Ta miƙe tsaye, ta ɗauki Little ta saɓata a kafaɗarta, ta fito falo.
Tana fita falon ya gauraye da ƙamshi, hakan ya yi daidai da fitowar Abbi, tare da Salima.
Bin Mami da ido ta yi, ba ƙarya Mami akwai iya gayu.
Major ya yi mata wani lallausan murmushi ya ce "Wurinki zan taho ai, na zaci baku tashi ba".
"Ni na tashi tun ɗazu" tai maganar tana nufar hanyar kitchen.
Salima ta ce "Honey dan Allah ko sau ɗaya a bani Little in ɗauka mana, tun da na zo gidan nan ban taɓa ɗaukarta ba".
Major ya ce "My dear, a taimaka a bamu aron Little mu ɗauka mana".
"Duk abin da ya shafeka ban mata iyaka da shi ba, amma abin da ya shafeni da iyalina ni ya shafa, dan haka babu ruwanta da iyalina".
"Na'ima meye haka ne? Wannan wace irin magana ce kike yi?"
"Sai kuma kayi ai" ta wuce kitchen abinta.
Ƙarfe goma da rabi na safe, Adnan ya tafi hanyar wucewarta ya zauna, ya shafe a ƙalla awa ɗaya da rabi, sannan ya hangota, tana tahowa, yau buhu ne ta maƙalo hammatarta, tana tafe tana murmushe gyaɗa tana ci.
Tana tunkaro wurin taji ƙirjinta ya tsananta bugawa, ga kuma ƙamshin turaren sa da ya cika mata hanci, ji tayi kamar ta juya ta gudu gida, karta kuma haɗuwa da mutumin nan da ba ta da tabbacin mutum ne ko aljani.
"Budurwar ƙauye, ƙaraso mana kina tafe kina ciye ciye, ko kunya ba kya ji?"
Tsayawa ta yi cak tana kallonsa.
"Idan kika gudu ba zan kai ki wurin 'yar uwakki ba".
Ta yatsine baki ta ce "Ai na fuskanci raina mini hankali kake, yaudarata kawai ka ke, jiyan in shiga gida in fito da Inna ka gudu, ka sa ta dinga yi mini faɗa, har da zata kaini wurin masu ruƙiya aljani ya shiga jikina".
Dariya Adnan ya yi ya ce "kin manta yadda ki ka dinga wahalar da ni ne nima? Ai ramawa nake yi, yanzu ina zuwa?".
"Gona zani"
"Me zakiyi a gona kuma?"
"Roro zani".
"Kinga, yanzu muje ki fara rakani gidan Sadi".
Waro masa manyan idanunta ta yi "Taɓ kawai aje a gaya wa Inna an gani a layin gidan, duk fa 'yan farauta ne a wurin masu shaye-shaye".
"Na dai ga alamar ba kya son in nuna miki in da iyayenki suke".
"Wai kai sai ka yi ta amfani da wannan damar kana tursasani, yanzu aiken Innan zan fasa muje naka?"
"Hukunci ya rage naki ai".
Ta ɗan tura baki sannan ta ce "Naji zan raka ka, amma da sharaɗi, nima zaka rakani gona ka tayani roro"
Shiru Adnan ya yi, sannan ya ce "Na amince"
"To muje, kuma daga baya zan tsaya in nuno maka gidan in dawo, dan karnuka ba zasu cinye ni a banza ba"
Nan ta yiwa Adnan jagora, suka nufi hanyar gidan Sadi ɗan kunama, wato baban yaron riƙaƙƙen ɗan ta'addan da ya addabi ƙasa tsawon shekaru.
Cin gyaɗarta ta cigaba da yi, Adnan ya fizge ledar gyaɗar ya jefar ya ce "Ke kamar ba mace ba, ko kunyar ciye ciye ba kya ji?".
"Kaga nifa ba zaka takurawa rayuwata ba gaskiya, kai Wallahi da gani mutum ne mai son kai, wannan 'yar uwa tawa da gani tana haƙuri, ka fiye masifar tsiya Wallahi".
Jikin Adnan ya yi sanyi da jin abin da Afra ta faɗa, sai ya kasa ce mata komai sai cigaba da bin ta da ya yi.
Sai da suka zo daidai wata ƙatuwar bishiyar tsamiya, ta ja ta tsaya ta kalleshi ta ce "Kaga hanyar can, da wancan karen me baƙin baki yake kwance? To duk wanda ka tambaya zai nuna maka gidansa".
"Muje ki nuna mini mana".
"Ai Wallahi ko me zaka yi, taku ɗaya ba zan ƙara ba, duk fa Mutanen banza ne a wurin"
"Alright, hakan ma na gode".
"To dan Allah yaushe zaka je wurin Inna ka gaya mata, muje ka kaini in ganta, ni ko ba 'yar uwata ba ce, dan Allah ka kai ni in ganta, ka ga kan in mutu dai na ga wani nawa a duniya"
"Ina wanda ya tsinto ki?".
"Ba nace maka ya rasu ba"
Adnan ya yi ajiyar zuciya ya ce "To ke a ina aka tsinto kin?".
Ta ɗan yi shiru sannan ta ce "Nima ban sani ba ni dai kawai yadda na ji labari, Baba ne ya tsinto ni, ya kai ni gidansa, sai ya je wurin 'yan sanda ya gaya musu ya tsinci jaririya, sai suka ce yaje Allah ne ya bashi. Sai Baba ya ce musu, ba wani bincike da za ayi? Sai suka ce ba yau aka fara haihuwar shegu a yar ba, dan da gani wannan kyan nawa ta hanyar banza aka sameni, ba lallai a samu iyayena ba, dan sun samini suna Afra saboda kyauna, yaje in zai riƙe sun bashi, to daga nan ya riƙeni ya sani a makarantar boko ai ta cewa bani da iyaye, samari da yawa na sona, amma saboda tsinto ni aka yi, sai su fasa aurena, wani ɗan gidan ɗan majalissa ne ya ce zai aureni, babansa ya ce bai yadda ba, da ƙyar babansa ya amince, an kusa kawo kuɗin Auren kuma, yayi hatsari ya mutu, kallon fa shegiya ake mini a garin nan" ta ƙarasa maganar fuskarta ta jiƙe da hawaye.
Hanky ɗinsa ya ciro a aljihunsa, ya shiga goge mata hawayen fuskarta.
"Angel, ke ba shegiya ba ce, ina da yaƙinin ke 'ya ce ta sunna, ina ga ke ce zaki dace kiga iyayenku, shiyasa Allah ya ɗauke mini Angel ya kawoni garin nan na haɗu da ke".
"Me kake nufi?".
"Twin sister ɗinki da na aura, Allah ya yi mata rasuwa kwanakin baya, ta rasu ta bar mini 'yar jaririya mace" yayi Maganar hawaye na zubowa daga idonsa.
Zubewa ta yi a wurin ta ɗora hannu a kanta ta ce "Na shiga uku!"
₦300 NE DAN ALLAH KU SIYA KAN KU KARANTA MANA
08081012143
[11/12, 3:38 PM] Abk: Ƙasa Adnan ya yi da kansa cikin ƙoƙarin tsayar da hawayen idonsa amma ya ƙi tsayawa, ganin yadda yake kuka sai jikin ƴar Baba ya yi sanyi. Idanunta cike da hawaye ta ce. "Ka daina kuka, ba a son yi wa wanda ya mutu kuka, haka Inna take ce mini idan ina kukan rashin Baba." Bai ce komai ba sai da ya share hawayen fuskarsa duka, cikin raunin murya ya ce. "Ai za ki maye mini gurbin ta ko?" Turo baki ta yi ta ce. "Huh'um, wallahi ni ba na son ka, kalle ka fa baƙi." Duk da halin da yake ciki na tuna Abra sai da ya murmusa saboda yanda ta yi maganar.
"Shikenan, tunda kin fi so na auro wata ta riƙe mini ƴata, in ma muguwa ce ta cutar da ita idan bana nan."
Shiru ta yi kamar mai nazari tana kallon shi na wasu sakanni, taɓe baki ta yi ta ce. "Ina son ƴar taka, tunda ka ce ƴar'uwata ce ta haife ta, yaushe za ka kawo mini ita ko kai ni na gan ta?"
"Ranar da kika fara so na." Ya faɗa idanunsa a cikin nata.
Janye idanunta ta yi da sauri, cikin raunin murya ta ce. "Amma ka san iyayenmu? Me ya sa suka yarda da mu?"
"Ban sani ba, amma ina nan ina bincike akan hakan, ni da wanda ya riƙi Abra."
"Abra."
Ta maimaita sunan kamar mai tunanin wani abu a cikinsa. Kallon yadda rana ta fito Adnan ya yi ya ce. "Lokaci yana tafiya, mu je ki raka ni gidan Sadin."
"Gaskiya ba zan iya zuwa ba, ni roro na zan tafi, na san yanzu ana can ana ta yi, an kusa rore gyaɗar ma duka ni ban je ba."
"Mu je na taya ki."
Kallon shi ta yi cikin mamaki ta ce. "Ai ba ka iya ba."
"Sai ki koya mini."
"Tom shikenan mu je."
Suna tafe yana tsokanar ta har suka ƙarasa gonar, wani irin farinciki da nishaɗi yake ji na kasancewa da ƴar Baba, ji yake tamkar Abransa ce ta dawo. Yara da manya damƙam a gonar, sun zagaye tumin gyaɗar kowa na roro. Cikin takaici Ƴar Baba ta dubi Adnan ta ce. "Ka ga har an cika ban zo ba, ni da nake riga kowa zuwa, kuma alƙur'an sai ka taya ni." Bai ce komai ba sai idanunsa da yake ba wa abinci yana kallon yadda ake roron gyaɗar. Ƴar Baba na ƙarasawa gurin aka fara kiran sunanta, ta kula wanda ta ga dama ta share waɗanda take jin haushi. Su kuwa ƴan ƙauyen sai kallon Adnan suke, cikin mamakin ganin shi tare da ƴar Baba, suna son su tambaye ta wane ne shi, amma yadda ta yi kicin-kicin da fuska ya sa kowa ya haɗiye gulmarsa bai fito da ita ba.
"Ka zo ka taya ni, ka tsaya kana kallo na." Ta yi maganar cikin sangartar ta.
Ƙarasowa ya yi ya tsugunna a kusa da ita ya ɗauki ganye ɗaya ya fara cire gyaɗar yadda ya ga suna yi cikin yamutsa fuska, a ransa yana tambayar kansa ko mene ne amfanin wannan abun?
Wasa-wasa sai ga SP Adnan ɗan gayu mai ji da kansa ya wuni a gona yana roron gyaɗa, don hana shi tafiya 'yar Baba ta yi da rigimar ta, Sallah ce kawai take tayar da shi, rashin sabo ya sa duk ya galabaita, kayansa suka yi futu-futu da ƙura da ƙasa. Ƴar Baba kuwa sai murna take gyaɗarta ta fi ta kowa yawa, saboda taya ta da Adnan ya yi. Sai da mai gonar ya zo ya rarraba ya ba wa kowa ladan roronsa sannan suka tafi, lokacin Magriba ta kawo kai.
Suna cikin tafiya 'yar Baba ta dube shi ta tuntsure da dariya, saboda yadda ya yi wani kalar tausayi, ga shi ya taka ƙaya a gonar da ɗingishi yake tafiya, ɓata fuska ya yi bai yi ce komai ba.
"Gaskiya kai rago ne, kana namiji amma ɗan wannan aikin ya wahalar da kai, ba ni kwanon abincina da robar ruwan idan ba za ka iya riƙewa ba."
Hararar ta ya yi tare da faɗin. "Idan na ba ki da wanne hannun za ki riƙe?"
"A kai nake ɗora buhun gyaɗata, sai na riƙe kwanon a hannu, haka nake yi kullum."
Jinjina kai ya yi, a ransa yana jinjina yadda mutan ƙauye suke shan wahalar rayuwa. Har ƙofar gida ya raka ta, har ta wuce za ta shiga gida ta dawo ta ce. "Yawwa na tuna, jiya na tafi kiran Inna shi ne ka gudu ko?"
Cikin gajiyar dake addabar jikinsa ya ce. "I'm sorry."
"Ba zan haƙura ba gaskiya, sai dai in ka yarda in kira Innar ta gan ka yanzu."
"Ki bari sai gobe, zan zo na gaishe ta my Angel, yanzu duk a gajiye nake, kin ji ma an fara kiran Sallah, ko da yake na ga ke duk wunin da muka yi a gona ba ki yi Sallar ba."
Murguɗa baki ta yi ta ce. "Ina ruwanka, dama saka mini ido kake yi." Murmushi ya yi tare da kama hannunta ya riƙe, idanunsa a cikin nata yana jifan ta da wani irin kallo.
"Na shiga uku! Don Allah ka cika ni, kar Inna ta leƙo ta gan ni ko Yaya Musa ya zo wucewa." Ta yi maganar cikin tsantsar tsoro da fargaba, idanunta duka a waje tana kallon zauren gidansu.
"Have a nice night, good bye, I love you."
Ajiyar zuciya ta sauke jin ya sakar mata hannu ta rarumi bugun gyaɗarta ta yi cikin gida da gudu a ranta tana gulmar Adnan. Inna dake alwala ta saki salati tare da faɗin. "Wai ƴar Baba kanki ɗaya kuwa? Da magaribar ma ba za kina tafiya cikin nutsuwa ba? Wunin yau bakina shiru amma yanzu daga dawowar ki zaki fara sa ni magana, me yake damun ki ne wai?" Ba ta ce komai ba sai da ta koma ta ɗauko kwanonta ta dawo, bayan ta zauna a kan kujera yar tsugunne ta ce. "Inna daga dawowa ta maimakon ki tarɓe ni da ruwan sanyi na randa da abinci amma sai ki fara da faɗa? Na je na gaji na wahala amma ko ki mini sannu."
"Ba zan yi ba, tunda ke yin abin da aka ce ki yi kike yi, yarinya kina girma amma kullum jiya i yau, ai ta maimaita magana ba kya ɗauka, sai dai ta shiga ta dama ta fita ta hagu, to in ma wani motsin ne a kanki gobe zan kai ki a miki roƙiyya a fitar."
"Taɓ, wallahi ba zan biki a zane mini jikina ba haka kawai." Ta yi maganar tare da miƙewa ta shige ɗaki.
A matuƙar gajiye ya ƙarasa gidan Hakimi, bai zauna ba sai da ya rage kayan jikinsa ya yi wanka ya shirya cikin ɓaddakama ta shiga irin ta matasan garin da kayan wani ɗan Hakimi da ya aro, bayan ya yi Sallah ya naɗe ƙafarsa da hanky, ya ci cakes ɗin da ya zo da su da lemo ya ɗauki torchlight da kuɗi ya fita. Da ƙyar yake iya tafiya saboda yadda ƙafar tasa ta ɗaure, ba ƙaramin cakar shi ƙatuwar ƙayar ta yi ba don da ƙyar ya iya zare ta saboda zugi da raɗaɗin da gurin yake masa a lokacin. Ba don dole ba da kwanciya zai yi a yanzu ya huta, amma aikin da ya zo yi ƙauyen ba na wasa ba ne, ga IG kullum sai ya tambaye shi akan ina aka kwana? Haɗuwa da ƴar Baba duk shi ya ɗauke masa hankali. Da ƙyar ya iya gano layin su Sadi ɗan kunama, yana shiga karnuka suka fara yi masa welcome da haushi..
"Kai, waye a nan?"
Muryar wani ɗan tauri cikin shaye-shaye ta doki kunnensa.
Cikin ƙwarewa a aiki ya sauya muryarsa zuwa ta yan yawa ya ce. "Ni ne, abin zuƙa nake buƙata, an ce mini babu inda zan samu sai nan."
Haske shi aka yi da fitila mai haske ba tare da ya san waye ba, sai da suka ƙare masa kallo sannan wanda ya yi magana da farko ya ce. "Kawo silalla a baka abun duniya Baba." Bai ce komai ba ya zaro kuɗi ba tare da ya ƙirga ba ya ba su. Wiwi suka ba shi da wani abu a kwalba wanda ya tabbatar giya ce, karɓa ya yi ya zauna ɗan nesa da su yana kallon gurin cikin nazari, wani ƙaton gida da ya banbanta da ginin gidajen garin ya ƙurawa ido, ko tantanma ba ya yi nan ne gidan Sadi ɗan kunama.
Mami ce zaune a main parlour tana ba wa little abincinta, bayan ta ƙoshi ta kwantar da ita akan carpet ta shiga kitchen don ɗauraye bowl. Kafin ta fito amarya Salima ta shigo parlour'n cikin wasu matsatstsun kaya riga da wando, sai baza ƙamshi take. Ganin little a kwance ita kaɗai ya sa ta ɗauke ta cikin sauri ta fara yi mata wasa tana shilla ta tare da yi mata waƙa.
"Mamana kin fi ta kowa, ƴar fara kyakkywa, mai kama da mamanta."
"Malama ya za ki ɗaukar mini yarinya kina ciccilla ta sama a daren nan? Mene haka?" Na'ima ta faɗa lokacin da ta dawo parlour'n tare da ƙwace little a fusace.
"Ki yi haƙuri kar ki karya mata haƙarƙari."
"In na karya kina da asara ne? Haba, bana son maita, na ce bana son ana ɗaukar mini yarinya amma don naci da rashin zuciya sai an ɗauka."
"A'a, hayaniyar me nake jiyowa tun daga baranda? Lafiya?"
Abbi da ya shigo gidan ya tambaya idonsa akan Nai'ma.
Hawaye Salima ta ƙaƙaro cikin kissa ta ce. "Ban san me ya sa ba ta son na ɗauki little ba, ko na yi mata wani lefin ne ban sani ba, ni kuma ina da son yara, shi ya sa bana zuciya na ƙi ɗaukar tata." Duban Na'ima dake huci ya yi ya ce. "Na'ima ke kika haifi yarinyar nan ne ko ke kaɗai aka haifawa ita? Abra is my daughter, ke da Salima kuma duk matana ne, don haka yadda kike da iko da abin da Abra ta haifa ita ma haka, don haka kar na ƙara jin wata rigima ta tashi don ta ɗauki little."
"Wallahi ba zai yiyu ba, Abran ai ni na riƙe ta ba wata can ba, don haka nike da iko da abin da ta haifa."
"Okay, abin da na faɗa ne ba za ki bi kenan? To cigaba kar ki fasa, kar ki ɗauka wai na sauya ne daga Khamal ɗin da kika san ni saboda kwana biyu ina ɗaga miki ƙafa, fitina ce kawai bana so." Ya yi maganar cikin fusata.
Miƙewa Salima ta yi ta kama hannun Abbi tare da kwantar da kanta a jikinsa, cikin muryar rarrashi mai cike da salo da shagwaɓa ta ce. "Honey please ka bar maganar, in dai little ce ba zan ƙara ɗaukar ta ba." Bai ce komai ba sai gefen fuskarta da ya shafa cikin ƙauna.
Tsaki Nai'ma ta ja ta yi wucewar ta part ɗinta, zuciyarta cike da tuƙuƙin baƙin ciki da kishi. Tana shiga ɗaki ta goye A'isha Humairah sannan ta ɗauki wayarta ta kira Aunty Wasila, bayan ta ɗaga ta fashe mata da kuka.
"To uwar kuka, yau kuma me ya faru?"
"Na gaji Aunty wasila, na gaji da zaman baƙin ciki da ganin takaici, wallahi zuciyata ba za ta iya ɗauka ba, idan aka cigaba da haka watarana sai dai ku zo ku tarar da gawata."
"Yanzu dai faɗa mini mene ya faru."
Cikin gunjin kuka Mami ta ce. "A gabana fa Khamal yake nuna wa yarinyar nan k'auna, ya rungume ta ko ya ba ta abinci a gabana ba komai ba ne a gurin shi, washegarin da aka kawo ta da yamma har da fitowa main parlour tana tafiya ƙafa a tale, a dole sai ta nuna mini an ɓurma ta, iskanci dai kala-kala."
"Ke ma sai ki tsuro da naki salon, mijinki ne fa, kin fi kowa sanin shi, ai kowa ya iya allonsa ya wanke kawai, amma kya zauna kina wani koke-koke, har yanzu ba ki bar shashancin nan ba Na'ima? Sai ka ce a kanki aka fara kishiya? Duk kin fice daga hayyacinki."
Shiru Mami ta yi ba ta ce komai ba, ita kaɗai ta san halin zafin kishin Mijinta da zuciyarta take ciki, idan ta ga Abbi tare da Salima sai ta ji tamkar ta shaƙe su saboda tsananin baƙin ciki, ga yarinyar da shegiyar kissa da iyayi da firirita.
Washegari da safe Nai'ma ta fito don haɗa wa kanta breakfast ta tarar da Abbi da Salima zaune akan dinning suna cin abinci a cikin plate ɗaya, Salima sai nanaƙe shi take tamkar za ta koma cikinsa, shi kuma sai jifan ta yake da wani irin kallo ƙasa-ƙasa. Wani irin abu mai kaifi da zafi ne ya soki zuciyar Mami, mijinta abin son ta wanda suka shafe fiye da 20 Years tare amma yau shi ne yake soyayya da wata macen da ba ta fi Yar cikinsa ba a gabanta, ji ta yi tamkar ta juya ta koma part ɗinta, amma dai ta ɗaure saboda kar a gane halin da take ciki ta nufi kitchen, cikin yaƙi da hawayen dake ƙoƙarin fita daga cikin idonta. Kamar yadda ta yi tamkar ba ta gan su ba haka su ma suka yi, sai Salima ce ta bi ta da kallon gefen ido tare da sakin wani munafukin murmushi.
Rasa abin da za ta girka ta yi, yunwar da take ji ma nemar ta ta yi ta rasa saboda mugun ganin da ta yi, tana hawaye ta dafa noodles guda ɗaya ta juye ta a plate ta fito bayan ta goge hawayen fuskarta. Kakarin aman da Salima ta fara ne ya sa ta tsayawa cak ganin ta tashi ta shiga toilet ɗin dake parlour'n da sauri, a ruɗe Abbi ya bi bayan ta yana faɗin "Lafiya Baby? Me ya faru?" Ba ta ba shi amsa ba sai da ta gama aman, kamo ta ya yi suka fito yana yi mata sannu, har lokacin Nai'ma tana parlour'n a tsaye ta kasa tafiya.
"Baby ko na ɗauko key ɗin Mota mu tafi asibiti ne?" Ya yi maganar yana shafa bayanta.
Ƙara lafewa ta yi a jikinsa tana kallon Mami cikin yamutsa fuska ta ce. "A'a Honey ba wani abu ba ne, kawai ƙamshin turaren da Maman Salman ta fesa ne bai mini ba, tunda ta fito cikina ya fara hautsinawa, da ta dawo kuma sai na ji abin ya tsananta." Duban Mami Abbi ya yi cikin ko in kula ya ce. "Please ki daina saka turaren da kika sa, kin ga ya sa Baby amai, ko kuma idan kin san ki daina fitowa parlour idan tana nan." Ya ƙarashe maganar tare da kama hannun Salima dake ta toshe hanci suka bar parlour'n. Tsananin baƙin ciki da takaicin da Mami ta ji ba zai misaltu ba, ba ta san lokacin da ta saki plate ɗin hannunta ba indomien ta baje a ƙasa ba, cikin kuka mai cin rai ta yi part ɗinta da gudu.
"Doctor magana fa nake maka ka mini shiru, haba, I'm tired da wannan sabon halin da ka tsiro da shi, gaskiya."
"Na miki dole ki zauna da ni a hakan da nake ko kuma na ɗaure miki ƙafarki ne na hana ki tafiya? Idan ba za ki iya ba you are free to go."
Cikin tsantsar mamaki da shock Hajiya Saudat ta ce. "Yusuf! Yau ni kake fadawa ba ka ɗaure wa ƙafa ka hana ni tafiya daga gidanka ba?"
"Uwata ce ke da ba zan faɗa miki haka ba?" Ya yi maganar yana jifan ta da wani mugun kallo, kasa magana ta yi saboda tsananin al'ajabi. Dogon tsaki ya ja ya ɗauki coat ɗinsa da briefcase ya bar mata ɗakin. A wahalce ta yi zaman ƴan bori a ƙasan ɗakin jin kanta na juya mata, wata irin mummunar faɗuwa gaba ce ta ziyarce ta, lokacin da wani tunani ya ɗarsu a ranta.
Daga yanayin yadda ya shigo asibitin ma'aikatan suka san babu lafiya, dama kwana biyu zuciyoyinsu cike suke da mamakin rashin zuwan shi Asibitin, kasancewar wannan ne karon farko da hakan ta taɓa faruwa. Suna gaishe shi amma ba ya amsawa, fuskarsa a cukule ya ƙara office ɗinsa. After 30 minutes ya aiko a kira masa Nurses and doctors ɗin dake asibitin. Bayan sun hallara ya dinga kiran su ɗaya bayan yana ba su wani envelope. Fuskokinsu cike da mamaki suke baro office ɗin.
"Na shiga uku! Takardar sallama fa na gani." Cewar Nurse Basira cikin tashin hankali.
"Ni ma haka." Sauran Nurses ɗin gurin suka haɗa baki gurin faɗar haka.
Kafin su ƙara magana wani likita ya fito daga office ɗinsa fuskarsa ɗauke da tashin hankali, yana share zufa ya ce. "Don Allah ko kun san laifin da na aikata da na cancanci kora a asibitin nan? A sani na ni dai ban yi komai ba."
"Ai ba kai kaɗai aka kora ba, mu ma nan duk korarraru ne."
"Innalillahiwa'inna'ilaihirra'un, to me yake damun Doctor Bulama? Me aka yi masa da lokaci ɗaya zai kori fiye da rabin ma'aikatan shi? Anya lafiya kuwa?"
"Ƴar Baba ki je ki ɗebo mana ruwan nan, ko na shiga banɗaki fa babu a gidan nan."
Diddire ƙafa ta fara yi tare da faɗin. "Wai don Allah Inna da girmana zan fita ɗiban ruwa? Salan a raina ni."
"Ni zan fita in ɗebo kenan? Don yau ɗaya mai ɗebowar ba ya jin daɗi shi ne ba za ki fanshe shi ba? Shi ba mutum ba ne kenan da kullum yake ɗebowa kike facakar ki da shi."
Ba ta kuma magana ba ta figi mayafinta ta ɗauki botikan ɗiban ruwan da guga ta fice kamar za ta tashi sama.
"Budurwar ƙauye."
Ta tsinkayi muryar Adnan a kanta yana kiran ta. Tsayawa ta yi amma ta ƙi juyawa ta kalle shi, sai cuno baki take kamar zai taɓo sama.
"Ni fa ba sunana budurwar ƙauye ba, ba haka Babana ya raɗa mini ba gaskiya."
Murmushi ya yi ya ce. "Ina zuwa da wannan botukan?" Ya soso mata inda yake mata ƙaiƙayi, hakan ya sa ta shagwaɓe fuska ta ce. "Yaya Musa ne ba shi da lafiya, shi ne Inna ta ce wai yau ni zan ɗebo ruwa."
"Ina ne gurin ɗibar ruwan?"
"Bayan nan ne." Ta yi maganar tare da nuna masa hanyar.
Bai ce komai ba ya karɓi botikan suka jera suna tafiya. Gurin ɗiban ruwan rijiyoyi ne da yawa, mutane mata da maza kowa ya zira gugansa yana ɗiba. Ƴar Baba na zira guga Adnan ya karɓa ya fara janyo ruwan yana zuba mata a cikin botikan, bayan sun cika ya ɗauka ya kai mata har ƙofa gida, ita kuma ta ɗauka ta shiga da shi ciki. Haka suka dinga yi har ƴar Baba ta cika komai na gidan.
"To ko ke fa, ba ga shi har kin gama ba, sannu Allah ya saka da Alkhairi, amma yau kin yi sauri, hala babu layi ne a gurin?" Inna ta faɗi haka lokacin da Ƴar Baba ta dire bokitin ƙarshe.
"Ke dai ba na deɓo miki ruwan ki ba?"
"To ai na ga da in kika tafi ɗiban ruwan sai ki wuni akan bokiti ɗaya, kina ta neman magana a can."
Tura baki ta yi ba ta ce komai ba ta fita gurin Adnan dake jiran ta a waje. ganin yadda duk ya jiƙa wandon jikinsa ya sa ta kwashewa da dariya har da ƙyaƙyatawa. Ɓata fuska ya yi ya ce. "What's funny?" Girgiza kai ta yi tana cigaba da dariyar. Ɗage kafaɗa ya yi ya ce. "Gurin Inna na zo mu yi magana a kan ki, sannan in sanar mata iyayena za su zo neman aurenk.."
"Taɓ, wallahi ni bana son ka ba zan aure ka ba." Ta katse shi da faɗin haka cikin serious dake tabbatar da abin da ta faɗa har cikin zuciyarta haka ne.
Littafin kuɗi ne, ku biya kafin ku karanta. 09047871750
[11/14, 9:13 PM] Abk: "Are you sure baki so na ba zaki aure ni ba?" Adnan ya faɗa cikin tsoro da fargaba maganar data nemi ta sar masa da mikin dake damun zuciyarsa na rashin Abra.
"Ni fa ba zan taɓa aurenka ba, gaskiya kayi mini baƙi da yawa kuma bana son ka shi ne kawai....,"
"Stop it.." ya faɗa a tsawa ce yana riƙe saitin zuciyarsa dake masa zafi lokaci guda, kalaman bakin Afra na neman sauya masa lissafi. Kasa magana ya yi sai idanunsu daya rufe zuciyarsa na harbawa.
"Na kawo maka ruwa kasha ne, naga kamar ka ƙware?" Ɗago jajayen idanunshi ya yi tare da zuba mata akan fuskarta wanda a kullum take masa gizo, ƙarfin hali yake kawai na Kasancewar su tare da yawan lokota sai ya ji kamar ya jawota ya rungometa ya faɗa mata how much he loving her!
Ya sauke numfashi a galabaici yana kallon yadda tai shiru tana binsa da idanu. Ba tare da ya ce komai ba ya juya ya bar ƙofar gidan nasu.
Ita ma bata kira shi ba, amma har zuciyarta ta ji babu daɗi a shirunsa da tafiyar ta shi, zuwa yanzu ta fara sabawa da shi.
"Wannan karan kuma mene ya faru kika shigo jiki a saɓule kamar kazar da ƙwai ya fashewa?" Inna ta tambayi Afra wacce ta shigo tana bin bango ta luuula duniyar tunani da alama bata ma san abin da Innar ke faɗa ba.
"Yau naga abin da ya ishe ni, anya yarinyar nan lafiyarki ɗaya kowa? Ina ta ɓaɓatu kin yi mini shiru?. Haka kurum kada naje ina tufka wani na warware mini ita na shiga uku"
Nan ma dai Afra ba ta ce komai ba sai bin bango da tayi ta zauna tana wawware idanunta. "Kee! Kee!! Ƴar Baba?"
"Na'am Inna"
Afra ta faɗa a gigice bayan Inna ta girgiza kafaɗarta.
"Lafiya ke dawa,ina kika je bayan kin kawo ruwan?"
"Gasky Inna tambayarki ba zata mutum ya yi ilimi ba, tunani nake fa amma gaba ɗaya kinsa na manta abin da nake ina jinki fa" Inna ta riƙe haɓa tana faɗin..
"Tunanin uban me kuma? Salon ki kawa kanki ciwo" ganin hawaye a fuskar Afra ya sanya jiki babu ƙwari Inna ta tana tambayar lafiya Meke faruwa da ita haka?..
"Inna tun bayan mutuwar wanda zan aura har yanzu babu wanda ya ce yana so na zai aureni, haka zan ta zama kenan kalli ƙawayena ko wacce tana yaranta abin sha'awa wasu kuma ciki garesu"
Cikin kulawa irin ta Uwa da Ƴa Inna ta kama hannun Afra tana cewa.
"A'a Ƴar Baba shi aure lokaci ne, na sha faɗa miki da lokacin ki ya yi ko bakya so sai kinyi auren nan, zaki auri miji wanda babu irinsa a garin nan ƙyakƙyawa ƙin kowa sai wanda ka taɓa,
Ba kiga kalarki ba wanke hannu ka taɓa kada ki saka wannan a ranki muna ta addu'a kema kici gaba da yi"
"Kuma bakya tunanin sbd bani da iyaye ba a zuwa neman aure na Inna?" Yanayin yadda ta yi maganar a raunace ya sa Inna yin shiru ita ma abin yana susa mata zuciya ainun bata da yadda za ta yi ne.
Ɗaki Afra ta shige zuciyarta babu daɗi abubuwa suka dawo mata sabbi a rai. Tana jin kamar bata kyautawa Adnan ba, bata ji daɗin yadda ya tafi ba babu farin ciki akan fuskarsa kamar kullum. Kuma ba lallai ya dawo ba. Kuka ta fashe da shi na rashin abin yi a haka bacci ya ɗauke ta.
Tun da ya shigo ɗakin ya kasa zaune ya kasa tsaye "Bana son ka" kalmar ta tsaya masa a rai, ashe haka ake ji idan an cewa mutum ba a son shi? Yaya matan da suka dinga son shi a baya suka ji a zuciyarsu? Afra akwai wauta amma zantunkan bakinta daga zuciyarta suke, babu alamar ƙarya ko wasa a cikinsu tana nufin abin da ta ce ne.
"What should I do? Adnan think, think" ya faɗa a hankali yana rufe idanunshi. Ba zai fushi da ita ba,amma dole ya ɗaga mata ƙafa domin fahimtar zuciyarta.
Wayarsa ya ɗauka ya kira Hajiya Mama tana ɗauka ya kwaɓe fuska tare da langwaɓar da kansa gefe guda.
"Son ya dai?" Cikin ƙasa da murya ya ce "Evening Hajiyata" ta amsa da "How are you? Ya zaman village? The you like it"
"Sure Mama, kawai ki tayani da addu'a wani abu na neman tunkaro ni kamar zai bani wahala kuma" Hajiya Mama bata fahimta ta ɗauka al'amarin aiki ne hakan ya sa ta ce.
"Addu'a kam kullum muna yinta Sp Adnan Aliyu Matawalle, Allah ya taimaka ya baka sa a Insha Allah zaka samesa cikin sauƙi"
Idanunshi ya lumshe yana jin nutsuwa na saukar masa a hankali ya mirgina gefe yana jan numfashi ya ce.
"That's why i always love you Mom..."
Murmushi tayi cike da jin daɗi domin tana ƙaunar Adnan ji take kamar ita ta haife shi duk da cewa ita bata taɓa haihuwa ba, maybe bata ɗaya daga cikin matan da suke haihuwa a nan duniya.
"Hajiya, Abba...." Ya faɗa cike da rauni domin ya fara gajiya Abba shi ne cikon jin daɗinsa dama samun nasarar baki ɗaya, sai da shi duniyarsa ke zama cikakkiya.
"Me Abba ya yi kuma Adnan?" A kasalance ya ce. "He still angry with me na rasa yaya zan yi ne bana jin daɗin"
"Adnan my Son kada ka damu da hakan, Abbanka surprise ɗinka zai yi very soon ka mai da hankali kawai wajan yin aikinka Please" Hira su kaci gaba dayi cikin nuna soyayya a haka Adnan ya manta da ɓacin ran da Afra da haddasawa zuciyarsa.
Yau ranar kirkin Mami ne tana zaune gefen gadonta lokacin kusan ƙarfe goma na dare ne, ta shirya cikin wasu haɗaɗɗun kaya na barci, hannunta ɗauke Aishatul-humaira wacce taƙi yin barci yau sai dry ta kewa Mami tana ɗaga ƙafa duk ta cire sosan da aka yi wa kanta ado da shi.
"Sweetheart yau hirar dare za mu yi kenan, kwana biyu daddynki bai neme mu"
"Idan ba Dady ai akwai grandfa right?" Abbi ya faɗa yana shigowa cikin bedroom ɗin sanye yake da ƙyakkyawar shiga ta barci sai ƙamshi yake zabgawa.
Mami bata kallesa ba hankalinta akan Aishatul-humaira iya kuzarin yarinyar abin sha'awa ne. Hannu ya sa ya ɗauki little yana mata wasa amma ta ɓata fuska alamar anyi mata ba daidai ba.
"Wato Na'ima na saka ki a bedroom tana hure miki kunne akan Granny naki ko, shi ne zaki ɓata fuska?" Kamar Aishatul-humaira ta fahimci abin da ya ce ta fashe da kuka sosai tana cilla ƙafa, Abbi ya waro ido yana miƙa wa Na'ima ita ya ce.
"Wannan soyayyar taku daga Allah take, maza ki bata haƙuri" jijjigata ta dinga yi a haka tai barci tana sauke ajjiyar zuciya. A nutse Mami ta kwantar da ita bayan tai mata addu'a ta miƙe zata bar ɗakin "Na'ima" Abbi ya kira sunanta yana bin jikinta da kallo ƙamshinta na fisgarsa zuwa gare ta.
Wajanta ya ƙarasa ya tsaya daidai bayanta tare da saƙalo waist ɗinta da hannunsa biyu cikin ƙasa da murya ya ce "Ni kike azabtarwa haka Na'ima? Ba zaki amshi wannan auren matsayin ƙaddararmu baki ɗaya ba? The you know how much i miss You? Baki san adadin son da nake miki ba ko?" Juyo da ita ya yi gabansa yana kallon yadda hawaye duk ya ɓata mata fuska ta wani shagwaɓe fuska.
"Am sorry first love uwar gidan Major Khamal Khamis, ki yafe masa mana?" Ɗaga ta yi suka haɗa idanu ta ɓalla masa harara dry ya yi mai sauti yana jawota baki ɗaya zuwa jikinsa ya matse ya ce "Ohhhu dai naji, muje na nuna miki wani abu?" Ya faɗa yana sumbatar wuyanta tare da janta zuwa other bedroom.
Washegari abin har mamaki ya bawa Salima ganin har 12 Abbi bai fito ba, kamar yadda ya saɓa ɗakinta ya tashi da wuri ya duba Na'ima da little ɗin. Tana zaune a Parlour watching TV taji dry ƙasa ƙasa da sauri ta juya zuciyarta ce ta buga ganin Na'ima cikin wani dakakken lace mai masifar kyau, sai Little a hannunta wacce ta farka tuni ita ta tashe su ma, Abbi ya saƙalo jikin Na'ima shi kansa bai san adadin son da yake mata ba. Zama sukai a saman Kujera Salima tai murmushi ta ce "Barka da fitowa honey?"
"Yawwa Barka baby" ta juya kan Na'ima wacce take latsa waya tana ƙoƙarin ɗaukansu a photo ta turawa Salman "Maman Salman an tashi Lafiya?" Mami na ɗora kai a shoulder ɗin Abbi kamar dole ta ce.
"Ya kike?" Kalmar ta daki zuciyar Salima sai kawai ta share, Naima na ƙoƙarin turawa Salmanun-faris photos taji Sallamar sa da sauri ta miƙe tsaye tana mmki, yana tsaye bakin ƙofa cikin wata dakakken shadda kyan da Salman ya yi ya ɓaci, ya zama cikakken matashi wanda samun kamarsa za a daɗe ga haiba da kwarjini. Cikin sauri ya ƙarasu yana ɗaukan Little wacce ta kafesa da idanu irin ta ganesa ɗin nan "My sweetheart my happiness daddy is here...
Tsayin kwanaki uku ciff Adnan ya ɗauka bai sake haɗa hanya da ƴar Baba ba, hankalinsa akan aikin daya kawosa baya son haɗa abu biyu domin ya fahimci yarinyar na neman bashi ciwon kai. Cikin ikon Allah ya samu nasara cikin daren wata rana aka zo aka tafi da Ɗan kunama da sauran muƙarrabansa. Adnan kuma ya ce akwai abin da ya ke jira. Amma duk wanda ya gansa ya san baya cikin nutsuwar ya faɗa tsoro da zullumin yadda zai ƙara tunkarar Afra a lokaci na barkatai suka ƙara wanzuwa a ransa, neman aurenta ya bambanta dana Abra domin cikin lokaci kaɗan ta amince masa.
Ƴar Baba na kwance abin duniya ya isheta ko abinci kaɗan take ci, tunanin rashin ganin Adnan kwana biyu ya addabi zuciyarta. Inna dake zaune ta juya tare da kallon Afra ta ce "Yau idan baki faɗa mini abin da ke damunki ba, babu abin da zai hanani yi miki doka wallahi"
"Haba haba don Allah Inna dame zanji ne wai? Kawai baki san meke damuna ba kici zaki dakeni, ko na faɗa miki cewa zaki aljanu suka shafan nidai kawai ki barni da abin da ke damuna"
Miƙewa tsaye Inna tayi tan ɗakko abin doka ta ce "Bari dai ki gani, kina zaton ba zan iya bugunki ba ƴar butu uwa kawai ja'ira" da gudu Afra ta bar gidan bayan ta ɗauki mayafinta.
"Kinibabbiyya ki tsaya mana kiga yadda zan yi dake yarinya ta mayar dani kamar kakarta" Inna ta faɗi haka tana ajjiye abin dokan data ɗakko.
Adnan na tsaye a ƙofar gidan cikin wasu ƙananun kaya masu kyau ya saka sunglasses a idanunshi ya harɗe hannayensa a ƙirji. Kamar daga sama ya ga ta fito tana haki ganin tana ƙoƙarin yin gaba ya sanya hannunsa tare da kamo nata.
Jin an riƙe hannunta tayi saurin waigowa idanunta ya sauka akan sa bata taɓa tunanin zata gansa ba, ganina ya sanya ta masa ƙuri da idanu wanda suka cika da hawaye. Baya ta juya masa tana sakin kuka tako a hankali cikin nutsuwa zuwa inda take suka fuskanci juna, tallafo fuskarta yai yana kallon yadda take kuka sosai kamar wacce ya daka me hakan ke nufi? Kewarsa tayi ko mene? Ita da ta ce bata son shi.
"Mene? Why are you cry" ya tambaya a hankali turo baki tayi tana ƙara fashewa da kuka. Adnan ya dafe kai ya ce "Goodnight Zaki tarwatsa mini zuciya angel bake kika ce bakya so na ba?" Cikin shassheƙar kuka ta ce.
"Kuma don na faɗi haka sai ka daina zuwa ko?"
"To tunda baki so na me zan miki?" Ta tura baki ta ce "Ni ba ruwana da kai,mun ɓata" ta ɗan dire ƙafarta tana ƙara sautin kukanta.
Juyawa ya yi ganin ba kowa a wajan ya ɗan lumshe idanunshi yana jawota gefensa trying to hug her ya ce "Ohhh am sorry my rigimammiya yanzu gani" ya share mata hawayen tas yana riƙe da ita sosai kuma ba tai ƙoƙarin guduwa ba. Ya riƙe haɓarta ya ce "Ina son ganin Inna Angel zaki kiramin ita?" Kai ta ɗaga masa yaja hancinta tare da kai baki kamar zai sumbaci wajan ta zilli da sauri tana masa dry. Girgiza kai kawai ya yi yana tsaye ta dawo ta ce Inna ta ce ya shiga, da fara'a Inna ta amshesa bayan sun gaisa ya zayyana mata abin da ke faruwa, da zuwansa garin da ganin Afra da ya yi ya ɗauka matarsa ya yi mata bayanin komai.
Ta jinjina kai ta ce "Ikon Allah, ashe rabon ganin wani dangin ƴar Baba ne ya sa kuka haɗu, Ubangiji ka amsa mana wannan addu'ar"
"Amin" Adnan ya amsa idanunshi akan Afra wacce tayi kwance a cinyar Inna sumarta gwanin sha'awa duk ta bayyana domin ita har tafi Abra tsayin suma.
"Ai ba zama bari a ki rawo kawonta sai an yi magana ta fahimta ko?"
"Hakan yafi ina son komawa,amma sai an tsayar da manufa" "Ƴar Baba maza jeki kira kawonki yanzu" miƙewa tayi ganin Adnan ɗin ne kuma yasa ba tai musu ba. Suna zaune ta dawo tare da kawon nata. Sun gaisa da Adnan cikin sakin fuska, da farin ciki bayan ya gama jin komai ya ce. "Allahamdulilla Allah abin godiya, yanzu dole mu fara ji idan ita ƴar baba na son shi kuma zata aure shi ko?" Inna ta ce "Haka ne" ya juya kan Afra ya ce "Ƴar Baba kina son Adnan ɗin?" Ta kalli Adnan wanda yake Kallonta yaji abin da zata ce duk a tsorace yake. Kamar daga sama yaji ta ce "Kawo gaskiya bana son shi, kawai iyaye na nake son a kawo mini ko akai ni wajansu amma ba zan aure shi ba" Innalillahi wata zufa ce ta shiga yankowa Adnan ya kasa cewa komai sai kansa da ya sunkuyar zuwa ƙasa.
"Yarona Adnan kada kaji komai, ina son ka kira wasu naka muyi magana ta fahimta batun ƴar Baba ka barta akwai ƙuruciya kaji ko?" A sanyaye Adnan ya yi musu godiya kana yabar gidan.
Ikon Allah ne kawai ya kai Adnan gida yana zuwa wani zazzaɓi ya rufe shi jikinsa sai rawa yake, barci ya gagari idanunshi rashin Afra tamkar rasa ransa ne. Da gari ya hawaye ya kira Abbi ya faɗa masa komai tunda ya san Abba ba zai ɗauki abin serious ba. Ya kira Uncle Khabir tare da Uncle Mustapha ya faɗa musu komai.
Abu kamar wasa har Abbi ya yi dirar mikiya a ƙauyen shi da Salmanun-faris Adnan bai iya cin komai ba, ya fito cikin ƙyakkyawar shiga ta amy colour ɗin shadda wacce ta yi masa kyau. Lokacin suna ƙofar gidan Hakimi Salman na cikin mota yana vedio call da Mami little nayin dry.
Ganin Adnan ya sa Abbi ya yi Sallama dasu Hakimi idanunshi akan Adnan ya ce "What happing to you son? You looks so Lean and weak" murmushi kawai Adnan ya yi ya ce "Am okay Abbi ya mutan gidan?"
"Lafiyarsu lou har little,tare muke da Salman ya dawo garin" shiru Adnan ya yi rabonsa da Salman har ya manta tun a ɗakin da Abra ta rasu, daman haɗuwar ƙarshe da sukai ba mai daɗi sukai ba, yasan zuciyar Salman ɗin cike da jin zafin shi.
"Muje mota mu ƙarasa ko?" "Abbi a ƙasa za a shiga" Abbi ya ce "Ohh to bari na kira Salman" Salam na cikin mota Abbi ya bubbuga yana kiran sunansa. "Yes Abbi" buɗe motar da zai yi idanunshi ya sauka akan Adnan wanda yake tsaye ya zura hannunsa a cikin Aljihu.
Fitowa ya yi shaddar jikinsa na ƙara wacce take iri ɗaya data Abbi, shi bai san me ya kawo su ƙauyen ba, bai taɓa tunanin zai haɗu da wannan mugun mutumin ba da bai zo ba.
Babu wanda yaiwa ɗan uwansa magana Abbi na lura dasu bai ce komai ba, duk da har yanzu babu wani babban dalilin daya sanya suke hakan a garesa zai ma iya ɗauka ko rashin sabo da juna ne. A haka Adnan da Abbi na gaba Salman na baya shima hannunsa a Aljihu yana ƙarewa ƙauyen kallo har suka isa ƙofar gidan su Afra daman kawon nata yana nan. Iso akai musu suka zauna saman tabarma Salman bai shigo ba ya tsaya ɗaukan wayar Ammi dake tsokanar shi.
"Yaronku ya zo mana da zance wanda a garemu zance mai muhimmanci ne, duba da halin da yarinya ke ciki muna saka ran ta dalilinsa zamu samu iyayenta, shi ya sa na nemi ganin wani nasa mu tattauna akai da kuma ƙara jin ta bakin yarinyar a karo na biyu" Abbi ya jinjina kai gaba ɗaya hankalinsa ya yafi zuwa inda zai ga mai kama da Abransa ya fito a hankali ya ce "Masha daga namu ɓangaren muma haka abin yake, zamu samu yarinya ta maye gurbin ƴar uwarta Sannan mu samu bayanin da zai taimaka mana wajan gano asalin abin da yake faruwa, ina kuka tsinceta?"
"To a yadda murgayi ya faɗa wata rana yaje wajan gari gefen jeji domin duba wasu magunguna na itace, acikin wannan lokacin ne kuma ya tsinci Yarinya a ƙasa ita kaɗai, sai a sannan ya fahimci kamar ƴan daba ne suka shigo cikin jejin domin sama sama yake yajin ƙarar bindigogi, ya ɗauki yarinya kawota wajan ƴan sanda suka ce sun bashi domin babu wasu iyayenta da za a samu, suka saka mata suna Afra wannan shi ne abin da muka sani"
"Ikon Allah, Ubangiji mai yadda ya su" Nan Abbi ya faɗa musu yasa ya tsinci Abra da komai har kawo rasuwarta "Yanzu ina ita yarinyar take, ai Wannan abin bana wasa bane muna buƙatar ta cikin familynmu" Inna ta shiga kiran sunan ƴar Baba fitowa tayi a ɗaki cikin ƙyakƙyawan shiga mai kyau, Abbi ya tsora mata idanu dauriya kawai ya yi da bai je ya riƙeta ba, yana ƙara jinjina girman zatin Ubangiji da ƙuddirarsa. Zama tayi tana gai da Abbi suna haɗa idanu da Adnan ta tura masa baki, ya yi mata kallon ki tausaya mini. Kawo ya gyara zama ya ce "Ƴar Baba zan ƙara tambayarki a karo na biyu kina son Adnan zaki aure shi ya sadaki da iyayenka na gaskiya?" Afra na ƙoƙarin magana Sallamar Salman ta daki kunnenta juya sukai banda adnan da zuciyarsa take cike da fargaba.
Mutuwar tsaye Salman ya yi lokacin da idanunshi ya sauka akan Afra bakinsa na rawa ya ce "Yaya...!!!"[11/16, 6:44 PM] Abk: A gigice Salman ya ƙarasa wurin da 'yar Baba ke zaune, ya rirriƙeta yana girgiza kai "Abbi ban gaya maka ba? Dama na san Angel ba ta mutu ba" ƙura masa idanu Afra ta yi, tana bin fararen idanuwansa da kallo, Masha Allah ga wani daddaɗan ƙamshi da yake fitarwa.
"Talk to me Angel, dan Allah ki yi magana Yaya".
A ɗan shagwaɓe Afra ta ce "Kai ka cikani" wani malolon takaici ne ya ƙule zuciyar Adnan, ya yunƙura yana ƙoƙarin ɓanɓare Salman daga jikin Afra.
Hankaɗe shi Salman ya yi, yana sake rirriƙe Afra.
Abbi ne ya ɓanɓaro Salman daga jikin Afra, yana faɗin "haba Faris, your sister is no more, wannan ba ita bace 'yar uwatta ce"
Dafe kai Salman ya yi, ya rintse idanunsa yana sauke ajiyar zuciya, ya kwanta a jikin Abbi yana ta maida numfashi. Tsura masa idanu Afra ta yi, gaba ɗaya tausayin Salman ya kamata, lallai suna matuƙar so da ƙaunar wannan yayar ta ta.
"Inna wannan ne baban nawa?" Tayi maganar tana kallon Abbi.
Abbi ya yi murmushin ƙarfin hali yana ƙarewa Afra kallo, idan ba wanda ya yiwa Abra kyakykyawan sani ba, babu yadda za ayi kace ba Abra ba ce ba.
"Ni ne na tsinci 'yar uwakki, na riƙeta na raineta, har zuwa lokacin da Allah ya karɓeta. Kamar ki ɗaya sak da ita, tabbas da a wani wurin na ganki zan iya cewa Abra ce"
Idanun Afra ya cika da hawaye ta ce "To ina babana, suwaye iyayenmu? Me yasa suka yar da mu? Ko mu ba 'yan halak bane?"
Abbi ya ce "Kul kika ƙara faɗar wannan maganar, ku 'yan halak ne nine nan uba a gare ku baki ɗaya".
Sosai Afra ta sake fashewa da kuka tana girgiza kai.
Abbi ya ce "Ka bita a hankali, haka Abra ma take da yawan kuka" A hankali Salman ya gyara zamansa ya jingina da jikin Abbi, yana cigaba da bin Afra da kallo. Ita kuwa yadda Salman ya kashingiɗa jikin Abbi ne abin ya burgeta, da alama shima shagwaɓaɓɓe ne.
Kawun su Afra ya ce "To yanzu ya muke ciki da batun neman Auren yarinyar nan da kuka zo?". Nan da nan Afra ta sake tsuke fuska tana harar Adnan.
Abbi ya ce "Wani hanzari ba gudu ba, me zai hana a jinkirta batun neman Auren nan, yarinyar nan ta samu nutsuwa a karo na biyu sai a sake tambayar ta. Sannan dan Allah ina roƙon wata alfarma, ina son ku bani Afra in tafi da ita gidana, tun da ina kan neman iyayensu, kuma ko ba komai Yarinyar da Abra ta rasu ta bari, zata samu shaƙuwa da kusanci da 'yar uwar mahaifiyarta".
Aikuwa Inna ta ce "Ai wannan abu ba mai yiwuwa bane, a gaskiya ba zan iya bada Afra ba, shekara da shekaru ina rainon a bata rana tsaka a rabani da ita ba, gaskiya ba zan iya ba" ta ƙarasa maganar a hasale.
Adnan dai ya rasa bakin Magana, sai bin su da ido kawai da yake yi, yayin da 'yar Baba ke ta zubar da hawaye, wanda ita kanta ba ta san dalilin hakan ba.
Salman ba kunya ya tashi, ya ƙarasa gaban Afra ya zauna, ya tsura mata idanu wanda sai da hakan ya takurata, ta ji jikinta na tsuma, saboda kwarjinin da ya yi mata.
"Yaya" ya furta a sannu. A hankali ta ɗago fararen idanunta ta kalleshi, duk da bata san dalilin kiranta da hakan ba.
"A duk lokacin da nake tare da Abra, babban abin da yake jefani a cikin damuwa da tashin hankali, shi ne zubar hawayenta, kamar yadda ta rayu da son ganin Farinciki da murmushi a fuskata, dan Allah ki daina zub da hawaye, ina ganinki ne kamar Abranmu, ni haryanzu ban yadda ba ke ce Abra ba, dan Allah ki bimu gidanmu ki maye mana gurbin Abra, duk da mahaifiyata na kula da Little, amma little na kewar mahaifiyarta. Ko zaki so ta rayu ba tare da sanin kowa nata ba, kamar yadda kuka rayu a mabanbantan duniyoyi ke da 'yar uwakki, dan Allah ki Angel ki taimakawa rayuwarmu, we still needs you in our lives, Ni, Little, Mami Abbi da sauran su"
Inna kuwa kuka ta fara yi, tana share hawaye, tana faɗin "Wallahi ba mai rabani da 'ya ta, ba in da zata je"
Kawun Su Musa ya ce "Hajara, wannan kukan da kike kina ba za su tafi da ita ba ba shine masalaha ba, dan Yarinyar nan ba zata cigaba da zama ba tare da an san suwaye iyayenta ba, wataƙila tafiyar ta su da ita ya zamana silar sanin in da iyayenta suke ba"
Nan aka shiga jayayya, ɓangaren su Abbi suna roƙon a basu Afra, Inna kuma ta dage ta ce ba zata bayar ba, Adnan ka sa jurewa ya yi, ya tashi ya bar gidan ya zauna a waje.
Sai da Inna ta ga an fi ƙarfinta, sannan ta amince ta ce sai an je wurin mai gari ayi abu a hukumance, kar a gudar mata da 'ya.
Haka kuwa aka yi, aka je gaban maigari, aka kuma sake yin bayani, maigari ya sake jadadda musu bayanin yadda aka tsinci 'yar Baba da irin riƙon da marigayi ya yi mata.
Nan Abbi shima ya kuma yi masa bayanin yadda ya tsinci Abra a daji wurin yaƙi, tare da nuna musu hotunan Abra, tare da yi musu bayanin buƙatar sa na a bashi Afra.
Da haka sai da aka dangana da wurin 'yan sanda, na wannan ƙauye, in da file ɗin Afra tsintar Afra yake, aka sake kaɗe File, Abbi yayi amfani da ƙarfin kaki a wurin, aka yi rubutu tare da amincewa zai tafi da Afra.
Sai bayan la'asar su Abbi suka koma gidan su Afra, nan Baffa suka tabattar mata da cewa, an bawa Abbi izinin tafiya da Afra. Ita kanta Afra gaba ɗaya ta kiɗime, da jin wannan batun, tana da burin ganin iyayenta a rayuwarta. Salman kuwa ji yake tamkar Abran sa ce ta dawo rayuwarsa, babban jin daɗin sa shi ne tafiya da za su yi da Afra gida.
Inna ta rungume Afra tana ta kuka, saboda sabo, shi kansa Yaya Musa sai da ya yi kuka, saboda 'yar Baba akwai shiga rai, tsawon shekarun da ta yi a tare da su, ba su taɓa rabuwa tsawon lokaci ba, sai dai yanzu rana tsaka an musu fin ƙarfi an raba su da ita. Haka Inna ta haɗawa Afra kayanta, tana kuka Afra na kuka su Abbi suka taho da ita.
Yau Little rikici take ji, saboda zazzaɓi da yake ɗan damunta, Mami sai fama take da ita amma sai koke koke take yi, da ƙyar ta samu ta yi bacci, ta kwantar da ita a falo, ta shiga kitchen a gurguje tana gabatar da ayyukanta, dan tun da Abra ta yi Aure, ba ta yadda a kawo mata mai aiki ba, saboda ba ta son ƙazanta.
Tana girki tana Mamakin yadda aka yi Su Abbi suka daɗe haka ba su dawo ba, wayarta ta ɗauka ta kira Abbi, amma bai ɗaga ba, ta kira Salman, shima sai da ta yi masa kira biyu sannan ta samu ya ɗaga.
"Hello Mami, Ina daughter na?"
"Kai na kiraka in ji ya akai na ji ku shiru, amma kana mini zacen daughter".
Faris ya ce "Mami muna nan tafe da wani abin mamaki mai girgiza zukata".
Saroro Mami tayi ta ce "Faris bana son shirme, wane irin abu ne haka?"
Jiki a sanyaye Faris ya ce "Mami ki kwantar da hankalinki, muna Lafiya mun kusa shigowa cikin Kano insha Allah".
"To shikenan, Allah ya kawo ku lafiya" ta ajiye wayar tare da komawa wurin da ta ajiye Little amma ba ta nan. Da sauri ta ƙarasa tana ɗaga filon kujera, amma ba ts ga Little ba.
"Ki daina wahalar da kan ki, ni na ɗauketa kin ajiye yarinya a kan kujera, idan ta tashi ta faɗo baki da asara, ko da yake ba abin mamaki bane, ita ma zaki mata irin riƙon da ki ka yiwa babarta ko?" Cewar Salima da ke wa Mami Magana cike da gadara.
Wani marurun takaici ne ya tokarewa Mami wuya, amma cike da salo na goggaun matan da suka kwana biyu a duniya, ta yi murmushi ba ta tankawa Salima ba, dan ba ta fi sa'ar Abranta ba, ta nemi wuri ta zauna a kan kujera, ta fara cin Abincin ta.
Salima ta so Mami ta tanka mata, ta yaga mata rashin mutunci son ranta, amma sai ta ga saɓanin abin da ta yi tunani.
Mami ta cigaba da kallo, tana sipping tea, suka jiyo Little tana ta tsala kuka, daga sashin Salima, da sauri Salima ta tafi ta ɗauki Little, sai dai juyin duniya, amma little ta ƙi yin shiru, sai cilla ƙafafuwa take tana rintse idanuwa, ba shiri ta fito da ita a kafaɗarta, tana miƙawa Mami ita.
Maimakon Mami ta karɓeta sai ta miƙe, ta bar falon.
Salima ta rasa yadda za ta yi da Little, gashi ita ba ta saba da kukan yaro ba.
Tun a hanya suka rabu, Adnan ya nufi Kaduna, dan zuciyarsa ba zata iya jure cigaba da kallon Afra tana furta ba ta son sa ba, yana ji yana gani, Abbi Salman, da Afra suka nufi Kano, sai dai Adnan tun kan ya ƙarasa Kaduna, wani irin zazzafan zazzaɓi ya rufe shi, gaba ɗaya al'amura sun cakuɗe masa, bai san ya zai yi ba idan har ya rasa Auren Afra a wannan karon, bai san abin yi ba. 'Allah sarki Abra, a kallon Farko da na yi mata, na ga tsoro a fuskarta, bayan nasarar kauda tsoron fuskarta da na yi, na maye gurbinsa da tsananin soyayyata a zuciyarta, sai dai kash na yi wautar da na sanya ƙiyayyata a zuciyar Abra, har kan ta rasu take sanar mini da bata ƙaunata, Allah ya jiƙanki matata ya yafe mini, Allah ya sa 'yar uwakki ta yadda ta Aureni' yayi Maganar yana zubar da hawaye.
Afra tsayawa ta yi tana ƙarewa harabar gidan kallo, da ganin yadda sojoji ke kaiwa suna komowa a harabar gidan, ta jinjina Arziƙi da Allah ya yiwa mariƙin Abra, sai dai jikinta duk a sanyaye yake, dan tun yanzu kewar ƙauyensu ta fara damunta, sai dai ba ta da burin da ya wuce ace ta sadu da iyayenta, komai talaucinsu komai muninsu.
Kukan little ne ya karaɗe gidan, Abbi ya shigo falo da sallama, ya tarar da Salima tana tsaye tana ta jijjiga little da ke tsala uban ihu. Ya ƙarasa ya karɓeta a hannunta, yana faɗin "Garin yaya aka barta take kuka haka?".
Salima ta ce "Oho, ajiyeta ta yi a falo tai tafiyarta ta barta"
Abbi ya karɓeta, ya nufi sashin Mami a fusace "Na'ima wane irin sakarci ne haka, zaki tafi ki bar Yarinya tana kuka a falo, kin san ƙyuya take kin barta da Salima sai kuka take mata, yanzu da tsautsayi ya sanya mun taho da mahaifin yarinyar nan, haka zai zo ya tarar da ita tana kuka".
"Kar ka sake yi mini tsawa Khamal, baka san maiya faru ba kawai ka zo ka sani a gaba da faɗa, kar ka kuma yi mini tsawa, bani yarinyata, kuma Wallahi matarka ta kuma ɗaukar mini ita saina wanka mata mari" ta ƙarasa maganar tare da fizge little daga hannunsa.
Shiru Mami ta yi, ta tuna watarana da ta taɓ haɗa baki da ƙawarta suka yiwa Abra sharri, har Major ya mareta, ashe haka Abra take ji idan ta yi mata ƙazafi. Wasu hawaye masu fitowa da ɗacin zuciya suka faa sakowa saman kuncinta.
Abbi ya yi ajiyar zuciya ya ce "Ki zo muje falo, ki ga wani abu".
"Ba abin da zan gani, kaje ka ƙyaleni kawai"
Major ya ce "Abin yana da mahimmanci, ki zo muje".
"Kaje ka nunawa matarka bani ba, ita ya dace taga abu mai mahimmanci daga gareka bani ba".
"Ko da kuwa abin da ya shafi Salman ne ko Abra?"yai Maganar yana kallonta. Sai kuma jikinta ya yi sanyi, Abbi ya sanya hannu ya janyo hannun Mami zuwa falo.
Afra kuwa tun da ta shigo, tangamemen hoton Abra ne da Salman ya yi mata maraba, babu yadda za'ai ka kalli hoton kace ba ita bace a jiki.
Jikinta ne ya hau rawa tana nuna wa Salman hoton. Salman ya taka ya ciro hoton ya miƙawa Afra ya ce "This is your sister, we are really missing her" yayi maganar ba tare da ya iya tsayar da hawayen da suka taho masa ba.
Salima kuwa bin su ta dinga yi da ido, tana son tayi magana, amma ta kasa magana, saboda yadda Salman ke mata kwarjini, sam yaron baya sakar mata fuska a matsayinta na matar mahaifinsa.
"Yanzu ta mutu? Yayata ce ko ƙanwata ce, ko mu biyu ne? Babu wanda ya sani sai Allah, me yasa ban haɗu da ke kan ki mutu ba? 'yar uwata me yasa kika tafi ban ganki ba, a rayuwata ace ko sau ɗaya naga jinina, yanzu idan ba a gano iyayenmu ba fa, shikenan kin mutu kin barni ni ka ɗai haba 'yar uwata" tamkar mahaukaciya, haka Afra take gunjin kuka, Salman ya karɓe hoton yana share mata hawaye, ganinta yake ba ta da banbanci da Afransa.
Mami ce ta fito tana hura hanci, hannunta ɗaya riƙe da Little, ɗaya kuma yana cikin na Abbi. Wata irin mummunar faɗuwar gaba ce ta ziyarci Mami, jikinta ya hau rawa bakinta ma haka.
Nema take ta saki Little, Abbi yai sarin karɓeta daga hannunta.
"Major me nake gani? Abra ce fa? Abra ce ko baka ganinta ne?".
"Calm down please, ba Abra bace ba kalleta da kyau".
Cikin tsawa ta ce "Ta yaya zaka cemini ba Abra bace, kalleta fa a kusa da Faris, Abra ba ta mutu ba kenan, ko kuma fatalwa ce" Salman ya taso da sauri ya karɓi Little, Mami kuwa gaba ɗaya ta birkice, Abbi ya zaunar da ita, amma ta kasa nutsuwa, sai nuna masa Afra take tana cewa Abra take gani.
Abbi ya yiwa Afra nuni da ta zo, Afra ta taso ta ƙaraso gaban Mami, aikuwa ta rirriƙeta ta ce "Abrana, Wallahi Major Abra ce kalleta fa".
Abbi ya kalli Afra ya ce "Afra, ga maman 'yar uwakki, ita ce ta riƙe Abra, wannan jaririyar kuma, ita ce wadda ta rasu ta bari, ki gaya mata ke ba Abra ba ce".
Afra ta riƙo hannun Mami cikin nata, tana hawaye ta ce "Mamanmu, ba 'yar ki ba ce wadda ki ka rasa, amma zan iya cewa 'yar ki ce ta dawo gareki, kamar 'yar uwata nima tsinta ta aka yi, aka riƙeni a wani ƙauye har na girma, mijin 'yar uwata ne yaje ƙauyenmu ya ganni, shima da fari cewa ya yi, ni matarsa ce amma daga baya ya gano, ba ita bace, ni sunana Afra ana ce mini 'yar Baba a garinmu, ni a ƙauye na tashi, Abranki kuma a birni, mijin Abra ya ce ta fini hankali da nutsuwa, da rashin hayaniya, ni kuma... Sai kuma tai shiru tana murmushi, a lokacin da hawaye ke zuba daga idonta.
"Major yanzu kana nufin ba Abra na ba ce?".
"Ba Abranki ba ce, 'yar uwatta ce" Nan Abbi ya yiwa Mami bayanin komai.
Mami ta rungume Afra a jikinta tana wani irin kuka, tamkar zata shiɗe, Afra ma ta rungumeta tana kuka.
Salima ta ce "Sweetheart, nifa ban gane meke faruwa ba, wannan ba ita ce 'yarka ta hoton nan da aka ce ta mutu ba?"
Abbi ya ce "Ba ita bace, zan miki bayani".
Adnan kam ko da ya isa garin Kaduna, a Asibiti ya samu masauki, saboda yadda zazzaɓi da ciwon kai suka rufe shi, sai da aka sa masa ruwa sannan ya wuce gida.
Ko da Adnan ya jewa Hajiya Mama da Abba abin da ya faru Abba ya ce "Lallai wannan lamari akwai ban mamaki a cikin sa, dan haka zuwa jibi insha Allah, zan shirya in je Kano da kai na".
Adnan ya ce "Dan Allah Abba idan ka je kace su bani Auren Afra, zan iya rasa raina idan ba sameta ba".
"In ka rasa ranka Allah ya jiƙanka, ai Nagode Allah da ya sanya yarinyar ta ce bata sonka, ni dai Adnan ba zan kuma yin jagoranci a nema maka Aure ba, da mahaifiyarka ma ta mutu dangana na yi, kaima in ka mutu Allah ya jiƙanka".
"Abba dan Allah, kai mini rai, na tuba nabi Allah na bika, ba zan sake maimaita kuskuren da nayi a baya ba"
"Sai kuma kayi Adnan, idan har ina raye babu mai aura maka 'yar uwar Abra, kaje can ka nemi wata 'yar ka aura, amma ba 'yar uwar Abra ba".
Mama ta ce "Dan Allah Yallaɓai ka sassautawa yaron nan, kalli yadda ya koma" Abba ya ɗaga mata hannu ya ce "Wannan yaron ba abin tausayi bane, kuma na gama Magana, kuma idan har ka takura sai sun baka yarinyar nan, zan tona maka Asirin irin riƙon da ka yiwa 'yar su" haka Adnan ya dinga kuka wiwi, kamar wanda uwarsa ta mutu.
"Ok Zuwa next week nake son Visa don Allah, abu ne na gaggawa ya taso mini, da yake buƙatar in je da kaina"
Hajiya Saudat ta zubawa doctor ido, tana saurarensa, sai da ya gama wayar sannan ta kalleshi ta ce "Wai ni don Allah doctor, sai yaushe zaka bawa iyayen yaron nan damar zuwa su ganka ne?"
"Sai na dawo daga tafiya"
"Ni ban ma tambayeka ba, ina zaka je naji kana maganar visa?".
Doctor ya gyara zamansa ya ce "Dubai zanje" hantar cikinta ce ta kaɗa, ta dube shi a firgice ta ce "Kaje Dubai kayi me?"
"Wurin wanda na ajiye zani, ai kin fi kowa sanin ina da ajiya a can".
"Me kake nufi? Me kake nema a can da babu a nan?".
Bulama ya ce "Abu mafi mahimmanci da kika sa na wofantar, dole in gano alaƙata da yarinyar da nake bincike a kai, dan haka dole in tafi Dubai"
Gaba daya ta rikice ta ce "Amma ka san zuwanka Dubai na nufin tonuwar Asirinka wataƙila ma da karayar arzikinka?"
"Ban damu ba, ida har abin da na rasa ne zai dawo gareni"
Wayar Hajiya Saudat ce ta fara ringing, jiki na rawa ganin lambar Meenal ce ta ɗaga.
"Muna magana da mahaifiyar Meenal ne?".
"Eh nice"
"Ku zo nan Asibitin Health well, yarinyarki babu lafiya, ana buƙatar sa hannunku ku zo ku biya kuɗ ayi mata aikin gaggawa"
₦300 kacal, a biya kan a karanta dan Allah 08081012143
[11/17, 2:50 PM] Abk: A kiɗime Hajiya Saudat ta ce. "Wacce Meenal ɗin? Ban gane ba bawan Allah, me ya samu ƴata?"
"Idan kika zo za ki fahimta, amma fa ana buƙatar ku yi gaggawar zuwan, saboda gudun kar a rasa rayuwar ta."
Suɓucewa wayar ta yi daga hannunta ta faɗi ƙasa, cikin gigita ta ce. "Doctor wai Daughter ce babu lafiya, tana health well ana buƙatar mu je mu saka hannu za a yi mata aiki." Babu yabo ba fallasa ya ce. "Allah ya ba ta lafiya."
"Haba Doctor, ya na ga kamar ba ka damu ba, ƴarmu fa Meenal nake magana a kai."
"Damuwar da nake ciki ta fi ƙarfin wannan, ki ɗauki ATM ɗina ki je a yi duk abin da ya dace."
Bai jira amsar ta ba ya fice daga ɗakin, zuciyarsa cike da tunanin wanne abu ne yake damun Meenal da har ya kai sai an yi mata aiki ba tare da sun sani ba? Da kallo Hajiya Saudat ta bi shi cikin bugawar zuciya, mamaki da fargaba sun cika mata fal a cikin ranta, yau Bulama ne take masa maganar Meenal tana cikin mawuyacin hali na ciwo amma ya kaɗa ƙafarsa ya yi gaba? Shi da ko ciwon kai take kusan tare suke jinyar saboda yadda yake nuna damuwarsa tare da ba ta kulawa. Lallai dole ta miƙe ta nemi mafita gami da kawar da abin da ya ɗauke masa hankali daga gare su.
Cikin matuƙar tashin hankali ta zari gyalenta da handbag da wayarta dake yashe a ƙasa ta yi waje zuwa asibitin da aka ce mata Meenal tana can.
Ɗakin Abra Abbi ya sa Salima ta gyara wa Afrah, bayan ta gama ta dawo parlour inda duk suke ta ce. "Our new daughter na kammala miki gyaran dakin, sai ki shiga ki kwanta ki huta." Murmushi Afra dake riƙe da Little ta yi, ba tare da ta ɗago kanta ba ta ce. "Na gode sosai Aunty." Cikin son cusa kai Salima ta ce. "Haba mene abun godiya don Uwa ta yi wa ƴarta abu?" Murmushi kawai Afra ta yi ba ta ce komai ba, sai shafa fuskar little take cikin ƙaunar ta da ta mamaye zuciyarta lokaci ɗaya, farinciki mara iyaka take ji a cikin ranta, yau ta ga jininta a duniya, Allah Sarki Baba, dama yana nan ya ga wannan ranar mai cike da tarin farinciki a gare su. Mami kuwa taɓe baki ta yi jin abin da Salima ta faɗa, Abbi kuwa murmurshi ya yi cikin jin daɗi ya ce. "Daughter, tashi ki je Antinki ta nuna miki ɗakinki." Cikin girmamawa ta ce. "Toh." Salman dake ta kallon ta ya miƙe tare da ɗauke little daga cinyarta, cikin murmurshi ya ce mu je na raka ki yayata." Da sauri ta kalle shi cikin mamakin jin ƙato da shi ya ce mata Yaya, shi ma kallon ta yake, hakan ya sa idanuwansu suka sarƙe cikin na juna, da sauri ta janye nata saboda wani irin abu da ta ji ya daki zuciyarta, bayan ya kai ta ɗakin yana ƙoƙarin fita ta ce. "Ka bar mini ita a nan." Fahimtar da ya yi little take nufi ya sa ya ce. "Kina buƙatar ki yi wanka a yanzu, ita kuma rigima ne da ita, kina ajiye ta za ta iya farkawa tay ta kuka, idan kin yin wankan sai Mami ta kawo miki ita." Gyaɗa masa kai ta yi ba tare da ta bari sun haɗa ido ba har ya fice, haka kawai ta ji suna mata kwarjini shi da Abbi, shi ya sa ta nutsu kamar ba ita ce Ƴar Baba gagarau ba. Bin ɗakin ta shiga yi da kallo, ƙawatuwar shi da yadda ya tsaru ba ƙaramin burge ta ya yi ba, sai tambayar kanta take yi wai wannan haɗaɗɗen ɗakin duk nata ne? Yau ita ce za ta kwana a birni gidan ƴan gayu mai kyau irin wannan, ba don halin kewar su Inna da take ba da sai ta raba dare tana tsallen murna a kan wannan luntsumemen gadon.
"Allah Sarki Innata, na san yanzu suna can suna kuka da alhinin tafiyata ita da Yaya Musana." Ta faɗi haka a fili ƙwalla na cika mata ido. A hankali ta zauna a bakin gado tana ƙara bin ɗakin da kallo, Adnan ne ya faɗo mata a rai, turo baki ta yi kamar yana gabanta, lokacin da ta tuno yadda yake yi mata magiya akan ta so shi.
Salima ce ta shigo ɗakin bakinta ɗauke da sallama, bayan ta amsa mata ta ajiye wata leda mai ɗauke da kayan bacci a kusa da Afra tare da faɗin. "Ga kayan bacci nan idan kika yi wankan sai ki saka." A hankali Afra ta ce. "Toh na gode, amma na taho da kayana ma suna cikin Mota ba a shigo da su ba ne."
"Okay, bara zan yiwa Honey magana sai a shigo miki da su yanzu, ki saki jikinki kin ji, nan ma gidanku ne, bari na kawo miki abinci.'
Gyaɗa mata kai ta yi ta ce. "Ina zan ɗebo ruwan da zan yi wanka da alwala?" Murmushi Salima ta yi ta ce. "Duk akwai a cikin toilet, mu je na raka ki, ki gani." Miƙewa ta yi ba tare da ta ce komai ba, duk wannan kanbanbar da Salima take ba ta wani yi mata ba, sai ta ji ta fi son farar matar nan mai kama da Salman. A toilet ɗin ma lalacewa ta yi wajen kallon yadda aka ƙawata shi, kasa ɗaurewa ta yi ta ce. "Yanzu nan ne bayin gida kamar wani ɗaki? Taɓ, ai da ni kaɗai na shigo fita zan yi na ce ban ga bayan gidan ba, na saba da namu na ƙauye ko rufi babu balle siminti." Murmushi Salima ta yi ta nunnuna mata duk abin da ta san zai mata wahalar ganewa da yadda za ta yi amfani da shi. Bayan ta fita ta ce. "Wai aljannar duniya, har da wani fanfon ruwan zafi? To shi daga ina yake zuwa kuma? Ko ta cikin ƙasa ake dafa shi?"
"Khamal wai me kake nufi da ni a gidan nan ne? Ina cikin damuwar rashin Abra amma mai kama da ita ta zo sai kaita tura waccan matar tana yi mata abubuwa? Alhalin gani a zaune."
"Na sani ko ita ma za ki ce ƴata ce karuwa ta haifa mini? Ki azabtar da ita kamar yadda kika yi wa Abra."
Cikin hawaye Mami ta ce. "Me ya sa kake son dawo da abin da ya wuce ne? Ai babu wanda ba ya yin kuskure a rayuwarsa." Wani kallo ya watsa mata ya fice ba tare da ya kuma magana ba. A zuciye Mami ta ce. "Kuma yarinya a gurina za ta zauna ba a gurin wata baƙar yarinya ba, sai dai a yi duk abin da za a yi. Ban da neman fitina yarinyar kusan sa'ar ta amma ita za ta riƙe ta, ita ma shegiyar da neman gindin zama har da wani ce mata ƴarta, ko a gidan uwar wa ta haifi kamar ta oho?" Ta ƙarashe maganar tare da jan tsaki.
"Doctor me yake damun ƴata da har ya kai a yi mata surgery without knowing us?" Hajiya Saudat ta tambaya a gigice.
"Mu ƙarasa office mana sai mu yi maganar."
"Ba ni da nutsuwar ƙara taku ko nan da can? Please tell me what happened to my daughter?" Ta yi maganar cikin kuka.
Cikin tausawa likitan ya ce. "Ki dai daure mu ƙarasa office ɗin, kin ga nan reception ne, bai dace mu yi magana ba."
Ba ta kuma magana ba ta bi shi suka tafi. Bayan sun shiga sun zauna ya ce mata. "An yi mata abortion ne, sai kuma aka samu matsala ta samu raptured utherus, mahaifarta ta ragargaje gabaɗaya, yanzu za a yi mata aikin gaggawa a cire t....."
"Innalillahiwa'inna'ilaihirrajj'un, na shiga uku! Meenal ɗin za a cirewa mahaifa? Mahaifa fa ka ce Doctor?"
"Eh, ta sha maganin abortion ne wanda ya wuce ƙa'ida, hakan ne ya janyo mata wannan matsalar, ba don da wata Nurse da take aiki a nan asibitin suka zo ba ma da ba za mu karɓe ta ba."
Gumi ne ya shiga yankowa Hajiya Saudat ta ko'ina a jikinta, cikin rawar murya ta ce. "Doctor, kuma babu wani abu da za a iya yi dole sai dai a cire mahaifar?"
"Babu." Ya faɗa a taƙaice.
A dole ba bisa son rai ba Hajiya Saudat ta saka hannu aka yi wa Meenal aiki, wadda ke cikin mawuyacin halin ciwo.
Ba ƙaramin tashi hankalin Hajiya Saudat ya yi ba da ta ga Meenal, Saboda yadda ta ɗashe ta yi fari fat alamun babu jini a jikinta, ga wata rama da ta yi kamar wadda ta daɗe tana jinya, tsabar galabaita ko magana ba ta iya yi, sai hawaye kawai take.
Washegari bayan Salima ta gama haɗa breakfast ta shiga ɗakin Afra don ta taso ta. Tarar da ita ta yi har lokacin tana kwance tana bacci, saboda jiya ba ta yi bacci da wuri ba, kewar Inna da baƙunta sun hana ta. A hankali ta tashe ta, bayan ta shiga toilet ta fice ta ɗauko mata sabuwar abaya da undies a cikin kayan lefenta, ta haɗo da su lotion da powder ta kawo mata. Cikin mintuna ƙalilan Afra ta shirya, kasancewar ta mai kazar-kazar ba kamar Abra ba. Sosai ta yi kyau cikin bak'ar abayar da ta haska farar fatarta. Kallon kanta ta tsaya yi a mirror cikin murmurshi, gani take ba kamar ba ita ba saboda kyawun da ta ga ta yi. Sai da Salima ta ƙara dawowa ta kira ta sannan suka fita tare.
Abbi na zaune a dinning suka shiga parlour'n, ɗagowa ya yi yana kallon su tare da amsa sallamar, cikin girmamawa Afra ta tsugunna ta ce. "Ina kwana?"
"Lafiya ƙalau, ya kwanan baƙunta?" Ya amsa cikin fara'a.
"Alhamdulillah." Ta faɗa cikin sanyin muryar da ta ara daga jiya, don sosai ta ji jikinta ya yi mata wani irin sanyi ba tare da ta san dalili ba.
"Ƙaraso mu karya." Cewar Salima tana nufar dinning area.
"Bari na fara gaishe da Mami idan ta tashi."
Cikin jin haushin abin da ta faɗa Salima ta ce. "Ai ko da ƙyar in ta tashi."
"Ta tashi, mu je na raka ki." Abbi ya faɗa cikin jin daɗin yadda ta nuna girmamawa ga Mami.
Da kallo Salima ta bi su zuciyarta cike da baƙin ciki, ta gama yi wa yarinya hidima sannan tana fitowa ta ce wani za ta gaishe da Mami? Lallai dole ta tashi tsaye don ganin ta ja Afra jikinta sosai, ta san hakan zai ƙara ninka ƙaunar da Abbi yake mata.
Mami tana shirya little suka shigo ɗakin, da fara'a ta ɗago tana duban Afra, Abbi kuwa juyawa ya yi ya koma parlour.
"Daughter har kin tashi?"
Gyaɗa mata kai ta yi tare da gaishe ta, rungume ta Nai'ma ta yi hawaye na cika mata ido saboda tuno Abra da ta yi, don ganin Afra cikin abaya ba ƙaramin ƙara kamar su da Abra ya yi ba, kasancewar ta ma'abociyar saka ta.
"Lafiya ƙalau daughter, dafatan kin tashi lafiya?"
"Lafiya ƙalau." Ta amsa tare da ɗaukar little, kamar wadda aka faɗawa yarinyar sai ba ta yi mata ƙiwa ba, sai ma dariya da ta shiga bangala mata. Socks Mami ta ɗauko ta fara saka mata tare da faɗin. "Lallai yarinyar nan, wato ke ba kya yi wa iyayenki ƙiwa ko? Da wani ne ya ɗauke ta da tuni kin cika ɗakin nan da kuka da ciccilla ƙafafuwa." Murmushi Afra ta yi tare da shafa sumar kan little, tana jin duk duniya babu abin da take so sama da yarinyar. Tare da suka koma parlour da Mami, lokacin har Salima da Abbi sun fara karyawa. Cikin son gwaninta Salima ta miƙe ta yi serving ɗinsu, don a gaban Abbi biyayya da girmamawa take yi wa Nai'ma. Ciki-ciki Mami ta ce. "Thanks." Abbi bai ji daɗin hakan ba, amma ya danne saboda Afra dake gurin bai nuna ba, fahimtar hakan ya sa Salima sakin murmushi cikin jin daɗi, dama abin da take so kenan a kodayaushe, Abbi ya dinga ganin lefin Mami a zamantakewar su.
Tsurawa kayan breakfast ɗin ido Afra ta yi, a kallon farko da ta yi masa ta ji yawunta ya tsinke, ga ƙamshinsa da ya cika mata hanci, tun kafin ta ci ta san ba ƙaramin daɗi zai yi ba. Inna da Yaya Musa ne suka faɗo mata a rai, ji ta yi dama a ce tare da su za su kwashi wannan daɗin, ga masoyin nata bread ƙatoto a gurin. A hankali ta ɗauki cup ɗin da Salima ta haɗa mata tea ta yi Bismillah ta fara sha, daidai lokacin Salman ya shigo parlour'n. Gabansa ne ya yanke ya faɗi ganin Afra, don gani ya yi tamkar Abra ce zaune a gurin, hakan ya tuno masa lokuta da dama da suke yin breakfast exactly like this da Abra. Addu'a ya yi mata sannan ya ƙarasa dinning area ɗin cikin sanyin jiki. Bayan ya gaishe da su Abbi ya ɗauki little dake bacci sannan ya zauna. Kamar yadda Salima ta yiwa kowa haka ta tashi ta yi serving ɗin shi. Ba yabo ba fallasa ya yi mata godiya. A hankali Afra ta ɗaga kyawawan idanunta ta kalle shi tare da sakar masa murmushi, mayar da mata murmushin ya yi tare da yin ƙasa da murya ya ce mata. "Morning Angel, da fatan kin tashi lafiya?"
"Lafiya ƙalau"
Mami dake lura da su ta yi gyaran murya, hakan ya sa Salman haɗiye abin da yake son faɗa, sanin da ya yi ƙa'idar Abbi ne idan ana cin abinci ba a magana idan ba dole ba, gyaran muryar da Mami ta yi kuma ya san tuna masa hakan take. Bayan kowa ya gama cin abincin Abbi ya dubi Afra ya ce. "Yata a ina kika tsaya da karatu ne?"
"Na yi Candy."
Gyaɗa ya yi ya ce. "Da kyau, islamiyya fa?"
"Muna izifi Ashirin."
"Masha Allah, yanzu kina da takardun WAEC da NECO?"
"Eh, na taho da ita ma, Inna ta haɗo mini a cikin kayana, amma NECO kawai na yi."
"Okay." Abbi ya faɗa tare da mayar da duban shi ga Salman ya ce. "Idan Allah ya kai mu gobe Monday ka je ka yi mata registration a school ɗin English Academy, saboda ta samu bakinta ya faɗa a Turanci kafin ta shiga University, idan an fara registration na JAMB sai a yi mata, Islamiyya ma ka kai ta wadda kuka yi ta cigaba da karatun a can."
"Insha Allahu Abbi."
Cikin matuƙar farinciki Afra ta ce. "Na gode sosai Abbi, Allah ya ƙara girma da arziƙi."
"Amin Daughter, babu komai. Yanzu sai ka kai ta, ta gaishe da su Ammi, idan kun dawo sai ku je tare da Auntinku ku yi mata shopping na kayan sawa da sauran abubuwan amfani." Ya ƙarashe maganar idanunsa a kan Salman.
Godiya sosai Afra ta yi masa har da hawayenta, ta so a ce Baba yana raye ya ga wannan ranar, don ba shi da buri da ya wuce na ganin ta yi karatu mai zurfi na addini da na boko, karamcin da Abbi ya nuna mata a yanzu ya ƙara tabbatar mata da an yi wa ƴar'uwarta riƙon mutunci a gidan, hakan ya ƙara kwantar mata da hankali akan zamanta a gidan.
Daren jiya Adnan bai samu ishashshen bacci ba saboda damuwar dake cunkushe a cikin ransa gami da fargabar rasa Afra. Raba dare ya yi yana kallon hotunan Abra cikin zubar hawaye tare da surutai, ta tafi ta bar shi cikin tsananin kewa da ƙaunar ta, ya samu wacce yake ganin za ta ɗebe masa kewar ta amma ita ma yana ƙoƙarin rasa ta. Sai bayan Sallar Asuba wani wahalallen bacci ya ɗauke shi, bai farka ba sai da goma ta wuce, ko sakkowa bai yi daga kan gadon ba ya lalubi wayarsa ya kira Mami, bayan sun gaisa ya ɓukaci ta ba wa Afra saboda muryar ta kawai yake son ji ko zai samu nutsuwa a cikin zuciyarsa, lokacin su kuma sun tafi gidan Ammi, cikin rashin jin daɗi ya yiwa Mami sallama, a ransa yana ƙudirce dole gobe ya yi wa Kano dirar mikiya.
Littafin kuɗi ne, don neman ƙarin bayani: 09047871750
[11/20, 7:09 AM] Abk: Washegari kamar yadda Adnan ya sanya a ransa haka ne ya kasance. Tun asuba ya shirya cikin wata shadda shampoo maroon colour ya murza hula duk da bata dame shi sosai ba, amma ganin weather ya sanya ya yi shiga mai kyau. Sai ƙamshin Pur oud yake lokacin daya fito gari ya yi duhu sbd hadarin dake kwance a garin Kadunan.
Ba tare da sanin Hajiya Mama da Abba ba ya nufi Kano cikin duhun asuba sai gudu yake shararawa burinsa kafin 11 na safe ya yiwa Kano tsinke idanunsu ya sauka akan Afra ko ya samu sauƙin ciwon da zuciyarsa ke masa akoda yaushe. Cikin wannan tunanin ya ƙarawa motar giya.
Afra na zaune cikin wata white-collared t-shirts tare da wani red cropped trousers ta ɗora wata red ɗin kinomo a saman kayan, tayi kyau sosai domin duk a cikin kayan da Abbi ya bada akai mata shopping ne. Hannunta riƙe da Aishatul-humaira wacce a kullum ƙara wayo take. Mami data fito ta ce.
"My dear kinji daɗi Little bata miki halin nata, ko dai ta gane ke Mother ɗin ta ce?"
"Wallahi Mami ina sonta sosai, bana son rabuwa da ita kamar muna kama ko?" Kafin Mami tayi magana Salman dake gyara zaman babbar rigarsa ya ce.
"Dake da ita ban san wanda nafi so, ina tunanin burina ya kusa cika"
"What are you saying Salman?" Ya shafa sajan fuskarsa yana basarwa ya ce "No Mami,ina breakfast ɗina?" Mami ta Harare shi ta ce.
"Liar, It's like I heard you say something?" Ya girgiza yana zama kusa da Afra idanun shi akanta ya ce.
"It seems that Mami's ear is starting to have problems. Amma breakfast na ce ta, yunwa zata hallaka miki ɗan yaro Mami"
"Allah ya shiryaka Salman, yunwar ka kewa haka?" Ya marairaice fuska sosai wanda ya bawa Afra mamaki ya sanya ta buɗe baki tana kallon ƙato da shagwaɓa. Da ƙyar ya ce
"Da gaske Mami yunwa na keji sosai, Yaya Please abinci" ya faɗa tare da juyawa ya kalli Afra wacce ke riƙe da Aishatul-humaira tana mata tsalle tsalle da ƙafa a cinya.
Barin wajan Mami tayi cike da fatan samawa Salman nasara domin ta riga da taji abin da ya ce.
"Why are shy yaya my angel?" Ya faɗa yana saka hannunsa zuwa haɓarta tare da juyo da fuskarta suka fuskanci juna. Fararen idanunsa masu kaifi wanda suke ƙara sawa Afra kwarjinin Salman a idanunta ya zuba mata ya ce.
"Ba haka yaya Abra ke mini ba, na sama hira da yayata sosai wani lokacin daja hancina kamar like this" ya ƙare maganar yana jan hancinta cike da ƙaunar ta wacce lokaci guda ta mamaye dukkan zuciyar shi.
Cikin siririyar muryar ta ta ce "Uhm to aini ban girmeka ba" ya lumshe idanunsa yana mai girgiza kansa kaɗan tare da tura hular kansa zuwa gaba ya ce.
"Injiwa? Tsakanina da Abra good 3yrs ne, ke da Abra twins shekara ɗaya aka haife ku Kinga kin zama yayata"
"Kuma na ganka ƙatoto ni kuma ƙarama" zuba mata gajiyayyun idanun shi ya yi yana karantar yanayin ta sosai kafin speaking calmly ya ce.
"Sbd ni ne mijin ai" ta ware ido ta ce "me kace?" Ya girgiza yana miƙewa tsaye tare da ɗaukan Little ya ce "I'll explain later" kafin tai magana ya miƙar da ita tsaye ba zato taji ya jawota ɓarin jikinsa ya yi musu photo yana murmushi ya ce "My family my happiness, zuri'ar Salmanun-faris" ita dai bata fahimta ba, sai saurin zame jikinta da tayi zuciyarta na bugawa da ɗan ƙarfi.
Dining room suka nufa a can suka samu Salima Abbi daman tun 7 yabar gida yin binciken asalin iyayen Afra da Abra. Jikin Salima na ɗan rawa ta ce "Salman my son bari na serving naka abinci" idanun shi akan Afra ya ce. "No thanks, Afra please serve me" ya faɗa fuska a kame.
Salima bata so hakan ba domin gaba ɗaya Salman birgeta yake tana neman duk yadda da zata samu connection da shi amma ya toshe ba lallai idan yana mata kallon matar Mahaifin nasa ba.
Afra tai serving nasa a nutse take har kar nan gudun kada ta kwafsa, ta nuna ƙauyancin nata shi ya sa ta kame kanta da kyau domin siyawa kanta martaba da ƙima a idanun jama'ar gidan.
Ganin daga Afra har Salman abinci suke ci babu wanda yako kalli inda Salima take, ya sanya jiki a sanyaye ta miƙe kamar zata ɗauki Little wacce take barci a jikin Salman ta wani ƙanƙame shi da duk hannunta biyu sai kawai ta fasa da ɗan sauri tabar wajan.
Suna cin Abinci Mami ta fito cikin kwalliya sai ƙamshi take, ganin Afra da Salman ya bata sha'awa. Ta ɗauki Little tare da bar musu wajan. Lokaci zuwa lokaci Salman ke satar kallon Afra yana jin kamar ya faɗa mata abin da ke zuciyarsa kada ya ƙara rasa damar shi a wannan karon.
"I love You"
Ya furta a hankali daidai yadda za taji da sauri ya ɗago kanta ta kalle shi ganin kamar ba shi ne ya yi maganar ba, yasa ta ɗauke taci gaba da cin abincin maybe kunnuwanta ne kawai suka ji haka.
Murmushi mai laushi Salman ya yi kyansa na fita calmly ya kuma cewa.
"Ina son ki Afra, and I ready to marry you....."
"Kai da Afra har abada domin ta haramta a gare ka ni ne zan aureta" daga Afra har Salman suka ɗago kansu, ganin mutum dake tsaye ya sanya Salman yin murmushi wato tarihi zai maimaita kansa kenan. Jikin Afra na rawa ta miƙe tsaye domin bata tsammani ganinsa ba a daidai wannan lokacin. Ƙoƙarin guduwa take ya sanya hannu tare da cafkota idanun shi sun kaɗa tare da yin jaa sosai kamar gauta cikin rawar murya ya ce.
"Ni nake son ki ƴar baba tun kina ƙauye, ni ne na yi sanadiyar zuwanki nan gida, kuma a shirye nake da aurenki idan kin amince Wallahi ina son ki Please don't say No!"
"Wallahi bana son ka, ba zan taɓa son ka ba, koda zaka mutu, ni ka rabu dani ka takura mini" Innalillahi Adnan gani yake da wannan maganar gwara ta ɗauki wuƙa ta caka masa zai fi masa sauƙin fahimta. Cikin damuwa ya ƙara matsawa gareta tare da ɗora hannunta a saitin ƙirjinsa idanunsa na sauya kala yana cika da hawaye ya ce.
"Ki taimaka, ki taimaki rayuwata Afra, ko baki so na ki aure ni haka, indai zaki zauna dani matsayin miji ban damu da rashin soyayyar ba.
"Ni dai ka sakeni, ba zan iya auren wanda bana so ba, sbd ba zan masa biyayya ba ga mata nan da yawa a duniya haba"
Tashin hankali ya bayyana akan fuskar Adnan yau shi ne mace ke wahalar da rayuwar shi har yake zubar mata da hawaye? Lallai soyayyar Abra tayi tasiri a zuciyar shi,
Domin son da yake mata ya sanya ba zai iya rayuwa babu Afra ba a yanzu komai nasu iri amma me ya sa halinsu ya bambanta?.
Yi ya yi kamar zai jawota jikinsa tayi saurin ja baya kusa da Salman hawaye na zuba a fuskar Adnan sosai ya ce.
"Don darajar Allah ki duba halin da zuciyata take ciki, ki sassauta yanayin ki a kai na, ki bani dama na sauya tunani zaki so ni ina da tabbacin zan sauya miki ra'ayi da kanki zaki furta kina so na, zan fifitaki da sauran mata, zan baki farin ciki da duk abin da kikeso, zaki rayuwar ƴan ci a gidan Adnan Aliyu Matawalle..... I love You Afra, i love You to the rest of my life, I can't imagine life without you wlh ina son ki ba zaki taɓa samun wanda zai so ki kamar ni ba"
Salman ya gyara tsaiwa tare da gyara zaman babbar rigarsa cikin nutsuwa ya kalli Adnan kana ya juya ya kalli Afra a hankali ya saka hannu ya kama nata cikin nutsuwa ya ce.
"Look into my eyes yaya" kasa kallonsa tayi Ubangiji yana gani Salman mugun kwarjini yake mata, yana yiwa idanunta tasiri sosai ba kaɗan ba.
"Please yaya" ya ƙara faɗa a taushashe har ƙamshin spraymintt mouth freshener ɗin bakinsa yana dokan hancinta wanda ya sanya tayi saurin lumshe idanunta. ganin da gaske ba zata kalle shi ba ya sanya gaba ɗaya ya tallafo haɓarta yana sauke mata numfashi a fuska kamar zai haɗe fuskokinsu ya ce.
"I love You Afra, From the moment I first laid eyes on you, I knew you were a perfect match for me. I love everything about you. Ina son ki so mai yawa, ina kishin da zai ɗauke numfashin sarrafa rayuwata, kada ki yi mamakin ganin bamu daɗe ba, ina jinki tamkar yaya a raina, ki bani dama na bayyanawa kowa irin soyayyar da nake maki, bana son nayi zurfin cikin da nayi a kan Abra. I will be always by your side in good and bad times, in happy and sad moments… because I love you! Accept my request please yaya"
Ya kama fuskarta da dukkan hannunsa wanda itama a lokacin ta buɗe idanunta tare zuba masa su. Tana son fahimtar da gaske wannan kyakkyawan farin ne yake son ta kuma yake son aurenta?
"Please yaya"
Ya marairaice fuska yana narke mata. Kasancewar rayuwar ƙauye tayi babu wanda kunya sosai a tare da ita bakinta kuma baya sarrafa wani abubuwan kafin ta faɗa. Muryar ta na rawa ta ce.
"Ina son ka ni ma, kuma zan aureka in dai da gaske kake zaka aure ni"
Ɓoyayyiyar Ajjiyar zuciya Salman ya sauke yana ƙara riƙe fuskarta da kyau! Wani farin ciki na ratsa zuciyarsa.
A fusace Adnan ya fisge Afra daga wajan Salman idanunsa na zubar da ruwa bakinsa da gaba ɗaya jikinsa suna rawa kamar ana kaɗa masa gangi ya ce.
"Ƙarya yake Afra, ta ya ya zaki aure wanda ki ka girma yayanki ne shi bai dace ya zama mijinki ba, ni ne daidai da rayuwar ki" ya faɗa yana jawota jikinsa sbd zafin da zuciyarsa ke masa.
"Don't try to hug the girl I'm going to marry again, na fika hauka zafin kishina yafi naka, kuma ka kusa daina ganin ko fuskarta, ita ɗin mallakina ce"
"Idan kai namiji ne sai ka hanani abin da na yi niyya" Adnan ya faɗa cikin raunin murya tare da ƙoƙarin kama bakin Afra da niyyar kissing. Cikin zafin zuciya Salman ya tattare hannun rigarsa farar fuskarsa ta yi jajir sbd abin da Adnan ɗin yake ƙoƙarin yi ɗin.
Saukar marin da Salman ya ji ne ya sanya ya tsaya da sauri baki buɗe yake kallon Afra wacce ta fisge kanta da ƙyar daga hannun Adnan ta kuma sauke masa marin da ita kanta bata san tayi ba. Idanuna ya cika da hawaye sbd nauyin marin da tayi ya kalli Adnan ta ce.
"Wa kake da suna? Wallahi na tsaneka ba zan taɓa son ka maye kawai"
"Koda zan faɗa miki su waye iyayenki na gaskiya?" Ta watsa masa harara ta ce "Ai ƙarya kake tun a garinmu kake yaudarata, babu wasu iyayena daka sani"
Adnan ya fara tari sosai idanunsa na rufewa tari yaci ƙarfin sa. Abbi da Mami da suke tsaye tun ɗazo suka ji kuma suka kaga abin da ke faruwa suka shigo cikin parlourn da sauri.
"Subuhanallah! Adnan lafiya me ya sameka? Na'ima kawo mini ruwa" Adnan yakai hannu bakinsa sai ka jini ya wanke masa tafin hannun da alama kamar aman jini yake. Bai damu da halin da yake ciki ba, tarin na sarƙafe masa numfashi cikin mayuyacin hali ya kalli Afra da jikinta ya gama sanyi baki ɗaya ya ce.
"Ko da zance maki Dr G.Y Bulama shi ne mahaifinki na gaskiya..." Cak numfashin sa ya tsaya jikinsa ya saki a jikin Abbi, a kiɗime Abbi ya ce "Salman get the car"
A hankali cikin nutsuwa da kamala Abdullah ke driving motar daga Airport zuwa gida. Yana mamakin abin da ya hana Uncle ɗin magana, girgiza kai ya yi yana mai da idanunsa kan titi yasan yau Ummi kwanan farin ciki za tayi speaking calmly ya ce.
"Uncle lafiya dai?" Wanda aka kira da Uncle ya juya ya kalli Abdullah a hankali ya ce.
"Alhmd Abdullah" ba wanda ya sake magana a haka suka ƙarasa gida, Abdullah yai horn a gaban makaken gidan iya haɗuwa ya yi gatekeeper ya buɗe, a parking lot sukai parking kafin Abdullah ya fita ya riga shi.
Ummi na zaune ta yi ado cikin wani dakakken lace sai ɗaukan ido yake ga gwalalen dake zube a hannunta. Ƙamshin turaren shi yasa ta tabbatar da zuwan mijin nata bayan wasu watanni zuwa shekara. Tsaye ta gansa ya zuba mata idanu cike da tunani a ransa da kuma son Ummi ɗin saura kaɗan ya yi kuskure a rayuwarsa.
Ummi ta miƙe tsaye tare da ƙara sawa gabansa ta ce. "Wlcm Man" murmushi ya ƙirƙira kafin ya ce "I missing Maaah" girgiza kai kawai tayi suka ƙarasa parlour idanunsa a kanta ya ce "Kiran gaggawa ina tsaka da buɗe sabon company hope lafiya dai?" Tai murmushi cikin sanyin maganar ta ce.
"Ka fara yin wanka kaci abinci?"
"I can't dole na fara jin damuwarki a gigice na tahu" ta gyara zama cikin damuwa ta ce "Abubuwa ne suke ta fara, gaba ɗaya dukiyata na neman lalacewa kullum cikin asara da rasa kuɗaɗe nake, na rasa inda abin ya samu tushe ina son magance matsalar, wannan dalilin ya sanya na saka Abdullah ya rufe company ta kalman dana buɗe" Ya runtse idanunsa domin abin ya zo masa a bazata bai ɗauka abin zai sauri har haka ba, shi bama wannan ce damuwar shi ba.
Yana ƙoƙarin magana wayar shi tayi ringing ganin wata number ya share, Ummi ta kafe shi da idanu can dai ya ɗaga a fusace ya ce.
"Wai mene?" Tsaki kawai yaja ya ce.
"Allah ya sawwaƙe" Ummi ta ce "Waye ba lafiya?" Yaja tsaki ya ce "No wani ma'aikacina ne" tana ƙoƙarin wata maganar aka sake kiran shi da sauri ya miƙe ganin number wanda yake ta jira. Jikinsa na rawa yama mance a gaban waye yake.
"Hello, Assalamu alaika" daga can wayar aka ce "Muna magana da Dr Bulama" ya juya ya kalli Ummi ya ce "E, shi ne" aka ce "Mahaifin Adnan Aliyu Matawalle ke magana, ina son ganinka domin samun tabbaci shin da gaske Abra da Afra yaranka ne kai ne real father nasu?" Gaba ɗaya jikin Uncle ko nace Dr Bulama rawa yake ya ce "Oh!ok yanzu haka Ina Dubai, amma zuwa gobe zan sauka Nigeria I'll call you" Abba da Abbi suka kalli juna a tare suka ce "Dubai????" Ya ce "Eh, amma gobe zan zo Insha Allah" kashe wayar ya yi gaba ɗaya jikinsa rawa yake ya ce. "Rumaisa daman yaranmu ba mutuwa sukai ba???" Ummi da Abdullah suka ce "What???....
[11/22, 4:52 PM] Abk: Cikin gigicewa, da gurɓatacciyar hausarta, ta fara haɗa larabci, turanci da kuma hausa, ta kalli Bulama ta ce "Wane irin zance ne kake mini haka? Kamar yaya yaranmu ba mutuwa suka yi ba? Bayan ina labor room, aka ce mini na haifi yara tagwaye amma babu rai?".
Jiki a sanyaye Bulama ya ce "Nima abin da nake mamaki kenan, ta yaya za ce suna raye?".
Ummi ta ce "Wai wani irin zance ne wannan? Baka tabattar ba kenan, ya kake son ka yi mini wasa da hankali Yusuf Bulama?".
Abdullah ya tattaro nutsuwarsa ya kalli Bulama, shi ya iya hausa sosai ba kamr rumaisa ba, ya ce "Ka sakamuna ruɗu ya kai Yusuf, ka sani cewa wannan maganganun naka barazana ne ga tunaninmu, da kuma zukatanmu, amma kuma biri ya yi kama da mutum, zan iya gasgata ka akan abin da kake faɗa, amma bamu labari, kafin ni in sanar da ku wani abu mai mahimmanci da Yakamata in faɗa".
Bulama yayi jimm, sannan ya basu labari tiryan-tiryan yadda abubuwa suka wakana, har zuwa lokacin da Abra ta rasu.
Gigicewa Rumai ta yi, yarana suna raye, ɗaya ta mutu? Waye ya yi mini wannan zaluncin, na rayu shekaru Ashirin da huɗu cikin ɗacin rai da ƙunar zuciya, yarana na raye amma suk rayu nesa da ni, ya za ayi ace na haifi yara aka ce mini sun mutu? Meyasa aka mini haka Ya kai Yusuf, ya a kai ka tabbatar da yarana na raye? Ka kaini in gansu a ina suke, ko da yake kace mini ɗaya ta mutu, to ina ɗayar a ina take? Dan Allah kar ka gaya mini abin da ba zai yiwu ba, in saka rai kuma in zo ba yarana ba ne".
Abdallah yayi ajiyar zuciya ya ce "A shekarun baya, da naje Nigeria, a garin Kano, naje sayayya wani mall, na haɗu da wata yarinya da sai da hantar cikina ta kaɗa saboda mamaki. Tana tsananin kama da shi Yusuf, kuma akwai wasu kamanni da ta ɗauko na ki, hatta wannan ɗigon baƙin na gefen idonki ta na da shi, mamaki da rikicewa ya sanya na kai hannu fuskarta, wanda suke tare da shi ya mareni, ina tunanin mijinta ne a wannan lokacin, ita yarinyar ta tsorata, har ta suma, ya ɗauketa suka bar wurin. Still a watannin da suka shuɗe, na haɗu da ita a nan Dubai, amma ita da wani daban n kuma ganinta, amma ban yi mata Magana ba saboda wanda suke tare ya mini kwarjini da yawa, kuma ina tsoron abin da ya faru wacan lokacin ya kuma faruwa, idan kuwa haka ne ina kyautata zaton ko da duk mutum ɗaya na gani, ko kuma su biyun ne Amma sanin gaibu sai Allah".
Fashewa da kuka Ummi tayi, tana fitar da tulin damuwar da ke mamaye a ranta, saboda tun bayan haihuwar yaran nan ba ta kuma samun wani rabon ba, kuma gashi Allah ya jarabce ta da son yara, yo ta ina ma zata samu rabo, miji ma wata ƙasar ita ma tana wata ƙasar daban, sai su shafe watanni huɗu wani bai sa wani a idonsa ba.
Cikin kuka ta ce "Abdallah, a gaggauta neman mini visa Nigeria, muje ya nuna mini 'ya'yana, ni da da yadda za ayi, a yanzun nan zamu tafi, amma ni haryanzu na kasa gazgata hakan"
Bulama ya rungumeta a jikinsa yana rarrashinta, tare da bata tabbacin cewa zasu tafi Nigeria tare, dan tabattar da abin da yake faɗa mata.
Afra kuwa ta ɗan fara tausayin Adnan, saboda yadda aka ce yana aman jini, gaba ɗaya baya hayyacinsa, amma sam ita Adnan bai mata ba, kallon mugu take masa, saboda yanayinsa yadda yake wasu abubuwan da zafi, Salman ya fishi kirki da bin komai a hankali, dan haka ita ba ta ga ta yadda zata zaɓi Adnan ba, ga salihi mai lallaɓata.
Adnan kuwa yana kwance a gadon asibiti, an ɗaura masa drip, sai dai yadda yake numfashi kawai ya isa ya tabbatar maka da cewar, yana jin jiki, daga nesa ana iya ganin yadda ƙirjinsa ke fat-fat da sauri da sauri.
Abbi kam mamaki ya cigaba da yi, dama Adnan ya san mahaifin Abra, amma yayi shiru da bakinsa bai faɗa ba? To yaya ma aka yi ya tabattar da Bulama ne mahaifinsu, ko dai zafin ciwo me ya sanya shi faɗar hakan, suka biye masa suka kira bawan Allah.
Hajiya Saudat ta rasa in da zata saka kanta, abin duniya ya isheta, ga Meenal a kwance ba lafiya tun da aka yi aikin nan, ta ƙi lafiya, an cire mahaifa ɗungurun gum, ba ta taɓa sanin Meenal na bin maza ba, ga uwa ba, abin da Bulama ke shirin yi, idan bar tone tone yayi yawa, tabbas akwai Matsala, dan daga ita har shi suna cikin tsaka mai wuya, nan ta koma tunanin yadda zata shawo kan lamarin.
Wayarta ta ɗauko, ta kira layin Bulama, ba ta damu da kuɗin da za a ja ba a waya, saboda kiran lambar ƙasar waje.
Har ta fidda ran zai ɗaga, ya ɗaga wayar.
"Hello, kana ina ne?"
Haushi ne ya kama Bulama ya ce "Meye hak sai kace wani ɗanki? Ya ma dace ki kirani a halin yanzu? Kin fi kowa sanin ina na tafi, ina tare da Rumaisa, kuma sai ki kirani a waya?"
"Dan me ba zan kirak a waya ba, in ruwana da wata Rumaisa? Ka tafi ka bar ni da yarinya da larura, ko ka kira kaji ya jikin nata"
"Saudat, abin da ya samu Meenal, ke ta shafa da ke da ita, ni ban yiwa Meenal tarbiyyar taje ta bi maza a waje ba, har ta zubar da ciki wanda ya kusa ajalinta ba, dan haka ki gaggauta rabata da gidana kan in dawo, i disowned her as my child, taje ta nemi wani uban".
"Wallahi ƙarya kake yi, Meenal jininka ce, 'ya ɗaya tilo da Allah ya baka, dan haka dole muyi haƙuri da ain daya sameta mu riƙeta".
"Dole kiyi haƙuri dai, amm banda ni ku san yadda zaku yi ke da ita" ya katse wayarsa.
Jifa tayi da wayar tare da taune lips ɗinta na ƙasa 'Anya zancen nan bai tabatta ba na cewar yaran nan suna raye ba, tun da har ya iya nuna halin ko in kula ga 'yar da ya ƙallafa ransa a kanta kasancewar ita kaɗaice ba? To yaya aka yi yaran suka rayu, bayan tun a Asibiti aka ce ba su zo da rai ba? Wane al'amari ne haka mai ban mamaki? Anya ba ƙarya bace da rainin hankali kawai? To amma hotunan da aka aiko masa fa kika ƙona' wata zuciyar ta tambayeta. Tabbs yarinyar jikin wannan hoton duk in da ta fito tana da alaƙa da Bulama. To ko dai matan banza ya fara bi? Aka haifa masa ita? Haka ta dinga tunani barkatai, ba tare da ta samo amsoshin tambayoyin ta ba, sai dai ta san tasowar wannan lamari barazana ne a gareta da Bualaman kansa, mussaman a kan sirrin da suka yi shekaru suna binnewa.
Abba ne da Abbi tsaye a kan Adnan, da aka samu ya ɗan farfaɗo daga fita hayyacin da yayi, lokaci ɗaya duk ya yi rama, yayi zuru-zuru, Mami da Hajiya Mama kuwa suna reception, suna wa Adnan Adduar samun lafiya, saboda ya sha wahala.
Abbi ya numfasa ya ce "Yanzu muna jiaran dawowar wannan mutumin, sannan shi Adnan ya ƙarasa warkewa, mu ji yaya aka yi suka zama 'ya'yan mutumin?".
Abba ya ce "Ba zamu jira sai ya warke ba, dole ai wadda za ayi idan mutumin ya dawo gari, ko mu muje, ko shi ya zo ya same mu".
Abbi ya gyara tsayuwarsa, yana kallon Adnan, a lokacin da Adnan ya gyara kwanciyarsa, yana bin sun Abbi da ido.
Abbi ya ce "sannu Adnan, Allah ya baka lafiya, in dai a ka Afra ne, ka kwantar da hankalinka, ni zan rarrasheta, za a aura maka ita insha Allah, dan ita ya dace ta maye maka gurbin 'yar uwatta".
Abba ya ce "In ji wa? Ai ida har ina raye Adnan ba zai auri Yarinyar nan ba, Salman shi ya dace ya auri Afra".
Abbi ya ce "Me yasa zaka ce haka?".
"Wa zai bawa Mutumin banza 'ya, ai shi ya san mai nake nufi"
Adnan ya haɗa hannayensa biyu, alamar ban haƙuri, yana girgiza kansa, hawaye na fita daga idonsa.
Abbi ya ce " Bai kamata ka faɗi haka a gabansa ba, bayan ga halin da yake ciki".
Abba ya ce "Wannan yaron ba abin tausayi bane, gara a bari ya ɗanɗana kuɗarsa, kuma sati mai zuwa zan karɓawa Salman Auren Afra a wurinka, idan har zaka mini kara, Salman ɗana ne"
Cikin hanzari Abbi ya janyo hannun Abba, zuwa waje ya ce "Duk laifin da yayi bai cancanci wannan horon ba, magana fa ake ta rayuwarsa".
Abba ya ce "Amma dai ka san Aurensa da Afra ba abu ne mai yiwuwa ba ko? Alhalin ga Salman".
"Na sani, amma sai a tausayawa halin da ya tsinci kansa a ciki, koma wani irin laifi ya aikata maka, bai kamata ace ka ɗau wannan zafin ba, har ka nesanta shi da tausayawarka ba, haba Alhaji Aliyu, ka zafafa da yawa, akwai buƙatar ka sassauta masa haka"
Abba ya girgiza kai ya ce "Ba zaka gane bane Major, halin da Adnan yake ciki, dai-dai da shi ne, shiya janyowa kansa".
Abbi ya ce "Ba ina son jin laifin da ya aikata maka bane, ina nema masa alfarma ne, dan Allah dan Annabi, a sassauta masa a duba halin da yake ciki, ka rage wannan fushin da ka ke da shi".
Abba ya ce "Na ji, amma ni yanzu babbar damuwata shi ne, ba zan bar garin ba, sai Mutumin nan ya dawo, mun cinma matsaya, na tabattar da abin da Adnan yake faɗa, gaske ne ko kuma ƙarya yake yi".
"Haba Alhaji Matawalle, ga gidana mai zai sa kaje ka kama hotel ka zauna, idan ma ba zaka zauna a gida na ba, akwai guest house ɗina, sai kaje can ku zauna, mu jira zuwan mutumin, Allah dai ya sanya mu ji alkhairi".
Afra sai koke koke take yi, gaba ta ma rasa kukan me take yi ne? Damuwa da halin da Adnan yake ciki? Ko kuma farincikin an san waye mahaifinta? Bana wannan ba, ai haryanzu lalube ake a cikin duhu, ba tare da an tabattar da sahihancin cewar wanda Adnan ɗin ya ambata shi ne mahaifinta ba, wataƙila ma ƙarya yake mata, kamar yadda ya yi mata ƙarya a ƙauye.
Kwanakin Adnan uku a Asibiti, ya ɗan farfaɗo jikinsa da sauƙi, Afra taje duba shi sau ɗaya yana bacci, ya yin da Salman kuwa, sai da Mami ta haɗa masa da zagi, sannan ya yadda yaje duba Adnan, duk da a ƙule yake da Adnan, amma ya tausaywa yadda ya ga Adnan ɗin ya koma.
Akwa abubuwa da yawa da Salman ba zai taɓa mantawa da su ba a rayuwarsa, daga shigowar Adnan rayuwarsu, ya rusa musu farinciki, zuwa ga mutuwar Abra, ba zai taɓa manta lokacin da a gaban idonsa, Adnan ya mari Abra ba dan kawai ta ce tana son sa, da ya tuna ire-iren wannan abubuwan da suka faru, sai tsanar Adnan ta ninku a zuciyarsa, ban da zuciyar musulunci, da kuma yadda Mami ta dage da babu abin da zai sanya ya zo duba Adnan. Kuma a wannan karon ya ƙudirce a zuciyarsa ko mai za ayi, ba zai barwa Adnan Afra ba, a wannan karon Afra tasa ce.
Wasa-wasa, sai da Bulama ya kwana biyar a Dubai, sannan passport ɗin Rumaisa ya zama ready, gaba ɗaya a kwanakin nan, banda aikin rarrashinta babu abin da yake yi, kullum cikin kuka take, ga gefe guda Saudat ta uzzura masa da kira, ƙarshe sai kashe wayarsa ya yi gaba ɗaya.
Ranar Asabar, Bulama da Rumaisa tare Abdallah suka sauka a Nijeriya, a garin Kaduna, sai dai a guest house ɗin sa na Kaduna suka sauka, saboda baya son wani dalili ya sanya wani ya san da cewar, sun sauka da Rumaisa a Nigeria.
Lambar Adnan Bulama ya duba, ya kira shi, sai dai sam Adnan ya ƙi bawa kiran mahimmanci balle ya ɗauka, kasancewar yana tare da su Abba a guest house ɗin Abbi, Yana kwance a falo, Hajiya Mama na gefensa tana jan carbi, ta ji wayar Adnan ta cika mata kunne, amma ba shi da niyyar ɗaukar wayar.
"Adnan ba wayarka ce take ringing ba"
Cikin numfarfashi na marasa lafiya, Adnan ya ce "Mama I can't pick it".
Mama ta miƙa hannu ta ɗaga wayar, cikin nutsuwa Bulama ya yi sallama, Mama ta amsa suka gaisa, Bulama ya ce me wayar yake nema.
Mama ta ce "Bashi da lafiya, yana kwance"
Bulama ya ce "Subhanallah, Allah ya bashi lafiya, dama nine Yusif Garba Bulama, wanda aka ce yarana na wurinku".
Mama ta ce "Ahh, Allah sarki, ka dawo garin ne?"
"Eh mun dawo, naje na taho da mahaifiyarsu ne, dan mu samu a tabattar idan yaran namu ne"
Mama ta ce "Alhamdilillah, muna nan Kano dama ku muke jira, da ka ce tun a washegari zaka zo".
"Eh, an tsaya gyara passport ɗin mahaifiyarsu ne, insha Allah gobe in Allah ya kaimu, da wuri zamu taho, sai a bani Address ɗin in da zamu zo".
Mama ta tashi, taje ta kaiwa Baba waya, suka sake yin magana da Bulama, ya yi masa bayanin Adress ɗin.
Washegari, wajen ƙarfe goma sha ɗaya na rana, Abba ya shigo ɗakin da Adnan yake ya ce "Ka tashi ka shirya, muje mu tari Mutanen nan, sai ka tabbatar mana da dalilin da yasa kace shi ne mahaifinsu, kuma ka gaya musu da ka auri 'yar su me kayi mata, da kuma dalili da ya sanya ka san in da mahaifin na su yake, amma ka ƙi faɗa da wuri". Marairaice fuska Adnan ya yi zai yi magana, amma Abba ya dakatar da shi ya ce "Kar ka gaya mini komai, ka tashi mu tafi, mutumin banza kawai, ai kai ba abin tausayi bane"
Jiki ba ƙwari haka Adnan ya kammala shiryawa, suka tafi gidan su Salman.
Suna zazzaune a falo, suna jiran zuwan su Bulama, Little da tuni ta fara rarrafe, ta na jikin Adnan tana wasa, ta ja masa gemu, ta ja masa gemu, yana kallonta yana murmushi, lokaci lokaci yana share ƙwalla.
Ko da Afra ta fito falo ta yi tozali da Adnan sai da gabanta ya faɗi, yayi rama tamkar ba shi ba duk yayi wani iri, gashi yadda numfashinsa ke fita ma zai ƙara tabattar maka yana cikin mawuyacin hali.
Kallo ɗaya yayi mata ya kauda kansa, ya cigaba da yiwa Little wasa, yana share hawaye, gaba ɗaya sai jikin Afra yayi sanyi, ko ba komai mijin 'yar uwatta ne, abin da tayi na nuna masa ƙiyayya, bai kamata ba, amma ba yadda zata yi, dan ita tafi son Salman a kansa.
Abbi ne ya shigo tare da Abba ya kalli Mami sannan ya kalli Afra ya ce "Afra tashi ki koma ɗaki, make sure baku bari ta fito ba, sai mun gama tattauanawa, gasu can sun ƙaraso" Afra tana ji tana gani, aka kaita ɗaki aka rufe.
Abbi ne ya yiwa su Bulama jagora, zuwa cikin katafaren falon gidan Major.
Rumaisa sai rarraba ido take yi, Mami ta tsurawa Rumaisa ido, a ranta ta ce "Tsarki ya tabbata ga Allah, su Abra dai 'ya'yan balarabiya ne".
Abdullah ya kalli hoton falon, cikin harshen larabci ya ce wa Rumaisa "Ai wannan ita ce yarinyar da nake baku labari, na haɗu da ita karo biyu".
A gigice Rumaisa ta nufi hoton, tana ta larabci, ba komai suke ganewa a maganar ta ta ba, saboda kukan da take yi, da ƙyar Bulama ya rarrashi Rumaisa, su Abbi suna ta rarrashinta cikin harshen turanci.
Tabbas babu wanda zai kalli matar nan ya ce ba ita ta haifi su Abra ba.
Har ta zauna ta miƙe a gigice ta nufi in da Adnan ke zaune yana binta da ido, dan hatta yanayin rikicewarta tana kuka tamkar Abransa.
Little ta ɗauka ta ƙanƙame, tana cewa Bulama wannan ma 'yar ta ce.
Cikin harshen turanci Bulama ya ce "Ta yaya wannan zata zama 'yar ki, bayan 'ya'yanki sun kai aƙalla shekaru ashirin da huɗu".
"To ina yaran nawa suke?" Ta tambaya tana zubar da hawaye, tare da sumbatar Little, duk ƙyuyar yarinyar amma ba ta yiwa Ummi ba, saima kallonta da take tayi.
"Bayani za ai miki ai, amma ki zauna"
Da ƙyar Rumaisa ta zauna, aka gaggaisa aka kawo musu ruwa, aka samu Rumaisa ta ɗan nutsu, sannan Abba ya kalli Adnan ya ce "To ka san dai kai ne silar taruwarmu a nan, dan haka saika warware mana abin da ka ƙulle a ranka, kayi da turanci yadda zata fahimta".
Adnan ya ɗan yi jimmm, sannan yai ajiyar zuciya, jiki a sanyaye idonsa fal ƙwalla ya fara bada labarin abin da ya faru.
Ya fara da irin soyayya da shaƙuwar da ke tsakanin sa da mahaifiyarsa, har zuwa lokacin da ta rasa ranta a sanadin Sakaci da son abin duniya na Bulama.
Ya cigaba da bada labari, yadda ya rayu, da kewar rashin mahaifiyarsa har zuwa ranar da ya raka Usman gidan Bulama wurin Meenal, da hoton Bulama da ya gani, da fari a kan Meenal ya so ya aura, kuma ga Usman, katsam da yaje Kano, ya haɗu da Abra. Nan ya basu labarin yadda ya je har Yola, garin su Bulama samun bayanai a kansa, a nan ya tabattar da Abra 'yar sa ce.
Rumaisa ta ce "Ita ba ta fahimta ba, wacece Meenal da ake magana a kanta, kuma wane Asibitin ake magana ba ta gane zancen ba?!
FARKON LABARI
YUSUF GARBA BULAMA ɗan asalin garin Adamawa ne cikin Yola
NA KUƊI NE, A BIYAMU HAKKINMU KAN A KARANTA
08081012143
[11/23, 12:57 PM] Abk: Su biyu kacal iyayensu suka haifa, daga shi sai ƙanwarsa Murja. Sun taso cikin kulawa da soyayyar iyayensu, duk da ba masu ƙarfi ba ne sosai amma suna da rufin asiri daidai gwargwado, kuma babu abin da suka nema suka rasa a rayuwa. Yusuf ya kasance mutum ɗan gayu, mai son rayuwar ƙarya da sabgar masu kuɗi. Tun yana karami Mahaifinsa Garba Yusuf Bulama ya fahimci wannan halin nasa, hakan ya sa kodayaushe cikin masa nasiha da nusar da shi ya tsaya a duk inda Ubangiji ya ajiye shi a rayuwa yake. Yusuf ya kan nuna kamar ya ɗauki maganar mahaifinsa, amma cikin ransa ƙara burika ma yake yi, addu'ar shi da burinsa a kullum Allah ya sa ya zama shahararren mai kuɗi, wanda za a dinga kwatance da shi saboda kuɗinsa.
Mahaifinsu ya saka su a makarantar boko da islamiyya, amma sai ya fi mayar da hankali a kan karatun boko, a cewar shi saboda shi ne karatun samun kuɗi. Suna daf da kammala secondary school suna SS 3 Allah ya yiwa mahaifinsu rasuwa. Bayan Mahaifiyarsu ta fita daga takaba sai Bulama ya fito da buƙatar cewa yana son ya cigaba da karatu, Mahaifiyarsu ta ce A'a, ita dai ta fi son ya zauna ya cigaba da kiwo ya gaji mahaifinsa, a ganin Bulama hakan faɗuwa ce a ce kamar shi wayayye ɗan boko da kiwo, ba zai iya ba gaskiya. Lallaɓa mahaifiyarsu ya dinga yi tare da nuna mata alfanun karatun fiye da Noma, har ya samu ta amince, aka siyar da wasu daga cikin shagun da baffansu ya bari aka damƙa masa kuɗin akan ya je ya cigaba da karatun da su. Yadda ake ba shi labarin ABU Zariya da kuma wasu daga cikin abokansa da suke can ya sa shi ma ya je ya fara karantar medicine.
Shigar shi makaranta ya ƙara masa ƙarfin burinsa a cikin ransa, saboda ganin yadda ƴaƴan masu kuɗi suke rayuwa, abun yana matuƙar burge shi. Ba ya abota da ƴaƴan talakawa yan'uwansa sai dai da masu kuɗi, kasancewar shi kyakkywa kuma ɗan gayu ya saka ake ɗauka shi ma ɗan masu kuɗin ne. Suna level 3 aka tafi wani strike mai zafi, a lokacin wani abokinsa Munnir yake sanar masa mahaifinsa ya tura shi ƙasar Dubai akan harkar kasuwancinsa, zai tafi idan aka koma school sai ya dawo. Ranar da ya faɗa masa kasa bacci ya yi, don ji yake dama a ce shi ne zai tafi Dubai ɗin nan, ya dinga ƙissime-ƙissimen me zai siyar a cikin gadon da mahaifinsu ya bar musu wanda zai ishe shi kuɗin jirgi zuwa Dubai ya bi Munnir su tafi tare, amma duk abin da ya ayyana zai sanar sai ya ga ba zai kai ba, don duk saboda karatunsa da ƙaryayyakin da yake kiran Inna ya yi mata akan kuɗi, ya sa duk ta sissiyar da abubuwa da dama na gadon ta tura masa kuɗin. Bayan kwana biyu abin yana cin shi a rai ya kasa dannewa, hakan ya sa ya yanke shawarar kawai ya kira Munnir ya sanar masa, ko Allah zai saka a dace su tafi tare.
Kamar wasa Munnir yana kai maganar gaban mahaifinsa ya amince, bayan ya kai masa Bulama ya yi masa tambayoyi a game da rayuwarsa, jin Maraya ne kuma ba shi da aikin yi ya sa ya amince, amma bisa sharaɗin sai iyayensa sun amince. Cikin tsantsar murna Yusuf ya koma gida ya sanar da Inna, da farko ƙin amincewa ta yi, sai da ya kira mahaifin Munnir ya yi mata bayani sosai yadda za ta gane sannan ta amince da ƙyar. Sun ci kuka lokacin da zai tafi ita da Murja wadda ake shirin aurenta a lokacin, amma shi ko ɗigon hawaye saboda farinciki da murnar da yake ciki, a ganin shi wannan dama ce da za ta taimaka wajen cimma burinsa.
Sun isa garin Dubai lafiya, babu ɓata lokaci kuma suka shiga abin da ya kawo su na business, Bulama jin zuciyarsa yake fess yau ga shi a Dubai, tamkar wanda aka tsunduma a Aljannah haka yake jin kansa don farinciki. Ranar wata Juma'a da ba zai taɓa mantawa da ita ba a rayuwarsa sun je wani shago siyayya suka haɗu da Rumaisa.
Shagon sayar da Gold's ne, su Bulama sun zo siya wanda za su tura wa Baban Munnir Nigeria ya sayar. Suna cikin zaɓa Bulama ya kai hannu zai ɗauka ita ma ta kawo kyakkyawan farin hannunta. A tare suka janye hannayen nasu tare da duban juna da sauri. Kasancewar ta mace mai fara'a sai ta sakar masa murmushi tare da faɗin. "I'm sorry." Cikin siririyar muryarta. Murmushin ya mayar mata tare da ɗaga mata hannu alamun babu komai, sannan ya bar gurin. Da kallo ta bi shi har ya ɓacewa ganin ta, ajiyar zuciya ta sauke ta cigaba da duba sarƙoƙin.
Tunda Rumaisa ta koma gida sai Bulama yay ta faɗo mata a rai, abin ya ba ta mamaki ba kaɗan ba, don duk da kallo ɗaya ta yi masa amma ta gane ba ƙabilarta ba ne, bai ma yi mata kala da fararen fata ba, ya fi mata kala da ƴan Africa, duk da fari ne tass shi ma. Bayan wasu kwanaki suka ƙara haɗuwa a hanya, a lokacin suna tare da ƙaninta Abdallah, amma duk da haka sai ta yi masa magana, abin mamaki shi ma ya gane ta, gaisawa suka yi cikin fara'a kamar waɗanda suka daɗe da sanin juna.
Watarana su Munnir sun je gurin da suke sayayyar kaya suka tarar kayan gurin duk an kwashe sai kaɗan, mai gurin ya ce su bari sai zuwa washegari za a jera wasu sai su zo su saya. Cikin rashin jin daɗi Munnir ya ce masa. "Ai kayan nan yau ake buƙatar su, saboda mahaifinmu yana ta kiran mu akan nasa sun kusa ƙarewa, kuma mun riga mun yi bucking Flight ɗin da zai tafi da kayan." Mai gurin ya ce musu babu damuwa, zai haɗa su da wata abokiyar kasuwancinsu, wadda Insha Allahu komai suke so za a su samu a gurinta. Ba su yi musu suka amince masa, bayan sun je suka tarar da fiye da abin da suka yi tsammani, don duk wani nauyi na Dubai gold akwai shi a shagon, kuma kayan gurin da sauƙi har ya fi na inda suke saya. Alokacin ba su haɗu da mai shagon ba sai yaranta, don ba ta zama ita a sati sau ɗaya take zuwa ta ga yadda abubuwa suke tafiya. Da za su ƙara sayan kaya sai suka koma gurin, saboda mahaifin Munnir ya yaba kayan sosai, ya ce idan za su ƙara saya su je can idan za a samu. A wannan zuwan Bulama suka ƙara haɗuwa da Rumaisa, ashe ita ce mai gurin. Ta yi mamakin ganin su sosai, shi ma haka. Tun daga ranar idan suka zo siyayya sometimes suna haɗuwa, har suka saba suka yi musayar contacts ɗin juna. Munnir ya dinga tsokanar Bulama yana cewa. "Ɗan fillo ko dai da ƴar Balarabiyar nan za a yi ne?" Idan ya faɗi haka sai ya yi murmurshi ya ce, babu ɗaya haɗuwar jini ce kawai.
Asalin Rumaisa Balarabiya ce Ƴar ƙasar Dubai, kyakkyawa ce don ko a cikin larabawan mai kyau ce, ita kaɗai iyayenta suka haifa, tun tana yar ƙarama mahaifinta ya rasu. Mahaifinta shahararren mai kuɗi ne, ya mutu ya bar dukiya mai ɗimbin yawa. Mahaifiyarta ta ƙara aure bayan rasuwar mahaifinta ta haifi Ɗa Namiji Abdallah.
Shaƙuwa mai ƙarfi ce ta shiga tsakanin Rumaisa da Yusuf Bulama, daga baya kuma ta rikiɗe ta koma soyayya. Tsakani da Allah Rumaisa take ƙaunar Yusuf, shi kuma yana son ta ne saboda tarin dukiyarta, amma ko kaɗan ba ya nuna mata hakan, don in ta ba shi abu ma ba ya karɓa sai ta nuna masa ɓacin ranta. Ƙauna da kulawa yake nuna mata sosai, wanda hakan yake ƙara dilmiyar da ita a cikin ƙaunar shi. Cikin haka aka janye strike ɗin da aka tafi na watanni goma sha uku, lokaci shekara guda cif da haɗuwar Rumaisa da Bulama. Ranar da za su dawo Nigeria ba ƙaramin tashin hankali da damuwa Rumaisa ta shiga ba, Yusuf ya dinga pretending as ya fita shiga damuwa, da ƙyar ya lallaɓa ta ɗan kwantar da hankalinta, a haka suka rabu zuciyoyinsu babu daɗi. Bayan Rumaisa ta gama cika shi da kayan arziƙi. Sun cigaba da soyayya kamar babu gobe ta waya, Rumaisa ta ɗauki dukkan yarda da k'auna ta damƙa wa Yusuf. Rumaisa macece mai kirki da addini da sanin ya kamata, matsalar ta ɗaya tana da zazzafan kishi, wanda wannan kamar a jinin larabawa yake. Tana mugun kishin Yusuf sosai, a kodayaushe cikin nanata masa kar ya ci amanarta take ko ya kula wata mace bayan ita, zuciyarta ba za ta ɗauki hakan ba, sannan ta yi masa alƙawarin tana nan tana jiran shi, ko shekara nawa zai yi kafin ya kammala karatunsa za ta jira har ya gama su yi aure. A tarayyar su ba ƙaramin kuɗi ta ba wa Bulama ba, duk da a zahiri yana nuna mata ba ya son ɗawainiyar da take shi amma ba ta fasawa. Lokaci ɗaya Bulama ya fara samun kuɗi, ya saya Mota da abubuwan more rayuwa. Inna ta san da zaman Rumaisa, amma ba ta san soyayya suke da Yusuf ba, a yadda ya faɗa mata abokiyar kasuwancinsu ce kawai suka saba da ita.
Bayan kammala karatunsu da N.Y. S.C Ta turo masa kuɗin jirgi ya tafi Dubai ya ɗora karatu, Rumaisa ce ta ɗauki nauyin karatun da gurin zamansa da abin da zai ci da komai na buƙatun rayuwa. A lokacin Rumaisa ta sanar da danginta Yusuf take so, wanda a karon farko suka ce ba su amince da wannan maganar ba, duk larabawa da ƴan'uwanta da suke son ta, ta rasa wa za ta ce za ta aura sai bak'ar fata ɗan Nigeria. Jin haka ya sa Rumaisa shiga cikin tashin hankali da damuwa, ta dinga koke-koke da roƙon su akan su amince, ita a haka take son Yusuf ko ma ɗan ina ne, amma suka ce ba ta isa ba, tun wuri ma ta rabu da Yusuf kafin su saka a ɗaure shi. Mahaifiyarta ce kawai ta goyi bayanta a lokacin, duk da ita ma ba ta so, amma tausayin 'yarta da ƙaunar ta ya sa take supporting ɗinta. An yi badaƙala da ja'inja ba kaɗan ba tsakanin dangin mahaifin Rumaisa da mahaifiyarta kafin su amince ta auri Bulama, amma sun ce babu ruwansu duk abin da ya biyo baya mara daɗi kar ta neme su. Ba a yi Auren ba sai da dangin mahaifiyarta suka zo Nigeria suka ga asalin Bulama, shi kuma ya yi cike-ciken takardu na yarjejeniya a Dubai ɗin. Al'amarin ya ba wa kowa mamaki a Adamawa, musamman Inna da Murja, Yusuf da auren Balarabiya, abun kamar almara.
Buri ya cika bayan fitar da rai da hakan, farincikin da Bulama da Rumaisa suka yi a lokacin Aurensu ba zai misaltu ba. Musamman shi da ya jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya, yana son Rumaisa sannan kuma ya san dukiyarta yanzu za ta koma tasa da ta ƴaƴan da za su haifa. Soyayyar da Bulama ya nuna mata a zaman Aurensu ya sa ta ƙara yarda da shi da ƙaunar shi. Bayan ya kammala karatunsa ya shirya don komawa Nigeria, a nan mahaifiyar Rumaisa ta ce ba zai tafi da ita ba, ba za ta yarda yarta ta yi nesa da ita ba. Shi ma ya ce ba zai fasa komawa Nigeria ba, saboda Mahaifiyarsa da ƙanwarsa shi kaɗai suke da shi, suna buƙatar shi a kusa da su. Ba don Rumaisa taso ba ta bar shi ya tafi. Dawowar shi ba jimawa ya fara aiki a wani babban asibiti a nan Adamawa. Bayan wasu watanni ya koma ya ga Rumaisa, a lokacin ta raba dukiyarta biyu ta ba shi rabi, ta ce ya je ya yi duk kasuwancin da yake so a Nigeria ya juya kuɗin. Kusan haukacewa Bulama ya yi saboda tsabar murna da farinciki, ranar ƙaunar da ya nunawa Rumaisa bai taɓa nuna mata kamar ta ba. Bai jima ba ya ƙara dawowa Nigeria, anan ya yi deciding ya buɗe Babban Asibiti nasa na kansa. Bai buɗe a Adamawa ba saboda wani dalili nasa ya buɗe a Kaduna, ya saka masa sunan mahaifinsa GARBA YUSUF BULAMA. A lokacin ya haɗu da Saudat suka fara soyayya. Saudat irin matan nan masu feleƙe da iyayi da son sabgar ƙarya. Farkon haɗuwar su da bulama ba ta zata yana da mata ba sai da ya faɗa mata. Ta ji takaici da baƙincikin fara mallakar wata da ya yi kafin ita, amma haka ta daure suka cigaba da soyayyar su. Sai dai cikin ranta ƙiyayyar Rumaisa ce fal duk da ba ta taɓa ganin ta ba sai dai a hoto. Abin da yake ƙara ƙona mata rai yadda Bulama ya ɓoye wa Rumaisa tarayyar su, ya nuna ba ya son ta sani. Kammala ginin G.Y HOSPITAL AND MATERNITY Ya yi daidai da lokacin bikin SAUDAT da BULAMA, don haka aka sha shagali ba na wasa ba. Auren ya kasance tamkar na cin amana, tunda ba da sanin Rumaisa aka yi ba kuma da dukiyarta. Bayan bikin da wata biyu Bulama ya koma Dubai, a wannan zuwan Rumaisa ta samu ciki, bai jima ba ya dawo Nigeria saboda yana son ya kula da Hospital ɗinsa, sai dai bai sanarwa da Rumaisa ya buɗe asibitin ba.
Watan cikin Rumaisa takwas ta kira Bulama ta ce za ta zo Nigeria ta gaishe da Inna ta zazzaga danginsa su san ta, ta san su. Bulama bai so hakan ba saboda gudun tonuwar asirin Auren Saudat, amma bai nuna mata ba saboda kar ta yi tunanin wani abu, dama tana ta complain akan yana daɗewa yanzu kafin ya je ya gan ta.
Bayan sun gama wayar ya fara haɗa kayansa, cikin mamaki Saudat da ta shigo ɗakin da yake ta ce masa. "Lafiya kake haɗa kaya da sakaliyar yammar nan Doctor?"
"Adamawa zan je."
Ya ba ta amsa a tak'aice
"Adamawa kuma? Shi ne ba ka sanar mini na fara haɗa kaya ba ni ma?"
Yana zuge zip ɗin trolley ɗinsa ya ce. "Ba da ke zan tafi ba, Rumaisa ce za ta sauka a ƙasar nan gobe, kin kuma san ba ta san da zamana a Kaduna ba balle aurenki da na yi, don haka dole ya zamana a Adamawa za ta same ni." Cikin takaici ta ce. "Sai yaushe kuma za ka dawo?"
"Sai ranar da ta tafi."
"Asibitinka kuma fa."
"Akwai masu kula shi kamar ina nan ai."
"To amma ni haka zan ta zama ni kaɗai, kana ƙasar ma amma ba za mu haɗu ba har sai ranar da ta tafi?"
Cikin fusata ya ce. "Haba Saudat ya kike so in yi ne? Ke duk watanni da nake yi a gurinki ban je wajenta ba, ba kya gani? Sai yau ɗaya za ki ɗaga mini hankali. Rumaisa tana buƙatar kulawata a halin yanzu sosai fiye da ke, saboda tana ɗauke da juna biyu, don haka ko da ba za ta zo ba ni zan je. And lastly kar ki kuskura ki kira ni ko ki mini text, ni zan na kiran ki da kaina, sai na dawo, zan miki transfer ɗin kuɗi idan na ƙarasa." Ya ƙarashe maganar tare miƙewa ya fita.
Da wani irin kallo ta bi shi cikin bugawar zuciya da tsananin tashin hankali har ya fice. Gwauron numfashi ta sauke tare da furta "Ciki?" Tana gyaɗa kai, lokaci ɗaya ta miƙe kamar wadda aka tsikara ta shiga kaiwa da komowa a cikin ɗakin.
Littafin kuɗi ne, ku biya kafin ku karanta. 09047871750
[11/25, 10:36 AM] Abk: Maganar samun cikin Rumaisa ya ɗagawa Saudat hankali, zuciyarta ta fara saƙawa kwakwalwarta mugun tunani. Ta ɓangaren Rumaisa ta samu iyayen Dr lafiya cikin karamci da walwala hakan yasa ta saki jiki har ta ce zatai wasu kwanaki. Tana saura kwana uku tafiyarta naƙuda ta kamata cikin gaggawa suka nufi asibiti tasha baƙar wahala ƙwarai har an fara tunanin za ai mata C.s sai Ubangiji ya sauke ta lafiya ta haifi twins.
Murna ta kama Dr G.Y sai dai murna ta koma ciki domin awanni wajan biyu da haihuwar aka dawo da jariran a hannu Allah ya yi musu rasuwa, daman da aka haife su ba wanda yaga kalar su sai da suka rasu. Haka akai musu suttura ba tare da mahaifiyar su ta gansu ba. Lokacin da Rumaisa ta samu labari kusan hauka ta kusa yi uwa uba akace ba zata sake haihuwa ba Wannan dalilin ya sanya ta saka damuwa a ranta ƙwarai da gaske.
Bayan sati biyu ta tattara ta koma Dubai hakan ya yi wa Bulama daɗi ya ƙara samun damar da zai zauna da Saudat, a lokacin ne kuma labarin rasuwar P.A ɗin Rumaisa ya riskesu ya yi hatsari ya rasu da shi da motar gaba ɗaya suka ƙone ƙurmus.
Bulama ya sanya wa ransa samun dukiyar Rumaisa ko ta halin yaya ne ta zama mallakinsa. Lokacin guda ya shiga amsar kuɗi wajanta da niyyar zai buɗe wasu, kamfanoni wani lokacin yace kuɗin sun gaza wani lokacin ya ce za a ƙaro kaya, wani lokacin ya ce ta bashi rance. Yarda da amincin da tai masa sai ta kalle shi tare da yin murmushi ta ce "Wanne irin rance ya kai Yusuf dukiyata taka ce dani da duk abin dana mallaka naka ne" idan Rumaisa ta faɗi haka sai Dr Bulama ya rungume ta tsam a jikinsa tare da maganganun masu daɗi.
Ganin abubuwa sun fara runcaɓewa Rumaisa ga P.A ɗinta ya rasu ya sanya ta ɗakko Abdullah ƙaninta ta dawo da shi wajanta, tare da ragama wasu gefe na dukiyoyinta yana kulawa dasu ta bashi matsayin sabon P.A
Daga nan ganin Dr Bulama ya ƙara yiwa Rumaisa wahala a cewar shi aiki ne ya yi masa yawa sosai, lokacin kuma tuni Saudat ta samu cikin Meenal farin ciki wajan Bulama ba a magana, ya tattara ya manta da batun ya taɓa haihuwar yara bai kuma damu da rashin haihuwar Rumaisa ba.
Da Meenal ta girma ya ƙara himma wajan kwashe dukiyar Rumaisa lokacin Abdullah ya tsaya tsayin daka akan kuɗin da ƙyar suke fita, sbd a kaso goma na dukiyar Rumaisa bai fi kaso huɗu ya rage mata ba. Babban dalilin daya sanya Rumaisa shiga tashin hankalin har ta saka aka rufe sabon companyn data buɗe. Wannan kenan.
Waje ya yi shiru cikin kuka Rumaisa ta ce "Wace kuma Meenal daga ina aka sameta shin itama yarinya ta ce?" Dr Bulama ya kasa cewa komai zufa na yanko masa sosai. A hankali Adnan ya sauke numfashi yana ƙara rungume Little a jikinsa ya ce.
"Ƴar ce wacce matar shi ta haifa masa"
"Ƴa tare da wata matar Yusuf? Da gaske ne abin da ake faɗa Ya kai Yusuf kada kayi mini ƙarya na amince da kai"
Gaba ɗaya mutanan parlourn suka zuba wa Ummi idanu cike da tausayawa ya aka ƙare da kishiyar daka sani ma balle wacce akai a bayan idanun ka, uwa uba auren cin amana anyi mata kishiya da kuɗin ta.
Cikin gunjin kuka sosai Ummi ta ce "Yusuf ka cuce ni kaci amanata, kaci amanar yarda da amincin da nayi maka na tsayin shekara da shekaru, kayi aure da dukiyata without knowing everyone Wallahi Wallahi Allah.....,"
Da sauri Abba ya ce "A'a Hajiya Rumaisa kada ayi haka, kiyi haƙuri don Allah ai ba a tabbatar auren ya yi ba" ya juya kan Adnan yana nuna shi da hannu ya ce.
"Kai kuma kada na sake jin bakinka manya na magana"
"I'm sorry Abba"
Abba ya watsa masa harara ya ce "sorry for yourself Adnan Aliyu Matawalle" Adnan yai shiru.
Abbi ya sauke numfashi yana mamakin rayuwa yadda bata da tabbas ɗin nan cikin nutsuwa ya ce.
"Yanzu Dr da gaske dai kana da wata mata bayan Rumaisa?" kan Dr a ƙasa ya ce. "Gaskiya ne ina da mata Saudat na aureta ba tare da sanin Rumaisa ba, amma ita Saudat ta san da zaman Rumaisa ina da yarinyar Meenal ita ce wacce nake cewa wani ma'aikacina bashi da lafiya"
Ya juya gaba ɗaya zai magana Ummi ta girgiza kai tana ɗaga masa hannu alamar bata buƙatar jin komai. "Ina yarinyar tawa? Kuyi haƙuri na kasa jurewa"
Murmushi kawai Abbi ya yi ya shiga faɗin "Daughter, Afra... Come here your parents are here" da gudu Afra ta fito daga cikin ɗaki kamar me jira. Tana fitowa Ummi ta miƙe tsaye hawaye na zuba daga cikin idanunta ta warewa Afra hannu muryar ta na rawa ta ce.
"Masha Allah, Allahamdulillah ta'al ya ɗiyata" Ummi ta faɗa a bayyane farin ciki ya sanya Afra kasa motsa wa ta durƙushe a wajan ta shiga rusa kuka da dukkan ƙarfinta. Ummi da kanta ta kama Afra ta rungome itama hawayen take sosai. Bulama ya kasa koda motsi sbd matsanancin kunya da kuma tsoron matakin da Ummi zata ɗauka. Shi kansa kallon Afra yake yana ji tamkar ya rungume ta.
Murmushin fuskar Abdullah ya kasa ɓoyewa kusan yafi kowa jin daɗi a yadda fuskarsa ta nuna, at least Yayar tasa zata samu nutsuwar zuciya.
Bayan komai ya lafa Abbi ya kalli Afra ya ce "Daughter inama kika ce an tsinceki" tana jikin Ummi muryar ta har lokacin rawa take ta ce
"Baba ya ce wai ko wata rana yaje daji neman wani magani aka fara harbe harbe ya labe wani waje ya daɗe a wajan kafin ya fito daga inda ya ɓoye, yana fitowa idanunsa ya sauka akan wani mafarauci wanda yake kwance anyi masa harbi wajan huɗu, daga gefen shi kuma yaga wata jaririya kwance tana kuka, hakan yasa ya ɗauki Jaririyar taho hanyar gida shi ne yaje wajan ƴan sanda amma ya ɓoye labarin kisan yace kawai tsinta ta ya yi"
Adnan ya kalleta domin ba haka ta faɗa masa ba, kamar mai karantar zuciyarsa ta ce "Wannan shi ne gaskiyar maganar Baba ya ce na ɓoye duk wanda ya tambaya na dinga faɗar abin da ya faɗa mini, sai na samu iyaye na gsky zan faɗi gaskiyar Abin"
Cike da gamsuwa Abbi ya jinjina kai ya ce.
"Babu mal wanda suke kashe mafaraucin nan sune kidnappers ɗin da muka kama cikin daji a can muka samu Abra, har wani yace mini wancan tasu ce kada na taɓa ta babu ko shakka a wajansu ta rayuwa tsayin shekaru uku har ta samu matsalar kunne, Allah mai iko Al-hakkumu bowayi gagara misali Allah mai yin Yadda ya su, ina ganin matsalar mu ta zo kusan ƙarshe"
"Gaskiya kam abin da yake ɓoye ya fito, saura nemawa Salmanun-faris auren Afra yanzu a gaban iyayenta" Abbi ya yi saurin cewa.
"A'a ba za a yi haka ba, ina da wacce zan bawa Salman Please Alhaji Aliyu"
"Shi Salman ɗin ya ce baya son Afra? Kai Salman kana son ta ko ya ya?" Ya faɗa yana kallon Salman wanda zuciyar shi ta fara harbawa da jin maganar ta Abbinsa.
Kasa cewa komai ya yi sbd Kunya kansa a ƙasa.
"Kaga ni ma kamar uba nake wajanka kada kaji komai yanzu zan amsar maka auren Afra da izinin Ubangiji"
Salman ya ɗago kai suka haɗa idanu da Afra tayi saurin rufe fuskarta a jikin Ummi. Ya ce "E, Abba ina son ta and I want marry her"
"Masha Allah Ubangiji ya sanya albarka" ya juya kan Dr Bulama wanda ya kasa cewa komai ya ce "Dr muna neman alfarmar wajanka, idan babu damuwa muna buƙatar ka yarje mana akan nemawa Salman auren Afra" kafin Dr Bulama ya yi magana Ummi ta ce.
"Sannu Alhaji, yanzu ɗiyata bata da wani Uba wanda ya shige ni, ni ce uwarta ni ce uban ta, Abdullah zai zama waliyi a gare ta"
"Kada ki yi making decision cikin fushi uba, Uba ne komai lalacewar shi"
"Don Allah kayi mini wannan alfarmar zuciyata a kusa take"
Abba ya ce "To shikenan Allah ya yi mana maganin komai sai haƙuri"
Ummi tai murmushin baƙin ciki ta ce "Afra daman taku ce ni kawai ƴar kallo ce an baku ita halak malak"
Da sauri Adnan ya miƙe tsaye tare da Aishatul-humaira da sauri Mami ta ce.
"Adnan son Ina zaka da Mamana?" Kasa yi mata magana ya yi, ya nufi ƙofar fita tari na sarƙe shi ya fara yi babu ƙaƙƙautawa jini na zuba, Little ta fara kuka tana ƙanƙame mahaifin nata da sauri Abbi ya miƙe shi da Hajiya Mama.
Mami ta karɓi Little tana faɗin "Subuhanallah sannu Son" Abba ya kasa motsa wa tausayin tilon ɗanshi ya mamaye zuciyarshi amma duk abin da ya same shi, shi ne ya kawa kansa.
"Ya Salam sannu Adnan, Salman get the car immediately, zamu koma hospital" hankalin Hajiya Mama ya tashi suka nufi asibiti da Adnan Little na ihu tana buga ƙafa zata bi ubanta sbd ta fara gane shi.
Abba ya dafe kansa da hannu bibbiyu fargaba da tsoro ya cika masa zuciya. "Daman bashi da lafiya ne? Allahu ya sauwaƙe" Mami ta cewa Ummi "Amin ga grandchild ɗin naki nata rigima" Ummi tai murmushi ko inda Dr Bulama yake bata kallo yana son cewa zai duba Adnan amma babu mai yarda da shi. Jiki a saɓole ya miƙe tare da yin waje ko zai samu peace of mind
Yana fita wayar shi tai ƙara ganin number Saudat ya sanya ya yi tsaki jin kiran ya yi yawa ya ɗauka cikin faɗa ya ce "Wai ya akai ne?" Ta cikin wayar tayi dry sosai ta ce .
"Oh calm down Dr Yusuf Garba Bulama" ya buɗe baki da kyau ya ce "Ni kike kiran sunana haka?" Ta ce "Daga lokacin dana san ka san su waye yaranka, ni ma na shiga nutsuwata kafin dani dakai duk mu rasa mu fara yawo a titi ya sanya na nemawa kai na mafita, while before i say anything zan fara da wanda zai girgiza maka lissafi, ni ce na sanya a kwashe Mini yaran da Matarka Rumaisa ta haifa, aka maye gurbin su da matattun yaran dana bada kwangila aka sato suma a ranar aka haife su, na shirya wannan plan ɗin da P.a ɗin Hajiya Rumaisa tare da alkawarin zan bashi miliyoyin kuɗi, dana tabbatar ya ɗakko yaran kuma bana da kuɗin nasa aka buge motar ɗaya ɗakko yaran babbar mota tabi da kansu, nayi mamakin yadda yaran suka kuɓuta domin an tabbatar da P.a da motar ƙonewa sukai, abu na farko daya bani tabbacin jininka na raye saƙon da aka bani na baka, ina buɗewa naga photon wata budurwa mai kama dakai, tare da wasiƙar cewa jininka ce"
Tai dariya sosai kafin ta ce "Wannan ke nan, abu na biyu tunda yaranka sun dawo nasan kawo yanzu Matarka Rumaisa ta samu labarin aurena da kai da kuma ƴata Meenal, so dole zata ɗauki matakin cin amanar da kayi mata, kafin haihuwar guzuma ɗa kwance uwa kwance na kwashi rabona dana Meenal, duk wasu file na filayenka suna wajena wanda ka saka hannu da sunan Meenal kai da duk wani abu daka san ka mallaka, dan haka kayi ta kanka ina jiran takardar saki saduwar alheri"
Kusan mutuwar tsaye Dr Bulama ya yi "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un" ya shiga faɗa tare da faɗin "Na shiga uku" yana tsaye aka fara masa messages an rufe dukkan wani acct bank ɗinsa, daga na gida zuwa na company har na asibitin wanda kuma aikin Abdullah ne ko Ummi bata sani ba ya fita zuwa baya ya shiga kiran ma'aikata.
Dr ya fito da sauri daga room Abba ya kasa haƙuri ya ce "Dr ya jikan son me ya sa me shi ina ɗana" ya buga ƙafaɗar Abba ya ce "just pray for him Ita yake buƙata" Hajiya Mama ta saki kuka ta ce "Kaga abin da kake shirin jawa Adnan? Me ya sa ba zaka taya shi neman abin da yake so ba? Gashi nan zai rasa rayuwar shi yabi matar tasa" Abba dai ya kasa magana Abbi ya ce.
"Insha Allah za a ba shi auren Afra indai a kanta ne" cikin sauri Abba ya ce.
"Kasan Allah idan har ina raye Adnan ba zai taɓa Auren Afra ba" yana faɗin haka ya nufi office ɗin Dr ya same shi zaune bayan sun gaida Dr ya ce.
"Adnan ya samu ciwon zuciya wani gefe har ya fara kumbura ayi ƙoƙarin nema masa abin da zuciyarshi ke buƙata kafin mu samu ya farfaɗo daga dugun suman da ya yi"
Abba ya ce "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un yanzu sai yaushe zai farka?" Dr ya ce "for now ba zan iya cewa komai ba, sbd jikinsa ya yi tsanani da yawa anyi wasa da zuciyarshi" da sauri Abba ya fita waya kare a kunnenshi.
Daƙiƙo na juyawa zuwa sekonni, sekonni na juyawa mintuna, mintuna na juyawa zuwa awanni, a hankali suke sauyawa zuwa yini daga yini zuwa kwana. Adnan ya ɗauki wasu kwanaki kusan arba'in a gadon asibiti ba tare daya farfaɗo ba. Har lokacin Ummi na ƙasar gidan Abbi, Bulama kullum sai ya zo Ummi bata kula shi bata nuna masa ta san Abdullah ya rufe komai nasa ba, shi ma Bulama ya kasa cewa komai. Saudat ya yi neman duniya ya rasa inda zai sameta daga ƙarshe ma wayarta baya shiga.
A hankali ya shiga buɗe idanunshi wanda sukai masa sosai da sauri ya mayar da idanun ya rufe sbd hasken da ya yi masa yawa. Slowly slowly ya ƙara trying na buɗe idanun, har ganinsa ya sauka akan drip dake maƙale a jikinsa.
Hannu ɗaya ya sanya ya dafe kansa dake masa ciwo a hankali ya zame hannun zuwa saitin zuciyarshi dake bugawa da ƙarfi yana jin ciwo sosai ta cikinta.
"Allahamdulillah son ka farka?" Hajiya Mama ta faɗa tana yin waje kiran Dr da kuma Abba da Abbi da suke waje suna tattaunawa akan a fitar da Adnan ɗin ƙasar waje.
Salman ya gyara tsaiwa ba tare da ya kalli Adnan ɗin ba, duk da cewa yana jin tausayi shi. Fararen idanunta ta ɗaga kaɗan tana kallon inda yake kwance da sauri ta ɗauke sbd wani abu mai kama da tausayi da taji..
Dr dasu Abbi suka shigo bayan Dr ya gama duba jikin ya ce.
"Allahamdulillah yanzu saura a ɗora shi akan magani" Abba ya yi murmushi yana faɗin "thank you Dr"
"Son ya jikin?" Cewar Abbi. Adnan ya buɗe idanu sosai kallon shi ya sauka kan Afra dake kusa da Salman, ya runtse idanun zuciyarshi na ƙara bugawa ya kalli Abbansa, da Hajiya Mama sai kuma Abbi. Ƙamshin da yaji a gefen shi na dama ya sanya ya juya dan ganin waye, ya zabura jiki na rawa ya miƙe zaune yana ƙara kallon wacce ke dab da shi, ya ƙara juyawa ya kalli ɗayar wacce ke kusa da Salman.
Ya mustsika idanu tare da diruwa daka bed ɗin yana tsinke ruwan hannunsa. "Abba idanuna ya samu matsala me ya sa Afra ke rabewa gida biyu ne?" Abba yai murmushi ya ce "A Lallai mukan ras namu idanun suke, mata biyu ko wacce daban" Adnan da jikinsa ke rawa sosai ya ƙara kallon wacce ke can kusa da gadon shi ko ɗago kai ba tayi ba, ya sake kallon wacce ke kusa da Salman, ya juya ya kalli Abba.
"Your wife Abra khamal Khamis" cewar Abbi Innalillahi da wani irin sauri Adnan ya nufi wajan wacce ke kusa da Salman yana zuwa Salman ya girgiza kai yana sakin murmushi ya ce. "No! Wannan is no longer your's. Is not your Abra is mine"
Adnan ya juya ganin haka ya sanya wacce ke zaune kusa da gadon ta miƙe tana tsare shi da idanu sosai alamar "Don't ever trying to come" da wani irin sauri Adnan ya nufeta gadan-gadan tamkar mahaukaci.....
Contact to subscribe
09047871750
[11/27, 12:18 PM] Abk: A gigice Adnan ya ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Allah ya sa ba kuma haukacewa zan yi ba, dan Allah ku tasheni idan bacci nake, ko dai nima mutuwa na yi ne, muka haɗu a lahira?".
Abba ya ce "Ba mutuwa kai ba, da ranka abin da kayi ka ke girba, tunda an salameka sai ka tashi mu tafi" A rikice Adnan ya nufi Abra zai damƙota, amma ta zura da gudu ta ɓuya a bayan Abba, tana kallon Adnan.
Afra ma tashi tayi ta koma kusa da 'yar uwatta, tare da riƙe hannun Abra , cike da so da ƙauna.
Adnan ya kuma nufo su, Amma Abba ya tare shi, ya ce "Ai baka isa ba, yanzu kazo mu koma gidan Major, zamu gabatar da ita ga mahaifinta da kuma mahaifiyarta, sannan ka zauna ka gaya musu abin da ka aikatawa 'yar su".
"Abba dan Allah kayi mini rai" Adnan yai maganar yana haɗa hannayensa biyu.
Abba ba sani ba sabo, ya haɗe rai ya dinga yiwa Adnan tsawa, suna fitowa daga ɗakin, Salman ya kuma rungume Abra, ji yake tamkar mafarki ne, ga Abransa a kusa da shi, abu kamar mafarki haka yake ganin faruwar abubuwan, Abransa is alive.
Wani baƙin ciki ya kishi ne ya mamaye zuciyar Adnan, zai yinƙura yai wajen su Salman Abba ya ce "Wallahi kai mini wani hauka, sai na ci mutuncin ka a wurin nan, wuce mu tafi" Duk in da Abra ta waiwaya 'yan uwane masoya ke ta farincikin sake ganinta.
Suna zuwa gida, suka tarar da Mami, ta na ta rusawa Ammi kuka, tana cewa akan me Major ya ɓoye mata Abra tana raye, ya jefa zuciyarta cikin ƙunci.
Ai Abra ba tayi sallama ba, ta tafi da gudu, ta danne Mami tana wani irin kuka kamar wadda ranta zai fita.
Kasa magana suka yi, daga Mami har Abra, tamkar Mami zata mayar da Abra cikinta,
falo ya cika ga Ammi ga Abba da mahaifin Abbi, ga su Inna da Yaya Musa, gida sai koke koke ake, Ammi ta tsare Abba da son jin dalilin da ya sanya, suka aikata musu haka a kan Abra.
A hankali idon Abra ya sauka a kan Little da ke hannun Salima, Abra ta zubawa Little ido.
Ammi ta ce "Kawo mata 'yar ta ta ganta, taji ɗumin 'yar ta" girgiza kai Abra tayi ta ce "Ni ba 'ya ta ba ce"
Gaba ɗaya suka kalleta, Ammi ta ce "wane irin abu ne haka kuma?".
"Ammi na barwa Adnan 'yar sa, ina son su fita daga rayuwata gaba ɗaya da shi da ita" tai maganar tana kuka.
"Baki da hankali ne? 'yar ta ki kike cewa kin barwa babanta?".
"Eh Ammi, nima haka na rayu ba iyayena, har gara ita tana da uba"
Abbai zai tsawataraa Abra, amma Abba ya ce "Ƙyaleta Major, tayi mini daidai, amma muna dakon jiran wani albishir da zamu yi miki ne, kan mu fayyace musu yadda aka yi mu kai musu haka ba su sani ba".