya yana Sosa kai goggo dake zaune gefe tace"Au zence kukaje jiya ko? to ai Allah yakamaku ja"irai.."tafada Tana dariya Sosa kai kawai jabir yake kafin yayi Wuf yafice yana fadin"Goggo ma gaisa da Rana."Yar dariya goggo ta sakeyi kafin tace"kai Jabiru da gadanga bansan wanda yafi wani Shegantakaba.."Take fada kan tatashi ta fada kichen domin ta kwaso musu Abun karinsu.
shiko Aliyu Tiryan Tiryan yake bin Azeema abaya suka fita daga gidan har zuwa bakin Titi kanzil bai cemata ba,itako tsoro yahanata ko waigo Suna zuwa ya taran mata wani dan adaidaita suka gaisa cikin mutumci kafin yadan duka sukayi mgana,ya fadamai ne Nawa zai Dinga biyansa yana zuwa yana dauka Azeema kullum yakaita mkranta ya dawo da ita,nan mai Adaidaita yace ya yarda buh ammh sai dai yafison adinga biyanshi Duk sati saboda halin Rayuwa..Nan take gadanga ya amince yace yakaita ya dawo sai suyi mgana bayan ya nunamai gidan da in yakaita zaizo ya sameshi,baya yayi yana kallonta kafin yace"oya ki Shiga yakaiki.."tsam tayi kafin tafara waige waige lura da hakan dayayine yasa shima ya waiga yana fadin"wakike nema..? bakinta na rawa tace"Az...Azeza.."bata Fuska yayi kafin yace"Wai Shin tsaya na tambayeki Azeezar nan ita ta haifeki ne? kokuwa dai ke Sakarcin ki haryanzu bai nuna miki kina zubar da kanki bane come get in kafin ki bani haushi.."dago kanta Azeema tayi idonta sun ciko da hawaye kafin taji kawai taji baki ya bude tace"Ban da kowa fa,ita kadai ce wacce zan daki kirji na nunata amtsayin yar"uwanta ba sakarci bane yaya captain kulafuncin yanuwantakane..",Tafada hawaye suna gangaromata,kuramata ido yayi baisan dalili ba,sai yaji kalamanta sun sanyarmai da jiki kallonta yake cike da tsausayi kafin ya jinjina kai yace"it ok wipe ur tears..Kije kidawo daga mkranta zamuyi mgana kinji.."yafada cikin sanyin murya gyada kai tayi tana Share hawaye kafin ta shiga adaidaita din Hannu ya sa aljihu ya ciro 1k yamikamata kin amswa tayi illah nuna mishi Hannunta datayi tana fadin"Goggo ta bani.."Kallonta yayi yadda idonta suka cika da ruwa sam baiji dadi ba juyawa yayi yana fadin"Ok Tunda kinfi son ta ringa baki da hannunta zan barmata sai ta baki..Take care of u self.."Mirmishi kawai tayi tana bin bayanshi da kallo har suka bacema ganinshi,har takai mkranta tana Tunanin yaya captain ita kadai sai sakin mirmishi take in ta tuna da wani Abun.
Itako Azeeza bata hakura ba Domin Tana Shiryawa tana Fitowa daga gida tazo gidan goggo,daga kofar gida ta tsaya ta faman leke,hango yaya captain tayi ya fito tsakar gida yana waya bayi da riga dagashi sai dogon wando gabadaya Sirrin jikinsa ya bayyana awaje,Azeeza dake labe Tuni taji ta manne da bango saboda shauki kirjinsa ta kurma ido lokaci daya tana wani lashe baki tama manta damai tazo yi Shiko yajuya baya ta jikin kofar goggo ya hango Azeeza ta leke bayan yajuyamata baya dayake kofar tanada glass daga samanta ne,mamaki yacikasa bai yanke wayar ba ya juyo yafara taku zuwa wajen yanayi yana dan kallon gefe Azeeza batama Fahimci cewa gadanga ya taho ba daga kanta kawai taji ance"Ke..."Cikin tsawa firgigit tayi saboda razana tasaka kafa zata zura da gudu gadanga yayi Wuf ya riko hijabinta yajawo ta baya ya watsar da shegiya kasa yana binta da wani banzan kallo,ammh mayyar hankalinta naga kan Suran jikinsa tana wani kifkifta ido nunata yayi kafin yace"ke ubanwa kike nema da kike ma Mutane labe..? bakinta na rawa tace"Adda Azeema.."tabe baki yayi kafin yace,"Oh yanzu kikasan da Adda Azeemar yaushema ta zama Addarki mara mutumci,ke nifa ban ma yarda dake ba gayamin waya Turoki ko Uwarkice taturo kizo ki cutar da Azeema..? yafada yana dukawa daf da ita baya Azeeza taja tafara tsorata da yaya captain din tsawa ya dakamata yana fadin"Zaki gayamin kokuwa sai na Fasa kanki da bindiga.."Jin zencen bindiga yasa Azeeza Saurin cewa"Armmm..A"a ba wanda ya Turoni.."Tafada idonta kyam akan kirjinsa sai alokacin ya fahimci inda idonta ke kai,mikewa yayi lokaci daya yajefa wayarsa cikin aljihun wandonsa yana jinjina kai yake fadin"Oho Yanzu na ganoki ke ashema ba iya rashin kunya kika tsayaba harda bin maza ko? Saurin girgiza kai tayi zatayi mgana ya dakamata tsawa yace,"Rufe min baki don ubanki zan miki karyane,kina kafe ne da ido kamar kin ga wani tsohon customer dinki ko? shegiyar daga ganin yadda kike kallona tsab aka kyaleki watarana zaki iya zama magajiyar karuwai,wlh tallahi kinji Rantsuwar dan musulmi in nakara kama idonki cikin nawa sai na fito da kwakwalwar kanki,Uselless kawai.."Yafada kan yasa kafa ya shureta yana fadin"Ur way out..Kar in kara ganin kafarki agidan nan.."Yafada yana nunamata kofa da Azama Azeeza tamike zata fice hawaye sun cikamata ido,Harta kusa Fita yace"ke tsaya..,kinga ko Azeema naga wani chanjin dabi"a awajenta ko naji wani lbrin wani Abu yafaru wanda ba halinta ba i swear daga ke har mahaifiyarka karnuka zasuyi watanda da Naman jikinku.."Yafada yana kadamata hannunsa,Azeeza tayi waje da gudu saboda kukan daya tasomata mkrantan data fasa zuwa kenan Inna Ramatu Ganinta kawai tayi ta shigo tana kuka,kuma tayi tambayar Duniyanan ammh Azeeza tayimata banza Kyaleta tayi,Saboda Yanzu kwata kwata tadaina gane kan Azeezar yanzu,itako kuka take da Duk Abunda tashirya sai Yaya captain ya Ruguxamata shirinta Kuka take da takaichi sai taga alamun Nasara sai kuma komai ya kwacemata.
Jabir da Aliyu suna cikin karyawa jabir ya samu waya daga Amminsa tana Fadamai mijin kanwarta dake jos Allah yayimai Rasuwa sakamakon hadarin mota yanzu hakama chan zata wuce yayi kokari yazo ya samu jana"iza Babu ko bata lokaci suna gama karyawa suka Shirya suka kama hanya Aliyu yayima Jabir din rakiya goggo tabisu da Fatan alheri tare da Addu"ar Allah yajikan wanda ya Rasu..Suna tafiya ba dadewa sai ga kawu bala ya zo,dayake ya shigo gombe yazo wani taro ne na Siyasa sai ya biyo nan wajen Suwaibar suka gaisa nan take fadamai yanzu su gadanga suka Dauki hanyar jos,Fatan isa lafiya yayi musu,Nan ya zauna sunata hira har bayan Azahar,har sai da Azeema tadawo mkranta ta tarar dashi,nan goggo ke koramai bayanin Duk Abunda ke Faruwa hakika ya tsausayama Azeema kuma yayi jinjina ga hikimar gadanga nan yayita ma Azeemar Nasiha tare da Shimata albarka da zai Tafi 30k yabama goggo Azeema kuma 10k yabama goggo 10k ta ijiyema mallam lawal saboda bazai iya jiransa har yadawo daga kasuwa ba,sallama sukayi cikin so da kauna tare kewa kafin su dau hanya shida tawagarsu goggo na bada sakon gaisuwa ga Umaima.
Aliyu kwana daya yayi ajos yadawo gombe yabar Jabir achan,shigan yammah yayi don bai shigo gombe ba sai Wajen biyar na yammah koda ya shigo gidan Azeema kadai ya tarar agidan wai goggo batanan Tatafi gidan kakarta Baba Ade bata da lafiya itama wainar Fulawa ta tsaya soyawa Goggo ko tace wlh bazata jirata ba,in tagama tazo daga baya toh tana kichen tana ta Faman Sauri taji shigowar yaya captain gabantane yayanke ya fadi Ras..,Sai da ta dafe saitin zuciyarta dakin goggo ya Shigo yana mamakin jin babu alamun mutum Agidan Motsin dayaji akichen ne yasashi Nufar nan Yana shiga yacikaro da Azeema tana tsaye tana kwashe wainar Fulawan Tsaye yayi yana kallonta itako ganinshi ya sata ta Rude bakinta na Rawa ta Furta.."San..nnu da zuwa.."Yamutsa Fuska yayi kafin yace"Baki amsa sallama ne?ina goggo..? ya jehomata tambayoyi fiki fiki tahau da ido kafin tace"Banji bane,goggo kuma tatafi gidan Baba Ade..."juyawa kawai yayi yana fadin!Taimakeni da Ruwa don Allah.."daga haka yafice daga kichen din.
_Allah yayi ma Rayuwarki Albarka Diyata LADINGO IKON ALLAH...Akullum ina alfahari dake Endless of love Dota_😘
*Comment..And share...*
*Janafty...*
*ALIYU GADANGA..!*
_(The Story of Young Soldier man)_
*Wattpad:Janafnancy12*
_Mallakar:Janafty💖_
*DEDICATED TO MY MOMMAH...HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*
_Special gift to my Real Dota RAHMA😘Ladingo yar mutan Niger_
*Intelligent Writers Association*✏
*Chapter..15*
""Da Sauri ta kwashe wainar Fulawan ta kashe gas din,Fridge ta bude tadaukomai Ruwa mai sanyi sama ta taka tahau ta bude drower din dake kichen ta dauko wani filet mai hade da kofuna da hanxari ta daurayesu ta dora Ruwan bisa kafin ta jeramai kofuna guda 2 Ta nufo Falon tana Faduwar gaba.
Yana Zaune kan daya daga cikin kujerun Falon saboda gajiya ko Takalmin kafansa bai cireba ya kishingida da cussion din kujeran idanunsa alumshe kamar mai barci,Tana isowa falon taja Center Table din dake tsakar dakin Ta dora Ruwan akai,ganin idanunsa alumshe yasa Tamike salaf salaf zata fice taji yace"ok ni kikeso na zuba Ruwan dakaina kenan ko? haka kika ga goggo na min..? kyam ta tsaya tana sauke ajiyar zuciya kafin ta waigo still dai haryanzu idanunsa alumshe suke Tahowa tayi tazo ta durkusa ta Bude Ruwan ta zubamai cikin kofin data hado dashi mikamai tayi tana fadin"ga Ruwan yaya captain.."Bude idanunsa yayi karaf ko suka hada ido,jikinta ne yafara rawa tana neman Mai bari da Ruwa yayi Saurin Amsan Ruwan yana fadin"ke shin wai meke damunki ne?ji yadda kikeneman min barin Ruwa ajiki.."Sunkuyar dakai tayi batayi mgana ba,bai sha Ruwan dayawa ba ya mikamata ta karba Mikewa tayi zata maida Farantin kichen taji yace"Jeki dawo yau dai naji menene mtsalarki.."yafada kai tsaye gabanta ya fadi tayi Saurin kallonshi shima ita yake kallo kauda kai tayi kafin ta Shige kamar zata fadi,bin bayanta yayi da kallo yana Tunanin anya yarinyarnan bata da Shafan Aljanu.
.
Sai da tabata lokaci kafin takoma,ita duk ta tsargu saboda bata da hijabi Sai wata doguwar Rigar Atamfa cikin wanda goggo ta dinkama ne,chan nesa dashi taje tazauna kanta na duke tana wasa da gefen dankwalinta kamar wata yarinya,kallonta yake yana Tunanin wani abu kai tsaye yace mata"Taso ki dawo nan mgana zamuyi kuma ba'a mtsayin mata da miji amtsayin Yaya da kanwa.."jin haka yasa tadago tana kallonsa gyadamata kai yayi alamar tabbatarwa tashi tayi ahankali ta isa kujeran dayake zatayi kasa yayi Saurin riko hannunta yayi ya zaunar da ita agefensa yana fadin"Sit here.."Jikinta ne yahau rawa lokacin da hannunsa yatabi nata balle da kafadanta ke dukan nashi,ganin yadda Ta rudene yasashi dan matswa Shidai baiji komai ba,kodon baisaka Abun aka bane baisani ba.
Yadade yana karema Surarta kallo Azeema ba Farace ammh tana da, hasken Fata sosoi wahalace ta maidata baka Tana da doguwar Fuska mai dauke da kyawawan idanuwa,hancinta bai cika tsawo ba,ammh yadace da kyakyawan Fuskarta tana gashin gira hade dana ido Masu kyau da Tsari bakinta dan karami ne,ammh leben sama yafi na kasa girma da kadan,in ta tsuke bakin sai ya birgeka yakuma baka Sha"awa doguwa ce bata da jiki,ammh tana Fadin kugu da kirji mai kyau kirjinta ba"a cike yake ba,sakamakon nonuwanta basu da wani girma na azo agani ammh Suna tsaye cur dasu,zarazaran yatsun hannunta yakoma yanabi da kallo kawai lokaci daya yaji ya tsaida kallonsa kan dokin wuyanta yadda wasu kananun gashi suka kwanta awajen,cikin kankanin lokaci tsigar jikinsa tafara tashi lumshe manyan idanunsa yayi kafin yakira sunanta.
"AZEEMA...."Cikin Sanyin murya da muradi bata amsa ba,ammh sai tadago tana kallonshi saboda jin muryan dayayi amfani da ita wajen kiranta idanunsa ya bude fess akanta yana kallonta sadda kai tayi kasa kafin ta amsa.
"Na"am..."gyara zama yayi kafin yace"Don Allah tambayanki zanyi waht i want is to tell me,d truth kinji ko.."Gyada mai kai tayi kafin tace"Toh insha Allahu."good yafada kafin yaciga ba da cewa,"Ina so kifadamin hakikanin meke damunki?mekike bukata?me kika nema na Halin Rayuwa kika Rasa Azeema,in mganar Gidanku ne,yanzu kin dawo nan buh ammh har yanzu abubuwanki basa raguwa sai karuwa don Allah kifadamin meye ke damunki kokuma miye matsalarki? kudi? mkranta kikeson achanza miki? kokuwa baki son zama da goggon ne natafi dake kaduna ai zaki zauna abariki ko? Duk Abunda yake fada tanajin sa,wani tsausayin kanta ya kamata tare da Tsausayin yaya captain,jin Abunda yace na karshe ne yasata dago kanta tana mirmishi ammh hawaye sun cikamata ido kai tsaye ta girgiza kai batayi mgana ba,Hade naman goshinsa yayi kafin yace"To meye? kifadamin meke damunki kinganni nan banda yawan mgana i know ahaka halittata take buh ur own Azeema yayi yawa baki da sakewa ko kadan.."Yafada da alamar Abun ya dameshi.
Dago kanta tayi tana kallonsa kafin tace"Hakika in nace nayi rashin wani Abu toh na zama butula babu Abunda na nema na rasa kuma ni babu Abunda ke damuna,in akwai Abunda na Rasa arayuwata abu dayane yaya captain..'kallonta yayi kafin yace"Maza fadamin meyeshi nikuma nayi miki alqawarin mgance miki duk wani Abunda ke damunki.."tadade kanta asunkuye kafin tadago idanunta na fitar da amon hawaye tace muryanta na Fitar da amon kuka.. *UWA...UWA..* ita na rasa yaya captain na rasa uwa wacce zata nunamin banyi daidai ba in gyara! na rasa uwa wacce zatamin fada ko tabani shawaran in wata mtsala ta sameni!,na rasa uwa wacce zan kwanta bisa kafadanta nayi kuka ta lallasheni!na rasa uwa wacce zata kalle ni ta sakamin albarka,duka na rasa wannan yaya captain na taso arayuwata nikadai nake gudanarshi,babana yana Sona ammh tsoron inna ramatu baya barinsa ya kebe dani ballatana har yasan damuwata na kasance duk wani damuwa da zan Shiga sai dai nayi kuka adaki ni kadai na lallashi kaina bani da dan"uwa ko wani Shakiki da zan Fadama damuwata yabani Shawara haka nake rayuwata nikadai,toyaya kewa tare da damuwa bazasu taru sunman yawa ba,ka fadamin yaya captain Tayaya...?Tafada tana Rushewa da kuka kamar zata shide.
Gabadaya kalamanta ya Sakashi jin wani tsabar tsausayinta ya kara mamayeshi kallonta yake tana kuka lokaci daya Shima damuwarshi ta dawo sabuwa,yasani shi mahaifi ya rasa ammh Goggo da kawu bala basu taba bari yayi kukan maraici ba,koda aboye koda asarari ne,itafa bata da kowa ba uwa ba,ba uba mai kula ma dangi ba wani dan"uwa sai da wanda Allah yaduba ya tsausayamata tabbas tafishi jin dacin rashin Abun Aranta fiye da yadda yakejin nashi Aransa.
Saboda tsausayinta baisan sadda ya mika hannu ya rikota ba,ya kwantar da kanta bisa kafadanshi yana bubbuga bayanta yana fadin"shiiiii....am srry kinji Stop Craying i promise i won let u down insha Allahu..."Yake fada yana sharemata hawaye da hannusa,gyara mata zama yayi suna facing din juna yace yana riko hannuta"Yanzu Firstly do u luv me,zaki zauna dani duk da ana ce nidin bani da cikakken asali wasu ma cewa suke bani da uba..? dago kanta tayi tana kallonsa dan hararansa tayi kafin tace"injiwa..? haba dai suma wasa sukeyi.." karkatar dakai yayi yana fadin,"Eh mana ko,kin manta dalilin haka aka hanani Auren Ni"ima Shine ma dalilin dayasa Auren yakoma kanki.."yafada yana cije lebe,kallonsa tayi kafin tace"Kayi hakuri haka Allah ya kaddara itadin ba matarka bace,..Kayi kokarin cire sonta aranka sai kaga komai ya wuce.."Zuru yayimata da ido kafin yace"who told u cewa haryanzu am in luv wit Ni"ima.."Sadda kai tayi taki mgana girgiza hannunta yayi yana fadin"Kiyi mgana waya fadamiki.."Kai tsaye tace"Azeeza ce..."Ware ido yayi kafin yace"Ohh i seee... wato ita ta zaunar dake ta tsaramiki haka,to kila ni nafadamata ko.."?yafada Fuskarsa na chanzawa saurin cewa Azeema tayi"A"a ni batace kai kafadamata b..."Toh meyasa kike yarda da duk Abunda tace miki,kina zaton ita da mahaifiyarta suna kaunarki ne,kinga dole fa in kinaso tamu tazo daya dake Azeema u should learn how to respect ur self,kiwani zauna yarinya karama na zana miki zence kawai don ta maisheki mara wayau.."yafada cikin Fushi Saurin Sadda kai tayi kafin tace"Kayi hakuri baza akara ba.."tafada tana Kwace hannunta ita tsoronta kada ya zuciya ya kaftamata mari.
Sakinta yayi yana fadin"it ok kikiyaye gaba,komai ta tambayeki as From today karki bata wata fuskan da zata sake sanin Sirrinki kina gaba da ita,ita din kanwarki ce so be carefully...'Yafada yana kauda kai shuru tayi tana wasa da hannunta kafin bazato yaji ta jehomai tambayar
"Toh in kadaina son Ni"ima wakake so..? saurin kallonta yayi yana hade naman goshinsa Cike da mamaki saurin sadda kai tayi,cike da kunya Dan dariya yayi kafin yace"Ada nasota lokacin danake Tunanin Ita zatama abokiyar rayuwata buh tun lokacin da mahaifinta yanemi cimin zarafi naji tafita daga Raina,any way kobana sonki Azeema kinada wani babban mtsayi Araina keda mahaifinki domin kun sharemin kasan da mahaifin Ni"ina ya watsamin.."Yafada yana kallonta kur da ido,kallon ne yabata kunya tayi Saurin tashi ta fice waje da gudu,da wani kallo yabita yadda kugunta ke kadawa rausayar dakai yayi yana cije baki,nan take mganar Jabir ta fadomai Aranar da"aka daura musu aure....
_Yarinyar tayi zaka samu duk Abunda kakeso wajen mace,tama fi Ni"imar komai..._Tuna haka dayayi ne yasashi shan mur yana kunkuni shidakai na yadda har jabir yarigashi gano Abunda shi yakamata yafara ganowa.
Azeema na Fita waje tacikaro da goggo daga gefe zaune kan wata kujerar roba dake wajen tana cin gyadanta soyayyiya hankalinta kwance baki Azeema ta rike kafin tace!la..Goggo yaushe kika dawo.."Kallonta tayi kafin tace"Na jima Azeema.."Karisawa Azeema tayi tana fadin"wlh goggo bamuji shigowarki ba.."Goggo tace"Ai bazaku ji ba,na Shigo ina ta rafka sallama har daga makota anajina,harfa leka dakin nayi naga ko barci kike sai na samu ana zantawa tsakanin mata da miji,shine nace toh toh..Bari nayi baya har kugama kada na katseku.."Tafada tana dariya kunya takama Azeema sai ta labe bayan goggo tana yar dariya.
Gyadar goggo ta nunamata tana fadin"kega Abunda baba Ade tabani tace sai kinzo zaki karbi naki.."mikewa Azeema tayi tana fadin"la gyada goggo,yanzu kuwa zan mata dirar makiya sai tabani nawa.."tafada tana fadawa daki,koda ta shigo sai taga kamar gadanga na barci sai ta shige kurya tadauko Abayarta ta fito harta kai kofa zata fita taji ance daga bayanta.."Ina zaki..?"Saurin waigowa tayi still idanunsa na kulle,cewa tayi"Gidan Baba ade zani.."lalle yarinyarnan to ki koma ki cire hijabin sai gobe yanzu yammah tayi.."Ya bata amsa.
Tura baki tayi da jin Abunda yake cewa,bude idanunsa yayi karaf ko suka hada ido dashi ga gudu ta kariswa bedroom din goggo tana dafe kirji,shiko mamakinta ne yacika ashe ta iya tsiwa dama,mirmishi yayi shi kadai kan yamike agajiye ya fice nan waje yaga goggo suka gaisawa alwala ya daura yafita sallar mangariba,itama goggo tayi nata ta shiga ciki tayi sallarta ita da Azeema wacce goggo kema gwalo da dariyan hanata fita da gadanga yayi sai mata kwalelen gyadan takeyi itako duk Haushi ya cikata sai da goggo tagama jan mata rai kana tabata gyadan,shiko gadanga a massallaci ya zauna har akayi issha,"i kafin yakoma gida,kuma bai ma koma barayin goggo ba yashige daki yayi Shirin kwanciya saboda gajiya.
****************
"Oh my god Sweetheart don Allah kibar wannan kukan,bai da wani amfani juz keep praying in Captain mijinki ne,ko duk duniyanan zasu hadu wlh basu isa suhana ba,kuka bai da wani amfani..."Muneera take fada tana Riko Hannun Ni"ima,Share hawayenta Ni"ima tayi kafin ta dago idanunta jajir Tace"Ya zanyi Ya kikeso nayi Sweetheart..Wlh i love Captain Bazan iya hakurin rashinshi ba,bakiji menake fadamiki bane,he told me bazai taba Aureba Sweetheart,yayi Aurensa ya barni."Tafada wasu hawaye suna kwaranyomata, Rumgumeta muneera tayi tana lallashinta tana fadin.
"Nidai ki daina yawan kukan nan Sweetheart..Wlh banijin dadi,insha Allahu captain Sai yazama naki da yardan Allah..."tafada tana bubbuga bayanta Lamo Ni"ima tayi tana Shesshekan kuka ahaka Mami tazo ta samesu Tana tsaye tace"Kingan ta nan Muneera haryanzu kukanta yaki karewa,Ni narasa wannan bala!in,sai kace Aliyun ne, kadai Namiji aduniya ko Rasashi Tamkar rasa rayuwace gabadaya,Allah tun inajin Tsausayinta hartakoma bani Haushi,ai sai kiyita kece keda wahala.."Tafada kafin tafice Cikin Fushi da nuna Abun ya dameta.
Bayanta Ni"ima tabi da kallo hawaye suna kwaranyomata,Zame jikinta tayi ta mike Tafada bedroom dinta tana sharan kwallah,bayanta Muneera tabi da kallo tana mamaki wani irin sone Ni"ima kema Captain data kasa hakura dashi Tunda yayimata nisa,gabadaya ta rame ta dishe ta lallace kamar ba ita ba,Abun nacimata Tuwo akwarya ammh babu yarda zatayi domin hartagaji da ba Ni"imar baki tahakura takoma ta zuramata ido saboda al"amarin nata yawuce duk yadda bawa zaiyi tsammani.
______________
Azeeza ko alama bata ja da baya ba,Abunda yakara bata tsoro ko School Azeema bata nemeta ba Abun ya matukar Dauremata kai,tafara Tunanin kodai ta ganotane ammh duk da haka bata ja baya,ba washegari dataje mkrantar agaban idonta maikeken yazo yayi Dropin din Azeema kuma Abunda kowa bai sani ba Duk motsin Azeemar a idonta domin tana labe akofar gidansu tagazuwam mai keken yazo Daukan Azeema,batayi mamaki ba,tasan kila aikin yaya captain ne,don taga He is very smart yana da Saurin Ramfo mutum tana ganin Azeema ta Shigo cikin mkrantar ta nufi ajinsu sai ta chanza shawara sai tabaro ajinsu ta ratso ta tsakiyar mkranta kamar zata office din Principal nan sukacikaro da Azeema wacce ke kallon Azeezar Tunda daga nesa tasha mur tana kallonta ammh ta kauda mata kai.,Kiran ta Azeema tahauyi ammh Azeeza tayimata banza kamar bataji ba,da hanzari Azeema tatake mata baya da dan gudunta sai gashi tasha gabanta tana fadin"Haba Azeeza mgana fa nike miki ke man banza.."Wani kallo Azeeza ta maka mata kafin ta raba ta gefenta zata wuce,ammh sai Azeema taki bata damar haka Ta hanyar riko hannunta.
Cak Azeeza ta tsaya ammh bata waigo ba,juyo da ita Azeema tayi tana fadin"Wai Azeeza duk miye ya faru ne ? nine fa Addanki Azeema ai yaci komiye nayi miki bai dace nayi mgana acikin mutane ki tsinka ni ba.."Yamutsa Fuska Azeeza tayi kafin tace"Dole na Tsinka Adda Azeema naga kin zabi Namiji,Namijin ma bare akaina,kinga ai sai naja baya.."Ware ido Azeema tayi kafin tace"lala..Injiwane Duk duniyar nan ina da kamarki ne.."Bata Fuska Azeeza tayi kafin tace"ba gashi ba,Tunda har wanda aka lakaba miki amtsayin mijinki ya iya cimana mutumci dagani har ke da baba ba wanda ya ragamawa.."Tafada harda matso kwallah Zuramata ido Azeema tayi kafin tace"Shi yaya captain din? da hanzari Azeeza tace"eh mana Ranar dana biya miki yayi min kaca kaca hardacemin wai daga gani na watarana magajiyar karuwai zan zama..'Takarishe fada harda fashewa da kukan karya.
Baki Azeema ta rike tana kallon Azeeza,Zuciyarta takasa gasgasata,Saboda Duk kalamanta babu gaskiya,ganin haka yasa Azeeza tashiga jerama Azeema rantsuwa hartana fadin yace kema wani Shiri kawai yake akanki da zarar yacinma burinshi zai baki takardanki,nidai don Allah Adda Azeema karki kuskura kiba dan iskan sojan nan kanki saboda bai da wani buri,illah ya maidaake karamar bazawara ya sakeki kuma Allah duk Abunda kikaga yanayi Duk shawaran uwarsace goggo..."Ai Sai Azeema tazama out of control zuciyarta tashiga zafi lokaci daya wani bangare na zuciyarta na amincewa da kalaman Azeeza wata kuma na kwabarta,Zuciyarta ta bata cewa in mganar Azeeza gaskiya ne,to ai yaya captain bai taba nuna wani zalama akanta ba asalima basu taba zaman Fahimta ba sai jiya,kodai kodau duk cikin plan nasa ne,Goggo kuma bazata taba cin amanarta ba,itace makwafin mahaifiyarta ta ci kashinta da fitsarinta goggo ta goyata da bayanta duk Abunda uwa zatayi ma danta shi goggo take mata,gaskiya bazata taba yarda da goggo za"a cuceta ba,to ammh mganar Azeeza Abun dubawane,domin akankantar Shekarunta bazata kitsa mgana kai tsaye ba,itako Azeeza ganin yadda Azeema tashiga Rudani Shiya bata damar kara mata famfo tana tsaro mata wasu mganganun wanda ita da kanta ta tsarasu,nan da nan Azeema ta amince da Azeeza ,100% harda kukanta tana fadama Azeeza ita yanzu yazatayi batasan ya rayuwarta zata je ba,shawara Azeeza tabata kan daga mkranta ta wuce gidan Baba Ade koda goggo taje ta tubure tace wlh bazata koma gidan goggo ba,bayan kwana biyu kuma ta bijuro da zencen sai yaya captain ya saketa.
Azeema ta yarda da shawaran Azeeza saboda yadda hakalinta yake atashema nan take tace Azeezar tazo ta rakata,Bakin Titi ta hau Abun hawa takoma gidan Baba ade,murna fal cikin Azeeza ta hanzari suka tafi office din principal,sukayi report kan Azeema bata da lafiya zata koma gida,nan da nan aka bata permission Azeeza ta rakata bakin Titi ta hau Keke tawuce gidan Baba Ade bayan Azeeza ta jaddadamata komai tambayan da za"a mata kada ta fadi dalili kawai tadai tada kayar baya,amsa mata tayi da cewa zatayi duk yadda suka tsara,Azeeza na dagamata hannu har suka bacema ganinta wata dariya ta kwashe dashi tana fadin,"Bye bye Adda Azeema i wish wannan karon bazaki tallakema tarko na ba..Yaya captain am coming iin to ur life Soon..."Tafada tana yar dariya kafin tajuya takoma cikin mkranta tana Dariyan Farinciki da nishadi.
_*Topha bala"i...Gaskiya my Fans sai yanzu nake ganin wautar Azeema dakuke tafadi,yarinya kamar kwalkwalarta ba Ta wani Tunani sai na Shirme,yanzu goggon zata gujema saboda dambala,...🤔🤔🤔Lalle Azeeza yanzu kika Fara wasan naki,toh bari mugani Shin gadanga zaifiki zama player ko yaya? Hmmmm i don't know..,Sai mun hade a next page,love u all my Fans*_