Yusuf ne yayi saurin ɗagowa ya kalli Hanne, Yusuf yace "Subhanallah, garin yaya kika ɓarar da Abinci?"
Widad kam ko motsawa ba tayi ba balle ta tashi daga jikin Yusuf.
Cikin rawar jiki Hanne tace "Tuntuɓe nayi shine ya zube, bari in samo in kwashe"
Ta juya ta fita da sauri, tana fita tsakar gida Gwaggo ta kalleta tace "ke meye haka, ba dai Abincin da nace ki kaiwa mara lafiyan kika zubar ba?"
Cikin inda inda tace "Amm.. Mm... Tuntuɓe nayi shine ya zube"
A fusace Gwaggo tace "kekam kamar mara hankali wani lokacin, kije ki kai Abinci kawai seki zubar dan shirme"
Hanne ba tace komai ba ta tafi ta ɗau tsintsiya da abun kwashe shara ta tafi gyara inda ta ɓata musu, cike da zullumin me zata je ta sake tararwa.
Gwaggo tace "Hindu tashi ki duba sauran kunu a ɗakina ki kai musu ba'a bar mara lafiya da Yunwa ba"
Sukam Maƙota da suka rako Yusuf ne suka dinga jinjina rashin ta ido irin na Widad, a gabansu ba kunya taje ta rungume mijinta.
Wani da'ake kira da Lado me Jakai yace "to ai kunsan su ba namu ne na nan ba, jama'ar birni ne baku ga matar tasa bama kamar balarabiya, su sun saba irin wannan bakomai ne ba"
Ɗayan da'ake cewa Liti yace "Aradu amma ai kunya wani abuce, tunda nasan duk abu Hausawa ne"
Lado yace "ku kuga haka, su a gurinsu ba wani abun bane ba"
Liti yace "Sumi sumi dashi haka, Amma ta rungume shi ya wani basar abunsa, memakon ma ya ɗanyi mata tsawa ya hanata"
Wani me shekaru a cikin su yace "Kai waye ya gaya maka suna hantarar matansu, lallaɓasu suke yi, ni wallahi birgeni ma suka yi"
Kwashewa sukayi da Dariya gaba ɗayansu, harda ƙyaƙyacewa.
Hindu tayi Sallama, da kofin kunu tace "gashi inji Gwaggo, tace dan Allah kuyi haƙuri Hanne ta zubar da Abincin"
Yusuf yace "bakomai Hindatu hakanma mungode"
Hindu tace "Amarya yau za'a ci Abinci, tunda me gidan ya dawo"
Yusuf yace "Ai naga alama bata cin Abinci ta rame sosai"
Hindu tace "bata ci, Gwaggo taita fama da ita sedai tayi ta kuka, ko bacci bata iyayi"
Widad ta yatsine baki tace "Akanme zanƙi bacci, in kasa cin Abinci toni ƙiba ma nayi, ci nake in ƙoshi"
Hindu tayi dariya tace "bari a kirawo Gwaggo a tambaye ta"
Sukayi dariya, Hindu tayi waje, Yusuf ya kalli Widad yace "bani kunun insha dan inajin Yunwa"
Widad ta miƙe ta ɗakko kofin kunu, tazo ta zauna tana bawa Yusuf, Saleh ne yayi Sallama ya shigo ɗakinsu.
Kallon Widad yayi yai murmushi yace "Allah me iko, Allah ba yadda be iyaba, wai Gimbiyar Daula ce ke bawa direbanta Abinci a baki, abun da mamaki"
Banza tayi masa ta cigaba da bawa Yusuf kunu, Yusuf yace "Saleh ƙaraso ka zauna mana"
Saleh yace "to bari in ƙaraso, ina fatan hankalinki ya kwanta ban gudu dashi ba, gashi na dawo miki da shi, kuma Alhamdilillah jikinsa yayi kyau"
Shiru ta kuma yi bata ce komai ba, Yusuf yace "Ana magana fa"
Widad tace "me zance?"
Saleh yace "base kince komai ba kam, Malaria me ƙarfi da typhoid ne suka kama Yusuf, sannan ulcer na damunsa, ga rashin sabo da wasu abubuwa da yake yi, wanda be saba ba, dan haka shine damuwa gajiya da pressure ga kuma zazzaɓi gaba ɗaya suka dameshi, amma Alhamdilillah mun samu an ceto miki shi, yasamu sauƙi Alhamdilillah, na samo Net guda ɗaya, yace min ba guri ɗaya muke kwana ba, dan haka ga guda biyu nan ke ɗaya shi ɗaya, likita yace 'ya dena zama da yunwa, ya dena barin sauro yana cizonsa, sannan a kula ya shanye magungunansa"
Widad tace "Aishi zaka gayawa bani ba, tunda ze iya kula da kansa ko"
Mamkine ya kama Saleh, ya tuna yadda ta dinga kuka ranar da zasu tafi da Yusuf, amma yanzu tana faɗar wata magana daban, shi kansa Yusuf beji daɗin hakan ba, amma ya basar.
Saleh yace "koma dai menene, Zan zauna zuwa jibi in Allah ya kaimu zan koma, nayi muku siyayya wajen gobe in Allah ya kaimu za'a kawo muku"
Yusuf yace "Mungode sosai da ɗawainiyar da kake mana, Allah ya saka da alkhairi, Allah ya biya ka"
Saleh yace "Ameen"
Ita kuwa madigar, miƙewa tayi tai waje abunta, ba tare da ta sake tanka musu ba.
Amal na kwance akan gadonta tayi shiru sosai take tunani, tayi zurfi sosai a tunani, Mummy ta shigo ɗaki Amal ta tarar a kwance tayi shiru tana ta tunani"
Mummy tace "ke meye haka? Tunanin me kike yi? "
Amal ta ɗan tura baki tace "lafiya ƙalau Mummy"
"Amma kika zauna kika yi shiru haka? Kina ƙarama dake kike tunani haka"
"Mummy ina ɗan zancen zuci ne kawai"
"to idan waccan uwar baccin ta tashi ki gaya mata zan fita, ni na rasa gane kan wannan baccin banzan dat take yi sekace wata kasa"
Ita dai Amal bata gayawa Mummy abunda Ramlan keyi ba.
Bayan fitar Mummy kwanciya Amal ta sake yi tana cigaba da tunani, kuma ba tunanin kowa take ba face Yusuf, tun tana dannewa yanzu abu yavfara gagara, bata iya ɓoyewa sam, Bata iya cin Abinci ba tayi zaton ƙaunar Yusuf haka tayi mat wannan mugun kamun ba, gaba ɗaya yanzu haushin samarin ta take ji, gani take duk cikinsu Yusuf yafi su komai dukda Kasancewarsa talaka, amma ya haɗu gashi nutsatse babu Hayaniya a tare da shi, ji tagi inama a sako Yusuf a riƙe Widad, dama itake hana ta rawar gaban hantsi, dan ta rasa wace irin Alaƙace ke tsakanin su, Widad bata da yadda kamar me, bata yadda kowa ya raɓe ta ba, amma ta yadda da Yusuf ya shiga jikinta sosai da sosai, Yusuf yasan abubuwan dasu da suke zaune da ita basu sani ba.
"Ke Amal! Tun ɗazu nake miki magana amma se kace wata kurma, kinmin shiru"
Firgigit Amal ta kalli Ramlah, tayi ajiyar zuciya tace "Meye nayi min ihu kuma?"
"na dole inyi miki ihu ba, tun ɗazu nake kanki ina magana amma kinyi shiru"
Amal ta miƙe zaune ta kalli Ramlah tace "ban san kin shigo abane, dana san kin shigo ai zanyi responding"
"Wai nikam wane irin tunani haka kike yi?"
"Ramlah tunanin komai ma inayi, Abubuwa da yawa sun dameni, Amma Ramlah jiya fa maye kike kika dawo"
"Maye kuma?"
"Eh mana, wallahi jiya a buge kika dawo gidan nan, Mummy kuma a ƙule take dake, fitar da kikayi da Fahad"
Ramlah ta ɗan ɓata rai tace "ba wani maye da nake, na gaji ne kawai, sannan me Fahad ɗin kuma yayi?"
Amal tace "Eh to, kin san sunyi faɗa da ɗan uwanta akan belin Yaya Anwar, shiyasa"
"to kuma shine seya shafi Fahad, laifin meyayi? Kuma shima bakiga yadda yake ƙoƙari akan lamarin ba, amma kin san halin babansu da kafiya"
Amal tace "wani tabacci kike da shi na yana ƙoƙarin nan, nifa kallon Fahad ɗin nan kawai nake, bakin maƙaryata ne dashi"
Ramlah tace "zaki fara ko? Karki kusakura kici masa mutunci"
Amal tace "ke niba wannan ba, nifa naji tana cewa za'ayi uwar watsi idan ba'a fito mata da Yaya Anwar ba, karta yi wani abu daza'a zo ana da nasani daga baya"
Ramlah tace "kuma fa hakane, kin san bata iya fushi ba, bari inje ɗakinta in sameta"
Amal tace "to ai ta fita"
"ta tafi ina?"
"Nima ban sani ba, ni dai tacemin zata fita"
Ramlah tace "Shikenan, bari inje kitchen in samu ɗan abunda zanci, da yamma zanje gurin wani birthday na 'yar gidan IG na ƙasa, na tura a ɗakkomin wata sabuwar motar megidan nan daga kamfani, da ita zanje, kin san gurine na manyan yara fa"
Amal tace "Mhmm yakamata kam"
"waini meke damunki ne Amal, bakya walwala fa"
"Ramlah wace walwala zanyi? Yaya Anwar a rufe, hankalin Mummy yaƙi kwanciya, ga uwa uba wallahi Ramlah Ji nake kamar inyi me saboda rashin Yusuf, na shiga damuwa wallahi ko bacci na kwanta yanzu mafarkinsa nake yi, na rasa inda zan saka raina, tun ina iya dannewa yanzu na kasa "
Wani uban dogon tsaki Ramlah taja tace " Aikin banza, shine zaki kashe kanki saboda wannan jakin"
"Karki sake kiransa da Jaki, Inda wanda za'a kira Jaki to tabbas Fahad ne, dan kunnuwansa ma irin na jakaine ga ƙaryar tsiya".
Haka abun nasa ya koma faɗa, ƙarshe sukayi baran Baran.
Widad ta fita tsakar gida, ta ƙarasa inda Gwaggo take tana murmushi, Hari tace "ohh ni Harira, se wangale baki kike miji ya dawo, kin ware"
Widad tace "Toke ya kika gani? A garin nan banda Allah se shi na sani, idan lafiyarsa ta taɓu akwai damuwa sosai"
Gwaggo tace "ƙyaleta Amarya, zolayarki take"
Widad tace "Mama, dan Allah abun nan na ɗakinki sunmin kyau sosai"
Gwaggo tace "me fa?"
Widad tace "kwanukan nan da kika shirya a ɗakinki, sunyi kyau sosai fa"
Gwaggo tayi murmushi tace "Widad kenan, kayan Su Samira da fanteka kenan, mu dasu mukeyin adon ɗaki"
Widad tace "Masha Allah, gaskiya sunmin kyau sosai Mama"
Can ta hango bulugari, a gefen Gwaggo zata kaɗa miya.
Widad tace "ya sunan wannan Mama? Wanda kike juya miya dashi"
Gwaggo tace "Bulugari kenan, dashi muke kaɗa miya"
"Mama wannan tunkunyar naganta baƙa sosai"
Gwaggo tayi murmushi tace "wannan itace Talle Amarya, tukunya ce ta ƙasa, muna girki a cikinta, miya tafi zaƙi da daɗi Sosai"
Widad tayi murmushi tace "taɓ Mama duk ban san wannan abubuwan ba, ban taɓa ganinsu ba"
Gwaggo tace "hakane dama, tunda ba kuyi rayuwar karkara ba ba lallai ki sansu ba, bari inje ɗaki in ɗakko abun kaɗi"
Gwaggo ta tashi ta tafi, tana tafiya
Hanne tayi tsaki tace "Aikin banza mutum ya zauna yaita ƙarya, mtseww aikin banza dana wofi, wai bata san bulugari da fanteka ba"
Widad ko waigawa ba tayi ba, tai shiru abunta, Hari tace "wato Wudas kinfi jin tsoron Hanne, ta gayamiki duk abunda data ga dama, kiyi ƙus amma da nice da tuni kim hayayyaƙomin"
Wani irin kallo Widad tayi wa Hari, nan take cikin Hari ya kaɗa, ganin wani irin kallo da Widad tayi mata, se taga kamar ta canza gaba ɗaya daga kamaninta, ba shiri Hari taja bakinta ta tsuke.
Saleh ya kalli Yusuf yace "Sannu Yusuf, gaskiya kana fama, yanzu haka kuke zaune? Tana maka wannan gadarar da jin kan, bayan taimakonta kake"
Yusuf yayi murmushi yace "lafiya ƙalau muke zaune da ita, duk wannan abubuwan bata Yimin, ƙalau muke zaune Alhamdilillah"
Saleh yace "kaga nifa bana son wannan kawaicin naka, kalli yadda take wani bintsire bintsire, tana cin magani, na zata tuni ta dena wannan halin nata?"
Yusuf yace "Kai da ita ta baka amsar wannan tambayar, Amma nan ma shigo ka tarar tana bani Abinci ai"
Saleh yace "kuma fa hakane, lallai kai ɗan baiwa ne kuma na musamman Yusuf, wannan yarinyar me Azabar taurin kai, amma take kula da kai haka, ta yadda ka shiga jikimta gaskiya abun da mamaki, kayi namijin ƙoƙari fa"
Yusuf yayi murmushi yace "Haka lamarin ubangiji yake, yanzu ya jikin mahaifinta?"
Saleh yayi shiru da alama jikinsa yayi sanyi yace "labari mara daɗi Yusuf, yanzu ma badan ka tambaya ba bazan gaya maka ba"
A rikice Yusuf yace "Subhanallah, meyafaru kuma?"
Saleh ya gyara zama ya waiga yaji babu motsin kowa sannan ya waigo ya kalli Yusuf yace "An sace Daula akan gadon Asibiti"
Dafe ƙirji Yusuf yayi yace "Innalillahi wa inna ialaihi raji'un, kamar yaya?"
Saleh yace "kaima dai ka tambaya, abun kamar almara, Kasan tunda yake rashin lafiya Anwar ne kawai yake sintirin jinyarsa, matarsa da sauran yaran ba ruwansu dashi, daga ya ɗan fito daga ɗakin, ya koma aka nemi Daula aka rasa, yanzu haka an kama Anwar da me Asibitin ana tuhumarsu, yau sati uku kenan sun tsare "
Dafe kai Yusuf yayi ya shiga murza goshi, wannan wane irin bala'i ne? Duk yadda yake zaton lamarin ya wuce tunaninsa, wane irin tashin hankali ne haka?
Saleh yace " ka kwantar da hankslinka fa, ban gaya maka dan ka ɗaga hankalinka ba, sedai ka tayata da Addu'a, sannan karka bari ta sani"
Yusuf yace "kuma ana bincike akan lamarin, ba'a gano inda yake ba?"
Saleh yace "kai dai ayi sha'ani, har yanzu babu Labari"
"Amma naji kamar kace kasan suwaye ke wannan abubuwan"
Saleh yayi murmushi yace "kaifa jami'in tsarone, kuma kai aka bawa wannan aikin na binciken, zuwa yanzu ai nasan ka samu haske akan binciken da kayi"
Yusuf yace "kamar yaya kenan?"
"Kana nufin baka gane me nake nufi ba? Ai shikenan mu bar zancen, kar tazo ta same mu muna maganar"
Yusuf yace "Ya Ummana kuwa Saleh?"
"tana nan lafiya, Suleiman yana kula maka da ita"
"Amma Saleh, Akwai wani abokin aikina Abbas, babban Abokina nane, yana Ibadan akan aiki, ko Suleiman yayi maka maganrsa, nasan idan yasan ina nan Abbas ze shiga damuwa ina da tabbacim se yazo nan"
Ƙura masa ido Saleh yayi, ya ɗanyi shiru sannan yace "gaskiya ba muyi maganar wani da shi ba, kai dai kunci gaba da haƙuri, komai ze wuce kamar ba'ayi ba Insha Allah"
Yusuf yace "Allah yasa"
Saleh yace "bari in ɗan fita waje, in zaga gari"
Yusuf yace "bari in bika bana son zaman gidan ne, gara in fita in ɗan tattaka"
Saleh yace "kar kasa matarka tamin tijara fa"
Yusuf yai murmushi yace "bakomai"
Suka fito shida Yusuf, Can Saleh ya hango Widad a kusa da Gwaggo suna hira, Widad ta maida hankalinta sosai akan Abunda Gwaggon take yi.
Saleh yace "iko se Allah, da a mafarki aka haskomin wannan abun ze faru, zance sharrin mafarki ne"
Widad ta ɗaga ido ta hango Yusuf, ya fito da alama fita za suyi, Widad tace "ya dai, naga ka fito, ina zaka haka?"
"You leave alone in the room, am so boring, Saleh is going out, so i feel like to follow him"
Widad tace "gaskiya ban yadda ba, ka koma ka huta in kuma ka faɗi fa?".
"Bazan faɗi ba insha Allah, ina son in ga gari ne kawai"
Widad tace "Shikenan, kar kayi nisa dai"
"As you wish your majesty"
Saleh jinjina kai kawai yayi, yayin da Yusuf yake jin wani irin matsanancin tausayinta, ko ya zataji idan taji labarin mahaifinta ya ɓata shima?.
Haka yabi Saleh suka fice.
A harabar gidan su Nurat kuwa, Nurat ce zaune a ɗaya daga fararen kujerun dake harabar gidan, ita da Barrister Khalil cousin ɗinta, teburin gabansu ɗauke da lemu ka da kuma kofunan glass.
Barrister Khalil yace "kince kina son ganina, gashi nazo amma kin kasa cemin komai"
"Brother, aini sam ban san ta ina zan fara maka bama, na rasa me ya kamata ince maka"
"Ki nutsu, ki gayamin komai a hankali, an fahimceki Insha Allah"
Ta ɗanyi ajiyar zuciya sannan tace "brother, game da maganar da mukayi da kaine na belin Anwar" Se kuma tayi shiru.
Khalil yace "Mhmm ina jinki, gayamin ke nake sauraro"
"Barrister, kai ɗan uwana ne, kona ɓoyewa kowa wani abun, kai bazan ɓoye maka ba, amma ina son maganar ta tsaya iya nida kai, ko Kasan akwai hannun mahaifina a cikin abubuwan da suke faruwa da Alhaji Daula?"
A hankali Khalil ya zare glashin fuskarsa, ya kalle ta yace " kamar yaya? Ban gane me kike nufi ba"
'Nasan abun ze baka mamaki, amma kasan Alhaji Daula me silar ɓacin siyasar Mahaifina? "
"Eh na sani, nasan da wannan"
"Mahaifina yayi alwashin ko ze mutu se ya rama abunda Alhaji Daula yayi masa, ya haɗa kai da wasu manyan abokan kasuwancin Alhaji Daula, suna ƙoƙarin ganin bayansa, zancen da nake maka, da saninsa aka sace 'yar gidan Daula da direbanta"
Hankici ya ɗakko a aljihunsa ya share gumin fuskarsa yace "wani tabbaci kike dashi, akan wannan maganar da kike yi"
"Brother, nikaɗai ce sheda, se Mummy amma kasan halin Mummy da tsoro, ba zata taɓa bamu goyon baya ba, yanzun kaima ma gaya maka ne, saboda yadda abun ke cin zuciyata, na rasa wa zan gayawa inji daɗi a raina"
Khalil yayi shiru sannan yace "am sorry to say, Nurat mahaifinki gaba ɗayansa zuciyarsa babu Allah a cikinta, yanzu muddin ya gano mum sam me yake yi to tabbas ze ɗau mataki a kanmj, nasan shi ba tun yanzu ba"
"Nasani brother, nikaina tunda naje na duba Daula a Asibiti ya samun takunkumi, ya hanani fita, rannan dana fita baka ga yadda ya shaƙeni ba kamar ze kasheni"
Khalil ya jinjina kai yace "yanzu Addu'a zamu ci gaba dayi, mahaifinki yana da goyon bayan manya sosai, dan haka babu wanda ze tsaya ya ɗau mataki, sedai muyi ta addu'a"
Nurat tace "hakane Brother, but am so much disturbed wallahi"
"Kakri damu, ki kwantar da hankalinki, Dukda haka zan duba inga me zan iyayi akai"
"Shikenan nagode sosai brother, Allah ya ƙara ɗaukaka"
"Ameen ya Allah karki damu kinji, ki kwantar da hankalinki, komai zezo da sauƙi"
Haka sukka cigaba da tattaunawa.
"Alhaji Musa wai yanzu duk kuna kallo haka ɗana ze cigaba da zama a prison? Ba zakuyi komai akai ba? Na gaji da yawon da kukemin da hankali fa"
Alhaji Musa yace "Ni yanzu me kike son inyine? Nifa bani na sa aka kama ɗanki ba, me kike so inyi?"
"Idan ba ku kuka sa aka kamashi ba, amma kuna da ƙarfin da zaku sa a sakarmin shi aiko? Wane irin abune haka, se zarya nake a tsakanin ku, amma kowa da kalar rainin hankalin daze mun"
"Kinga saurara, ni babu abunda zan iyayi akan wannan al'amarin, wannan babban case ne da yake buƙatar bincike, idan bashi da laifi zasu sake shi fa"
Hajiya Halima tace "Shikenan nagode sosai da abunda kukayi min, wato na gama yi muku amfani, zaku watsamin ƙasa a ido, zaku ga abunda zanyi"
Ta juya fuuu tayi waje kamar zata tashi sama, tana tafe tana banbami, ofishin Bulama ta tafi, ta tarar yana shirin fita, ya kalle ta yace "Halima lafiya kuwa?"
"karka ƙara tambaya ta ko lafiya, lafiyar kenan kana nan hankalinka kwance, ni kuma nawa a tashe ko baccin kirki bana samu, na zama kamar mahaukaciya, ɗana yana can a tsare, kun nunamin halin ko in kula, kun nuna baku damu da halin da nake ciki ba"
Bulama yace "Nikam Halima kina bani mamaki, ɗanki fa ɗana ne, nima nawa hankalin ba'a kwance yake ba, muna iya ƙoƙarin mu, amma abunda ake gayamana shine, ana zargin da sa hannun Anwar a wannan abu daya faru, kuma duniya ta kasa kunne taji wani mataki za'a ɗauka, me kike tsammani idan aka ji da sa hannuna aka saki Anwar? "
" Kaga sauraramin dan Allah, bana son maganar banza data wofi, na sani ka sani Anwar baze iya aikata laifin da ake tuhumarsa ba"
"A'a karki shedeshi, ba'a shedar ɗa a zamanin nan"
"Bulama, na gama magana da kai, zanje inyi abunda ya dace kawai"
Bulama yace "abunda ya dace kamar yaya?"
"Ka zuba ido zaka gani, bar ganin kai ɗan uwanane zan iya yin komai akan ɗana, na gaya maka"
Bulama yace "hmm kibi a sannu dai, kin san ido ya fara dawowa kanki yadda kike wadaƙa da wasu daga cikin kadarorin mijinki? Mutane sun san me kike aikatawa, ki sani tsalle ɗaya ke kai mutum rijiya, amma se yayi dubu be fito ba"
Tsaki tayi, ta ɗau mukullin motarta tace "wannan kuma kai ta shafa bani ba, nasan abunda nakeyi"
Tai waje abunta, tana fita Bulama ya ɗau waya, ya danna yasa a kunnensa yayi shiru, can kuma yace "Yawwa kana jina da kyau, ina son ku ƙara tsananta tsaro da sa ido akan yaron nan Anwar, under no circumstances zaku bada belinsa, ku matsa se ya faɗi inda Daula yake, dan uwarsa ba abunda ba zata iya ba"
Daga cam ɓangaren yace "Ok sir an gama Insha Allah"
Bayan barin Hajiya Halima Office ɗin Alhaji Musa, su Alhaji Haruna suka dira, dukda haushinsu da Musa yake ji, amma ya maze ya sakar musu fuska yace "kun san yanzun nan wannan mahaukaciyar ta bar gurin nan"
Alhaji Haruna yace "wa kenan?"
"Hajiya Halima mana, tazo nan tana ta banbami, wai munƙi saka baki a sakar mata ɗa"
Alhaji Munir yace "ƙyale wannan mahaukaciyar, ni wata shawara nazo mana da ita"
Suka tattara masa hankalinsu, suna saurarensa "Abunda nake gani shine, mu samu lauyoyin Daula, mu siye su, su saka hannu su fitar mana da wasu daga kadororinsa, a sasu a kasuwa a karya su, sannan ayi takaddun ƙarya, muce muna binsa zunzurtun bashi"
Alhaji Haruna yace "kayi magana mekyau, sedai abunda ka manta shine, lawayoyinsa basu san kan dukiyarsa kamar yadda wannan koɗaɗiyar 'yar ta sani ba, ta san komai tasan inda komai yake"
Alhaji Munir yace "to tunda yanzu ba ita babu ubanta aise muyi yadda zamuyi mu kwashi rabonmu, ko so kuke se wannan mahaukaciyar matar tasa ta ƙarar da komai ita da' ya'yanta? A ɓoye fa se saida kadarorinsa sukeyi, haka zamu zauna mu zuba ido."
Alhaji Musa ya nisa yace "duk naji ta bakin ku, kuma kowa yazo da magana me kyau, zamu jarraba lawyoyin suma, danni yanzu kuɗin tsayawa takara nake nema"
Kallonsa sukayi gaba ɗaya sukace "kamar ya tsayawa takara?"
"kamar yadda na gaya muku, bazan zauna bani ga tsuntsu bani da tarko ba"
Alhaji Haruna yace "hala ka manta da baƙin fentin da kake da shi, a dalilin Daula?"
"ina fa na manta, sedai a ƙasar nan indai kana da kuɗi ba abunda baze yuwu ba"
"Amma baka ganin hakan, ya saɓa da Yarjejeniyar mu, idan kayi haka kamar ka zame daga cikinmu ne, kuma me zaka cewa Bukar?"
"Bukar ubanane, ko haifata yayi? Ba gudu ba ja da baya, ina tare da ku amma tabbas zanyi takara"
Gaba ɗaya Yusuf ya fara jin kunyar mutanen da yake ja