A gigice Baby ta cillar da jakar hannunta, cikin waro ido ta kurma wani uban ihu tare da ficewa daga ɗakin hotel ɗin a ruɗe. Ƙarasawa Janna ta yi ta shiga girgiza ƙafar Ihsan cikin kuka da tsananin tashin hankali.
Ɗaya daga cikin ma'aikatan hotel ɗin ne ya hawo sama da sauri jin kururuwar Baby.
"Hey, Lafiya kike mana wannan kwakwazon?"
Kasa magana Baby ta yi, nuna masa ɗakin kawai take yi da hannu tare da toshe bakinta. Shiga ɗakin ya yi cikin sauri, cak ya tsaya tare da dafe ƙirjinsa cikin firgici.
"Innalillahiwa'inna'ilaihirra'un!" Abun da ya furta kenan a fili idanunsa akan gawar Ihsan dake kwance cikin jini malel-male. Da sauri ya juya ya fita ya je ya sanar da Manager na hotel ɗin abun da yake faruwa.
After some minutes
Su Janna ne zaune a police station mafi kusa da hotel ɗin, idanuwansu sun yi luhu-luhu alamun sun ci kuka sun gode Allah, sai zazzare idanuwa suke yi cikin firgici.
D.p.o dake bin su da kallo ɗaya bayan ɗaya ya dubi wani jami'i ya ba shi umarnin ya shigar da Janna cikin cell, kuka ta fara tare da yi masa magiya tana ba shi haƙuri, tsawa ya daka mata wanda ta sa su duka suka razana, ba shiri ta yi shiru ta shiga jujjuya kai. Tasa ƙeyarta jami'in ya yi har cikin cell.
"Ki nutsu, tambayoyi zan miki, kuma ki faɗa mini gaskiyar abin da kika sani, domin idan ma kin mini ƙarya zan gano daga baya, kuma hakan ba zai haifar miki da ɗa mai ido ba." Cewar D.p.o yana kallon Baby da jikinta ke tsuma.
"In...insha Allahu zan faɗa maka gaskiya yallaɓai."
"Good." Ya faɗa cikin gyaɗa kai.
"Mene ne alaƙarki da wacce aka kashe?"
"Ƙawata ce."
Jinjina kai ya yi ya ce. "Tsawon wane lokaci kuka ɗauka tare? Kuma a ina kuka haɗu?"
"4 Years back, a makaranta muka haɗu, A.b.u Zaria, course ɗinmu ɗaya da ita."
"Okay, shi ne aka haɗa baki dake kenan aka kashe ta?"
Cikin kuka Baby ta ce. "Wallahi ba haka ba ne Yallaɓai, ba ni da masaniya akan kisan Ihsan, ta yaya ma za a haɗa baki da ni a kashe ta? Ƙawata ce fa." D.p.o ya ce. "Ku ƴan wanne gari ne?"
"Dukanmu ƴan Kaduna state ne."
"Kaduna? Amma me ya kawo ku Abuja?"
Shiru Baby ta yi ta fara sosa kanta tana rarraba idanuwa.
"I'm toking to you my friend." Ya faɗa cikin tsawa.
Zabura ta yi ta ce. "Mun zo ganin wani mutumi ne?" Ya ce. "Wane wanin? Daga Kadunan kuke yanzu?"
"A'a, muna zaune a school hostel ne, daga can muka zo nan."
Jinjina kai ya yi cikin nazartar ta ya ce. "Okay, cigaba da bayani, gurinwa kuka zo?"
Cikin rawar murya ta ce. "Wani tsohon Soja ne, ita ƙawar tamu da aka kashe muka rako nan Abuja, don ta gana da shi akan wani abu." Tattara hankalinsa gabaɗaya D.P.O ya yi a kanta ya ce. "Wanne abu ne wannan da kuka taho tun daga Kaduna har Abuja saboda kawai su yi magana a kansa?"
Baby tana hawaye ta ba shi labarin duk abun da ya faru tsakanin Ihsan da General Ibrahim, ganin ba ta da mafita, kuma tana son ta kuɓuta daga zargin su da ake yi. D.P.O ya ce. "Kin tabbata abun da kike faɗa mini gaskiya ne?"
"Wallahi gaskiya ne ranka ya daɗe, kuma dalilin da ya sa ma ba mu fita tare da ita ba saboda zai zo su haɗu a lokacin." D.P.O ya ce. "Kuna da tabbas ɗin ya zo sun haɗun bayan kun fita? Kuma menene shaidar ku akan abun da kika faɗa." A raunane Baby ta ce. "Eh, lokacin da ya zo ta kira mu ta sanar mana zuwansa cikin murna, dan muna tunanin ya zo ya ba ta kuɗin da muka nema ne daga hannunsa, shaidar kuma akwai short video na tattaunawarsu ita da shi akan cikin jikinta a cikin wayoyinmu, wanda muka yi masa barazanar da shi."
Numfashi D.P.O ya sauke tare da shafa kansa ya ce. "Ya sunan shi Sojan?"
"General Ibrahim A.M"
"What? General Ibrahim A.M? Are You sure?" Ya tambaya cikin shock.
Gyaɗa masa kai ta yi cikin tabbatarwa.
Girgiza kai ya yi ya ce "Oh My God!"
Duban jami'in da ya kai Janna cell ya yi ya ce. "Officer."
"Yes sir." Ya faɗa tare da ƙamewa.
"Ka shigar da wannan ciki ka fito ɗayar."
A ruɗe Baby ya ce. "Yallaɓai dan Allah ka sallame ni tunda na faɗa maka gaskiyar abin da ya faru, wallahi ba mu muka kashe ta ba, ba mu.."
"Shut up, tashi mu je." Officer ya buga mata tsawa da faɗin haka. Kuka ta fashe da shi tare da miƙewa ta yi gaba.
Exactly abun da Baby ta faɗa shi Janna ta faɗawa D.O.P, bayan ta gama yi masa jawabin ya bayar da umarni aka kawo masa wayoyinsu da aka karɓa, ya cewa Janna ta ɗauki tata ta cire key ta nuna masa videon tattaunawar Ihsan da General Ibrahim. Da wannan damar Janna ta yi amfani ta ɗora videon a social media in seconds, sannan ta miƙawa D.P.O wayar.
Bayan ya gama kalla ya dubi wani police dake tsaye a gabansa ya ce. "Inspector, a cigaba da tsare yaran nan har zuwa lokacin da za mu gama bincike, sannan a je a taho da General Ibrahim A.M, yarinyar da aka kashe kuma a san yanda za a yi iyayenta su samu labari, and lastly aje a zo mini da Manager na hotel ɗin da abun da ya faru a ciki yanzu, a kuma bincika CC TV camera domin a tabbatar da General Ibrahim ya je hotel ɗin a yau ko akasin haka."
"Done Sir." Inspector ya faɗa tare da sara masa.
Bayan ya fita D.O.P ya dubi Janna dake ta kuka ta ce. "Wannan ya isa ya zama izna a gare ku da masu hali irin naku, yara ƙanana da ku iyayenku sun tura ku karatu amma kuna irin wannan rayuwar, yanzu wa gari ya waya? A misali idan General ɗin ne ya kashe ta hakan ya isa ku gane ba ku da wata daraja da ƙima a idanun irin waɗannan Mazan da kuke bi, ba su ɗauke ku a bakin komai ba, sun mayar da ku kamar ledar pure water saboda yawan da kuka yi a gari. Ya kashe ta ne saboda ya tsira da mutuncinsa kar abun da yake aikatawa ya fito fili, kuma a lokacin da ya kashe tan yana fita idan ya haɗu da wata ɗaukarta zai yi ya je ya sheƙa ayarsa da ita hankali kwance, ita kuma wannan ya gama da ita, da ita da Dabba duk matsayinsu ɗaya a gurinsa. Ina baki misali ne kawai ba wai ina faɗa dan ya aikata ba, dafatan kin fahimta?"
Janna da kanta ke ƙasa tana hawaye ta gyaɗa masa kai. Girgiza kai ya yi cikin takaici ya ce. "Allah ya shirya." Sannan ya bayar da umarnin a mayar da ita ciki.
General Ibrahim A.M ne zaune a gaban kujerar gaban table ɗin D.O.P, cikin shiga ta kamala, ba zaka taɓa cewa shi yake aikata baɗala da Ƴaƴan cikinsa a bayan fage ba. Bayan sun gaisa cikin ƙwarewar aiki D.P.O ya ce. "General, muna son za mu yi maka wasu ƴan tambayoyi ne a kan kisan wata yarinya da aka yi mai suna Ihsan Sadam Malali a Aminci Hotel."
Damm zuciyar General Ibrahim ta buga, amma da yake cikakken ɗan duniya ne kuma ya san ta kan harkar bincike sai ya ce. "D.P.O ni kuma? Wacce yarinya ce wannan? Me ya sa kuka gayyato ni akan kisan ta? Ba na jin ko a cikin familynmu akwai mai sunan da ka ambata balle na yi tunanin ko ina da wata dangantaka ta jini da ita, Ihsan ka ce ko wa?" Cikin nazartar shi D.P.O ya ce. "Bari ka ga hotonta, na san idan ka gani may be ka shaida ta." Bai jira cewar shi ba ya ɗauki wayarsa ya latsa sannan ya nuna wa General Ibrahim pics ɗin fuskar Ihsan da ya cika screen ɗin wayar. Ƙarɓa ya yi ya duba, cikin ɓoye razanin da zuciyarsa take ciki ya ce. "Gaskiya ban san wannan yarinyar ba D.P.O."
"Ko?" D.P.O ya faɗa tare da karɓar wayarsa.
"Ina jin mistake kuka yi ba ni za ku kira ba."
"Kai kuwa za mu kira, saboda bincikenmu ya tabbatar mana da a guest house ɗinka yarinyar ta sauka ita ƙawayenta shekaran jiya."
Cikin maziya General Ibrahim ya ce. "Eh hakan zai iya yiyuwa, saboda akwai abokaina da dama da suke saukar baƙinsu a gidan ba tare da na sani ba, because mun zama ɗaya na yarje musu hakan. Cikin gyaɗa kai D.P.O ya ce. "General please kar ka wahalar da mu ka wahalar da kanka, ka amsa kawai ka san yarinyar nan, in yi maka tambayoyin da zan yi maka, that is all."
"A'a fa, ban san ta ba zan amsa na san ta ne? Da kuka kira ni in zo akan abun da ban sani ba na yi muku musu? Na taso na zo duk da ina gaba da ku a matsayi da miƙami, amma saboda ina girmama kaki da mahukunta ya sa na zo cikin salama ba tare da jayayya ba." General ya faɗa cikin harzuƙa.
"Akan aikina nake General, kuma sanin kanka ne babu ruwan doka da wani muƙami ko matsayi, idan abu ya biyo ta kan mutum ko waye shi dole a tuhume shi, but ba wannan ne a gabanmu ba yanzu, let me show you something." D.P.O ya faɗi haka tare da ƙara ɗaukar wayarsa a karo na biyu.
A ɗarare ta shiga gida zuciyarta cike da tsoron Na'ima, kasancewar Major ba ya gari. Allah ya taimake ta Na'ima ba ta main Parlor tana ɗakinta, ajiyar zuciya ta sauke ta shige ɗakinta. A bakin gado ta zauna tare da ƙurawa wayarta ido, sai dai a zahiri ba wayar take kallo ba, tunanin wanda ya ba ta wayar da kasancewar da suka yi tare na wasu mintuna take tunawa. Har yanzu zuciyarta ba ta daina bugawa ba, ta tsorata sosai da farko, dan wannan ne karo na farko da ta taɓa daɗewa tare da wani Namiji bayan relatives ɗinta. Sassanyar ajiyar zuciya ta sauke tare da kai wayarta kan hancinta ta shaƙi ƙamshinsa, tun a jikin i.d card ɗinta ta ji tana son ƙamshin, sometimes idan za ta kwanta bacci sai ta ɗauko ta shinshina. Mr unknown ne ya faɗo mata a rai, da sauri ta latsa wayar ta cire password tare da cire ta daga Flight mode ɗin take, kamar jira ake messages suka dinga shigowa. Hannunta har rawa yake wajen dannawa ta buɗe ta karanta. Messages ɗinsa ya kai 15 ta gani, duk na yanda yake tsananin son ta ne da missing ɗinta da ya yi, a ƙarshe kuma sai ya roƙe ta akan ta taimaka ta yi masa reply koda da "Okay" ne, dan ya ji daɗi a cikin ransa. Murmushi ta yi ta tura masa da.
"Hey, How are you."
Message ɗin yana tafiya kira ya shigo cikin wayar da sabuwar Number, kallon special Numbern ta tsaya tana yi, sai da ta kusa katsewa sannan ta yi pick.
"Assalamu alaikum." Wata murya mai cike kamala da daɗin sauti ta doki kunnenta.
Sai da gabanta ya faɗi jin muryar wanda ba ta za ta ba, lumshe ido ta yi a hankali tare da gyara zama ta amsa masa cikin sassanyar muryarta.
"Na kasa cigaba da driving a dalilin kyakkyawar fuskar matata dake ta mun gizo gami da tunaninta da ya addabi zuciyata, shi ya sa na kira ki don na samu nutsuwa, i hope kin shiga gida lafiya?" Ya yi maganar cikin wani irin salo da ya ratsa zuciya gami da ko'ina a jikinta. Shiru ta yi ta rasa me za ta ce, jin al'amarin take wani mai girma a kanta.
"Ba na son ina magana ana ji na a yi shiru" Ya faɗi haka a ɗan kausashe kamar ba shi ya gama magana cikin kulawa yanzu ba.
Turo baki ta yi kamar yana gabanta ta ce. "I'm sorry, ban san me zan ce ba ne." Murmushi ya yi mai sauti ya ce. "Just say I love you My husband." Waro ido ta yi ba ta ce komai ba. Ya ce. "I'm waiting for you Madam." Nan ma shiru ta yi sai sauke numfashi kawai take yi. Murmushi ya ƙara yi ya ce. "Okay bye, thank you, take care of yourself." Bai jira amsar ta ba ya kashe wayar.
Ajiyar zuciya ta sauke tare da zare wayar daga kunnenta. sai ta tsinci zuciyarta da blaming kanta, kamar ba ta kyauta masa ba da ta yi shiru, to amma me za ta ce masa? Ita fa jinta take duk a takure, ga wani kwarjinin da yake yi mata, ga kunyar shi da take ji duk ita kaɗai.
_Adnan_
ta ambaci sunansa a cikin zuciyarta, sunan ya yi mata daɗi ba kaɗan ba. Lumshe idanunta ta yi tana hango yanda yake magana cikin nutsuwa yana motsa ƙananun lips ɗinsa kamar ba ya son maganar ko wanda aka yiwa dole. Murmushi ne ya kufce mata ba tare da shirya yin sa ba, saboda tuno kyawawan fararen idanuwansa da yake tsare ta da su.
"Angel!"
Salman ya faɗa da ɗan ƙarfi lokacin da ya shigo ɗakin yana ƙare mata kallo. Da sauri ta buɗe idonta cikin ƙoƙarin daidaita nutsuwarta.
"Me ya sa kika taho ba tare da kin sanar mini ba?"
Kalar tausayi ta yi ta ce. "I'm sorry bloody, bayan na baro class ɗinku na ji ina son shiga toilet, kuma ka san i can't use toilet ɗin school, that is why na taho gida." Ajiyar zuciya ya sauke ya ce. "Shikenan, amma kin ɗaga mini hankali sosai, kin san irin neman da na yi miki kuwa?"
"Sorry sweet Bro, ka je ka huta bari na tashi na haɗa maka delicious yanzun nan." Murmushi ya yi ya ce. "Baby girl, shi ne kika zo kika ba ni kunya a class."
Cikin shagwaɓa ta ce. "Kunyar me kuma Faris?"
"Ba ta komai, ni abun da ya fi ba ni haushi yanda ake ta tanka ki, bayan mun fito harda masu cewa in ba su contact ɗinki wai kin burge su." Ya ƙarashe zancen tare da jan tsaki. Murmushi kawai ta yi, ta rasa me ya sa Salman yake mata haka? Ba ya so ya ga maza suna kallon ta ko su yi mata magana, yanzu zai shiga ɓaɓɓata rai da jan tsaki. Lallaɓa shi ta yi ya sauko daga kumburin da yake, ta nuna masa an ba ta wayarta yau, taya ta murna ya yi sannan suka fita tare, ta shiga kitchen shi kuma ya yi ɗakinsa.
Ba ƙaramin firgicewa General Ibrahim ya yi ba da ganin wannan videon, wani irin gumi ya shiga tsatstsafowa a jikinsa. D.P.O dake karantarsa ya ce. "Zaka ce ba kai ba ne wani ne ya yi amfani da fuskarka? Wannan ƙaryar da ka yi ta ƙara sanya mini zargi a kanka." General dai kasa magana ya yi, sai goge zufa yake yana zare ido. D.P.O ya janyo laptop ɗin dake gabansa ya yi yan danne-danne sannan ya juya ta yanda za ta fuskanci General Ibrahim, bai ce komai ba sai wani kallo da yake bin sa da shi. General Ibrahim ya ɗaga ido daƙyar ya dubi laptop ɗin, videon lokacin da ya shiga reception ɗin Aminci Hotel ne.
"Wannan ma ko za ka musa ne? Ka saka facemask a lokacin dan ka yi badda kama, ma'aikacin hotel ɗin ya buƙaci ka buɗe fuskarka ya gan ka, sai ka ba shi cin hanci na 20k dan ya ƙyale ka wuce ka je ka kashe ƴar mutane. A matsayinka na babban jami'in tsaron ƙasa, wanda ƙasa take alfahari da kai."
"Haba D.P.O ya zaka dinga alaƙanta ni da abun da ban sani ba? Ni fa ba ni ba ne wannan da kake magana akansa." General Ibrahim ya faɗi haka cikin borin kunya zuciyarsa na tsananta bugu.
Miƙewa D.P.O ya yi ya ce. "Idan mun je gaba ka yi musu duk wannan bayanin." Bai jira cewarsa ba ya ƙwallawa Inspector kira, bayan ya shigo ya ce masa. "Ku tafi da shi headquarter tare da ƴan'matan nan, I.G yana jira, ya ce a mayar da case ɗin can, i will fallow you back.
Kafin dare labarin kisan Ihsan da videon da ta ɗauka nasu ita da General Ibrahim ya gama zagaye ƙasa da kewaye, duk inda ka je zancen ake yi. Al'amarin ya girgiza manyan ƙasa da Sojoji waɗanda suka san General Ibrahim, saboda yadda yake nuna shi na Allah ne akan komai, da yawa ba su yi tunanin zai aikata hakan ba.
Kwance yake akan gadonsa ya mimmiƙe baƙaƙen ƙafafuwansa, wata mata wadda da alama Matarsa ce tana yi masa tausa. Taba ce a hannunsa yana ƙarawa sama hazo daga kwancen da yake. Wayarsa dake gefensa ce ta shiga ruri, tsaki ya yi cikin maganar riƙaƙƙun ƴan daba ya ce. "Ba za a taɓa barin mutum ya huta ba." Ɗaukar wayar ya yi ya ɗaga ya kara a kunne, sai da ya zuga ya fesar sannan ya ce. "Ina jin ka ya aka yi ne? Kira da sakaliyar yammar nan?"
"Ban gane in hau WhatsApp za ka tura mini abu ba, kawai ka faɗa mini, ka san ni yanar gizon nan ba wani gane mata nake ba."
"To na ji, tunda ka dage zan hau." Ya ƙara jan tsaki sannan ya katse wayar. Yana ƴan mintocinsa ya siyi data ya kunna ya shiga WhatsApp. Wani uban ihu ya kurma tare da yar da wayar a ƙasa, cikin zafin zuciya ya cillar da tabar hannunsa tare da narka wani uban ashar ya ce. "Yata Ihsan ɗin aka kashe? Sannan kuma wancan tsohon matsiyacin gajeren Sojan ake zargi? Bayan ya gama lalata da ita? Taɓdi jan, Ibrahim ya deɓo ruwan dafa kansa, wallahi, wallahi, wallahi sai na ɗauki fansar jinin ƴata."
Aruɗe mahaifiyar Ihsan ta miƙe cikin ƙaraji ta ce. "Innalillahiwa'inna'ilaihirra'un! Mai gida me kake cewa ne? Ban fahimta ba, wacce Ihsai ɗin aka kashe? Ba dai yata ba?"
"Ita fa Rabi, wai tun rana abun ya faru, ana ta kiran wayarmu daga ni har ke ba a same mu ba. An taɓo tsuliyar dodo Rabi, za a yi yaƙin da ba a taɓa yin kamar shi ba a duniya wallahi."
Rabi da ba fahimtar abun da yake cewa take ba ta ɗauki wayar da ya cillar cikin rawar jiki ta latsa, videon gawar Ihsan da bayanin abun da ya faru ya bayyana, ƙara ta fasa tare da zubewa a ƙasa sumammiya.
Na'ima na zaune a parlour ita kaɗai tana kallo wayarta ta fara ringing, murmurshi ta yi tare da ɗagawa.
"Hello Hajiya Maryam ya ake ciki ne?"
Daga ɗaya ɓangaren Hajiya Maryam ta ce. "Komai ya kammala ƙawata, ba dai level 1 take ba department of Mass communication?" Da sauri Mami ta ce. "Nan ne."
"To ki kwantar da hankalinki tamkar tsumma a cikin randa, wanɗanda na bawa aikin nan ba ni da haufi a kansu, gwanaye ne, ba su taɓa aiki an samu matsala ba, ke dai kawai da zarar aiki ya cika ki cika musu aljihunsu da ƴaƴan banki."
"Ba su da matsala da wannan, kin san kuɗi ba damuwata ba ne, ni dai kawai buƙatata ta biya, tsinanniyar yarinyar nan ta bar mini gida ko na huta, haba na gaji, na yi makircin na yi amma har yanzu ban ci nasara ba?"
"To daga wannan karon kin gama cizan yatsa ƙawata."
Murmushi Na'ima ta yi ta ce. "Da kuwa na zuba ruwa a ƙasa na sha." Maryam na dariya ta ce. "Ko acikin kwata ne ma ki zuba ki sha, duk a cikin celebration ne." Dariya suka yi a tare cikin tsananin farinciki.
Washegari 8 Salman yake da lecture, Abra kuma sai 10 hakan ya sa ba su tafi tare ba. Ƙarfe 1 Salman ya fito daga lecture, bayan ya yi Sallah ya nufi department ɗin su Abra, ya jira har ƙarfe biyu suka fito daga lecture. Yana tsaye a bakin class dinsu yana zuba idon ganin ta, amma har kowa ya gama fitowa bai ga ko mai kama da Abra ba. Cikin mamaki ya shiga dudduba cikin department ɗin nasu amma bai gan ta ba, ya kira wayarta ya fi sau 20 ba a ɗauka ba. Hankali a tashe ya kira Na'ima ya tambaye ta ko Abra ta dawo gida? Sanar masa ta yi tana zaune a main parlour tun 12 amma ba ta ga shigowar Abra ba, direbansu ya kira ya tambaye shi ko Abra ta kira shi ya zo ya ɗauke ta? shi ma ya ce masa ba ta kira shi ba. Hankalin Salman idan ya yi dubu ya tashi, duk inda yake tunanin zai ga Abra ya duba amma bai gan ta ba, ya tattambayi classmates ɗinta amma duk amsar ɗaya ce ba su gan ta ba, majority ma ce masa suke yi ba su san ta ba, tunda kullum cikin facemaks take. University ba secondary school ba, balle ya yi report ya ce bai ga Abra ba, to wa ma zai yiwa report ɗin?
Littafin nan na kuɗi ne ₦300 NE
Via 0116886423 Sulaiman Na'ima s union Bank. Idan katin waya ne mtn na 500 idan transfer ne ɗari uku kacal.
Evidence of payment 07063065680 ko 09047871750.
[10/1, 3:01 PM] Abk: Wani irin Yarrr Abra ta ji a jikinta, saboda rashin sabo, nan da nan ta ji ta shiga wani yanayi, da ba ta taɓa tsintar kanta a ciki ba.
Ya janyo hannunta zuwa kan ɗaya daga cikin kujerun gurin ya zaunar da ita.
Abra kam ji take tamkar ta nutse a gurin nan, saboda yadda kusancin su yayi yawa, ga wannan turaren na sa mai matuƙar kashe mata jiki.
Adnan ya fuskanci yadda Abra ta shiga fargaba na rashin sabo, dan tamkar kace kyat ta gudu, sai sauke numfashi take yi.
Cikin dakakkiyar muryarsa mai cike da kwarjini yace "Abraaah" yadda ya ja sunan na ta ne ha sake jefata cikin wani yanayi, me wuyar fassara.
"Look up" yai maganar yana sake tsareta da idanunsa.
Yayi ajiyar zuciya yace "Shikenan, ba gaisuwa ma, ko ba ki yi murna da zuwana ba?"
Ta girgiza masa kai.
"Talk mana, ya kike mini rowar muryar ta ki".
"Ina wuni".
A shagwaɓe yace "gaskiya sai kin kalleni".
Murmushi ne ya suɓuce mata, har sai da ta rufe bakinta tana dariyar.
Yace "Na baki dariya ko? In dai ni ne za ki sha shagwaɓa, dan shagwaɓaɓɓe ne ni, the only son of his parents, dan haka sai kin yi haƙuri".
"Ba ka da ƙanne?" Ta tsinci kanta da yi masa tambayar, ba tare da ta shirya ba.
Ya yi murmushi ya ce "Ni ka ɗai ne, shiyasa Aka takura mini in yi Aure, ko iyayena saga jikokinsu, ban yi planing ɗin yin Aure ba yanzu Abra, na fi son mai da hankalina akan aikina sosai, saboda yanayin aikina na rashin zama guri ɗaya, amma ina ganinki komai nawa ya canza, ni ban ma zaci zan iya soyayyar ba, dan ban taɓa yi ba, shiyasa na ke jin tsoro, Allah ya sa kar wani ya yi mink kutse" shiru Abra tayi ba tace Komai ba.
"Angel" ta ɗago ta kalleshi.
Yace "Say something mana".
"To me zance?" Yadda tayi maganar ne, cikin halin na ta na shagwaɓa ya sa ya sake ƙure ta da ido.
"Abra kina son Adnan?".
Jin Maganar ta yi a bazata.
"Ki gayamini, ba na son doguwar magana, amma saboda ke sai surutu na ke, duk na gaji, kuma kin ƙi yin Magana".
"Ba ka sha ruwan ba" Abra ta faɗa tana ƙoƙa