Ta kwana da matukar tunani a wannan daren, Rayuwar ta da Ahmed, distance relationship, hatred tsakanin ta da y'an uwan shi, musamman Khaleel, she don't really know why, bata kaunar ganin shi, idan akwai Wanda zata nunawa tsana itace mommy wadda ta hanata sakewa a Rayuwar Auren ta, but why him? So take ta nemo Amsar takasa, juyi takeyi cikeda mutuwar jiki, idan tace bata cikin damuwa tayi karya, Ace Auren ta wata cikin na biyu ba kwanciyar hankali, batasan dadin miji ba batasan dadin zaman Aure ba infact ba Abinda ta karu dashi sai girki da gyaran gidan, Wanda anayi ne domin a kuntata mata, basusan ta horu da aiyuka agidan ubanta ba, ba aikin da zai gagare ta, tsoranta daya a rayuwa kar a rabata da mijin ta, domin duk Abinda ke faruwa soyayyar shi bata ragu a zuciyar ta ba, sai ma karuwa da tayi duk wani moment ita da Ahmed idan ta kadaici cikin farin ciki take kasan cewa, idan tana tuno su, tasani duk ranarda ta samu freedom da mijin ta zaman su zai yi d'ad'in gaske. Bata cire tunanin wata rana zatayi farin ciki ba, Wanda tana fatan tayi nasara insha Allahu. Tashi tayi tareda yin sallah ta roki Allah akan ya cire idanun ta akan duk Abinda zai faru da kuma Wanda ya faru a baya, tareda neman juriya da nasara a rayuwar ta ta yanzu da kuma nan gaba.
Washe gari aka tashi da shagalin biki, Wanda tun da safe jikin ta yagaza dauka daka kalleta kasan tana cikin tsananin damuwa da kadaici, Ahmed ya boyewa ganin ta baki daya, Wanda batada masaniyar baida lafiya ne, Saida khaleel ya kawo mai likita batareda sanin kowa ba.
Yana tareda d'an uwan shi har safe bai runtsa ba Abu biyu ke damun shi a zuciya, why yayan shi keda mugun hakuri? And wani gefe kuwa kanshi yake tuhuma, why why why? Domin shi karan kanshi da baida karfin zuciya cikin wata biyun nan da ya ga likitan zuciya, he is in big trouble, big mess Wanda yasani shi karan kanshi, he is a fighter domin duk Wanda ke yaki da zuciyar shi shine babban jarumi, Wanda kowa yasan yaki da zuciya Abune mai matukar wahala.
Dafashi da akayi yasa ya dawo cikin hayyacin shi tareda kallon yayan nashi, daya tashi zaune yana murmurshi kadan, kana ganin shi kasan cikin jinya yake. "All night bakayi bacci ba khaleel, why kuma kasan yau ranar Auren kane dole ka raya wannan daren. "Yaya ya jikin naka? "Alhamdulillah inajin sauki a jikina, ya Naziya kagan ta? how is she? " Yaya all you worried about is her? Why bayan ita bata damu da neman kaba if tasan Abinda ya dace me zai hana ta nemeka? "Kafada mata banda lafiya? "Nop Yaya. "Kaga batada masaniya, and please Khaleel take care of her, that girl deserve to be happy. "How Yaya bayan kaine zaka kula da ita she needs you more than me, kaine mijin ta. "I know khaleel. Ya Rungumo shi a jikin shi, yace "you have alot of responsibility, mommy, Fauziya and our company, I know you are stronger than me. "Yaya please stop All this you know you're breaking my heart, Yaya I have something in mind, Wanda bai kamaci in sakashi a zuciya ta ba I hate myself please forgive me. "What is that khaleel, me kakeso I promise to give it to you koda rayuwa tace saboda kaine farin ciki na. Wasu irin hawaye masu zafi suka gangaro a kwayar idanun shi for the first time, yaji he need them, saboda sometimes tears heal some wounds.
"Noo Yaya bana son destiny din da zai zamo musayar rayuwar ka, I don't want that destiny, but Yaya is really painful, bansan yanda zanfada maka ba and please don't ask me too much question bazan iya amsaka ba. "Is OK bazan tanbaye ka komai ba, but dole inji dalilin zubar hawayen jarumin kani na, what is that, meye ya taba zuciyar the stone heart Ibrahim khaleel? "Yaya. "No am not asking the new ango but am sure kana kukan farin ciki ne yau zakayi Aure and you will last on bed more than me. Yafada yana daga gira daya, ya tuno da irin question din da yamai ranar da sukayi hira a dakin shi da Naziya. Dafe kanshi kawai yayi tareda sakin yayan nashi, "Hmmm yaja dogon Ajiyar zuciya, "I know kani na sai yafi thirty minutes. Mikewa yayi cikin sauri, am coming Yaya bari inje cikin gida. Yafita fuuu dagashi sai guntun wando yau ko singlet babu a jikin shi yama manta da taron matan dake gidan, burin shi ya ganshi a cikin gidan.
Dayake kowa na sha'anin gaban shi sannan kuma an Waye ba wani Abu bane don haka no one care, har ya shiga main palo, dai dai taci kukan ta tayi nak har wani zazzabi takeji ta fito jikinta kamar ba ruwa ba Wanda ya damu da ciwon zuciyar ta. Taga shigiwar khaleel fuuu ya wuce dakin shi, bayan shi ta hanga yana shigewa Wanda dole ta bishi taji inda zataga Ahmed domin ta gaza zuciyar ta tayi rauni, ta leka dakin khaleel din yafi sau goma tun jiya dukan su basa ciki, infact ko gyaran datayi bai baci ba.
Shiga yayi ya kalli gadon cike da wani irin zafi zuciyar shi keyi Wanda bai taba jin irin shi ba, ya fisge zanin gadon ya jefar tareda zubewa kasa yasaki wani irin kuka mai karfi kadan Wanda ba Wanda zai jishi,
Tayi matukar tsorata da kuma jin mamakin kukan namiji, tun dosowar ta kofar dakin kuma tanada yakinin a cikin dakin khaleel yake fitowa, wake kuka haka? Bude kofar tayi cikin Sauri, ya dago fuskarshi karab cikin idanun ta, tayi matukar girgiza, bata taba kawo zata ganshi yana kuka ba, meye yasa shi kuka haka ? The great mai girman kai, this is serious, kokarin juyawa tayi kawai domin a tunanin ta koma meye ba hurumin ta bane. "Wait. Yafada cikin sanyi tareda mikewa yana share hawayen shi, tsayawa tayi cak har ya iso wurin, hijabin dake jikin ta tarike gefen shi gam tana jiran taji me zaice, saida ya matsa ya tura kofar ya datse, ta zaro idanun ta, "meye na rufeni a dakin ka, bana son rainin wayau ka bude min kofa intafi. Tafada bakin ta na rawa kamar zatayi kuka, "Hmmm, me kike nema? "Mijina. Tafada kai tsaye batareda ta kalli y'an da ma yake ba, "bakida lafiya ne? Saurin dago kanta tayi ta kalle shi akaron farko tun shigowar ta, da gudu ta datse makullin idanun ta, "Auzubillahi. Tayi saurin ja baya, Wanda Abun yayi mugun batamai rai fiyeda tunani,
Bata taba ganin bear chest din namiji ra'ayil aini ba sai yau ga kirjin nashi da shegen fadi da wata irin suma mai tada tsigar jikin mace,
Fisgo hijabin ta da yayi cikin zafin rai yasa tafara istigifari tareda bude idanun ta tana mai kallon that's why I hate you, "you are behaving like baki taba ganin namiji ba kaya ba, kina Abu kamar wata saliha, look karki daukeni jahili ko mara sanin iyakar shi, I know my limit shiyasa kike tsaye agaba na batareda wani Abu yafaru dake ba, ni kikeyiwa a'u'ziya? kamar Kinga shedan. Cikin tsiwa da zafin zuciya tace "meye banbancin ku da shi, kana ratsa mata tsirara bayan kasan haramcin Abun sannan wuce limit! yes you cross All the limit da ka rikemin hijabi now let me go. Tafada cikin karaji, saurin sakin hijabin yayi tareda sai daita kanshi yana shafo sumar kanshi tareda d'an naushin iska.
"Am sorry, kiyi hakuri am worried ne because my brother is sick tun jiya. Saurin natsuwa tayi tareda sakin jiki tace "Ina yake? Jikin ta na rawa, yana part d'in mu na waj... Ko gama sauraran shi batayi ba ta bude kofar ta fice da sauri,
She knows it shiyasa itama batada lafiya, saboda Ahmed d'in ta is sick,
Tana fita ya datse kofar tareda zubewa kasa ya hade kai da guiwa, "khaleel you are so dead. Ya furta yana sakin Kara.
Da taimakon mai aiki tasan inda Ahmed din yake Wanda shine karon farko data shiga wannan part din Wanda ya kamata ta kasance a ciki, tundaga falon take zuba ido domin tasan dukiyar dake ciki bata malam bace, infact ko kudin labulen dake cikin falon zai siya kaf kayan dakin ta, wani irin karyewa zuciyar ta tayi takasa daga kafarta daga nan ta zube, shikenan tata takare za ashiga tsakanin ta da mijin ta domin tasan burin mommy ya cika ta Auro mai burin ranta,
Jin kukan ne yasa yafito daga bedroom ya ganta a wurin da gudu ya karaso gaban ta, "Naziya Naziya, ya zube tareda rikota zuwa jikinshi, "Am sorry please, Allah yagani kukan ki yafi komai daga min hankali please kiyi hakuri komai nada dalili believe me, dago kanta tayi ta ce"harda guduna kadawo dakin Amaryar ka tun bata tareba, Ahmed meye ribar zama na a karkashin inuwar Aurenka? "Soyayya ta Naziya, soyayyar kice Ribar Auren mu, Wanda nayi miki Alkawari muddin baki tare cikin gidan nan ba bazan taba samun farin cikina ba kece walwala ta kece farin cikina, am sick Naziya saboda damuwa datayi min yawa zuciya ta na ciwo. , Hawayen ta tayi saurin sharewa, "Ahmed Ina son zama dakai, ka koyamin sonka duk da bamu zauna tare ba, halin ka hakurin ka tarbiyar ka, Ina son halayen ka, kaddarar rayuwar mu, nadauka am not blaming you for that shine kaddarar mu, please karkayi ciwo zan shiga damuwa kaji, tafada tana shigewa cikin jikin shi da kanta kuma a karon farko, taji ta iya sakin jiki dashi batareda kunya ko nuku nuku ba, Ajiyar zuciya ya sauke ya gyara zaman shi dakyau tareda rungume ta gam a jikin shi shima, "Wow Naziya sarkin kunya yau ta rungume ni haka? What a lucky day, kice intashi ingirgice kawai mu shige daga cikin dakin mu yau. Sunne kanta tayi cikin kirjin shi tana jin kunya, tareda kokarin tashi ta gudu, "no karya ne yarinya kinkawo kanki don haka let go inside ki bani Abinci inci domin rabona da Abinci tun shekaran jiya, "why? Tafada cikin damuwa, "because am worried about you kullum Ina tunanin Ina shiga hakkin ki idan namutu ubangiji zai tanbayeni hakkin ki Naziya, kiyafemin kinji. "No bakayi min komai ba, muje in hada maka Abincin kaci, akwai komai a ciki ne? "Yes let go, yafada yana Rungumo kugunta. Ya dade a tsaye yakasa shigowa falon yana ganin yanda take shigewa jikin Ahmed, komawa yayi kan kujera ya zauna tareda runtse idanun shi gam only God knows what is going on in his mind,
Dagewa tayi ta shirya mai girki lafiyayya domin takara zama expert yanzu saboda shine kawai aikin ta a gidan, yana biyeda ita har cikin kitchen din, yana shige Mata harta gama yace suje falon domin yaji muryar khaleel na waya, kuma shima tunjiya baici komai ba saboda yaga yayan shi baici ba, tayi mugun jin haushin shi domin ya katse musu lokacin mai dadi ta hanyar zuwa musu gida,
Fitoda komai yana tayata, yana zaune a wurin batareda ya motsa ba, idanun shi a rufe har suka jera Abincin, tana gefen Ahmed yasa hannu ya cire hijabin jikinta batareda ta shirya ba, doguwar riga ce a jikinta mai kyau ta kanti, wadda ta d'an kamata shiyasa take yawo da hijabin, saurin kallon shi tayi tareda narke fuskar ta "kana so ingudu ne? "No wife inaso inyi kallon matata ne, Kinga yanda kikayi kyau, and,,ya matsa daidai kunnen ta ya rada mata "this your chest baby please agama abani hakkina I need them very badly.
Hannu tasa ta datse fuskar ta tana girgiza kai, "Allah zantafi fa. Cikeda wata irin murya mai daukeda tsantsar shagwaba mai burge y'an maza, Wanda saida khaleel ya daure ya kalleta, a yau yake ganin dariyar ta da kyau hade da farin cikin ta, he feels a little happy one side, ga dimple d'in ta wow,. "Yaya Am hungry yafada domin katse moment din, "let eat brother, ta zuba musu tareda cewa "wannan Abincin ai wasu basu san dadin irin shiba, oh zaka iya cin Abincin mu na Nigeria ba kyankyasai ba. "For the first time a lokacin yaji wata irin dariya tazomai, shima Ahmed Saida ya dara, "ke Waye yafada miki sunan su kyankyaso? " oho nidai ai mutum ba Abinci yakeci ba sai tarkace, daga kunama sai k'wari.
"Hmm, kawai yace yafaracin Abincin shi batareda yace tak ba yaci sosai saida ya kusa cinyewa tace "little brother inkara maka ne? Dago kanshi yayi ya kalleta wani iri kafin yace "am OK Aunty babba tanks. Ya mike, "Wow Wato kasan Aunty karama na zuwa ko? Harara ta watsawa Ahmed d'in tareda daukar hijabin ta ta Mayar, zata wuce. "Wait my Hajiya ai muje a yimin wanka ki karasa ladanki tukuna.
Kokarin tafiya takeso tayi, khaleel yace "Yaya please let her go kafin mommy ta ankare. "Muje intayaka tafada kai tsaye, domin batasan meye matsalar shi na yimusu karan tsaye ba yanaso ya hanata sakewa a lokacin da ta samu damar ta,
"Toh munafuka Y'ar gidan masu kwana kan buzu, zoki fita shashasha, ko kunya an narkawa yarinya dukiya kinzo kin shige, zo ki wuce, kai kuma Ahmed idan ka wuce iyakata banyafe ba, kaima khaleel dakai ake haduwa anamin bita da kulli, kuzo ku shirya ku tafi daurin Aure, in mace ce matsalar ka Ahmed na zabo maka ta kece raini ba wannan Y'ar shilar ba, koma daka nayi baki. Da gudu ta fita while khaleel ya wuce Abinshi batareda ya tanka ba Ahmed ma haka ta karaci sababi tareda turo masu aiki su Kara gyara duk Abinda aka bata a turare shi.
Saida ta shaki kukanta ta tashi tayi wanka ta caba Ado wayar ta ta dakko taga sakonnin shi da basa taba rabuwa da wayar ta, "Am sorry matata idan muka dawo zankira ki mu fita shakatawa kinji. Dariya tayi kamar dagske yanzu mommy nace wa Ahmed zai sunne kai, "my gentle man. Tafada cikin nishadi, so hana ganin laifi,
Biki yayi biki ko Ina ba masaka tsinke a cikin babban birnin na kano a yau Auren yaran manyan mutane guda hudu at once, ga kuma Y'ar masu kasa Wato fauziya,
Daurin Aure ne Wanda ya jirkita garin ba kadan ba manyan baki ta ko Ina, kawu wakilin Angwaye Wanda baisan da zancen Auren Salifa ba sai ranar Auren, ya fara fada kamar zai Ari baki, har cikin gidan yazo ya kirata "Hajiya bilkisu halina na nan, yanzu saboda Allah yaro Aure wata biyu kisa ya karo Aure? Hajiya bilkisu kiji tsoron Allah. "Toh nidai bani nasa yaron nan Karin Aure ba ka kirashi ka tanbayeshi. "Koda bani na haifeshi ba jini nane nasan halin Ahmed nasan tirsasashi kikayi kuma Ina gargadinki da kibi a hankali. Shigowa Khaleel yayi ya zauna tareda gaida kawun yace "don Allah kasa baki ta bar yarinyar ta tare a part d'in ta kafin wata tazo kuma kawu ai itace uwar gida yakamata ace ita tafara shiga wancan gidan. "Yanzu kokarin kai karata kakeyi Ibrahim, Wato ya turoka kazo kasa kawunku ya yanke ni toh ka koma ka fadamai wallahi sai Salifa ta shiga Wannan gidan kafin Wannan Y'ar gidan malaman ehem. Tayi fuuu ta shige, ya so ya cire son zuciya ya agaji yayan shi amma mommy, Hmmm. "Khaleel ku shirya mu wuce ka Kira d'an uwan ka, mu ake jira,. Yafada domin lokaci natafiya kuma suntara manyan Kasa harda mai kano baki daya, kuma zai dawo mata idan komai ya natsa.
Andaura Auren fauziya da Khaleel sai kuma Salifa da Ahmed, Wanda akan sadaki mai matukar tsada akan miliyoyin kudi, domin gadarar mommy, Wanda Ana gama daurin Aure angwayen suka dawo dakunan su kowa kajishi shiru, ba wani motsi, lokacin da aka Kira mommy andaura ta rangada guda tareda kawayen ta, kannin mijinta ne suka iso suna Allah Sanya Alkhairi badon sun soba, babbar tace Ina uwar gidan Ahmed d'in? Tana nan zuwa anjima za akawo ta. Mommy tafada da gadara, "Hmmm Allah ya shiryeki bilkisu Wato harda yayan mu bai duniya baki canja bakin hali ba ko?, to wallahi sai Kinga sakamako idan kika cutarda Y'ar mutane. "Toh ku dama wayake taku dama ai duk kannin miji y'an bakin ciki ne don haka ni yau banda lokacin ku nayiwa ya'ya na AUREN GATA.
Taci gaba da guda, dakin Ahmed suka nema inda suka sameta zaune yan uwan ta sunzo tana ta walwalar ta ta fauwala wa Allah, Wanda ta mugun burgesu zama sukayi a dakin suka sake sosai sukasha hira anan suke fada mata su gwaggwnin mijinta ne, ta saki jiki ta kula dasu itama dasu Aunty Raliya sai hira sukeyi.
Damuwar ta kadan ce zuciyar ta na wurin Ahmed batasan halin da yake cikiba Wanda saida yakira likita ya dubashi yace "gaskiya Ahmed idan zuwa gobe bakaji sauki ba kazo Asibiti ayima xray saboda ciwo a kirji yanada matukar Matsala.
Godiya yayi yasha maganin shi ya kwanta yayi bacci sosai har magrib.
Taro ya ragu zuwa Karfe bakwai duk taron Naziya sun watse sai ita kadai, yau ta yabawa d'an gin Ahmed harda y'an gidan kawu gefenta suka tare sun share mommy da gayyar ta, yanzu bakajin komai sai kai da kawon su Aunty zarah iyayen ango,
Takwas aka kawo Amare Wanda kafin Wannan lokacin ba Wanda yasan inda angwayen suke.
Main house aka shigo dasu cikeda guda Wanda tanaji, a take wani kuka yazo mata, shikenan rayuwar da tafara mafarki watace zatayi da mijin ta, shikenan sun samu third party tunkafin su mori Auren su.
Saida suka gama feshe feshe kafin kai Amaren gefen su wainda kowacce cike take da tata salon rashin kunyar hade da rawar kai.......... 🖊
*Matar Soja*
🌻🌻AUREN GADO🌻🌻
*Matar soja ce*
Daga marubuciyar
KUKURE NA
BARIKI AUREN SOJA
MUK'ADDARI
WANAKE AURE
ZANYI BIYAYYA
Y'AY'AN GATA
And now AUREN GADO,
Ga masu bukatar Wnn littafi ku turo kudin ku ta Asusun banki na 7304736012 nafisa sani hassan Fcmb ko katin wayar ku ta Wannan number 09011251444, sai kuma y'an 🇳🇪 Niger ku tuntubi Wannan number domin biyan naku, +225 0748153903, littafina Dari biyar ne kacal 500 sai najiku nagode,
🆓 page
1⃣7⃣&1⃣8⃣
........... Sai Karfe goma sha daya suka shigo main house, mommy na zaune sai faman jiran su takeyi,ta gwada numbobin su ba Wanda yake shiga, tanata sababi Su zarah na tausar ta, da sallamar shi ya shigo cikin falon while khaleel na biyeda shi cikin shigar shadda bugaggiya Y'ar gaske fara dal, "ko kin ga y'an rainin hankalin ko sai yanzu zasu shigo gida kusan Karfe goma sha daya. "Ahmed ne ya matso gefen ta tareda zama yana gaida Aunties dinsu, tareda cewa sorry mommy muna tareda Abokai ne. "Which abokai? Kai inkanada Abokai shi Wannan miskilin nadasu ne? Kun bar ya'yan mutane sukadai suna jiranku kamar masu gadi.
Carab ya bude baki a karon farko yace "jiran me sukeyi mana? Bayan ba ayi budar kai ba, sai su jira nan da sati daya idan an yi budar kai sai muje wurin su ni bacci nakeji, Yaya good night. Yafada batareda ya jira Amsar suba ya wuce Abinshi, ido kawai Ahmed yabishi da shi, bakin mommy a sake tace "Allah ya hadani da yaron banza, kai kuma bazaka tashi ka wuce dakin Amaryar taka ba? "Mommy gaskiya ne ita baza ayi mata budar kan ba? " ubanka kaji tashi ka wuce ko ranka ya baci yanzun nan, shima zanje in same shi. Mikewa yayi domin baijin dadi sosai dauriya yakeyi kuma Allah yagani bayason kowa yasan halin da yake ciki yanzu.
Yana kallon kofar dakin shi kamar yashiga yakeji yasan halin da take ciki, Amma ba hali mommy ta kasa ta tsare. "Za abiyoka da kazar Amarci nasa anyi muku gashi mai kyau. Ko amsawa baiyi ba ya fita, a zaune Amaryar tashi take tayi dai dai cikin wasu irin fitinannun nighties duk jikinta a bayyane gata ba wani shahararren kyau ba, sai faman tauna chewing gum takeyi tana kas kas kamar wata tsohuwar karuwa.
Tundaga falon ya hango ta kafa daya kan daya tana jijjiga, zai iya cewa yaune karo na biyu ganin shi da ita Wanda baima san ta Ina zai fara yimata magana ba, domin ko ganin farko bai wani mata kallon arziki ba, don haka ko yanzu yana shigowa ya dauke kanshi ya wuce ta gaban ta. "Kai, tace cikin zafi. "Kashi ka wuce? ace ankawoni tun Karfe takwas kowa ya watse ya barni baka shigo ba sai yanzu? kuma ka ganni kamar wata Kashi ka gani. "Oh sorry ya fada batareda ya kalle taba domin bai sha'awar hakan, murmurshi tayi tareda matsowa tana karkada jikin ta da shirin rungume shi, yayi saurin ja baya tareda cewa "please bacci nakeji sosai kuma kaina naciwo, am very tired please let me go. Ya wuce da sauri yabarta tana cizon yatsa, batasan da yanajin lafiya yau sai ya nemo Matar sonshi yaci Amarci kota halin Yaya, Amma bayajin dadi shikadai yasan me yakeji a jikin shi. Yana shiga dakin shi ya datse gam batareda ya jira wani Abu ba, idanun ta sun nuna mai zata iya mai fyade inyayi wasa ta karasa shi, saida ya kwabe ya zube kan gado domin yayi sallolin shi a waje, ya janyo wayar shi yafara neman ta, tana kan dadduma tana lazumi taji Karar wayar, tasan shine don haka cikin Sauri ta mike ta dauka, Ajiyar zuciya yasauke yace "Y'ar Aljannah." Ina wuni, ta gaidashi cikeda tausayin kansu domin yama fita zama Abin tausayi, "ba lfy my wife, ko in zo ne? " aa. "Why?" mommy na falo suna hira. Hmm! zaki tayani hira har safe? eh, Amma hakkin Amarya fa? "Don't say that again sai kisa inji guiltiness akan ki" naki hakkin fa? " ni na yafe. "Nikuma fa? Ni Ina bukatar hakkina Naziya, kinsan cewa ba Abu bane mai sauki namiji yayi ido biyu da Mace kamar ke ya kawar da ido ba, mommy ce ta tsaya min akan layi da tuni munfara lissafin wata biyu cikina. Rufe idanun ta tayi gam saboda kunya kamar yana ganin, "shy girl, nasan kin rufe ido.
Hira sukasha sosai yana yi yana bata hakuri tareda alkawura masu yawa.
Gefen Amarya ta cika ta batse momyn ta ta Kira tana kuka tafada mata angon yaki ko shigowa dakin ta, a daren Karfe biyu ta Kira mommy tana sababi, "nifa ba dutse nakai muku ba yarinya ce shakaf mai jini a jika don haka kari nji kar ingani, zancen wulakan ta min ya'. Tayi ta bata hakuri kafin ta gwada kiranshi yana busy, ta hakura ta barwa safiya, banzar kuwa kazarta ta yaga iya son ranta ta sha baccin ta nak, domin tasan dai dole yagama gudun shi yadawo mata domin a shirye take tsab.
Fauzy ma tasan halin kayan ta batasa akaba tasani tunda dai ta shigo, a juri zuwa rafi wata rana tulu zai fashe, Amma zama daram itada Khaleel tunda buri ya cika.
Gefen shi ma baccin shi yasha har safe batareda tunanin wata kaya fauzy ba,sai Asuba ya fito da shirin zuwa masallaci, ya samu mommy zaune itada bata tashi da wuri, tace Yauwa ku nake jira kuyi sallah kuzo kaida d'an uwan ka Ina jiran ku yanzu, fita yayi kawai Abun shi yasan tatsuniyar gizo bata wuce ta k'oki.
A masallaci suka hadu, saida suka idar yace "her excellency is calling. "Who? "Your mom. "Oh ba MAMAN ka bace kai? Shiru yayi kawai, domin shikam baisan me zaiyi mommy ta canja ba, ciki suka shiga yana mai nasihohi masu ratsa jiki da taba zuciya, suna saka kafa tafara sababi "nikam yau zanyi maganin ku duka sai kunfada min inkunada wata uwar bayan ni, Ina muku gata yara kuna watsa min kasa a ido, toh yau dukan ku Ina bukatar ku dakin matayen ku banason jin rashin kunyar ka Ibrahim. Sannan kai tunjiya Ina kiranka kaida ubanwa kake waya? Da ka kwashe tsawon dare kana busy? "Mommy kiyi hakuri, nida Naziya ne. "Innalillahi, Wato tanan ka bullo Ahmed kuna hadewa ta waya, ita kuma munafuka kamar salaha, mayya ta lashe min kurwar yaro to wallahi zanyi maganin Abun, karyar buzu tsohon ta yakeyi, mu munsha tabara mun sha yaseen , ta rangada mata Kira, Wanda duk tanajin komai.
Da sauri ta fito da hijabin sallar ta tace "gani momy. "Ni ba uwar ki bace ta cikin bukka munafuka, ke kin kaini bango hakurina ya kare akan ki inba zuciyar kare kikeda ba kizo ki koma gidan ubanki, ace mace don rashin zuciya miji bai neman ki baidamu dakeba saboda kin rab'i Ac kin like kin manne kamar kaska, ke wa ya iya da bakin nacin talaka? zo don Allah kibarmin gida Ahmed dai yayi Aure aje aci gaba da cin tuwon dawa da gero.
Tafada tana nuna mata hanya.
Kuka takeyi tunda momy tafara magana Wanda Wanda duk sauran bakinta sun taso, fauzy ma data bugo sammako ciki taji komai, tana dariyar mugunta tareda komawa ta Kira Salifa tazo kar ayi bata, domin tasan da zaman Naziya kuma tasan komai akai don haka tasan zatayi farin ciki yau idan taga Abinda mommy tayi,
Dafe kirjin shi yayi yana mai wani irin zafi tuni numfashin shi yafara seizing batareda kowa ya luraba, domin kan Khaleel na kasa idanun shi kamar wuta saboda bakin cikin halin mommy, da kuma irin cin zarafin da takeyiwa Naziya.
Zubewar da yayi Tim yasa khaleel ya zabura yayi kanshi, Wanda yabawa sauran damar ganin Abunda ke faruwa, har mommy tuni tayi dif kamar ruwa ya cinyeta,
"Yaya" khaleel yafada cikin tashin hankali, ya tarai rayoshi, saidai tuni jini yafara bin hanci da bakin shi, wani irin zubewa Naziya tayi jikin ta na rawa kukan da take ya tsaya ba Abinda take kallo sai jinin dake fita a fuskar Ahmed, cikin tsananin jarumta da mazantaka khaleel ya cirashi da gudu yayi waje yana mai kwalawa driver Kira yakawo mai key, yasaka shi cikin motar tareda rungume shi cikin tashin hankali driver yaja suka fita a guje domin gari yayi haske,
Mommy daskarewa tayi tana jin numfashin ta kamar zaifita saboda tashin hankali, Ba Abinda takeso duniya sama da ya'yan ta da kuma dukiyar ta, batasaon rasa kodaya a cikin biyun nan, don haka ganin yanayin Ahmed yasa tajita kamar ana zarar ranta. Saida zarah ta jijjigata ta dawo dai dai, "zarah muje wurin dana ingan shi, kar yarona ya mutu muje inga halin da yake ciki.
Ita ta dakko mata key da hijabi suka fito, su fauzy na tsaye turus basuda niyyar motsi, sanin halin khaleel yasa suka Kira driver yafada musu inda suke, Naziya kuwa kuka takeyi kamar zata mutu, idan ta kalli jinin dake kwance inda aka dagashi, hijabin jikinta ta zare cikin rudu ta goge kasan tiles din tsab tana kuka, Aunty Raliya ta Kira tana kuka tafara fada mata, ta lallashe ta tareda cewa "kiyimai Addu'a Allah yabashi lafiya ba kuka ba, banason shirme. Toh Aunty. Ta datse kiran tana mai dauro Alwala ta koma kan dadduma hannayen ta a Asama domin neman sauki wurin mai duka.
Gefen mommy koda suka isa Asibiti daidai da zuwan kawu modu domin Khaleel ya kirashi, hawaye yake sharewa tareda sintiri, kawun na zuwa yace " Meya same shi khaleel? " d'an uwana Kawu yana Aman jini hanci da baki suna ciki har yanzu basuce komai ba, ya mugun fita hayyacin shi, matsowa Mommy tayi jikinta na rawa "Ibrahim me yasamu d'ana?. Dago idanun shi yayi ya kalle ta cikin kallon kece sanadi mommy. "Look at it mommy kinga irin ta ko, d'an uwana na cikin Wannan halin because of you, mommy don dai ke uwata ce Amma in wani ne bazan taba yafe mai ba, now just pray d'an uwana ya tashi lafiya I promise dole abashi farin cikin shi that's enough! hakurin shi yayi yawa. "Ibrahim ' kawu ya daka mai tsawa, "me yasa kake fadawa mahaifiyar ka magana haka, me yafaru? Matsawa yayi cikin karyewar zuciya, ya fada jikin kawun ya saki kuka mai zafi Wanda ba Wanda zaice jarumin namijin ne ke irin Wannan kukan.
Bubbuga bayan shi kawu yayi " ya isa insha Allahu zai tashi lafiya, Kayi shiru haka. Fitowar likita ne yasa ya yi saurin share hawayen yace "lafiya doctor yaya na fa? "Please kaine Khaleel?. "Yes". Come your brother is calling you.
Bin likita yayi da Sauri kawu ya bishi shima, mommy zata shiga likita yace su tsaya waje mutane zasuyi yawa a emergency.
Jinin ya tsaya kadan sai Wanda ke bin hancin shi kadan kadan, yana isa yaja gefen rigar shi ya goge mai, "yaya please ka cire damuwa zaka tare da Matar ka I promise you kaji. Wani irin numfashi yaja mai wuya tareda fitarda murmurshin dole.
Yace "kawu", tareda mika hannu yace ga Amanar d'an uwana, kawu don Allah ka kula dashi ka tsaya mai akan komai, inason yayi farin ciki, kawu don Allah make him happy kar ya shiga damuwa idan bana nan, Khaleel take care of Naziya, where is she? Please call her, ka kawo min ita Ina so in roketa gafara please go and bring her. Ja da baya yayi tareda girgiza kai, " no no no stop that yaya nothing is going to happen to you, bari inkawo ta please yaya kadaina magana haka ciwo ai ba shine mutuwa ba, I don't like this, stop it. Am sorry Khaleel. Yafada yana mai kallo mai cikeda sakonni, fita yayi da sauri yana yi kamar zai tashi sama, riko hannun kawu ya kuma yi, "kawu don Allah kar Kabari Naziya ta fita agidana ko bani, kawu kabawa Khaleel ita ya Aura nasan zai bata kulawa saboda soyayyar da yake min please kawu". Mugun sanyi jikin kawun yayi domin Abun ya tsorata shi, a'a Ahmed kadaina irin Wannan maganar, haka d'an uwana yatafi yabarmin Amanar ku, bangama saukewa ba zaka bani wata, Insha Allahu zaka tashi kaji, likita kuyi aikin ku mana,. Yafada cikin tsawa, "Alhaji muna bakin kokarin mu Amma zuciyar shi tariga tagama kunbura shiyasa yake Aman jini, tunfarko yasan yanada ciwon zuciyar yabari tunani yashige shi Wanda yafi karfin zuciyar.
"Karka kawo min hauka nawa zanbiya ayi mai aiki, inba zaku iya ba infita dashi waje. Mommy ce ta shigo tana kuka tareda matsowa kusa da gadon da yake" Ahmed meke damun ka? Me yafaru dakai? Don Allah katashi.
Rikota kawai yayi dakyar ma yanzu yake fitarda numfashi, "ki ya fe min mommy na. Ya fada daya bayan daya yana riko hannun ta gam Wanda tanajin rikon cikin jijiyoyin ta rikone mai matukar karfi irin na fitar rai, koda takalle shi kafin tace wani Abu sai dai ganin jinin tayi yana Kara fitowa tareda kafewar idanun shi sama, kafin ya saki Hannun ta. Suman zaune tayi na wucin gadi kafin likita da kawu su gama magana su juyo, zarah ma tashigo, wani irin tsinkewa jinin ta yayi domin ba tantama Ahmed dai rai yayi halin shi,
"Innalillahi wa Inna ilaihirrajiun. Kullu nafsin za'ikatul maut. Kowane rai tabbas ne zai daddani zafin mutuwa don haka sai muyi fatan cikawa da imani, Ahmed dai yatafi yabar Wannan duniya mai cikeda rudani.
"Aunty Ahmed yatafi" Zarah tafada tana dora hannun ta saman kai, kawu wani irin zuface ta karyo mai tuni ya ciro hular kanshi yana fifita, "ya Allah" Kawai ya iya fada saboda sarkewar kalmomin bakin shi, saida zarah ta jijjiga mommy, kafin ta fasa kuka"wayyo Allah na ni balkisu Ahmed tafiya Kayi kabarni, why Ahmed why?
Rufeshi likita yasa Akayi da farin zanin gadon, yace Alhaji sai hakuri Ahmed lokaci yayi. Dakyar kawu ya iya saita natsuwar shi yana goge gumi kamar ya hadiyi kunama, ya ciro wayar shi a Aljihu ya yakira Khaleel, " kana Ina? "Yanzu na shiga gida kawu zan dakko Matar yaya. "Stay there muna zuwa. "Why yaya yac.... "Just do as I said, yafada cikin fada kafin ya katse kiran.
Shi ya hada komai yayi clearing aka basu Ambulance Abunka da kudi cikin minti kadan suka tafi da gawar su,
Mommy kamar ta haukace ji take kamar a mafarki wai Ahmed dinta ne ya mutu. Aunty zarah ido yayi Hulu Hulu.
Naziya tun fitar su take kan dadduma, zuciyar ta bugawa takeyi da karfi takasa ko motsawa, su kuwa Amare suna hakimce kowacce taci Ado kamar masu gasar gwal. Sun hakimce a falon,
A harabar kuwa Khaleel ya kasa gaba ya kasa baya saboda tashin hankali, ga umarnin kawu, yana daskare jikin motar yaji kukan Ambulance, wani irin kallo yake wa motocin su mommy, ganin yanda Aunty zarah ta riko mommy sannan kawu shima ya fito kai ba hula, ya maida idanun shi akan Ambulance yana kallon nurses din suna bude motar, ganin sunfito da mutum rufe da farin kyalle ya zube kasa war was, domin baya bukatar Karin bayani akai. Masu aikin ne suka ruga wajen shi domin jin faduwar tashi Tim.
Mommy ta tafi luuu itama tana shirin zubewa, shima ya mutu ko zarah? In ya mutu shima ni tawa ai takare kenan. Tafara sambatu, zarah ta riketa tana jijigata a'a Aunty bai mutuba, kai ku shiga dashi ciki, kawu dai nata gawa yasa aka shige dashi ciki, hakama Khaleel anyi ciki dashi,
Wanda tuni hankalin kowa ya kawo kan abinda yake faruwa banda Naziya, domin Amarya Salifa ita kanta jikin ta yayi mugun sanyi, wane irin Abu ne haka Auren ta jiya miji ya mutu yau,
Kukan da mommy ta fasa yasa Naziya fitowa jiki na tsuma da carbi, ganin mutum kwance akasa ga kawun su zaune agaba ya dafe kai yasa tafito jikin ta a mace tana sand'a kamar barauniya.
Kukan dasu Aunty zarah dasu Salifa keyi yasa ta gano duk Abinda yake faruwa. Dabas ta baje akasa kamar kurma, kafin kace me, tuni ji da ganin ta sun dauke.
Koda ta farko, taga dakin ta makil da mutane harda su gwaggon nin ta dasu Aunty Raliya da kuma matan kawu.
Zabura tayi tana kallon jikewar da jikin ta yayi da ruwan da aka rika kelaya mata,
Ganin ta zaburo Aunty Raliya ta riketa, "Naziya bi a hankali ruwa ne a hannun ki. Kallon hannun tayi, tareda kallon mutanen tace mafarki nakeyi ba mutuwa yayi ba ko? Aunty bai mutuba ko? Ku fadamin Ina yake?
Dafata kanwar malam tayi tace "ki yawaita Inna lillahi Wa Inna Ilaihir Raji'una Naziya. Tafiya takuma yi luuu. Suka kwantar da ita, kowa na share kwalla,
Khaleel kuwa saida akayi da gaske ya farfado, lokacin angama hada gawar Ahmed, zabura yayi kawai, ko digon hawaye yakasa fitowa a idanun shi.
Kannen shi ne yaran kawu maza suka rikeshi "yaya Khaleel bi a hankali karka fadi. "Let me go. Yafada cikin fada. Kafin ya fisge ruwan yafice cikin Sauri lokacin za adauki gawar zuwa makwanci, harda malam yazo gidan yau.
Cikin sauri yace "kawu kubari inyi mai Addu'a, fuskar shi ba ko Alamar hawaye domin ance kuka wuri yake samu watarana zuciyar shi ta cushe ta inda bako digon hawaye dake shirin zubowa.
Kowa yasan na zuci yakeyi Wanda ke cin zuciya, don haka malam yace "Ibrahima, ka saki zuciya Kayi kuka bakyau hadiye Abu yana illata mutum cikin sauri.
"Malam muje akai yayana makwancin shi. Yafada yanasa hannu ya daga makarar gefe daya domin yasan idan shine yayan shi zaiyi mai har wankan karshe, Amma tunda bai samu yimai ba shine zai sakashi cikin Kabari tareda samai kasa da binshi da Addu'oi.
Yabawa kowa mamaki yanda ya sakawa kanshi jarumta, har zuwa makabarta, inda da hannayen shi yasakashi cikin Kabari, tareda yimai kallon karshe, Wanda anan zuciyar shi ta karye ya fara fitoda hawaye, shikenan yayan shi yatafi, gatan shi Wanda saboda shi yadawo Nija, da ana dawo da hannun ago go baya da ya canja tsarin rayuwar Dan uwan shi , da ya hanashi shiga bakin ciki, Amma me komai mukaddari ne baida Wannan damar komai, yanda Allah yatsara haka zai kasance.
Lallabo shi akayi dakyar zuwa gida malam da sauran y'an uwan su, harma da mutane gari Wanda kowa mutuwar Ahmed din ta girgiza shi, Wanda sai ka mutu ake sanin halayen ka, wasu nacewa dazufa sun gaisa a masallaci, Wanda ita rayuwa haka take yanzu kana nan Anjima baka sai wani kuma, rai bakon duniya, Allah yasa mucika dakyau da imani.......... 🖊
"Kai jama'a bantaba k'isa ba a littafina irin Wannan don haka nikaina na koka na girgiza Wanda nasan watarana saidai labarina nima zantafi, ya Allah Kayi mana kyakkywan karshe kasa mucika dakyau da imani don darajar ma aiki, S. A. W🙏
*Matar Soja*
🌻🌻AUREN GADO🌻🌻
*Matar soja ce*
Daga marubuciyar
KUSKURE NA,
BARIKI AUREN SOJA,
MUK'ADDARI,
WANAKE AURE,
ZANYI BIYAYYA, Y'AY'AN GATA, And now AUREN GADO,
Ga masu bukatar Wnn littafi ku turo kudin ku ta Asusun banki na 7304736012 nafisa sani hassan Fcmb ko katin wayar ku ta Wannan number 09011251444, sai kuma y'an 🇳🇪 Niger ku tuntubi Wannan number domin biyan naku, +225 0748153903, littafina Dari biyar ne kacal 500 sai najiku nagode,
*my fans masu maganar Ahmed yabar k'wanshi, ai mommy zataji dadi gwara tayi nadama ta har Abada tasan Allah yabata yaro mai yi mata biyayya har bayan idon ta, kuma shine zai zamar mata tabo har karshen Rayuwar ta don haka muje zuwa dama bahaushe yace in kana mugunta bakayi wa kanka ba to baka cika mugu ba*
Last 🆓 page
1⃣9⃣&2⃣0⃣
.............. Naziya kuwa Abin kamar a mafarki haka take ganin shi, koda ta farfado manya suka natsar da ita sunayi mata nasiha, sai Ajiyar zuciya takeyi takasa koda fitarda hawaye, Saida Akace mata har an sallace shi an dangana shi da makwancin shi ne ta fasa kuka, shikenan yanzu bazata kuma ganin shi ba, haka rayuwar su tazama tarihi Auren ta dashi yazama tarihi, Wannan wace irin kaddara ce ta bullo a cikin Rayuwar ta? Istigifari ta farayi domin kar Imanin ta yayi rauni, Amma kowa yasan bakaramin ciwone a zuciyar taba rashin mijin da kukayi Aure wata biyu yatafi yabarka, kowa ya tausaya mata, har kanin Baban su Ahmed din na gidan sunzo, mommy kuka take tana birgima, cikin masifa Aunty Fatima tace "Wallahi bilkisu kukan ki baida Amfani ai saiki tashi kiyi farin ciki, Ahmed yatafi yabar miki duniyar, ba Auren kece raini ba! yau gashi yabar miki matan duka, kiyi Addu'a ma ko jika ace yabar miki jikin Y'ar talakar da bakyaso, kin hana yara sakat ai munsan komai kallon ki mukeyi kawai kijira Abinda zai biyo baya, wallahi sakamako na zuwa. Matar kawu ce uwar gidan tace "Aa Fatima kubarta haka rashin d'a tayi kuma kuzo ana zama kuna tada fitina. "Nayi shiru Matar yaya".
Kuka Momy ta fasa, yanzu take data sani mara Amfani Ina ma Ina ma, Allah yasa Naziya tanada ciki, Allah yasa zata ga Abinda zai cire mata kewar d'an ta mai hakuri, Kuka takeyi mara Amfani domin batada damar maida hannun agogo baya.
Khaleel kuwa zazzabi mai karfi ya rufeshi Saida likita yazo ya kuma dubashi, su Malam na tausar shi tareda mai nasiha mai ratsa zuciya, kabi d'an uwan ka da Addu'a shine kawai soyayyar da zaka nuna mai yanzu.
Gefen Amare Fauziya tafi d'an natsuwa domin mutuwar ta taba zuciyar ta don duk shashancin mutum yau ace Wanda kasani yafadi ya mutu, dole kaji jikin ka yayi sanyi idan akwai Imani a tareda kai.
Gefen Amaryar Ahmed mommyn ta da y'an uwan ta nafama akan ta shirya takaba tace atafau bazata yimai takaba ba tunda ko kwana basuyi ba tare, maganar har taje kunnen mommy, bata iya cewa komai ba domin ta shiga rayuwar kurame na wucin gadi, Naziya kam bazata iya bude baki tace wai mijinta bai kusance taba, domin akwai Alkunya kuma ko saboda soyayyar datake mai tareda hakkin igiyoyin nan uku dake wuyan ta dole tayi mai takaba, in akwai Abinda yafi haka ma zatayi mai domin ita tasan tayi rashi babba Wanda maida irin shi zaiyi wuya, ita ai jitake ma ta rufe shafin Aure a rayuwar ta.
A cikin kwanakin uku zuwa bakwai bamasu sauki bane ga duk makusantan mamacin, tun daga kan mommy, Naziya, Khaleel da duk wasu masoyan Ahmed,
A dakinta take tanayi mai takaba mai tsabta tareda binshi da Addu'oi dare da rana, kuka kuwa kullum dare sai tayishi rayuwar da sukayi dashi batada tsawo Amma yabar mata memories da zasu rika tuno mata dashi har karshen Rayuwar ta.
Seven days
Khaleel Ko part d'in shi bai zuwa tun ranar da fauzy ta shigo ko kallon ta baiyi ba, Abinci ma baya iya ci ya rame a fuskar shi sosai daka kalle shi, Aunty zarah ce ta shiga dakin shi yana zaune rikeda waya karatun Alqur'ani mai girma natashi, idanun shi a rufe, sanye yake cikin jallabiya fara, "Ibrahim" kazo Alhaji na Kira ta fada tareda juyawa, tashi yayi yana sa stop tareda rike gefen jallabiyar shi ya fita, a katon falon ya samesu dukan su har Naziya tana nade cikin hijabin ta, gefe daya Maman Salifa ce da ta Fauziya duk suna hakimce sai kuma Amaren a gefe, Wanda shi tun ranar da aka kawo su bai sasu a idoba, Kawu da malam ne zaune a kujera sai kannin kawun mata biyu gefe, mommy ce tayi shiru kamar ruwa ya cinyeta, kana ganin ta kasan mutuwar ta tabata. Kawun ne yace "Malam Abubakar na taraku ne anan saboda Abubuwa uku na farko dai Ina Kara mika ta'aziya ta gareka Ibrahim domin kai Kayi rashi, Allah ya Kara maka dangana tareda ikon daukar nauyin da aka dora a wuyanka, na biyu akan maganar Matar Ahmed, sun kirani akan zasu tafi da ita gida domin bazata iya yimai takaba ba, don haka ga Malam muji shima idan zai tafi da Ita uwar gidan ne gida. Saurin dago kanshi yayi ya kalli gefen ta, sai yanzu yaga yanda ta rame tareda yin zuru zuru, gwanin tausayi, ya ce Kawu duk yanda kukayi daidai ne. Abinda ya iyacewa kenan,
Addu'a malam yayi kafin yabisu da nasihohi ya karayi musu ta'aziya, ya dora dacewa Idan so samune Naziya ta zauna a dakin ta, Amma a yanzu saboda dalilai masu yawa zan mayarda ita gida tayi takabarta, Allah ya gafartawa Ahmed.
Wani irin daci Khaleel keji a zuciyar shi, yarasa wane irin tunani zaiyi baida kalma daya da zai iya furtawa a halin yanzu,
Kukan mommy ne yasa suka kalle ta, ba Wanda yaji tausayin ta har Khaleel din ma, domin tsawon kwana bakwai din nan baya ko kallon gefen ta.
Toh Hajiya bilkisu Ahmed ya tafi, Amaryar da kika buga kirji kukayi mai yau tace bazata iya zama dashi ba, sannan Inada yakinin mugun halin ki ne yasa itama Matar tashi za a tafi da ita, domin ni Nafi kowa sanin halin ki bazaki taba canzawa ba, da zaki canza da mutuwar yaya na zata fara canzaki, mundade muna daukar mugun halin ki yau kinga ni, Allah yasa ki dauki darasin idan har akwai sauran kwakwal akan ki.
"Ya isheka Modu karka manta d'ana na rasa babban dana duk Wanda yayi kukan mutuwar nan Kara yayi min, sannan maganar bakin hali, naji abarni da kayana duk ko wacce tafi ruwa gudu cikin su, ni Abarni da zafin rashin d'ana kawai, tafada tana mikewa cikin zafi tayi daki tana kuka mara madafa.
Ko dago kai Naziya batayi ba Saida malam yace "su shukrah na nan zasu hada miki kayan ki su taho dake, ni zantafi dalibai na jirana a gida. Ya musu sallama yatafi. Saura y'an uwan kawai da iyayen matan, Maman Fauzy tace toh Saura mu yaza'ayi da yarinya tun da tashigo ace bata samu kwanciyar hankali ba.
Cikin zafi yace "Zaku iya tafiya da ita in kun so I don't need her.
Yafada cikin fada da kuma iyakar gaskiyar shi, "dama momy ta Aurota idan kunga bazaku iya zama ba ga hanya.
Cikin rawar jiki tace " no mommy please kuje ni Ina nan. Tafada domin tana matukar kaunar Khaleel, bayan ta aureshi da kyar ta yaya zatayi sake ta fita, don haka tuni ta kashe bakin uwar, salifa ce taja uwar ta gefe, "mommy nidai kinga kisa kawun su yasa Khaleel ya Aureni tunda anayin Auren gado, kinga yafi ma Ahmed din haduwa mommy wallahi zan zauna in ya Yarda. "Y'ar gari nima tunani na kenan ai kinga yaron ya Tara dukiya kan dukiya gatashi gata uwar shi gata d'an uwan shi yanzu, ke fa uwar shi duk cikin mu tafimu kudi shegiyar, bari mukoma inyi magana.
Jiki na rawa suka koma falon lokacin Naziya ta mike tayi daki inda su Aunty Raliya ke hada mata kayan ta, daga Khaleel sai kawu sai gwaggon nin shi, mommy dasu zarah na daki,
Zama Maman Salifa tayi tana Washe baki "Alhaji Inada magana. Suka zuba mata ido kafin yace "munajin ki. "Yauwa nace ba, tunda dai ga d'an uwan shi mezai hana ayi tunani mai kyau a bashi Salifa sai a hada Auren gado. Wani irin saurin dago kanshi yayi tareda watsa musu kallon kun haukace ya ce "kuna hauka wallahi kun haukace, toh kusani kune sanadin duk Abinda ya faru a rayuwar d'an uwana, koda ace mata sunkare a duniya bazan taba Auren Y'ar kiba, don haka kawu ni natafi Inka gama domin one more minutes a nan zanyi Abinda bashi bane. Yafada yana wucewa a zuciye,
"Toh kunji sai ku tashi kubamu wuri, inji daya daga cikin matan, shigewa dakin mommy sukayi jiki a sanyaye,
Dayar tace "yaya dakasa baki ya Auri Wannan Y'ar mai Hankali, itace Matar Aure ba wa'innan y'an barikin ba. "Zamuyi Wannan maganar ba yanzu ba kubari mu gama war ware rashin da mukayi sannan shima Khaleel baya cikin natsuwar shi yana bukatar natsuwa, company su ma manager din ne ke kulada komai tunda ba Ahmed.
Dakin mommy su zarah ke lallashin ta domin sunsan koma meye ita tafi kowa rashi, har suka samu tayi shiru tana Ajiyar zuciyar, Shigowar kawar tata yasa tace kuna nan Hajiya? Eh kawata ai na canja shawara, nace ai basai na dauketa ba kawai tunda zumunci mukayi niyyar hadawa tun farko ko yanzu bata baci ba tunda kanin shi na nan sai a hadasu Auren gado kawai.
Kallon su tayi kawai domin tasan Waye Khaleel kuma yanzu bata isa ta tunkare shiba sai bayan komai ya natsa, amma Ajiye mata biyu irin Salifa da fauzy Abun Alfaharin tane a matsayin surukai.
Zarah ce tace, "ai yanzu saidai abari komai yanatsa kafin Wannan maganar ta taso, kuma Karku manta yanada wata Matar fauzy kuma kinsan Y'ar waye. "Badamuwa nidai inzai Aure ni zan zauna da ko mata goma ne Salifa tafada, domin itafa kawai tasa rai.
"Oh Allah kasa mu zamo iyaye nagari ga ya'yan mu Amen.
Kwana ki natafiya Naziya yanzu tana gidan su duk kayanta dake gidan ankwashe har wainda bata moraba, tafara warware wa Amma kusan kullum cikin yiwa Ahmed Addu'a take da sadaka idan tasamu hali, har Azumi takeyi litinin da Al hamis domin Allah yakai ladan kabarin shi. Khaleel kuwa haryanzu bai dawo dai dai ba, fauzy tayi binshi har tagaji bai komawa kanta, ko fuskar shi bata gani. Yau yana kwance a katon falon mommy ta shigo ciki ita kanta ta rame, "Ibrahim, wai kai wane irin yaro ne, yazaka sawa yarinya ido tun kawo ta gidan ku bayan kasan akwai hakkin ta akan ka, kai bazakayi koyi da halin d'an uwan ka ba, Ahmed dina ba haka yake ba, idan har kaunar da kakewa d'an uwan ka gaskiya ne Kayi koyi da halin shi.
Dagowa yayi tareda cewa " koyi nakeso inyi da Rayuwar da kika dora shi akai mommy, Ina ganin yadda yayi Rayuwa batareda Matar shiba, kuma kece kika sashi, ke kika hana yaya na ya sauke hakkin da ya dakko har yabar duniya, mommy kina tunanin Allah bazai tanbayi d'an uwana Wannan hakkin ba? Ta dalilin tsanar da kike yimata har tabar gidan nan bataji dadin rayuwa da mijinta ba why Mommy? Don haka itama Matar son taki tayi biyayya irin nata tagani.
Ibrahim banson rashin kunyar ka haka kaga Ahmed.... "Mommy enough, kidaina kwatance da yaya, ribar me yaci, kinga Amfanin Abinda duk yakeyi? See to avoid you and your wife, am going back to bangkok, zanje in kulada duk wani aiki da yayana yakeyi, bana ra'ayin zama anan, I don't need her idan tagaji tasan hanyar gidan Uban ta.
"Ibrahim, zan hadaka da kawun ku inni bazakaji magana taba. Wucewa kawai yayi, dama so yake kawai ayi fourty days ya yi gaba Amma yanzu baijin zai iya Kara ko kwana daya a garin kano gwara yatafi ko zai dawo dai dai.
Duk gurmin da Akeyi Fauziya ta shigo tana kallo, yana wucewa a zuciye ta nufo mommy cikin kallon tsana da kece sanadi, tace Wallahi bantaba sanin Abinda kikayi zai shafi farin cikina ba dana taka miki burki, kuma zanje in shirya inbi mijina. Ta buga mugun tsaki, "Fauziya karfa ki manta ni uwar mijin ki ce kike fadamin maganar da kikaga dama. uwar miji uwata ce ko uwar ubana ce? I beg give me a break. Ta yi gaba zuwa dakin shi dake part d'in .
Yana hada kayan shi, tayi sallama yayi wurgi da Abinda ke hannun shi saboda haushin takurar ta, ya juyo cikeda haushi, "can't you learn from Naziya, kintaba ganin tana bin yaya the way you are following me? Please have some shame.
"Oh baby yazaka hanani bin mijina, you are my husband Inada right akan ka, and ka daina hadani da Wannan village and stupid girl....... Wani irin kukan kura yayi a wuyan ta, tareda shake ta ya hada da gini idanun shi kamar na bakin kumurci, "what did you said? Cikin karaji, don't repeat that again if not kin gama numfashi a duniya, I promise you, kin ce hakki ko kinada hakkina? gani ki diba in kinada karfi, hakkin na karfi ne kizo ki kwata, useless, now get lost. Ya saketa tareda hankada ta waje,
Da mugun kuka tafita falon Wanda mommy naji tayi Saurin tarar ta, Fauziya lafiya Me Khaleel din ya miki? karki tabani kuma wallahi sai na fadawa daddy na ke kikaja Wannan aikin da kike taka ma dashi sai kin barshi. Tafita tana kuka, hannu ta dora aka, kunga yaro zaimin salalar tsiya, Allah sarki Ahmed da kana nan kaine kadai mai iya takawa yaron nan birki, Allah ya jikan ka yaron kirki Allah yakai haske kabarin ka.
Ta share kwalla tabi bayan shi,
Lokacin yagama shirya jakar shi, kallon kayan tayi tareda zubamai ido, yanzu Khaleel bangama war warewa a rashin d'an uwanka ba zaka tafi kabarni bayan kasan banda kowa sai ku biyu kacal, yanzu shi yatafi kai kuma zaka tafi kabarni.
Baice mata komai ba yayi hanyar bathroom, fita tayi tana fitar da hawaye, wayar ta ta dakko tafara kiran number wayar kawun nasu, yana dauka tasa mai kuka tareda fadamai komai akan zaman shi da Fauziya, da kuma tafiyar da zaiyi. Yace mata Yana zuwa kawai ya katse kiran.
Bayan hour biyu kawun ya iso lokacin yaci Ado cikin manyan kaya Wanda rabon shi dasu tun kafin mutuwar yayan nashi,
Lekowa mai aiki tayi tace Ana kiran shi a falon, ya ce tace yana zuwa, fitowa yayi, yasamu mommy gwanin tausayi gefen kawu akasa yau tunda tana neman taimakon shi. Sallama yayi yagaida shi, zama yayi a kasa kanshi akasa, fuskar shi ba annuri ko kadan, kawu yayi gyaran murya yace "Khaleel tafiya zakayi batareda sani na ba? "Aa kawu yanzu ma gidan naku nake shirin zuwa infada maka.Toh Amma me zakaje yi kabar nauyin da yake wuyan ka anan, nafarko Matar ka, na biyu mahaifiyar ka na uku company, sannan wasiyar d'an uwan ka, ko bazaka cika mai burin shi bane, domin yafadamin tun ranar da zai rasu saboda rashin natsuwa banyi maganar da kowa ba, sai Malam, dago kanshi yayi domin jin wane magana akayi harda malam zai shiga ciki, "Ya bar maka Amanar Auren Naziya, kuma munyi magana da malam tunda zance ne na wasiyya ya Amince sai dai muyi Addu'a ta fita takaba lafiya sai a daura muku Aure da ita.
Wani irin zufa Kebin ta kowane kofa ta jikin shi, yakasa koda motsi baya iya koda daga yatsar hannun shi balle ta kafar shi,
Kukan mommy ne yasa yadawo hayyacin shi , wallahi bazai yuwu ba, yaza ayi yaya ya Aura ya mutu kanin shi ya Aura, kuma dole ne ni sai nayi Rayuwa da Wannan yarinya mai kamar mayya, nidai ban Amince ba gaskiya bada yawuna ba.
Kallon banza kawun yayi mata kafin yace " ni nasan bazaki canja ba balkisu, kuma nasan ilimi yayi miki karanci da kin koma islamiyya, tunda bakisan Ibrahim zai iya Auren Naziya ba, kuma Ina so insani me yarinyar tayi miki, ko ince meye laifin ta? Ni tanada laifi A wurina kana ganin saboda soyayyar ta dana ya hadiyi zuciya ya mutu, banason ta kuma lashemin zuciyar Khaleel din da ya ragemin nidai bada yawuna ba.
"Yawun ki basuda Amfani a wurin mu don haka Khaleel gareka idan ka Amince kafin ka wuce kaje kaga malam Allah ya taimaka ya kuma tsareka, sannan zancen Matar ka Wannan kaidai ba jahili bane kasan hakkin Aure to don haka Kayi kokari Kayi Abinda ya dace ni natafi.
Yafada yana mikewa, tashi yayi jikin shi a sanyaye yabi kawun Saida ya shiga motar shi yadawo gidan, tana nan ta cika tayi tab. Kana jina Ibrahim, wallahi kar kasake inji kadawo min da Wannan yarinya mai farar kafa gida, karka sake ka Amince da Wannan Auren nafada maka.
Wucewa kawai yayi cikin dakin shi, ya datse key tareda zubewa akasa, wasu irin hawaye masu zafin gaske ne suka zubo mai, wainda baisamu yinsu ba tuntuni, Ashe maganar da Ahmed kullum yake fadamai zata kasance gaskiya, Wato akwai Abinda Allah ya boye shiyasa ya cusa mai muguwar soyayyar Naziya wadda bai taba yarda da itaba domin yasan is prohibited,
Yasha wahala yana kuma kan shan wahalar, zai iya rantsuwa da Al'qur ani yafi yayan shi son ta, Wanda baisan ya akayi soyayyar ta ta shiga zuciyar shi ba, how? when? Wani irin kuka yakeyi Am sorry yaya am sorry my brother da nasan zaka tafi kabarmin ita da na roki Allah ya cire min soyayyar ta ya barmin kai a rayuwa, Am sorry for loving your wife more than you brother, am sorry for feeling jealous idan kuna tare baka sani ba yaya, Inada kishin ta sosai yaya I use to cry behind door saboda zafin kishin ta, you are my brother but Ina kishin ganin ku tare, bansan ya akayi soyayyar ta ta shigeni ba, I love her more than the way you love her, I hate myself for that I swear to you, I control my feelings because of you.
You're dead because of hidden destiny, hawayen shi ya share tareda hadiye kukan, "I will make her happy yaya zancika maka burin ka, zanbata farin ciki fiyeda yanda Kayi mafarkin bata, zansata dariya fiyeda yanda take dariya idan kuna tare. Mikewa yayi ya zari key din hadaddiyar motar shi tareda goge fuskar shi da kyau ya fita cikin hanzari a falon da yabar mommy a nan ya same ta tana waya tana fadawa y'an uwan ta bakin labari, Modu ya rantse sai ya cakuda jinin ta da talaka........ . 🖊
"Comment share the free pages please and Wannan ne last free page ku biya ku karanta cigaban yanda zata kasance, ya za ayi da rayuwar Naziya shin zata Amince, shin zataso Khaleel, ya rayuwar su zata kasance da Fauziya, idan Naziya ta Amince da Auren Khaleel wace wainar mommy zata toya????? Muje zuwa yanzu za afara wasan this is just the beginning, let's go my fans 💃, ga masu bukatar biya kofa a bude take chart me up 09011251444
*Matar Soja*
🌻🌻AUREN GADO🌻🌻
*Matar soja ce*
Daga marubuciyar
KUSKURE NA
BARIKI AUREN SOJA
MUK'ADDARI
WANAKE AURE
ZANYI BIYAYYA Y'AY'AN GATA
And now AUREN GADO,
Ga masu bukatar Wnn littafi ku turo kudin ku ta Asusun banki na 7304736012 nafisa sani hassan Fcmb ko katin wayar ku ta Wannan number 09011251444, sai kuma y'an 🇳🇪 Niger ku tuntubi Wannan number domin biyan naku, +225 0748153903, littafina Dari biyar ne kacal 500 sai najiku nagode,
2⃣1⃣&2⃣2⃣
................ Tuki yakeyi cikin kwarewa tareda bin k'aidar hanya, ya riga yasan hanyar gidan nasu Naziya, tunda yazo sau biyu, har kofar gidan ya isa, lokacin yana mak'il da Almajirai, da Alama Malam na gida, fitowa yayi yana wani irin sheki da haske duk da ya rame saboda mutuwar d'an uwan shi, wani Almajiri ya Kira yace yamai iso wurin Malam yace mai Ibrahim ne kanin Ahmed, ko minti biyu ba ayi ba saiga Malam cikin fararen manyan kaya, tsohon akwai tsafta da kwarjini, yayi saurin dukawa zai gaida shi, a'a Ibrahima tashi shigo daga ciki,
Har tsakar gidan yajashi domin zauren akwai mutane, yanayi yana kallon tsarin wurin Wanda zuciyar shi ke ayyana mai komai, tsakar gidan akwai inuwar bishiya wadda a karkashin ta aka samai kujera ya zauna Malam ma ya zauna suka gaisa kafin Matar k'irki ta fito, d'an dukar da kanshi yayi ya gaidata ta Amsa tareda yi mai gaisuwa, kafin Malam yace Hauwa Kira min Naziya, kafin nan shukrah ta kawowa bako ko sobo ne mai sanyi. Wani irin lugude yaji zuciyar shi tayi jin ankira sunan ta, ta' aziya Malam yakuma yi mai tareda fatan Samun Rahamar ubangiji, yabishi da nasihohin da duk in zakazo wurin shi sai ya maka su. Shukrah ce ta kawo zobo mai sanyi a tsaftataccen sabon jug cikin na Naziya, ta Ajiye tareda gaida shi tayi gaba,
Fitowa naziya tayi cikin katon hijabin ta, kana ganin ta kasan ta rame sosai,
Sallama tayi, ya dago kanshi suka hada ido, Wanda tunda akayi rasuwar daga ita harshi basu hadu ba.
Allah ya gani bata son shan inuwa daya da gayen nan don kawai yaci Albarkacin Ahmed ne batada yadda zatayi dashi, Amma tunda yanzu mai rabawa ta raba shikenan ta huta,
Gaida Malam tayi batada niyyar gaida shi, saida Malam yace ga kanin mijin ki naziya, dama Ina so in samu lokaci muyi magana daku dukan ku, akan wasiyar da mijinki yabari, wani irin faduwa gaban su yayi duka shi tsoron reaction dinta yakeyi ita kuma batasan wace wasiyya bace.
"Ibrahim Alhaji Amadu yazo min da maganar kuma ni bazanyi jayayya da wasiyyar mamaci ba" don haka yanzu magana na wurin ku, Naziya mijinki yabar wasiyya d'an uwan shi ya Aureki, don haka idan kinfita takaba sai adaura muku Aure.
Wani irin kukan tasa tareda zama gaban Malam d'in. Kallon lafiya Malam ke yi mata, shikuwa wani irin tsalle zuciyar shi keyi saboda fargaba, "Malam don Allah karka Yarda nidai bazan koma gidan su ba, ni bazan yi Aure ba ni bana ma son shi kawai abarni haka, ni karatu nakeso inyi don Allah Malam karka hadani dashi.
Tashi kibani wuri Naziya banson shiririta, yaushe kika canja hali haka? tashi kafin ranki ya baci, wucewa tayi da gudu dakin Inna, Malam ya kalle shi, Kayi hakuri kaima bansan naka ra'ayin ba, Amma tunda kaine namiji in har ka Amince Naziya ita ba Matsala bace, kaje Allah ya maka Albarka yajikan d'an uwan ka, Ameen yace kawai zuciyar shi na wani suya, maganar ta ta bata son shi really touch his heart, wani irin zafi yakeji a kirjin shi, cikin dauriya yace Malam Wannan filin nakusa daku yaya Ahmed ya siye shi da sunan zai gina maka dakunan Almajirai batareda sanin kowa ba, bayan rasuwar shi Nagani a rubuce ya gama biyan contract din komai Allah bai nufa ya yi ba, inaso Inturo su, su duba yadda zasu tsara komai zanbar komai kafin intafi, zanje domin shigo da wasu kaya,
"Allahu Akbar Allah ya jikan shi yasa mutuwa hutuce a gareshi" Allah ya Albarkace ku baki daya. Ya Amsa da Amin, ya tashi yana farin cikin zai fara cikawa d'an uwan shi burin shi, duk da yatafi da ciwon maganar Naziya.
Bayan tafiyar shi ya kira Inna kulu da Naziya, ranshi a bace yace "Hauwa bansan cewa zan haifi yaron da zai yi musu dani ba, yau Naziya ke da nake yabonki kike kokarin watsamin kasa a ido, a gaban yaron nan kice bakya son gidan su bakya son shi, a Ina kika koyo Wannan d'abi'a? "Subuhanallahi Naziya me nake shirin ji"? Inna ni dai Don Allah ku yafemin Amma ni bana son komawa gidan nan nayi hakuri batareda nayi wa kowa korafi ba, yanzu idan na koma mutuwa zanyi, wallahi bana sonshi baida hali ba irin Ahmed bane, malam baka san shi ba.
Toh Hauwa tariga ta girma Y'ar taki, ni bazance komai ba tunda ta isa da kanta. Yafada tareda tashi yabar gidan kawai, a tarihin rayuwar shi itace ya' ta farko data farayi mai musu da gaddama.
"Naziya me kikeso ki yi"? Kin taba ganin ko Y'ar nan malam ya yi magana ta amsa shi bare ke? Wane irin abu ne nake gani ni kulu yau? "Allah Inna bana son shi ya zan iya zama dashi ni dai bazan koma gidan nan ba. Ta tashi tana hawaye tareda shigewa dakin su, kwalawa shukrah kira Inna Tayi, "gani Inna. Kiramin Y'ar nan a waya. Tasan wa take nufi don haka takira Aunty Raliya ta bata, Inna tace "kuzo kuyiwa Y'ar uwar ku magana ta canjo hali, nan tafada mata komai, tace karta damu za tazo tayi mata magana ita da Aisha. Dakin su ta koma tana kuka, tareda kudurin duk Abinda zai faru sai dai yafaru bazata taba Auren Khaleel ba, saboda tun farko jinin su bai hadu da juna ba, tayi hakuri ta zauna da Ahmed saboda tana son shi, Amma bazata taba Y'arda ta zauna da Khaleel ba, wai ma yaza ayi ta yarda da Wannan kwamacalar, bayan agaban shi yaga yanda Ahmed yake nuna mata so lokacin da suka samu sarari,
Shigowa shukrah tayi tace "Aunty wai fadan me Inna takeyi yi miki? Kuka kikeyi me yafaru? Rungume shukrah tayi tareda jin wani sabon kuka, "Shukrah bana son shi. "Waye bakyaso Aunty? " Khaleel, I hate him, bana sonshi wallahi bazan zauna dashi ba. "Ni Aunty bansan me kike fada ba.
"Ya za'ayi kisani tunda Auren ya koyo mata taurin kai, Naziya ki rufawa kanki Asiri karki wahalar da kanki a banza idan Malam ya karb'i lamarin nan ba mai canja shi, don haka na hore ki kiyi biyayya ki gama lafiya shine kawai.
Hadiye kukan ta tayi, dif jin fadan Inna, Shukrah ta tashi tabar dakin domin tasan ba hurumin ta bane, zama Inna tayi gefen ta tafara yimata nasiha akan bin duk abinda Malam ya zartar, shiru kawai tayi domin bata saba jayayya da iyayen ta ba, Amma zuciyar ta bata lankwasu ba, Sam bataji zata iya zama da wani kanin mijin ta ba, dama wani ne ba Wannan ba.
Yana tuki yana tunanin kalmomin ta," ni bana son shi. Kalmar datafi kona mai rai, don haka speed ya Kara, saida yagan shi cikin gidan su ya fito a zuciye, ya matsu gari bai Waye ba yagan shi yabar kasar nan, kwabewa yayi tareda watsar da kayan jikin shi ya zube akan kujera zuciyar shi mugun zafi da turiri takeyi, she is the first girl da ta kalli tsabar idon shi tace bata son shi, huci yake fesar wa saboda zafin zuciya.
Har zuwa dare ya kasa bacci shi kadai yasan ciwon zuciyar shi, a kwance yake dagashi sai boxer jikin shi na sheki kadaicin d'an uwan shi kawai idan aka barshi dashi wani Abu, amma yana ganin duk duniya ba wanda zai iya fahimtar halin da yake ciki, how he wish yayan shi na tare dashi, yafi son rayuwar shi fiyeda soyayyar Naziya, wadda ya Amince ta kashe shi akan yarasa d'an uwan shi gwara shi ya mutu, saboda yanzu ma ba Amfana zaiyi ba don ya dade da sanin bata kaunar ganin shi.
Turo kofar da akayi ne yasa yadago kanshi, fauzy ce, ta shigo cikin Sanyin jiki fuskar ta sharkab da hawaye, tana sanye cikin kana nan kayan bacci, kusan duk komai nata a bayyane yake Wanda shi ba abunda ya burgeshi ciki, domin zuciya ma saida natsuwa take samun wani feelings, halin da yake ciki ko tsirara ta shigo gaban shi ba tashi zaiyi ba.
Zubewa tayi kan jikin shi tasa mai kuka mai ban tausayi, "meye illa ta, meye aibuna da ka kasa bani koda sakon zuciyar kace? Khaleel Ina sonka why ni baka sona? nayi hakuri da duk wani halin ka, yau kusan sati biyu Auren mu ba wani kulawa baka ko zuwa gefen da nake, Khaleel nifa mutum ce Inada jini, ni lafiyayyar mace ce, dole in bukaci mijina please tauye hakkin yayi yawa, sannan me nakeji? Auren Naziya? "That village girl"?.
Tunda take magana jikin shi yayi mugun sanyi, yes she is right ba ruwan Ubangiji da halin da yake ciki, tunda igiyar Auren ta na wuyan shi bai kamata ya watsar da hakkin Allah ba, amma this her last statement mess up things. Wani irin wancakalar da ita yayi kasa tareda mikewa yana nuna ta da yatsa " look that girl, I value her more than you, she is more important to me right now, karki sake inji wani mum munan kalma daga bakin ki akan ta, duk wani Abu da ya shafi d'an uwana yanada muhimmanci A rayuwa ta, ko a mafarki naji kin kuma kiran ta village girl sai na saba miki.
Tashi tayi tareda girgiza kai " lallai Khaleel, tell me, yaushe kafara sonta? This is not About yaya Ahmed ,this is about you, yes saboda naji yanda kukayi da salifa why kaki Amincewa da salifa ka amsa Naziya, why?
Zaburowa yayi ya nufota kamar zai shake ta, "baki Ajiye ni ba so don't question me again, kuma kije kiyi duk tunanin da zakayi I don't care, one last thing, in kinga ban Aure taba sai in bana raye, idan zaki iya zama ki zauna idan bazaki iyaba see your road. Yafada yana nuna mata hanya, juyawa tayi da gudu tafita ya bita da tsaki tareda cewa "useless.
Dakin momy tafada har bacci ya dauke ta Wanda ta dade batasamu tayi irin shiba domin rasuwar Ahmed, yau ma da taimakon maganin hawan Jinin da Aka bata ta samu yadan dauke ta, fadowar datayi tareda buga kofar yasa ta zabura tareda dafe kirji tana jin bugawar zuciyar ta yana karuwa, "kalu innalillahi, ke Fauziya lafiya kika bugamin kofa tareda fadomin daki kamar y'an fashi.
Kuka tasa mata mai karfi, kince zakiyi mai magana gashi yace sai ya Aureta, ni wallahi bazanyi kishi da yar talaka ba kuma Y'ar kauye. "Oh yanzu bazaki iya bari muyi maganar da safe ba? kinga bacci nakeji. "Allah bazaki runtsa ba Indai ni bazan runtsa ba."Toh baki Yarda dani bane Fauziya? nice fa, bazan taba Amince wa a hada min iri da jinin talaka ba, saboda soyayyar da Ahmed ke mata ya fadi ya mutu yabar ni don haka bazan Yarda ta dawo ta karasa min gudan da yarage ba, kina ganin Y'ar nan kinsan ta gaji maita daganin ta mayya ce.
"Ni Ina ganin yana sonta ne fa. "No no no ba wani so, yaushe d'an uwan nashi ya mutu ke baki san soyayyar dake tsakanin shi dashi bane ko Auren ki ya karba saboda sa bakin Ahmed badon niba, a duniya Khaleel zaiyi komai saboda Ahmed Inada Wannan yakinin, don haka kicire zancen Khaleel zaiso yarinyar nan bayan yanada mace kamar ke. "Hmmm ni ai baya sona kema kin sani Khaleel baya son kowacce mace baida lokacin mace, Ina tsoron ranar da zaiso wata irin su basu iya fadawa soyayya ba, ranar za ayi biyu kuwa domin zan iya kashe macen da duk Khaleel yaso, ni nayi dakon soyayyar shi don haka idan har akwai wadda Khaleel zai so to nice.
"Naji zo ki kwanta a nan don girman Allah kibarni in kwanta maganin nan aiki yakeyi ajikina. Da k'yar ta samu ta kwanta sukayi bacci.
Asubar Fari yabar musu kasar su batare da yajira sun tashiba, maid ya fadamawa tafada ma mommy ya tafi, Wanda saida tayi kuka sosai lokacin da yarinyar ta fada mata, wani gefe tana mai kewar Ahmed yaro mai biyayya, "Allah ya jikan ka yaron kirki", zabin ka ne kawai ya sabawa ra'ayina Amma kai d'a ne nagari Ahmed, Allah yakai haske kabarin ka.
Koda ta nemi wayar shi, lokacin yayi nisa a sararin samaniya, Wanda yatafi da kewar Abu biyu, Wanda yana fatan kafin yadawo yarage tunanin su domin samun zaman lafiyar zuciyar shi.
Gefen Naziya haduwa sukayi washe gari Wanda Aisha tabi bayan Naziya tareda cewa "gaskiya Innan mu Ki cire kara ki fadawa Malam gaskiya kar ya Yarda da had'in nan, domin tasha wuya a gidan nan batareda mun fada muku ba, nidai bana goyon bayan ta Auri wani kanin mijin ta, wane dadi ta tarar a gidan mijin nata da zata koma cikin shi?.
"Toh madallah naji ku kuma nasan inda tasamu zuga, Wato dukan ku kun canja hali banida labari? Malam ya fara fada kafin ya karaso ciki ya zauna, "Hauwa, ki zama sheda, da farko bani nayiwa Naziya zabin mijin ta ba duk da a Musulunce ni keda hakkin zaba mata mijin Aure a matsayin ta na budurwa, banyi hakan ba, can suka hadu dashi tace taji tagani, duk Abinda ta fuskan ta a gidan Aure kaddarar tata rayuwar kenan, kuma yanzu mijin ki ya tafi yabar wasiyya akan d'an uwan shi ya Aureki na fita hakkin ki a matsayi na na mahaifin ki ba neman shawarar ki nakeyi ba, Agaban ido na da na yaron nan ki kace wai bakya son shi, saboda rashin da'a, to ki rubuta ki Ajiye Indai Ina numfashi, daga ranar da kika fita takaba daga ranar zan daura miki Aure da Ibrahim don Allah Naziya kifito ki nunawa duniya ni Malam Abu nayi miki Auren da bakiso, don haka nagama magana. "Kayi hakuri Malam" inji Inna da sai yanzu ta fara magana, don Allah karkayi wani dogon tunani kazartar da duk Abinda yake dai dai, nasan duk hukuncin daka yanke kana da taka hikima. "Malam Kayi hakuri kokarin lallashin ta mukeyi wallahi. Inji Raliya, tashi yayi kawai ya kade babbar rigar shi ya fita, Wanda sai lokacin tasaki d'an karamin kuka tareda toshe bakinta kar Malam ya jita, "Akul Naziya, Aure na sama da shekara talatin idan kikaja min bacin rai saboda boyayyan bakin halin ki bazan yafe miki ba. A'a Inna ya haka? don Allah karkiyi saurin yimata baki. Inji Raliya, ba baki nake mata ba dawo da ita nake cikin hayyacin ta. Rarrafawa tayi da sauri ta rike kafar Inna. "Na tuba Inna wallahi bazaki kuma jin nace wani Abu ba akan maganar nan, ba zan kuma musu ba, ki yafemin don Allah Inna. "Allah yawa Rayuwar ku Albarka baki daya, Aisha kirika hakuri ke babba ce a saman ta in bazaki kwantar mata da hankali ba karki nemi tayar mata dashi.
"Afuwan Inna kuyafe mana. Tashi tayi itama tabarsu a cikin dakin, suna Kara tausar ta. Matsowa Raliya tayi tareda dafa ta tace " ki share hawayen ki, jikina nabani Naziya zakiyi farin ciki fiyeda Auren ki na farko, kinsan me? Girgiza kai kawai tayi badon tana farin ciki ba sai don tana gudun bacin ran iyayen ta, "saboda Khaleel daban yake bazaki gane ba sai nan gaba keda kanki zaki fadamin. Allah kadai yasan Abinda ke ranta amma ita tasan bazata taba son Khaleel ba domin jinin ta da nashi bai hadu ba, zaman ta da Ahmed soyayya ce sanadi Amma shi tasan zama ne bamai dadi ba. Haka suka wuni suka tafi gidajen su, Wanda daga nan ta Kama kanta tareda dukufa Addu'oi akan mijinta.
Wasa wasa aka fara aikin ginin malam Wanda batasan daga Ina Abun ya samo Asali ba, cikin wata guda har angine dakunan Al majirai sunkoma andawo gyaran cikin gidan Wanda aka rushe gefen da suke ciki aka bugawa Inna flat Dan madai daici Da bazai cinye filin tsakar gidan ba sai dakuna biyu a waje, daya na Malam daya nasu Naziya. Aiki ne dayaja kudi Abunka da akwai su gamasu aiki birjik, mamaki takeyi sosai akan Wannan gyaran Wanda saida takasa daurewa ta tanbayi Inna shin Waye yake musu irin Wannan gyaran ne? Tafada mata wasiyyar mijinta ce kanin shi ke isarwa, a ranar saida ta shiga daki tayi kuka sosai.
Tareda yi mai Addu'ar Allah yakai haske kabarin shi, tasan tayi babban rashi a rayuwar ta, a duk lokacinda ta tuna da kudurin shi nason ya huta da ita sai tayi kuka, yaso ya taba kirjin ta kamar me kunya ta hanata, Ina ma ana dawo da hannun agogo baya da ta Bashi dama yayi yanda yaga dama da jikinta kila data rage takaici, wani irin bakin ciki takeji idan ta tuna cewar Khaleel zata Aura domin tasani Malam baya magana biyu.
Cikin wata uku gidan nan yayi tsab bazaka taba gane shiba waje da ciki kowa sai ya yaba a unguwar, Almajirai sun samu gata domin odar katifu irin na yan boarding akayi musu Wanda a wanna dalilin yasa tsangayar take Kara bunkasa. A gefen gidan momy kuwa tun bayan tafiyar khaleel da sati biyu Fauziya ta tattara nata tayi tafiyar ta Tareda cewa "wallahi sai mijin ta yadawo zata dawo bazatayi gadin wata uwar miji ba, Wanda hakan ya taba mommy sosai domin tasa ran ita zata tsaya ta debe mata kewa, wani lokacin ta kanyi kukan rashin Ahmed don dai tana fita aiki ne Amma zaman kadaicin yana mugun tabata, watannin Sam ba masu sauki bane a wurin ta. Gefen Fauziya a kullum suna waya da khaleel yana kiranta tareda fada mata tayi hakuri idan yadawo komai zai dai dai ta, domin yasan cewa akwai hakkin ta a wuyan shi yana kokarin tursasa zuciyar shine kawai gudun hakkin ubangiji, bata taba fadamai cewa bata gidan ba, sai ranarda sukayi waya yafada mata yana hanya cikin satin bayan ya kwashe kyawawan watanni hudu a kasar ta China,
Kawai Mommy ganin ta tayi tana shiga part dinsu lokacin tafito zata tafi aiki, "A'a Fauziya andawo? " eh bakya kaunar indawo din ne to na dawo. "A'a murna nakeyi ai gidan shiru ni kadai, yanzu dai zanje aiki in nadawo mayi magana, ta bita da harara, "Y'ar sa ido kawai mtswew.
Wanda Mommy murna takeyi domin ita zaman Fauziya a gidan ta Kara mata girma yakeyi tareda mutunci a cikin kawayen ta don haka duk yanda zatayi zatayi taga ta rusa maganar Auren Naziya da khaleel, zakuma ta gyaro zaman Fauziya da khaleel Indai ita tahaife shi....... 🖊
*Matar Soja*
🌻🌻AUREN GADO🌻🌻
*Matar soja ce*
Daga marubuciyar
KUSKURE NA
BARIKI AUREN SOJA
MUK'ADDARI
WANAKE AURE
ZANYI BIYAYYA
Y'AY'AN GATA
And now AUREN GADO,
Ga masu bukatar Wnn littafi ku turo kudin ku ta Asusun banki na 7304736012 nafisa sani hassan Fcmb ko katin wayar ku ta Wannan number 09011251444, sai kuma y'an 🇳🇪 Niger ku tuntubi Wannan number domin biyan naku, +225 0748153903, littafina Dari biyar ne kacal 500 sai najiku nagode,
2⃣3⃣&2⃣4⃣
.............. A katon filin jirgin yafito yana Takawa daya bayan daya kamar wani prince, sheki yakeyi yana wani irin haske, idanun shi dauke da katon eye glass, baka ko ganin kwayar idanun shi, fuskar shi dif take ba Annuri yakara haiba da cika ido, watannin hudu sunyi matukar taimaka mai wajen warkar da damuwar rashin dan uwan shi kadan, driver ne tare da manager dinsu ya tareshi, gaisawa sukayi ya shiga motar suka zuba mai duk kayan da yazo dasu, suna tafiya yana discussing harkar business din su Wanda an samu cigaba sosai a cikin watannin fiyeda shekarun baya, domin shi mai zafine kuma baida sanyi kamar yayan shi, yana bin diddigin komai ma'aikatan sun san an samu canjin boss ba wasa, kuskure kadan yagani ko yaji tun yana China zaisa ayi firing mutum a aiki.
Kamar daga sama suna zaune dai dai itada mommy suna hira mommy na Kara lallashin ta tareda alkawarin komai zaiyi dai dai idan yadawo tunda yafara sauraran ta. Kawai sukaji sallamar shi sama sama, wani irin zabura sukayi duka tareda sakin baki, suna mai welcome, zama yayi kawai gefen mommy ya gaida ita tareda dan sakin fuska, domin uwa uwace koda kuwa abola take yawo, he missed her domin fushin da yakeyi da ita yasa tunda yaje baya kiranta baya son ko jin muryar ta sai in ita takirashi, he know she is wrong, kuma shima he is wrong, domin ba Wanda yabashi damar watsar da uwar shi, riko Hannun ta yayi tareda sakin murmushi, "mommy am back. I'm glad my son, ya harkokin ina ji a bakin manager komai na tafiya normal. "Yeah Alhamdulillah. Wani irin rawar kafa Fauziya keyi ta matso tareda zama gefen shi tadafa cinyoyin shi dake cikin blue jeans dinshi sabo dal, "Baby wannan irin surprise haka dama kafada, am happy wallahi. Ture hannun ta yayi tareda mikewa yace" OK bari inshiga ciki zanyi wanka in huta, mommy please am hungry. Jikin ta narawa tace bari in hada maka meal din ka just five minute,Ta wuce murna fal cikin ta, tarar shi Fauziya tayi tace "darling muje part din mu mana nan akwai takura ba sakewa".
Mugun kallo ya watsa mata kafin cikin zafin rai yace "uban waye zai takuraki anan, now listing I know exactly what you are doing, ko ki dawo nan ko ki yi ta zama acan ke kadai, saboda bana ra'ayin zuwa wanna gidan if you are ready ga dakin ki can! Ya wuce abun shi.
"Kutumar uba wato dakin da Y'ar kauyen nan ta zauna yakeso ta dawo wallahi bazata dawo nan ba sai dai duk Abinda zai faru ya faru. Bin bayan shi tayi bayan ta gama dogon tunanin ta, lokacin harya tube ya daura towel, tuni taji wani irin feeling ya taso mata domin khaleel fa namiji ne complete ba algus ya ginu ya keru, wani fesar da zafin bakin ta tayi kafin ta matsa tana karairaya zata rungume shi.
Hannu yadaga mata "please, bana son disturbance, nagaji now get out.
Haba khaleel wane irin daukar Alhaki ne wannan? you're my husband why All this?, ko bankai mace bane, Auren mu wata hudu Amma ace ko hug baka bani damar yiba. "Go and ask mommy idan ta Amince da hakan saiki dawo now out. Yafada yana wucewar shi bathroom. Fita tayi kawai rai abace taci karo da mommy, me yafaru kuma kinfito da bacin rai? "Ba dole ba, yaza'ayi ace wai sai na tanbayi izinin ki zan rungumi miji na? gaskiya kekam a bincike ki kina wa yayan ki asiri ne wane irin biyayya ce suke miki kike cutar dasu, so kikeyi nima inyi rayuwa irin ta Naziya? wallahi ko kina so ko bakyaso sai kinganni da cikin khaleel. "Haba Y'ar lelen mommy zo kiji, ke baki iya siyasa ba keda zaki caba ado ki makalewa mijin ki, ya zakice banason hada iri dake Fauziya, duk soyayyar da nake nuna miki haba ki rika ragamin mana. "Nidai kiyimai magana yadawo gefen mu Ina jiran shi. "Jeki zanturo shi kin ji. Ko sauraran ta batayi ba ta fice, saida ya dauki kusan minti talatin yana kwance tareda runtse idanun shi a cikin ruwan, shi kadai yasan tunanin zuciyar shi, wani irin murmushi yayi na gefen baki, kafin ya fito ya dauraye jikin shi, ya daura towel ya fito, mommy da ya gani zaune da Abincin shi tana jiran shi yasa yace "oh my mommy am coming tank you, I really miss your cooking.
"Oh son kayi kasa kaya kazo kaci. Kananan kaya yasaka kafin yadawo yazauna, akaron farko yafara bata labarin komai kafin yayi shiru, domin tuno da dan uwan shi da yayi, "I promise, Yaya zanyi duk Abinda kake burin yi kafin nawa. Shiru tayi tareda dafashi, "khaleel, mutuwar Ahmed gibi ne babba a rayuwa ta and all tanks to wannan Y'ar gidan talakawan, look son kaga idan Har na isa dakai kar inji ka yarda da Auren yarinyar nan, idan kana so ka ciremin kewar dan uwan ka kabi Abinda nakeso. kallon ta kawai yayi ya janyo Abincin shi yafara ci, bai kuma cewa komai ba har ya cika cikin shi fal ya kora da juice, "mommy zan kwanta domin nagaji sosai, later zamuyi magana.
Kallon dan rainin wayau tayi mai kafin ta kwashe kwanonin ta tafita, wato duk maganar ta bata bukatar Ansa, saida yaga ta fita yaja numfashi, "am sorry mommy she is my wife now! Auren mu ya dauru tundaga ranar da tafita takaba, don haka soon zata tare agidan nan.
Baccin shi ya shaka bayan ya rufe kofar saboda bai son damuwar Fauziya.
Tana can ta cika tab tana jiran mijin ta ga mommy ko zancen batayi mai ba saboda damuwar Auren Naziya yafi tsaya mata arai. Bai tashi ba sai la'asar yayi sallah ya shirya yafito domin yanada Abunyi, part din yayan shi ya leka yaga ba kayan salifa, wayar shi yaciro tareda kiran manager yabashi umarni, akan ya nemo mai best company na furniture's a kano saboda he want to renovate the house, baya bukatar tsohon Abu a ciki, saida ya gama tsara komai ya fita daga gidan.
Tun fitar ta takaba ta murmure tayi tas da ita ba ruwan ta da komai fitama batayi dama kuma ita bamai yawo bace, tana cikin gida tana taya inna aiki ko tana chat a wtstp domin yana rage mata tunani da kewar Ahmed dinta, a kullum ta kalli yanda baya duniya Amma ya inganta rayuwar su Abin na mugun faranta mata zuciya, hatta da dakin su an saka musu gado da sabuwar katifa, dama basuda talaucin Abinci domin Malam ba mutum bane da ke zama, nema yakeyi iya karfin shi, a zaune take yanzu a karkashin bushiya itada shukrah suna hira sama sama tana chat, tana cikin adon ta cikin riga da sket na shadda orange sabuwa da Aunty Raliya ta dunka mata na fita takaba, dinkin yayi kyau sosai yayi cib a jikin ta, jikinta ba ko mayafi dankwalinta yadan zame kadan kana hango kwantacciyar sumar ta agaban goshin ta, yanzu Almajirai basa shigowa gidan saboda duk Anfitar dasu waje, suna sakewa sosai, Inna ce ta fito dauke da robar gyada mai bawo ta zauna itama a wurin, "Shukrah sa hannu mu bare gyadan nan da ita zamuyi sanwar dare, waccan inta dauki waya bata ji bata gani. Ajiye wayar tayi tana Dariya, "kai inna ai zan Ajiye tunda ga aiki, Amma inna me yasa bakya son a bare miki gyada a injin sai barar hannu? "Kyuiya ke damun ku yanzu" mu da Ina mukaga wainnan Abubuwan, ko nikan masara sai mu niketa a dutse, Yanzu aiku yan gayune, inkai gyada ta injin a farfashemin rabi yabi bawo. Sallamar da akayi ne yasa suka amsa tareda dagowa, Inna ta saki baki tareda cewa" maraba da mutanen ikko, mai sunan Malam kaine a gari?, dukan su sakin fuskar su sukayi, Shukrah ce tafara cewa " Yaya Sadiq oyoyo kaine? Matashi ne kyakyawa ba laifi ya matso wurin da suke Shukrah ta Bashi wurin zama ya zauna ya gaida Inna tareda gaisawa da Naziya tareda yimata gaiduwar rasuwar mijinta, Sadiq Almajirin Malam ne da yazauna a gidan kusan tun yana yaro yataso hannun Inna kamar d'anta, har makaranta yayi a hannun su yanzu yana business a Lagos kuma Alhamdulillah ya samu Abun rufin Asirin shi, shima don har gida da motar hawa ya mallaka na kanshi, yanada rufin asiri dai dai gwargwado, hira sukeyi tsakanin su domin ya zama dan gida basa mai kallon bare infact matsayin Yaya suke kallon shi,
Sallamar da Malam yayi ne tareda kuma khaleel yasa Inna ta tashi saboda kunyar taga khaleel, Wanda Naziya bata lura ma da shi ba, dariya takeyi har dimple dinta na lotsawa, saboda sun saba da Sadiq sosai,, saida ya zo gab dasu ta shaki kamshin turaren shi, dago kanta tayi sukayi two eyes ido cikin ido tuni Annurin fuskar ta ya dauke kamar yanda nashi ya dauke dif, dama ba wani fara'a yakeyi ba, mikewa tayi kawai ta dauki robar gyadar tayi kitchen zama sukayi su uku a wurin Shukrah na gaida su ta wuce itama, fuskar shi tamke suka gaisa da Sadiq, Malam yafada mai koshi waye a wurin shi, "Ibrahim Mai suna na kamar su Naziya yake a wurina, yana kasuwanci a ikko yau ya shigo. "Sadiq wannam shine mijin Naziya na yanzu". Saurin kallon Khaleel yayi domin yana ganin shi yasan wani ne kuma ya tara ko kuma dan wani, wani iri yaji yace "Malam andaura ne? "Eh kamar yanda nafada maka rasuwar mijinta wannan dan uwan shine. Shiru yayi kawai shi yasan Abinda ke ranshi, fuskar khaleel a tamke yace "Malam zan iya ganin ta? "Bismillah ai gidanku ne ga dakin ta can kuje kuyi magana. Yafada tareda juyawa suna magana da Sadiq, "yanzu dai baka komawa sai ka kawomin Matar Auren ka Sadiq tunda dai kasamu rufin Asiri Bana son zaman magidanci ba iyali. "Insha Allahu Malam" kafin intafi zan nema.
Wucewa khaleel yayi hannun shi sanye cikin pocket din manyan kayan nashi, shadda ce fara Y'ar gaske, tayi matukar haska shi, dama ga iya wanka,
Zaune take tana cewa Shukrah" shi kuma wannan daga Ina? kalla yanda ya fadowa mutane cikin gida. "Kai Aunty bakya ganin tare yakeda Malam kuma karki manta kin kusa zama Matar shi tunda ki ka ganshi yanzu, ni Ina tunanin ma kamar baya garine tun zuwan dayayi bai kuma zuwa ba sai yau. "I don't care da yazo da kar yazo kinsan da Allah zai taimakeni Malam ya fasa zancen Auren nan da nafi kowa farin ciki. "You are too late. Yafada bayan ya daga labulen dakin nasu ya shigo, saurin tashi Shukrah tayi, ya kalleta" sister excuse us please. Yafada yana murmushi kadan, tace "tom" da sauri ta fice, karasa shigowa yayi, taji kamar ta zura da gudu, juyawa tayi tareda daukar katon hijabin ta ta zura. "Hmmm. Kallon dakin yayi dakyau yaganshi fes yana kamshin turaren wuta ba wani tarkace daga gadon su sai Karamar waldrp da akwatunan su sai mirror dake dauke da kayan kwalliyar su.
Matsawa yayi gaban mirror batareda yace mata komai ba, ya dauki turare daya ya kalla ya Ajiye. Kallo take binshi dashi kawai domin rainin wayan shi yawa ne dashi, kuma so take taji ya karasa maganar daya faro tun farkon shigowar shi. Ganin baida niyyar cewa komai gashi haibar shi duk ta cika mata daki, duk taji she is not comfortable at all. "Malam ka taimaka ka fadawa Malam baka ra'ayin Aure na, domin ni bana ra'ayin Aure yanzu, musamman dakai. "Sai da wancan kazamin ko da kike wa dariya kamar wawuya right? Yafada yana juyowa tareda matsowa kusa da ita. "Nidai koma meye ni bazan Aureka ba". Hmm Ashe igiyar Auren a hannun ki zata zauna idan an daura? dago kanta tayi tareda kallon cikin idanun shi domin fadamai magana, "wane irin cin Amana ne zaisa ka Amince da Auren Matar yayan ka, kuma bayan kasan ba kaunar juna mukeyi ba? That's your opinion not mine! and listing, Aure an daura shi tun daga ranar da kika fita takaba, don haka ko kiso ko kar kiso you're under me, kina karkashin inuwar Aure na, sannan kina maganar cin Amana ko what ever, ai kece mai cin Amana har kin manta da Yaya na kin fara sakewa wani banza fuska kina dariya, listing to me, am not like my brother ni ba zakiyi min Abinda kikaga dama ba, wannan rayuwar da kikayi a baya ki gogeta this is Ibrahim khaleel, you better change your way, be a responsible house wife, if not bazakiji dadi naba.
Wani irin zafi zuciyar ta ke mata yanzu ji take da tana da karfi shakeshi zatayi har sai ya daina numfashi domin irin maganar dayake fada mata a sulale.
"Malam idan kana tunanin Naziyar daka sani ce a baya you are mistaken, inada nawa tsatstsauran ra'ayin idan naso, don haka karkayi mafarkin zanyi irin rayuwar da nayi da Ahmed a gidan ku, naso Ahmed shiyasa na jure wulakanci kuma kai kasani ba zaman dadi a rayuwar da baso sai tsana a cikin ta. "Hmm that means you hate me? "We hate each other. Tafada tana murguda baki, "ni bazanyi zaman Aure dakai ba. "OK naji kuma duk na haddace and lokaci ne zai fada mana komai, Malam ya tanbayeni yaushe zandauke ki da nace end of the month, yanzu nafasa so nake kitare a gidana domin inga ra'ayin waye zaiyi tasiri. "Nidai bazanje ba don Allah ni ka sakeni kafada musu kafasa. Har ya juya zaifita kalmar saki tasa ya juyo, tareda Kara tamke fuska, " in your dream. "Ni bazan zauna da wata kishiya ba ai Kanada mata, ni kuma bazan zauna da namiji mai mata ba, Tafada ne kawai badon Abinda ke ranta kenan ba sai don ta rasa wane irin excuse zata kawo mai.
"get ready domin zama zakiyi da kishiyoyi ba kishiya ba, and saboda careless baki kosan bana gari ba, anyway am back tsarabar ki sai kin tare, bye. Ya fice cikin hanzari, tabishi da kallon mamaki, duk zafin nan da take ganin yanada shi bai nuna mata ba, wai da gaske an daura mata Aure dashi? Ya bata sani ba? Shukrah ce ta shigo tace "Aunty da gaske fa Malam ya daura muku Aure da khaleel ya sadiq kefada min yanzu. Zama tayi kawai tareda dafe kanta, ta Ina zata fara zama dashi, wace irin rayuwa zasuyi, yazata zauna da Ahmed yanzu shima ta zauna dashi?
"Aunty nidai karki sa tunani kiyi Addu'a Allah yasa kiji dadin Auren nan fiyeda na farko. "Hmm Shukrah, bakisan halin shi bane, ni bazan taba sonshiba. "Aunty kin sani fa bakyau kaki mutum da yawa in zaki so mutum kiso shi don Allah haka in zaki k'i shi ki k'i shi don Allah.
Bansan wane irin zama kukayi da Yaya Ahmed ba Amma ki kyautata zatonki kisawa zuciyar ki hakuri zakiyi farin ciki. Shiru tayi tareda mikewa ta fito domin tana bukatar Amsa wurin inna..
Zama tayi a kitchen din tareda daukar Alayyaho tana gyarawa "Inna yaushe aka daura min Aure ban sani ba? Dago kai Inna tayi tace "kije ki tanbayi Malam ai kin San baya magana biyu, don haka karki manta da furucina, kuma kar inji musu ko jayayya akan zancen nan, kinji nafada miki kiyi ki yanka kitashi ki tuka tuwon nan ya dahu. Ta fada tana fita tabarta, wasu hawaye ta share masu zafi tareda ci gaba da aikinta, tayi Alkawari koma meye zai faru atsakaninta da shi ne zaiyi daya sanin Amince wa Auren ta.
Sai dare ya koma gidan su domin bai bar gidan Malam ba sai bayan magrib daga nan yayi gidan kawu, suka tattauna kafin yayi isha'i yadawo gida.
Lokacin Fauziya na zaune a falon cikin gida tana jiran taga inda zai bullo, mommy tuni ta shige domin batason rigimar ta, tsawon rana tana korafin yaki komawa gefen su, shigowa yayi da sallama, "me kikeyi a falo ke kadai Ina mommy? " ta kwanta, Ina kafito inata nemanka a waya baka picking? Tsayawa yayi tareda kallon ta " yaushe wannan yafara a tsakanin mu dake? Aike na ki kayi ? OK naje wurin Amaryata ne. "Wace irin Amarya, khaleel Aure zaka Kara? "Don't act like you don't know about it," salifa ka Auro min again ko wata ka samu? Wadda bakyaso ki fada dai itace kuma ba Aure nake nema ba Aure an riga an daura in kina lissafi daga ranar da zata fita takaba daga ranar ni mijinta ne, don haka next week zata tare nan gidan.
Wani irin ihu ta buga tareda zubewa ta zabga Ashar " kutumar ubancan ni zaka wulakanta duk halaccin da nayi maka sakamako na kenan kishiya da wannan yarinyar, Wayyo ka cuceni wallahi bazan hada miji da wannan ba. "Toh sai ki bar mata dama itama bata ra'ayin kishiyar kuma in zabe za ayi kinsan bazan zabe ki in barta ba, saboda Amanar Yaya na ce, zanyi komai domin in kulada Amanar shi.
"Wallahi Khaleel baka isaba Indai nono na kasha saika saketa" Aure aka daura muku bada yawuna ba, lallai Modu ya kai karshen mugu kuma munafuki, na fada maka bana son hada iri da talaka bazaka gurbata min zuri'a ba, kuma zanyi fito na fito da duk munafukin da keda hannu a cikin hadin Auren nan , sun samu nasarar lashe min kurwar yaro na babba kaima sun fara galaba akan ka, ai dole akuma likamaka tunda anga daula ba'aso abarta wallahi khaleel zakusan koni wacece muzuba nidaku da duk Wani dangin ubanka. Wucewa yayi kawai daki domin maganar ta isheshi kuma baida Abunyi akai Aure dai an daura ba fashi shi yasa yace kar kawu yafada mata,
Kwana sukayi da fauziya basu runtsa ba, zata iya Yarda asiri akewa dan ta shi yasa suka samo kanshi inba hakaba me zaiyi da ita.......... 🖊
*Matar Soja*
2⃣5⃣&2⃣6⃣
.................. Kuma kasaurare ni idan har kai ka nuna isarka ta Auren wannan yarinyar nima ka jini da kyau, saika Auri salifa itama. Wani irin Kallo yake musu daga ita har Fauziya, "mommy kinayin duk wannan Abubuwan saboda wannan useless woman din ne ko, Toh ki fada mata itama tolerating dinta kawai nakeyi a gidan nan badon Ina son ganin taba, kin san cewa ba Wani Abu da aka doramin akai mai nauyi samada igiyar Auren ta? Wallahi in kun Auro wata tare zasu tafi, wallahi bazan hana ku daura Auren wata ba, Amma igiyar a hannu na take, I won't hesitate to cut it all. Ya nuna ta da tuni tayi tsit saboda jin maganganun shi, "try and make another commotion here" zakiga true colors dina one by one now move out of my way ya fada cikin tsawa, ta fita da gudu saida ya ga tabar part din ya zauna tareda riko hannun mommy yace "sit my mommy let's talk. Ibrahim kar ka maida ni Karamar yarinya na san me kake shirin yi, Auren salifa bazan fasa ba ehem. "Mommy mommy mommy", please ki saurare ni baso nake ki canja ra'ayin kiba domin nima nawa bazan canja ba kawai mu zauna mu fahimci juna, kinga ba Abinda nake kokarin yi sai cika burin Yaya Ahmed, bazan taba wasa da Abinda yake matukar kauna a duniya ba, nafarko ke nabiyu kuma Naziya, mommy Yaya Ahmed nason ki haka Matar shi, kun Aura mai salifa batareda yana so ba, ranar da ya rasu wasiyyar in Auri Naziya yabari ba salifa ba, mommy akwai alkawarin da Yaya Ahmed yayi a gabana akan Naziya, idan har kika dawo da salifa zaki taimaka min wajen cika mishi wannan Alkawarin, forgive your only son Mommy, Ina kokarin yimiki biyayya ne domin ku Amanar Yaya Ahmed ne a wurina. "Khaleel na dade da sanin akwai raini a tsakanin mu dakai. Zamewa yayi tareda rungume ta " ba raini a tsakanin uwa da dan ta, sai soyayya da neman Albarka. "Toh in Albarka ta kake nema ka saki yarinyar nan ka zauna da zabin zuciya ta.
"Ita Naziya meye laifin ta? "Kasan matsala ta akanta bana kaunar hada jini da ita idan ka sake ka Auro Y'ar nan bazakuji dadi naba Khaleel.
Tashi yayi kawai saboda ya lura tayi nisa kamar yanda shima yayi nisan, kuma ba wanda zai kirashi ya dawo baya, wannan Alkawarin zuciyar shine, he is ready for them tundaga kan naziya mai cewa bata Son shi har fauziya da uwar gayyar. Wucewa yayi kawai yayi dakin shi tareda rufewa gam yayi baccin shi mai dadi, wanda Naziya bata samu ba, ta Kwana kukan Auren ta da shi, tareda tunanin yanda zasu zauna inuwa daya, yaza'ayi ta Amince ko hannun ta ya rike.
ta kwana Alkawarin yanda zata gasa mai Aya a hannu yanda ba abarta ta rayu da mijin da takeso ba shima bazata yi zaman jin dadi da shiba, mommy kuwa ta Kwana tsara yanda zatayi da Naziya a gidan,
Washe gari ganin kawai sukayi Ana fitarda tsoffin kayan gefen Ahmed Ana shigo da wasu na yayi masu tsadar gaske da kyau, fauziya ce ta fito da sauri tana kallon gefen, tasan halin khaleel kamar yunwar cikin ta, wato da gaske yakeyi sai ya kawo wannan yarinyar gidan nan, gidan ta shiga da gudu saboda bakin ciki mommy na zaune tafado falon kamar saukar Aradu, saida mommy ta dafe kirji saboda tsoron da taji, "oh ni Balkisu" Fauziya ki rika tunawa inada hawan jini kirika yin Abu a hankali kar kisa wata rana in zube a banza, "ba damuwa ta bane ni yanzu damuwa ta itace kifito kiga irin uban kayan da khaleel yasa ake sakawa a gidan Ahmed saboda wannan Jakar yarinyar. Tashi mommy tayi tareda cewa wane irin kaya kuma bayan wainda ke ciki ko morar su ba ayi ba? Dukiyar da muka tara zai narkawa Y'ar talak......., shiru sukayi domin ganin Ana shigo da wasu irin new designer boxes wainda basu dade da fitowa ba wajen saiti uku, sunyi tsaye kamar ruwa yacinye su, kafin ya shigo da wata katuwar Leda a hannun shi, sanye yake cikin kanan kayan nashi na fama, fuskar shi a sake yace musu suje part din shi a store zasuga wasu set biyu su kwaso su, zama yayi yana murmushi yace "mommy ki ga kayan Auren Naziya kisa Albarka. "Khaleel" zan matukar bata maka rai fiyeda tunanin ka, wannan Y'ar matsiyatan kake kashewa irin wannan Dukiyar haka kana hauka ne?, sannan duk wannan uban kayan way'enda kake cewa a kwaso kuma na uban waye? "Momy ki duba mana Abinda baiyi ba a karo mata. Ya duka tareda bubbude akwatunan, kayane na gani nafada karshen kudi kowane akwati kalar kayan da ke ciki, komai har nighties nasu akwatin daban, gefe daya Wani dan madaidaicin kit ne shakeda sarkokin gold, diamonds Harda tsadaddun passion way'enda sunyi kudin Wani zinarin, sakin baki momy tayi tace "khaleel", way'ennan kayan ko Fauziya Y'ar gidan Wani ba akai mata irin suba, don iskanci kasan kayan mata shine kabarni da siyan na fauziya?, ko kwandala baka bayar ba, yanzu akan wannan yarinyar ka narkarda Dukiyar ka haka khaleel? Shiru tayi lokacin da suka shigo da wainnan akwatunan, way'enda ya siyo ma Ahmed da niyyar ya hada a lefe suka boye, English wears ne masu matukar kyau da tsada da dogayen riguna way'enda har hango yanda zasuyi a jikin ta yakeyi, Wani irin hawaye ne ya ciko idanun shi yana tuna yanda ya yi da yayan shi akan akwatunan, a zuciyar shi yace "Yaya she is going to wear them insha Allah.
Fadan mommy yasa ya dawo daga tunanin shi, "khaleel" ka nuna min ban isa ba ko ka nuna min kai kafi dan uwanka mallakuwa ko? yayi kyau, wallahi zakaga mai zaifaru muddin ka kawo Y'ar nan cikin gidan nan. Ta wuce fuuu. Fauziya ce dake fitar da hawayen bakin ciki ta matso "Allah ya isa tsakani na dakai khaleel , wato akwatin Auren ma da sadaki na duk bakasan zafin suba, no wonder bakasan mutunci na ba banda wata kima ko daraja a idanun ka.... Wani irin hankada ta yayi baya tareda mikewa ya nuna ta, zaman yan bori tayi har tana dafe kugu, "look ba macen da keda damar fadawa khaleel magana sai mutum biyu daga mommy sai Naziya sune keda Iko da khaleel, thank God kin gane inda hakkin Auren ki yake, that's hannun mommy so from today don't ask me your hakki go ask mommy. Ya Kira masu aikin yace su kwashe mai kayan zuwa part din shi, idan masu aikin sa kayan sun gama su sakasu ciki, karku bar wurin domin za'a iya saka musu wuta saboda bakin ciki.
Suka kwashe suka fuce, yana tsaye, "khaleel" nasan me ka keso dani infita in bar maka gidan ka wataya da Amaryar ka, wallahi yadda baka bani kulawa ba itama bazata samu kulawar ka ba, mu zuba cikin gidan nan. Tayi waje tana kuka,
Girgiza kai yayi tareda cewa "let me shower and go to her, am coming baby, kema zan zo inji kalar naki salon maganar naji na nan ya isa, now is up to you.
A tsakar gidan suke tana hira dasu Sadiq yau ma ya shigo suna taya inna tsinke zogalen da zatayi musu dambu domin sadiq nason danbu sosai, hirar su sukeyi suna dariya, Malam yayi sallama, tareda khaleel yana cewa "iso Ibrahim kaima dan gidane ai basai ka jira iso na ba. Jin maganar shi baisa ta daina hirar ta ba infact bata ko dago kanta ta kalle shi ba, sanye take cikin doguwar rigar atanfa mai kyau dinkin ya matukar fito da yarintar ta da kyanta, idanun shi akanta suka sauka, zama yayi gefe tareda gaida Inna, ta amsa ta kwashe zogalen ta ta mike, tabarsu dama ba Shukrah agida tana makaranta,
Malam yace "Sadiq kana cikin mata kuna aiki inka gama kafito muyi magana. Yafada yana fita, yi tayi kamar bata san Allah yayi ruwan tsiyar shi a wurin ba,
Har suka gaisa da Sadiq, taci gaba" ya sadiq kasan Ina son in karanta mass com, saboda aiki a gidan redio ko tv Abun na burgeni sosai. Tafada tana dariya, Wanda ke karawa fuskar ta kyau, da zaka kalli fuskar khaleel da zaka hangota kamar manja saboda ja, "kai haba ai mace tafi mutunci da aikin likita Naziya, ni da badon anyi min kafa ba da tuni na jefaki school of nursing ma. Dariya tasa, wadda saura kiris ta tafi da numfashin khaleel, mikewa yayi tareda fita a zuciye, ya samu Malam a zaure, "Ibrahim harka fito? "Eh Malam magana zamuyi. "Bismillah Toh. "Nace ba laifi idan yau nadauke ta ta koma gidan mu? "Aa kaida Matar ka ai bawani laifi kawai ko yanzu ka so zaku iya wucewa, bari in fada ma mahaifiyar ta. "Toh zan tafi zuwa dare zan dawo in tafi da ita, ai badamuwa idan ba arakata ba ko? "Babu hakan shine daidai ma tunda ba Auren farko bane, Allah yabaka ikon rike Amanar dan uwan ka tareda sauke dukkan hakkin da ke wuyan ka. "Amin yace, yabi Malam suka koma ciki lokacin ta mike tsaye zata shiga dakinta, bin bayan ta yayi kawai,
Tana shiga taji mutum a bayan ta saida ta zabura, tayi baya kamar zata zube saboda tsorata datayi daganin shi, saurin riko hannun ta yayi domin zata fadi, ya fisgota zuwa jikinshi Wanda saida ta runtse idanun ta kafin tayi saurin ja baya tana fisge hannun ta, jitayi kamar ta warta mai mari, "me yasa zaka tabani? Ta fada jikin ta na rawa, "oh ba atabaki ne? Ai bansani ba, yafada yana bata Wani irin kallo mai cikeda ma'anoni tun daga sama har kasa.
Saurin bin jikinta tayi da kallo tareda juyawa tana shirin daukar mayafi, yayi saurin matsawa, " akwai Abinda zan iya yi idan har kika aikata Abinda ke cikin zuciyar ki, ni ba shashashan namiji bane, kina iya tsayawa a gaban Wani banza yanda kike so idan kinganni saiki rika neman Abun rufe jikin ki me kikeso ki boyemin?
"Kaga Ina jin kunyar ka don haka karka bari inbude baki infada maka maganar da bazaka manta daniba. "Say it am ready to hear. "Kaga kana cin Albarkacin Ahmed shi yasa kake yi mun Abinda kaga dama Ina kyale ka, not anymore, tunda kace zaka wuce gona da iri, karka manta kai kanin mijina ne, matsayin mijin da kake kokarin dorawa kanka zuciya ta bata karba ba ban Amince ba.
"Hmm first in history, naji mace na deciding yanda zasuyi zaman Aure itada mijinta, yafada yana rike gemun shi cikeda rainin hankali, "husband, yes I am your husband believe it or not, and secondly, ni nake tsara rayuwar da nakeso inyi, inaso kije ki bincika tarihi na kiji bana daukar ra'ayin Wani, I only did what I think is right, ya zakiyi rayuwa me kikeso me zaifaru dake, duk nine zanfada miki yanzu, wannan rufe rufen jikin da kike yi idan naso zan iya hanaki saka ko pant da breziya a cikin gida na, watch out wannan mijin da kike gani bakisan waye shiba, and third, later in the night you are going to my house, enough of all this hira da kikeyi da katon banza, so get ready in time, first in history miji zaizo ya dauki Amaryar shi, ya matsa gab da ita tareda cika mata fuska da hanci da tsadadden kamshin jikinshi ya hura mata iska yayi ficewar shi kamar Wani walkiya,
Ya sumar da ita da kalaman shi, saida ya fita ta zube akasa tana hade jikinta, she can feel his presence up to now, a dakin jikinta kamshin shi duk ya Kama, kalmar shi na ko pant da breziya sai yana ra'ayi zata sa ya tsaya mata arai, lallai tantiri take gani a gaban idanun ta na bugawa a jarida, zata iya rantsuwa kalmar bazata taba futowa daga bakin shi ba, yanda yake behaving like gentle man, now she is mistaken, infact batasan me zai yi nan gaba ba, kallon tsintsiyar hannun ta tayi tanajin nashi haryanzu a nata, Wani irin Yar takeji fiyeda yanda takeji idan Ahmed ya riketa, hannun shi kamar Wanda yake massaging dinshi da baby oil, saboda softness ko ita mace hannun ta baikai nashi laushi ba, she can still feels his heart beat, lokacinda ta fada na second biyar, zuciyar shi bugawa take da mugun karfi. Tashi tayi tareda kwabe kayan jikinta ta zubar akasa, ta datse kofar ta koma zubewa akasa, kallon shape dinta nayi, ta tsaru dakyau jikinta nada tsari da Wani irin kyalli abunka da fara, juyowa tayi ta zubawa tukunyar fulanin ta ido nasan cewa yes Ahmed yayi rashi babba da bai more way'ennan Abubuwan ba, a cike suke tam a girke zaune Alamar bazasu taba kwanciya ba, tashi tayi ta kalle su tasa kuka " am sorry Ahmed dana sani nabari kayi yanda zakayi dasu da nasan bazaka rayu da ni ba, bazan kasa kai maka hakkin kaba, yanzu tayaya zan iya bawa dan uwan ka kulawa, bazan iya ba kaine ka dace da duk wannan Abun ba kanin kaba, murje idanunta tayi tareda daura kuduri mai girma. Kiran da taji Inna nayi mata yasa ta zabura ta mike, wasu kayan tasa domin ta tsani way'ennan saboda kamshin shi da sukeyi, ta fita idanun ta sunyi ja. "Toh" Malam yace Anjima zaki tare gashi wannan Karon ko shiri ba'ayiba don haka na Kira yayar ku tace tana zuwa kije ki hada Abun bukatar ki. "Toh" tace kamar zatayi ihu saboda damuwa, gwara zama da mommy sau dubu da zama da khaleel a wurinta, a tunanin ta tagama zama a wannan gidan sai gashi rayuwa takuma juyawa da ita ta bahagon hannu.
Tunda yafita gidan su yana barin unguwar yayi tafiya mai nisa yayi parking a gefen titi wajen da ba hayaniyar komai ya Dora kanshi a jikin sitiyarin motar shi, wani irin numfashi yake fitarwa da sauri da sauri, yanajin kamshin turaren wutar da take Amfani dashi akaya, he can feel her chest a nashi har yanzu, runtse idanun shi yayi da karfi yana dukan iska, fauziya tasha rungume shi by mistake bai taba jin haka ba, wani irin racing zuciyar shi keyi, itace mace ta farko da ta fara sashi yaji shi a namiji, bayaso ya nuna mata rayuwar Aure sai yakoya mata sonshi, sai ya cire mata bakin cikin zamanta na baya sai ya bata dukkan farin ciki, so yake yazama bawan mace a Karon farko, Amma sai yayi amfani da nashi salon, "Am sorry Yaya, zuciya batada k'ashi, batada limit, I don't know when and how? I think tun ganin ta nafarko yes that's it, love at first sight.
"But kai take so, bana bakinciki because she love you, zan tayaka bata farin ciki I promise you bazan taba cutar da itaba that's my promise to you my brother.
Hour guda cur ya kwashe yana tunani a wurin kafin ya wuce ya samu kawun shi yafada mai yau zata tare, yasa Albarka tareda Bashi shawara akan zaman Aure, da kuma akan mahaifiyar shi, sai kayi da gaske, ina fatan kasan halin Hajiya balkisu fiyeda ni yanzu, don haka Allah yabaka ikon sauke duk wani hakki.
Godiya yayi yatafi tareda wucewa gidan,
Bakowa duk sunfita, mommy taje wurin zarah domin neman mafita ita kuma Fauziya tayi gidan su,
Tabe bakinshi yayi ya shige dakinshi ya kwanta yana murmushi, yana hango yanda maganar shi ta sa takoma kamar gunki, "this is just the beginning baby. Tafin hannun shi ya kalla, yana jin kamar har yanzu yana rike da tsintsiyar hannun ta, yasan dole taji yanda yakeji shima, ya dauki lokaci yana tunani kafin yayi bacci mai dadin gaske,
Gefen Naziya kuwa tana zaune batada zabi Shukrah ta zana mata lalle jada baki gefe Aunty Raliya ta shirya mata lafiyayyar kaza tasata ci, zama tayi ta nagi kayarta tasan aikin banza sukeyi kawai yanda Ahmed yatafi haka shima zai gaji ya sallamo ta, ba Abinda zai shiga tsakanin su, sayi sa gama. Haka ta murjeta da dilka tas, zuwa magrib ta yi wanka da ruwan kamshi da yaji hade hade, suka bata sabon kaya ta saka, tayi sallah,
Ta dade a sujudarta tana neman Allah ya taimaketa kar ya bawa duk wani makiyinta sa'a akanta, bayan isha'i Malam ya shigo gidan ya zaunar da ita tareda yimata nasiha mai ratsa jiki.
"Naziya nasan zakiji a zuciyar ki banyi miki adalci ba, nasan bakya son wannan Auren, kuma nayi matukar mamaki da kike kokarin bujurewa hukunci na, shin kin manta bana yin Abu dakai, kin manta duk Abinda nake nema sai na nemi zabin Allah, na hango miki farin ciki Naziya idan har kin daure kin karbi kaddarar rayuwar ki, kije Kiyi biyayya Albarkar mu tare da Addu'ar mu tana tare dake, Allah yayi miki Albarka. Kuka takeyi kasa kasa hawaye sharkab a idanun ta, Inna ma tayi nata tareda sa ma rayuwar ta Albarka.
Sallamar shi ce tasa Malam ya fito tareda tarar shi cikin murna "sannu Ibrahim ka iso. "Eh Malam. "Toh Hauwa fito da ita ga mijinta, "wani irin nishadi yake jinshi a ciki, tun bayan mutuwar dan uwan shi yau ne yake jin kamar Ana wanke mai zuciya da ruwan madara.
Cikin manyan kaya yake sky blue yard na maza yanada wani kyalli kyalli kana iya hango farar singlet dinshi, gayen yasan sirrin ado, kuma duk shigar da yayi kyau take mai saboda cikar zatin shi, ko dago kai batayi ba data fito cikin katon hijabi kalar kayan jikinshi, Wanda yana kallon ta yayi murmushi cikin duhun daren, wannan fitinannen kamshin nashi duk ya cika musu tsakar gida,
Inna gaisawa sukayi tace bari insa Shukrah ta kwaso kayanta. "Abar kayan zandawo inkwashe su gobe. Yafada tareda yi musu sallama ya fita, komawa tayi ta rungume Inna tasa kuka, jikinsu duk yayi sanyi, Malam fita yayi yana cewa idan kungama Shukrah ta rakota waje,........ 🖊
*Wacce wainar zamu soya a gidan khaleel my fans, wane irin rayuwa ce zatayi tareda wainnan mutane ukun fauziya momy and khaleel, meye ra'ayinku akan kudurin Naziya? Waye zaiyi nasara a wnn tafiya khaleel or Naziya? " muje zuwa time will tell insha Allah*
*Matar Soja*